Yup, tace Yaya kasan Tsoho– dnt worry i handled everything, dadih ya sa ta hawaye shima kamar ya tayata kukan ta rungume yayanta I love you Yaya, yace shuttup nd tell me wani course kike so ta danyi tunani kadan tace Medical Engineering.
Cikin Lokaci kadan Har Suraj ya gama ma Islah Komai, tafia kadai ya rage, toh xasuje England Embassy a Abuja, don suyi processing Tafian,sun yanke hukuncin Tafia Abuja Gobe, suraj yana zolayarta yace wai Isi ko Airport kin taba zuwa? Tacee kaii yaya, mu da every year sai munje Makkah, yace keeee Isi qarya, wlh yaya be fi 1year da mukaje makkah ba yace toh na yarda je ki kawo min E Passport dinki, tace toh.
*****
Diyya Gaban Bokanta, tace wai shin boka yanzu meye abunyi? Danginsa barazana ne a rayuwata, har yana iqirarin rabuwa danih, Boka yace na gaya miki a baya, kakan nan nashi tsaye yake, Namijin duniya ne, ba bu yadda zakiyi dashi, Sai dai kiyi dabarun ku na mata, kisisina da chusa kai, ta hakan zaki rabasu, tace yauwa boka, mesa Zaid ke min gardama? Har ya kan kai ga gaya mun baqar maganganu, Na kasance me yawan buqata, dan tahalikin nan sai dai ya tsallakeni ya barni kwance, Boka yayi daria kema ai baki da sassauci, ko ni nan tsoronki nake Diyyan Shagali, diyya tayi fari, nidai samo mun mafita, so nake na tankwarashi, sai yadda nayi dashi, ya zama mijin tace, Boka yace wai diyya baki ganewa ne? Ba me iyawa da jarabbarki, kuma tun kafin auren ku sai da na gaya miki komai kan Shi, kakansu Tsaye yake kansu gabaki dayansu, ba me iyawa dashi, kije kawai ki kwashi rabonki tunda dama kina kan kwasa, yanzu dai bani nawa kason, Ran diyya ya baci ta rufe ido ta zazzaga boka rashin mutunci tace wlh tunda ba biyan buqata ko sule biyar ba zata bsshi ba, yace kar muyi haka da ke ta miqr tace ai munyi, yace kina da kudi fah, ji dai yanzu qarya kuka mai zakuje India ke da Uwarki, ya cika ku da daloli amma kice ba zaki ban komai ba, kije zaki gani. Tace Alheri zan gani, yace toh ki sani Zaid da matarsa ya koma, Gabanta ya fadi, ta fita a harzuqe, shi ko boka yayi daria, in kinsan wata ba bakisan wata ba, Diyya kin kwashi Rabonki a wajena, sai dai nace Allah bayyanar da ciwon da gaggawa tunda ni nasan makomata. Ni biebee nace Ciwo? Wani iri ciwo kuma?
Abuja
Zaid da Maysah sun iso lapya, Shi ya shigar mata da kayan har dakih, ta kalleshi cikin sanyinta tace nagode Allah saka da Alheri, Me zan dafa maka YayaZayd, yayi gaba ba tare da ya kalleta ba yace No thanks, M okay, tace ko sai zuwa Anjima? Yace na hutassheki, ya bar mata dakin. Zama tayi kan gado tana tunanin dis is her chance din karakato hankalin Zaid gunta, Shi ko yana shiga daki ya sa mukullin fridge ya bude firij tare da dauko Gwangwani Star ya kwankwada, ya sake dauko na gulder ya qara kwankwada, sai da ya sha gwangwanin giya kala 5, kafin ya fara gaya mai qarya, ya fara tangadi tare da zubewa kan gado. Tayi ta sallama taji shiru, niyyarta ta hada mai ruwan wanka. Tayi gangancin tura qofa tareh da shiga dakin, sheme ta ganshi kan Gado, shabeshabe, idonta ya kai ga kan Gwangwanayen Giya, Hawaye ya shiga zubo mata a idoh, daman be bar shayeshaye ba? Zuciyarta na qunah ta bar dakin. Badiyya ko sai neman wayan Zaid yake tana ringing amma be dauka ba, hankalinta ya tashi, da ba san tace mai yau zata tashi da qarfe 10 ba da ba abunda zai hanata yin safkon garin Abuja.
Kano
Islahulkhair da Yayanta a parlor duk ta daure fuska wai ita fushi takeyi dashi, sbd ya qi biyawa suga Fadila a Kaduna, kuma har sukaje Abuja suka kwana biyu Gidan abokinsa, a cewaarsa ba xai je gidan Zaid ba don kar ya raina mai hankali, shikuma ba zai iya haquri ba, duk da gidan shi yaje, ta ce yaya gun Maysah fa zamuje ba shi ba, yace Yaushe rabonki da Maysah da zaki damu muje gunta, ai naga ko kwana 5 bakuyi da rabuwa ba, tayi shiru ta qyaleshi haka suka baro Abuja, suka wuto kaduna, suka dawo Kano. Ya kalleta yayi murmushi wai duk fushin ne haka? Ai bansan kinayi ba sai naga bakinki yayi tsini, ni shiga ki kira min matana, ta tabe bakih, za a mun iyayi wai mata, sai kace tana ma magana ta tashi ta shiga ciki, ya bi bayanta da daria, kwance take ta na karanta novel din Baby Aisha na “Abu Daya Tak”a Whatsapp Islah ta shigo da Sallama, Matar Yaya, yaya na kiranki, Bilkisu taji wani iri, toh meye kuma? Ta san dai ba abun da ke hadasu sai gaisuwa, ta dai yi shiru kafin ta miqe ta fita, a parlor ta iskeshi kinshigide yana kallon ball, ta dai zauna ita bata ce mai komai ba, ganin bata da niyyar tankashi ya sa shi magana, Kamar yadda kika sani on Saturday Islah zata tafi Skool, kuma ni Zan kaita kuma zan dan kwana 2 a chan, so gobe zan kaita Maiduguri tayi sallama da su tsoho kafin mu dawo nan ran thursday mu bi jirgin Lagos sai mu wuce Ingilar, so ki shirya zamu tafi tare gobe zan barki a Maiduguri har sai na dawo, ta sauke ajiyar zuciya dama jira take ya gama maganan tace mishi ni kuma fa? Sai kuma ya fadi mata abunda yake son ji, Allah ya kaimu kawai tace ta miqe ta komawarta dakih, Zuciyarta kuwa Murna ne zata gida after a long period of time..
Kaduna
Alhaji Haladu Maidala dan kimanin shekaru 45 attajirin me kudih ne wanda Maaikatar Matatan mai na kaduna Na NNPC ke taqama dashi, Tauraruwarsa na haskawa amma tun bayan Zuwan Jawad Mudassir Zailani tauraruwarshi ta fara dakushewa, Yaron da be wuce ya haifeshi ba ke neman dakusar da tauraruwarsa, yaron da ko shekara 2 be rufa da fara aiki a gurin ba amma har gwamnati ta son dashi, ynz duk wani man da zaa tatto sai da izinin Jawad, duk wasu ayyukan da Alhaji Haladu ke yi ya dawo kan Jawad, babu yanda beyi ba don ganin ya dawo da matsayinsa a Maaikatar amma abin ya faskara, don abun daga Sama yake. Fitowa yayi daga motarsa ya shiga 9starsShopping Complex, tunda ta gansa ta susuce da ga ganinshi akwai kaya gunsa, da sauri ta qarasa gunsa, Alhaji sannu fa ta dinga karkashe Mai idanu. Alhaji abun nema ya samu dama goggagen dan bariki, yace sannu fa yanmata, tace toh Ya? Daidai ne, na leqo shopping ne ok, muje na tayaka shopping din, sai da ya jidan mata kaya sannan suka koma mota, yace yadai yanmata, Ina mukayi? Tace gidanka, yace noo sai dai gidanki, tace ni baquwa ce banyi 3hrs cikin garin kaduna ba, yace Ok sai muje Hotel koh? Tace Anyhow, sorry i dint get ur name, Ta kashe mai Idanuwa tare da sakin murmushi, Sunana BADIYYA
[truncated by WhatsApp]
37. Gidan Gandu by Biebee Isa
.Wow Badiyya nice name, tace tnx, nikuma sunana Alhji Haladu mai Dala, ta zaro ido da sauri tace na NNPC? Ya ce ni din ne, wani dadi ya ziyarci zuciarta, nan ga ja mota sai Guest House dinshi. Nan suka shiga aikata Sabo Waiyazubillah, Allah ka haskaka mana zukatanmu Amin.
Dalilin Zuwan Badiyya kaduna Shine tazo yawon bude ido da wanda zai dinga debe mata kewa don Zaid be san harka ba, sai kuma Allah ya kawo mata Alhaji Haladu Maidala, ita ko kakarta ta yanke Saka….
*****
Maiduguri
Sun iso Maiduguri lafia, Da gudu Bilkisu ta fita tayi Sassansu da gudu, gidansu ta wuce a parlor ta iske Mamarta Aunt Sadiya, ta rungumeta, Mami i missed u so much, jin dadi ya ziyarci Anty Sadiya, ganin diyarta cikin walwala, tace dota shine baki gaya min kina nan zuwa ba, tace daman suprise nakeso na baki, kuma na baki, suka gaisa sosai kafinta ce bari naje na kai gaisuwa gun Tsoho.
Sun kwana 2 a Maiduguri gobe ne Su Islah zasu wuce Kano don tafia Lagos, cikin kwana ki biyun nan ta gama Sallama da kowa, Yanuwanta na nesa da na kusa duk ta kirasu ta shaida musu tafiarta ta na cewa a yafe a yafe.
Bauchi
Ko da ta shigo taga ya hada kayansa cikin Akwati ta san cewa tafia zaiyi kuma Maiduguri zaije, tace Yasamir Tafia xakayi? Ba tare da ya kalleta ba yace eh, tace har dani zaka tafi koh? Ya watsa mata wani hararan da ta ga tsanarta a idonsa, tace Yasamir why are u doing dis to me? U cant leave me here, ta fashe da kuka me ban tausayi, tace I cant take dis anymore, Y do u hate me soo much? Ya zakayi tafia ka barni cikin wannan tangamemen gidan ni kadai? Is not fair, ko me na maka ai be kamata ka dinga gallaza min haka ba, do u know rashin tankani da kakeyi yana Bata mun rai? It tears me apart wenever u reject me or u push me away, Y yasamir? Isit bcoz i love u? Ta fashe ds wani kuka me ban tausayi ta durqusa gabanshi, wani abu yaji ya soki zuciyarsa. Wai shin meye laifin Amira? Me tayi mishi ne da ya tsaneta haka? Tausayinta ya shigeshi, tare ds nadamar abubuwan da ya mata, ashe ta na sonshi, toh shi ya zaiyi ya fara sonta? ya daure dai yace Amirah, ta shi ki shirya kayanki, ki dauki kaya kala 5, muje mu ga idan zaa samu ticket dinki, idan babu we have to wait, bata san sadda murmushi ya subuce mata ba tace Thanks BigbroSamir u d best, i love u. Murmushi wanda be kai zuciyarsa ba ya sakar mata, wai shi nan murmushi yayi, oh ni su Amira ba aji har ta sakko.
Lagos
Da dokinsa ya shigo, Hanifa hanifa Gobe Su Islahulkhair xasu xo, tabe bakih tayi, yace Hanifa bakiji bane? Tace idan naji me zanyi?ina ruwana da su? Murna xanyi ko meye? Ni kawai Mallam ka kaini Gida, i am tired of staying here kamar wata Maiyah, Zayyad yace Hanifa, m ur husband, watch ur tongue, dont take my silence for granted, ba zaiyuwu ba ina miki maganar arziqi ki maida mun ita na tsiya, ba ke ba har Mu’ammar na girma, amma duk maganar da tazo bakinki ki yaba mun, i tke ol of it don a zauna lafiya, toh i wont take it anymore, gida kuma ba zan kaiki ba, u are stuck in here sweety, ya tashi ya bar mata dakin, kuka ta fashe dashi, kaii ashe ya iya fada, duk abun da take mai be taba tankawa ba sai yau, ita ya zatayi, tunda bilkisu ta kirata tace mata kwanan ta 2 Maiduguri hankalinta ya tashi, son ganin gida ya dirar Mata, Haka ta rungume pillow tana hawaye, Zayyad kuwa yayi ba qaramin Namijin Kokari yayi ba , har ya iya bude mata ido, da Kyar yayi hakan sai da yakai zuciyar sa nesa, kiran Bestynsa yayi ya fada mata yanda sukayi, ta taba mai tace yauwa dan gidana kayi qoqari, Kar ka damu Slow and Steady Win d race..
Maiduguri
Gida ya kachame da Murna don ko Samir Da Amira sun diro, Murna gun Hajia Babba ganin qawar fadanta wato Amira ta xo, sai nan nan akeyi da ita, Amira baki har kunne, nan ta fara Sakarcin da ta saba, Samir dai mamakin yanda take ta zuba Shagwaba ba gun Hajia Babba da babanta takeyi, suko sai biye mata sukeyi, kamsr ba Amiran nan ba wanda ta koma silent a bauchi, wai ko donta ga nan gidane? Hajia Babbs tace kuje ku gaida Tsoho, Kila ya dawo daga gurin Dr Munir din, Samir yace to Tsohuwa, tace wlh samir ka fita idona, ya miqe yana daria Amira ta rufa mai baya, tafiarsa ma abun kallo ne, ta tuno tafiar su zuwa nan yau cikin Jirgi, ba uhm ba uhm, kai wlh i lob u bigbrosamir. Suka shiga parlorn Tsoho da Sallama, Tsohi hannu biyu ya sa yana tafi, Gata Gata, Amira ta rugo da gudu tana fadin gani gani, tsohona wlh nayi kewanka, wata kusan 6 rabona da na ganka, yace ai Amira saura Kiris na sa Usman ya kaini Bauchi da kayana don cewa nayi gidanki zan koma da zama, sbd nayi kewan Sakarcinki, sai da aka hadu aka dinga bani haquri kafin na haqura, ta kwashe da daria, Samir dai ya murmusa ya duqah yana kwasar gaisuwa, Tsoho ya musu ya hanya kafin ta shiga bashi labarin Bauchi abunda ya ba Samir mamaki shine bata gaya ma tsoho kallan xaman da sukeyi da Samir ba, lallai kam Amira tyi hankali, Tsoho ko dadih yakeji wai sun hada kansu.
Samir ya miqe yace bari ya shiga Sauran Sassan, tsoho yace daiki matarka ka tafi da ita ta fara hadassa min ciwon kai, tace ai wallahi sai mun gama firan dakai, Samir dai be tanka ba yayi wajei. Sassan Hajia Ama ya fara yi, daga nesa ya hangota, duk chanjin da tayi besa ya kasa ganeta ba a hankali ya furta Islahulkhair? Kwata kwata bata ga kowa a gabanta ba, burinta ta qarisa gun tsoho, waya takeyi da Fadila tana mata list din abubuwan da zata sayo mata a England idan zata dawo, ke dilla tun ynz xaki fara list, ba fa gobe zan dawo ba, gobe zan tafiiii– hooking tayi ganin taci karo da wani abu, wani abun ma Yasamir, sun fi minti 3 tsaye ba wanda ya iya furta kalma daya tak, chan samir ya hadiye wani mugun miyau, yace Sister, Ya kike? Bakin ta na rawa tace ina wini yaya samir, ganinsa ya sunce mata abubuwa da dama, kasa amsa mata gaisuwan yayi ya shiga duniar tunani, daidai lokacin ne Amira ta fito daga parlorn Tsoho, idonsu kyar kansu, tace Islahulkhair? Me takeyi anan? Wat is she doing wit my husband? Ta tunkaro su kamar zata tashi sama. Nidai nace Islah watch out, meerah is coming to pull ur hair
38. Gidan Gandu by Biebee Isa
Samir yayi saurin katse shirun ta hanyar cewa ,Yaushe kikazo? Tace na jima, M leaving for London tomorrow, wht? Why? Tace xan tafi skul, zan fara skulling a Cambridge Uni, daidai na Amira ta tsaya, ta ki qarasowa ta labe tana jira su ci amanarta tayin maganar soyayyah ta dauko shebir din kusa da ita ta rotsa musu kai lol, Samir ya ja tsaki, ya san da tafiar Mu’ammar, don dai be san inda yaje ba wlh da sai ya bishi ya gaya mai Islah doesnt deserve dis, ranshi ya qara baci, Yace Islah are you happy? Tace YaSamir ofcoz i am, yace Islah it kills me inside dat Mu’ammar hurts u, ba yanda xanyi ne, coz i dont have any rights to u, but u deserve to be happy, tayi murmushi me ban tausayi tace Yasamir, its ok m fine, Ina fatan komai yana tafia daidai tsakaninka da Amirah? Ya shafa qeyah yace Islah is not da Easy, i tried, ta bata rai tace wat do u mean u tried? Ynz kake ce mun i deserve to be happy, ita kuma fa? Dont she deserve to be happy? Samir yace Astagfurullah Islah i cant get u off my head, hawaye ya zubo mata daga idanuwa, ta goge ta daure fuska tamau tace U can and u will, Amira is a good person tho sometimes she behaves childish, wannan ba dalili bane, m married, m not ever coming back to u, Amira ce matarka, Yasamir u hate to see me hurt? Den learn how to love Amira, ina so son da kake min ya rikide ya koma ma Amira, ta wuce ta barshi nan tsaye, Amira na ganin Islah ta taho ta boye don bata son Islah ta ganta tana labe.
*****
Sai data share hawayenta ta shiga da Sallama, Tsoho gani, yaiwa Islahulkhair zo zauna a nan, ya nuna kusa dashi, taje ta zauna, Yar Nasiha zan miki, kinga gobe ne tafian ki koh? Ta gyada kai, yace Islahulkhair to kar ki ga an kaiki wata qasar da baki da uwa baki da uba kice zaki sauya halaiyarki ta gari, kice zaki sauya ki koma halaiyar turawa, to kiji tsoron Allah, ki riqe Addininki da ibada, ki san da cewa akwai Aure akanki, kar ki ci Amanar Aure, kar ki zubar mana da mutunci, kar ki manta daga gidan da kika fito, karki manta akwai Jinin Zailani tattare dake, karki bamu kunya, Nasiha sosai ya mata me ratsa jiki, a karshe ya shaida mata dole zata dawo idan Mu’ammar ya dawo. Ta share hawaye tace InshaAllah Tsoho ba zan baku kunya ba, InshaAllah zakuyi Alfahari dani, nd bazakayi nadamar Amincewar da kayi naje Karatu wajei ba, ya murmusa yace Na yarda da tarbiyyan da kika samu, jeki Allah miki Albarka tace Amin..
******
Da Daddare Amira Ta Iske Islahulkhair a sashensu, Islah ta ce Amira damar harda ke a ka zo? Amira ba ta tanka ba ta xauna kan gadon da Islah ke hada kayanta. Amira ta nisa tace kina sonshi ko? Islah tace What? Who? Amira tace Ya Samir, Islah tace ke ce matarsa, amira tace amma kece masoyiyarsa, ke yakeso, tace ba haka bne, tace Yaya ne? I saw u talking to him, Islahulkhair sai yaushe zaki gane har yau ya samir yanasonki, saboda ke Yasamir ya tsaneni, ba yason kulani. Amira ta fashe da kuka, Islah ta fara lallashinta, chan kuma ta ga Amira ta zabura kamar an mintsineta, tace da Islah you and i are not friends ryt? Islah tace eh mu ba qawaye bane, Amira tace kuma u know i dont like u ryt? Islah tace yes as more as i dont like u too, Suka fashe da daria tare ds rungune juna, i miss u Meerah, i missed u too Islah, Islah tace tell me ya xaman ku yake sa Yasamir? Nan Amira ta kwashe komi ta gaya mata, tace wlh dama tsoho ya raba aurenki da Ya Muammar, sai ya aurs miki Yasamir, qila hakan zaiss ya dinga kulani, kila ma ya soni, Islah taji tausayin ta, ba ta ji dadin abun da Samir ya mata ba, tace Amira kece Matarsa, ke ke da hakkin ya soki, ta kamo hannunta gaba ki daya, tace listen to me n listen good, kece zaki sa ma Yasamir sonki a ransa, Tace How? Amira ina so ki daina bada kanki gurinsa, ki daina mai kuka, ki daina shishige masa,ki dinga Jan aji, ta bata rai Kina nufin banda Aji? Islah tasan halin Amira ynz tana iya burkuce mata, tace aa ba haka nake nufi ba, ina so ki fita batunsa ne, kar ki fasa duk abubuwan da kike mai da, amma ki nuna mai ke ba ki san Iskar da ta debo shi ba, Kingane? Ta gyada kai, to idan ya share ni fa shima? Tace watever he does kar ki sake kai kanki gurinsa, zai dawo gareki eventually, tace zo kiji ta mata rada a kunne, suka kashe suna daria. Ba zan bar Maiduguri ba sai na siya kayan, don nasan idan mun koma bauchi ba zan fita baa, nan suka cigaba da fira, har Bilkisu ta shigo, Amira tayi mamakin ganin Bilkisu a Sashen Uncle Umar, Amma Islah batayi msmaki ba don ta san Bilkin Yayanta ta fara sakkowa..
WasheGari a Lagos
Tun da Suraj ya mai Waya yace Yanzu zasu taso Zayyad ya bar Aiki ya nufi MMAirport Lagos, ya tsaya jiransu. Yana nan har jirginsu ya dira, be sha wahalar ganosu ba, ya Rungume Suraj cikin murna, watansa6 be ga na gida ba, Ya ba Islah hannu suka tafa, tace YaZayyad ina Hanifa? Yace tana gida, Suka dunguma Sai Gidan Zayyad.
Tana jin qarar motarsa ta lewa ta window, ta tabr bakih duk da taji dadin ganinsu, daki ta wuce suka karaso da Sallama, kafin ya tafi sai da ya siyo abinci a TANQUIEEZ eatery, yace mu ci Abinci ko? Suraj yace Ok, suka hau dinning, Islah ta bude murya tace ina matar gidan ne?bataji tayi baqih ba? Hanifa naji tayi biris, Islah ko da neman dalili ta tashi tayi hanyar dakin, kamar Zayyad ya hanata, sai ya qyaleta, zaune Ta ganta, haba Hanifa baki ji mu bane? Hanifa ta kalleta ta watsar, Islah tayi murmushi taceOh i see, u still carry dat hatred for me afta ol dis whyl, m oready married to him, sannan hanifa ta tanka, ai naga u are married to him amma ya tsallake ki ya bar qasar ba tare ds ya kwana ko sa daya gidanki ba, tsanar tayi tsana, Islah taji zafih but sai ta dake tace, wat matters is dat m still married to him, nd i said it once nd i wil say it again, YaMuammar is never evr coming back to u, thers nothing u can do abt it, dama kin kwantar da hankalinki kin rungumi YaZayyad kafin Yan Matan lagos sun janye miki shi, tafita ta barta zaune, kuka ta rushe dashi me sauti, Suraj yace Isi wat did u do to her? Ta mai wink nothing wr just talked Zayyad ya harareta yace waya ce ki sa min mata kuka? Duk suka yi daria, a ran Zayyad be san kukanta so ya ke ya je ya lallasheta, but ba zai iya ba coz is part of d plan.
8 na dare suka gama shirin tafia don flyt dinsu is by 10, bata daddara ba ta leqa tana nan kwance kan Gado tasha kuka , tace Hanifa ni na tafi, Kuma bansan rannar dawowa na ba, A yafe, Sai Wata Rana Allah ya hada fuskokin mu da Alheri, I love u, Ci kanki Hanifa ba tace ba, tana jin shi ya tada Mota, ta leqa window ta ga tafiarsu Hawaye mai zafih suka fara bin kuncinta…
Airport
Sun gama clearance, a nan sukayi Sallama da Zayyad bayan ya qara ma Islah Nasiha da Waazi, sukayi musabaha, ya juya su kuma suka wuce Boarding Gate. Karfe 10 da kwata Jirginsu Islah ya daga zuwa Qasar England duk ds xasuyi transit a Dubai.
Toh Islahulkhair Allah ya tsare ya sa ayi karatu a Sa’a Idan Fans sun hada min kudin Jirgi zan biyoki England don jin yadda Kike.
_Bibilicious Biebee_
39. Gidan Gandu by Biebee Isa
Kaduna
Kwankwasawar Kofa taji, da sauri ta tashi ta nufi kofar don a zaton ta Mummy bon ce, wani ta gani tsaye, ta ganeshi sbd wata rana ta kan ganshi da Jawad, da Alamu direba ne, ya na ganinta ya rusuna, Ina kwana ta ce ina kwana? Dama Yallabai ne yace na daukeki na kai ki Maiduguri chan gida, zaiyi tafiya ne kuma zai kwana biyu. Fushi, takaici, masifa ya dirar ma fadila lokaci guda, ta san cewa idan ta bude bakih ta ma direba magana to tabbas ba me dadi zai fito daga bakinta ba, kuma direban ya manyanta, ba zata so ta mai rashin kunya ba, ba tare da ta tanka shi ba ta maida kofarta ta rufe, zubewa tayi nan tana kuka, tunda aka kawota sai yau ta xubds hawaye kan abun da Jawad ya ke mata. Ko 2hours beyi ba da fita Bazai iya ce mata ta shirya zai sa a kaita Maiduguri ba, ya mata maganan ne ya ke ganin asara, wato da ya bude bakih ya mata magana ya gwammace ya turo mata direba, to ba inda xata, duk yadda take son Zuwa Maid ta haqura, Su xuba shi da ita, shege ka fasa. (nidai nace Uhm Uhm Fadila, ba a fushi da gida). Mallam Idi Direba ya sake Rafka Sallama, ta goge hawayenta da sauri ta leqo, yace Hajia baki ce komai ba, tace Ka tafi kawai ba inda zani, yace Hajia zamanki ke kadai a gidan be kamata ba, akwai hatsari, tace ba inda Zanih, Ya jinjina kansa ya ce to sai anjima. Ta rufe qofa ta sake fashewa da kuka.
Jawad na cikin jirgi Zaije 3weeks Workshop a Amsterdan, ya kira Idi Direba, Mallam Idi kun fito? Yace Alhaji tun daxu na ke ta kira wayarka be shiga, tace wai ba zataje ba, cikin fushi ya kashe wayar yace ita ta sani, ana tausayin zamanta ita kadai a gidan bata sani ba, tayi ta zama har sai na dawo ita ta sani..
Bayan Sati 1
England
Sai da Suraj ya tabbatar ya tanadar ma K’anwarsa komai na buqatar ta, ya zaunar da ita bayan sun dawo daga yawano bude idanuwa ya shiga yi mata nasiha, Kinga idan kikayi wani abu ni zaa ga laifi, ni zaa ce sanadi sbd nina jajirce akan sai an kawo ki nan, ki ba marada kunya, ya shiga mata waazi ta sigar lallashi. Ta rungumeshi tana hawaye, i wont let u Down Yayanah, yace i know, share hawayenki ki tashi mu fara kwasar kayanki mu kai chan skul din. Don so nake Gobe ki fara kwanan hostel, tace toh Yaya, yaushe zaka tafi? Yace i think Jibi ko Gata, tace toh Allah shi kaimu. Haka suka tsaida CAB suka loda kayan Islah a ciki suka nufi Cambridge Uni don shirya mata dakih.
Key ya sa ya bude room din,Dakih ne Babba, Gadaje biyu, da Alama akwai wata a dakin, ta kalleshi tace Yaya Ashe ba Single room bane? Yace Sorry i cudnt get u a single room, ba vacant sai multiple, tace Itsokay i can manage, nan suka shiga gyara dayan side din, suka saka komai inda ya kamata, kafin Suraj ya zube kan Kujera tsabagen Gajia, yace washhh nagaji, Kai yaya dan aikin nan ne ka gaji? Yace ehmana tun da mukazo England 6 days back ban zauna ba, ban nan ban chan, ban neman gida, ban neman kaza, ban neman kaza kuma ki ce dan aiki? Ta qyalqyale da daria, ai ynz sai ka tashi mu koma chan masaukin mu koh, be bata amsa ba sai ganin wata sukayi ta shigo tana kallonsu da mamaki, sanye take da dogon jeans da er top sai dan jacket kanta sanye da qaramin hijabi Himar. Suraj ya miqe yace Hii, m Suraj dis is my sister Islahulkhair yarinyar fara kyakyawa tace Assalam Alaikum, suka amsa mata da murmushi a fuskar su jin dadin kasancewarta Musulma, tace i gt a call frm d ABlock, i was told abt my upcoming roomate Islahulkhair? So i knw abt her. Its nice to meet u, Islahulkhair ta yi murmushi tace my pleasure. suraj yace good, what is ur name? Oh sorry my name is ZAINEEMA USUF Isi tunda kinsamu Kawa, ai inaga gwara ki fara kwana a nan koh? Ido zaineema ta bude tace lahhhh daman kunajin hausa? Su ma suka bude ido da mamaki, suraj yace ai kece zamu ma tambayan nan, tayi daria tace Ni er Nigeria ce yar garin Yola, mu fulani ne amma ina jin hausa sosai, Islah tayi daria tace muma yan Nigeria ne but A Maiduguri muke, Zaineema tace lallai ba kuyi kama da yan Nigeria, nafi baku Iran da Somalia sukayi daria, Suraj yace ok i will leave u two, zan koma na huta, Suka mai rakiya har wajeh. Kafin kace meye Zaineema da Islahulkhair har sun zama best of friends.
Bayan kwana 2 Suraj ya Bar qasar England bayan Islah ta sha kukan tsiya, ya dinga lallashi da qyar ya zameta daga jikinshi ya tafi bayan ya danqa amarta gun Zaineema.. A Dubai ya tsaya don yana son ya huta kafin ya koma Gida Nigeria. Sim ya siya ya kira mamarsa da babansa suka sha fira, ya shadai musu yana dubai kuma zai danyi 1week kafin ya dawo suka mai Allah ya kiyaye, ya kira Tsoho suka gaisa, karshe ys kira Islah ya sanar mata ya na dubai har yace ta turo mai Numbern Bilkisu .
Suraj kwance a tafkeken Gadon Hotel, ya gama kallon ball, yau a gajiye yake be son xuwa ko ina, Ya kasa Dialling numbern Bilkisu da Islah ta turo mai tun jiya, wata zuciyar na so ya kira wata ta hamashi, samun kansa yayi da bude Whatsapp da Numbern Dubai din, ya. Be yi filling information din komi ba, Bilkisu ya duba, ya ganta Online Karfe 11 na dare a qasar Nigeria, Samun kansa yayi da tunani da wa take chatting da daddaren nan? Wani abu ya tokare mai rai, ya daure ya mata typing Hii.
Maiduguri
Kwance take kan gadon Mummynta, tana chatting da Hanifa da GC dinsu na makaranta, ta ga sabon Number yace mata Hi, ba dp ba status, ta duba number taga ba na England bane, number tafi kama da na UAE to kodai Ya’Ammar ne? Da sauri tayi replying Hello, Bayan dan gaisuwa tace sorry pls who are u? Yace Ur secret Admire, tace u knw me? Noo, but i want to knw u, coz my heart Tells me YOU ARE THE ONE i. Ta tura mai wannan smiley din na kallon Sama(🙄) yace nd my heart tells me ur name is Bilkisu mai Gadon Zinare.Nan gabanta ya fadi, ta san wannan ba Ya Mu’ammar bane, don ba sa kalan wasan nan dashi, Kuma Wannan ba Ya Jawad bane don tunda akayi aurensu ba su sake magana ba, nd Tasan tabbas wannan ba Ya Suraj bane don ba sonta a zuciyarsa kuma wannan dan zafin kaine ba zai biyo mata ta haka ba.
To Waye Wannnan??ta tambayi kanta…
_Bibilicious Biebee
5
40. Gidan Ganduby Biebee Isa
Kina jina? Bilkisu kinyi shiru, tace pls sorry m not interested, yace fine i will let u think zan baki 1week but pls i want us to be friens bfr den, ta danyi jim kafin ta mai typing OK, ta ce zata kwanta ya ce sleeptyt my Angel. Tabe bakih tayi ta kashe data dinta ta kwanta ta na tunanin wannan dan Bawan Allahn. Shi ko Suraj ya dafe kai yana fargaban amsar da zata bashi bayan 1week, kar dai ta amince mai. Haka ya dinga sake sake, daga karshe ya watsa ruwa ya futa gari..
Kaduna
Kwanankin da tayi da Alhaji Haladu tayi su ne cikin Jin dadi, har dan k’ibah tayih, ta kuma wara haske, Miqah tayi ta miqe tace YaAlaj zan dan leqa supermarkt yace toh Diyyahta nawa kike buqata? Tace i think 100k will do, ya ce ok, dan brief case ya bude ya zaro bundle din 1k ya miqa mata yace here u go. Ta amsa ta na mai karkashe ido. Wayarsa tayi qara ya dauka, Hello, PA, miqe wa naga Alhaji yayi ya na fadin What?? Ya tafi Amsterdan? Why m i jus told? Ya kashe wayan a fusace da qarfi ya sake ihu, diyyan kanta sai da ta tsorata da shi, a hankali ta matso ta fara mantar dashi bacin ransa, sai da ya dan sausauto tace YaAlhaj lafia? Tsaki ya buga karo na ba adadi yace Wani ke barazanar kwace matsayina a gurin aiki, Amsterdan aka turashi, dat shud be me, na dade ina jiran lokacin da za a turani chan, ko maganar banji a nayi ba sai dai kawai naji ya tafi, for GodSake m d General Manger, diyya tace to ka koreshi mana, yace ba zaki gane ba, ya samu daurin Gindin Gwamnati, Abun daga sama ne, diyyah tace rabu dashi Alhaji na, We’ll get him soon, ya jinjina kai, yace muje dai zuwa, a zuciyarsa kuwa cewa yake Dat Jawad idan nayi sake zai dakushe mun tauraruwata, bazan bari hakan ta faru ba.
Lagos
Jigib ta fadi tana juyi, Yau ta fara Jinin Aladarta, tun data zo lagos take fama da Wani Azababben Ciwon Marar da bata san dashi ba, Da qyar ta shiga toilet ta gyara kanta, juyi take kamar zata mutu, kamar daga sama sai gashi ya dawo gidah, ganinta haka ya qara firgitar dashi, Hanifa? Ciwon ne ya tashi? Ya kai hannu zai dauketa, idonta a rufe tayi saurin tureshi, Hanifa lemme help u, bakinta da be mutuwa tace i dont need ur help, Ba zai jure ganinta haka ba, ya gaji da ganinta a haka kullum wannan larurar ta sameta ta na hanashi taimaka mata, yau ko ba ta isa ba, nade hannun rigarshi yayi ya sabeta kamar jaririya, wuntsila wuntsila ta fara yi, duk da azabar da mararta keyi ba ta daina dukan shi a jiki ba, shi ko ko a jikinsa wai an tsikara kakkausa, sai da ya sata bayan mota ya finciki motar sai Asibiti. A Hanya ya kira Abokinsa Dr Davina, yace gashi nan zuwa wit his wife, ba su jima suka isa asibitn, nan da nan Dr Davina ta turo nurse su ka kaita Office dinta, nan da nan aka kwantar da ita kan Gadon office din, bata sha wahala gun gano matsalar hanifa ba, bayan ta kora Zayyad Wajei, Allura tayi mata, ko 15mins ba ayi ba ciwon ya lafa, Dr Davina Ta mata wasu tambayoyi game da yanda take tsintar kanta yayin da take period a da, tace a da bata jin ko ciwon yatsa, haka kawai xata ganshi, yanda yazo haka yake tafia ba tare da ya haddassa mata ko da ciwon yatsa, Dr tayi rubutu tace ynz fah? Tace ynz har suna takeyi, kamar yaushe kika fara ciwon marar? Tace tun da tazo lagos, kusan 7months kenan, Dr tace but uo married, be kamata ace kina ciwon mara ba, hanifa tace mesa? Akwai wani magani ne specially fr married ppl da zai hanata wannan ciwon? Dr ki bani pls, Dr Davina ta qura mata ido, taga qarancin shekaru da yarinta tattare da ita, bata sha wahala ba ta tambayeta kalan zaman da suke da Zayyad, hanifa kuwa ta shaida mata ba wata mu’amala da ya taba shiga tsakaninsu da shi, Dr davina tace beht y? Hanifa tace coz i dont have d slightest feeling for him, bana sonshi, Dr Davina Tace ynx me kike so? Tace ki rubuta min mgn, Dr davina ta daga kafadu ta rubuta mata maguguna tace wadannan magunguna pain relievers ne, zasu dinga relieving dinki daga ciwon but not completely, every month zaki dinga sha, coz ciwon naki zai dinga zuwa miki every month nd only God knows damage din da magungunan zasu miki. Maybe su lalata miki mahaifa nd maybe su hanaki haihuwa it depends dai, hanifa ta dago cikin razana, Wat kind of a Dr are you? Mesa zaki rubuta min magungunoni masu ilahh? Ba tare da damuwa ba tace they are the only ones i know, amma kinsan akwai Maganin ds zai warkar miki da ciwon nan gabaki daya? Ba tare ta da ta jira cewar hanifan ba tace its too bad ur husband is d only cure to uo sickness, qila idan kika bada kai bori ya hau Allah sa a dace, nd ke da ciwon nan har abada, think abt it hanifa, u need Ur Husband, u need Zayyad. Hanifa ta tashi a fusace, tayi wajeh, bakin qofah ta iske Zayyad, yace Hanifa how are u feeling? Harara ta banka mai, duk a idon Dr, ya kalleta yace Dr? Tace u guys can go ahead zan kira ka na ma bayanin komai yace okay thnx, hanifa na gaba ya na biye da ita…
GIDAN GANDU 41
Bauchi
Sanye take da kaya Riga da Skirt English wears, tayi kyau matuqa, ya shigo gidan da Sallama, kallo daya Amira ta mai ta watsar, ta cigaba da wayarta, tsayawa yayi yana kallonta, tunda yake be taba ganin ta mai wannan kallon ba, ji ko a jikinta kamar ba ta san da tsayuwarshi a gun ba? Miqewa tayi tana wani irin taku ta bi ta gabanshi ta wuce dakinta. Bakih bude Samir ya bita da kallo, Anya kuwa? Amira ce nan? A fili yace Wat’s got to her head dis days? Ya lura tunda suka dawo daga Maid bata fiye mai magana, ta daina kulashi, ta daina shiga harkarshi, to meye haka? Chan kuma yayi tsaki, zuciyarsa na tambayarshi why are u even worried? Ya sake wani tsakin a fili yace I dont Care, tafi nono fari. Ni dai nace Anya kuwa bigbro Samir? Mu dai je zuwa muga yadda xaka kareh da lilsismeerahn ka…
Abuja
Zaid ya shigo gidan da Misalin karfe 4 na rana, zaune ya ganta tana kallo, tana ganinsa ta miqe, sannu da zuwa Yazayd, ya kaw ar da kai ya Amsa, yayi hanyar dakinsa, har ya kusa shiga dakin ya juyo ya kalleta yace ki hado min Credentials dinki, Gobe zan fara miki processing Baze University, bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba, sai yaga ta mishi kyau, da sauri ya kawar da kansa, tace Yazayd ya tsaya chak don yaji kiran nan, ya juyo tace thank u, kai ya gyada ya juya ta sake kiransa, shi ko baya son kiran nan da take mai, ya sake juyo wa, duk ta marairaice tace na zuba maka abinci please? Haka kurum yaji tausayinta, bazai iya dizga ta ba ta hanyar kin cin abincinta da ta mai tayi, a hankali yace sai nayi wanka, da sauri ta nufo shi ga mamakinsa sai ta shige dakinsa, binta yayi a baya ya ga me zatyi, toilet dinsa ta nufa ta shiga hada mai ruwan wanka, ta fito tace ur water is ready Yazayd, samun kansa yayi da ce mata Thanks, ta fita shi kuma yayi toilet yana ture tunanin Maysah, befi 25mins ba sai gashi ya fito, tana nan zaune tana jiransa, tana ganin shi ta miqe tayi kan dining ta ja daya daga cikin kujerun kan dining din Tace Yazayd pls sit, beyi gardama ba yaje ya zauna, (ni biebee nace Ke maysah meye na wani lallabashi, ke ya kamata ama haka fah mtsw) ta shiga zuba mai abinci, kamshi ya doki hancinsa tuwon semovita ne miyan agushi, da stew me Ganda, Zaid da be cika son Solid food ba sai gashi Mallam Zayd ya kwashi tuwo har mulmula 2da rabi, be taba cin girkin ta ba, be taba zaton tayi abinci haka ba, ya ji dadin tuwon nan, ya dade be ci abinci haka ba, ya miqe zai tashi tayi saurin cewa Yazayd ga Sobo, ta tsiyayo mai cup daya, ya amsa yana sha ya na me lumshe idanuwa, dadin sobon kamar ya tsinka mai kunne, sai da ya sha kofi biyu, ya miqe tare da kallonta yace thank u, Ya koma kan kujera ya sauya channel zuwa CNN, kwashe kayan abinci tayi ta kai kichin, zuciyarta fes, dadi fal ranta, har bata san sadda ta turgude ba, tray din hanunta ya fadi, jug da cups din glass suka fashe Zaid ya juyo da sauri ya kalleta, yace hankali fah, tace its ok, i will jus clear d mess, ya juya kallonsa ga TV tare da fadin be careful dai, ba ta lura ba ta taka wani glass, qara ta sake don taji zafih sosai, kuka ta shiga yi, da sauri zaid ya taso, dama akwai takalma a qafansa, ganin Glass ko ta ina gashi ba takalma qafarta ya sa shi dagata sama ya aje kan kujerar cikin parlorn, ita ko zafih be sa ta ji dagin da ya mata ba, ido ya tsura mata, to meye abun kuka kuma? Ji yanda ta dage ta na kuka, leqa kafar yayi ya ga alamun gilas a ciki, dakinsa ya wuce ya dauko wani qaramjn akwatin first aid box, wani abu ya ciro kamar scissors, ya jawo wani dan stool ya dasa gaban kujerar da Maysah ke zaune, ya kamo kafar ya daura kan cinyarsa, Wani shock ya ziyarce su ba ita da ke cikin jin zafi ba har shi Goggan yaji wannan abun me wuyar fasltuwa.
_Bibilicious Biebee_
3 hrs · Public
More
4⃣2⃣ 🏡Gidan Gandu🏠 by 💕Biebee Isa💕 Zaineema ta bi bayan Islah a fusace tana qwala mata kirah, Islah ta juyo itama a fusacen, zainee tace what d hell was dat? Islah tace wat d hell was wat? D next time he attempts to touch me, he'll get something worse than dis, ta wuce ta var Zainee tsaye, straight dakinsu ta wuce, Zainee ta bita, zama tayi kusa da ita, tace haba Isii meye laifin Asad? He's handsome, nd brilliant, besides his a Muslim, y cant u accept him? Islah cikin daga murya tace I cant, coz m married, Zaineee ta tsura mata ido, tace stop lying, u knw if u dont like Asad jus tell him, kar kiyi Karya da aure, ta fita ta bar ta cikin dakin, Islah ta runtsen ido, tana tunano kalaman Tsoho, inda ya ke cewa Islah ki tsare kanki, ki tsare mutuncin ki, kar ki manta da Akwai Haqqin Aure Akanki, kar ki ci Amanar Aure..
Lagos
Ta shigo gidan da Sallama, Gaban Hanifa ya buga lokacin da suka hada ido da me Sallamar, jiki ba k'wari ta amsata, Madam Atutu ta ma kanta mazauni tare da crossing leg, suka gaisa da Hanifa ba yabo ba fallasa, Atutu tace na san baki ganeni ba koh? Hanifa tace Eh Gaskia, yeah dama baki sanni ba, Sunana Fatima, nd nice keda Tanquieez Eatryz, nazo ne gun Yayanki, pls idan yana nan ki kira minshi, Hanifa tayi jimmm, ta dai daure tace baya nan Indai ce Lafia koh? Atutu tayi farr da ido, yea lafiya sai Alheri, dama maganar auren mu ne, Iyayena sun ce na gaya mai ya turo, Wata uwar ashar hanifa ta kyabo, ta miqe tace kam balaeee, Iskancin mata iri na legas ne bin mazaje gidan su na aure? Toh wlh ba zai aure ki ba, Idan ma ce miki yayi ni qanwarsa ce to ya miki babban qarya, ni matarsa ce ta aure, and kuma bani ba kishiya wlh, so fitar mun daga gida ko wlh in sa mai gadi ya fitar dake, Atutu ta hadiye wadannan baqaqen maganganun Hanifa, ta miqe tare da sabar jakkarta, tace tabbas na san ke matarshi ce, amma ni ban daukeki mata ba, matsayin ki a nan be wuce qanwarsa ba, me kike tsinana mai a gidan da kike iqirarin ke matarsa ce? Ke kanwarsa ce nikuma matarsa, ki bari idan na shigo sai kiga yadda ake kula da miji da tattalinsa,nan ba da jimawa ba zan zama mata a cikin gidan nan, kuma lokacin ba ki isa ki gaya min baqaqen maganganu na kyaleki ba, don ko ni ba sa'ar yin ki bace amma ynzu kin ci darajar Yayanki da na keso kuma zan aura, so na barki lafiya, ta juya ta fita ta bar hanifa tsaye, kamar bishiyar da aka dasa, YaZayyad zai sake aure? Kawai sai ta tsinta kanta da fashewa da kuka, da gudu ta shige dakih ta zube kan gado tana kuka, damuwa fal ranta, Saboda me zaiyi aure? Zuciyarta tace sbd ba kya bashi kulawar da ya kamata, zunbur ta miqe tace to don me zata bashi wani kulawa? Ai ba sanshi takeyi ba, zuciyarta tace toh meyasa kike kuka? Da sauri ta share hawayenta, i miss home ta ba zuciyarta amsa, ta miqe ta koma parlor, duk yadda ta so kawar da zancen a zuciyarta taka sa, tunanin hadaddiyar yarinyar da ta zo neman mijinta takeyi, wai shin menene haka? Ni ko nace Hanifa Kina Kishin Yayanki Zayyad..
K'arasawa tayi inda yayi parking motarsa, ta bude gidan gaba ta shige tare da sauke ajiyar zuciya, jikinsa har rawa yakeyi, yace Yadai besty? Ya ku ka qareh? Tayi murmushi tace i can see anger and fear in her eyes, lokacin da na ce mata ina nemanka, ta shiga fargaba, ta na kishinka, nan ta kwashe duk ynda sukayi da ita ta gaya mishi, Tana kishinka Zayyad, ita kanta ba ta sani ba, so use dis Oppurtunity, Zayyad yyi shiru yana tunani, for her to do all wat she did to u, d anger d jealousy, it only means 1thing, She loves me, Hanifa na Sonaah.
Kano
Allah Allah take ta gama abinci tazo ta bude Whatsapp don Chatting da wanda Zuciyarta ke bege, Umar Z, tana mai so maras misaltuwa, amma ba ta taba nuna mishi ba, So ma take ta daina tunaninshi ynz har sai Allab ya kawo qarshen xamants da Suraj, Musamman ya dawo Naija don ita, ta qi yarda su hadu, kullum sai ya matsa mata kan sai sun hadu tare da gaya mata irin son da yake mata, ta kan ce mishi u are just a frnd Umar, i cant meet wit u coz m married, sai yace haba Bilkis, ina sonki, kuma na san kinasona, pls ki bani chance din zuwa gurinki, i want to see u, musamman na baro aikin da na keyi a Dubai don ke, i prove mysef to u, please, tace frndshp is all i can give u nagaya ma m married koh? Allah idan ka a qara min maganar so Zanyi blocking dinka. Tana son ganin Umar amma ba ta son Tsinuwar Mala'eeku, kuma har Skool Suraj ya sata, NWU, bata taba using opportunity tace su hadu a skul ba, don ta san matsayinta. Akwai auren Suraj a kanta, tunda ya dawo daga tafia da kuma dawowarsu gaisuwa kadai ke hadasu, sai cin abinci, sai kuma idan da safe ta shirya zai ajiyeta skul, idan ko bata shirya ba drivernsa ke kaita ya daukota, Musamman ya siya sabon sim da waya don kawai chatting da Bilkisu, ita kadai ke da numbern, a yanzu ya san ya kamu da son Bilkisu sosai, kusancinsu a Whatsapp ya sa ya gane kalar son da yake mata, Irin son da ko Fadila be taba mata irinshi ba, Ya kuma yarda da amincinta, ya gane ta san darajar aure, duk da ya lura ta kamu da son wanda suke chatting amma bata bi son zucyarta ba, Fargaban shi daya kar ta ce zata rabu dashi idan ta gano cewa shine Umar Z, Ya sha attempting Sanar da ita gaskia, amma sai ya rasa hanyar bi gun sanar da ita. Amma InshaAllah komai yazo karshe, zai bayyanar mata da gaskia, Zai bar wahalar da Zuciyoyinsu, zai bayyana mata sirrin da ke ransa...
Abuja
Da karfi suke buga k'ofar parlorn shiru, ta kwalawa maigadi kirah da karfi, ya rugo da gudu, wai ba kowa ne gidan? Yace eh hjia, oga yaje aiki, madam kuma taje skul, a ranta tace Skul? Ta kalli mamarta, mamar tace dama ta fara zuwa makaranta? Diyya cikin fushi tace shine don wulqanci ka bar mu mu ka shiga ciki, baka iya ce mana ba kowa? Yace sorry ma, i tot kina da key ne, ba ta kula shi ba ta ciro wayarta ta kira zaid, ringing uku ya dauka, hello diyya nah, kunyi landing kenan? Ba ta amsa shi ba tace haba Zaid, mun dawo ba kowa gidan, gashi mama bata son rana, Zaid yace ohh sorry, ai bansan yau zaku dawo ba, da na bar muku key, Gashi yarinyan nan na skul, Cikin masifa tace ni ka kirata ta kawo ma mutane key, ba zan iya tsayuwa ba, yace O'O gashi ban ma da numbernta, amma ki yi haquri, its pass 2, nasan tana hanyar dawowa, kiyi hqr kinji Diyyata? Katse wayar tayi xuciyarta na tafarfasa, mamar ta tace badiyya, kinga abun da nake ce miki koh? Yarinyar nan ta samu karbuwa gunsa gashi har ya sata makaranta ba tare da saninki ba, ko ya fara sonta, da qarfi badiyya ta ce haba mummy meye haka? Bakiji me yace bane? Ko numverta be dashi so pls just shutup ki daina qarama zuciyatah zafih, Uwar tace ohh Sorry ny dear, Horn sukaji, Maiguard ya wangale gate din, Motace Qirar Focus ta danno kai, duk suka zuba ma motar ido, wata kyakyawan farar mace ke tuqin,, a idonsu tayi parking, ita kuwa bata san sunayi ba, ta fito sanye da riga jalabiyya mai kyan gaske, Zuciyarta ta bata ana kallonta, waigawar da zatayi ta ga Badiyya da Mamarta tsaye cirko cirko, da alama basu ganeta ba, ta qarasa gunsu da murmushi, Aunty kune sannu da zuwa, Hankalin Badiyya yayi mummunar tashi, a hankali tace Rumaisah, Rumaysah ce wannan?
4⃣3⃣ 🏡Gidan Gandu🏠by 💕Biebee I§Λ💕
Maysah ta katse mata dogon tunani tace bismillahnku, Yadda kuka san hoto haka Badiyya da uwarta suka maids Maysah, duk inda ta sa kai idanuwansu na biye da ita, Badiyya takasa daurewa tace wai ina kika je ne kika bar mutane wajei? Tace ohh sorry wlh daga skul nake, tace ok, erhmm yanzu mun iso da yunwa, ina so ki hada mana lunch, Maysah tace ok Aunty, bari na chanxa kaya, tana shiga dakih maman badiyya ta sake ashar, haka yarinyan nan ta xama? Har Jamiaa ya sanya ta? Iya kacin ki SS3, kin yarda kishiya ta fiki, sai nayi magana sai kice min ba ya sonta, baya sonta xai kai ta wannan makarantar turawa Baze? Badiyya tace ni dillah mama ki min shiru naji da abunda ke damuna. Da sauri mamar tace ohh Sorry...
Badiyya na nan zaune tana karkada k'afa hade da tunanin clean din data ga Maysah, tunani takeyi Could it be possible Zaid is-- da sauri ta kar kada kanta tare da kawar da tunanin nan, Zaid ba zai mata haka ba, zaizo ya sameta, idan ko taga abu zai gagareta, gurin bokanfa kawai zata kai Maysah ya gama da ita.
Ba a jima ba, sai ga Maysah ta fito da tray a hannu, har ta ajr kan dinning, maman badiyya tace ke kawo shi nan, tace toh Mama, Ta kwaso abincin ta dire musu tsakar carpet din parlorn, ta juya xata tafih, Badiyya tace keh, ni kikeso na zuba abincin? Kamar Maysah ta juya, amma sai ta juyo ta shiga xuba masu, Ganin Doya yasa Badiyya cewa, uban wa zaici doyan nan? Allah ya sa bani kikeso nacin wannan farar doyan ba kamar wata bakatafa, Maysah tayi shiruuu, dallah dauke wannan abun daga gabana, ki kawo min wani abun, ji tayi ance why dont u go cook for urself? I think zaki fi sanin abun da kikeso, kiyi shi yadda kikeso. Gabaki dayansu suka juya suna kallon me maganan, Zaid ne sanye da Riga da Wando na Ash suit, Tana ganinshi taji duk wani bacin rai ya yaye, ta miqe ta nufe shi da sauri Oh My Zaid ta rungume, shima dai rungumetan yayi, tare da fadin hows my baby diyyah? ta shagwabe fuska tace I miss u, i miss u more diyyah na, Kan Maysah a qasa, gabanta sai faduwa yakeyi, ta rasa me ke mata dadi, miqewa tayi ta wuce dakinta, Don yau ko gaisuwa be samu ba. Sannan ne Zaid yazo yana ma mamar Badiyya ya jiki, sun sha India, tayi hquri be kira ba, don badiyyan ba ta nemesa ba, tace sorry myzayd, we cudnt get a sim, jinta kawai yayi tare da daga kai ba wai don ya yadda ba, ya wuce dakih don chanzawa. Badiyya ta kalli mamanta suka sheqe da daria, tace shegia diyata, kina Indian Kaduna, suka chafe, tace ai mama Halinki na kwaso kaff, ynz ma dai bari na kira Alhaji Haladu nahh
Bauchi
Yau ya kama Weekend, Samir na zaune kan kujerar parlornsa yana waya, Amira ta fito sanye da riga da skirt na English Wears, tun kafin ta fito jikinshi ya bashi ga lil sismeeranshi nan fitowa, a kwanakin nan wani abu yakeji game da ita me wuyar fasaltuwa, shariyar da ta ke mishi ya fi komai daga mai hankali, Ya so ya dauke ido daga dubanta, amma sam ya kasa, don ta mai wani irin kyau, Iya rayuwarshi a kasar waje, be taba ganin macen da Riga da Skirt ya mata kyau kamar Amira ba, ji yayi sonta na fizgarshi, kasa jurewa yayi ya miqe ya janyota jikinshi, Murtuk ta daure fuskanta, ta hade girar sama da na kasa, tace meye haka? Mamaki ta bashi, Gani yayi ta rikide ta koma Amirar daaa wacce bata Mutunci idan an takata, amma da yake shima namijin dunia ne sai yace Haba Lilsismeerah, me bigbrosamir dinki ya miki da kika daina mai magana? Ki ka daina kallo nah ko ta gefen ido ne? Wani mugun kallo ta watsa mai, tace ohh so daman jin dadin wulaqantani kake idan na magana? Dama so kake na dinga binka kamar mayyah kana shareni? Ba so daya ba so biyi nake binka ka kulani amma kayi kunnen uwar shegu dani. For 8th good months, Samir ya rintse ido, m so sorry Amira, wlh i truly regret dis, i can make it up of u, just let me, tace its too late, ba zaka qara gani na ina roqon ka min magana ba, or ina roqon ka sanar dani laifin da ban taba aikata ma ba, sannan ta lura da wannan riqon da ya mata, tace let go off me, ka cika ni, ka qyale ni mana, yace Amira kiyi haquri, Wallahi nayi nadama, dama i was angry nd Miserable, but not anymore, tace hmm lallai, saboda Islah ka chanza, saboda tace ka chanxa shisa ka chanza, da sauri ya girgiza kai, yace wlh dis isnt about islah, i dint do it for her, ki yarda danih, nan da nan zuciyarta ta karaya, dama da qyar ta ke gaya ma bigbrosamir dinta magana mara dadi, sai da ta kai zuciyarta nesa, ta dai daure fuska tace Najih sake ni, yace Na dai qyaleki for now. Komawa tayi ta zauna chan nesa dashi tana latse latsen waya, ya zuba mata ido kamar sabon maye, Sonta na shigarshi, ta mai kyau matuqa, kasa jurewa yayi yace Lilsis? Kallonshi tayi ba tare da ta tankashi ba, yace Kinyi kyau wlh, kayan nan sunyi fitting dinki, ta miqe ta qare kallon jikinta tace Allah koh? Da sauri yace Ehwlhh, inason kayan sosai, a ranta tace Oh kayan kakeso? Ba tare da tace komai ba tayi hanyar dakih, da sauri ya sha gabanta don be son ta katse mishi wannan jin dadin kallonta, yace Ha'an ina zakih? Tace zanje na cire kayan nan ne na zubar, cikin mamaki yace saboda mey? Cikin halin ko in kula tace sabida kanaso, ta raba ta gefenshi ta shige dakih, shi ko Samir ya ji zafin kalamanta, Waiyo Allah, shikenan Amira ta gama tsanenshi, ya ja ma kanshi, yanzu me zaiyi ya wanke kansa gun lilsis dinshi? Taya zai nuna mata matsayinta cikin zuciyarshi? Yace bakomi, i wont give up zan shanye duk da zaki min Amira, coz ni na ja ma kaina, amma Wlh Amira ina sonki. Amira na kallonshi ta windown dakinta, dadi ya lullubeta sonshi na qara ruruwa a ranta, nd taji dadi da yayi nadama, ta yafd9e mishi but sai ta rama abunda ya mata, sai tayi proving dinshi wrong,sai ta gwada mishi she's not a cheap person, and ba zai sameta a sama ba...
Kaduna
Wayarta tayi qara, ta rugo da gudu don ganin ko waye, TSOHONMU ta gani a Screen, da sauri ta dauka tare da Sallama cikin jin dadi. Ya amsa tare da kirarin da ya saba yi mata na Almasifatu, ta shagwabe fuska kamar a gabanshi tace zaka fara koh tsoho? Yayi dariya, yace kewanki ya cika ni, kin watsar dani a bola shisa nace bari na latsoki, ta marairaice tace wlh ba haka bane, ko shekaran jiya ai na kiraka da Asuba, jiya kadai nefah, yace da yau ma, tace ai gashi ka kira, yace ai naxata mijin na kine ya sa kika manta da mu, kamar yadda ya manta da mu, ya mance yana da yanuwa a Maiduguri, fadila ta tabe bakih tace shidai ya sani, ni ko kallo be isheni ba, sai yayi tayi ai, tsoho yayi shiruu yana tunani, dama hannunka mai sanda ya ke mata, yana so ya fuskanci halin da take ciki da mijinta, Fadila wani irin Zama kukeyi da mijin naki? Cikin halin rashin damuwa tace ko wa harkar gabanshi yakeyi, ai ni ina jin magana be taba hada mu ba, sai wata rana da ya gaya min baqah gaban qawata, Ran tsoho ya baci, wata 8? Magana be hadasu ba? Shifa beyi hadin nan ba don ya kara tarwatsa tsakaninsu, yayi hadin nan ne don ya hada kansu, Yace idan na isa da ke, idan ya dawo kice mai ina nemanku, kuzo Gida, tace Yo tsoho satinshi 3 rabonshi da gida, sai bakin direba nakejin tafiar nashi, Tsoho cikin bacin rai yace Zan ga Ubanshi, ke dai kiyi haquri, zan kamo bakin zaren...
[truncated by WhatsApp]
3 hrs · Public
More
Like
4⃣4⃣ 🏡Gidan Gandu🏠 by💕 Biebee Isa💕
Lagos
Tuni take jiran dawowarsa, bashi ba alamunsa, gashi yanzu har qarfe 11 da rabi na dare, abunda beyi kenan tsayuwar dare, sai ta samu kanta da shiga damuwa, zuciarta na mai mata saqe saqe, toh ko zance yaje? Nan da nan ta tuna wannan me suna Fatima data zo neman sa, ta tuna kalamanta inda take shaida mata xata shigo gidan, kaii sam ba zata ta bari wata ta shigo gidan Zayyad ba, jin tsayuwar motarshi ya tabbar mata da shine ya iso, ts sauke naunauyar ajiyar xucia, ta miqe tayi parlor, anan sukayi kicibus, kallonta ya tsayayi kafin nan ya rabata ya wuce, bin bayanshi tayi tace kajih, yayi gaba, ta qara cewa kajih, ya juyo ya dan hade rai, wai nih? Duk tayi tsuru tsuru, ta rasa yadda zata fara mai magana, ganin bata da niyyan magana ya sa shi yin gaba ya shigewarsa dakih, zama tayi kan kujera game da fashewa da kuka, ta miqe da sauri ta shiga dakin, lokacin har yayi kwanciyar shi, gadon ta hau a hankali tace Ya Zayyad, wani abu ya ji ya dirar mai a tsakiyar kai, tunda yake be taba jin ta kira sunan shi ba, ya juyo yana me fuskantar ta, bakih na rawa tace YaZayyad dazun wata tazo nemanka, ya hade fuska yace mun hadu, kun hadu kace? Yace eh daga gurinta ma nike, ta zaro manyan idanuwanta tace dagaske ita zaka aura?Yace InshaAllah, Kuka yajih ta fashe dashi, tace pls Yazayyad ka kaini gida, i really want to see my Mum, i missed home, be son kukan nan, yace kiyi shiru, ba yanzu za muje Maid ba, sai nan gaba, cikin fada tace for how long yazayyad? Tunda akayi auren-- sai tayi shiru ta kasa cigaba da maganan, yace Ehen ina jinki, ta dan muskuta, tunda na zo lagos din nan, wata8 kenan ban taba zuwa gida ba, kawai ka ajiyeni a nan don ka kuntata min, don kawai ka ga banda kowa, yanzu har aure zaka qara, ta sake fashewa da wanih kukan, miqewa zaune yayi, yana kallonta ta ma rera kuka bi hakki,Yau sai yaga duk tayi sanyih, ta qara kyau, beyason kukan nan da takeyi, amma yanaso ya tabbatar da sonsa da takeyi, yace kinaso kije gida? ta gyada kai da sauri, ya qara cewa bakya so nayi aure? Nan ma ta gyada kai, yace ki bani reasons not to marry again, tayi shiru, yace Hanifa, ina so na aure fatima, sabida tana sona, nan da nan ta sauya fuska, kar ya bata shirin sa ya sa yace i will take u home in two days, amma da sharadin zakiyi min biyayya nd zaki kula da all responsibilities na da ke kanki, only den i will decide if m to marry again or i will take u home kin gane? Ta gyada kanta a sanyaye Yace oya zo ki kwanta, ba gardama ta matsa kusa da shi ta kwanta tana ajiyar zuciya, shi ko Zayyad godia yayi ma Allah da ya sauko masa da hanifa cikin ruwan sanyih, Allah ya sa hakan ya dore Amin
Kano
Tana kichin tana hada lunch taji wayarta na ringing, ta fita don parlo don duba me kiran nata, Umar Za tagani, mamaki tayi, don tsawon taraiyyarta da Umar be taba kira ba, Sai chatting, kuma rabonsu da chatting tun shekaran jiya, bata ankara ba wayan ya tsinke, bata gama tunani ba wani kiran ya sake shigowa, ta dauka jiki sanyaye, Asssalam Alaikum My Angel, ta lumshe ido don taji muryan nan very familiar, ta amsa mai sallamar, yace Zuciyata ta kasa jurewa da fushin da kikeyi dani don nace kituro min hotonki, naga ai ba laifin na bane, laifin zuciyata ce da ta kamu da sonki Bilkisu, Ki daina min irin wannan hukuncin, ta bude lumsassun idanuwanta, tana jin dadin muryan shi, tabbas idan ta cigaba da sauraronshi, zata karaya har ta fara bayyana mai sirrin da ke ranta game dashi, amma ba zata taba barin hakan ya faru ba, tunda har yanzu akwai auren Suraj a kanta, cikin masifa tace kai mallam wai baka da hankali ne? Na gaya maka ni matar aurece, da mijina, wani alaqa ba zai taba qulluwa tsakaninmu ba, saboda haka ka kyaleni, kar ka sake kirana, Suraj yayi Murmushin jin dadi yace wlh ba zan daina sonki ba, kuma kina iqirarin kinada aure abinda mijin bai da mu dake ba, mijinki solobiyo me sakarai muna maza, ran Bilkisu yayi matuqar baci jin Umar ya zagi ya Suraj, tace ba wawa muna maza solobiyo, sakarai kamar ka, kasani mijina yafi karfinka, idan kayi zuciya kar ka qara kirana, yace ai ba zan taba zuciya Ba har sai kinzama tawa, don ko gani a qofar gidanki, ki fito muyi zancen soyayyah, tace kan ka dai akeji yace ba ki yarda ba koh? Shin ko ba gidan bane No 3 Nassarawa GRA gida me black gate with brown roofing, hantar Bilkisu ta kada, gabanta ya fadi, yace ki fito naga sanyin Idaniya or else zan shigo wlh, tace wlh yau sa kayi dana sanin sani ka jira gani nan zuwa, yau sai ka ga karshenka me bin matan aure, ta latse wayar tare da lalubo wayar suraj karo na farko a rayuwarta, sai dai har ya kaste suraj be dauka ba, yana ganin kiran yaqi dauka, Bilkisu ta kalli Agogo 6 saura na yamma, lokacin dawowan Suraj yayi, kar wannan shegen umar din ya shigo ciki suraj ya dawo ya ganshi ya mata mummunar fahimta, da sauri ta shiga dakih ta fita wajen gidan bayan ta sanya hijabi. Zaune ta ganshi kan mota, gabanta ya fadi, yaushe ya Suraj ya dawo? Da sauri ta qarasa ginshi, yasuraj, dama dama wanih ne yake ta damuna, yanzu wai yace yazo nan gidan, shine shi-- Sshhh Bilkisu, suraj ya katseta, theres noone here just me, duba kiga, sai a lokacin ta kalli unguwar ba kowa kamar anyi shara, ba kowa, suraj ya diro kan motar, tace ya Suraj sunanshi Umar, wlh he's bin disturbing my life, suraj ya riqo hannunta yace Bilkisu, look at me, ta dago ta kalleshi, yace Do u love him? Dont lie to me, murya na rawa tace Yes i do, but its u m married to, i have no intentions of cheating on you pls believe me, ya qara riqe hannuwanta gam, fuskarsa dauke da murmushi, yace listen to me Bilkisu, Ni neh Umar Z, ni ne muke chatting dake tun tafiar Islah, Na tsaya a dubai ne, anan muka fara chatting, everything data happened was All me, Tsananin mamaki ya lulube Bilkisu, zuciyarta ta shiga zafih, hawaye suka wankr mata fuska, ta daga hannu ta kamtse Suraj da marih, how could u do dis to me? Ta juya ta shige gida da gudu..
3 hrs · Public
4⃣5⃣ 🏡Gidan Gandu🏠 by 💕Biebee Isa💕
Bayanta ya bi da sauri, yana kwala mata kirah banza tayi dashi, kichin ta shige inda take ji qaurin abincinta, ta ma manta ta bar abu a wuta, da sauri ta kashe gas din, ta shiga kwasar Abinci, Suraj yazo ta bayanta ya na mata magana, Bilkisu kiyi haquri mana, this is d only way i cud think of, i want u to love me like d way i do, ta juyo da sauri tana kallonshi, yace yes Bilkisu ina sonki, son da ban ta ba yi ma ko wacce mace ba, ana da ina tunanin Nayi so, a yanzu kuwa nagane a baya ba so nayi ba, Hauka nayi, yanzu kuwa ke nake so, Shisa na bullo ta haka, don ina tsoron rabuwa dake, don a ganina kin tsaneni, duk abunda na fada a matsayin Umar gaskia ne, ban miki karya a kan komai ba, duk abinda na fada miki a chat haka yake a zahiri, Fargaba na daya, kullum shina ke tarrabi, ina tsoron ki amince ma Umar, ina ta gudu kar ki fada halakan da wasu matan auren ke fadawa, cikin masifa tace ka yaudareni, i am not perfect but my parent raised me well, ina da tarbiya daidai gwargwado, na san haqain aure bazan ci amanar aure ba duk da ba na sonka, amma kasan zuciya bata da kashi, da a ce na amince fah? Ni zaka ga laifi, yayu saurin cewa i baki amince ba Alhamdulilah, you have a good heart, ki yafe mun ki maido son da kikewa Umar ki dawo dashi kan Suraj, duk da kece ba ki gane ba, Da Suraj da Umar duk suna nane, karki manta Sunana Suraj Umar Z. Bilkisu ta fashe da wani kukan, kaci amanata, ka yaudareni, u were fooling me all dis while, u were-- da sauri ya zura harshensa cikin bakinta, ya shiga bata hot kiss, tayi tayi ta tureshi ta kwaci kanta, amma ta kasa, sai da ya ga tayi laqwas kafin ya saketa dan kanshi ya kalleta idonta a runtse yace Bilkisu I was just testing you nd Alhamdulilah u've passed uo test, zan baki lokaci kiyi tunani, ki gano cewa i mean u no harm, kuma nine Masoyinki na gaskia. Ya fita daga kichin din, a sannan nan ne naurar aiki ya dawo jikinta, abunda ya hadata da YaSuraj ya dawo mata, ta sa yatsarta kan lips dinta tan shafawa, tare da fadin what just happened??
Bauchi
Amira look what i bought, ta kauda kai, ya juyo da ita haba Amirah, kalla fa, tickets ne xamuje Makka muyi Umrah ni da wifey na, nd za mu je 2countries of ur choice for our honeymoom, ya qarashe fadin haka tare da daga girarsa, ta tabe bakih ta miqe tace nifa ba inda zani, Ya fincikota ta fado jikinsa, ya matse ta, murya kasakasa me kama da rada yace haba lil sis meerah, nine fa bigbrosamir dinki, ko me namiki ai yaci ace kin yafe mun, Uhm? Ya mata peck a goshi, ya qara wani a kan hancinta, ya sake mata wani a gefen neck dinta, jikin Amira ya hau kyarma, ganin bigbro dinta na neman wuce gona da iri ya sa ta cewa fine, i will come with u, ya sake murmushi, yace dats my lilsis, i love u kinji? Ta kauda kai, yace ko bakiji ba? Da sauri tace naji wlh, yayi daria ya dagata yace me tsoro kawai...
Kaduna
Fitowar ta wanka kenan Ta tsaya a bakin sif dinta, tana tunanin kayan da zata sa, ita dai yau ba zata sa wani manyan kaya ba, idonta ya kai kan wasu riguna da Mummy bon ta siyo mata da taje dubai, a cewarta wai ta dinga ma Jawad kwalliya, tunda ta jefa rigar cikin wordrob ba ta qara waiwayansa ba sai yau, ta daga rigar chapdijam, daya ta daga, wannan riga haka, rigar ta hadu iya haduwa, saidai kirjin budadde ne, kuma iyakatar guiwa, kawai sai ta ga tana son sa rigar, tunda ba kowa gidan bari kawai ta sa, ta sa rigar nan ta kalli kanta, woooooww, wallahi nayi kyau kamar wata ba indiya, ta gyara gashinta ta yi dan kwalliya, ta fita parlor, Wayarta ta jona a AUX ta qure volume ta sa waqar Falguni, ta shiga rawa a hankali, Thats wat happens wen u are home alone tace a ranta..
Cikin barcinshi yaji Kida na tashi samasama, da sauri ya miqe, kanshi ya shiga sarawa sakamakkon kidan da yakeji, alamu a parlorn gidansa ne, waye ya sa Waqan nan? A gajiye yake, yana son ya samu barcinnan, be dade da shigowa kasar ba, daga Amsterdan inda yaje Workshop, yafi kwana 3 beyi bacci ba, burinshi ya samu hutu, shi yasa yana dawowa gidan da misalin qarfe 7 na safe ya shige dakihnsa don hutawa, amma ga wani kidih na son hanashi bacci, a zucciye ya tashi ya yi hanyar parlorn.
Baki bude ya tsaya kallon halitar da ke rawa tsakaninta da Allah, Rawa take cikin kwanciyar hankali, kallo daya za kai mata kasan cewa kyakyawa ce, rigar da ta sa yayi mugun birgeshi, hannayenshi ya nade ya na kallonta, karo na farko kenan da Jawad ya tsaya kallon Fadila, ji yayi wani abu na fizgarsa, wani abu yakeji game da ita, haka kurum jikinta ya bata ana kallonta, da sauri ta waiga suka hada Ido, daskarewa tayi, yaushe ya dawo? Tambayar da ta ma kanta kenan, sai kuna taji kunyar shigarta bayan ta lura da mayataccen kallon da Yajawad ke binta dashi, Jawad ya dawo hayaccinsa, da sauri ya murtuke fuska don kar yarinyan nan ta raina shi, ya shiga borin kunya, yaje ya kashe socket din, ya nufo ta gadan gadan, ya ce keee uban meyasa xakicika min kunne da waqah, baki san ina sonyi bacci bane? Ta murguda bakih tace wa ma ya san ka dawo? Haka kurum yaji murgudenta ya mai kyau, ya kamo ta, tare da matse bakinta wa kike murguda ma baki? Ta saki qara waiyo bakina, yace kika qara sai na cire bakin, ta qara murguda mai baki, haan mutum da bakinsa? Ina ruwanka da ni? Ya qara kamo bakin da hannunsa tare da matsewa, yace kina qaryar rashin kunya ne, ni tsaranki ne? Don kin ga na sa miki ido shine kike min abubuwan da kika ga dama koh? Ya qara matse bakin, Ihu takeyi amma ba aji sbd ya matse mata bakin da qarfih, ya dan sasauto riqon da ya mata sakamakon idonshi da ya sauka kan kirjinta, ya shagala da kallonta, ita ko da sauri ta tureshi tayi cikin dakinta, shiko ya dadi kan kujera yana maida numfashi, haushi kansa ya fara ji, zuciyarsa ke tmbynshi meye haka? What jus happened? Kar ka ba yarinyar nan chance din raina ka. Ya miqe ya yi dakinsa yana me sakin tsakih me qarfih..
3 hrs · Public
More
4⃣6⃣ 🏡 Gidan Gandu 🏠by 💕Biebee Isa💕
Zubewa tayi kan gado tana maida numfashi, lokaci guda taji ta tsani wannan rigar, ta tuna abun da ya shiga tsakanin ta da Ya Jawad, wayarta ta dauko. Ta latso Amal, ta na dauka ko gaisuwa babu, tace kizo ki amshi yan iskan rigunan da kika kawo mun, bana so wlh, Sai da Amal taci dariarta sosai kana tace me sukayi halan? Ta kwashe komai ta gaya mata, Amal ta ska wani dariar, tace lallai kam jawad ya fara dawowa hanya, karki damu ina nan zuwa da wasu kayan, dole muke qara haukatar da Jawad, Takaici ya sa fadila kashe wayar tana bambamin masifa...
Abuja
Ringing Uku ya dauki wayar, ya duba Samir ne ke kiran, ya kalli patient din da ke zaune gaban desk dinshi yace just a minute pls, ya dauki wayar tare da fadin Hello Sam, Samir yace hey Zaid, ya ne? Ya iyali? Yace lfy lao ya aiki? Yace wlh fine, had to dump it tho, Zaid yace Meyasa? Samir yace Zamuje honeymoon neh da madam, ya fada tare da kallon Amirar da tayi kanar bata jishi ba, Zaid ya jinjina kai, lallai abun naka azimun, har aiki ka ajiye don Amira? Samir yace har abunda yafi aiki zan ajiye takan Lilsiswifey nah, Zaid yace daniska Sam ka zabure, yace va laifi na bane, So ne, yanzu dai ba wannan ba, Yimin texting adireshin gidanka ga mu a Abuja, don Gobe jirgin mu zai tashi, Gashi lilsis tace ba zata kwana a hotel ba ita dole sai gun Maysah, Zaid yace oryt ni dai ina Asibiti i will be closing by 2, but i will text u d address, ok bro, sukayi Sallama, nan take Zaid ya tura ma Samir Address din gidanshi. Samir ya nufa Gwarinpa basu sha wahalan gane gidan ba, Hannun Samir maqale da na Amira suka nufa cikin gidan bayan Maigadi ya tabbatar mai nan ne gidan Dr Zailani, Knocking sukayi a parlorn, Maysah tafito cikin sanyinta ta bude kofahn ihu suka sake me qarfih tare da qanqame junansu, Samir yace oh ni zaku kashe min kunne, Maysah tace Yasamir sannu da zuwa, lallai u suprised me, ba waya ai da na shirya tarabnku, suka shigo suka zuve a gado, ta gaida Yasamir, ya amsa tace Yazayd din na gurin aiki sai 3yake dawowa, yea dont worry munyi waya, shi ya min kwatance ai, ta miqe tace bari a kawo abinci, ya miqe yace noo nidai ga amanar baby na dai, Idan Zayd ya dawo Qila naxo, idan kuma ba tym sai gobe idan zamu wuce, Maysah tace tohm Ya Samir, tafiya zakuyi halan? Yace Honeymoon zamu ko lilsismeerana? Ta kauda kai, Maysah kuwa ta shiga tafi da kyau yayanah, yace yauwa qanwata, ki lallaba min lilsiswifey nah, tana fushi dani, Maysah tace ai ta yafe maka ma ta gama, yauwa bari na dan shiga garih, ya matso saitin Amira ya bata light peck a kumatu, yana fadin take care, Maysah ce ta rakashi har qofa, kafin ta dawo gun Amirah, kee whatd dat for? Sai shan qamshi kike kina shashare yasamir, me ya mikine?Amira tace ke kyaleshi, sai ynz ya mato kaina, da har kuka fa nake mishi don ya kulani amma ko a jikinshi, ynz kuwa lokacina ne da zan rama ta kwashe komi ta gaya mata, Maysah tace lallai Amira har yau kina da wauta, wallahi garin jan ajin ki zai zo ya tsinke ku koma gidan jiya, Mazan yanzu sai ana lallabasu, tunda har ya gane laifinshi ya kuma bada haquri ai sai ki bada kai bori ya hau, cikin mu 6 wa kika ga mijinshi na mai yanda Yasamir ke miki?Think, this is ur opportunity, Amira ta jinjina kai, tace toh shkn sis, kuma Allah ya karkato zuciyoyin mazajenku kanku, tace Amin, Wayar Maysah tayi qara, ta dauka ta duba Fati tahir ta gani, ta dauka hello guntuwa ya akayi, a bangaren fati tahir tace ke wallahi kizo skul, gashi nan Xaks yayi fixing lectures,nan da 30 mins kinsan halinsa sarai, maysah tace Oh Allah, toh gani nan zuwa, ta kashe tana cewa sis, zuwa skul ya kamani, wani lecturer ne yayi fixing lectures yanzu nd i have to go, Amira tace dont worry ai ina nan, yauwa sis make ur sef at home, akwai Abinci a kichin, tayi hanyar dakih don shiryawa. Maman diyya ce ta turo kofah tana yatsina, ta kalli Amirar da kallo daya ta mata ta watsar, maman diyya tace kee, wacece wannan? Maysah da murmushi tace kanwata ce, maman diyya ta tabe bakih, tace mekika dafa? Maysah tace jollof rice ne, ta yatsina fuska tace ki dafa min doya ki daka min sakwara, ni ba zan ci shinkafan nan ba, Maysab tace Mummy pls, lectures xanih, i need to attend it, Maman diyya ta wurga mata harara tace zakiyi ko ba zakiyi ba? Maysah tace kiyi haquri zanyi, Amira da ta zuba musu ido ta miqe tace yi tafianki Maysah, lemmie handle dis, Maman diyya tace keee, meye haka? Amira tayi murmushi tace Mummy lectures zataje, kar ki damu ni zan miki sakwara, da egusi kikeso ko? Tace eh, karki damu, Maysah muje ki nuna min kayan amfanin, Maysah baki bude take kallon Amira, mamakinta ya rufeta, Amirar ce tayi sannyi haka? Lallai kam aure ya chanza Amira, tace ok sis muje kichin din, maman diyya tace ki min sauri 30 mins na baki, yunwa nakeji, Amira tace karki damu Mummy, 15mins yayi yawa, Suka shiga kichin ta nuna mata komai, a gurguje Maysah ta shige dakih ta fito da jakka ta kalli Amira tace Sisi na tafi, thank u so much u really saved my ass, Amira tace dont mention, jus take care and take ur time kinji, oryt bye..
Amira ta shige dakin da Maysah ta fito, ta rage kayan jinkinta ta dane gado ta bararraje ta shiga sharar bacci.
Maman Baddiya ta ji shiru, ta kalli agogo karfe 3:45, har an fara kiraye kirayen sallah laasar, ita da tace a mata sakwara tun kafin qarfe daya, Har ynz shiru takeji, ko alamun daka bata ji ba, ta miqe dai ta fita parlorn, ta kalli Dinning, kulolin dazu ne, ba ta yi qasa a guuwa ba ta qarasa ta bude kular, jollof rice din da Maysah ta girka ne, tayi tsaki ta nufa kicin, ba alamun an fera doya balle an daka, ta gama dube dubenta bata ga wani abu me kama da sakwara ba, ran ta yayi mutuqar baci, ta fita kamar zata tashi sama, ta banka dakin Maysah, Amira ta gani kwance ta na sharar bacci, ta matsa gadon ta daka ma mata duka a baya ke don kutumar ubanki waye tsaranki?ni zakiyi wa bariki, Amira ta tashi a firgice tana mustsutsuka ido, tace lafiya? Nace don ubanki ina sakwarar da kika ce zaki man? Ke bakiyi min ba kin hana a yi min, idon amira ya qeqeshe, ta kalli Maman badiyya tace ke dai banza ce wlh, harbkin yarda xan miki sakwara? Yo uban waye bawanki da zakisa aiki? In ba zaki ci abin da aka girka ba ki barshi, ke in banda abun kunya kinzo ki tare gidan diyarki har kina sa Matar gida aiki, wallahi Maysah kika samu, Ki gode ma Ubangiji da ba nice matar Zaid ba, da sai na shayar dake madarar mamaki. Baki bude maman diyya take kallon Amira, ba ta taba zaton zata iya gaya mata magana haka ba, ta zata itama kamar Maysar take, ta ma tsorata da alamuran Amira, yarinya qarama ta ke gaya mata magana haka? Ai ko yau zataci uban yarinyar nan, sai ta saukar mata da duk abunda ke kanta, tace ke yau sai naci Uban Babanki, amira ta kalleta tace Uban babana? Tsoho kenan? Maman diyya tace shifa shege Maye, ai muna da labarin Musbahu Zailani bokan zaure ne, shege tsohon banza, yau sai naga uban da ya tsaya miki, Don uban-- ba ta qarashe ashar din ba Amira ta daddage ta kamtse maman badiyya da mari, bata gama tunanin ko marinta akayi bat ta qara jin wani marin, ta dago kai ta kalli Amira, kika mareni? Ta ko qara mata wanih, ta dafe kuncinta ta sake ihu waiyo na shiga uku tace jamaa ku taimakeni jikan Mayu sun kamani, jikar Zailani, Amira ta daga hannu zata qara mata wani marin Maysah ta shigo da gudu...
3 hrs · Public
More
4⃣7⃣ 🏡Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕
Ganin Maysah be hana Amira kara ma maman badiyya wani marin ba tare da nuna ta da yatsa, tace ki ka qara cewa tak sai na lakada miki dukan tsiya, da sauri maman Badiyya ta riqe bakinta don ta fi danganta Amira da wadda ke aiki da Aljannu, amma in banda Aljannu wacece zata kalli girmanta ta daga hannu ta mara har kala 5? Maysah da sauri ta janye Amira tace Haba Amira me-- shut d hell up amira ta katseta, tace ba a haifi uban da zai zagih tsoho gabana ban mareshi ba wlh, duk tsufan ka, ko da gemun ka na jan kasa ina iya kamtse ka da marih, ko waye, ni gwara a zage baba da a zage tsohonmu, sum sum maman maysah ta ja tsamin jikinta ta bar dakin kar ta qara jin wasu yatsu biyar a kumatunta, Maysah tace yau na bonu! Amira kin san me kika ja min? Allah kadai ya san me zai faru idan diyarta ta dawo, amma Meerah be kamata ba-- Amira tace Maysah i told u to shutup dint i? Wai ke me ke damunki? Kina gidan mijinki amma baki da maraba da er aiki, ke baiwarsu ce? kin tsaya suna juya ki, toh wlh idan zaki kwatar ma kanki 'yanci ki kwatar, in ko ba haka ba, duk sharar da suka dibo kanki zasu zubar tana kaiwa nan ta shige toilet don watsa ruwa.
Tare suke da Alh. Haladu a wani hotel sun gama aikata sabo, qarar wayarta taji, ganin mamarta ne ya sa ta sake tsaki ta dauka, hello mama, ya akayi ne? Ji tayi maman na kuka, Badiyya ba lafiya, yanzu na sha tagwayen mari kala 3, badiyya ta zaburo, wani dan abun uban ya mareh ki? Nidai ki dawo, ko nayi tafiata, Badoyya ta miqe a gurguje tace ma Alhaji haladu zata je gida Emergency ne, be bi baasi ba ya ciro bandir din 1000 yace zasu yi waya.
A sittin ta shigo gidan, tayi dakin mamar, Zaune ta sameta zaune kan gado Fuska ya suntume ya kumbura, fuskar tayi jaaa, Mama me ya sameki? Waya miki rauni a fuska? Tace Wata ce ta zo gurin Rumaisah, Badiyya ta shirga uban ashar tare da kwabe dankwalin kanta ta ci dan mara, tayi hanyar fita, tace kul badiyyah, Wlh yarinyar nan ba ita kadai bace, Tare take da Aljannu, mama ba Aljannu ba Allah ya sa Almatsutsai ne sai na ga uban da ya tsaya musu a gari Abuja, ta fita tayi dakin Maysah, Amira na zaune tana shafa, Maysah na Sallah, ta sa kai tana sujjada Badiyya ta fincikota, ta maqureta, Amira tace ke karuwa, bakisan darajar Sallah bane da ba zaki iya bari ta idar ba ki mata ko me zaki mata? Au na manta fa ke jahila ce, Badiyya ta juyo ta kalli Amira da bata fasa shafar hodan da takeyi ba, tsaf ta ganeta, yarinyar da ta taba mata rashin kunya ne wata rana da taje neman Zaid a Maid. Amira ta rufe powdern ta ajiye, tace ni kike nema, ba Maysah ba don kamar nice na mari uwarkih kamae so 5 ne ko 6 i cany remember dai? Ta kalli maman Badiyya da ta labe a bakin kofah ta kasa shigowa tace, Mummy mari nawa ma na miki? Badiyya ta sake Maysah, tace Amira kike ko uban wa? Karon mu na farko na qyaleki, wannan kuwa zan nuna miki ni ba saar ki bace balle kuwa uwata, ta matso gadan gadan ta nufi Amirah, Maysah tayi saurin riketa Aunty Badiyya kiyi haquri, laifina ne, wlh laifina neh, ni zaki hukunta, Amira cikin fushi tace Maysah kinci ubanki, ki kyaleta muga abun da zata yi mana? Da alamu tsautsauyi yake niyyar kawota kusa danih, jin haka yasa maman badiyya zuwa ta kama diyyarta, badiyya ya isa, na gaya miki yarinyar nan ba ita kadai bace, ni wlh na yafe, Allah kadai yasan abun da zata miki, Nan Badiyya ta tirje ta shiga bambami da ihu da masifa, mamar ta riqeta gam.
Tunda suka shigo gidan suka san cewa va lafia, da sauri Zayd yayi parking ya fito, Samir din ma parking din yayi suka shiga da sauri, Dakihn Maysah suka nufa, ganin maman Badiyya riqe da ita ta na tirjejen a barta ta bige Amira ya sa Zaid zuwa ya janye Badiyya, Shima Samir ya janye Amira tare da rungumeta, a hankali take sakar da ajiyar zuciya, Maysah kuwa sai kuka take tayi, Zaid ya ce Sam matarka is unstable, ka kwasheta ku tafi, kaga yanda ta maida min gida? Samir ya kalli zayd ya wurga mai Harara, yace ka dai san waye unstable not my wife, ya dago Amira dake kwance a kan kirjinsa yace meerah na me ya faru? Ta dago ta kalli Zaid tace Kalli fuskar sirikar ka, ba gardama ya juya ya kalli fuskan maman Badiyya da ya kumbure, yace subhanAllah Mummy me ya sameki? Badiyya tayi caraf tace marinta fa tayi Zaid, Zaid yace Mari?? Amira tace ba daya ba, marirrika ta sha, kuma ko yanzu ta sake yin abun da tayi zata samu fiye da haka, Ran Zaid ya baci, ya kalli Maysah cikin tsawa yace ke kika sata koh? Kuka ta keyi ta kasa cewa komai, ya kalli Samir yace Sam ka ga abun da nake ce ma ko? Ka hukunta matarka ko ni wlh na hukunta ta, ba zan dauki raini , ba zan yarda a rai na min Iyalina ba, don rashin kunya ki daga hannu ki mari someone that is old enuf to b ur mother? Samir yace Easy mana zaid, ai ba mu ji meye dalilinta ba, ya fuskanci Amira yace lilsis tell me what happened? Cikin rashin tsoro ta warware musu komai tun bayan tafian samir har zuwa yanzu. Ran Zaid yayi mumunan baci, fita yayi daga dakin ya fada dakinshi, Ran Samir ya baci ya kalli Maman Badiyya yace ki gode ma Allah ba a gabana kika zage tsoho ba, wlh da yanzu kina kwance gadon Asibiti ya kalli matarshi yace lets go ya fita shima. Amira ta kalli maman badiyya tace dis is wat happens wen u mess with Musbahu Zailani ta suri jakkarta ba tare da ta kalli Maysah ba tace mun wuce. Badiyya ta fice daga dakin maman ta bita a baya. Maysah ta zuve kan gadi tana kuka a hankali..
******
Mama me kike tunani da kika zagen musu kaka haka? Kinsan me kikayi kuwa yanzu? Kinsan yanda suke son wannan tsohon? Ai ko mahaifansu ba sa son su kamar yanda sukeson tsohonsu, yanzu shikenan kin ja min, Zaid yayi fushi, Mamar Badiyya ta kalli diyarta tace kiyi haquri, ban ta ba tsammanin abun nan zai juye ya koma haka ba, indai Zaid ne ba matsala yanzun nan ba sai anjima ba zai sauko, ta miqe ta dauko wani turare ta bata tace ta shi ki shafa kije gunsa, ina tabbatar miki da cewa sai yadda kikayi dashi. Badiyya tayi shewa tace woo mummyna shisa nake sonki, ta miqe ta fada toilet don gyara jikinta kafin ta nufa dakin Zaid..
****
Tunda daga kofar dakin ta ke cin karo da kwalba da gwangwanin giya, Hakan ya tabbatar mata da gogan nata ya sha giyarsa yayi tatul, don ta san fushin da ya dauka giya kadai ce zata kwantar mai da hankali, chan kusurwa ta hango shi yana baje, idonshi lumshe amma ba bacci yakeyi ba, tun kan ta qarasa gunsa yaji wani qamshin turare, da sauri ya bude idonsa, Giya ce ta fara gaya mai karya, ganin badiyya yayi ta rikide ta koma mai Maysah, da sauri ya fincikota ta fada jikinshi, ya shiga sarrafata, badiyya abin nema ya samu ta biye mai suka lulu duniyar maaurata.
What?? Alhaji Haladu yace cikin kidima, Jawad aka ba contract din da nake expecting? PA dinsa yace eh yallabai, yanzu ma yazo refinery yayi signing contract din, yace zai tafi in 10days time, Zufa ya shiga tsatsafo ma Alhaji Haladu, Yaron nan na so ya shige gaba na? PA yace ai Alhaji daga sama ne abun, ni ya kamata naje Amsterdan, aka ce na barshi ya za a ban contract din Niger-Delta na barshi ya tafi don na san zan fi samu a na Niger Delta din, yanzu kuma sai ace shi zaije to wlh ba zai rayu ya ga wannan ranar tafian nashi ba, wlh ba zan barshi ya dakushe min tauraruwata ba, yaro kankani ya shige gabana ba. Wayar sa ya lalubo Gambo Kisa Gayu, ringing biyu ya dauka hello ya Alhaj, be tsaya sauraron kirarin da ya saba mai ba yace kana ina Kisa Gayu? Wlh gani Damaturu ina wani operation ne, kayi maza ka zo kaduna Gobe Goben nan, kaii Alhaj anya zan iya zuwa? Gaskia ina wani dan aiki ne zuwa jibi ko gata zan diro,Ni ka dawo gobe ko nawa ne zan biya ka, yace Alhaj kayi haquri ka bari har na dawo, idan kuwa emergency ne sai na turo ma yarana, Aa Kisa gayu na fi yarda da aikinka, na baka nan da kwana 3, yace lafia lao lokacin na gama komai anan, me kakeso ayi ne? Yace Akwai wani yaro da ya shige hancina ya qudundune, yaron da ya hanani rawan gaban hantsi, wai shi Jawad Zailani so nake a min maganinshi, Yallabai me kake so a mai me? Yace so nake a kasheshi..
3 hrs · Public
4⃣8⃣ Gidan Gandu by 💕Biebee Isa💕
Tohm zanyi qoqarin dawowa da wuri, idan ban samu damar dawowa ba, zan turo ma yarana, suma kwararru ne, Alhaji Haladu yace banso a samu matsala, yace Kar Ka damu Alhaji, sai dai kaji daga gareni, a haka sukayi Sallama, Alhaji Haladu ya tattara kayanshi ya wuce Kaduna..
Lagos
Zuciyarta ta amince da Shawarar da ta ba kanta, inda zuciyar k ce mata, ta manta komai da ya faru a baya, ta rungumi mijinta, tunda be da wani aibu, hasalima shi ke biye da ita, ita kuma na wulaqantashi, ya kamata ta zage damtse wurin kyautata wa mijinta, tunda har ya kai ga shaawar sake wani auren, kuma har ga Allah kyautata mata da yakeyi zuciyarta ta kamu da sonshi, son da ba ta tunanin ta taba ma wani mahaluki irinshi. A yau tayi niyyar faranta Ran Mijinta Zayyad, Yau zata Roke shi gafarar abubuwan da ta mishi a baya, da sauri ta tashi ta shiga kicin don daura abinci, Watanni takwas kenan da zuwanta legas ba ta taba yin abinci don Zayyad ba, yau kuwa gashi ta shiga shirya mai kayan dadi, sai da ta gama fried rice dinta da fried plantain, kafin ta yi pepper chicken dinta, wurin karfe 1:30 ta shirya komai kan dining, da sauri ta fada toilet don yin wanka, ba jimawa ta fito, ta shirya cikin wasu riga da skirt na atamfar hollan da ya yi matuqar yi mata kyau, rabon da ta shafa kwalli a idonta har ta manta, yau ko Hanifa har da kwalliya, ta feshe jikinta da turarruka masu kamshi, ta kashe daurinta, hanifa tayi kyau har ta gaji, kallo daya zaka mata kasan tana cikin nishadi. Karfe 2:30 taji horn din shi, da sauri ta leqa window, shi din ne, sai yanzu ta qare mai kallo, Zayyad kyakyawa ne gashi da kyan zuciya, ita kanta ta san YaZayyad yayi haquri da ita, shisa yau takeson faranta mai, don runtse ido zatayi ta rungumeshi, da sauri ta fita daga dakin, ta zo fitowa kenan santsin tiles ya kwasheta da sulbe ta fadi ta gurde kafa, Azaba ya hana ta sake ihu, amma hawaye tuni ya fara sunturi. Shigowa yayi da Sallama, idonsa ya sauka kan hanifa, da sauri ya qarisa gunta ya na tambayan lafia? Kasa magana tayi, hawaye kawai take iya, fadiwa kikayi? Sannu kinji tashi, ya danyi yunqurin ta da ta, ta saki ihu me qarfi, Yaya kafana, Me ya samu kafan? Ya kalli Kafar ya ga ya dan jirkice, nan ya fara salati ya rude iya rudewa, sabarta yayi kamar wata baby ya kaita daki ya shimfide kan gado, yace sannu, bari najeh na siyo Robb ko Deep heat na shafa miki kinji? Ta kasa cewa komai, da gudu ya fita, ba ayi minti 15 ba sai gashi ya dawo, da Magunguba cikin leda, Ya dibo maganin zafin ya shiga shafa mata a qafa a hankali, ita kuwa sai ihun kuka takeyi don Zafin da takeji, sai da ya shafe mata kafa da robb kafin ya ballo Ibrufen pain killer da wani sleeping pills, ya bata ta sha, sannan ya shiga shafa mata kai yana cewa sannu kinji, try nd have some sleep, cikin kuka take cewa Yaya Abincin kan Dinning, da sauri ya kalleta, mamaki ya rufeshi, amma har a ranshi ya ji dadi, yau shine da abinci?Lallai kam Allah na gode ma, yace karki damu Hanee, zanci but sai kinyi bacci, bata tsaida kukanta ba har bacci ya kwasheta..
Kano
Tunda ta gano gaskia game da YaSuraj ta kulle kanta ta shiga tunani, ta fuskanci son da yake mata gaskia ne, ita kuma ta aminta da zuwa yanzu ta kamu da sonshi, Toh meyasa ba xata yafe mishi dab qaramin laifin da ya mata ba? Ta rungumi mijinta wanda take ma Zazzafan So ba tare da saninta ba? Toh dai lokaci yayi da bygones will be bygones, zata rungumi mijinta zabin Allah a gareta, fatan ta Allah ya kara Hada kansu, ta tashi ta bude kofar ta ta fita, karfe 12 da rabi, ta san Yasuraj ya dade gurin aiki, da ya kan dawo cin Abinci, amma tun bayan abin da ya faru ya daina dawowa, don ya san ko ya dawo ba zai ganta ba saboda kulle qofarta da tayi, shikuma be son ya takura mata, ya fi so ta sauko don kanta. Bilkisu ta shiga kichin ta hada abincinta mai rai da lafiya, ta dawo ta ta sake wanka ta yi kwalliya ta dawo parlo ta kunna tv, binibini sai ta kalli agogo. Kamar daga sama sai gashi ya dawo daukan wasu files da yake da buqatansu a gurin aiki emeegency, yayi mamakin ganinta zaune a parlor, suna hada ido ta kauda kanta, Tace Sannu da Zuwa, murmushi Yayi zuciyarshi cike da jin dadi yace Yauwa Billy nah, erhm daman na yi mantuwa ne, bari nashiga na dauko, be jira amsarta ba ya shiga daki dauko files din, sai gashi ya fito, Billy bari na tafi sai na dawo, ta dago kai ta kalleshi, tare da marairaicewa tace ga fa abincinka nan fa? Wani dadi ya mamaye zuciyar Suraj, yace tohm sakko min dashi nan, ta miqe a yangace ta nufa dinning din ta kwaso kayan ta zo ta zube gabanshi, ta shiga zuba mishi fried spagetti da vegies sauce, ta tsiyaya mai lemu a cup, ta miqe zata tafi yayi saurin riqo hannunta, ta zuba mai idanuwanta, ya ce sorry i cant eat alone, ta ce sorry m not hungry, yace ai baki isa ba, ya zaunar da ita kasa kusa dashi, yace cikin ki beyi kama da wanda yaci abinci ba, bata sonyi mai musu sai tyi shiru, haka ya dinga ci ya na bata a bakih, tun tana kunya har ta daina ta xage tana ci, sai da suka ci plate 2suka sha lemunsu ta tashi ta kwashe kayan, binta yayi kicin, ya rungumota yace Billy m so sorry for-- ta katse shi ta hanyar sa yatsunta biyu kan bakinshi tace yaya, let bygones be bygones, lets forget d last nd focus on d future, ya ji dadi sosai, yace Billy please let me teach u how to love me, tace no need, coz i already love u, Ohmy God, i love u so much Billy, nd u wont regret loving me, Dagata sama yayi kamar baby ya nufa dakinsa da ita, zuciyarta ta shiga dukan 3 uku, a tsorace tace Yaya, files dinka, yace shhh forget d files i dont need dem again.
Abuja
Zaid din ya tafi aiki kuma kinsan be dawowa Sai 3 nd dis is just 1, kuma kinsan ki yana nan he cant do anything, he's under my control, so muje na fanshe bakin cikin da wannan shegiyar Amirar ta kunsa min jiya kan Rumaisah, Badiyya ce ke maganar nan, Mamar tace wlh Tunda nake ba a taba min cin fuska irin na jiya ba, na tsorata da yarinyan nan, da qyar in ba ta aiki da mutanen boye, amma tunda Annobar ta tafi muje mu ci uban Rumaisahn, Suka fita da ga dakin suka nufa na Maysah, tana kwance tana barci sbd yau ba lectures, Jin wayar redio tayi a jikinta, da sauri ta miqe tana salati, ganin Badiyya da mamanta tsaye ko wannensu riqe da Wayar redio, hantar cikinta suka kada, Muryar badiyya taji yau ina me cetonki? Tace me namuku Aunty? Tambaya kike? Suka shiga lafta mata a jiki, ta saki ihu tana kuka, dukkanta suke kamar Allah ya aiko su, abunku da mutun fari tuni suka farfasa mata jiki, hakan be sa sun daina ba, illah qara tsaula mata da sukeyi, Da qarfii sukaji ance Badiyyyyaaa, chak suka tsaya, suka waiga don tavbatar da abun da kunnensu ya jiye musu, Zaid ne tsaye bakin kofa, idanuwansa sun rikide sun koma jaaa, Gaban badiyya ya fadi, bata taba ganin fushi kwance a idon zayd kamar yau ba, ta tsorata da yanayinshi, a hankali ya tako har inda Maysah ke kwance ta na kuka, ya dagota, ya share mata hawaye tare da girgiza mata kai, alamun tayi shiru, hannunta ya riqe gam ya yi gaba tana biye dashi a baya suka bar dakin.. Fans me kuke ganin zayd zai ma badiyya da uwarta?
_Bibilicious Biebee_
0 comments:
Post a Comment