<"FCT ABUJA UNGUWAR maitama wani hamshakin gidane na alfarma family mai cike da farinciki da da kaCOMMENT
na hajiya *SALMA* ce zaune acikin kayataccen paloun ta tana kallon labarai a *CNN* wayarta ce tafara ruri neman agaji
Cikin nutsuwa ta mika hanu ta dauka tare da amsawa...
"Assalamu Alaikum"
Daga dayan bangare tajiyo sautin kuka "Aunty Salma ki taimake ni"....
"Subhanalillah" sister Aisha lafiya?
Cikin kuka tacigaba ki taimakeni yaya salma *MUNUBIYAH* tana neman tafi karfina tunda ta gama school na rasa gane mata dan ALLAH sister ina son ta dawo gidanki saboda na sami sauki kozata daina wannan halin nata....... Hajiya *SALMA* cikin sanyin murya ta tasoma magana.....,,
"Kada ki damu sister wannan bazai zama matsalaba" ki bari zan shirya zuwan nata dama ina neman ma taimaki agurin aiki kinga hakan sai yaza kamar tazo cikin sauki"
"Cikin murna tace nagode sister wallahi idan kika yi hakan da kin kyautamun"........ "Kada ki damu sai mun yi magana ki sanarda ita tafara shiri Alhaji yana dawowa zakiji ni insha Allah"....... "Nagode sister Allah yabar zumunci atare suka ajiye wayar".......
"Hajiya salma tayi shiru na tsayin lokaci daga bisani tamike tashiga dakinta kwanciyarta kenan bacci mai nauyi ya sace ta"...........
Acikin bacci takuma yin wannan mafarkin dai wanda yazamar mata sabo kullun sai tayi sai dai na yau ya bambanta da kowanne wata kyakkyawar yarinya ce mai matukar kyau ahankali ta ta karaso gurinta cikin maganarta mai dadi tace kada ki damu zan kular miki da yaranki zan warware komai kawai kije insha Allah zan iya sannu ahankali kowa sai ya gane gaskiya ki tafii! Ki tafii! Ki tafii!!! Nace dake, "tamkar haske ta bata tajuya ko ina amma ba kowa sai dai wani katon rami daya ke gaban ta katon gaske sai wata yarinya matashiya wacce shekarunta basu wuce 20years ba fuskarta dishi -dishi ta dage ta hankada ta cikin wannan katon ramin maimatukar duhu"
Tafarka cikin matukar tsoro da firgici "innalillahi'wa'innah ilaihirra'ju'un" gumii duk ya jika mata jiki jagab jikinta yana matukar rawa,
*ASHRAB* da *FARHA* suna zaune agefenta mummy lafiya hanu tasanya ta rungumesu tafashe da kuka mai tsuma zuciya ina kaunarku yaranah bana son na rabu daku ina kaunarku sosai
"Maganar tata sai tazoh musu wani iri mummy lafiya Ashrab ta tambaya tare da damuwa itace babba dan haka sai ta tsinci kanta adamuwa farha ganin yayarta cikin damuwa yasanya ta jin wani iri.....
Ta matsa kusa ta kara rungume ta tace muna kaunarki dan Allah ki sanar damu damuwarki kinga yaya Ashrab duk ta damu
"Ta dago takallesu na tsayin lokaci sannan tace ba komai kawai dai mafarki nayi ne kuma irin dai wanda na sabayi sai dai na yau yayi matukar tsoratar dani Amma kada ku damu inafatar bakomai insha Allah",,,
"Muma muna fatar hakan muma Amma mummy mekike ganine awannan mafarkin naki ne"?
Ta dago mubar zancen Ashrab kutafi kuyi sallah dadyn ku yace zai kira muyi vedio call insha Allah
Cikin farin ciki suka hau ihun murna haka suka fice daka dakin cikin zumudin jiran kiran Abban nasu.....
Karfe 7:00pm dai-dai kiran Alhaji *MUSADDIQ* yashigo tangameme yar WAYAR hajiya *SALMA* cikin zumudi suka rankayo dukan su cikin farinciki dady barka da dare *ASHRAB* tace cikin girmamawa *FARHA* ma haka sannan hajiya salma cikin sakakkiyar fuskarsa ya yi murmushi ya amsa cikin farin ciki da kaunar iyalinsa ya kk yace cikin farin ciki...... Hajiya taja ajiyar zuciya hummmmm!! Dady muna cikin kewar ka yakamata ka dawo wallahi ina bukatar ka akusa dani....... Cikin kulawa ya amsa( what happened my dear) ,,
Ki sanar dani dear kinsan bana son damuwarki ko kadan "no don't mind, "insha Allah everting clost to an end,
"what do you mean dear? ""
Kada ka damu my dear when are you coming back?
Gobe zan dawo bazan iya zama ba dear kuna bukata ta gobe jirgin safe zan biyo insha Allah farha ta kwala ihu my dady Tamike tasoma jan shokii dady Allah ya kaimu dama mummy bata hira damu kwanan nan mu kadawo muringa ball wallahi munyi mising ball two days......
Dariya yayi kada ki damu autan dady gobe ma zakiyi ball don't worry kinji mamanah hajiya *Salma* tayi shiru tana sauraron su tana kara jin kaunar family dinta cikin ranta...... Can ta tuna da mafarkinta take taji zuciyarta ta tsinke me mafarkina yake nufi ni *salma*?"
Magana yakeyi amma tayi nisa a tunani hakan ya kara tayar da hankalin Alhaji *MUSADDIQ* matuka Ashrab ta janye kanwarta farha suka bar gurin ahankali ta dago kayi hakuri wallahi kaina. Ne ya tafi caji cikin murya mai rauni...... "Tabashi tausayi matuka, "dear kina cikin damuwa nafuskanci haka tun lokacin da muka fara waya"......
Hawaye masu zafi suka zubo mata akumatu kada ka damu idan kadawo zamuyi magana diff ta kashe wayar ya mike jikinsa babu kwari
"menene damuwarki dear?
Menene yake barazana da farin cikin ki masoyiyata?....
"Bazan taba samun sukuni ba har saina naga karshen damuwarki".... "Kiyi Hakuri ina nan tafe gareki" .....
WASHE GARI
tun karfe bakwai Alhaji yabar garin ikko ya nufo Abuja, yayi dai-dai da zuwan *MUNUBIYAH* gidan saukarta ke nan cikin zumudi ita da yaranta suka rankaya tarbarshi hakan sai ya ya susa munu ganin sunfi nuna zumudin ganin Alhaji akanta π¨too munu inbanda abunki ai Alhaji ne abun marmari bakeba bakuwaπ,
tana zaune tana kalon yanda hajiya salma take zuba shagwabarta agaban yarah batare da jin kunyaba hakan sai ya dasa wani abu azuciyar munubiyah jitayi gaba daya Alhaji yagama tafiya da imanin ta tabbas irin shi ne mafarkinta dan haka zata san abunyi π¨ashe akwai Matsala babbah munubiyah kin manta da matsayinki ne?
To masu karatu sainaji daga gareku
Yawan COMMENT YAWAN TYPING.....
VOTE
SHARE PLSSSSS
TAKUCE LAURAT MUH'D BELLO
πππππππππ
BANGARE NAH
(part of me)
ππππππππππ
WRITING BY
LAURAT MUH'D BELLO
DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
YA CUTAR DANI
YAR'ZAMANI
(mai kwadayin duniya)
And now
π
BANGARE NAH
(part of me)
*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*π¦{Arewa ginshiΖin al'ummah}π¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl
ALHAMDULILLAHI
MASOYANAH COMMENT DINKU YANA SAKANI ACIKIN FARINCIKI
INAYINKU IRIN OVER DIN NAN I A LOVE U WUJIGA-WUJIGAπ
π
Ώ<><><><><><><><><><>3⃣➡4⃣
<><><><><><><><><><><"bakin ciki takaici duk ya addabi zuciyar munu ji take kamar ta shake wuyan hajiya Salma kishin ta takeji sosai azuciyar ta tamike tare da yin gyaran murya hajiya ta dago"
"Tana murmushi tace ayyah munu kiyi hakuri na manta da ke kinsan idan dear yana tare dani mantawa nake da kowa, "maganar da hajia
salma tayi takara tunzurah zuciyar munu, ta washe baki na munafurci tace ba komai mummy hakan yanada kyau ai"πta washe baki kamar da gaske nan kuwa ita kadai tasan abunda ta ta kudurah aranta",,
"Tooooπ¨ Allah ya tsare dai dan fah akwai Matsala"
"Ta kwallawa delu kira, ta zoh cikin gaggawa na'am hajiya tace cikin girmamawa ki nunawa munu dakinta kinji ko, kuje munu idan kina bukatar wani abu ki sanar dani kinji koh kisaki jikin ki,
"Ta kara narkewa ajikin mijinta wanda ganin hakan munu taji kamar zuciyarta ta fito waje saboda kishi"
Suna shiga dakin tajuyo "to delu kike ko wa? kin gama aikin ki sai kiyi waje koh, "kuma daga yau idan har bani na gayyacekiba to bana son nakara ganinki, delu mai aiki ta dago cikin mamaki ta kalleta batare da tace da ita komai ba tajuya zata fice daga dakin har ta kusa kai kofar ta kirata kuma wallahi kika sake naji wata magana agurin mummy wallahi ni ba ruwana da tsufan da kikayi, idan kinji to jiki ya tsirah......
Delu har tuntube tayi, saboda tsoron yanda munu tayi maganar saboda tagama fuskantar lallai munu bata da mutunci kuma ga alama zata iya yin komai kamar yanda tace...."lallai munu daga zuwanki"
WASHE GARI
"tun shida munu tafara jin hayaniya da ihun *FARHA DA ASHRAB* tare da dadyn su suna hand ball "wallahi dady ni naci amma shine zakace Ashrab ce ni gaskiya bazan yarda, ba tasoma buga kafa,
na shagwaba hajiya salma ta taso zo zo zo yarinyar mummy ya akayi ne? cikin shagwaba tace ba dady bane ta fashe da kukan shagwaba to ya isa ta dago haba dady yazakayiwa yar'auta haka?"yayi dariya ya matso kusa da ita yanzu tsaya me kike so ayi autar dady, gaya mun ko mene tadago cikin murmushi tsere nakeso muyi sai nagani idan yanzu zakayi mun aringizo, "kuma baza'ayi da Ashrab ba mummy ke zakibawa kowa maki"
A'a tsere kuma *Farha* eh mummy ki duba sosai kisan dady yanda yake haka kuwa akaya suka zama cikin shiri Ashrab itace bangaren dady mummy tana bagaren Farha,..... Dan haka aka fara gasa hajiya ta hura usur ai kuwa kamar barewa farha ta wuce dady cikin yan mintina tayi masa fittt ta wuceshi tun kafin su iso mummy tafara winner we are winner da kyar dady ya karaso saboda dama farha mugunta tamasa tasan ita zata ci so take sai ta rama ai kuwa yana karasowa Ashrab ta mika masa glucos dady kasha naga ka gaji π€£tana dariya
Ya karba ya sha sosai ita kuwa mummy da farha sai murna suke sun yi winning
Saida dady yasamu nutsuwa ya dago yanzu auta muguntar da kika yimun ke nan zan rama ni gobe seeming zamuyi zamu gani mummy tace A'a wallahi bazai yuyu ba sai dai acanja wani abun haka wasa ta tashi farha nayiwa dady da Ashrab dariya
Munubiyah tana daga tsaye gefen window dinta tana kallonsu tace aikin banza duk yazama kamar wani sakarai sai wani biye musu yakeyi kamar wani sha-sha-sha...... Ai wallahi duk sai na yi maganin ku dukan ku banzaye kawaiπ...
Tabdijam too Allah ya tsare
Tasaki labulen cikin bacin rai taso magana cikin hasada da bakin ciki yazama dole nasan yanda zanyi na janyo hankalin Alhaji dole ne yasoni kota halin kaka sai nayi sanadin rushewar wannan farin cikin
Wannan farincikin bana son nacigaba da ganinsa indai ina raye....
Haka ta wuni cikin bakin ciki hajiya salma ta tura delu kiran munubiya bayanda ta iya tadoshi dakin ba kowa asaman dan haka ta doshi dakin babu tunanin komai ahankali tasomajin magana kasa-kasa wallahi insha Allahu na dauki wannan alwashin sai na mallaki gidan da abunda yangidan suke takama dashi indai ina raye kaidai bari kawai a'a a'a kada kazoh abunda yasanya bazan zoh ba kasan suna ganin ni bakuwace agarin kabari sai an kwana biyu tukunnah akwai abunda nake shiryawa aa my darling ka fahinceni mana bana son mutanen gidan su ganoni da wuri kaidai kabari kawai nima wallahi hakuri kawai nakeyi ina fama da rashinka akusa dani na sani amma kayi hakuri eh to sai anjima bana son wani yajini ina waya kasan inason sai kowa yagama yarda dani ne kagane ai...... Bey sai mun hadu eh diffffff!! Ta datse kiran.....
Jikin delu yasoma rawa babu abunda take fade sai innalillahi wa'innah ilaihi'raju'un. Da kyar ta iya dai-daita nutsuwarta ta soma kwan-kwasa dakin ahankali cikin tsoron masifar munubiyah.....
Waye tace cikin sanyin murya duk tunaninta hajiya salma ce delu ta ce nice ranki ya dade hajiya tana jiranki akasa cikin izzah da mulki tace dama kice kikemun bugu haka tafada tare da bude kofar afusace hanu tasaya ta fincikota da karfi ta iza keyarta ciki ta kalleta kinkai minti nawa anan? "yanzu nazoh" ki gayan gaskiya ba abunda kikaji?"
"Cikin rainin hankali delu tace kamar na me ranki yade" fice mun daga daki, "kice da ita ganinan zuwa"....
"To delu tace ta ficedaga dakin ciki sauri gabanta yana faduwa tabbas akwai matsala agidan nan tabbas matukar ina raye bazan bari acutar da su hajiya ba insha Allah"......
Suna zaune a darning suna cin abinci hajiya sai zuba shagwabar ta take shikuwa oga sai lallabata yake farha tana kusa dashi dady wai mummy kawai kake so da yaya Ashrab amma ni bakasona ta karasa maganar tana langabar da kai abun tausayi me zasuyi sai dariya yayi dai-dai da isowar munubiya jitayi kamar ta koma saboda bakin ciki
Haka ta karasa ta sunkuya dady good morning batare da ya dago ba, yace morning ya cigaba da cin abincin shi ranta ya sosu matuka amma ta tajuya ta gaida hajiya cikin sakin fuska ta amsa naga baki fitoba shi isa na aika kizoh kiyi break.....
"Bacci nakeyi ne mum shi isa tajuya ta kalli delu tare da sakar mata muguwar harara ta ja kujera wacce take kallon Alhaji yanda zasu gajuna sosai dashi
Shikuwa ogan bai ma san tanayi ba dan shi ayanzu baya ganin kowacce macce sai matarsa ruhinsa kuma masoyiyar sa *SALMA*
duk rabin cin abincin nata kallon Alhaji ne amma dai-dai da sakan bai dago ya kalleta ba abincinsa kawai yake ci yana kuma ciyar da matar sa farha ta zauna tana kallon shi can kuma tace dady ina kaunarka kai da mummy dariya sukayi atare sukace muma muna kaunarki Auta
Ashrab tayi dariya ni bakya kaunata no my sister wallahi duk duniyar nan idan kika cire dady da mummy bana son kowa sai ke ina sonki yar'uwata yayata farinciki na tashi tayi tazoh ta rungume ta kam suna murmushi lomar bakinta da kyar ta iya hadiyeta ta mike mum zan shiga ciki naji kaina yafara ciyo tajuyo tana murmushi tace Ayyah Sorry idan kin shiga kisha magani kinji tana tafiya ta amsa to mum........ Ji take kamar kafarta bazata iya kaita daki ba saboda azabar da zuciyarta ke mata.........
Tana shiga dakin sai hawaye shar kamar an bude fanfoh π¨ too aiki ya sameki munubiya
Sukuwa basu kosan tana yiba haka suka cigaba da hirar su irin ta nagartaccen family mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali......
Da kyar ta iyakarasawa dakin tana shiga dakin sai kuka hawaye sharrrrrr kamar an bude fanfohπ¨toooo aiki ya sameki munubiya
Haka ta wuni adakin ta cikin bakinciki da takaici a kwance take tayi zumbur ta dauko waya tasoma kiran layin saurayinta *BASSAM*
Bugu daya ya dauka darling kana ina ina cikin matsala yaza'ayi mu hadu baby ni banda damuwa ke dai ya za'ayi ke ki fito tayi shiru can ta mike kajirah ni zuwa miti talatin muhadu inda muke haduwa...... To yace sukayi sallama ta ajiye wayar tasoma shirya kayarda zata yi tasamu ta fita daga gidan
Tana zaune hajiya *Salma* ta turo dakin tare da yin sallama tace mun ya jikin naga baki futo ba tun dazu ta shagwaggwabe fuska yanzu dama nakeson zuwa asibiti naji jikin ya matsa mun Ayyah tace basai kinjeba bari na kira family doctor na ya dubaki ta dago cikin kissa mum kibari naje asibitin inaga zaifi kinga kafin ya zoh wata kila ni naje ina ga zaifi ai
Tayi shiru can kuma tace to ba damuwa ki shirya in yaso baba umar direba sai ya kaiki ta dago tace na gode mum cikin yan mintina ta shirya direba ya dauketa sai sharaton hotel baba umar ya kalleta hajiya ai nan ba asibiti bane ba ta dago tayi masa kallon wulakanci tace to sai me ai nasan inda nazoh kuma wallahi idan naji zancen agurin hajiya ni zanyi sanadin aikin ka dan haka sai ka kiyaye
Tabdijam muje zuwa dai to kome *MUNUBIYAH* Tazoh yi hotel?
Koma dai menene zakuji kudai kubiyoni
YAWAN COMMENT YAWAN TYPING
VOTE
SHARE PLSSS
TAKUCE LAURAT MUH'D BELLO
08164949554
πππππππππ
BANGARE NAH
(part of me)
πππππππππ
WRITING BY
LAURAT MUH'D BELLO
DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
YA CUTAR DANI
YAR' ZAMANI
(mai kwadayin duniya)
And now
π
BANGARE NAH
(Part of me)
________________________________
*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*π¦{Arewa ginshiΖin al'ummah}π¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/119016616251942/?app=fbl
FREE PAGE
BISMILLAHIR~ RAHMANIR~RAHEEM.
ALLAHUMMAH INNI'AUZUBIKA MINAL BARASI WALJUMI, WAL'JUZAMI WAMIN SAYYU'IL ASKAM....
AMEEN YA HAYYU YA QAYYUM..
DEDICATED TO AUNTY. HAU'WA SPECIAL GIFT TO MY LOVELY FAMILY.....
π
Ώ<><><><><><><><><><>5⃣➡6⃣
<><><><><><><><><><" ALLAH ya baki hakuri ya gyarah parking din motar ta fice daga motar batare da tace dashi komai ba jijjiga kansa yayi azuciyarsa yace lallai wannan yarinyar sai ankiyaye ta dan na fuskanci batada mutunci"
Dakinda *BASSAM* ya gayamata can ta dosa tana shiga ya rungumeta suka shiga aikata masha'ar su dama can sun saba aikata mummnar dabi'ar su sai bayanda suka gama iskancin su tukunah ta ce *BASSAM* Ina cikin Matsala"
Ya janyota jikinsa sosai "bakida damuwa indai har muna tare dake"
"Ta tirushi daga jikinta"
"Yakamata kagane mafita nake nema" ya manna mata kiss agoshi
Ya kike so ayine"
Shawarah nake nema ya zanyi wallahi inason Alhaji *MUSADDIQ* idan har ban sameshi ba zan iya mutuwa
Yaji zafin maganarta ya share "to ki sanar dashi abunda kike so mana nafasanki munu idan kinason Abu bazaki taba hakurah ba harsai kin samu",,.
Tayi wani shu'umin murmushi ta dago "kana ganin hakan zaifi? akwaifah matsala fa?"kasanfa dan iskan baya ganin kowa sai wannan banzar matar tasa dakuma yan'iskan ya'yan nasa nifah banida wani kima agidan shakuwar family tayi yawa wallahi......
Yayi dariya toki hakura mana inaganin zaifi tunda harke da kanki kince family sun shaku dayawa..... Ya janyota inasonki munu ki soni mana kirabuda family nan.....
Ta janye jikinta tamike tare dayi masa wani wulakantaccen kallo kanada hankali kuwa *BASSAM*? Kasan Abunda kakecewa kuwa?
kasan yanda nake son Alhaji Musaddiq kuwa?"
"Kasan yanda nake son mallakar dukiyar gidan hajiya *SALMA* kuwa?"
"To wallahi bazan taba barin wannan damar tawa ba,dan Haka shawarar ka nake nema idan kayi haka kaima kaci arziki kafita daga cikin wannan bakin talaucin da kake ciki idan kuma ba hakaba zaka dauwama acikin bakin talaucinda ka gada a gurin danginka matalauta....
Ta mike cikin bacin rai zata fice daga dakin yayi saurin rikota tsaya mana munu zo muyi magana menene na bacin ran to" tayi banza dashi batare da tace komai ba mekikeso nace nace dake ki sanar dashi idan har bai Aminceba kawai a kaddamar masa saboda bashida wani Amfani...... Ta dago kamar yaya a kaddamar masa to kawai ya kauce kinga kowa ya rasa keda hajiyar taki koya kike gani tayi shu'umin murmushi inason Alhaji fah Amma shawarar ka tayi.........
Kaga zancen shakuwa ya kare kenan sai muci duniyar mu da dukiyar ba wani mafadi dan na fuskanci yana da tsare gida dayawa.....
Ta duba agogon hanunta karfe 5:00pm na yamma ta mike arazane nashiga uku haka lokaci yaja Allah dai yasa wancen banzar bai tafi ba kada yaje ya hadani da hajiya dan na fuskance shima dan iskane......
Ta fito cikin sauri *BASSAM* yana binta kamar wani wawaπ koda suka fito farfajiyar hotel din babu baba direba babu dalilin sa jikinta har rawa yake nashiga uku kagani ko dama nasan wannna dan rainin wayon sai yabata mun shiri tan gurin wayarta ta soma ruri
Tana dubawa hajiya *SALMA* ce jikinta kamar dan mazari ta dauki wayar tare da dai-daita nutsuwar ta
"Hello hajiya tace ahankali tamkar marar lafiyar gaske",,
"Munubiyah! kina inane ga deriba nan yadawo tun dazu ba ke"
"Ta Kara raunana muryar ta, "hajiya doctor din ne ya dan bani hutu na awa hudu, to banida number dinsa baranta na sanar dashi, sai yanzu kuma ina fitowa shine ban ganshiba hajiya kice ina jiransa jiri nake ji sosai bana son yawan magana"
"Ayyah munu to ba damuwa gashinan zuwa nida har hankalina ya tashi wallahi"...
"Hajiya yace dake wani abu ne?"
"A'a ba abunda yace kawai dai yadawo gida tayi ajiyar zuciya mai karfi har hajiyar taji
"lafiya munu?"
"Akwai matsala ne? "
"A'a zuciyata nakeji wani iri ina jiransa ta datse kiran"....
Hankalin hajiya Salma atashe baiwar Allah sarkin tausayi ta fito tana kwallawa baba umar direba kira ya taho cikin sauri ya russuna ranki ya de gani tace yi maza kaje ka dauko munubiyah ashe likitan ne yadan bata hutun awa hudu shi isa kaga baka ganta ba kayi sauri dan Allah tace bata jin dadi sosai kada tayita jirah...... Yayi tsaye cikin mamaki baice komai ba yace to ya shiga motar ya fice daga gidan.....
Zuciyar sa cike da tunani fal afili yace tabdijam wannan yarinyar bala'ice....
Har ya isa hotel din tunani yake suna tsaye itada da *BASSAM* makale da juna tamkar gam
Yana shiga ya hangosuπ¨idonsa kamar yafado kasa dama wannan yarinyar haka take tabdijam lallai
A zuciyarsa yace hajiya kina tare da bala'i dan wallahi wannan yarinyar masifa ce
Duba kigani tana nan tana holewar ta amma tayi karya da likita..
Ta ganshi amma shu'umar sai ta kara narkewa ajikin *BASSAM* takaici ya ishi baba direba ya fito ya nufi inda take muje ko yace zuciyarsa cike da takaici ta dago ta gallamasa harara takunah ta juya sweet heart zan tafi sai kaji yanda mukayi ......
Murmushi yayi tare da manna mata kiss a kumatu ta tayi wani irin fari da ido tajuya ta shige motar baba umar direba yaja da karfi saida ta dungura ta gabaπ€£
Hankalinta atashe tace lafiya meye haka?....
Kamar dariya ta subuce masa ya hadiye sorry hajiya
Azuciyarsa yace ga iskanci ga shegen tsoroπ€£
"Ka kula dan Wallahi ina son raina dan iskanci kana nema ka ruguza mun shiri yadago da sauri shiri kuma?"
Ta shareshi dan tayi kusan sakin bakinta....... "Wannan kuma bai shafeka ba katafi ahankali kaji ko"
Bai kuma cewa komai illah tunanin wane irin shiri ne wannan munubiya take yi?
"Me wannan yarinyar take shiryawa su hajiya dan yasan tabbas akwai wani abu. Kuma jikinsa yana bashi akan su hajiya ne"......
"To menene wannan shirin?"
Har suka isa gidan zuciyarsa tana cikin tunani yana parking ta fito tana tafiya tana dafa bango tare da dafa kanta kamar da gaske hajiya salma ta karaso gunta cikin sauri ta riketa sannu munu jikin ne tadaga kanta shidai baba direba yana kallon ikon Allah
*FARHA* tana tsaye agurin haka kawai ita dai munu bata yi mataba ta tabe baki ko sannu batace da itaba
Mum ki saketa mana tace A'a FARHA bakiga batada lafiya au batada lafiya ne
Daga haka bata kuma cewa komai ba hakan kuwa sai ya sosa ran munu azuciyarta tace lallaima yarinyar nan sai nayi maganin ki wallahi...
Suka shiga ciki *ASHRAB* tana zaune afalo tana har hada kan wasu takardun da dady yasata hadawa tun shigowar munu I don'ta yana man *ASHRAB* babu burinta illah taga ko takardun menene ake hadawa..
Hajiya Salma ta rakata har dakinta tace ki kwanta ki huta zamuyi magana anjima idan kin tashi.....
Maganar me kuma mum tayi murmushi ki bari kawai yanzu bakyajin dadi zamuyi magana anjima... Ta fice daga dakin
Hajiya tana fita daga dakin ta mike zaune kamar wacce aka tsikara wace magana ce wannan mum take so muyi Allah dai yasa aikin ne zan farah shike nan nasami damar Kara kusanta kaina da dukiyar Alhaji nasami damar fallasa sirrin zuciyata
Ta fada saman gadon da karfi tana murmushi my dream will soon become true ta sheke da dariya kamar wata sha-sha-sha....
Delu tana kofar dakin tana jinta ta rike baki
Ahankali ta salallaba tabar kofar dakin zuciyarta cike da wasiwasi
Hakan nan ta fito paloun gidan wasai saboda amatse take taji abunda mum zata sanar da ita
*ASHRAB* ce kawai a paloun hakan sai. Yayi.Mata dadi ta karasa gunda take azaune tana wani murmushin mugunta tace my cousin sister kina zaune ke kadai batare da ta dago ba tace eh sister aiki nake dady ne yasakani tattarah ta kardun duka kadarar shi data mum tunsafe nake abu daya wallahi na gaji sosai
Gabanta yafadi kadara kuma to saboda tsaro kinsan yanzu mutane basuda tabbas banki zai kai yafi kwanciyar hankali
Tayi murmushin yake hakan yana da kyau ai inbanda dady kudin da kadarar nasa sunada yawa ne dayake tsoro haka takarasa cikin dariya kamar ba wani abu
*ASHRAB* Ba wayo tadago sai taga bama ita take kalloh ba tace lallai sister kinsan kuwa nawane. A'a
ta ina zanyi nasani sister"
Ta bude baki kenan zatayi magana dady yayi sallama yashigo ta mike oyoo. Oyooo dady oyoo taje dagudu ta rungume shi ya daga yajuya sannan ya ajiyeta sannu da zuwa dady
Ya amsa cikin far in ciki sannu da aiki kingama dai ko
Ta da ja ajiyar zuciya hummmmm!! Ban gama dady amma nayi kusa
Wallahi yau dady duk ka gajiyar dani
Yaja kumatun ta uwar son jiki hada takardun ne angaji cikin shagwaba tace Allah dady aiki ne mai wuya
Ni ajiyewa ma zanyi sai gobe zan karasa bara na kai dakina na ajiye π¨ dakin ki a'a ban yarda ba kikai dakina ki ajiye mun munu datake zaune tanajin su ta ciji lebanta taga samu taga rashi duk shirinta na ta bugi cikin *ASHRAB* ya ruguje ta mike dady sannu da zuwa tace tana yi masa kallon kurillah baiko dago ba lafiya yace agajarce ya taya *ASHRAB* kwashe sauran takardun da ya fuskanci munu tana son ganin kona menene muje ko suka bar gurin batare da ta sunkara kallonta ba
Bakinciki da da takaici yagama cika mata zuciya tayi kwafah tamike tabar gurin zuciyarta tanata tafarfasa....
Tana shiga dakinta tabuga kofar dakarfii jikake gammm!!
Delu datake a makale tana kallon komai ta fashe da dariyah harda hawayeπ€£
Itakuwa tanacan sai kullawa take tana war-warewa ta daki hannunta yazama dole na gano takardun nan tunkafin dare yayi munπ¨tooo
Alhaji saika canja shiri dan kunada yar'majiya tare daku...
Muhadu A next page danjin yazata kaya....
Takuce
AKULLUN
LAURAT MUH'D BELLO
YAWAN COMMENT
YAWAN TYPING
VOTE&SHARE PLSSSSSS
08164949554
πππππππππ
BANGARE NAH
(part of me)
πππππππππ
WRITING BY
LAURAT MUH'D BELLO
DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
YA CUTAR DANI
YAR'ZAMANI
And now
π
BANGARE NAH
(part of me)
________________________________
*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*π¦{Arewa ginshiΖin al'ummah}π¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl
BISMILLAHIR~RAHMANIR~RAHEEM..
BISMILLAHIL LAZI LAYADUR'RUMA ISMIHI SHAI'UN FIL 'ARDI WALA'FISSAMA'I WAHUWAS SAMI'UL ALIM
π
Ώ<><><><><><><><><><>9⃣⏩π
<><><><><><><><><><><"A fusace ta fito daga office din baba direba yana jiranta a mota"
"Ko kallonsa batayi ba tayi wucewar ta cikin matsanancin fushi"
Daga kafadarsa yayi danshi dama yasan za'ayi haka dan yasan sarai Alhaji bazai dauki wannan iskancin ba..
Tana fita daga ma'aikatar ta tari adai-daita tashiga jitake kamar zuciyarta Kamar zata tarwatse saboda takaici...
Tun ahanya tayiwa *BASSAM* waya ringing daya ya dauka
"ya akayi ne?"
Cikin disasshiyar murya "tace kana ina *BASSAM* ? "inason mu hadu ina cikin matsala"
" ina sharaton kishigo kawai"
"To kawai tace ta kashe wayar ta"
Baba direba yabi bayanta ahankali yana bin bayan adai-daitar har suka isa sharaton hotel dama yasan haka saita faru domim kuwa ya gama fuskantar munu yar bariki ce ta ajin karshe
Cikin sauri ta biya mai adai-daita ta shiga cikin kamar zata tashi sama
Baba direba ya fito shima yabiyo bayan ta room mai lambar 107
tashiga a kofar yatsaya tana shiga ta fada jikin *BASSAM* ta fashe da kuka mai karfi
"BASSAM!
"Alhaji *MUSADDIQ!* baya sona ya tabbatar mun da bazai taba sona ba"
yaji dadin maganar amma bai nuna ba ya janyota jikin sa ya sumbace ta toki kiyi shiru mana inaga bai kamata ki bata lokacin ki kiyi kuka ba sweet heart ki kyaleshi kawai inaga zaifi..
"Ta dago jajayen idanuwan ta, ta kalleshi
Ta girgiza kanta wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Bazan kyaleshi ba
"Idan har bazai soniba to wallahi sai naga bayansa inyaso kowa ma yarasa"
" wannan shine kudiri nah, ni munubiya ban taba kudirar abuba na gagara aiwatar dashi ba
"ka shirya mun yarah"
Ayau nakeso ku kaddamar masa bana son Alhaji *MUSADDIQ* yakoma gida inason kota halin kaka yau kada ya kwana acikin duniyar nan.
"Inason yau na dan-danawa iyalan Alhaji *MUSADDIQ* bakin ciki da kunci da radadin Abunda yayi mun
"Baisan ba'a tabani ba dan duk wanda yanemi shiga gonata to wallahi sai na hada dashi na nome dan ni bakar zuma ce mai mugun harbi..."
Maganar ta girgiza *BASSAM* sosai ya janyo hanayenta sweet heart basai andauki wannan hukuncin ba inaga ki share kawai wallahi inajin tausayin iyalinsa dashi kansa
Amma fa shawara ce cikin tsawa "to bana bukata ai wallahi tunda na iya dukan mahaifiyata banga wani wanda zai sha gaba naba ban hankada shiba wallahi"
"Ya daga kafadar sa"
"Well wannan ba matsalata bace kamar karfe nawa kike son a aiwatar da aikin"
"Da dare idan yadawo kina nufin agida za'a kashe shi inaga wannan ba shawara baceba saboda unguwar tanada tsaro sosai"
"Kuma kinsan za 'a zargi wani abu inaga ki bari kawai a kashe shi ta hanya mai sauki"
"ta dago ta yaya?"
"Yayi murmushi yace ta hanyar zuba masa poisin acikin abun sha kona ci wanda idan yaci ahankali zai ringa cuta har yamutu batare da kowa ya zargi wani abuba"
"Ta kankameshi sosai ajikinta *BASSAM* inasonka ada naso akashe munshi agaba na a shakemun dan iska har sai ya mutu"
"Bakida hankali ai sai bincike ya kawo kanki kema amma yanzu idan yasha slow poisin ba mai tunanin komai har ya gangara ya ware kawai muci dukiyar mu da tsinke".......
"Baba umar direba jikinsa har rawa yakeyi saboda tashin hankali da kyar ya iya barin kofar dakin ya fice daga hotel din"
Ya ja mortar sa da karfi yabar harabar gurin duk da sanyin AC da ke cikin motar Amma gume yakeyi ya jike jagab
Addu'a yakeyi yana sharara gudu Allah ya tsareka Alhaji Allah ya kareka da sharri wannan bakar muguwar azzaluma mai fuska biyu
"Baifi mintina talatin ba ya isa gidan idi mai gadi yabude masa kofa ko gyarah parking baiyi ba ya fito, "idi Alhaji ya dawo kuwa?"
"Eh"
"Yana ciki tun dazu Amma lafiya kake tanbaya?" "kuma sai naga kamar hankalinka atashe yake lafiya?"
" Ba komai kawai ina tanbaya ne"
Ya wuce dakinsa saboda baya tare da nutsuwar sa ya idan yace zai dade to idi zai gano wani abu
Alhaji *MUSADDIQ* yana jikin hajiya Salma yayi lamo kamar mai bacci ta dago fuskarsa dear ya na ganka haka lafiya kuwa
Ya kara janyota jikinsa sonki ne yake dawainiya da zuciyata Amma bana tare da damuwar komai ya shafi face dinta ya gangaro izuwa labbanta ya kai bakinsa ya sunbaceta
Ta dada janyoshi jikinta dear inaganin canji atare da kai kasanar dani kasan bazan juri ganin ka haka ba kayi gaggawar Sanar dani tunkafin zuciyata ta Gaza
"Kada ki damu kawai gajiya ce amma bana tare da damuwar komai"
Ta langabar da kanta Allah yasa haka dear
Daga nan zance ya sauya suka shiga sabuwar duniyar masoya ina ganin haka na janyo iyalan kafa ta na fito dan da alama idanuwana basu iya kallohπ ba
Ya manta shaf dawata munu danshi daukar ta yakeyi wata sha-sha-sha ce π¨ tabdijam
Aikuwa munu ta dauki damarar daukar fansa
*ASHRAB* tana zaune tana typing saman cumputer *FARHA* ta matsa kusa da ita ta dafata yaya dama ina son na tanbayeki ta dakata da typing dinda take ta dago tace meya faru
Dan Allah kina son zaman Aunty munu gidan nan
Dariya tayi tace idan bana so ya zanyi Amma me yasa kika yimun wannan tanbayar
Tace ni wallahi bana son zamanta agidan nan haka kawai nakejin bana kaunar ganinta agidan nan
Allah yasani badan ko muna da arziki ba a'a kawai dai zuciyata takasa Aminta da ita
Idan na ganta sai naji gabana ya fadi
Narasa meyasa inajin tsoro sosai kada Aunty munu ta cutar damu
*ASHRAB* ta ajiye abunda takeyi tace ashe kema zuciyar ki tana yimiki wannan tunanin nima haka nake ji game da ita Amma kuma data zauna tare damu sai naga kamar zuciyar muce kawai take zargi insha Allah ba matsala ki sa hakan acikin zuciyar ki...
Jinjina kanta tayi to yaya Ashrab zanyi kokarin ganin na yaki zuciyata Insha Allah
Munu sai da ta tanadi poison din da zasuyi amfani dashi tukunnah tabaro hotel din sai misalin karfe 7:00pm ta dawo gida
A farfajiyar gidan suka ci karo da baba umar direba ko akallonsa batayi ba baranta tace dashi wani abu tayi shigewar ta ciki
Girgiza kansa yayi yakuma kudira aransa zai taimaki Alhaji indai yana raye
Tana shiga ciki bakowa acikin paloun kowa yana dakinsa sai delu kadai tana kwashe kayan abincin da sukaci har ta wuce ta kuma dawowa baya delu zoh ta dago na'am tace kizoh nace dake
Tace to ta waiga bakowa tukunnah ta tanbayeta Alhaji ya dawo ne
Tanbayar tabata mamaki tace " Eh
Amma meye na tanbaya haka kawai sunyi dinner ne
Nan ma tace eh
Ta juya aranta tace zakaci ubanka wallahi ko yanzu ba tsallakewa kayiba.
Yau'wa akwai lemo a fridge eh tace agajarce dan ta fara jin tagaji da tanbayar ta haura sama ciki sauri
Tana shiga ta fada wanka ta tsaftace jikinta da kazantar da ta dauko
"Ta fada gado ita salla bama 'a zancenta dan kwata-kwata bata tunanin ta ma"
"Sai karfe1:00am ta tashi ta sauko kasa cikin sanda ta nufi bangaren Alhaji musaddiq yana zaune yana aikin da bai karasa ba a office
Lemon fresh milk a gefensa yana aiki yana korawa"
"Yajuya gunda hajiya Salma take kwance tana barci kanta bai hau dai-daiba ya mike ahankali ya sunkuya ya dauketa ya Nufi daki da ita"
"Ya shimfidar da ita saman gado harya mike ta janyo hanunsa dear ka kwanta mana kabari gobe ka karasa ya shafi fuskarta to bara naje na dauko takardun sai nabari sai goben"
"Munu tana ganin ya shiga dakin cikin azama tayi wuf ta shiga ta bude lemon ta tuttula masa poison aciki tayi sauri ta fice daga palourn.. Cikin sauri"
"Yana zuwa baiyi tunanin komai ba ya dauki lemonsa ya kora yadan taba aiki tukunnah ya shiga ciki"
"Ya ajiye takardun a ma'ajiyar su yadowo kusa da hajiya ya zauna ya kara janyo lemonsa ya cigaba da sha ahankali saida ya shanye lemon tass tukunnah ya ajiye ya je ya kuskure bakinsa ya dawo ya kwanta akusa da matar sa"
"Jikinsa yaji yayi masa weak sosai ahankali yakeji kamar jikinsa yana canja masa alamar rashin lafiya yakeji ajikin sa da kyar ya iya bacci saboda yanda yakeji"
"Allah sarki Alhaji musaddiq π ina tausaya maka"
"Munu tayi maka cizon dan maciji"
"Allah dai ya kyauta"
"Tun daga ranar Alhaji musaddiq yafara rashin lafiya a tsaye batare da yabari iyalansa sun sani ba"
"Yafara gazawa dan kullun acikin abunshan sa sai ya sha wannan gubar batare da yasani ba duk sa idon delu wannan lokacin Allah bai bata ikon gani ba hajiya salma tafara fuskanci bashida lafiya"
"Amma shi ya ki ya Amince da hakan yana kwance ramar sa ta fito sosai hajiya salma ta zauna akusa dear yakamata kaje asibiti baikamata ka zauna agida ba"
"Ya janyo hanunta shikadai yasan wahalar da yakeji numfashin sa jiyake kamar zai dauke masa da kyar yake jansa ya some magana ahankali dear ki daina damuwa nagaya miki ba wani Abu bane ba"
0 comments:
Post a Comment