"Ta karaso gunsu tace kuyi hakuri Allah yana tare da ku hakika ku kanku kunsan hajiya ta canja matuka Amma babu wani abunda zaku iya yi akan lamarin kadarar kuce kuyi hakuri ku cinye wannan jarabawar Allah yana tare daku"
"Ashrab ta goge hawayen fuskarta tace nasani delu tabbas akwai wani bakon Al-amari atare da mahaifiyar mu bakon lamari yashi shigo rayuwar mu wanda bamuda wani wanda zai taimake mu sai Allah"
"Da farko rasuwar mahaifin mu, nabiyu ciyon yar'uwata wanda har zuwa yanzu babu wanda yasan sillarshi, na uku rashin samun kulawar mahaifiyar mu, ki gaya mun delu tayaya zuciyoyin mu zasu daina kunah da radadi? "kowa yasan yanda mum take kaunar mu kowa yasan yanda take kula da damuwar mu Amma yanzu ki duba ki gani aure mum zatayi batada muradi ayanzu irin tayi aure kuma ma abun takaicin da yaron da bai wuce sa'an kaninta bah"..... Ya zanyi da damuwa delu ya zanyi?"π......
"Delu zuciyar ta a dagule tace kuyi hakuri hakika kunga canjin yanayi amma bashi zai sa kuki yarda da kaddarah ba"
"Har yanzu kuna da wanda baya gyangyadi barantana bacci Kuma yace ku rokeni na Amsa muku kinga kuwa ko yanzu baku makara ba"
Farha tana zaune tanajin su Amma bazata taba iya yin magana ba bakin a daure takeji amma tana fahintar su
"Hawaye suka zubo mata kanta yana juye yawu na zuba Ashrab ta goge mata hawayen tace kidaina kuka yar'uwata kina da ni har yanzu insha Allahu bazan taba barin kiba....,,
"Kuma Allah yana tare damu"
Delu ta mike bara naje na karasa sauran aikinah, to delu na gode da kulawar ki gare mu
"Murmushin yake tayi tace kada ki damu jinku nakeyi kamar ya'yanah dana haifa"
Tafice daga dakin tanajin tausayin su cikin ranta..... Tana fita daga dakin suka hadu da mun
Wani kallon raini tayi mata tace daga ina kike tun dazu ana jiranki kitchen" na dan wanke bandakin su Ashrab ne yanzu zanje kitchen din.......taja dogon tsaki mtssssss tsohuwar kawai tace tayi shigewar ta delu ta girgiza kanta tace azuciyar ta Allah ya shirya"
Dakin hajiya Salma ta nufa tana kwance a kan sofa tashiga ciki tare dayin sallama tace mum kina hutawa ne
Eh munu ya akayi tace da ita tamike zaune
Lafiya da naso muyi magana akan sauran shirye -shiryen da bamu yiba
"Ok ba damuwa ai inaga kadanne abunda yarage koh Eh sai zancen dinner da kikace ko an fasa da sai naga kawai a fasa kinsan surutun mutane kuma kinga ciyon Farha za'ayita zance awaje"
" Ta hade girar sama data kasa saikace itace hajiyar "
"Amma mum kin ban mamaki yanzu maganar wasu banzayen ce zata hanaki rawar gaban hantsi ni aganina ki daina tunanin wasu can kiyi kawai abunda kike muradi dan idan kika daka ta mutun to ba abunda zakiyi wallahi,...... "Kuma da kike zancen ciyon Farha kema kinsan ciyon Farha ba mai warkewa bane dan Haka kadama ciyon ya dameki kawai kiyi harkar gabanki......"
"Ta nisa kumafah gaskiyar ki danni wallahi ciyon nan nata yafara isata yanzu haka tunanin nake nasamo mata mai kula da ita zaifi saboda na gaji dayiwa katuwar budurwa tsarkin kashi,..... Munu ta shegeke da dariya mai karfi tace kingane kenan"
"Dama kuma wannan ai ke kika soh tun farko naso a kaita gidan kula da musakai kikace a'a zaki iya dama nasan bazaki iya ba wallahi..,,
"Nifa da koni na haifeshi bazan dinga wahala akan shiba"
"Hajiya Salma tace nima ai kinga yanzu abun yana damuna ni yanzu bama wannan ba tunani nake ko na mayarda su itada Ashrab can bangaren baya kinga hankali kwance sai Ayi hidimar bikin nan lafiya qalau basai sun takurawa kowa ba"πInnahlillahi wa'innah ilaihi raji'un MUNUBIYAH kiji tsoron Allah......,,
Tace kai Amma mum kinyi shawara mai kyau hakan yayi tace bara na tashi naje na gayawa delu tafara gyaran bangaren dan nasan yade a rufe....
Gaskiya ba'a taba zama ciki ba da wasu yan aiki danayi suka zauna amma yanzu ba kowa aciki... Tayi dariyar samun nasarah tace good
Bari na hanzarta,,
Tana fitowa daga dakin ta sheke da dariyar mugunta a fili tace kadan ma kuka gani wallahi sauran tozarci da wulakanci yana gabahπ¨
Lokacin da na mallake komai na dukiyar gidan nan na kuma kawar da duk wani makiyi nah Alokacin ne zan takarawata son rainah.....,,
Muje zuwa dai da Munubiyah kuke zancen barka kunama kenan
Kai tsaye dakinsu ta nufah bako sallama ta shiga tana shiga ta fara toshe hanci ta yamutsa fuska a wulakance tace warin me nakeji haka kamar an fasa dungen kwai..... Ashrab ta dago wari kuma Aunty aikuwa ba warin komai a dakin nan inaga dai hancin ki ne.....
"Ta yamutsa fuska ba wani hanci nah naji warin ne shi isa na fada yanzu dai ba wannan ba kufara hada kayanku zaku koma dakin baya saboda sha'anin biki kinga bazai yuyuba ace ana tsakiyar biki Farha ta batawa mutane guu da kashi ba gakuma yawun nan dasuke fita kamar fanfoh hajiya tace ku koma baya saboda kada ku takurawa mutane ana cikin sha'ani"
FARHA tana zaune acikin kujera ta runtse idanuwanta hawaye masu zafi suka gangaro mata Ashrab bakinta yana rawa tace mum ce tacedake haka
Ni ce sukaji muryar hajiya salma ta dago cikin mamaki tace mum kece kuwa?" da bakin ki kike cewa mubar cikin gida mukuma baya mum ina soyayyar da uwa takeyiwa danta take ina tausayi da tsantsar tausayinda kike mana yatafi.... Munu hehehehe tsaya malama daga magana zaki fara wasu zantuka tajuyo ta kalli hajiya Salma shige ki tafi barni da su"
"Haka hajiya Salma ta wuce sum-sum-sum batare da gardama ba ta bar dakin ....."
"Tana fita Munu tace Naga Alama har yanzu bakuyi bakinki bai mutuba wallahi Idan bakiyi hankali ba ke ma sai kashinki ya bushe
Dan haka ki kiyaye ba'a yimun gardama...... Tajuya ta bar dakin zuciyar ta a hasale"
"Delu na makale jikin labule ta fito cikin sauri tace Ashrab dan Allah bana son kina mayarwa munubiya da martani idan tayi magana na fuskanci muguwace kuma zata iyayin komai dan haka ki kiyaye bara nayi maza naje na gyarah muku sashen ba komai kuyi hakuri wata rana sai labari ta juya tallalaba ta bar dakin"
Tana fita Ashrab ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ta rungume yar'uwarta tace Ya Allah kazama gatan mu Ya Allah kayimana maganin wannan lamari ya Allah ka gaggauta bimana hakkin mu.........
ZAKU RINGA SAMU KO KADAN NE INSHA ALLAH KUYI MANAGE
PLSSπ
TAKUCE A KULLUN
LAURAT M BELLO
SHARE&
COMMENT...........
πππππππππ
BANGARE NAH
(part of me)
πππππππππ
STORY&WRTITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO
DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
ALKWARI
AND NOW
BANGARE NAH
(part of me)
BISMILLAHIR..... RAHMANIR..... RAHEEM....
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*π¦{Arewa ginshiΖin al'ummah}π¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
.............2️⃣9️⃣⏩3️⃣0️⃣..............
_____________________"Ameen na furta ahankali yaran suna bani tausayi matuka amma ba abunda zan iyayi kada nima na hadu da makircin munubiya"
Tun a ranar aka kwashe musu kayansu aka mayar dakin baya tamkar marasa gata dakin daya ne kuma karami da karamin bandaki aciki....
BASSAM yana zaune a babban palourn zuciyar shi tana matukar tausayin yaran amma bazai iya yin komai ba a gaskiya yana tausayawa rayuwar yaran kiri-kiri an rabasu da gatan su batare da daliliba haka kawai saboda son rai dakuma son abun duniya....
Munubiya tashigo palour tanta sheka dariya babu wani abunda yake damunta duniyar tana gara mata yanda take so Bassam ya kawarda kansa tamkar bai ganta ba haka kawai haushin ta yakeji
Ta kula da hakan sarai amma ta basar ta karasa gunsa ranka ya dade mijin tsohuwa
Yayi mamakin maganar ta baice komai ba ta zauna dan nesa dashi sannu da zuwa yau'wa yace batare da yakara wani dogon motsi ba... Ta gado wai lafiya naga sai wani shan kanshi kake
Ya kalleta na tsayin lokaci yace munubiya yakamata ki sassautawa iyalan nan haka, inaga abunda kike nema kinsamu ki rabuda zuri'ar gidan nan haka na rokeki da Allah,..... Tuni idanuwan ta suka canja ta dago cikin mamaki tace BASSAM da bakin ka kake tunkarata da irin wadan nan zantuka, sanin kanka bazasuyi tasiri a zuciyata ba dan haka kada ma kabata lokacin ka gurin gaya mun maganar da bazata yi tasiri bah,.... Kuma da kake zancen na samu abunda nake so inaga mantawa kayi har yanzu ban cika buri nah ba hajiya salma tana nan da ranta fah kuma har yanzu su Ashrab basu dan-dana dacin talauci ba har yanzu suna nan da gatan su
"A yanda nakejin zuciyata wallahi bazan taba barinsu ba har sai na tagayyarah su sun wulakanta sun tozarta duk wata gata dasuke tutiya da ita tatafi komai nasu ya dawo mallakina sannan zan samu nutsuwa....... π¨ya dago cikin mamaki yace haba munu meya ragewa yaran nan yanzu komai na gidan nan yadawo hannun ki gatansu ya subuce musu kulawar mahaifiyar su sun daina samu basuda wani abu yanzu illah kunci da bakinci dan Allah ki sassautawa yaran nan wallahi ina yimiki gudun ranarda Allah zai wai-wayeki yayi miki kamun kazar kuku..... "Ta tintsire da dariya wow nayi mamaki da bakin ka kake fadar haka, to kayi a hankali idan baka son kaima ta shafeka dan na kula yanzu zuciyarka ba irin ta maza bace,...... Tamike zantafi Amma kasa azuciyar ka babu wani mahaluki da isa ya dakatar dani ciki kuwa har kai tafice daga palourn. hankalin takwan Ce..,,
"Dafe kansa yayi zuciyar shi tana masa wani iri baya son wannan halin na munu ayimaka rana kai kuma kamayar da sharri ai wannan ba halacci bane yakuma kudirah aransa zai taimaka iya iyawar shi....
"Tana fita dakinta ta wuce ta sabi mayafinta ta bar gidan,.... Tana fita ta tari adai-daita tashiga sunyi tafiya mai nisan gaske sannan tace dashi tsaya ya tsaya tace dashi kada ka tafi ka jirah ni anan. ya dago hajiya ba dai nisa zakiya ba dan sauri nake tajuyo afusace kaga malan ina nema ka fito ka jirah kamar yanda nace zanbiyaka ko nawane kudin ka harma da kari idan kayi hakuri........ Tajuya abunta shikuwa mai adai-daita yanajin maganar kudi ya kara gyarah zaman sa to sai kin fito, tana ta lulawa cikin dajin can na hango wata karamar bukkah a tsakayar dajin ba gida gaba babu a abaya tana isa naji tace gafara dai mugun shaidani wata irin dariya naji ta fito daga cikin bukkatar can naga mutun a zaune gajere sosai kamar ka kifashi da kwano yana washe bakaken hakoranshi yace dama na gaya miki zaki dawo......
Yakara babbaka dariya mai rikitar wa nida nake binta dan na dauko rahoton komai kamar na saki fitsari a wando saboda tsoro Amma ita munu ko a jikinta ta zauna nadawo akwai matsala mugun shaidani *BASSAM* yana son yabani matsala wallahi tun yanzu yana neman ya bujirewa bukata ta.,
Yayi wani ihu wata kwarya ta bayyanah yakira sunan *BASSAM* har sau uku amma wayam babu abunda ya ya fito ya dago yace hajiya saidaifa kiyi hakuri wannan yaron bazai taba saduda ba ki kawo wata bukatar tadago kamar yaya yanda kikaji na fada tace harda *ASHRAB* ma tana neman ta ruguza mun aiki yayi dariya yace ai babu wani wanda ya isa ya ruguza mun aiki wannan ai karamar kwaruwa ce mekike so ayi da ita kasheta za'ayi ko a haukata ta taringa bin bola
"Ko daya so nake a rufe mata baki ta daina cewa uffan, takoma kurma idan ta haukace mutane zasu dago akwai wani abu a kasa to banason kowa yayi tunanin wani abu akayi"
"Sannan sai hajiya inason bayan aurensu tayi sining din dukan kadarar su tabani komai nasu yadawo da sunana sannan daga karshe a kasheta bayan nagama karbar komai na dukiyar ta.....
"Angama sai kuma me kike so shike nan mugun shaidani yayi dariya zakiga shaidanci kuwa yayi wani irin abu saiga hajiya ta bayyanah yace itace wannan ai koh munu ta leka Eh itace yace ki dauka komai yafaru Amma da sharadi"
Ta dago sharadi kuma Eh aikin zai bada wahala domin kuwa har yanzu tanason ya'yanta dan kawai mundanne tane anyimata fin karfi Ranar da duk ta kara Ido biyu da ya'yanta to ina tabbatar miki aikinda akayi akanta ya war-ware zata koma kamar da kuma zata fahinci komai dan haka idan kin Amince yanzu zan cika aiki ana daura auren komai zai dawo hanunki "
"To abatar da yaran mana banason aikinah ya war-ware mugun shaidani,...... "Na gayamiki yaran baza'a batar dasu ba kikawo wata bukatar hankalin munu ya kai kololuwar tashi tace nifa gaskiya inason dukiyar nan bana son asami Matsala......ki kaddarah kin gama samun nasara ai aikinah kamar yankan wuka yake"
" Ya dauko wani kullin ruwa yabata yace kizuba mata a abinci idan dai taci har abada bazata taba tuna tanada wasu ya'yaba a duniya ko zancensu bazata taba tayarwa ba...... ,Ki tabbatar taci domin kuwa idan har bataci ba to asirinki yana gab da tonuwa dan tabbas zata dawo hajiya salman ta da kika sani kuma zata gane kece silar komai"
"Kada kadamu zan kiyaye yakara bata wani maganin yace wannan kibawa yarinyar zakiga abun mamaki tana murmushi ta karba ta ajiye masa makudan kudi ta tafi zuciyarta wasai har tafara jin kamshin kudi atare da ita.....tana zuwa mai adai-daitar yaja suka dawo....
"Tana shiga ta taradda hajiya salma a tsaye tana kallon bangaren da su Ashrab suke, atake gaban munu yafadi cikin sauri tace hajiya lafiya naga kamar kina cikin damuwa? Eh wallahi jina nake kamar can bangaren yana bukatata ta nuna bangaren da su Ashrab suke jiki munu har rawa yake ta ja hannunta muje ciki hajiya kina bukatar hutu,
"Haka ta janyeta suka shiga ciki suna shiga tace muje ki kwanta kinga garin akwai rana ta turata daki tasanya makulli ta rufe kofarπ¨.......
TAKUCE A KULLUN
LAURAT M BELLO
HABA MY FAN'S KUN DAINAH COMMENT FAH INASON NAGA CANJI
SHARE
VOTE&
COMMENT..........
πππππππππ
BANGARE NAH
(part of me)
πππππππππ
STORY&WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO
DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
ALKAWARI
AND NOW
BANGARE NAH
(part of me)
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*π¦{Arewa ginshiΖin al'ummah}π¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
BISMILLAHIR.... RAHMANIR....RAHEEM...
...........3️⃣1️⃣⏩3️⃣2️⃣...........
___________________"Tajuya cikin sauri ta nufi kitchen tun kafin ta karasa tasoma kwallawa delu kirah delu! delu!! delu!!! na'am ta amsa ta fito cikin Sauri..... Kingama abinci ne eh tun dazu to bani na hajiya zan kaimata bata dan jin dadi ne"
"Delu ba abunda ta kawo aranta ta zubowa hajiya salma abincin ta bata tace Allah ya sauwake Ameen tace ta bar gurin cikin sauri....... „
"Saida ta biya ta dakinta ta zuba maganinda boka yabata ta juya sosai ko ina yaji sannan ta gyarah rufin abincin ta dauka ta nufi bangaren hajiya salma dashi......„
"Ta sanya makulli ta bude dakin hajiya tana zaune ta buga tagumi tarasa me yake damunta amma tabbas tasan tanada damuwa tana ganin munu ta shigo tamike yau'wa munu dama ke nake jira wallahi inaji ajikina narasa wani abu atare dani amma kuma ban san ko menene ba,.... "Jikinta har rawa yake muje kici abinci kina bukatar hutu a'a munu bana jin yun'wa yanzu muje kici hajiya inyaso kina gama ci sai muje neman abunda kikejin kin rasa din.....„
Ta janyo plate tayi shiru na tsayin lokaci kamar mai tunani sannan ta fara cin abincin.......
"Munu! tayi murmushin samun nasara aranta tace Alhamdulillah....."saida hajiya salma taci abincin sosai sannan ta ture tace munu bani ruwa nan ma tabata ruwan maganin ta daddaka sosai sai ta mike munu tana murmushi hajiya ina zuwa tace zan dan kwanta ne bacci nake ji......„
"Kin fasa fitar ne? ta dafe kanta bazan iya fitaba kaina nakejin wani iri zan dan kwanta tayi hamma tace kije kawai„...... "Tayi dariya a bayyane tace ba matsala zan tafi kamar yanda kika ce a fito lafiya...... "Ta fice daga dakin tana dariyar mugunta......„
" *BASSAM* kullun cikin tunani yake yaran hajiya salma suna bashi tausayi matuka gashi bayada wani tudun dafawa tabbas yasan halin munubiya zata iya aikata komai akan abunda takeso"
"Yazama wajibi yabi duk abunda zaiyi ahankali batare da ta fahimci komai ba.......,,
Ya tashi jikin sa ba dadi yanufi gidan hajiya salma tun daga kofar gate ya hango Ashrab tayi zaune tayi tagumi abun duniya yayimata yawa hawaye masu zafi suka mata tasanya bayan hanu ta goge ......zuciyar shi a raunane ya karasa gunta tana hangoshi ta mike ahankali ta fara magana kada ka matso kusa dani kaine silar komai babu abunda zaka gaya mun.....,,
"Jikinsa yayi sanyi matuka dama zai iya gayamata komai da yafada mata asalin yanda abun yafaru,.... Amma bazai iyaba saboda gudun faruwar wani abun yayi shiru na tsayin lokaci batare da yace komai ba...... "Sannan yasoma magana kiyi hakuri Ashrab bana nufin cutarwa agareku hasalima inajin tausayinku keda yar'uwarki Farha Amma nasan ayanzu bazaki taba fahimta taba saboda Kina ganin kamar nine silar faruwar komai"
Ta share hawayen da suka gangaro mata cikin rawar murya tace duk wanda yakeda hannu gurin ganin ya cutar damu munbarshi da Allah saboda shine babban sarki baya bacci barantana gyangyadi ta mike ta shige ciki tana sharar kwallah.......
Tausayinta yakara lullube zuciyar BASSAM ya kara jin zuciyar shi takara yi masa rauni haka kawai yana jin tausayin yaran hakan nan ya karasa shiga ciki..... Jikinsa a sanyaye ya karasa cikin gidan.... Hajiya salma tana zaune tana kallon labarai yayi sallama ya shigo tana ganinshi ta mike cikin sauri taje gunshi ta rumgumeshi..... Ya sanya hanun shi ya zagaye ta ya rungumeta sosai yana shafa bayanta...... Ya akayi ne dear...... tana jikinshi tasoma magana ina bukatar ka a kusani ne kawai nayi kewar ka sosai yayi dariya yace to gani nazoh me zan samu ta dago cikin shagwaba...... Ai karigada kasamu komai tunda munkusa zama abu daya
Ya lumshe idanuwansa haka ne muje muzauna nazoh miki da wata muhimmiyar magana...... Munu tana rakube tana ganinsu zuciyarta kamar ta fito waje saboda bakin ciki....... Hajiya salma tana jikinsa suka zauna ahankali ta dago ta kalleshi dear wallahi ina sonka bana son wani ya shiga tsakanin mu na rashin kyautawa dan Allah kayi mun Alkawarin bazaka taba cutar dani ba ayanzu banida kowa saikai kaine kadai bakejij zaka iya taimako na...... Jikinsa asanyaye yace bana nufin cutarwa atare da ke dear ko kadan bantaba tunanin yin hakan ba dan haka kiyi hakuri ki kwantarda hankalin ki na miki alkawarin bazan taba bari wani abu na cutarwa ya kusanceki ba........ Ta kara narkewa ajikinsa ina fatar haka haka kawai nakejin kamar akwai wani abu dayake neman cutar dani........ Hummmm!! Ki daina irin wannan tunanin inaga hasashe ne kawai kike yi dan haka ki kwantar da hankalinki..... Haka suka cigaba da hirar su mai dadi yayinda munubiya take can cikin bakin ciki tanaji tana gani wata kwance jikin BASSAM ba itaba abunda tafi kishi dashi akan komai yau agaban idonta suna nane da juna hawayen takaici suka gangaro mata.....
Acan kasan zuciyarta tace amma ba komai munu kwantarda hankalin ki wannan ba permanent abu bane zai wuce cikin kankanen lokaci akwai lokacin da zaki maye gurbin hajiya salma kema ki dama kamar yanda ake damawa da ita ki mallaki dukanni dukiyar ta...... Tayi murmushi tare da jan doguwar hajiyar zuciya hummm!!
Tana cikin wannan wasikar jakin mahaifiyarta ta shigo dakin tare da yin sallama tamike a zuciye yazaki shigo mun daki ba neman izini hajiya Aisha ta ce idan ma nayi sallamar zakiji ne kin lula cikin tunani sai faman murmushi kike kamar wata sabon kamun hauka....."naji meya kawoki dakina?"
"Na jima da zuwa naga banganki ba banga su Ashrab ba nace bara nagani ko bacci kike ashe idonki biyu..... Ina su Ashrab ne naga dakinsu ba kowa aciki suna ina ne?"
Ta dago idanuwanta da suka canja cikin kankanen lokaci tace suna bayan gida na mayar dasu can saboda banga amfanin su ba shi isa na mayar dasu can jikin hajiya Aisha har rawa yake tace inalillahi wa'innah ilaihi raju'un kina da hankali kuwa munubiya wannan wace irin rayuwace yara da gidan ubansu a mayardasu dakin masu aiki ita hajiyar tana aikin me?
Saida ta gama sannan munu tace kin gama bambamin naki to wannan ra'ayi nane ba na hajiyan ba kuma babu wani wanda ya isa ya ce ba hakaba...... Idan kin gama sai ki fita kuma bana son da kuskure ki kara tayar da zancen su Ashrab agidan nan idan kuma ba haka ba wallahi kinsanni sarai....... Gaban hajiya Aisha yafadfi damm!! Dan kuwa tabbas tasan halin yar'ta zata iya yin komai dan haka sum-sum ta bar dakin amma zuciyar ta cike da tunani kala-kala"
Hajiya salma ta manta da rayuwar su Ashrab kwata-kwata babu kuma wani mai tayarda zancen su agidan saboda shine umurnin damunu ta bayar.....
Haka aka fara hidimar bikin hajiya salma da BASSAM yan'uwa sai shige da fice akeyi a gidan amma babu wani awanda ya ko tanbayi Ashrab da Farha kowa sabgarshi kawai yakeyi.......
Abangaren su Ashrab kuwa tana can daki rungume da yar'uwarta yau sun tashi jikin Farha yakara rikicewa gashi kuma babu magani sai kuka takeyi sosai tarasa yanda zatayi da ita ta kwantar da ita tace bara naje na gayawa mum tabawa baba direba a siyo miki magani..... Ta mike tana sharar kwallah ta nufi kofar fita daga dakin ta ja sosai tajita gam takara jijjigawa kofar arufe take gam da makulli anrufe ta baya Ashrab cikin tashin hankali ta shiga bubbuga kofar tana kiran baba direba Amma kasancewar suna baya babu kowa haka ta gaji da bungun kofar ta koma koda taje gun yar'uwar tana kuka mai tsuma zuciya tace sun rufemu FARHA ba kowa anan saidai muyi hakuri Farha tana daga kwance hawaye suka gangaro mata yuwu suna zuba ga jikinta yayi zafi zau alamar zazzabi mai zafi yakara rufeta cikin dan kankanen lokaci tafara suma hankalin Ashrab yakai kololuwar tashi duk ta rike ce babu abunda take saidai kuka babu wani mataimaki..... Barantana yakawo masu dauki........
TAKUCE A KULLUM
LAURAT M BELLO
SHARE
VOTE& COMMENT..............

*ALHAMDULILLAHI ALAHKULLI HALIN*
..........3️⃣3️⃣⏩3️⃣5️⃣..........
_________________________" A ranar kwana sukayi a kulle babu ci babu sha haka suka kwana cikin matsananciyar yunwa,........ "Itakuwa hajiya tana can tana shan Amarcin ta itada Angonta *BASSAM* tama manta da rayuwar wasu su Ashrab...."
Delu ta zaga tabaya zatayiwa munubiya shanya taji bugun kofar da *Ashrab* take tana kuka batare da tayi shanyar ba ta karasa gurin cikin Sauri cikin daga murya Ashrab waye ya rufe ku innalillahi wa'innah ilaihi ra'ju'un Ashrab tana kuka kubude mu dan Allah kada Farha ta mutu ki taimaka mana delu"
"Da gudu ta juya tanufi gurin baba direba tana haki baba dan Allah kazoh ka bude yaran nan kada Farha ta mutu bata da lafiya kuma kofar arufe take subahanalillahi bara na lallibo safayar makullai ya shiga dakin shi ciki sauri ya hau binciken inda ya ajiye makullan gidan......,,
"Da kyar ya gano makullin yafito cikin sauri suka nufi bangaren"
Saboda dadewar makullin da kyar ya iya bude dakin *FARHA* tana kwance saman katifar a sassakame kamar matacciya yayin da *ASHRAB* take yashe a tsakkiyar dakin asume saboda wahala...... Delu ta rugo aguje cikin tashin hankali tana kiran sunan ta ina tuni ta dade da fita daga hayyacin ta....
Cikin matsanancin tashin hankali ta shiga jijjigata amma shiru baba direba a rude yace yakamata mu dauki yaran nan zuwa asibiti kada wani abu mummuna yafaru dasu..... Haka yadauki Ashrab ya fita da ita kamar baby yadawo yadauki farha a mimmke kamar gawa suka fita.... Delu tana kuka tace bara nayi sauri na gayawa hajiya yakamata ta sani...... Tashiga cikin gidan cikin sauri tana shiga cikin palourn sukayi kicibus da munubiya ta dauko plate din abinci daga gani tashinta kenan........ "Tana ganin delu arude ta tareta ke lafiya ina zakije kuma? Gun hajiya zanje su Ashrab ne ba lafiya gasu can baba direba zai kaisu asibiti shine yace na sanar da hajiya halin da ake cikin"
"Wata mummunar faduwar gaba taji dammm!! damm!!!. daga hannu tayi dakata malama bakida hankali ne? Ba wata hajiya da za'a gayawa wallahi babu wani ciyo karya ce da rashin mutunci iron nasu oya juya ki koma hajiya bata tashi daga bacci ba...... Aikin banza kuna dai son ku takura musu ne oya bace mun da gani......ta kwada mata tsawa mai karfi.... Jikin delu yana rawa ta bar cikin palourn tana sharar kwallah...... Baba direba yana hangota ya tashi motar tana karasowa tashiga suka tafi batare da tace komai ba.... Kuka takeyi sosai tausayin su Ashrab yagama mamaye zuciyar ta".tabbas koba'a gaya maka bakan da akwai wani abu ta dago jajayen idanuwan ta tasoma magana cikin kuka wannan wace irin rayuwa ce wannan wane irin cin zali ne yara da mahaifiyar su amma basuda halin ko ganin su..... Yanzu kana ganin kememe ta hanani ganin hajiya baranta na sanar da ita halin da akeciki...... Ta sanya hannu ta ta goge hawayen fuskar ta shiru sukayi na tsahon lokaci babu wani acikin su daya kara magana"
A dai-dai wani karamin asibiti suka tsaya baba direba yashiga ciki da sauri ya kira nurses suka turo gadon daukar marasa lafiya ciki sauri aka kwashe aka shiga dasu emergency saboda abasu taimakon gaggawa.......
Zuru-zuru sukayi azaune saboda rashin sanin abunda zai faru...... Bayan awa da shiga dasu likita yafito ranshi abace baba direba yana ganin su ya ya taso cikin sauri likita ya ake cikin....... Cikin fushi yace ku biyoni office yayi gaba abunshi suna ganin haka jikin su yabasu da matsala...... Jiki asanyaye suka bi bayan shi hankalin su atashe da kuma fargaba"........kiran da likita yayi musu,
Yana shiga suma suka shiga ciki ya zauna yabasu umurnin zama suma suka zauna Amma zuciyoyin su cike da tunani"
Ya dago fuskar shi a daure kece mahaifiyar su?"
Delu ta soma girgiza kai a'a yallabai ni mai'aikin gidan su ce ina iyayen su?...... Mahaifinsu ya rasu mahaifiyar su kuma tana nan tana ina yanzu?
Tana gida ranka ya dade tana gida fah kika ce Anyah kuwa yaran tane kuwa ki duba kiga yanda yunwa take neman hallaka yaran wannan wane irin rashin kulawa ne ita marar lafiyar mai lalurar shanyewar jiki har ma naga abun yana neman shafar dayan bangaren ta mai lafiya..... Yayinda babbar tana fama da ciyon zuciya da hawan jini sannan kuma yunwa tana neman tayi mata babbar illah yanzu haka sai mun yimata aiki wani bangare na hanjinta saboda ya cinye dole sai an cire inda ya lallace...... Idan ba haka ba komai na iya faruwa"
Delu kuka ya kubuce mata mai karfi inalillahi wa'innah ilaihira'ji'un likita yaushe wannan lamarin ya faru yanzu yarinya karama tana dauke da wannan lalura haka....... Baba direba yayi shiru na tsayin lokaci baice uffan ba can ya nisa likita menene abunyi ya tambaya a raunane?"
"Likitan yace aiki zamuyi mata cikin gaggawa..... Ayau ba sai gobe ba saboda tsayawa jinkiri yana iya haifarda wata matsalar"
To likita kamar nawa ne kudin aiki kudin da yawa sosai Amma ku bada nairah dubu dari takwas da hamsin saboda aikin nata yana matukar hadari
Delu arude tace inazamu samu wadan nan kudaden likita yaran nan mun gaya maka mahaifinsu..... Ya rasu kuma mahaifiyar yaran tafi karfin kudin Amma bana tunanin zata iya biyan wadan nan makudan kudin.......
"Baba direba! yace ki kwantar da hankalin ki delu! insha Allah za'a samu kudin nan batare da matsala ba a ina baba direba, a ina zaka samu?....... Bai bata amsa ba yace likita kufara shirin aikin nanda yamma zan kawo kudi insha Allah"
Likitan yace ba damuwa suka mike dukansu suka fito a tare daga cikin office din.........
TAKUCE A KULLUM
LAURAT M BELLO
SHARE
VOTE&COMMENT............. π️
πππππππππ
BANGARE NAH
(part of me)
πππππππππ
STORY& WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO
DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
ALKAWARI
AND NOW
BANGARE NAH
(part of me)
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*π¦{Arewa ginshiΖin al'ummah}π¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Ina farawa da sunan Allah mai rahma mai jikan
*SADAUKARWA AGAREKU MASOYAN LITTAFIN BANGARE NAH MUSAMMAM*
*AMATULLAH SAFIYANU*
*MARYAM TUKUR*
*MRS ABDULWAHAD*
Hakika comment dinku yana kara bani kwarin gwiwa ina matukar kaunar ku dari bisa dariπ₯°πΉ
........3️⃣6️⃣⏩4️⃣0️⃣.......
______________________"Delu tana kuka duk hankalinta ya tashi tunani take ta ina baba direba zai samo kudi masu yawa haka"
"Baba ya kai duban shi gareta bara naje zan kawo kudin insha Allah kada ki damu Allah yabaka sa'a baba direba Allah yasa a dace"
Ameen yace yafice daga cikin asibitin yana fita kaitsaye gidan sa dayake kusa da gidan Margayi Alhaji musaddiq ya nufa ya bude ya shiga har nakawo kai naji an bamo kofa dole na tsaya a wajen ina jira amma naso naga abunda baba zaiyi acikin gidan nan........ Baifi mitina talatin ba yafito dauke dauke da jaka matafiya yana sauri ya rufe gidan yanufi asibitin hankalin sa a kwance...... π¨ cikin mamaki nabi bayanshi da dinbin tambayoyi a bakina tabbas ina son nasan meye sirrin"
"Yana shiga harabar asibitin delu tana zaune tayi cc tana tunanin hanyar da baba zai samo kudin aikin nan girgiza kansa yayi ya karasa gunda take tana ganinsa ta mike baba ya akayi ankuwa dace? Yayi murmushi yace muje ciki kibari idan hankali ya kwanta zan sanar da ke komai"
"Ta share gumin da ya tsatstsafo agoshin ta ta saki wani irin murmushi Alhamdulillahi mun gode Allah wallahi tunda ka tafi ina nan cikin fargaba na gagara samun nutsuwa kwata-kwata......ki kwantar da hankalin ki yanzu komai yazo karshe insha Allah". ....
Yana kai kudin yasaka hannu aka shiga da ASHARAB aiki cikin gaggawa........ Suka koma dakin da Aka kwantar da Farha tana nan dai kamar yanda aka kawota babu wani canji saidai addu'a, baba direba ya kara gurin gadon da take akwance ya kura mata ido na tsayin lokaci kana yace wallahi delu ciyon nan na *Farha* ya tsaya min arai kiduba ki ga duk wanda ya san *Farha* yasan yarinya ce yar gayu mai ilimi ga sanin ya kamata ga girmama manya Amma yau gata anakashe bata iya yiwa kanta komai batada wani wanda zai kawo mata dauki kuma duk muna kallo mun kasa yin komai yarinya yar'gata amma yau ba gataπkaicon mu da muka gagara taimakawa baiwar Allah....... Delu ta goge hawayen fuskar ta tace wallahi baba ba tun yauba inajin bamu kyauta ba na rashin taimakawa yarinyar nan Amma kuma duk lokacin da nayi wani yunkuri sai kaga nakasa ai watar da komai kuma na kasa sanin dalili....... Baba yace ba ke kadai ba delu ni kaina ina ganin rashin kyautawar mu Amma insha Allah komai ya kusa zuwa karshe da yardar Allah........... Bara a sallame su muga ya za'ayi a nemi maganin hausa a gani ko Allah yasa A dace dan abun yana da matukar rikitarwa ciyon anrasa gane masa kwata-kwata........hakan yayi Allah ya nuna mana..... Ameen yace ahankali"
Likitoci sunyi kokari sosai gurin yin aikin Asharab kuma sunyi aikin cikin nasara anfito da ita saidai fatan Allah yasa anyi a sa'a......
______________________ "ABANGAREN hajiya salma kuwa tana nan tana cin Amarcinta son ranta babu wani abunda yake damunta haka shima *BASSAM* bayada masaniyar ciyon su Asharab hasalima ya shagala da Amarya shi iya shagala saboda kwasar Amarcin sa kawai yakeyi hankali kwance.......,,
Munubiya kuwa tana fatattakar delu tayi komawar ta daki bata sanar da kowa ba a nata tunanin delun ma ba taimakon su zatayi ba saboda tasan bata wani abunda zata taimakawa da shi...... Addu'ar takeyi Allah yasa ma su mutu kowa ma ya huta saboda ta matsu ta yar'da kwallon mangwaro ta huta da kuda"
Sai yamma ta fito su hajiya suna zaune a palourn sunata zuba soyayyar su tana ganin *BASSAM* rungume da hajiya salma saida wani jiri ya debeta kamar ta fadi saboda kishi da kyar ta iya karasawa tana dariyar yake bassam ya kula da yanayinta sarai Amma yayi banza da ita sai yanzu yaga taimakon da munubiya tayi masa nayi masa hanyar auren hajiya salma dan kuwa tabbas yanzu yasan dadin mace ashe duk matan da yake mu'amula dasu lami suke babu wani armashi atare dasu ita kanta munubiyar yanzu sai dole zai iya koma yin wani abun da ita......... Hajiya salma tamike zaune a'a munu ya akayi ne duk yau ban ganki ba.... Azuciyar ta tace zakici ubanki da wannan tambayar kiyi abunki na dan lokaci dan bazan iya ganin wannan takaicin ba..... A fili tayi yake wallahi koyanzu yunwa ta fito dani "
Ayyah kisamu abunda kika ci kinsan zama da yunwa bai yiba
Kada kidamu maganin yunwar yana tare da ke
Me kikace
A'a ba magana nayiba tayi gaba ayyah sai naji kamar kina magana a'a tayi gaba
Bassam ya fahimceta sarai Amma ya kasa tashi saboda shi yanzu wallahi ko sha'awarta baya yi har takai kofar fita ta kara juyowa karaf idanuwan su suka hadu ta jijjiga kanta shikuwa ya daga kafadar shi batare da ta ganshi ba
Tabdijam ashe akwai kurah a gaba
"Yau kimanin kwanansu Asharab goma a asibiti amma babu wani wanda yasani agidan daga baba direba sai delu...... Ita mun tama manta da wasu su Ashrab barantana hajiya salma da jinta take tamkar bata taba yin wasu iyaliba sai yanzu dan kuwa ta manta da komai ayanzu muradinta ta kyautatawa mijinta kawai
Shikansa bassam ayanzu bashida tunani illah ya ga ya kara samun gurin zama a zuciyar hajiya salma badan ya cutar da itaba......
Itakuwa munu kullun tunaninta bai wuce taga komai yadawo hanunta ba kamar yanda suka tsarah Amma haryanzu basu hadu da bassam ba barantana taji ina suka kwana kwata -kwata yanzu shi bata wannan yake yiba tunanin sa kawai yaga ya samu karbuwa matar shi dan haka ma yake kin rabuwa da hajiya salma kullun suna tare da ita babu yanda ta iya saidai kalloh........
Bayan sun gama hutun amarcin su suka koma office duk wasu kadarorin ta, tadankawa *BASSAM* su office din baban manajan kamfani yadawo hanun bassam yasamu guri sosai hakan ya dan ragewa munu radadin rashin bassam a kusa da ita yanzu burinta ta karbo takardun su dawo hannunta sauran kadarorin kuma tabi ta karkashin kasa wajen ganin ta karaba cikin ruwan sanyi"
________________ "A yau za'a sallamo su asibiti Amma saboda rashin gata mahaifiyar su bata ma san suna asibiti ba ta manta dasu shaf arayuwar ta....... Asharab tana zaune tayi tagumi hawaye suna zuba a idanuwanta baba direba ya shigo yana ganinta ahaka tausayinsu ya kama shi janyo kujerah yayi ya zauna yadanyi gyaran murya sannan ya soma magana cikin nuna kulawa kuyi hakuri Asharab hakika nasan kuna cikin jarabawa Amma kuma hakuri shine maganin komai duk kan tsanani yana tare da sauki kuyi hakuri ku cigaba da addu'a insha Allah bazaku tabe ba Allah shizai zama gatan ku........... Ta shafe hawayen da suka gangaro mata tace "bakomai yake damuna baba illah rashin kulawar mahaifiyar mu garemu kada kamanta baba bamuda kowa aduniyar nan sai mum itace ta ragemuna itace farincikin mu mahaifin mu ya rasu mahaifiyar mu ta yada mu ba ruwanta damu ya zamuyi baba me mukayiwa mum dazata koremu daga cikin gidan da mahaifin mu ya gina da gumin sa mun koma yan ai'ki ma sun fimu matsayi a cikin gidan mu.......... Ya zamuyi da wannan bakin cikin, wallahi baba ji nakeyi kamar zan mutu saboda yanda nakejin zuciyata tana mun"
"Ashsha Asharab ki daina fadar haka kiyi hakuri komai zai wuce........ Allah yasa baba Amma yaushe zamu kara samun kulawar mum anan gaba kana ganin fa ko kallon mu bata son yi ta nisanta damu, baba direba yayi shiru na wani lokaci sannan yace ba komai akwai Allah shine zai kawa muku dauki cikin gaggawa....... Ya mike suka fara hada kayan su ya fita karbo takardar sallama sukuma suka karasa had a kayan ita da delu Farha tana kallon su hawaye suka gangaro mata.........
Bayan baba ya dawo suka fito zuwa gida
Sun koma gida delu tacigaba da kula da su tamkar mahaifiyar su ba wanda yasan suna gidan sai delu da baba haka Asharab ta cigaba da kula da kanwar kamar yanda tasaba doctor deen wanda yake duba su asibiti tun da ya ga Asharab yafara sonta shakuwa mai karfi ta shiga tsakanin su hakan ta Sanya kusan kullun sai yazoh ganin su dan ya fuskanci yaran suna bukatar kulawa
Kulawar da suke samu agurin doctor deen yasanya suka rage yawan damuwa...........
Wata rana doctor ya zoh gun Asharab suka fito zata rakashi munu tana zaune a gurin shakatawa tana ganin doctor saida gabanta ya fadi ta mike tsaye haka kawai ta tsinci kanta cikin matsanaciyar fargaba yana kallonta ya dasa A yar tambaya akanta jikinsa yabashi abubuwa da yawa game da ita"
Tana tsaye suka wuce ta gaban ta suka fita daga gidan suna fita doctor yace dear wannan wacece? .....yar kanwar mum ce ya akayi yace naga kamar batada gaskiya kamar yaya? Yayi dariya ba matsala amma inason nasan tarihinta dan tabbas inada shakku akanta
Tooooooπ¨ munu wata kila watan kunyarki yakusa tsayawa
Allah dai yasa karshen wahalar kune ya zoh
KUYI HAKURI DA WANNAN π
TAKUCE A KULLUN
LAURAT M BELLO
SHARE& COMMENT...............
0 comments:
Post a Comment