dakinta take nufi zata kai kayan Badiyya, to ita ina zata kwana? Muryar badiyua ya katseta yace ke ki min sauri, hakan ko Maysah tayi, Maman badiyya tayi daria woo diyata baki da wasa, Badiyya tayi daria tace ai mama Yar aiki muka samu, tunda tayi qoqarin shiga gonata ga hukuncinta, ai naso auren nasu ya dore ya dade da ta mun bauta har sai naga wannan kyaun ya disashe, amma duk da haka zan moreta na sati 1, tunda lokacin aurensu zaiyi expire. Suka dau shewa tare da kashewa. Nan suka zauna suna kallo ba Maghriba balle Ishai, ita ko bayan sallah ta shiga kichin ta gyara, sai da ta qara tuqa tuwon don akwai sauran miya.
Wuraren qarfe 11 maman ta ma diyarta sallama ta shiga daki don huta gajiya, Badiyyan ma ta shige dakih da watsa ruwa, tun dazu maysah ke kichin zaune, har ta fara gyangyadi, bacci kawia take sonyi, jin ta daina jin hayaniyarsu yasa ta leqowa parlor, ba sa nan, zuwa tayi ta kashe tv din, ta dauko throwing pillow ta ajiye a kasa ta kwanta ta re da chusa hannayenta tsakankani cinyoyinta alamun sanyi. Nan bacci yayi awon gaba da ita.
Ko da ya fito parlor ya kunne wuta ganin ta yayi kwance, kallo daya ya mata ya dauke kai, dayan dakin ya shiga, kwance ya ga Maman Badiyya daga ita sai Underwear tana waya, bata yi wani yunqurin suturtace jikinta ba shima be damu ba, yace mom ina Badiyya, tace tana dayan dakin, ya rufe yana mamakin dayan dakin kuma, dakin ya nufa ganinta yayi xaune gaban dressing mirror tana shafa, ta mirrir ta hangishi, myzayd ya dai, ya dan bata fuska, yace kinsan dakin yarinyar nan ce nan ko? Tace toh me kake nufi? Yace gata chan kwance parlor, tace y do u care? Yace i dont, but its not fair a zo gidan ta a fidda ta wajeh, badiyya ta qwale ido, kar dai Zaid taussyin yarinyar nan yake, in haka ya faru ita kam ta kade. Ta dai daure tace ya kake so ayi? Yace ki koma dayan dakin ita kuma ta dawo dakinta. Tace ni gaskia ba zan iya kwana da mama ba, kwana take ta na waya, ya danyi tsaki, tace sai dai ko dakin ka, ya yi hanyar fita yace ko ina zaki kwana ki kwana, just leave dis room,. Parlorn ya koma, da qarfi ya dinga cewa Keh, keh tashi ki koma dakih, cikin bacci taji kaman muryan shi, da sauri ta miqe tacw Yazayd ina wuni, ka dawo lpy? Yayi hanyar dakihnsa yace ki shiga dakinki, nan ta daskare ganin badiyya ta fito da wata irin shegiar nyt gown tayi dakin mijinta. Hawaye suka shiga reto wlh da ma kwanciyarta tayi a parlor ta bar mata dakin, ds ta bar wata ta shiga dakin mijinta. Tana gani badiyya ta shige dakin Zaid tare da kullewa. Maysah ta zube kasa tana kuka. Da ta ga hakan ba zai fisshe ta ba ta shige dakih ta dauro Alwala ta hau Sallah.
Kwanciya yayi kan gadonsa, ita ma badiyya ta haye, nan suka fara iskancinsu, Zaid na ganin badiyya na qoqarin wuce gona da irih yayi saurin tunkudeta, idonta ya kada yayi jaaa, cikin dakusheshen muryarta tace please Zaid, just once, pls Zaid, ya miqe tsaye yace kinga abunda ke hadani da ke ko?nace miki bana so, yayi shigewarsa toilet, Badiyya ta fita hayyacinta ta shiga murqususu a kan gado, har ya fito kallo daya ya mata ya kawar da kai, da qyr tace Zaid pls help me Help ne i need u, ya ce ok, briefcase dinshi ya dauko, ya ciro wani magani ya dago fuskanta ya titila mata ko minti 5 ba tayi ba ta fara bacci. Ba ta farka ba sai 11safe. Ranta a bace ta waiga ta waiga ba Zaid, ta ha ba brief case dinshi. Ta jayo wayanta ta kwada mai kira, A lokacin kuwa ya na zaune a office ya na duba wani patient, kiranra ya shigo, yaqi dauka sai da ta mai 3missed calls, a na hudun ne ya kalli patient din yace excuse me, ya dauki wayan Hello Diyyana, cikin fada ta fara fadin Zaid y are u doing dis to me? Isit bcoz i lov u? Cikin mamaki yace me na miki diyyata? U knw i wont hurt u knowingly, tace i asked u to help me not to doze me off, ya danyi murmushi yace dats d only help i cud give u, I told u na tsani Zani, ki yi haquri har muyi aure mana, yanxu dai ina diba patient, sai na dawo ba tare da ta ce komai ba ya kaahe wayarsa. Baqinciki ya tokareta Wato ya tafi Aiki ya barta kwance a nan kamar kayan wanki,Bata taba ganin Dan iska irin zaid ba, wato baka zina amma kana shayeshaye? To meye bambancin dambe da fada? Zaid ka bini a sannu tayi kwafa ta shige toilet.
Tun da tayi asuba ba ta koma ba, ta na kichin tana hada musu breakfast don ta san Zaid zaije office, wurin 7 ta shiga wanka, ashe har zaid yayi tafian shi, ba ta sani ba, tana ta zama jiransa ba shi ba alamarsa, duk yan gidan dai bacci sukeyi. Qarfe 12saura badiyya da uwarta suka fito suka hau kan table suka kwashi abinci, Maysah ta zo tana gaidasu ba wanda ya amsa, da ta gaji ta miqe zata tafi Maman badiyya tace ke Rumaisa jeki soya mun doya zallah bana son me qwai din nan, haka maysah taje ta sake wani soyen. Haka dai Maysah ta yini ta na bautar Diyya da Mamarta..
5days later.
Haka rayuwan Bayin Allahn nan ya cigaba da gudana duk gidajen nan ba Zaman Arziki, Ba me kula kowa, Amira kullum sai ta ma Samir magana a takiace ya ke bata amsa, Zayyad kullum sai ya ma Hanifa magana ko tana da buqatar wani abu ko kallo be isheta ba, Jawad ko kula fadila ba yayi, trust fadila ita ma harkan gabanta takeyi, ko abinci daidai cikinta takeyi, Bilkisu da Suraj kamar mage da bera, kullum sai ta mai rashin kunya, Islahulkhair bata qara saka Mu’ammar a idonta ba har ta saba da zaman kadaici, Maysah kuma na yin bautar karuwa da uwarta, Zaid ko lasan abincin ta be ta bayi ba, ita kuma bata taba gajiya da aikinsu ba, Kullum sai tsoho ya kirata bata taba nuna mai komai ba nan zai ta mata nasiha yana samata Albarka….
Bibilicious Biebee
Like · Reply · Report · Aug 5
Phatee Lamin
25. Gidan Ganduby Biebee Isa
Yau Juma’ah misalin qarfe 11 na safe Ya shigo gidan tana bacci a parlor taji ana qwanqwasawa abun har ya dan bata tsoro, ta miqe ta nufa qofa ta bude, Mu’ammar ne tsaye, tayi mamakin ganinsa ba tare da yace mata komai ba ya raba ta gefenta ya shige ciki bayansa ta bi da kallo, ya shige wani dakih. Zamanta tayi a parlo ta kunna TV, Wayarta tayi qara fadila ce ta dauka sis yane? Tace lapya ya gida,? Tace hmn ga gida nan, ina Ya Jawad? Fadila ta tabe bakih, yau wurin 10 ya shigo gida naga ya hada kayansa qila Maiduguri zaije, Islah tace kuma bakwa magana? Fadila tace ni ko iskar da deboshi ba sani ba, Islah zata ce wani abu taga Mu’ammar ya fito da dan jakka a hannu ya na waya, okay kana qofar Gidan? Gani nan fitowa ya bar parlorn ba tare da ya tankata ba. Islah ta fashe da kuka, fadila na tambaynta ta kashe wayar gabaki daya.
Bayan Jumaa Suraj ya fito da dan akwatinsa ya kalli bilkisu dake lunch yace Ni na tafi Maiduguri, tayi tsalle tace wa zaka bari a gidan nan? Yace ke mana, tace kambu, ai baka isa ka barni ba, tare zamu tafi ko wallahi ba zaka dawo ka sameni ba. Yace toh ki yi yanda kikeso, don ni kam ba inda zaki bini, ya fita tare da rufe kofar wajeh ya ja motarsa. Ihu bilkisu ta sa ta dinga tsine tsine.
Maiduguri
Jawad da Mu’ammar sun iso Maid lafiya kasancewar tare suka taho, Jawad ya biya ya dauki Mu’ammar straight Sashen Hajia Babba suka nufa, Ta na ganinsu ta hau murna, ga mutanen Garin Gwamna, sannunku da zuwa, daman kuna tafe, Mu’ammar yace ba dole ki ganmu ba, ai nan Zuwa mukayi don a raba auren nan, don tun da aka kaita ban kwana gidana ba, Hajia babba tayi daria tace shege Ammar, kuzo ku ci abinci sai muje ayi magana. Suka qarasa ciki, suka ci abinci ko wannensu yayi sashensa, Aunt Abida ta rungune Jawad, Son haka kayi baqih? Yace Umma ba dole ba, ina kwana gida daya da maqiyyana ai dole na ke chanza kala, tace Ina danuwanka? Yace wai ba zai samu damar zuwa ba week din nan don shine Dr on call saturday nd sunday, but yace idan an raba auren zai sa yarinyar a jirgi, tace toh shkn, Abunda sai mu jira muji me Hajiar ta shirya. Mu’ammar ya kira Jawad yace kai mu hadu Sashen Tsoho kar labari yaje mai mun iso tun dazu ba muje mun gaida shi ba, yace toh muje..
Ko da suka isa Sashen Tsoho, Suraj na nan zaune suna labari da tsoho Sallama sukayi, Muammar ya daure ya ba Suraj hannu suka gaisa, banda jawad din da ya dauke kansa ya maida hankali gurin gaida tsoho, Tsoho yayi murnar ganinsu, ya dan zolayesu da Angwaye kun sha qamshi, aiko suka sha kunu dukansu, suka miqe zasu fita yace ku zauna mana muyi hira, haka tsoho ya dinga jansu labari, ina matayenku,? Ince dai ba wata matsala koh? Shiru suka mai. Sallamar Hajia Babba ta katse musu hanzari, Anty Abida da Aunty Sadiya na biye da ita a baya, Bakih har kunne tsoho yace Karime kinga Angwaye koh? Ta tabe bakih, tace Alhaji magana nake so yi, ya dan gyara zama yace wace irin magana kenan?Alhaji Auren da a aka ma yaran nan nakeso a warware shi gabaki daya banda na Amira da Samir yanxu, tsoho ya kalleta sosai. Yace saboda me? Ai idan na daura aure, ba warwara ba sakih duk rintsi duk wahala ya qullu kenan sai mutuwa zata raba, Hajia karime ta harzuqa, Kai Alhaji kar ka raina mana wayau mana, Auren da aka daura don a sama maka lapya yaran nan suka amince, ba sa son junansu amma tunda ka warke yanzu dole za a raba, ko wannne a bashi wacce yakeso, Tsoho ya kalle ta sosai, cham ya kwada ma Sarkin Gida kirah, sai ga Mallam Iro ya shigo jiki na rawa, Tsoho da idonsa yayi jaaa yace je ka kira min Kowa. mallam iro ya fita, yaje ya kira duka yan gidan cikin mintuna kadan kowa ya hallara parlorn tsoho, parlorn yayi tsit ana jiran aji abinda tsoho xaice, ya kalli hajia Babba da take murnan haqanta ya cimma ruwa, yace Karime maimaita abun da kika fada, ba kunya ta maimaita, Tsoho ya miqe ya shiga dakih sai chan ya fito Da Alkurani izzu 60, ya riqe ya ce ni Musbahu Zailani, nayi rantsuwa da kuranin nan, duk randa daya daga cikin maauratan nan da aka daura aurensu jummar da ta gabata, ya saki matarsa ko da saki days ne, to Na saki Karime saki 3, kuma na tsine ma mahaifansa, Inallilahi wa ina ilaihir rajiun kowa ke maimaitawa, Banda Hajia babba da ta sake Ihu na shigesu, Alhaji Me yayi zafih haka? Yau na banu, ta fashe da kuka, ita tasan ba zata iya rayuwa ba tsoho ba,(lol)shima tsohon ya san karime na sonsa, ta dinga kururuwa, Hajia Ama da Umma Hajja suka jinjina kai. Ya kalli su Mu’ammar da jawad da suka kidime iya kidima yace Ku gaya ma yan uwanku saqo na, idan har kuna so na tsinewa iyayenku, na kuna saki kakar ku toh ga takarda nan ku rubuta wa matan ku saki. Ya ce ku tashi ku tafi na sallame kowa. Jiki ba qwarih aka fara watsewa, banda karime da tako kusa da Tsoho, don Allah Alhaji kai man rai, tun kuriciyar mu baka saken ba sai ynz? Ka san ina sonka, don Allah kar kai min haka, yace karime ina sonki, ba xan sakeki ba , amma da yaran nan sun saki matansu, to kema a bakin aurenki fah, da sauri tace wlh ba me sakar kowa, ai auren nan mutu ka raba, Allah ya basu zaman lapya ya hada mana kawunannasu, Tsoho yayi murmushi ya san karime ciki da bai hakan kadai ne maganinta. Yace Amin karime ta
Tafia sukeyi amma ba me ganin gabansa, Mu’ammar yayi tangartangar zai kife Jawad yayi saurin taro shi, yace haba mana Mu’ammar, calm down mana, Mu’ammar cikin fushi yace Calm down? Ana nufin idan na sake yarinyar nan za a tsine ma uwata? don na san ko ya tsine ma baba ba zai bishi ba, don ba shi ya haifeshi ba, Amma dagaske yake sai ya tsine ma er sa ta cikinsa, uwata? Wallahi na tsane yarinyar nan, ba na sonta bana qaunarta, Kamar yanda nima Bana son Bilkisu kuma bana kaunarta ba, jawad da Mu’ammar sukayi saurin kallon me furucin nan, Suraj ne ya nufosu, ashe yana jinsu, Jawad ya tunzura, yace ance maka ita ta na sonka ne? Ni jawad ni kadai takeso, zaka qarasa rayuwarka da matar da ba ta sonka, nd its going to kill you inside dat she loves me alone, Suraj yayi murmushi ya juya dubansa ga Mu’ammar yace let me make one thing straight, Islahulkhair is my only sister, ina sonta fiye da kaina, Idan na sake naji ka mata wani abu wlh baza mu kwashe da kyau ba, dat reminds me, M married to your sister Bilkisu, Hurt my Sister and i will hurt yours. Don Er uwa ba ta fi Er Uwa ba. And to you Dummy ya kalli Jawad, kai ma kasani fadila ba ta sonka bata kaunarka, ni kadai takeso nikadai ke zuciyarta, kaga we have one thing in common. So i can leave wit this. Nd da kake ikirarin bilkisu ba za ta taba sona ba, yayi dan daria ka manta ni Architect ne? Toh idan ka manta bari na tuna ma I am an Architect, i will do what i do best, I will Redesign, Rebuild and Reclaim her Heart. Yana kaiwa nan yayi tafiarsa ya bar su tsaye kamar Robot.
_ Bibilicious Biebee_
Like · Reply · Report · Aug 5
Phatee Lamin
26. Gidan Ganduby Biebee IsaRansu in yayi dubu ya baci, ko wannensu ya wuce dakinsa ransa na mai Zafih, Jawad na shiga dakih ya kira Zaid, ya Zayyane masa komaibda abinda Tsoho yace, Zayd yayi dan jim, chan kuma sai yace shidai ya sani, ni banda matsala, tayi ta zama da igiyar aurena, ba sai na kulataba?
Asubar fari Mu’ammar ya baro borno motar haya ya hau, ko Jawad be san ya tafi ba, ba zaria Yayi ba, Abuja ya nufa, sai dai muce Allah ya tsare.
Badiyya zaune gaban Bokanta, ta muskuta tace yanzu kai boka ka na nufin na baro Abuja na zo Maiduguri kuma ba biyan bukata? Wlh na matsu da Zaid, kamar nayi hauka, Boka yayi daria yace Diyyan shagali, yanzu ya kike so nayi? Na gaya miki hakan ba zai taba yuwu ba, Zaid ba zai taba kusantarki ba indai har ba aure kukayi ba, Daniska ne amma baya zina, Abu daya zance miki, ki sashi ya aureki, kar ki bar Garin nan ba tare da kin samu karbuwa wurin danginsa ba, tace ta yaya? Yace ki kutsa, ni kuma zan miki aiki, dukda wannan kakan nasa dan iskan kansa amma na ga Aure tsakaninku, tayi murmushi yauwa gatana shisa nake sonka, haka ta cika mai al aljihu, sukayi sallama bata yi ko ina ba sai gidan Mubahu Zailani, ko dar ba ta ji ba ta tambayi sassan Hajia Babba aka nuna mata, ta shiga dakin da Sallam bayan ta gyrara tsayuwar gyalenta, Hajia Babba ta amsa daga cikin daki, Badiyya ta ma kanta masauki kan sani lafiyayyen kujera, Hajia Babba tace tou ina muka samo Yar Gayu? Badiyya tayi murmushi ta risina hajiarmu ina wuni, Waiyo Allah dadi xai kashe hajia babba ta ji yar gayu tace mata hajiarsu, nan badiyya ta gaidata cikin barikanci, ta amsa, sai dai ban shaidaki ba, Allah sarki hajiarmu Badiyya ce K’awar Zaid ce ni amma ni a zahiri ni Aurenshi nake so nayi sai dai naji ba a auren bareh a gidannan Hajia babba ta jinjina kai tace eh haka ne, Badiyya ta zamo ta riqe kafat hajia babba ta na roqonta ta taimaka mata, lokaci daya ta siye zuciyar hajia babba da zantuttuka masu dadi har hajia babba taji za ta tsaya ma Badiyya tunda tace zaid din na sonta, ta shafa kanta tace karki damu Badiyya abun da wuya, amma zan miki kokari har Allah ya sa a dace. Da Sauri diyya ta rungume hajia babba tace kai Amma nagode hajiarmu, Allah ya ja rai, ya barki da tsoho, ai kamar an tsundumata a Aljannah taji dadi, Badiyya ta cikata da kudi, duk da kudi ba matsalar hajia babba bane amma bata da godian Allah. Har badiyya ta miqe hajia babba tace yauwa jikata dani da Hajjo wa yafi kyau da diri? Badiyya a ranta tace wacece kuma Hajjo? Amma a fili tace wai daman cewa akayi kyau ne da ita? Ai wlh hajiarmu kin wuce a hadaki da wata hajjo, Hajia babba taji dadi matuka, baki na rawa don bata san kalan amsar da za a bata ba ta ce Aishalle fah? Badiyya ta tabe bakih ba don ta san waye Aishalle ba tace wannan me kama farar mayu. Shewa hajia babba ta sa ta rungumi diyya tana tafa hannaye, yauwa Yar gari, da wannan kodawar da badiyya kema hajia babba taji zata yi yanda tayi don Zaid ya auri Badiyya haka sukayi sallama cikin jin dadi, Hajia Babba na zuwa dakih ta Kwalama khalil kira, Autan baba mudassir, yazo da gudunsa, ta mika mai wayar tace kira mun Zaidu, khalil yayi daria, wai hajia ba kya ganewa ne? Har hoton Yazayd a ka samiki a contact picture don ki ganeshi amma kullum sai kin kirani, cikin fushi tace zaka kira minshi ko sai na kwashi buraubaka a hannu? Daria yayi yace Maida wuqar hajia ya kira mata Zaid Bacci yakeyi misalin Karfe 2 na rana, hutu kenan na kwana 2, yanda yaji dadin weekend dinnan Diyya ba ta nan taje Maiduguri, Mamanta ma bata gida, kamar a sama yaji wayarsa na ringining tsaki ya sake, duk zatonsa wayar asibiti ce ake kiransa, haushi ya cika shi daya ga personal wayarsa ce, screen din wayar ya hasko mai Grams, guntun tsaki ya saki ya dauka,Hello Grams ina wuni?daga bangarenta kamar tana waya da wanda yake Sama ta bakwai, da karfi tace Hello Zaidu, Yanzu Yar Gayu tazo, haushi ya cikashi, wacece yar gayu? Haba wannan diya me sunan larabawa, fara me kyau, ni wlh na mance sunanta, tace min kuna soyayyah, hajia babba ta fara mai kwatamce don tsakaninta da Allah ta manta sunan diyya, tuna min sunanta mana? Tsaki Zaid yayi ya kashe wayan. Tsaf ya gane Badiyya ce, miqewa yayi ya fita daga dakin. Zaune ya ganta tana kallon Zee World. Tana ganinshi ta tashi tsaye, ko kallonta beyi ba ya yi kichin, doya ya dauko da wuk’a ya fara fira, shigowa kichin din tayi yace Yazayd ga abinci fa a dining yanzu na gama, kamar ba zai tanka ta ba yace bana ci, ki daina abinci da ni kinaji? Bata tanka ba sai cewa tayi kawo na fere ma doyan toh, shiru yayi sai da ta kara maimaita mai, yace kije na hutassheki. Jiki ba kwari ta bar kichin din. Nan zayd ya gama fera doyanshi ya soya, ya soya Kwai har da sauce dama zayd ba daga baya ba gun girki. Tana kallonshi ya xo ya bude fridge ya dauka fresh Milk yayi dakinsa, miyau ta hade me ciwo ta na ba kanta tausayi, dukda jiya dayau ba ta wahala ba, ta wala a cikin gidanta kasancewar Badiyya da uwarta basa nan..
Bauchi
Bigbro Samir, ya dago ya kalleta kadaran kadahan, tace mena maka ne? Me sa ka tsaneni haka? Kamar ba kai ba? Idan ka bar gida sai dare ka ke dawowa, kamar baka son bude idanunka ka gannin, Kamar m not ur lilsismeerah, eyi yasamir? Me nayi maka ne? My heart cant dmtake dis anymore, ka fada mun idan da akwai abunda nake ma wanda bakaso wlh a shirye nake na barih, because i love u, i can do anything for u, kallonta kawai yayi ya watsar, zuciyanta ya shiga zafih, cikin masifa tace is dis because of Islahilkhair? Its high time da zakayi letting feelings din Islah flow kayi replacing dinshi da nawa coz m stuck here with u forever nd u have to deal with dis, U will never Get Islahulkhair back kadai ji abunda Tsoho yace, idan ka na tunanin in anyway she’d get back to u, toh stop dreaming nd wake up frm ur slumber. Ta tashi ta bar mai parlorn shi ko kalamanta sun mai zafib har be san time din da ya fara hawaye bah.
Kaduna
Karfe 5 na yamma fadila ta hade cikin riga da skirt na atamfa, tana kallon The Vow taji ana Sallama ta mik’e ta bude tare da Amsar sallaman, wata kyakyawar Mata da bata wuce 25 years ba riqe da wani kyakyawan yaro me kama da ita ta gani tsaye tana mata murmushi, kaman ta santa ta mata iso har parlorn Fadila ta sa hannu ta amsa yaron ta cillashi sama tace Bonbon yadai? Shi ko yaro sai kyakyata daria yakeyi, suka gaisa cikin mutunci, ta ajiye shi ta shiga kicin ta hado drink da ruwa ta dire gaban matan, suka Kara gaisawa, Matar tace sunana Amal, mu ‘yan garin Gombe ne, jiya muka dawo garin nan don anyi ma mijina transfer zuwa garin nan, gidan mu ne jingine da wannan idan kin leka zaki hange katangan, Hakkin Makotaka yasa nace bari na shigo, Fadila tayi murmushi tace Allah sarki ni ma kwana 12 a nan gidan Lahhh Amarya ce? Fadila ta tabe bakih, ta chanza topic din. Ya sunanka Bonbon? Amal tace Irfaan, nima banyi 2years da aure ba, ta miqe tace bari na tafi, Fadila tayi murmushi tace InshaAllah nima zan shigo, toh shkn sai kin shigo Amarya, fadila ta bata rai nidai sunana Fadila, Amal tayi daria ta dauki Amal, fadila tayi cikin daki da sauri ta hada ma Amal kayan kamshi ta mata rakiya, Suna haraban gidan ne suka ga Mai gadi ya wangale gate, duk suka bi motar da ta shigo da ido, Jawad ne fuskar nan ba annuri, tamk’e tamau, nan da nan kamar an aiko ma Fadila mutuwa itama ta tsuke fuska, Amal na lura dasu duka, a ranshi yace wato an fara yi mishi shigeshige ko? Toh ba zai dauka ba Ya fito kamar zai tashi sama…
Bibilicious Biebee
27. Gidan Gandu by Biebee IsaSuna tsaye har ya karaso, kallon da suka wurga ma junansu ya sa Amal fahimtar irin zaman da sukeyi lokaci guda, nan da nan ta fuskanci ba jituwa tsakaninsu, Amma sai ta basar ds yake itama waiyayya ce, Amal ta bude bakinta tace ina wuni? Kwarjininta da Girmanta ya sa ya amsata da muna lpy?tace lpylao, Amal da bakinta tace Ashe Sabin Amare ne, Allah Ya bada Zaman lapya ya kwabe fitina, ya bar ku tare, ya kawo yara masu Albarka ta qarashe maganan da zolaya, Hankalin Jawad ya tashi ainun, be son lokacin da ya ce mata Toufa, wa’annan adduar sa ki nayi? Ko ce miki nayi ina sonta? Ya kallk fadila yace keee Ba ki gaya mata yadda akayi auren nan ba? Toh kiyi gaggawar sanar da ita k’ila ta sauya Akalar Adduarta, Fadila ta buga tsaki da karfi, tace rashin sani ya fi dare duhu kai an gaya ma– Amal tayi saurin rufe mata bakih tare da girgiza kanta, Jawad ya kalli Amal yace ai da kin barta ta nuna miki ba ta da tarbiya, ko da ba a aura mata ni ba na girme mata nesa ba kusa ba, ya juyo ya kalli fadila yace Ke kuma kar ki daukeni kamar sakarai, ko ki ga kina mun abubuwa ina kallonki, idan nace zan bigeki karya ki xanyi, the next time da zan miki magana kikace zaki mayar min ko kice zaki min rashin kunya wallahi sai kin gane baki da wayau, sai kin gane masifar ki ta k’arya ce, ya wuce ya barsu, Fadila da zuciyarta ke ta tafarfasa, gashi Amal ta dade mata bakih da hannunta ta hana magana ai wlh da sai ta mayda mai ta ga abun da zai mata, kambu ance mishi tayi kama da wands mazajensu ke dukansu? Ai wlh da sunyi dake dake. Sai da Amal ta ga shigewar Jawad ta sake fadila, fadila ta balla mata harara. Amal ta kalli fadila tace don girman Allah kar ki kulasa idan yanayi, don Darajan iyayenki, ta dinga hadata da Allah har sai da ta sakko, tace InshaAllah zan shigo, don ina son na gaya miki wani abu, nan fadila ta mata Alqawarin ba zata ce komi ba. Amal ta juya da danta suka bar gidan, ta lura dukkansu na da Zafih,a ranta tace InshaAllah sai kunyi zaman lapya, sai kunso junanku don Wallahi kunyi matuqar dacewa da juna, sai kun kasance masu Alfahari da junanku. Allah ya bamu rai da Lafia Amin.
Lagos
Shigowan sa gidan kenan ya ganta zaune a parlor tana cin Abinci tana kallo, ko sallamarsa bata amsa ba, Yunwa yakeji Kamar me don beyi break ba, yace Hanifa don Allah taimaka min ds Abincin nan, Banza ta mai,da ya ga bazata kulashi ba ya mik’e ya shiha kicin don zubowa, aiko tsalle tayi ta dauke dan cooler, ya kalleta yace lpy? Eh ita ta kawo hakan ni ban dafa abincin nan da kai ba, nawa ne, kai ma sai ka dafa naka, ya kalleta yace haba Hanifa me sa kike min haka? Ni fa mijinki ne, aiko wannan kalamin da yayi ya tuno mata da ta rabu da Mu’ammar har abada fah, nan ta zage ta rufe ido ta shiga yayyafa mai ruwan masifa, bawan Allah Zayyad sai da yayi nadamar dawowa gidan, haka ya bar mata gidan ya wuce TANQUIEEZ EATERY don cin abinci.Restaurant din na Best friend dinsa ne me sunan Fatiti amma customers sun fi saninta da Madam Atutu, ba ya son Abincin saidawa amma yana son abincinta don ta iya sosai, gata da Tsafta, Ga ma’aikata masu tsafta da ladabi, Matashiya ce da ba ta wuce 25years ba, dukda ita din Yare ce amma kyakyawa ce ga kirki, tunda Zayyad ya fara Aiki a Lagos suke shiri, Restaurant din nan na ta ne, yawanci sai da daddare take shigowa shagon don itama ta na zuwa aiki a wani company. Kusan a tare suka yi parking a restaurant din, Hararansa tayi tace Ango ka sha Kamshi sai yau ake ganinka? Yayi murmushi yace Fatiti yunwa nikeji muje ki ban abinci, suka shige ciki ta kaishi VIP table, da kanta tayi serving dinsa, ta zauna kusa dashi, sai da ya cinye abincin nan tas kafin ya dago kansa, tana nan ta kura mai ido, tace Ehennn ina jinka, ya kalleta cike da mamaki, yace menene? Tace mid to tell me wat ur problem is? u look disturbed. Zayyad yace Its my wife, cike da mamaki tace d bride? Wat happened? Nan ya kwashe komai ya gaya mata farawa daga yanda akayi auren har zuwa ynz, ta nisa sosai gun tunani, tace Zayyad bani nan ds kwana 2, i will find u a solution yayi godia sukayi sallama.
Abuja
Zaid ne zaune kan kujerarsa a office bayan ya gama ganin patients dinsa, Mu’ammar ne zaune gefensa, Zaid yace muje gida ko Ammar? Mu’ammar yayi dan guntu tsaki yace noo bana son ganin wannan maysah din, Zaid yayi dan murmushi yace kai ina ruwanka da ita? Ni bana son ganin abinda zai hadani da yan dakin Hajia Ama. Yanzu zaid daria yayi har da riqe ciki, ka dauki abun da zafih, ynz ba ma wannan ba, dole sai kayi tafian nan? Inaga idan ka zauna ba sai ka kulata ba koh? Kamar ni nan gaisuwa kadai ke hadani da yarinyan nan, idan na ga dama ko gaisuwar ba zai hada mu ba, kayi xamanka, Mu’ammar yayi guntun tsaki yace ni i’ve made up my mind, i just need to be alone, so nake nayi forgeting sister dinka don yanzu ta haramta gareni, Zaid yace shisa ni ba ruwana da wani soyayyah, balle ynz na zama abun tausayi, jus look at u Amar, duk ka rame kayi bak’ih coz of dis worhtless love. Amar yace ba zaka gane ba, not evryone is like u, Zaid yace toh ita yarinyan chan zaka barta, zarian, alla alone? Tsaki ya buga, yace ni ina ruwana da ita? I dont care abt her, idan sun gaji sa raba auren da kansu, Shisa zanyi tafiana ba tare da na gaya ma kowa ba, balle a chusa min bakin ciki, ko su Mummy sai na tafi zan sanar dasu. Zaid yace when is ur flight? Yace nan da 8:00pm, kana ma da time, muje mu zagaya sai na kai ka Airport…
28. Gidan Ganduby Biebee IsaA Month Later (Bayan wata daya )
Nidai Zaid Gaskia na Kaqagara muyi aure, wallahi ni sai na ga kamar baka sona, kamar ba aure na zakayi ba, Zaid pls help me i really want to be ur wife, Zaid yayi shiru yana tunani, ko giyar wake ya sha ai ya san ba zai iya tunkarar Danginsa da wannan batu ba, Aure?kuma bareh? Kukan da ta keyi ne ya maidosa daga tunanin da yakeyi, Haba Zaid ina ta magana baka tankani ba? Zaif mesa kake min haka? Ko don kaga ina sonka? Girgiza kai yayi, tare da riko hannuwanta, haba Diyya, kinsan dai gidanmu ba a auren bareh koh? Ina neman hanyan da zasu barih muyi aurene, kuma kinsan bazan je wani guri a daura min aure ba, ba zan yi aure ba tare da sanninsu ba, tace idan basu amince ba fa? Yace sai muyi Adduar amincewrsu, tashi ki kira min yarinyar nan, wacce yarinya? Ya kalleta yace matar gidan, A ranta tace Zaid dan iska ne, ji yanda yake sha min Kamshi, toh ko me dai zakayi sai na aureka ta shiga har dakin Maysah da ke kwance ta qwala mata kirah, firgigit ta tashi kasancewar yanzu ta gama shan wanki maman diyya, ta dan rusuna Naam Aunty, My Zaid na kira tana kaiwa nn ta juya, ita ko Maysah jiki na rawa ta bi bayanta, watan daya da wani abu ba ta taba jin Zaid yayi kiranta ba.
Zubewa tayi, Yazayd ina wuni? Be amsata ba, yace kingane, ina so muyi magana ne, ta tattaro hankalinta ta ce toh Yazayd, ya kawar da kai, Gobe Zamuje Maiduguri, ta dago da murna ta kalleshi, tunda kika zo gidan nan na taba miki kallon banza ko harara ko kyara ko wani abu? Da sauri ta gyada kanta, yace Good, a ranta tace baka taba ba, amma karuwarka da mamanta sun maidani Baiwa, Jin muryarshi tayi yana cewa, Zan yi Aure!! Zan auri Badiyyah, Dam Gabanta ya fadih, Nd ke zaki taimaka min gun Tsoho, hawaye suka cika Idonta Fal, So Gobe idan munje, na ma tsoho bayani ya kawo min Gardama, toh sai ki san abinda zakiyi kingane? Ta gyada kai, yace tashi ki tafi, jiki a sanyayye ta bar dakin, Aure? Ko wata biyu ba suyi ba? Wani xuciyar kuma na ce mata ai gwara suyi auren da suyi ta irin wannan Zama na Haramun da sukeyi. Haka ta kwana tana kuka, tunda tayi aure takeson Ganin Tsohonta, Ammanta, Umma hajjanta, da Hajia Amanta, Sai dai kwatakwata bata Murnar zuwa Maiduguri, ji tayi kamar tace mai ba ta zuwa, sai dai ba zata iya ba, ba ta da yanda xatayi sai Roqon Allah ya sa mijinta ya auri Karuwarsa…
Maiduguri
Suna isa gidan Straight dakin Hajia Babba suayi har ita Maysah din, kasancewar an sanar dasu zuwan, an shirya musu kayan tarba da yawan gaske. Wani abun haushin har da ita uwar badiyya
Hajia Babba ina Aljannah ta sa zaid, shi ko sai wani qamshi yake sha mta, Allah ya dora mata son Zaid, ta fi sonshi duk cikin jikokinta, ta saki Zaid da ta hango badiyya ta rungumeta Ga Yar Gayu ga Yar gayu, Badiyya tace ga hajiarmu, ta nuna uwarta da yatsa tace Hajiarmu ga mamata, Hajia Babba akaje aka rungume uwar badiyya tana ga maman yar gayu, ta kalli Maysah ta wurga mata mugun harara, Maysah ko tunani take ina Hajia babba ta san Badiyya? Bayan an zazzauna ne Hajia Babba tace ku zo ku ci abinci koh? Suka miqe duka wani harara ta wurga maysah dashi irin me Alamun ban dafa da ke ba, Zaid na kallonsu, cikin saa ko suka hada ido da Maysah, baki na rawa tace bari na shiga cikin gida, ta juya be tanka ba sai hajia Babba tace da dai ya fi miki don wlh ko dandano ba kici, Girgiza kai kawai Zaid yayi, nan suka hau fira da su Badiyya kamar tun da sun son juna.
*****
Sai da ta leqa parlorn, kamar yadda ta zata yana Zaune kan kujerarsa, juyowa yayi suka hada ido, murmushi ta sakar mai tare da fadin Assalamu Alaikum Tsoho na nan?? Shima dariar yayi, yace Aa Baya nan, da gudu kuwa ta nufeshi shi ko ya bude mata hannuwa tashige jikinsa ya rungumeta, sai da ta yi hawaye don ko tayi missing dinsa fiye da kowa, Ya dago ta ya shafi kanta RUMAH kece nan? Ke da maigidanki kukazo? Shine baki sanar min ba? Ita murna ya hanata cewa komai, sai daria mara sauti take tayi, Agogon dakin ya buga Karfe 2:00 na rana, yace ai tun da kinzo, jeki sakko min da tiren abincin chan, yau a tsakiyar parlo zamu ci abincin rana, haka kuwa akayi suka ci suka sha sukayi nak, ta kwashe kayan, tace bari nayi cikin gida, ban shiga sashen kowa ba, Tsoho yace ina maigidan naki? Ta qaqalo murmushi tace yana nan shigowa. Yauwa in kin shiga ki turo min babanki yazo na sashi aiki, Tace toh A hanyar fita taci karo da Hajia Babba da su Zaid na biye da ita, kanta a qasa ta wuce su, Da Sallama suka shiga parlorn, Tsoho cikin murna mara misaltuwa yake ma Zaid kirarin Likita bokon turai, Sannu ka da zuwa, Zaid yayi murmushi ya durfana gaban tsoho, Barka da Rana Tsoho mai ran karfe, Shafa kansa yayi yace Zaidu, muna lafiya? Lfy qalaw Tsoho, ya karfin jiki? Tsoho yayi wani shuumin murmushi yace ahh jiki da sauki, Hajia Babba ta katse su, Alhaji baka ga da Bakih muke ba? Ya dago ya kalli Badiyya da mamarta lokaci guda yaji ya tsanesu duka, amma da yake shima dan dunya ne yayi murmushi yace ina na lura dasu, Durkusawa sukayi sauna kwasar Gaisuwa, ya amsa ba laifi. Ya kalli Hajia Babba, Karime ina muka samu Bakih? Ta dan sosa Qeya tana so ta san inda zata fara, sai chan tayi dabarar cewa Alhaji Amaryarka ce da mamanta, Yayi murmushi yace Amaryata? Ke kina son tsoho? Kin yarda ki zauna cikin tsoffin mata na? Wayaga Auren buta, ita ko badiyya harda sinna kai ita wai nan kunya tajih, Ai Alhaji sun dade da daidaitawa da Zaid, shine sukazo gaidaka, Ba tsohon ba, har shi Uban gayyar sai da yaji faduwar Gaba, Tsoho ya maze yace ban fahinceki ba, ita ko tace Budurwar Zaidu ce, ita yakeso ya aura, Tsoho yayi shiru, na wasu sakwanni, kan Zaid a Kasah kamar na kirki, yace idan na fahimce ki karime, ita wannan ya nuna diyya ita ce budurwar zaid wacce zai aura, ita kuma wannnan uwarta ce, sunzo gidansu saurayi kawo gaisuwa?? Cikin murnar Tsoho ya fahimceta ta gyada kai Eh hakan ne Alhaji, Tsoho yace toh ba a gidan nan ba. Duk suka dago suka kalleshi, Bangane ba, Tace ke karime ki fita idona, ke sakara ce, wannan ce kike so Zaidun ya aura? Toh ba zai faru ba, ya kalli Badiyya yace yarinya, kije ki nemi miji kiyi aure ba dai zaidu na ba, badiyya ta rarafa ta kama kafar tsoho, donAllah Grandpa kayi min rai, i love Zaid alot, Tsoho ya kalleta, yace Ke er bariki, bazan aura miki zaid ba, wai Grandpa, zaki zo kina nun karairaye, ni ba yaro bane, ke ga er boko koh? Toh Bature ma yaci ubanshi, hajia karime tazo ta dago badiyya dake ta kuka tace haba Alhaji menene haka? Zaid da jikinsa yayi sanyi ya daure yace Diyyah, ta dago ta kalleshi, ya cire key a aljihunsa ya miqa mata, go home, i got dis okay? Zaid pls help me, dont let him do dis to us, u knw i cant leave wothout u, yace Diyyah kije, i want u to trust me, i will find us a way i promise. Ya kalli mamar yace mom kuje gida zanzo, ta miqe tana hararar tsoho ta ja hannun diyarta, Tsoho yace oho dai agayas akai kasuwa, Zaid ya daure fuska kamar be tava daria ba, fuskar nan daure tamau, tsoho yace ni wannan daure dauren da kakeyi be shigata, kazo ka bugeni sai na san kanayi, in banda rigima irin taka, ina kai ina wannan fyarinyar? Dukaduka yaushe akayi aurenka? Kai a ce kayi shekara 10 da aure ance maka zan yarda ka auri bareh ne?, balle duka ko wata 2 baka rufa ba da aure. To udan mafarko kake ka tashi. Ni Musbahu Zailani ba zan yarda ka auri Bareh ba.
_Bibilicious Biebee_
Like · Reply · Report · Aug 5
Phatee Lamin
29. Gidan Gandu byBiebee IsaZaid ya juya ya kalli Tsoho yace Ina so ka aura min Badiyya, ina sonta, da ka aura min Wannan yarinyar nayi biyayya na xauna da ita duk da na tsani na bude idanuwa na naganta cikin gidanah, amma saboda biyyaya ko kallon banza ban taba mata ba, ds Su Mu’ammar suke ta kuka suna hadaka da Allah kar a hada auren nan, ban ce komai ba ni, yanxu kuma nazo ina roqonka ka aura min Badiyya kana ce min aa, bakai min adalci ba, tunda na bi umarninka, to nima a bani zabina, tsoho Yayi shiru yana nazarin maganganun zaid, chan yace Zaidu da dai a cikin gida ka ga mace to ina iya aura ma, amma Bareh ne bazan aminta ba, Ba ka taba ganin an auri bareh ba, toh ba kuma zaa fara daga kanka ba, Zaid yayk wani shuumin murmushi, ba a taba auren bareh ba? To kakar yarinyan nan micece? Inace bare ceh? Er wata qasar ma, ko kana zaton bamu da labarin Uncle Abbakar da yaje karatu Russia ya aurota? Naga itama din bareh ce, Tunda har ka yarda ya aurota, nima hakan zaka yarda na aureta, Tsoho ya bude bakih galala, Zaid ni kake gaya ma magana? Hajia babba tace ai ba batun gaya magana sai gaskia, shi Habubakarin finshi yayi da ya auro tubabba? Uncle Abbakar da Maysah da ke tsaye bakin kofa suka qaraso ciki, duk zancen da sukayi a kan kunnenshi, ya kalli hajia babba rai a bace yace Raijana ba tubabba bace, a musulmarta na ganta, ya kalli Zaid yace Zaidu, zaid ya kasa dagowa su hada ido da Uncle Abbakar, don shi Allah ya mishi kwarjini, qaryan tsageri ya kalli baban maysah ya mai tsageranci, Zaid dai ya amsa ba tare da dagowa ba, Uncle Abbakar yace Lokacin da naje karatu russia, sai da nayi shekaru 5 kafin na dawo gida, mu ba mu samu gatan dawowa gida hutu kamarku ba, wanda duk lokcin da kuka so dawowa kuke dawowa, Ganin shekara 5 ba nan kusa bace, gudun kar na fada ga halaka yasa na auri Raijana, mamar matarka, sai da na dawo su baba suka san nayi aure, na sha fada amma da na nusar dashi dabarata tayi aure ya fahimceni, kagane? Zaid da yaji kunyan Uncle Abbakar ya lullubeshi be ce komi ba. Badiyya kake son aure koh? Sunannta kenan? Ya gyada kai, Uncle Abbakar ya durqusa gaban tsoho ya shiga hadashi da Allah, da Magiya kala kala na kan ya bar Zaid ya sake aure, Maysah ma ta durqusa ita ko harda kuka, ganin kukan da takeyi ne ya sa Tsoho cewa sai yaje yayi tayi, ni ba ruwana cikin alamuaaran zaid, na zare hanuna daga duk wani shaani nashi, Zaid ya matso yace ayi mun haquri tsoho, na tuba, na mata Alqawarin aurene, banso ta dauke ni a matsayin mayaudari, Tsoho yace kai dai kasani. Uncle Abbakar yace kace mata ta turo magabanta ni zan tsaya ma, ni zan aura maka ita, Da sauri zaid ya kalli Baban matarshi, yayi saurin sadda kai kunyar uba da ‘yarsa ta lulubeshi, wasu irin mutane ne wannan?Wani uba zai ma diyarsa kishiya? Wata mata zata roqa ayi mata kishiya? Jin muryan Uncle Abbakar yayi inda yake cewa kaji ai, ina so na gana da magabatanta, zaid yace nagode Allah ya qara girma. Wayarsa ya ciro ya sanar da Badiyya ta zo da Magabanta ta yanzu, cikin doki ta sanar da uwarta, cikin rawar jiki sukaje suka kwashi Kawuninta da basu dauke su a bakin komai ba, wani kawunta yace sai yau kuka san damu? Sai da aurenta yazo kuka san amfaninmu? Nan badiyya da uwarta suka shiga bada haquri don basa son abun da zai hana auren nan, sai da suka cikasu da kudih kafin suka bisu, niko nace dama Mace ke tura magabatan ta ba maza ba?
****
Bayan an sanar da yan gida akwai daurin aure a parlon Tsoho, bayan an hallara nan take Uncle Abbakar ya daura Auren Badiyya da Zaidu bisa sadakin Naira dubu 100 lakadan ba ajalan ba, uncle Abbakar ne waliyyin ango, gaban tsoho akayi komi sai dai tak ce ce musu ba, tausayin Rumarsa yakeyi. Bakin Badiyya kamar gonar auduga, yau ta zama mallakin Zaid, sai yashe haqora take tayi a dakin hajia Ama.
Ita ko Maysah kulle kanta tayi dakin Ammanta tana ta ruzgar kuka, tausayin kanta takeji, anya batayi ganganci ba? Allah gani gareka. Haka ta dauro alwala ta dinga jera nafilfili Allah ya kawo mata sauqi a kan har bacvi ya kwasheta kan dardumanta, bata farka ba sai Assalatu.
Zaid ya shigo dakin badiyya tayi tsalle ta rungumesa, ya dagata ya juya,cikin murna yau gani na zama taka, bantaba tunanin hakan ba, har na cire rai fa, zaid ya ja hancin ta yace i told u i got dis dint i? Yes u did ma hubby, yace kun shirya? Tace ehhh, yace breakfast fa? Ta mai fari tace its too early, yace toh mu tafi, tace mom tace xa mu barta anan, zata biyo mu daga baya, akwai abun da zatayi a nan din, yace ba laifi, ya shiga dakin hajia Babba ya gaidata ya mata sallama yanaso ya iso Abuja da wuri, don yau Monday, ta musu rakiya, suka shiga sashen su Zaid, ya gaida Mamarsa da Babansa, badiyya tana ta jin kunyan qaryar, nan suka musu Sallama, har zasu tafi Zaid yace muje muyi ma Tsoho Sallama Badiyya ta turbune fuska, tace i dont like dat old man, Zaid ya galla mata harara yayi gaba, bata da wani choice din binshi a baya, Da Sallama suka shiga parlorn, yana zaune yana lazimi, Zaid ya durqusa itams hakan tayi, sai da yayi minti 30,kafin ya shafa, Zaid ya ce Barka da Asuba Tsoho, ba laifi Tsoho ya amsa amma ba kamse yadda yake mai da ba, Badiyya da ta gama quluwa da shanya sun da yayi ta gaisheshi tana harareharare, lpy kawai yace mata, Zaid yace Tsoho dama yanzu zamu wuce Abuja, kasancewar yau akwai aiki ban dauki excuse ba, Allah ya Tsare kadai tsoho yace, Zaid ya Amsa da Amin ya miqe har sun kai bakin qofa Tsoho ya cire bakih yace Zaiduu, Zaid ya juyo tare da amsawa, tsoho yace Rumah fa? Zaid ya fara in-ina shi ya mance da wata Maysah, ya shafa qeyarsa yace ita ta na nan, sati me zuwa zan zo na dauketa, Tsoho ya daga kai Alamar toh, Zaid yayi saurin barin parlorn dan kar tsoho ya jaza mai Aiki.. Tsoho kam takaicin Zaid yayi, yana son zaid sosai amma wannan abun da yayi kawai yaji zaid ya sire mai, ya mai ciwo, Duk cikin jikokinsa ba wanda ya ma gata kamar Zaid, don tunda ya aura ma Zaid Maysah yasan ya mishi babban gata, samun Rumah a matsayin mata Alheri ne babba, Amma da yake Zaid sakarai ne, be gano hakan ba, tsoho yace bakomai Duniya ce, Duniya ce zata ladabtar dakai. Yana cikin tunanin zuci Rumah ta shigo da Sallama ya amsa mata cikin sake fuska. Kallo daya ya mata yasan ta sha kuka sosai, tausayinta ya lullubeshi, Nan ta zauna suka shiga hirar yaushe gamo ba tare da ya sanar da its tafian Zaid ba
Abuja
Karfe 5 suka shigo gida, Badiyya ta gaza sukuni burin ta ta samu Zaid a yanzu, tun cikin mota take ta shafa shi, sai da ya dakatar da ita, yace wai so kike muyi accident? An riga an daura auren nan m all yours, i think u can wait har mu isa gida, if not i can find a place park my car nd u suit urself, ganin gatse ya mata ya sa ta shafa mai lafia. Tun a parlor ta fara shafashi tana kissing, haka dai ya biye mata har badiyya ta samu cikar burinta. Zaid ya ga salo salon iskanci, lallai kam badiyya tayi nisa. Sai a yau ne ya tabbatar da ya auri karuwa.
_Bibilicious Biebee_
Like · Reply · Report · Aug 5
Phatee Lamin
30. Gidan Gandu by Biebee IsaKaii I cant take dis anymore, da sauri ta janyo wayarta ta shiga laluben wayarshi.
Kano
Bilkisu ina abinci nah? Ta kalleshi ta watsar, sai da ya maimaita mata kana ta dago ido ta kallesa, tace ban dafa da kai ba, ya kalleta cikin mamaki yace sabida mey? Sbd ni ba baiwar ka bace, kuma ai naga kana da hannu koh? Zuciyya ta ci Suraj, haqurinsa be kai ta dinga gasa mai magana ba ya qyaleta ba, yau ya lashi takobi sakko mata da wannan rashin kunyar da girman kan nata, Shaqr mata wuya yayi ta sakeh ihuu, ya daga hannu kenan zai mareta wayarsa tayi kara, guntun tsaki yayi ya wulla Bilkis gefe, ya zaro wayarsa, Lil sis screen din ya hasko da hoton lovely K’anwarsa yasa ya dauka da sauri, Hello Islah? Ya kike? Jin muryan yayanta ya sa ta fashe da kuka be tsuma rai, nan da nan Suraj ya rude, Islah? Are you Ok? happened to you? Cikin kuka tace yaya Wlh m not alryt, come get me outta dis hell, ina Mu’ammar? Kinsan i dont have dat ryt to pick u up, tell me is Mu’ammar hurting u? Yaya tinda aka kawo ni so daya na ganshi, rannan ma ko 20 mins beyi ba, kayanshi ya kwasa ya bar gidan, What? Inji Suraj, u mean to say ke kadai ce a gidan for 1month 15days? Ya shiga ciki da sauri yace so sorry sis gani nan zuwa, key kawai ya dauka ya fitow, ya na fadin i promise u duk inda Amar ya shiga a garin zaria sai na binciko shi, he’s going to pay for hurting u. Bilkisu ta fashe da daria, Suraj ya kalleta, goodluck in finding ya Ammar, ba Zaria zaka tsaya ba, ka hada da Kasashen wajeh, dan be K’asar kallonta yayi sosai, zuciyarsa na mai zafih, ransa ya baci sosai, a hankali ya furta me kike nufi? Ko tausayi tace gani yayi ba zai iya zama da ita ba, kuma an fi karfinshi an hana shi sakinta, shisa ya bar Qasar kuma ba zai dawo ba har sai yaji kun raba auren. Idanun Suraj sukayi jaaaa, ya ga bata lokacin shi yake yi nan gun bilkisu ya fita a fusace ya ja motarsa ya bar gidan ya kama hanyar Zaria. Nidai nace Suraj a dai bi a hankali, Allah ya tsare ya kai ka lapya..
Bauchi
Ya Samir pls ka samo min Islamiyya na dinga zuwa, zaman gidan ba dadi, nikadai a ciki, idan ka fita sai dare, pls yasamir, kallonta kawai yayi so daya ya wuce be ce da ita qala ba, haushi ya isheta ta miqe ta nufa dakinsa tajishi a kulle, nan ta fashe da kuka tana ta buga kofa amma yayi biris da ita, abunda samir yake mata ya fara isanata, anya zata cigaba da haqurin nan??
Kaduna
Ko da ta bude K’ofa Fadila ta gank tsaye, Amal ta harareta ta shige ciki, fadila tayi murmushi, tace haba Mummy Bon wai fushin ne haka? Wai ba gashi na zo ba? Amal tace sai da aka kusa wata zaki zo? Tace ai min haquri, ina Irfaan? Tace yana bacci, nan suka zube a parlo suna ta fira, cikin dabara Amal ta tambayi fadila ya zaman ta yake da Jawad, Fadila ta kwashe komai ta gaya mata har sillar auren su,da rashin jituwarsu tun kafin ayi auren, Amal ta nisa ta na tunani, ji labarin nan kamar a fim, tace Fadila listen to me and listen good, Ba zaki biye ma Jawad kuyi ta xaman nan ba, kin dai ji abun da tsoho yace, ba saki cikin auren ku, whch means u guys are stucked together forever u need to learn how to leave with eachoda, nd love eachoda. Fadila ta zaburo, me kike so kice min mummy bon? Ni zan kai kaina gunshi? Na roqe shi ya soni? Kindaiji me ya ce kwanaki koh? Ke ganau ne ba jiyau ba, so ki bar wannan maganar, ba zan taba kwantar da kaina na bishi ya wulaqantanni ba wlh, so bar ma wannan zancen,Amal tayi murmushi, Fadila kenan, ba nufi na kenan ba, namiji sakarai ne, kamar yaro yake sai yanda kikayi da shi, ke fa mace ce, akwai yan dabarun mata da zaisa hankalinsa karkatowa gunki, Fadila ta miqe a fusace tace No thanks, kar Allah ya sa hankalin nasa ya karkato gurina, muyi ta zama haka har dunia ta nade for all i care, Amal ta na mamakin zafin kai irin na fadila, amma she wont give up har sai ta ga ta shirya wadannan maauratan.
Lagos
Riqe take da cikinta tana Murqususu, hawaye na bin kuncinta, ta gama galabaita, ta kawo ma kanta mutuwa, yarda kasan tana ciwon Naquda, ta nayin scramps sosai, amma na wannan month din yayi worst, Waiyo Allahn ta, da qyar ta shiga toilet ta watsa ruwa, tana jan jiki ta fito daure da towel dafe da cikinta, jiri ya dibeta ta zube a qasa, Shigowar sa kenan ya ganta a K’asa, da gudu Zayyad ya K’arasa gun hanifa, Hanifa hanifa, are you ok? Kamar ta ga wani dodo tayi karfin matsawa, ya sa hannunsa zai dago ta, ta buge mai hannu tana hawaye, Cikin damuwa Zayyad yace pls Hanifa, lemmie help you, ko karfin magana bata da, amma da yake jinin hajia babba na cikin bargonta, tayi qoqarin bude bakih tace I dont need your help…
31. Gidan Ganduby Biebee Isa
tsura mata ido yyi yana kallonta, chan ta cije bakih tare da fadin Waiyo Hajiarmu, da sauri Zayyad ya kira wata nurse a waya ta shaida mai gata nan tafe, Hanifa ta jigata amma taqi yarda Zayyad ya taimaka mata, Har isowan nurse din tana nan kwance da sauri nurse din ta shiga agaza mata, bayan ta gano bakin zaren neh, ta mata Allura, ta rubuts magunguna tare da ce mai kar ya tada hankalinshi, period ne wands ke xuwa ma mata everymonth. Ita nata da hakan yazo, Zayyad ya tausaya mata sosai, har ya na tunanin dama zai iya dauke ciwon ya maida ma kansa da yayi, don shi Allah yayi shi da tausayin mace, Yanzu duk month haka zata kasance? Allah sarki Allah ya baki lpy.
Zaria
Ko da ya iso Zaria, Staright gidan Ammar yayi, yana sakawa da warwarewa, har ya danna horn a gaban gidan, cikin rawar jiki me gadi ya budeh, Islah ta leqo ta window, ganin Yayanta ne ya sa ta fita da gudu, yana parker motan ya fito, Islah ta rungumeshi tare da fashewa da wani irin kuka me tsuma rai Suraj ya rungumi k’anwarsa, yana bubbuga mata baya alamun rarrashi, tayi shiru tana ajiyar zuciya, ya ja hannunta har parlo, Ya kalleta yace Isi meya fadu dake? Nan ta kwashe komai ta gaya mai, Ran Maza ya qara baci, ohh baki san cewa baya ma kasar ba? Ta dago rinannu idanuwanta ta kalleshi, baya kasar? Ina yaje? Suraj ya mike, yace i dont know, nd i dont care, all i knw is dat u wont sleep a day here again, je ki kwaso kayan ki, da gudu ta shuge dakih A gurguje ta hada kayanta cikin Katoton Akwati, ta dauki duk wani abun da zaats amfana, ta qwala mai kirah, yaya i need help here, zuwa yayi ya ja akwatin tare da fadin ragguwa, tayi daria tare da kulle ko ina, suka fita ta ba ma mai gadi key, Mai gadi na son tmby amms ganin ba fuska ya sa shi yin shiru, haka suka dauki hanyar Kano. Ba su rufe Awa 3 suka shigo kano, Bilkisu na nan zaune, Islah ta shigo da Sallama, kallo daya ta musu ta watsar, sai dsi ta amsa sallamar chan ciki, Islah tayi murmushi kisuwa matar yaya, ta kalleta ta harara, Islah dai ta zauna tana jiran suraj ya shigo, Sai ko gashi da Akwati, Bilkisu ta miqe tayi hanyar daki, ya kalleta yace madam a nuna ma Isi dakinki inda zata kwana koh? Harara ta banka mai tace ba shegiar da zata kwana min dakih, Yayi azaman damk’o wuyanta, da sauri Islah tace haba Yaya ka barta mana, ni ko a parlor sai na kwana, Suraj ya ja kayanta Ya tura dakin Bilkisu yace idan har bazaki iya kwana daki daya da ita ba, to u have to choice ko dakina ko parlor, Allah ya sawwaqe na kwana dakin ka, kuma ba zaa zo gidana a sani kwanan parlor ba Wlh ta buga tsoki ta shige dakin, Suraj yayi murmushin takaici yace yau zaki gane baki da wayau, yayi niyyar bin ta daki ya lallasata Islah ta tsaida shi, haba yaya, ai ba a biyewa, Bilkisu qanwarka ce fa, zakaji dadi Yayanta ya duke nih? Ka kwantar da Hankalinka, zan kwanta parlo, wlh bazaki kwanta a parlo ba, saidai ki kwana chan dakina nisai na kwanta a parlo, tace ok none of us will sleep here, i will talk to bilkisu. Suraj yace dnt waste ur tym sis, she’s never going to change, dnt forget she’s got hajia babba’s blood running thru her veins, Islah daria tayi tace i will try my best.
******
Kan Gado ta iske ta, zama tayih kusa da ita tare da riqo hannunta, bilkisu ta harareta tare da janye hannunta, Islah ba ta daddara ba ta sake riqe hannunta tare da murmushi, ta cire baki ta kira ta, Bilkisu, ba ta damu da rashin tankata ta fara magana, Bilkisu, u are my lil sister and i love u so much despite d fact dat u hate me much as u hate my brother, tun muna yara mu ka tashi da tsabar junan mu ba tare da sannin tak’amaiman abun da ya sa mu ke kin jinin junan mu, yes zamuce babu shiri tsakanin iyayenmu da kakaninmu, Shekara da Shekaru maganar arziki bata taba shiga tsakanin mu ba, fadan yau daban na Gobe ma daban. Gashi har munyi aure, I got married to u brother, nd u got married to mine, ji dai saboda kiyayya, Yayanki ya tsallake ni ya bar Kasar ba tare da sanina ba, saboda tsanar daya mun bema son ya bude ido ya ganni cikin gidansa, tunda aka kaini betaba kwana gidan ba, ji dai zamanki da yaya suraj, babu wata magana me dadi, ki kalli girman YaSuraj ki maida mishi magana,kiyi mai rashin kunya, kuma kina sane da wannan auren anyi shi ne har abada, idan kina tunanin Yajawad xai dawo miki, to ki cire wnnan tunsnin, theres NO chance dat we’ll all get back to our lovers, Mesa ba zamu cika ma Tsoho burinsa ba? For how long zamu cigaba da wannan rayuwa? For how long xamuyi tayin gabar nan? Think Bilkisu, think, i knw u have a good heart, itsjust dat u let Anger controls u. Kiyi tunani Bilkisu. Tana kaiwa nan ta haye gado ta kwanta, Jikin Bilkisu yayi Sanyih, ta san duk abin da takeyi ba daidai bane, duk abinda Islah tace hakan ne, zama tayi tana tunanin Rayuwa, Abun da ta kasa ganewa shine Suraj ne mijin ta na har abada, ta bar tunanin Jawad, lokaci daya hawaye ya fara sintiri a idonta, dama tun Asali Bilkisu bata da nayi sai abunda Hanifa tace tayi, bar ta dai da riqo idan ka mata laifi, Hanifa ke controlling dinta, daga karshe Kwanciya tayi gefen Islah.
******
WasheGari Bilkisu na tashi ta shiga kicin ta hada musu breakfast, abun da bata taba yi ba, wato hada abinci da Suraj, sai da ta kammala ta shiga dakih, har ynz Isi na bacci da yake tana fashin Sallah, Bilkisu ta shuga wanka, ta fito tana shiryawa ne Islah ta tashi, tare da fadib matar yaya good morning, harara ta sakar mata amma irin hararan nan na wasa me murmushi, Islah a ranta tace Alhamdulilah, ta fara sakowa, toilet ta shiga ta shirya. Misalin Qarfe 8 ya fito parlo, Ganin Coolers akan dinning ya sa shi mamaki, ko da yake kila lil sis dinshi ce ta hada musu break don yasab strongheaded Bilkisu ba zatayi ba, da Karfih yace Isiiiii, Islah tace Yaya ka fito? Yace yup. Ta ja hannun Bilkisu bayan ta gama shiri, tace zo muje parlo, Bilki ta bata rai tace kije kawai, haba mana matar yaya, ki ajiye wannan pride din gefe, ur husband is awake, Bilkisu ta tunzura, kinga dai bana so koh? Ya haquri, zo muje parlorn, da qyar ta bita parlorn, ya bisu da ido, sunyi matuqar kyau da kama da suka jero, Islah ta lura da mayatacen kallon da suraj ya bishi da su. Suraj ya mazeh yace Islah naji girkin ki na qamshi zo kiyi serving dina i cant wait to eat lil sis cooking, islah tace Yaya, i dint cook dis food, cikin mamaki yace who did? Ta daga kafadu tace ur wife did. Bilkisu ta dauke fuska kamar bata san da zamansu a parlorn ba, Suraj ya kalli bilkisu, wato yau yaci darajar Islah har break aka yi mishi, yaji dadi amma ya share yace Islahulkhair yi sauri ki karya, don yau nake son na dawo ba kwana zanyi ba, Bilkisu na san cewa ta bishi amma girman kanta ya hanata, haka suka gama breakfast suraj ya sa kayan Islah mota, Islah ta rungumeta tana jin hawayen bilkisu a kafadun ta, amma batace mata komai ba, har bakin mota ta raka Islah batare da ta kalli Suraj ba, ta koma ciki da gudu sakamakon hawayen da ke niyyar fito mata, bro donAllah muje da ita, tunda ba kwana xakayi ba, ya girgiza kansa, ta bashi tausayi, yace gwara tayi zamanta lil sis, sai nan gaba ita da maiduguri, idan ba haka ba Hajia Babba da Aunty Sadiya za su kara chusa mata wasu abubuwan banza a rai, na samu ta fara sakkowa. Islah ta jinjina kai. Haka Suraj ya bar gate din gidan suka kama Hanyar Maiduguri.
32 & 33. Gidan Ganduby Biebee Isa
Abuja
Da Kyar ya samu ya zame jikinsa daga jikinta, ya fara gajia da jarabbar Badiyya, shikenan ita ba ta da wani aiki sai wannan, gashi sai kiransa akeyi a asibiti, yau shine Dr on Call, ya kalli Agogo Karfe 10 da rabi, tsaki yayi ya shiga wanka, ko da ya fito tana nan kwance kamar ruwa, tsaki ya sake bugawa, a gurguje ya shirya cikin suit dinshi, ya bar gidan.
Maiduguri
Fitowar ta kenan daga Sassan Umma Hajja ta ga wani mota kamar motar YaSuraj ya danno kai, shi din ne k’ila da bilkisu donsu biyu ne, ta fada a ranta, ta tsaya tana kallo har sukayi parking, Islah ta fito suka hada ido, ai da gudu suka rugo suka rungume Juna Maysah tace Hey Sis, me kikeyi a Maiduguri? Noo i shud be asking u d same, Suraj yace Maysah ba ta ganni bane, da sauri Rumaysah ta sake Islah ta qarasa gunshi tana daria, sorry Yasuraj, wlh i was carried away, ina wuni! Suka gaisa tace ina mutan gidan? Suna Sassa, Amma Aunty Hussaina(maman su Islah) ds Aunty Hassana sunje biki, islah tace toww, bari na kai gaisuwa gun Tsoho, i missed him alot, taja hannun Maysah sukayi gaba, Suraj ya daga murya Isiii wa zai daukar miki wannan k’aton Akwatin? Tayi daria haba bigbro, ka qarashe ladarka mana, yace zaki sani, suna tafia Maysah tace Islah wat ar u duin here har da qaton Akwati? Islah tace kar ki damu sis sai dai mun zauna. Haka suka qarasa parlorn Tsoho, Hajia Babba ce zaune kusa da Tsoho suna cin Tuffah, Sallama sukayi tsoho ya dago ya amsa, sai kuma ya fadada murmushin shi, Rumah wacece na ke gani kamar Islahulkhair. Itace tsoho, Islah ta qarasa gunsa tare da daura Kanta kan cinyarsa, tsoho ya shafa kanta yana daria, Islah kin yi kewa na da yawa, nima haka.tayi murmushi ta durqusa ta gaida kakar mijinta hajia babba, sai da Hajia Babba ta gama hura hancinta kafin ta amsa, ko uban wa ya kawo ta? Bata gama tunani ba sai ga Suraj yayo sallama, Tsoho yace kai Surajo yanzu kaima kake tafeh? Suraj ya shigo ya duqah yana kwasar gaisuwa. Tsoho ya amsa cike da jin dadi, irin jin dadin da yakeji a duk lokacin da jikokinsa suka zo gaidasu, yana sonsu sosai, Rumah yau baki be rufuwa an ga Yar uwa, maysah tayi murmushi, Islahulkhairi ina Mijin naki? Ko sai ya gama gaida iyayensa kafin zaizo gaisheni, Damm gaban hajia babba ya buga. Islah tayi shiru, yace ina Mu’ammar din ne wai? Da qyar Islah tace ba tare muke ba da Yaya Suraj nake, A’aha chan kika bark mijin naki? Suraj yayi saurin cewa ai yayi tafia ba ya ma qasar, hajia karime tayi saurin tashi don barin wurin, sai dai tsoho ya katse mata hanzari. Karime ina Mu’ammar yaje? Yands tsoho yayi maganan zaka san cewa ransa a bace yake, ta fara inda inda, Ai ya danyi wata tafiya ne, amma ya kusa dawowa, tsoho cikin bacin rai yace Mu’ammar ya ya bar kasar nan ba tare da sanina ba? Tayi karaf tace Ai ba dadewa zaiyi ba, ke karime, ki fita idonaba dadewa zaiyi ba? Toh mesa ba a gaya min ba? Ke kinsani me sa baki sanar dani ba? Tace yi haquri na Shafa’ah ne, ya juya ya kalli Islah ke Islahulkhair me yasa me tafi dake ba?kyarma ta fara yi don bata taba ganin bacin ran tsoho kamar na yau ba, Suraj yace ki bude baki kiyi magana, ta lura shi suraj ko a jikinsa, ta kasa magana karshe sai ta fashe da kuka. Suraj yace Tsoho bari dai kaji maganar gaskia, tun da aka daura auren nan aka kai Islah Zaria bata saka Mu’ammar a ido ba, be taba zuwa yaji ya take ba, ya ta kwana ko me take buqata, haka ya barta ta dinga kwana a gidan ita kadai cike da tsoro da fargaba, bata taba sanar da kowa ba, Hajia babba ta fara borin kunya yo dama ya zaiyi ya kwana gida daya da ita, ya rantse ya maya ba zai iya kwana rumfa daya da ita ba don ko ba sonta yake ba, ina dalili? Sursj ya harzuqa, wato mu da muke kwana da wanda ba ma so miye kashe mu? Ko ce miki akayi muna sonsu? Maysah ta ce Yasuraj kayi shiru DanAllah, kayi haquri kabar maganan, Hajia Babba tace bar tsinannen, bar shi ya cigaba, karshe ma ya bugeni, da wannan gaya min magana da yakeyi, Islah dai kanta a kasa tana kuka.. Sallamar baba hassan da Baba Umar yayi daidai da sake Sallatinsu, Baba hassan ya qaraso da sauri yana fadin hawaye? A idon baba? Waya sa baba kuka? Gabaki daya suka juya kallonsu ga tsoho, abun mamaki hawaye kwance a kumatun tsoho, hajia babba tace hawaye? Lallai abun ya girmama, baba Umar ya zube gaban tsoho yace Allah ya huci ranka babanmu, ka fada mun wanne daga cikin yaranmu suka sa ka kuka mu tsine musu su bi dunia. Ya kalli yaransa islah da suraj yace wallahi sai na tsine ma ku in dai a dalilin ku baba ya zubda hawaye. Tun Yarintata har girmana ban taba ganin hawayen baba ba sai yau, ba abun da zai hana nayi muku bakih, da qyar tsoho yace Umaru, baban suraj ya kalli tsoho, yace kullll na qara jin kace xaka ma dan cikin ka baki, ka bari, ba ka san hadarin bakin mahaifa ba? Shi dai be ce komai ba, ya kalli Baba Hassan, yace Hassan jeka kiramin Labaran koma dai kira min kowa a gidan. Baba hassan ya fita jiki na rawa, hajia babba kuwa jikinta yayi sanyih matuqa, tunani takeyi wabi hukunci tsoho zai yanke don taga ya dauki abun da Zafih…
Lagos
Hanifa ya jikin naki? Wata uwar Harara ta zabga mai, yace Allah ya bki haquri, zan fita ne idan da akwai abun da zan siyo miki sai ki fada, ko tanka shi batayi ba ta tashi ta bar mai dakin ta shigewarta toilet,zama yayi bakin bedside drawer tare da dafe kanshi, oh Allah yanzu shi kuma haka zai cigaba da rayuwars? Hanifa fa qanwar qanwarsa ce, don ko ya girmi Zaid, ya kuma girmi Jawad amma yana tolerating din hallayarta. Wayarsa ya jawo ya kira besty dinsa, ringining daya ta dauka, hello Atutu, yes Ango, kina ina ne? Ina gida, kasan ina shirin tafia, ina zaki? Tace gobe zan tafi Umrah ya dnyi jim, tace anything? yace yes lets meet up pls, tace now? Yes like now where? Yace ur eatery, tace ok i will jus dress up, see you there, ya miqe ya fita ya shige mota sai TANQUIEEZ Eatery, Befi 15mins da zuwa ba itama ta iso cikin shigarta ta alfarma. Ta zauna Ango lafiya? Haka ka koma? Yace Fatiti ya znyi da Hanifa? Bata sona, ba ta qaunata, ba ta mun magana, shekaranjiya she fell sick kamar zata mutu, tana ta murqususu kamar zata shideh, nazo cikin tashin hankali ina tambayarta wats wrong wlh fati in kin tanka itama ta tanka, na zo zan taimaka mata ta tashi, yanda kika san wuta ya tabata tayi saurin janye jikinta, nace let me help u hanifa, qiriri qiriri naga tsanata a kwayar idonta, yarinyan nan ta kalle ni taxe she doesnt need my help, zayyad ya qarashe maganarsa kamar zaiyi kuka. Atutu tayi shiru tana nazari tare da tausayin abokin nata, tace Zayyad ka cigaba da haquri da Addua, InshaAllah she will come to her senses, nd nasan tana sonka, ya girgiza kansa no, bata sona i can see hatred in her eyes, tace we will find out if she loves u or not. Yace how?? Tace we will make her jealous…
*********
Duk sunyi zaune sunyi tsuru tsuru kowa na son ji me ya faru, barin ma aunty hussaina da ta shigo ynz, ganin Islah da suraj gaban Tsoho ya sa hankalinta tashi, Allah kasa taron nan ban dan su bane, Allah yasa ba laifi sukayi ba. Tsoho ya kalli Baba Labaran(Baban Mu’ammar) Da Aunty Sadiya yace Labaran kunsan da tafiar Mu’ammar kasashen waje? Baba labaran ya rasa ta cewa ya fara inda inda, Ke Saadiya da izinin ki Mu’ammar ya bar matarsa ya bar kasar? Tayi shiru, ya juya ya kalli yan parlorn ya zayyane musu komai abun da ke faruwa tsakanin Islah da Amar, wuri ya dauki salati, Aunty Hussaina sai da tayi hawaye sbd tausayin diyarta. Baba labaran ya ce ayi haquri Alhaji, mun tuba, a yafe mu. Tsoho ya kalli baba labaran yace Labaran idan ban isa da kai ba, ban haifeka ba ai na isa da matarka kuma nine na haifeta. Kuma ina tunanin ya ci ace an sanar dani tafiar Mu’ammar, da sauri baba labaran yace donAllah kar kace haka wlh tallahi bamu da uba sai kai, ni da danuwa na Mudassir ba mu da wanda ya fika, kaine uban mu, kar ka juya mana baya. Ni kaina bansan da tafiar Mu’ammar ba sai rannan da zai tafi, ka yafe min. Tsoho ya tabe bakih yace kira min Mu’ammar a wayah, nan fa daya duk gidan ba me numban Mu’ammar, tun tafiarsa be kira kowa ba, Baba labaran ya rantse be da numban Mu’ammar don be kira sa ba, Aunty Sadiya ma tace ba ta da numbern shi. Tsoho yayi shiru ya kalli Islah yace kiyi haquri Islahulkhair, Mu’ammar ya bar qasar nan saboda be son bude ido ya ganki koh? Yana so har sai na gaji da ganinki na raba aurenku koh? Toh ga sako zuwa ga Mu’ammar, ni Musbahu Zailani ba zan raba auren Islahulkhair da Mu’ammar ba, Idan ya dawo nan kusa falillahil Hamd, idan ko be dawo ba, ko shekaru dubu zai yi qasar waje to ya san da saninsa cewa Islahulkhair na nan da aure, ko da xai sake wani auren ba tare da saninmu ba, Auren Islah na kansa, Akwai Aurenshi akanta, kuma Auren nan har abada sai dai in daya ya riga daya mutuwa, ku isar da saqona gunsa in ma hanani numbarsa kukayi to a Banza, ku tashi ku tafi na sallami Kowa.
_Bibilicious Biebee_
Like · Reply · Report · Aug 6 at 9:27am
Phatee Lamin
34. Gidan Ganduby Biebee IsaIslahulkhair zatayi magana Babanta Ya girgiza kansa ta ja bakinta tayi shiru, haka suka fara fita daga parlon tsoho, Hajia Ama ta ja Islah sashenta, ta dinga bata magana ta hanyar Waazi da kalamai masu sanyaya rai, ta rungumeta tace kar ki sa komai a ranki, ki tafi sassan ku ki huta kinji? Maysah ku je, Maysah ta ja hannun ta sukayi Sassan Baba Umar, Islah tace ke Maysah baki gaya min ynda zamanki da yazayd ya kasance ba, ina fatan zaman naku da sauki, Maysha tace hmmm kinji kinji, ta kwashe komai ta gaya mata tun daga barinta gidan tsoho da yanda suka biya suks dauki diyya har zaman bautan da ta ma diyya da uwarta xuwa dawowanta nan, Islah ta jinjina kai, lallai kinyi qoqari, ynz sai da yaxayd ya auri karuwarsa? Ke gwara muyi zaman mu nan da mu koma gidajen mu muna kwasar bakin ciki. Kinsan qazantar da baki gani ba toh maidata tsafta. Maysah ta jinjina kai Allah ya mana da kyau tace amin. Mu danno Fadila. Ringing daya biyu ta dauka, Amaryar Ya Amar Islah tace banza ki hau IMO muyi VideoCall tace ok, Nan suka fara video call, Islah tace Guess what? Fadila tace ke banason guessing games tell me, Islah ta hasko mata Maysah Ihu fadila ta saka tace noway, wlh ba zan yarda ba, ke kikaje Abuja? Ko ita ta zo Zaria? Wait kamar dakinmu na Sassa, suka kyalkyale da daria, wai wat are u two doing in Maiduguri? Its a long story my sis, dallah ku gaya min, nan Maysag ta kwashe labarinta ta fada ma Fadila, Islah ma ta fada mata nata, Fadila ta hau masifa, ke Maysah haka kike dama? Duk da bani san jawad wlh be isa ya kawo min karuwa da uwarta nayi hidima da su ba, kambu, kin hadiye da yawa, sanyin zuciyarki tayi yawa haqurin ki yayi yawa, gashi yaso ya ajiyeki, lallai, kaii dangin hajia Babba ba suyi ba, Shine Ya’ammar ya tsallake qasar ko? To yafi ruwa gudu, kar ya tsaya kasar sin ya qara gaba, Amma wlh banso hukuncin da tsoho ya yanke ba, tsoho na shiga haqqinmu, da sauri Islah tace keee yi shiru, kar ki sa su baba su tsine mana, duk suka yi daria. Maysah tace Eeelerh ya zamanki da Yajawad, fadila ta kyaba bakih, tace ni ina ruwana dashi ba abunda ya dameni dashi. Kowa harkar sa yakeyi. Suka ce laaa Allah shi kyauta.
*****
Ya Suraj ne ya leqo yace kuna ina?ni zan juya, Islah da Maysah suka fito, Yaya ka kwana mana, noo Isi, i need to go now, toh Allah ya tsare, wai Maysah me kikeyi ne anan ko kema Zaid din ya bar qasar ne? Duk suka sa daria tace Aaa yaya aure ya qarah, Suraj ya zaro ido yace Aure? Waya aura? Tace wata Badiyya ce, suraj da mamaki yace Bareh? Tsoho ya yarda? Tace ehh amma Appa ya daura auren, suraj ya girgixa kai ya na mamakin uncle Abbakar da ya daura auren kishiyar diyarsa. Suka rakashi ya ma Umma hajja bankwana, suka shiga sashen Hajia Ama, sannan sukayi sashen Tsoho inda tsoho yace Suraj ka ji tsoron Allah, kar ka Wulaqanta Bilkisu don kaga Mu’ammar ya wulaqanta Islah, kowa yayi da kyau zai gani, Suraj yace InshaAllah Tsoho ya mai sallama…
Bayan wata 3(3months later)
Ba abunda ya sauya nadaga Rayuwar Xuriar Zailani, ko wanne na chan na fama, Duk lokacin da hanifa zatayi period dai ta sha wahala, yanzu ya abun ya shahara har suma takeyi, ta gwammace ta mutu da Zayyad ya taimaka mata a cewarta. A bangaren Samir da Amira kuwa kullum Amira sau ta bibiyeshi tana mai magana, wani zubin ya amsata wani zubin kuma ya watsar da ita, abun ya dameta, amma ba taba gaya wa kowa ba, kusan da cewa Amira tayi sanyih ba Amirar da bace, Suraj da Bilkisu kuwa fada ya ragu tsakaninsu, Bilkisu za tayi abinci dashi, amma ba ya ganinta, rayuwar dakih ta komayi, zata gama abinci kafin ya da wo aiki da ta gama zata shigewarta daki, shi ma da ya dawo xai ci abinci yayi dakinsa, be nemanta don yana jin buruntunta a cikin dakih. Jawad da Fadila kuwa ba Uhm ba Uhm Uhm, kowannensu jiran dan uwansa yakeyi ya tanka su hau sama da masifa, amma kowannensu na kame kai, ba ruwan kowa da kowa, in ma ya fita be dawowa sai chan dare, ita kuwa da ta gaji da xaman kadaici sai tayi shigewarta gidan Amal maman Irfaan, Amal ta zaunar da ita tana mata nasihohi da waazin haqqin miji, amma fadila kunnen uwar shegu takeyi da ita, maganan ya shiga tanan ya fita tanan. A fannin yan Abuja, Ango da Amaryarsa, cin karensu sukeyi ba babbaka, Badiyya ba ta da wani aikinyi sai neman zaid, shi ko Zaid ya qi jin abubuwan da take mai, ba dare ba rana, har beson dawowa daga aiki, in ma ya dawo ya ga zata matsa mai sai dai ya tsallake ta ya wuce ys shige dakinsa ya kulle, in ko ya mata haka har kuka take mar. Islah ko da Maysah sunyi qibarsu ba su da wata matsala, kullum suna tare da tsoho, Mu’ammar na chan wata uwa dunia ba wanda ke ds labarinsa. Tsoho ya sama Zaid ido be kirashi ba be nemeshi ba, jira yake ya gudun ruwansa ko xaizo daukar matarsa ko ba zai zo ba. A gun Zaid kuwa tsakanin sa da Allah ya manta da wata Maysah, tunda ya bar maiduguri ve qara waiwayenta ba sai Yau Asabar.
Daga shi Sai Diyyarsa cikin mota, Kadan ya rage su iso Maiduguri, Gun Maman diyyar sukaxo, wai bata jin dadi ita diyyar zata rakata India, so shi zaid din gobe zai koma Abuja, ko da suka iso Gidansu Zaid suka wuce duk da diyyar bataso hakan ba, straight dakin Hajia Babba tayi shikuma yayi Sassan Tsoho, Ganin mutum sukayi qiqam a kansu, Aunty Abida tace ina muka samo wannan kuma? Hajia babba ta duba tace Laaaah Er gayu ce, diyya ta qaraso hajiar mu ina wuni, lafya lao er gayu, ta kallo Aunty Abida tace Sannu, Aunty Abida tace yauwa, Hajia wacece wannan? Hajia babba tace ban son tsiyar banza, Badiyyar ce baki gane ba? Mtsw Er gayu ke da zaidu kuke tafe? Ina zaidun yake? Ta tabe bakih, yaje gun wanchan tsohon, Aunty Abida tace keee iya bakinki, baban namu ne wanchan? Baki da tarbiya koh? Badiyya ta mata wani mugun kallo, har ga Allah bata gane itace mamar zaid dinta ba, Hajia Babba tayi karaf tace ke Abida ban son wulaqanci, baqonka annabinka, Hajia wani irin iskanci ne wannan? Baban namu ne wanchan? Ke Abida tafi sasshenki, Anty Abida ta fita ranta a bace, duk rashin kirkinta ta na son Tsoho, wai wannan ce matar Zaid? Lallai ta mata kallon tsoro da farko. Mata kamar karuwa, ji uban gashin doki a kai, wai ita zata kalla tace mata sannu, ta tuna yarinyar arxiki Maysah kullum sai ta shigo gaisheta, idan ko zata gaidata sai ta zube qasa ta ce Ina kwana Mummy, amma ko kallo bata isheta ba, kuma babanta zata ce ma wanchan, wato shi ba komai bane, Tayi qwafa tace bakomi, koma menene Zaid kai ka ja mun da ka auri fitsararriya.
****
Tsoho me ran karfe, Yace Wani kamar Zaid, yace ba kama bane, nine, yaxo ya kwashi gaisuwa, tsoho yace daman ana ganinka? Rabonka da nan wata kusan hudu kenan, Zaid ya shafa kansa, kayi haquri Tsoho wlh aikine, yace toh oo ni dai na zata amaryarka ta sa ka mance da mu kamanta da matarka da ka bari anan. Dam Gaban Zaid ya fadi, ya maimaita kalmar mata a ransa, be dinke ba sai da yaji sallamar Maysah ta shigo da sauri tana tsoho zskaci Kwadon Rama? Gabanta ya fadi da suka hada ido baga lurs dashi ba, shi ko sai a sannan ya tuno da cewa Yarinyar nan na nan. Da sauri ta saita nutsuwarta tace YaZaid ina wuni? Kazo lafiya? Be kai ga Amsawa ba sai jin badiyya yayi tana cewa Myzayd kazo mu tafi pls, kasan mama na chan itakadai ba ta jin– maganan ya maqale a fatar bakinta Idonta ya kaiga Maysah, ta qara hakse ta ciko sosai. Kallon da take mata ne yayi yawa hakan yasa Maysah shan jinin jikinta da sauri tace Aunty Badiyya ina wuni???
_Bibilicious Biebee_
35. Gidan Gandu by Biebee Isa
Tsoho yace Rumah me kika ce? Aunty? Qanwar babarki ce? Kar na sake ji, da ta shigo parlorn nan kin ga ta gayyar dani? Kallo ban isheta ba, Zaid ya wurga mata harara me cike da ma’anoni batayi niyya ba tace Ina wuni, yace da ban wuni ba ai baza ki ganni ba maras mutunci, Badiyya tace my zayd, i wont stand dis, ta miqe ta fice, Zaid ya dan risina yace ayi haquri tsoho, ya bi bayanta, Maysah ta ce haba tsoho ai ba a biyewa, yace ni na biye, wlh kar ki sake kiranta da Aunty, Mijinku daya, ki zage damtse, ki shirya zaku tafi tare Gobe, Gaban Maysah ya buga bata son musa mishi tace toh ta miqe yace zan ci kwadon ki kawo min, ba tare da ta kalleshi ba tace toh. Murmushi kawai yayi.
Wuceta yayi hanyar Sashen su, bata da zabin sai binsa a baya, dakin Aunty Abida ya wuce, Da sauri ya qarasa kujerar da mamansa ke zaune, don ganin fuskarta yayi murtuke mutuk, ya dora kansa akan cinyanta, Mummy me ya faru? Wa ya tabaki? Tana karkada kafa tace Zaid ashe dama akwai waccce zaka aura da zata wulaqantani? Ni Zaid? Da sauri ya kalli Badiyya tare je fa mata mugun kallo, ta karaso da sauri itama ta zube qasa tare da kama kafafun Aunty abida, mummy sorry wlh na tuba bansan me ya sameni ba, ki yafe min, Anty Abida tace shkn ya wuce. Nan suka gaisa da Zaid, yace bari yaje ya kai diyya gida tace sai ka dawo, suka fito suka shige mota, A mota ta rasa gane kan Zaid, Shiru ya mata, ta dinga mai magana yayi banza da ita sai da tace Zaid m sorry, ya dan sasssuta fuska, Badiyya listen to me, I dont let anyone mess with mh Family, My family comes first, Kin raina min Tsoho ba kya ganin mutuncinshi, to bari kiji, wannan tsohon namu shine gattanmu, nd now my mum? zan iya rabuwa dakeh ta kansu, hantar cikinta ya kada, da sauri tace Dont do dis to me, tsohonku dont like me nd wlh bnsan itace mum dinka ba, amma kayi hqr ba zaa qara ba, yace it better not repeat itsef again. Tace it wont i promise, a ranta kuwa cewa take dole ta koma gun Mallam don Aiki ya fara suncewa…
Islahh ce ke hada ma Maysah kaya, don gobe da faran safiya zasu tafi, shawarwari suke ba junan su abun gwanin ban tausayi, Islah tace Allah ya karkato hankalin Ya Zayd gunki tace Amin Amin. Nan suka kwanta bacci.
******
Washegari da Misalin Qarfe 6 na asuba, Zaid na durqushe gaban Tsoho, yace Tsoho ni ynz zan wuce, kai kadai xaka tafih? Eh maman baddiya bata jin dadi so na barta ta dan kwana 2, Tsoho yace Maysah fa? Xaid yayi shiru, Tsoho yace ta shirya sai kuyi ta tafia, Zaid yace toh, Yauwa Xaidu ina son yarinyar nan ta cigaba da karatu, Toh tsoho ai sai a samo mata UNIMAID ko? Yo sbd me? Mijinta na abuja me zai sata karatu nan? Ko ba makarantu ne chan abujar? Yace akwai to a nemar mata wani tana da JAMB dinta, zaid yace to shkn tsoho na san wasu a Baze University, zan sa a nema mata sai ta fara next semester Tsoho ya murmusa yace toh tashi ka tafi, Rumah na chan sashensu sai ka leqa kace tafito, Allah maka Albarka, Amin Amin tsohonmu, Yauwa ka leqa ka gaida Aishalle da hajjo. Zaid yayi shirrrruuuu chan yace toh. Abunda be taba yi ba kenan ya tsinci kansa da bin umarnin Tsoho, Sashen hajia Ama ke kusa da na Tsoho nan ya fara shiga, tana chan kurya tana lazimi ta ji Sallama, ta fito Ganin Zaid zaune ya bata mamaki sosai. Yace Barka da Asuba, Ama tace Zaidu lpy lao, ya aiki? Yace Alhamdulilah shkn fa duk suka yi shiru, sai da suka bata 10mins zaune ya miqe yace na tafi, Tace Toh Allah ya tsare nagode Allah ma Albarka ya amsa da Amin. Yayi sashen Umma hajja itama ya gayyar da ita kafin yayi gidan Uncle Abubakar, Ya fi mintuna 10 ya na tunanin yanda zai shiga, chan dai yayi ta maza ya shiga da Sallama, be taba shigowa nan ba, Uncle Abbakar ya leqo Zaid ne? Bismillah tare ds miqa mai hannu, abin mamaki sai ga Zaid ya dyrqusa har Qasa ya na gaida Uncle Abbakar. Ya miqar dashi ya ja shi har parlo, Aunty Raijana ta fito suka gaisa Samasama, Xaid yace dama Erhm zan tafi ne yanzu, Uncle Abakkar yace toh Raijana jeki ce da Maysah ta fito, ta ce toh,, Maysah suka fito tare da Islah suna jan Akwatinta, suka gaidashi be kallesu ba ya amsa. Ya miqe yace tooh na tafi, Uncle Abbakar ya musu Addua. Ganin zasu bata mai lokaci yasa shi amsar akwatin daga hannunsu. Ya kai mota, ya wuce Sassan hajia babba, da sauri maysah taje sassan hajia ama, umma hajja da tsoho ta musu bankwana, dama sunyi bankwana da sauran mutan gidan daga karshe ta koma sashen hajia babba inda ta iske su har sun fito rakoshi ta gaida su Aunty Abida kadaice ta amsa ta sama sama. A bakin mota ta rungumi Islah suna hawaye dukkansu. Da qyar suka rabu ta shige gaban mota inda Zaid ya jasu suka bar Gidan. Safe journey.
Like · 1 · Reply · Report · Aug 6 at 9:31am
Phatee Lamin
Haka suke tafiya ba me kula danuwansa, kafin su iso kano Maysah tayi bacci kala kala, suna isa kano yace kina jin yunwa? Da sanyinta ta girgiza mai kai, yace Uhm? Ba tare da Ya kalleta ba, tace naqoshi bana jin yunwa, be ce komi ba ya cigaba da zarara gudu, sai da suka iso wani qauye yayi parking, wani guri taga ya shiga be dade ba sai gashi, ya miqo mata envelop ta amsa ta ajiye, ya qara komawa wani shago sai gashi ya dawo ya tada motar suka dauki hanya, kilishi ne da yoghurt, ta bude ta fara ci a hankali, tace Yazayd kai ma kaci pls, ba tare da ya kalleta ba yace No, thanks..
Karfe 2 ya shigo Maiduguri, straight Sassan Tsoho ya wuce da Sallama, Tsoho ya amsa kai Surajo, kai baka jin tafiya ko? Tafiya be ma wuya, yace tsoho nayi kewanku ne da yawa, yayi daria, suka dan taba fira, kana yace Tsoho Ya maganar Islah,? Yace Surajo inace ai nagama maganar Islahulkhair koh? Kar ma kayi tunanin zan raba auren nan. Suraj yace Tsoho amma zamanta haka beyi ba, wata hudu da tafiansa amma ba wanda ya san me yake ciki, ya kamata ko karatu ta fara, Tsoho ya jinjina kai yace dama so nske ta fara karatun, Amma ni bansan jamiar garin nan, Suraj ya murmusa don shi so yake Qanwarss ta bar kasar itama taje wajeh karatu, yace Tsoho ai ni har na gama samo mata makaranta, har na biya umurnin ka kawai nake jira na kaita, Tsoho yace haka ake son yayyi masu kula da Kannensu, ko bayan ran mu munsan zaku kula dasu, a wani gari ne? Suraj yace Tsoho a Ingila ne, ya zabura Ingila dai surajo? Ya zaayi a bar matar aure ta fita waje karatu ita kadai, to ban amince ba, ban lamunta ba, duk jami’ar kasar nan ba wanda ya maka sai ka fidda ta wajei don kankamba, to ba inda zata, Suraj ya marairaice yace kayi haquri tsoho, nayi laifin da har na zarce hukuncin biyan mata kudin makaranta ba tare da saninka ba, tunda ba kaso ba zata je ba, kudin kuma bakomi, amma sai naga kamar zamanta anan ta na yin shi ne cikin kunci, duk saointa na gidan mijinsu, ba dadi zata dinga wasu tunaninka daban har ta jefa kanta wani hali, amma idan aka ce ta tafi chan ta fara karatu hankalinta ya kwanta, idan Allah yayi Mu’ammar ya dawo sai naje na dawo masa da matarsa, amma tunda baka so na bari. Jikin tsoho yayi sanyi. Suraj ya dauresa da jijiyoyin jikinsa, ya yi shiru yana nazari, yace kace ka riga ka biya kudin komi? Yace eh, har nawa? Suraj yace kusan 10000 lbs(pounds), tsoho ya zaro idanuwa pan ba dalla ba? Yace eh Tsoho pounds ba dollars ba, tsoho ya jinjina kai, surajo ina ka samo maqudan kudih haka? Ya murmusa, tsoho ko ka manta jikanka ba zaune yake ba? Yana aiki, aikin ma na Architecture, tsoho ya jinjina kai, lallai ba zan bari ayi Almubuzaranci ba, Na amince ta tafi amma da sharadi, suraj yace wani irin sharadi tsoho? Eh sharadin shine Duk randa Mu’ammar ya dawo to ko ranar take xana jarabawar karshe ta gama degree zakaje ka daukota. In ka amince toh na amince, da sauri ya gyada kai yace na maka Alqawari. Toh shkn sai a fara shirin tafia. Suraj ya dinga zuba godia tare da miqewa Tsoho yace Bilkisu fa? Ya maganar makaramtarta? Suraj yace InshaAllah xsn fara nema mata Northwest University da ke nan kano, yace toh yayi kyau..
Suraj ya wuce sashensu straight, ko Islah be nema ba, ya ciro System(laptop)dinshi ya fara nemar ma Islah makaranta a London England, don be ma san inda zai yi enrolling dinta ba kawai dai ya daura tsoho ne kan layihh, ni biebee nace Allah ya sa Tsoho ya dago ka.
0 comments:
Post a Comment