Misalin karfe 11 na ranan Yau
Xaune yake yana diba wasu patients, yaji kanshi ya mai nauyi kamar zai rabe biyu, xafi sosai, sai da yayi excusing kanshi yaje common room da kyar, kan ya kai kusan minti 30 yana ciwo, kafin ya ji ciwon kan ya dauke dif, daidai nan ya shiga tariyo abubuwan da suka wakana tsakaninshi da badiyya tun yana london haduwarsu da komai, har zuwa yau, kanshi ya dafe ya na maimaita Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Wacece Na aura? Badiyya? Karuwa? Allah na kasance Mashayi amma ban taba aikata Zina ba, Allah na tuba, meyasa na Auri Mazinaciyya? Me ya kaini har na kaiga auren badiyya? Na yi wa Tsohona gardaman, na ruguza mai Akidarsa, Na mai rashin kunya, na juya wa Zabinsa baya, Oh Allah, Tsanar Badiyya ce danqare a zuciyarsa, tuna abunda ya faru tsakanin matar Sam da uwar Badiyya ya shiga dawo mai jiya, Yau kam sai mamar badiyya ta bar mai gida, ita kuwa bazai kara barin ta tafi ta ko nan da kofa ba balle taje tayi akuyancinta ta kwaso cuta ta shafa mai shikuma ya shafa ma baiwar Allah Maysah. Da sauri ya fito daga common room ya isa parking lot, ya finciki motarsa yayi gida, kansa dauke da tunani kala kala, isowarsa gida ya ga irin Dukkan da suka yi ma Maysah nan ya qara jin tsanar su dole xai yi maganin su tunda har suka taba Zabin tsohonsu..
Tie din wuyarshi ya fincike, ya bude firij ya dauko kwalbar giyar R2A, ya bude, Maysahn da take lura dashi tayi sauri miqewa tare da riqe mai Hannu tana cewa donAllah yazayd kar ka sha, wani kallon da ya mata ya sata yin lakwas, bata taba ganin yanayinshi a haka ba, Yace kwanta kar kuma ki sake ki fito, haka ta koma ta kwanta, tare da runtse ido, ya daga kwalbar giyar nan ya kwankwadi kayanshi, chan ya fara jinshi a sarararin samaniya, wani murmushi ya sake tare da bude er jakkar laptop dinshi, Chargern laptop din ya dauka ya na hada hanya ya fita daga dakin, dakinsu badiyya ya banka, a tsorace suka dago, dama ynx ta gama shafa turaren nan zataje dakinshi, turaren ya daki hancin zayd, wani irin wari yaji, kanshi ya sara, ya Nufosu kamar Zakihn da ya kwana 2be ci abinci ba, Badiyya ta tsorata, idon zayd a halin yanzu cike yake da fushi, rashin imani, da rashin tausayi, bata gama tunaninba sai jin wani abu me kauri tayi a bayanta, ta gantsare baya kafin ta sake ihu, mamar na cewa hava zayd matark- jin nata a baya ne ya hanata karashe zance da takeyi, ya shiga laftarsu da chargen laptop din kamar Allah ya aikosu, sai da ya dukkan kawo wuqa, sai da ya ga sun rungume juna a qasa sun ma kasa kuka sbd azaba, sai da ya gaji don kanshi kafin ya daina dukkansu, cikin yanayi na maye ya kalli uwar badiyya yace na baki 10mins ki bar min gidana, ke kuma, ba inda zaki, ya hada hanya ya fice dakin ya koma dakinsa ya zube kan Maysah ya fara bacci, da qyar ta janye jikinta daga gareshi tana kuka, cire mai Takalma da socks tayi, ta gyara mai kwanciyar shi, ta koma Gefe tana kallon Zayd, Ya Allah ka shirya Yaya Zaid.
ENGLAND
Asad ya shigo dakin bayan sub mai izinin shigowa, heyy dear, zainee tace hey, Ya kalli Islah yace hello princess, murmushi kawai ta mai, yace hop u guys are prepared for today's Awards? Zaineema tace i wanna come but Islah said we're not coming, so we are not comin. Asas ya marairaice fuska ya matsi kusa da islah ya zauna, yace d time u told me u'r not interested in me, i was so hurt, i felt so bad, nd since den i never talked to u about it, coz i respect ur feelings, i trust u not to hurt my feelings, if u dont want to see me hurt please come, ur presence is needed, yana kaiwa nan ya miqe ya fice daga dakin, Zaineema ta dawo kusa da Islah tare da riqe mata hannu. Islahulkhair meyasa kike haka ne wai? Wannan taron na kasar ce baki daya fa? Duka Universities din ENGLAND ne, kuma anan xaayi balle kice ba kyason tafia me nisa, kar ki manta an gayyaci manyan Celebrities gun taron nan, tun last month ake ta maganar EnglandHighschoolsAwards, Asad na da kirki, tunda har ya kaiga roqon mu muje ai sai muje ko, kuma na san ya riga da ya siyan mana tickets, kuma da tsada, kar yayi asara pls, just dis one time please, ta kalleta tace fine, zamuje shikenan? Yauwa my frnd. Bari na kira Asad na sanar dashi. Kudai kuka sani
*****
7pm
Islahulkhair ta shirya cikin wata doguwar riga milk colour me touches din cofee brown, ta daura dankwalinta brown color, tayi matuqar kyau don har kwalliya zaineema ta mata da qyar, sunyi kyau kamar mene, takalma me tsini ta sa suna jiran Zuwan Asad, Sai ko gashi yashigo da Sallama, sandarewa yayi ganin islah, don ta mai kyau, Zainee tace Asad? Yayi saurin dauje kai, islah tace give me that look again nd i promise u m not coming, ya ce sorry, shall we? Yayi gaba suka bi bayanshi.
suka isa gurin taron, Wurin qato ne, an hallara, wasu daga cikin Manya manyan celevrities wanda ake ji da su a duniya sun hallara, Makarantun Jamio'in kasar England sun hallara. Har an fara gudanar da Awards din, yanda abun yake za a kira Celebrity ta fito ta fadi category din award din, da sunan makarantar da za'a ba da kuma wanda ya chanchanci award din, sai ka tashi kaje ka amshi kyautarka. Haka aka tayi, Su Islah sun duqufa wurin kallo, da an kira sai su taba, amma zuwa yanzu ba su ji ankira makarantarsu ba, Islah ta gaji don anyi nisa da yawa, tace Zainee kin ga har 10 yayi, kice mai yazo ya kaimu gida, Zainee tace pls bari 10:30 yayi. Ji sukayi ance, "Ladies and Gentlemen, to present this award for d category of MOST UNIQUE, Please welcome Justin Bieber nd Nicki Minaj, Rafraf wuri ya hau tafi da ihu, Islah ma ta gyara zama, yau gata ga best artiste dinta JB, JB da Nicki minja suka hau kan stage suna daga ma mutane hannu, Nicki minaj ce ta fara dan surutai kafin JB yace tonyt its not about us, tonyt its about d "Most Unique" d Award for the "Most Unique" goes too.. suka hada bakih shida Nicki Minaj Sukace From CAMBRIDGE ENGLAND, ISLAHULKHAIR ZAILANI, Ihuuu yan CE suka sa don sunsa wacece Islah indeed shes unique, Ihu Zaineema takeyi har da miqewa tsaye, ta kalli Islah da ke zaune ta rafka uban tagumi da alamu bata san wainar da ake tonawa ba, zaineema ta zungureta, tace bakya jine? Islah tace meye? Nan JB ya qara maimaitawa, Islah Ta bude bakih tace what? Zainee ta gyada kai tace go get it, Islah ta kalli Asad ta san aikin shi ne wannan, jiki ba qwarih ta miqe kamar zata fadi qasah tana tafia, idanuwa aka zuba mata ana binta da tafih, har ta zo kan steps din dake gaban hall din, Justin bieber ya sauko daga kan stairs din ya miqa ma Islah hannu, bata san lokacin da ta sake murmushi ta miqa mishi nata hannun ba ya taimaka mata ya hauda it kan matakalar benen da be wuce 10 ba, Nicki minaj ta rungume Islah tare da bata Award dinta, shima JB din rungumetan yayi tare da janta gun Microphone don ta bada speech.
*****
Zaune yake yana shan cofee, ya dinga chanza channel din Tv har ya tsaya kan Channel EE, da alamu awards ake, shi ya zata films Awards ne shisa ya bari, sai da ga baya ya fahinci ashe EHSA akeyi, tsaki yayi ya ce shirme, yazo chanzawa kenan yaji muryan nicki da jb suna kiran Islah, kamar zai chanza sai dai ya tsaya yana kallo ya ga wacece wannan islah, ganin an haskota tana tafia a yangance, gabanshi ya yanke ya fadi, zuciyarshi ya shiga dukkan 3uku, ba abun da ya fi daga mai hankalin irin yadda ya ga JB ya riqo hannunta har da rungumeta. Kanshi na fitarda tiririn Zafih. Ba zato ba tsammani sai gani hawaye yayi a idonsa, a hankali ya ke tambayan kansa shin mafarki nakeyi!!? Nikuma biebee nace kai kuma a suwa danwake a hotel? Wanene wannan Jamaa?
[truncated by WhatsApp]
3 hrs · Public
5⃣0⃣ 🏡Gidan Gandu🏠 💕B👂iebee Isa💕 Tagumi yay hannu bibiyu yana kallon ta Tunani kala kala, haka ya cigaba da kallan ikonAllah cikin bacin rai, Islah ta fara Speech dinta kamar haka "OMG! Standing beside NickiMinaj and Justin bieber is like a dream come true, i never in my widest dream thought of seeing them dis close to me, too many people to thank, Thank U Asad for everything, thanks roomie Zaineema, ily, nd dis Award is for all the Nigerian people studying in Cambridge University, M only their representative, Coz we all are Unique, Naija no dy carry last " Raf raf gurin ya kaure da tafii, ta sake rungume Nicki minaj ynx dai ba ta rungume JB ba, suka matsa gefe tare da kangawa aka dauke su hotuna, a yangancen ta koma mazaunninta, Zaineema ta rungumeta cikin murna, har a ka cigaba daga inda aka dasa.
******
Ajiyar zuciya ya sauke me karfi, tunanin Me takeyi a Cambridge? Its obvious mana, Karatu takeyi, amma ya akayi tsoho ya barta ta zo karatu nan? Don ya san tsoho be barin mata fita waje karatu balle kuma ita da aurenta? Wata zuciyar tace Kasan ko an raba auren? Damm gabanshi ya fadi, da sauri ya ba zuciyarshi amsa, ba a raba, tsoho be raba aure, ya koma ya zauna, amma duk yadda yake tunanin be damu ba karya yake, hankalin shi ya gaza kwanciya, da sauri ya shiga dakin baccinsa ya bude case din shi cinki rashin kwanciyar hankali yake neman MTN sim dinsa, sim din da tunda yazo qasar be sake waiwayanshi ba, ya dauko hannu na rawa ya sa, Contact ya shiga, ya dinga bin lambobin wayansa da ido daya bayan daya, wa zai kira? Wa ya isa ya tunkara da maganar Islah, wani kunyan abun da yayi ya mamaye shi, number bilkisu yayi dialling a dayar wayan, unfortunately wayan kashe take, kamar yayi kuka, da sauri yace bari na kira Samir, ba zai rasa masaniya ba, ai numbern Samir be ma shiga don be ma qasar, ai be isa ya kira suraj ba don kunya. Haka ya dinga bin number en gidan nan duk ba sa shiga, ihu ya sake da qarfi, yanda ya ga dare haka ya ga rana.. Sai wurin asuba bacci ya kwashe shi..
Kaduna
Karfe 8 na Safe ta fito daga dakinta sakamakon kwankwasawar da taji ana mata a kofa, ta fito, direban Jawad ta gani, suka dan gaisa, yace kin shirya koh? Cikin mamaki tace na shirya ina? Yallabai yanzun nan da xaifita yce min na kaiki KASU zaku zana post ume, Kambu fadila tace a ranta, wai me mutumin nan ke nufi da ita ne?Gidan ya kwana, ta tuna wurin 11 sunyi clashing a kichin, amma ya iya furta mata ta shirya zataje post ume ne yake ganin asara? Shine zai aiko mata da me gadi? Haka ya mata na zuwa Maiduguri to lallai ya kaita bango, ba za ta yarda da irin haka ba, ganin idan taqi zuwa PostUme din ta ma kanta ne, daman yadda take son karatu, idan ta ce ba zataje ba karatun ya tafi kenan, sai dai ta daure, tace haka ake zuwa musu post ume din? Yace ai ke credentials dinki kawai xaki dauko, sauran abun buqata yanzu ya miqo minsu a file. Mamaki take yaushe YaJawad ya fara mata processing Makaranta? Chan kuma tayi tsaki, koma meye yau sai an yi ta ta qareh, bata son aiken da yake mata.
Lagos
Mai makon kafa ta warke sai kafa ta kunbure, hanifa taci kuka har ta gaji, da ita da Yazayyad din ba wanda yayi tunanin goce wane, sunyi zaton normal turgude wa ne, haka aka kwana aka yini, Zayyad ko nan da kofar gida ya qi zuwa, ji yake kamar ya dawo da ciwon kafar jikinshi, shi ke mata komai, ya yi abinci ya dauketa ya kaita toilet, ya jirata ya fiddota, Hanifa cikin ranta tace Yana da Kirki, ya dinga shafar mata kai har bacci ya kwasheta, a haka Tsoho ya kira Wayar Zayyad, Ringing daya, ya dauka da sallama, Allah ya ja da ran tsohon mu, Mallam Zayyad, dadi mata ya sa ka shareni na kwana daya, ko ka kira kani ya muka tashi yau? Zayyad ya dan marairaice, Allah ba tsoho haquri, Matarka ce bata lafia, Dadi yaji har ransa, tunda yake kiran jikokinsa wannan ne karo na farko da suka maida mai magana me dadi, a ranshi yace Allah ya sa ciki ne, amma a zahiri sai cewa yayi SubhanAllah, me ya sameta? Wlh jiya ne ta turgude kafa, yau kuma kafar ta kunbure sunntum, SubhanAllah, Ince ka kaita an dubata? Zayyad yace aa tsoho, ina dai shafa mata magani, amma ynz da na kusanto kafar, ta dinga ihu kenan, tsoho cikin damuwa yace Zayyadu ta goce ne, ka kawo min ita yau a diba kafar nan, kafar tayi tsami, cikin damuwa Zayyad yace an gama tsoho, bari naje na ga idan zan samu tickets, yauwa Allah ya sawwaqe, ganin har yanzu bacci takeyi ya sa shi fita siyan tickets kafin ta farka..
Kano
Fitowa sukayi hannun su maqale da juna gwanin ban sha'awa, Kallo daya zaka musu kasan masoya ne masu tsannanin son junansu, sai da ta rako shi gaban mota kafin ta bashi brief case dinshi, tace Allah ya kare min kai Ya suraj, Allah ya bada saa, sosai yaji dadin adduarta ya janyota ya rungume, yace Amin Billy nah, sai da ya bata hot kiss kafin ya ja motarsa ya wuce, ta bi bayanshi da so da kauna, ta koma ciki cike da jindadi.ji tayi wayarta na qara kan dining, da sauri ta qarasa don tunanin ta Ya suraj ne, ko yayi mantuwa, gani number +44 ya tabbatar mata da Islah ce, ta dauka, hello, sabanin Islah taji, ji tayi yace Hello Chuss, Duniya shi kadai ke ce mata chuss, da murna tace Ya'Ammar? Kaine? Kana London ne? Are u ok? Ya Mu'ammar? Dan guntun tsaki yayi yace zan amsa miki tambayoyinki but before den, An raba aure na da Islahulkhair? Tmbyr ta zo mata a bazata, amma taji muryar shi like he's serious, tace aa yaya ba a raba, yace na ganta nan England, ya akayi haka? Ta kwashe komai ta gaya mai, kunya yaji matuqa, yaya gaskia baka kyauta ba, ya marairaice yace U knw u are my only sister u ar d only one dat can help ur bro, pls ina son details din inda take zaune like now, tace now dai? Yace do dis for me pls, tace ok Yaya bari ma duba dakin Yasuraj nagani, don naga wani files me dauke da sunanta, idan babu zan kirata na mata siyasa har sai ta fada mun, yauwa darling sis, remember noone must find out, ko ita, tace kar ka damu yaya, bani minutes i will get back to u. Ta shiga da sauri ta dubo file din, kamar yadda take tsammani hakan yake, duk wasu important informations kan Islah a Cambridge ta samu, harta numbern Room mate dinta akwai a takardun, da sauri ta mai texting, tnx kawai ya mata replying.
Cambridge England
Karfe 9 ya mishi a Cambridge, don bala'e train ya biyo daga london zuwa Cambridge tafian kusan 1hr 30mins, be sha wahala ba gurin gani dakin su Islah, kasancewar yau Saturday, ya fi minti 10 gaban dakin, gabanshi na dukan 3uku, ta ina xai fara? Sai ynz yake tmbyr kanshi me zai ce mata? Sai da yayi shahada kafin ya kwankwasa kofar, zuwa tayi ta bude qofa, sanye take da dan nytgown, Goodmorning? Zaineema ta amsa cike da faraa, how can i help u? Errhm m looking for Islahulkhair, i hop i dint missed d room, ta fadada murmushinta tace and u are??? Oh m Mu'ammar m her--- ya rasa me zaice, uo her wat ta katse shi? Da sauri yace brother, zaineema tace dagaske? Mamaki yayi ta iya hausa yace dagaske kuwa, tace bismillah, ya shigo ya zauna kan kujera, tace ya gida ya su Tsoho da ya suraj? Yayi dariaa, duk kin sansu kenan? Tace eh kaine ba sani ba gaskia, ko da yake Kasan Gidan naku GIDAN GANDU ne sai hada da paper nd biro. Yayi dai yaqeh, so yake ya tmby islah, zainee tace ohh ta dan fita m sure batayi nisa ba, ynz za ta dawo don ko break ba muyi ba, yace ok, fira Zaineema ta ke janshi da amma be jin komai, binta kawai yake da Eh ko Aa, jin an kwankwasa kofar ya sa zaineema cewa that must be her, Mu'ammar yace Wait pls, ta tsaya yace i will get d door, bari na bude mata, tace sure, Mu'ammar ya nufa kofar gabansa na faduwa ya bude, sandare wa sukayi gabaki daya da suka hada ido, suka tsaya kallon kallo, mamaki fal a ransu, shi tunanin chanzawanta yake, ita kuma mamakin ganinshi take, rabawa tayi ta gefe ta shige ciki ta barshi bakin kofa tsaye, Zaineema kinsan ynz su Freya suke cewa wai sai sun hada party, partyn mene? Tace wai partyn kawo "Most Unique" Cambridge, Zainee tayi daria tace dolee ne ai, erhm ba wannan ba, bakiga bakon ki bane? Islah ta bata rai baqo wani irin baqo kuma? Tace ke da er iska ce, baki ga YaMu'ammar tsaye ba? Ta dan kalleshi a wulaqance tace waye haka nan? Au wannan? Gaskia ban sanshi ba, zaineema tace ke ni fa bansan haka, yaxo ya na nemanki, yace shi yayanki ne kuma wlh yana kama da Yasuraj, Islah cikin fada tace Zaineema whats ur problem? Ko wani jakkin tom dick nd harry yazo ya ce miki shi danuwa nane sai ki yarda? Kin fin sanin yanuwa na ne? Toh ki fitar dashi tunda ke ki ka shigo dashi don ni ban taba ganin irin me hallitarshi ba..
_Bibilicious Biebee_
Like · Reply · Report · Aug 9 at 10:07am
Feenah Yahay
Tenx
Like · Reply · Report · Aug 9 at 10:08am
Phatee Lamin
5⃣1⃣🏡Gidan Gandu🏠 by 💕Biebee Isa💕 Zaineema ta kalli, ba wani alamun wasa a fuksar Islah don tsakaninta daAllah take ita ba ta sanshi ba, Mu'ammar da yayi tsaye ya na sauraron zancen Islah, ya kasa cewa komai, jin muryan Zaineema yayi tana cewa Mallam danAllah ka tafi, tace ba ta sanka ba, Mu'ammar ya marairaice yace wlh ta sanni, ni yayanta ne, fushi takeyi dani, amma zanso ta saurareni ta ji me xance mata, zainee tace danAmlah mallam ka fita, zaiyi magana kuma sai ya fasa, ya juya ya fita, Islah ta bi bayanshi da kallo kafin ta buga tsaki da karfi, ranta a bace, tambayoyi Zaineema ke san yi mata amma sai ta share.
Bawan Allah ashe ba tafiya yayi ba, yana nan zaune kan wasu kujeru da ke nesa da dakin ya yi tagumi hannu bibbiyu, tunani yake yi ga hawaye maqale a idonsa, yana kallon mutane. Karfe 3 agogonsa yace, awan sa 5 zaune kan kujerar nan yana neman mafita, gani yayi sun bude kofar dakin sun fito tare, sanye suke da jallabiya da mayafansu, da alamu unguwa xasu, ba ta da wata damuwa, haka suka dinga tafia wasu na daga ma Islah hannu itama tana mayar musu da martani, a ransa yace shes popular, miqewa yayi da sauri ya je ya sha gabanta, tamau ta murtuke fuska, yace Islahulkhair hear me out please, ki saurareni kina wulaqantani, hararshi tayi ta ja hannun Zaineema suka wuce da sassarfa ya bita ta re da riqo hannunta, ta na juyi wa ta kamtse shi da mari, Dont u touch me, ka kyaleni koh? Nace ban sanka ba, leave me alone koh? Dalibai suka juyo suna kallon su, duk aka xagayesu, rai a bace yace Ni Islah kika mara? Tace ka sake yunqurin tabani sai na maka wanda ya fi wannan, rai a bace yace amma kin iya ba qaton arne jikin ki ya rungumeki koh? Don ni mijinki na taba hannunki ki ka mareni? Ta fara kuka, tace ka damu ne? Meye dameka? Da ni da banza daya muke a gunka, banda wata amfani, ka ha'inceni da ka barni cikin tagamemen gida har wata 6 don kawai ba ka sona, sauran yanuwan mu da suka zauna da zabin da aka musu gaya min mutum daya da ke son daya, ai tun da Ya jawad ya yarda ya zauna da fadila su da basa shiri ko kadan, ina ga zaka iya zama dani ni da ko kallon banza be taba hada mu ba, amma kai sbd tsanar tayi yawa ba ka iya kwana dani rumfa daya, sbd tsana ni kadai har wataAi ina ga ko kwance ka ganni da kato ba abinda ya dameka? Ba ka damu dani da ba, kuma kar ka damu dani yanzu ba, ka rabu dani kawai nayi rayuwata, ta na kaiwa nan ta koma daki da gudu ya bita da kallo, yana hawaye kwata kwata yasan be kyauta mata ba, zai bita zaineema ta dakatar dashi tace let her be, itama ta wuce Mu'ammar ya juya ya nushi iska cikin haushi, sai a sannnan ya lura da turawan da sukayi dandazo a gurin suna kallonsu amma ba su fahimci ko me suke cewa ba..
Abuja
Ruma, Ruma, kiran da taji Yaxayd na kwala mata, ta fito da sauri murmushi dauke kan fuskarta, yace yau nake gama housemanship dina, Allah ya sa bakya da lectures ki rakani asibiti, dadi taji ya ziyarce zuciarta, yo ko tana da lectures ai ta soke shege balle babu, tace Babu Ya Zaid, yace good, ki shirya ynz, tace a shirye nake sai dai brkfast yace dont worry zamuci a chan, ta juya tace ok bari na kira Aunty Badiyya, da sauri ya fincikota yace dont ever mention her name to my face again, ya saketa ya shige daki a fusace, be son ganinta ko sunanta be sonji, dukda suna zaune cikin gida, shi sakinta ma zaiyi, ya dauko giyarsa cikin firij zai bude, da sauri Maysah ta yi sauri isowa ta amshe gwangwanin, ta kalleshi ta girgiza kai, tace its too early Yazayd, na shirya muje koh?haka kurum ya ji zuciyarshi tayi fes,Zabin tsoho ta wanke mai duk wani baqincikin da badiyya ta sashi,shi ya san ba sonta yake ba, amma kallonta ma sashi farin ciki yakeyi, ya ce Muje Rumah, murmushi ta sake, yace me sa idan nace miki Ruma kike murmushi? Tace saboda Tsoho kadai ke kirana da sunan, Yayi murmushi shima yace kice mazajen ki kadai ke kiranki da sunan, koh? Ta sa hannu ta rufe fuska, ya miqe tare da riqo hannunta, oya muje Zabin Tsoho, ta kalleshi tayi murmushi, a ranta tace nakusa Zama zabinka.
Akan idon badiyya suka fita, hankalin ta ya tashi, har ynz jikinta a kumbure yake, da sauri ta lalubo wayar ta ta doka ma Bokanta kira, ya na dauka ya fashe da daria, dama jiran kiranki nakeyi don na san dole ki kirani, cikin tashin hankali tace boka, na gama aiki, aikinm ya karye, jiya zayd dukan kawo wuqa ya min da mahaifiyata, ya kuma korata, kuma yanzu kan idona suna fita da matarshi, ka taimakeni, boka ya fashe da daria, yace ai ba wani taimakon da zan miki, ni na karya asirin da na ma Zayd, ke duk asirin dana yi a rayuwata sai dana karyashi, sbd mutuwata nake jira, banda lafia kuma nasan mutuwata na kusa, taimakon da zan miki be wuce na ce miki ki je Asibiti ki fara neman magani, dif ya kashe wayarsa Badiyya ta shiga juya maganganun Boka, abun da ta ka gane shi ya karya Asirin Zaid amma ba ya ga nan ba ta gane komai ba.
Duk inda Zaid yayi da Maysah na gefenshi, sunyi kyau matuqa, kallo daya zaka musu kasan sun dace da juna, sai tambayanshi akeyi Dr. Zailani, who is she? Kai tsaye yake ce musu she's my wife..
Kaduna
Ya na dawowa ta sha gabanshi, tace wai meye haka? Meyasa kakeson aiko min direba? Mu kwana gida daya amma ka na baqin cikin yi man magana? Nidai in har ka na son wani abu daga gareni ni zaka fada mawa kar ka qara aiko min direba, bakinta ya matse da karfi,ta sake ihu, yace ba na hanaki rashin kunya ba? Ni tsaranki ne? Kika qara min haka sai na lallasa ki cikin gidan nan, ya jefar da ita kan kujera, ta shiga murguda baki tana matsa. Kwallah, a ranta kuwa cewa takeyi na tsani wannan Jawad din.
******
Misalin karfe 12 da rabi na dare, Jawad na zaune na shan cofee yana rubutu kan dining, fadila dake bacci a dakinta taji kamar an duro ta windonta, ta miqe ta leqa, hantar cikinta ta kada sakamakon wasu da ta gani su 2 zuwa 3 ba ta tabbatar ba dai, da bindigogi a hannu, cikin kidima ta wawuro wayarta ta rasa wanda zata kira, kawai sai ta danna emergency number 911 dukda ba ta da tabaccin yana aiki, cikin saa aka dauka cikin rudu amma a hankali ta ke sanar dasu abun da ta gani, wani gari take? Tace kaduna, ta ba su full address, sukace nan branch din lagos ne amma ynzu zasuyi alarming kaduna As soon As possible, kyarma takeyi bata son yin kwakwaran motsi sujita, tana kallo suka daure maigadi, suka nufo parlorn.
Ji yayi ansa mai wani abu kamar bindiga akai, ya dagi da sauri, Inalillahi wa ina ilaihir rajiun yace, ya daga hanayenshi sama alamar surrender, yace kar ku kasheni, zan baku kudih wlh, daria suka fashe dashi, we dont need ur money rich boy, all we need is ur life, but before den sai ka dauko mun signed contracts din da zakayi a Niger Delta, cikin Jawad ya duri ruwa, yace pls lets talk dis out, buge mai kai yayi da bindiga, yace zaka dauko min ko sai na tarwatsa kanka da harsashi na? Jawad yace Aa, Alamun jiniyar mota na waje yaji, ya leqo cikin kidima ya ce boss, ga masu bakin kaya, ya dago da mamki yace ya akai suka san muna nan? Dd u call anyone? Jawad yace ai bansan da zuwan ku ba, kai da waye a gidan nan, da sauri yace ni kadai ne, a zuciyarshi yana me roqon Allah kar fadila ta fito, yes boss dama oga yace shi kadai ne be da mata, kawai mu kashe shi mu gudu kafin su shigo, ji sukayi ance we are advicing u to put ur guns down, ur hands behind ur heads, come towards us slowly, u try to make a wrong move we fire, you are surrounded, i repeat u are surrounded, a hankali sukayi yadda polisawan sukace suka fita a hankali, signal dayan yayi suka arce a guje, babban police din yace hold ur fire, no one shoots, we need dem alive nan suka bi su a guje, tuni suka dire, polisawan suka bisu. Ya jawad ya yu hanyar fita don ganin meke faruwa, Tana fitowa ta ga wani ta window yayi saitin bayan Jawad da bindiga, da sauri ta rugo gunshi da karfi tace Yajawaddddd, juyowan sa yayi daidai da harbin, jin harbin bindiga yasa sauran polisawa sukayi gurin da sukaji harbin, Ganinta yayi kwance jini ya malale wurin da karfi yace Fadilaaa ya rugo da gudu ya tsugunna gaganta ya tattaro ta jikinshi, yana kuka yace stay with me fadila, dont leave me please, i got u, jini na bulbula daga bakinta da qyar tace Yaa jaawaadd dif ta dauke, cikin tashin hankali da karfi Jawad yace Someone Help!! Ambulance! We need an Ambulance!
_Bibilicious Biebee_
5⃣2⃣ 🏡Gidan Gandu🏠 by Biebee Isa💕Da gudu wani polive ya shigo, yana tambayan jawad sir are u okay? Cikin tsawa yace we need an Ambulance u stupid idiot, cant u see? Da sauri poloce din ya kira Ambulance, cikin mintunan da basu wuce Goma ba sai ga Motar taimakon Gaggawa, akai akai jawad ya matsa a dauki fadila a sata cikin mota fir yaqi sai dai shi ya daga abarsa ya kai mota, a motar ma tana rungune dashi har suka isa asibitin 44 dake kaduna da sauri akayi da ita Accidents and Emergencies, aka amsheta, Dr ya ba Jawad wasu forms yayi signing zaa ma matarshi operation don ciro bullet din da ke cikin kafadarta, da sauri ya sa, aka ja gadon fadila bayan an sa mata oxygen akayi theatre room da ita, jawad na biye a baya, zai shiga dakin wani security da ke tsaye bakin kofar yace sir u cant come in, jawad yace try to stop me, ya raba ta gefenshi ya shige, nurse na ganinshi tace sir, u cant be here wani hararan da ya wurgi nurse din dashi ya sa ta matsa mai, Ganin haka Dr yace let him, nd lets get to work. Haka suka duqufa aiki kan fadila, jawad kuwa sai Addua yakeyi Allah ya tashi kafadun matarshi, she cant die.
Maiduguri
Isowarsu kenan, straight dakin Mamanshi Aunty Nuratu yayi da ita, bata tunanin ta taba shigowa sashen, duk sai taji kunya, Hanifa ta gaishe da Aunty Nuratu da ke gyaran gadon da zayyad zai ajiyeta, ta amsa don ba ta tuna ranar da Hanifab ta gaisheta ba, sannu ya kafan ta amsa, Zayyad ya shimfideta kan gado ya fita yayi sassan tsoho, tsoho da kansa ya zo gaida hanifa a dakin Aunty Nuratu, yayi mamakin yadda kafar ya kumbure, ya yi umarni da Baba Hassan da ya kira me dorin kafa. Har gida akaje dauko me daurin kafan, hajia babba ta riga ta gyara dakin da Hanifa zata sauka, sai ji tayi ance sun iso har an kaita dakin Aunty Nuratu, Ashar ta sake tace ba zai sabu ba, ta fita Aunty Abida Maman Hanifa ta rufa mata baya sukayi sassan Baba Hassan, Masifa ta so saukewa ganin tsoho tsaye ya sa ta yin shiru, Zayyad ya gasiheta ta kalleshi a gyatsine ta amsa, ya gaida aunty abida ta amsa, Tsoho yace bari ya koma sassan sa, tsoho na fita Hajia babba tace kai dan wulaqanci, ban taba ganin mugu kamar ka ba, kaje ka aje yarinya chan qasar kabilu ba uwa ba uba ko leqen gida ba ta zo ba har watanin 8, don mugunta, ba ka kula da ita, sai da kayi sanadiyar turgudewarta zaka kawo mana ita nan? Toh ba zaiyu ka ajiyeta nan ba dakina zan tafi da ita don ta samu kulawa, ba Zayyad ba har Hanifa sai da taji ba dadi, yace kiyi hquri hajia, bari a maidata chan dakin naki ta juya fuuu, tace da dai ya fi, Aunty Nuratu na zaune ba dai ta tanka ba, Maman hanifan ma ba ta ji dadi ba, sumsun tavi bayan mamanta, hanifa ta kalli mijinta ciki tausayawa, a ranta tace bawan Allah, haqurin shi yayi yawa, yace hanifa bari akai ki dakin hajia ko? Batace komai ba, ya dagata sama, a hankali tace kayi haquri Yaya, murmushi yayi ya fita da ita. Ko da me gyaran yazo dakin hajia babba akayi dashi, yace zaa ja kafan a gyara, zayyad na gaban Matarshi, hajia babba tace kai dalla mallam zoka fita zaa ja mata kafa, kayi wani kane kane, hanifa ta kasa haquri tace haba hajia, me yayan ya tsare miki ne eyi? Tun dazu na yi shiru na kyaleki? To ba inda zaije ta qarashe tare da murguda ma kakan nata baki, bakih bude hajia babba take kallon hanifa, ita da ta san hanifa ta tsani Zayyad amma gashi ynz sai kareshi takeyi, Zayyad yayi murmushi ya shafi kumatun hanifa yace bari dai na jira a waje, hanifa tace no yaya, hold me pls, Zayyad ya kalli hajia babba da har ynz bakinta a hangame yake sbd mamakin hanifa, yace ma mai gyaran bismillah, mai gyara ya kama kafan hanifa ta kwallara ihu tare da janye kafar, har cikin kwakwalwar shi yaji ihun nan, hajia babba ta kalleshi tace ai sai ka riqeta kar ka min tsaye a ka. Zayyad ya zauna ya riqe hanifa, me gyara ya cigaba da jan kafar, shi ko harda hawaye don jin yadda hanifa ke ihu.
********
Suraj da Bilkisu sunzo Maiduguri don duba hanifa, hanifa da bilkisu suka kulle a dakih suna firan yaushe gamo, suna ba juna labarin rayuwarsu bayan aure, Bilkisu tace lallai hanifa dole ki sauko ki nuna ma Yaya zayyad so a zahiri da badini, don ya yi hquri dake ba kadan ba, idan kuma kikace zaki tsaya jan aji wannan fatitin zai aura, a maidaki yar kallo, hanifa ta ja numfashi tace wlh Bilkisu na yi nadama, duk abubuwan da nake mishi be taba fisho dani ba, Ni so nake mu koma gidanmu, tunda naga tsoho da mamana ban marmarin gida, naji sauki wlh, Bilkisu ta yi daria tace kamr kinsan for a 2nd bansan yin nesa da Yasuraj, don wlh Ya suraj ya qware a iya love, suka chafe tare da kwashewa da daria.
Cambridge England
Shopping tazo ita kadai don zaineema na lectures, ta gana siyan kayab da suke buqata ta fito wajen Mall din, ta na tafia da ledojin ta a hannu tana jiran Cab, Ji tayi ance Islah don girman Allah ki saurareni da sauri ta juyo ta kalleshi, kallo daya ta mai ta ga ya rame ya yi duhu, ganin bata ce komai ba ya sashi fara magana kamar haka; Dalilin da ya sa na zo london shine ina so na manta da Hanifa, ina so cireta a raina, don nayi mata zazzafen so, sbd son hanifa da nakeyi har pricking fingers din mu mukayi muka sha jinin juna, its hard for me to forget her easily, ganinki kuma na bata raina i dont want to hurt u shisa na bar Gidan don i dnt knw wat i will do to u idan ina ganinki a matsayin matata, shisa na bar kasar ba tare da na gaya ma kowa inda zani ba,don kar a tilasta min na dawo, i chose to come to London dan na saba da garin, i chose to be alone just to forget hanifa nd come back to u, mu fara rayuwar mu mu biyu, nd wallahi i forgot every single thing abt her last 3 months, i taught my self how to love u sincr den, ynz kece nakeso, kece zuciyata ke tsanannin so,Son da ban taba ma yi ma wata ya mace, wlh ko son da nayi ma hanifa be kai kwatan wanda nake miki a yanzu ba, wlh lokaci daya sonki ya shige ni, kece nakeso ki zama uwar yayana, i want to spend d rest of my life with u Islahulkhair. Tun tuni na siya return ticket to Nigeria, flight ina in d next two weeks, i wannid to come home to u, i want us to start a new life, nd unfortunately i saw u here, Islah pls ina fatan kin fahimceni da dalilaina, Islah da idanuwanta sukayi ja, ranta a bace, Mu'ammar din nan ya ma gama raina mata wayau, tsaki ta buga ta juya ta cigaba da tafia, ya biyota a baya haba hanifa, kar dai baki gamsu da maganganu na ba, ya riqota tace let go off me, ka raina ma kanka hankali, u Stomped on my pride d moment u left me, i dont want nythn to do with u jus lemme be pls, girgiza kai yayi yayi saurin rungumeta ya na hawyae, i cant leave without u, forgive me pls, Islah ta ture shi da qarfi, da gudu ta qarasa gaban motan polisawan dake parke, Mu'ammar ya bita da ido don ganin me zatayi. Ta ce officers, someone's bin chasing me, i dont knw him? He's embarassing me, suka fito suka ce We'll deal wit him, suka nufa amar suka kama shi, daya da ga cikin officers din yace, why are u chasing her? Ya kalleshi cike da takaicin abun da ta mai yace she's my wife, da sauri tace he's lying m not, officern ya kalli Amar yace keep off, yace da Islah wenever he bothers u again u knw wat to do, ta gyada kai tace i will call u ryt away. Good u can go, ta kwashi ledojinta ta yi gaba zuciyarta fal da farin ciki, Amar cike da bacin rai ya juya beson inda yake jefa kafanshi ba, ya nufa titi wurin tsallaka titi ne wata mota tayi gaba dashi, chan gefen titi a kaga Amar kanshi ya bige da wani qarfe, kan shi na zubar da jini, da sauri aka kamshi a ka sa shi cikin mota akan idon Islah akayi komai, taso tayi tafiarta ganin shi ya miqe da kafarsa, amma rashin imaninta bekai nan ba, ta tsaida mota ta ce ya bi bayan motar chan.
Abuja
Shigowarshi kenan, ya ji wayarsa na kara, da sauri ya ciro wayar daga Aljihu, Jawad ya gani ya dauka, hello jawad?daga bangarensa ya na kuka yace brother m scared? Zaid ya ce me ya faru jawad? Me ya sameka? Yace its fadila, she's bin shot, took a bullet for me, Inallilahi wa ina ilaihir rajiun inji zayd, is she dead? I dont knw, tun qarfe 11 aka fiddota daga theater room, sunce operation din is successful amma har ynz bata farka ba, Bro i cant loose her, Zaid cikin rudu yace Gani nan zuwa, ka kwantar da hankalinka, she's gonna b fine kajih. Ya shiga ciki suka ci karo da Maysah ta fito daga kicin yanda ta ganshi ta san cewa ba lafia,Ya zayd lafya? Yayi dan tsaki, kana yace matar Jawad ce a ka harba, maysah ta zaro ido, Fadila? Yazayd is she alright? Yace shine xanje kadunan ynz, yazayd m coming with u, ya danyi shiru, kafin yace yi sauri ki shirya, we are leaving now.
*****
Tana ganin tafiansu ta sakr ajiyar zuciya, ko sallama be mata ba, dama so take ta samu damar fita balle ynz da ta quduri zuwa asibit sbd wasu manyan kurajen da ta gani a gabanta. Ta shirya ta nufi wani Prvt hospital, bata sha wahala ba ta shiga ganin likita, bayan yan tmbyoyin da likita ya mata game da kurajen, har dai ya nemi ya gani, ya sake mata wasu tmbyoyi, likita ya kalleta sosai yana son karantar wani abu a fuskarta, chan kuma ya ciro wata na'ura ya ce zai dan chaketa da allura a yatsa, zai mata test, badiyya ta miqa yatsarta bayan ya sa hand gloves ya dan diba jini tare da sawa kan strip din injin. Bayan wasu mintuna machine din yayi qara, Dr ya maida glass dinshi ya duba machine din ya dago a raxane, ya kalli Badiyya, ya ce Mrs Zaid Zailani, what m abt to tell u is - tace cut d crap n tell me wats wrong wit me, ya tabe baki yace you are HIV POSITIVE...
5⃣3⃣ 🏡 Gidan Gandu🏠 by 💕Biebee Isa💕Cikin tashin hankali diyya tace HIVn Uwarka? Ni fa ban san iskanci, ta figi jikkarta ta fice daga office din a fusace, gabanta na dukan 3uku, Dr ya dauko File dinta ya kara karanta sunanta ya tsaya yana tunanin. Tashin hankali ya bayyana karakara a fuskar diyya, ta gaza sukuni, wani asibitin ta nufa, ta na zuwa tace amata HIV test, gwajin farko ya nuna tana da cutar HIV, ihu Badiyya ta kurma tare da daura hannu a kai, sai da ta gama kururuwarta kafin ta nemi ganin likita, don neman shawara, haka liktita ya shiga gaya mata abubuwan da zata kiyaye da abubuwan da zatayi, ta fita jiki ba kwari, ta biya chemis ta siya magunguna kafin ta koma gida cike da damuwa...
Cambridge England
E&A aka kai Mu'ammar don har ynz kanshi na fitar da jini, Dr Miracle ya kalli wanda ya kawo shi yace yayi loosing blood sosai and dole zaayi mai karin jini, yaje ya siyo a blood bank, Orange Negative (O-)zai siyo, ko da yaje siyo jinin baa samu O- ba, mutumin yace a aunashi aga idan jinin yayi daidai da na Amar, ko da aka Aunashi, kwatakwata ba zaiyuwa a dibi jininshi a sama Amar ba, Likita yace dole ake samo jinin da za'ayi transfuse a jikin Amar before he runs out of blood, if he does, he will die eventually, Islah da ta gama jin abunda dr din yace ta qaraso da sauri tace I am (O-) i will b d one to donate the blood, mutumin da ya buge Amar yace nd you are? Da sauri tace Relative, Dr yace ok, d earlier d better, bayan an auna jininta aka jininsu yayi daidai aka dibi leda biyu na jini Islah, kafin aka bata kayan marasa lafia aka kaita dakin da amar ke kwance ya dan samu bacci, kusa da gadonshi aka kwantar da ita don ta huta bayan sun bata madara tasha. aka hada jinin a jikin Amar...
Kaduna
Karfe 5 ta musu a kaduna straight Asibitn da aka kwantar dasu Fadila suka nufa, Zaid ya kira Jawad ya musu kwatancen dakin, yace Amenity Ward room 11. Ba su sha wahala ba suka gano dakin, Jawad na zaune kan gadon marasa lafiya yana sanaarsa wato kuka, duk ya tattaro fadila da ba tasan inda kanta yake ba zuwa jikinsa, ga rungumeta kamar zaa kwace masa ita, ga drip a hannunta ga oxygen a hancinta, suna turo kofa Jawad yayi saurin xame jikinsa tare da fadawa kan Zaid ta fashe da sabon kuka, ita kuma Maysah ta ruga gurin da fadila take kwance itama ta sa kukan, Zaid yace Jawad yi shiru mana, be a man, ya girgiza kai yace Brother, i cannot loose fadila, she cannot die, she took a bullet for me, dat was my bullet, zayd ya matseshi a jikinshi yana bubbuga bayan kanin nashi, gudan jininshi, yace shes going to be fine, InshaAllah, have faith, Allah zai tashi kafadunta, Jawad ya dago cikin bacin rai yace i promise u whoever did dis to my wife is going to pay, Zaid yace ya isa haka jawad, ya sakeshi ya qarasa gun gadon fadila, tare da yin dube duben su na likitoci, Zaid yace kar ka damu, bacci takeyi, kai kawai Jawad ya daga mai, Maysah ta ce Yaya Jawad Allah xai bata lafia, zata warke, u two will live to see ur kids, be san sanda murmushi ya kubuce mai ba, yana tunanin kalan yaran da wannan ma bakin tsiwan zata haifa mai. Da sauri ya qarasa kan gadon ya riqo hanunta yace fadila, i know u can hear us, wake up, i need u, i miss u, i missed everything abt u.. Zaid yace i dont think ko lunch kacih, yace rabona da abinci tun dinner din jiya, hankali na a tashe yake, Xayd yace yanzu Rumah ta tsaya a nan, sai na kai ka gida kayi wanka kaci abinci, kafin mu dawo ta tashi InshaAllah, Jawad cikin d'oki yace ok bro, Rumah bari muje mu dawo ko? Tohm yazayd Allah ya kiyaye Amin. Jawad yace Rumaysa ki kula min da matata, kar kaji komai Yayanah, zan kula maka da ita toh ngd suka fice.
Maiduguri
Salatin da Tsoho ya rafka ne yasa duk yan dakin zuba mai ido, Zaidu tun yaushe hakan ta faru? Zayd Yace ka kwantar da hankalinka tsoho, jiya ne da daddare, amma ynz har Anyi mata aiki kuma an dace bata dai kaiga farfadowa bane,Nima yau Jawad din ya kirani ya sanar dani shine muka taho da rumah, Tsoho ya ce InshaAllah gobe mu na nan tahowa, Zaid yace tsoho wani tafia zaka iyayi? Duk kuyi zamanku, ba sai kunzo ba, tsoho yace bazai yuwu ba, yau ma don marece yayi ne da ka ganmu amma asubar fari zaku ganmu. Zaid yace toh Allah shi kaimu. Tsoho na aje waya duk suka hada baki gun cewa lapya? Yace yan bindiga ne suka je gidan Jawad jiya har sun harbi fadila, hajia babba ta aza hannu akai wayyo mun shiga uku, Allah ya sa ba su halbi Jikana jawad ba. Tsoho ya galla mata harara. Ya kalli Suraj da Zayyad yace Fadila ce aka harba amma an mata aiki ynz haka suna asibiti, Suraj ka shirya gobe zamuje, kai Zayya ka tsaya da matarka, Bilkisu tace tsoho nima zanje danAllah, yace aa ki tsaya kiyi jinyar yaruwarki, ya kalli hajia babba yace ki shirya ke da Abida da ku zaa tafi goben, Alhaji baka gaya min ya jawad dina yake ba? Tsoho Yayi banza da ita ya fita daga sashenta Yayi sashen Hajia Ama, ya ko ci saa Aunty Hassana na zaune, yace Hassan ina Aliyu? Tace barka da maraice baba, tun da ya fita be dawo ba, yace ina Aishalle? Tace bari na kirata ta miqe ta kirata tazo ta zauna, wani tsautsauyi ya faru a kaduna jiya daddare, Dam gaban Aunty hassana ya fadi, A ranta tace Allah ka sa ba wani abu ya samu diyata fadila ba, tsoho ya cigaba Yan bidinga suka shiga gidan Jawadu da niyyar kasheshi cikin rashin saa suka harbi Fadila a kafada, Ama da Aunty Hassana suka fashe da kuka, tsoho yace ku kwantar da hankalinku. Xaid yace da sauki gobe zamuje daku gabaki daya. Kar ku tada hankalinku. Sai da ya kwantar musu da hankula kafin ya miqe ya shige Sassan Umma hajja..
*****
Asubar fari suka dauko hanya mota biyuu akayi da babba da karama, karamar motar baba hassan ce, shike tuqa tsoho, hajia Babba da hajia Ama sai Umma Hajja, ba yanda basuyi da tsoho kan yayi zamanshi ba fir ya qih, Babban motar kuwa bus ce ta Gidan Gandu. Sai da laasar suka samu suka iso. Zaid ne ya je ya dauko su a Kawo, suka iso Asibitin. Yau asibitin 44 ta shaida da zuwan Familyn Zailani, Straight dakin suka nufa suka shiga da Sallama, Maysah ta ruga da gudu ta rungume tsoho cikin jin dadi kafin ta shiga gaida kakaninta da uncles and aunties. Ganin iyayenshi da kakkani be sa ya xame daga rungumar da ya ma fadila ba kan gado, Tsoho yace Sannu jawad ya me jiki? Ya fashe da kuka Yace tsoho ba sauki har ynz bata farfado ba, baba hassan yace Ai jawad zata farfado, Allurar ce bata sake ta ba, Zaid yace na gaya mishi ai, wasu idan aka musu anaesthesia sai bayan kwanaki 3-4 suke farfadowa. Jawad yayi saurin cewa Allah ya sa ta tashi ynz suka amsa da Amin, Tsoho ya umurcesu da suyi mata addua, nan kowa ya dinga ma fadila addua, suka shafa, Jawad ya labarta musu abun da ya faru, ya hada da cewa tsoho wlh ina son matata bana so ta mutu, ta cece rayuwana, ta mutu wlh nima sai na bita, karaf hajia babba tace ja chan sakarai, don me zaka mutu? Alhamdulilah tunda kalau kake, Ni na bi na tashi hankali na duk zatona barayin suna maka wani abun ko baka da lafia, wlh dana san haka ne da nayi zamana, wani muguwar harara jawad ya wurgi kakarsa dashi, ran tsoho ya baci ds jin magangannun hajia babba zai yi magana sai dai yayi shiru, Jawad ya hade rai tumuk ya kalli Aunty Abida yace mom get dis woman outta here i dont want to see her, Aunty Abida ta harari Jawad, tace shes my mother, mom rwly? Bakiji me take cewa game da matata ba? Dint u here me say she took a bullet for me? Mom da yanzu nine fa a kwance kila na mutu, sakkayar da zaku yi ma wacce ta ceci raina kenan? Dis shud hav bin me, she doesnt deserve dia at all,Jikin anty abida yayi sanyi, ta kalli fadila cike da tausayawa lokaci daya taji son fadila a ranta, ta ji dadin da danta ya auri jaruma kamar fadila, Hajia babba zatayi magana Zaid yayi saurin janta yace muje daga waje kakus, tace yauwa don na gaji da tsayuwa, na sha hanya a banza muje ka ban labarin yar gayu, ya ma sunanta? Dif zaid ya dauke wuta ya yi kamar be taba daria ba, ya kalli tsoho yace Tsoho ina jin ya kamata kuje masauki, don dr yacr patient bata son hayaniyya, ya'll shud get going, tsoho yace haka ne, muje masauki Gobe ma dawo, daya bayan daya suka fita, aunty abida ta matsa kusa da fadila ta mata kiss a goshi tace Allah miki Albarka nagode, jawad kadai jita yayi murmushi Yace thanks mom, ta shafi ganinshi tace take care of my daughter inlaw, yayi smile sosai yaji dadi yace i will mom. Ya kalli Aunty hassana da ta tsaya ta kurawa diyarta fadila ido tana dan hawaye, yace Mummy m so sorry, wlh bansan da zuwan fadila gurin ba, duk a zatona tana dakih, forgive me mummy, aunty Hassana ta girguza kai tace ba laifinka bane jawad, Allah ya riga da ya qaddara fadila ce za a harba, so stop blaming ursef kajih dana? Yace thank u Mummy. Duk suka fice, Zayd ya bi bayansu don nema musu masauki duka...
*****
Maysah nakan sallaya ta idar da sallar maghrib, jawad kuma na kan gadon da fadila ke kwance har zuwa yanzu bata farfado ba, rashin farfadowanta ya fara bashi tsoro, ya riqo hannunta yana murzawa a hankali, ya na magana me kama da sambatu, inda yake cewa ke me tsiwa, kika sake kika mutu sai na biki, toh meye amfanin rayuwata idan kin mutu?ai ban gama jan bakinki ba idan kika murguda min bakih, so its early for u to die, sai kuma ya fara hawaye, kamar an tsunguleshi ga goge hawayen idanunsa ya dan daga murya yace ke dallah ki tashi. Kamar tajishi, cikin ikonAllah fadila ta bude idanuwanta a hankali, ta sauke su fes kan Jawad da sauri ta hade rai tare da murguda mishi bakih. Da sauri jawad ya hada bakinshi da nata.
_Bibilicious Biebee_
5⃣4⃣ 🏡Gidan Gandu🏠 by 💕Biebee Isa💕Fadila ta daddage ta gantsara ma jawad cizo a bakih, ya dan saki karah ya saketa, ta sake murguda mai bakih, shi kuma ya ja bakin a hankali, yace you are Okay, Dont make me worry too much about u like dis, sai a sannan komai ya dawo ma Fadila, ta tuno cewa harbinta akayi, ta sa hannunta ta shafih kafardarta taji bandage, da sauri tace Ya Jawad someone was trying to shoot u, yace shhh, save ur strength i know wat happened, a halin yanzu an kama su, amma sunqi magana, sunqi fadan wanda ya turo su, but it wont be long before they expose who sent dem. Tayi ajiyar zuciya, Fadila,e kikeso?ina ke miki ciwo? Ta murgudi bakih, tace ni ka kaini gida, ni ka kaini maiduguri, ina son ganin tsoho da Mummy, yace karki damu, su tsoho na nan kd, basu dade da tafia ba, Gobe zasu dawo kinji? Ta gyada kai a shagwabe, yace look who's here, ta kallo inda yake kallo, tayi yunqurin tashi tace Maysaaah, yayi saurin maida ta, yace ke mallama koma ki kwanta, Maysah da ta tsaya kallonsu don kalar Soyayyar su ta birgeta, ta qaraso kan gadon ta riqo hannun fadila Tace sannu sis, ya jiki? Fadila tace yaushe kikaxo? Kwana nawa anan? Kwananki 2, ta zaro ido, tace m happy to see u sis, Maysah tace same here, get well soon kinji? Fadila ta turo bakih tace ni fa ba abunda ke min ciwo m okay. Jawad yace yauwa baby haka nakeso, ta harareshi tace mallam ni ba baby bace sunana fadila, yace yarinya bari a sallame mu mu koma gida, sai na yi maganin ki, ai kinsan halina. Fadila ta koma ta kwanta kan cinyarshi inda taga kanta da farko ba tare da tankashi ba. Shi kuma ya shiga shafar kanta fuskarshi dauke da farinciki.
*****
Washegari su Tsoho da iyalanshi suka dawo, sunji dadin ganin fadila ta ji sauki don ynz ma Zaune take Jawad na bata abinci a yangance take amsa. Tsoho yace tunda ta farfado da alamun ta warke, yau xasu koma, Baba hassan yace Jawad ya maganan Gunmen din? Har ynz ba su fadi wanda ya turo su ba? Yace Eh baba basu fada ba, ni ban masan me ake ciki a yanzu ba, Zaid yace yanzu idan na rakaku zanje Police Station din naji abinda ake ciki, Hajia babba dai ta sha jinin jikinta ganin Jawad ko kallonta beyi ba balle ya gaisheta, ga Zaid nan ma fushi yake da ita, ta na son jikokinta, Sai da Tsoho yace ayi addua don nemar lafiyar fadila da karfi tace Ameeen, amma hakan be sa Jawad kallonta ba. Haka dai yan Maiduguri auka tafi, Zaid ya shaida ma Maysah suma yau din zasu koma da laasar. Fadila ta sa Maysah ta kira mata Amal, baa yi 15mins ba sai ga Amal da mijinta Rufa'i, mijin Amal yace da Jawad wlh baka kyauta mana ba, a matsayin mu na Makwafta mu ya kamata mu riga kowa sani, abu har an kwana biyu ba muji ba? Jawad yace kuyi hqri, tunda akayi abun so daya na koma gida, kuma ban dade va, suna cikin fira sai ga Zaid ya dawo, suka gaisa da Rufa'e, zayd yace da Jawad ya tashi suje police Station, Jawad yace aa bros, kai dai kaje, ni ina nan da matata, fadila ta murguda bakih tare da hararashi, hakan da tayi ya basu daria dukah, Maysah tace Ya Jawad kuje kawai, trust me zamu kula maka da matarka, kaga ma maman Irfan, tana nan ko? Amal ta gyafa kai, tace uo wife us safe, ya danyi shiru kafin ya kalli fadila yace baby naje? Ta murguda baki tace sai ka dawo, ya xo ya bata peck suka juya zasu fita, har waigen ta ya ke juyowa yanayi.
*POLICE STATION*
Har ynz sunqi magana sir, Zayd ya ce suna ina? Wani kofur yace suna nan cikin interogation room, Zayd yace i want to see dem, be sha wahala ba aka barsu su ka shiga, suna nan an daure su gam su 3, Wurin dan karamin Zayd ya nufa, ya ce kai, wa ya turo ku ku kashe Kani nah? Mutumin ya dago zai yi ma Zaid rashin kunya, yana dagowa suka hada ido da shi, eye in eye, sai ya dauke fuska dob Zaid din ya mai wani irin kwarjini, Allah ya ma Zaid wani baiwa, duk iskancin da tsagerancin mutum ya hada ido da zayd sai ya raina kanshi, hakan ta faru a yanzu don zaid ya juye ya koma terror dinsa, barin ma da ya amshi bindiga ya saito kan mutumin, Zaid yace ka ganni nan, i care less abt u, is either u tell me who ur boss is, or i will shoot u, tuni mutum ya rude kallo daya ya ma zaid ya san zai aika, murya na rawa yace pls dont shoot, i will tell u what happened, Gambo Kashe Arna da aka daddaure aka yi selotaping bakinshi ya fara jijjiga yana zaro ido, alamun be so a tona ubangidanshi. Mutumin da ya ce sunanshi killerman yace Ranar wednessday, Oga ya kira mu, yace zamu mishi aiki Officer yace waye oga? Killer man ya nuna Gambo kashseArna da hannu, yace na boss dinshi ne, shi time din yana lagos, so kuma aikin Emergency ne, shi ne ya tura mu gurin shi Boss din, ni da frnd dina muka je Guest house dinshi don mu ganshi ya bamu bayannin yanda yake so aikin ya kasance, so boss be ji dadi da ya ganmu ba, don yace shi yafi yarda da aikin Oga Gambo, i assured him dat he has nothing bto worry about, don Oga trained me well, ni ne nayi Gadonshi a wannan Sana'ar, so nan boss ta bamu Full Address na Gidan Jawad, nd his picture, we asked if he's married or living with his parents yace no he is living alone, nan muka tabbatar mishi by d end of d day Jawad zai mutu. So sai nace mishi me yake so a mishi? Sai ku Amsar min Documents din da yayi signing na Contracts, sai ku kasheshi, bance kuyi robbing dinshi for money, i will give u Enough, i dont want any mistakes. Nace kar ka damu Boss, zakaji sanarwar mutuwar jawad kafin jibi. Muka tafi mukaje ni da abokina, bansan yadda akayi polisawa suka shigo ba, mu kaji tsoro sosai, so we ran for ourlives tho we were captured. Officer yace toh kuna nufin ba ku ku ka harbi ba? Then who did?Killer man yace Oga ne, Ashe tym din da muka tafi gidan Jawad tym din ya dawo daga lagos, akan hanyar ne na sanar dashi gamu nan zamuje chan, so sai ya biyo bayanmu. Shi kuma yayi harbi. Zaid cikin daga murya yace wai who are we talking? Who is dis motherfu**er dat wants my bro dead? Da sauri killerman yace sunanshi Alhaji Haladu Maidala NNPC, Iya rudewa da kaduwa Jawad ya shiga, yana mamakin Alhaji Haladu, mutumin da ya ke girmamawa kamar mahaifinshi, mutumin da yaje bi sau da kafa, baba ma yake ce mishi, shine yake so ya ga bayanshi? Me ya mishi haka? Zaid ya juyo ya kalli jawad yace u knw someone by d name Haladu? Kai kawai ya girgiza mai Alamar, Eh, Zaid ya kalli Officer yace you guys shud go get Dis Haladu of a guy, or i will, nd if i do i will be d one to kill him, DPO yace no sir, lets do dis d right way, ka bar hukuma tayi maganinshi, Zaid yace hukuma ai bata hukunta babban mutum kamar Haladu, nasan zaayi cukucuku a barshi ya fita, DPO yace na tabbatar maka wannan case dib bazaayi cukucuku ba, don daga sama aka kira mu, daga chan Lagos aka kiramu, kaga kuwa magana na hannun manya, dole a saka Haladu behind bars, Good inji Zaid, Nan take aka bada order din aje a zo da Haladu, motoci 3cike da yansanda suka tafi chapko shegen. Ba kuma su sha wahala ba gurin gane inda yake, suka nema ya bisu a hankali yaso kawo musu gardama, nan wani police mara mutunci ya chafko wuyarshi, aka saka mai Ankwa aka tasa qeyarshi sai police Station, Haladu ya kalli sergeant yace waya baku damar ci mun mutuci gaba mutane haka? Do u know who i am? Jawad ya fito ya kalleshi yace Baba me na maka kakeso kaga bayana? Me na taba ka? Where did i ever go wrong? Alh Haladu yayi mamakin ganin Jawad, duk a zatonshi an kashe shi, yace forgive me Jawad, wallahi ban taba sonka ba, duk abun da nake maka munufurci ne, zuwan ka NNPC ka min illa babba, ka kwace min matsayina a gun gwamnati, da maaikata, komai sai dai a ce Jawad, ka fara dakusar min da tauraruwata da ta haska diniyan nan, duk inda ya kamata aga Haladu Maidala ba a ganinshi saidai aga Jawad Zalani, Alhalin nafi Shekaru 20 ina aiki a wannan Maaikatar, shisa nace kawai bari na ga bayanka, Jawad ya kalleshi cikin tsana yace its not my fault dat m more hardworking dan u, Hassada ce matsalarka, da ace ka gaya min haka da na bar maka aikin kwatakwata, don mu ba matsiyata bane, Jawad ya juya ya fita daga Office din, Zayd ya kalli DPO yace sunyi filing case akanshi, so sun makashi kotu, nd kuma kar a bada belinshi har lokacin, Alhaji Haladu yace Noo, pls dont do dis to me, Zaid ya kalleshi galala yace; this is wat u get wen u mess with a Zailani.
Cambridge England
A hankali ya bude idonshi, ya sa hannu ya shafa kanshi, qaton bandage ya ji, nan Dr ya shigo tare da mutumin da ya buge shi,You are finally up inji Dr, murmushi kadai Amar yayi, What happened? Last i check i checked i was brot here, dr ya mai bayanin duk abun da ya faru, tare da gaya mishi yanda aka sha wahalan neman jini, da kuma yarda yaruwarshi tazo aka bada jini, da sauri yace who? Dr yace she said she's yo relative, she was here earlier but she left after being sure that she's all okay, da sauri yace did she leave a message or something?Yes she left her number incase something came up, may i have d number, Dr ya bude file dinshi ya ba Amae number, ganin sunan Islah ya fito kan wayar yasashi cixge drip din hannunshi,yace i gotta go, Dr yana kiranshi amma be tsaya ba, sai da ya bar Asibitin. Straight Cambridge University ya nufa.
********
What? Kika ba wannan mugun jinin ki? Inji zaineema da ta tsani Mu'ammar don Islah ta gaya mata waye Mu'ammar a gareta, Islah tace Eh zaineema, he was running outof Blood, nd kuma ba inda ba a nema O- ba, ba a samu ba, so i helped, Zaineema xatayi magana sukaji ana kwankwasa kofar, islah ta tashi ta bude, ganinshi tsaye ya sa ta mamaki, a ranta tace wato ya warke kenan? Islah nagode, Allah ya saka miki da Alheri, naji dadi sosai, haka ake so ka zama mai yafiya idan aka maka abu, dis shows dat u'v forgiven me, dakatar dashi tayi ta hanyar daga mai hannu, tace haka mukayi da kai? Kar ka ga na maka donating blood ya sa ka fara jin dadi, ko ka yi tunanin na mance abun da ka mun, to ka sani har yanzu ina jin haushinka, har yanzu ban son ganinka, har yanzu na tsaneka, it doesnt change anything. taimakon ka kawai nayi, ko ba kai ba naga wani na neman taimakona na zan bashi, don na gaji taimako wurin Kakata, Islah me zanyi ki yafe min? Wallahi na kamu da sonki, ta tabe bakih tace shisa ake so idan mutum zaiyi abu ya dinga tunanin abunda zai faru Gaba, dubeka yanzu u look miserable, u left me Ya Amar, yace M here now, tace too late, ka koma gurin hanifar ka, yace haba Islah ya kike magana Haka? Kar ki manta hanifa matar wani ce, ba kyau, islah ta tabe bakih, tace ka manta soyayyarku? Har shan jinin juna kukayi saboda shaukin so, Amar yace kar ki maida hannun agogo baya, ni da hanifa mun zama history, Hanifa mace ce, ta dade da zubar da wannan digon jinin months ago gurin period dinta, nd u knw wat matters d most now? I hav ur blood running through my veins, shine abunda yafi muhimmanci gareni a yanzu.
_Bibilicious Biebee_
5⃣5⃣ 🏡Gidan Gandu🏠 by 💕Biebee Isa💕DonAllah Islah ki bani wani chance, wallahi ba zakiyi nadama ba, We'll start afresh, we'll build our home, a new life here, saboda karatunki m willing na xauna a nan har sai kin kammala, i wont cut u off, jus gimme ds one chance, Islah ta kalleshi galala, tace ba ka da abun da zaka ce min, ta shige ciki tare da banko kofah. Ran Mu'ammar in yayi dubu ya baci, ya zaayi ya tsaya yarinya kamar Islah ta dinga wulakanta shi? Amma kuma be kamata ya ji haushi ba don laifi ya mata take hukuntashi, but Dole zai koma Naija cikin week dinnan, don ya san Tsoho kadai ne zai daidaita tsakaninsu, amma ta ya zaije ya samu tsoho da wannan zancen? Da wani ido zai kalli Tsoho? Ai ido da kunya, but InshaAllah zai kokarta ya je dai cikin satin nan.
******
Islah ina tunanin abunda kike ma Ya'amar is too much, wlh naga yayi nadama, har ya fara ban tausayi, kinsan wani bazai taking nonesense dinki ba, amma shi tunda ya san shine me laifi nd he wants to make it up for u, beyi fushi ba, amma shawara zan baki, ki haqura haka nan, ki zauna da mijinki ki manta da komai, Islah ta kalli qawarta zaineema, tacd Zainee what he did cant be forgiven dis soon, Zainee ta tabe bakih tace A dai bi a hankali kar garin jan Aji ajin ta tsinke, Islah tace haba dai ai wuce naaan...
Kaduna
Zaid da Maysah sukayi shirin dawowa Abuja, har bakin mota jawad ya rakosu, ya rungume Zaid ya na mai godia sosai, Zaid yace dont be silly bro, kar ka mun godian komai, Maysah tace Ya Jawad a kula min da kanwata, lalala matata ce kanwarki? Tace eh mana, na bata 11days, yace bawa ni tace ka tambayeta, ya maqe kafada kamar wani yaro ba wani, wayon yayi yawa, ya zaayi ku girmi miji kuma ku girmi mata?Zaid yayi daria, yace Kyaleshi kinji Ruma, shiga mota mu tafi kar muyi dare, ta shiga mota zaid ya ja motar suka bar haraban Asibitin, jawad na ta daga musu hannu har suka fice, shi kuma yayi hanyar Dakin da aka kwantar da Fadila.
_Bayan kwana 10_
Amal ce ta shigo dakin da basket a hannu, Jawad yace su Mummy Bonbon sai a juya a koma gida don An sallame mu, tace barka, wato kaima sunan nan ya shiga bakinka koh? Yace ehmana tunda baby haka take ce miki nima haka zan dinga ce miki, fadila na jinsu bata tanka musu ba, Amal tayi daria tace, Toh zaman me kukeyi? Eh discharge letter zaa kawo mana sai muyi ta tafia. Tace ok, suna zaune sai ga nurse tazo, Jawad yace tasa wasu attendants suzo tayasu kai kaya mota. Wata nurse ta nurse ta shigo da wheelchair, Jawad yace wannan fah? Nurse din tace na patient ne, za ta hau a kaita mota, jawad ya zabga mata harara yace matata ba gurguwa bace, we dont need it, jawad ya nade hannun rigarsa ya sabi fadila sama kamar wata baby ko kunyan Amal be ji ba yayi waje da ita, ya na tafia yana cewa baby gida zamuje kinji? Ta murguda bakih tace ai naji komai ko mallam? Yace wai idan bakiji bane sai na qara fada miki. Ta turo bakih, ya duqa yayi kissing dinta, tace ya jawad wats dis? Nan ya dan karkata ya bude back seat, yace kar ki daina murguda min bakih ki gani. Ya kalli Amal dake ta musu daria yace Hajia muje koh?tace ina zan bi wadannan fightlovers din? Kar ka damu da mota nake zan bi bayanku? Yayi daria ya bude driver seat, yace kinsan kawar taki yar rigima ce, ya dan kalli Fadila ta ko galla mai harara, yayi daria ya shiga motar.
******
Tun bayan dawowansu gida, jawad Ke kula da matarsa, har Amal tace zata samo musu mai aiki Jawad yace kar ta damh, its his duty to take care of his wife, musamman aka bashi break a gurin aiki, sun ma kori Alhaji Haladu a aiki don ana Zarginsa da Murder Case, Jawad ya na kula da fadila, ita kuwa sai Shagwaba take zuba mai san ranta, shi kuma yayi ta lallabata yana biye mata, don jin ta yake kamar jinin cikin hantarsa, A zaman da sukayi a asibiti ne ta fahimci cewa Jawad na da saukin kai, da kuma barkwanci, uwa uba ga iya Soyayayh.Wani azababben sonsa ke shigarta, har tana jin Jawad cikin ranta.
Maiduguri
Tsoho ya kura ma kofar parlornsa ido yana so ya tabbatar da idonsa ba gizau yake mishi ba, Mu'ammad da ya kasa karasowa ciki saboda kunya ya zube guiwa bibbiyu yana hawaye, Shi din ne inji Tsoho, Amar ne, tsoho ya kauda kansa gefe, da rarrafe Mu'ammar ya qaraso cikin parlorn ya kama kafaffun tsoho duka yana neman gafararsa, Tsoho ka Yafe min, na tuba, lh na tuba, ba zan sake ba, kayi min rai, Tsoho na da saurin karaya, ga shi kuma yana son jikan sa sosai, nan da nan ya ji tausayin Mu'ammar, ya dagoshi ya rungume, Amar, ba ka kyauta min ba, Amar yayi saurin daga kai, na sani tsoho, shisa nake neman gafarar ka, Tsoho yace na yafe maka. Amma ka gaya min dalilinka na barin gida, Abunda Mu'ammar ya gaya ma Islah shi ya kara gaya ma Tsoho, tsoho ya jinjina kai, yace ba kyauta ba, in banda wauta irin taka nisa da gida zne zai sa ka manta soyayyar wata kuma ka kuma fara soyayyar wata?yanzu kana sonta ita islahr?da sauri Amar yace fiye da komai tsoho, kuma gashi kafin dawowarka na tura ta karatu, Mu'ammar yace karatu har ina? Tsoho yace kusa daku chan Ingila, muammar ya jinjina kai, sam be nuna ma tsoho ya ga Islah ba ko ya san inda take ba. Tsoho yace ka tashi kaje, zanyi shawara.
Mu'ammar ya mike ya rungume tsoho yace Nagode. Ya fita, sai da yaje dakin Hajia Ama da duk sassan dakinta ya gaidasu duk suna mamakin dawowarsa da kuma sauyi da yayi na zuwa gaishe su, kafin ya shiga Sassan Umma hajja da Sassan dakinta duka ya gaishesu, suma dai mamakin Shi sukeyi. Sassan su ya nufa wato sassan hajia Babba, ba ta nan taje sunan jikar wata kawarta, A kofar parlor yayi Sallama tare da kutsawa ciki, Hanifa ce zaune kan carpet da alamun ta ji sauki kafar ta warke, da sauri ta kalli wanda ya shigo tace Yaya Mu'ammar? Murmushi ya mata a yanxu banda so na yanuwantaka, ba wani son da yake mata, ita ma din haka don ta maye gurbinsa da Zayyad, tace sannun da zuwa, yauwa Hanifa, ina mutan gidan? Wallahi sunje suna, me ya sameki a kafa? Tayi murmushi tace wlh turgudewa nayi na dan goce anma naji sauqi sosai, Allah sarki ina maigidan naki? Tace yanzu ya fita, Bilkisu ce da Suraj sukayi Sallama, Ganin Mu'ammar tsaye yasata qarasawa da gudu, oyoyo ya'amar, mu'ammar ya dagata sama yana juyawa, oyoyo lil sis i missed u, me more bro, Mu'ammar ya ajiye Bilkisu ya miqa ma Suraj hannu don suyi musabaha, suraj yayi kicinkicin da fuska, bilkisu ta mishi Alama da ido, haka dai ya daure ya bashi hannu, suja gaisa, be yarda Mu'ammar yaja shi da fira ba ya fita waje don har yanzu yana jin haushin abunda ya ma qanwarsa. Kafin kace kwabo magana ta zagaya Gidan Gandu Mu'ammar ya dawo. Da labari ya iske hajia babba a gidan suna dole ta musu sallama ta dauko hanya don ganin Jikanta..
Abuja
Sir, Senior Consultant na neman wa yanda suka gama housemanship, sakon da ya iske Zayd kenan a office dinshi Yace okay, gashi nan xuwa, ya miqe Ya nufi Conference room na meeting din Doctors, Senior Consultant na nan tsaye ya na Congratulating dinsu akan gama programme dinsu da sukayi for almost a year, zai gaisa dakai sai ka fada mishi sunanka, da aka zo kan Zaid, ya bashi hannu suka gaisa, yace i am Dr Zailani, Mutumin ya kura ma zaid ido, yana son tunano sunan, yace Dr Zailani as in Dr Zaid Zailani? Xaid ya yi murmushi yana mamakin yanda akayi ya san sunanshi Zaid, don duk asivitin dr Zailani ake kiranshi dashi, yace yes sir, Dr james yace are u married? Zaid yace yes sir, Dr yace after dis, meet me in my office, Zaid tace ok sir.
******
Zaid zaune gaban Desk din Dr James, Dr James yace Dr Zailani, ina so muyi wata magana dakai, but m not sure dai, but before dat whats d name of ur wife? Ba tarw da Zaid ya kawo komai a ransa ba yace Rumaisah Abubakr Zailani, dr james yace ohh, daman nace m not sure, sorey for d diaturbance u can go, Zaid yace no problem sir, but why dd u ask? Dr James yace 2weeks back akwai wata da tazo private hospital dina da daddare bearing d name Badiyya Zaid Zailani, Gaban zaid ya yanke ya fadi, i am familiar wth hausa names but bantaba jin irin sunayenta ba, dy are unique, shisa da kamin introducing kanka as Dr Zailani i tot she's uo wife or ur sister. Zaid da zufa ya shiga tsatsafo mai yace Dr, Me ya sameta? Was she sick? Dr ya tabe bakih, yace d girl is too arrogant she dint listen to me wen i was advicing her about HIV and AIDS, Zaid ya xaro idanuwanshi baki na rawa yace is she?? Dr James yace Yes She's HIV positive. Luuuu Zaid ya fadi sumamme.
56★Gidan Gandu by Biebee Isa
Da sauri Dr James ya tari gaban Zaid, ganin idanuwansa bude ya sashi zaton ko mutuwa yayi, ya dagoshi yaga jikinsa da nauyi, ajiyar zuciya ya dake da ya lura akwai rai jikin Xaid, sai a sannan ya lura ashe ba suma xaid yayi ba daskarewa yayi lol, fiffita ya shiga yi ma Zaid, hawaye kawai ke sunturi a idon Xayd, nan Dr ya fara zargin wani abu, ko dai badiyyar matarshi ko yaruwarsa? Ya dan kalleshi a sanyayye yace Zailani let me get u help, Dr na fita, Zaid ya sulale ya bar office din Dr James, yana hada hanya yana tangartangar kamar xai fadi ya nufi motarsa, ya ma rasa tunannin da xaiyi, ya fincika motarsa sai gida, a hanya Zaid ya sha kwalbar giya ta kai hudu, irin gudun da zaid ke shararawa ya wuce misali, fuskar shi bacin raine zallah, Allah kadai ya kawo Zaid gida lafia, be ma iya jiran megadi ya bude mai gate ba ya fito ya shige, tun daga Gate Zaid yake kwalla ma Diyya kira har ya shigo parlo, Badiyyan da yanzu tayi baqih ta rame ta ji kiran xaid agogonta ta kalla ko 1 beyi ba, lafia toh ya dawo gida yanzu? Ta miqe tazo parlo, da karfin hali tace swthrt ka dawo, tayi Yunqurin Rungumeshi, Fayau ya taske ta mari, ya qara marinta, cikin ihu tace Zaid me na maka ka tsaneni haka? Cike da takaici yace me kika man? Har kina da bakin tambayan me kika min? Ya shiga kwallo da ita ta na kuka, duka ko ta ina yake mata, da hannunsa da kafar sa, harda su nushi.
Tunda tayi parking tasan cewa gidan nan babu lafiya, da sauri ta ftp tayi cikin gida, da gudu ta qarasa ta riqo Zaid, Haba Yazayd, kayi haquri, xaid ya daddage ya ture Maysah iya kar karfinshi ta fadi kasa rajagab, ya cigaba da cin uban badiyya ta kwala ihu. Maysah bata daddara ba ta miqe ta qara nufoshi tana jan hannunshi, yana juyowa ya kamtse ta da marih, ya ja hannunta ya wurgata dakinshi, yace stay outta dis, ya dawo yana cire belt din jikinsa ko a haka ya bar badiyya ta ci duka, Zaid ya shiga laftar badiyya, a yanxu kasa kukan tayi, cikin tsawa yace ni kika cuta badiyya?ni kika shafa ma HIVand AIDS? Da sauri Badiyya ta dagi ta kalleshi, yanzu ta gane dalilin dukar nan, tana mamaki ya akayi Xaid ya gane, tayi karfin halin cewa Myzayd, kayi haquri pls, we can spend d rest of our lives together, Dr yace if we can abide by d rules we are safe, Zaid pls forgive me, we can live long, Akwai hanyar da zamu morewa rayuwa nd even have kids of our own, Ya zabga mata belt a gadon baya, ta saki ihu, Allah ya sawwaqe na, ke ki haifa man yara? Allah ya kiyaye Mazinaciya ta haifa min yaro, ni ba dan iska ba, ban taba Zina ba, Diyya tayi wani murmushi tace yes kai ba mazinaci bane, Amma kai mashayi ne a wurin Allah daya muke, so gwara ka sakko mu rufa wa juna asiri aikin gama ya gama, yau ko sai kin san kin auri mashayi dan giya wani nushin da Zayd ya ma Badiyya a baki sai da bakin ya fashe hancin ya fara habo, ya yarda belt din ya hau ruwan cikinta na SAKEKI, BADIYYA SAKI 3 sai dai kanjamau ya kashe ni da na cigaba da zama dake, ya dinga jibgarta yana nusarta ba sassauta wa,. Rumaisah ta fito da gudu fuskarta yayi jaaa, idonta cike da hawaye, ta gama jin komai, kuma idan ta bar Yazayd zai iya Badiyya, Iya karfinta ta tattaro Zaid jikinta, da qyar ta iya turashi daki ta kulle, ke zabin tsoho zo ki budeni kafin na hada dake, kizo ki budeni, Maysah ta ki kulashi, tazo gurin da Badiyya ke kwance ta na nishi sama sama, tace Aunty Badiyya Kiyi kokarin tashi na kaiki Asibiti, Badiyya ta girgiza kai na, tace pls Maysah ki yafe min, kar ki bari Zaid ya rabu danih, ba ya cikin hayyacinshi ya sakeni, Daga nesa Yace kutumar Uban da yace ba cikin hayyacina na sakeki ba, na sake ki don uwarki, ke zabin tsoho ina tausayinki idan bakixo kin budeni ba. Ke kuma badiyya na fito na iske ki wlh sai na kasheki, ki bar min gida while u still can else gawar ki xa’a fidda, da sauri Maysah tace Bakida kowa a Abuja? Badiyya tace kira min mum a waya pls, Maysah ta dauko wayyar Diyya ta kira mamar diyya ta sanar da ita diyarta ba lafiya cikin 15mins sai gashi sunzo ita da wani mutume sun kwasheta sun tafi. Allah ya raka taki gona inji maigadi.
*****
A hankali ta tura kofar a zatonta bacci yakeyi don taji shi shiru, chan ta ganshi maqale ya hada kai da guiwa sai kuka yake tayi, Maysah na kuka ta qarasa gurinshi, ta rungumeshi, a tare suka sake fashewa da kuka, cikin kuka yace Zabin tsoho tawa ta kareh, I am HIV+, banda amfani, i got married to a whore, wallahi bansan ya akayi na aureta ba, Ki ce ma su tsoho su yafe min, tawa ta qare, Gobe ki koma chan Maiduguri, da sauri ta girgiza kai tace ba inda zani, i will be right here with u, m not going to leave you, Zaid ya tureta da karfih, are u in ur ryt senses? Ko baki gane ba? Cewa nayi ina da kanjamau, tace yes na jika na gane, kana da kanjamau kuma ba zan barka ba, in yaso ka shafa min kanjamau din sai mu xauna na tare in yaso mu mutu rana daya. Zaid ya fincikota yayi hanya waje da ita ya yasar da ita a kasa, yace da alamu baki da hankali, Ya nuna ta da yatsa wat u are trying to do is a suicide, stay away frm me, ya juya daki ya sa key ya fashe da kuka…
PARIS, FRANCE
Suna isa Hotel dinsu na Paris Las Vegas Hotel suka nufa dakinsu a gajiye, ta kwanta kan gado, yazo zai fado mata tayi saurin miqewa ta bata rai, shi ko sai dariya yake mata, yadai lilsismeera? Tace wlh nagaji da yawa bigbrosamir, yau mun sha yawo, ni gaskia ba inda zamu kara fita, kullum sai fa mun fita, yace lallai kincika laziness, gashi ko _EIFFEL TOWER_ ba muje ba, tace wlh ba za mu ba, nagaji yace yarinya baki xo paris ba kenan in har ba kije eiffel tower ba, ta tabe bakih tace yo ni ina ruwana, ya janyota yace oya zo na miki massage, ya dinga mata tausa ya na bata light kiss,ya na neman wuce gona da iri ne wayarshi tayi kara, ohh shit, ita ko Amira sai dariya take mai tana gwalo, ya harareta ya dauki wayar, yace d only mistake i made was calling u da nazo paris, Suraj yayi daria, yace kai lover boy a dawo gida hakan nan, Ina zan dawo gida ga lilsis nan ta mantar dani ku, muna cin karen mu ba babbaka, suraj yayi daria yace I dont blame u kuna ParisCity of love. So ya kake ya kanwata? Samir yace gatanan ina mata massage, suraj yace kai shege nima fa ina da matana kar ka min wani Iyayi, Samir ya fashe da daria, so whats happening over there? Suraj yace so many things has happened yanzu ma haka muna Maid, Samir yace me ya faru? Is everyone okay? Da sauri Amira ta miqe ta kwace wayar a kunnen samir, tace halo Ya suraj, is everyone okay? Eh qanwata, a long lost family is back, tayi daria tace Ya Mu’ammar? Yace yes, tace finally, nd hanifa ta karya kafa, amma da sauqi, fadila kuma last2weeks Barayi suka shiga gidan su suka harbeta, Amira ta saki ihu, yace dont worry, taji sauqi itama, tace We are coming home gobe goben nan, suraj yace dont bother lil sis duka sun ji sauqi, duk sun warke, ku cigaba kawai da honeymoon dinku we are all fine, tace Aa wlh, ai hankalina yayi gida, sai munzo dai yayi daria yace gotta go kar mijinki ya zageni yace na zigaki, tsoho na kirana byebye, ka gaida minshi, to xaiji, Samir ya kalleta yace bangane zamu koma gida gobe ba?tace beht so many things happened whyl we are away, har fadila aka harba fa, ya zaro ido tace but da sauqi, bigbrosamir hankalina yayi gida, i want to go home, i just want to see for myself everyone is ok, in yaso daga baya sai mu dawo, pls yasamir, ya rungumeta yace anything for u my love, Gobe zanje naga if its possible mu koma gida a goben, if not sai na sake mana processing tafiar tayi tsalle ta rungumeshi tare da bashi hottkiss tace i love u bigbrosamir yace love u too lilsismeera.
Maiduguri
Baba Hassan,Hussaini da baba Gambo, Baba Mudassir da Baba labaran da Baba Umar a gefe, Mu’ammar zaune a kasa kanshi a kasa, jikinshi yayi sanyi matuqa ya na jiran hukuncin da zai yanke game dashi. Tsoho yayi gyaran murya yace Mu’ammar, na yi shawara da iyayenka gasu nan. Suraj yayi sallama duk suka amsa mai, Tsoho yace yauwa surajo kaima zauna, jikin suraj yayi sanyi don yasan taron nan na Islahulkhair ne, ya samu guri ya zauna kusa da Mu’ammar. Tsoho yace madallah. Yauwa kamar yanda nake ce maka Mu’ammar, na yanke hukunci akan ku kai da Islahulkhair, a komai da zanyi ina kokari na kamanta adalci tsakaninku kar daya da ga cikinku yace an kwareshi ko ba a kyauta mai ba, tafiar da kayi ka kware Islah, ka shiga hakkinta, a yanzu kuma ba zan yarda a qara shiga hakkinta ba, Suraj kafin tafiar Islah sai da muka yi yarjejeniya da ku cewa idan Mu’ammar ya dawo to karatun Islah a kasashen waje zai tsaya, ko da final exams zata rubuta, haka ne?suraj ya hadiye miyau yace haka ne Tsoho, tsoho yace to madallah, idan aka ma Islah haka an qara shiga hakkinta, ba wai na janye wannan batun bane, don Gobe ma nakeso ka fara shirin tafiarka Ingila zakaje ka taho min da Islah kagane? Suraj ya gyada kai cikin rashin dadi eh nagane. Ya kalli Mu’ammar yace Islah zata cigaba da zama matarka bisa sharadi, Mu’ammar ya dago da sauri tsoso yace eh sharadin kuwa shine Sai ta yarda da kanta cewa Zata cigaba da zama da kai a matsayin mijinta, idan bata amince ba dole zan raba Aurenku, kuma ta koma ta cigaba da karatunta, Mu’ammar ya kalli tsoho cikin tashin Hankali..
0 comments:
Post a Comment