"Kutumar uban can" Lazeera ta fad`a lokacin da tayi tsalle da nufin shako wuyan Fateema. Yarima ne yayi gaggawar shiga tsakanin su ya rike Lazeerar "meye haka? dukan ta zakiyi?" "Eh ko zaka rama mata ne?" ta fad`a a tsawance tana kallon shi cikin ido Fateema tace "he ai Wlh in gaya miki ba'a ramawa Fatee duka, da ya barki ki gani hmm" ta juya musu baya tana wani girgiza da karkad`a kafa (ni kuma Nasmy nace "yan iskan kauye sun motsa Liz)
Yarima yabi bayan ta da kallo yanajin wani Abu na yawo a ziciyar shi, sai ya tsinci kansa da sha'awar yadda take lamuranta cike da kurciya. Shi kanshi ya san tsanar da yake mata ta ragu a ransa. A hankali cikin sanyin nan nashi ya raba jikinshi dana Lazeera wadda keta faman huci tana jifan Fateema da mugun kallo, ya zaunar da ita bakin gadon ba tareda yace komai ba yaja hannun Fateema suka fice fallo
Tirkashi a wannan lokacin Lazeera ji tayi kamar numfashin ta zai yanke, zuciyar ta ta hau bugawa da matsanancin karfi. Fateema kuwa sai da suka kai kofa ta juyo ta dalla mata gwalo. Ta rumtse ido da karfi jitayi kamar an yanki naman jikin ta tabisu da kallon takaici na rashin abinyi ta san Yarima sarai ta kuma san halayen shi, dole ta zauna badan ran ta ya so ba.
A falon kuwa sai da ya zauna sannan ya saki hannun Fateema wanda yaji kamar yaci gaba da riki shi, kujerar dake daf da tashi ya nuna mata yace "zauna" ba musu ta zauna tana mai tilasta idon ta barin kallon Yarima ta maida su kan yatsun hannun ta da take murzawa, a ran ta kuwa sake-sake take da tunanin taya zata tambaye shi kud`i?. Yarima Fahad ya zuba mata ido yana mata wani kallo da shi kanshi baisan dame zai fassara shi ba shin so ne, ko sha'awa? Tayi mishi kyau sosai kamar su dawwama yana kallon ta. Zaman shirun yayi mata yawa "Yaya" ta kira sunan kaman mai ciwon baki, shiru bai amsa ba hakan yasa ta d`ago da nufin yi mishi magana karaf idonta suka had`e da nashi daya kafe ta dasu da sauri tayi kasa da nata zuciyar ta na zarya akan lamari na soyayyar *Yaya Fahad* cikin kankanin lokaci jikin ta ke fara shock idan ya tsareta da irin kallon nan take take rasa tunanin ta
Ginin girma zai fad`i yasa Yarima ya Kauda kan shi ga barin kallon ta. cikin kasaitar shi yace "kin ce gurina kika zo kuma kinmin shiru" Fateema tace "eh dama kasan ni ban iya komai bane na girke-girke da sauran abubuwa na nan, to shine su Bilki ke gaya min da akwai wata Hajiya mai koyarwa sai dai suka ce zata bukaci kud`i da yawa. Yanayin yadda take maganar ma abin kallo ne baice komai ba ya mike ya shiga bedroom d`inshi bai jima ba ya fito hannun shi rike da jakar hannu ta maza wato briefcase yazo ya zauna kan kujerar daya tashi ya bud`e jakar nan cike take makil da kud`i yan dubu-dubu layi-layi ya mayar da jakar ya rufe duk abinda yake tana kallon shi ta gefen ido
Bazato taga ya mika mata gaba d`aya jakar yace "gashi ki ajiye a hanun ki duk abinda kika bukata kiyi, idan suka kare kimin magana"
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•257/258•*
Fateema tabi jakar nan da kallo ido waje. Sannan ta d`ago ta kalle shi "Yaya meye zanyi da duk wannan kud`in?" Tana maganar tana zare ido hakan ya burge shi sosai yanayin yarantar ta na bala'in burgeshi, ya kuwa zuba mata ido yana murmushi, a ran shi yace "Wato ita a komai ma haka take" yace "Fateema ai ke yar'uwa tace ko ba komai ai kinfi karfin wannan kud`in a wurina" maganar shi ta shigeta ba karamin dad`i takejiba idan Fahad na magana. itama dai cikin sanyin jiki ta zame daga kujerar tazube kasa tace "na gode Yaya Allah ubangiji ya biya kuma ya saka da alkhairi..."
"Shiiiiii ya katse ta ta hanyar d`ora yatsa a baki "No Fateen Goggo" duka hannayen sa biyu yasaka ya tallafo kafad`un ta ya mikar da ita tsaye suka fuskanci junan su a lokacin da idon su suka had`u "huhhh!" Suka sauke wata nannauyar ajiyar zuciya a tare, cos dukkan su ba wanda baiji wani sabon al'amari ba ta dalilin kusanci da had`uwar da idon suka yi. Yarima ya kasa jurewa tunanin shi ya fara dawowa tsohuwar soyayyar Fateema ta motsa masa bai san lokacin da ya kaiwa bakin ta cafka ba ai kuwa yafara tsotsa da tand`a kamar wanda ya sami lollipop, Fateema kam sandarewa tayi a wurin tamkar busashshen itace.
Hakan yayi dai-dai da fitowar Lazeera cikin fushi janye da trolley a hannu da nufin barin gidan as tayi fushi zata gidan su. Ai kusan fad`uwa tayi a dalilin abinda idonta yaci karo dashi "Ya Prince" ta fad`a da karfi tareda kolalo duka idanuwan ta waje, da sauri Yarima ya saki Fateema ya maida kallon ahi ga Lazee wadda idon ta yake fess akan shi, kome tayi mishi sai kawai ya tsinci kanshi da fad`uwar gaba tareda jin nauyi da shakkar Lazeera. Fateema kam yana sakin ta ta suri jakar kud`in tayi waje da gudu. bawai dan jin tsoron Lazee ba a'a kawai ganin abin tayi kamar aafarki, tana tafiya tana tuno wani lokaci daya wuce a baya kamar dai haka daya faru yanzu yasha faruwa tsakanin ta da Yarima a babban lambun gidan inda suke zama da yamma a lokacin nan datayi zama gidan.
Lazeera kuwa matsanancin tashin hankali ne ya riske ta zuciyar ta kamar zata faso kirjin ta ta fito saboda tsananin bugun da take mata, "me ke shirin faruwa dani ne?" Ta tambayi kanta a fili "inaaa" ta fad`a cikin d`aga murya "this will never be" ta fisgi jakar tayi waje daga ita sai wata tsinanniyar riga doguwa ce amma ta d`ame ta sosai ba ko mayafi haka ta fice
Suka bar Yarima tsaye kamar wanda aka dasa shi a gurin, tunanin shi duk ya hargitse yarasa abinyi shikan shi ba zai iya gane abinda yake yiwa Lazeera ba shin So ne ko tsoro? Bakaramin d`aga mishi hankali tafiyar ta'ta tayi ba. Hannu yasaka ya shafi kanshi a hankali ya furzar da wani iska mai zafin gaske. Dakyar ya iya Jan kafa'fun shi ya shiga d`akin baccin shi da zuwa ya zube kan gadon cikin mutuwar jiki ya d`ora hannu akan goshin shi dake yimasa rad`ad`i ya lumshe ido abin uwa na masa yawo a kwakwalwa
Lazeera kuwa ikon Allah ne kad`ai ya kaita gidan su, saboda tukin gangancin datayi. Da isarta ko dai-daita parking batayi ba ta fita da gudu ta shiga gidan a babban falon kasa tayi kicibis da Umman Yarima zaune a kan kujera tayi zugum abin duniya duk ya ishe ta tun ranar da ta baro gidan Mai Martaba tasan asalin wace ce Yayar ta, dakan ta ta zauna ta fed`e mata biri har wutsiya akan muguwar manifar su akan tilon d`an ta Yarima da dukiyar gidan sarauta harma da ita kanta sarautar, ranar Umma tasha kuka har ta gode Allah ta kuma yi nadamar goyon bayan data basu suka asirce d`an ta, jitayi a ran ta inama da wata hanya dazatabi ta fad`akar da Iyaye masu hali irin na ta akan su gyara su nisanci duk wata hanya ta asiri da bin nakaman tsibbo domin babu wani alkhairi a cikin ta, hanyace mara billewa itakam tayi nadama yanzu adu'a take baji ba gani akan Allah ya ceto d`anta su kuma ya toni asirin su, tun ranar ita da Hajiya ba mai shiga sabgar wani kowa na bangaren shi ko had`uwa sukayi banda mugun kallo da harare-harare ba abinda keshiga tsakanin su
Wani mugun kallo Lazeey ta wurga ma Umma sannan ta haye up tiers tayi saman Umman ta tana kwalla mata kira
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•259/260•*
"Momy! Momy!! Mo....." Bata karasa na ukun ba dan ganin wadda take kwallawa kira d`in tsaye a gaban ta, a razane ta fito saboda jin muryar Lazeera da kuma irin kiran da take mata. Tana ganin Uwar ta wurgar da jakar hanun ta ta tafi da gudu ta rungume ta sannan ta fashe da kuka. "Ke lafiya meya same ki? Ina mijin naki yake?" Hajiyar ta ce mai yimata tambayoyin cikin kad`uwa ita kuwa sai ta kara tsananta kukan tareda kankame momyn "Umma na shiga uku yarinyar nan zata kwace min mij......." Da sauri ta kai hannun ta ga bakin Lazeey ta toshe ta hanata karasa maganar a hanzarce ta ja hannun ta suka kure Uwar d`akin ta.
Ta kalli yar zuciyar ta na harbawa tace "me kike so ki gaya min Lazeey?". Sai sa taja hanci tace "abinda kunnenki yajiye miki Momy wallahi asiri ya karye ya'Prince ya koma son Fateema" Umma ta koma kallon ta cikeda rashin yarda don tariga ta yarda da Bokan su, samada shekaru Goma suna mu'amala dashi ta harkar asirai amma ba'a taba samun matsala ba da zarar yayi musu aiki kamar yankan wuka haka suke cewa, to baremma wannan da ta tabbatar mishi yafi duk ayyukan da ya saba yimusu muhimmanci kuma ya gamsu harma ya tabbatar musu da babu wata hanya da Fahad zai koma had`uwa da Fateema saboda tsan-tsan tsana da kiyayyarta da akasa Aljanu suka dasa masa a cikin zuciyar shi
Tace " to wanne dalili kake dashi wanda ya tabbatar miki da haka?" Nan da nan Lazeey ta bayyane mata duk abinda ya faru tsakanin Fateema da Fahad a d`akin ta. Take jikin Momy yayi sanyi kalau tace "inko haka ne ai zama bai same must ba maza tashi muje mu gurin Boka" ta fad`a a lokacin da ta mike tana ciro mayafi a wardrobe. Lazeey ma mikewar tayi tabi bayanta suka fice
Zaune suke a gaban Bokan nasu sunyi shiru bayan sun gama koro mishi bayanin abinda ya faru, shi kanshi Bokan yayi mamakin jin maganar dan a yanayin aikin da yayi musu hatta inda Fahad yake Fateema bata isa ta kusanci gurin ba. Ba tareda ya ce musu komai ba ya bazama ga buga kasa da surkullen tsafin sa. Can kuma sai ya had`e fuska cikin sigar fushi ya fizgo wani d`an karamin shantu baki wulik yana rataye a jikin bangon d`akin ya dire shi gaban sa, ya shiga karanto wasu surkulle na d`alasimman tsafi. Nan da nan d`akin ya kaure da hayaki tareda kuka da kururuwar Aljanu take d`an shantun nan yai bindiga ya fashe ji kake d`uuuu- d`uuuu
Hajiya da Lazey suka shiga ihu da bankaura suna gwara kanun su, A gigice Bokan ya daka musu tsawa "Ku asararru marasa nasara maza ku tashi ku fice kafin in hallaka ku, mahaukatan banza kunje kun jangwalo mana masu riko da addini gashi kun saka tsananin addu'ar su ya illata min Aljanu gashi duk sun tarwatsa min fada ta. To kusani wayannan mutanen ayanzu sun riga sunfi karfin Ku babu wani asiri da zai iya tasiri akan su. Haka kuma duk wanda kuka shirya abaya yanzu ya la'lace kutashi Ku fita" yafad`a da wata iriyar murya mai rugugi da gudu suka fice suna had`a hanya
Boka kuwa cigaba yayi da sambatu yana cewa "kuje zaku sani na tabbatar idan kowa ya barku Aljani Auhal ba zai barku ba, wannan bakar azaba dayasha saboda aikin ku"
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•261/262•*
Abinda su Hajiyar basu saniba shine tun ranar da Mai Martaba ya gano al'amarin na asiri ne, sai yasaka kullum sai an sauke Alkur'ani mai girma tareda manyan addu'oi, sannan a yanka babban bujimi ayi sadaka kuma har yau ba'a daina ba. Addu'oi ake baji ba gani, ba dare ba rana. ana nemawa Yarima da Matar sa tsari da kariyar Allah akan duk wan sharri, na mutum ko Aljan.
Wannan kenan
Cikin su ba wadda ta kalli ko inda motar su take, da gudu suka nufi hanyar da zata sadasu da babban titi, suka tare napep suka shige. mota kam a gurin suka barta
Fateema na shiga sashenta su Rukayya suka mike dan tariyar ta da kuma son ganin ko tayi nasarar samo kud`in?, Sai da ta zauna sannan ta shiga maida numfashi dakyar kamar wadda tayi gudun kilomita biyar.
A hankali ta bud`e lumsasun idon ta, wani irin farin ciki takeji Mara misaltuwa, sabon yanayi, sabon Al'amari, mikewa tayi ta rungume Bilkisu cike da farin ciki tace "Allah ya biya wadda takawo wannan shawarar, da badan wadda ta kawo wannan shawarar ba da zaman nisanta da takatsantsan na shirya zanyi da yayana, saboda tunani na yana bani baya sona, amma a dalilin wannan zuwan da nayi gareshi na gano har yau akwai tsagwaron so da kauna ta a ransa. Tsabar tsoron da yakewa Anty Lazeera shi yake hanashi isarwa ko bayyanawa"
Bilki tayi murmushi tace "Alhamdulillah yanzu kinga kin kara samun kwarin guiwa na neman horo da gogewar da zaki iya gogayya da kowacce irin mace saboda mijinki"
Fateema tace "sosai ma kuwa" ta fad`a tana gyad`a kai, kyakkyawar fuskarta d`auke da murmushi. Rukayya tace "to kud`in fa, an samu?" Bata bata amsa ba ta mika musu jakar kud`in data shigo da ita. Suka kurawa jakar ido cike da mamaki Bilki ce takai hannu ta zuge zip d`in, ai suna d`agawa suka rud`e tare suka kalli Fateema baki na rawa Rukayya tace "A..Anty Fatee baki yayi ko d`aukowa kika yi?, Tayi mata wannan tambayar ne saboda dalilai guda biyu.
na farko saboda ganin yawan kud`in da ta yi, na biyu kuma saboda sanin halin kiriniyar Fateen da ta yi, ko a gaban shi zata iya d`auko su ta gudo muddin ta tambaya bai bata ba. Murmushi tayi musu kafin tace "Ku kwantar da hankalin Ku kukam Wlh da kanshi ya bani da hannun shi". Suka rike baki cike da mamaki suka ce amma ya akayi hakan? Hala dai Anty Lazeera bata gurin? Nan fa Fateema ta tintsire da datiya sai da tayi mai Isar ta sannan ta kwashe duk abinda ya faru ta gaya musu, amma bata gaya musu batu na kissing d`inta da Yarima yayi ba. A ganinta da kuma tunaninta wannan iskanci ne sai dai ba yadda ta iya tunda halin shi ne haka, saboda son da take masa zata dinga rufa masa asiri na duk tabin da zai yi mata.
A Sokoto kuwa hankalin Iyayen Fa'eez ne a matukar tashe. Tsayayyen soja jarumi, wanda tun lokacin kuruciya ya taso da jarumtakar sa juriya da zurfin ciki. Amma sai gashi saboda yarinya d`aya ya rasa duk wad`annan Abubuwan. Tun daga lokacin da ya kira wayar Yaya Bashir, ya tabbatar masa cewa Fateema fa ta koma ma mijinta Yarima. To tun daga nan aka rasa kan sa, ya shiga damuwa da rud`u sosai, ba shikad`ai ba hadda Iayaye da kannen shi kai da duk wani makusancin sa
Yanzu ma kamar kullum zaune kawai yake kan kujera a falon d`akin shi. Yayi zuruu ya zurawa fankar dake ta faman juyi Ido kamar mai nazarin wani Abu gameda fankar. Momyn shi ta shigo da sallamar ta fuskar ta ba walwala, idonta akan fuskar d`an nata wanda bai ma san da shigowarta d`akin ba. Momy ta girgiza kai a lokacin da take zama kusa da shi idon ta fall da hawaye zuciyar ta cike da tausayin babban d`an nata. Tasaka hannu ta dafa kafad`ar shi a sanyaye ya d`ago da jajayen idon shi ya kalli mai dafa shi, ganin Mahaifiyar shi ce sai Ya koma sunkuyar da kanshi ba tareda yace komai ba sai wasu zafafan hawaye dayaji suna bin kuncin sa. Momy ta rungume shi a lokacin da kuka ya subuce mata. Cikin kukan ta fara magana "a'a son ba zai yiwu ba, sam bazan barka ka kashe kanka saboda mace ba. Ya kamata ka dawo hayyacin ka son, ka zama cikakken musulmi ka yarda da kaddara kayi imani wani ba zai Auri matar wani ba ka yarda Fateema ba rabonka bace"
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•263/264•*
Fa'eez ya fashe da kuka ya kankame Momy cikin yanayin sadakarwa ya fara magana "na hakura Momy, Wlh na hakura pls kar ki koma yin kuka kinji?" Ya fad`a yana share mata hawayen fuskar ta. Momy kuwa dad`i ne ya tirnike ta jin hakan daga bakin sa, ta raba jikin ta da nashi sannan ta zaro wani photon Kati ta Mika mishi. Ya karba Yana kallon photon da alamun tambaya a fuskar shi.
Tayi murmushi sannan tace "Sameera ce fa, baka gane ta bane?" Ta tambaya tana kallon fuskar shi. Ya Kara kallon photon da kyau sannan yai murmuhi yace "haba Ina kallon fuskar kamar na Santa, yarinyar ta bace min da gani, mortharn 5years." tace "eh kasan tana landan course din likita, kwanan nan ta dawo yau satin ta daya a garin" shiru ya ratsa d'akin na d'an lokaci Sameera yar'kanwar momyn shi ce duk a sokoto suke, satin ta d'aya da dawowa daga London inda ta dawo a matsayin cikakkiyar likita. Ya sake kallon ta yace "to Momy photon fa" tace "na kawo ka duba ne kafin kaje ku gana, nida hajja mun yi shawara akan had'a ku aure kai da Sameera". Ta takaita maganar tana kallon shi domin ta ga wane irin karba yayiwa maganar?. Ga mamakin ta sai taga yayi murmushi Yana sake kallon photon yace "duk yanda kuka yi da mu yayi Momy na, Ina son Sameera and nasan itama zata soni Allah yayi mana jagora" cikeda farin ciki Momy ta rungume shi "na gode yarona nagode Allah ya yi maka albarka" ta sumbaci goshin shi ta fice zuciyar ta fall da farin ciki.
acikin satin aka shirya komai kasancewar duka su biyun sun amince, da sati ya zagayo kuma aka d'aura aure masha Allah ansha biki abin Sai wanda ya gani Auren Soja da likita, abin Dai gwanin sha'awa a cikin abinda baifi wata d'aya ba Fa'eez ya fara saituwa kasancewar Sameera wayayya Mai ilmin boko dana addini ta iya tafiyar da namiji, cikin kankanin lokaci ta goge tabon da soyayyar Fateema tayi a zuciyar shi ta maye gurbin da d'inbin kaunar ta tuni yayi watsi da soyayyar Fateema ya rungumi ta matar da Allah ya kadarta Ita ce rabon sa, ya yarda da kaddara kuma ya karbe ta hannu bibbiyu. Sai Dai ya kudirta a ransa zasu cigaba da zumunci da dangin Fateema.
*Garin Gombe* Yarima ne kwance bisa lafiyayyen gadon shi, Sai sheka bacci yake cikin kwanciyar hankali a zahiri amma a bad'ini mafarke-mafarke ne yake tayi akan zaman takewar shi da matan shi duk wani wulakanci da tozarcin da yayiwa Fateema sai da ya gansu. Bangare d'aya kuma bautar dashi da Lazy tayi ita da mahaifiyar ta da Umman shi, har ma da dawowar Fateema gidan shi Sai da yazo inda ya bata kud'in nan ta fita da gudu yai firgigit! Ya farka Yana fitar da numfashi Mai sauti "Innalillahi wa Inna Ilaihi raji'un" ya shiga Karantowa Yana waige-waige ba makawa tunnin Fahad ya dawo babu abinda bai tuna ba hatta fitar mahaifiyar shi daga gidan da kuma tafiyar Lazeera. Godiya ya yiwa Allah daya kasance ita Fateema tana gidan, da sauri ya mike ko brush baiyyiba ya nufi sashen Fateema. baiga kowa a falon ba, hakan ya bashi damar wucewa kaitsaye izuwa d'akin baccin ta.
Kwance ya sameta tayi share-share a kan gadon ta, baccin ta take cikin nutsuwa fuskar nan ta'ta kamar tana murmushi wani irin dad'i ne yaji Yana sakkowa tun daga ko'kon kansa har izuwa tafin kafar sa. Cikin gaggawa ya zube kasa a inda yake ya fuskanci alkibla yakai goshin shi kasa yai sujjada inda ya dinga kwararowa Allah (s.w.a) Yabo yana jinjina da kirari Yana Kiran sunayen sa tsarka'ka Yana gode mishi godiya marar adadi, ya rufe da salatin mazon Allah (s.a.w)
ya mike jikin shi har bari yake yi ya Isa gaban ta ya gurfane bisa guiwoyin sa ya zubawa kyakkyawar fuskar ta ido, a ransa Yana dad'a godewa Allah bisa wannan babban rabon da yayi masa na dawo mishi da Fateema wadda a kullam yakejin kanshi incomplete saboda rashin ta a kusa dashi Sai dai bashida damar tunawa ko kuma yin wani katabus na neman ta. ya d'an rankwafa fuskarshi ta dawo daf da ta'ta su na iya jin numfashin junan su Yana shirin Kai Mata sunbata tai firgigit ta farka daga baccin da take, ganin sa yasa tayi baya da sauri, nan fa suka shiga kallon-kallo da ita da shi.
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
265/266
Cikin in Ina tace "Yaya lafiya?" Ya kalle ta da wani irin kallo Mai d'auke da sakonnin da shi kanshi bai san adadin su ba, "barka da safiya My Princesses" ya fad'a da wata iriyar murya kamar mai yin rad'a. sai da ta d'an harare shi ta kasan ido sannan tace cikin karamar murya "yau kuma? Ko dai batan kai Yayana yayi yau?" maganar yarinyar ta ratsa shi, musamman da ya tuna irin zaman da ya yi da ita tun lokacin da ya aure ta. "a'a Fateen gwaggo, karki soma, pls kizama mai yafiya na roke ki." yayi folding hannayen shi yana kallon fuskar ta, Fateema tayi shiru tana kallon yanayin Prince. tabbas yayi laushi sosai alamu da yawa sun nuna da gaske yake yayi nadama sai dai a ganin ta ba cikin sauki haka ya kamata ta karbe shi ba, ya zama dole ya karbi hukunci. Duk da tana son Yarima hakan bazai hana ta ganar da shi yayi kuskure ba, duk kuwa da cewa ba a hayyacin shi ya aikata ba. Duk wannan dogon tunani da take *Yaya Fahad* yana nan gurfane a gaban ta, yayin da idon shi ya ciko tam da hawaye, yana jiran jin hukuncin da zata yanke masa. "pls Fateema" ya sake fad'a a mutukar sanyaye kamar mai shirin fashewa da kuka. tamkar wadda aka tsikara haka tayi tsalle daga kan gadon ta nufi kofa da gudu tana waiwayen sa. Yarima ya bita da kallon mamaki sam bai san lokacin da Fateema ta cika ta zama babbar budurwa haka ba, kayan bacci ne a jikin ta, rigar iya guiwa mai had'e da gajeren wando sun amshi jikin ta sosai fatar nan ta'ta tayi shar ga laushi ga alamun santsi kamar ta jinjirai tana gudu sassan jikin ta na motsawa tuni ta fice ta rufo mishi kofar amma idon shi na nan kyam akan kofar siffar ta da halittun jikin ta nayi masa yawo a kwakwalwa "huhhhh" ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jiki ba kwari ya mike ya ja kafa dakyar ya nufi d'akin shi dake cikin sashen nata, wanda rabonshi da ya shiga cikin sa tun lokacin da Lazeera tana bangaren. Amma ga mamakin sa sai ya tarar da d'akin fess da shi sai tashin kamshin kalolin tiraruka da yake yi, ya ja numfashi ya fitar cike da shauki. a ran shi yana tuna lokacin da Lazy take sashen, sam d'akin baya samun gyara haka. Ga wannan da ko shigo mata baya yi hakan baisa tayi wasa da gyara muhallin sa ba. "Allah ya albarkace ki Fateema" ya fad'a yana shafa kirjin shi wanda yake ji kamar a cikin sa Fateeman take. Ya nufi toilet zuciyar shi na dad'a yin nitso a soyayyar Fateema
ita kuwa tana fita daga d'akin ta shige d'aya d'akin ta saka key, ta shige toilet tayi wanka ta fito ta saka wata doguwar riga ash colour bata tsaya komai ba sai da ta fara gabatar da salla, sannan ta d'an gyara fuskar ta ta zaro wani karamin mayafi black ta d'ora ta fita kitchen dan sama ma cikin ta abinci. Ta samu an gama kammala komai suna ko'karin fita dasu zuwa danning ta tsayar dasu ta d'ebi iya abinda zata iya ci da drinks a babban tire ta nufi d'akin da take. Mintuna kad'an Yarima Fahad ya fito cikin shigarshi ta ya'yan sarakai fuskar nan tashi ba walwala ya nufi d'akin Fateema. Ganin bata d'akin yasa ya nufi d'aya d'akin da yake kyautata zaton can ta shiga da kuzarin sa ya tura kofar amma sai yaji ta a datse gam.
"Fateema" ya kira sunan ta a sanyaye hannun shi na rike da handle na kofar. "Fateema dan Allah kiyi hakuri ki saurare ni kinji, wlh nayi nadama Teema ina son ki, ina kaunar ki Fateema." ya saurara da maganar yana tunani ko zatayi magana amma shiru, ya kai mintuna goma tsaye a gurin amma ba ko alamar motsin Fateema. wadda yayi imanin cewa tana jin shi. Sosai yaso ya ganta amma ya zayyi? dole yaja sanyayyin kafafun sa ya fita ko breakfast bai tsaya yi ba ji kawai yayi yau ya tashi da matukar kewar mahaifiyar shi kuma kai tsaye gidan su ya nufa inda take. Umman tana zaune a falon kasa as usual hanunta rike da carbi tana ta yin lazimi, istigfari da hailala. sai ganin su tayi sun shigo a rikice ko sallama babu suka haye saman benen inda d'akunan baccin su suke. kallon mamaki ta bi bayan su dashi a ranta tana jinjina cewa duk abinda ya koro su haka mai girma ne, Wato Lazera da momyn ta. Tana cikin saka da warwara taji dukkanin su suna zunduma ihu sun nufo kasan a kid'ime, ta mike da nufin hawa saman domin ihun da suke bana wasa bane. a up tiers d'in suka had'u da har ta bud'i baki zata tambaye su lafiya suke wannan ihun haka? amma ina a bakinta kalmomin suka makale saboda ganin abinda ke faruwa a saman. gobara ce gagaruma ta taso wacce ta kama dukkan d'akunan bacci hud'u dake saman. rigegeniyar sakkowa sukayi dukkanin su a matukar tsorace suka nufi farfajiyar gidan suna kururuwar neman agaji direba da mai gadin gidan sune sukayi ta maza suka kira ofishin hukumar kashe gobara. domin duka matan ba wadda keda tunanin yin hakan Lazy da Momyn ta sai kuka suke suna ihun kiran duka dukiyar su ta kone domin wutar ci take tamkar ana bulbula mata fetir, haka tayi ta cin kayan dake d'akunan har zuwa lokacin da masu kashe wutar suka karaso, suka fara gudanar da aikin su an sami nasarar kashe gobarar ba tare da ta sakko kasan ba, sai dai a saman kam ta gama lashe komai ko tsinke bata rage musu ba. ganin hakan ya sanya Momyn Lazy kifewa a gurin tana borin hauka had'e da sambatu marar kan gado. A haka Yarima ya same su cirko-cirko a tsakiyar gidan kowa ya watse sai su kad'ai Momyn na ta zuba sambatu Lazy na ta faman kuka tana rarrashin ta Umma na daga gefe tana kallon ikon mabuwayi al'ajabin duniya ya cikata. shuru Yarima yayi daga inda yake yana sauraren maganganun dake fita daga bakin Momyn Lazy wayanda da yawan su duk akan cutar da sukayiwa shi Yariman da Fateema ne, Umma ma ido ta zuba mata domin wasu abubuwan bama da sanin ta ake yin su ba.
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
267/268
Jiki a sanyaye ya fito daga motar ya nufo inda suke, ganin shi ya basu mamaki dan ba wanda yasan da zuwan na shi.
Momy na ganin shi ta fisge jikin ta daga cikin na Lazeera ta isa gaban shi ta tsuguna bisa guiwoyin ta duka biyun tana shirin kama kafafun shi, ya d'an ja da baya yana mata kallo irin na tsana da ala'wadai.
Cikin kuka mai sauti ta fara magana "Fahad dan Allah kayi hakuri ka gafarce ni nayi kuskure d'ana wlh nayi nadama ka ceceni yace bazai barmu ba, gashi nan ya fara aibata ni ya saka min wuta a gaban idona ya kona min komai". Ta fashe da kuka mai tsanani "shikenan yanzu banida komai na rasa komai sai rayuwa, na shiga uku gashi yazo nan ma" ta fad'a tana nuna gefen ta da yatsa cikin yanayin tsoro, ta mike tsaye tana ihun wai ga aljanin nan yazo zai kashe ta tanayi tana neman mafaka. Lazeera ce tabi bayan ta cikin kuka ta riko ta tana lallabata, tun daga nan al'amarin ta ya dawo kamar hauka koda yaushe cikin sambatu take abu dai kamar ciwon hauka. Allah ya kyauta haka Fahad yace ya kad'e rigar shi ya isa ga mahaifiyar shi wadda tsananin kunyar shi da dana sanin abinda ta aikata suka lullube ta, ta kasa motsawa daga inda take. hawaye na bin kumatun ta tausayin kan ta ya kara kamata lokacin da ta koma kallon inda yayar ta'ta take, a ran ta tace yanzu da ita ce a wannan matsayin ya zata yi?,
godiya tayiwa Allah daya ceto ta kuma ya kare ta daga sharrin su. A fili tace "ya Allah ka kutubar da matan musulmi da suka raja'a da bin bokaye da malaman tsibbo, Allah ka ganar da su sudawo bisa hanyar gaskiya, haki'ka duk wani abin da zaka nema agurin wanin da ba Allah ba to kuskure ne babba" wannan gaskiya ne (Muyi tunani mai zurfi mu dawo hayyacin mu mata, Allah (s.w.a) shine yafi can-canta da mu kai kukan mu gareshi a duk lokacin da muke da bukata mu sanar mishi, mu roke shi shine mai bayarwa, kuma shine mai hanawa. Kisani yake yar'uwa mace zuwa wajen wani boka ko malami neman wata bukata la'lata imani ne. Kuma koman daren dad'ewa karshen ta bazai zamo mai kyau a gareki ba. Allah ya ganar damu baki d'aya). Taku uku Yarima ya kara ya isa gaban Umman shi wadda ta sunkuyar da kanta kasa saboda kunyar abin. "Umma" ya kira ta cikin sanyaya murya sannan ya tsuguna a gaban ta, daga aljihun shi ya ciro wani lallausan handkacip fari mai kamshi ya fara share mata hawayen dake fuskar ta zuciyar shi fall da farin ciki domin hakan ya tabbatar mishi cewa Umman shi ta saduda. Kuka ne mai karfi ya kwace mata ta rungume d'an nata, "Son dan Allah kayafe min kai da Fateema kuyi min aikin gafara wlh son nayi nadama, ka yafe min kaji d'ana" Yarima ya d'ago ta yana kara share mata hawaye yace "babu wani abu a rai na Umma wlh na yafe miki, kuma su d'in ma na yafe musu nasan Fateema ma zata yafe musu. Ina sonki Umma na pls karki koma yin nisa dani kinji"
maganganun nashi sun kashe mata jiki sosai domin duk yadda take son zama dasu dole ta hakura tunda Mai martaba ya saketa kuma ya kore ta. ta koma fashewa da wani kukan ta kankame shi "a'a d'ana bazan maka wannan alkawarin ba tunda Abban ka ya koreni daga gidan sa ba yanda na iya, sai dai ka dinga kawomin ziyara kuma dan Allah ka nemamin gafarar Fateema da Abban ka kaji." "ki daina kuka hakan nan Umma pls banajin dad'in shi, Mai martaba ya koreki a lokacin da kike cikin kuskure, yanzu kuma kin gane gaskiya na tabbata zai karbe ki" ya fad'a yana kama hahhun ta suka mike tsaye tare. da kanshi ya gyara mata mayafin ta basubi ta kan komai ba ya sakata mota shima ya zaga ya shiga ya mata key suka fice daga gidan suka nufi gida
misalin karfe biyar na yammacin Hajiya Binta mai gyaran jiki ta amsa kiran da Fateema ta aika mata dashi. Sai da ta jira akayi mata iso sannan wasu kuyangi suka shigar da ita babban falon baki dake sashen bayan kamar mintuna biyu da zaman ta Gimbiyar ta fito "Masha Allah" inji hajiya Binta kasancewar basu da wani nisa tsakanin gidan ta da gidan sarauta yasa taji labarin had'uwa da kyawun matar Yarima a wurin matan dake zuwa gidanta koyon abubuwa amma sam bata d'auka kyan yarinyar da kuruciyar ta sunkai haka ba.
Ta d'auka zatayi jiji da kai sai kuma taga ba haka bane. Cikin saukin kai da sakin jiki Fateema tayi mata bayanin duk abubuwan da take so ta koya daga gareta. Hajya Binta ta gamsu harma ta karawa Fateen wasu na daban wayanda suma sunada muhimmanci sosai gare ta sun dai-daita maganar kud'i harma sun saka lokacin da zata dinga zuwa (sis hours) zata dinga yi a gidan tana koyar da ita abubuwan, sai dai tace zata na d'an leka gida lokaci lokaci saboda yara
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍.
*269/270*
Karfe goma da rabi Yarima ya shigo gidan sarautar d'auke da mahaifiyar shi Umma, wadda take ta d'ari-d'ari da shi tunda ta shigo motar batayi magana ba Sai ma shi da yake yi Mata magana jifa-jifa. Kai tsaye sashen ta suka nufa tana gaba Yana binta a baya, kuyangi da ma'aikatan gidan Sai zubewa suke yi suna gaishe su, idan suka wuce Sai abi bayan su da kallo masu masaniya akan barinta gidan su fara kus-kus-kus haka Dai suka ratsa sassan har suka Isa bangaren ta.
Jakadiya na ganin ta ta rangad'a gud'a ta shiga antayo Mata kirari da yabo tare da nuna farin cikin dawowar ta. Yanayin da take ciki yasa bata tsaya ta kanta ba, ta wuce uwar d'akin ta. Fahad yabi bayan ta, Sai da ya tabbatar ta zauna sannan ya fice ya nufi sashen mahaifin shi kasancewar time d'in fita fada bayyi ba.
Bai tsaya wani boyo ko noke-noke ba Kai tsaye ya sanar da Abban shi komai dangane da mafarkin da yayi, da kuma abinda ya faru a gidan su Lazeeran Sai kuma farin cikin shi daya bayyana wa Abban nashi akan dawowar Fateema gare shi ya tabbatar masa duka aikin asiri ne. yanzu ya dawo hayyacin sa kuma yana son matar sa. Mai martaba yaji dad'in al'amarin sosai har ya dinga sakawa d'an nashi albarka tare da addu'ar Allah ya kare gaba. Daga karshe Yarima ya rufe da rokawa mahaifiyar shi gafara ya sanar da shi cewa ya dawo da ita, kuma tariga tayi nadamar abinda tayi a baya, Yana da tabbacin bazata koma aikata maka mancin sa ba. Tunani mai zurfi dattijan yayi kafin ya d'ago yace na maidata Yarima taci albarkar ka Ina Mata fatan sabuwar rayuwa Mai kunshe da alhairai nan gaba. Yarima yaji dad'in hakan har cikin ran sa bai bar uban ba saida ya tasa keyar sa har sashen Umma suna tafe suna hira cikin raha da walwala ya dad'e rabon da ya rabi mahaifin nashi haka, haka shima Uban ya kyale shi ne kawai amma yaron Yana ran sa Sai yazamana dukkan su suna cikin farin ciki da wannan zaman nasu na yau. Umma kam da tayi ido biyu da Mai martaba Sai ta diririce kunya da takaicin aikin ta na baya suka baibaye ta. Amma dayake mijin nata wayayyen mutum ne Sai ya basar yayi Mata magana kamar wani Abu bai faru ba.
Haka Yarima ya barsu suna gaisawa bayan fitar d'an ne yayi Mata nasihohi masu karfi da sanyayar da jiki, Umma kam Sai kuka take tana rokon gafara kuma tace ya saka musu rana suje garin kukunba ta roko gafarar Baffa da Gwaggo. Yace wannan ba komai zasu je nan bada jimawa ba.
Zuciyar shi fari kall ya nufi gidan shi sashen Fateema da shigar shi sashen kamshi yayi mishi marhaba, da alama Ana had'a wani delicious ne inji zuciyar shi. Sai a lokacin ya tuna ko breakfast bayyi ba. Da sand'a ya nufi kitchen d'in kamar wani barawo domin yasan Fateema tana da masu aiki Yana so ya gani ne ita ce a kitchen d'in ko ma'aikatan gidan ne Dan magana ta gaskiya Yana so yaga matar shi kewar ta yake ji sosai. A d'an koridon hanyar kitchen d'in ya make Yana lekawa abin mamaki Sai yaga Fateema da wata mace suna shirya girke-girke ga dukkan alamu matar tana koyar da ita ne, farin ciki ya ziyarci zuciyar shi dad'i ya lullube shi. Ya dad'e tsaye a wurin domin kallon da yake mata yana faranta masa, gani yayi sun kammala komai suna shirin fitowa da sauri yabar wajan ya shige d'akin sa. Hajya Binta ta taimaka mata wajan jere kayan akan table wanda shima duk cikin horon ne, daga nan suka wuce d'akin ta inda ta saka ta shiga wanka da wani had'in turaruka na wanka wanda ta bawa Fateen ta had'a da kanta. Tana jin dad'in koyar da yarinyar abubuwa domin tanada brain, da sauri take haddace abu. gaban mirror ta zaunar da ita bayan fitowar ta daga wankan inda ta koya mata yadda ake amfani da hand drayer ta busar mata da gashin kanta mai tsayi da laushi sannan ta nuna mata irin kalolon mayukan da zata dinga amfani dasu a kan nata. daga nan sai aka zarce sashen make-up inda take nuna mata yadda zatayi tanayi da kanta kafin kace me fuskar nan ta d'auki sheki da walwali ga sihirtaccin turaruka sai zuba kamshi take. Suka koma gefen saka kaya nan fa tashiga nunawa Fateema had'in colours na kaya da mayafai, takalmi da jakunkuna ko wanne kalar kaya da kalar mayafi da takalmi da jakar da ta dace da shi. Tana kuwa d'aukar darasin sosai komai yana shiga kanta yadda ya kamata.
Doguwar riga ta saka ta wani tsadadde material mara nauyi rigar ta amshe ta matuka tun daga kalar ta data kasance marum ta d'aura mata d'ankwali na wani yadi mai kyan gaske porpul plat shoe ta saka suma porple ta manna mata d'aya daga cikin sarko'kin ta na zinari had'e da yan'kunne da warwaro cikin abinda baifi 30 minutes ba Fateema ta dawo asalin sunanta na tauraruwa (Zara) kyawun ta ya kara bayyana ita kanta Hajya Binta sai da ta bata snap, sannan tayi mata sallama ta tafi har kofar shigowa bangaren ta rakata tana ta yi mata godiya ta tafi. Juyowar da zata yi ne kawai sai ji tayi tayi karo da mutum tayi baya da sauri idonta a kan wanda tayi karon da shi Yarima ne ga dukkan alamu binta yake a baya. Ta tsuke fuska sannan tayi gefe zata raba shi ta wuce wani irin kamshi ya daki hancin sa, sai da ya lumshe ido, baisan lokacin da ya kai mata cafka ba ya kuwa rungumeta tsam a kirjin sa yana sauke numfashi tamkar wanda yayi gudun kilomita biyar. ta shiga kiciniyar kwacewa
"Yaya Fahad Allah ka sake ni bana So" ta fad'a tana cinno baki yayi murmushi *i miss you* Fateen gwaggo ya rad'a mata a kunne sai da tayi jim idon ta suka lumshe saboda wani bakon al'amari da taji a jikin ta. bai tsaya nan ba wuyanta ya shiga shaka yana shinshinar ta kamar tsohon maye, ya zagaye ta da hannayen shi ya mata kyakkyawar runguma ta mintuna biyar sai yaji kamar ruhin shi yana dawowa jikin shi wata irin nutsuwa yaji wadda rabon shi da jin makamanciyar ta tun lokacin da yake rabuwa da jikin Fateema. Ya koma sauke numfashi sannan yace "Alhamdulillah" sai z lokacin ya sake ta amma hannun ta yana rike da nashi yaja ta zuwa danning inda yaga an shirya abinci ba musu Fateema ta bi shi suka zauna da kanshi ya zuzzuba musu abincin ya zauna da spon d'aya ya ciyar da kanshi da kuma ita sam bata ki ba taci abincin sai da taji ta koshi sannan ta danne da drinks. Yarima Fahad kam ya raja'a da kallon kanwar shi kuma kyakkyawar matar shi Fateema wadda baya taba gajiya da kallon fuskar ta wani irin fari tayi mishi da ido baisan lokacin da ilahirin gabobin jikin sa suka saki ba kasala da mutuwar jikin suka dirar mishi lokaci d'aya yaji ya kwad'aitu da matar sa kuma abar kaunar sa Fateema sai dai kafin yayi wani yunkuri tuni ta raba jikin ta da nashi ta ruga aguje takai kofar d'akin ta sai a lokacin kuzarin sa ya dawo "Fateema" ya kira sunan ta da sauri murmushin mugunta ta sake mishi sanna ta shige d'akin ta ta leko kanta ta dalla masa gwalo tana dariya "a'a Fateema kar kimin haka pls" ya mike ya nufota da sauri ta datse kofar tamurza key ta barshi a jiki Allah sarki Fahad kuka ne kawai bayyi mata ba amma yayi magiyar duniyar nan taki ta bud'e d'akin dole ya hakura ya kwashi kanshi ya koma d'akin shi ya kife kan gado. Ya dinga matse filo yayin da zuciyar shi ke dad'a afkawa cikin kwad'ayi da sha'awar Fateema. Ita kam tsalle tayi ta haye gado aranta tana cewa "kad'an ma ka gani tukunna ai har marin da kayi min a rafin kukunba sai na rama wlh" ta kece da dariyar nan tata ta shed'anci (niko Nasmy nace anya Fateema bazaki tausayawa Fahad ba) to haka dai rayuwar gidan ta d'ore musu kullum cikin abu d'aya fiye da wata d'aya ya kasa samun Fateema, sai yaga kamar ya kama sai tayi escape. Umma ta roki gafarar ta kuma ta yafe mata yanzu zaman mutunci suke yi da mutunta juna Umma tanajin dad'in Fateema sosai sai yanzu ta fahimci yarinyar tana da kirki kusan kullum sai ta jewa Umma hurar dare wani lokacin hadda Yarima wanda idan suka had'u suna hira ba wanda zai ce da akwai wata damuwa a tsakanin su. Fateema ta kara gogewa ta zama wayayyar mace kimanin watanni biyu kenan tana d'aukar horo a gurin Hajya Binta yanzu ma har ta daina zuwa saboda d'alibar ta'ta ta zama malama ta gama kwarewa ta kowanne fanni tazama tauraruwa a gidan sarautar kuyangi da bayi da ma'aikatan gidan sunajin dad'in ta sosai. Mai martaba na ji da ita kusan fiye da kowa a gidan. Sai da ya tabbatar zaman su yayi dad'i komai ya dai-daita a yau yace musu su zama cikin shiri gobe zasu tafi kukunba, dukkan su sunji dad'in maganar tafiyar amma basu kai Fateema ba wadda tayi kewar gidan su matuka tunda tazo gidan bata koma ba haka suma tunda suka zo sau d'ayan nan suka tafi ba wanda ya dawo sai dai sukanyi waya kodayaushe kasancewar itama yanzu tayi wayar kanta farin ciki ne zallar sa a ranta yau sai rawar kai take ji take kamar anbata kyautar zuwa hajji hatta Fahad yau ya shaidi hakan domin da suka koma bangaren su tsalle tayi ta d'ane bayan shi tana ihun murna Yarima kam ji yayi kamar su dawwama a hakan bisa kuhera ya sauke ta tanata dariya shiko sai kallon fuskar ta yake baki a sake bakaramin kyau dariyar take kara mata ba sai da tayi mai isarta sannan ta tsagaita ta kalke shi "Yaya Fahad, kaima kanajin yanda nake ji ko?" "eh" yace yana kare mata kallo baisan yaushe Fateema zata daina yaranta ba. "Nasan yau kina cikin farin ciki, Fateema dan Allah ki tsaya mu fahimci juna kinada iliminki dai-dai gwargwado shin bakisan akwai hakki na a kan ki ba?" kasa tayi da kanta tana wasa da yatsun hannun ta hakika wasu lokuta Yayan nata yana bata tausayi. Ita kanta daurewa kawai take yi amma tanajin dad'in zama a kusa dash. A ranta tace ya kamata ta tausayawa mijin ta abinda takeyi sam bai dace ba ta d'ago ta kalle shi "kayi hakuri Yaya na insha Allah ya wuce zamu zauna kamar yanda kake so amma fa sai ka cikamin burika na guda biyu tareda bani amsar tambaya d'aya" da sauri ya d'ago ya kalleta
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*271/272*
"Meye wad'annan burikan naki Fateema? Wlh zan cika miki su, mece ce tambayar ki? Fateema zan amsa miki" bakin shi har ruwa yake idanun shi a kan ta. tayi murmushi "da fari dai kaga ina son cigaba da karatu, zaka nema min admission ka barni in cigaba" ta tsagaita tana kallon fuskar shi. Murmshi yayi mata sannan ya kai hannun shi ya shafi gefen fuskar ta yace "amma inaga ai kin san dokar ko Fateema?" Kin sani sarai ba'a irin wannan fice-ficen a gidan sarautar nan" Fateema ta bata fuska tana shirin mikewa tsaye yayi saurin rikota ya zaunar da ita "ina son ki Fateema, zan iya yin komai saboda faranta ranki, amma me kike So ki karanta?" sai a lokacin ta saki fuskar ta "ina da muradin na zama likita ne abinda zan karanta kenan, dan Allah Yaya ka taimaka min kaji?" Janyo ta yayi saida ta mannu da kirjin sa yace " I'll do anything for your happiness Teema na, zakiyi karatu amma fa kisani ba dai a gombe ba dole sai in kin lamunta mubar kasar nan da sunan zanyi wani cours kinga sai kiyi karatun ki cikin kwanciyar hankali ko" batasan lokacin da tayi mishi kyakkyawar runguma ba. "Thats my yaya" ta fad'a lokacin da ta kwantar da kanta bisa kirjin sa, shi kuma sai yaji kansa kamar bai taba rungumar wata macen ba sai ita kad'ai. Sbd dad'i da sanyin da yaji a rayuwar sa. Ya d'ago fuskar ta yana fad'in "naji bukatar ki ta farko Fateema, mene ne na biyun?"
ita kanta sai da abinda yake ranta ya sakata dariya kafin ta koma d'aure fuska tace "gobe zamuje kukunba, ko zaka iya tuna marin da kayi min a hanyar mu ta dawowa daga rafi?" Yarima yai shiru yana tunani can ya d'ago yace "eh na tuna, lokacin da kika ce kina sona ko?" Ya tambaye ta yana sosa kyeya cike da jin nauyin abin. tayi murmushi "to shi zan rama, kuma a dai-dai inda kayi min a can zan rama" ya zuba mata ido cike da mamakin ta a zatan shi wasa take, amma a fuskar ta sam bai ga alamar wasar ba. hannu ya saka ya tallafo kumatun ta suka fuskanci juna "Fateema, da gaske kike zaki iya marin Yayan ki?" Cike da yaran ta tace "eh ai kai ne ka fara Allah yaya sai na rama" ta karashe maganar cike da shagwaba "to naji na yarda zaki rama, meye abu na ukun?" "uhum dama zan tambaye ka ne akan anty Lazeera ance min ta tafi, shin meye gaskiyar maganar?" Shiru sukayi duka na yan mintuna kafin ya fara magana, ya kwashe duk abinda ya faru ya sanar mata, daga karshe yake shaida mata ya riga yasake ta saki d'aya, kuma shi da wata macen ma hayatan-hayatan har Ă bada yana kallon fuskar ta yace "in dai har kika yarda dani kika So ni Fateema to zan zama naki ke kadai har karshen rayuwa, wallahi yanzu ina son ki Fateema fiye da wanda kike yimin dan Allah ki yarda dani ki daure ki karbe ni amatsayin mijin auren ki" ya fad'a lokacin da ya zame daga kujerar ya tsuguna a gaban ta. Tausayin Yarima da mamakin rayuwa suka kama Fateema
Wai yau ita ce *Yaya Fahad* yake bibiyar ta yana barar soyayyar ta, Allah sarki rayuwa ba shakka maganar magabata gaskiya ce (mahakurci mawadaci ne wata rana) zuwa yanzu Fateema tariga da ta goge da ilmi na soyayya da sanin makamar namiji. hannayen ta duka biyun ta mika mishi ya rika su cike da farin ciki ta jashi izuwa kan kujerar daf da ita ya zauna idanuwan shi akan fuskar ta. murmushinnan nata ta koma yi mishi hannayen ta na rike a cikin nashi idon su na sarke suna yiwa junan su wani kallo tace "Yaya Fahad a yau kuma a wannan ranar nake yimaka albishir cewa duk wani shirme ya kare, ni Fateema har yau ina son ka kuma zan ci gaba da son ka har izuwa karshen numfashi na, ina son ka yaya na" ta karashe zancen da lumshe ido hawaye suka gangaro daga idon nata da sauri Yarima Fahad yakai harshen sa kan kumatun ta ya lashe hawayen nan tas batare da yabari ko d'aya ya sauka a kasa ba.
"Na gode miki Fateema, na kuma godewa Allah daya nuna min wannan rana. Allah ya albarkaci rayuwar mu kuma ya bamu zuriya ta gari". Fateema kam har zuwa lokacin idon ta rufe suke gam tana jin kanta Kamar yau ta fara rayuwa a duniya. hakan ya bawa Yarima damar manna bakinshi a nata yana tsutsar leben ta ahankali ji yake kamar yana shan wata madara wadda bai taba jin mai d'and'anon ta ba lokaci mai tsayi suka d'auka a hakan kafin ya d'auketa cancas ya shige d'akin shi da ita. Suka zube kan lafiyayyen gadon shi Yarima ya shiga wasanni da sassan jikin Fateema wadda ta kwanta lif ajikin na shi ko motsin kirki batayi sam bata hanashi abinda yake yi ba sai ma ta tsinci kanta da jin dad'in yanayin da suke cikin
A kunnen ta ya dinga rad'a mata wasu dad'ad'an kalamai na soyayya wayanda ko a mafarki bata taba kawowa zataji su daga bakin Yaya Fahad ba, hakan ya zaburar da ita batasan lokacinda ta shiga mayar mishi da martanin kalaman nashi ba a ranar dai haka suka kwana cikin farin ciki da faran tawa juna, duk da cewa babu wani abu daya shiga tsakanin su amma fa sun shayar da junan su madarar So da kauna washe gari da safe haka suka tashi cikin fari ciki sai tarairayar junan su suke abin dai gwanin birgewa. haka sukayi shirin zuwa kukunba karfe goma na safiyar Mai martaba ya aiko yace su fito Masha Allah haka kowa yake cewa lokacinda suka ratsa tsakar gidan sarautar Yarima da Gimbiyar shi sun sha kyau kamar yau suka fara yin ado da kayan sarauta. Suka shiga sashen iyayen nasu inda suka tarar da Mai martaba da Umma cikin shiri da ado na kasaita. Suka zube suka gaida iyayen suka amsa cikin farin ciki suka sakawa yaran albarka sannan suka mike suka shige gaba yaran na take musu baya suka nufi farfajiyar gidan inda motoci suke a fake an riga an gama shirya komai.
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*273/274*
Masha Allah abinda kowane bafade ke fad'a kenan tun bayan auren Yarima basu taba fita irin wannan ba. kana'nan motoci guda biyar ne aka shirya domin tafiyar. d'aya ta Yarima da Matar shi, d'aya kuma ta Mai martaba da Umma. Ukun kuma na security da fadawa ne sannan aka tanadi hillous guda biyu wayanda aka cika su da kayan tsaraba tun daga kan kayan abinci har izuwa kayan sakawa turamen zannuwa da shaddodi da yaduka. bayan duka sun shiga motocin aka tayar suka fara tafiya. Fateema ta kalli mijin ta wanda tunda suka shiga motar bai d'auke idon shi daga kallon ta ba. "to kallon fa?" Ta fad'a Tana kallon shi, Yarima Fahad ya saki lallausan murmushin nan nashi tsadadde ya janyo Fateema zuwa jikin shi yai mata kyakkyawan mazauni a kirjin shi. "Ina kaunar ki Fateema, dan Allah ki daure kiyimin matsuguni a zuciyar ki, ki so ni Fateema, dan Allah ki kaunace ni." mamaki ya cika Fateema jin saukar hawayen Yarima bisa kumatun ta. da sauri ta tashi ta zauna da kyau Tana kallon shi tabbas kuka yake Innalillahi.
Hannayen ta ta saka ta tallafe kumatun sa "Haba Yaya na, meyasa zaka yimin asarar hawayen ka akan abinda kake da tabbacin ka samu? Yaya, na so ka tun bansan miye so ba, na kaunace ka tun bansan kaina ba, to meyasa zan ki ka yanzu da na mallaki hankali na? na tabbatar zuciya ta bazata taba aikata wannan kuskuren ba" ta rungume mijin ta Tana share mishi hawaye dad'i da farin ciki suka lullube Yarima "cikin farin ciki yace "na gode Fateema nayi miki alkawarin zama bawa gare ki a wannan rayuwar, na zama rakumi kuma na hannunta miki akalar Fateema *ni naki ne* , ki taimake ni ki cigaba da kasancewa kusa dani kamar haka. dan Allah kar ki koma yin nisa dani kinji" "bazan koma barinka ba *Yaya Fahad* Ina son ka" suka koma rungume juna kowannen su najin dad'in sabuwar rayuwa da sabon yanayi na kusanci da suka tsinci kan su a ciki dai-dai nan suka ji motar ta tsaya ya d'aga ta daga jikin shi sannan ya karbi jakar ta ya ciro bandir-bandir na kud'i guda biyar ya zuba Mata a jakar ta, ga wannan ki rabawa mutanen kukunba Ki tabbatar musu yanzu ke gimbiya ce Matar Yariman Gombe, sauran kayan tsarabar suna mota anjima za'a fito dasu" hawaye ne suka ciko idon Fateema "na gode yaya na, ubangiji Allah ya bani ikon binka in maka biyayya kamar yanda addini ya tanada" ya share Mata hawaye kiyi farin ciki Fateema, ni naki ne har abada" shine ya fara bud'e motar ya fito lokacin ne wani security yazo da sauri zai bud'e gefen da Fateema take Yarima yayi gaggawar d'aga masa hannu, mutumin ya koma baya Prince ya taka da kanshi ya bud'ewa gimbiyar shi ta fito.
Sai a lokacin ta fara karewa kauyen nasu da kofar gidan su kallo Mai martaba ma tsaye yayi kamar wani bako Yana kallon gidan d'an'uwan nasa. Sauye-sauye kam kauye ya samu sannan gidan su Fateema an canza mishi gini daga yanda yake da zuwa katafaren gida Mai zagaye da fulawoyi hadda gate d'in mota. Ga manyan shaguna guda biyu a gefe, inda suka hangi yaya Bashir Yana fitowa daga cikin su ya nufo su da saurin shi ya tsuguna Yana gaida Mai martaba. daga cikin gidan kuma Baffa ne ya fito Yana lale marhabi da zuwan su. Farin ciki Mara misaltuwa ya lullube Fateema. da hanzarin ta ta Isa inda suke ta tsuguna har kasa ta gaida Baffa da yaya Bashir suka kalle ta cike da kulawa suka amsa Baffa ya kalli Mai martaba cikin harshen fulatanci yace "yaya yar'ka fa ta girma da alama ta nusu, yau Fateema a kukunba duk dad'ewar nan ba ihu ba tsalle?" dukkan su sukayi dariya har ita d'in hakan yayi dai-dai da isowar Yarima inda suke, ya tsuguna gaban Baffa ya gaishe shi ya amsa cikeda kulawa Yana tambayar shi "yaya hanya" yace Alhamdulillah" Mai martaba ya kalli Baffa "d'an'uwa wannan sauyin gida haka ba sanarwa?" Baffa yayi dariyar su ta manya yace "hana ni akayi yaya, aikin Yarima ne, duk shi yayi komai kuma yace kar in sanar maka Wai duk randa kazo zaka gani" sosai Mai martaba yaji dad'in lamarin domin hakan ya kara tabbatar mishi yaro ya dawo hayyacin sa, Kuma ya d'auki Matar shi da daraja. Umma da Baffa suka gaisa sannan suka d'unguma zuwa cikin gidan inda suka tarar da kyakkyawar tarba daga Goggo tsabagen murna da farin ciki tarasa inda zata saka Fateema taji dad'in yanda ta ganta yarinya tayi jajur da ita ga yadda jikin ta yayi kyau ko manafuki ya kalle ta yasan tana cikin kwanciyar hankali. aka gabatar musu da kayan abinci kala-Kala dad'i da farin ciki sun cike zuciyar Fateema soyayyar mijinta ta dad'a ninkuwa a zuciyar ta gidan su yayi matukar kyau ciki da waje kamar tana cikin Masarauta haka take ji.
An dad'a yawan d'akuna a gidan an zuba masu taya Goggo aiki yan'mata guda biyu an kafa fanfuna da ababen more rayuwa a kowane lungu da sako na gidan ....
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*275/276*
A babban falon gidan aka sauke su inda suka ci mai dad'i suka sha mai dad'i, a nan ma Fateema ta gano cimakar gidan su ma ta canza, an Sami ci gaba sosai. Bayan sun kammala cin abinci da gaishe-gaishe ne Umman Yarima ta fara rokon gafarar iyayen Fateema tana dad'a basu hakuri akan abinda ya faru a baya. Suka ce ai komai ya riga ya wuce, baya-baya ce yanzu kam Sai dai a fuskanci gaba. Taji dad'i sosai Sai jan Goggo a jiki take ita kuma ba saban ba har yanzu d'ari-d'ari take da ita Yarima Sai kallon Fateema yake ta koma can nesa dashi ta zauna ta d'ora kanta a cinyar Goggo. Sai yaji Ina ma a cinyar shi ta kwanta ya shiga ayyana yanda zai ji. Su Baffa da Mai martaba suka mike suka koma d'akin ajiye baki na kofar gida Wanda shima yanzu an kawata shi da lundum-lunduman kujeru da Kayan kawata falo irin na manyan mutane. d'akin ya rage saura Goggo da Umma, Yarima da Fateema Dan Yaya Bashir kam tun d'azu aka Kira shi waje za'a sayi Abu a shago yanzu ya zama d'an kasuwa domin shi Yarima ya ginawa shagunan kuma ya cika mishi su da Kayan business na bukatun al'umma.
Yarima ya mike Yana sosa keya yace "Ina son zaga garin nan gashi bansan ko Ina ba, ga yaya na kuma shago ya rike shi". Iyayen sukayi dariya Umma tace "to ai ga Matar ka nan, Sai ka sakata gaba ku tafi" Fateema kamar jira take tayi zumbur ta mike tsaye "yawwa yaya muje, kaga daga can sai ka cika min alkawari na ko?" "haka ne fa" ya fad'a Yana fita daga d'akin ta bi shi a baya. Iyayen suka girgiza Kai suna murmushi cike da Jin dad'in yanda yaran suke tafiyar da rayuwar su. dai-dai kofar gidan sukayi karo da Innawuro (kawar Fateema) da gudun ta tazo kamar zata tashi sama, tana ganin Fateema ta kankameta sam bata damu da Wanda ke gefen ta ba. Itama ihun murna ta saki suka rungume juna cike da murnar sake had'uwa Yarima kam gefe ya matsa Yana kallon yaranta. Suka saki juna Innawuro tace "Kai Fatee kin ganki kuwa?, ya Salam!,wayyo Allah Fateema wlh kinyi kyau kamar ba ke ba. Wayyo Fatee na" ta koma rungume ta. Fateema tace "kedai bari yanzun ma ta gidan ku naso biyowa in mun dawo, fita zamuyi da yaya" ta fad'a tana kallon inda yake.
Sai a lokacin ta lura da Yana wajan ta rusina ta gaishe shi ya amsa da fara'a yace "Ki shiga ciki yanzu zamu dawo" "to" tace ta shige ciki tana cewa Faeema "kar fa ku dad'e Adda tana jira na a gida" "kekam Ki shiga ciki yanxu zamu dawo" ceear Fateema tana washe baki yau dai kam farin cikin ta ya kasa boyuwa dad'i takeji sosai a ran ta. suka fice ita da Yarima a jere suka ratsa garin kukunba duk inda suka bi sai a bi su da kallo samari da yammata duk Wanda ta sani idan ta ganshi sai ta tsaya sun gaisa ta bud'e jaka ta ciro kud'i masu yawa ta basu. da haka har suka Isa dai-dai wurin da Yarima ya mare ta taja ta tsaya cak "yaya a nan ne fa" ta fad'a tana kallon shi Sai a lokacin ta lura da canjin da fuskar shi tayi kamar ran shi ya baci maimakon ta damu sai ta fashe da dariya
"kaga yaya da wayau,borin kunya da wayau zaka yi min? Allah ni fushin ka bazai hana ni rama mari na ba". da karfi ya fisgo ta, ta fad'a jikin shi yayi amfani da d'aya hannun shi ya matse bakin ta sai da taji zafi batasan sanda ta saki Kara ba "kaga mugu wani ma zaka dad'a akan wancan? Allah shima Sai na rama" cikin bacin rai ya fara magana "ban damu ba kiyi ta mari na Fateema, amma Sam bazan lamunci ganin kina gaisawa da katti kamar haka ba, shin kin manta da matsayin Ki ne? Kefa Matar aure ce kuma gimbiya Matar d'an sarki ya kamata Ki kula kusan mutuwa nayi lokacin da kike musu murmushin nan" mamaki ya mamaye Fateema lallai ma Yarima wato abinda ya bata mishi kenan tayi rau-rau da ido sai hawaye shar akan fuskar ta da sauri ya sassauta Mata rikon da yayi Mata "meye abin kuka kuma Fateema?, no pls ya Isa haka kiyi hakuri amma Ki dinga tausaya min kinji mata'ta" ta gyad'a Kai tareda cewa "to" ya raba jikin shi da nata suka fuskanci juna yace "gani gaban Ki kuma na baki dama ki rama marin da nayi Miki Fateema" tayi murmushi lokacin da ta d'ora tafin hannun ta bisa lallausar fatar fuskar shi "bazan taba iya marinka ba Yaya na, ka sani na kawo ka nan ne domin ka tuna ranar da na fara furta maka so da kuma tsayin lokacin, Yaya ba ranar na fara son ka ba, na so ka tun banida wayau da wannan nake tabbatar maka bazan taba barin son ka ba" ba karamin dad'i kalaman Fateema suka yi mishi ba ya kasa cewa komai sai dai janta da ya koma yi ya manne ta da kirjin shi "na gode Fateema da wannan nake Kara tabbatar Miki ni *Fahad naki ne* ciki da waje kin kulle ko Ina kanwata"
lokaci Mai tsayi suka d'auka a hakan kafin ta raba jikin ta da na shi ta rike hannun shi suka kama hanyar gida zuwa lokacin gabad'aya garin ya d'auka sarki yazo gida da shi da iyalan sa, hakan yasa Mai gari da mutanen garin fitowa domin kawo gaisuwa ga Mai martaba sarkin gombe. An rarraba tsaraba sosai ga yan'uwa da makota harma da mutanen garin sannan aka cika store na gidan fall da kayan abinci Fateema ta bawa Innawuro kaya niki-niki da nata da na Umman ta da kuma na sauran kawayen su sannan ta kara musu da kud'i. Suka yi ta godiya sukayi sallama. Bayan ta gama rabe-raben ne ta kirga ragowar kud'in dubu d'ari uku da arba'in duka ta bawa Goggo su tace ta ajiye ita ma ta fara wata sana'a Uwar tayi ta godiya da d'inbin alkhairi domin nata manyan turamen zannuwa ma daban aka kebe Mata su.
Karfe biyar suka yi sallama da kowa suka kama hanyar gombe zukatan Su cike da farin ciki. Tun a mota Fateema ta fara yiwa Yarima godiya akan irin gyaran da yayi wa gidan Su ya rufe Mata baki Yana fad'in "karki d'auki abin da banbanci Fateema, Ki tuna matsayin Baffa gareni ya fi karfin wannan a gurina. a shekarar nan ma duk tare da Su zamuje aikin hajji insha Allah" ta kwantar da kanta bisa gefen kafad'ar shi a hankali tace "ka tare ko Ina da ko Ina yaya na, Ina kaunar ka" yayi murmushi ya shafi fuskar ta "nagode Teema na" lokacin da suka iso fada magariba ta kawo Kai shiyasa Yarima da Mai martaba suka nufi masallacin fada, tareda mutanen da suka tarbe Su. Fateema da Umma ko cikin gidan suka wuce inda suka yi Sai da safe kowacce ta nufi sashen ta
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*277,278*
Yau kam gaba d'aya rayuwar Fateema fess take, ji take kamar ma bata taba jin farin ciki kamar na yau ba kamar yadda take jin soyayyar mijin ta na tafasa a zuciya da sassan jikin ta kamar dai wannan shine farkon soyayyar inji (Nasmt đ) da shigar ta d'akin ta rage Kayan jikin ta ta shige toilet tayi wanka da had'in turarukan ta sannan ta d'auro alwala tazo ta fara gabatar da salla bayan ta d'auki lokaci Mai tsawo tana roka musu zaman lafiya da kwanciyar hankali ita da mijin ta tare da neman kariyar Allah akan duk wani Mai nufin Su da sharri. Ta mike ta zauna gaban madubi cikin kankanin lokaci ta rangad'a kwalli fuskar nan tayi shar da ita, kyawun ta da kuruciyar ta suka Kara bayyana a lokacin da ta d'auko wata doguwar Riga ta roba ta saka rigar yar ficik ce mara nauyi irin Masu bin jikin mutum d'innan, tayi wa gashin kanta wani style a gaban sannan ta zubo ragowar baya sai ka rantse baindaya ce.
Kasancewar yanzu Fateema take tasowa gabad'aya albarkatun jikin ta sun cike kyakkyawar surar ta Mai fizgar imanin duk wani cikakken namiji ta bayyana ta feshe jikin ta da had'ad'd'un turarukan ta ta kimtsa wurin ta nufi kitchen a can ta Sami Rukayya da Bilki wayanda yanzu sune Masu kula da abincin gidan ta duk da ita take girkawa amma suna taya ta. Yau kuma ganin bata gidan yasa suka d'ora Mata. "Sannun ku da kokari yan'mata" ta fad'a cike da zolaya "Kai anty Fatee, Wai yan'mata sannun Ki da dawowa" suka gaisheta duka ta amsa cikin sakin fuska "yau na barku da aiki ku kad'i" "banda abin Ki anty ai aikin mu ne, Kin Sami mutanen gidan lafiya?" "lafiya lau na same Su Sai alkhairi" Bilki ta canza maganar da cewa "Kai anty Faty tubarkalla wlh kullum Kara kyau kike yi, kin gan Ki yau kuwa?" Tai murmushi "zaku fara ko?" sukayi dariya "ai fad'ar gaskiya baya zama laifi". Ta kyale Su ta shiga duba abinda suka girka. Tuwon doya ne da miyar agushi ta sha kifin hausa busashsshe Sai farfesun kaji daban Sai kuma soyayyen naman shanu Wanda yaji had'in yaji na gargajiya, ta yaba ma aikin Su sannan ta saka plate kowanne ta d'ibi kad'an dai-dai da bukatar Su tace Su d'auki sauran suje Su ci kar Su baci sukayita godiya ita kuma ta d'auki babban tiren da ta jere Kayan ta nufi d'akin Yarima. Bata sameshi a d'akin ba amma taji motsin ruwa a bayi alamar Yana wanka. Hakan ya bata damar Kara gyare d'akin ta feshe shi da turare a cikin wardrobe d'in shi ta d'auko mishi kayan sakawa wasu na Shan iska mara nauyi ta ajiye Su gefen gado bayan ta feshe Su da kalar turaren daya ke amfani da shi. da fitowar shi yayi tozali da ita cikin irin shigar da yafi so a jikin ta Sai da ya lumshe ido yayi godiya ga wanda ya bashi Fateema sannan ya Karaso gare ta inda ta tare shi kamar ba ita ba sosai ta bashi mamaki domin da kanta ta tsane mishi ruwan jikin shi ta shafa mishi Mai da turaren jiki ta taje mishi gashin kan shi ya kwanta yayi luf-luf sannan ta bashi kayan da zai saka sannan ta d'auki Wanda ya cire ta kaisu cikin wata drower inda suke tara Kayan wanki.
Ya bi ta da kallo lokacin da yake saka kayan ganin Kayan abinci a d'akin shi yau ya tabbatar mishi cewar da gaske take ta canza komai cikeda zumud'i ya gama saka Kayan inda ya sameta bisa lallausar garass capet dake tsakiyar d'akin tana zuzzuba musu abincin ya zauna daf da ita ya rad'a Mata wani Abu a kunnen ta bansan me ya gaya Mata ba naga Dai tayi murmushi sannan ta ajiye abinda take ta manna mass kiss a gefen kumatu " *I love you* " ta fad'a kanta a sunkuye farin ciki ya Kara lullube Fahad haka Fateema ta zama? ya Tambaya a ransa "Alhamdulillah" ya koma fad'a a fili. Abincin suke ci amma dukkan Su ba Su maida hankali ga abincin ba domin dama ba yunwa suke ji ba wasannin Su suke da tsokanar juna haka dai har suka kammala zuwa lokacin an fara Kiran sallar isha yashiga bayi ya d'auro alwala ya tafi masallaci ita ma tashin tayi ta harhad'a kayan abincin ta mayar kitchen ta kimtsa wurin sannan takoma d'akin ta tayi alwala tayi sallar farilla
tana addu'a ya shigo ya zauna gefen ta lokacinda ta shafa addu'ar ta mike domin yin nafila shima ya mike ya shiga gaban ta Yana fad'in "yau jam'i zamuyi Ni da mata'ta" ba musu ta bishi sukayi bayan sun kammala ya koma umartar ta suka mike sukayi wasu guda biyu Inda suka d'auki lokaci Mai tsayi suna godewa Allah bisa barin Su tare dayayi dakuma neman zaman lafiya Mai d'orewa a tsakanin Su daganan Yarima ya fara janta a jiki. da wayau ya kaita bayi da rigima da komai ya rabata da kayan jikin ta ya sake musu ruwa Masu sanyi wanka na farko da ya taba yi tare da Fateema Sai yaji kamar kar Su fito amma daya tuna da muradin shi a yau Sai kawai ya d'auko ta cancas bai direta ko Ina ba Sai bisa gadon ta a lokacin sanyi take ji sosai Sai kudundunewa take a jikin shi shikuwa dama haka yafi so ya shiga sarrafata cikin salo da kwarewa tun suna gano kan Su har suka yi nisa da wannan duniyar suka daina gane komai (ganin hakan yasa na had'a Yan papers d'ina nace bari inabawa yarima guri domin cike burin rayuwar shi, a kunne na rad'awa Fateema asuba ta gari lolz)
*Yar'mutan Arkilla* ✍
đđđ *yaya*đđđ
đđ *fahad*đđ
đđđ
đ
đđđ *Nawa*đđđ
đđ *ne*đđ
đđđ
đŻđđŻ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍. . *280* *The* đ.
Washe gari misalin karfe hud'u na asuba ta farka domin Yarima kam ko baccin bai samu ba tunda ya Sami Fateema bai koma gane komai ba Sai bayan yasami nutsuwa Sai a lokacin ya lura da halin da take ciki da Tsanani wuya da galabaita hankalin shi yayi mutukar tashi sai kuka take mishi tana kiran Goggo, cikin Daren ya Kai ta bayi ya gasa Mata jikin ta bayan ya tsaftace Mata shi har ya kwantar da ita bata daina kuka ba yashiga aikin rarrashi da bata baki Yana lailayeta da hannayen shi a haka yasamu bacci Mai nauyi ya d'auke ta a cikin baccin ma tanata shesheka da sauke manya-manyan ajiyar zuciya Allah sarki Fateema Sai tausayin ta ya mama shi tsananin so da kaunarta suka Kara bin sassan jikin shi, tun da tayi baccin yake makale da ita idon shi kyar akan ta ya kasa bacci har izuwa yanzun da ta farka. Ganin idon shi tamas ya tabbatar Mata da bai rintsa ba tausayin shi ya kamata tana shirin janyo shi jikin ta Sai ta tuna da abinda ya faru a Daren jiya. da sauri ta sake shi sannan ta kudundune fuskarta a mayafi yayi murmushi "feel free Teema na, a yanzu ke cikakkiyar mace ce, ina tayaki murna na samun nasarar kawo budurcin ki gidan mijin ki. Fateema ke babbar mace ce wadda irin ta ke wahalar samu a wannan lokacin, zanyi iya kokarina wajan ganin ban koma rasa kiba kece rayuwar Yarima Fahad" ya fad'a yana had'ata da kirjin shi lokaci d'aya taji duk wani ciwo da rad'ad'in da take ji dun kau, soyayya da kaunar mijin ta suka mamaye ta ta rugume shi tsam Tana hawayen farin ciki da godiya ga Allah da irin tsare-tsaren da yayiwa rayuwar ta. hakika abin farin ciki ne ga kowacce mace ya kasance her first love been her husband. Yarima ya mike ya d'auki matarshi suka shige bayi sukayi wanka suka fito tare suka gabatar da sallar nafila sannan ya fita masallaci ya barta Tana shirin kabbarta farilla. A wunin ranar ko tsinke bai barta d'agawa ba shine ya wuni yimata hidima yana tarairayar t. Bayan kwana biyu yazo mata da passport na barin kasa ya tabbatar mata maganar zuwa aikin hajjin nan ce ta taso kasancewar an fara d'aukar mahajjata an riga angayawa su Baffa suna can suna shirye-shirye. tayi marin cikin jin hakan bayan kwana uku aka kira su su duka suka tafi Mai martaba da Baffa, Yarima da yaya Bashir da Umma da kuma Fateema abin dai sai wanda ya gani. A daddafe ya samu aka gama aikin hajji suka dawo gida domin yayi kewar matar shi matuka ita kuwa ko ajikin ta yanzun ma da suka dawo d'akin Umma ta sauka ganin Goggo a gidan ta sauka kafin gobe a kai su kukunba Yarima sai zagaye yake ya rarasa yadda zaiyi ya sami Fateema bayanda ya iya haka ya hakura ya koma ya kwanta can cikin dare ya ji shigowar ta Umma ce ta korota tace taje gidan ya hakannan da sand'a ta shigo dan tun da suka iso ta lura da take-taken sa. Hmmm bata san idabshi biyu ba ta shige bayi tayi wanka ta fito Tana sand'a saida ta murje jikin ta da mai da turarukan ta sannan ta kwanta a silale azaton ta Prince bacci yake sai ji tayi an rungume ta ta baya ido waje ta juyo Tana kallon shi cike da tsoro sai ta bashi dariya ya kuwa yi mai sar sa sannan yace "yi hakuri kanwata ki taimaka min wlh a hanu nake, kuma bazan miki irin na wancan karon ba i promise" hawaye ne suka ciko idon ta "Allah yaya ni tsro nake ji" ya shiga share mata hawayen yana rarrashinta da haka har ya cimma abinda yake So. Washe gari da kwarin ta ta tashi ba kamar wancan karon ba karfe tara sukayi breakfast suka shiga gida dan gaida iyayen su suka gaishe su. Sun d'an taba hira a nan kafin ya tashi ya fita fada saboda masu zuwa gaisuwar barka da dawowa. Ya barta nan tare da gwaggo da Umma suna shan hira. Karfe uku na yamma aka kai su Umma kukunba. daga ranar Hajiya Fateema da mijin ta suka zama irin masoyan nan da basa son rabuwa ko kad'an, bata so yarima yayi nisa da ita haka shima a nashi bangaren ga wani irin so na Fateema dake kara mamaye ilahirin sassa da gabobin jikin shi jin ta yake kamar ransa tattali da kulawa kam sai wanda ya gani. haka satuttuka da watanni suka shud'e wata shida da dawowar ta su Fateema ta fara laulayin ciki Allah sarki Yarima Fahad sai ya kara zama wani abin tausayi ko motsi tayi sai ya tashi koda kuwa a cikin bacci ne, farin ciki ya lullube iyayen kasancewar Yarima kad'ai suka haifa a duniya. gata na duniya kam Fayeema ta same shi bayan watanni tara ta santalo d'an ta, fari sol mai kamada Uban sa. Farin ciki kam ba'a magana duk inda ka duba yan taya murna ne ga d'aukacin iyalan mai martaba. A ranar suna kuwa mai jego tazama tauraruwa abar son kowa, d'aukacin mutane mota biyu aka ciko daga kukunba na yan'uwa da abokan arziki ina aka sha biki naji da fad'a ilahirin membres na Nasmat novel duk sun halarci bikin haka ma na King boy Isa novel, (King hadda bada babbar jaka yace Hadiza hadi ta ciko masa da kayan makulashe lolz đ) haka membres na Ama Alhaji kabir novel, ga yan gidan Asmart &deeyart ga na Maryam Ameen kai gaskiya su Yarima sun ga baki yaro yaci sunan Aliyu taron suna kam ya kai taro garin gombe ma ya shaidi hakan. Tun daga wannan ranar alkhairai suka kara kunno kai a gidan sarautar. Bayan shekaru Uku dana koma gidan a falon Umma na sami Aliyu yaron Fateema yanata kiriniya yana wasa da Umma. A sashen Fateema kuwa akasin hakan ba tarar domin samun su nayi suna ta jibga kaya a jakunkunan tafiya kallo d'aya nayiwa fufkarta na gano Tana d'auke da karamin ciki suka gama had'a kayan suka fito cike da annuri a fuskokin su dai-dai kofar fita daga sashen nasu suka tsaya tare suka kalli juna suka saki murmushi ya sanya hannayen sa duka biyu ya tallafo kumatun ta cikin sigar soyayya ya fara magana "Yau na kudur ta aniyar cika miki burin ki matata ina yi miki albishir da cewa lokacin da kafarki zata koma tako nan gidan to kin zama cikakkiyar likita" tayi murmushi Tana fad'in "kai cikakken namiji ne yaya na, na tabbata zaka iya duk abinda kayi niyya, godiya ga Allah daya bani miji mai riko da alkawari sakallahu bi khair" "na gode da yabon ki matata sai alkawari na biyu dazan miki shine na bayar da aikin gina miki babbar asibiti wadda na tabbatar kafin mu dawo an kammala ginin filin yana nan bayan mu direct za'a fitar miki da kofa daga cikin sashen nan zuwa cikin asibitin ki ina kaunar ki matata" farin ciki ya lullube Fateema ta rungume mijin ta cike da murna "wayyo Allah Yaya na na gode Allah ya saka maka da mafificin alkhairin sa Allah ya biyaka da mafificiyar aljannar sa" "Ameen Teema na Allah ya sauke ki lafiya " yaja hannun ta suka isa sashen Umma da shigar su yaro Aliyu ya rugo gun su da gudu "oyoyo dady na momy ina zaki?" Yarima ya kalle dhi cike da mamakin wayo irin na yaron kamar ba d'an shekaru uku ba ya tsuguna dai-dai tsayin yaron yace "inda nace maka zamuje mana boy, ko ka manta ne?" "Oh na tuna dady, inda zakayo corse kazama babban lacturer ko?" "thats my boy nasan bazaka manta ba" Umma ta fito daga d'aki Tana fad'in "a'a matafiyan har sun fito?" "mun fito Umma" inji Yarima Umma tayi musu addu'a da fatan alkhairi tareda fatan Allah ya bada abinda zaije nema (kamar yanda ya gaya musu zaije wani course ne na shekaru bakwai amma zasu dinga zuwa hutu lokaci-lokaci) shine fa Umma ta dage bazai d'auke mata Fateema kuma ya raba ta da Aliyu ba dole ya bar mata d'aya hakan ne yasa zasu bar Aliyun gida tun jiya sukayo sallama da mutanen kukunba tare da rakiyar mai martaba aka kaisu filin jirgi a gaban iyayen da d'an su jigin su ya tashi suka bar kasar haihuwar su zuwa Ijeep neman ilmin matar sa. A kasar ijip sun sami tarba mai kyau da kyakkyawan masauki gidane sukutum aka mallaka musu dukayi sati d'aya suna hutu a sati na biyu ne ya nema mata admission a wata babbar jami'a wadda aka gina ta musamman domin karantar likitanci duk fanni da mutum yake da bukata Yarima kuwa makarantar horar da malamai ya shiga domin ya samu gogewa akan lacturing bayan yan watanni karatu ya kankama na kowannen su sai dai a bangaren Fateema Tana fama da d'awainiyar ciki cikin da yariga ya tsufa dai-dai lokacin ne kuma suka sami hutun karshen shekara. Sosai taji dad'in samun hutun na watanni hud'u hutun bai Kai sati d'ayaba ta haihu inda Allah ya azirtasu da ya'mace a nan ya d'auko wata likita ta Riga kula da Fateema da babyn ta Su kad'ai suka aha suna inda yarinya taci suna Ameena mutanen gida kam sundai ga baby a photuna da vidio call, yarinya Meena Tasha gata da tattali Sai suke jinta kamar yar'fari bayan watannin hutu baby ta fara kwari yar raino aka samowa Fateema wata dattijuwa musulma Mai suna Aysha raward. Ita ce Mai kula da Meena kafin Umman ta ta dawo daga school karatu kam Fateema ta dage babu kama hannun yaro shine ma yasaka ko hutun shekarar farko basu Sami zuwa ba a hutu na biyu ne suka je Nigeria inda suka sha tattali da tarairaya yaron Su Aliyu ya Kara girma da wayau har an sakashi nursery yaro d'an 5yars soyayyar Fateema da Yarima Fahad kam sai wabda ya gani kullum idan ka gansu Sai kayi zatan ko saurayi da budurwa ne, haka hutu ya kare suka koma egeep rayuwa tacigaba da tafiya satika suna ture watanni su kuma suna ture shekaru hausawa Dai sun ce komai yayi farko zai yi karshe yau Dai Allah ya kawo karshen karatun Fateema Allah yayi ta kammala suk kuma dawo gida Nigeria inda suka zowa da Familyn da wani sabon al'amari wato Fateema ta zama cikakkiyar likitar Mata abin mamaki da al'ajabi bangare d'aya kuma abin fahari domin an kammala ginin asibitin ta Mai suna (Mrs. Yarima women hospital) shi kanshi Mai martaba bakaramin dad'in al'amarin yaji ba gagarumin biki ya shirya musu inda yan'uwa da abokan arziki suka zo taya murna ta Sami cikakkun takardu na shaidar zamanta likita Mai zaman kanta tunda suka dawo busy suke kullum cikin shirye2 suke komai na dangane da Kayan aiki sun gama had'uwa hatta wayanda akayo order sun iso, an gama Diban ma'aikata horses da wasu likitoci Mata Alhamdulillah yau itace ranar da aka kebe domin fara aiki a asibitin Dr Fateema masha Allah jama'a kamar jira suke asibiti ta cika ta tamgatse ayau burin Fateema ya cika a rayuwarta babu abinda ta tsana kamar ta ga Mata musulmi a hannun likita namiji Wanda akasarin Su ma ba musulmi bane. Yau gata ga yan'uwanta Mata Masu neman agajin mace yar'uwar Su. idan tana ganin Su a gabanta Sam bata jin kasala ko lalaci aiki takeyi tukuru Yarima tun Yana damuwa Yana cewa ta huta har ya gaji ya barwa Allah yanzu yaran Su uku Aliyu (littlePrince) yanzu ya zama matashi Mai shekaru goma sha d'aya Sai kanwar shi Meena yar shekara takwas Sai karamin Su Al'amin d' an shekara hud'u yara Yan gata ta gaba da baya duk inda suka yi dad'i da gata suke sha fannin iyayen Su ko na kakanin Su baremma in sunje hutu a gidan kakanin su na kukun ba ko kuma in anclule Fa'eez d'in Su yaxo daga sokoto dashi da yaran sa da matarsa Anty Sameera wadda yanzu kawabce ne Mai karfi tsakanin ta da Fateema haka Yarima da Fa'eez da kuma yaran Su duk da ba koyaushe ake had'uwa ba Su Fa'eez d'inma sune Masu yawan zuwa garin gombe kam sun more sun mance matsalar ciwo takai Su ga likitoci maza sadai jarumar Su Mai burin share kukan Su *Dr Fateema* tammat bi hamdallah dukkan yabo da kuma godiya sun tabbata ga Allah (s.w.a) daya bani dama da ikon kawowa karshen wannan labari na *Yaya Fahad Nawa ne* labarin dake d'auke da sakonni daban-daban jigo acikin Su shine
*HAKURI* musamman gare mu mu yan'uwa Mata ma dage mu zama Masu hakuri domin shine solution na kowacce matsala ta duniya duk wani kalubale da zaki fuskanta Ki saka hakuri a gaba Wanda ya jarabce Ki da wannan matsalar zai kasan ce tare da ke ya kuma magance Miki ita in a simple way taku har kullum (yar'mutan Arkilla) nagode da kaunar ku gareni da kuma bibiyar littafi na da kukayi inaneman ggafarar duk Wanda na batawa rai a cikin wannan rubutun nawa ko ta dalilin shi daga karshe kirana ga yan'uwa marubuta mu watsar da girman Kai mu so juna ta yanda hankali da nutsuwar makaran ta zai daidaita garemu aikin mu shine fad'akarwa
*Godiya* ga ilahirin members na kungiyar ZAMANI writers association bisa gyararraki da shawarwarinku ga Nasmat Ana matukar taređ¤ Allah ya Kara d'aukaka ZAMANI WRITERS ASSOCIATION makaranta labarin Yaya fahad nasan koda da sunayen groups nayi amfani bazan iya kirga ku ba Sai dai in ce nima Ina kaunarku fatan alkhairi gareku a duk inda kuke. Albishir da zan muku shine mu tafi Kai tsaye ga sabon Novel d'ina na gaba (JA'JIRTACCE) đ
*Yar'mutan Arkilla* ✍
0 comments:
Post a Comment