Jaruma Hadiza Gabon ta caccaki jaruman Kannywood da suke yiwa jaruman Big Brother Naija shishshigi, inda ta dinga wallafa rubutu a shafinta na Instagram tana yi musu shagube.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka kammala shirin da ake na Big Brother Naija, kashi na shida, wanda aka shafe sama da watanni uku ana yin shirin da ake haskawa a gidan talabijin na Startimes.
Wannan shiri dai ya samu kalubale daga Malaman Addini da masu fadakarwa na Musulunci da na Kiristanci, duba da yadda ake gudanar da al’amura da suka ci karo da koyarwar addinan guda biyu.
Sai dai kuma matasa da dama sun raja’a wajen kallon shirin da kuma bibiyar sa duk da nuna rashin da’a da fasikancin da ake yi a ciki.
Jim kadan bayan kammala wannan shiri zakaran da ya lashe gasar da me bi masa, da kuma sauran wadanda suka kasance cikin shirin sun yiwa jihar Kano tsinke domin wani shagalin taya murna da kamfanin Multi Choice na masu Dstv da Gotv suka shirya musu, inda aka gabatar da taron shagalin a dakin taro na Tahir Guest Palace dake garin Kano.
Jaruman Kannywood da dama sun samu halartar wannan taro, inda suka yi hotuna gami da taya White Money murnar lashe wannan gasa, cikin wadanda suka samu halartar wannan waje sun hada da Ali Nuhu, Adam A Zango, Abubakar Bashir Mai Shadda, Nazir Dan Hajiya, Abba Elmustapha, Baba Karami da dai sauran su.
Sai dai a yayin da jaruman ke murna da wallafa hotunansu da jaruman na Big Brother din, ita kuma jaruma Hadiza gabon ta gwasale su gami da yi musu shagube kan yadda suke zakewa da shishshigi kan jaruman na Big Brother din.
Da fari Hadiza Gabon tayi tsokaci ne a hoton da Nazir Dan Hajiya ya wallafa tare da White Money din, inda ya yi masa kirari da kurantashi cikin harshen Turancin, inda Hadiza Gabon ta yi masa tsokaci
“Da gaske ne dan su nasu ba za su taba ganin girman mu ba, saboda yadda muke zubar da shi.”
@adizatou
“Ashe kin gane”
@uzee_usman
“Amma kin san ina zuga ki
@nazir_danhajiya
“Ni bana bukatar zugi kawai shishshigin ku ke ban dariya.”
@adizatou
“To naga Kannywood sun dage shiya sa na ce su kan nasu suke wannan dagiyar da ba haka ba.”
@adizatou
Hadiza Gabon ta yi musu shagube a shafinta na Instagram
Bayan haka Hadiza Gabon ta sake wallafa wani matsakaicin rubutu a shafinta, inda ta ce:
Ba a jima ba ta sake kara wallafa wani rubutun, inda ta ce:
Mutane sun cigaba da bayyana ra’ayoyin su kan wannan lamari, inda mafi akasari suke ganin baiken jaruman da kuma gaskata zancen na Hadiza Gabon.
0 comments:
Post a Comment