Ta na tsaye ta zuro kanta ta na kallon masu wucewa ta layinsu da gefen layin,duk Wanda zai shige sai ta d'aga masa Hannu tana washe baki,duk kuma lokacin da ta d'aga hannun sai an hango hammatar ta amma ko a jikinta.
Ta na nan tsaye wani Mahaukaci ya b'ullo ta layinsu,a al'adar wannan Mahaukaci unguwa unguwa yake bi da zabgegiyar bulalarsa yana b'oyeta a malum malum d'in jikinsa,babu abin da yake nema sai mata masu lek'e,duk macen da ya kama kuwa kan ta ankara ya fito da bulalarsa ya jik'a mata aiki,kamar yana da masaniyar zai tadda Saratu sai gashi Allah ya jefoshi BAHAGON LAYI.Duk da wasu sunce aljanun kansa ne ke sanar da shi guraren da zai samu mata masu lek'e.
Yana yankowa layin da Saratu ya fara yin arangama ta na mak'e a soro ta na lek'e,gadan gadan ya nufota ita kam bata lura da shi ba hankalinta yana d'aya gefen ta na kallon wasu samari da suke zaune suna lido,yana zuwa dab da ita ya shammaceta ya fiddo bulalar ya d'aga ya zumbud'a mata,cikin d'aukewar numfashin Azaba ta zabura ta juyo ta na kallonsa,tana niyyar magana taji ya kuma sauke mata wata a kafad'arta,inalillahi wainna ilaihir raji'un,ai da Saratu ta kurma wani uban ihu jin zai sauke mata kafad'a tayi tsalle ta fad'a gidanta a guje ta na tumami,gabad'aya ta manta bata kulle k'ofar ba,shi kuwa Mahaukacin ganin k'ofa a bud'e kawai sai ya bita cikin gidan, ya tarar da ita ta na zagaye tsakar gida ta na ihu da Sosa kafad'a,ba k'aramar razana tayi ba da ta ganshi a gabanta,ta d'ora Hannu a ka ta saki wani gigitacen ihu da ya zabura wannan mahaukacin Yayi kanta ya soma tafkarta,ko ta ina kai mata duka yake har Saratu ta fad'i k'asa zaninta ya zame daga ita sai D'an diras,birgima kawai take yi yana jibgarta da bulalar hannunsa ta na ihu.
Ihunta ne ya cika layin da k'arar ihunsu Harira da ke tasowa,wad'anda suka yi matuk'ar jigata saboda azabar duka da tiyagas,fuskokinsu sun motse kamar na b'era.
Da hanzari wad'annan samarin masu yin lido suka taso kusan su shida suka nufi gidan Saratu saboda sun ga shigar mahaukacin gidan,da k'yaleshi za su yi ya yagalgalata saboda ta zauna lek'e,domin takaicinsu duk d'agowar da za su yi sai su ga ta kafesu da idanu ko Riga babu a jikinta,to jin ihunta da Neman taimako shiyasa suka taso dan kar mahaukacin ya kasheta.
Suna niyyar shiga gidan sai ga Salisu ya b'ullo layin,Yayi mantuwar wasu kud'i ya dawo d'auka,tunda ya shigo layin kuma yake jin muryar Saratu na ihu,ga kuma mutane a k'ofar gidan,da hanzari ya k'ara so Dan ya zaci gobara ce ta tashi a gidan ta rutsa da Saratun,a gigice yake tambayar samarin abin da yake faruwa,nan kuwa d'aya daga cikinsu ya sanar da shi komai,tun daga zamansu a gefen layin suna yin lido har fitowar Saratu soro ta fara lek'e,har zuwan Mahaukacin layin da jibgar Saratu da ya fara har ta gudu ya bita cikin gidan.
Ya na gama saurara suka afka cikin gidan shi da samarin,Salisu Yayi mummunan gani,matarsa kwance tumb'ur daga ita sai wando wani k'ato na jibgarta ta na birgima da ihu,kaf halittunta a waje,tayi dama dama da kashi da fitsarin da ta saki don azaba,jikinta Yayi bird'in bird'in na duka da bulala,Salisu ya d'ora Hannu a ka saboda tsananin bak'inciki,shi kuwa da me zai kwatanta wannan b'acin ran a duniya?su Kansu samarin kauda kai suka yi cikin tsananin kunya.
Saratu kam ihu take da Neman ceto, da k'yar wad'annan samarin suka janye Mahaukacin suka fita da shi waje sai nishi yake,Saratu ta na jin ta daina jin duka a jikinta tayi wuf ta mik'e tana Neman gurin buya.
Salisu yana ganin ta mik'e shi ma yayi wuf ya mik'e hawaye na zubo masa na tsantsar takaici da bak'inciki,ji yake tamkar ya shak'e Saratu ya rabata da duniyar saboda muguwar tsanarta da yaji ta mamaye k'irjinsa,a gigice take gabad'anta,duka ya zautar da hankali ta, shiyasa ta nufo Salisu jikinta na rawa da makerkyata tana zunduma ihu tana shirin b'uya a bayansa,surutai kawai take zubowa cike da gigita,fad'i take.
"Wayyo Salisu na shiga uku na lalace,Dan Allah ka b'oyeni kar wannan mahaukacin ya dawo ya tarfa ni,innalillahi wa inna ilaihir raji'una yau naga bala'in duniya da na lahira,hasbunallahu wa ni'imal wakilu yau an min bugun sakwarar yarabawa,subuhannahi talatin da uku ,wal hamdu lillahi saba'in da takwas,wal lahu akubar tamanin da tara,wa subhanallahi bukratan wa asilan miliyan bakwai,la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalimina,zalimina mahaukaci,zalimina mahaukaci,zalimina mahaukaci"
Haka Saratu ta dinga subad'ad'i tana dirango nonuwanta na rawa da tsalle tana nufar Salisu da takaici ya kusa shek'ashi lahira a tsaye,shi kansa ya san dukan Mahaukacin nan ya gigita Saratu ba kad'an ba,kamar wadda ta zauce haka take sakin maganganu tana kuka da tsalle.
Dab da zata iso wajensa ya d'aga Hannu yana dakatar da ita,cak! Ta tsaya jikinta na mugun mazari bakinta na rawa tace.
"To ,to ,to,na tsaya Malam Salisu,Alaramma bafaden Malam Munzali me almajirai,An gaisheka titib'iri masomin gardi,takawarka Lafiya na Saratu k'olon Gandujiyya,gaba salamun baya salamun jijjib'i na Saratu alherin Allah.......
" Ke! za ki nutsu ki min shiru ko sai nazo nan na k'ara cin kutumar Ubanki?
Salisu ya ambata cikin zazzare ido yana nuna ta da Hannu,sannan ya cigaba da magana a fusace yana kallon yadda take Sosa jikinta da nonuwanta kamar sabuwar kamun Hauka.
"Da alamun wannan Mahaukacin da ya dakeki ya goga miki Hauka kema,Dan Haka ni nan me hankali ne ba zan iya zama da Mahaukaciya Y'ar macukule ba,ki tsaya nan na cillo miki Riga da hijabi kisa ki ficemin daga gida na sakeki Saratu asararriya,ba don ina jin kunyar Malam ba ma da a haka yadda kike tsirara tunb'ur zan koraki,kinga za a tabbatar da kin kamu da haukan na ainihi,Jaka ,jahila, sak'andama ,wadda bata san ciwon kanta ba"
Yana fad'in hakan ya fad'a d'aki ya d'akko mata doguwar Riga da hijabi ya cillo mata,tana durk'ushe tana ta surutai marasa kai da gindi tana ihu,da yaga zata b'ata masa lokaci sai ya fad'a wani d'aki da yake ajiyar kayan gonarsa,daman duk damina yana zuwa gonarsa yayi noma,yayi dira dira idanuwansa suka fad'a kan gatari da fatanya,da hanzari ya kwaso su a Hannu ya fito ya tadda ita a kwance sai birgima take ta na ihu,ya daka mata muguwar tsawa,ta zabura ta mik'e tana kallonsa,ya d'aga gatarin yana nunata yace.
"Kin d'ibi kayanki kinsa kin fita ko sai na sassaraki?na rantse da sarkin da ke busamin numfashi idan baki b'acemin da gani ba yadda ake sara ice a faskarashi haka zan sassaraki na faskaraki na k'uk'k'ula da wayar kebir,k'ullin ashirin k'ullin goma a zo a siya ayi makamashin wuta dake tun a duniya,kafin aje lahira namanki ya zama abincin wutar jahan.......
Wuf!ta mik'e kafin ya k'arasa ta yayimi rigarta ta zumbula,mamakin Salisu take yi daman D'an daba ne,ko dai wiwi da sholisho da ermo ya zuzzuk'a?
Yana ganin ta zura hijabi ya kai mata fafara da fatanya,da gudu ta fita ya bita a baya ya nayi mata rakiya har bakin layin,samarin nan da ke waje bayan sun kad'a Mahaukacin suna zaune,nan da nan suka mik'e ganin Salisu ya biyo Saratu a guje,kawai sai suka kama dariya da tsalle suna ihun cewa.
" Rakata Salisu,Rakata Salisu,Rakata Salisu"
Salisu bai juyo ba sai da ya rakata har k'arshen layin sannan ya juyo cikin takaici ya koma Gidan,ya zauna ya zabga tagumi hawaye na sintiri a idanuwansa,a hankali ya zaro wayarsa ya danna lambar Malam Munzali mahaifin Saratu,Malam yana jin muryar Salisu ya tabbatar ba lafiya ba,aikuwa nan Salisu ya fara zayyane masa abin da ya faru yana kuka,sannan ya bawa Malam hak'uri a kan shi dai ya gaji da halin Saratu kuma ya saketa,ba zai iya jurar takaicinta ba.
Malam baiji zafin Salisu ba illa tausayinsa ma da yaji,ya dinga bashi hak'uri akan bak'incikin da Saratu ta dinga jaza masa,suka yi sallama zuciyar Malam kamar ta faso k'irjinsa,ya san yanzu Saratu zata iso gidan,shiyasa yayi shirin tarbarta da k'alubalen da zata fuskanta a gidan.
Saida ya tsinto almajirai ashirin masu tsananin k'azanta a cikin almajiransa,yace duk su fito da kayansu wad'anda suka yi daud'a an samu mai wanki za a wanke musu,aikuwa suka yi ta murna suka firfito dasu,kayan bak'ik'k'irin sai d'oyi da zarnin fitsari suke,D'an guntun kashi da fitsari duk sun mak'ale a jikin kayan tuli guda.
Saratu kam a k'asa ta isa gidansu tana ta kuka,duk inda tayi kallonta kawai akeyi kamar Mahaukaciya,tun a zaure taci karo da mahaifinta a tsaye ya goya hannuwa a bayansa yana tsumayin zuwanta,yana ganin ta yayi murmushi yace.
"Sannu da zuwa Saratu,madalla da zuwanki,shigo ki fara abin da ya kawoki"
Ya sata a gaba har zuwa cikin gidan,kuma yak'i sauraran duk maganar da zata fad'a masa,ya nuna mata tulin wankin almajirai yace.
"Fara da wannan Malama Saratu, idan kin kammala na tanadar miki wajen kwana cikin y'an uwanki tumakai"
Ya nuna mata turken awakai da yake kiwo yace.
"Kingansu can y'an uwanki ne domin irin halayyarsu kike yi,Dan haka cikinsu za ki shiga,akwai dusa da harawa idan kinji yunwa sune abincinki"
Yana fad'in hakan ya wuce ya barta a gun tana kuka,sannan ya hana mahaifiyarta kulata balle ta tausaya mata,tilas haka Saratu ta fara wankin Almajirai kamar za ta yi amai Dan tashin zuciya,ga rad'ad'in da jikinta ke mata,ga k'unar zuciya,haka ta yini tana wanki domin Malam yace idan ta sake magariba tayi bata kammala ba sai yasa gardawa sun d'aga masa ita ya zaneta ciki da bai ya k'arasa sauke mata kafad'ar ta.
Saratu dai taga ibtila'i a wannan ranar tamkar ta mutu ta bar duniyar haka take ji,nadama Mara amfani ta risketa a sanda lokaci ya k'ure mata.
***************
A Gidan Amarya kam D'an sanda sai da ya casa su sosai ciki da bai,domin sai da ya karya Habiba a agara,Harira kam hannuwanta duk biyun sai da suka karye,Shafa'atu Yayi mata malolo a wuyanta,yayin da ya kusa saukewa Zahra'u kafad'arta ta hannun hagu,bayan ya gama jibgarsu sun shak'i tiyagas sai Yayi nufin wucewa dasu police station domin a k'ara ragargazarsu,da k'yar Hauwa ta lallab'a Idrees ya bawa ofisa hak'uri,sai dai ya rattaba musu babban horning akan duk wadda ta sake shigowa Gidan sai dai uwarta ta haifi wata,kuka ma kasawa suka yi daga k'arshe saboda masifar da suka shiga,tamkar Akuyoyi haka ya dinga binsu yana kad'asu waje da duka, ya watso su waje yana ta tunkud'a k'eyoyinsu,babu wadda ta kalli wata a cikinsu,kowacce burinta ta kai kanta gidanta,ita kam Habiba me karyayyiyar k'afa da Jan gindi ta kai kanta gida,ko wacce tana shiga gidanta ta zube a tsakar gida ta na maida numfashin wahala da azaba.
Idrees kam bayan ya sallami ofisa unguwar yabi ya samo lambobin mazajen matan BAHAGON LAYI,ya kira kowannen su akan idan ba damuwa yana da muhimmiyar magana dasu, idan da hali yana son kowanne ya baro gurin sana'arsa su had'u a bakin layin domin su tattauna.
Cikakken awa d'aya duk suka hallara,Idrees ya jasu soran gidansa ya shimfid'a tabarma suka zazzauna,bayan sun gaisa suna cike da mamakin kiran da Yayi musu,sai ga Salisu ma ya shigo fuskarsa d'auke da tashin hankali,ya nemi waje ya zauna suka gaisa,sannan Idrees yayi gyaran murya ya fara magana.
"Y'an uwana Assalamu alaikum,dalilin taramu anan muhimmiyar magana ce akan matayen mu dake zaune a wannan layi,duk da kasancewar ni bak'o ne a cikinku amma nayi matuk'ar mamakin ganin yadda kuka bari matanku suke rayuwa tamkar dabbobi ko akuyoyi,kun kasa d'aukar mataki a kansu kuna jin tsoronsu,bayan ku shugabanni ne a garesu kune sama dasu,ku Allah ya bawa wakilcin kula da tarbiyyar su,amma kun zama solob'iyo suna juyaku suna abin da suka ga dama kun kasa d'aukar mataki,zuwan mata ta unguwar nan har sun fara hure mata kunne zasu b'arar mata da tarbiyyar da ta zo da ita,Dan haka ni ba zan jure wulak'ancinsu ba,shiyasa a yau na d'auki matakin da ko ance su k'ara dosar gidana wallahi sai sun ruga a guje"
Daga nan ya cigaba da basu labarin dukkan abin da ya faru har dukan da suka sha a hannun D'an sanda da tiyagas,yayi matuk'ar mamaki da yadda yaga mazan suna murna da dariya akan abin da aka yiwa matansu,K'asimun Zahra'u ne kawai yaji ba dad'i sosai,duk da dai matarsa ce tayi silar kawo maganin mallakar da ya fallasa komai,Shi Babalalo ma sai a lokacin yaji ashe Habiba aljanun k'arya tayi sanda ta ciji malam Arabi a cibiya,Kamilu ne yake fad'a masaa lokacin, wai Sahafa'atu ce ta bashi labarin hakan,Haka nan K'asimu ya fad'awa Sunusi cewa Harira Asiri take masa shiyasa baya iya tab'uka komai take gallaza masa,wai Zahra'u ce ta fad'a masa,nan da nan tone tone ya tashi,kowa yana tona asirin matar kowa,bak'inciki kamar ya kashesu,nan Sunusi da Babalalo suka ce wallahi aure za su yi sun gaji da wannan wahalalliyar rayuwar,nan Kamilu ke cewa Sunusi ai Amina k'anwarsa tana sonsa,tana son ta aureshi ko Dan ta gyarawa Harira zama da tarbiyya,nan da nan Sunusi ya amince yace shima yana son Amina.
Shi kuma Babalalo yace akwai d'iyar K'anwar babarsa da zai aura nan da wata uku,domin gininsa yayi nisa anyi rufi flasta da fenti kawai ya rage,za su tashi daga layin shi da Habiban su tare da galleliyar Amaryarsa.
K'asimu ma yace tashi zaiyi daga layin ya nemawa Zahra'u wani matsugunin me kyau,kyakkyawar unguwa wadda babu irin su Harira a cikinta,domin duk ita ce ummul aba'isin lalata musu matansu.
Shi kam Sunusi cewa yayi Gidan iyayensa zai maida Harira da zama,daman akwai wani d'aki d'aya na gadon Babansa a ciki zai sakata ta k'arata,in yaso yasa Amina a wannan Gidan su more amarcinsu.
Kamilu kam yace zai cigaba da zama a BAHAGON LAYI saboda bashi da halin tashi ya kama wani Gidan Haya,sai dai zai kula da tarbiyyar Shafa'atu ya taka mata birki,tilas ta gyara halayenta,duk da dai ya san yanzu dukan D'an sanda ya firgitasu.
Sai da kowa ya gama maganarsa sannan Salisu ya tofa tasa,ya basu labarin abin da yazo ya tarar tsakanin Saratu da Mahaukaci,Abu biyu ya had'e musu,wato takaici da dariya,nan suka rok'i Salisu yayi hak'uri ya dawo da Saratu,amma ya kafe wallahi sai tayi wata uku a gida malam ya dila ta sannan,kuma shi ma da amaryarsa zai tare,Dan duk iskancin mace da an mata kishiya take nutsuwa ta kama kanta.
Bayan sun gama tattaunawa suka yi addu'a taro ya tashi kowa ya nufi gidansa,kowa kuma ya tadda matarsa cikin tsananin azabar dukan da suka sha.
Tsawon kwanaki kafin kowacce ta warke daga raunukan da suka samu,dukkansu sunyi laushi tamkar damammiyar fulawa,kowacce nadama da hankali sun shigeta,dukkansu suka gyara alak'arsu da mazajensu babu fitsara da rashin kunya,babu yawo, babu rashin mutunci da akuyancin da suke yi,amma fa wad'anda suka samu d'ambar aure sun ce babu fashi.
Tuni Zahra'u da K'asimu suka bar layin zuwa wata unguwar suka tare.
Ragowar da suke zaune a layin suka kama kansu babu wadda take fita balle ta lek'a Gidan wata,Gidan Amarya Hauwa kuwa ko shashin Gidan basa kalla,idan suka tuna azabar da suka sha a hannun D'an sanda har runtse idanu suke,basa fatan su kuma cin karo da D'an sanda a rayuwar su.
Hahaha(D'AN SANDA ABOKIN KOWA).
*K'ARSHEN WANNAN LITTAFI KENAN NA BAHAGON LAYI,ABIN DA NA FAD'A DAI DAI ALLAH YA BANI LADA,ABIN DA NAYI KUSKURE ALLAH YA GAFARTA MIN,NAGODE MASOYANA DA JIMIRIN BINA DOMIN KARANTA RUBUTUNA,YANZU DAI NA FITA KO BA SABULU NA WANKE MUKU ZUCIYA A BISA KUKAN DA NAKE SAKA KU CIKIN LITATTAFAINA,SAI KUMA MUN SAKE SADUWA A CIKIN SABON LITTAFINA WANDA NAKE FATAN YA ZARCE DUKA LITATTAFAINA NA BAYA,MA'ASSALAM*👏🥰😘😍
*Bayan comment d'in da za ku yi a wannan shafin ina so ku fad'a min abubuwan da kuka k'aru dasu a littafin,da kuma wane waje ne yafi birgeku?wane waje ne yafi Baku dariya?wane waje ne yafi Baku takaici ko haushi?waye jaruminku ko jarumarku a labarin?wane muhimmin sak'o ku ka d'auka a labarin?Ga wad'anda basa group d'ina ko basa cikin groups d'in da nake zasu iya aikamin sak'onsu ta kan watsapp ta lambata kamar haka:08080049548*
*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️
0 comments:
Post a Comment