Cikin tausayawa hajiya tace sannu Farha Allah yabaki lafiya.....Ameen suka ce gaba dayan su itakuwa kallonsu kawai......take har zuwa wannan lokacin ta kasa cewa uffan saboda nauyinda bakinta yayi...
Asharab ta matso kusa da ita tana murmushi kina bukatar wani abun ne
Kallo takara binta dashi batare da tace uffan ba ta share hawayenta tace Allah ya baki lafiya hajiya mahaifiyar doctor tace ki rage yawan damuwa insha Allah zata samu lafiya .....dama sai tayi hakan saboda ta dade tare da lalurar kinga kuwa sai ahankali zata dawo normal ta jima tana lallabata sannan ta kaisu dakin da aka tanadar musu bayan sunci abinci shima kadan Asharab taci damuwarta kawai ta ga yar'uwarta ta warware.......
WANNAN KENAN
Munubiya tayi iya kokarinta gurin son ta hana hajiya salma komawa dakin ta Amma ina dan *BASSAM* yazoh dakin yafi akirga daga karshe ya fito fili yanuna bacin ransa.....
Cikin rauni hajiya salma tace dear kayi hakuri dan Allah kasan yanda nake jin tausayi araina wallahi bana son na barta ita kadai shi isa ya dago cikin bacin rai "yace haba dear kinsan bazan taba iya kwanciya ni kadai ba kada ki manta wannan Alkhawari ne da muka daukarwa kan mu babu wani abunda zai raba mu sai dai mutuwa....idan har kika barni zanji araina kamar mutuwar ce dan nasan ita kadaice zata nisan tamu da jin dumin juna......hanun hajiya salma takara damkewa tana kuka mum wallahi tsoro nake ji dan Allah kada ki tafi kibarni....
Bassam yace kada ki damu delu na nan zata kwana tare dake Amma ina bukatar matata.....
Ta kara fashewa da kuka mai karfi sai can tayi luuuuuu ta rufe idanuwa kamar ta mutu hankalin hajiya salama yakara tashi na shiga uku dear bani ruwa kaga suma take fah......hasashen da *BASSAM* yake yagama tabbata dan yagano tabbas akwai wata akasa ....ya ciji lebansa ya nufi fridge ya dauko robar ruwa ya dawo gunda take baiyi wani tunani ba ya bude robar ya kwalala mata ruwan taja dogon ajiyar zuciya da karfi ta dada kankame hajiya salma kicece ni mum zasu kashe ni na shiga uku.......
Hawaye suka zubowa hajiya salma na tausayi tace kiyi shiru munu ba abunda zai same ki ina tare dake kinji ta daga kai cikin sauri kamar kadan garuwa....
Azuciyar shi yace idan kinsan wata baki san wata ba karamar shu'uma *Bassam* yace ba matsala zanje na kwanta saida safe a fili ta saki wata ajiyar zuciya yana ganinta yayi murmushi yace a ransa hakar ki bazata taba cimma ruwa ba.....muje zuwa......
hajiya salma tayi murmushi tace na gode dear saida safe
Kiss ya manna mata a goshi yafice daga dakin.....
Yana fita munu ta kara gyarah kwanciyar ta saman cinyar hajiya salma tace mum zansha ruwa kuma inajin yunwa....bara naje na hado miki wani abun mai dan sauki kici ta zare ๐จ idanuwa inajin tsoro zasu zosu sace ni dan Allah kar ki tafi...cikin tausayawa tace bara na kira delu sai ta hado miki wani abun ta kira wayar delu tanata ringim amma shiru ba'a dauka ba ta kara kira har miss call biyar amma shiru ta ce inaga tayi bacci kinga dare yayi bara na kira dear ko tea ne yahado miki ko kuma naje da kaina....a'a dan Allah kada ki barni ni kadai.....
Ta shiga neman layin *Bassam* tayi ringin har ta katse yana kallon wayar bai dauka ba takara kira ya lalibo wayar kamar mai bacci yace hello cikin muryar bacci dear ya akayi tayi murmushi tace sorry na tayar da kai, "ba damuwa kina son wani abun ne? Eh munu ce take jin yunwa na kira delu inaga tayi bacci dan Allah ka hado mata tea "ok kawai yace ya kashe wayar.....
Wani murmushi yayi ya mike ya bar dakin ya nufi kitchen..........
Yada murmushi ko dai kaima zaka aikata wani abun ne๐ค
kuyi manage dashi๐
*COMMENT*
*SHARE*
*by Laurat M Bello*
TYPING๐ฒ
BANGARE NAH
Part of me
๐๐๐๐๐๐๐๐
STORY&WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO
Marubuciyar littafin
*SUKHAINAH*
AND NOW
๐BANGARE NAH๐
Part of me
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*๐ฆ{Arewa ginshiฦin al'ummah}๐ฆ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAH*
๐
ฟ️8️⃣1️⃣to8️⃣5️⃣
"Tea ya hada mai kauri ya juyar da bayansa daga inda nake arakube na dan leko naso naga abunda yake amma sam na kasa hangowa hakan nan na hakura .....nasan dai idan tayi tsami ma ji๐
Yana tafiyar kasai ta ya nufi dakin saboda tsabar makirci saida hajiya ta taimaka mata ta mike zaune.....hajiya salma ta karbi shayin ta bata shi kuma ya fice tare dayi musu saida safe.....
Saida ta shanye shayin duka sannan ta ajiye kofin wani lafiyayyen bacci ne ya soma fizgarta zuwa yan dakiku bacci mai nauyi yayi a won gaba da ita.....hajiya salma tayi mirmushi tace Allah sarki ashe tun daxu yunwa ce ta hanaki bacci ta kara gyara mata kwanciya ta koma saman kujera ta kwanta itama baccin yayi awon gaba da ita.....
A hankali ya turo kofar dakin ya shigo yana wani shu'umin murmushi ya nufi inda hajiya salma take akwance ya sunkuce ta yafice daga dakin.....daukar tayi mata dadi sosai tasaki jiki takara makalkaleshi....bai direta ako inaba sai a makeken gadon su cikin kwarewa ya cire kayan jikinta ya sauya mata da wasu masu na bacci shima ya sauya nasa ya kashe musu wuta daga nan kuma suka tsunduma cikin duniyar ma'aurata.....
๐จ๐จtoo akwai damuwa kenan .....
Munu tana dakinta sai sharar bacci take bata masaniyar abunda ke faruwa......yayinda su kuma suke can suna raya daren su cikin farin ciki da kaunar juna...
Washegari sai 8:00 hajiya salma ta soma bude idanuwan ta ganinta a dakinta yasanya tayi mamaki yana kwance a kusa da ita yana murmushi a hankali tamike ya akayi na zoh nan dama ba mafarki nake ba.......
Maganar ta tabashi dariya yace A'a da kin zaci mafarki kike?
wallahi na zaci mafarki ne nake ashe da gaske ne...ya kara janyota jikinsa yace na kasa jurewa ne na je na sato ki๐
dariya tayi sosai tace kai dear yaushe kazama haka kasa mun bar yar' mutane ita kadai.....kuma kasan tana jin tsoro.....rabu da ita haka kawai ayimun kwacen mata shine naje nayo kednaping dinki๐kai dear baka dama wallahi tamike ya janyo hanunta ina zakije kuma zan danyi wanka ne naje na duba ta....
Make kafada yayi yace naki wayon ba inda zaki nasan delu yanzu taje gunta dazu na gaya mata ta kula da ita nikuma ki kula dani anan saboda ina neman kulawar nima....
bayanda ta iya da *Bassam* haka ta hakura atare suka yi wanka suka shirya suka karya sannan suka kara komawa bacci.....
*Wannan kenan*
"Farha ta kai kwana bakyau bata ce uffan ba sai dai ido kawai da take bin mutane dashi
A ranar malan yabada hayaki yace aturara mata ....haka kuwa akayi hayakin na fara shigarta ta soma zunduma ihu cikin kakkausar murya ta ce dakata malan kada ka kona ni malan yayi dariya yace bazan taba kyaleki ba har saina naga kin koma marar amfani.....
ya kara zuba hayakin acikin wutar hayakin yakara turnikewa Farha tamike sambal tana wani irin murkususu ta dago awahale tace turo mu akayi ance mu nakas tata mu wulakanta mata rayuwa......waye yaturo ki bani kadai bace muda yawa dan Allah kada ka kashe ni.......
ya kara zuba hayakin ta kurma kara kana sabular mun da fatar jikina wallahi zan fita daga jikin ta Amma fa bani kadai bace munada yawa ni bakinta kawai na rike amma wallahi bani na rike sauran sassan jikinta ba......
ya tsiyayo wasu ruwa acikin galan ya yi addu'a aciki ya furza mata wata atisha tashiga jerawa babu kakkautawa tayita tafi akirga daga nan kuma tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta...........
Can bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita......
*COMMENT*
*SHARE*
*BY Laurat M Bello*
TYPING๐ฒ
BANGARE NAH
Part of me
๐๐๐๐๐๐๐๐
STORY&WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO
Marubuciyar littafin
*SUKHAINAH*
AND NOW
๐BANGARE NAH๐
Part of me
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*๐ฆ{Arewa ginshiฦin al'ummah}๐ฆ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAH*
๐
ฟ️8️⃣1️⃣to8️⃣5️⃣
"Tea ya hada mai kauri ya juyar da bayansa daga inda nake arakube na dan leko naso naga abunda yake amma sam na kasa hangowa hakan nan na hakura .....nasan dai idan tayi tsami ma ji๐
Yana tafiyar kasai ta ya nufi dakin saboda tsabar makirci saida hajiya ta taimaka mata ta mike zaune.....hajiya salma ta karbi shayin ta bata shi kuma ya fice tare dayi musu saida safe.....
Saida ta shanye shayin duka sannan ta ajiye kofin wani lafiyayyen bacci ne ya soma fizgarta zuwa yan dakiku bacci mai nauyi yayi a won gaba da ita.....hajiya salma tayi mirmushi tace Allah sarki ashe tun daxu yunwa ce ta hanaki bacci ta kara gyara mata kwanciya ta koma saman kujera ta kwanta itama baccin yayi awon gaba da ita.....
A hankali ya turo kofar dakin ya shigo yana wani shu'umin murmushi ya nufi inda hajiya salma take akwance ya sunkuce ta yafice daga dakin.....daukar tayi mata dadi sosai tasaki jiki takara makalkaleshi....bai direta ako inaba sai a makeken gadon su cikin kwarewa ya cire kayan jikinta ya sauya mata da wasu masu na bacci shima ya sauya nasa ya kashe musu wuta daga nan kuma suka tsunduma cikin duniyar ma'aurata.....
๐จ๐จtoo akwai damuwa kenan .....
Munu tana dakinta sai sharar bacci take bata masaniyar abunda ke faruwa......yayinda su kuma suke can suna raya daren su cikin farin ciki da kaunar juna...
Washegari sai 8:00 hajiya salma ta soma bude idanuwan ta ganinta a dakinta yasanya tayi mamaki yana kwance a kusa da ita yana murmushi a hankali tamike ya akayi na zoh nan dama ba mafarki nake ba.......
Maganar ta tabashi dariya yace A'a da kin zaci mafarki kike?
wallahi na zaci mafarki ne nake ashe da gaske ne...ya kara janyota jikinsa yace na kasa jurewa ne na je na sato ki๐
dariya tayi sosai tace kai dear yaushe kazama haka kasa mun bar yar' mutane ita kadai.....kuma kasan tana jin tsoro.....rabu da ita haka kawai ayimun kwacen mata shine naje nayo kednaping dinki๐kai dear baka dama wallahi tamike ya janyo hanunta ina zakije kuma zan danyi wanka ne naje na duba ta....
Make kafada yayi yace naki wayon ba inda zaki nasan delu yanzu taje gunta dazu na gaya mata ta kula da ita nikuma ki kula dani anan saboda ina neman kulawar nima....
bayanda ta iya da *Bassam* haka ta hakura atare suka yi wanka suka shirya suka karya sannan suka kara komawa bacci.....
*Wannan kenan*
"Farha ta kai kwana bakyau bata ce uffan ba sai dai ido kawai da take bin mutane dashi
A ranar malan yabada hayaki yace aturara mata ....haka kuwa akayi hayakin na fara shigarta ta soma zunduma ihu cikin kakkausar murya ta ce dakata malan kada ka kona ni malan yayi dariya yace bazan taba kyaleki ba har saina naga kin koma marar amfani.....
ya kara zuba hayakin acikin wutar hayakin yakara turnikewa Farha tamike sambal tana wani irin murkususu ta dago awahale tace turo mu akayi ance mu nakas tata mu wulakanta mata rayuwa......waye yaturo ki bani kadai bace muda yawa dan Allah kada ka kashe ni.......
ya kara zuba hayakin ta kurma kara kana sabular mun da fatar jikina wallahi zan fita daga jikin ta Amma fa bani kadai bace munada yawa ni bakinta kawai na rike amma wallahi bani na rike sauran sassan jikinta ba......
ya tsiyayo wasu ruwa acikin galan ya yi addu'a aciki ya furza mata wata atisha tashiga jerawa babu kakkautawa tayita tafi akirga daga nan kuma tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta...........
Can bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita......
*COMMENT*
*SHARE*
*BY Laurat M Bello*
TYPING๐ฒ
*BANGARE NAH*
*Part of me*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*BY. LAURAT MUHD BELLO*
*Marubuciyar littafin*
*SUKHAINAH*
*BISMILLAH*
*Wannan shafin nakune dukkanin yan'uwa na AREWA WRITERS ASSOCAITION*
*AUNTY HAW'WA (maman usman shugaba ta gari mai kyawawan halayya Allah ya tsare ya kareki aduk in da kike*
*Amin*
*ummun intisar*
*ummu Affan*
*ummun Naseem*
*Mrs Sadiq*
*Hopscal*
*Fast class*
*Sa'amlad*
*Maryama*
*Lashminzy*
*mummy's freind*
*Rashida usman*
*Wasila ummu Aisha*
*mum islam*
*Maman khalil*
*yan'uwa na gari nakune halak malak kuyi yanda kuke so da abunku*๐ฅฐ
*Ina rokon Allah subahanuhu wata Allah ya kara sanya Al-barka acikin wannan kungiya tamu yakara tsare mu da sharrin mahasada, yan sa'ido da masu mummunan zato ya Allah ka kara tsare duk wani member namu daga dukkanin sharri da abun ki*๐คฒ๐ป
*AMIN*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*๐ฆ{Arewa ginshiฦin al'ummah}๐ฆ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
8️⃣6️⃣to9️⃣0️⃣
"Har wajejen magariba Farha tana bacci bata farka ba hakan kuwa ya tayar da hankalin Asharab matuka ajima- ajima sai ta lekata hajiya mahaifiya Suraj tana kula da ita tace kada ki damu dama yace zata samu bacci sosai kinga dama duk tsahon wannan lokacin ba baccin take samun yi ba dan haka ki kwantar da hankalin ki kinji.....daga kanta tayi tare da share hawayen fuskarta yaw'wa koke fa inji hajiyar Suraj murmushi Asharab tayi tana matukar kaunar hajiya jinta take tamkar mahaifiyar ta hajiya tace dama ina son naji labarin ku Suraj ya sanar dani yace mahaifiyar ku tana nan da rai koh?
Asharab ta goge hawayen da suka kara gangaro mata saboda hakika hajiya ta tuna mata da wani dafin da ya dade a zuciyar ta ya kasa goguwa...."Eh tace ahankali bakinta na rawa....ayyah sorry kiyi hakuri idan tanbayata ta bata miki rai...
"Girgiza kanta tayi tace cikin muryar kuka ba komai hajiya anan tafara bata labarin su har zuwa lokacin da Farha tafara wannan lalurar duk sai da ta zayyana mata komai.....hajiya ta share hawayenta tace hakika Asharab labarin ku ya taba zuciyata matuka na tausaya muku kuma insha Allahu zan rike ku kamar ya'yana....kiyi shiru ki daina kuka duk wanda yashiga tsakanin ku da mahaifiyar ku Allah shima bazai barshi ba tun a duniya zai gani...
"A hankali tace har yanzu zuciyata ta kasa gasgata mun wani zai iya yi mana asiri,bamu taba fada da kowa ba ko a makaranta bama cacar baki da kowa.....wani murmushi hajiya tayi tace Asharab kenan har yanzu je yarinya ce kin manta yanzu mutun ake akiwo ba dabba ba ke dai Allah ya karemu da sharrin makiya da mahasada,amma duniya yanzu ta lalace.
ta kara share hawayen fuskar ta tace wallahi duk wanda yayi silar fadawar mu cikin wannan halin matukar aka sanar dani shi sai ya gane kuskuran sa,
"doctor Suraj yana zaune yayi murmushi yace duk wanda yayi miku haka ba wai yayi ne dan ku rayu ba to ku godewa Allah da kuke raye ayanzu...
"Ta kara share hawayen da suka kara gangaro mata tace Allah zai isar mana saboda shi ba azzalumin sarki bane Allah ka bawa yar'uwata lafiya,Amin Suraj yace yana mai kara tausaya musu.......
"Bayan Farha ta dauki dogon lokaci tana bacci ta farka da wata irin karah mai rikitarwa tana kiran sunan "Anty munubiya! dan Allah Anty kada ki kashe ni dan Allah ๐ญ๐ tana kuka tana rokon ta.
"Fargaba tashin hankali marar misaltuwa sune suka ziyarci Asharab wani kallon kallo suka dinga yiwa junan su ita da su hajiya da Suraj...."bakinta yana rawa tace Farha Anty munubiya fa kika ce...ba Anty anan mu kadai ne Farha cikin kuka tace wallahi itace Asharab tace itace wa itace yaya Asharab itace zata kashe ni dan Allah ki boye ni zata kashe ni๐จ
"Inalillahi'wa'innah ilaihi raji'un ita kadai bakin ta yake iya furtawa ta juyo ahankali cikin mamaki tace hajiya na kasa gasgata abunda kunnuwa na suke jiye mun a yanzu......๐ญta fashe da wani marayen kuka, kuce dani ba gaskiya bane dan Allah kuce ba gaskiya bane....na shiga uku yanzu dama wannan lalurar harda saka hannun Anty munu.....malan da yake azaune shigowar sa kenan yayi murmushi yace Alhamdulillah ta dawo hayyacin ta kenan Asharab ta cigaba da kuka mai ban tausayi tana mai kara jin tsanar munu acikin zuciyar ta ta mike zumbur ta kama hanyar fita cikin sauri...
"Suraj ya tareta cikin mamaki ina zakije kuma? ta dago jikakkiyar fuskarta tace............
tace me?๐ค
kucigaba da bibiyar yar mutanen *ARGUNGU*
*Laurat M Bello*
*Dan Allah kuyi hakuri da jina shirun da kukayi wallahi banida lfiya ne kuyi manage da wannan plssssssss* ๐
*COMMENT*&
*SHARE*
TYPING๐ฒ
*BANGARE NAH*
*Part of me*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*BY LAURAT MUH'D BELLO*
*Marubuciyar littafin*
*SUKHAINAH*
*Bismillahi rahmanir raheem*
*Sadaukarwa gareku ya'yana*
*Fatima* *(khairat)*
*Muhammad(modibbo*)
*Ahmad(Ahsan*)
*Al-hasan(Raihan*
*Wannan page din naku ne yarana Allah ya rayamun ku Allah ya tsareku aduk inda kuke....Allah ya kareku daga sharrin Abunki*
*AMEEN*๐คฒ๐ป
Book one
๐๐๐๐๐๐๐
9️⃣1️⃣to1️⃣0️⃣0️⃣
"Ya zama dole na gurfanar da Anty Munubiya domin ta girbi abunda ta shuka ta karasa ragowar kazamar rayuwarta a kurkuku.....
Karo na farko da mahaifin Suraj yace wani abu ya taso daga inda yake azaune yace" kiyi hakuri ya'ta har yanzu lokacin baiyi ba ki bari yar'uwar ki takara samun lafiya inaga zai fi
Hummmm! Taja dogon ajiyar zuciya tace kayi hakuri Abbii Amma zuciyata bazata taba samun nutsuwa ba har sai naga Anty Munu a karkame dan Allah kayi hakuri ka taimake ni๐ญ๐ wallahi har wani zafi nake jin zuciyata tana yimun
Hanun sa ya daura saman kanta yana murmushi ba wai ina nufin Munubiya taci bulus bane a'a this not the right time ina son sai kanwar ki takara samun lfy tukunnah ki kara hakuri ๐
Sunkuyarda kanta tayi tana sharar kwalla jikinta amace ta koma ta zauna tacigaba da shash-shekar kuka mai taba zuciya....
malan yace to Alhamdulillahi nayi farin ciki matuka abu nagaba shine mahaifiyar ku dakuma kara warrewar ita mai lalurar ku kara kwantar da hankalin ku insha Allah komai ya kusa zuwa karshe da izinin Allah
"A nan ya kara basu hakuri dakuma yi musu nasiha mai shiga jiki daga bisani yayi sallama dasu ya nufi gida
-----------------------------------
Wannan kenan
"Tun shayin da Munu ta dirka yau kwana daya darabi kenan tana bacci sai dai tayi juyi ๐takara mai da kai tacigaba dan kuwa ba karamar kwaya *Bassam* ya zuba mata ba.....
Hajiya Salma na hango sai mutsu-mutsu take tana sharara gumi tana maganganu acikin baccin ta *Bassam* yana zaune yana duba wasu takardu na office yaji sai haki take cikin sauri ya kunna wutar dakin mai haske yayi dai-dai da farkawarta tana ihu na shiga uku ya'yana๐ญ zata kashe mun ya'ya na....
"Rungumeta yayi kam ajikinsa yana magana kasa-kasa shhhhhhhht bude idanuwanki waye zai kashe miki ya'ya ki daina kuka gaya mun waye tana haki tasoma magana wata mata ce nagani rike da yara na ta nufi katon rami zata jefasu sai Allah ya kubutar dasu Amma ni ta jefani aciki dan Allah ka kaini naga ya'ya nah kada a kashe mun su sune farin cikina bazan iya rayuwa ba su ba๐ญ๐
"Tirkashi! Yafada azuciyar sa yace yabdijam Hummmmm!
Ta kara jijjagashi da karfi nace dakai ka kaini gurin ya'yana kara rungumeta yayi jikinsa yana shafa bayanta ki nutsu zan kai ki amma sai kin nutsu daga kai tayi cikin sauri tace na nutsu dan Allah muje wallahi bazan sami nutsuwa ba har sai nagansu agogon bango ya kalla yaga to 3:00am na asuba yace kiyi hakuri yanzu dare ne kada mu tashi yan gidan suna bacci ki bari zuwa asuba sai muje ki gansu ta share hawayen da suka gangaro mata takara kwantar da kanta ajikin sa tana sakin ajiyar zuciya jefi-jefi...a hankali ya cigaba da tofa mata addu'a har bacci yakuma awan gaba da ita.......
"Karfe 4:00am Munubiya ta farka a firgice cikin matsanancin tsoro da fargaba ta waiga bakowa adakin sai ita kadai hanu ta daura akanta tashiga sallallami tana cewa na shiga uku wannan wane irin baccin asara ne nayi haka ta janyo wayarta akashe taja tsaki ta kunnata bayan ta kunnah ne ta ajiyeta ta shiga bandaki ta kama ruwa ta dawo amma zuciyar ta still tana cikin tsoro a fili tasoma tanbayar kanta tace ina hajiya Salma taje "daga bakin kofa ya amsa mata tana dakinta tana bacci cikin kwanciyar hankali da farin ciki kasancewarta mai tattali agurin mijin ta a razane! Ta dago gaban ta na wani irin bugawa kamar ana buga ganga dam! dam!!dam!!!
Girgiza kanta tasoma yi shikenan ka kashe ni *Bassam* ka ruguza mun aiki na shiga uku...Hhhhhhhhh yace da karfi kana ya cigaba da magana yace banine na ruguza miki aiki ba Allah ne ya ruguza shirin ki......saboda kasancewar sa sarki mai adalci wanda baya taba barin azzalumai su ci galaba hakika ko a wancen lokacin talala Allah yayi miki yabarki saida kikayi haka mai zurfin gaske kika angiza kanki da kanki aciki....ki sani Hajiya Salma ayanzu Allah ya kubutar da ita daga zaluncin ki domin kuwa a yanzu babu wanda take muradin gani a idanuwanta sai ya'yanta dan haka aiki yarage naki ya juya yayi gaba abunsa
kwasa tayi aguje ta nufin kasan gadonta wayam babu kwaryar tsafinta ta kurma ihu nashiga uku delu ce ta fado dakin kamar an jefota tana tanbayar lafiya Munubiya?
Ko kallonta bata yiba ta shiga harhada kayanta cikin a kwati jefasu kawai take tamkar kamun hauka tana sambatu karfe 5:00am ta fito daga cikin dakinta cikin matsanancin sauri kicibus sukayi da hajiya Salma๐จ ta zaro gwala-gwalan idanuwan ta waje kamar zasu fado hajiya Salma tana ganinta tayo kanta ina ya'ya na suke ki fito mun da ya'ya na bakinta yana rawa ta saka kuka ban gansu ba ki duba dakin su nima yanzu mama nace tayo waya tana son ganina cikin gaggawa shine zanfita ki duba suna ciki cikin sauri hajiya Salma ta saketa ta nufi dakinsu Asharab cikin sauri.....Munubiya tana ganin haka tayi wuff tayi waje kamar zata tashi sama.....
Delu tace ikon Allah yau jama'ar gidan nan ba mai lafiya.....cikin sauri ta nufi bangaren da hajiya Salma ta nufa dakin yana rufe Gam da makulli ta juyo cikin sauri tace ina ya'yana suke delu ina ya'yana ta fadi kasa riffffff kamar gawa.....wata irin kara Delu ta saki tayo kanta innalillahi wa'innah ilaihiraji'un hajiya!hajiya!!hajiya!!! Ta mike cikin sauri ta nufi firinjin da yake coridor ta bude ta dauko ruwa mai sanyi gaske ta dawo gunta ta kwara mata wata lafiyayyiyar ajiyar zuciya ta saki Hummmmmmmm!!!
Ta dago idanuwanta cikin kuka tace delu ina su Asharab da Farha kada ki gaya mun magana marar dadin ji ๐ki taimake ni dan Allah nayi mummunan mafarki akan yara na dan Allah kice dani suna da rai basu mutuba ๐ญ
Delu da farinciki yagama mamaye zuciyarta tayi murmushi tace Alhamdulillah cikin sigar rarrashi tasoma magana ki kwantar da hankalin ki yaran ki sunanan saidai basa gidan nan da sauri ta goge hawayen fuskarta muje na gansu dan Allah bani da kowa sai su sune farinciki na ki taimaka mun๐....
kiyi hakuri za'a kaiki gunsu
Ta mikar da ita tsaye ta rakata dakinta amma zuciyar ta a dagule take jinta saboda rashin ya'yan ta a kusa da ita.....
"Sai da ta rarrasheta sannan ta fita kai tsaye gun baba direba ta nufa yana ganinta ya taso lafiya delu kika fito cikin sauri haka, "ita kuma waccen da ta fita cikin sauri ina zata je naga kamar ma bata cikin hayyacinta.....hummmm! taya ni gani kaidai yau gidan nan akwai damuwa yanzu haka hajiya tana ciki da kyar na lallabata su Asharab take son gani ...wani murmushi baba yayi yace Alhamdulilla๐คฒ๐ปHakika Wannan labarin naki ya faran ta mun rai matuka bara na kira shi doctor na sanar dashi dama jiya yace duk abunda yafaru a sanar dashi delu tace aikuwa ka gaya masa duk gidan nan ya rikice ......waya ya zaro ya shiga neman layin doctor cikin sa'a kuwa ta shiga doctor yana ganin kiran baba direba yayi sauri ya dauka tare dayin sallama bayan sun gaisa baba ya gaya masa komai murmushi yayi tare dayin hamdala ga Allah yace ina tashi daga aiki zan dauko su sai muzoh gidan tare.....baba yayi murmushi yace to sai kun zoh ya katse kiran.....
delu tana gurin taji komai tace Allah na gode maka dama na dade ina add'uar Allah ya dawo da hajiya acikin hayyacin ta
Allah ya kare mu da sharrin masu sharri "Amin baba direba yace sun dan jima suna hira sannan ta shiga ciki.....
Munubiya tana fita daga gidan taxi ta tare sai kauyen bokanta koda taje gun bakowa sai bukkar sa ba ko dan tsuntsu agurin hanu ta sanya akai ta kurma uban ihu nashiga uku naga samu naga rashi *Bassam* ka cuce ni๐ญ wallahi bazan taba kyaleku ba dukan ku sai na ga bayan ku, ba wanda zan kyale acikin ku......ta fito daga cikin gurin fuuuuuuu kamar zata tashi sama ta kara hawa mota tashigo da ita cikin garin Abuja.....wani karamin hotel takama daki.....ta zaro wayarta ta kira *BB* babban yaronta ne kuma abokin sha-shancinta ringin daya ya dauki waya kazoh ina son ganin ka wata dariya yayi yace kina ina ne *VIP* hotel diffff ta katse kiran ranta abace zuciyarta tana tafarfasa cikin yan mintina ya iso hotel din kai tsaye dakin da take ya nufa ya kwan kwasa tace shigo ya turo kofar yana ganinta yasan ba lafiya cikin izza ya shiga ciki ya a kayi baby naga kamar kina cikin bacin rai gayamun ko waye yanzu ya bakunci kiyama bai shirya ba.....wasu kana nan kwari ne gobe ina son kaje gidan gaba dayan su ka babbaka musu wuta๐ฅkowa ma ya huta bazan taba samun nutsuwa ba indai ina ganin su araye wata dariyar gefen baki yayi yashafi sajen fuskar sa yace angama ta kara daure fuska tace kafin ku saka musu wuta ku tabbatar da kunyi saching din gidan kun kwashe komai mai amfani sannan ku aikasu lahira kowa ma ya huta.....zasu san sun taba ni wallahi......
Ya mike yana bahagon murmushi yace ki kaddara gobe by now sun dade da zama toka....ya fice daga dakin yana busar sigarin sa......wata kara ta buga ta dafe kanta wallahi! wallahi!! wallahi!!! duk sai naga bayan ku zakusan da wa kuke ta kwanta tanata hasashen gobe iyanzu ta samu duk abunda take da muradin samu acikin dukiyar hajiya Salma......
*********************
Doctor yana barin asibitin gida ya nufa Alhamdulillah Farha ta warware sosai jikinta yayi kyau tana tafiya da yar sanda saboda ciyon ya taba kafarta amma tafara samun sauki sosai dukan su suka dunguma suka nufi gidan su Asharab kana ganin su saika gane akwai tsoro da fargaba atare dasu umma mahaifiyar doctor ta kula da hakan matsowa tayi kusa da su tadafa Asharab ahankali tace"ku kwantar da hankalin ku insha Allah mahaifiyar zuwa yanzu itama tana bukatar ku a kusa da ita,dan haka ku daina damuwa Abbii yayi murmushin karfafawa haka dai suka isa gidan....
"Baba direba yana daga zaune akofar gidan ya hango motar doctor Deen yayi maza yataso cikin farinciki ya bude masa get".....
Motar ya danna ciki ya samu guri yayi parking atare suka fito baba direba yakaraso bayan ya rufe kofar cikin farin ciki suka gaisa ya nuna farin cikin sa sosai jagora yayi musu suka shiga gidan tana zaune tayi shiru *Bassam* yana zaune shima saboda ganin matar sa a cikin damuwa yakasa samun sukuni kwata-kwata......."Suna zaune baba direba yayi sallama ya shigo atare suka Amsa yace "hajiya kina da baki ne ta dago cikin damuwa tace ka shigo dasu baba...
Sallamar Asharab ce ta daki dodon kunnenta ta dago cikin hanzari tare da mikewa tsaye wani kayataccen murmushi ta saki *Bassam* ya mike shima cikin sauri ganin su tawaga guda ya sanya shi yin sororo a tasaye tare da mamakin ganin Farha tafe da kafar ta....doctor ya karaso gunsa suka gaisa Abbii ma haka hajiya Salma farinciki ne shinfide a fuskarta aguje ta karasa gunsu suka rungume juna cikin farin ciki wani marayen kuka ya kwace musu haka suka ringa kuka kamar wadan'da aka gayawa sakon mutuwa.....saida sukayi mai isar su sanan malan da Abbii suka rarrashe su malan ya daura da nasiha ba kuka zakuyi ba godiya ga Allah zakuyi dan hakika an cutar daku Alhamdulillah komai ya warware da ikon Allah.....hajiya Salma ta dago jajayen idanuwan ta tace "malan nakasa gane abunda ya sha kaina da har na yi fatali da yarana kuma farin ciki na wallahi bansan abunda yake faruwa da ni ba,murmushi yayi sannan yace hakika ba yin kanki bane anmantar dake sune ta share hawayen ta tace bana fatar nakuma mantawa da yara na har abada saboda sune farin ciki na sune rayuwata,Farha da har yanzu kuka ya gagara tsayawa a idanuwanta tace "mum me muka tsarewa Anty Munu ne?" da take son ganin bayan mu, me kika rageta dashi?".......wasu hawaye masu dumi suka kara gangaro wa hajiya Salma ta sanya hanu ta share ki rabu da mutun Farha mu godewa Allah da ya bayyanar da ita muka san wacece kuma da izinin Allah itama zata girbi abunda ta shuka komai daren dadewa
Su umma sun dade agidan a dan zaman da sukayi sun fuskanci akwai soyayya mai karfi atsakin uwar da ya'yan ta,rayuwar gidan ta burge umma sosai delu bakin ta har kunne saboda farin cikin dawowar su Asharab.
A ranar kowa ka kalla sai ga farin ciki a fuskar sa Sai yamma suka tafi zumunci mai karfi ya kullu a tsakanin su.hajiya Salma tarasa me zata bawa Umma gani take batada tamkar ta domin kuwa tana matukar kaunar mai son ya'yanta
Doctor sai dare ya bar gidan bayan sun gama shan soyayyar su shida sahibar sa Asharab,yana fitowa daga cikin gidan ya hango wata bakar motar parke a dan nesa da gidan, baka iya hango kowa na ciki saboda duhun gilasan ta ga kuma duhun dare haka kawai yaji bai sami nutsuwa ba zuciyar sa tana ta wasi-wasi ya wuce yabi ta bayan layi ya gangara gefe yayi parking motar sa ya cire kot din da take saman rigarsa ya ajiye a motar ya tako da kafa yana karyo kwanar yaga wani katon mutun yafito daga cikin motar ya nufi gidan su Asharab doctor ya dan rakube gefe saboda kada ya ganshi,katon yadan tsaya ya dauki lambar gidan sannan ya juyo yashiga motar yaja yayi gaba aguje......yana tafiya doctor yakara komawa gunda ya ajiye motar sa ya dawo gidan cikin sauri yayi hon baba direba ya taso ya bude get ganin doctor sai abun yabashi mamaki yabude masa kofar ya shiga yayi parking ya fito cikin sauri baba rufe kofar hajiya tana ciki eh yace lafiya doctor akwai matsala ne? Mushiga ciki baba suka shiga ciki cikin sauri hajiya dasu Asharab suna babban palour suna hira baba direba ya shigo cikin sauri "hajiya doctor yana son ganin ki, Asharab tana jin haka ta mike zaune tace wane doctor baba? shi dai ku shigo baba ya koma suka shigo tare yana shigowa suka gaisa yace hajiya ku shirya muje gida akwai matsala hankalin hajiya Salma atashe tace matsala kuma doctor me yafaru anan ya gayamata duk abunda yagani aikuwa ba abunda suka tsaya yi suka sassaka mayafan su suka fito gabadayan su har su baba direba suka fice daga unguwar cikin sauri......doctor ya kira wani babban dan sanda yasanar dashi yakuma yi masa kwatancen gidan ai kuwa cikin dan lokaci suka yiwa gidan hajiya salma kawanya suna dakon ganin abunda zai faru......
A bangaren Munubiya kuwa tagama shirya musu komai da kuma yanda take son aikin ya kasance....yayinda *BB* yagama tanadar yaran sa sun gama shirya kayan yakin su kowa yana dauke da manyan bindigun sa suka nufi gidan hajiya Salam da misalin 1:00am..........
*Karshe*
Muhadu acikin littafin Bangare nah 2
Ina masoyana masoyan littafin Bangare nah kubiyo ni acikin littafin bangare nah 2 domin jin yaya zata kasance,
*Alhamdulillah*
Ina
godiya ga Allah da yabani damar kammala wannan littafi ina kuma Addu'ar Allah yabani ikon kawo muku cigaban sa lafiya
Amin ya Allah
0 comments:
Post a Comment