Dady da momy dakuma fa,eex da fateema kaitsaye sashen gidan waxiri aka kaisu kafin cikar lokacin hutunda likita yabuqaci abawa mai martaba dama can matar gidan tasan fateema basu fuskanci wata matsalaba antaresu cikin girmamawa da karamci part daya aka ware musu mai daki biyu da babban falo kowanne daki yanada bayi acikinsa
Afalon sukafar yada xango nanma aka koma gabatar musu da kayan abinci dana sha harmada maqulashe kasancewar aqoshe suke yasa basuci wani abin kirkiba suka bige da hira ta jajanta yanda lamarin ya kasancewa mai martaba lurada iyayen sukayi yaronsu yana buqatar ganawa da fateema yasa suka miqe sukashige daya dakin dake gidan sukabar subiyun afalo
Hakan yasa falon yaxame masu shiru dan acikinsu bawanda yakoma magana tsawom daqiqu fateema kanta yana sunkuye aqasa fa,eex yakasa haqura domin kaikawo da xuciyarshi take masa abisa tunanin dayayi naganin yau xuwa gobe xasu rabuda fateema rabuwarda yakeganinta kamar shine ganin qarshe daxai mata gashi har yau bai isar mata da saqon xuciyarshi ba,
Shine yaqatse shirun tahanyar yin gyaran murya yace fateema! batareda tadago kaiba tace na,am saikuma yakoma yin shiru kafin yadorada fateema kiyi haquri kiyafemin baxan boye miki sirrin xuciyata ba tundaga waccan ranar danafara dora idona akanki naji nakamu da qaunarki xama damukayi dake nakwana daya amota jinsa nayi kamar rayuwata ce tafaro daga wannan lokacin nakamu da sonki fateema, sbd hakanan bbu irin tunanin da banyiba naganin kinbaro gidanku a yanayi da shekarunki sai wata xuciyar tabani kamar kin aikata wani mummunan laifine yasa kika gudo daga gidan iyayenki dukda hakan ban iya rabuwa dakeba saboda tsananin qaunata gareki fateema
Saida yadan ja numfashi kafin yacigaba wannan ne dalilin dayasa nadage da bibiyqrki har saida nakaiki gidan mu sannan nasami kwanciyar hankali da nutsuwa fateema tunda aka haifeni banyi soyayya ba nikwata kwata bansan soba saida Allah yahadani dake bayyanar gaskiyar lbrn dakika bamu ayau yaxamo wata iska da taqara rura wutar so da qaunarki axuciyata ina sonki fateema kidaure kisoni kisakani a xuciyarki, idankikayi hakan xaki sami ladar ceton rayuwa dominko ina tabbatar miki rayuwa fankoce indai babuki acikinta idan kikayi kuskuren qina kuwa saiyayi shiru hawaye suka fara bin kuncinshi yadibi dan lokaci ahakan sannan cikin wata disasshiyar murya yace idan kikaqini fateema ba makawa mutuwa xanyi, yaja numfashi tareda share hawayen fuskarshi
Allah sarki rayuwa fateema yarinya ce mai matuqar bawa soyayya girma da daraja tayarda da SO kuma tana tausayin duk wanda yafada cikinsa, kuku tafarayi ciki ciki wai yau itace ake bararr soyayya daga gareta itace qasaitaccen mutum kamar wannan yake tabbatar mata xai iya mutuwa sbd ita, yau itace awannan matsayin.................. tsugunawar da fa,eex yayi agabanta itace ta katse mata wayannan tunanikan aganta ya tsuguna bisa guiwoyinsa idonshi na fitarda qwalla yace fateema ni bawane ga soyayyarki ta takurani ta hanani sukuni pls fateema nariqeki kada kibari in rasaki kitaimakeni wlh ina qaunarki fateema wlh nibasan haka SO yakeba dan Allah kisoni wlh inkika qini xan mutu mutuwa xanyi fateema
Kuka mai qarfine ya qwace mata ba shakka Allah (s,w,a) yayi gaskiya tabbas shidin mai rahamane ga bayinsa fateema ta taso tana soyayya batada wani burin dayawuce asota amma hakan bata samu ba ayau kuma daga wani wajan Allah yafiddo mata dawani masoyin daban wanda xai iya bada rayuearshi ya ceci tata, aranta tace tabbas wannan damace taxomin wadda xata ceceni daga abinda nake tsoro daga iyayena wato mayarda aurena ga *yaya fahad* haqiqa xanyi qoqarin cusaka araina fa,eex koba komai kana nunamin So abinda nafiso arayuwata kenan xankoyi sonka natabbatar baxansha wahalar sakaka a xuciyata ba
Wannan duk maganar xuciyar fateema ce alokacinda ta kafe fa,eex da ido ko qiftawa babu, shikuwa alokacin neyasami damar qarewa fuskar tata kallo alokacin yaqara tabbatarwa kanshi tabbas fateema itace matarda yake muradi komai nata 100% dana matar da yakeda burin yasamu tsawan shekaru
Sun qurawa juna ido bamai so yaqifta domin kuwa ita fateema tunani takeyi axuciyarta sam batamasan irin kallonda takewa fa,eex kenan ba, shikuwa hakan datayine yabashi damar kallon nata, duikaninsu sunyi nisa da abinda sukeyin
Qarar bugun qoface tadawo dasu hayyacinsu tafirgigit tagyara xamanta akan kujera shikuma yamiqe daga tsugunon dayayi agabanta saida yasaka handkerchief yashare fuskarshi sannan ya isa ga qofar yabude qofar dan aikane daga mai martaba yadawo hayyacinshi yana buqatar ganinsu duka
*Nasmy ce*đ
Yar mutan arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐
⭐
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•216/220•*
Daga inda take tanajin abinda dan aikar yake fadi tamiqe xumbur tana sharar qwalla wanda hakan yayi daidai da shigowar dady da momy falon kallo daya sukayiwa yaran suka tabbatar kowannensu yayi kuka ganin fa,eex shiru2 yahaifarwa momy da faduwar gaba kardai fateema bata karbi soyayyarshi ba shikuwa abinda ya susuta shi shine fateema bata bashi kalma kodayaba xuk da cewa bai hango qinshi a idonta ba amma yafiso yaci daga gareta koxai sami sassaucin xogi da radadin xuciya
Asanyaye yasanar dasu saqon mai martaba suka ce alhmdllh to ai saimutafi kawai momy ta kama hannun fateema dady yai gaba suka rufa mishi baya
Adakin mai martaba kuwa shikadaine kishingide a kan makeken gadonsa sukayi sallama bayan anmusu iso suka shiga duka suka gaisheshi tareda yimishi yajikin ya amsa dasauqi sosai fateema har gabanshi taisa taxauna agefenshi su dady nadan nesa dasu kadan ahankali yafara magana yace yihaquri yata natura akiramin yayan naki sannan nakira baffanki suna hanya insha Allah xuwa anjima duk suna nan yamaida kallonshi ga dady yace alhji nagode ubangiji Allah yasaka maka da mafificin alkhairin sa Allah yabiyaka dady ya amsa da ameen ya rabbi Allah yabawa sarki lfy shima yace ameen
Da sallama aka turo qofar dakin gabadaya suka juya dan ganin mai shigowa umman yarima ce dakuma shikanshi yariman Wanda saida tasha fama sosai kafin tasamu yafito daga gidanshi domin amsa kiran mai martaba
Bayariman ba hatta umman ganin fateema xaune agefen mai martaba yayi matuqar girgixata harsaida takasa boyewa tace fateema fuskarta cikeda mamaki fatee takalleta kawai amma bata amsa mataba ganin yarima saida yamotsa xuciyar ta saitayi gaggawar kawarda kanta gefe, shikuwa yarima qirjinshi ne yashiga dukan uku uku qwaqwalwarshi taso ta tunano mishi wani abu amma hakan yafaskara saidai dunbin damuwa dayaji ta mamaye duk wani saqo da lungu na xuciyarsa adarare suka qarasa gaban mai martaba suka xaxxauna suka gaisheshi tsoro da firgici qarara afuskar yarima xuciyarshi tahau bugu kamar xata fallo qirjinshi tafito, fa,eex yabishi da kallon raini wanda shi yariman baimasan daxamanshi agunba
dattijan ya yunqura ya daidaita xamanshi ya fuskance su sannan yace yarima fahad ayau wani mummunan labari riskeni cewa kasaki auren dana daura maka da qanwarka fateema shin gaskiyane? Hannu yasaka yashare guminda ke yankomasa yagama rudewa amma dayake yasan halin wanda keyimasa tambayar yasa koda wasa bayyi tunanin fada mishi qaryaba wata tambayar yakoma jeho mishi yace kainake sauraro shin gaskiyane kasaketa? Eh abba...........tasss yaji saukar wani raxanannen mari afuskarsa wanda yahaifar mishi da jiri saida kowa adakin ya raxana nandanan lafiyayyar fatar fuskarshi tayi jajir fatarda sam bata taba sanin xafin dukaba idonshi suka kada kamar gauta
Yadafe kuncinshi yana jinjina girman abinda yasaka abbanshi ya iya dukanshi xumbur ummanshi tamiqe tahau sababi a ah dakata mai martaba dafa d`afake gani baifi d`a ba akanme xaka dakeshi akan yar dan uwanka tafishi agunkane? To wlh ni tunwuri kasani baxan taba bari aure ya yuwu tsakanin yarima da fateema ba, kuma wani abu dabakasaniba na hada auren yarima da yar yayata laxeera yau kwanaki biyu da daura auransu harma da tarewarsu sbd haka kasanyaya xuciyarka karma kayi wani tunanin gyara auren nan wlh baxan lamunta ba
Tunda tafara maganar bawanda ya katseta saidai bawanda baiji abin awani daban ba musamman fateema saita tsinci kanta da jin xafi daciwon auren laxeera da,akace yarima yayi duk dacewa ayanxun ba qaunarsa takeba shikuwa fa,eex maganar umman yarima tafimasa komai dadi arayuwashi na cewar datayi baxata taba bari agyara wannan auren ba, falon yayi tsit kowa da abinda ke yawo axuciyarshi
*Nasmy ce*đ
Yar mutan Arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐
⭐
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•226/230•*
Umma Gabaki dayan Idanunta ta War-waro Innalillahi mai Martaba? Mexan gani haka? Mekake nufi? Sakina Kayi wai? Nashiga uku Dangirma Da Darajar Allah Kayi Haquri Kamaidani Kafi kowa Sanin Iyayenmu Sundade da Mutuwa wlh Banida kowa sai yayata Kataimakeni, taja Guiwa ta isa Ganasa sai Alokacin tasamu damar Fashewa da kuka tayi Magiyar Duniyar nan amma sarki ko Kallon Gefenta bai koma yiba, baffa da goggo ma duk jikinsu amace ko Magana sun kasayi, Bashir kuwa jiyake da Dahukunci dayafi hakan dashi Xa,aimata haka tagaji da Gunjin Kukanta ta tashi fita,
Lokacinda tafita me Yarima yasami Damar Miqewa Shimadai Barin Dakin yayi Xuciyarshi Cikeda Takaici da Tashin Hankali Tunda yake Abbanshi Baitaba fushi dashiba Ballantana yai Tunanin Dukanshi, Gashi ayau ba wanda bai Samuba, Agaban kowa da kowa yace babushi-babushi harda Korarsa daga Gidan, yasaki ummanshi yasalam! Damuwa tarigada tayimasa yawa Jiyake kamar ya kurma Ihu, yana Tafiya yana Waswasi Kokadan Baya Ganin Abindake Gabansa Ikon Allah ne Kadai Yakaishi Sashenshi, Afalo yasami Sarauniyar tasa Tamiqe Akan Doguwar kujera, tasha make-up taci ado da Wata Damammiyar riga ta roba Gajera ce Bata wuce Cinyarta ba, Tana Ganinshi Tamiqe Dasauri ta Taroshi da Murmushin nan na kissa a Fuskarta ta Rungumeshi kafin takai masa kiss a Gefen Fuskarshi, yasalam! Frnds muji Tsoron Allah kuma Muji Tsoron Asiri, Tabbas Hausawa sunyi Gaskiya dasukace Tsafi Gaskiyar Maiyinsa, Duk Tsananin damuwa da Tashin Hankalinda Yarima Yashiga yanayin Arba da Laxeera Yanemi Damuwar Yarasata Hankalinsa Yakwanta Rayuwarsa Tadawo Tsaf! Sam Yamantada Mahaifin Nasama Ballatana Wani Abu daya Hadasu, Nandanan suka lula Wata Duniyar Baikoma Tunanin Mahaifiyarsa ba Balle Halinda Take ciki
Umma Tashiga Rudu hadida Matsanancin Tashin Hankali Kuka take Kamar ba Gobe, Da Lalube tanemo Lambar Yayarta Wato Mahaifiyar Laxeera cikin Kukan Tasanar Mata Duk Abinda Yafaru Saida Tagama Bayanin sannan umman laxee Ta Katse wayar Batareda tace da ita Wani Abu ba, Matuqar Mamakine Yakama Umman Yarima Takafe Wayar da Ido Kamar Xataga Fuskar Yayar tata Aciki, Taxata Yankewa wayar tayi Shiyasa takoma Danna kira wayartayita ringin Harta Yanke Ba,a dagaba, Ganin Abin Xaicimata Lokaci Yasa Tafara Hada Kayanta Tanayi Tana xubda Hawaye
Umman Laxee kuwa Tanaganin Wayar Umma Dagan-gan Taqyaleta Aranta kuwa Cewatake Anxo Wajan...................
Tadauki Waya Takira Laxeera Tashaida Mata Cewa tayi duk Yanda Xatayi Tafiddo Yarima daga Gidan nan Yadawo Hannunsu Tayanda Xasu Tatseshi Yanda Sukeso.
Shikuwa mai Martaba da Hawayenshi yaita Rarrashin fateema dakuma roqonta gafara yace" fateema kiyi haquri bansan fahad xaiyimini hakaba wlh daban hada auren nan ba, yajuya ga baffa shima dai kukan yakeyi yaita bashi baki daban haquri. Agidan suka kwana haka su momy ma sashe daya aka hadesu goggo tayita yimasu godiya
Gariya waye har baqi suna shirin tafiya wato su momy da dady dakuma fa,eex amma basu koma ganin fateema ba tun daren jiya taboyr kanta, babuta babu Alamarta. Fa,eex yaga har anmusu rakiya a inda sukayi parking amma babu fateema, gashikuma babu damar tambaya dan mai martaba ne dakansa yayomusu rakiya tareda baffa da bashir yayan fateema, gata babu waya ahannunta balle yayi tunanin kiranta koda sunje gidane
Dabaru yayi yakarbi number yaya bashir dan yatabbatar da ita xasu tafi
Akayimusu gomasha na arxiqi sukayi sallama suka tafi xuciyoyi cikeda abubuwa daban-daban soyayya, waswasi, mamaki dakuma tausayin fateema....................................................Nikaina Nasmat Abinda ya Mamayeni Kenan Bansan Lokacinda Alqalamina ya Subuce ba
*Readers Kumin Afwa Anan Xan Dakata Sai Kutareni After Ramadan, Wato Bayan Salla Domin jin Cigaban Wannan Labarin na Yaya Fahad Nawane, Dominjin Mokomar Rayuwar Fateema, dakuma Qarshen Tirniqin Tsafinsu Laxeera da Yarima Fahad, shin ya Tsakanin Umman Fahad da Umman Yarima Xai Kasance? Hmmm Muhadu A Bayan Salla Dominjin Qarshen Wannan Badaqalar, Fata anan Shine Allah Yasa Munada Rabon Ganin Lokacin*
*Nasmat tana muku fatan Alkhairi Gabadaya Madoyana Happy Ramadan Kareem*
Masoyan gaske
Maimuna Ibrahim isah
Sis Hawwa
Asiya Isa
Baby Maryam
Ruqayya
Sis Ama
Nadiya
Zeesah
Mmn zee
Mom Nasren
Action baby
Unique
*da Gabadaya Members na Nasmat Novel group, Ina sanku kuma ina Alfahari daku Allah ya Albarkaci Rayuwarmu dakuma ta ya'yanmu baki daya, Zanyi akewarku Sosai, love you all*đ
Jinjina ga qungiyar : *Zamani Writers Association* Allah Yaqara Daukaka da Farin Jini Ameen ya Rabbiđ
*Nasmy ce*đ
Yar Mutan Arkilla Love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐
⭐
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•221/225•*
Mai martaba baiceda umma komaiba yarima kuwa ko motsawa yakasayi daga inda yake sai matsar qwalla yake axajiri wani sashe na xuciyarshi yafara nadama akan abinda ya aikata wanda shikanshi baisan dalilin yinshi ba, fateema kuwa kuka tahauyi baji ba gani momy tajanyota jikinta tana rarrashi, yayinda dady yake bata baki, fa,eex kuwa jiyake kamar ya dauketa subar wajan yaje can wani kebabben guri ya rarrasheta domin yanajin kukan harcikin kwanyar kanshi
Adaidai lokacin ne akaturo qofar da sallama baffane tareda goggo dagudu fateema ta tari mahaifiyarta suka rungume juna matsanancim kukan da fateema take yatsorata goggo yayanta bashir ne yajata jikinshi xonan qanwata meyasameki haka? Takasa magana tayi shiru ta kwanta lif ajikinshi abinda yakusa yasaka xuciyar fa,eex bugawa sukanemi guri suka xaxxauna, suka gaisheda mai martaba da umma wadda take faman huci kamar xata fashe goggo taqara tsinkewa da lamarin kardai duka tayiwa fateema,? Kai inaa ai baxaiyiwa ba wannan duk maganganun xuciya ne, yarima yagaishesu cikin wani yanayi ba boye2 sunriga sun fahimci ba lfy ba, saidai koma mene ne to dasauqi tunda Allah ya bayyana musu yar'su fateema
Suna cikin gaisawa dasu dady da momy ne aka kuma turo qofar da sallama wannan karon su waxirin sarki ne da shamaki dakuma mai fada. Wayannan sune manyan mutanenda mai martaba yake shawara dasu kafin ya yanke duk wata shawara data shafi fada, ganisu yasaka jikin umma da danta yarima yayi sanyi bashiri tanemi guri taxauna. Suma suka xaxxauna suna sauraren mai martaba
Yafara magana Ahankali kamar bayasanyin maganar bakomai bane yasakashi yin hakan saidan tsananin mutuwar jiki da nauyin bakinshi dayakeji adalilin wannan baqin cikin da yarima da mahaifiyarsa suka haifar masa , yace " Ayau kuma awannan lokacin agaban wayannan mutanen masu daraja da mutunci a idona, Na cire yarima fahad daga rayuwata na yafeshi duniya da lahira, sannan na haramta mishi gadon sarautata kobayan rayuwata bana buqatarshi kusada gawata in fact ina buqatar yabarmin gidana dashida mahaifiyarshi sunisanta dani dakuma masarautata ayau basai gobe ba.............innalillahi wa inna ilaihi raji,in abinda gabadaya mutanen dake wajan suke ambato kenan
Yarima kuwa baikoma jin komaiba kamar yadda yadaina ganin komai adalilin daukewar da ji dakuma ganinshi sukayi lokaci daya, wani irin bugu xuciyarshi tahauyi kamar xata fallo qirjinshi tafito waje, kanshi yahau sarawa da qarfi
Umma kam awurin tasuma daga xaunen datake
Fateema ta qara fashewa da kuka
Baffa kam miqewa tsaye yayi ya isa gaban yayanshi "haba yaya haba yaya mekake shirin aikatawa haka? Me yarima da hjya sukayi wanda yakai kayanke musu wannan dayen hukunci?
Mai martaba cikin daga murya yace "Auren damuka daura masa yasaki tunbaishiga dakin amaryar ba, dan uwana yarima yasaki fateema harma ya auri wadda yake So duk bada saninmu ba
Baffa da goggo suka dauki salati shamaki dasu waxiri ma haka,
Jikinsu yayi sanyi matuqa yaya bashir kuwa wani mugun kallo yashiga bin yarima dashi dan yariga ya cuci yar,uwarsa qanwarsa ya bata mata suna agari wanda hakan xai iya xama silar rasa mijin aure gareta, ace miji yasaketa a ranar farko data tare gidanshi wannan xai haifar mata da xargin mutane, yana kawowanan atunaninsa yafasheda kuka yaqara rungume fateema xuciyarshi fall da tsananin tausayinta
Baffa bakoma cewa komai ba ya silale yaxauna awurin danjin danyen aikin da yarima yayiwa yarshi yatabbatar rayuwar fateema ta tarwatse, yarima yacuceta tunda quruciyarta ba mamaki naxata taba samun mijin aureba harta mutu indai a qauyen kukumba ne sbd wannan sakin da,akamata yanada gagarumar fassara acan qauye
Goggo kam kuka take hani'an
Mai martaba yarubuta takarda yasaka hannu yajefawa umman yarima wadda tundaxu sanyin a,c yadaketa ta farfado saidai ba laka ajikinta takasayin koda motsin kirki daqyar tamotsa ta dauki takardar
Innan lillahi
*Nasmy ce*đ
Yar mutan Arkilla love you all đ
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐
⭐
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•221/225•*
Mai martaba baiceda umma komaiba yarima kuwa ko motsawa yakasayi daga inda yake sai matsar qwalla yake axajiri wani sashe na xuciyarshi yafara nadama akan abinda ya aikata wanda shikanshi baisan dalilin yinshi ba, fateema kuwa kuka tahauyi baji ba gani momy tajanyota jikinta tana rarrashi, yayinda dady yake bata baki, fa,eex kuwa jiyake kamar ya dauketa subar wajan yaje can wani kebabben guri ya rarrasheta domin yanajin kukan harcikin kwanyar kanshi
Adaidai lokacin ne akaturo qofar da sallama baffane tareda goggo dagudu fateema ta tari mahaifiyarta suka rungume juna matsanancim kukan da fateema take yatsorata goggo yayanta bashir ne yajata jikinshi xonan qanwata meyasameki haka? Takasa magana tayi shiru ta kwanta lif ajikinshi abinda yakusa yasaka xuciyar fa,eex bugawa sukanemi guri suka xaxxauna, suka gaisheda mai martaba da umma wadda take faman huci kamar xata fashe goggo taqara tsinkewa da lamarin kardai duka tayiwa fateema,? Kai inaa ai baxaiyiwa ba wannan duk maganganun xuciya ne, yarima yagaishesu cikin wani yanayi ba boye2 sunriga sun fahimci ba lfy ba, saidai koma mene ne to dasauqi tunda Allah ya bayyana musu yar'su fateema
Suna cikin gaisawa dasu dady da momy ne aka kuma turo qofar da sallama wannan karon su waxirin sarki ne da shamaki dakuma mai fada. Wayannan sune manyan mutanenda mai martaba yake shawara dasu kafin ya yanke duk wata shawara data shafi fada, ganisu yasaka jikin umma da danta yarima yayi sanyi bashiri tanemi guri taxauna. Suma suka xaxxauna suna sauraren mai martaba
Yafara magana Ahankali kamar bayasanyin maganar bakomai bane yasakashi yin hakan saidan tsananin mutuwar jiki da nauyin bakinshi dayakeji adalilin wannan baqin cikin da yarima da mahaifiyarsa suka haifar masa , yace " Ayau kuma awannan lokacin agaban wayannan mutanen masu daraja da mutunci a idona, Na cire yarima fahad daga rayuwata na yafeshi duniya da lahira, sannan na haramta mishi gadon sarautata kobayan rayuwata bana buqatarshi kusada gawata in fact ina buqatar yabarmin gidana dashida mahaifiyarshi sunisanta dani dakuma masarautata ayau basai gobe ba.............innalillahi wa inna ilaihi raji,in abinda gabadaya mutanen dake wajan suke ambato kenan
Yarima kuwa baikoma jin komaiba kamar yadda yadaina ganin komai adalilin daukewar da ji dakuma ganinshi sukayi lokaci daya, wani irin bugu xuciyarshi tahauyi kamar xata fallo qirjinshi tafito waje, kanshi yahau sarawa da qarfi
Umma kam awurin tasuma daga xaunen datake
Fateema ta qara fashewa da kuka
Baffa kam miqewa tsaye yayi ya isa gaban yayanshi "haba yaya haba yaya mekake shirin aikatawa haka? Me yarima da hjya sukayi wanda yakai kayanke musu wannan dayen hukunci?
Mai martaba cikin daga murya yace "Auren damuka daura masa yasaki tunbaishiga dakin amaryar ba, dan uwana yarima yasaki fateema harma ya auri wadda yake So duk bada saninmu ba
Baffa da goggo suka dauki salati shamaki dasu waxiri ma haka,
Jikinsu yayi sanyi matuqa yaya bashir kuwa wani mugun kallo yashiga bin yarima dashi dan yariga ya cuci yar,uwarsa qanwarsa ya bata mata suna agari wanda hakan xai iya xama silar rasa mijin aure gareta
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*Assalamu Alaikum masoya na, masoyan "yaya fahad" novel barkarmu da dawowa hutun salla. Da fatan dukkanin ku kunyi salla lafiya, Allah (s.w.a) ya karbi ibadodin da mukayi.*
*Fans kumin afwa da rashin dawowa bakin aiki da wuri, hakan yafaru ne a dalilin matsalar dana samu nayi jinya sosai amma yanzu kam Alhmdllh naji sauki kuma insha Allah zan kawo muku karshen labarinku har ma mushiga sabo daku.*
*Ku kasance dani u will always been in happiness guys, keep smiling đ masoyan Yar'mutan Arkilla* ANA TARE đđ¤
*•231/235•*
Fateema kuwa tana can saman bene daga d`akin mai martaba tana kallon duk abinda ke wakana, tana kallo Fa'eez da iyayen sa sukayi sallama da kowa suka shiga motar, Fa'eez shine na karshe a shiga motar dan tsayuwa yayi yana nazari kamar mai jiran wani abu kai da gani kasan bayason tafiyar ko kuma wani abu ne yake bukata kafin ya tafi, daga karshe dai bisa dole ya shiga motar direba ya tayar suka fice. Sam bataji dad`in kaucewar fuskarshi daga ganin ta ba, a wannan halin da take ciki ta tabbatar a yanzu babu SO a ranta sai dai ta yarda kallon fuskar yaya Fa'eez na d`aya daga cikin ababen dake rage mata rad`ad`i da zogin abinda yarima yayi mata. Tayi nisa sosai a cikin tunanin da take saiji tayi an dafata ta baya juyowar da zatayi sai taga Bilki ce d`aya daga cikin kuyangin dake mata hidima idan tazo gidan. hakan yasaka ta fad`ad`a fuskarta da murmushi domin ta saba dasu sosai "Bilki ya dai, ina Rukayya? " ta fad`a cikin ko'karin ta na boye damuwar da take ciki. Bilkin ma murmushin ta mata kafin tace " ranki ya dad`e wlh ni kad`ai nake kuma wurinki nazo zamuyi magana kafin su goggo su dawo" Fateema ta kalleta cike da mamaki ta ce "magana Bilki?, to ina jinki Allah dai yasa lafiya" Bilkisu ta karayi kusa da Fateema sanna tayi kasa da muryar ta ta fara magana a hankali cikin rad`a tace " wlh anty fatee yarima na matukar kaunar ki, Fateema ta d`ago da sauri dan ko kusa ba abinda tayi tsammanin ji kunnen ta yaji ba. kamar zatayi magana sai kuma Bilki ta katseta ta hanyar cigaba da cewa " wlh yana sonki sai dai an riga an fi karfin sa, alamun mamaki karara a fuskar Fateema take kallon Bilkisu. tace "eh wlh fin karfin sa akayi dan asiri akayi mishi Umma ce da Hajiyar Lazeera ke harma da Lazeeran, anty Fatee nida nake nan nizan gaya miki komai yanda yarima ya tsani anty Lazeera da can wlh ko gunda yake zaune bata isa ta raba ba, idan ya ganta ji yake kamar ya kasheta saboda sha'shanci da rashin kamun kanta." Nan dai Bilkisu ta kwashe duk abinda ta sani ta shaidawa Fateema. Allah sarki hausawa suka ce sauran SO yafi sauran KIYAYYA domin kuwa cikin kan'kanin lokaci tsanar da Fateema ta yiwa Fahad ta juye ta zama tausayi
Jikin ta yai sanyi matuka tausayin yayan nata ya kamata soyayyar shi kuma ta dawo sabuwa fill a zuciyar ta, cikin zubda hawaye ta kalli Bilkisu tace "na gode Bilki da kika sanar dani wannan sirrin kafin nabar garin gwambe tabbas ba inda zani har saina ceto d`an'uwana kuma miji na daga wannan halin da yake ciki, na gode da kika gayamin tana shirin rabashi da gidan nan ina tabbatar miji cewar bata isa ba, wannan gidan namu ne, masarautar gombe tamu ce, kuma *YAYA FAHAD NAWA NE* na rantse miki saina karbo Abina" ta fad`a tana share kwallar dake fitowa daga idanun ta. zuciyar ta ta riga da ta dake ta rika hannun Bilki dan su koma babban falon
Juyawar da zasuyi sai sukayi kicibis da duka iyayen nata Baffa da Mai martaba Goggo da yaya Bashir dukkanin su sunyi jugun-jugun alamu sun nuna ba abinda basuji ba daga hirar tasu. "Ya Rabbi" Fateema ta fad`a tare da sunkuyar da kanta kasa Bilki kam tsoro ne ya baibayeta.
Mai martaba da kanshi yaja hannun Fateema tareda cewa Bikkisu "kema biyo ni" yayi gaba su Baffa suka rufa masa baya kafin Bilki itama tabi su sumi-sumi
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•236/240•*
_Wannan shafin sadaukarwa ne gareka fasihi matashin fikira,fasaha, da d`inbin basira dole muyi alfahari da kai autan writers_ *KING BOY ISAH* _Allah ya kara baiwar brain kuma ya kara d`aukaka *ZAMANI WRITERS*đ
Bai tsaya babban falonshi da suba har d`akin baccin shi ya kure dukkanin su suna biye da shi a baya. haka yaje ya zauna a wata kayatattar kujera dake d`akin sannan ita ma Fatee ya zaunar da ita gefen shi, su Baffa ma zaman suka yi a matukar rauna ne saboda maganar da suka ji ta gama kashe ilahirin lakar jikin su. Mai martaba yayi hmgyaran murya sannan ya kalli Bilkisu yace "shin ki tabbatar abinda naji daga bakin ki gaskiya ne?" Bilki cikin rau'rawar murya tace "eh-eh Allah ya taimake ka, wlh gaskiya ne ba'abinda na dad`a wlh inajin su kuma sau tari ina gani suke aikata wasu sirrukan. tayi shiru, iyayen suka cika da al,ajabi ya yarda dan yasan halin Umma sosai kawai kawar da kai yakeyi a zama da ita kasancewar shi mai sarautar babban birni sakin Aure ba nashi bane, yau d`in ma dan ta kaishi kwano ne. tunani ya shiga yi da nazarin abinyi, d`akin yayi tsit ba abinda ake ji sai karan (a.c)
Idan ka d`auke Fateema da Bilki kowa a wurin tunani yake yi na hanyar da za'a bulluwa lamarin, Faeema kuwa tun kafin su shigo d`akin ta samu way out a zuciyar ta, hakan ne yasaka batayi kasa a guiwa ba wajen sanar da iyayen nata sai dai kafin tace wani abu Baffa ya rigata da cewa "to kaji fa yaya yanzu yaron nan duk abinda yakeyi ba bisa hayyacin sa bane, gashi ka yanke masa tsatstsauran hukunci". Goggo tayi caraf tace "to yanzu yaza'ayi kenan meye mafita akan wannan lamarin?" Shirun da taji Mai marta yayi shine ya bata damar amayar da abinda ke zuciyar ta, sai da ta sunkuyar da kanta kasa sannan ta ara magana cikin ladabi da sanyaya murya tace "Ya'baffa tunda abin hakane ni inaganin kayi hakuri kawai kamaida aurena da yaya fahad, kuma ka hanashi barin gidan nan sai afara nemo masa magani da abubuwan karya asiri, ni kuma nayi muku alkawarin zan shanye duk wani wulakanci da cin zarafin da zasu yimin har zuwa lokacin da zamu samo hankalin sa, domin ni a ganina wannan ce hanya mafi sauki dazamu bi mu ceto rayuwar shi. Mai martaba ya kafe yarinyar da ido tsananin tausayin ta da hakuri da kuma zurfin tunanin ta sun burgeshi. Ahankali yayi gyaran murya sanan ya fara magana "Fateema Allah (s.w.a) yayi miki albarka irin tunanin kinan shine ya zomin a zuciya ta sai dai ina nazarin yanda zaki d`auki lamarin keda iyayen ki idan na furta, sai gashi kin fad`a da kanki ba abinda zan ce saidai Allah yayi miki albarka kije d`akin ki zamuyi magana dasu waziri".
Fateema ta mike zuciyar ta cike da was'wasin abinda ta ballowa kanta anya zata iya kuwa? haka dai ta fice Bilkisu na take mata baya. Kai tsaye sashen ta ta nufa inda ta fara tarewa har takai ga ko'far Bilki tayi saurin riko hannun ta, tajiyo da sauri a d`an razane Bilki tace "ki gafarceni anty a yanzu Yarima da Amaryar sa ne ke rayuwa a d`akin ki na da kiyi hakuri kishiga d`ayan part d`in tunda shima akwai komai a ciki gyara ne kawai wancan yafi dayan dashi". Wani shu'umin murmushi Fatee ta sake wa Bilki kafun tace " Ai wannan da kika gani shine asalin gida na saboda ni aka gyara shi, kuma ni nafara tarewa cikin sa saboda haka babu wanda ya isa ya hana ni zama a cikin sa, bata jira me Bilkisun zata ceba. kawai saita kunna kai a babban falon dayake shine farkon shiga gidan, subhanallah! Tafad`a da karfi a dalilin abinda idon ta yayi arba dashi ta kawarda kanta gefe Bilkisu kam waje ta koma da gudu tun Yarima bai ganta ba, Yarima ne da Lazeera suketa shagalinsu har sun fara barin duniyar da suke ciki sai yar karar da Fateema tayi ce ta dawo dasu hayya cin su, cikin kad`uwa da mamaki Lazeera tamike zumbur tazubawa Fatee ido taga yarinyar tayi fresh ta goge fuskarta fayau ba make-up amma hakan bai hanawa sihirtaccen kyawunta bayyana ba. Yarima kam kusan d`aukar abin yayi ba gaske ba dan a tunanin shi daga inda yabar ta bazai koma ganin ta ba. Dukkan su dai sunyi nisa
Fateema tayi murmushi ganin yanayin data jefa su a tashin farko. Lazeera ce ta daure ta kauda shirun cikin dakewa ta dakawa Fateema tsawa "ke jaka meki ka zo yimin a gida?" Wani irin juyi Fatee tayi da idonta tace gidan ki ko gida na? Ba Laxee kad`ai ba hatta Yarima sai da maganar ta girgiza shi, Lazeera kam zuciyar ta tagama rufewa me wannan yarinyar take nufi? Juyowar da zatayi sai ganin Fateema tayi zaune akan kujera ta d`ora kafa d`aya akan d`aya tana jijjigawa har Lazee ta d`aga baki zatayi magana sai Fateema ta tari numfashin ta da cewa "kinga malama idan kinada abin da kikazo da shi nan to kiyi gaggawar d`auka ki fice dan mai gidan ta dawo shi wanda ya aurekin bashida wani wajan da zai ajiyeki ne? Mintuna biyar su na baki ki tattara kibarmin gidana" ta karashe zancen cikeda gadara da rashin tsoro. Cikin d`aga murya Lazeera tace "kan uban can lallai yarinyar nan kin rainani wlh kuwa yanzu zakiyi laushi a gidan nan" ta daka tsalle tayi kan Fateema da nufin dukan ta sai a lokacin Yarima ya motsa da sauri yasha gaban Lazee yace haba my dear yanzu akan wannan yarinyar zaki wahalar min da jikin ki?, Noo ba sai ke ba barni da ita kawai
Ya juya ya fuskanci Fateema yace "ke me kikazo yi a nan d`in? Ko bakisan mata da miji ne suke rayuwa a nan ba? Bai jira amsar taba dan yasan batada abun cewar ya ci gaba "tashi ki kifita" ya fad`a yana nuna mata hanya banza tayi da shi kamar bada ita yake ba, taci gaba da jijjiga kafar ta "keee! Ba da ke nake magana ba" Ya daka mata tsawa saida ta razana a zuci amma bata yarda ta nuna a fuska ba Fahad ya gama cika da takaicin ta dan ya tsani a kawo masa raini a lamuran sa shima dai kanta ya nufa da nufin d`aukar ta ya wurgata waje Tsoro ne ya dirar mata taji kamar ta ruga waje kafin ya iso gareta amma inaaa zuciya ta dake ko gezau batayi ba, baifi taku uku ya rage ya isa gareta ba suka jiyo sallamar Sarkin gida a kofar falon
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•241/245•*
Wannan shafin kuma naki ne kawa ta gari abar fahari sis *AMA ALHAJI KABIR* U mean more than a friend to me, u are nown my sister. keep trying sis I believe one day our dream will be come true *INSHA ALLAH*
Tsayawa yayi cak ! Sannan ya juya ya nufi kofar ba tareda ya amsa sallamar ba. Daga inda suken suna jin naganganun da sukeyi shida Sarkin gida sako ne daga Mai martaba cewa yazo yanzu yana son ganin sa, ai kuwa kaitsaye yabi d`an aikar suka tafi tare. Nan akabar Fatee da Lazeera suna kallon kallo kafin Kazeerar taja dogon tsaki ta bar falon ta shige bedroom d`inta ta bankowa Fateen kofa, Fateema tabi bayanta da murmushi mai d`aukeda sakon zaki fito ne
Tana shiga ta d`auki wayar ta ta dannawa lambar hajiyar ta kira, ringing biyu a na uku aka d`aga wayar da "hello Doughter na" cikin shagwaba ta amsa "momy wai meke faruwa ne Fateema nagani a sashena wai hadda cemin infita in bata gidan ta, badai ta dawo gidan Fahad ba?" Momy tayi shiru na d`an lokaci sannan ta ce "ki kwantar da hankalin ki Fahad kam yanzu ai naki ne sai yanda kikayi dashi yanzu gayamin me ya faru?" Nan ta kwashe duk yanda akayi ta gaya mata. Tace to banda abinki inma dawowar tayi ke ina ruwanki tunda miji ake yiwa kishi kuma yana hannun ki kedai kawai ki dage ki cigaba da amfani da nagungunan da boka ya baki kinji" ta amsa da "to Momy Nah lov u bye!"
A d`akin Mai martaba kuma manyan mutane nan ne wayanda ya tara su daga farko dasu Baffa sai Fahad daya shigo daga baya ganin taron ya tuna mishi da abinda ya faru tsakanin shi da mahaifinshi d`azu take idonshi suka kawo ruwa ya nemi guri a d`an nesa da uban ya zauna hawaye nabin kuncin sa. Mai martaba yayi gyaran murya ya kira sunan Fahad ahankali Yarima ya d`ago idonshi tam da kwalla ya kalli Abban nashi tareda cewa "na'am Abba" Mai martaba yace "nasan bakasan dalilin kiran danayi maka ba" ya d`aga kai alamar "eh" yace "to na kiraka ne akan abinda ya faru na hukuncin dana yanke maka d`azu shine zan janye amma abisa wani sharad`i guda d`aya" da sauri Yarima ya d`ago kai bakinshi har rawa yake yace "nagode Abba kafad`i sharad`inka nayi alkawarin zanbi shi ko mene ne shi mutukar bai saba sharu'ar Allah ba" dattijan ya gyara zama sannan yace "to madalla auren ka zan mayar da Fateema wato matarka zata koma gidan ka bayan saki d`aya da kayi mata, kuma inaso kayimin alkawarin zaka rike yar'uwar ka amana zaka zauna da ita ba cuta ba cutarwa, kar ganin hakan yasa ka wulakanta min yarinya Yarima muddin ka tozarta Fatee babu ni babu kai har abada". Gabad`aya d`akin suka d`auka "subhanallah" Yarima cikin kuka yaja guiwa ya isa ga mahaifin nashi kayimin afwa ka gafarceni Abba na wlh bana son bata maka kasani fushinka akaina ba alkhairi bane, nayi alkawari zan rike amanar Fateema Abba xanyi iya ko'karina wajen yin hakan" yana kaiwa nan ya fashe da kuka Mai martaba ya shafi kansa yace Allah yai maka albarka tashi ka tafi. Yarima ya mike ya koma gun Baffa ya tsuguna bakinshi har rawa yake yace "kayi hakuri Baffa ka yafemin wlh har ga Allah ina son Fateema bansan meke damu na ba dazarar naganta sai inji na tsaneta Baffa ka taimake ni kar in komayin wani abinda Abba na zai tsane ni" ya koma fashewa da kuka Allah sarki gabad`aya tausayin sa suke ji, dakyar Baffa ya rarrashe shi da kalamai masu sanyaya rai tareda bashi wasu manyan addu'oi na neman tsari da kariyar Ubangiji (s.w.a) yace yaje yaji da matanshi duka biyun ya kasance mai adalci a agare su". Nan ma yayi godiya ya mike ya fita
Suka bishi da kallon tausayi Mai martaba ya kalli Liman yace "gafarta Malam yanzu kuma sauran aikin naka ne kaje ka d`ebi sauran Malaman dake fada kuyi karatu a sauke Alkur'ani mai girma a yanka dabbibi ayi sadaka a gayawa Allah damuwar nan na tabbata zai yaye mana Yarima zai sami kanshi" gaba d`aya suka amsa da "insha Allah" yace "to na sallame ku" suka tashi suka fita d`akin ya rage daga shi sai Baffa da Goggo da kuma Bashir nan suka shiga ja'jantawa juna da godewa Allah daya bayyana musu wannan da wuri daga bisani su Goggo suka koma masaukin su suka bar Mai martaba ya huta.
Yarima kuwa tafiya yake yana nazari yarasa inda tunanin sa ke zuwa idan yaga fateema gaba d`aya sai yaji ya tsane ta, idan ta kaucewa ganinsa kuwa ba abinda yake tunani sama da ita yasan yana mutukar Son Fateema amma idan yaganta sai tsanar ta ce take maye gurbin ti meye wannan? Ya tambayi kansa a lokacin da yake shia gidan nashi
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•246/250•*
*Wannan shafin kuma naku ne Ilahirin members na NASMAT NOVELS GROUP ina mika d`inbin godiyata gareku sakamakon so da kaunar da ku ke nunawa littafi na, haka ku ma KING BOY ISAH NOVELS bazan manta ku ba Allah yabar zumunci da kauna Allah ya Albarkaci rayuwarmu da ta yaran mu Ameen* đ
Kamar yanda yabar Fateema haka ya dawo ya same ta hard`e akan kujera. Da sauri ya kauda kanshi daga kallon nata, dan gujewa jin haushinta. Ita kam ko kallon gefen shi batayi ba saida ya shigeta sannan tabi bayan sa da kallo, sai taga yayi sanyi kalau ko a yanayin tafiyarshi ma mutum zai fahimci hakan. Kai tsaye d`akin baccin Lazeera ya nufa kwance ya same ta ta kifu kan gado tana ta faman aikin na ta wato chat. Jin shigowar tashi ne yasa ta tashi ta zauna tana kallon shi cikeda mamakin yanda yayi sanyi ga wani uban ja da idonshi sukayi wanda ya tabbatar mata da kuka yayi. Mikewa tayi ta taro shi tareda rungumo gefen jikin shi "Ya Prince lafiya kuwa? Ya naganka haka?" dakyar ya d`aga hannu ya shafi gefen fuskarta "bakomai dear Mai martaba ne ya kirani yace yana so...." Sai kuma yayi shiru sakamakon fad`uwar gaban daya riskeshi a lokacin da ta kafeshi da ido sai yaji yanajin nauyi da tsoron gaya mata ance ya maida Fateema
"meye yace wai?" Ta tambayeshi cikin d`aga murya, yayi shiru kanshi na sunkuye a kasa. ya Rabbi abinda yake nanatawa a ransa kenan baisan daliliba kawai tsintar kansa yayi da mugun tsoron bacin ran Lazeera. Kanshi na kasa yake gaya mata "kiyi hakuri ki had`o kananan kayanki zamu koma d`ayan part d`in can mubar mata wannan" Lazee ta zaro ido "mene?" "Inbar gidannan nan wai? hmmm ai bazai yuwu ba wlh bazata sabu ba wai bindiga a ruwa, kaje ka gaya mishi bazan fita ba nasan dai ba wanda zai ce haka sai shi to wlh bai isa ba..." Keee! Yarima ya katse ta da wata irin tsawa mai firgitarwa "mahaifin nawa ne bai isa ba?" ya tambayeta yana kallon cikin idon ta. Mamaki ne karara ya bayyana a fuskarta kodai asirin ya karye ne? Ta tambayi kanta sai kuma ta cije dan koma jarrabawa tace "eh shi d`in ko rama masa zakayi?" Yarima yaji kamar ya rufeta da duka amma ina azahiri rarrashinta ya hauyi da ban baki akan ta taimaka masa su barwa Fateema gidan, tare da alkawarin zai kara gyara mata wancan ita ma. Dakyar yasamu shawo kanta, da taimakon shi suka tattare duk wani abu dasuka zo dashi sannan ya fita yashigo da kuyangi biyar suka kwashe kayan suka fita, sannan su Yariman suka fito Lazee na gaba yana binta a baya d`auke da babbar jakar ta, ta wuce tana wurgawa Fateema kallon banza tanaji a ranta kamar ta rufe ta da duka, sosai tabawa Fateeman dariya, ta kuwa dara. sannan itama ta raka su da harara kafin ta make murya tace da yarensu na fulatanci ("kord`o reube") wato "bawan mata" da harshen hausa, a fusace ya juyo "me kika ce min?" Tace ni? Ta fad`a tana yatsina fuska bance komai ba. yanda tayi maganar ma abin kallo ne, ji yayi ta kara fusata shi ya dawo dabaya da nufin dukan ta, ta mike da gudu ta shige d`akin ta tana masa gwalo. ya tura kofar yaji a rufe gam sai kuma ya tsinci kansa dajin haushin hakan yaso ta tsaya yayita ganin ta koda yanajin haushin ta ne
Lazeera ce ta daka masa tsawa a fusace to wai meye hakan? Wasa ma zaka tsaya yi da ita? Yarima ya turbune fuska da me zan tsaya wasan? yaja tsaki sannan ya rufawa Lazee baya dan ita tuni tayi gaba zuciyar ta na mata zafi da tiriri. Wai an maida Fateema yanzu zaman kishi zasuyi kenan? ta tambayi kanta uhum tayi wani murmushi inaa wlh bazata sabu ba ta dai dawowa gida amma ba Yarima na ba. Da wannan tunanin suka isa d`ayan part d`in wanda yake kusan had`e da na Fateema suna fuskantar juna ginin duk iri d`aya ne komai da ke nan akwaishi a can banbancin d`aya ne na gyare-gyaren da akayiwa na Fateema kaman sabanta fenti da zuba sababbin furnitures da kayan kitchen.
Shine ya nemo wasu kuyangin suka gyare musu sashen tas! Akwai komai a ciki duk ba kowa a sashen hatta kayan abinci babu wanda babu sai dai ba wani dad`in ganin hakan yaji ba kasancewar gimbiyar tashi ba girki take ba a cewarta ba aikinta bane shi kuma Yarima baya iya cin abincin masu aiki sai dai su siyo su ci kullum suna hanyar restaurant abin na damun sa, haka dai aka gyare ko ina aka feshe da turaruka. Lazeera kam zaune take tamkar gumki ba um ba um'um hatta chatting d`inda ta mayar sana'a yau gagararta yayi duk abin duniya ya isheta, tunani take ta inda zata bullowa zaman ta da Fateema hanyoyin dazatabi ta killace Fahad take nema sai saka take tana warwarewa
Fateema kam tana shiga d`akin tashiga gyare-gyare dan a cewarta bazata kwanta akan dettin su ba, tana cikin yi Bilki tashigo tareda Rukayya su suka taya ta ta canza was bedsheets ta kwashe kayan make-up dake kan mirror ta zuba wasu sababbi nacikin kayan lefenta, kayan ta kam suna nan ba'a taba mata ko tsinke ba. Lokaci d`aya sashen ya d`auke da kamshi na had`ad`d`un turarukan wuta sannan ne tasami damar fad`awa bayi tayo wanka su Bilki suka can cara mata kwakliya taji da fad`a sannan suka bata wuri tasaka wata doguwar riga ta material wadda awayiwa zubin ado na stones kamar ba d`inkata akayiba
Wohoho wani irin kyau da sheki yadin ya kara mata hatta Rukayya da Bilki dasuka ganta saida suka kusan zaucewa gaskiya Fateema kyakkyawa ce ta gaban kwatance abinka da sabon jini kuruciyar ta gabad`aya ta bayyana a wannan kayan. Ta kalli kanta a nadubi tayi shiru a hakan na d`an lokaci kawai saiga hawaye suna bin kuncin ta,, cikin kad`uwa da mamaki yan'matan suka fara tambayar ta Rukayya tace "subhanallah anty Fatee lafiya kuwa, meyasa kike kuka?
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•251/252•*
Fateema taja numfashi sannan ta share hawayenta da bayan hannunta tajuyo da jyau ta fuskanci Bilkisu da Rukayya tace "kuka ya zame min dole Rukayya ki kalleni, ki kalli kyan da Allah ya bani wanda ni kaina nasan inadashi, ga farin jini, bazan iya kirga muku samarin da suka soni ba, amma sabida jarraba ta rayuwa ban taba jin son wani namiji samada wanda nakeyiwa *Yaya Fahad* ba tun daga kurciya har girma haka yayita bautarda zuciya ta yana azabtar da idanuwa na, babu wani zuwa dazaiyi kauyen mu batareda ya sakani kuka ba, tun ina karama ya tsane ni, ba abinda yakeso samada ganin hawaye na, ni kuma ganin fuskarshi kad`ai ya ishi zuciyata farin ciki mara misaltuwa, yau takai ta kawo nazama matar auren shi amma duk da haka baya yimin kallon mutum ballantana inkaiga darajar matar shi, taja numfashi tareda share kwalla a karo na biyu tace tunda nake sau d`aya na taba ganin sona a idon Yarima a ranar da nazo nan a matsayin matar shi tabbas na hangi soyayyata a idon shi wannan ranar sai kuma daga baya ta rikid`e ta dawo kiyayya da tsana irin wadda bai taba nunamin ba koda a shekarun baya, wannan ne dalilin daya sa nayarda da maganarki tacewa asiri akayi masa ya ki ni kuma ya tsane ni domin kafin rabuwarmu naga sauye-sauye dayawa a tattare da shi,"
Tayi shiru kamar mai nazarin wani abu su Rukayya kuwa jikinsu ne yayi sanyi lis maganganun Fateema sun ratsa su hakika soyayyar datakeyiwa Yarima ga'garuma ce kuma abar kwatance. Can ta d`ago ta kalle su tace "shin ku bakuyi mamakin amincewata ta dawowa gidan auren Yarima ba? " gabad`aya sukayi shiru. Tayi murmushi tace "hmmm nasan zakuyi mamakin hakan saidai sam ba abin mamaki bane idan kukayi la'akari da irin son da nakeyiwa d`an'uwa na, sai dai fa kusani inada babban kalubale a gaba na" a tare suka kalle ta cikeda mamakin jin kukanta na neman tsananta cikin kukan tace "wlh yanzu gaba d`aya rayuwa ta abar tausayi ce na sadaukar da farin cikina domin ceto na iyaye na, na sadaukar da rayuwata gayin abinda ko alama banida ilmi da sanin yinshi, ya ake zama da miji ma bansani ba balle takaini yin kishi kishin ma da gogaggiyar mace yar'bariki, maibin bokaye da malaman tsibbo nashiga uku ni fateema na sanya kaina a hallaka" ta fashe da kuka rairas tayita raira abinta dakyar yan'matan suka rarrasheta tayi shiru Bilkisu ce ta fara magana "kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki anty Fatee indai wannan ne nayi miki alkawari zan taimaka mki da akwai wata Hajiya a babban layi take aikinta kenan horarda mata akan zamantakewar aure musamman kanana kaman ke, tana koya musu girke-girke da make-up, sanin makamar namiji, tana gyaran jiki, mace ta goge ta iya kowane irin dressing Hajiya Binta bata tsaya nan kad`ai ba akwaita da sani na ilmin addini a wurinta zaki sami addu'oi da nafilfilin da zaki rike domin kare kanki da kuma ceto mijinki daga hannun waccan shaid`aniyar"
Cikin zumud`i Fateema "tace kai amma nagode Bilki a ina wannan Hajiyar take?" Bilkisu tace "a babban layi take nan bayan gidan sarauta saidai matsalar ita ce nan gidan ba'a fita kasafai haka sai dai na tabbata in akwai isassun kud`i Hajiya Binta zata iya zuwa har nan ta koyar dake komai. Fateema tayi shiru tareda kurawa Bilki ido kamar mai karanta wani abu a fuskar ta'ta, sannan ta nisa tace "to yanzu Bilki kamar nawa kike gani za'a bata kuma a ina zamu same su?" Bilkisu tayi shiru tana nazari kafin tace "wurin mijin ki za'ki samu mana, adadin su ne dai ban sani ba". Rukayya tace "kibari gobe idan mun fita zamu tambayo miki ita, kuma ma zamu karbo miki harda lambar wayar ta sai kuyi magana ko?" Fateema batasan sanda ta sake dariya ba tace "banda abinki Rakayya aini ban taba rike waya tawa ta kaina ba, sai dai tazo muje can mu same ta sai ayi maganar koya kuka gani?" Rukayya da Bilki suka kalli juna kafin suka fashe da dariya dukkan su Bilki tace "kai anty Fatee da abin dariya kike shin kin manta yanzu da da ba d`aya bane? Yanzu fa ke matar Aure ce "Rukayya ta cafe da "matar ma ta gudan Yariman gombe" suka koma saka dariya. Abinka da kurciya nan da nan suka manta da damuwar su suka bige da hire-hire, Fateema taji dad`in hakan sosai dan koba komai ta manta da damuwar Yarima. Haka Goggo tashigo ta same su sunata hira taji dad`i sosai da taga yarinyar tata bata saka damuwa a ranta ba, su Rukayya suka fice suka barta daga ita sai Goggo nan ne Goggo ta sami damar zaunar da Fateema tayi mata nasihohi masu shiga jiki tareda jan kunnen ta gameda kiriniya ta jaddada mata yanzufa tariga ta girma ba kaman da bane, harma ta tsorata ta da cewa "muddin ta fita bada sanin mijinta ba kafarta d`aya zatafi d`aya tsawo ta dawo d`ingishi" ai kuwa ta tsoratan dan harda kukan ta. Tace "to dan Allah Goggo ki rokamin shi yadinga barina idan na tambayeshin". Gogga tace "wannan ba matsala bane in Allah ya yarda zai barki" hakadai tayita lallabata har suka tashi tafiya. har wurin mota ta raka su tana makale da Goggo sukayi sallama harda kukanta, sai taji wani iri kamar ba gidan da tasaba zama ba
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•253/254•*
Da gudu ta juya tanufi bangaren su,Mai martaba yabi bayanta da kallo na tsayin lokaci kafin ya gyad`a kai ya koma sashen shi. Sosai take bashi tausayi na zaman da zatayi a gidan Fahad saboda tabbatarwa da akayi baya cikin hayyacin sa.
Fateema na shiga falon ta ta zube kan Capet ta shiga raira kuka mai ban tausayi, hakika ayanzu nikaina lamarinta ya fara bani tausayi. Tambayoyi ta shiga yiwa kanta a zuci "shin wane irin zama ne zatayi a gidan Fahad? Meye matsayin ta gareshi? Taya zata iya zama batareda fita ko'ina ba?" Sallamar su Bilkisu ce ta dawo da ita daga duniyar tunani-tunanin data tafi, a sanyaye ta amsa musu sallamar idanun ta sharaf da hawaye. wuri suka samu suka zazzauna shiru na d`an lokaci kafin Rukayya ta kauda shirun da cewa "Anty Fatee yanzu fa ba lokacin kuka bane, lokaci ne da zaki tashi tsaye da kafarki kiga kin kwaci mijin ki".
Fateema ta kalle ta cikin yanayin rashin fahimta "ban gane ba" ta bukaci karin bayani. Rukayya tayi murmushi domin sanin wace ce Fateema da tayi. tace "da sannu zaki gane" ta kalli Bilki ta kashe mata ido. Bilki ta mike ta shiga bayi na d`akin Fateema ba jimawa ta fito tana Fad`in "na had`a" Rukayya ta mike rike da hannun Fateema suka shiga d`akin kai tsaye bayi ta zarce da ita da shigar su wani dadda'd`an kamshi ya musu marhaba Fateema ta lumshe ido tareda bud`e hancin ta ta shaki kamshin mai matukar kwantar da hankalin wanda ya ji shi, ta sake mata hannu tareda cewa "kiyi wanka ki fito, muna jiranki". tana gama fad`ar hakan nan ta juya ta fice tareda ja mata kofar
Fateema ta since kaya ta shiga cikin bahon wankan ta kwanta shiru na wani lokaci mai tsawo dad`i da kamshin ruwan sun hanata tabuka komai, shiru kawai tayi kamar mai nazarin wani Abu. Karar bugun kofar ya farkar da ita daga nisan da tayi daga wannan duniyar wanda batasan abinda ya d`auke ta ba tsakanin bacci da tunani. muryar Rukayya ta ji tana fad`in Anty Fatee kiyi hanzari lokaci na tafiya.
Sauri-Sauri ta wawwatsa su tafito badan tana so ba. Sallar azahar suka fara gabatarwa suka ci abinci sannan suka zaunar da ita akan dressing mirror suka fara tsantsara mata kwalliya Masha Allah. Fuskar nan ta fentu tasha kyau harta gode Allah. Bilkisu ce ta fiddo mata wata koriyar riga doguwa asalin rigunan gidan Sarauta tareda mayafin ta suka ce ta saka, sannan suka fice falo suna jiran fitowar ta
Masha Allah wa tabarakallahu Ahsanal khalikeen! Bawai su Rukayya ba hatta ni Nasmy baki na sake ina kallon ikon Allah Fateema ce ta fito cikin koriyar rigar nan da Bilki ta fiddo mata tayi kyau tamkar yar'tsana kamar ba Fateen Goggo ba. Rukayya ta dafe hanci tareda rangad`a gud`a "gafara mahassada ga fitila, uwar gida sarautar mata, farar mace alkebbar mata, matar Yarima ikon Allah" gabad`aya suka kwashe da dariya. Yau ce rana ta farko da Fateema taji wani irin dad`i da aka kirata da matar Yarima! Ta zauna akan kujera tana kallon su tace "to ai sai ku gayamin dalilin wannan Uwar kwalliyar da kuka min?" Bilkisu tace "kina dai so ki sami kud`in da zamu biya mu d`auko Hajiya Binta ko?" Tace "eh" cikin zumud`i tana murmushi suma murmushin sukayi kafin Rukayya ta kama kunnen ta ta rad`a mata wani abu
Fateema ta d`ago fuska a raunane ta kalli Bilkisu dake gefe tace "anya zan iya kuwa?" Bilki ta d`aga mata kai "zaki iya mana"
Lokaci mai tsayi suka d`auka suna karfafa mata guiwa sannan ta mike tasaka wasu hills shoe da suka fiddo mata ta fice daga sashen tana rike bango Wai kar takalmin su yaddata. Kai tsaye sashen dake fuskantar nata ta nufa, kuyangin dake hidima a farfajiyar gidan sai zubewa suke suna kwasar gaisuwa
Da sallama ta shiga falon sai dai ba wanda ya amsa mata kasancewar falon shiru ba kowa. Bata jira komai ba ta nufi kofar da zata sadata da d`akin, shima dai tana murd`awa kofar ta bud`e idon ta fess akan su dai-dai lokacin da Lazeera ta doshi bakin Fahad da nufin sumbata tana kwance bisa kirjin shi akan gado. Wani uban ihu Fateema ta saki tayi tsalle ta hankad`e Lazeera daga kan Yarima tana rafka salati
Hatta Yarima sai da ya tsorata ya mike a razane yana kallon ta tareda mamakin abinda ya shigo da ita nan kuma. Fateema bata damu da halin daya shiga ba ita kam Lazee take kallo cikin ido cike da mamaki tace "lallai Anty Lazeera bakida imani yanzu saboda Allah da kika danneshi haka kashe shi kike so kiyi?"
Lazeera da ta gama kuluwa ta kalli Fahad dan ganin wane mataki zai d`auka akan Fateema? Ga mamakin kawai sai gani tayi yana murmushi
0 comments:
Post a Comment