Yana ji amma giyar dake kansa ya hanasa yin motsi ma balle ya kallesu. Umma ko ganin shi baje baje yana kwance ya barta tsaye a kofa yasa tace tashin hankali hannu tasa ta daka masa duka amma me makon ya tashi kawai sai ya janyo pillow ya rufe kansa Dan yasan bai wuce tazo tace masa ya koma gida bane.
Gyara liffayar dake jikin ta tayi tace wato yanzu lud so kake ka mayar dani mutuniyar banza ko? Nace ma ka koma gida wajen matarka shine kace babu uban da zai dawo dakai gidan ko?toh AI shikenan tunda ka nuna min ban isa dakai ba bazan mayar dakai gidan ba saide kamar kayi mantuwa. Ya dauka zata ce yabar giyarsa yaje ya dauka kawai yaji an hankado masa mutum.
Tace ga matar ka nan yanzu ba nauyin mu bace in kaga dama ka zauna da ita in kaga dama ka sake ta kai zaka mutu ba ni ba in kaga dama kuma ka kaita kwata a yanka kaji ko ? Tana kaiwa nan tayi ficewar ta tabar marakisiyya yaketa kuka me sautin da ba sauti.
Umma tana fita yace d.......uw*r nan wani kafa yayi wa marakisiyya sanda ta fado daga kan gadon yace shegiya kazamar banza har kika wani baje wa mutane a gado wallahi in kika yadda na shaki numfashin da kika sha ma sai naci.....
Tari ta fara saboda yadda numfashinta ya sarke tsabar yin kuka kwandon harara yake juye Mata kamin ya Mike daga gadon yace kai an gama rainani hankali fa. Ya za'ayi ace ni lud musbah na auri tsolon rake?
Ita de har yanzu tana cikin gyalen ta a dukunkune tana kuka. Dafe kai yayi yama rasa mai zaiyi ko yace kawai sai ya saka rigarsa ya kalleta yace ke idan ba so kike ki kalli yadda yayanki ke jarumta ba toh kar ki kuskura in dawo baki koma gidan uban ki ba.
Yana kaiwa nan ya buga kofa ya wuce abinsa. Kuka ta kara fashewa dashi yana fita kamar da ga gan aka samu matsalar wuta wani wire biyu suka hade hakan yasa aka kashe wutan hotel din gaba daya. Da gudu ta fito tana neman lud ta hango shi ya kusa fita. Da lalume da gwarewa ta karasa ta rungume sa ta baya tana gunjin kuka. Cikin muryar ta da baya fita tace ya lud Dan Allah kaeka barni wallahi tsoro nakeji bazan iya kwana ni daya a hotel ba idan wani ya... ya fada min fa?
Lud kuwa tunda ta kankame sa komai nasa ya tsaya baki daya. Zuciyar sa kawai ke bugawa yana tsittsilla ido sama da shekara ashirin kenan tunda marakisiyya tazo gidansu in ya kalle ta sai gabansa ya fadi. Ko su umma basusan yasan marakisiyya ba kanwar sa bace.
Haka ta dinga biniyar rayuwar sa a komai in yana game tazo ta takura mai, cin abinci, hatta bacci sai ya ganta a mafarki ya dauka da gangan takeyi toh amma yau ya gane inda matsalar take. Yanzu kam ya fahimci komai. Ya game dalilin da yasa take da naci gata da shegen taurin kai. Juyowa yayi ya kafeta da ido har sanda ta kusa zamewa ta fadi hannu yasa ya kamo fuskanta a hankali kamar me jin bacci yace tsolon rake DAMA KE MAYYA CE?
.......
M. Ahmad zaune a parlourn sa ya zuba uban tagumi kamar Wanda akayi wa mutuwa yana karanta wasikar jaki. Yanzu marakisiyya ko a wani hali take oho. Anya baiyi kuskure ba da yayi rejecting dinta ? Toh amm gara hakan in ya aure ta AI ya cuce ta gara da ya bari Dan uwan ta ya aure ta ko ba komai zai iya biya Mata bukatar ta.
Ji yayi an bude kofarsa yayinda ya kafe TV da ido dukda ko hankalinsa ba s kai yake ba yace ummi na me kike nema ne baki kirani ba kikazo da kanki ? Ji yayi an sakale hannu ta wuyansa an sumbaci kumatunsa yayi murmushi ya juyo yana fadin yau kumabkaunar ce ta mots....
Kasa karashe wa yayi ganin m.salis a Dan tsorace yace m. Salis lafiya dai ko me ya faru ba ganka da daddaren nan. Kewayo wa yayi ya kwanta a cinyar sa yace lafiya na kalau aboki na kawai kadai ci ke damuna kuma banda kai babu Wanda yasan matsala ta shiyasa nazo ni Dan nayi alkawari wa kaina bazan sake yi ba.
Shafa kanshi m. Ahmad yayi dukda yaji abun banbarakwai namiji da suna hajara amma sai yace karka damu m.salis komai zai ware zaka dena kaga ni dama can ban fara ba balle na tsoma kaina a ruwa. Zamu dinga zuwa asibiti ana maka therapy insha Allah zaka dena daga nan kuma sai musan yadda za'ayi mu fara sha'awan mace ko ya kace? Rike hannunshi m. Salis yayi yace wannan shawara ce mai kyau gaskiya nagode sosai fatan bazaka damu ba in na kwana anan? M. Ahmad yace ba damuwa zaka iya kwana.
Dariya m. Salis yayi yace nagode sosai aboki na. Daga nan suka ci gaba da hiran su yayin da suke shan shayi.
.....
Umma kuwa tana komawa gida ta samu yayar daddy wato atine ta saka shi a gaba tana kwashe masa albarka wai me yasa ya raini marakisiyya kuma har ya boye Mata Dan yaga ba mahaifiyar su. Wai in da mutunci AI ita uwa ce a garesa. Sauran kannen NASA sai hakuri suke bata suma ta samu take fada musu baka. Da abin ya bawa umma haushi ne tace atine ya isheki kuma enough is enough for a wise kina ji na ko ki fita sabga ta da na miji na.
Atine race dalla yi mana shiru asararriyar iwan kawai Wanda ta kasa tarbiyantar da danta sai shaye shaye yake yana yawo a gari. Cikin bacin rai umma tace jibi me magana sai kace ba kece kwanan nan aka tsamo ki daga harkar madigo ba kikayi wata sama da 10 a asubiti kamin kika fara dawowa saiti. Kodan banga laifinki ba da alama a garin harkar taku ce aka tsetse miki kwakwalwa.
Kukan borin kunya ta fashe dashi wai musbahu yanzu a gabanka wannan matar taka ke zagina kayi shiru kana ji. Bude baki yayi cikin in ina yace kiyi ha...hakuri.... ahhh innalillah wa inna ilaihi raji'un kawai ya dafe zuciya ya fadi kasa ashe basu sani ba hawan jinin sa ya tashi tazo ta kara masa zafi.
......
Marakisiyya kuwa dago kanta tayi da sauri ta zuba idonta cikin nasa yace damn it! Ga irinta nan kin gani ko? Dafa kafadar ta yayi cikin tsawa yace Dan..... ki ki sake min kurwa ta! Azabtarwan ya isa shekaru 20 kina bibiya ta me na miki? Nace me na miki? Ba rantse da Allah ko me suna irin naku na sake ki bare na gani saina karya miki kafafu balle kuma na ganki dama kisan inda dare ya miki yana kaiwa nan ya hankade ta ya fice.
Da sanda kamar barauniya haka ta fara haurawa sama Dan ma a floor na 2 suke. Da yake sanda aka kawota a cikin gyale take batasan room number din ba kuma sanda umma ke tambaya ita kukan ta take masga. Taimako daya Allah yayi Mata da take kallon kasa tana ganin kasan kofofin da suke wucewa kuma in batayi kuskure ba toh kofa na 5 ne nasu hakan yasa tayi shahadar kuda ta tura kofar ta shiga.
Har zata zauna a bakin gadon sai ta tuna da abinda yace Mata ta samu kujera ta Dan dosana mazaunan ta tana jiran tsamma a haka har bacci ya soma kwasarta. Kamar a mafarki taga Kato a kanta daga shi sai gajeran wando Wanda ta tabbata ba mijin ta bane.
GASKIYA INA JIN DADIN COMMENTS DINKU SISTERS WANDA BASAYIN COMMENT KUMA KUNAYI MIN DAN ALLAH.
NAGODE DA KAUNAR KU GARENI KARDE A MANTA DA YI VOTE
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
14th August,2020.
CHAPTER 19
Ba tare da bata lokaci ba Dan dolen ta ta bude ido war. Tsaye yake da tulelen tumbinsa yan washe Mata wasu hakawaran sa kamar jeren alkama yace wow hotel dinnan sunyi ashe har budurwa yar kasar masar ake kawo wa.
Daga shiga wanka kawai sai na fito na tsinci yar shila? Cikin bari marakisiyya ta kara kankame gyalenta tana goge hawayen da batasan ya zubo Mata ba tace Dan Allah kayi hakuri kuskuren daki aka samu.
Ajiyan zuciya tayi yana lashe baki ya zauna a gefen ta da sauri ya ja baya yace Ayya daga gani ke sabuwa ce a harkar nan ko? Look innocent prostitute ki saki jikin ki kawai ki kwashi naira.
Ke daliba ce? In ke daliba ce kawai ki fada min jami'ar da kike da ajinku sai MATRIC number dinki shikenan babu ke babu carry over. Dube dube ta fara tana neman abinda zata rotsa masa. Yayinda ya kamo bakin gyalen ta.
Hankade sa tayi tace dalla matsa daga jiki na ni ba yar iska bace amarya ce! Tsayawa yayi cak ya biya da kallo kamar na second biyar kawai ya fashe da dariya yace AMARYA A HOTEL? ke kinga alamun nasha kwaya ne. Yana kaiwa nan ya sake nikita.Kokuwa suka fara yi yasa hannu ya toshe Mata baki yana shirin zube Mata zip din less din dake jikin ta.
.......
M. Ahmad zaune yana aiki a laptop yayinda m. Salis ya kwanta cinyar sa yana masa shagwaba sama sama yake jinsa kawai yana masa murmushi yayinda yake shafa kansa domin shi a kani ya daukesa ba komai ba. Ko ranan ma da aka samu matsala kasa jurewa yayi amma komai ya warware.
Shima m. Salis din a yaya ya daukesa domin tsakanin su akwai shekaru kusan 6 dalilin da yasa kuwa yake Abu kamar mace saboda an Riga da an sabar masa ne Wanda yana kokarinsa wajen danne wa da komawa namiji. Shine in yana magana sai kaga kamar yanga yakeyi.
Wayar m. Ahmad dinne tayi kara ya duba yaga vc ke kiran sa. Da mugun mamaki yake bin wayar da kallo. Vc yana neman level coordinator? Bawai yasa a kirashi ko a turo letter ba? Toh Allah yasa lafiya. Ajiyar zuciayan kwado yayi ya dauka da sallamar sa suka gaisa vc din nasu bashida girman kai.
Nan take sanar dashi yayi bako ne na kunya Dan siyasa ne amma baya gari kuma bakon dama tsayawa yayi na kwana daya su gaisa da vc din kamin ya wuce gaba. Toh shine ya duba yaga a staff dinshi m. Ahmad na daya daga cikin masu gaskiya da kuma hankali dama kuma can akwai Dan sani tsakanin baban m. Ahmad da vc din.
M Ahmad din yace okay sir ba damuwa insha Allah yanzu zanje ko? Vc din yace yeah yanzu zaka je. Kaji ko yana da wani Abu da yake bukata. Zan turo maka address din yanzu.
M. Ahmad yace toh ba matsala sir. Tana kammala wayan m. Salis yace ya akayi? M. Ahmad yace tashi ka shirya zaka rakani anguwa ne. Gyada kai kawai m. Salis yayi ya Mike shima suka shirya suka fita zuwa hotel din. Bayan sunje reception anan aka sanar musu da room number din mutumin tare da yi musu gargadi cewa minti 15 garesu dan 12 na dare yana yi za'a daina kawo ziyara saide kama daki.
A hankali m. Ahmad ke taku yana bin kofar ko wani daki da kallo Dan tun dazu da ya baro marakisiyya gaba daya jikin sa yayi sanyi. Jin kamar ana bige buge a wani daki yasa suka hanzarta domin da alamu ba lafiya ba. Har m. Ahmad zai bude m. Salis yace kul bro ka manta nan hotel ne zasu iya Kira maka yan sanda ayi filing case kayi INVERSION OF PRIVACY.
Juyawa m. Ahmad yayi zai wuce kawai sai ya juyo yace ba nan dakin zamu zo ba? Kalli room number din. Cizo marakisiyya ta gantsara masa hakan yasa ya hanzarta sakin ta yayin da ta fara ihun neman taimako. M. Ahmad najin muryar ta baisan yadda akayi ba kawai ya tsinci kansa ne yana mai kaiwa wannan tulelen banzan naushi ne ta ko ina.
M. Salis kuwa da sauri ya dauko liffayar marakisiyya ya yane Mata jikinta domin zuwa yanzu riganta kamar na mahaukaciya gaba daya a yage yake.
Police m. Salis ya Kira suka taho wiwi bayan sun gama bata lokaci wai a hakan ma sunje ne Dan an turo musu kudin mai. KAI YAN SANDAN KASARNAN KU GYARA HALIN KU. BAZANCE DUK DAYA KUKE BA AMMA YAWANCIN KU BAKWA TSORON ALLAH AKAN NAIRA 100 SAI A KASHE RAYUKA KO SU HALAKA.
YA KU MATA YAN UWA NA KUMA IYAYE SANNAN HAJIYA A WAJEN OGA, IN KINSAN MIJIN KI DAN SANDA NE KO SOJA, INA HADAKI DA ALLAH KO WANI LOKACI KI DINGA TUNA MASA GIRMAN AMANA DA HATSARIN CIN TA KIYI MASA WA'AZI DA NASIHA ME TSIMA ZUCIYA YADDA ZAIJI TSORON ALLAH YAYI AIKI BISA AMANA DA BIN DOKA.
ANA YAN DOKA SUNA KARYA DOKA KUGA YADDA SOJOJI KEYI AKAN HANYA SUYI TA KARBAN KUDIN JAMA'A, AKAN NAIRA 20 KO HAMSIN SAI A WUCE DA BOMB KO WASU MIYAGUN ABUBUWA. ALLAH KA KARA SHIRYA MANA YAN UWAN MU KA SAITA AL'AMRAN KASAR MU ME ALBARKA.
Isowar su keda wuya aka sanar dasu Wanda zasu kama nan suka fara kallon juna wannan ya kalli wannan wancan ya kalli wancan hakan yasa babu bata lokaci m. Ahmad ya Kira yazeed(na KURUCIYAR MINAL) Yace yayi magana a aiko yara suzo su wuce da Dan iskan nan.
Ana cikin wannan gwaramar lud ya dawo a bige tilif dakinsa yazo zai shiga yaga kofar bata gama ruwa ba yace ji wato mayar nan tara min sauri tayi a daki? Tsaki taja tace au ashe a hotel nake habu sauro. Fadawa yayi yaga empty yace that's good for her ashe tana da hankali yanzu gwaramar mu daya ce. Shine kawai ta sake min kurwa da anyi wannan mun raba jaha.
Jin karan ruwa a bandaki yasa yace sweety, kin dawo ne? Cikin kashe murya sailuba tace wanka nake yace ashe kin dawo. Yatsine fuska tayi tace kar ka cemin a bige kake. Yace na bige kan uw**ki. Kawai yayi tsaki ya sake kwanciya.
Mikewa yayi da kyar Dan yunwa yake ji toh banda shiririta Wanda ya sha giya ga wata ya dauka ya Kira reception mana kawai sai ya fito Wanda yayi dai dai da lokacin Da m. Ahmad ya fito da ita daga dakin bayan ya yankasa hannun yan sojoji Dan yasan mj yazeed bazai taba bari Dan siyasar yasha ba.
Kara bude ido lud yayi Dan ya tabbatar wa kansa abinda yake gani tabbas itace dafe kai yayi yace kai jama'a yanzu maiyar nan wai sa na ganta ko ina ne? Har zai wuce yaji m. Ahmad yace marakisiyya ke da aka daura auren ki me ya kawo ki hotel? Ajiyan zuciya tayi ta sake fashewa da kuka Dan zuwa yanzu muryarta ta dena fita kwata kwata.
Karbar wayan dake hannunsa tayi ta rubuta masa komai tare da karashewa da na gode da ceto na. M. Ahmad yace toh ina ne dakin naku? Da kafada tayi masa alamun itama bata sani ba. Lud suka gani tsaye a gaban su yace sheegiyaaaa karuwar banzaaaa daama bazaaaki Sami ba AI wato da nace ki koma gida shine ke da Dan iskan saurayin naki kuka kama daki ko? Har ma kin manta dakin mijin ki.
Yana kaiwa nan yayi shiru yana maimata kalmar mijinki,mijinki? Itama dai a anata kwakwalwar haka ne domin maganar tazo musu banbarakwai. M. Ahmad ne yace Mr. Lud am sorry to say but ka fahimci maganar nan a baibai. Daga masa hannu lud yayi yace gara ni maganar ce na fahimta a baibai ba tunanina ne baibai ba.
Take m. Ahmad yaji kamar lud yasan me ke faruwa dashi domin maganar tayi daidai da rayuwar m. Ahmad din wani lieutenant ne ya fito yana kiran sunan m Ahmad yace ina yarinyar ana bukatan ganin family dinta don jin dalilin da yasa aka barta tazo hotel.
Lud ne ya kallesu kamar Wanda ba yanzu yake tambele ba ya gyara nutsuwar sa muryarsa tar cikin tsurewa ya kalli sojan yace hey! Yana mikawa officer din hannu musbah sukayi cikin harcen turanci yace ni mijin ta ne kuma yau aka daura mana aure, fita nayi Nemo Mata abubuwan da Mata ke bukata sai aka samu matsalar wuta ita kuma tana tsoron duhu. Kawai sai ta fito wai tana nemana ne.
Da taga bana nan garin komawa daki shine ta shiga wrong room. Rungumeta ta yayi Wanda gaba dayan su sanda sukaji kamar an watsa musu ruwan sanyi yanda suka wani yi vibration. Peck ya Mata a goshi yace na godewa Allah ba abinda ya same ki zo muje in miki tausa.
Baki da hanci m. Ahmad ya saka jin yadda lud yake kwantara karya Wanda da ka gani kasan bawai yana yi bane Dan yana jin tsoron sojojin, ah ah so yake a basa marakisiyya ba tare da an kaita gida ba. Kuma babu shakka bawai Dan yana tausaya Mata bane zai karbeta.
Lud kuwa yana kaiwa nan ya kama hannunta suka shige daki ya rufe kofa harda lock KYAM!
AYYA! AYYA!! TUN KAMIN NA RUBUTA NEXT PAGE NASAN ZAI BADA JUICE ME SUGAR.
KARDAI KU MANTA KU TUNKUDO MIN COMMENTS YAN UWA.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
16th August,2020.
https://my.w.tt/
CHAPTER 20
Lud kuwa yana kaiwa nan ya kama hannunta suka shige daki ya rufe kofa harda lock KYAM! Cikin huci ya wullata kan gado ya bude fridge ya dauko Zuma ya zuba ruwa a Kofi yasa zuman cokali 2 ya garwaya ya shanye.
(Wannan hadin sunan shi honey water kuma yana rage karfin giya a jikin mutum sannan yakan hana yin ciwon kai da mashaya ke yi)
Zama yayi a bakin gadon yarufe ido. Bayan kamar minti uku ya bude ya taso ya cacimi wuyan Rigan marakisiyya ya dangana ta da gini yace ke Dan uw......ki shine daga fita na kika fita naki karuwancin ko?
Yar.....uba ba cewa nayi ki koma gida ba ? Falla Mata Mari yayi sanda jini ya tsiyayo ta gefen bakin ta.
Yace wow ya sake ta yana tafawa yace wato Dan kinga an mana aure shine kika rainani ko?
Toh AI tunda abinda kike nema kenan kin zo gidan ta. Amma kinsan inda aka Sami matsala ? Kinyi min karama sosai rashin imani na bai kai na tabaki ba. Ke bama wannan bace matsalar, ke har maita ma kina da shi babu tsiyar da zanyi dake yana kaiwa nan ya rufe kofar ban daki Wanda sai luba ke ciki.
Wakar da ta kunna da karan ruwa ya hanata jin hayaniyar da yake yi. Shi kuwa bed ya dauka ya daure a window ya dauko hannunta yace toh maza kama wannan ki sauka ki tafi gida.
Girgiza kai ta soma tana fadin ya lud kar kamin haka Wanda baya ma fita me kyau. Janyota take tana cijewa shi a dole sai ta kama bed sheet din ta sauka Allah yaso suna hawan farko.
Ganin zata bata masa lokaci yasa ya bude drower dinsa ya dauko safe defense bindigar sa Wanda ya nemi license. Daga shi sai boxers yace kina da zabi uku.
Ko ki fita salin alin, ko ki hau gado na kashe ki ko kuma na miki kisa mai sauki da bindiga zabi daya kamin na irga biyar ko kuma na miki duka ukun.
Tsayawa yayi bata motsa ba yace daya, biyu,uku,hudu.... tasan yadda yasha giya ba abinda bazai yi ba dukda ya rage karfinta. AI yadda kasan yar China batasan sanda ta tsallake window ba.
Bubbuga kogan bandakin sai luba ta fara tana fadin baby kofar nan tayi jamin fa ko kai ka rufe? Ciro bed sheet din yayi ya wulla a gado ya bude kofa bandakin bayan ya rufe ragan net din.
Lekawa yayi Dan ya tabbatar ta tafi yaga ta zauna ta dukun kune a kasan saitin window dinsa. Tabe baki yayi yaje ya bude sailuban yace ta gyara gado bacci yake ji. A ranta race bakada kai naje nayi shaye shayen maganin Mata na kace min bacci kake ji?
Gyara gadon dai tayi kamar yadda yace ya kwanta yana miko Mata hannu alamun tazo jikinsa a ranta tace yauwa yanzu naji batu. Hawa gadon tayi ta kwanta a jikin sa tana tsammanin taji labari sai taji shiru.
Pecking bakinsu tayi tace wai me ya sameka ne? Ajiyan zuciya yayi ya matsa daga gefenta ya bata baya yace bazaki gane ba kiyi bacci.
Matsowa ta sake yi tace haba mine haba nifa na lura cikin kwana ukun nan gudu na kakeyi kasan fa kai ka janyo matsalar nan ya za'ayi......
hannu ya daga Mata yace kiyi bacci kawai babe. Tashi yayi ta zauna tace wallahi baka isa ba yo in ba abinda zakamin wa yace ka kawoni ka ajiye ka hanani kula kowa? Ko ance ma ni yar tsana ce da zaka saka a gaba kana kallo?
Shima tashi yayi ya zauna yace ki iya bakinki ki, dalewa cinyarsa tayi ita dole zata masa karfa karfa. Ya kankade ta ya janyo belt dinsa dake ajiye gaban madubi ya fara lafta Mata yana masifa.
Ni sa'anki ne? Nace ni sa'anki ne? Ina cewa ah ah kina dagewa shegiya yanzu ma AI bakiyi latti ba sai ki tashi kije ki kula duk uban da kikeso.
Zama yayi akan kujera ya Dade kai yana tuno bakin cikin daya gaji a idon umma sanda ta fita. Shi dama tun sanda aka daura masa aure jikin sa ma yayi sanyi.
Haka kawai shi yakeyin komai ya fita a kanshi so yake ya mutu ma ko ya suma ko ma de menene.
Cikin kuka tace Dan Allah kayi.... have kina ban hakuri sai naci.......ki shegiya karuwar banza tashi ki ficemin a daki ko in zagi ubanki.
Rarrafowa ta fara ya jefeta da timberland dinsa. Tashi tayi ta saka riganta dama ita dayace sai pant a jikinta ta fice da gudu saboda yanda ya biyota.
Cikin daga murya yace yar..... uba dama gobe kizo ki kwashe tsimmokaranki babu ke babu ni dakikiya kawai.
Rufe kofar sa yayi ya fada gado yana ta huci kamar wani zaki.
.....
Tana kuka da barin sanyi a haka har bacci ya fara saceta tana gyangyadi. Kawai aka sa Mata tsumma aka toshe Mata baki burburwa ta fara yi na suka hau kokuwa har ta samu ta kwace ihu neman taimako take amma shiru kake ji ba muryar ta tafi duwatsu take diba tana so ta jefa ta windown lud amma ba wani taimako.
Lud na zaune yana busa sigari Dan har yanzu bai huce haushin yar iskan can ba haka kawai yaji zuciyar sa ta tsinke.
Nazari ya fara yana fatan ba wani matsalan ne zai taso masa ba.
Har ya kwanta ya daura hannunsa a ka yaji ana jifan window dinsa sai ya dauka ko iska ne ya kwaso Datti hakanan Dan ana iska me sanyi ne.
Mikewa yayi zai rufe window din Dan shi ya manta da cewa ya kori marakisiyya ma kawai yana lekawa yaga ana kokarin danna mutum a cikin buhu.
Tabbas dukda baya iya ganin fuskar yasan liffayar marakisiyya ne da mugun zafin nama ya kama ya dira Dan yasan kamin ya fito za'a tafi da ita. Gurde kafarsa yayi amma ko a cikinshi ya riko gayu guda biyun ya dinga karasu.
Duka ya musu ya canja musu hallita tare da hade musu jini da majina yana Duran musu ashar dama ta nan ya kware sai a lokacin mai gadin da security suka iso.
Nan ya danka musu mutanen tare da dura musu ruwa a ciki cewa zaiyi reporting gobe gobe a kirasu Dan yana daya daga cikin masu manya manyan shares are hotel din.
Zo kaga yadda suke cin karo da juna wajen basu hakuri, rashin mutunci ya lafta musu ya ciccibi marakisiyya Wanda ta kankamesa tun sanda yazo tsabar tsoro.
Kallon fuskanta yake yana haura Benin har yanzu ta rikoshi kamar ranta na jikinshi ta rufe ido gam. Har ta rame banda hanci ba abinda kake gani.
Dan murmushi kawai yayi Dan dariya ma ta basa. Bude dakin yayi ya shigo yazo bakin gado ya tsaya jin ya tsaya yasa ta bude idonta Dan ita komai ya tsaya Mata tun sanda ya fara dukan kidnappers dinnan ta rasa tunanin me zatayi ma. All that she knows is she is safe.
Kallon fuskarsa tayi ya daga gira daya tace me ? Taan kallonsa alamar tamabaya jin babu abinda ya fita yasa ta tuna muryarta ya dashe saide ta dinga aiki da maganar iska, kamar rada.
Kallon hannunta yayi da sauri fa cire daga bayan wuyansa tana sunne kai ta yace je kiyi wanka ki shirya kiyi bacci tsamin duniya kikeyi Dan ba na Abu daya kikeyi ba.
Sum sum ta wuce ya girgiza kai yana murmushi a ranshi kuwa fadi yake ta cinye kurwata shiyasa da ta shiga matsala naji a jikina wato yanzu an jona min ala kakai ko?
Yana zaune yana latsa wayarsa har ta gama wanka ta dauki lifayarta Wanda yanzu shine kayan da take da shi Dan kayan jikinta sunan shi sorry. Ninke kayan nata ta fara yi yace ke dalla shashasha saka tsimman nan a wandon shara.
Ba musu ta yar sai tayi masa kikam saboda dalili 2 na farko batada kayan da zata sa tana tsoron kar garin burgima ta bude cinema.
Ba biyu kuma batasan inda zata kwanta ba. Yace in kin gama rayuwar sai ki shinfida hakarkarin ki AI tace um dama kaya nakeso. Yace me? Tace kaya yace ni ba jinki na ke ba matso. Matsowa tayi ta sake cewa kaya nake so.
Wannan karan ya jita sarai amma sai yace matso ban jiki ba take nace kaya nakeso kayan da zansa.
Yace kai da alamu sai kin bani wahala kin taso dani daga gadon mikewa yayi yazo daf da ita tace me kike so? Sauke kanta kasa tayi cikin rawar baki tace ka.. kaya. Yace au kaya kike nufi.
Toh matsalar AI babu sayan sailuba da zai shigeki saboda yanayin halittar taki amma zo riko hannunta yayi ya fara warware Mata liffayar rikewa tayi a jinyace taja da baya da sauri ta nufi wardrobe Wanda take sa ran zata samu kayan sai luba ta fara dubawa saide me?
KARKU MANTA DA YIN COMMENT DA VOTES FA YAN UWA NA.
DAN ALLAH DUK WACCE BATAYI FOLLOWING DINA BA A TAIMAKA AYI FOLLOWING KYAUTA NE WALLAHI.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
17th August,2020.
https://my.w.tt/
14 -
CHAPTER 21
Wannan karan ya jita sarai amma sai yace matso ban jiki ba take nace kaya nakeso kayan da zansa. Yace kai da alamu sai kin bani wahala kin taso dani daga gadon mikewa yayi yazo daf da ita tace me kike so? Sauke kanta kasa tayi cikin rawar baki tace ka.. kaya. Yace au kaya kike nufi. Toh matsalar AI babu sayan sailuba da zai shigeki saboda yanayin halittar taki amma zo riko hannunta yayi ya fara warware Mata liffayar rikewa tayi a jinyace taja da baya da sauri ta nufi wardrobe Wanda take sa ran zata samu kayan sai luba ta fara dubawa saide me?
Duk kayan dake wajen babu wani na arziki Wanda zata iya sawa, daga me budadden baya sai me budadden ciki da cinya ja da baya tayi ta kalleshi tace babu kayan da zan sa a nan din. Manna Mata yayi yaci gaba da game dinsa tace ya lud ya juya kwanciya matsowa tayi a tunanin ta bai jita bane ta tsaya a saitin kansa tace ya lud nace babu kayan da zansa a kayan nata.
Yace wai bakiyi primary bane ko bakusan in za'ayi wa manya magana a tsuguna bane? Durkusawa tayi ya sauko yace zo muje. Kama hannunta yayi.ya kaita wajen wardrobe din a bayanta ya tsaya yana dudduba kayan yana nazari abinda bai sani ba shine marakisiyya gaba daya a takura take saboda kusancin dake tsakanin su.
Juyowa tayi tana kyakkyafta ido tace uhm ya lud bari in jira ka samo min rigan. Sunkuyawa tayi zata fita daga gabanshi ta koma baya ya riko liffayar ta ya janyota baya yace dawo nan wurin ki tsaya. Dan ni banji me kika ce ba ma wani half vest ya miko Mata yace sa wannan tace amma yace ba musu. Mini skirt ya miko Mata tace ta yaya zanyi bacci da skirt? Yace toh ko in matsa ne uwar iyayi? Girgiza kai tayi ya dauko wani three-quater na wando ya bata karba tayi ta shiga toilet ta saka.
Fitowa tayi kawai ya fashe da dariya yana nuna ta da yatsa kallon kanta takeyi ita bata ga wani matsala ba yace jar uba tsigi tsula din kenan. Kai jama'a gaskiya tsolon rake Allah yayi ki siririya jibeki a ciki vest dinnan fa ji cikinki kamar slippers. A ranta tace mutumin nan bashida mutunci ko kadan.
Sallah tayi Dan tsabar fadi tashin da ake ko sallah batayi ba. Sanda ta Mike rana ninke sallah lokacin lud yana gefen karamin tea table dinsu yana zuba ruwa zafi.
Hawa gadon tayi zata kwanta yace hey! hey!! hey!!! Bitch ya haka ? Wani kallo marakisiyya ta watsa masa yace Dan na yarda kin shigo daki na ba yana nufin cewa a gado na zaki kwana ba ki zabi daya kujera ko kasa.
Dirowa tayi daga gadon tana dangwalar sa tace who did you called a bitch? Nace wa ka Kira da wannan sunan? Wai kai wani irin mutum ne Wanda bashida imani? Me yasa bazaka taba kyautawa kanka ka kyauta mana ba. Ka sani ka cutar da mahaifiyar ka hatta mahaifin ka sanda muka fito na tabbata daddy ba daidai yake ba. Faduwa gaban lud yayi jin hakan.
Tace rashin imani ne zaisa ka koreni cikin dare na koma gida wannan bai isheka ba kana gani an kusa ayi min FYADE amma me da kazo sai ka daura min sharrin zina na dauka a kalla tunda kaga 12 ta kusa zaka barni sai gobe ka miyar dani amma Dan rashin ganin darajar mace sai kace na tsallake na fita ta window.
Kuma sai gala kamar mutumin arziki kazo ceto na ka sani da wani Abu ya same ni a daren nan da tabbas Kaine sanadi kuma ka sani umma na bazata taba barinka ba. Jikinsa ne yayi sanyi ya riko hannunta yace marakisiy.....
Daga masa hannu tayi tace dakata malam kar ka Kira sunana ko da wasa wallahi Dan sunana yafi karfin bakinka. Kuma karka damu bazan kwanta maka a gado ba dama pillow na hau zan dauka Dan ni kaina bazanso na kasance kusa sa kai ba amma me ? Shi kanshi pillows nasan wace tsiyar akayi dashi ba da kake gurin matarka na sunna gara ka zauna da karuwa Mtsw! Dukda muryarta na tafiya yana dawowa babu abinda baiji ba.
Ita ko tana kaiwa nan ta juya zata kwanta a kujera ya warbo ta ya wulla man gado yace da kinyi bayani da wuri ai kanki tsaye kice hakkin ki kike nema. Kokuwa suka fara yace yana fadin shegiya fitsararriya nadauka kinyi hankali naga kin zama abin tausayi har ina hada miki shayi saboda muryanki wai ni nan na tausaya miki shine zaki ce min banida imani ko? Ta tashi Dan uw*ki.
Kamo gashinta yayi ya wulla ta a dogon kujeran ya dauki kofin shayi mai zafin yace karbi kisha sh*giya muna fuka kawai dauke kai tayi tana kuka ta daka tsawa tace bazan sha ba ! Yace oh bazaki sha ba? AI kuwa baki isa kiyi min asarar kudina ba wallahi.
Kamo bakinta yayi ya dura Mata tana burburwa duk ya koma Mata baki da lebenta. Cilli yayi da kofin yace aikin banza kawai. Anan ta kwanta tana kuka Dan ribbon dake kanta ma yayi Mata cilli dashi gefe. A ranta fadi take ina ma m. Ahmad ta zaba tasan ko ba komai bazaiyi Mata wannan cin mutunci da diban albarka ba a haka har bacci ya kasheta tana ta ajiyan zuciya.
Bayan ya daina jin shesshekan ta ya tashi yayi wanka da towel dinsa ya fito yana goge jiki ya wani iri yaji a zuciyan sa. Bude wardrobe yayi ya dauko wani rigan pillow da bargo ya canja rigan pillown sailuba ya daura kan marakisiyya. Murmushi yayi ganin yadda ta turbune fuskan ya ja hannunta yace yace yar iska ne yarinyar nan gata da bada haushi ga abin tausayi.
Goge Mata hawayen yayi ya dauko ribbon dinta a hankali ya daure Mata gashin a gaban goshi.
Rufeta yayi da bargon ya dauko man baki ya shafa Mata saboda yadda yaga lebenta yayi ja. Shafa kanta yayi yana ta kallonta tana bacci a hankali yace kiyi hakuri!
Mikewa yayi yaje ya kwanta zuciyarsa sske saken abubuwa da dama da kuma yadda zai mayar da ita ba tare da ran kowa ta baci ba.
M. Ahmad ma tunda suka tafi zuciyar sa ke masa wani iri bai tanajin yayi kuskure ba sai akan auren marakisiyya nadama ne ya lullube shi ta ko ina. M. Salis yace kasa hakuri a ranka Ahmad komai zai wuce ni naga kaunarsa a idon mijinta in ma na yan uwantaka ok a matsayin ta na matarsa nasan komai zai wuce insha Allah.
Ajiyan zuciya m. Ahmad ya sauke nan suka kashe wuta m. Salis yayi bacci yayinda m. Ahmad ya dinga juye juye bayan ya turawa VC email akan abinda ya faru.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
18th August,2020.
https://my.w.tt/
CHAPTER 22
Da asuba marakisiyya na tashi ta zabura shafa inda ta kwanta tayi ta sauke ajiyar zuciya tunowa da cewa ta sha maganin ta muma ta saka pad yau bata tsula ba. Da sauri ta shige bandaki ta cire ta gyara jikinta tayi su alwala sannan ta fito sai lokacin ta lura ma ashe ba a gida take ba tunowa yayi da duk abinda ya faru jiya Wanda yasa ta kara murtuke fuska tana jin kamar tayi wa lud mugun duka Dan ba karamin haushi ya bata ba jiya bayan tayi sallah ne tazo ta tsaya a kansa.
Sai zata tashe sa sai ta fasa sai zata tashe sa sai ta sake fasawa. Rufe ido tasa hannu a kafadar sa ta bubbuga, juyi yayi yace uhmm? Menene? Cikin dashesshiyar muryarta Wanda bai gama gyaruwa ba tace ka tashi kayi sallah. Sake gyara bargonsa yayi yace Sally ki rabi dani don Allah me zan miki da sanyin safiyan nan? Sake bubbuga shi tayi a kufule ya tashi ya zauna ya finciko ta ya manna Mata peck a baki ya sake kwanciya fuskarsa na kallon sama yayinda Rabin jikinta ke kan cinyarsa yana fadin shikenan AI ko? Bye bye sai kin dawo. Mikewa marakisiyya tayi ta goge bakinta kamar zatayi amai ta daka masa duka a cinya.
Da ashar don da ta fara da k*tma ya Mike ya Damkota sai a lokacin ya kalli marakis ce yace tsolon rake Dan.....ki me kikeyi anan? Ni sa'an ki ne zaki dakeni? Tabe baki tayi ba raini ba gimamawa tace yi hakuri ba da niya nayi ba da farko dai so called aure ne ya kawo ni dakinka.
Ba biyu kuma ni ba sa'ar la bace ka girme ni, saide dalilin da yasa na dake ka shine..........
Yace kaji makaryaciyar banza da wofi. Ni me zanyi da tsiya irinki wai ke tsolo in bakiyi karya bazaki rayu bane ko me? Yanzu ace mutum kamar sandan rake AI ko yaro ba abinda zaiyi dake bare babba. Tace munji dai ko ba komai AI sanda rake yana da zaki ga ruwa ta ko ina kuma yafi gundiren doya Wanda sai anci wuya ake dafawa.
Kaga sandan rake ko na 200 ka siya ta ishi kowa ya samu amma doya fa ansiya karama yar 900 kuma ba kowa zai koshi ba mutum 2 ma sai su cinye,abinda nake nufi shine nafi albarka akan o'o.
Yace kut! To ke banda shirmen ki daga an shanye rake ake watsar da totuwar a titi, race shi kuma bawon doya kirashi ake gaban madubi ko? Yace bitch, wai Sally na kike zagi ? Tace sallyn ka? Kananu tayi da ido tace ka sake kira na da bitch ? Wow! Hmm ni na jawa kaina.
Kama kanshi tayi ta kwantar a pillown tace ayi bacci lafiya ta koma kan kujera ta kwanta taja bargon ta bashi baya. Nazari ta fara ya akayi ta samu bargo bayan da liffayar ta ta rufu? Murmushi tayi da tayi tunanin lud ne yasa Mata daure fuska tayi da ta tuna rashin mutuncin da ya Mata.
Shima saukowa yayi kamar barawo da sanda ya leka fuskarta yaga ta rufe da bargo hakan yasa ya fara dagawa a hankali. Tunani marakisiyya tayi what if jiya ya yi Mata wani abun da sauri ta dago zatayi masifa suka gware goshi yace what in h*ll is this ? Kanki daya kuwa jiyadda kika gwara min wannan jirgin naki a goshina.
Tace ba ma wannan ba me kamin jiya da ka saka min bargo ? Murmushi yayi yace ba komai fa kawai Dan kalle kalle nayi kuma ma sai naga babu abin kallon amma bari muga. Ya kai hannunsa wajen riganta da sauri ta dafe tasa kafa ta turesa tace Dan iska kawai me ma ya kawoka kusa da fuskana? Yace morning kiss nazo karba amma sai na samu morning collision a goshi.
Yake tayi tace AI da ka fada da wuri zo in baka tsugunawa yayi ya sakala hannunsa biyu a kwankwason ta yayinda take zaune a kujera saka hannun ta tayi ta riko fuskarta ta kawo kusa na nata a take murmushin dake kan fuskarta ta dauke tace me zai hana kaje wajen so called Sallyn ka? Sai ta baka warm k*ss ko ya kace? Um? Ta daga gira? Dariya yayi yace Allah yasha dake bakya sona bare ki samu heartbreak dama gwadaki nati kin wuce test number one.
Yana kaiwa nan ya shiga toilet yana sauke ajiyan zuciya. Tsaki taja ta kwanta yayinda shi kuwa ya kunna kansa ruwa yana nazarin yadda zaiyi ya kwato kurwansa a hannun marakisiyya domin kuwa tana kara cinye kurwarsa Dan yanzu a cikin jikinsa yake jinta. Solution daya ne kawai zaiyi kokari su rage yin fada daga nan sai ya roketa ta bashi kurwarsa tana bashi sai ya Mata na jaki.
Da wannan shawaran ya fito daga wankan ya samu har ta koma bacci. Sallaya ya shinfida yana tunanin ta ina ma zai fara sallar kuma raka'a nawa? Dan shi banda sallah na Eid sai juma'a sauran kawai sai rabbi yayi ne yake jona masallati ayi dashi. Tagumi yayi yace kai ya kamata na hankalta fa kar mala'ikan mutuwa yayi wuf dani Dan tun sanda aka daura mina ure da wancan yar tsana na gane banida iko da kaina.
Daukar wayan sa yayi tare da searching komai akan yadda ake yin sallah tare da sunnoni har ma farilla duk ya koya Dan kusan 30 min ya ribanta yana research. Bayan ya idar ne yaga marakisiyya tayi fale fale Rabin jikinta ma ya sauko a kujeran. Daukota yayi ya daura a gadon bayan ya gyara ya rufeta da bargo yana kallonta.
Riko hannunta yayi a hankali yace yar kanwata na gode da kika tashe ni nayi sallah. Gaba daya jikin sa ya mutu saboda a Dan binciken da yayi ya ga yadda hukunci marasa yin sallah da bari ta fita akan lokaci take yaga yadda Allah ke kafurta su. Baisan sands hawaye ya zubo masa ba. Haka kawai ya ji a ransa yanason ya samu Karin Ilimi akan Islam.
Shiryawa yayi cikin wasu manyan kaya wanda bai taba saka su ba ya fita domin siyo wa marakisiyya kayan da zata Dan saka kamin ya kaita shopping.
Kamin ya fita ne ya rubuta letter ya ajiye kamar haka "morning tsolon rake! Idan kin tashi kiyi order din abinci kice dakin LUMA za'a kai. Sauran kiyi order mai tsada ni da ke ne. Sai na dawo."
.......
Umma kuwa tana zaune a gefen daddy Wanda aka daura ma drop a gida sbd yanayin NASA baiyi tsauri ba. Riko hannunta yayi bayan ta gama bashi shayi lace Mata ta ni kadai, mai zai hana ki kaiwa yarannan ziyarar ba zata? Kallonshi tayi tace amma Alhaji AI bakada lafiya ya zanyi na barka cikin yanayin nan.
Yace karki damu bacci zanyi in kika tafi zan jira ki dawo. Kinsan halin yaron nan ba kadan daga aikinsa bane ace yarinyar ba a waje ta kwana Dan tunda kika tafi da ita hankali na bai kwanta ba.
Tace toh shikenan mijina zanje. Gyara masa kwanciya yayi taje ta shirya, driver ya kwashe ta bai tsaya ko ina ba sai hotel din da lud yake kamar yadda umma ta sanar dashi.
Receptionist na ganinta ta gane ta. Gaishe ta tayi umma ta amsa sama sama. Receptionist din tace oga Luma ya fita fa. Umma tace ba wani luma nake nema ba Dana nake nema. Receptionist race eh shi nake nufi AI umma tace matar sa da. Girgiza kai receptionist tayi.
Hawa sama umma tayi direct ta nufi dakin da ta kai diyar ta tana budewa taga hajiyarku an Sami gado ta Mike cinya tayi dai dai a tsakiyar gado. Ribbon ma yasan inda dare ya masa. Dariya kasa kasa umma tayi ta sauke ajiyan zuciya. Tace umm su cuwuna (mai suna na) an Sami dadi sai bacci ake.
KAI KAI HANNUNA CIWO YAKE MIN TSABAR WAHALAR TYPING. NASAN JIYA KUN JINI SHIRU IN FADA MUKU WAI SAIDE MESSAGE YA SHIGO NI NAWA BAYA TAFIYA SHIYASA MA KO TIRAWA BANYI BA SANDA NA KIRA CUSTOMER SERVICE TUKUN YA GYARU.
TUNATARWA: A CIKIN ISLAM ADDININ ANNABI MUHAMMAD (SAW) BABU WANI ABU KAMAR BIKIN ZAGAIYOWAR SHEKARA. DOMIN WANNAN BIKIN ARNA NE KUMA MU A KOWANI LOKACI SO AKE MU SABA MUSU. A LOKACIN SA SAHABAI BASUYI WA JUNA MURNANR SHIGA SABUWAR SHEKARA KO MAKAMANCINSU SAIDE:
HADRAT BN ABDULLAH BN HISHAM YA RAWAITO CEWA SAHABBAI SUNA KARANTA WANNAN ADDU'AR IDAN AN SHIGA SABUWAR SHEKARA KO WATA:
اللهم أَدْخِلْهُ عَلينا بِالأمْنِ وَالإيمان وَالسَّلامَةِ وَالإسْلام وَرِضْوَانٍ مِّنَ الرَّحْمن وِجوارٍ مِّنَ الشَّيْطان
Allahumma adkhilhu 'alayna bil amni wal iman, was salamati wal islam, wa ridwanim minar Rahman, wa jiwarim minash shaytan
(Al-Mu'ujamul Awsad' Na Tabarani, Hadith: 6237)
WACE LITTAFIN HADISI NE MU'UJAMUL ASWAD?
Al-Mu'ujam al-Awsat (a larabci: المعجم الأوسط للطبراني), daya daga cikin manya kuma sanannun littafi ne na hadisai Wanda wani babban malami me suna Abu 'l-Qāwsim Sulaimān Ibn Ahmad ibn Ayyoob ibn Muṭawyyir al-Lakhmī ash-Shāmī at-Ṭabarānī Al- Hambali
Na shekara(874-971 CE, 260-360 AH).
FATAN DAI KUNA YIN AIKI DA DARUSAN DAKE CIKI DAN IN BAKUYIN AIKI DASHI BABU ANFANIN SHI..
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
20th,August,2020.
CHAPTER 23
Rufe kofar dakin umma tayi ta shiga yare da dama a bakin gadon ta Daka wa marakisiyya duka tace tashi mutuniyar banza. Juyi marakis tayi tace ya lud nayi fushi karka dameni.
Bubbuga ta umma tayi tana fadin ke taahi ni ba mijinki bane bare kimin shagwaba munafuka Lamar ba jiya kika gama rusawa mutane kuka cewa bazaki zo ba.
Baki a washe marakisiyya ta Mike tana fadin la umma na dama kece yaushe kika zo? Murmushi umma tayi tace ta yaya kuwa zakiyi kisan nazo kin shanya baki sai bacci kike kamar kasa ina mijin naki. Waigawa tayi bata gansa ba tace nima ban sani ba kila ya fita ko yana bandaki.
Baki bude umma tace Allah manyan mats toh mijin naki fita yayi receptionist din hotel ma ta sani bare ke matar sa.
Marakisiyya ba fa haka zaman aure yake ba shi aure da sauri marakisiyya ta dira daga gadon tana fadan umma na gode yanzu shekaru 5 kenan kina maimata min zance daya tun ina da 15 da nace zanyi aure kike maimatawa.
Tana kaiwa nan ta fada bandaki umma tace kaji min ja'irar diya, toh aiko zaki tsara ne maza kiyi kiyi ki fito ki karbi guntun tarukucen ki. Bayan marakisiyya ta fito ne tazo ta zauna a gefen umma ta turo baki tace umma gaskiya ni ina so ki koma gida tare da ni.
Zaro ido umma tayi tace sannu uwar hauka kinsan kalar mijinki shine zaki gudu, toh in kin tafi sai ya dawo da sarauniya sa bazawarar arniyar nan. Dariya marakisiyya tayi tace kai umma na.
Umma tace ke ni na manta ban tambaye ki ba tana ina ? Dage kafada tayi ta sauke tana tabe baki tace nima tunda nazo ban ganta ba.
Amma umma me ya kawo ki? Umma tace jiya bayan mun tafi nasan kema kin lura de toh da na koma na samu abban ku bashida lafiya shine fa yau ya dage sai nazo muku surprise naga zaman ku.
Bude baki marakisiyya tayi zata ce AI da jiya kika zo bazaki sameni a dakin ba ma sai kuma taga zata hada fada tsakanin uwa da da kawai sai tayi murmushi tace amma umma tare zamu tafi na duba daddy ko?
Umma tace a'a ki bari de mijinki yazo sai ku ta fi turo baki marakis tayi umma tace banason tashin hankali maza tashi kije kiyi wanka ki jirashi ni zan wuce ki kara hakuri kinji? Daga kai marakisiyya tayi ta shiga wankan har umma ta tashi ta hango paper a ninke.
Dubawa tayi taga bayan an rubuta from amazing husband to his loving and beautiful wife. Dariya tayi tace oh yaran nan munafukai ne ji yadda suke Abu kamar makiya amma daga dinkewa har an fara baron love letter ma juna. Marakisiyya tace umma me kike nifi.
Toshe baki umma tayi Dan kar tayi dariya kamin tace in kin fito zaki gani ni bari na rufawa kaina asiri na tafi kamin na karanta na makance Dan yaron nan ba kan gado ne dashi ba yanzu sai naga batsa.
Ta fita zata janyo musu kofa kenan idonta ya fada kan wani gajeran wandon lud da sauri ta rufe tana goge glasses dinta tare da fadin ba da ni ba.
Abinda umma bata sani ba kuwa lud gatse yayi wa marakisiyya saboda fadan da sukayi da safe yayi ne Dan ya tsokaneta shiyasa cikin letter din ya fara da tsolon rake.
Daure da towel marakisiyya ta fito tana zumbure zumbure Dan ba karamin haushi taji ba da umma ta tafi ta barta ji tayi an hankade kofar da fiton sa ya tsirmo dauke kai tayi tace haba ya lud ya zaka shigo ko sallama babu ni fa dakin nan ma gani nake ko sallaya basa karuwa idan na koma gida sai na sake su.
Ka gama sheke ayarka da doyarka da sauran kadangarun dake binka kuma yanzu ka wani zo ko Dan sallam baka yi kila shaidan su ragu.
Yace tashin hankali, toh bar batun sallama tukun uban waye ya baki izinin taba min towel Dina?
Hararan sa tayi tace toh ba kaya kake so na zauna ko me? Yace toh in kin zauna ba kayan ma ance miki yana da wani banbanci ne a waje na? Wai ke me kika dauki kanki ne ma iye? You think you are a goddamn beauty damsel ne? Hararan sa tayi tace AI ni yanzu ba damsel bace ko ka manta nayi aure ne ?
Cikin ko in kula yace toh banda bada sadakin ki da akayi Fadamin marabarki da budurwa. Tsaki taja ta zauna a bakin gado ta daura kafa daya akan daya tace
Banida kayan sawa ka Nemo min. Yace nima Riga ce sai ki sakani.
Wayar sa ya ciro ya danna numbar sailuba ringing din farko ta dauka tace haba honey nide nasan cewa bazaka iya kwana daya babu ni ba domin wannan tsiyar matar taka babu abinda zata iya yi maka. Yanzu dai yaushe zaka zo ka dauke ni kaga a gidan kawata fa nake zaune tunda dai kasan.....
Yace hey! hey!! hey!!!dallah yimin shiru duk kin cika min kunne da surutu kinyi brush kuwa Dan wani hamami make ji ta cikin wayan yanzu dai ba wannan ba ina kika ajiye min kayan tsiyar matar tawa? Dan tabbas naga umma ta shigo da akwatin ta kinga fa tun jiya ba kaya take zaune ki taimaka mana.
Yanda ya fada kai kasan so yake ya bata haushi. Ita ko dafe kirji tayi Dan tabbas ba ko shakka tasan halin sa kana zaune da kaya ma bai barka ba balle ba kaya a ranta tace shikenan nikam tawa ta kare sunana sorry.
Cike da bacin rai tace banza Dan iska da alamu sharholiyar taku bata je jikin window ba da kaga tsimmokaranta a bayan labule. Ba tsane ka lud wallahi na tsane ka. Dariya yayi yace daga baya kenan "honey" ya maimata kalmar da ta fara masa magana dashi sanda ta dauki wayar.
Kashewa yayi ya bude akwatin. Wani pelazu da t-shirt ya dauko Mata yace yauwa dama ni kullum cikin wannan labulen rigunan make kallonki yau wannan zaki saka min tace kai de ka sani dalla bani.
Karba tayi hat zata shiga toilet ta dawo tace ka dauke min tsiyar gajeran wandon ka Dan mahaifiyar ka ma ta kalla.
Da sauri ta shige yace me kike nufi? Sharesa tayi sai bayan ta fito ne tace ya ka gani yace flawless dariya tayi tace ya lud muje gida dazu umma tazo take cewa dad bayida lafiya.
Lud da ya shagala da kallonta ya bude baki da hanci yace me kika ce? Maimatawa tayi yace na'am na'am dad yana kiran mu? Make kafadarsa tayi tana kare kirjinta tace dalla can me kuma zaka gani a tsiyar lemon tsami na duk ka yafeni da mujiya? cemaka nayi dad bashida lafiya!
Zabura lud yayi yace toh me kike jira muje tace muje toh har zasu fita ya juyo ya kalleta yace bazaki sa mayafi ba? Tace buhu ne fa rigunan ko ka manta ne kuma naga ko doya ma ai ba kaya take fita.
Rike hannunta yayi yace wasa nake miki kayan ne sukemin kyau da gangan nake cewa buhu Dan na tsokaneki. Daura mata after dress din yayi yaja hannunta suka fita sauri sauri gudu gudu.
Garin saukowa a beni ne ta gurde kafarta sanadin cogen da ta saka Wanda lud ne ya dage a cewar sa bai taba ganin ta saka ba. Fadawa tayi jikinsa lokacin daidai waitress zata kai masa special coffee dinsa kamar kullum.
NAJI RUWAN COMMENT FA TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
21st August,2020.
CHAPTER 24
Fadawa tayi jikinsa lokacin daidai waitress zata kai masa special coffee dinsa kamar kullum. Sanadin fadawan da tayi jikin sa hakan yasa ta tankwabe kofin coffee din.
Sulewa sukayi dukan su biyu ta bige bayanta. Ihu ta kwala da sauri ya rufe Mata baki ya Mike dam shima ya bige guiwar sa. Daukarta yayi da sauri suka fice Dan bayasan yan restaurant din su kawo masa raini.
Receptionist kuwa sai zuba murmushi take tace awwn ashe matarsa kyau gareta wallahi sun burgeni ko ba shi ba fa amma da kullum yana tare da wannan sh*giya dukurkuran karuwar. Rike hannun wata waitress tayi tace Dan Allah bata yi miki kyau ba?
Gyada kai tayi wata ma'aikaciya ma dake gefe tace har na ga yaransu wallahi sun shiga raina. Receptionist tace kede bari da ina planning yadda zanyi na samesa amma yanzu na fasa wallahi matar tashi ta shiga raina Allah ya basu zaman lafiya. Ameen kowa ya amsa.
Shugaban ma'aikata ne yazo zai wuce yace ms tahir(receptionist) ya naga hat yanzu kece a duty bayan shift dinki ya wuce. Tace wallahi sis mariya ne tace bazat zo da wuri ba yau shiyasa ban tafi ba.
Har ya wuce zai tafi ta biyo sa da sauri ta nuna masa hotan su lud tace sir kaga mutumin mu oga luma. Kalla yayi yana murza hana yace kai amma wannan karan yayi kamu mai kyau saide daga gani sabon shiga ce yarinyar ko?
Kallon me yasa baka zuwa gana ta masa ta sauke ajiyan zuciya tace kash dadi na dakai ba kyautata zato toh aure yayi matar sa ce. Yace what? Dariya ya fashe dashi yace cabdi oga luma manya me salo salo yau kuma hotel ya kawo matar ? Toh Allah ya bada zaman lafiya.
Har yayi gaba yayi baya yace baki ji ba, kur kur kur ta matso yace naga alamun nutsuwa a jikin sa dukda cewa hotone. Dariya suka fashe dashi tace kamar kana raina oga yace toh ya isa ya isa maza koma bakin aikin ki. Nan dai suka ci gaba da hiran lud da marakisiyya da yadda sukayi
Suna shiga mota ta kifa kai a cinyanta. Cikin bacin rai yace me haka tsolon rake ya zaki tsinkani gaban mutane kaman wasu sakarkaru. In so like ki taba six packs Dina ba sai kinyi wannan drama din ba.
Dagowa tayi fuska shabe shabe da hawaye tace wato kai abinda ya dameka kenan wani mutuncin da babu shi? Baka damu da cewa baya na yaji ciwo ba ko? Kai mutane ne suka dameka matar ka ko oho ko? Da sauri ya taba wajen ta danyi kara yace sorry yi hakuri bansan kinji ciwo bane.
In Munje gida sai inyi miki ruwan dimi ko? Ya fada yana danna wajen a hankali ture hannunsa tayi tace ka matsa banaso. Ba dai fada kake min ba? AI sai ka yankani ka huta.
Dafe kai yayi cikin tsawa yace wai ku Mata menene matsalarku? In an muku tsawa kuce an muku tsawa ba'a damu daku ba in an lallabaku kuma ku tsaya kuna jan aji wa mutum.
Hannu tasa tana dangwalan kirjinsa tace matsalar mu shine bakwa fahimtar mu da fari bamason ana mana mu'amala Lamar anayi da bayi. Qur'an mai girma ya tabbatar da cewa mu Mata a matsayi abokiya ya kamata ku rikemu saboda babu abinda mukeso kamar muga an nuna ansan Kumar mu.
Toh mu kuma a matsayin shugaba akeso mu rike ku domin babu abinda mukeso kamar respect sannan kun tsani raini kaga in haka ta samu sai zaman lafiya ta wanzu. Amma ya zakayi ka bawa kura dusa ka bawa akuya nama kace yunwa bazata kashe su ba?
Amma kai a rayuwanna....jamyota yayi ya rungume yace shhhhh! Ya isa ni banason kukan nan haka nace na daina ko? Kuma AI bansan ba da gangan kikayi ba. Yi shiru yar umma dariya suka kyalkyale dashi Dan tasan tsokanan ta yakeyi domin kuwa duk sanda take kuka haka umma take Mata, kuma ranan abinda take so shi za'a dafa a gidan.
Tunowa da wannan yasa yace kin samu paper din da na ajiye miki? Dan hade gira tayi yana goge Mata hawayen da ya fara bushewa tace ah ah ban gani ba. Yace okay.....
Waya ya daga yace large special threat muna mota. Tace abinci kayi mana order ? Da gira ya Mata alamun eh yana gyara sajen dake shinfida a fuskar sa.
Bayan minti 5 zuwa 6 sai gashi an kawo musu karba yayi ya kunna motar sa ya kama hanyar gidan su. Bayan sun isa ne ya tsaya daga bakin gate ya bude abincin da suka siya.
Dauke kai tayi kamar bata gani ba ya bubbuga kafadar ta yace uwani abincin ma fushi ake dashi turo baki tayi ta sake kallon gefe ya kamo fuskanta ya rike bakin kyam ya tura Mata abincin furzarwa zatayi yace kina furzarwa zaki ga me zan miki a motan nan. Haka ya dinga dura Mata abincin abinda bai sani ba shine tana da allergy na green beans tace ya lud na koshi.
Yace baki isa ba so kike umma tace kin rame a sakani a gaba ko? Wai ke yaushe zakiyi imani ne kullum burinki kiga umma na tana min fada ko? Kicin kicin tayi da ido tace da inaso ayi maka fada da na fada Mata abinda kayi min jiya kuma da kake ce min yaushe zanyi imani kai kana da shi ne? Ko makiyiyar ka ce ni bazaka fitar dani cikin dubun daren nan ba amma haka ka diro dani ta window.
Sannan kuma ba umman ka bane umma ta ce ni daya can ka tafi ka nemi naka tunda saka ta kuka kake yi. Murkude baki tayi tana Dan yatsine domin jin yadda zuciyar ta ya fara daurawa. Yace God have mercy! Me zanyi da yarinyar nan ne ?
Kallon ta yayi yace wai ke wace irin zuciya ce dake baaaakida tafoya ko kadan ince abun nan ya wuce ko bakiji me bature yace bane past is past iye?
Tace ba wani past is past da an sameni da yanzu kana can kana fiki fiki da ido kana fesawa umma na karya yadda kayi wa yan sandan nan.
Yace iko sai Allah yau naga ma mutum ke wai ba har hakuri na ba....... shiru yayi ganin in yaci gaba da biye Mata raini ne kawai zai shiga tsakanin su nace wanne ne ma ba'ayi ba?
Tace inajin ka yace share kawai cire robbin yayi masu abinci kuma ya mayar cikin package dinsu ya ajiye a motan fita yayi ya fara shirin shiga.gida tace ah ah ni kuma fa ? Yace me zan miki ? Tace bazaka shigar damu gidan bane ? Yace me aiki kafafun ki ? Abin tausayi tayi masa tace Ayya banana banida baya ko ka manta ne?
Tsaki taja yazo ya dauke daidai zai saka kafarsa a gate yaji wani dam a kirjinsa hakan yasa ya tsaya da taku kallon fuskarsa dake kallon straight hanya tayi tace menene kuma?
Kin kallon ta yayi tace da taga kamar bayason ya kalle ta ma tace akwai wani Abu a fuskanta na ne? Waiyo Allah na karde muni nayi? Ko pimples ne ya fito min?
Baisan sanda ya kalleta ba yace wani makaryacin ne yace miki kina da kyau? Maiya kawai yana kaiwa nan yaci gaba da tafiyar sa yayinda marakis ke cika tana batsewa.
Yana salo kai kuwa yan aiki kowa sai zai miko gaisuwa sai mamaki ta rike masa baki. Da ido hanci da baki har da kunne haka suke binsu da kallon wasu har muttsika ido suke domin tabbatar wa wai shin da gaske Alhaji karami da hajiya karama ne kode matsala aka samu.
Me gadi ne ya jinjina kai yace aure dadi lud yace a gidan uban ka ba. Yana wuce wa kowa ya saki dariyar da yake kunshewa me yanke flower yace duk yadda Alhaji karami zaiyi hankali halin bazai canja ba. Knocking din kofa lud yayi yayinda yake fadin tsolon rake gaskiya nauyi gareki kan bala'I.
😂😂YACE BAYAJIN GARI YA DAUKA ZAI JI TA KAMAR PAPER
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
23rd August,2020.
CHAPTER 24
Harara ta banka masa tace ni kaga banson neman magana in kasan bakar magana zaka dinga fadamin da can nace ka dauke ni ne ? Yace au haka ma kika ce? Tace kwarai yace AI shikenan sauke ki kuwa zanyi. Tace ka Riga kuda..... kamin ta karashe taji ta dam a kasa.
Rufe ido tayi sanda hawayen azaba ya sauko Mata kawai ta dafe gurin. Yace tashi mana uwar rash......hawayen da yaga ya sauko daga fuskarta yasa ya tsuguna yace menene? Juyar da kanta tayi ya kalli inda ta dafe daura hannunshi yayi yace nan ne ? Ture hannun nasa tayi ya ciccibe ta.
Burburwa zatayi bayan ta ya rike babu shiri ta dawo saiti. Kama hannun kofan yayi ya bankada ya shige daidai lokacin ne kuma umma ke shirin bide musu kofar.
Ganin yanayin marakisiyyan yasa a tsorace tace subhanallah me ya faru? Faduwa gabanta yayi da wani tunani ya zo Mata wani kallon kisa take aikawa lud da sauri ya daga hannu yace wallahi umma ni ban Mata komai ba kawai hannunta na rike mukayi bacci.
Cikin kuka marakisiyya take aika masa kallon da izinin wa ka rike min hannu? Tabe baki yayi yace kin manta yanzu ma na daukeki?
Ajiyan zuciya umma ta sauke ganin ba abin da take tunani bane yayinda wani bangare na zuciyar ta yayi la'asar ganin cewa bata wani canja zani tsakanin yaran nata ba.
Tace ku duba abban naku yana cikin daki yana jiran ku. Tashi lud yayi ko a jikin sa zai shige dakin daddy. Marakisiyya tace ubale kayi mantuwa fa.
Da hannu ya Mata alamun me ja manta ? Tace kayan wankin da ka jibge a Kan kujera mana. Banka Mata harara yayi ya dawo ya tallafe ta suka karasa har dakin tare da sa kai ciki.
Daddy na kallonsu ya tashi ya zauna yana murmushi yace yaran albarka kun iso? Daure fuska marakisiyya tayi tana Dan yatsine amma a haka ta daure suka gaisa da daddy.
Numfashin ta ne ya fara sauyawa ta Mike zata falla da gudu ta fada ban daki amma me? Tim ta fadi a kasa.
Amai ta kwararo daidai lokacin da umma ke shigowa tace subhanallah marakisiyya ya haka? Me ya sameki? Lud shi ya rasa ma tsayawa zaiyi ko zama?
Bayan ta gama kakare kakaren ta umma tace dauketa ka gyara Mata jiki a toilet ba musu ya dauketa dukda cewa yana jin kyankyamin suma shiga toilet ya dangwarar ta kasa ya tsuguna a gabanta yace Dan shine kika kwararawa mutane amai ko?
Hararandhi tayi tace bance maka bazanci abincin nan ba ka dage sai naci? Am allergic to green beans. Kuma baka ma fara ganin komai ba tukunna.
Ni ka wanke min jiki mu fita. Gini ya samu ya jingina a jiki yace AI Allah me rahama ne shiyasa ya baki hannu biyu yadda ya bani zaki iya gyara jikin naki.
Yake tayi masa tana shafa gemun da babu tace ya lud kasan menene? Yace me? Tace da kai malami ne zakayi bala'In haduwa saide kash....
Tunowa yayi da lokacin da sailuba tace masa in da shi malami ne da zai burge kowa sanda sukayi kwana 3 suna rigima wai so take ta maidashi Dan kauye.
Tabe baki yayi yace oya ota gyara jikin ki na fitar da ke. Tace toh ka taimaka min ka kaini bakin famfo din. Da yatsa ya Mata alamun no! no!! no!!! Sannan ya sake ninkewa ya adana ta a kirjinsa.
Fuskan abin tausayi ta saka masa sanda gaban shi ya tsinke hakan yasa ya dauke kai tare da cire rigan dake jikinsa ya wulla Mata yace shima ki wanke shi.
Haushi ne ya cika Mata zuciya batasan ta Mike ba....luuuuuu ta tafi zata fadi ya tare ta gaggawa yace ke wace irin zuciya ce da zaki tashi?
Tsaki taja tace dalla malam matsamin nayi abinda ke gaba. Kara riketa yayi gam gam hakan yasa dukan su fadawa cikin bath tube. Duka ta kaima tana fadin ka dagani banason mugunta banza,waiyo bayana nikam sunana sorry.
Janyota yayi ya rungume tayi luf a jikinsa ba mai magana... a hankali yace tsolon rake. Dagowa tayi ta kallesa yace wannan fa munafurci ne, ji yadda kika makale min a jiki amma da anyi nagana ki nuna ke zaliha baiwa ce?
Tace yanzu me ya hanaka tafoya? Fita. Yace bazan fita ba turesa tayi tace ka fita nace yace babu inda zani fa. Ture ture duka fara kawai sulbi ya kwashe su kafar marakisiyya ta bige famfo Wanda hakan yayi sanadin saukar ruwa zuwa dakin kwakwalen gami da jikin su.
Umma be tace kar de a manta muna cikin dakin fa. Wannan zancen ne yasa suka hanzarta wajen yin wanka da kaya kowa na hararan Dan uwan sa.
Suna fitowa umma ta juya fuskarta gefe ta watso musu da wasu kaya. Ba tare da ta juya ba tace kai lud ka kwashe kayanka dan haka wannan ma ka saka ne yana kayan wanki ne.
Murmushi marakisiyya tayi ganin daddy yana lekosu ta kasan bargo kama hannun lud tayi ta rike har zai kwace ta damke shi har suka fita. Yace ke uwar Mata da izinin wa kika rike min hannu? Tsaki taja ta shige dakin ta ta sauya kaya sannan ta koma.
Shima dai lud abinda ya faru kenan saide tunda ya shiga daki yake tuna yadda ta rike hannunsa. Dago hannun sa da ta rike yayi yana kalla. Murmushi yayi sannan ya fita zuwa wajen su umma.
Zaunar da marakisiyya umma tayi tace aurenki de kwananshi daya bae nace karuwa aka samu mai ya sakaki yin amai? Kwanciya tayi a jikin umma ta nuna lud da yatsa yace ni kuma?
Kallon umma tayi tace abinci me green beans ya dura min dafe kirji umma tayi tace ya kashe ki. Keda ko gani kikayi sai jikin ki yayi kaikayi?
Turo baki tayi tace sanyi ma nakeji. Umma be ta kalli lud tace maza maza dauki matar ka ku tafi kuma dama yau in ka kuskura kayi bacci ban yafe ba dole ka zauna ka kula da lafiyan matar ka, kuma yar uwarka.
Gyada kai yayi ya ciccibe ta ya dannan a mota. Yana shiga ya kama kunnenta ya murda sanda Dan kunnenta ya fadi yace ke maiya ki bani kurwata!
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
24th August,2020.
15 -
CHAPTER 26
Gyada kai yayi ya ciccibe ta ya danna a mota. Yana shiga ya kama kunnenta ya murda sanda Dan kunnenta ya fadi yace ke maiya ki bani kurwata!
Kokarin ture hannunsa ta fara tana no ka sake min kunne na zafi yake min bana son mugunta kuma in ka kara ce min mayya sai na fada ma umma na banza mugu kawai.
Sakin kunnen yayi ya juyo ya kalleta da kyau yace ni kika cewa banza mugu? Share sa tayi tace gaba da kukan ta tare da dafe kunnenta da yayi jajawur.
Kunna Moran yayi ya fincika bai tsaya ko ina ba sai hotel bude kofar motan yayi ya ciccibo ta tare da matse Mata kashi ya wullata mai gadin mukulli motar sa yace ya gyara parking ya bada mukullin a reception.
Ita mur tasha kamar bata jin zafin abinda yake Mata. Kallon kallo suke kowa da abinda idonsa ke fada shi fadi yake duk taurin kanki saj kin bada gari zan kyale ki. Ita kuwa idonta fadi yake ko kashe ni zakayi bazan taba nuna ma ina jin ciwo ba a tare suka saki tsaki.
Kowa na kokarin cinye San uwanshi kai a nesa in ka kalla sai ka dauka kauna ake zubawa bakasan kwarya kwaryar yaki akeyi ba. Yana saka roomcard dinsu tana bada dit ya wani daki kofan ya fada dakin.
Cilla ta yayi a kan gadon sanda bayanta yace kat... Dan motsata tayi taji bayan ya rage zafi ashe kashi da ta Dan goce ne ta dawo saiti hamdala tana gyara kwanciya taji muryar sa yace taso Dan.....ki. Sharesa ta yi ya ce ko ba da ke nake yi ba gwamma?
Mikewa tayi tace wai meye Dan wani jiri jiri take ji. Hannun yasa ya janyo kafarta har sanda ya adana ta da kasa yace maza maza yi kneel down.
Ganin fuskarsa ya tabbatar mata ba da wasa yake yi ba hawa kan kafarta tayi yace haka akeyi a kauyen ku? Ko bakije school bane?
Kneel down me kyau tayi yace daga hannu sama. Kallonsa tayi yace maza maza bude baki tayi zatayi korafi da sauri ya tsuguna a gabanta tare da daura yatsa a bakin ta yace shhhhh! Banason korafi maza daga hannunki sama.
Dagawa tayi Dan rabi haka yace me kyau mana! Zabura tayi saboda yadda ya daka Mata tsawa hakan yasa ta nutsu ta daga hannun tare da rufe ido.
Dan sauke hannun ta sake yi tace okay na gane matsalar daga hannun nata yayi me ya fara balle botir din after dress dinta da sauri ta bude ido tare da rike hannunta tace menene hakan ?
Tsaki yaja yace me kuwa naga rigar ta miki nauyi kin kasa daga hannu me kyau shiyasa. Tace kasan inada hannu ko ? sai ka bari na cire da kaina yace ni zan cire da hannuna. Tace ban yarda ba. Yace nine miji dole kibi Umarni na.
Tace ni kuma nice me jikin kuma nace kar a tabani. Murmushi ya yi yace da jikin da me jikin mallaki na ne ai. Tace toh da jikin da me jikin da mamallakin jikin da me jikin nayi kuma mallakin waye? Yace Allah mana.
Tace correct to kuma Allah yace bayason zalinci ni kuma ga zalinci kana min ita karara tunda kasan naji ciwo a baya na kake min hukunci da ya shafi baya.
Kaga tunda kai ma ka kasa bin umarnin ma mallakin ka me yasa ni zanbi umarnin ka? Yace naji cire da kanki munafuka kawai sai shegen cakwaikwaiwa da zakin baki.
Murmushin cin galaba tayi ta cire rigan. Kunna AC yayi ya kure sanyi kawai ya kwanta ya shige cikin bargo. Kamin kace me hajiyar ka ta fara bari baki na rawa tace ya lud sanyi nake ji ya manna Mata tace ya lud sanyi nake ji. Ganin shiru ba amsa yasa ta Mike tana neman remote din.
A hannunshi ta gani ta dauka yayi bacci yasa ta fara ja a hankali har ta zare tana shirin ragewa yace kina ragewa zaki wanke bandaki.
Tace sasssanyi nake ji. Yace na dai fada miki nazari tayi Dan batason sanyi ko kadan Dan haka gara ta rage ta wanke ban dakin.
0 comments:
Post a Comment