11. GIDAN GANDU by Biebie Isa
Qrfe takwas na safe, Hajia Babba ta farka tayi zumbur zata miqe, ji tayi jikinta ya mata nauyi, ganin Amira tayi kwance kanta da qarfi ta tureta, Amira ta farka ta na soshe soshen idanuwa, ke wani irin bacci mukayi haka? Amira ta kalli agogo ta pashe da daria Baccin awa 12 mukayi kakus, karime ta dafe qirji shkn gari ya waye, ban samu ganin tsoho ba, Amira ta tashi ta kwashe jug din sobonta gami da cewa ke dai kakus wani tsoho ko asuba ba muyi ba?.
Tun daga ranar duk inda Hajia Babba ta sa Qafarta Amira na bayyanta, tayi fadan tayi masifan tayi lallashin amma ta qi rabuwa da ita, daga baya ma tare suka dawo kwana a daki, wai ke meye kike bibiyata haka? Ynx duk inda na sa qafa kina biye dani kamar raqumi da aqala, amira tace ynx kakus har na isheki? To wlh duk inda zaki sai na biki ehe, Da wannan kwafsin da Amira kema hajia babba yasa bata koma gurin bokarta ba…
*******
Duk shirin da Hajia Babba keyi Amira ke rugujewa, don haka yasa ta yanke hukuncin sararawa na dan lokaci kafin ta san abinyi.
*****
1year later
Haka Rayuwa ta kasance cikin gidan M.Zailani, da dadi ba dadi, Har ynx Gaban yan sassan hajia Babba na nan, yan dakin Hajia Ama da na Umma Hajja kadai ke xumunci, yan dakin Hajia Babba daga harara sai hantara sai kuma zagege da gori suke bin yan dakin sassan dasu. A wannan lokacin samarin nan sn gama Service ko wannen su ya fara aiki Garuruwa daban daban, yanmatan kuwa ko wacce na da certificate din Computer skul. Soyyayar su kuwa qara habaka yake da girmama, Har tsoho ya san da soyayyar da suke wa junan su, kuma ya yanke hukuncin aurar dasu ga waenda suke sonsu tunda sun sassanta junan su lokaci kadai yake jira a shafa fatiha.
*****
M.Zailani ya kalli Baba Mudassir Yace kai Mudassiru kira min Zaidu kar ya maidani tsohon banza. Jiki na rawa baba mudassir ya kwada wa Zaid waya, sai da wayar ta kusa tsinkewa kafin ya ansa ds Sallama. Handsfree ya sa Assalam Alaikum Baba barka da marece, tsoho yace Kai Zaidu ka natsu ka san abun da kakeyi, ka dawo gida ga yan uwanka nan shekara daya da yan watanni da dawowansu har sun gama Bautar qasa sun kama aiki kai ka tsaya shashanci, Zaid ya yi daria na yan duniya Tsoho me ran karfe, kaine da kanka?Lallai kunyi kewata, toh su ba su ce maka yanayin karatu na da nasu ba daya bane? Toh karatun likitanci nayi kuma ni course dina shekara 6 ne, Kar ka damu komi yazo qarshe, nagama komai, expect me any time frm now ka fara baza idon ganina, ka gaida mun tsofin Matanka kafin nazo, kafin tsoho yace komai Zaid ya kashe waya tsoho yayi daria yace Shaqiyyi.
*****
Zaune gaban bokanta, cikim damuwa tace Boka, nagaji nagaji nagaji. Aure nake sonyi cikin shekarar nan, ace duk samarina ba na aure? Boka yayi daria, yace diyyan shagali, aike kika watsar da Daman ki, lokacin da ya dace kiyi auren ki ka yi shahadar rabuwa da saurayi me nagarta me hankali, kuma wanda ya yi niyyar aurenki, tayi tagumi tace wai ni kaina, nayi nadamar rabuwa dashi, nayi nadama sosai, haba a ce shekara 2 da rabi na kasa mance shi, sonsa na nan daram a raina, wai ganina saka mai da Alheri shine abun da ya kamata nayi a wannan lokacin, amma yanzu bndamu ba, duk yanda zanyi sai na sameshi ko ta halin qaqa, Boka yace Anya kuwa zaki sameshi iyayenshi tsaye suke kanshi, tace kaii rabani, duba min shi, yana ina? Ina zan sameshi? Boka ya duqufa yana binciken shi, yace Yana nan a qasashen waje, kuma shirin dawowa qasa Nigeria, yana tare da Iyalensa Matar shi Yaransa biyu kuma da Alamu yan biyu ne. Sai ki jira idan sun dawo qasar, sai ki nemeshi ki ga ko zaki samu saa, tace wa? Ai a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, ynx bani adireshin su na chan, boka ya zaro ido yace na Ingilar? Tace ko na sin ne, yayi yan bincike binciken shi kana yace leqa qwaryar nan, ta na leqawa taga Garin da yake da street din da yake har kwanar gidan da cikin gidan ta gani, yauwa boka garqanjo sai kajini, yace toh shkn sai kin dace, tayi daria tace dole ne sai na dace, Badiyyan shagali dagaske kike sai kin sameshi? Ta miqe tare da sabar jakkarta tace da na qyaleshi, amma ynz ba zan qyaleshi ba, ko yaya ne sai na samu ZAID ALI MODIBBO.
12. GIDAN GANDU By Biebee Isa
Zayyad da Rumaisa zaune a parlorn tsoho, Yazayyad na basu labarin London, bini bini suna kallon juna suna aikawa juna saqqonin soyayyah, tsoho na kallonsu yana murmusa wa, salon Soyayyahr ku Rumah na burgeni, ba kwa nuna wa a fili, amma kallo daya na muku na san kuna son junan ku, kuma tabbas kun dace da juba, ko da ba ku fada soyayyar juna ba, ku din dai zan hada don ku haifa mana jikoki masu kunya kamarku, habawa Zayyad kunya Rumah kunya, Maysah ta sadda kanta qasa, shi ko Zayyad sai murmusawa yakeyi, Tsoho yace kunga da Sarkin rashin kunya ne Jawad har kama hannun Bilkisu yakeyi a gabana yana wani karkashe mata ido kamar sabon makaho.Duk suka tintsire da daria, Zayyad yace Tsoho gobe InshaAllah zan koma Kano, don jibi litinin, Tsoho yace Allah shi kaimu, ya maka Albarka ya qara budi, naji dadin Shadar da ka siyo man wlh, Zayyad yace ba komai tsoho, Albarkar muke so, yace kullum muna muku adduar dacewa, Allah ya muku Albarka ya qara hada mun kanku suka amsa da Amin. Yace bari shiga sassan Hajia Ama, yace ba wani kuje dai ku cigaba da soyayyah da sauri Maysah ta fita tana daria.
*****
Yanzu idan ka tafi yaushe zaka dawo? Mua’amar yakalli Hanifa cike da qauna yace i promise u every weekend zaki ganni, kuma sallan matan Abuja su kalle min kai?Kace ka fasa aure na ta fada cikin sigar shagwaba, Amar yayi daria yace hey listen to me, sonki a jinina yake, ba zan taba son kowacce mace ba idan ba Hanifa ta ba,Ba zan iya rayuwar aure da kowacce mace idan ba Hanifa ba, ba zan ma kowacce mace kallon soyayya ba idan ba hanifa ba, farin ciki Mu’ammar Hanifa, sbd haka kisa a ranki Hanifa ta Mu’ammar ce, kuma Mu’ammar na hanifa ne ita kadai ba tare da kowa ba,dnt u eva forget dis,Farin ciki ya mamaye zuciyar Hanifa, Dadi kamar ya kasheta, tace i belive u Ya’ammar,Ta ciro wani dan qaramin Allura, yace Becareful kar ki tsire hannu, tace so nake ka sha jinina, na sha jininki? Wat are u saying, tace by doing dis i will see ur love for me, ya dago ya kalleta yace do i need to drink ur blood to prove my love for you? Ta gyada kai, yace den i will do it, but i dnt want to see u get hurt, tace dont worry its a small prick, ta runtse ido ta chake yatsar ta dan kadan, Yamu’ammar ya sa yatsan ta a bakinshi ya sha jininta har sai da jinin ya tsaya(ewww )Allurar ta miqa mai ya amsa yayi yanda yaga tayi itama ta sha jininshi (wayaga Vampires) lol, ta dago ta ce we are one nothing is going to tear us Apart, murmushi ya mata yace NOTHING.
*****
Fadila ce da Maysah cikin Mota sun dawo daga Sayyayar kayan shafa, fadila ce ke tuqin, a lokaci daya kuma tana waya da Yasuraj, horn tayi Baba maigadi ya wangale gate, ashe lokacin Jawad ne cikin motarshi ya zo fita daga haraban gidan, a zaton ta ita aka bude ma gate, a zaton shi shi aka bude ma gate, kowa ya doso suka ci karo,Fadila ta fito a zafafe, Jawad ya fito a zuciye, Jawad cikin masifa da daga murya yace Ke wace irin mahaukaciya ce? Ba kya ganin me fita ne? Wai wa ma ya baki mota ne iyi? Fadila cikin siririyar muryarta me hade da masifa tace, kai dalla rufawa mutane baki, isit my fault dat u are getting blind? Baka ga shigowa na bane? Rashin haquri Kai kana sauri kafita, to sannu sarkin sauri, Jawad mamaki ya hana shi magana yaga idan be mata dukkan tsiya be yi ba, ya daga hannu zai mareta, tayi saurin cewa babban balaeen chan, wlh tlh ka tabani sai na rama, sai munyi duke duke koni ko kai cikin gidan nan(jimun ikon Allah sai kace wata me qarfi), Jawad ya fara zare belt din jikinshi zai ma fadila duka, da sauri Maysah ta fito, bata zaci abun yayi zafi haka ba, Ta janyeta daga gaban Jawad Haba Fadila wats ur prblm? Yajawad din kike ma tsawa haka, da qarfi fadila tace ma Maysah Quite just shuttup md watch him flog me, Kai kuma idan har baka dakeni ba baka cika Jawad Mudassir Zailani ba, Aikam Jawad ya daga belt zai shauda mata Mu’ammar ya qaraso gun da gudunshi tare da riqe belt din, Ya ja Jawad baya, yace cool down man, ba girmanka bane, huci jawad kawai yakeyi Fadila tace ai da ka bar shi ya daken niko na shayar dashi mamakin rayuwa wlh, Jawad ya zabura Mu’ammar ya riqo shi, wai kai meke damunka ne? Sai kace baka san halin jikokin hajia Ama da umma hajja ba? Ai ba da’a ne dasu ba, basu da kunya, Fadila ta ma Mu’ammar kallon tara saura kwata, tace aiko muke da da’a da kunya, ga babban marasa kunya nan, masoyan ku da Bilkisu da Haneefa, idan kuwa babban mara da’a kuke nema toh ga Amira, jikokin waye? Last i checked jikokin Hajia– maysah tayi sauri rufe mata baki, Ta kalli su, Tace Yajawad, Ya’ammar don Allah kuyi haquri, ba don halin mu ba, Jawad ya yarda belt dinshi, yana ma fadila kallon tsana yace Amar lets go, i dont like dis Girl at all, fadila ta gantsara ma maysah cizo a hannu, maysah ta saketa da sauri tana yarfa hannu, Fadila ta riqe qugu, hey, i dont need–inshort i dont want to be liked by someone like u, as a matter of Fact, i dont like u either, tana kaiwa nan ta ja hannun Maysah ta wurgata cikin mota, ta zagaya ta shiga ta fincike motar ta yi reverse yare da barin unguwar gabaki daya.(Eeelerh u get lever oooo)
13. GIDAN GANDUBy Biebee Isa
Maysah tace ina zaki kaimu? Ki tsaya, Fadila tayi parking tare da sauke ajiyar zuciya, first of all kar da ki qara yi man haka, Shikuma Jawad din ya qara gigin tabani yagani, zan bashi mamaki wlh, Maysah tace kiyi haquri sis let it pass, fadila tace ya wucei, Maysah tace let me drive, ba musu fadila ta fito ta koma sit din Maysah ita kuma ta koma ta shige tare da jansu suka nufa Gida.
*****
Jawad ke hada kayanshi, shi zqi koma Gombe, tunda uwashi ta haifeshi ba a taba Embarassing dinshi haka ba, kamar ace yarinya kamar wannan fadilar ta gaya mai magana be ma ta komai ba? Dole yake barim garin, haka ya bar Gidan be ma kowa Sallama ba har bilkisu. Ba wanda ya san anyi, Mu’ammar be fada ma kowa ba, Maysah ma haka.
Bilkis tayi tayi ya fada mata abin da yasa shi tafiya ya qi fada, sai kuma ta sa kuka wai satin shi 3 bezo weekend ba, gashi yau friday bazaizo ba? Bayason kukanta yace kar k damu zan biyo Jirgi InshaAllah Yau din nan, just to see u, don ni zaman Maid ya Isheni, dadi kamar xai kashe Bilkisu ta shiga kichin don hada ma Yajawad Abinci. Kafin ta shiga ta tsara kwalliya.
******
Badiyya ce ta fito daga Airport din Garin London, kasancewar ba yau ne ta fara zuwa qasar ba, ta sha zuwa da Alhazawarta, Taxi ta tsaida tare da fadawa ciki, tace ya kaita cikin gari, sai da sukayi tafia me nisa kafin ta sauka ta biyashi, sannan ta tsaida wani Taxi din, tace Ya kaita Illford shopping center, ya kaita ta sallameshi, ta shiga ciki, wurin Babban wuri ne, ba shagon da babu, wurin bangaren yara ta nufa, ta siya Toys da kaya, kafin ta matsa ta shiga lodo chocholates, tayi siyayya sosai kuma ta kashe kudi, Fitowa tayi ta tsaida Cab, tace akai ta Rand Street, Ba ajima ba suka iso Unguwar, ta lumshe ido tana tunano kwatancen gidan Zaid Ali a qwaryar boka. Ta na tunowa ta na ma me mota kwatance sai ga su har gaban Gidan, a lokacin har dare ya farayi, ta biyashi tare da kinkimar leda ta yi qofar gidan, hannu ta sa ta danne Bell din.
*****
Wata hadadden yarinya nagani da ba ta wuce 20years ba tsaye kan stool, gaban ta wani ne da alamun dai mijinta ne hadadde ne me cikar kamala, tie ta ke ciremai, shi ko sai kissing kumatunta yakeyi yana mata waqan My short wifey, tana mutsu mutsu tace Yazayd kaga dai ka Bari, sauri nake da wanne zanji da rigiman babies dinka ko da rigiman Ka? A lokacin ta gama kwance tie din, ya sunkuceta cike da so da qauna yace Yarinyata,bazan gaji da fada miki ina sonki ba, i love u so much. Hanyar daki yayi da ita sukaji an dann Bell, Zarah tayi sauko wa daga jikin mijinta, tace I will get dis, i think mummyn becky ce, kaje ka fara shower din kafin nazo, idan kagama ka fara masu Miemee da Biebie, tana fadan hakan ta na tafia don bude qofa, unlocing qofar tayi tare da bude qofar, Gabanta ya yanke ya fadi, mamaki ya cika Zarah, hasken da ta qara besa ta qi ganeta ba Baki na rawa tace Ba–diyyah, Badiyya a ranta tace shegia guntuwa sai kyau take qarawa, a fili kuwa murmushi tayi tace Hello Baby Zarah, its good to see u too, ta raba ta shige gidan tare da barin matar gidan a waje, zarah ta shigo tana qoqarin qaqaro murmushi sannu da zuwa, ta shiga kicin ta kawo mata juice da cookies, Zayd ne ya sauko yana Yarinyata ke da waye? Maman becky– maganar ta maqale a fatar bakinshi sakamakon ganin wata yayi kamar Badiyya, Badiyya ta miqe ta tako kusa dashi, murya qasa qasa tace Hello Luv, Zarah tayi saurin shan gabanta, me ya kawoki Gidan na? Diyya tayi murmushi tace mutum yana tare da wanda yakeso, nazo qasar ne, shisa nace sai nazo na gaidaku, ban kyauta ba? Zarah tace kin kyauta mungode, now leave, Diyyah ta kalli Zaid Ali tace how rude of ur wife, is dis how she treats ur visitors? Zaid ya jefeta da wani irin mugun kallo, yace badiyya ki bar gidan nan, tace not until i have wats rytfully mine back, Zarah da qarfih tace kina hauka, wasu yara yan duguiw guduiw kyawawwa suka fito da gudu daga wani dakih, Badiyyah ta nufesu tare da rungumesu, Hello sweethearts, look wat i bought for u, ta miqa musu ledojin tsarabar da ta musu, Miemee ta kalli uwarta tace Mummy who is she?? Zarah tace miemee do u remember dat monster dat was chasing u in ur dreams?? Da sauri ta gyada kai Tace is she d monster mummy? Zarah ta daga mata kai alamun Eh, da gudu miemee ta ja er uwarta biebee sukayi daki. Badiyya ta dago cikin duniyanchi tace dats very brave, kina brainwashing yaranki, mesa baki fada musu m dia daddy’s first love ba? Zaid ya daka mata tsawa Enough, get out now before i call d cops, nd u knw here u dont bribe cops, so ki fita tun muna shaida juna Badiyya, Zarah tace u are asking her nicely, ta finciko badiyya ta wurgar a waje kamar wasu kayan waki, ta koma da sauri ta dauko ledojijinta ta watsa mata su a fuska ta nuna ta da yatsa stay away frm my husband. Kika sake dawowa gidan nan zakiga abunda zai faru dake.Ta kullo qofar sa qarfih. Zaid ya sunkuceta yace karki damu, she isnt going to ever come back, nd if ta qara dawowa, she is going to face me not u. Ta rungume shi tace i love u yazayd lets go nd calm ur babies down yayi murmushi tare da nufar dakin yaran da ita(wanda basu karanta Akwai Lokaci na biebee isa ba, ku nema ku karanta).
****
Kuka Badiyya keyi sosai, wai itace nan? Mqewa tayi tana bin hanya tana kuka, Zarah nd Zayd must pay for dis, wayarta ta ciro ta latso Bokanta, tana kuka tace Boka sun wulaqantani boka ina so kayi musu— shiru tayi ta bi wani gu da kallo, Numfashinta qiris ya rage ya dauke sakamakon wanda ta gani tsaye daga gefe sanye da 3qtr da top sai Hula Qube ta mazan hausawa, waya yakeyi kuma da harshen hausa, Boka yace hello hello diyyan shagali kina jina? Da sauri Badiyya tace zan sake kiranka, ta share hawayenta ta nufa gurinsa tun da ya dago kai ya kalleta be dauke idonsa ba, ya cigaba da wayarsa Jawad kasan dai banda manyan kaya? Ka dinko min kuma kace ma tsoho ba sai ya biyoni ba, cikin satin nan zan dawo, Bye i gotta go. Daidai nan Badiyya ta fashe da kuka da sauri ya qarisa gunta Hey Miss, are u okay? Ta girgixa mai kai, wat happened to u? Cikin kissa tace yau na xo banda ma sauki, kallonta yayi yace kina jin hausa ne dama? Ba gashi nayi kaji ba? Muje na sama maki masauki, tace bansan kowa ba, pls take me wit u, bansan hannun da zan fada ba, kaga kai musulmi ne danuwana pls ka taimakeni ya danyi guntun tsaki yace da uban wa ya kawo ki nan din? Tace wlh Grads naxo, ya tsaida musu Cab, ya shiga gaba ta fada baya da sauri, Wooow take fada a ranta, wannan gayen ya hadu,ban taba ganin hadadden gaye kamarshi ba, yo wannan ai ya fi wanda tazo qasar danshi kyau, Ai dole zatayi aiki kan wannan, dole take samun wannan a matsayin Miji, tana tunane tunanenta suka iso wani dan qaramin gida, Ya fito ta bi bayanshi ya bude suka shiga, har dakin shi ya kaita, yace ki kwana a nan kafin gobe na sama miki gurin zama, ta yi mai far da ido, tace Nagode sosai Allah ya saka da Alheri. Ya miqe zai fita, tace Bawan Allah kai dan Nigeria ne? Ya daga kai eh, wani gari yace Maiduguri, tayi farr da ido, laaa ashe dan garin mu ne, pls ya sunanka? Cikin qosawa yace Sunana ZAID MUDASSIR ZAILANI
14. GIDAN GANDUbyBiebee Isa
Badiyya ta maimaita sunan Zaid sunanka? Ya ce eh sunan kenan, ya bar mata dakin, badiyya ta fada gado tana murna, Zaid ya tafi Zaid ya dawo, wannan zaid din yafi Zaid Ali kyau da wayewa, to su zarah a jiqa zaid a sha na sami wanda ya fi shi komai, daman wanin halin ga Allah baiwa ne wannan zaid din bazan yarda ya kubuce mun ba, haka ta kwanta tana me farincikin wannan sauyi da Allah ya mata.
*****
Zaid M.Zailani jikan Alhaji M.Zailani, da Hajiya karime da ga Mudassir da Abida Fari dogo me cikar halitta, Shekarunsa 28, a yanzu ya gama karatun likitancinsa a nan Oxford University, Zaid ya cika komai saidai matsalarsa Daya shaye shayen da yakeyi da taurin zuciya, be bin mata, a ganinsa mata matsala ne, yanmatan turawa sun sha chusa kansu gunsa amma ya na basarwa, Tina kadai yake saurara itama Iyakarsa da ita romance be zarcewa da yaga ta na neman wuce gona da iri zai tsallaketa, Zayd be shakkar kowa abunda ya sa agaba shi yakeyi, ba me chanza mai raayinsa tun yana qarami, ko Jawad sai dai ya shafa mai lafiya gurin Kaffiya, sun Sha fada da Zayyad, Lokacin da suke makaeanta Zayyad na mai nasiha kan shayeshaye, amma sai ya fara mai masifa yana fadin its a free world, so kowa yayi harkan gabanshi, duk Zuri’ar M Zailani daga iyayen zuwa jikokin ba me shan ko da sigari ne, sai Zaid, be fiye shan taba ba sai Giya, shan giyansa ma na masu aji yakeyi, sai dare yake sha. Hakan ya kasance a yanzu, fridge ya bude ya dauko kwalbar Giyyanshi ya fara kwankwada, yana lumshe idanuwa. Badiyya ce ta fito daga dakih ta na neman kicin Ganinshi tayi kwance kan 1sitter, daga shi sai singlet, nan da nan diyya ta kwadaitu da shi, haka ta haye Zaid, cikin bacci yaji ana shafanshi, ya miqe da sauri idanuwansu suka qanqance, Zaid ya hankadeta, cikin tangadi yace keee, are u trying to rape me?? Diyya ta mai far da ido, ta sa hannunta kan bakinta tace mai shhhh, ya koyi shirun, ta fada kanshi ta shiga kissing dinshi, ya biye mata, tana qoqari zuge mai belt yayi saurin watsar da ita a qasa, ya nuna ta da yatsa dont even think abt dis. Yayi cikin daki ya barta yashe a qasa, side smile Badiyya tayi tace muje zuwa. Daki ta bishi ta ganshi yashe kan gado, gyara mai kwanciya tayi ta zo ta baya ta runguneshi, suka yi bacci, assalatu ya tada Zaid, ganin Badiyya yayi rungume dashi tana sharar bacci, komi da ya faru jiya ya dawo mai, ya qare ma Badiyya kallo, kyakyauwa ce, daman akwai masu kyan nan a Naija, well haka yake son mace wayayya, ya miqe ya shiga toilet yayi wanka tare da dauro alwala, be tada ta ba ko da yayi sallah, ya shiga kicin dan hado musu brk fst, 8am ta fito Tana wannan yauqi tana kwarkwasa ta zube jikinshi,ta bashi peck G’mrn My Zaid, be hanta abunda take mai ba, m so hungry, yace i cooked u brkfast, tayi farrr rwly? Show me, Yace i will if u let me, ta gane me yake nufi ta daga shi da sauri, ya riqo hannunta ya kaita har kichin, suka zauna suka ci tare, harda feeding juna, cikin kwana 3 badiyya ta siye zuciyar zaid, haka yake son Matan Naija su kasance a waye, kullum suna maqale da juna. Badiyya ta fahimci Zaid, iyakanshi Romance. Sai ta daina zaqewa tana biye mai yanda yakeso.
*******
Ta kalleshi cike da qauna tace My jawad, wats troubling u dis days? Yayi faking smile yace bakomai baby, tace me ya sa ka tafi ba tare da kamin bankwana ba lst 3weeks? Kuma da kazo last week ba mu samu munyi magana ba, me ya faru? Yace bakomi kissu na, tace har ka fara boye mun abu ko ya jawad? Noo baby ba haka bne toh menene? Nan ya kwashe komai ya gaya mata game da abunda ya hadasu da fadila, bilkisu ta tashi tana huci kam balaee, Shine ka qyaleta? Yace hey babe chill mana, ya wuce, tace wlh be wuce ba, ya kamo hannunta duka biyu yace nace ya wuce ko? Ta ce naji, ta miqe ta barshi zaune.Dakin Aj ta shiga ta na huci ke lpya? Tace kinji kinji, ta kwashe komai ta gaya mata ita ma tace balaee, harda Ya’amar dina aka ma rashin kunya, tashi muje sassan su.suka fita gabaki daya.
*****
Hajia Ama zaune tana bare gyada, su Bilkisu suka shigo, sai da gaban hajia ama ya fadi don ba zata iya tuna ranar qarshen da suka shigo sassanta ba, Ba su da niyar gaisheta, tace mai gado lapya? Bilkisu ta watsa mata harara hanifa tace ina maras kunyan jikarki? Fadila nake nufi Hajia Ama tace ba sa nan suna chan gidan Yayanku hafiz dukkansu 3, yayansu dai ba yayanmu bq, don mu ba hada jini da mayu da aljanu ba, hajia Ama tace kuyi hqri, Bilkis tace idan bamuyi hqr ba hauka zamuyi? Suraj da Zayyad da suna cikin dakin Ama, tun shigowar su sukejin su, Suraj yace yaran nan basu da kunya, ya fita Zayyad ya bi bayanshi, ke uban wa kuke ma magana haka? Hanifa ta kalleshi galala ta watsar, dan ubanki nikike ma wannan kallon? Tace an kalla din, bilkis tace ke kika tsaya kulashi, ni ai idan na raina bola ko shara ba zubawa cikinta, tass kakeji ya kamtseta da marih, ya juya ya ba hanifa nata Allah ya isa mugu azzalumi shege daniska, charr ran maxa ya baci, belt ya ciro ya fara shauda musu, Zayyad ya qwace su yace ku gudu, yaja shi yana haba, meyasa ka biye musu, hajia Ama ma fadan biye musu da yayi takeyi. Da gudu suka yi sassan Hajia Babba suna kuka, hankalinga ya tashi, da qarfi ta fito, wai waye, uban me kuke ma kuka? Nan suka shirga mata qarya da gaskia, wai Zayyad da Suraj ne suka kullesu suka musu dan banzan duka, ko dankwali bata sa ba tayi sassan Hajia Ama da sauri masifa na cinta, Aishalle yau sai kin ci buhun ubanki, kika sa jikokin ki suka ma bayin Allah duka ko? Nima yau sai munyi na mu, Ama ta fito, suraj da Zayyad na bayanta, tana kar ku sake kuce komai, kuna jina? Ama ta kalleta tace kiyi hqr yaya karime, ba haqurin da zanyi, shegu mayyu wanda suka gaji maita, sai na daka ki yau cikin gidan nan, tayo kanta gadan gadan ta maqure nata wuya, Suraj ya finciko hajia babba ya watsar a qasa, wani irin Ihuuu hajia babba ta sake kamar an sa Lasfika, daidai nan Jawad ya iso, yana zuwa ya sakar ma Suraj nushi a hanci, suraj beyi watawata ba, ya rama nan dambe ya kaure, Zayyad yazo da niyyar rabasu, Jawad ya kaimai nashi nushi a baki, nan zayyad ya zuciya ya rama, sai abun ya koma 2in1, Ihu su hanifa keyi hajia babba nayi, Hajia Ama tayi saurin shiga sassan Umma hajja don ta ga ko su baba Abbakar na nan, fadan qarfi akeyi anan fadila, Maysah da Islah suka shigo gidan, ganin fadan maza yasasu sakin kuka duka, Maysah tayi sassan Tsoho da gudu, bawanda ya iya shiga fadan sbd duk mata ne, Islah tayi boys qrts don neman Yasamir. Har jawad ya far habo ga jini ta baki.
*****
Shigowan shi gidan kenan, daga nesa ya hango su suna dambe, hango jawad yayi yana firda jini, danuwanshi uwa daya uba daya aka ma wannan taron dangi? Balaeee, yarda trollynsa yayi ya cire er whyt top dinsa yayi wurgi da ita, ya ruga da gudu, wani tsalle yayi ya chafko zayyad ya hadashi da bango, ya finciko Suraj ya dinga kaimai nushi, abunka da wanda ke gym’n Jawad ya dago kai ya kalleshi ya sakar da murmushi suka tarar ma Suraj, suna duka, daidai nan Tsoho ya iso gurin Ba kasafai yake fitowa daga parlornsa ba, amma yau shine har sassa, Su hanifa sai kuka akeyi, hajia babba na ganin tsoho ta qara fashewa da kuka, Samir ya rugo da gudu tare da Mu’ammar zasu shiga filin dagan Tsoho ya musu alamu su tsaya, tsoho yace ku bar fadan nan, Ku bari nace, Jawad ya bar dukan Suraj, shi ko wannan cigabawa yayi da kilar suraj kamar Allah ya aikoshi, tsoho ya qara cewa nace ka bari ko? Ai da alamu be jin tsoho, da qarfi Tsoho Yace ZAIDU
15. GIDAN GANDU byBiebee Isa
Ture Suraj yayi tare da zuwa ya dauko rigarsa ya nufi sassan su, duk suka bishi da kallo, Tsoho ya kalli Samir tare da miqa mai wayarsa ya ce kiramin Dr Munnir, hannu na rawaSamir yayi dialling no din, ringing daya ya dauka ya miqa ma tsoho, Allah ya qara ma tsoho tsawon rai, Dr muna lpy? Ya amsa, yauwa danAllah kazo ka duba min yara na nan, yace toh gani nan zuwa, Tsoho yace kowa ya tafi sashensa. Zayyad ya kama suraj ya kaishi dakin Ama, aka watse. Ba a jima ba Dr yazo, a duba Suraj, ya bashi pain reliver Tsoho yace aje a duba Jawad, ko da Dr yaje sashen hajia Babba korarsa tayi tace ba sa buqatar likita munufukan banza..
******
Har kwana 2 shiru kakeji, kowa yayi zaton Tsoho zaiyi magana akan fadan shekaran jiya qala be ce ma kowa ba, kamar baayi ba, Be qullaci kowa ba, ko da Zaid yazo gaisheshi be nuna mai komai ba faramfaram, yana mai wasan kaka da jika, har suna sa ran Tsoho zai masu magana amma be ce komai ba.
Hajia Babba ji take da Zaid, duk cikin jikoki ta fi yi dashi, amma gurza mata RM yakeyi, mamanshi Abida ma tafi sonsa.
*****
Lamarin Gidan ya qara tuburewa sabon Gaba ya qara qulluwa, Samarin Gidan kuwa zumuncin su ya baci, dama suke zumunci a gidan amma tin bayan fadan nan ba me cewa dan uwansa qala, Gaba me qarfih suka dauka da junansu. Duk wa’annan abubuwan da suke Tsoho na sane da su.
Ya samu su Ido, yana tunanin shikuma haka Qaddararsa take? Gaban da Iyalansa keyi na matuqar damunsa. Amma InshaAllah komi yazo qarshe, yasan abinyi..
****
Haka ne bigbrosamir abubuwan gidan nan ya rinchabe, kowa gaba yakeyi, ni ba abunda ya damen da gaba kowa nawa ne, yace shiya sa kike burgeni ba ruwan ki da ‘yan ubanci,tace kaima ai haka bigbrosamir shisa nake sonka, yayi daria, yanzu ka fa da mun wannan shigar zai burge Yazayd? Samir yace sis na fiso ki bar mgnr Zaid, tayi rau rau da fuska zatayi kuka, ba zan mishi ba ko yasamir? Ba zaiso ni ba? Duk ta bashi tausayi don yasan ta na son zaid, yace kar ki damu zai soki, bana so kikai kanki ne, na fiso ya zo gunki tace toh shkn bigbrosamir, zan kama kaina.
*****
Ta shigo Gidan da motarta, Taci gayu sosai, ta fito ta na taku daidai, fitowar Amira daga sassan Umma hajja kenan taga baquwar fuska, Amirah ta nufeta da murmushi sannu da zuwa, Badiyya tace yauwa, Amirah tace gun Hajja Ama kika zo ko umma Hajja? Badiyya tayi far da ido, ko daya, gun Zaid nazo da fatan yana nan, Nan da nan fuskar Amira tayi dif, tace bashi kike binshi ko tara? Diyya tayi dan murmushi yan dunia tace ko daya naxo ansar zuciyata ne da ya sace min, da fatan kinsan inda ya ajiye shi, in ran amira yayi dubu ya baci, tace ke shegia eriska me bin maza har gidansu, ki bar gurin nan ko wlh na miki tunbur kuma na lalada miki dan banzan duka Badiyya tayi daria, ke yarinya, kinsan dai ni ba tsarar ki bace ko? A banza zan baki shekaru 5 ko 6, zan miki uzuri daya dan naga kina kama da myzayd, nd kamar kina hauka da sai kinyi nadamar furucin nan, Amirah tace na rantse da Allah ina iyawa, idan kin san mutuncin kanki ki bar gidan nan ynz, in ko ba haka ba, zaki ga Haukana don mugun bugu zan miki, na kareraya ki, na kaiki asibiti na kuma yi jinyarki, Daria sosai badiyya keyi, Amira ta kwnace dankwali au daria ma na baki ko? Tayi dammara, daidai nan Maysah ya qaraso gun da gudu ta sha gaban Amira, Haba Amira me ya hadaki da baquwa? Wannan er iskar zata shigo mana gida tai mana karuwanci, wai her Zaid, ko uban wa yabata yazaid din, haba Amira kiyi hqr mana, ke dalla matsa matsoraciya, tsayuwar rin wannan cikin gidan nan balaee ne, Ji gashin doki, ji man kanti ji matsatsun kaya, wlh kamar jikar bokan tudun qarfe, ai wlh sai ta bar gidan nan ynz ba anjima ba, kafin Allah ya jarrabe mu da Kwarantsa cikin Gida, Maysah tace haba Amira, ita ko diyya daria kawai take, Maysah ta juya ta kalli diyyah haka kurum taji gabanta ya fadi, ko me ya sata faduwar Gaba oho? Ta dai daure tace baiwarAllah kiyi haquri danAllah, Yazayd kike nema? Bari a dubo maki shi, ta ja hannun Amira, daga nesa suka hango Yazayd din na jogging, ita ko badiyya ta qarasa gun shi, shikuma ya daga ta sama suka rungume juna, Haka kurum Maysah taji gabanta ya tsananta bugawa, Amira kuwa baki ta bude galala, kaiii Rumguma? Tsanar Yazayd da karuwa(sunan da ta samata)ya shigeta, meye haka, gabansu suke iskanci? Bata ga komai ba sai da taji badiyya nacewa haba Zayd kai da kace zaka nemeni har kwana 5 shiru? Nayi missing dinka, ina tunanin ko ka mance ni? Cikin sigar lallashi yace so sorry my diyyah, wlh i was busy ne, har yau ban siya sim ba shisa ban nemeki ba, but its a good thing u came over, i’m glad to see u, ya akayi kika gane gidan? Ta mai far da ido, kasan familyn Zailani ba boyayye bane, yace haka ne, Sai sannan Zaid ya lura da Meerah da ke tsaye wata a gefenta ba tare da ya kalli Maysah ba, ya kalli Amira yace ke ya ma sunanki?? Amirah ta watsa mai wani mugun harara, Badiyya tace kai honeybunch ur sis is hilarious, ya danyi gyatsine yace haka take bata da hankali, ya qara kallon Amira yace Zo ki kai Badiyya gurin Hajia Babba kice mata baquwa tace, Badiyya tace Oh no dear, ba yau ba, i jus came to check on u, but next time musamman zanzo gaida Inlaw’s na, yayi dariar jin dadi yace yauwa sweety, ya ja hannunta ya rakata har mota, Amirah da Maysa suka bisu da ido, Maysah na tir da wannan hali nasu, Ameerah kuwa takaici da baqin ciki kamar tayi kuka, Maysah ta ja hannunta ta fizge tayi dakin Yasamir,Yana ganinta ya miqe tsaye yace lilsismeerah menene waya tabaki? Ta na huci, bigbrosamir daman Yazayd dan iska ne? Ynz wata tazo gidan nan nemanshi kaga yanda ya rungumeta? Ta kwashe komai ta gaya mai, Samir yace toufa, shima Zaid da rigima yake, yasandai ba wanda zai aura mishi bare, kar ki damu kece matarshi, na auri wannan? Allah shi kyauta na aureshi, kai kaga abunda sukeyi? Ai wlh bazan aureshi ba, shi gashi wayayye. Yayi karatu turai ya zama chris tucker, toh wayewa ma ya ci ubanshi, Samir daria ya fara, isit funny bigbrosamir? Ni ynz wa zai aureni? Kowannen ku is in lov? Kuma ni ba zan auri daniska ba wlh, kar kuma Tsoho yace zai zaban mun daga cikin yayyinmu wanda sukayi aure. Shidai Samir har yagaji da surutan Amira, ya daiyi shiru yana jinta, wani Lokaci tabashi daria wani Lokaci ta bashi takaici, shidai yace Allah ya shirya Amira nikuma biebee nace Amin
16. GIDAN GANDU by Biebee Isa
Hajia Babba, Hajia Ama da Umma Hajja zaune a parlor, Tsoho ya kalli Ama yace Aishalle me ya faru sati 2 da suka wuce? Aishalle tayi murmushi don ta san ko ba dade ko ba jima sai yayi maganar, nan ta kwashe komai ta fadi mai tun daga shigowan su Hanifa har fadan, Tsoho ya jinjina kai, Charaf hajia babba ta chafe, baka da labarin rashin ta idon da Fadila ta ma Jawad, rashin kunya da zage zage, amma be ko kalleta ba balle ya duketa, toh shi suraj ya hade bilkin da hanifan ya zane, shi ko zaid ya zo ya lakada mai na jaki ai dan’uwa befi danuwa ba. Tsoho yace shikenan, Allah shi kyauta, ku tashi ku tafi, ya kalli Umma hajja, yace ki turo mun Hassan Hussaini da Gambo tace to Mallam hajia babba ta buga tsoki, M.Zailani ya gyada kai Allah ka shirya.
*******
Baba Hassan, B.Hussaini da B.Gambo zaune a kasa kan carpet, Tsoho yace toh kunji hukuncin da na yanke ya kuka gani? Baba hussaini ya nisa yace anya Baba wannan abu xai yiwu, kasan gaban nan me qarfi ne tun kafin a haife mu akeyinshi, sai nake ganin kamar wuta za a qara ma lamarin, tunda duk basu jituwa bane, maganin kar a fara kar ayi, Baba Hassan ya girgiza kai yace aa ina ga hakan ne maslaha a cikin wannan gaban, dole muke kawo qarshen wannan Gaban kuma inaga wannan ce hanyar da zai sa a samu sulhu, So ina ga Baba hakan daidai ne, Baba Gambo yace Hakan daidai ne kuwa baba, sai dai a roqa Allah ya daidaita tsakanin mu duka, M.Zailani yace Hussaini ka fahimci abun da Yayanka yace? Baba Hussaini ya gyada kai, yace wannan gaskia ne, daman bawai naqa bane ina gani kamar ba za a daidaita ba, baba hassan yace always pray for d best broda. Yace toh Allah ya sa mu ga da kyau. M.Zailani yace toh shkn tunda har kun amince da Raayina. Hakan zaayi (ni nace me zaayi tsoho? Harara ya wurgo ni da ita)
********
Maysah da Tsoho suna zagaya gida, ya na bata labarin Soyayyar shi da Aishalle, tana ta daria yace muje mu kaima Yayanki Ziyara, Tace wanne daga ciki? Yace muje dai, rabon da Tsoho yazo bangaren samari Har mantuwa ta manta, kai tsaye dakin farko ya qwanqwasa ya shiga, Zayd ne kwance da fara singileti ba bacci yakeyi ba amma daga ganinshi buge yake, ga kwalbar giya ta Gulder da Star ya shanye, Gefenshi Diyya ce kwance tana bacci, Tsoho firgici Maysah firgici, tsaf tagane wanda tayi fada da amira ce shekaran jiya, lallai Abun Yazayd ya girmama, har gadon baccinshi yake kawaota, Allah ya shirya! A hankali Tsoho yace Giyah? Ga mace Kwance a cikin Gidana? Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Zayd ya miqe duk da ya dan tsorata amma da yake dan dunia yace me ran qarfe lafia ka shigo Sassan mu? Ko nema na kakeyi? Tsoho ya share yace ziyara kawai na kawo ma, Amma bari muje kafin ya ce komai Maysah ta riga tsoho fita, jikinta rawa yakeyi, har suka koma Sassan tsoho basu tanka wa Juna ba, Duk Zuri’ata Zaidu kaine Daban Allah ya shiryaka Dole na muku Aure, dole nake aurar daku duka, Ya Allah kai mana da kyau.
******
Fadila da Suraj a dakin hajia Ama suna Soyewa, tana zuba mai shagwaba Wai gaskia ba zai tafi kano week din nan ba, yace baby kiyi hqr so kike a koreni a wajen aiki? Tace ba sai a maka transfer ba? Yace ina kike so mu zauna idan munyi aure? Ta daga kai sama tana tunani tace Kaduna, yace daman tunanin mu daya, kar ki damu da hannuna na zana gida a kaduna har an fara gini fadila tayi ihun murna tace thank u mysuraj, Sarkin Gida ne ya shigo da Sallama yace Tsoho na kiran ku, suraj yace mu suwa? Yace dukkan ku na cikin dakin nan, har da Hajia Ama, taro ne na gaggawa, suraj yace toufa Allah ya sa lapya, fadila gaya ma su hajia a ciki da su Islah, aka sanar dasu duka. Kowa ya Hallara abun mamaki harda yayyinsu da matansu da sukayi aure na nesa ne kawai babu to lapya inji Islah?duk suka zazzauna, One by One tsoho ke kallonsu, daga matayensa zuwa yaransa zuwa jikoki harda masu musu Abincin GANDU, Tsoho ya gyara Murya Ina Zaidu?? Jawad yayi qarfin halin cewa yana Dakih, be ji aikena bane? Jawad ya miqe bari na kirashi, yace kai Jawad Zauna, Ya kalli inda mata suke yace RUMAH jeki kira yayanki Zaid, gabanta ya fadi haka ta miqe tayi Sassan Samari, ta kusa minti 5 tana tunannin yanda zata shiga dakin, sai tayi jihadin Sallama da qarfih, fitowanshi wanka kenan, daga shi sai towel, yace waye? Shigo, ta shiga saurin rintse ido tayi, ya daure fuska ke Lapya? Uban me ya kawo ki dakinah? Tace kayi haquri, Tsoho ke kiranka, kowa na chan kai kadai ake jirah, tana kai wa nan tayi saurin fita yayi dan jimm tabbas ya san meeting din nan nashi ne, ya dan firgita amma dayake namijin dunia ne ya dake ya zira jallabiyansa yayi cikin gida da takunsa. Ya shiga wakeken parlorn da Sallama, Gabanshi ya fai ganin idanuwa akansa, duk ya tsargu ya sha jinin jikinsa, kusa da Jawad Ya zauna.
Tsoho yayi Bismillah tare da guntun muqqadima da sallama duk aka amsa mai, Ya fara cikin maganarsa ta manya : Ahh, batare da bata lokaci ba, kamar yadda kuka sani a wannan Zuriah tawa, idan Namiji ya fara aiki, Mace ta gama sakandire ana masu aure, kuma ni ke zaban musu mataye da mazaje, kuma DOLE abi umarni nah, kasancewar ina da Zuriah da yawa nake hada aure uku uku, ko hudu hudu wata sain har biyar biyar, wannan abu ne da kuka sani ba sai na dinga nanata shi ba a duk lokacin da zanyi hadi, Bana Zaa aurar da Mutane 12, maza 6 mata 6, gaban Masoyan nan 12 yabada HINGIM, fargaba ya shiga zuciyoyinsu, kunsan dai duk maganar da na yanke ta zauna, ko da yake ban yi tsammanin musu daga daya daga cikinku ba don na san kunsan Qaidojin Gidan nan, ba a soyayyah ko auren bare, wacce ko wanda M.Zailani ya zaba shine magana. Gabansu ya sake yankewa ya fadi Tsoho ya cigaba da jawabi, Toh na riga nayi tsarina kamar haka ; ZAYYAD na baka HANIFA, SAMIR na baka AMIRAH SURAJ na baka BILKISU MU’AMMAR na baka ISLAHULKHAIR, JAWAD na baka FADILA, ZAYD na baka RUMAYSAH. Tashin hankali, Firgici, Rudani, Kurumta, Makanta, Bebanci ya dirar ma Masoyan nan 12lokaci Guda ba sa gane komai ba sa jin komai ba sa fahimtar komai ba kuma sa ganin komai…
Shin wannan Hadin Zaiyiwu?
Shin Wannan Gaba zata tsaya kuwa?
Shin Akwai Sulhu tsakanin yan Dakin Hajia babba, da Dakin Ama da na kuma Umma Hajja?
This is just the Beginning
17. GIDAN GANDUby Biebee
Parlorn yayi tsit kamar ba kowa cikinta sai qarar fanka, Tsoho ya cigaba da magana, kuma zaa daura auren nan ranar jumaah me zuwa ma’ana nan da kwana 7, firgigit suka dawo hayyacinsu kallo daya zaka masu duka zaka ga tashin hankali a fuskokinsu, Jawad ke maimaita sunan fadila a bayyane tare da kallon inda yammatan ke zaune kuka yaga rabin ransa bilkisu keyi, zuciyarsa ya hau zafi da ya hango fadila rakube tana cizgar kuka, lokaci daya ya tuna rashin kunya ta da shirga mishi, nan da nan haushin ta da tsanarta suka darsu a ransa da sauri ya girgiza kai wlh ba zaiyuwu ba da sake.
A bangaren Mua’amar kuwa Tunani yake yama za ayi ya auri watan da ba Hanifa ba, ai ba zai mayuwu ba da sauri ya rarafa gaban tsoho tare da ririqe mai kafa, yace tsoho, kar kayi mun haka, ka taimakeni ka bani Haneefa, haneefa ce rayuwata. Baba Mudassir yace kai Mua’amar meye haka?Tsoho ya daga ma baba mudassir hannu yace, barshi ya gama, ina jinka Amar, ko kunya be jiba ya cigaba da cewa tsoho ka taimakeni, kaji tausayina ya qarashe fadi tare da kuka me zafih da ya kubce masa, Tsoho ya shafi kanshi a hankali yace kayi haquri, na san menakeyi, Wata rana zakayi Alfahari da wannan hadin nawa, Girgixa kansa yayi da qarfi tare da runtse idanuwa, Samir ma ya matso yace tsoho danAllah kar ka rabani da Islahulkhair ya xa ayi ka hadani da Amira? Damm gaban Amira ya yanke ya fadi, bata qin samir hasalima ita bata yi baqincikin wannan hadin ba, fargabanta daya Samir Islah yakeso, to idan samir ya qita to wa zai sota? Suraj zaiyi magana Baba Hassan ya wurga musu harara shi da Zayyad ba shiri sukayi gum, Shi ko Namijin duniya wato Zaid, ko a jikinsa don ya san wannan abu ba zai yuwu ba, ya ma xaayi ya auri wannan qaramar yarinya? In short ba me mun auren dole, ni banda mata da ta wuce badiyya so tsoho ma zai tashi daga wannan mafarki coz it will never happen.****
Tsoho ya bi su duka da Ido, Kuka sukeyi ba mazan ba ba matan ba, Idonshi ya tsaya kan Ruma ganin hawaye kwance kan fuskar Maysah yasa zuciyarsa sosuwa, ya furta a hankali Rumah zo nan, a hankali ta miqe ta nufa gunsa, yace Rumah me ya saki kuka? Rumah bakya son wanda na baki? Kuka me tsuma rai ta fashe da shi. A hankali daidai yanda zaijita taceTsoho kar ka mun haka, ya zaayi ka hadani da Yazayd? Tsoho ko ka manta rannan da– da sauri ya katseta ta hanyar sa hannu a bakinshi, ta girgiza kai, ta dan daga murya ba zan yarda ba tsoho, ba zan yarda ba, Mashayi? Mazi— tasss kakeji, Baba Abbakar ya kasheta da mari, abunda be taba yi mata ba kenan, Maysah ta dago idanuwanta da suka rine sukayi jazir ta kalli babanta, a hankali tace Appa ya nuna ta da yatsa, yace ke kin isa Tsoho yayi miki zabi kice ba kyaso? Toh idan ni na haifeki baki da mijin da ya wuce Zaid, sai anyi auren nan, sai dai ki mutu Rumaysa, cikin isa da gadara Zaid yace wai wani zaid din? Ni fa ba zan auri wata yarinya a dangi ba, ina da wacce nakeso, Uncle Abbakar ya wurga mai wani mugun kallo, duk tsagerancin Zaid sai da ya ji shakkun Babban Maysah. Hajia Babba dake zaune ta gama cika pal, tace ai ba qarya yayi ba, duk cikin wannan hadi ba wanda xaiyuwu, babu yanda xaayi ni ko jikokina su hada iri da dangi Aljanu da Mayu, to Alhaji tun wuri ka chanza wannan maganar don wallahi ba zaiyuwu ba, wannan maganar maganar nosense ce, maganar banza, jikana ya auri jikar Hajjo ko Aishalle? Sai dai a mafarki wollai, Parlorn yayi shiru, ta inda Hajia babba ke shiga ba ta nan ta ke fita ba, sai bambami take tayi. Kowa ya xuba mata ido, sai zagezage take tayi, Miqewa yayi Qyam sakamakkon jin kanshi da ya sara Qirjin shi ya shiga yi mai zafih ya sa hannu ya dafe, ba wanda ya lura dashi don hankaliksu na chan gun Hajia Babba da ke ta faman masifa ita ba zata hada iri da dangin mayu da Aljanu ba , Hanyar Qofa ya nufa hannunsa dafe da qirjinsa, ji yayi qaffafuwansa sun gaxa daukar sa jiri ya fara dibarsa, sai ji suke Timmm Tsoho ya Xube qasa, nan aka shiga rigerigen nufan inda tsoho yake, Baba Hassan ne ya sa hannu wurin hancinsa be ji tiririn nishinsa ba, cikin kaduwa ya ce A dauko mota, Jawad Zaid Muammar Suraj da Samir ne suka fita da gudu don dauko mota hankalin su Ya tashi ganin ba alamun Numfashi tattare da tsoho, Suko matan kuka suka sa barin ma Maysah, ita ko Hajia Babba kuwa kururwa take tana cewa waiyo Mallam Kar ka mutu ka barni, kayi haquri kar baqin cikinmu ya kasheka, ka tashi Mallam. Baba Usman ne yace haba Hajia ce miki akayi ya mutu? Tayi saurin cewa Auuu be mutu ba? Be tanka ta ba anan ne Suraj Ya shigo ya ce baba ga motan nan gaban parlor, nan su jawad suka shigo ko wannensu ya dauko motarsa, nan Zaid ya cicibe tsoho shi kadai yayi wajeh dashi, bayan motan da ke parke gab da parlon ya shimfideshi a baya, kowa ya samu mota ya shiga Suraj kuwa da Tsoho ke bayna motarsa ya zagaya ya ja Motar sai Asibitin Dr Munnir na Alheri Hospital. Convoy akayi, saboda kidima Hajia babba da Hajia Ama, da Umma Hajja mota daya suka shiga, motar Zaid, Iya rudewa sun rude, hajia Ama da Umma hajja dai hawaye suke don tun rasuwar Baba Rabi’u basu qara ganin tashin hankali ba irin na yau, ita kuwa Hajia Babba bata fasa ihu ba tana Allah kar ka kashe Alhaji, Allah ka raya shi, Waiyo ni karime, Zaidu ba a iso bane? Zaid da ya qulu sosai, yana son Tsoho sosai yana fargaban rasa shi amma wannan matar ta cika mai kunne, tsawa ya daka mata yace idan ba ki min shiru ba zan zubar dake a nan, da sauri ta kama bakinta.
*****
Islah a bayan mota riqe da hannun Maysah riqe da hannun Fadila a bayan motan Samir, Amira na gaba kowannen su Hawaye ke bin kuncinsu, tunda suke a rayuwansu ko ciwon kai basu taba ganin yayi ba. Amma yau shine harda yanke jiki ya fadi, Suna cikin matsanancin tashin hankali wanda roqonsu Allah ya tashi kafadar Tsohonsu..
***
Ko da suka isa Asibitin Already Dr’s and Nurses na jiran su a entrance don tun a hanya Baba Gambo ya kira Dr Munnir ya Sanar dashi komi. A haka aka daura tsoho a kan gado aka jashi zuwa A&E wato Accident and Emergency. Tsoho Allah sa a Dace
18. Gidan Gandu by Biebee
Da sauri Liktoci suka du’kufa gurin ceto ran tsoho, Zuriarsa na wajeh hankalin su tashe yake, kowa da kallan tunanin da yake, Hajia Babba sai kai kawo take binibini ta lewa dakihn, Hajia Ama kuwa ta kame guri guda da tsura ma dakin ido, bayan kamar rabin awa, Dr Munnir ya fito yana shar’ce gumi, da sauri suka xagaye shi, ya kallesu ya girgiza kai, yace ku muje office. Har wasu dai suka riga Dr shiga ofishin shi, nan da aka zazzauna, wasu kuma na tsaiytssye don duk Girman Opishin Dr ya gaza dauke Iyalan Zailani.. Dr ya kalli Manyan Yarsn Tsoho, Yace ya akayi haka? Su Baba Hassan duk suka zaro ido? Yace ya kuka bar Ciwon Zuciya ya ma Tsoho mummunan kamu farat daya? Duk suka dau sallalami, Ya kuka yi wannan sake? Hajia Babba tace wlh baqin cikin mu ne, Waiyo ni kaina. Zaid ya watsa mata mugun harara, ya cigaba da cewa, munsamu mun shawo kan matsalan da qyar. toh gaskia Dole ku kiyaye bacin ran sa, dole kuke mai abubuwan da yakeso, nd ku nisantar da shi daga abubuwan da baya so, Nd dolenku kumai abun da yakeso kafin ya farfado, don gudun hakan na iya sa wa zuciyarsa ta buga farat daya. Gaban kowan nensu ya fadi, Mu’ammar ya girgiza kai ya fita daga dakin, Jawad ya bishi hakan nan Zaid. Duk aka bisu da ido, Dr yace idan kuma kun gaji da hidimar sa tunda ya tsufa ku barshi kawai ya mutu, Hajia babba ta zunduma uwar ashar, Dr kaci Kwal Ubanka, mu barshi ya mutu fa kace? Yace ahtoh, ai don ina ganin abunda ya ke so me girma ne, ba zaiyuwu ba, tace Dole kuwa zai yuwu, dole a aurar dasu ga maqiyansu,. Ke kima waanan jikokin naki magana, dole suke aurensu ba don na so ba, sai don ceto ran Mallam. Ta miqe tare da fadin tashi dan Usmanu, muje mu ga yaran nan. Balki ku biyo mu duk suka bi bayanta jiki a sanyaye, ya rage daga Zuriar Umma hajja sai na hajia Ama cikin ofisihn Dr. Dr ya miqe yace toh bari na barku ku zanta.
*****
Ai wallahi ba zan yarda na auri wata Islahulkhair ba, Ya zaayi ma hakan? Da sauri Aunty Sadiya ta riqi danta tace Amar baka fini Tsanar wannan hadin ba ban qi ayi tashin hankali ba don a fasa auren nan, but bamu da choice, i love my Father, i cant watch him die, please sonn, u nd bilkis will listen to me and marry dem for a short period of time, da Yaji sauqi xaka saketa ka auri Hanifar ka kaji? Kema dole muke matsa ma Suraj ya sakeki kinji? Bilkisu ta na kuka tace indai wannan zaisa Tsoho ya tashi ya ji sauqi toh wlh ko waye xan aure shi. Aunty Sadiya ta rungumeta yau diyata. Its just for a short period of time. Aunty Abida ta kalli nata yaran tace dat goes same for d u three, Zaid, Jawad, Hanifa bama son wannan hadin but we love our Father. Shine Gatanmu da duk wanda muke taqama dashi. We cant let him die. I knw y’ll love Tsoho nd Ya’ll sacrifice for him ryt suka gyada kai, then do dis for him okay? Nd remember its just for a short period of time…
Aunty Zainab rungume take da dants Samir daga chan gefe Baba Gambo na kallonsu cike da takaici, kuka ko Samir kamar mace? Amirar Annoba ce? Aunty Zainab ta kalleshi ta mai Alaman ya fita, Baba Gambo yayi gaba. Ta shafa summar kansa tace *Samir* yace Mami kiyi shiru, dole zan Auri Amira don ceto ran tsoho Amma dole zanyi kukan rabuwa da Islah. Mamin tace haba Samir, abunda yayi Islah shi yayi Meerah, ka duba ka gani, da sauri yace wlh shes nothing like dat– yi shiru mana. There are times da zaka so abu sai Allah ya hanaka don ba Alheri bane a gareka, sai ya Musanya maka da abun da yafi Xama Alheri, Maybe Islah ba Alheri bace a gareka, Maybe Amirar ce Alheri, kuma ita Allah Ya tsagaa rabonka da ita. Think wise son, u are d bravest i’ve ever seen, ya qirqiro murmushi yace i will marry Amira. Tayi murmushi tasan ba ya amince da Amira ba ne Aa sai dai don kawai ya faranta ran maminsa.
****
Toh ni ba sai nace muku komai ba, duk nan kun mallake hankulanku, nd kunsan whats right, so i trust u to do the right thing, Baba Hassan ne ke wannan maganar.Umma Hajja tace ai na san Yan jikoki na da ladabi da biyayya, masu son Farincikin Uwayensu, nasan ba zasu bar son zuciyarsu ya shiga cikin wannan Lamarin ba, Baba Hussaini yace toh ya kuka ce? Hajia Ama tace ai nasan jikokinmu sun Amince, don suna son wannan tsohonsu sosai koh? Rumaisah tace idan akwai wanda yafi makaho makanta, kurma kurumta gurgu gurgunta, zan aureshi don ceto ran tsoho, wanda ya soni ya qaunace ni, Fadila ta kalli Suraj, tace nima na amince zan auri YaJawad duk da na san aurensa baraza na ne a kaina, Amma ina son Tsoho sosai, dole nake haqura na ba Tsoho abunda zaisa sa farinciki. Islah na matsar kwallah tace Zan auri Ya Jawad. Zayyad yayi karaf yace muma mun Amince zamu auri Hanifa da Bilkis Allah ya sa hakan yafi zama Alheri Aka Amsa da Amin. Hajia Ama ta kalli Baba hussain tace na gaya muku yan jikokina Akwai ladabi Biyyaya. Yace ai nagani Allah muku Albarka Ameen…
Hajia Babba ta shigo da zurianta a bayanta fuskokinsu murtuk, suka zazzauna. Dr Yashigo yace toh duk kun shirya ba Tsohonku abun da yakeso? Sukace Ehhh. Yace toh MashaAllah. Allah ya tashi kafadun shi. Yace kuma a barshi ya huta, yana so kowannensu yaje gida don be son hayaniya. Haka Baba Hassan ya sa aka tattarasu akwa maida Gida. Da qyar Hajia Babba ta amince zata tafih. Daga shi Sai Baba Ussaini suka tsaya…
GASKIAN LAMARIN.
Kwana 2 kafin (2days Back)
TSOHO zaune da Family Doctor dinshi Dr Munnir, kuma amininsa wanda ya san duka Sirrin Tsoho da yanayin GIDAN GANDUnsu, , amma Tsoho ya girme mishi nesa ba kusa ba, don ko tsaran su Baba hassan ne, Tsoho yace Dr bansan yanda za’ayi yi na hada auren nan ba, don kasan dan yanzu ka haifeshi ba ka haifi halinsa ba, suna iya bijire mun suce tunds basu na haifa ba zasu mun rashin ta ido balle dukkansu soyyaya suke, toh ina tsoron su ki Amincewa. Dr ya nisa yace Akwai Shawara idan zaka iya, Tsoho yace me ke nan? Dr ya sausauta murya ya ma tsoho qusqus a hankali me kama da rada, Tsoho yayi daria yace hakan ma zaayi, ta wannan hanyan zan magance duk wata matsalata. Zanga idan Zasuyi man Hallacin na, Zangani idan ina da mahimmanci a rayuwansu, naji dadin shawarar nan amma taya zanyi na zube qasa har na dauke numfashi na? Yace kar ka damu, akwai maganin da zan baka ka sha, be da illa. Zai taimaka maka gun aiwatar da qudurinka, kuma idan aka kawo ka asibiti, da drip din da Allurorin da zaka sha duk masu Amfani ne ga me lafiyayyen jiki kamar su Bcomplex d.s. so kar ka damu, ba abun da zai shafi Lafiarka. Tsoho yayi murmushi yace nagode likita Allah ya sa mu dace yace Amin…Toufa jamaaa kuna jin wannan plan din na Tsoho? Duk yabi ya tada ma Zuriarsa hankali🤔🤔 nidai nace kaiii Tsohon nan Namijin Duniya ne.
_Bibilicious Biebee_
Like · 1 · Reply · Report · Aug 4
Phatee Lamin
19. Gandu Gandu by Biebee Isa
Sai da Tsoho yayi Baccin Awa12 kafin Maganin bacci ya sake shi, A lokacin Daga Dr sai Baba Yan 3, Dr munnir yazo yana duba shi, DrMunnir ya kashe ma tsoho ido alamun komai daidai. Sai yace MashaAllah jiki ta warware, ina ma iys sallamanka. Amma zan barka ka dan huta, Tsoho yace me zai zaunar danih tunda naji sauqi kunsan da ina cikin hayyacina ai da ba a kawo ni nan ba. Dr yayi daria yace haka ne. Nan ya rubuta musu takadar Sallamah, Baba Hassan ya kira Suraj yace kazo kai maida mu Gida.
*****
Kowa yayi murnan ganin tsoho ya tako da Kafarsa. Barin ma maysah da take kukan murna, don ta ba Tsoho mutuwa. Sashensa yayi Hajia Babba sai rawan Jikin Alhaji me kake so? Alhaji me za a maka? Yace wanka zaiyi, nan BabaAbbakar ya umurce kowa da a bar Tsoho ya huta…
WASHEGARI
Tun daga nesa ta hangoshi bataso ya cimmata sai ta qara sauri, tun jiya take avoiding dinshi, da gudu ya tankarota, yana kiran Fadila, haba Fadila ki tsaya mana, Ya qaraso, Fadila y are u avoiding me? Tace Ya Suraj yace shhh, fadila Tsoho ya ji sauki, ba abunda ke damunshi ynz, lets run, lets leave dis place, muje wani wuri a daura mana Aure, i cant do without u, kukan da take boye ya kubuce, sai da tayi me isarta ba tare da ya hanata ba ta girgiza mai kai, tace Yasuraj wallahi tallahi ina sonka, zan auri Ya Jawad and zaka auri Bilkis, idan muka gudu, mukaje aka daura mana aure me mu kayi kenan? Mu bijire ma iyayen mu? Bakin cikin mu ya kashe tsoho? Gaban ya cigaba da wanzuwa frm generation to generation? If we leave, they will be seperated forever, maybe this f only way to End our Family’s Malice, Ka roki Allah ya sa hakan yafi Alheri, And Allah ya ba mu ikon rungumar wannan Kaddarar, tana kaiwa nan ta ruga da gudu. Tayi sashensu, A hanya ta ci karo da Bilkisu da ta fito daga Sashen Tsoho, taja ta tsaya, Bilkisu na watsa mata harara, tace listen to me Fadila kar ki ga kamar Gobe Zaki zama Mallakin Yajawad kice zaki zake, ki kira kanki matarshi, to bari kiji Yajawad nawa ne, Aurenku suna ne kingane? na dan wani lokaci ne, idan komai ya daidaita zai sakeki ya aureni, so i want u to keep ur distance, ban yarda ayi seducing masoyina ba. Fadila tayi murmushi ta shar hawayenta. Tace Bilkisu bana son Jawad bana kaunarsa toh mesa xanyi tunanin Jan hankalinsa ko ra’ayinsa? Kuma da kike cewa nan ba da jimawa ba zai sakeni, kin ga na miki kama da wadda zata zama bazawara in future? in kinso ki ka she aurenki ki zama bazawara, ki sami wani miji amma badai Jawad ba, i dont love him but i will make sure dat he never ever gets back to u get dis into your thick skull Jawad ya miki nisa. tayi gaba ta barta bakih bude tana mamakin karfin Halin fadila ita da ba sonsa take ba.
*****
Islahulkhiar kwance a green carpet din field din Gidan idonta lumshe, tana tuna moments dinta da Samir, time din da suke kwallo, ko kwallon kwando ko skipping rope, Maganar Hajja Ama ta tuna inda take cewa _kuyi haquri da wa’enda aka zaba muku, ku roki Allah ya sa sune Alheri, ku Maida Soyayyar masoyan ku a kansu, ku maida Soyayyar Masoyanku Soyayyar yanuwantaka don ku Yanuwan juna ne Allah muku Albarka_ islah ta matse hawaye tace Allah kasa Ya Mu’ammar shine Alheri a gareni. Tsaki taji an buga tsuuu Ta na dagowa taga Amira da Hanifa. Amira tace lallai kam kin ma kanki Kiyamul laili, gwanda da kika haqura da Yasamir, don nice matar da aka zaba mai. Gwara da kika dangana Allah hada kanku da Ya Mu’ammar din Islah ta girgiza kanta ta miqe ta kakkabe jikinta tayi gaba don bata son hayaniya. Hanifa da qarfi tace aikin banza, ko me zakiyi Ya Mu’ammar ba zai taba sonki ba, ni yake so ni kadai, jini na ke gudana a zuciyan shi, da komi ya daidaita zai sakeki ya aureni, dan ba zai taba hada iri da dangin mayu da aljanu ba. Chak Islah ta tsaya, kamar ba zata yi magana ba kuma sai ta dawo da baya, ta tsaya Daf da Hanifa tace, Wai tada jijiyoyin wuya na meye ne? Naga dai tsoho ya san dake ya zaba mishi ni? Duk da jinin naki na gudana a jikinshi, ki bari ya sakeni mana yazo ya aureki kafin ki gaya min magana, but as far as m concerned ni zai aura Gobe, nd m d choosed person its not my fault dat m more beautiful and talented dan u, its not my fault dat i’m chosen for him, so Maybe tsoho ya ga rashin dacewar ku ne ya zaba mishi ni, if u have a problem go meet Tsoho, amma idan zaki bi shawara ta, ki koya ma kanki Son YaZayyad don Ya Muammar will never ever come back to u, tana kaiwa nan tayi gaba ta barsu baki sake, chan kuma Amira ta pashe da daria, kaii ashe Islah na da baki haka? Wai its not her fault wato shes more talented nd more beautiful dan u, ooo Islah got attitude, Hanifa takaici goma da ashirin, ashe wannan haka take? Ai bata taba zatan zata tanka mata ba, Ga haushin darian mugunta da Amira ke mata. Ji tayi kamar ta sa Ihu don takaici.
********
A yau Jummaa Wurin Huduba Liman yayi sanarwa za a Daura auren Jikokin me Masallacin nan, ana buqatar kowa ya tsaya bayan an Idar da Sallan Jummah. Haka kuwa akayi, ana Idarwa aka daura Auren ZAYYAD da HANIFA, ZAID da RUMAISAH, JAWAD da FADILA SURAJ da BILKIS, SAMIR da AMIRA da kuma MU’AMMAR da ISLAHULKHAIR bisa Sadaki dubu Hamsin lakadan ba Ajalan ba, aka shafa kuma aka wadata su da Rengem na shinkafa(lol) Tsoho baki har kunne, Angwayen kuwa kadaran kadahan duk da Mu’ammar da Jawad ba su tsaya daurin auren ba. Nidai nace oho dai an riga da an daura. Ko da ku ko baku sai da Tsoho ya Daura muku aure
_Bibilicious Biebee_
Like · 1 · Reply · Report · Aug 4
Phatee Lamin
20. Gidan Gandu by Biebee Isa
Daren da Aka daura Auren abu dunia ya ishe Sabin maauratan, da Angwaye musamman Amaren, daga Zaid sai Amira kadai ne basu da wata damuwa sosai ko wannensu na sashensu jikinsu duk yayi sanyi.
Kuka wiwi Rumaysa keyi, Shikenan me afkuwa ta afku, YaZayyad ya mata nisa, yanxu YaZayd ne mijin ta. Allah ka ba ni ikon Cin wannan Jarabawar. Amma ce ta dafata da sauri ta share hawayenta don bata so Amma taga kukanta hankalinta na iya tashi, Amma ta mata murmushi cikin hausarta da har yau be fita tace Maysah kuka kike yi koh? Tace Aa Amma, Amma tace liar, na ganki kina kuka, kamar jira take ta fashe da kuka, Amma ta rungumeta sai da ta yi me isarta, tace Amma Yazayd Dan iska ne, Mashayi kuma Maz— Amma ta dakatar da ita ta hanyar sa mata hannu a bakih, Sai kuma ta mata murmushi tace Maybe ke xaki kubutar dashi daga sinful acts dinshi, ki nuna masa hanya madaidaiciya, Amma how? I cant, Amma tace shhh, mya Baby i trust u, u can even do more, Have Faith kinji? Ta gyada mata kai. Tace Oya tashi tsoho ya aiko A kiraki nace kina wanka, tashi kijei, jikih ba qwari ta daura dankwali ta fita. Amma ta bi bayan tillon diyarta da ido, tausayinta ya mamayeta, Allah ga Baiwar ka nan, Allah ka shige mata Gaba Amin..
******
Tsoho ya kalleta yace Rumah Nah, ba tare da ta kalle shi ba tace Naam Tsohona, yayi murmushi yace yau ko kallona ba zakiyi ba? Ko har ynz fushin akeyi dani? Ta qaqalo murmushi, haba Tsoho nah, wani irin fushi a na zaune kalau, ya girgiza kai yace Rumah kenan, my favourite among them all. Tayi murmushi, yace A tunanin ki na shiga tsakaninki da farincikin ki na hadaki da baki’n ciki, A Ganinki na hadaki da kunama me zafin Halbi, na san xakice anya Tsoho na sona? Ya hadani da Mashayi kuma Mazinaci? Maysah na san abinda nakeyi. Allah yayi yarinya me hankali, me tunani, me hangen nesa, da sanin ya kamata uwa uba ga ki da Hakuri, kinyo gadon kakarki Aishalle, Auren Zaid Jihadi ne, ke kadai zaki iya hakuri da halayenshi, ke kadai zaki tsaya tsaye a kansa har Allah ya sa ya bar halayensa, kuma nayi istihara tun kafin nayi hadin nan, naga Aurenku Alheri ne, Kece Rufun asirinsa. Rumah kin fahimce ni? Maysah ta daga kai tana kuka, tace eh Tsoho, Allah ya bani iko Allah ya sa hakan yafi zama Alheri tsoho yace Amin Rumah nah, sannan Abu na gaba, munyi magana da Mudassir yace Zaid zai fara housemanship dinshi Nextweek a Abuja a nan National Hospital, Asibiti ta bashi Gida, Amma na baku daya daga cikin gidaje na na Maitama, na yanke hukuncin dake zai tafi, sai ki fara Shirin tafia, gaban Maysah ya bada Hinqim tace Allah kaimu. Yace Amin, Gani yayi sai Kyarma takeyi, hakan yasa yace toh kina iya tafia, sannan Akwai Taron duka Gida Gobe da Safe Misalin Karfe 10 na safeh. Tace toh Tsoho Allah kaimu Goben. Yace Amin Ta miqe guiwa a sake ta bar Dakin tsoho.
******
Wallahi da an san yanda na tsana ganin Fadila da ba a yi gigin hada auren nan balle a daura, wlh na kijininta, Bilkisu tace ni wai ya ma za a aura mun Azzalumi kamar Suraj, ji dai randa ya kamamu ya zane, wlh na tsaneshi, Mu’ammar da yake ganin kamar ya fi su tashin hankali, babban tashin hankalinsa kuwa shine ganin an daura auren Hanifa da wanninsa, Zaid kuwa ba abunda ya damesa, chatting dinsa yake da Diyyan Shagali. Amira kuwa ta maidasu TV sai kallo take wannan yace ka za wannan yace kaza. Aunty Saadiya tace hajiar mu kice wani abu mana, toh dan ubansu sun ishe mutane da surutan banza su saman ido mana suga yanda zan warware alamarin nan, jira nake na ji ta bakin Alhaji, sai na san abunyi, Amma sun tasa ni gaba sai babatu suke tayi, ba sai na sa musu ido ba, Aunty Abida tace ynz dai haquri zamuyi gabaki daya, Sai mu jira muji me baban zaice gobe. Kun gane koh? Duk suka gyada kai, Amar yace hajia me zakiyi ke goben, ni burina a warware auren nan kawai, hajia tace kai dai ka bari sai Goben u shud all trust ur Grandma. Hajia Babba Ta kalli inda zaid ke zaune tace dan gidana Yaya dai banji kace komi bs? Ya kalleta ya watsar yace ban da ta cewa, tace wai ni mesa kake man haka ne? Miqewa yayi yace Jawad ka kirani idan baba ya dawo ya fice daga parlon, hajia babba ta hau masifa ina sonka kana gurxa man, sai wulaqancin tsiya shege me qiran samudawa, kowanensu sai da ya dara..
Gabaki dayan su sun Hallara parlorn tsoho suna zama jiranshi, da sallama ya fito daga dakinsa suka amsa mai, kujerarsa ya zauna aka fara kwasar gaisuwa, sai da aka gama kafin yayi gyaran murya tare da gajeruwar Muqadima, yace Ahhh A jiyan ne aka daura auren Jikokina su 12, Allah sa Alheri, ‘yan dakin hajia Ama da Umma Hajja kadai sukace Amin, Hajia Babba kuwa sai hura hanci take tayi, abu na farko, ya kira Hanifa yace taso nan, ta miqe ta nufeshi ya ciro wata envelop ya miqa mata kamar ba za ta amsa ba ta amsa yace dubu 50 ce sadakin ki ne, jiki ba qwari ta koma mazauninta ta xauna, haka ya kira Bilkisu, Islahulkhair, Amira Fadila da Rumaysah ya danka musu sadakin su a hannu, Sannan yace Ahh gobe lahadi, nasan gobe yan mazan zasu koma bakin aikinsu, to na yanke hukuncin kowannensu zai tafi da matarsa, Jikokin Hajia Babba suka zuba mata ido alamun zasu yi magana hannu ta daga musu alamun suyi shiru, bari taga iya gudun ruwanshi, Tsoho ya cigaba na bada kudadde zaaje Dubai a ma yanmatan kayan daki da na kitchen, da kuma lefe kuma na mallaka ma mazajen Gidaje a duk garin da suke aiki, Sannan kuma na chanza ma kowa mota nd kuma. Toh ina umurni da matan su Shirya, gobe zasu bi mazajensu… Hajia Babba tayi karaf tace kagama? Haba Alhaji? Ran tsoho a. Bace yace Karime menene haka? Tace bangane kowa ya bi mijin shi ba? Sbd me? Daga daurin aure jiya, sai kace an gaji da su,,, ta cigaba da bambami, Tsoho ya fara tarin karya kamar xai shife, tarin da karfi, kuma sai Allah ya kawo mai atishawa me zafi, ai nan hankalin kowa ya tashi, Hajia karime ta rude, sannu Ahaji, Baba hassan ya ruga firij ya dauko ruwa yana fadin Baba sha ruwa, ya ture ya shaqe murya yace ba ruwan da zansha ai haka take so ta ga karshe na koh?toh bazan sha ruwan va, ku barni na mutu kawai tunda ba za a mun yadda nakeso ba, ai nan ta fita hayyacinta, ta fara cewa ya haquri Alhaji, danAllah ka sha ruwa, wlh ko ynz kace su tafi zasu wuce, daman wai naga ba a shirya ba ne, amma yadda kace hakan zaayi, Allah ya huci zuciyarka, danAllah ka sha ruwa, Tsoho ya kurba Ruwan nan taro ya watse bayan an Tsaida maganan gobe kowa xai wuce da matarsa..
*****
Mu’ammar kamar zai yi hauka, fadih yake Hajia wai menene haka? Bangane ba? Ya akayi kika amince masa? Hajia babba tace dan ubanka so kake mijina ya mutu, haquri kawai zakuyi ku tafi dasu din, bayan sati 1ko 2 ku danqara ma shegu saki 3 3, da dadin bakih da jan magana suka amince da tafiar
Hajia Ama da Umma Hajja ne zaune parlorn Umma Hajja su ka tasa Jikokinsu gaba suna musu nasiha me ratsa jiki da ban haquri, tare da jadadda musu haqqin zaman tare da na auratayya, Da kuma ban Haquri, duk wanda yyi haquri zai ci ribar rayuwa a karshe suka samusu Albarka, sannan sukayi umarni da yanmatan suje su hada kayan buqattunsu kafin a aiko musu da wasu, haka suka miqe suna matsar Kwallah kowa yayi sashensu don shirya kaya..
RANAN
_Bibilicious Biebee_
Like · 3 · Reply · Report · Aug 4
Phatee Lamin
21. Gidan Ganduby Biebee
Tsoho ya kalli Aunty Nuratu da Aunty Zainab yace ku zaku raka Rumah Abuja dukda shi Zaid din yace sai Gobe litinin zaiyi reporting so tafianku sai gobe, ke Abida da Hassana zaku raka Islahulkhair gidanta da ke Zaria, Hussaina da Sadiya ku zaku raka Amira gidanta dake Bauchi, Raijana da Maryam ku xaku raka Fadila gidanta dake Kaduna, Yusrah da Rafiyyah kuma zasu kai Bilkisu gidanta dake Kano. Zayyad kuwa zai dauki matarsa Hanifa su tafi chan gun aikinsa a lagos… Ban san tashin hankali, Amare kawai nace a kai gidajensu bance ayi tsegunguma ba, ku tashi ku tafi, Allah ya tsare hanya. Suka amsa da Amin, nan fa aka fara bankwana masu kuka nayih, barin ma Islah, rumah da fadila da suka rungume juna suna kuka, sun ba kowa tausayi, don shaquwarsu ya wuce misali, ko tsoho kansa sai da ya share hawaye. Da qyar aka tura Fadila motar Ya jawad Aunty maryam da Aunty Raijana suka shiga baya, jiki Ba qwari ya Jawad ya zo ya durqusa gaban tsoho Tsoho ya mai Adduan Allah ya tsare, haka ma akayi da Islah Aunty Abida na huran hanci ta shiga motar don bata son tafian nan take ba. Haka Ya Muammar ya shiga motar bayan tsoho ya mai Addua, Yaya Yusrah, da Yaya Rafiyya suka ja Bilkisu zuwa motar Suraj, inda yaje yayi bankwana da kakaninshi kafin ya shiga motar Tsoho yace to ku tunda tafiar ku hanya ce kuna iya tafia. Allah ya bada zaman lafia ya kawo kazantar dakih, ba wanda ya tanka mai, Suraj ne ya fara jan motar sanna Mu’amar ya bi bayanshi sai jawad ke qareshe, Convoy sukayi suka bar gidan mudai sai dai muce safe journey.
******
Baba usman ne ya kebe da samir inda yake cewa Samir kaga kai da na ne, sbd Zainab kanwata ce ita ke bi mun, Akwai shaquwa tsakanina da Mahaifiyarka, ina so ka riqe min Amanar diyata Amira, donAllah kayi haquri da halinta, quruciya ce da sakarci ke dawainiya da ita A sannu zata dawo daidai, Samir ya hadiye miyau me dacih, wato kowa yasan Amira bata da wayau, har ana hada shi da Allah yayi haquri, wato yayi ta haquri shi yana cutuwa, da qyar yace ba komai baba, yace yauwa Samir Allah bada zaman lafia, Anya ba zaku bar tafian nan gobe ba ku bi jirgi? Yace aa bari mu ta tafia ynz, ina da abunyi gobe a office yace toh Allah muku Albarka, Samir yayi bankwana da kakaninshi, ya kwashi Amira da Aunties dinta biyu da zasuyi mata rakiya zuwa Bauchi state.
******
Gudu suke ta shatatawa, ba me cewa juna qala. Balle duk motan ba sa shiri, dama dama motar Suraj Rafiyya da Yusrah Kawayene su kan taba hira. Amma tsohon nan akwai hadin doya da manja. In banda dole me zai hada Aunty Abida da Aunty hassana a mota guda? Haka dai suka daure kowa na kai zuciya nesa har Allah ya kawo su Kano lafiya Unguwar Nassarawa GRA, Gida ne da ya amsa sunansa Gida, a yau ne Tsoho ya mallaka ma Ya suraj gidan nan, ko da suka iso maaikata sun gyara gidan sun kalkale, Fadila da Islah suka fito don kama ruwa, Aunties ma duk suka shigo banda Jawad da Ammar, Yaya Rafiyya tace ku Jawad ba za ku shigo ba? Ya gimtse fuska ganin An kawo bilkisu gidan waninsa be ganin zai iya shiga yace no yaya wadannan ma su fito mu tafi kar maghriba ta mana, yaya yusrah dai ta tabe bakih, tace ina kano ina kaduna? Mu’ammar ne ya yi qoqarin shiga ya dan leqa gidan, auntt tace ku ku muje ko? Kun san tafia mun da nisa, duk suka mimiqe, Islah ta kama hannun Bilkisu ta mata Sallama tace Allah ya hada fuskokin mu da Alheri, Harara bilki ta jefeta dashi, Fadila ko kallo bilkin ba ta isheta ba suka bar dakin, Bilkisu ta rungume Yayanta ta na kuka, Yaya pls kar ka tafih, bana son nan, Muaamar ya share mata hawaye a hankali yace dont cry sis, kin manta abubda Hajia babba tace? Dis is for a short period of time okay? Jus take care of urself Ta gyada kai u too, Suraj na kallonsu ya tabe bakih ya kaufa kai. Mu’ammar ya fita. Haka suka qara daukan hanyan Zaria, in less dan 3hours suka iso Zaria, Cikin gari sukayi Kuyambana Lowcost, inda Tsoho ya ba Mu’ammar gida, haka dai suka shiga gidan suka firfito har yan motansu Jawad, shima dai ya fito, suka nufa ciki, Akwai dan Kurah a gidan suka kakkabe, don shi Mu’ammar ya qiyin waya a zo a gyara. Bayan sun dan huta ne su Jawad suka musu Sallama hardasu Aunty Abida da Hassana don gobe zasu bi flight din maiduguri kuma ta kaduna zasu tashi, Islah ta sha kuka sosai, don ba wanda aka bar mata daga ita sai Muaamar, tana kallonsu suka shige mota suka nufa Kaduna, suna barin gidan shima Mu’ammar ya bar gidan don bejin xai iya kwana under same roof with wata idan ba Hanifa ba. Nidai Bie nace Islahulkhair u are on ur own oo
Gab da Isha’i suka shigo Garin Gwamna, sai da Jawad ya biya dasu Mr Biggs sukayi take away, ya kuna tsaya a One Eleven ya siyo musu Kaza da Masa kafin yayi Unguwar rimi Lowcost dadi inda Tsoho ya ba Jawad Gida me dan karen kyau. A gajiye suka shiga gidan, gidan yayi kyau matuqa. Nan suka zauna a parlo suka huta.
Samir ya kira Jawad yace yadai kun isa? Yace shigowar mu kenan, shima Samir din yace mu ma ynz muka shigo bauchi, Allah huta gajia sukayi bankwana…
WasheGari
Ya Suraj ya kai su Yaya Raffiyya Airport don yau zasu wuce Maiduguri bayan su mai nasiha sosai,haka ma Samir ya kaisu Aunties dinsu Airport, Jawad ma ya yankan musu Tickets din komawa Maiduguri…
Maiduguri
Haka ma aka kawo Yazayyad da Hanifa Airport su biyu rak bayan ta sha kuka sosai, suna zaune suna jiran jirginsu da zai tashi zuwa lagos. Shi ko Zaid ya kwashi Aunty Nuratu da Aunty Zainab da Maysah a mota suka bar gidan bayan Tsoho ya kebe da Rumarsa ya qara jaddada mata, sun kusa wajen Garih ne ya latso wayarsa ji kawai sukayi yace Na kusa dags bisani kuma suka ji ya gangara bakin titi ya parker, ba wanda ya tanka mishi, ta gilashin mota ya hangota, ya kalli Maman Samir da ke zaune gaban mota yace Aunty Zee dan koma baya, mun qara samun pasinja, tace pasinja kuma? Be tanka ta ba ya bude murfin kofa duk suka bishi da ido gurin wata suka ga ya nufa, Ta sha Ado sosai ta na janye da Akwatin Trolley, Gaban Maysah ya buga sakamakon wacce ta gani ba kowa vace illah wannan da suka ga ta na bacci kan Gadon Yazayd, wacce sukayii fada da Amira, toh wacece wannan?to ba kowa bace illa Baddiyan Shagali, Da sauri Maysah ta fara maimaita inalillahi da ita zaa Abuja? bude booth yayi ya tura Akwatin Diyyan Shagali, kafin ta zo ta bude gidan Gaba ta fada tana me karya jiki da feleqe ta juya baya ta bi su da kallo daya bayan daya ta watsar, bata da niyyan tankasu, duk irin tsageranci na Zaid sai yaji be ji dadin hakan da tayi ba, a hankali yace Dear, My Aunties, ta dan juya tare ds yin kicinkicin da fuska tace Ina kwananku? Aunty Nuratu ta kasa haquri dai tace Zaidu wai Wacece wannan????
_Bibilicious Biebee_
Like · Reply · Report · Aug 5
Phatee Lamin
22. Gidan Ganduby Biebee IsaZaid ya danyi gajeran tsaki yace Aunty sunanta Badiyya, Aunty Nuratu ta yi shiru da bakinta haka suka dauki hanyan Abuja, Gudu suke ta shatatawa, sun tsaya sun ci abinci a kano kafin suka dauki hanya kuma.
Lemmie help u wit ur seatbelt, ta galla mai harara tace i dont need ur Help, Zayyad ya yi murmushi ya saka nashi belt din, Jirginsu ya fara tafia Matuqar tsoro ta tsorata, ba yau ta fara hawan jirgi ba amma ta tsorata da tashin Jirgin yau, bata san tym din da tayi saurin dafa YaZayyad ba da jirgin ke niyyan tashi tare da rintsa ido, Zayyad yayi murmushi yace Ashe yarinyan na da tsoro, da sauri ta janye hannunta daga nasa ta galla mai harara, be tankata ba, illa ya ciro Chalbin shi a aljihu ya fara Ja. Haka suka daidaitu a sama suna tafia har bacci dai sai da tayi a kafadun YaZayyad ba tare da saninta ba, Cikin Awa daya da yan mintuna suka iso LAGOS, hanifa ta gaji sosai, Cab ya tsaida musu suka hau, har gidansa da ke wani unguwan da sai na tambayo sunansaGida ne self contained, ya biya me tazi din ya kwashi kayan shi da nata ita ko handbag ta dauka, Nidai nace Waiyo Allah Zayyad Bawan Allah, be dau abun da Zafih ba, idan ta qi bada kai ka zane ta kawai
Zayyad Hussaini Zailani Matashi ne dan kimanin Shekaru 29, yaro ne kyakyawa wanda be da matsala ko kadan, hak’urin shi ya wuce misali, Yana aiki ne a Birnin Lagos A wani Companyn Oil And Gas. Rokonsa daya Allah ya bashi Zaman lafia da wannan er Zafin kai ni dai nace Amin.
Sai dare suka iso Abuja, Straight sai da yaje Garki ya ajiye Diyya yace mata sai yazo, kafin ya dauki hanyar Gidan da Tsoho ya mallaka mai dake Maitama, Gida ne na ‘yan mala’u masu brush da cinyen kaza, gidan ya tsaru iya tsaruwa, Su Aunty nuratu suka shige dakih da huta gajia.
Zaid Mudassir Zailani tsaran Zayyad ne amma Zayyad ya bashi kwana 14, ya na da kwalin degree na likitanci, A gobe ne zai fara HouseManship a National Hospital Abuja, Zaid be da wata matsaala in banda ta shaye shaye da kuma tsageranci, Toh gashi an hadashi da Salihar Mace, toh ko ya tafian nan zaiyuwu?🤔
Ko da Jawad ya kai su Aunty Abida Airport bayan tashin su straight Office dinsu ya nufa, Jawad Mudassir Zailani Matashi me ji da kanshi dan kimanin shekaru 27 ya karanta Industrial Chemistry, ynz haka yana Aiki a NNPC kuma tauraruwarsa na haskawa don yana da himma da qwazo, Jawad na da zafih be son raini kwata kwata, gashi an hada shi da Macen da ba a tabata ta kyale duk girman mutun. Toh ku biyoni dai muje.
Samir kuwa tunda ya kaisu Aunty, ya tafianshi Office, Samir dan kimanin shekara 27 ya karanta Engineering, samir na da sanyin zucia, be da matsala, Samir Injiniya ne wanda ake damawa dashi a garin bauchi, Matashi ne ko shekara daya be rufa da fara aiki a Bauchi ba, Amma ko ina damawa ake dashi, balle gwamnati da ke bashi kwangiloli, Samir Gambo Zailani kenan Matashi me ji da kudi, Young Billionaire. Toh ya zaman shi zai kasance da Psychic lilsismeeranshi?🤔
Hmmm Mu’ammar Labaran Zailani, Matashi me shekaru 28 a dunia, Ya hadu iya haduwa, Shima dai Injiya ne amma na jirgi, wanda ake kira da Air Police Engineers, Mu’ammar na aiki ne a nan Air force Aviation da ke Zaria, Mu’ammar dan zafin kai ne, Shi ya sa abu a gaba to sai ya cimmai, in ko ba haka ba ya shiga damuwa, Tunda ya iso Zaria ya bar Yar baiwar Allah ita kadai ciki, ita kadai ta kwana, ya tare gidan wani Abokinsa Ahmad, don shi gani yake ba zai iya kwana gida daya da Islahulkhair ba, don ya na mata tsana me zafih, toh su Amar ga shawara idan zaka k’i mutum ka k’i shi saisa saisa don ba a san wanda gari zai waya ba.
Suraj Umar Zailani dan shekara 27 a dunia, Matashi ne dogo kyakyawan gaske, ya Karanta Architecture, Yana aiki ne a nan kano mostly Gwamnatin kwankwaso ta tsaya mai wuri zanen Tituna masallatai, makarantu d.s, Suraj ya qware ta fannin zaneh, ko mutum zai zana shi tsaf, Suraj na da kirki yana da haquri amma abu kadan ke bata mai rai baya son raini ko kadan, Arch. Suraj kenan Angon Bilkisu er baba labaran.
Da Daddare
9:30pm;; Samir ne ya paka motarsa ya fito, da take away a leda ya yi hanyar parlonsa, zaune take gaban kofar parlorn, gashi dare ya farayi, kawai ganinta yayi zaune, sai da ta bashi tsoro, ita kuwa tana ganinshi ta miqe da sauri, Ta nufo shi ds niyyar rungumsshi, Ya gimtse fuska tare da matsawa baya, Bigbrosamir, tunda safe ka bar gidan nan, ina ta kiran ka ka qi dauka qarshe ma ka kashe wayanka, ina taji tsoro nikadai a gida, be tankata ba ya raba ya bude kofa ya shiga ciki, ledar take away din hannunsa ya ajiye kan dinning, ya shigewar sa dakih donyin wanka. Zuwa tayi ta bude ledar taga kazah ce da Fresh Yoghurt, ta nufa kicin ta dauko plate tayi dakin samir dashi, tym din ya fito wanka ya na tsane kansa da dan qara min hand towel, dagowan da zaiyi ya ganta tsaye, dan guntun tsaki ya sake, tace bigbrosamir ga abinci kazo muci, kamar ba zai tankata ba yace ni na koshi, wannan nakine, Tace Allah ko? Toh nagode, ta zauna kan kujera kamar zai yi ihu don takaici, ya daure dai yace Amira i want to dress up, ba tare da ta kalleshi ba tace go ahead mana, m ur wife ryt? Ganin idan ya biye mata ranshi zai baci ya zira jallabiyanshi ya koma toilet, ta gama cin kazarta ta sha yoghurt ta kai plate kichin, ta shiva dayan dakin ta yi wanka tare da sa nughtgown, ta koma dakin Samir, har ya kashe wutan Dakin ya kwanta yana latsa waya, Gadon ta haye, da sauri ya miqe tare da kunna side lamp, ya daure fuska, ke Amira Lafia?? Tace menene bacci zanyi, Yace ki fita mana ki koma dayan dakin, tace jar uba, ni kadai ral cikin dakih, to ba zan iya ba, ka fita ka barni ni kadai na haqura ynz u expect me to sleep all alone? Hell No, wlh nan zan kwanta, samir kamar zaiyi hauka don takaici, a hankali yace Amira pls ki fita, tace lallai bari ma ka gani, ta gyara kwanciyarta kan gado, Cikin daga Murya yace Amiraaaa ta dago sosai dan taji muryan sa kamar me shirin yin kuka, yace please leave, tace nifa na gaya ma i aint going anywhere, ya miqe ya dauki pillow yace Please Amira dont make me hate you..
Like · 1 · Reply · Report · Aug 5
Phatee Lamin
23.Gidan Gandu by Biebee Isa
Mamaki ya rufe Amira, Toh me yayi zafih haka? Ya samir me na maka haka har kana kira min kalmar Tsana? Be tankata ba ya dauki pillow ya bar dakin parlo ya nufa ya kwanta kan doguwar kujera, Ba ta san lokacin da ta fashe da kuka ba, a rayuwarta yau ne a ka taba mata abu ba tare da ta rama ba, yau ne aka mata abu ta tsaya tana kuka ba tare da daukar mataki ba, in banda Yasamir wa ya isa ya takata haka? Waiyo Allahnta, ya zatayi? Ga wani son samir da ya shigeta farat daya, haka ta dinga rubzar kuka har bacci yayi awon ga ba da ita.
Kaduna
Ko da Jawas ya iso gidan karfe 10 da wani abu, xaune ya iske hakimar wato Fadila a parlor ta na kallon Series din nan na “Married Again ” Dakinsa ya wuce straight ita kuwa bayan sallamar da ta amsa mai ko kallonshi ba tayi ba. Ta cigaba da kallonta tana kada k’afa daga bisani ta miqe tayi kicin don dafa indomie. kichin din shaqe yake da kayan Abinci ko mi akwai don Tsoho sai da ya cika su da komai na abinci kama daga kayan miya, nama, kaxa, kifi, kai harma da tolotolo
Lagos
Shigowar sa kenan Gidan ya nufa dakih, ka sancewar gidan 1bed room ne amma dakin me girma ne, kwance take kan gado tana hawaye, ya cire bakih ya kirata yace Hanifa, hanifa, banza tayi dashi kamar bata san yanayi ba, da yaga ba zata kulashi ba ya shigewarsa toilet din dakin, ya yayi wankansa ya dauro Alwala yayi shafa’i da wutr, yazo ya chanza kaya zuwa na bacci, ya hau gadon ya kwanta, kukan ta takeyi ba ta fasa ba, Shi filazal baya son kukan mace, ya daure dai ya ce Hanifa donAllah kiyi shiru, bana son kukan nan naki, ko me yayi zafih maganinshi Allah, kiyi haquri mana, cikin tsiwa ta miqe tace kai mallam saurara min, ina ruwan ka da kuka na? In kaji zafih ka sakeni, yayi murmushi yace banji zafih ba Allah ya baki haquri, have a Sound sleep, yayi kwanciyarsa tare da juya mata baya, takaici ya sa ta saki wani kukan da qarfi, shi ko yayi saurin runtse idanuwansa, da yaga taqi shiru pillow ya dauko ya fita sitroom, tsoro ya mamayeta kamar tace ya dawo, Amma taurin kai da irin zuciyar Hanifa ya sa ba ta nuna komi ba, amma harga Allah tana tsoron kwana dakin nan ita kadai, haka ta kwanta rabin ido daya a rufe rabi a bude (lol)
Zaria
Taci kuka har ta qoshi, tayi sallah ba adadi, a tsoroce take, tun jiya rabon da taga Mu’ammar, haka ta kwana cikin tamfatsetsen gidan nan ita kadai, hankalinta ya gama tashi, da qyar ta dafa Taliya tacih, ta kira Wayan Maysah a kashe, ta kira fadila ta ci saan wayar ta kunne yake, amma ba a dauka ba, kasancewar wayar na chan dakin ita kuma fadilar tana parlor tana kallo, wani kukan ya subuce mata, gashi ba ta san kiran Umminta don kar hankalinta ya tashi, Dare kuma Ya Tsala, haka Islahulkhair ta kwana tana kuka, da ta ga kanta na neman Bugawa sai ta dauko Alkurani mai girma ta shiga karatu. Shi ko Mu’ammar na nan Gidan Abokinsa Ahmad, ya ma manta da yana da wata mata a Gida.
Kano
Ya shigo da sallama ta na jinsa amma tayi biris dashi, ya qara doka sallama tayi banza dashi, qarshe ta hau karkada kafarta, da qarfih yace keee bilkisu, ba ki jin ana sallama ne? Ko ba ki iya amsawa ba? Cikin tsiwa ta kalleshi ta haraeshi, tace naji kana sallama, na iya amsawa, ban dai ga damar amsaka bane, fuuu ta wuce dakinta, zuciyarsa tayi k’una, har ya bita dakin don ya lakada mata na jaki, sai zuciyarsa ta haneshi, ya danne zuciyarsa, yayi kwafa. Ita kuwa tana shiga dakin ta dinga murna ta bakanta ma Suraj, haka ta dinga kullah yanda zata dinga chuzguna mai har sai ya saketa kafin Hajia babba tayi na ta aikin.
Abuja
Da Safe, Ya kaisu Aunty Nuratu Airport, bayan sun dade kan Maysah suna mata nasiha don sun lura da take taken zaid, tasha kukanta, haka suka rabu, sai da yaga tashinsu kafin ya wuce National Hospital, yaje yayi reporting dama suna expecting dinshi, aka bashi office da tag dinsa a rubuce an sa Dr. Z.M Zailani Nan take ya fara ganin patients cikin kwarewa, yanda kasan bature haka yake tafiar da Alamuransa. Har misalin karfe hudu, ya tattara yana sa yanasa yayi signing out ya tafiarsa. Hotel din da ya sauke Badiyya ya nufa, ya kirata a waya, ringing daya biyu ta dauka, yace gani na iso,sauko qasa, a yangance tace ba ni kadai ce ba fa, yayi jim chan yace ke da waye? Tace ni da mamana, shirun ya qarayi chan kuma yace yaushe tazo? Tace yau din nan, to ku fito muyi ta tafia, bayan mintina 12 sai gashi sun sauko, ta side mirror ya hangosu, ko wannensu dauke da akwati trolley, maman baddiyya ta qi amincewa ta tsufa, irin shegun matsatsun kayan nan ke jikinta, fuskan nan tasha coiling ga gashin doki a kai, wannan shine like mother like daughter. Kwankwasa mai tayi yayi winning glass da murmushi a fuskanta tace Oga a bude Booth ko? Yayi smilling back tare da bude booth din badiyya da uwarta sukayi kiciniyar saka kaya a booth gogan ko fitowa beyi ba. Suka shiga motar, ko kallon arziqi be ma uwar Badiyya ba yace, Ina wuni mama,Ita ko a ranta cewa take Ashe diyyata bata yi karya ba, Zaidun nata hadadde ne, ta amsa cikin wani murya sai da diyya ta juyo ta kalleta. Zaid ya ja mota sai gidansa dake Maitama.
Ta zage ta dafa Tuwon semo miyan agushi da yaji ganda, ta kai kan dinning ta ajiye, tun dazu take zaman jiranshi, har bacci ya dauketa kan 3sitter, Sun iso gidan suka dinga kwankwasawa shiru, Zaid ya kwala ma maigadi kira yazo jikinsa na rawa, yace kai wata ta fita daga gidan nan? Yace auu akwai mutum ciki? Zaid yace ba tambayar da na maka ba kenan, yace Yallabai indai ka bar mutum a nan to ta na ciki, don tun da safe ina nan zaune ba inda naje. Zaid yayi tsaki ya ciro keys ya kalli su badiyya yace muje Badiyya da ta gama cika tayi fam kamar ta pashe ta ja akwatinta uwar na biye da ita a baya, suka zagaya baya, zaid ya sa mukuli ya bude wani qofa ashe ta kichin ne, tun daga kicin din suke jin wani daddadan k’amshi, har suka iso parlorn, kwance ya ganta tana bacci, kallo daya ya mata ya dauje kai, idonsa ya sauka kan dinning yaga kulolin abinci, ya tabe bakih, Diyyan ta kade ganin tsaruwar gidan, ya kalli uwar diyya yace feel at home mama, ta sakar mai murmushi ok son, ya kalli diyya yace bari na shiga na yi wanka, tace dear, ai da ka barih kacih abinci yar matarka, ta qarashe tana zolayarsa, ya dan bata rai yace nahhh, you go ahead, ya ja briefcase dinsa yayi dakihnsa, suko nan suka dire kayansu suka nufa kan table, Diyya na bude kular miya taji wani qamshi, nan da nan miyonta ya tsinke, sai da ko ta lasa, ta zuba a plate, ta sam mamanta, nan suka hau ci, daman mulmula biyar ne, diyya da Maman ta suka kwashi tuwon nan tassss. Cikin bacci taji ana buruntu tayi sauri ta tashi, idonta ya sauka kan Diyya da mamanta, Gabanta ya yanke ya fadih. Diyya ta juyo ta ganta tsaye, Auu Rumaisah kin tashi? Zo ki kwashe kayan nan ki kai kicin, sannan kizo ki shigar min da kayana dakihna, ki nuna ma mama dakinta, Hantar cikin Maysah ya bada Kulululu. Meke shirin faruwa da ni? Ta tambaya kanta.
0 comments:
Post a Comment