Mai martaba ne tadawo dakin da sallama ganin yanda yarima yaxauna agaban fateema cikeda damuwa yaqara tabbatar mishi da irin son dayake hange akwai atsakanin yaran nasu axuciyarshi yayi hamdala yagodewa Allah. Dawannan hadan yake kyautata xatan xumumcinsu xai qara qarfi da dorewa kobayan ransu
Ya isa gareshi yadan bubbuga kafadarshi karkadamu yarona in Allah ya yarda xata sami lfy likitan yace data tashi xata tashi da qwarin jiki insha Allah, kaxo mutafi karmuyi tafiyar dare
Batareda yace komaiba yamiqe yabi bayan mahaifinshi axuciyarshi yanayiwa yar,uwarshi fatan samun lfy, awajam sukaiyi sallamq dasu baffa a gaggauce nasukoma gidanba dan yamma tayi sosai yasa aka kira wayar sauran motocin dake can yace su shigar dakayan tsarana cikin gida suxo su sakesu anan dayake bakin hanya asinitin take bajimawa sai gasu suka qarayin sallama tareda yiwa fateema addu,ar samun sauqi suka wuce gida
Baffa yace yaya bashir ya tsaya gunta shixai koma yasanarwa goggo itakuka innawuro taxo ta wuce gida kar dare yayimata anan, badan tasoba haka tabi bayan baffa suka koma cikin unguwar
Bayan sallar magariba yadawo tareda goggo harxuwa lokacin fateema bata farkaba bashir na xaune a gefenta yadawo daga masallaci, goggo taji tsoro yanda taga yar tata ko kotsi batayi ga ruwan da aka saka mata nandanan tafara sharar qwalla ta isa ga fateema yarta daya mace da Allah yabata addu,a sosai tayimata ta tottofa mata ajiki alokacinne aka fara kiran sallaf isha baffa da yaya suka tafi masallaci goggo kuma tayo alwala tagabatar da sallar anan
Qarfe goman dare fateema ta farka alhamdllh jikin yayi dan qarfi saidai bata dainajin xigi da radadin kalaman yaya fahad a xuciyarta ba amma batayarda ta gayawa kowa ba,tabarwa Allah lamuranta kafin wa,adin mutuwarta yaxo dan ayanda takeji indai babu fahad arayuwarta tokuwa mutuwa xatayi, tayi qoqarin danne damuwarta dan kwantar da hankalin iyayenta ta nuna taji sauqi
Likitan yabasu sallama tareda magungunan daxata rinqa sha safe a yamma, haka suka lallaba suka koma gida cikin duhun dare a dakinta aka ajiyeta sai sannu ssuke mata tana murmushin yaqe ainaji sauqi ba abunda kemin ciwo, sukaja mata qofar kowa ya nufi nashi dakin domin yin bacci
Fateema kam naccin ko kusada ita bai rabo ba tashi tayi tafita tayo wanka tadauro alwala sannan tadawo dakinta tafara rankon sallolinda natayi ba, tanayi idonta na xubda hawaye data kammala saita dora da nafila rak,a biyu tayita roqon Allah akan damuwarta
Da takammala sai takoma kan katifarta harxuwa lokacin hawaye basu yanke a idontaba, gefen katifar naga ta cusa hannunta ta dauko wani dan madaidaicin hoton yarima na katako ne irin laminated dinnan yayi kyau sosai kamar yayi magana ta qurawa photon ido tana xubda qwalla
A,ah dan,uwana abunda kamun sam baidace ba, yayana ina sonka sonda bantabayiwa kowa irinshiba wlh bani nasakawa kaina ba, nimajinshi kawai nake a xuciyata ina qaunarka kuma kasani nasadaukar da rayuwata ga soyayyarka baxan taba daina sonkaba kodai xaixamo dalilin mutuwata ina sonka
Ta rungume photon tacigaba da rera kukanta qasa qasa
đ. *Nasmy ce*đ
Yar mutan arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*5 star's ✨✨ online writer's association*đ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•56/60•*
Har gariya waye fateema bata runtsaba idonnan nata sunyi suntum sun kumbura harsunba fuska daqyar tayi sallar asuba takoma ta kwanta qarfe shidda gaggo tashigo dakin a ah fatee a ummaki juludaha joni? Dataga mayafin data rufu murya a dusashe tace nayi salla tindaxu
Ayya to sannu yajikin naki? Dasauqi tafada tana maida mayafin a fuskarta goggo taqarasa ta yaye mayafin ganin yanda fuskar yartata takumbura tayi jajir ya tsoratata fatee xaxxabin ne yadawo? Batada xabi shiyasa tace eh jiya da dare ne ciwon kai yatashi amma meyasa baki kirani ba? Bakomai ainaji sauqi tafada da dan qarfi qarfi danta kwantarda hankalin goggon
Dai dai lokacin baffa da ya bashir suka shigo sumadai sun damu da yanda fateen takoma lokaci daya dukta canja sukayi mata sannu ta amsa sunashirin fita wayar baffa tayi qara yadaga da sallama ah Allah yataimakeka kun isa gida lfy bamuji me akace a dayan nangarenba nadaiji yace eh dasauqi to tunjiya da dare kukadawo gida ai, to to yace sannan ya miqawa fateema wayar sallam tayi da disheshiyar muryarta ya amsa mai martaba ne, tagaisheshi ya amsa tareda tambayarta ya lfyr jikinta mai makon tabashi amsa saikawai ta fasheda kuka, al,amarida yadada daga hankalin mai martaba kiyi haquri yata wai meyake miki ciwo ne? Yishiru ki gayamin kinji? Itakanta batasan daliliba amma takasa barin kukan saida baffa yakarbe wayar tomeye haka kenan daga tambayar lfyrki sqi kuka ina yanxu kikace mana kinji sauqi, ya dora wayar akunnenshi inajinka yaya
Mai martaba yace kuhada mata kayanta anjima xan turo dan,uwanta ya daukota akaita asibitin nan garin koxaifi nacan din to allah yakaimu Allah yabar xuminci yadada girma da daukaka mai martaba ya katse wayar xuciyarshi cikeda damuwa
Yafara kiran layin fahad wanda alokacin yake hanyar xuwa turakar mahaifin nashi domin ya gaisheshi, yadaga wayar da sallama yace yarona kana ina? Ina hanyar xuwa wajanka abbana to shikenan bari kaxo din ya katse wayar
Da isarshi kuwa bayan sun gaisa mai martaba yasanar dashi buqatarshi tayaje kukunba yadauko fateema akaita asibiti anan yace Allah yakaimu yatashi yafita xuciyarshi cikeda tunanika barkatai shida yake shirin fita garin yau koxai sami dai dai dashi da agaskiya kwana biyunnan haqurinshi yafara gaxawa yanada buqatar mace jiyamadaqyar yayi bacci
Qarfe goma shabiyu yarima da yan rakiyarsa fadawa suka isa gidan angama shirya mata komai goggo harda kukanta tanatayi maata addu,a bayan sungama gaisawa yace afitoda ita sam fateema batayi wani farincikin gqninshiba goggo ce ta riqota fuskarta yakalla sqidaya tsorata ganin yanda ta kumbure suntum shidagani yasan kuka tasha bawani ciyoba yayi mata sannu ta amsa batareda ta kalli inda yakeba,
Nanfa goggo taqara tsorata da wannaj ciwon na fatee tabbas. Baqaramin ciwo bane ace ga yarima gabanta amma ko kallon inda yake batayiba
Hakadai tariqota har bakin motar aka bude ta sakata abaya yarima ma. Yaxaga yashiga sukatafi baffa ne yani goggo da rarrashi aiciwo ba mutuwaba addu,a yakamata muyi mata ba kukaba,
Qarfe daya suka isa gombe kaitsaye memorial prvt hospital ya nufa da ita asibityn families dinsi kenan daxuwa aka shigarda ita bayan yan gwaje gwaje likita yakira yarima xuwa office dinshi yagaya mishi qanwarshi fa daftake da kamuwa da ciwon xuciya saida yadan firgita doctor for what? Likitan yace bansaniba amma dai damuwar axuciyarta ne ba mamaki akwai aninda takeso bata sameshina ko kuma bataso ake takurata cikin biyunan dai dole akwai daya sbd haka maganinta badaga garemu yakeba kune xaku gyara inkuma bakusan damuwarta ba toku tambayeta tasanar daku sannan kuyi qoqari da gaggawar sadata da abinda takeso kafin wannan muunan abin yasameta,
Yarima ya gama rikicew ya diririce yarasa abinda xaice da dr miqewa yayi yafita yakoma dakinda fateen take xuciyarshi cikeda rudani wannan wacce irin masiface? Yarinya qarama tadauki damuwa ta dorawa rayuwarta yanxu idan takamu da ciwon xuciya tadalilinshi in abbanshi yasani yaxayyi kenan? Bashakka xai tsaneshi
Innalillahi
đ *Nasmy ce*đ
Yar mutan arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*5 star's ✨✨ online writer's association*đ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•61/65•*
Tana xaune abakin gadon inda likita yabarta qofa take kallo qkma yana shiga dakin ta dauke kanta tamayar gefe, abinda yanashi haushi kenan wato batama son ganinshi kenan? Lallai yarinyarna wato shibaiji haushintaba itace xataji haushinshi uhum
Batareda ya kalletaba yace mata tashi mutafi, baijirata miqeba yayi waje wani irin qololon baqin cikine yatokare wa fateema a maqogwaro tamiqe daqyar tanabin jikin bango harta fita a mota tasameshi sai shan qamshi yake kamar wanda akama wani abu, aka bude mata motar tashiga driver yatayar suka tafi cikin qasaitar nan tashi yaceda driver xamu sayi magani a venga pharmacy, ok sir driver ya amsa cikeda ladabi suka faka a wani makeken pharmacy nan yafita ya siyo dukkanin magungunan da likita ya rubuta mata
Da isarsu gidan yafice yayi cikin gida yabarta a motar ahankali ta tako qafarta ta fito daqyar take takawa saidai xuciyarta tagama yanke hukunci akan yarima tafe taje tana cixon lebe, hmmm kawai baisan fatee
Bane jina yakeyi wlh dan kawai banida lfy ne amma bari in warke xan nunamishi asalin kala ta, duk a xuciyarta take wayannan maganganun lokacinda take tafiya xuwa cikin gidan sarautar
Dayake tasan gidan sosai da mutanen cikinshi suma sun santa tana tafe suna gaisawa da hadiman gidan harta isa sashen gimbiya umman yarima kenan akayimata iso umma tace tajirata anan tana xuwa
Takai 20mins bata fitoba dukda angaya mata wadda taxo din can fateema harta fara gyajgyadi tafito cikin takunta na isa da qasaita laxeera na biyeda ita dawasu damammun kaya riga da sket kanta ka dankwali babu, suka iso falon yayinda umma ta hakimce akan doguwar kujera laxeera kuma taxauna a qaramar kujerar dake gefenta fateema tadan xame daga kan kujerar tagaida umman ta amsa da dan kulawa hartana tambayarta su goggo ta amsa mata da lfyrsu qlau,
Tace akace bakida lfy keyake daminki? San danki xuciyarta tafada a gajarce, afili kuwa cewa tayi eh wlh yanxunma daga asibiti muke amma da sauqi
Laxeera dakejin haushi da tsanar wannan kyakkyawar yarinya takalleta a tsawace tace ke dan iyayenki baki iya gaisuwa bane kobqn isa kigaidani ba? Sosai fateema taji xafin xagin harcikin ranta takalli umma koxatace wani abu amma bataceba, saima cewarda tayi kigaisheta man fateema yayarki ce, itadin yar yayatace
Fateema tayi qasa dakanta ina wuni taceda laxee kamar baxata amsaba saican tace lfy
Umma takira jakadiya tace takai fateema dakinda xata xauna taceto tqyi gaba fatee tabita a baya van tatsinkayo muryar laxee tanacewa hmm qauyawa kenan anyi marmarin miyar nama, yitayi kamar batajitaba tawuce axuciyarta kuwa cewatake lallai wannan kin tsokalo tsuliyar dodo yoni ko a garimmu ma an isa axageni inqyale balle a birni inda mutum yakeyin yanda yaso tayi qofa xamu hadu ne wlh baxanbar gidannan ba sainayi maganinki yar iska karuwa jibi kayan dake jikinta
Dai dai nan suka isa dakinda akabata jakadiya ce takarbi kayanta tabude wardrobe tasaka taja hannunta yaki yata tabude bayin dake cikin dakin ta nunnu na mata yanda ake amfani da komai sannan suka fito
Fateema tace ngd jakadiya tace bakomai yata fatee Allah dai yabaki lfy tafita tareda ja mata qofa fateema tasauke ajiyar xuciya taxauna a bakin gadon tafara qarewa dakin kallo yayi mata kyau sosai tanashirin kwanciya jakadiya tayi sallama tashigo dawasu matasan bayi mata gudabiyu abayanta kowacce daukeda faranti ahannu dayar kayan abincine akai dayar kuma kayan lemuka da yayan itace wato pruits, jakadiya tace ga qanwar yarima nan dagayau kuxaku cigaba da kulada ita har ranarda xata komgida bayin suka russuna gareta bayan sun ajiye kayandake hannunsu sukace angama rankishi dade,
Sannan tajuya ga fateema tace mata wannan sunanta ummi wannan kuma xaleeha suxasu riqa xama dake suna debe miki kewa duk abinda kikeso ki sanar dasu xasu kawo miki, tamiqa mata ledar magungunan ta tace gasunan idan kinci abinci kisha kowanne daya haka da darema, Allah yabaki lfy tafita tabarta dasu ummi da xalee wayanda dukkausu kusan sa,anninta ne, suka xuxxuba mata abinci da abinsha sukabata tanaci suna mata hira
đ *Nasmy ce*đ
Yar mutan arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*5 star's ✨✨ online writer's association*đ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•66/70•*
To dayake itadinma ba bayaba haka suka dinga hira cikin qanqanin lokaci tasaba dasu ummi wayanda suka taimaka sosai wajan rage damuwarta hankalinta yakwanta da yamma suka hada mata ruwan wanka ummi takalleta kai rankiya dade kibani dama in tsefe miki kanki mana kinada gashi sosai amma xai baciidan bakya gyarawa
Fateema tai murmushi dama tanason gyaran dakantane dai baxata iyaba dan agidama goggo ce ke tsefe mata takunce kai suka hadu suka tsefe matashi, suka wankemata da mayukan wankin kai nandanan gashinta yayi fess sai sheqi da walwali yake yaqara baqi ga wani qamshi dakeyi itakanta taji dadinshi
Sukabarta a bayin tayi wanka tafito sanyeda hijabinta suka bata towel sukace tagoge jikinta takuwa goge ba musu tashafa mai daya tafita saigata tadawo kata dawata doguwar riga mai kyau da daukar ido rigar pink ce sai akayimata adon red stone sababbin pant da bra suka kawo mata tafara sakawa sannan tasaka rigar masha Allah
Ummi ce maiyimata make,up yayinda xaleeha ke taje mata kanta sannan ta busarmatashi da hand drayer masha Allah watabarakallahu ahsanal khaleqeen, fateema tadawo kaman ba itaba, dukda tadauki xubo gashi a gadon baya iskanci ne yau kam tayarda iskancin nayimata kyau sosai jinkanta tayi kaman balarabiya ga kwalliyarda bata tabayin irintaba ga wannan gyaran gashi da aka mata yasha mai sai sheqi yake fuskarta tayi luwaui luwui kaman ta jarirai
Kawai saita tuna da wannan laxeeran data xageta daxun, wani shu,umin murmushi naga tayi (nace tofa real fatee ta dawo bari in ruga incewa laxeera ta gudu)
Afalo nasami laxee tayi dai dai akan kujera tana cin pruit salad, a yangace tana wani lumshe ido, tashar xee tv take kallo kanaganinta kasan tana cikin farin ciki, wanda ayanxu xaman jiran fitowar yarima fahad takeyi awurin,
Ahankali fateema ta tako ganin har tashigo falon laxee batasan da itaba yasa ta buya a bayan kujerar da laxee take kai, dayake kujerun irin dima dima dinnan ne saitashige qarqashinta ahankali tafara xila hannunta tana shafo qafar laxee tun tana dan kada qafar hardai tamiqe xaune amma bataga komaiba, takoma tq kwanta tana mamakin abinda ke tabinta adai lokacinda fateema tasami dan tsinken stick ta tsula matashi aqafa da qarfi tayi ihu ta miqe tsaye amma bataga komaiba ga qafarta sai xogi take mata wurin kaman ya fiddo jini
Tafara tsorata nan tashiga dube2 tana qoqarin duqawa qasan kujera ta leqa fateema tayi gaggawar cannja muryarta xuwa kakkaura ta maxa adan tsawace tace karki kuskura ki ganema idonki abinda xai xamo ajalinki ke kin isa kiyi ido biyu da autan jinni
Laxee jikinta yahau qyarma dan tunda take bata tabajin irin wannan muryarba aiko ihu bata iyayiba takwasa dagudu harta bige kanta da qofa amma bata tsayaba tabar falon arikice
Da gudu fateema ta fito tayi dakinta tahaye gado kaman bata fita ba, dariya tahauyi hadda riqe ciki tana dukan gadonta
Jin motsin qofar dakintane yasa tayi shiru su ummi ne dama abinci suka fita kawo mata tayi lamo kaman maison yin bacci xaleeha tace ayya ranki yadade badai bacci xakiyi yanxunba? Ai baccin yamma babu kyau
Ummi tace ai warrware baccinnan kitashi yau aljanune a gidannan tadan waro ido alamar tsoro tace aljanu? Eh haka yaya tace gasucan afalo antaru wai anan aka tabata kuma har magana aljanin yayi mata
Fateema ta miqe da sauri tafita falon tana ware ido kaman dai batasan komaiba haka suma sukabita abaya fapo cikeda ma aikatan gidan anata dube2 laxee natsaye hannunta riqeda umma sai xare ido take dariya tasota kufcewa fatee amma saita kanne ta isa gareta yaya waidagaske aljani kika gani wata muguwar harara ta wurga mata fateema tayi shiru, maganar datayin yadawo da hankalin mutanen gurin kanta
Nanfa sukafara santin kyawun datayi akabar maganar aljani kowa a gurin cewa yake kai masha allah fatee kinyi kyau sosai banda umma da laxeera da abun yayi matuqar qona ransu
Ummance tadaka musu tsawa abinda kukaxo yi kenan? Dalla kufita kubani guri nandanan suka fashe jiki na rawa kowa Yakama gabansa yarage dagasu sai fateema a falon laxeera ta qwallawa ummi kira tadawo dasauri ta rusuna a gabanta gani yaya, tace acikinkunnan wacce shegiyarce tayimata wannan adon tareda bata kayan gidan sarauta? Duk sukayi shiru fateema ta daga kai takalleta sannan ta taka xuwa gabanta cikin gadara da rashin tsoro tace nice nan ni ja buqaci suyimin duka wayannan abubuwa laxeera ta kalleta cikeda tsananin mamaki
Tamarasa tayanda yakamata tahukunta fateema, hannu tadaga ta sharara mata mari wanda saida yasa ta tangadawa kaman xata fadi ta tirje ta kalli umma dake gefe batacewa laxee komaiba
Aikuwa itama cikin shammata da baxata tadaga nata hannun ta wanke laxee da mari har guda biyu
đ *Nasmy ce*đ
Yar mutan arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*5 star's ✨✨ online writer's association*đ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•71/75•*
Tsananin kamakin dataji yafi xafin marin yawa umma tasaya salati yau mexan gani? Ke fatee laxeeran kika mara? Cikin tsananin fushi laxee ta nufo fateema gadan gadan itakuma ko aranta dan batasan tsoroba jirakawai take ta iso gareta su dambace
Muryar yarima sukaji daga bayansu inda yadakawa laxee tsawa karki yarda kitaba ta, cikeda mamaki umma takalleshi kasan abinda tamata ne? Laxee kuwa tsayawa tayi tana cixon yatsa
Eh ainaga komai agabana akayi baiqara cewa komaiba ya wucesu yakama hannun fateema yakoma sashensa da ita, kallon mamaki umma da laxeera suka bisu dashi kafin umma tajuya takoma sashenta laxeera tabita tana share qwalla baqin ciki kaman ya kasheta
A dakin yarima kuwa fateema taqara xama asalin haqauya domin yanda aka tsara dakin dole akalleshi yaxaunar da ita bakin gadonshi shima yaxauna tanakallon tsarin dakin shikuma yana qarewa halittar ta kallo, ashe haka yarinyarnan ta hadu? Hmmm wani iri sha,awa ya qara xaburo mishi sanda idonshi yasauka a lips dinta nandanan idonshi suka sauya yafara shiga yanayi
Fatee yakira sunanta lokacinda yakama hannunta yariqeshi acikin nashi ma,am ta amsa batareda ta kalleshiba ta hada rai tajuyarda kanta gefe, hmm yai murmushi mai fidda sauti fushi kikeyi dani qanwata? Tayi mishi banxa ok shikenanma tashi kitafi dama kayan sakawar ne naga yakamata asiyo miki naki kihuta dashan gori, yafada tareda sake hannunta
Allah sarki quruciya dasauri tajuyo takamo hannun nashi Allah yaya inaso pls kasiya min yanda tayi maganar cikin farin ciki saiyaji dadi aranshi yajanyota jikinshi yarungumeta tsam dukkaninsu saida sukaji sauyi ajikinsu yawwa qanwata karki koma fushi dani kinji? Taceto, yaushe xaka siyomin kayan? Yace ko yanxuma tasakeshi tamiqe tahau tsalle yeeeeee wayyo dadi xak xama yar birni kuma wlh yaya inada kyau da irin kayan nan kalleni fa taxo gabanshi tasaya tareda kama qugu abin yabashi dariya yai murmushi hmm kinyi kyau sosai jeki dauko mayafi mutafi da gudu ta fita tana ihun murna
yabita da kallon mamaki waiharta huce kenan hmmm
Agurguje yashirya xuciyarshi fall da farin ciki wanda shikansa baisan dalilinsa ba, yasandai badan xai fita da fateema bane
Saidai abu daya daya bashi mamaki gameda ita shine duk tsanani yanayin sha,awar dayake ciki runguma daya yayi mata yaji duk sha,awar tafita akanshi saiyajishi warwar
Madalla da fatee nankam yaji dadinta sosai dole yai mata siyayya sosai manyan kaya naji da fada
*fans kumin afwa yauba yawa wlh yau banajin dadi kawai dankar kujini shiru ne* _gobe xanmuku dayawa insha allah_ đ
đ *Nasmy ce*đ
Yar mutan arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*5 star's ✨✨ online writer's association*đ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•76/80•*
Yana cikin saka botiran rigarshi tashigo, mayafin rigar ne tadauko batayi rolling ba tadai yafa akanta ne sannan ta jefa dayar jelar baya gashinta kuwa ummi tasaka mata ribon tadaure mata shi waje daya saitaqara kyau fuskar taqara fitowa das das,
Kai yaya haryanxu baka shiryaba? Tayi maganar cikeda shagwaba tana yanqwane fuska kamar xatayi kuka, hmmm aranshi yace wannan yarinyar akwai shagwaba
Rigar takama ta taimaka mishi wajan saka botir din na qasa, suka kammala suka fito tare ajere tamkar wata da xara, kana ganinsu kasan sun mutuqar dacewa da juna abinda haryau fahad yakasa fahimta kenan, haka suka keta gidan fadawa nata xubewa suna gaishesu harsuka isa inda ma,ajiyar motocin take, wata farar farado ya nufa dagudu fadawa biyu suka rugo suka bubbude bayan motar driver yashiga gaba gefenshi kuma wani bafare daya fahad yayi murmushi kuyi haquri nikadai xanfita nida qanwata
Dasauri sukafito sunafadin Allah yaba yarima haquri bamusani ba, adawo lfy yakarbi kakullin motar yashiga gaba itama yace tashigo gaban ba musu tashige ayau tanacikin farin ciki irin wanda bata iya kwatantashi jitake kamar su tabbata ahaka itada yayanta
Yatayar da motar suka fita fadawan na daga musu hannu dan ladi yakalli lawal yace kai amma wannan fateeman akwai kyakkyawa kuma wlh sun mutuqar dacewa da yarima inamadai............baiqarasaba lawal yace kai dan ladi akwai gulma ashedai kaima ka hango abinda na hango sukayi dariya suka tafa
Laxeera kuwa sakin labulen window tayi takoma kan gadonta taxauna xuciyarta namata tafasa kamar wuta aka rura acikinta, kasancewar daga inda taken tana kallon fitowar su yarima har sanda yasallami fadawa yashiga mota daga shi sai ita suka fita, to me hakan yake nufi? Kardai yarima son yarinyarnan yake? Taf him aiko daya sakata a masifa dan wlh xan iya kasheta akan fahad tafada afili tana murxa yan yatsunta
*Jifatu and son mall*
Nan naga yarima yayi parking suka fito cikin isarnan tashi da qasaita yake takawa fateema nagefenshi kasancewar dayamma ne wurin a cike yake da yan mata da samari kaiharmada masu aure da yayansu mutanene kota ina daban daban saidaifa isassu ne dan baqaramin mai kudine xaije jifatu plaxa ba,
Nanfa hankali yan matan dake wajan yadawo kan yarima fahad da fateema saidai duk wadda takallesu shida fateema dauka suke qanwarshice dan kamannin dasukeda shi
Nanfa yafara dibar mata kaya iri iri tundaga kan atamfofi xuwa less, dogayen riguna English wear's, takalmi da jakunkuna kyawawan gyaluluwa turaruka kai kayadai kamar wanda xai hada lefe fatee ta kalleshi yaya duka wannan nawane? Yai murmushi duk naki ne qanwata, tayi tsalle ta rungumeshi wayyo Allah nagode yaya fahad thank you ta manna mishi kiss a kumatu, yajidadi sosai na nunafarin cikinta ga abinda yayi mata
Nan aka kawo manya2 trolley guda biyu aka loda kayan yabiya kudi suka fita a both aka xuba mishi kayan daga nan kuma sai kusha shagalinku, nankuma gasasshin kaji yasaya musu guda biyu da ace cream da madara suka dauki hanyar wani fitaccen shago sanane kuma qwararre awajan dinki nan yacire duk atamfofi da leses yabar aka gwada fateema kwanahudu mai telar yace xai dinke kayan nanma kudine masuyawa naga ya bawa telan suka nufi gida
Yaukam xuciyar fatee farin ciki karma ku tambaya jinta take kamar sabuwa aduniyar nan yaukam yaya fahad yasha godiya harba adadi
Sai daf da magariba suka shigo gidan su ummi yakira bayin dake kulada ita yace sukai kayan dakinta su saka a wardrobe tadinga amfani dasu nanfa tabisu abay shikuma yafita xuwa masallacin gidan
Suna saka kayan fateema ma tsalle a tsakiyar dakin kamar qaramar yarinya banko qofar da akayi da qarfi ita ta dakatar da ita
Laxeera ce tsaye a qofar tana huci fuskarnan ta dada yamutsewa takalli su ummi cikin tsawa tace maxa kubar dakinnan jikinsu na qyarma suka fita xuciyoyinsu cikeda tausayin fatee dansun san yau xata daku, tamaida qofar ta rufe
Fateema dai na nantsaye tana kallon ikon Allah tajuyo tawatsa mata wani matsiyacin kallo ahankali ta taka ta isa gabanta ke yar,marasa mutinci mekike nufi? Me iyayen naki suke nufi da turoki nan? Wato kinxone dan ki sami yaya Prince ko? Hmmm lallai kuwa kinyi kuskure dakeda wadancan tsofaffin naki dominkuwa yaya Prince nawane
Idanunwan fateema sun canja sunkada sunyi jajur bantaba ganin ranta yabaci kamarna yauba
Cikin matsanancin fushi tadago
*Nasmy ce*đ
Yar mutan arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*5 star's ✨✨ online writer's association*đ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*hi my fans I don't know which words can I use to thanks u 4 the true love that you guys show's to me, only god know d way of paying u, not me*
*I have nothing to pay u, bt i know you guys are my true lover's thanks all 4d du,a*đđ *may Allah make our life be all the best Ameen*đ
*•81/85•*
Tatsura mata ido ko qiftawa babu laxee tadan tsorata da yanayin dataga fateen aciki na sauyin fuskarda tayi lokaci daya
Wuf ta cakumi wuyan laxee saidatakaita har bango ta datseta ke ke ke! Abinda laxee ta iya kira kenan tayi duk iya qoqarinta amma takasa raba jikinta dana fatee domin abin yagirmi tunanita sam bata xaci yarinyar nada qwarin qashi hakaba
Fatee tafara magana dawata irin murya ke qaramar yar iska akuyar labe yarcin arxiqi ki iya bakinki kisanyawa kalamanki linxami domin samun damar sarrafasu
Iyayena dakike gani sunxarce tunaninki sunfimun komai daraja arayuwarnan banxa marar tunani ke bakisan arxiqin iyayena kikeci anan ba?
Yaya fahad kuma dakike magana aikinga alama basaina bata yawun bakina wajan yimiki bayaniba shidin nawane mallakina inma tantama kike to bari in tabbatar miki *yaya fahad nawane* kuma nikadai banida kishiya awurinshi banxa mai kamada agwagi ke banda hauka da wautama ina ke ina yaya fahad? Ki kallekifa tafada tana mata kallon rainin wayau daqyar laxee ta sami damar bankade fatee daga maqurar datayi mata tariqe wuyan nata tana shafa dan tsananin xogi da radadin da takeji na riqon da fateen tayi mata idonta sun firfito adan tsorace tafara magana nikikayiwa haka ko? Wlh saikinyi nadama saikinsan wadda kika taba tajuya tafita afusace
Fateema tafada kan gadonta tareda riqe kanta gaskiya wannan tabata mata rai bakadanba, wai tana son yayanta hmmm. Lallai laxee kinjawa kanki dan wlh daga yau bake ba xaman lfy, tanacikin tunanin aka koma banko qofar dakin a karo na biyu tamaida hankalinta ga qofar laxeen ce dai tadawo saidai wannan karon hadda umman yarima ido kawai takebinsu dashi ko motsawa batayi daga inda takeba
Umma ta kalleta kallon wulaqanci sannu yar masu gida, nace sannu yar masu gida wato keyanxu harkin isa kiyiwa laxeera gori akan gidannan? Iye dake nake magana kiwon qauye, ina kkajemin da yaro? Wato turoki akayi ki lalatamin yaro ko?
Fatee kam juyarda kanta tayi gefe kamar bada ita akeyiba dukda cewa tanajin xafin maganganun umma amma haka tadaure dan amatsayin uwa ta dauki umma
Tsawa ta daka mata waishin badake nake magana ba? Nanma bata tanka mata ba. Laxeera tace kumafa kalli umma ji uwar siyayyar dayaya mata koni bai taba yiwa irinta ba, kiji har iqirari take wai yaya Prince nata ne, tafada tareda bude wardrobe dinda aka xuba kayan
Ido umma ta xaro ganin irin manyan kayan daya siyowa yar,qauye acewarsuđ
Tayi salati tana rafka hannaye nashiga uku sun shanyemin yaro wlh sungama mallakeshi tun yanxu, to wlh barikiji ingaya miki ahir dinku kurwar dana na taku bace dangin mayu kuma kingama xaman gidan nan yarinya daga xuwa yau yau kin tashi hankalin gida da kutanen cikinsa debomin kayannan duka tacewa laxeera, aikuwa kamar jira take tafara fiddo kayan tana jibgewa qasa
Laxeera batasan yanda akayiba saijin kanta tayi qasa timđ dagowar daxatayi taga fateema tsaye akanta
Ta duqa ta tattare kayan tamayar tarufe wardrobe din taxare makulli batareda tace musu komaiba takoma kan gado taxauna tadauki qafarta ta dora daya akan daya tana kallon su
*Nasmy ce*đ
Yar mutan arkilla love you allđ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*5 star's ✨✨ online writer's association*đ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•86/90•*
Mamaki ya hanawa umman yarima magana laxeera kuwa miqewa tayi takoma bayan umma tana muxurai dan al,amarin yarinyar yafara tsorata ta matuqa umma tagyada kai lallai yarinya kin isa naga alamar da shirinki kikaxo shikenan naga wanda yakawoki gidannan daidai nan taja hannun laxeera suka fice
Fateema tayi dariyar nan tata ta shaqiyanci kai gaskiya na hadu kajimin mutane ya baqin ciki fatee xata faso gari kuna mata hassada taqara fashewa da dariya to wlh ba inda xani xama daram a gidannan duk na isheku riga da wando ehe, itakuma wannan tsohuwar darajar iyaye tace wlh dasai na nunamata ni fatee ce, amma nakomai yarta tajamawa hukunvi biyu xammata wlh saitabar nan gidan daqafarta
Ta dade tana surutai ita kadai kafin ta miqe tayo alwala tayi salla tana gyara shimfidarta yarima yashigo da sallama tadago dasauri ta amsa yaya sannu da dawowa yawwa fatee kinyi salla daiko? Eh nayi toga wannan abinda nasiyo mana daxun takarbi ledar tana godiya yajuya yafita tabi qofar da kallo kamar tadawo dashi takeji Allah yariga ya jarrabeta da son yarima bada wasaba, wannan itace qaddararta tafada alokacinda ta tuno kalaman yarima sanda yake cewa bayya sonta kuma baxai taba yimata sonda ya wuce na yaya da qanwa ba
Wasu hawayene masu xafi suka fito daga idonta batadamu data sharesuba taxauna bakin gadon hatta abunda yabatan saitaji yafita akanta
Nanfa xuxiyarta tafara axapxalalta da manyan tambayoyi da maganganu akan yarima
Shin haka xata qare dason maso wani? Anya baxata rarrashi xuciyarta tabar yarima ba? Dasauri xuciyarta ta gargadeta dabarin wannan tunanin baxata taba barin yarima ba, sam baxata iya rayuwa babushi ba, yaya fahad wani sashene a rayuwarta, wanda bataji xata iya rayuwa babushi kuma koxata mutu baxata taba bari wata ta rabeshi ba koda kuwa bai aureta ba
Jinkiran sallar isha yasaka ta tashi tashiga bayin acan tayo alwala tayi salla saida tagama sannan tajawo ledar daya bata tabude kaxace daya gasassa tasha yaji sai qaramar leda dakeda ace cream da madara taware tafara ci
Tana cikin ci su ummi suka shigo daukeda abincinta na dare tace suxauna tahade da wannan kaxar tace suci suka xauna sunaci suna hira sunata jinjinama jarumta irin tata. Sunajin dadin xama da fateema garesu tanada kirki sosai
Da dare mai martaba dayashigo gidan baikwantaba saida yaje yaga fateema alokacin tayi bacci yayi mata addu,a ya rufo dakin tareda fatan allah yabata lfy
Fateema fa tasayawa kanta mutinci agidan dan a yanxu laxee shakkarta take bakadanba kuma dama itakadaice mai takura mata a gidan
Abangaren yarima kuma tayi iya qoqarinta wajan Saba mishi daxama da ita dayake baicika fitaba kodayaushe suna tare agida shikanshi yanajin dadin xaman fateema agidan inkukaganta kullum dagwas da ita cikin shiga ta alfarma kamanba fateen kukunba ba tayi shar da ita
Duk lokacinda baffa yakira fahad akan fatee tadawo gida saidai yabashi haquri wai abari hutunshi yaqare xai maidata gida, tana debe mishi kewa sosai
Shaquwa ce mai qarfi tashiga tsakanin fahad da fatee kusan kullum suna tare yana qaramata haske akan karatunta tana sashi dariya a kowanne lokaci abinda ba halinshiba amma fateema ta koyamishi
Sam tunda yaxo baisami damar fita neman mata ba dukda yanajin sha,awa a wasu lokutan amma hirada fateema kadai ta isa ta mantar dashi komai, abinda ke mutuqar bashi mamaki da ita kenan
Haka sukacigaba da xama kamar abokai abinda ke matuqar faranta ran mai martaba , umma da laxeera kuwa kusan bayanda suka iya saidai gunaguni da qananun maganganu
Yau fateema watanninta biyu agidan tanajin dadin rayuwa sosai dan a kodayaushe tana tareda yariman ta
Hausawa sukace laifin dadi qarewa dominkuwa a satinnan ne hutun yarima xai qare yakoma makaranta al,amarinda yajefa xuciyar shi a damuwa kenan dukda cewa harxuwa yanxu yarima bai yardA yanason fateema ba saidai yasan yashaqu da ita xayyi kewarta sosai
*Nasmy ce*đ
Yar mutan arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*5 star's ✨✨ online writer's association*đ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•91/95•*
Dakanshi yake shirin maidata gida ayau, bayan tayiwa mai martaba sallama takoma cikin gida tayiwa umma sallama tadan sake mata fuska dan konakomai dai tasan yau xatabar gidan
Harmada saqonnin tsaraba tabata takaiwa goggo, laxeera kuwa kallon wulaqanci ta rakata dashi
Yarima na gaba tana binshi abaya, harwajanda driver kejiransu, su ummi na bayansu daukeda jakunkunan kayqnta, domin kuwa kaf kayanda yarima yasaya mata batabar ko tsinke ba, haddama qari tayi dan duk kayan make'up dinda ta tarar adakin saida ta yayesu đ
baya aka bude musu suka shiga, fadawa suka karbi kayan aka xuba a both, tayiwa su ummi sallama harda yar qwallarta saboda sabo datayi dasu
Nanfa sukadauki hanyar kukunba, shiru ne yaratsa a motar tsakanin ita dashi bawanda ya iya magana kowannensu da abinda yake saqawa aranshi, saida sukayi tafiya mai nisa sannan a hankali yarima yajuyo ya kalli fatee wadda ta tsareshi da ido ko qiftawa batayi
Fateema yakira sunanta a sanyaye shiru bata amsashiba, yakirata harsau uku amma ko ajikinta hakan ya tabbatar mishi bata tare dashi tayi nisa sosai a xurfaffen tunani
Yakama hannunta tareda hura mata iskar bakinshi a fuskarta firgigit tadawo hayyacinta nandanan kunya ta lullubeta tayi qasa da kanta yai murmushi mekike tunani haka qanwata? Tayi shiru fateema yakoma kiran sunanta na,am ta amsa qasa qasa, fateema kiyi haquri nasan na cutar dake kiyi haquri kiyafemin fateema nasan kina sona nasani fateema amma inadada baki haquri cos magana ta gaskiya bantaba jin sonki a xuciyata ba fateema ina sonkine kawai amatsayinki na yar,uwata ina fata kema xakiyi qoqarin juya sonda kikemin xuwa haka
Yayi shiru fateemadai batace komai ba sai hawaye dake xuba daga idonta domin kuwa abinda yake roqonta tayi abune da baxata taba iyawaba, magana ta gaskiya sonda takeyiwa fahad a xuciyarta kullum qaruwa yakeyi,
Kiyi haquri fateema dukda bansan komai akan so ba, nafahimci abin yanada xafi dakuma nauyi amma idan kika dake komai xai daidaita kinji, kiyi haquri qanwata banaso ki koma jefa kanki adamuwa kamar yanda kikayi abaya, dan Allah naroqeki kifitar da komai aranki kinji
Tadago jajayen idonta ta kalleshi saitaji tausayin kanta ya qara kamata dominkuwa babu digon soyayyarta a idon fahad, tayi qasa da kanta cikin takaici dajin haushin xuciyarta na nacewa wanda baya sonta
Cikin qarfin hali da kannewa tace karka damu dan,uwana insha Allah xanyi qoqarin yaqi da xuciyata kamar yanda kace xan soka amatsayin dqn,uwana tabbas xan aikata hakan nagode da kulawar dakake nunawa a gareni ina maka fatan alkhairi a ilahirin rayuwarka kayafemin yayana bansanba koxamu sake saduwa
Mutuqar tausayinta yashigeshi yarinyar tayi hankali yanxun yajata jikinshi ya rungumeta shima dai saida idonshi suka cicciko da qwalla wadda ya tabbatarwa kanshi ta tausayin fateece, nikuma nasmy nace anya kuwađ¤
Hmmmm muje xuwa!
*The game is nown started*
*Nasmy ce*đ
Yar mutan arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*5 star's ✨✨ online writer's association*đ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•96/100•*
Tayi shiru a qirjinshi tanajin wani ni,imtaccen sanyi na ratsa qirjinta haka shima a bangarenshi dama shi batun yauba yanajin irin haka idan jikinshi yahadu da nata wata irin nutsuwa yakeji a rayuwarshi amma sam baitaba dauka wani abu hakan yake nufi ba,
Take nutsuwarta ta daidaita amma saitaji takasa raba jikinta dana Prince, a hakan har suka isa qofar gidan wanda isartasu saida ta haddasawa yarima faduwar gaba wadda baisan dalilintaba
Yaya bashir suka fara karo dashi a qofar gidan dagudu ta tafi ta rungumeshi tana murnar ganinshi yai dariya fateen goggo andawo kai qanwata taxama yar birni, tayi dariya tayi cikin gidan da gudu a takiyar gidan ta tararrda goggo nanfa ta cakumeta tana ihu wayyo my goggo nayi kewarki wlh goggo ta mangareta gefe da wasa. ni tafi can karki karyani wanne kewata kikayi aida tuni kika dawo tayi dariya
Yaya fahad da bashir sukayi sallama suka shigo kowannensu daukeda qatuwar jakar kayan fateema, goggo ta tareshi da murna aka shimfida musu shimfida suka xauna suka qara gaisawa yake tambayar baffa tace ai yaje xagayen gwana bai dawoba tukanna, yace to gashikuma gobe in Allah ya yarda xankoma aa ah tafiyar ta tashi kenan cewar goggo yace insha Allah, nandai tayi mishi addu,a yaciro wayarshi yakira baffa yasanar dashi xuwan nashi bajimawa kuwa saigashi yaxo dayake gwanar ba nisa,
Addu,a sosai sukayiwa yarima yayi musu alkhairi mai yawa sannan yatafi yabar fateema tanata xubda hawaye, yatafi cikeda tausayin yarinyar axuciyarshi
Bayan komawarshi gida kuwa saiyaji ba dadi kasancewar yariga ya saba da hira da fateema yawan shirme da shagwabarta suka dinga dawo mishi saiya tsinci kanshi dayin murmushi ahankali yace smart girl
Washe gari kuwa jirgin safe yabi qarfe tara nacan yq sauka sweezland tsaf tsaf yasami gidanshi kamar yanda yasaba yasami tarba ta musamman gun sonia kasancewar yasanar da ita xuwan nashi, dayake yakan kira wayarta sudan taba hira sometimes lokacimda yake 9ja, wanka ta tusashi agaba tayimishi sannan ta dauro mishi towel tajawo hanjunshi xuwa danning area shikuma binta kawai yake kamar qqramin yaro duk sai yaji yanda tajeyi dashi din wani iri kasancewar an dade ba,ayiba haka tadinga bashi abinci abaki har saida yace ya qoshi sannan itama taci suka koma toilet sukayi brush to tundaga canfa tafara rikitashi da wasanninta masu daukar hankali abinkada mai nema Prince dama andade ba,ayiba ya dauketa cak sai bedroom dinshi nanfa suka hau aikata masha,arsu nidai nabar musu dakin
gun fatee nakoma a kukunba baiwar Allah harya xuwa wannan lokacin tanan takure takasa sakin jikinta da iyayentama dakinta tashige kaj katifarta ta dauko photon nan na yaya fahad tafara kallo tana shafawa kamar wadda ta shekara bata ganshiba, innawuro ce tashigo dakin dagudu tana ihun murna wayyo my fatee oyoyo ta rungumeta itamadai qanqameta tayi dan tayi kewar qawarta ba kadanba
Kai fatee awodi kinyi kyaufa wlh kinxama yar birni tafada tana kallon fuskar fateen yanda tadada yin fresh ta goge tayi dariya ba dole inyi kyau ba qawata wlh bakiga yanda yaya fahad yake ji dani ba ta dauko qaramar jaka taxaxxageta kayan mayuka ne kawai sa na make-up tace kallifa irin wannan kayan danake shafawa yanxun tabude mata manyan trolleys dinnan taga irin kayandake ciki innawuro takama baki cikeda mamaki kai fatee wlh kekam Allah yabaki wannan yayan naki yana sonki Allah yasakamu a danshinku
đ *Nasmy ce* đ
Yar mutan arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*5 star's ✨✨ online writer's association*đ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•101/105•*
Wasu hawayene masu xafi taji sun cicciko idanunta suna qoqarin xubowa tayi hanxarin maidasu dan hatta qawar tata bataso ta fahimci yaya fahad baya sonta amma agaskiya tana tsananin tausayin kanta
Takawar da maganar da yar dariya kai innawuro kema in Allah ya yarda xaki sami naki gwarxon to Allah yasa sukayi dari nan tafiddawa innawuro kala uku masu kyau cikin kayan ta bata. Tayita godiya dan tajidadin kayan sosai da murnarta tanufi gidansu
Bayan tadawo daga rakiyar innawuro ne ta dauko kayan duka tanunawa goggo sosai goggo tayi mamakin fahad dayiwa fateema wannan hidimar haka. Aranta tace to kodai yafara son fateen ne?
Afili kuwa har kama baki tayi kai fatee wannan kayan haka saikace kayan aure? Tayi dariya hmm kaji goggo wlh ni kayan aurena saisunyi goma irin haka itama goggon dariya tayi to Allah yakawo mijin xamu gani ai inda rai fateema ta kiklnkimi kayanta tashige daki dan itakam miji indai ba yayanta fahad bane ta haqura da aure duka
Sati biyu da dawowar fatee ta ware tafara komawq fateen nan mai yawan tsokana fara,a da walwala kullum cikin bawa kanta haquri take akan soyayyar yayanta dukda tasan naxata iya barin sonshiba amma tana neman sauqi akan abin
A bangaren fahad kuwa sam baisan fatee wata abace ga rayuwarshi ba saida suka rabu yau kwana biyu kenan daya kori sonia kasancewar duk abinda yakeyi da ita yakasa samun nutsuwa kwatan kwacin wadda yake samu idan yana tareda fatee suna hira, ahalin yanxu yagama yarda da cewa shima yakamu da son fateema, cos tunqnita dayasakashi agaba ako ina, yake kuma akoda yaushe tuna kyakkyawar fuskarta yake mqganar ta, yanayinta, shagwaba, da abin dariya kai komai ma, komai na yarinyar burgeshi yake
Yagama tabbatarwa yana sonta kuma ashirye yake daya aureta akowane lokaci dan yanxun shikadai yasan yanda yake axabtuwa da rashinta a kusa dashi idan yaji kewar tata ja neman illatashi sai yakira kawu sugaisa daganan saiya yanemi abata wayar sukan dade suna hira saidai baitaba gaya mata yanxun shima yana sonta ba, yanaso yafara maganar da mahaifinshi ne,
Kwanci tashi ba wuya awajan Allah yau wata biyu da tafiyar yarima yakai qarshen haqurinshi da boyon soyayyar fatee dayakeyi aranshi wani lokacin ma jiyake kamar yadawo gida ayi auren yakoma da ita, amma yanxunma yace yasan abinyi
Fatee kuwa ayanxun jarrabawa ce ta dauki hankalinta ssce da suke rubutawa wato warc and neco karatu take sosai dan ayanxun tanaso ta ilmantu taxama cikakkiyar yar birni wayayya mai aji burinta kenan arayuwa taxama likita intasami dama, hakan ne yasa ayanxu ko wayar yarima ta daina amsa saidai tace agaisheshi ita karatu take, abinda ke matuqar bashi mamaki da tsoro kenan kardai yarinyar nan tasami wani ta manta dashi
Yau takam ranar jummu,a ne babbar rana dayanayin hadari kuwa agarin hakan yasaukarda ni,ima sosai ga maxauna garin, daga can fadar mai Martaba akaturo mota ta musamman aka dauki baffa akaj cewar mai martaba yanason ganinshi cikin shiga ta alfarma baffa yashirya sukatafi da yaya bashir
Qarfe hudu nayamma baffa ya dawo cikeda farin ciki tareda rakiyar dinbin mutane da kayan aure yashiga gida da sallama bayanshi kuwa mutane ne dauked kaya goggo ta taresu cikeda mamaki bayan fitar mutanen yaciro kudi dubu hamsin daga aljihunshi ya ajiye agabanta taqara cikada mamaki yace ina fateema take? Tace ta tafi gidansu injawuro, yaceto madalla dama banaso taji me xamu tattauna goggo taqara gyara xama inajinka yace ayau dai Allah yayi andaura auren fateema goggo ta xaro ido tace aure? Baffa yace aure kuwa murya a sarqe take tambaya aure kamar ya malam? Dawa kenan? Yai murmushi yace da dan,uwanta fahad mana nanfa goggo ta hau murna da farin ciki kai alhmdllh yau fateema buri ya cika dama ashe da aure tsakaninta da fahad Allah sarki Allah mun gode maka
Baffa yace to ai wani hanxari ba guduba, yaya yace kar asake asanarwa fahad wannan auren harsai ya tabbatar shima yana sonta danfa wannan hasashenmu ne yarima bai taba fada yana son fateema ba saidai mu amatsayin mu na manya mun fahimci akwai so atsakanin su
*Nasmy ce*đ
Yar mutan arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*5 star's ✨✨ online writer's association*đ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•106/110•*
Goggo taqara murmusawa akwai so mana malam nima da nadauka ita kadai ke dawainiya da sonshi ashe bahaka bane abaya-bayan nan na fahimci shima yana Santa dan irin kulawa da hidimar dayakeyi da ita ma ai bana wasa bane kai madalla yau fatee xatayi baccin farin ciki
Hakadai suka cigaba da tattauna yanda mai martaba yatsara xa,a tafiyarda komai ahankali amma itakam lallaine asanar mata saidai baxa,a gaya mata bada sanin fahad din akayi ba kartaji wani iri,
Dai dai lokacin fateeka tayi sallama tashigo gidan sanyeda kayan makaranta ganin manyan akwatunan da ke jibge a tsakar gidan yasata sassauta tafiya takalli goggo wannan fa daga ina? Kayaj me wannan goggo?
Tayi murmushi kayan auranki ne, tabata amsa ataqaice ta qara kallonta cikeda rashin fahimta da Neman qarin bayani tace banganeba goggo taja hannunta ta xaunar da ita a gefenta sannan ta kalleta nakine fateema ayau dubannin mutane ne suka shaidi daurin aurenki a garin gombe babban masallacin mai martaba fateema ta xaxxaro ido aurena fa kika ce goggo
Nanda nan qwallq suka ciko idonta wannan wane irin hukunci aka yanke mata yanxu shikenan an gurgunta mata burinta nayin karatu mqi xurfi taxama likita hawayen suka gangaro kan kumatun ta goggo tayi murmushi nikaina bansanda xancenba fateema haka Malam ma, wannan hukuncin na mai martaba ne yadaura aurenki da yayanki fahad bisa yarda da tarbiyyarki tareda tabbacin baxaki bijire masaba, nikuwa abin yayimin dadi dan nasan kinason fahad din, kuma koba komai gwara hakan duk sa,anninki a garinnan suna gidan maxajensu wasu hadda haihuwa
Sam fateema bata tareda goggo saidai idonta nakan fuskar goggon tanaganin lebenta suna motsi alamar magana take mata saidai ko kasheta xa,ayi batasan me goggon take cewaba, tun daga likacinda taji wai an daura aurenta da yaya fahad, innalillahi
Tajuya ta kalli baffa idonta cikeda hawaye saidai takasa furta komai haka tamiqe taja qafufuwanta daqyar ta isa dakinta me hakan yake nufi? Andaura aureta da yaya fahad? Tanaxuwa ta xube kan katifarta nanfa hawayen sukacigaba da surnanowa itakanta takasa tantance wane mataki take ciki shin farin ciki ne ko baqin ciki?
Shin yaya fahad din ne dakanshi yanemi aurenta kodai qaqaba mishi ita akayi? Tabbas tasan babu sonta ko kadan a xuciyar fahad kuma bata tunanin xai sota naxaman aure saidai na xumunci kamar yanda akowane lokaci yake tabbatar mata,,
Hmmm yanxu inhar tunaninta yatabbata meye makomar rayuwarta a gidan yaya fahad, meye makomar burinta nakaratu daxama cikakkiyar likita? Nanfa wani sabon kuka ya qwace mata
Kafin kace meye lbrn auren ya karade gari, domin baffa yaje yasanar da mai anguwar shikuma ya sanar masu jin dadi sujaji masu baqin cikin rasa fateema kuma nayi domin kuwa sosai takeda masoya a garin kawai kulasune batayi
Haka mata suka dinga tururuwa xuwa wajan ganin kayan lefen nata abinda ba a taba ganiba wato ba wadda aka taba yiwa kwatan kwacin haka a qauyen adda ma taxo daj goggo ta aika yaya bashir yakirata haka innawuro tabiyo bayanta bayan gama ganin kayan tabi qawarta daki domin tayata murnar wannan al,amarin farin ciki na baxata, fateema tayi iya qoqarinta ta danne damuwarta sundan dade suna hira anan innawuro tace kin gode Allah yau muka xana jarabawar qarshe da an hanaki iyarwa yanxukam sai jiran sakamako ko baffama xai karbo miki tayi wani dan tsaki banda abinki qawata meye amfanin resold din tunda an riga anmin aure ai karatu kam yaxo qarshe tace hakane kam toke fatee ai kema saninki ne ba wani karatu daxa,a barki kiyi agarinnan ba aure, danma Allah ya taimakemu mungama wannan danmafa bakiji yanda ake xagin mu agarin nan bane wlh kin huta nima nasan nan bada jimawaba auren xa,amin sukayi dariya kafun fateema taji kira daga goggo ta tashi tafita wata dattijuwa tasamu xaune a gefen ta, tagaishesu sannan itama ta raba gefe taxauna tace gani goggo ta kalleta tace wannan inna kenan daga yau ba inda xaki koma fita inna itace wadda xata cigaba da kula dake agidannan kuma karki yarda inji tace ga abinda xakiyi kimata gardama fateema ta amsa da to tamiqe xata koma daki dawo aitundaga yanxu xa,a fara tatusa qeyar fateema suka shiga bandaki wasu ruwane dasukaji hadi da kayan qamshi dasu tayimata wanka bayan tasha fama da ita wajan cire kayanta haka ta fito tana sharar qwalla goggo bata kulata takoma dakinta tana gunaguni qasa qasa tasamu innawuro ta wuce hakan yasa tacanxa kayan jikinta tabi lfyr shinfidarta
0 comments:
Post a Comment