Jiya da daddare wajajen karfe Goma na dare ta fito daga wanka a dakinta ta shirya abinta tasa key a dakinta ta kwanta ta kashe wuta ta kwanta kunna wayarta tayi tahau WhatsApp. Messages dayawa suka sauko na mansura ta bude kamar haka.
"Babe good news! Nawa zaki bani idan na fada miki?" Ganin tana online yasa marakisiyya ta Mata reply da zamu je shopping ni da ku.
Duba beeba tayi itakuma ta rubuta " ranki shi Dade har mansura ta baki babban labarin ko ? Muyi video call naga dadi kikeji ko kuka kikeyi " turo baki tayi giranta a harde tace wadannan biyun lafiyan su kuwa?
Note:lokacin nan batasan za'a bata class rep ba.
Message taga ya shigo daga mansura kamin ta bude taji an daura Mata hannu a cinya. Da sauri ta mike tana laluman lamp. Kamin ta samu daman kunnawa taji an danneta ruf tare da toshe Mata baki da hannu.
Yace shhhhh yimin shiru shashar banza kawai kunna wuta mara haske yayi Wanda zasu iya ganin juna yace idan kika sake kikayi ihu kinga gidan nan sound proof ne ba mai jinki Dan haka kiyi min shiru.
Tace mmmmmm kwantar da kansa yayi a kirjinta yana shafa cinyarta yace marakisiyya kike ko ta daga ksi da sauri Dan fata take Allah ya fitar dashi a dakin cikin gaggawa lar ayi abin kunya domin tunda take bata taba hada jiki da wani da namiji ba dukda cewa wannan din yayanta ne.
Dan dariya yayi yace ke uwar jarababbu dena wannan rawar jikin ai naji labarin tsiyarki wajen su mom ashe kema jarababbiya ce sai anyi magana ki dinga ce min Dan iska ko? Cikin mugun tsoro ta janye hannunsa daga bakinta tace Dan allah yaya lud kayi hakuri ka dagani dukda cewa kai muharrami na ne yanzu mun zama baligai bai dace mu zama cikin irin wannan yanayi ba.
Yace ke uw*ki yi min shiru dalla can shinshinan jikinta ya soma yi kamar maye yace ke sandar rake sabulun wa kika Sato? Me sunan shi? Kuka ta fashe dashi sosai Dan ji take ta jika jikin ta sharkaf.
Kukan da tasa ya saka ya dawo haiyacin sa da sauri ya Mike yace ke k*tmar ub*nki da kike wa mutane kuka nace zan miki wani abun ne ? Toh me ma zanyi dake ne nikam ? jibi fa dubeki Abu kamar babu ba ta ankare ba ya yage Mata Riga ihu ta kwala ta sauka daga gadon.
Dariya yayi harda kama ciki yace what the heck babe me kike boyewa? Ba komai a wajen fa... saboda ki rufa asirin ki yasa kike bazan fankama fankaman Riga kamar limamiyar kauye. Cacumarta yayi ya lika da gini ya turmude fuska kamar bashi ya gama Mata dariyar mugunta ya Narko wata ashar Wanda jinta kadai zaisa maka jin jiri yace toh Dan ub...ki idan kika kuskura ko da wasa kika sake yi min gardama ko fitsara kinsan de nasan lalurar ki toh wa billahil azim ba yaga miki Riga zanyi nan gaba ba.
Yana kaiwa nan ya hankade ta ya fice abinsa yana fito tare da komawa wajen sailuba.
CIGABAN LABARI
Mikewa tayi tana dingisawa ta fice kicibis kuwa tayi da daddy a parlour yana fadin yauwa yarinyar arziki ina yayan naku naga motarsa a waje amma.....bude Bali yayi ganinta shabe shabe yace auta zamewa kikayi a bandaki ? Yi hakuri daina kuka ina ummanki? Nuna kofar dakin tayi ya shiga yana fadin marakisiyya me ya samu me sunanki ne? Hakan yayi sanadiyyar tsayar da fadan da take yayinda sailuba wacce akayi wulli da ita ta fada gefen kafar daddy.
Yace lafiya kuwa? Ya haka zamuyi bakuwa kuma naga kamar akwai tashin hankali anan? Umma dake kuka tace me zance maka ne Alhaji na yaran nan abinsa ya fara fice min aka yanzu ka duba wannan halittar dake gefenka wai kta fa zai aura yarinya sai kace tsatsar fir'auna wallahi in bata girmeshi bama zasuyi sa'anni.
Dukda cewa ba zunubi bane AI sai ya nemi kamila wai ita fa zamu nunawa jama'a muce matar danmu ce. Daddy na kallonta ya dage kafa yana fadin bismillah sai kace yaga najasa ko aljani.
Naira dubu 3 ya zaro a aljihunsa ya mika Mata yana fadin baiwar Allah ga wannan kiyi kudin mota kije gida kinji ? Lud din zaizo ya miki bayani kinji ? godiya tayi yace ba komai Allah yayi albarka ya haskaka rayuwa.
Haka ta tafi tana jin haushin ummi kuma tana yaba kirki irin na daddy. Tana fita kuwa daddy ya dauke lud da Mari. Har haki yake Dan bacin rai yace ban yarda cewa baka da hankali bakasan me kake ba sai yau. Duk dafa maka kafar da nake ina ganin zakayi hankali zakayi hankali bazaka taba yi ba sai kaga dayan fuskana toh ka shirya dama kaman nasan zaka bani kunya. Toh akwai yar Alhaji sabo tun last month muka gama magana yace ko wani lokaci za'a iya daura auren Dan haka nan da kwana 3 zan Aura maka ita kuma billahi in ka sake kuka rabu ko ka zalinci ta toh ka sani tana fita a gidanka muma ka fita daga gidan mu ba mu babu kai.
A tsorace yace haba daddy maganar baikai nan ba fa. Daga masa hannu daddy yayi yace tashi ka bani guri gobe dama kaje ka ganta in akwai abinda suke bukata ka basu sannan in kaga dama karkayi shiga ta mutunci kaji ko?
Yana kaiwa nan yace maman mu ki sameni a daki. Toh kawai tace ta Mike rabi bayanta Dan tasan in ta biye wa lamarin lud sai ta tsine masa ma ba tare da ta sani ba.
Nan suka barshi yayi jungum jungum yana fatan Allah yasa wancan yarinyar tana da fasali sannan wani bari na zuciyarsa tayi sanyi. Shi kanshi yasan baya kyautawa abinda yakeyi amma bazai iya dainawa ba.
Wani lokacin sai yayi tunanin ya zama mutumin kirki kawai sai yaji ya kasa idan ya suna yaga abubuwan da ake bukata kamin ka zama mutumin kirki.
.
10 - CHAPTER 10
Mom na shiga dakin daddy ya janyota jikinsa yace haba my hajiya irin wannan lokaci da kika bata haka? Kinsan fa kamar uba kamar da. Murmushin manya kawai tayi tace ai ni ina da Dan nan tsoro suke bani yace yauwa hajiya tayanzu dai kamin na fada wata Harkan kar na manta ban fada miki ba. Inajin my dagawa yarinyar nan marakisiyya kafa muyi Mata aure ko ya kika ce.
Umma tace AI ni dama tunda banki ayi Mata auren ba Kaine de ka dage sai tayi karatu. Yace hakane amma naga abin ya fara Mata ysauri ne ta takura domin daga school clinic sun Kira ni Duke cemin ai abin ya motsa Mata a makaranta harda suma.
Umma tace innalillah wa inna ilaihi raji'un toh fa baby na akwai matsala mu hanzarta mu gaggauta muyi Mata aure toh amma ka hana kowa zuwa wajenta AI. Yace toh kiyi Mata magana in tana da wani ta fito dashi Dan dama ta sameni tayi min magana ma. Umma tace Ayya kai Anya Alhaji baka cuci yarinyar nan dayawa ba?
Kasan ta da kunya sosai ba kamfai take irin wannan zancen ba musamman dakai kila ta kasa jurewa ne gara ayi Mata auren kamin ta kawo mana abin kunya. Yace toh naji mu karashe wannan zancen gobe yanzu dai.... dariya tayi tace kaide ka shiga uku mutum yana tsufa amma kamar ana masa service 😂
.......
Lud kuwa direct gidan ubana na biyu ya nufa wato hotel. Yana shiga kuwa Sally ta fada jikinsa tana fadin haba baby dama haka mom dinka take ka duba cin fuskar da tayi ture ta yayi da karfi cikin tsawa yace ke sh*giya yar.... dalla wannan ne a gaban ki kina gani ance za'a auramin wacce ban Santa ba gashi ba saki nika na rantse auren da zanyi ba saki toh in batayi min ba fa?
Cikin shessheka tace amma honey AI basuce ba karu ba ko in bata ma sai ka turo ni ko a boye ne. Da sauri ya dago ta daga kasa ya rungume harda pecking bakinta yace wow baby wow shiyasa duk yadda zaki bani haushi bana iya rabuwa dake. Kin hadu wallahi bari nayi wanka nazo mu daura daga inda muka tsaya ko?
Girgiza kai tayi tace yau saide kayi hakuri Dan ina dawowa al'adata yazo. Yace shit men! Ya janyota ta wando ya shafa kunzugun yace kai Dan iska ya zaka min haka? Nifa na gama shiri na sannan ya kalli fuskar sailuba wacce ke zabga murmushi. Cikin muryar tausayi yace toh yanzu ya zamuyi?
Fadawa gado tayi tace je kayi wanka AI kasan ina da hanyoyi na yace woooohuhu my Sally kinyi aradu kin hadu waiyo ni Dan gata yana cilli da rigarsa harda tsalle ya shiga wanka.
Marakisiyya kuwa tana shiga dakinta ta fada kan gado tana fadin waiyo Allah na na shiga uku me wannan Dan iskan yake nufi dani ne ? Kode na fa da ma umma ne? Amma bazan iya ba Dan ko suma na lura sai sunyi jan ido yake bin umarnin su kar yaji haushi yazo ya lalata min rayuwa ko yace sharri na masa.
Wannan wace irin masifa ce? Ace Dan uwanka Wanda ya sakar maka mulki ka karba yace zai nemeka? Kuma wallahi gaskiya ya fada shi bayason Mata iri na bawai Dan banida kyau ba fa... shire yadi so yaga komai naki kamai buhun flour. Toh me yakeso dani tunda ni ba irinsa bace? Tun muna yara ko ince yana tsulu (sabin balaga irin 16-19 Wanda bai gama zama saurayi ba ) baya kallon film din turawa saboda sirara ne yawanci yafi so ya Nemo tashan lukutaye. Toh me yakeso?
Wata zuciya ce tace me kuwa yakeso yan Mata? So take ya kaiki ya baro ki. Dan tasha irinshi ma, brandi nawa yaci ya yaga ledar? Kuka ta sake rushewa dashi nan zazzabi ya rufe ta mansura ne ta dinga kiranta har sau 6 tukun ta dauka. Murya a shake tace hello mansy... mansura dake kwance a cinyar beeba ta Mike ta zauna tace marakis karki cemin abin ne ya motsa... ina umman kin ?
Marakisiyya tace ba abun bane nasha maganina yanzu fa sauki gaskiya baya haukata ni. Beeba dake gefe da shike wayan a hands free yake tace toh menene? Tace lud ne wallahi lud ne yake nema ya rabani da mutunci na. Wani yar sukaji a jikinsu har tsokan jikinsu na tashi sukayi shiru can mansura tace wai yayanki guda dai lud?
Marakisiyya tace shi fa shi din nan dai. Beeba tace kai marakisiyya ki tambayi su umma Anya iyayenki daya da Dan iskan nan? Kode mamansa ta fita a gidan? Dan guarantee me yar umma ce tunda ga birth certificate dinki. Tace toh shima a nashi ai shima Dan umman ne.
Beeba tace toh kubar zancen nan ayita gobe kiyi hakuri ki daina kuka... yanzu ko nake bawa mansy labarin saurayi na tuno marakisiyya ta mance da wani banza ta Mike tace kice Allah. Toh bani labari nasha yar uwa. Nan fa suka dinga hira abinsu tini ta mance da wani bakin cikin lud abinta.
Washe gari da da yamma Wanda ya kama weekend ne lud ya sha shaddarsa das dashi kamar mutumin arziki yayi kyau sosai. Ya shigo parlour din umma ya sameta tana kallon TV marakisiyya na kwance a cinyarta yace ah ah yar Lelen mama yau ba gaisuwa ne? Ba marakisiyya kadai ba hatta umma sanda ta saki remote ta kalle shi.
Daddy dake gefe yana shan shayi sanda ya kware. Dariya lud yayi umma tace lallashi dakyau tace Allahu AKBAR malam lud Kaine? Yace wallahi fa nine umma daddy ina wuni? Daddy yace la...la...lafiya ina zuwa haka?
Yace zanje na dubo surukarku ne mana dad ko ka manta ne? Yace masha Allah toh AI haka akeso kaga gaka nan ka fito kamilin mutum dakai ko kai kanka bakaji dadin jikin ka ba? Shida kawai washe musu baki yake yana uhmm .
Toh bari ni na wuce dad, mom zan tafi...little sis sai anjima. Cike da mamakinsa sukace toh a dawo lafiya kaji yaron kirki Allah yayi albarka yasa hali ya dore. A dawo lafiya godiya yayi ya fice yana tunanin wannan rigar halin daya sa shine mafi ALKHAIRI a gareshi yanzu in su umma suka yarda ya zama mutumin arziki ko yarinyar batayi masa ba. Bazai nuna ba sai washe gari haka sai yace ga wani halin ta da baiyaso.
Murmushi yayi yace hmm nine fa lud the one and only king wasa dani yafe wasa da wuta da ka rabani gara ka taba dalma da ka fadamin bakar magana gara la tauni reza. Waigawa da zaiyi yaga marakisiyya a bayansa. A take yasha JININ jikinsa.
GENG! GENG!! GENG !!! TOH ANZO WAJEN.... SHIN KO MARAKISIYYA TAJI ZANCEN LUD? ZATA FADA MA SU UMMI KO KUWA? YAYA ABIN ZAI KAYA NE ? KO SHIN YARINYAR ZATA YI MA LUD? KUDAI BIYONI A SANNU.
INA TSIMAYIN COMMENTS DA VOTES DINKU SISTERS💃🏻
NAGODE DA KAUNARKU....TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
30th July,2020.
11 -
Baki bude take kallon sa yayinda ya sauke ajiyan zuciya yace kash ashe ma Kece ni na dauka mom ne ma.
Finciko ta yayi ya manna da gini yace ummm! Little sis kamshi kike yi. Itadai rawa kawai take Dan guntun fitsarin da takeji ta sake ya hankade ta yace dalla matsa min jaka kazamar banza kawai.
Sulewa tayi ta fadi ya damko gashin ta ya danna wajen kafarsa yace maza lashe min fitsarin da kika min a kafa na. Kuka ta fara yace zaki lashe ko sai naci....ki? Harsher takai zata lasa umma tace marakis magana kuke yi ne? Yayinda take tunkaro su.
Da Sauri ya dagata yace gurde kafa tayi kinsanta da rawar kai ga ragonta shine fa ta tsula wa mutane fitsari. Dariya tayi tace kai jama'a yanzu ke banda abinki marakisiyya menene na yin fitsari Dan kin gurde kafa.
Agogon sa ya kalla yace mom ni zan wuce kar tayi ta jira na. Umma tace Toh a dawo lafiya Dan albarka.
Kamo hannun marakis tayi suka shige ciki.
Shi kuwa yana isa gidan su yarinyar yace wa mai gadi ayi masa iso. Nan take aka yi masa maraba aka kaisa wani babban parlour jinjina kai yayi yana fatan Allah yasa yarinyar ta hadu Dan da gani gidan masu Hannu da maiko ne. Bawai yafi nasu ba amma dai bai taba aure Daga babban gida ba.
Kusan minti 20 yana zaune yana jira kannenta Suna ta zuwa mika masa gaisuwa sai hadiyar yawu yake Kamar maye. Har ya sima hajiya da jira ranshi ya fara baci kawai yaji takun takalmi. Dago kansa fa zaiyi yaci karo da wata zukekiya Allah ya mata diri ta kyau ta ko ina.... Baisan sanda yace wow! Perfect!
Dauke da murmushi a fuskanta tazo ta gaishe shi Dan dama ita ma da nata plan din Idan bai mata ba sai taga fiye da yadda ta tsammata.
Kallo yake kare mata a ranshi yace yawa yanzu na sami mata yadda nakeso. Ta ma fi sailuba kai wa yake ta wani sailuba karuwar banza. Su marakisiyya rakiya suka yi wallahi. Dan ya tsine yayi tunawa da yayi Cewa zancen marakisiyya yake a ransa.
Yace shegiya wato maiyar nan ko ina ni na take har a mafarki.
Hada ido sukayi yaji wani yammm!
Yace shit! Murmushi tayi tace lafiya yace ina ai kyawunki ne zai kashe ni. A kunyace tace thanks for the compliment ! Ruwa da juice ta zuba masa yasha Daga nan dai hira ta barke a tsakanin su.
Da yamma marakisiyya na gyara gadon Umma sai ga Umma ta shigo tace albishirin ki marakis cikin murmushi tace goro. Umma tace dad dinki yace an baki dama ki kawo Wanda kike so.
Tsalle ta daka tace Alhamdulillah Umma kice Allah. Dariya Umma tayi tace zan miki karya ne? Ta girgiza jai ta rungume ta tace wow nagode Allah yabar min ke Umma na.
Da gudu ta tafi dakin ta domin bawa su beeba labari. Nan suka fara tsokanar ta Wai amaryar m. Ahmad Suna ta dariya.
........
M. Ahmad ne yayi sallama tare da shigowa parlourn mahaifiyar tasa yace mami na barka da war haka tace barka de baba na. Ya kake ya ayyuka? Yace Alhamdulillah fatan kin yini lafiya?
Shafa kanshi tayi tace Ras dani ma kuwa dukan su biyu Suka murmusa. Tace ahmad.... Gyara zama yayi domin yasan zancen me nahimmanci ne dan bata kiransa da Sunan sa. Ya na'am mami tace yaushe zaka yi aure ne? Kaga fa kullum kara girma kake yanzu har an fara yada jita jita Wai zina ce ta hana ka yin aure bun mata kake yace wa iyazu billa Allah yayi min tsari!
Muryarsa da ta soma rawa ne yasa mami tayi saurin Dafa kafadar sa tace baba na menene? Ko bakada lafiya ne? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
Rungume ta yayi yace mami banason hankalinki ya tashi yasa ban fada miki ba amma bazai yuwu Nayi aure ba. Tace kai ban gane ba kara min haske.
Ajiyan zuciya yayi yace mami abinda wannan mutumin ya fada ta tabbata wallahi,mami ya zanyi? Ni kaina kyamar kaina nake ko Nayi aure ma sai de Nasa matar a gaba ina kalla Kamar yar tsana.
Suman zaune mami tayi m.Ahmad yace mami shiyasa na yanke shawarar zama ni daya ba aure. Tallafe fuskarsa tayi tace baba na my innocent baby kana nufin yanzu dayan kake yi? Da sauri ya girgiza kai yace bazan taba iya yin hakan ba mami bazan iya ba saide ina shan wahala a makaranta domin kuwa yawanci dasu nake Hulda in ka fiya Hulda da dayan bangaren sai zargi ya shigo saide kash ni basusan an sami matsala ba.
Salati mami tayi tace baba na kayi hakuri Komai yayi zagi maganinshi Allah kaji Komai zai wuce ka rike mutuncin ka yace Insha Allah mami nagode.
Ranan Monday da sassafe m.Ahmad ya fita makaranta domin Suna da meeting... Bayan an kammala meeting ya Koma office dinsa. Wani lecturer mai suna m.salis ne ya biyoshi office knocking yayi m.Ahmad yace come in.
Sallama yayi m.Ahmad ya amsa yace m. Salis Allah dai yasa lafiya. Hannu m. Salis ya miko masa domin suyi musabaha yana fadin ba wata matsala bace dama...
Ganin m.Ahmad din bai miko masa Hannu ba yasa ya zauna yayi ajiyar zuciya yace yallabai ba raini ba amma zanso Nayi maka wata tambaya.
M.Ahmad ya gano Inda zancen ya nufa amma sai yace ina jinka. M.salis yace tunda nake ban taba ganin kayi musabaha da mutane ba Kamar ko wani musulmi kuma dai Nasan ba Girman kai bane dan baka da ita Wai shin me yake hanaka yin musabaha da mu ne ko kana da wani cuta ne?
Murmushi m. Ahmad yayi yace ayya bazaka fahimta ba m. Salis amma kayi min uziri kaji? M. Salis yace ba wannan zancen kawai yasa Hannu ya riko na m. Ahmad sanda numfashin sa ya dauke na sakanni zai zare m. Salis ya rike tam.
Yace m.Ahmad yanzu da na rike hannun ka Mun mutu. Take idonta m. Ahmad yayi ja murya a sarke yace fadin ka sake ni m. Salis ka tashi ka fita karka cuce mu. Giran m. Salis ne ya hade yace m. Ahmad ban gane ba me kake Cewa ne? Tashi m. Ahmad yayi ya fara Jan m. Salis zai fitar dashi Daga office dinsa.
Cike da tsoron yadda m.salis yaga idon m Ahmad hakan yasa ya sarke hannayen sa duka biyu cike da kulawa yace malam Ahmad menene matsalar ka ? Kaf cikin colleagues dinka babu Wanda ka yarda dashi Kamar ni ka sanar dani duwar ka kika Nasan maganin ta.
Kamar mahaukaci m. Ahmad yasa hannunsa a kunkumin m.salis ya janyo sa jikinsa tare da daura goshinsa akan NASA yace m. Salis maza ne Matsala ta musamman ma kai.... Kana burge ni tare da rikita min lissafi. Nayi iya kokari na ban taba yi ba amma yanzu dole na rage wani abin kar na mutu, m.salis ka kasheni ka gama da ni. Yana kaiwa nan ya hade bakin su waje daya.
TOH NIKAM BANIDA TA CEWA DAN BAN MA GANE ME KE WAKANA BA. WAI ME ZAKU IYA CEWA GAME DA WANNAN AL'AMARI NA M.AHMAD?
KUNA TUNANIN LUD ZAI AURI YAR ABOKIN DADDY KO ZA'A SAMI MATSALA ? YA BATUN MARAKISIYYA DAKE SHIRIN ZUWA TACE WA M. AHMAD YA AURE TA? KAI JAMA'A AKWAI KURA WALLAHI.
KARKU MANTA KUYI VOTING, COMMENTING TARE DA SHARING.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty💕
5 August, 2020.
12 -
CHAPTER 12
A tsorace m. Salis ke bari da kyar ya tattaro Dan guntun kuzarinsa ya ture m. Ahmad Wanda ke zubda hawaye.
Cikin sauke numfashi da rawar murya m. Salis yace m. Ahmad dama kaima... kaima abin da kake aikatawa kenan? Dama kaima azzalumi ne asararre. Kuka m. Ahmad ya fashe masa dashi yace m. Salis ka yarda dani tunda uwata ta haife ban taba kusantar wani ba kuma ba'a taba kusanta na ba.
Tabbas bans sha'awan Mata kuma bazan iya sabawa Allah na auri namiji ko nayi mu'amala dashi ba. Ni kaina bansan me ke faruwa dani ba ko dalilin da yasa Mata basa min. Abu daya Dana sani shine mahaifi na ne ya janyo kuma sai na gano kan zauren nide Burina ka taya ni da addu'a kawai.
Da karfi m. Salis ya rungume m. Ahmad din yace m. Ahmad na fahimce ka kuma nasan ba laifinka bane. M. Ahmad yace sake ni m. Salis kana kara tura wutan ne. M. Salis yace kayi hakuri m.ahmad amma wallahi ina SONKA?
Kallon baka da hankali m. Ahmad ya masa tare da zare hannunsa dake kwankwason sa yace me kake nufi m. Salis ina sanar dakai bazan sabawa Allah ba kana....wait... are you a ga..gay?
Ajiyar zuciya m. Salis yayi ya zauna yace dogon labari ne amma bari na dunkule maka shi. Zauna mana girgiza kai m. Ahmad yayi yace bazan zauna ba Dan ban yarda dakai ba zaka iya sawa na tsallake iyakar Allah. Murmushin takaici m. Salis yayi yace hmm nima ba son raina bane.
Kamar yadda ka sani Allah yayi wa mahaifi na rasuwa. Yatsine fuska m. Ahmad yayi jin an anbaci mahaifi Dan shi ya tsani nasa. M. Salis yaci gaba da cewa kawu na shine ya rike mu ni da yar uwa ta. Ba tada matsala shiru shiru ce muna rayuwa ba takuri ba walwala.
Lokacin da nayi shekaru 17 lokacin kanwata tana 14 na lura kamar tana da damuwa yin duniya nayi ta fada min sai tace babu komai daga baya sai na lura daga an Kira sunan kawun mu ko ta ganshi sai ta dinga zabure ita daya. Dukda banida wani hankali sosai lokacin kasan tabbas dole na zargi wani abun.
Hakan yasa na saka musu ido sosai wata rana cikin dare na tashi shan ruwa haka kawai naji inason in duba lafiyan kanwata. Amma me shigana ke da wuya na samu kawuna yana anfani da ita ba nan zalincin ya tsaya ba domin kuwa daure ta yayi a jikin gadon kamar wata tinkiyar layya.
Bansan yadda akayi sai gani nayi na bude ido na amma sai na ganni a daure jikin kujera. Dariyar kawuna yasa na juyo har wannan lokacin yana samanta
Kuka na fara ina hada sa da Allah ya bar cutar da kanwa ta. Amma ko a jikinsa sanda yayi mai isaesa sannan ya sauko yazo inda nake ya shafa fuska ta. Dauke kai nayi ya riko bakina ya matse yace salis kenan Dan samari kanason kanwarka? Ashar na daura masa nace da bana sonta akace ma?
Yace min easy easy! AI ba sai ka daga hajiyar wuya ba indai kanasonta toh sai ka fanshe ta. Harararsa nayi nace ban gane ba domin lokacin bamu wani San wannan iskancin ba. Yace min abin da yake nufi shine ba bada kaina a gurbin ta ban gane inda ya dosa ba amma haka kawai nace na yarda bansan na dibo ruwan dafa kaina ba.
Haka ko wani dare zai kaini zaure yayi duk abinda takeso dani sai ta bani kudi wani lokacin har abokan yana Kira. Bana so amma ba yanda na iya duk sanda na tuna ceton kanwata nake yi, run yana min zafi har ya dena. Bayan wata 4 kawai sai ga kan wata sa ciki.
Wai ashe dukan mu biyu yake hadawa ni da dare ita kuma da asuba🥺😭 hakan yasa ta daina zuwa makaranta nayi kuka har na gaji anan ne na Sami matsalan ido. Kullum sai matan kawuna sun dake ta wai a ina tayi ciki ga aikin wahalar da suke bata dukan su su 4 har cikin ta ya tsufa... wata rana rana cikin wanke wanke matar kawuna ta uku ta jefi Mata itace me wuta azaba da firgici ga wahala yasa ta soma nakuda.
😭 rokon su nake Allah da annabi su taimake ta amma suka ki. Gashi lokacin mu ba wani wayewa mukayi da asibiti ba haka na kwanta da ita a cinya ta domin kuwa rufe dakin da aka bata sukayi wai kai ta sa musu najasa dama kuma can dakin dabbobi be aka gyara ko window babu.
A tsakar gidan nan muka zauna Dan nasan in muje zaure kawuna nuna can suna masha'ar su. Kuma ba abinda ta samesu da yanayin ta a hakan ma zasu kasance mu ne. Muna cikin wannan yanayin aka barke da wani ruwa Wanda kar de nayi karya da sai nace ban taba ganin ruwa mai karfinsa ba. Ajiyar zuciya ya sauke yace in takaita maka labari haka ta mutu.
A taimake ni ayi Mata Jana'iza ma ki akayi ni daya nayi komai hakan yasa na gudu na bar gidan. Saide kash tun daga lokacin banida zaman lafiya har sai a kusance ni nayi kuka har na gaji kawai bayan wata 3 nabi dare na banka musu wuta bayan na kwashe makudan mudin kawun nawa.
Cikin sa'a suka ba Wanda ya fita da rai... tabbas bai dace na dauki hukunci a hannuna ba tunda akwai hukuma amma matsalar shine yana da hanyar da zai kubutar da kansa.
Wannan kudin nasa Wanda a zahirance ma na gadon mu ne shi na dinga juyawa ina zaune da mahaifiya ya sanna kuma ina karatu na.
Lokacin da naga na gaji da abinda ake min kawai sai na siya abin saduwa na roba hakan yasa ni daya nasan me ke faruwa dani har na kai zuwa yanzu Dan ko mahaifiya ta bata sani ba sai yanzu Dana fada maka. So literally na daina da mutane nima.
Cikin kuka m. Ahmad yace mugun tausaya maka m salis amma ka sani zina zina ce ko da me kayi saide wani yafi wani girma amma duka manya ne. M salis handkerchief dinsa ya ciro ta goge hawayen sa ya riko fuskan m. Ahmad a hankali ya furta na sani tare da goge masa hawayen sannan ya sumbaci bakin sa.
Kallon sa m Ahmad yayi irin bakaji me nace bane Dan murmushi m. Salis yayi yace ina MATUKAR so in daina domin a da ina anfani da abun sau 5 ne a rana ina ragewa a hankali yanzu sau daya nake yi wata rana ma bana yi.
Shiyasa nake so mu taimaki juna mu zama friends with benefit kawai Dan tabe tabe zamu na yi amma kar mu taba ratsa junan mu kaga kai bazaka je ka fadawa wani ba nima baza'a fada min ba.
Shiru m. Ahmad yayi yace zanyi tunani m. Salis ka koma bakin aikin ka. Murmushi yayi yace nagode da ka saurare ni har zuciya ta ta rage nauyi .
Murmushi m. Ahmad yayi yaba sake nazarin maganar m. Salis Dan shi m. Salis gani yaje ya sanar masu mafita bai San ya kara tsoma kansu ruwa bane.
Kewayo wa yayi ya zauna a cinyar m. Ahmad din tare da rungume sa a Dan tsorace m. Ahmad din ya shafa bayansa dai dai lokacin da m. Salis ya Mike marakisiyya ta hankade kofar.......
CABDI JAN BARI NA GUDU KAWAI DAN ZA'AYI GWARAMA A NEXT CHAPTER KARKU MANTA KUYI VOTING. SHARING TARE DA COMMENTING.
ME KUKE TUNANIN ZAI FARU?
Miss untichlobanty 💕
6th August, 2020.
CHAPTER 13
Kofan ne ya rike Mata Riga hakan yasa ta dakata Tare da zare Wanda ya bawa m. Salis damar barin jikin m. Ahmad din. Murmushi suka sakar Mata tace malam salis ina wuni? Yace lafiya kalau malama.... tace marakisiyya yace oh dama itace marakisiyya? Ya jefawa m. Ahmad tambayar daga kai yayi m. Salis ya mika masa hannu irin zasuyi musabaha dinnan yace m. Ahmad ni zan wuce.
Ita dai marakisiyya taji wani iri ganin yanda suka rike hannun amma bata kawo komai a ranta ba. Sanda m. Salis yaje bakin kofa ya jiyo yayi blowing kiss ma m. Ahmad shide wani ban bara kwai yake jin abin amma sainkawai ya masa murmushi juyowa marakisiyya tayi taga har ya fice.
Zama tayi a kujera bayan m. Salis ya fita suka gaggaisa da m. Ahmad din shiru tayi shima baice komai ba yana binta da kallo ganin bazata yi magana ba yasa yace marakisiyya dazu HOD ya aiko min letter wai yanzu kece class rep ko? Daga ksi tayi yace masha Allah toh Allah ya taya riko tace ameen.
Yace akwai matsala ne? Tace eh...ins nufin ah ah. Dafe kai tayi yace ko class rep properties kika zo karba Dan dazun tsohon class rep dinku yayi handing over gyada kai tayi yace yauwa toh bari muga wasu abin sabi ma za'a baki. Sannan duk sati za'a dinga saka miki katin 1k tace toh na gode malam.
Yace ba komai ai dokar makaranta ce. Wani jaka ya miko Mata yace toh gashinan akwai komai a ciki ko. Ta karba ta nufi waje sai zata fita sai ta juyo kamar de ta fada masa kuMa sai ta fasa. Yace marakisiyya akwai wani Abu ne kuma? Girgiza kai tayi yace toh sai mun hadu ko ? Dan yanzu kusan kullum zamu dinga haduwa.
Murmushi kawai tayi ta fita. Mansura ne tace ke me yace ? yi sauri ki bamu labari mai Romo Romo. Ajiyan zuciya marakisiyya tayi ta turo baki kamar zatayi kuka tace na kasa fada mai. Dungure ta beeba tayi tace kede anyi sokuwa toh yanzu da kukazo nan wa mutane zakiyi kuka a haka zakuyi aure?
Rufe ido zakiyi ki fada masa... kamin ta karashe marakisiyya ta girgiza kai tace bazan iya ba kwarjini yake min. Mansura tace toh AI ta kwana gidan sauki dayan biyu tunda yanzu kece class rep kina da list din malamai da numbobin su. In kuma kina so ki zama more romantic sai ki rubuta masa lette ya kikace ? Ta fada tana yi Mata sigina da gira.
Ajiyan zuciya ta sauke tace bari dai mu gani.
A gida kuwa an raba katin gaiyata mutane har sun fara taruwa gobe daurin aure. Su lud baki har kunne ana ta yi masa San barka kowa fadi yake ya canja nutsuwa ta shige sa basusan jiya Iyau bane. Likimo yayi musu.
Da daddare marakisiyya na kwance a gadon ta rike da wayar ta in ta taifa sakon da zata turawa m. Ahmad sai ta goge ta ma rasa me zata rubuta taji ana buruntu a kitchen. Karan bani yasa ta sauka tana shiga taga wuta a kashe lallabawa tayi ta dauko serving spoon.
A sanda sanda ta karasa bakin fridge ta kwalawa mutumin da ke tsaye yana lalume yace ouch! Zata kurma ihun barawo ya matse Mata baki yace a gidan ub*nki?
Ciccibarta yayi ya fice daga side din ya kaita dakinsa ya wulla a gado duk wantsalwantsal dinta ji yake kamar ya dauki kaza. Make ta yayi yace ke tsolo ko kimin shiru ko na bige wallahi ki natsu. Tsim ta tsine waje daya ya dauko kwalbar giyansa tare da ajiye kankarar daya dauko a fridge.
Lungun gado ta samu ta makale Dan ta dauka giya zaisha sannan ya keta Mata haddi. Dan haka ta kifa kai take masgar kukan ta. Ko kallon inda take baiyi ba sanda ya zuba wiskin sa a Kofi yasa Ankara ya kurba. Yace ahh finally! Har naji wani sanyi a ruhi na wallahi kwana uku bamu hadu ba.
Karamin pillow ya dauka ya cilla wa marakisiyya ta dan zabura yace ke tsolo bani labari. Sautin kukan ta ne ya karu yace zaki bani labari ko sai na daura wa uwarki ashar? Jiki na bari tace an.. anbani class rep a makaranta giyqr daya kurba ne ta dawo mai ya fashe da dariya yace amma babu dakiki Lamar wanda ya bawa tsiya irinki shugabanci .
Tabe baki yayi ya sake jingina yace ba wannan nake son ji ba bani wani me Dan sugar hakannan. Tace bani da wani labari AI yace okay zo ki tayani sha toh Dan kinga daga yau ba haduwa zamuyi ba balle na jijjibgi banza shiyasa nakeso muyi hira a mutunce.
Tace AI ni.... ai ni bana shan giy.... kamin ta karasa ya watso Mata wani harara da sauri ta gyara tace banashan lemon manya. Murmushin yafi miki yayi Mata ya kwankwade kofin dake hannunsa.
Zuba wani ya sake yi yace ke kar ma fa kiyi tsammanin komawa cikin gida yau anan zaki kwana. Kuka ta fashe dashi tace Dan allah ya lud karka yi min haka ka barni ba koma cikin gida kaga fa akwai baki a gidannan me zance musu? Yace ansa mai sauki daga dakin yaya na nake.
Kwankwade kofin dake hannunshi tayi yana fadin ahhh! Dan zuwa yanzu ta tada kwalba daya har zufa yake yi. Botir biyu ya balle na t-shirt dinsa ya yarfe gumi yace ke... wani lulu yake kallonta yace kara min AC... tace sanyi nake....daga hannu yayi yace karamin ac nace miki ko na nemi shawara ne ?
Daukan remote tayi ta kara yace kure sanyin baki daya. Kurewa tayi ta janyo bargon dake gefe Wanda ba a ninke yake ba ma zata rufu ya bige Mata hannu yace cire.... ta zare ido tace me? Cikin alamun bugawa yace hijabin jilin ki zaki cireeee.
Ta bude baki zatayi musu ya kama ya fincike ya kwalla Mata Mari yace Dan.... ki ni sa'anki ne? Da sauri ta girgiza kai tace kin mantani ko tace ah ah ban manata ka ba. Yace good yafi miki ajiye kwalbar yayi ya Mike yana tangal tangal ya cire Riga. Tsikan jikinta ne ya tashi amma take cikinta ya duri ruwa sanda lud ya zare mukulli ya nufo ta.
Kuka ta fara masa waiyo Allah na umma yaya lud karka min haka karka bari giya ta rude ka ka bude idonka ka gani nice fa kanwarka ce fa. Dariya yayi yace sokuwa da kin dauka wani abun zan miki? Toh wani tsiyar zan samu anan ? Dallah karbi ya jefo Mata rigansa yace ninke min wannan ki gyara min gado kamin ya fada ban daki.
Wanka yayi ya fito ya samu ta gyara komai da komai. Murmushi yayi yace yar kwal uba kawai kika ce baki jin gari. Ya kika bar wadannan anan? Tace me? Yace kwalaben nan mana. Cikin muryar kuka tace kayi hakuri ya lud bazan iya taba su ba.
Yace dauka dalla dauka nace miki.... girgiza kai tayi ya kamo hannunta ya daura akan kwalbar yace kin mutu? Nace kin mutu? Toh dauki kije ki ajiye min a kitchen sannan kizo akwai wani special task da zan baki.
Kitchen din ta shiga sai lokacin ta tuna rana da wayar ta aiko ta Kira umma har sau 3 amma shiru bata dauka ba ta buga na hudu kawai taji an sankame ta, tace dan Allah yaya lud ni fa banason irin wannan abin aure zanyi kaima aure zakayi dukda mu muharramai ne kana wuce gona da iri bige Mata baki yayi yace gonan uw*rki na wuce ko na ub*nki toh taka rawa zamuyi.
Kunna music yayi ya fara juyata wai shi dole sai sunyi rawa. Kawai bacci ya kwashe shi suka fada gado. Yin duniya tayi ta tureshi amma yadda kasan an daura Mata buhun hatsi. Vibration taji wayanta yayi tana nishi ta bude kawai taga message daga m Ahmad a tsorace ta bude Dan tasan bata taba yi masa magana ba kawai sai taga ashe ta tura sakon da ta rubuta dazu by mistake.
Salati tayi domin kuwa abinda ta rubuta shine "Salam m. Ahmad Dina barka da war haka! Fayan kana cikin kishin lafiya? Tun rananda na sanya ka a idanuna nake muradin samun ka... shin zaka aure ni?" ita duk a tunaninta ta goge sakon Dan Sam taji bai tsaru ba gashi bata taba yin soyaiya ba balle tasan yanda ake kalamai.
Sake maimata sakon nasa take tana addu'a Allah yasa ya amince sakon kuwa da ya aiko Mata kuwa shine " toh fa class rep daga samun numbers dinmu kuma sai zolaya kar de kije ki tsokale HOD ko DEAN a kwace mukamin😂 bari gobe zamuyi magana yanzu dare yayi"
Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin yanzu ya zatayi ta koma daki Dan bazai yuwu ta kwana anan ba, saide kar tayi bacci domin tana da matsalar da ba Wanda yasan da ita. Tana yin FITSARIN KWANCE!
😳😂😂 TASHIN HAKALI TOH WATA SABUWA KUMA DAI. KAI JAMA'A YANZU IDAN LUD YA SAMU WANNAN LAGWAR NATA SHIKENAN KUMA. YANZU DAI BARI MU JIRA GOBE A DAURA AURE MUGA YAYA ABIN ZAI KAYA A GIDAN MALAM LUD.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
8th August, 2020
CHAPTER 14
Ganin babu sarki sai Allah yasa ta yanke shawarar zata kwana a bandaki kawai in ta tsula ma kawai sai ta kunna wa kanta shower ta nuna kamar jikewa tayi. Mikewa take kokarin yi lud ya kara gyara kwanciya ya dauke Mata nauyi baki daya hakan yasa ta fara tunanin toh bari ta kwana ido biyu amma matsalar bazata iya kwana da nauyin katon nan ba kar da safe a kwashi gawa ta.
Ajiyan zuciya tayi fara burbuwa ko Allah zaisa ya daga ta amma shiru. Turo baki tayi tace umma na za'ayi kisa za'a kashe miki diyar ki. Sautin Hhhha lud ya furta cikin buguwa yace ke... daina mutsu mutsu kin hanani bacci.. mtsw mutum sai kace tsutsa.
Numfashi ya sauke yaci gaba da baccin sa yayinda taci gaba da kallon ceiling. Dariya dariya ta soma jin yadda numfashin sa ke dukan wuyanta kamar cakulkuli. Gyatsa yayi ta dauke kai saboda warin giyan da ya daki hancin ta. Tace eww yayinda take tunanin in ba tsautsayi da asara ba menene abin dadi a cikin giya?
A haka har bacci ya dauketa. Kiraye Kirsten assalatu yasa ta bude idonta tana shirin mikewa da gudu Dan haka take yi a cewar ta inka bude ido ka Mike a take kamin ma kayi addu'an tashi daga bacci in ba haka ba toh saide kaga rana a tsakiyar kanka. (This is literally me😂)
Jin nauyi da kuma dakin da taga tsarinsa, fasalinsa, kalarsa hatta kamshin sa yasha banban da nata yasa ta tuna da abin da ya faru. Ba sai ta tambayi kanta ba domin kuwa tabbas tasan cewa ta tsula. Dan haka ta fara bubbuga bayan lud Wanda yanzu Rabin jikinsa na kan hannun ta yayin da yayi matashin kai da kirjinta ya sakala hannu ya rike ta, ya danne kafarta na hagu yayinda ta lubga masa na dama.
Hakan yasa ya zamto hannunta na dama is free. Turo baki tayi tana kunkuni tace nasan maganinka. Dakarkarewa tayi ta hankade sa sanda ya fado daga gadon Tim. Da ashar ya bude bakinsa yace bakida hankali ne Dan......ki me ma kike yi a dakin nan? Shegiya munafuka? Haka kawai ta abinci bakinta da cewa da uban wa yace ka dauko ni ? Kazo kasha giyar ka sannan ka tsula min fitsari kuma Dan wulakanci kake tambaya ta me Nike a dakin ka? Yanzu dubi yadda hannuna na hagu ya sha jini.
Hankade ta yayi karyar banza da wif nasan na kawoki daki na amma kawai gyara min na kawoki yi ya akayi kika hau gado na?
Kamo hannunsa tayi fuska a turbune ta sakashi a inda take jiya ta daukwalbar giyan nasa ta fara tangal tangal yadda yayi jiya ta fada jikinsa amma ko gezau baiyi ba sai ma hade gira da yayi. Ido cikin ido suke kallon juna ganin zata zame gashi bayida niyan rike ta yasa ta mike da kyau ta tsaya ta saka yatsa tana dangwalar kirjinsa da babu Riga yayinda dayan hannunta ke kwankwason ta tace haka kayi min jiya ka danne ni da kyar nake numfashi yin duniya nayi ka barni na tafi sai ce min kayi na daina mutsu mutsu kamar tsutsa.
Tabe baki yayi yace karyar banza ya cacumo hannun ta ya finciko ta zuwa jikinsa sai ta dawo kamar wata yarinya dukda tsayin sa take da shi yace Dan uwaki kinga alamun inason in kalli wannan kananun lemon tsamin naki bare in taba. Tace hhhhh tana bude baki kamin tayi magana taga yayi yatsine, kawai ya wanke ta da amai tun daga tsakiyar kanta Wanda ta tufke har zuwa kafarta.
Da gudu ya shiga ban daki ya karashe yayinda ta raho a zafafe ta fara bubbuga kofar tace wallahi ka bude mugu kawai ga Mari ga tsinka jaka ya zakayi kayi min fitsari ka ci min fiska sannan kayi min amai yanzu sai na sake wanke kaina.
Kurkure bakin sa yayi ya bude kofar ya cafko wuyan riganta ya hankada ta bayin ya bude Mata shower ya samu guri ya tsaya ya fara latsa wayar sa. Ganin bayi da niyan tafiya yasa tace um..ah zanyi wanka.

Ba tare da ya kalle ta ba yace da na bude miki shower wanki nace kiyi? Tace AI.. naga..ka..ka tsaya ne. Yace toh duk daya ai tsolon rake wai me zan gani a jikin ki ne? Ke banda abinki ya kamata ki gane cewa tsabar bakiyi ba dukda kudin da daddy yake dashi da komai har yau bakida saurayi amma ni dubeni.
Yan Mata ta ko ina ni suke mafarkin samu,har fans ma akwai masu crushing in karya nake ki tambayi miss untichlobanty. Abinda yasa daddy bai miki aure ba kenan yanaso atleast in zakije gidan Wanda kaddara ta kaddaro masa ki Dan kai koda certificate ne na kwakwalwa tunda ba a haifo ki da na jiki ba. Nide nasan mom Dina akwai shape kamar ita tayi kanta.
Haushi zancen ya bawa marakisiyya ta ja tsaki tace shiyasa naga an makalkale ni jiya da daddare kuma aka tsaye min a ban daki. Bige Mata baki yayi sanda ya fashe yace AI ni ban taba bacci mara dadi irin na jiya ba. Shiyasa na dinga mafarkin ana jifana da dutse ashe kashinki ne ke tokare ni.
Kasa kasa tace banza makaryaci in ma kaga an jefe ka da dutse ai hukuncin zina ce akayi maka. Murmushi yayi Dan sarai ya jita kuma maganar ta sokeshi kawai ya fice Dan yasan in yasa ta a hannunsa balla ta zaiyi babu musu.
Parlour ya fita ya kunna TV abinshi club ne ma ake dauka ya soma shan coffee ya barbaje yana kallo.
Marakis kuwa wanka tayi ta fito amma ya zatayi tayi sallah ba kaya?
Wajen kayansa ta nufa ta dauko wani farin riga tasa tare da saka hijab dinta tunda har kasa ne tayi sallah. Sum sum ta fito zata gudu yace zo nan. Tsayawa yayi yace da izinin wa kika taba min kaya? Zare ido tayi... ya akayi ya ganta?
Yace ba leka ki nayi ba ko me kika taba a area na waya na zai turo min alert, hakuri kawai ta bashi ta fice bayan ta furta ka tashi kayi sallah sannan ta fice kallonsa ya ci gaba da yi bai ma bi ta kanta ko maganar ta ba.
Tana shigowa parlour tayi mika tace ahh kai gaskiya na gaji sosai mugu kawai gashi da shegen nauyi juyowa da zatayi suka hada ido sanda numfashinta ya tsaya Dan tabbas sunji zancenta kuma duba da idon su to tabbas sun dauki zancen a baibai.
NO CAPTION 😉
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
10th August,2020.
CHAPTER 15
Girgiza kai marakisiyya ta soma tana bude baki da rufewa suma girgiza wa suke suna kallon juna da sauri suka cacimi hannunta sukayi dakin ta da ita tana fadin ku tsaya nayi bayani Dan Allah ku tsaya nayi muku bayani umma da ke fitowa daga dakin ta tace hayaniyar me ake yi ne? Au ashe su habeeba ne. Mansura ya mahaifiyar taki?
Tura marakisiyya daki sukayi suka ce wallahi kuwa umma muna fa AI ko wanka bamu yi ba muka iso tace naga alama Dan yanzu dakyar in 7 ma tayi gaskiya kun kyauta. Wai sin bayanin me za'ayi ne ? Habeeba ne ta Sosa kai mansura tayi sauri ta cafe tace umma wannan diyar taki ce mana ace za'ayi auren yayan mu guda amma ko sanar da mu batayi ba sai a Instagram dinta muka ga anata posting IV card.
Umma tace Ayya yi hakuri kunsan bikin yazo ne a gaggawa a kasa da sati za'a yi sa shi ya saka. Beeba tace Ayya bari mu shiga ciki mu sameta toh. Kamar munafukai sidim sidim suka shiga dakin marakisiyyan suka rufe harda saka key.
Mansura tace ke marakis me kikayi haka yanzu jarabar taki takai har ki kasa daure wa kije kiyi da yayan ki? Haba marakis ina tsoron Allahn naki ? Mu da muke kwai kwayon ki toh yanzu yaya kenan? Ita de marakisiyya tunda suka soma take girgiza kai ganin ba dai nawa zasuyi ba yasa yace ke banziya kinsan ko wuka aka sa min a wuya bazan kusancin wannan Dan akuyan ba, dadin dadawa yaya na ne fa.
Ta yaya ma za'ayi na yi zina dashi ? Haba kuyi tunani mana. Beeba ta zauna tace da alamu labarin nan zai bada kala sosai Dan haka farfan kunnena kamar antena bamu musha akwai yar uwa ya akayi kika kwana a dakin yayan ki kuma me yasa kike sanye da rigar sa? Mansura ce tayi caraf tace kuma kema banda abinki, ya zakiyi ki cire hijab a parlour.
Tabe baki marakisiyya tayi tace ke ni na dauka ba kowa ganin cewa sanyin safiya ce dama larai me shara ke bude gida itako tawa ce ko nayi laifi rufamin asiri take balle ma banayi. Kuma yadda akayi naje dakinsa shine ji nayi ana motsi kitchen kuma saboda ba a haiyaci na nake ba duk na tsure Dan ina kokarin turawa m. Ahmad Sako sai na dauka barawo ne bayan fa nasan an rufe gida kuma akwai mai gadi kawai sai na kwaleshi.
Ko haushi yaji ko menene oho kawai ya sankame ni ya kaini dakinsa wai ashe kankara yazo dauka kamar fridge dinsa ne ya baci. Yanzu nasan kun dauka wani abun arziki zaisha mansura tace toh me za'asha da kankara ? Beeba tace haba mansura Dan kinason sa sai kina kwana ma halinsa ? Sarai kinsan ruwa zai Kora. Marakis tace toh ko zaku fara fadan ne bakwason labarin?
A tare sukace kar muyi haka dake muna so mana. Tace toh Abu de yayi Abu yasha yayi tatil yasa ni na gyara masa daki kuma ya rufe kofar kinga dole na Kwana a ciki. Da safe kuma yayi min amai anan ne na dauki kayansa. Mansura tace kai Anya baki tsallake wani Abu ba naga da kika ce kika gyara masa daki sai kika dauke kai kode kode zaro ido marakisiyya tayi.tace wai ni ban gane ba kunaso nayi zinan ne ko yaya toh ba wani abin bane ya faru fa garin masifa ne bacci ya kwashe shi a jikina.
Beeba tace awwn ! I wish zamu iya auren yayun mu. So romantic marakis tace a gidan tsohonki suka kyalkyale da dariya.
Biki yayi biki Mata an taru ana ta ciye ciye dama wasu abinda ya kaisu kenan. Maroka na ta yi wata a gefe ita aka fi bawa kudi hakan yasa na maida hankali sai na ga ashe sod'i marokiya ce sai fadin kirarin ta na da'Iman take tana takawa tana zufa tana SAI NI SOD'I GAIYAR BIKI, BA'A CE BA MA SAI IN FINDUMA DAN RASHIN ZUCIYA.
Kayan lefe aka dauka akwati ne dozen ba tsiya ba almubazzaranci aka kai gidan su amarya. Guda aka yi lokacin da dangin ango suka shigo nan akayi musu lale marhaban aka bude kaya yan tsurku na irgawa ana guda. Kawai sai ga uwar amarya ta fito aka fara wasa ta.
Tace a dakata kuma a saurara kowa kallon ta yayi tace don Allah na hadaku da Allah ku rufe musu akwatin su ku basu kayan su su koma. Kanwar umma ce tayi dariya tace oh ashe har yanzu ana wannan al'adar a dura wa dangin ango ruwa a ciki? Girgiza kai umma tayi tace ba wasa bane. Tabbas mum fasa bada yar mu yanzu haka mahaifinta yana kan hanyar tafiya wajen daurin auren domin ya bawa mahaifin yaron hakuri akwai wata matsala ne da ta taso kuyi hakuri tana kaiwa nan ta koma ciki.
Nan fa gida ya juye Mata aka rikice haka guiwa a sanyaye su umma maimuna kanwar daddy suka koma suka bar musu kayan a gidan. Nan suka isar da labari gidan su marakis ma aka shiga garari.
A wajen biki daddyn amarya ne kawai yazo banda shi babu Wanda yazo hannun daddy kawai ya kama ya ja shi gefe yace Alhaji ka sani wannan maganar da nake maka ba wai Dan in tozarta ka ko in wulakanta ka bane wallahi zanyi ne domin hakkin da Allah ya daura min in nemawa yara na mazaje na gari aboki na kayi hakuri bazan iya cutar rayuwar diyata na bayar ga danka ba domin halayen da bincike na ya nuna min yana da su.
Tabbas nasan kunyi kokarin ku wajen bashi tarbiyya ka sani wannan ma jarabta ce, duk sanda ya canja hali Allah ya shiryasa ya daina auri saki da duk wani Abu da yake nayi alkawari koda wannan tayi aure ni mai bashi wata ne. Ajiyan zuciya daddy yayi yace ba laifinka bane na fahimce ka.
Dama ni nayi masa sha'awan diyan ka kila ta zama sanadin shiriyar sa amma hakan ma da kayi na gode Allah ya bar zumunci gaisawa sukayi abban amarya ya hau motansa driver ya dauki titi bayan sun koma cikin jama'a ya sanar dasu diyarsa ce ba lafiya tana asubiti ma amma za'a iya daura auren da wata in wancan ta Sami sauki sai a daura da itan ma.
Tsimi tsimi kowa yayi yana bin hayakin motan daddyn amarya. Kananun maganganu aka fara kowa na fadin shi bazai bada yarsa ba domin kuwa ansan halin lud darajar mahaifin sa yasa suka zo bikin.
Ciki daddy ya shiga kunya ta rufesa wai yau da shi kowa ke gudun hada zuri'a yana shiga part dinshi ya lafta wa umma Kira tana zuwa tace baby na ba sai ka fada ba na sani. Yace marakisiyya toh ya zamu yi? Riko hannunsa tayi tare da ajiyar zuciya tace ba zai yuwu mu Sami wata ba? Kwalla ya goge yace babu Wanda ya shirya mayar da diyar sa bazawara.
Umma tace Alhaji mu fasa, yace ban gane ba kallon idonsa tayi kawai ya girgiza kai tace no bazan iya ba my wife it will break her. Tace toh yanzu haka zamu bar jama'a su watse? Karka manta ita ma fa tana son auren nan kuma nayi imani zata iya daukar duk abinda yake Kira jaraba. My love Allah mahaifinta ta gado.
Ajiyan zuciya daddy ya sauke yace kenan kina nufin irin mu ce? Murmushi tayi tace baka ga idon ta ba? Ta ma fiku. Daddy yace if that is the case ina ganin hakan ma zai kara mana dankon zumunci ni da marigayi kanina. Kira min yaran nan a waya kice suzo su su same ni. Lud din ma ai ko zuwa masallatin baiyi ba.
Bari na Kira liman din ayi sanarwa an canja venue din aure ya dawo masallatin kofar gidan nan. Bayan mintuna kalilan sai gasu sun shigo dukansu biyu lud ana ta gyara zaman hula yana fadin afwan dad naso na makara ko? Daddy bai kulashi ba ya kalli marakisiyya yace ke kinada miji tsayaiye a kasa? Kallon umma tayi, umma ta dauke kai.
Marakisiyya ta girgiza kai Dan a tunaninta hada auren su akeson yi. Kallon lud daddy yayi yace kai an fasa auren ka da wancan yarinyar kanwarka marakisiyya zaka aura kuma babu musu.
Dariya lud us fashe dashi tace jar uban nan Abu sai kace a kannywood please daddy muna yin latti tashi mu tafi.
Umma tace kai banason shiririta fa ko bakaji me akace ma bane? Marakisiyya ne tace umma ban gane ba , kamar ya na auri yaya na? Ajiyar zuciya umma tayi tace look babyn umma.
Kanwata itace ke auren kanwar daddyn ku kamar yadda kuka sani lud me sunan kanin daddy ne ko? Toh hakan yasa kanin daddy ma yasha alwashi zaiyi ma daddy suna saide kash baya gari sanda matar shi ta soma nakuda tsabar jin dadi da farin ciki yasa yayi loosing control ya rasu a take Wanda wannan labari ne sananne a wajen ku.
Munce muku kanwata ta koma ita da abinda ta Haifa, toh anan ne bamuyi gaskiya ba domin ni da ita rana daya muka sauka saide na riganta da awa 3 kuma nawa ya koma hakan yasa na dauki nata na mayeshi da gurbin nawa tunda ta rasu Wanda hatta likitoci badu sani ba domin daddyn ku ne ya saka ki cikin babban Riga yayi swapping.
Ki sani koda wannan diyar tawa bata rasu ba da zan daukeki kuma zan kaunace ki kamar yadda nake miki yanzu ke din diya ta ce ko ba Dade ba jima. Dan Allah kar ki bamu kunya. Mikewa marakis tayi tace Sam ni bazan iya auren Wanda ya maida mace takalmi ba Dan bana ce Riga ba domin Riga a jiki ake sawa dukda ana canjawa, takalmi kuwa a tube ko yaushe sannan kuma a take sa.
Daddy ne yace look my daughter nasan ke din diyar ALKHAIRI ce kuma ke zaki canja mana wannan yaron, amma kar na takura ki dayawa idan har zaki iya fito da miji yanzu toh bazan aura miki lud ba amma in har bazaki iya fito da miji ba toh bakida wani zabi. Yana kaiwa nan ya Mike yace kinada minti 30 kadai kinji yar arziki?
Sama ya haura yasan nan da awa daya labari zai samu kowa an canja wurin daurin aure zuwa nan kuma yasan marakisiyya bazata iya fito da kowa ba. Da gudu marakisiyya ta fice ta shiga dakinta su mansura na zaune ta fada gado ta fashe da kuka harda burburwa.
Mansura tace menene? Beeba tace cewa akayi an fasa baki kudin da zakiyi Karin ango? Tsaki mansura taja tace wannan ne a gabanki. Cikin kuka marakis ta zauna tace wai Dan allah fisabilillah ace in fito da miji cikin awa daya ko a aura min Dan iskan tayan can nawa? Suka ce mene?! Riko hannun beeba tayi tace ya zanyi mansura ku taimaka min wai ashe ni ba yar su daddy bace? Ashe lud cousin Dina ne kuma wai shi zai zama mijin.... kai bazai iya karasawa ba kyamarsa nake wallahi.
Mansura tace banziya kina da awa daya kika tsaya kike kuka? Ki duba duk DMs dinki duk Wanda kika ga aure ne ya kawosu kice ya fito in yaso sai a canja date din auren ko?
Beeba tace kuka tsaya kuke wannan shirmen yaushe zata gama duba dm gararin ma ta kwaso Wanda yafi lud din.
Dage kirjinta tayi tace babu abin da ke min ciwo a rai kamar in na tuna jiya Wanda ba muharrami na ba a kan kirji na ya kwana. Beeba tace ke nifa in ta nine ki cire kunya kawai ki Kira m. Ahmad ba wani zubda mutun ci wallahi nana khadija ma ita tace ma annabi ya aure ta kawai sai ki dabbaka sunnah.
Mansura tace kinzo da plan....kiran m. Ahmad tayi har sau biyu sai a na uku ya dauka banda sallama bata kara kokai ba kawai tace yazo kofar gidan su ta gate din baya tanason ganinsa rayuka zai ceta. A cewar ta in ta auri miji na gari yaranta zasu Sami uba na gari kuma maganar ta DUTSE.
baifi 30 minutes ba sai gashi tana fitowa ta shiga motarsa gaisawa sukayi yace class rep ya naga kamar kinyi kuka. Tace malam Ahmad zaka iya aure na? A ba zata maganar ta dokesa yace kamar ya fa? Tace m. Ahmad in baka aure ni ba ka sani cousin Dina za'a aura min kuma wallahi Allah mashayi ne,mazinaci ka taimaka min nasan baza ka so rayuwar mutane dayawa ta tagaiyara ba. A ranshi ba shakka babu abinda zai karanta masa shi da mahaifiyar sa kamar wannan toh amma kuma AI shima tana da NASA matsalar bazai iya kare ta dafa fadawa zina ba tunda bazai biya ma buka ta ba.
Da ace ta aure Dan snooker gara ta auri mazinaci, kallon ta yayi yace marakisiyya kiyi hakuri batasan sanda ta riko hannunshi ba tace kar ka bani hakuri kawai ka amince. Yace bazan iya ba ne da zan iya da na aurenki ki fahimce ni. Idonta yayi ja cikin daga murya tace wallahi m. Ahmad sai ka aureni wallahi bazan iya zama da mazinaci ba. Zare hannunsa yayi daga nata yace FINE ! SAI KI ZABA WA KIKESO YA ZAMA UBAN 'YA'YANKI, MAZINACI KO DAN LUWADU?!
😳OSHEY! BA KANTA
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
KARKI MANTA 18TH SEPTEMBER NE RANAR ZAGAYOWAR HAIHUWA NA WANDA DA IZININ ALLAH ZANYI SHEKARU GOMA SHA SHIDA A DUNIYA FATAN ZAKUYI MIN ADDU'AN ALKHAIRI DA FATA NA GARI.
11th August,2020.
13 -
CHAPTER 16
Karkarwa marakisiyya ta fara baki na rawa tace me? Me... me kake nufi m Ahmad? Cin kwalar rigar sa tayi tace Dan bakason la aureni shine sai ka miyar da kanka fasiki? Karya kake yi wallahi kai mutumin kirki ne Dan Allah ka taimaki rayuwa ta Dan Allah.
Zare hannun ta yayi a hankali yace marakisiyya karki manta ni ba muharramin ki bane ki daina rikeni ki sani komai yayi zafi baifi karfin Allah ba da ina da ikon aurenki da zan aurenku babu shakka akan hakan domin kina burgeni tsarin rayuwar ki gwanin sha'awa ce kiyi hakuri ki auri Dan uwanki kinji.
Fita kawai tayi da gudu ta koma daki tana shigowa mansura ta rafka salati Dan tasan an Sami matsala beeba tace yanzu dole sai ta auri mazina cin nan? Mun shiga ukun mu.
Marakisiyya tace beeba ku kalle ni menene AI bina da zan rasa miji ? Banida kyau ne ko Ilimi ne banida shi? Tarbiyya na rasa? Me yasa? Me yasa kaddara zatayi min haka ya zanyi na auri Dan iskan can waiyo Allah na! Waiyo zuciya na.
Umma be ta turo kafar tace kiyi hakuri marakisiyya na fahimci matsalar ki amma ki sani wannan aure contract ne tsakanin mu da ke a matsayin ki na yar mu kiyi mana biyaiya ki aure sa ki bashi tarbiyya daga ya shiru sai mu raba auren ki auri Wanda kike so.
Da sauri tace umma da gaske kike? Umma tayi murmushi tace kwarai kuwa diya ta diyar albarka da gaske nake ba sai kin yi rayuwar ki da lud ba. Ki yafe min da na biye wa duniya harma da ke cewa ke ba diya ta bace kaunarki ya mantani yin hakan kuma ki sani bamu taba shiryawa ko tsammanin akwai abin da zai kawo dole sai mun fada muku gaskiya ba.
Ki yafe min kinji ki yafe min. Goge hawayen ta tayi tace AI shikenan tunda ba sai na hada zuri'a ta da nashi ba zan aure shi umma kuma duk randa ya shiru zan barshi domin auren farin cikin rayuwa ta. Zanyi muku halacci kun rikeni amana bazan Baku kunya na ki taimakon jinin ku ba wannan hali sai butulu.
Fitowa umma tayi ta shiga da daddy daki ta sanar dashi cewa marakisiyya ta aminta da contract din ga paper din ma tayi signing karba yayi ya ajiye a killaceccen waje.
Dawowa parlour sukayi lud dake buga game din God of the war yace wai kuna bin garu kuna wani shawara ni ba'aji ta baki na ba. Allah sarki umma da shike ta dauka nutsuwa tazo mai tace babyn umman sa AI nasan bazaka ki farin ciki na ba ko ? Munsan zaka auri yar uwar ka kuma..... Daga hannu yayi yana wani bata rai yace look woman kina ji na ko? Dama fa bawai na aje makamai na bane boyewa nayi Dan na wallafa rai a wannan yarinyar amma yanzu da bazan same ta ba babu wani auren da zanyi.
Haba in ba an rena min wayo ba ya zaku aura min wannan kashin yarinya kirjinta kamar allo. Babu abin da zanyi da wannan halittar look malam musbah Aminu bazan auri muciya da zani, diyar kajinka ba.
Ya Kira sunan mahaifinsa yana nuna sa da yatsa yayin da ya fadi wannan maganar. Wani Mari umma ta sauke masa sanda zoben hannun ta ya yage masa kumatu. Tace kaicon ka lud, asara ta kare ma mai hali irin naka toh billahil azim ko kaki ko kaso sai ka auri yarinyar nan. Abin naka ya ishi mutane ka fita a kaina wallahi har na fara nadamar haihuwan ka.
Cikin bacin rai yace dakata dakata dakata malama nace ki dakata! Dan kin haife ni sai akayi kaka? Ni nace ki haifo ni? Ko na rike kafar ki daga shiga dakin zubda ciki? Ni duk surutun nan da kike ya daina tasiri a zuciya ta tsinewa ce karshe bismillah ga fili ga mai doki. Yarinya ce nace bazan aura ba ko ana dole? Yana kaiwa nan yayi cilli da babban rigan ya fice zuwa ban garen sa ya janyo akwati Dan guntun kayan NASA ma kwashedu yayi ya nufi hotel Dan yasha alwashi indai akayi auren bazai kara kwana cikin ba.
Kuka umma ta zube a kasa tanayi tace Alhaji na kar muyi kuskure fa Anya bazamu fasa auren nan ba? Dad yace kenan mubi umarninsa kike nufi? Ya zama dole mu nuna mai mu muka haifesa. Ba shi ya haifemu ba. Hakan da yayi ya kara tabbatar mon kansa ba daya yake ba. Aure ba fashi in an daura saide ya kashe ta.
Yana kaiwa nan ya fita da karfin guiwar sa. Har mamaki yadda ta fito jama'a suke zama yayi ya bawa al'umma hakurin bata musu lokaci nan liman ya karbawa lud auren marakisiyya a wajen daddy jama'a kowa ya rikice liman ma Kato bara yayi bayan an daura aure
Mai sanarwa ya bude makokoro yace ye kuwa jama'a dukda ni kaina ban gane me ke wakana a wajen nan ba, San dai fadi abinsa kunnena yaji ne. An daura auren lud musbah Aminu da kanwarsa Wanda a sunanta ni na sanar cewa sunanta marakisiyya musbah aminu amma dai yau ance ainihin sunanta marakisiyya lud Aminu. Baban amarya da ango ko zamu saaaamu Karin bayani?
A cikin gida Mata gaba daya aka Mike aka tsaye wa umma hajiya mu fa bamu gane ba wannan wani irin jahilci ne yaza'ayi wa ya auri kanwa? Umma tace da alamu bakiji sunan amaryar da kyau ba ko? Toh marakisiyya lud aliyu akace ba musbah ba. Marakisiyya yar kanwata ce kuma nice nan na raine ta.
Wata Mata Mata aikin banza yanzu ke da kikayi bayanin nan kin dauka an warware komai toh nonon da kika bata tasha fa ? Murmushi umma tayi tace tabbas babu shakka nice nan na shayar da marakisiyya tun daga ranan da tazo duniya kuma nice de na dauki cikin lud ba Dan wani ko wata bane.
Kowa ya tsaya kallonta wata Mata tace ke hajiya marakisiyya da alamu ke da mijin ki kunyi dimuwa ko ? Da alamu dai fasa auren danki ya taba muku kwakwalwa yasa kuke ta shige da fice.
Murmushi umma tayi domin zagin ya shigeta amma sai tayi shiru tana bin matar da ta fada Mata wannan maganar da kallo dan bata gane matar ba amma kamar ta Santa.
Ajiyar zuciya dadday yayi yace a takaice ba diya ta bace diyan kanina marigayi lud mai sunan Dana ce. Fatan Allah zai yafe ni kuskuren kauce batun manzonsa da nayi Wanda yace a Kira ko wani Dan Adam da sunan mahaifinsa koda kuwa Dan da aka samu babu aure ne.
Mai sanarwa ya hura speaker ta bada sauti yace toh kunji uban ango kuma marikin amarya yace amaryar diyar kanin sa ce Wanda akwai dogon jawabi dake boye amma dai da wannan kawai ya barmu saboda wani abun ba na tattaunawa a jama'a bane.
Umma ce ta Kira lud a waya yana kallo yaki dagawa kara rungume sailuba yayi wacce ke yi masa tausa yace my love nayi missing dinki fa. Tace Allah ko? Sako ne ya shigo wayar tasa dubawa yayi yaga umma ta rubuta lud idan kanason farin cikin rayuwar ka kazo ka gida Dan yau za'a kai maka matarka bangaren ka bayan matan ka sun gama idda a gyara gidan ka.
Emojin dariya ya tura Mata yace room number na is 156 sai kunzo. Kawai ya kashe wayarsa. Umma kuwa sake karantawa take tana hango diyata kwance a gadon hotel inda kazami karuwai suka kwanta. Wani zuciyan ne yace to sai me. Murmushi tayi tace wallahi ko ka dawo gida ko na kai maka ita har hotel din....
GENG ! GENG!! GENG!!! CABDI GASKIYA LUD RASHON MUTUNCIN SA YA WUCE TUNANI NA TOH FA WA YAGA AMARYA MARAKISIYYA A HOTEL? CABDI
KU BIYO NI DOMIN JIM YADDA ABIN ZAI WAKANA. TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
12th August,2020.
https://my.w.tt/
CHAPTER 17
Tsaki yaja ya kashe wayar tashi ma baki daya ya Mike ya zura rigarsa ya dauki mukulli. SaiLuba tace my love ina zaka? Yace babu ruwanki sannan ya rufe kofa ya fice direct pool party da akeyi a hotel din ya nufa.
Dayan wayarsa da ke silent ya bude ya duba yaga calls dayawa daga mutane ma banban ta ga messages wasu abokan shaye shayen sa ne wasu kuwa congratulations suke masa akan aurensa, wasu bashi hakuri basu halarta ba suke,Wanda suka sanshi kuwa sunsan marakisiyya kanwarsa ce Dan haka suke neman Karin bayani saide sako daya ne yasha banban da ko wanne. Sakon aminin sa kuma abokin sa zannurain Wanda Sam halin su ma ba daya bane.
Zannurain ya kasance salihin bawa ne Wanda bayason tashin hankali ko kadan abotan su kuwa ta fara ne tun suna primary lokacin da ake cin zalin zannurain din sai lud ya dinga tsaya masa.
Toh sakon da ya aiko masa ne kadai sakon da yasha banban inda yake sanar dashi daraja da kuma kima na aure sannan yake bashi hakuri akan auren da akayi masa ba da yatsarsa ba.
Kiran sa lud yayi yace buddy ya akayi ? Zannurain Yace kaide kullum sai munyi da kai ka dinga farawa da sallama baka ji. Yake lud yayi Dan yanzu ma already ya kurba wasu saboda haka a sama sama yake jinsa.
Zannurain yace kai Alhaji kana ina ne haka naji kida ya dame ni? Naji kida yayi yawa cikin maye yace buddy ina gidana na biyu ne. Ajiyan zuciya zannurain yayi yace kai Alhaji wai kai yaushe zaka canja hali ne? Kawai lud ya fashe da kuka ya kashe wayar.
Da sauri zannu ya kunna motarsa bai tsaya ko ina ba sai hotel din da lud ke zama. Reception ya nufa yace MR. Lud musbah yake nema. Nan sukayi directing dinsa zuwa pool area din.
Yana shiga lud ya rungu me shi yace aboki na me yasa aka tsaneni ne me yasa za'a aura min wannan halittar? Yarinyar ban fa batada komai fa wallahi ba a kafa ba ko a takalmi aka daura min since ta zanyi shine mom ke wani cewa zata kawo min ita.
Na yarda dazu nayi musu magana yadda bai dace ba amma dukda haka jni cutata akayi da za'a auramin wannan halittar. Toh AI shikenan a kawotan a gani wallahi bazata shiga daki na ba kut! In kansu yana rawa ni zan nuna musu ni mahaukaci ne. Da sauri zannu ya rufe masa baki yace ka daina fadin haka aboki na iyayen ka ne fa.
Yanzu dai tashi muje gida kana ji na ko zo muje kayi wanka sai ka dawo. Shi zannu yayi ne da niyan yayi masa wayo baisan cewa ya tattare kayansa ba yace AI ba komai nawa a gidan nan ka barni kawai. Sako ne ya shigo wayan zannun dubawa yayi yaga umma ce take ce masa yazo gida tanason yin magana dashi. Haka kuwa ya tashi bayan yayi sallama da lud Wanda ya budewa idon sa tokai cewa bazai koma gidan nan gidan tsiya ba.
Zannurain yana isa ya samu umma ta fito parlour don wani sabon jagwal aka tayar Mata wai wallahi baza'a kai marakisiyya ko ina ba tunda uwa daya ce ta shayar dasu ran umma ne ya baci ta boye marakisiyya dake bayanta wacce ke ta kuka abinta tace wai nikam idan ma uwa daya ce ta shayar dasu menene naku aciki? Nace menene naku a ciki? Ince zunubin nawa ne toh bari kuji da kyau sanda na haifi diyata dalilin da yasa ta rasu shine yunwa domin kuwa ni cikin dare na haihu gashi babu ruwan mama kuma babu madarar da zamu dama mu bata Dan sai sunyi wata uku nake fara bada madara.
Haka mukayi kokarin bada ruwa yayin da mijina ya fita ya dinga yawo makota makota yana neman a taimaka masa da majaran jarirai ko ruwan nono amma ba'a samu ba duba da cewa lokacin ba Musa hali sosai babur ne dashi babu ko mota. Gashi dare ne kuma bazai yuwu ya dauki mai jego a machine ba haka ya fantsama colin duhon dare ga ruwan sama ya nufi asibiti ko akwai abinda za'a iya yi anan aka bamu madara amma kamin ya dawo Allah yayi wa yar tawa cikawa.
Dan haka koda washe gari aka samu aka kaini asubiti anan ne na samu labari daga mijina cewa kanwata ma nakuda ya kamata da asuba. Likita ne yace wani cuta ne ya kama tissue din mama na Wanda ya haddasa kafewa ruwan mama sannan koda na Sami ruwan ya fara sauka kar na shayar domin madarar zata iya illata jaririn Dan haka ni na rike marakisiyya amma ban shayar da ita ba ta rayu ne da shan madarar bature.
Yanzu ko za'a iya fice min a gida na? Nagode da zumunci tana kaiwa nan ta mayar da marakisiyya daki tana jiran isowa zannu domin ta bashi assignment din kawo Mata lud. Batasan ma har ya iso ba wayan ta ya Kira ta fito lokacin kowa ya watse sai kannen daddy guda 3.
Daya daga cikinsu dama haushin umma takeji Dan haka ta dinga sukarta da ba'a wai ta kashe yar uwarta Dan ta kwace musu diya a cinye gado. Gaishe ta zannu yayi ta kaishi parlourn daddy tace maza Kira min abokin ka a waya kace masa nace yazo gida yazunnan.
Kiransa yayi dukda yasan babu wani nasara da za'a samu ya saka a handsfree yace Dan uwa umman ka fa tace ka dawo gida. Yace sau nawa zance ma bazan dawo ba. Umma tace wallahi Allah lud ka bar hotel dinnan ka dawo gidannan kasan Allah mai suna na bazata kara kwana daya cikin gidan nan ba sai a dakin ka.
Yace please mom banason muna batawa juna rai. Ni fa banga uban da zaisa nabar hotel dinnan ba ehe, in taga dama ta mutu ni babu abinda ya tsaye min kawai malamai duk kubi ku hakuri rayuwar mutum. Ni kuma min asarar yawu na. Kaima kanaji na ko buddy in ka kara min zancen wannan yarinyar that's it babu ni babu kai yana kaiwa nan ya datse kiran.
Umma ta sauke ajiyan zuciya tace ni lud zai mayar yar iska? Zai nuna mana bamu isa dashi ba toh AI ni na haife shi ba shi ya haife ni ba. Daddy da ya dafe kirjinsa ne ya zauna yace rabu dashi marakisiyya ki bishi a hankali kawai na lura da muke masa tsauri bata lokacin mu mukeyi yanda muka lallabasa har ya baci haka zamu lallabasa ya gyaru kinsan tunda yace bazai dawo babu Wanda ya isa ya dawo dashi kimin rintsi.
Fitowa tayi ta tarki tar uwar daddy me suna atine wacce batason umma labe tana sauraron zancen su. Tabe baki tayi tace yo ba dole da ya guji gidan uban sa ba? Yadda aka bi aka saka masa idanu tun ubana yana kaunar sa aka raba kansu a barsa ya wayata ya hole lokacin sa ne.
Hararan juna sukayi ana kallon kallo umma ta shige dakin ta. Zama tayi a bakin gadon tana nazari ya zatayi? Nazari ta dinga yi kusan minti sha biyar kawai tayi alwala tai sallar magrib ko addu'a na kirki batayi ba ta Mike ta fada dakin marakisiyyan ta sake yaga Mata gyalenta tace ke mansura, habeeba maza ku janyo min akwatinta biyun nan da na hada dazu ku biyoni dasu.
Kuka me sauti marakisiyya ta saka ta fara cijewa Dan a yanayin umma tasan ba makawa kaita zatayi. Fadi take umma na kiyi hakuri kar ki kaini dakinsa wallahi Allah bazan iya Kwana ni daya a side dinsa ba gashi ko mala'ikun rahama dakyar su shiga Dan cike yake da giya Sanfuri sanfuri.
Umma Dan Allah kar ki kaini jiya ma da ya kaini mugunta kawai ya dinga yi min. Mansura ne tayi saurin karashe zancen da cewa kwana tayi tana shara da goge goge har amai yayi. Ta fadi hakan ne Dan kar a fahimci marakis a bai bai. Umma de janta takeyi har suka sauko a Benin AI kuwa zannurain yana jiran su tace toh maza maza muje.
Danna marakisiyya akayi a motan Dan zuwa yanzu muryarta ma ya fashe ta daina kuka sai hawaye dake zuba. Atine kuwa fadi take ke shegiyar yarinyar nan har kina da bakin kuka shi Dan namu ludu ba mutum bane shi baiyi kuka ba sai ke majogana langai ko? Shegiya me bakin jini kamar uwarta no wonder na tsaneki tun kamin nasan uwarki ta asali Dan nafi tsabar uwar ki lami ma akan uwar rikon taki.
Danne zuciya kawai umma tayi jin yadda atine ke zagin su ta manta da cewa marakisiyyan ma diyar Dan uwanta ne. Zannurain bai tsaya ko sai a kofar hotel. Lud kuwa tun sanda yake wajen pool party sailuba tazo ta karbi kudin shopping ta fice abinta.
Koda ya koma tubewa yayi ya baje a gado sai bacci.
Umma kuwa suna shigowa receptionist ta tsayar dasu tare da musu barka da zuwa tace daki nawa za'a basu umma tace ba daki zasu kama ba sunzo ganin lud musbah Aminu ne. Kallonta receptionist din tayi daga sama har kasa tace gaskiya sai mun tambayesa Dan bakiyi kama da kalar matan da zasu zo wajen sa ba. Umma tace ni uwar sa ce kuma wannan ta nuna marakisiyya dake rakabe tana kuka tace MATARSA CE yau aka daura auren kina da magana?
Jiki na rawa receptionist ta nuna musu hanya harda sawa a dauka musu akwatin yayinda zannu yake jira a waje. Suna isa umma tayi knocking shiru... dunkule hannu tayi ta bubbuga juyi yayi yana surutai irin na mashayi yace ko ma wani shegen ne ka koma inda ka fito. Umma tace toh tashi ka bude SHEGIYAR UWARKA CE.
0 comments:
Post a Comment