*_Da sunan Allah me Rahama me jinqai salati da ɗaukaka su tabbata ga manzon tsira Annabin mu Muhammad (S.A.W). Ya ubangiji kayi min katangar qarfe da duk wanda ke shirin ɗaga min hankali a yanar gizo Ko waneneshi Mace ko Namiji🤲 sannan kayi riqo da hannuna wajen Rubuta dukkan abinda ze amfani al'umar musulmi gabaɗaya._*
*_wannan littafi ba Sabo bane tsoho ne zan sake faɗaɗa muku shi ta yanda waƴanda basu karanta ba A baya zasu samu damar karantashi , amma sedai salon zesha banban dana farko kamar yanda sunan littafin ya canza Salo daga BAFULATANA zuwa BAFULATANA RETURN. Fatan Ubangiji yasa mu Amfana da darusan dake ciki_*
***
*_GYAMBU ((TARABA STATE))_*
______Tafiya suke cikin daji tare da shanunsu wata matashiyar yarinya Ce wadda bazata wuce shekaru goma sha hudu ba se kuma dattijon dake kusa da ita da alama dai mahaifin ta ne, cike da damuwa yarinyar ta daga Kanta ta kalli mahaifin Nata cikeda damuwa tace "wllh Baba nagaji kawai ka tafi Gida idan na huta zan tawo da shanun ta Ƙare maganar Da damuwa akan fuskarta.
Tunda ta fara magana mahaifin nata Ke kallonta sannan Yayi murmushi yace "to Rabe Babu damuwa amma fa ki kula sosai Da kanki. a nitse ta amsa da to "Baba.
Shafa kanta yayi sannan ya juya ya Kama hanyar gida Ya barta a Dajin tareda Dabbobin, yana tafiya Rabe ta nufi wata Ƙatuwar bishiya dake gefanta ta zauna dan ta huta a nitse ta Ta fara cire Takalmin Robar dake Ƙafarta, tana Gama cirewa ta Jingina da jikin bishiyar bata jima da kwanciyar ba Wani gajiyayyen bacci ya Samu nasarar ɗauke ta sabda Tsabar gajiyar dake tareda ita, kallo daya Zakayi mata ka fahimci tana jin dadin baccin da takeyi.
A hankali iska me daɗi ta fara kadawa Tareda ƙamshin ƙasa wanda hakan ya gauraye a guri guda ƙamshin ya canza zuwa wani yanayi me daɗin gaske, can kuma se aka fara iska me qarfi wadda itace ta zama sillar farkawar Rabe daga baccin datakeyi, a hankali ta daga Dara-Daran idanunta Sama Tana kallon hadarin daya gauraye sararin Samaniya ya koma launin baki aiko da sauri ta mike tafara kada shanun tana fadin su kama hanyar gida cikin harshen fulatanci tayi maganar, nan da nan shanun suka fara tafiya kamar yanda tace musu, suna cikin tafiya Yayyafi ya fara sauka a hankali can kuma se ruwan ya balle kamar da bakin Ƙwarya, A maddin ta nemi maɓoya se kawai ta dinga tsalle tana murna Ruwan na sauka a jikinta tana dariya, Haka nan Ruwan yayiwa Rabe dukan tsiya amma itako ko a jikinta wai an tsikari kakkausa inji 'yana magana lol
Cike da annashuwa take tafiya tana tsalle tana kuma shiga cikin ruwan da ya taru a kan hanya Har Ruwan ya ɗauke Kasancewar kayan jikinta na farin Saƙi ne yasa Duk yayu jajir Sabida jar Ƙasar dake hanya, haka tai ta shiga cikin ruwan dake kwance bisa hanyar tana bin shanun Suka kama hanyar gida, basu jima ba suka iso gida seda ta fara kai shanun cikin garken su sannan ta Ƙarasa inda bukkokin su suke, da gudun ta ta Ƙarasa bakin Ƙofar da zata sada ta da Bukkar matar babanta da sallama ta shiga Ɗakin cikin harshen Fulatanci tace " inna na dawo.
cike da bacin rai tare da tarin tsana take kallonta, cike da masifa tace " Uwar me zan miki da kike gayamin kin dawo shegiya me mugun hali, Zaki fita ko sena fito naci ubanki shegiyar yarinya me baƙin jinin tsiya har yanzu kinƙi auruwa sabida baƙin jininki, uwarki ma a tsiyace ta Ƙare kuma kema a haka zaki Ƙare Tinda kikayo gadon tsiya. Inna ta ƙare maganar tana hucci kamar macijiya
Tunda ta fara maganar Rabe Ke kallonta cike da rashin fahimta dan harga Allah bata fahimci abinda Innah Lauren take nufi ba Sam, kullum tana gaya mata haka amma Sam abin Be taɓa damunta Kamar yau ba, tambaya ɗayace ke mata yawo a cikin zuciyarta a gameda maganganun inna laure shin meyasa kullum take Maimaita mata magana ɗaya babu canji? Shin meyasa take yawan tunani akan magar innar a yan kawanakin nan?
Tana cikin duniyar tunanin datakeyi ne taji Saukar murfin kwano a daman goshinta!
Inna Laure ce ta buga mata tana huci lokaci guda kuma ta suri kwanon dake gabanta ta
Cike da Mugunta ta jefi Rabe dashi Daidai saitin hancinta aiko nan da nan Jini ya fara fita a goshin ta Da hancinta, gigicewa ta juya tana nemam hanyar fita daga bukkar Tana Neman agaji sabida Jinin data gani yana Zuba daga hancinta da goshinta, sosai ta gigice sabida a Rayuwarta batason ganin jini komai ƙanƙantarsa tsoronsa take ji. Da gudu ta nufi hanyar garken shanunsu Tana kuka sabida batado Babanta ya dawo ya gani tabbas bazata taɓa jin daɗin haƙan ba.
Karo taji tayi da mutum cikeda tsoro taja da baya zata fati taji an riƙeta gam, mahaifinta ne malam moddibo,
Cike da tashin hankali yake firta "innanillahi'wainnah'ilaihirraji'un
Cike da tashin hankali ya Jawota jikinsa tare da kama goshin Yana dubawa da sauri, hannunta Ya kama suka nufi Ɗakinsa dan yasa mata maganin daze tsayar da zubar jinin, cikin ikon Allah kuwa jinin ya tsaya amma sedai goshin ya kumbura sosai kuma Yayi jajzir kasancewarta fara, a hankali take sauke numfashi sabida zafin da gurin ke mata cikin sanyi murya baban ya fara magana Kamar haka
"Rabi'atu kiyi haƙuri da rayuwa kamar yanda nake gaya miki kullum kuma dik abin da ze dinga hadaki da Laure ki dinga kauce masa sbda bata da burin daya wuce ta illatamin ke, sanin kanki ne bani da kowa Daya rage mini a yanzu seke, tunda na rasa mahaifiyarki nakejin a raina cewar na rasa wani Ɓangare na rayuwata, shikuma dan Uwana tuna kina jaririya aka nemashi aka rasa seda ga baya aka samu gawarsa a bakin hanya, A kwai cuwuka sosai a cikin Rayuwata wanda banaso ma na dinga tunasu sabida yanda zuciyata ke zafi a sanadinsu. A sanadin mutuwar ɗan Uwama muka dena bin titi da dabbobin mu Har zuwa lokacin da mahaifiyarki ta haifeki, tunda na rasa iyaye na ban Ƙara samun farin ciki ba seda na auri mahaifiyarki, amma itama daga baya Allah ya karbe Rayuwarya ta rasu ta barmin ke, tun kina shan nono a haka kina fara girma ina kula dake
Bayan rasuwar mahaifiyarki da shekara 2 malm iro yazomin da shawarar na Ƙara aure Kodan sabida ki samu rayuwa me in ganci, cike da damuwa na kalleshi nace " Banƙi shawararka ba Iro sedai inajin tsoron wace mace zan Aura wadda zata iya riƙemin Rabe bisa gaskiya da Amana?
Har ga Allah bana so Rabe ta rayu da ciwon maraicin Uwa A Rayuwarta Ko kaɗan. da kulawa malm Iro ke kallon Aminin nasa
Yayi murmushi yace "indai wannan ne ba wata matsa bace Moddibo zan baka Ƙanwata Laure ka aura nasan zata riƙeta da Dukkan gaskiyarta fatana kawai ka Amince da wannan batun Kuma ka kwantar da hankalin ka.
badan zuciyata taso ba na Amince Da maganar Auren laure, koda
malam Iro ya fahimci zuciyata bata gama amincewa da mganar auren ba se ya sake murmushi a karo na biyu yace "indai Har ka amince ka aureta nikuma nayi maka alƙawarin zan zama me koyar da Ƴarka Rabe karatun addini Tayanda zata zama daban a cikin sauran yaran dake maƙotaka da Rugar mu. Ya ƙare maganar cikeda murmushi
Batare da tinanin komai ba na amince zan auri Laure. Ashe abinda ban sani ba shine sanadin tarwatsewar rayuwar gidana da farin cikin Ƴata ba Auro. Moddibbo ya Ƙare maganar Yana Kuka
A nitse Rabe ta rarrafo kusa da mahaifin nata ta rugumeshi tana kuka tare da share mai hawayen dake Sauka a saman kumatunsa da tafin hanunta, seda moddibo Yayi kuka me isarsa sannan Yayi shiru, cike da kulawa Ya shafi gefan fuskarta yace "kinci abinci Kuwa? Da sauri ta Ɗaga masa kanta alamar ae kuma a zahirin gaskia bata ci ba, Ta amsa masa da Ae ne kawai dan hankali n mahaifin nata ya kwanta
Moddibo yay murmushi yace "to maza tashi ki tafi daukar karatun don kar lokaci ya ƙure miki banda tsayawa wasa kinji Allah, ya albarkaci rayuwar ki Rabe na.
Ta amsa da amin sannan ta tashi ta nufi makarantar Allon malm iro inda take daukar karatu,
Dik da cewar su fulanin daji ne amma Sam hakan Be zama illa garesu ba Kuma be hanasu karatun addini Ba, duk cikin sa' oin Rabe babu wacce batayi aure ba se ita da Ƙawarta Ruƙatu sune kawai suka rage a yaran da basuyi auren ba,
Rabe kyakkyawar yarinya ce kallo Ɗaya zakai mata ka fahimci hakn, tana da manyan idanu tare da gashin gira me yawa hancinta dogo ne sosai kamar na mahaifin ta sannan yana da dan fadi kadan, labbanta ma daidaita ne kuma suna da dan tudu kadan tanada yalwataccen gashin kai ma'ana yana da tsayi sosai Irin na Fulanin Asali kuma ƴan gado, Rabe doguwa ce Sosai tayanda tsayinta yafi ƙarfin shekarunta, kallo daya zakayi mata ka fahimci tana da kyau da diri irin na fulanin Usuli, Rabe miskilace ta ajin Ƙarshe magana ma ba damunta tayi ba Se idan ta zama dole, sedai Sam hakan baya hanata Gaida mutane
Rabe yarinya ma'abociya fara'a da son karatu hakan ne yasa malm iron ke Ƙaunarta sosai
Sbda tana gane karatu Cikin sauƙi, koda wasa bata sakewa samarin Rugar tasu wannan ne yasa suke cewa tana da girman kai , amma a zahiri sam ba haka bane Mutum ɗaya ne ya nace mata har seda yasa ta fara kulashi sabida baƙin nacinsa Ana kiransa da Suna BAMANGA shima baɗan Rugarsu bane ɗan Rugar dake maƙotaka da tasu ne, a nitse ta qarasa makarantar Abin mamaki babu wanda yazo se ita kadai, Ajiye Allon ta tayi sannan ta dauki tsintsiya ta share gurin Tass ta shimfiɗa tabarman kabar Dake jingine tahau ta zauna ta fara bitan karatunta dan a ranar zata wanke Allon ta
Tana cikin karatun ne Ruƙatu ta Ƙara so da sallamar ta amma Rabe bata Amsa ba Har seda takai aya sannan ta daga kai da murmushi ta ansa mata sallamar,
Ruƙatu tayi dariya tace "sannu sarkin hadda shine ko ki biyo min ko?? To ai gashi nazo nima kuma nasan dan ki rigani wanke Allo ne yasa kika tawo kika barni to ai na gane wayon naki
*_((duk wannan maganar cikin harshen fulatanci suke Yinta nayi haka ne dan me karatu ya fahimci gundarin labarin sbda idan nayi ammafani da harshen fulatanci ba lallai wani ya fahimci abinda labarin Ya ƙunsa ba))_*
Rabe tayi dariya Tace "Ruƙatu kenan keda zakiyi aure kwanan nan ai kin ma kusa ki dena zuwa makarantar Gabaɗaya saurin me zakiyi kuma?
Haɗe rai Ruƙatu tayi Sannan tace "to ai se munyi sauka zanyi Auren kuma yau saura sati biyu mu sauke da ikon Allah.
murmushi Rabe tayi sannan tace "to Allah ya nuna mana sati biyun.
*_Gareku masoyana kuma mabiya littattafaina, idan har salon yayi muku zan gane daga Yawan comment Ɗinga ga wannan littafi. Ima muku batan Alkhairi tareɗa baku tabbacin cewar wannan littafi ze zo muku da zarar na kammala littafina me taken KUYARDA DANI👏_*
Sonso Fisabilillah❤
Sushmah💋
Comment
Nd
Share
[3/3, 5:22 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*_Page: 2-3_*
*_A JIYA NAYI MISTAKE A MADADIN NA NACE GYAMBU ((TARABA STATE)) SENA SAKA GYAMBU ((ADAMAWA STATE)) A FARKON PAGE 1 MANTAWA NAYI CEWAR GYAMBU BA'A CIKIN JIHAR ADAMAWA TAKE BA A CIKIN JIHAR TARABA TAKE FATAN ZAKU FAHIMCENI MABIYA WANNAN LITTAFI😊_*
✍️____Da haka suka rufe hirar tasu sakamakon Ƙarasowar malam Iro gurin, cike da girmamawa suka gadashi ya amsa tare da sakin fuska yace " An gaida Ƙawayen juna Idan har akaji maganar Rabe to da Ruƙatu ne koda Moddibbo. Malam Iro ya faɗi hakan yana murmushi
Suma murmushin sukayi Basuce komai ba kansu a sunkuye, Ruƙatu aka fara biyawa Allonta sannan aka biyawa Rabe Ma nata, suna kammala Karatun ba jimawa sukayiwa malam Iro sallama kana Suka kama hanyar gidajensu, a hanyar komawar ne sukai kacibus da Aliko Wanda ze auri Ruƙatu, Tun kafin su ƙaraso inda yake ya kafesu da idanu kamar ze cinyesu, turo Baki Rabe tayi sannan ta zinguri Ruƙatu tace "da alama nan gaba wannan maƙale matan naki har makaranta ze dinga binmu idan har ba'a ɗaura muku igiyar Aure ba. Rabe ta faɗi hakan yayin da take nuna mata Aliko
A nitse suke tafiya har suka ƙaraso inda Alikon ke tsaye cike da fara'a suka gaisa da Rabe ita kuwa Ruƙatu se Faman boye fiska take a bayan Rabe wai ita Ala dole kunyarsa takeji,
Basu jima a tsaye ba Rabe tayimai sallama ta nufi gida cike da tinanin Abinda zata tarar Na daga bala'in Inna Laure, siyasa taita wasa a hanya harta gama cinye sairan lokacin daya rage mata sannan ta kama hanyar gida sabida tasan mahaifin duk inda yake a wannan lokacin to ya koma gida, bata dawo gida ba se yamma liƙis kasancewar suna da nisa da makarantar, cike da fargaba ta Ƙarasa dakin da take kwana ta kwanta tare da sauke ajiyar zuciya.
A hankali ta firta Kalmar "Alhamdulillah Bisa rashin haɗuwar da basuyi da inna ba, Sabida har ga Allah batason duk abinda ze ƙara haɗata da inna Laure dan tasan haduwar Tasu ba alkairi bane, tana cikin wannan tinanin ne taji Antaɓa Labulan buhun ɗake jikin Ƙofar bukkar ta, da sauri ta mike tsaye A matiƙar tsorace har jikinta na Rawa sabida yanda tsoron ya tsirga mata Duk a zatonta innah Laure ce , da sallama ya shigo Ɗakin Yana kallonta Da mamaki sabida yanda yaga jikinta na rawa irin haka da gudu ta Ƙarasa gareshi ta rungume shi Gam Lokaci guda ta fashe Masa da wani irin kuka.
Shiru yayi yana sauraron kukan nata tamkar wadda ke shirin shiɗewa, sosai Yakejin kukan na taɓa zuciyarsa Sedai beyi yunƙurin hanata ba Donta damu damar yin me isarta, hannunsa yasa ya share mata hawayen dake zubo mata yace "kiyi haƙuri Rabe nasan Kinada Cikakkiyar hujjar Da zakiyi kuka sabida rashin dacen da kikayi da matar uba irin Laure, ki Ƙara haƙuri Insha Allah wata rana se labari kinji ?
Da sauri ta Ɗaga kanta alamar To.
A hankali Moddibbo ya kama kafadunta ya zaunar da ita a bakin katifar ciyawar dake Ɗakin yace "daga yau nayi miki Alƙawarin Cewar bazaki sake kukan rashin uwa ba Insha Allahu kinji Rabe? Be jira cewarta ba Ya Nufi ƙofar fita Daga bukkar zuciyarsa na zafi akan lamarin Laure.
Da sauri ta ɗago tace "baba Don Allah kayi Min Aure ko zan dena ganin innah Laure!
Cike da mamaki moddibbo ya juyo yana kallon Ta yace "Aure kikace Rabe? Ba tare da tinanin komaiba ta daga Masa kai alamar Ae,
Jikin sa a mace ya tako Har inda take zaune ya dafa Kafaɗunta cike da kulawa yace " dagaske kike kina son aure Rabi'atou?
Ba tare da fargaba ko shakkaba tace " Ae Baba Ina so Indai zan dena ganin inna. Ta faɗa tana kallonsa hawaye na zubo mata, harga Allah bata San me ake nufi da Kalmar Auren ba Kawai tana jinta a bakine Batareda da tasan tarin Abubuwan dake cikinsa ba kawai ta fada ne dan ta samu sauqi a zuciyarta.
Modibbo yayi murmushi yace "shike nan zan kawo miki mijin da zaki Aura har gida Tunda dai kince Auren kikeso kinji?
Da sauri ta washe baki cike da yarinta tace "to Babah yaushe zaka kawo Min shi??
Sosai Maganarta ta bawa moddibo dariya Don haka ya kasa cewa komai illa dariyar dayakeyi kawai, itama murmushin tayi
A hankali ya kama kumatunta yace "nan da 'yana kawanaki kadan zan kawo miki shi Rabe na. yana kaiwa nan ya Fice daga bukkar ya nufi masallaci,
itama tashi tayi taje tayi alwala tayi sallah sannan ta ta nufi dakin Babanta, tana shiga Ɗakin ta sameshi a zaune yana Hada magunguna Gargajiya, dayake Abinda yakeyi kenan bada magani irin na GargajiYa, duk Rugar su shi ake kira idan rashin lafiya ya samu wani Kuma cikin ikon Allah ana dacewa da maganin Nasa Idan har ya bayar.
Da sallama ta shiga ta zauna Daga gefansa tayi shiru batare da tace komai ba, hakan ne ya Bawa moddibbo damar fahimtar yunwa take ji, be ce mata komaiba ya Ɗakko kwanon dake gefansa ya mika mata da sauri ta karɓa Ta buɗe faifan da ka rufe kwanon dashi furace da nono nana da nan ta kafa kai tafara sha Batare da ta sauke kwanon ba, daga yanda take shan furar ne abin ya bawa moddibo mamaki a nan zuciyar sa ta fara zargin anya kuwa Rabe taci abinci kuwa???
Tabbas ze Iya Ɗaukar komai Da Laure zatayiwa ƴarsa guda ɗaya tak a Duniya amma fa banda Horon yunwa, a fusace ya tashi ya nufi bukkar Laure ko sallama be mata ba Sabida yanda Ransa ya Ɓaci ya Hauta da bala'i kan cewa ze jure komai da zatai masa amma fa Sam banda yiwa gudan jininsa Rabe horon yunwa,
Tunda ya fara masifar Laure ke kallonsa cike da mamaki sabida tunda take da moddibo be taba Ɗaga mata murya ba balle Har yayi mata faɗa Irin haka, Ashe Dama haka moddibo yake?? Tabbas ta yarda ransa ya Ɓacci sosai shiyasa bata Tanka masa ba tunda ya fara fadan, idan Har tace zatayi magana tofa tabbas Zasuyi ɓatacciya donta lura komai ze Iya faruwa Wanda kuma ba lallai yay mata dadi ba,
Yana gama zazzaga mata Faɗan ja juya yay gaba ya barta da fargabar Faɗansa,
Yana Fita Ɗakinsa ya nufa da sallama ya shiga Ya zauna yay shiru yana kallonta, har ya fita ya dawo Rabe na zaune a inda ya bar ta Bata tashi ba Har seda ta shanye Furar tas sannan ta miƙa masa kwanon tace "Baba gashi na Shanye.
Murmushi Ya ƙirƙiro yayi Mata tareda shafa kanta Yace "Allah yayi Miki albarka Rabe. Tana kallonsa tace "Amin Babana
Hira suka dingayi dashi jefi-jefi tana tayashi tankaɗe maganin dake gabansa har suka gama sannan ta kwashe ta zuba masa a cikin Boronsa ((jaka)) dayake zuba magungunan a ciki, sun jima tana yi masa shirmen hirarta har ya gaji yace taje tayi bacci Dare yayi, nanfa Rabe ta Tubure ita fir Bazata tafi Ba seya rakata Har ɗakinta, haka kuwa akayi har Ɗakin ta moddibo ya Rakata Be fito ba har seda ta fara bacci sannan ya tofa mata addu'o'i sannan yay Fita ya Rufe mata ƙofar ɗakin da ƙofar karan dake gefe.
Wshe gari da zanyi safiya Rabe ta fito cikin shirinta na tafiya kiwo, sanye take Kayan farin Saƙi irin nasu na fulanin asali Ƙafarta sanye cikin rufaffen takalmi na roba Yalo shar dashi,
Ɗakin moddibo ta nufa da sallama sannan ta shiga ta zauna Daga Ɗan nesa dashi Kaɗan yana Karin kumallo,
da fara'a ya dubeta yace " Matso kusa dani mana Rabi'atou na. Cike da fara'a ta qarasa jikn Baban nata cike da soyayya ta faɗa jikin sa Tana murmushi,
Tare sukayi Karin kumallon Safen dashi bayan sun gama ne suka fito tare Da ita Yana riƙe da hannunta A waje sukaci karo da Laure tana ƙoƙarin sauke ruwan zafin dake kan murhu. Hade rai Tayi kamar taga mutuwar ta Sannan ta ɗauke kai daga barin kallonsu,
A dan tsorace Rabe ta gaisheta, seda ta faki idon moddibo sannan ta watsawa Rabe wani ɗan iskan kallo Wanda hakan yasa da sauri Rabe ta koma bayan moddibo ta Ƙanƙameshi.
bece komai ba ya kama hannunta suka fice daga Gidan Ko waiwayen laure beyi ba
Suna fita garken Shanu suka nufa dan su fita kiwo,
A nitse ta kalli Moddibbo tace "Baba yau ni kaɗai zani kiwo Base mun tafi tare ba kaga se mu raba shanun Gida biyu Keman, kai kayi hanyar gabas nikuma nabi yamma idan muka dawo se'a ga Shanun waye sukafi Ƙoshi Idan mun dawo ?
Cike da kulawa yace mata to muje sena raba mana, da sauri take binsa cike da zumudin zata kiwo ita kaɗai,
Basu wani ɓata lokaci ba ya raba Musu shanun gida biyu ya Tisa nasa yay gaba itama tayi gaba Da nata, seda yay mata kashedin ta kula da kanta sosai kuma kada tayi nisa sosai Kuma banda bin titi sbda ya tsani bin titi A rayuwarda tunda ya rasa Ƙaninsa Zakhariya.
Tafiya take Hankalinta a kwance kallo ɗaya zakayi mata ka Fahimci tana cikin farin ciki mara misaltuwa, Yawo sukaitayi a Dajin Suna karaɗe ko ina, Har suka shafe kimanin Awanni a cikin Dajin seda suka Ɗauki lokaci Me tsayi sannan Rabe ta lura Da lokacin zuwa makarantar ta Yayi,
Dole Yasa ta kora shanun suka kama hanyar gida Badan Ranta yaso ba.
koda ta dawo seta fahimci babanta be dawo ba, Saɓanin kullum Lokacin daya saba dawowar, tambaya ɗayace keyi mata yawo a kwanyar kanta shine "meyasa Har yanzu Babanta be dawo Gida ba??
Ɓangaren moddibo kuwa Tafiya kawai yake tareda shanun Amma sam hankalinsa naga ɗiyarsa wadda ya tura daji da shanu batareda ya haɗata da kowa ba, addu'a kawai yakeyi Allah ya tsare mas ita da ikonsa, daidai kan kwanar daze yanka ya ɗauki hanyar Ya hangi mutum kwance Ƙasan wata ƙatuwar bishiyar Marke, Be kawo komai a ransa na harya ƙaraso jikin bishiyar kasancewar ta gefanta ze Ratsa ya kama hanyar gida Seyayi zaton ko hutawa Mutumin keyi sabida hali na tafiya amma daya Ƙaraso seyaga sabanin tinanin sa,
Yaro ne matashi sanye Cikin wata Dakakkiyar shadda light blue an masa dinkin Muhammed se faman yararin tsada da kyau takeyi kansa babu hula An Kafta masa wani Ƙaton Sara Daga gefan kansa ta hagu, hakama Ƙirjin sa da kuma bayan sa, gefan cikinsa kuma Alamace na sukar wuƙa babu abinda ke zuba a jikinsa se
jini.
dik da saran dake jikin sa hakan baze hanaka fahimtar kyau Da tsarin Halitta irin na matashin ba, cikin sauri moddibo ya Ƙarasa kusa dashi ya dago shi Lokaci guda kuma ya ɗora yatsunsa a saitin Wuyansa dedai babbar jijiyar dake kai saƙo zuwa ƙwaƙwalwa a nan ne ya fahimci Da sauran numfashi A taredashi, sabida tsabar Rikicewa yama rasa ta Inda ze fara bashi taimakon gaggawar,, (Emergency treatment )
Can wata dabara ta faɗo masa, nan da nan Moddibo ya Ɗaga matashin da ƙarfin tsiya Ya Dorashi a bayan Ɗaya daga cikin shanun ya Ɗaure shi Tamau a jikinta ta yanda baze faɗi ba Sannan ya nufi hanyar gida,
Sun jima Suna tafiya sannan suka Ƙara so gida.
a Ƙofar gida suka hadu da Wadda tun dawowarta taƙi yarda ta shiga gidan ta kafa ta tsare A waje tana jiran dawowar Modibbo,
Da sauri moddibo yace ta shiga da shanun cikin garke Ta ɗauresu ba tare da ta kula da mutumin dake ɗaure a bayan saniyar ba tayi gaba, da Ƙar moddibo ya kwanto shi daga jinkin saniyar Yayi hanyar dakinsa dashi, suna shiga ya kwantar dashi akan tabar marsa Sannan ya mike ya Ɗakko Boronsa dayake sa magani A ciki ya ajiye Ta daga gefe Sannan ya Ɗakko wata Ƙarya ya ajiye Wadda ke ɗauke da Ƙaho da kuma Aska a ciki se wani garin magani da kuma wasu manyam ganye masu kimanin girman tafin hannu duk a cikin ƙwaryar.
take moddibo ya Ya ɗauki wannan Askar ya shiga yanka rigar dake jikin matashin "Subahanallah Shine kawai abinda Moddibo Ya iya firtawa Kenan sabida yanda yaga jini ya taru a gefan Ƙirjinsa Da kuma irin saran Rashin Imanin da akayi masa, da alama seda aka dake shi sannan aka sareshi Wanda hakan ya bashi tabbacin Kashe matashin ake ƙoƙarin yi,
A nitse ya dauki Askar ya daidaici gurin da Ɓakin jinin ya taru sannan ya yanka nan da nan Mataccen jini Daya taru a gurin ya fara fita, a hankali ya shiga goge mai Jinin har seda ya gama gaba Ɗaya sannan ya shiga samai magani a jikin raunukan Dake jikinsa.
bayan ya gama sa masa maganin ne ya fito yana kwaɗama Laure kira, jikinta na rawa ta Ƙaraso tace " gani mlm Lafiya dai ko?
Be kulata ba Yace " maza ki kawo min ruwan zafi Yanzu-yanxu jiki na rawa ta tashi ta hada wuta ta Dora Masa ruwan zafin......
Sushmah💋
[3/3, 5:22 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*_WRITING BY :CHUBAƊO_*
*_Page:4-5_*
_____✍️Ta ɗan ɗauki lokaci kamin ta kawo ruwan zafin sabida sha'anin itace a lokacin Damuna a kwai wiyar sha'ani, dakyar ta samu wutar ta kama sannan ta ɗora Ruwan se faman minta takeyi ba'a jimaba Ruwan ya tafasa,
Wata ƙatuwat ƙwarya ta ɗaukko ta juye masa ruwan zafin a ciki sannan ta ɗauka ta nufi dakinsa dan ta kai masa ruwan.
Sallama tayi daga bakin ƙofar batareda ta shiga ba sannan yay mata izinin shiga, Ruwan Ya karɓa ya Ajiye a gefe sannan ya ɗakko wani farin saki ya jefa a cikin ruwan zafin seda ya fara hucewa sannan ya ɗakko wani garin magani a ɗaure cikin tsumma ya zuba a cikin ruwan, duk wannan abinda yakeyi ita dai Laure banda kallon moddibo babu abinda takeyi bakinta a cike fal da tarin tambayoyi amma ta rasa ta inda zata fara yin Tambayar.
A hanzarce moddibo ke gabatar da komai sabida matashin ya Rasa jini dayawa, Inna Laure na nan tsaye Rabe ta shigo ɗakin tanabin ko ina da kallon Sannan ta kalli Moddibo tace Baba wannan shine mijin daka samo min din?
Be kalleta ba yace "A'a sam wannan bashi bane Raɓe amma na tabbata shima ɗin zezo nan bada jimawa ba.
ya ƙare maganar yana saka yatsansa a saitin inda aka cakawa matsin wuƙa a ciki donyaji ya yanayin zurfin ciwon yake.
Cike da damuwa ta kali Mahaifin nata tace "Nikam baba inajin tsoron karmu taimakishi a ƙarshe ya citar damu tunda bamusan waye shi ba. Ta faɗi hakan tareda leƙa raunin dake jikin matashin
Moddibo be damu da ya bata amsa ba sabda shi gaba daya hankalinsa yana kan wannan matashin burinsa kawai a wannan lokacin be wuce yaga ya ceci Rayuwarsa ba,
Kamar zatayi kuka tace "baba amma wannan daga ganinsa baƙo ne ko dubi irin kayan jikinsa Sam ba irin namu bane?
Itadai Laure batace musu ƙala ba Har Rabe ta kama surutunta sannan ta jefo tata tambayar tace "mlm a ina ka samo wannan yaron? Kai yanzu baka jin tsoron ɗaukko shi nan gaba yazo ya zame mana masifa?
Moddibo ya kalleya yay shiru sannan yayi murmushi yace "haba Laure meyasa kike magana irinta yara ne a ina kika taɓa ganin inda taimako ya zama masifa?
shiru tayi masa tana kallonsa ba tare da tace ƙala ba, daya ga bata da niyar magana seya cigaba da magana nan ya labarta mata komai tin daga Hauwarsa da yaron har zuwa ɗakko shin da Yayi be ɓoye musu komai ba,
Nan da nan idon Rabe ya fara zubda hawaye dama ya lafiyar kura balle kuma tayi Zawo.
Ita ko Laure ko a jikinta balle ma har ta tausaya masa dataga abin na neman isarta seta fice daga ɗakin tana mitar wai moddibo ze jawo musu bala'i daze fi ƙarfinsu.
Shidai be kulata ba sema cigaba da gogewa matashin busashen jinin dake jikinsa da ruwan maganin daya haɗa,
Cikin muryar kuka Rabe tace "baba!.
ya ɗago yana kallon ta sedai bece mata komai ba, a hankali tace "dame zan Iya taimaka maka naga yana zubar da jini?
Murmushi Moddibo yayi yace so nake kullum ki dinga yi masa adduar samun lfy kinji shi kaɗaine taimakon da zakiyimin dani dashi? daga masa kai tayi alamar gamsuwa sannan ya dubeta yace "maza kije Rugarsu Bamanga ki Samomin ƙayar ɗinki zanyi amfani da ita yanzun nan.
Da sauri ta juya ta fita daga ɗakin zuciyarta fal tausayin matashin Saurayin wanda basusan daga wace nahiyar ya fito ba.
Tana zuwa Rugarsu Bamanga Direct ta nufi inda ƙayar take ta fara karyowa harta cira dayawa sannan ta juyo hanyar gida, koda suka Haɗu da Bamanga ba irin kiran da beyi mata b Amma ta shareshi tayi hanyar gida, dataga ma yanshirin takura mata seta sanya gudu dole tasa ya ƙyaleta
Ko Sallama batayi ba ta shiga ɗakin Moddibo ta ta zube masa ƙayar a gabansa tana nishi tace "baba gashi. Karɓa yayi cikin mintunan da bazasu gaza 5 ba ya fara haɗa naman gurin da aka soƙeshi da wuƙar yana tsirewa da ƙayar harya gama ɗinke ciwukan dake jikin matashin sannan yasa magani a gurin, cikin ikon Allah da hikimarsa kuwa zubar jinin ta tsaya.
Tunda ya fara ɗinkin Rabr ke kuka harya kammala, share mata hawayen yayi da hannunsa sannan yace ta tashi ta wuce ɗakinta ta kwanta, ba musu ta mike ta tafi ɗakin kamar yanda yace mata.
A wannan Ranar dai Rabe batayi wani baccin kirki ba.
A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau matshinnan ya cika sati biyu Cif a gidansu Rabe amma ba abinda alamar farkawa a taredashi haka kuma babu inda yake motsi a jikinsa sedai kawai numfashi, tun suna sa ran farkawarsa har suka cire rai farkawar sa a nan kusa.
Rabe ce kawai take kula dashi itace ke saka masa magani har zuwa kan abinci, kunu ne kawai ke iya shiga cikinsa sabida yanda haƙoransa suka datse.
Kullum itake zuba masa kunun a baki da ludayi tin baya shiga bakin har yazo yana shiga kaɗan-kaɗan,
Kallo ɗaya zakayiwa matashin ka fahimci ya rame sosai akan ranar da moddibo yazo dashi Gidan, tun ranar da aka kawoshi gdan Laure bata ƙara leƙowa dakin ba.
A cewar ta idan masifar ta zo to ta afkawa moddibo shikaɗai da ƴarsa,
Kujifa masu karatu😂
Wasa-wsa Rabe ta shafe kwanaki bata zuwa makaranta Haka kuma ko kiwo bata zuwa, amma Sam hakan baya damunta sabda Damuwar datasa a ranta, Abinda tasa a ranta kawai shine taimakon mutum yana daya daga cikin dabi'u masu kyau A Rayuwa. Dole tasan wata rana zasuci Ribar abinda abinda sukayi na taimakon wannan matashi
Mlm iro yazo yafi a Ƙirga kan Rabe ta dawo makarantar ayi suka da ita amma fir taki yarda ta koma dan a ganin ta idan ta fita koda Ƙofar gida Ne to waye ze Kula da wannan bawan Allahn?
Moddibo ne ya shigo Ɗakin hannunsa riƙe da wata saiwa ya mika mata yace " maza jeki tafasa Min ita ki kawo min kinji.
Da sauri ta karɓa taje ta haɗo Ƙirare ta Kunna wutar ta Dora maganin, ba'a dau lokaci me tsayiba ruwan ya fara dahuwa tareda saiwar bata sauke ba hae seda Wutar ta mutu Gaba ɗaya sannan ta juye maganin a qwarya ta kaiwa moddibo, da murmushi a kan fuskarsa ya karba yana sa mata albarka, seda maganin Ya fara hucewa moddibo ya dago kan matashin ya shiga zubawa Masa abaki.
dikda cewa ana zubawa wani na zubewa ansamu wani ya shiga cikin nasa, bayan ya gama ne ya shiga goge masa jiki da sauran maganin, tundaga ranar
Kullum Se'an masa haka har aka shafe Tsahon wata Guda anayi amma still babu wani ci gaba. Itako Rabe bata da aiki se kuka Ta wani ɓangaren kuma ga Bala'in inna Laure, nan da nan duk tabi ta rame se hanci da idanu Kamar ba ita ba.
Sosai Abin Hakan ke ƙara Ɗagawa moddibo hankali to amma bashida yanda zeyi illa kawai yayta addu'a.
Laure CE ta Shigo Ɗakin da sallama ya amsa mata Ba yabo ba fallasa.
A dakile tace " yame jikin? Modibo yace "Da sauƙi Alhamdulillah sannan yayi murmushi a karo na biyu yace hala fita zakiyi Nenaga kin shigo min ɗaki?
Basarwa tayi kamar batajishi tace "ae Fita zanyi dama ta rasa ta Inda zata fara tambayar sa cewar zata fita, a takice yace mata"sekin dawo Indan kinje kya gaida su Iro da Gwaggoji.
Bata amsa Shi ba tayi gaba bayan fitarta Tana sababi.
hamisu Ne Ya shigo gidan hankalinsa a matiƙar tashe yace " don Allah malam modobo kazo muje ka duba mahaifina wllh jikin nasa ne ya tashi. Hamisu ya faɗi hakan yana kuka
moddibo be Ɓata lokaciba ya fito suka wuce Gidansu Hamisun, har sun fita ya dawo yace Rabe ta koma dakinsa sabda maralafiyan,
Da sauri ta mike tare da yi masa Allah Ya kiyaye ta koma dakin ta zauna, zubawa matashin ido tayi ba tare da tace komai ba Nanda nan hawaye Ya fara wanke mata Fusaka cikin muryar ta fara magana Kamar haka "wai kai yaushe zaka tashi ne?shin kasan yanda mukeji a ran mu Duk a gameda kai? Dan Allah ka tashi ko hankalin babana ze kwanta Na roƙeka!!
Ta jima tana suru tanta kamar wata zararriya sannan tayi shiru ta cigaba da kukanta fukarta dik tayi Ja idanunta Duk sun kumbura abin ka da farar mace....
Ta jima tana kukan sannan bacci ya dauke ta,
A hankali matashin ya fara motsa hannunsa daƙar ya Iya daga hannun sa ya maidashi Ƙirjinsa Sabida tsabar Azabar dayakeji a jikinsa,
A hankali ta buɗe idanunta sabida jin da tayi kamar motsi yasa ta bude idanunta daƙar ta maida kallon ta gareshi, Nan da nan ta miƙe zaune sosai ta Ƙara buɗe Manyan idanunta sosai Tana mamaki
ya akai hannunsa ya koma Ƙirjinsa? Tambayar da take mata yawo Kenan a zuciyarta.
A nitse ta maida kallonta kan fiskarsa Ta ƙura masa idanu kamar meso gano wank abu a taredashi, ta jima tana kallon sa kamar bazata dena ba kamar a mafarki taga yana Ɗan motsa idanun sa, Ƙara zaro idanunta Tayi waje cike da mamaki Ta miƙe tsaye still idanunta akansa,
A hankali ya fara bude Idanunsa har ya gama buɗesu gaba ɗaya Yana me ƙarewa ɗakin kallo harya dauke manyan idanunsa a kan fuskar Rabe,
A firgice ya fara Ƙoƙarin tashi yana so yaja Da baya sabida Yanda ya tsorata da Ganinta.
Ƙara Ya saki sabida wani Irin azababben zafi dayaji a gadon bayan sa Har zuwa saitin gefan cikinsa na Dama, bashiri ya koma ya kwanta yana maida numfashi, da sauri Rabe ta sake matsowa kusa dashi sosai sannan ta fara magana cikin harshen fulatanci take cewa "kayi a hankali sabda jikin ka akwai rauni Sosai!
Tunda ta fara magana yake kallon Yanda take motsa bakinta har ta kai Ƙarshen maganar. dikda cewa be fahimci abinda take faɗa ba hakan be hanashi Ƙare mata kallo ba, kyakkyawa ce Sosai ta gaban kwatance don tafi kamada irin larabawan yankin ƙasar Misira, tana gama maganar ta sakar masa murmushi Wanda seda tasa gabansa ya faɗi ya ɗauke idonsa da suri daga barin kallonta
mikewa ta fita daga dakin ,
Tana fita dakin ta nufaa ta Ɗakko wani rufaffen kwano Wanda Moddibo ya bata kafin ya fita sannan ta dawo ta sake zama dab dashi Tana murmushi a karo na biyu sannan tace Dashi " zaka iya tashi kuwa ?
Kura mata ido yayi cikeda rashin Fahimtar abinda take faɗa. dataga be gane me take nufi ba setai mai nuni Da hannu alamar ya tashi,
A hankali ya Fara yunƙurin tashi a karo nabiyu amma kuma seya kasa ya Dole yasa ya koma ya kwanta, alama tayi masa da hannunta kan cewar ya sake ƙoƙartawa Amma kuma setaga bashida niyar yin hakan.
mikewa tayi sannan ta koma bayan sa Ta fara ƙoƙarin dagoshi,,
cike da mamaki yake kallonta tare da Girmama Ƙarfin hali irin nata, jibeta fa 'yar qarama da ita wai zata Ɗagashi, lallaima yarinya nan Ta gama raina masa Hankali ya faɗi hakan a zuciyayarsa, ba zato yaji ta cakume shi Da dukkan ƙarfinta ta fara giji-gijin ɗagashii, Wata uwar Ƙara Ya saki sabda zafin dayaji na ciwon dake bayan sa, bata damu da ihun dayeke ba har seda ta zaunar dashi,
Daƙar Sannan ta zube ƙasa tana maida numfashi.
Dakyar ya Iya ɗago idon sa da suka fara canza kalah dan azaba ya kalleta lokaci Ɗaya itama ta dago idonsu ya sarƙe cikin na juna.
gabanta ne ya Yanke ya fadi da sauri tayi Ƙasa da idonta, a nitse Takai hannunta kan kwanon da ta Ɗakko a daki ta buɗe, fura ce da nono Wadda aka zugawa uban suga ta Ɗiba ta miƙa msa Bakinsa alamar yasha, sarai ya gane nufinta a hankali ya fara Ɗago hanunsa amma kuma seya kasa, ya jima yana kallon ludayin sannan ya maida kallonsa kanta Batareda ya karɓa ba.
Tambayar Dake yaWo s kansa itace "wai shin inane nan?
"Kuma wannan yarinyar wacece ita?
"Waze tambaya ya bashi amsoshin wannan tambayoyi nasa?
Data ga bashi da niyar bude bakin ne seta sake miqa masa ludayin har yana taba lips dinsa , sa'a sannan ya dawo daga duniyar tinanin daya afka, a nitse ya buɗe bakin ya fara seeping Furar a hankali, se kuma ya kauda kansa da sauri kamar Wanda ya tina wani abu,
Daqar ta samu ta lallabashi ya sha sosai.
Bayan ya gama sha ne ta Ɗakko masa maganin sa shima ta bashi yasha , tunda ta Fara bashi maganin yake mamakin yarinyar
Badan komai ba se yanda take Da zafin nama a komai nata, ƙoƙarinta ya zarta na shekarunta dubada yanda taketa dawainiya dashi, harga Allah ya jinjinawa jarumtar ta matiƙa.
tana gama shafa mai maganin ta taimaka masa ya kwanta yana kwanciya moddibo ya shigo Ɗakin da sallamar da gudu Rabe ta nufeshi ta rungumeshi tana fadin " baba ya tashi wllh ya tashi,
Kana kallonta zaka fahimci tana cikin Farin ciki ba kaɗan ba.
Tunda ta fara magana moddibo yake kallonta da murmushi yace" to yanzu kuka ya Ƙare Kenan ko?
Da sauri ta rufe fuskarta da zarazarn hannayenta tana dariya.
Tun shigowar moddibo matashin yake kallon su har zuwa sanda Rabe ta rungumeshi, se kallon su yake cike da burgewa da alama mahaifin tane ya fada a zuciyar sa, sabda suna bala'in kama da juna!
Sushmah💋
[3/3, 5:22 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*_Page :6 -7_*
*_WRITING BY: CHUBAƊO_*
____✍️A nitse moddibo ya Ƙarasa kusa da matashin ya sunkuya da murmushi Kwance a kan fuskarsa yace "sannu da jiki Yaro kashe doguwar jinya.
Cikin harshen fulatanci moddibo Yayi maganar.
ido kawai matashin yake bin moddibo dashi Batareda yasan abinda yake faɗa ba. Kallon Rabe moddibo yace "da alamafa bayajin abinda muke faɗa. Ya ƙare maganar da damuwa akan fuskarsa
Itadai batace komai ba ta zuba musu idanu kawai tana kallonsu
Koda ya fahimci matashin baya gane abinda yake faɗa sabida banbanci yare se dabara ta faɗo Masa ya kalli matashin Cikin kwaɓaɓɓiyar Hausarsa yace "Shannu yaro ya shikejin ƙarfin jukin naki?
Matashin ya bude baki da nufin ya amsawa moddibo amma sedai muryanshi bata fita sosai sabda mura data kamashi Yace "Alhamdulillah da sauki.
A nitse moddibo ya fara magana kamar haka
"Yaro nasan zuciyarka a cike take da tambayoyi akan mu, haka
Kuma nasan zakaso kasan meye dalilin zuwanka wannan gurin? To magana Ta gaskia itace ina Kan hanyar dawo wata daga kiwo ne Allah ya hadani dakai A cikin mayuyacin hali kana kwance cikin jini !!
Haƙiƙa duk abinda Alla ya hukunta shiyake faruwa shiyasa ma har nabi hanyar dana Daɗe amma da Allah ya Ƙaddara haɗuwarmu dakai se Gashi ya nufeni da bin hanyar Duk dan na ceci Rayuwarka.
A lokacin dana tsince ka Ban taɓa zaton zan sameka da sauran numfashi a tareda kai ba amma Dana tabaka sena fahimci kana numfashi, a haka na ɗakko ka a daji na kawo nan mukaita kula dakai tareda rauni kan Dake jikin ka har Allah ya amince mana ka tashi A yanzu.
Nan da nan idon matashin ya kawo ruwa ba komai ne yasa shi hawaye ba se irin karamcin da moddibo yay masa A Rayuwa tabbas bashida abinda ze iya biyasa dashi,
Yanzu babbar damuwarsa A yanzu Itace be San halin da Mahaifinsa yake ciki ba, sedai bashida wani zaɓi wanda ya wuce yaci gaba da zama tareda wannan bawan Allahn kuma ya mant da rayuwarsa ta baya!
Cike da kulawa moddibo ya dafashi yace "kayi haƙuri yaro nasan dole zakayi kewar gida tareda ƴan uwanka amma ka Ƙara haƙuri jikinka ya Ƙara Ƙwari Inyaso seka Koma garesu Kaji?
Ɗaga masa kai kawai matashin yayi ba tare da Yace dashi komai ba ya mayarda idanunsa ya kulle,
Har moddibo ya mike se kuma ya sake sunkuyowa yace da matashin yaro ya sunan ka??
Gabansa ne ya faɗi yayin da yaji tambayar da Modibbo yayi masa amma, nan da nan wani ɓangare na zuciyarsa yace masa "karka sake ka faɗi cikakken Sunanka dana mahaifinka idan ba haka ba Mutanan nan Zasu gane gane waye kai cikin sauƙi kuma su mayar dakai hannun maƙiyanka waƴanda suka jefaka a wannan halim da kake ciki a yanzu!
Ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske Still idanunsa a Rufe ba tareda ya buɗesu ba Yace "Uhm uhnn Sunana Sunana Muhammad Ali.
Ɗan jim kaɗan Moddibo yayi yana kallonsa sannan yayi murmushi yace "Masha Allah Muhammad ai babban Sunana To Allah ya ƙara lfy.
Duk wannan hiran da suke Rabe na jinsu a nitse ta Ƙaraso kusa da matashin da murmushi a fiskarta tace "Anya sunan Muhammad ne?
Da sauri ya buɗe manyan idanunsa yana kallonta har seda gabansa ya faɗi sannan ya ƙaƙalo murmushi a karo na farko yace " Ae Sunana kenan kamar yanda kikaji Muhammad Ali. Ya faɗa yayin dayake ɓatar da murmushin dake kan fuskarsa a lokaci guda.
Tun daga lokacin da Matashin yayi mata murmushi har zuwa sanda ya gama magana take kallon sa ,
Ba komai take kallo ba se tsabar kyau Da tsarin halitta irin nasa, bata tabbatar da shi kyakkyawa bane seda yayi murmushi A iya Tsahon rayuwarta Har zuwa yanzu bata taɓa ganin mutum irinsa ba,
Mutane dayawa Kan fada Mata cewar tana da kyau amma yau Kam taga Wanda ya fita kyau da tsarin halitta,
(Nima kaina Danake kwaso muku rahoto seda na dan tsorata da kyawu irin na wannan matashi lol)
Seda moddibo ya dafata sannan ta dawo daga duniyar tinanin da take,,,
A daburce tace "baba yaushe za'a kuma bashi abinci?
Harga Allah ba abinda tayi niyar fada ba kenan tsabaragen daburcewa ne yasa ta fadi hakan, sosai moddibo ya fahimci halin data Samu kanta a ciki amma kawai seyay murmushi ya fita daga Ɗakin.
A hankali A hankali ya Buɗe idanunsa ya ɗago kansa ya kalleta yace ya sunan ki?
A taƙaice tace" Sunana Rabe.
A hankali ya kuma maimaita sunan Yana wani yamutsa fuska yace "what's that does mean?
Ƙura masa idanu tayi tana kallonsa, hakan yasa ya taɓe baki ƙaɗan Yace" ok lem me call you with Fulani, I can't even call you with that locally name is it Rabe or what ever. A taqaice Ya sake kallonta still itama kallonsa take batareda tamasan abinda yake faɗa yace "You can't thanks for everything Fulani girl. Ya faɗi hakan yana mayar da idanunsa ya kulle
ta jima tana juya kalmarsa ta ƙarshe a ranta dikda cewa bata San meyake nufi da ita ba, amma setaji Kalmar tayi mata dadi Kuma ta tsaya mata a Rai. A haka taɓar ɗakin tana ta juya maganar a Ranta
har yamma
Moddibo Rabe bata ƙara dawowa ɗakin ba Har lokacin shafa masa magani yayi Shida kansa ya shafa masa maganin, sannan yasa Rabe ta Dora masa ruwan zabi ta kawo masa tana kawowa tayi waje abinta, moddibo ya tashi ya nufi inda Matashin ke kwance a hankali ya fara kiran sunan sa,
A nitse ya buɗe idanunsa a fiskar moddibo,
Murmushi Yayi masa sannan yace ka gyara zan goge ma jikin ka , a nitse ya fara Ƙoƙarin tashi amma kuma seya kasa tashi moddibo ne ya taimaka masa Harya tashi zaune.
wani farin saki moddibo ya Ƙara Ɗakkowa ya tsoma a cikin ruwan ya fara gasa Masa jikinsa, dik da cewa jikinsa nayi masa ciwo sosai hakan be hana moddibo gsa masa Shi yanda ya dace ba,
Yana gamawa ya Ɗakko maganin shafi ya shafa masa sannan ya taimaka masa yayi alwala, Cikin mintunan da bazasu gaza 5 ba ya shiga rama sallolin da ake Kansa.
ya Dade yana yi dik da cewa besan adadin kwanakin daya Kwashe baya cikin haiyacinsa ba a Wannan Ƙauyen,
Seda ya Ɗau lokaci me tsayi sannan ya idar, moddibo ne ya tai maka masa ya kwanta sannan ya Ɗakko wani zanin saki ya lullube shi ba'a Ɗau lokaci Me tsahi ba bacci yay a won gaba dashi
*****
Ɓan garen Rabe kuwa tunda ta fita bata sake dawowa Ɗakin ba
Sallah ta gabatar sannan ta fito ta gabatar da aiyukan da ta saba na yau da kullum seda ta gama tsaf sannan ta koma daki da nufin ta gabatar da sallar ishsha'i, bayan ta idar ta jima tana adduo'inta sannan ta shafa,
Da sauri ta mike ta cire mayafinta ta nufi katifar ciyawarta Dake ɗakin dan ta kwanta sbda sanyin daya fara busawa,
Kamar daga sama taji an banko mata cikin Ɗakin aiko da sauri ta miƙe sabda sanin ko wacece ta shigo Ɗin, dan indan da sabo Yaci ace ta Saba da halin Laure.
Masifa fal ranta ta shigo Ɗakin tare da y
Binta da wani wulaƙantaccen kallo tace " to yar gatan gata rere A fito kiyi min ayki dakike Koƙarin kwanciya Bacci ƴar mowa Wato ga baiwa Ubanki ya ajiye inyi muku wahala ko ? To wllh baki isa kiyi bacci yanzu ba Har sekin gamamin aiyukan dake cikin gidan nan.
Bata jira cewarta ba ta fincikota sukayi waje, wasu tarin kwanuka ta gani an jibge Matasu gefe kuma Ruwane a cikin wata Ƙatuwar fanteka da alama Ruwan ya Dade a gurin Batun base an fada ma ya dau sanyi ba,,
Kallo daya zaka yiwa kwanukan ka fahimci babu Wani datti ko kadan a jikin su kawai tsabaragen mugunta ne yasa Laure ta Fito dasu.
Ba musu Rabe ta sunkuya ta fara Ɗauraye kwanukan tanayi jikinta na rawa sabda sanyi Dake busawa har taci Ƙarfin kwanukan, da laure taga bazata Iya jure sanyi ba setai shigewarta Ɗakin tabar Rabe a waje tana fama Da sanyi, ta ɗau lokaci me tsawo Tana ɗauraye kwanukan sannan ta gama ta kife mata su,
ta wuce daki jikinta Se rawar sanyi yakeyi, tana shiga ta kwanta dikda cewa ta lulluba amma Sam bata dena jin sanyin ba,,
Abu kamar wasa Haqoranta suka fara haduwa da juna Suna fitar da wani sauti na daban, nana da nan zazzabi me zafi ya rufeta daƙar ta samu bacci ya Ɗauke ta
Ba ita ta farka ba se bayan an idar da sallar asuba, daƙar ta samu tayi alwala ta gabatar da sallar
Ko data idarma kasa tashi tayi daga inda Tayi sallar sabda wani irin azababben jirin data keji.
Har gari Yayi haske sosai kowa ya fara harko kin Gabansa amma Rabe bata fito ba.
A Ɓangaran moddibo Sosai Yayi mamakin rashin ganin Giftawar Rabe har wannan lokacin Bata fitoba, azatonsa ko bacci takeyi shiyasa be wani damu sosai ba,
A nitse ya gama gabatar da komai na karyawa Wanda Matashin zeyi Karin kumallo dashi, amma
Har ya gama bega idon Rabe ba, se kuma abin ya fara damun moddibo
Ɓangaren Matashin saurayin kuwa tunda ya tashi daga baccin safen da yayi ya afka duniyar tunanin meyasa Yakeda tarin maƙiya ne a Rayuwarsa? Me yay musu suke son ganin bayansa a Rayuwa? Me kuma ya tare musu har haka?
Modibbo ne ya Katse masa tunanin dayakeyi ta hanyar shigowarsa ɗakin tareɗa abincin Sa A hannunsa yace " ya kamata ka tashi kaci abinci kasha maganin ka ko?
Ba musu ya fara Ƙoƙarin tashi dikda cewa ba iyawa zeyi ba,,
Moddibo ya saki murmushi yace" yaro gaskiya kana da Ƙarfin hali sosai ka Ƙara haƙuri Insha Allah ka kusa fara tashi da kanka.
Tunda moddibo ya fara magana idon Matashin yana kansa se kuma Yayi murmushi yace "to baba Allah yasa Hakan Sedai bazan gaji da Ƙara jaddada godiya ta a gareka ba sabda Haƙiƙa ka taimaki rayuwata, Ablokacin dana fitar da ran akan Rayuwar duniyar gabaɗaya!! Shiru ya ɗanyi sannan ya sake kallon moddibo yace " thank you for saving my life,,, ya Ƙarashe maganar tare da hawaye
Da sauri moddibo ya dafa kafaɗunsa yace "kada ka damu yaro ni nayi maka dan Allah ne badan wani ba, dan haka ka dena zubar da hawayenka kaima kamar Ɗa kake a gurina kuma nayi maka Alƙawarin Cewar zan kula da kai har zuwa ranar da zaka Samu sauƙi ka koma ga iyayen ka. ya Ƙare maganar da murmushi A kan fuskarsa
Canza fuska matashin yayi a likacin da moddibo yayi masa zancen komawa gida, Sosai yake jin kalaman moddibo a Saman zuciyar sa harga Allah dattijon ya shiga ransa, moddibo ne ya share mai hawayen sa sannan ya fara bashi kunun Daya shigo dashi irin nasu na Fulanin Asali, Sosai Matashun ke jin daɗin kunun dan haka yasha sosai sannan yace ya Ƙoshi.
Moddibo yayi murmushi yace masha Allah tunda yanzu ka Ƙoshi bari na shafa maka maganin ka se kuma kasha na shan ko?
Matashin yace "haka ne.
Seda moddibo ya gama shafa mai maganin sannan ya bashi Nashan shima ya shanye. yana gamawa yace to yaro bari in je inga Rabe ko lafia naga har yanzu bata fito ba.
Matashin yace" hakane kam yakamata a duba agani ko lfya,
Daga haka moddibo yay waje ya nufi Ɗakin Rabe da sallama, tana nan a Inda tai sallah jikinta se rawa yake da sauri moddibo ya nufeta yana tambayar ta Meya sameta?
yana taba jikinta yace " subahanallah!!
Rabe meya sameki be jira cewarta ba ya kinkimeta yayi Ɗakinsa da ita banda hawaye babu abinda ke fita a idonta a haka ya Ƙaraso Ƙakin da ita,
Da sallama ya shigo Ɗakin sannan ya kwantar da Ita.
tunda suka shigo Ɗakin gaban Sa ya faɗi ganin wadda moddibo ya kwantar Daga ɗan nesa dashi, a rude yake tambayar moddibo abinda ya sameta har yana Ƙoƙarin tashi daga inda ya ke kwance,
Sosai moddibo ke kallonsa girmama sanin yakamata irin na matashi, cikeda tsantsar so da Ƙauna Moddibo yace "yaro ka kwantar da hankalin ka ba wani Abu bane zazzabi ne kawai Kuma zata samu sauƙi da izinin Allah. Ya faɗi hakan yana kallonsa
Har ga Allah moddibo yaji Matashin ya Ƙara kwanta masa a rai musamman dayaga ya nuna kulawar sa a kan tilon 'yarsa guda daya!
Wai shin wanene wannan matashin ne kuma mene cikaken sunansa?
Sannan kuma meyasa yake fargabar komawa ga iyayensa ?
Menene hujjarsa na ƙin gayawa modɗibo sunansa a lokacin daya tambayeshi Ya gaya masa wani sunan na daban?
Comment
And
Share
Sushmah💋
[3/3, 5:22 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
_Page : 8-9_
*_WRITING BY: CHUBAƊO_*
____✍️Murmushi moddibo yay masa sannan ya juwaya ya ɗakko ƙatuwar Boron sa (jaka) dayake sa magani a ciki ya ɗaukko wani farin magani ya jiƙashi a wani madaidaicin kwanon sha, seda ya ɗan ɗauki lokaci sannan ya ɗgota ya fara ƙoƙarin bata,
Ba tayi masa gaddama ba ta karɓa tasha sabda bata ƙin magani kokaɗan.
Duk abinda suke idon sa yana Kansu se kallon su yake a ransa yana mamakin yanda moddibo yake Iya gane ko wani ƙullin maganin dake cikin jakar, shi'a tsarinsa sam be yarda da maganin Gargajiya ba sena Asbiti a cewarsa wai a maganin Gargajiya baya maganin cuta sedai ma ya ƙarawa mutum wata cutar. Amma se gashi a yau maganin Gargajiya yayi masa ranah fiyeda zatonsa.
shiyasa a rayuwa kada ka raina baiwar da Allah yayiwa wani ko wata komai ƙanƙantarta idan ba haka ba watara seka samu kanka da a ƙarƙashin Abinda kake Rainawar kuma yayi maka Rana.
A hankali seyaji abin yana birgeshi sosai lallai ilimin sanin itace shima abune me zaman kansa bawai kowa ne yake da wannan baiwarba, domin kuwa shima abune me zaman kansa. Bata jima da shan maganin ba bacci ya ɗauketa ta banda zufa ba abinda takeyi wanda hakan ya bawa moddibo tabbacin cewar zazzaɓin ya sauka.
Matashin ya kalli moddibo cike da damuwa yace "ya Kamata kayi wani Abu kagafa se gumi take kodai zamu kaita asibiti ne??
Kallon tsaf modibbo yayi mai da mamaki kwance akan fuskarsa sannan yace "hmmm a wannan ƙungurmin Dajin kake tinanin Samun Asibiti?
Batare da tunanin komaiba yace "ae mana aiko ba'a
Nan ba ina zaton idan muka fita da ita zuwa cikin gari zamu sami Asibitin dazamu kaita. Ƙura masa idanu moddibo yayi harya kai ƙarshen maganarsa take yanayinsa ya canza yace "yaro ka gani nan tunda na tashi da iyayena a nan muke Rayuwa bamu taɓa tunanin muyi nisa da nan ba tunda muka dawo nan muka yada zango damu da jama'armu, Asalin mu 'yan jihar Adamawa ne Haifafun NUMAN ne mu ba Asalin cikin garin Adamawa ba a cikin Daji muke Rayuwa tareda Dabbobin mu, dolece tasa mukabar Mahaifarmu muka dawo nan Sabida wata Masifa data Afka mana.
Modibbo sauƙe ajiyar zuciya yacigaba da cewa " mu uku kacal iyayenmu suka Haifa, mu biyu ne maza se kuma Ƙaramar kanwar mu BADDO wadda a halin yanzu bansan inda take ba Shin tana Raye ne kokuma ta Mutu Allah shikaɗai ne masani!!! Ya faɗa Hawaye na Sakko masa.
Wani irin kuka ne ya taso masa wanda ya daɗe beyi irin sa ba a wannan lokacin, koda Wasa Matashin beyi yinƙurin ya dakatar dashi ba sabida ya samu Zuciyarsa tayi Sanyi
Seda yayi me isarsa sannan ya daidaita nutsuwarsa ya cigaba da cewa " tun daga Ranar da muka nemi ƙanwata Baddo Muka rasa iyayen mu suka shiga tashin hankali mara misaltuwa, bayan wanda muka samu kanmu a ciki kafin ɓatanta, wannan dalilin ne yasa muka tattara ƙwanmu da ƙwar-kwatan mu mukabar NUMAN muka dawo nan da zama sakamakon ƴan fashin da suka sa mu a gaba ba dare ba Rana, babban takaicin ma shine ba Iya fashin da suke mana bane matsalar har yaran mu mata ƙanana suke yiwa Fyɗe a gaban idanun mu ba tareda imani ko tausayi ba.
wannan Shine dalilin dayasa muka bar jaharmu ta asali muka Dawo wannan dajin, dikkan mu dakake gani duk ƴan uwan juna ne, shiyasa muke zaune lfy lau a nan ɗin batareda mun leƙa cikin gari ba ko hanyar titi bama bi Tunda ɗan Uwana Zakariya ya gamuda Haɗarin mota a sanadin tsallaka titi, a lokacin da muka ɗakkoshi ya Rasa jini sosai shiyasa muka yanke shawarar mukaishi Asibitin, mashin ɗin malm Iro muka hau mu uku muka nufi Babban Asibitin Gwamnati dake cikin garin gyambu Amma sam sukaƙi taimaka mana, munaji muna gani a gaban idon mu Zakariya ya Rasa Rayuwarsa munyi kuka har muka gode Allah sannan muka sake ɗakko gawar muka dawo da ita gida, tundaga lokacin zuwa Asbiti ya gama ficemin a rai wllh ko sunansa ma banason sabida mutanan mu na wannan lokacin a cike suke taf da son zuciya gamida Rashin tausayin talaka.
"sosai jikin matashin yayi da labarin Moddibo wanda yay matiƙar taɓa masa zuciya sannan yace "A zaman danai dakai na fahimci cewar kai mutum ne na musamman wanda yakeda shahararriyar baiwar da kaikanka bakasan iyakarta ba, da ace Hukumar lfy zasu samu labarinka tabbas dasun Amfana dakai ta ɓangare da dama musamman abinda ya shafi sani akan itacen gargajiya
"Hmmm kaidai ai sha'ani kawai yaro amma lamarin mutanan dake cikin wannan duniyar sesu,
Wata rana da yamma bana mantawa wasu mutane suka shigo mana Nan da sunan Su jami'an hukumar lafiya ne, kuma sunzo ne don su kafana mana Sansaninsu a nan sbda muma mu samu cigaba.
"batareda tunanin komai ba muka karbe su hannu biyu Ashe abinda bamu sani ba shine cutarmu sukazo suyi, Dayawa a cikin mu kasuwanci shanu mukeyi wanda ya zame mana tamkar Sana'ar Gado seda suka bari kowa ya dawo daga kasuwancin sa yaxo da kuɗaɗe masu yawa sannan suka far make mu cikin Dare suka ƙwace komai sannan suka kashe na kashewa,
Tun daga lokacin bamu ƙara yarda da kowani mahaluki ba, hatta baƙi ma muka dena karbarsu koda kuwa daga ina suke.
"shiyasa tunda naju ka ambaci sunan Asibiti kaga yanayina ya canza yaro sabida ko sunan Asibitin banason ji wllh, yanzu zancen danake maka wllh da mutanan Rugar nan zasu samu labarin zuwanka tabbas da se sun koreka kokuma ma su kashe ka.
A firgice Matashin ya zaro manyan idanunsa yana kallonsa jin kalmarsa ta ƙarshe wato kisa sannan yace "to Baba meyasa lokacin da abin ya faru Baku nemi tai makon jami'an tsaro ba ???
Moddibo ya kalleshi yayi murmushi irin na takaici yace " yaro da fari minyi ƙoƙarin gwada yin hakan amma daga baya se muka gane itama hukumar se a hankali.
Matashin yayi shiru a zuciyarsa yace "Ashe Dama a kwai mutane masu fiskantar irin wannan rayuwa?? Be taɓa zaton a kwai irinsu moddibo dake Rayuwa a cikin wannan halin me cikeda ƙunci ba,
Tabbas Allah ne ya Ƙaddara zuwansa wannan gurin dan ya Ƙara Imani a kan rayuwar duniya,
Haƙiƙa baka sanin Allah yayi maka Wata ni'ima a Rayuwarka har seka ga Wanda be kaika ba sannan kake sanin Allah yayi maka Gagarumar Ni'ima,
Haka kawai seya samu kansa da jin tausayin su tareda ƙudurtawa kansa cewar insha Allah seya temakesu da wani jinjinan Abu daze Amfanesu da izinin Allah.
Tunda garin Allah ya waye Laure ta fice daga Gidan sabda bata da wani buri yanzu a rayuwata daya wuce Rayuwar Rabe bata inganta ba kamar ta Sauram Sa'o'inta, tafiso tayi Rayuwa a ƙasƙance ta ƙare a tantal baɗeɗe, shiyasa ta ɗorawa zuciyarta tsanar yarinyar tun batakai haka ba, duk wani buri na laure a yanzu be wuce taga ta samu haihuwa da Moddibo ba ta hakane kawai zata iya mallake dukiyar sa.
Tabdi kujifa masu karatu!
Dama ance yanzu ba'a maƙiyin nesa , ya Allah ka shiga tsakanin mu da maƙiyan mu na sarari Dana boye🤲
********
*ZAFAR ENTERPRISES* shararren Companyn dayay fice a ɓangaren kasuwanci a cikin ƙasashen Duniya guda 12 , waƴanda suka haɗa da America, Germany, Cairo,London da sauran ƙasashen duniya wanda yake mallaki ga babban Ɗan kasuwar nan Alhaji Abdulwahab Abdullah, dandazon ƴan Jaridan na hanga a Harabar Babban Companyn nasu dake Garin abuja banyi ƙasa a gwiwa ba na kutsa ta cikinsu yaja tunga na tsaya don in samu damar ɗakkowa masu karatu Rahoto.
Wani farin Mutumi ne ya fito wanda baze wuce shekaru Sittin ba a duniya (60years) Sanye cikin wata dakakkiyar Suite Baƙa wuluk da ita se ɗaukar idanu takeyi, tafiya kawai yakeyi Fuskarsa a tamke babu Annuri, inda bodyguards ɗinsa majiya ƙarfi kimanin Mutum biyar suke take masa baya harya ƙaraso ga ƴan jaridar, nan da nan Sukayi masa caa tamkar ƙudajen da sukai arba da Buhun Sikari abinka da babban mutum kuma me wahalar gani
Kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci irin tashin hankalin dayake ciki duk a sanadin Ɓatan tilon ɗansa tsahon wata Uku babu wata ƙwaƙƙwarar magana akan yaron, cikeda Damuwa Dattijon ya sauke glass ɗin dake idanunsa ya fuskanci, wani irin takaici ne ya ƙara samun muhalli a zuciyarsa sabida besan abinda ƴan jaridar nan suke nema dashi ba, wannan wace irin masiface ??
A halin dayake ciki a yanzu bayajin zasu iya samun koda kalma ɗaya daga gareshi, Wata matashiyar yarinya ce ta fito daga Companyn itama sanye da Suite Royal blue riga da wando, ƙafarta sanye take cikin wani dogon takalmi me tsinin gaske ta sanya wata irin hula wadda tafi kamada ta mata ƴan ƙwalisa, inda ta rufe idanunta a cikin wani baƙin glass wanda ya mamaye rabin Fuskarta.
A ƙasaice take takowa harta ƙaraso inda ƴan jaridar suke ta tsaya daga gefan Dattijon tace "duk wanda keda burin yiwa Mahaifina tambaya toya dunƙuleta a guri guda ya faɗeta don bamuda lokacin ɓatawa, sannan ta kalli Mahaifin nata tayi murmushi tace "Abie ya kamata kayi magana dasu koda kaɗan ne.
Cikeda ƙosawa ya dubeta yace "Fadilah I can't say anything about my son at this moment, please tell them to leave Don Allah ya faɗa yayin da aka buɗe masa mota ya shiga sukabar harabar gurin zuciyarsa a cike tab da kewar Ɗansa.
*_Thank yo so much my dearest sister's, wllh har zuciyata nakejin dadin comment ɗinku akan wannan littafin, ngde sosai da qaunarku gareni sonso fisabilillah❤_*
Sushmah💋
[3/3, 5:23 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*_Page : 10 - 11_*
*_Naji qorafin wasu daga cikin masu bin wannan littafin kan cewar typing Error yanayin yawa, to magana ta gaskiya sedai ince kuyi haquri dani a haka amma maganar Editing kam bazan iyayi muku shi ba, sabida a kwai abubuwa masu yawa dake gabana a halin yanzu. Ina muku sonso Fisabilillah duk masu bin wannan lottafi 🥰_*
*_WRITING BY: CHUBAƊO_*
____✍️Sam ba haka Fadilah taso ba taso Ace Abie yayi magana da ƴan jaridar a ƙalla ta samu Sunanta itama ya ɗagu a duniya kamar na YayantA Muzaffar, tsaki taja lokaci guda kuma ta faɗa motar dake bayan ta Abie sukabar harabar Companyn
A cikin wata ukun da suka shuɗe na ɓatan MUZAFFAR ABDULWAHAB ABDULLAH THE C.E.O OF ZAFAR ENTERPRISES, ba ƙaramin girgiza Al'uma abin yayi ba abinka da masu hannu da shuni duk sanda ka kunna Redio da gidajen talabijin koda yaushe zancen akeyi tareda yaɗa hotunansa a shafukan sada Zumunta, koda yaushe zancen akeyi tamkar baza'a dena ba amma still babu wanda yaji labarin sa kokuma wata ƙwaƙƙwarar magana a kansa.
MAITAMA WUSE II ABUJA
Unguwace data haɗa manyan Ginagine na alfarma hakakuma wadda aka ƙawata da abubuwa dayawa na jin daɗin Rayuwa a gurin, duk wanda kagani a gurin tofa yaci ya tara dukiya ne ba kaɗan ba, a haka motocin daƙe ɗauke da tambarin Sunan Alhaji Abdulwahab Abdullah suka sulalo cikin Unguwar suna masu tsala gudu, a gaban wani tangamemen gida suka tsaya lokaci guda kuma suka zabga uban horn Get ɗin da kansa ya wangale kansa sannan suka danna hancinan Motocin zuwa cikin babbar harabar gidan wadda taji kayayyakin ƙawa na ban mamaki.
Fitowa sukai da Sauri Guards ɗin suna masu Azamar buɗewa me gidan nasu ƙofa ya fito, Direct ƙofar dazata sadashi da maine Perlour ɗin dake gidan ya nufa still damuwa kwance akan Fuskarsa, Hajiya Sakinah ce zaune kan ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman manyan Royal chairs ɗin dake falon hannunta ɗauke da Rumote tana kallon abinda ke faruwa a duniya, kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci tana cikin babban tashin hankali mara misaltuwa, da hanzari ta miƙe ta nufi me gidan nata idanunta na shirin kawo ƙwalla tace "Abie har yanzu babu wani labari akan Muzaffar?
Kasa ce mata komai yayi sabida damuwa lokaci guda ya zube akan ɗaya daga cikin kujerun dake falon yace "har yanzu babu wani labari Sakinah wllh inaji a jikina tamkar wani babban lamari ya faru da yarona! Kullum bana iya bacci sabida tunanin Halin dayake ciki, jiya naje mun zauna da IG akan lamarin yace zasu ƙara tsaurara bin ciki wllh Hajiya Sakina tabbas nima kuna dabda Rasani muddin Ba'aga Muzaffar ba.. Ya faɗa yana dafe kansa da a lokaci guda sabida wani irin Sara masa da kan yayi
Ƙwalla ce ta taru a idanun Hajiya Sakinah lokaci guda kuma suka zubo sannan ta zube a gaban Abie tace "Haba Abie kaifa musulmi ne ya kamata kayi imani akan dukkan abinda Allah ya aiko maka, muzaffar fa ba ɗanka bane kaikaɗai nima kaina ɗana ne amma meyasa kakeso ka dinga nuna gazawarka a gabana ne shin baka tunani akan tawa damuwar ne?
Kasa bata Amsa yayi har Fadilah ta shigo Falon kanta tsaye ta zauna daga gefan Abie batareda tace dasu ƙala ba. Wata uwar Harara Hajiya Sakinah ta sakarma Fadilah Sannan tace "waike meyake damun tunaninki ne Fadilah?
"wannan wace irin shiga ce haka sekace ɗiyar Kafurai? Har zuwa wani lokaci zaki ɗauka a haka kafin kiyiwa kanki faɗa a Rayuwarki?
"kai Momy Don Allah to meye aibun shigar tawa ?
"Uwarki ce aibun ai, nace Uwarki ce aibun Fadilah. Momy ta katseta ta hanyar faɗar hakan sannan ta ƙara da cewa "bazance komai ba a kanki tunda Allah ma sheda ne akan irin tarbiyar dana baki, yanzu ke don Allah ko kunya bakiji ba Ace ɗan uwanki namiji Guda ɗaya tilo yau an nemeshi an rasa tsahon wata huɗu kenan amma ke kina nan kina yawo a gari da shigar ƴan iska?
"anya kuwa Fadilah Rayuwa zatayu miki a haka kuwa?
Miƙewa Fadilah tayi tana tura baki tabar Falon tana faɗin "aini dama an daɗe da tsanata a gidan nan kowa yafi fifita Yaya Muzaffar akan kowa da ace nice ma na ɓata I'm sure of that wllh babu wanda ze damu irin haka daga ke har Abie ɗin. Ta faɗa tana biga ƙofar glass ɗin dake falon
Da ido kawai iyayen nata suka bita batareda iya furta komai ba.
GYAMBU RUGAR ARƊO
A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau Matashin ya cika wata Uku cur a Gidan moddibo cikin ikon Allah ya samu sauqi sosai, a ɗan watannin daya shafe taredasu yasa har ya canzawa Modibbo matsayi daga wanta ya taimaki Rayuwarsa zuwa muhalli na Uba, tabbas moddibo mutum ne na musamman wanda ya kamata ya bawa muhali mafi daraja daga zuciyarsa, sabida Samun irinsu a wannan lokacin abune mawuyaci
A ɗan zaman dayayi dasu ya ƙara ilimi akan zamanta kewar Rayuwar duniya musamman ta ɓangaren mu'amala da jama'a
Rabe ce ta fito ɗauke da babbar Fanteka zataje ɗebo Ruwa, a zaune ta samu Muhammad Ali ya zubawa Shanun dake cikin garkensu idanu tamkar me nazari akan wani abu, harta ƙaraso gurin besan tazo ba hakanne yasa ta ɗauki wani ƙaramin sanda ta jefa masa.
Miƙewa yayi da Sauri yana kallonta sannan ya Haɗe Rai yace "what's that does mean? Tsaki yaɗan ja sabida sanin ba gane abida ya faɗa take ba common Hausa ma wani abun se yayi da gaske sannan take Fahimta balle kuma turanci sannan yace "meye haka ?
Dariya tayi har seda beauty point ɗinta suka lotsa sannan tace "kawai na gwadaka ne don na gane ko kanada tsoro
Turo baki yayi yana kallonta sannan yayi murmushi yace "ni sam ba matsoraci bane I'm a hero. Ya faɗa yana ɗaga mata hannayensa duka biyu Sama
Dariya ta sakeyi sannan ta ƙurawa bayan sa idanu batareda tace dashi ƙala ba. Ɗagowa yayi yana kalonta yace "meye kike kallo haka?
Ɗaga kafaɗunta tayi sannan tace " ba komai kawai Gizo-Gizo nakuma shaquwa na gani a kan rigarka ta baya.
Ihu ya saka yana tsalle lokaci guda kuma ya faɗo kanta suka faɗi ƙasa still yana zuba mata ihun likaci guda kuma ya ƙanƙameta yana Rintse idanu.
Tureshi tayi da Sauri lokaci guda kuma ta miƙe tana karkaɗe jikinta ta ɗauki Fantekarta ta nufi Hanyar Rafi tana me ƙyalkyala masa dariya.
Tsaki yayi lokacin daya kalli gwiwar hannunsa yaga yaji ciwo kaɗan jini na fitowa kaɗan-kaɗan abinda da Ajebo 😂
Bayanta yabi fuskarsa a ɗaure treda ƙudurtawa kansa cewar seya Rama abinda tayi masa, a haka har duka ɗebo Ruwan suka ɗauki hanyar komawa gida, tafiya kawai suke bame cewa wani ƙala a tsakaninsu har suka iso hanyar data raba Rugarsu Rabe da kuma tasu Bamanga.
Lokaci Guda sukaga an kewayesu, Bamanga ne dashi da jama'arsa ko wanne hannunsa ɗauke da Sandar gado lol
Ɗaure Fuska Rabe tayi tana kallon Bamanga cikin harshen fulatanci tace "meye haka zakuzo ku tare mana hanya kamar wasu ƴan Daba?
Kallon Tsaf Bamanga yayi mata Sannan yace "yanzu ke har kinada bakin magana akan na tareku? Yau kwa nawa kenan ina zuwa gidanku kullum seki ce min in tafi baki da lfy Ashe wannan Kaɗon shine ciwon dake hanaki fitowa gurina ? Bamanga ya faɗa yana nuna Matashin dake gefan Rabe a tsaye yana kallon ikon Allah.
A ƙarshe da abin ya isheshi Fantekar Ruwan yasa Hannu a kanta ya ɗauke sannan ya kalleta yace "if you handle the game with this guy you will meet me at home ya faɗa yana barin gurin gabaɗaya
Be jima da tafiya ba Rabe tabi bayansa da gudu lokaci guda Su Bamanga suka bita da idanu baki a Sake.
A iya ɗan wannan lokacin da suka kwashe tare da Rabe za'a iya cewa a kwai shaƙuwa metarin yawa wadda ta samu gurbin shiga tsakanin SuRabe sedai bazamu fassara shaƙuwar da sunan syayyah ba, sedai kawai mu kirata da sunan ƴan uwantaka sabida a tsarin matashin babu batun soyayya a lamarin sa.
Wannan shi bahaushe ke kirada sabo tirken wawa, a haka suka shafe kwanaki a ƙarƙashin muhali guda ɗaya
Sosai yakejin daɗin Rayuwar gurin sedai har cikin Zuciyarsa yana kewar Mahaifinsa da mahaifiyarsa, idan tunanin ya isheshi se kawai yabi Rabe su tafi kiwo, sosai yakejin daɗin hakan har zuciyarsa
******
*BAYAN SATI BIYU*
Washe garin da safe moddibo ya gama haɗa masa komai nasa wanda ya tsinceshi dashi saɓanin Rigarsa wanda jini ya ɓata da kuma yagewar dake jikinta yasa moddibo ya jefar tun a washe garin Ranar daya tsince shi, Wata Rigar Farin Saƙi irin tasu ta Fulani ya Ɗakko masa tareda miƙa masa yace "karɓi ka sanya a jikin ka tare da wandon shaddar taka na tabbata wata rana a ƙalla idan ka kalli Rigar zaka tuna damu.
karɓar rigar matashin yayi ya sanya a jikinsa lokaci guda kuma ya maida kallonsa ga Moddibo, ba ƙaramin kyau Rigar tayi masa ba domin kuwa tsayawa faɗin irin kyan datayi masa ma ɓata lokaci ne
Bayan ya gama ne moddibo yay gyaran murya irin nasu na dattijawa ya kalli matashin yace "yaro yau dai gashi ka warke cikin ikon Allah bayan doguwar jinyar ɗakasha a tareda mu yau gashi har kana shirin tafiya, sedai kuma har yau bamu San Ainihin kokai waye ba, se nake ganin a yanda mukai sabo dakai ya kamata musan koda kaɗan ne daga tarihin Rayuwarka ko babu komai m ƙulla zumunci.
Sabida wata rana bamu San a inda zamu sake haduwa da juna ba!
Sosai kalaman moddibo suka taɓashi dan harga Allah yanajin tsohon a Ransa, tabbas gaskiya ya fada
Ya kamata ya gaya musu ko shi ɗin wanene.
Murmushi yayi sannan yace " sunana Muzaffar Abdulwahab Abdullah the C.e.o of zafar Enterprises .....!
Sushmah 💋
[3/3, 5:23 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*_Page :12-13_*
*_WRITING BY: CHUBAƊO_*
____✍️"Ni ɗane ga Abdulwahab Abdullah, mu uku kawai Mahaifinmu ya haifa kaf cikinsu nine babba se Fadilah Sannan zainab, ni kaɗaine Namiji kuma wanda ke jan ragamar kamfanoninsa dake nan gida Nigeria harma dana ƙasashen waje. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ƙara da cewa
"mahaifina Haifaffan Garin kano ne a unguwar Hotoro Su biyu ne kaɗai a gurin iyayensu dashida ƙanwarsa Asma'u muna kiranta da Mama.
Mahaifinsu Shahararren ɗan kasuwa ne sosai, wanda ya kasance kaf garin na kano ana matiƙar jidashi a ɓangaren shaharar kasuwanci, ya Rasu yabar duniya a lokacin da Mahaifina yake dabda kammala karatunsa na Scondry school inda Asma'u kuma take dabda shiga sas 2, bayan Rasuwar kakana ba jimawa Itama mahaifiyarsu ta bishi sakamakon Ciwon zuciya, bayan Rasuwar Hajiya da kimanin shekara 2 Mahaifina ya fara tasowa sosai a ɓangaren Kasuwanci sabida yanda Allah ya sanyawa dukiyar Albarka, cikin ƙanƙanin lokaci Sunansa ya zarta na Mahaifinsa a fanin shahara a duniya, bayan Asma'u tayi Aure ne ta buƙaci da A raba musu gado
Sosai Mahaifina ya nuna mata rashin dacewar hakan amma sam taƙi fahimta dole yasa ya amince da abinda tazo dashi ɗin kuma ya yakai maganar kotun Musulunci dake Kano aka raba musu gadon, bayan an Raba musu gado dashida Ƙanwarsa Asma'u Itama ta fara business da kuɗaɗenta sedai bata ɗauki lokaci me tsaho ba jarin nata ya karye, shiko Mahaifina tamkar ana ƙara ɗagashi haka dukiyar ta dinga haɓaka sedai sam hakan besa ya canzawa ƙanwar tasa ba yana matiƙar sonta sosai sabida shikaɗaine ya Rage mata a Rayuwa don haka dole ne ya kyautata mata.
Koda Muzaffar yazo nan a zancensa seya kalli moddibo yace "baba wannan shine tarihina a taƙaice.
Zuru Moddibo yayi masa yana kallonsa cikeda Rashin Fahimta yace "har yanzu yaro baka sanar dani abinda nake son ji a tareda kai ba, kana so ka gaya min cewar dama ba Sunan ka muhammad Ali ba kamar yanda ka gayamin a baya ba?
"Meyasa ka zaɓi hanyar yaudarata bayan nida zuciya ɗaya na zauna dakai?
Jikin Muzaffar ba ƙaramin sanyi yayi ba sannan yace "don Allah ka gafarce ni Baba karkaga laifin pls, ni mutum ne me mu'amala da mutane kala-kala a hakan kuma wanda ake farautar Rayuwarsa ta ɓangarori da dama, shin laifi ne don nayi ƙaryadon na kare kai na?
"a'a yaro sam ba laifi kayi ba indai har ta fuskar tsaron lfyar ka ne, amma ta wata fuskar tabbas ka cutar da yarda ta a gareka. "aa don Allah baba karkace haka wllh bada nufi nayi ba amma tabbas nasan nan gaba zaka Fahimceni akan manufata na ɓoye maka Asalina! Modibbo yay Ajiyar zuciya yace "Shikenan na karɓi Uzirinka sannan innai maka fatan Alkhairi a Rayuwark ta gaba, sedai kafin ka tafi zan baka wata babbar gudun mawa wadda nake da tabbacin cewar zata taimakeka da izinin Allah koda ko wani irin yanayi zaka shiga. Moddibo ya faɗi hakan a lokacin dayake miƙawa Muzaffar wani jiƙo dake cikin ƙaramin ƙoƙo ya shanye.
Seda ya shanye tass sannan ya kalleshi yace "Baba wannan maganin na menene ? Moddibo ya kalleshi yace "maganin tsarin jiki ne dana gajeshi a gurin mahaifina wanda ya gargaɗeni kan cewar kar in badashi ga kowa se wanda naji zuciyata ta Amince dashi sannan zan iya badashi, har A raina nakejin cewar na yarda dakai shiyasa ma harna baka wannan dafa'in namu na gado wanda nakeda tabbacin cewar zakaga amfaninsa a gaba koda kuwa banan kusa bane, nidai nasihata a gareka shine ka riƙe Gaskiya da kuma amana karka taɓa bari zuciyarka ta ruɗeka ka cutar da wanda yayarda dakai komai rintsi.
Sosai jikinsa yay sanyi da kalaman Moddibo dan haka ba tareda zato ko tsammani ba yay jashi jikinsa ya Rungumeshi yanajin wani iri a zuciyarsa wanda ke kamada yanayi na kewa.
Zare jikinsa yayai daga na muzaffar sannan ya ɗau Boron Maganinsa yayi waje abinsa ba tareda yace dashi ƙala ba, shima muzaffar ɗin fita yayi waje seda ya ɗauki lokaci me tsayi sannan ya koma cikin gidan a ciki suka haɗu da Rabe tana ƙoƙarin shiga ɗakin Moddibo, bin bayanta yayi shima
Yana shiga ya nemi guri ya zauna itama zaman tayi tunda ta zauna take kallon sa tun be lura ba har ya ya fahimci irin kallon da take masa, amma seya share sabda yasan indai ya kalleta dena kallon sa zatayi, shi kuma haka kawai yaji baya so ta dena kallon nasa, haka kawai yaji yana son hakan har cikin Randa.
Ta jima tana aikin kallon sa sannan ya dago idanunsun ya sarƙe cikin na juna kashe mata ido,
Da sauri tayi ƙasa da idanunta sbda wani irin kwarjini dataga yayi mata bugu da qarima ga kashe mata idon dayayi.
Abine ya bashi dariya sosai sannan yace" o'o yau na kama Fulani Girl tana satar kallona da alama she wants to say something oya say it. Ya faɗa yana wani kallonta
Kasa ɗagowa tayi haka kawai setaji tanajin kunyarsa dukda irin damuwar dake Ranta akan tafiyarsa, kamar me koyon magana haka ta fuɗe baki tace "meyasa zaka tafi bayan mun saba dakai?
Ɗan jim yayi yana kallon gefanta kaɗan sannan yace "sabida inaso naje namu gidan nima naga iyayena I'm sure of that Suna nan suna nemana wata ƙilama har abinci basa ci. Faɗa fuskarsa na sauyawa
"Nasan suma zasu shiga damuwa duk a rashin ganinka da basayi, na tabbata muma irin damuwar zamu shiga a sanadin sabon da mukayi dakai. Rabe ta faɗi hakan hawaye na taruwa a manyan fararan idanunta
Kasa ce mata komai yayi hakan yasa ta kalleshi tace "meyasa ka ɓoye mana gaskiyar sunan ka?
Kallonta yayi yace "sabida lokacinda ya kamata ku sani beyi ba shiyasa.
Kallonsa kawai takeyi a ranta tana mamakin halinsa, yanzun nan ze sake dakai har kuyi hira amma lokaci guda seya gimtse kamar bashi ba, taɓe baki tayi tace "inaso nasan sunan naka da bakaso a sani?
A taƙaice yace "Muzaffar Abdulwahab Abdullah.
Kallonsa tayi tareda wara manyan idanunta tace "gaskiya sunanka yanada tsayi sosai zan iya kiranka da Zafar?
Kallonta kawai yake harta kai ƙarshen maganar sannan ya sauke numfashi yace "As you wish
Bata sake cewa komai ba tayi shiru wanda hakan ya bashi tabbaci akan cewar bata cikin yanayi me daɗi
Jikinsa a mace ya kalleta yace"wllh bana so ki dinga sa damuwa a ranki gameda tafiya ta nace miki idan na tafi zan dawo wani lokacin bazan daɗe ba kodan sabida ke.
Ya ƙare maganar tare da nuna ta da hannunsa
Sosai maganarsa tayi mata daɗi har hakan yasa ta saki murmushin daya ƙara baiyana kyawunta sannan tace "na yarda dakai yaya zafar! Nasan bazaka manta dani ba kuma nima bazan manta dakai ba zafar komai yawan shekarun daza'ayi nan gaba.
Da sauri ya kalleta a ransa yana mamakikn yarinyar, wayonta da maganganunta ya zarta shekarunta da ace zata samu wayewa a tareda ita tabbas da anyi cikakkiyar ƴar baiwa a nan wajen iya tsara magana cikin hikima.
A nitse ta kalleshi tace Hamma zafar idan ka tafi zanyi kewarka sosai bazan gaji da gayamaka cewar na saba dakai ba koda zan maimaita shekarun haihuwata ne ina faɗa maka, ni kaina bansan dalilin daya sa nake jin zafin tafiyarka a raina ba zafar!
Sosai yake kallon ta tunda ta fara magana sannan yace"ni kaina Ina jinki a raina Rabi'atu! Ta yanda har nake jin bana so na tafi na barki a nan! Har ga Allah naji jini na ya hadu dake, bama Iya nanan abin ya tsayaba kinada gurbi a zuciyata kamar yanda Zainab take da muƙami a cikim Raina!
Kamar daga sama yaji ta jefo masa tambaya tace "wacece Zainab?
Murmushin gefan baki yayi yace "she's my younger sister, inasonta Sosai sabida tana iya haƙura da komai don tabbatuwar farin cikina, shiyasa nakeji da ida Except Fadilah.
Taɓe baki tayi sannan ta kauda kanta don harga Allah ba gane maganarsa take sosai ba, abu ɗaya kawai ta gane shine ƙanwarsa ce.
Murmushi kawai yayi sannan yacigaba da cewa "duk duniyar nan Bayan Abie da Momy tareda sauran ƙannena babu wanda ya samu kusanci dani se ke! Dan haka kina da matsayi na musamman a zuciyar Muzaffar Abdulwahab Abdullah.
Yanda ta nutsu tana sauraransa seka rantse tana fahimtar abinda yake faɗa mata , ta Daɗe tana juya abin a ranta daga ƙarshe data kasa gane manufarsa seta jefa masa tambayar datasa har seda ya ɗago ya kalleta tace "Hamma zafar dama ana Iya bawa mutum matsayi a zuciya?
Da sauri ya ɗauke kansa daga barin kallonta sannan yace " a'a ba'ayi kawai dai na faɗa ne nima. suna cikin maganar Laure ta bankade ƙofar ɗakin tace "to tsinanniya fito nan kiyi min aiki
Kin shige ɗaki da garjejen namijin da a tsaye yafi ubanki ƙirar ƙarfi da tsayi kuna lalata, in banda masifa da jaraba irinta yaran zamani inake ina wannan gabjejen ƙato wanda ko babbar macen kirki ma setaci baƙar wuya a hannunsa Amma dan rashin kunya se liqe masa kike yi se kace ba BAFULATANA ba !
Shegiya me bin maza karuwan wofi.
sosai abin yayiwa muzaffar zafi a rai dukda bada hausa tayi maganar ba ya fahimci komai, amma seya danne zuciyar sa yay kamar be gane abinda take faɗa ɗin ba.
Rabe kuwa banda kuka ba abinda takeyi sabida zafin da kalaman inna Laure sukayi mata a zuciyarta, Sarai tasan abinda bin maza ke nufi dukda ƙarancin shekarun ta.
A hankali ya matasa kusa da ita yana kallonta yace "kiyi haƙuri Rabi'atou insha Allah wata rana se labari.
Taɓe baki Laure tayi sannan ta karkace ta dinga zuba tijara sannan ta fice ta bar musu dakin!
Sosai abin ya batawa muzaffar rai dan haka ya kasa cewa komai, cikin tatatausan lafazi yace " tashi kije ki shirya mutafi kiwo.
Tana jinsa amma setayi kamar bataji me yace ba ta cigaba da kukanta, sosai kukanta yake taba zuciyarsa amma yayi shiru yana kallonta
Dan kanta ta rarrashi kanta tayi shiru, a haka moddibo yay sallama a ƙofar ɗakin sannan ya shigo, kokaɗan beyi mamakin ganin su a tare ba sabda hakan sam ba sabon Abu bane,
Da gudu Rabe ta ta nufi Baban nata ta rungumeshi se kuma ta sake fashewa da wani sabon kuka. cike da damuwa moddibo ya ɗagota yana kallon fiskarta yace "meya faru kuma ?
Bata CE komaiba sabda kukan daya ci ƙarfin ta, bataso ta sanar dashi abinda inna laure tayi mata shiyasa tayi saurin nuna muzaffar da hannunta wanda ke tsaye daga gefe tace "baba yaya zafar ne yake faɗamin wai zetafi Gidan su ya barmu! ta ƙarashe mganar tana kuka.
Murmushi moddibo yayi sannan ya dafa Kafadunta yace " haba kekuwa meyasa zakiyi haka?
Kadafa ki manta ke ɗin ƙanwarsa ce dole wata rana ze sake zuwa kodan ya ganki dan haka ki dena kuka kinji?
Da sauri ta daga kanta alamar ta yarda da batun Baban nata, dan hka ta share hawayenta sannan ta koma kusa da muzaffar tace "Hamma Zafar baba yace "zaka dawo wata rana dan haka bazan sake kuka ba sbda babana baya min ƙarya komai ya fadamin gaskiya nake daukar sa.
tunda ta fara maganar muzaffar ke kallonta sosai yake nazarin yarinyar gata karama amma tana da kaifin tunani wannan idan ta kai shekara 20 yazata kasance?
Lallai Rabi'atu tana da wayo kuma yana jinjina irin soyayyah dake tsakanin ta da mahaifin ta,
Murmushi yayi mata tare da Jan hancinta da hannunsa dikansu sukayi dariya sannan suka yiwa moddibo Sallanar sesun dawo sannan suka wuce kiwo ita da Muzaffar.
*******
*_MUMBAI BABBAN BIRNIN ƘASAR INDIA_*
ƙarfe 8:00 na dare agogon ƙasar ya buga, wata hamshaƙiyar matace ke Sakkowa daga saman benan dake cikin wani ƙayataccen falo wanda yafi kamada aljannar duniya kunnenta ɗauke da wayarta ƙirar Iphone da alama waya takeyi, a hankali take sakkowa cikin isa da ƙasaita hannunta jere da wasu murɗaɗɗun zobuna na zinare, sanye taƙe cikin doguwar rigar less ɗan ubansu wanda yaji uban stones a jikinsa a haka harta iso cikin falon ta zauna. Daga ɓangaren Abie yace "Aisha lallai ya kamata komai yazo ƙarshe wllh na gaji da zaman nan naki a wata ƙasar ta daban don haka a cikin satin nan ya kamata ki dawo ƙarsarmu ta haihuwa mu zauna tare a nan cikin iyalai na.
Ɗaure Fuska Hajiya Aisha tayi sannan tace "ina me baka haƙurin sanar dakai cewar bazan iya barin ƙasar india in dawo Nigeria ba, ina ganin gara ba baka lokaci ka samu kayi tunani akan maganata wata ƙila zaka sakko muci gaba da zama kamar da, amma idan na dawo Nigeria waze cigaba da gudanar da lamari Zafar Enterprises ?
Kasa magana Abie yayi ya katse kiran sabida takaicin ta, wani irin abu yaji yana taso masa wanda yafi kamada na ɓacin rai sannan ya jefar da wayar a gefanta.
*_ABUJA NIGERIA_*
ɓangaren Abie kuwa daƙar ya iya miƙewa ya nufi toilet donya watsa ruwa , gabaɗaya tunaninsa ya tsaya cak babu wani abu dakeyi masa daɗi komai ya fice masa a rai, a dadafe yayi wankan ya fito cikin mintunan da bazasu gaza goma ba ya gama shiryawa cikin riga da wando na farar shadda ayi mata ɗinki irin nasu na manyan masu Hannu da farcen Susa, ba laifi kayan sun masa kyau dik da irin ramar dake kan fuskarsa da gangar jikinsa, kana kallon sa zaka fahimci baya cikin kwanciyar hankali a haka ya fito daga part ɗinsa cikin shirin fita, Momy ya samu zaune a falo se fadilah da Zainab wadda ke zaune kusa da momy duk lamarin Duniya ya isheta.
Remote Fadilah ta ɗauka tana ƙoƙarin Kunna Ƙatuwa Tv bangon dake falon tamkar ba Ɗan uwanta ciki ɗaya ake shelar nema ba a kafafen yaɗa labarai da duk wani saƙo da lungu dake duniya ba
Kallonta kawai Abie keyi zuciyarsa na tafarfasa yace "bazance miki komai ba Fadilah ma na tabbatarwa da kaina cewar sena shata miki layi da komai nawa sannan zaki shiga taitayinki. Abie ya faɗi hakan zuciyasa na zafi akan Halaiyar Fadilah
Ficewa yayi daga falon harya fito harabar gidan Guards ɗinsa suka buɗe masa ƙofa sannan Driver yaja motar sauran suka mara musu baya suka ɗauki hanyar gidan IG
Momy najin fitarsa Wasu zafafan Hawaye suka shiga zubo Mata tana kallon Fadilah
A fisace Zainab ta tashi itama tana kallon Fadilah tace "ban taɓa ganin irin wannan haukan ba wllh se'a kanki Fadilah, wannan wani irin Rashin imani kike dashi?
Karfa ki manta Yaya ɗan uwa ki ne Uwa ɗaya uba ɗaya amma kuma kike gwada masa wannan ƙiyayyar ta ba gaira ba dalili? Wllh ban taɓa ganin hka ba se'a Kanki wai ace mutum yana girma amma yana rasa hankali.. Zainab ta faɗa yayin da take kallon Fadilah tana huci
Gadan-Gadan Fadilah tai kanta Hannunta ɗauke da Cokali me yatsu lokaci guda kuma zainab ta Saki ƙara..
.
*_Wllh Biki su Chubaɗo suke daƙyar ma ta iya zama tayi muku wannan page ɗin, fatan zakuyi min Uziri🥰_*
Comment
Nd
Share
Sushmah💋
[3/3, 5:23 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*_Page :14_*
*_WRITING BY: CHUBAƊO_*
____✍️Miƙewa momy tayi a fusace ta nufi Fadilah da ƙarfin tsiya ta ɓanɓare Zainab wadda ke kuka ta ɗauke fuskar Fadilah da kyakkyawan mari wanda yasa har seda taga taurari sannan ta nunata da yatsa tace "don uwarki nan gaba seki san irin Rashin tarbiyar dazakiyi a gabana, wllh Fadilah na fara tantama a kanki anya kuwa ke jinina ce?
Ɗagowa Fadilah tayi da jajayen idanunta tana kallon Momy hawaye na zubo mata tace "Momy yau ni kika mara akan Zainaba?
A fusace tace "na mareki Fadilah wllh muddin kikaci gaba dayin irin wannan rashin tarbiyar senayi miki abinda yafi haka muni ma.
Momy ta faɗi hakan a fusace sannan taja hannun Zainab suka bar mata falon, sosai hakan yayiwa Fadilah Zafi a rai lokaci kuda kuma ta kife akan ɗaya daga cikin kujerun dake falon ta dinga gurzar kuka kamar wadda uwarta ta mutu.
Ɓangaren Dady kuwa Direct office ɗin IG ya nufa, cikeda damuwa ya fuskanceshi yace "na rasa abinda yake min daɗi a cikin wannan duniyar IG komai ya tsayamin cak har yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar magana akan ɓatan ɗana kullum abu guda kake gayamin zakuyi bincikd. Dafa kafaɗunsa Dady IG yayi sannan yace "Haba abokina karka wuce iyaka a maganarka mana, kada ka manta Allah kan jarraba imaninmu ta ɓangarori dadama wata ƙila ya ɗauke ɗanka yayi nisa dashi daga gareka donya gwada imanin ka ne. Na tabbata dukk irin son da kakeyiwa Muzaffar da irin nuna damuwarka akansa Bakai rabin irin damuwar da Annabi Ishaq (A.s) ya shigaba a lokacin da ɗansa Yusuf (A.s) ya ɓata ba, amma kuma dayay haƙuri da jarrabawar data sameshi na ɓatan ɗansa wani sakamako ya samu a sanadin haƙurin dayayi?
Sosai jikin Dady yay masifar sanyi a sanadin maganar IG, cikeda jin kunyar kansa ya ɗaga kai sama yace "ya ubangijina ka gafarta min kuskurena a gareka Bisaga Rauni na ya Allah, sannan ka baiyana min ɗana a ɗuk inda yake ko a mace ko a raye ya Arahmurrahimin!
Da Ameen IG y amsa sannan ya dubi abokin nasa yace "insha Allah zamu ganshi da ikon Allah, sannan zamu ƙara faɗaɗa binkicen mu a jahohi daban daban fatana kawai a gareka shine ka ƙara haƙuri na ɗan lokaci insha Allah komai zeyi dedai.
Shawarwari IG ya dinga bawa Dady daga bisani kuma sukai sallama da juna.
*_RUGAR ARƊO (Taraba State)_*
Zaune suke cikin Dajin da suka kutsa tareda dabbobinsu Rabe ta kalli muzaffar tace "ina cikin farin ciki sosai yau. Murmushi yayi sannan yace "meyasa kike farin cikin? Ya faɗi hakan yana kallonta
Sinkuyar da kanta ƙasa tayi tace "Sabida ka biyoni kiwo a Rana ta ƙarshe wadda bayan ita banida tabbacin cewar zan sake ganinka, ni'a ganina wannan babbar nasara ce dana samu a Rayuwata a zamantakewar da mukayi dakai don Allah Hamma Xafar idan ka koma Gidanku Karka manta Dani!!!!!
Tunda ta fara maganar yake kallonta tareda maida duk wani hankaƙinsa a gareta sannan yace "a duk irin jerin mutanan da kika fassara Muzaffar a fanin zamantakewarsa dake to'a irin yanayin zaki sameshi don haka abinda kike fata na karna manta dake Tabbataccen al'amari ne wanda ke gudana a tsakanina dake Rabi'atou, kada ki manta cewar kefa ƙanwata ce dole watarana koban dawo sabida kowa ba zan dawo Sabida ke. Ya faɗa yana kallon tsakiyar ƙwayar idanunta
A haka dai kiwon nasu ya kasance har suka dawo gida, tun'a daren Ranar Rabe bata sake shigowa ɗakin ba har Garin Allah ya waye muzaffar ya fara shirin tafiya, ko kaɗan bataso ta haɗu dashi a lokacin tafiyarsa tafi so ta fara koyawa kanta haƙurin Rashinsa a tareda ita. Da wannan Batun ta samarwa kanta matsaya Tun bayan fitowar alfijir datayi Sallar Asuba tayi nesa da Gidan har Muzaffar ya kammala shirinsa ya fito sanye cikin shigar kaya Na farin Saƙi irin na Fulani
Sosai kayan suka karɓi jikinsa tamkar dama can Bafulatanin ne
Har a ransa yaji cewar yanaso ya sake ganinta kafin tafiyarsa amma sam ya kasa tambayar Moddibo ina take, sam beso Sabonsa da ita har yakai wannan matakin ba sabida bayaso zuciyarta takaishi wani matsayi na daban wanda ya wuce na ƴan uwan taka kamar yanda ya ajiyeta a matsayin ƙanwa, shiyasa sam wasu lokutan yake jan baya da ita a irin alkhairan da mahaifinta yayi masa bayaso shaƙuwarsa da ƴar ya Rushe wannan dangantakar a tsakaninsu.
A haka suka fito daga ɗakin har bakin ƙofar bukkar Inna Laure Muzaffar ya tsaya tareda durƙusawa ya kalleta yace "To Inna ni zan wuce gida ina roƙon Allah ya saka muku da alkhairi bisa taimakon da kukayi min a rayuwa ta, a zaman danayi dake idam har na taɓayi miki wani abu mara daɗi don Allah ki gafarce ni pls. Ya faɗa yayinda yake miƙewa daga ƙofar ɗakin ya juya
Taɓe baki Inna laure tayi sannan tace "o'o ɗannan bakamin komai ba, hasalima ni daɗin tafiyar taka nakeji har Raina sabida bansan tsiyar datake tareda kai ba, nida zaka temakeni ma wllh idan ka futa daga Rugar nan ka roƙi Allah mantar dakai hanyar shigowa garin nan gaba ɗaya.
Murmushi kawai yayi sannan yace "insha Allah zanyi Addu'ar amma sedai nace Allah ya mantar dani ƙofar ɗakinki badai ta Rugar nan gabaɗaya ba. Be jira cewarta ba yayi gaba abinsa
Har cikin zuciyar Moddibo yaji tafiyar yaron sabida yanda yakejinsa a Ransa, Babur ɗin malam Iro moddibo ya karɓo Aro sannna ya ɗauki muzaffar a bayan Mashin ɗin suka Tafi donya kaishi tashar dake cikin Gari.
Har tasha yakaishi sannan ya biya masa kuɗin mota ya juya ze tafi, da sauri muzaffar ya biyoshi ya Ringumeshi tareda kama Hannunsa yace "Banida isassun kalmomin dazanyi godiya a gareka Baba amma ina roƙon Allah ya gina maka gida a gidan Aljanna!!
Zare jikinsa Moddibo yayi daga nasa sannan ya juya da Sauri yana hawaye batareda ya juyo ba ya kunna mashin ɗin yabar Gurin muzaffar na kallonsa.
Sosai yaji shima zuciyarsa tayi mugun Rauni amma kuma bashida wani zaɓi dole ne ya koma gida kodan sabida iyayensa da sauran ƴan Uwansa. Yana nan tsaye har motar ta cika suka kama hanyar Abuja zuciyarsa a cike Fal da kewar Fulanin Dajin.......
*_Naga ƙaunar ku da Soyayyarku akan wannan littafi gamida Addu'o'in alkhairinku gareni, thank you all for the Support and Comment ubangiji yabar zumunci_*
Comment
And
Share
0 comments:
Post a Comment