Page_1_2
Inama Allah godiya da ya nunaman nafara wannan Book din lafiya,Allah ya nunaman na gamashi lafiya.Ameen
Godiya ta mussam gareki Aunty Nabeelart lady Allah yabar zumunci.Ameen
Bissimillah Rahmanir Rahim.
DEDICATED TO.....MY SISTERS.
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
-----------Subhanallah Matii me ya faru?? Na fadi hakan a cikin tsoro!!
Kallona yayi yace "yar gidan liman kiyi hakuri yau ma motar ta samu matsala " nayi ajiyar zuciya na kalli mutanen dake a cikin motar,kowa sabgar gaban shi yake, daga mai shan rake sai mai cin kosai sai mai rike da biredi.
Walkiya naga ana yi gashi motar a bude take,ga hadari dake haduwa.
Matii dan Allah zaka isa kauyan mu??
"Kiyi hakuri yar gidan liman bazan samu isa chan ba iyaka ta nan saboda babu yan kauyan ku a cikin motar ke kaɗai ce"
Hawaye ya cika idona ganin zai zubo nayi saurin daukar fanteka ta da gammona,daman gefe nike na dire " Mati yace ba zaki jiraba na ida? "nace a'a hadari ke akwai a garin na mika mashi Murtala biyu "yace nagode kiyi ratse ta cikin gonakai yanzu zaki kai "nace to.
Yan Matan cikin motar su kallona suke sai suka kwashe da dariya,na juya na kallesu cikin bacin rai "nan naga wata na nunani wai taje kauyan mu biki ta ganni duk kauyan mu bamai sona guduna ake "shine suke dariya mai bakin jini "na kalleta kamar nasanta??Nan na tuno kawar Ma'u ce kenan Ma'u ta Fadi mata.
Ganin hawayen dake makale zasu zubo,yasa nayi saurin barin wajen.
Tafiya nike ina goge hawayen dake bin fuskata,bana ganin gabana tafiya nike cikin gonakai,sauri nike harda dan gudu,walkiya ake hakan yasani jin tsoro ga duhu sai kara sakkowa yake gari na baki.
Gashi babu ko fitila a tare dani.
Ina cikin tafiya ruwa ya sakko,kasancewa cikin daji nike ga dare babu wajen fakewa hakan yasa na kara azama.
Koda na shigo kauyen mu,ruwa ya dauke nayi ajiyar zuciya nace Alhamdulillah tunda na iso lafiya.
Jikakken Hijab dina na jawo na dan rufe fuskata saboda gudun kada wani ya ganni,da naga ana haskani saina boye,har na isa gidan mu.
A hankali nayi sallamar, Subhanallah!!
Na ambata tare da dafe girji "Bakar munafuka mai bakin halii jinin tsiya da bakin jini shigo yau ni naga sheɗaniya kenan??"
A hankali na iso inda take "Barikin naki har ya kai ki da kikai dare haka "Wallahi Innah wallahi tallahi kinsan kullun sai motar Matii ta lalace yauma lalacewa tayi a kafa na taho tun daga Tudu kinga ma ruwa ya jikeni.
Kallona take tun daga sama har kasa "tace inma gaskiya kika fada matsalar ki dan kin kwaso shege ai ba komai bane tunda kema shegiyar ce"
Kuka ya kuɓuce man "tace kukan mi zaki yi sharri nayi makii?? Ke ba shegiya bace idan ba shegiya bace fadaman uwar ki da ubanki a garin nan? Malam fa a chan wajen yawon shi ya tsinto ki dadin bakin banza ne da yake ce maki diyar shi har yana fifitaki akan jinin shi "kuka nike sosai wai mizan ma matar nan na samu sauki wajenta??
"Assalamu Alaikum "muryar Baban mu naji,cikin sauri na juya tare da jin dadi nayi saurin goge hawayen dake bin fuskata duk da dare ne,Amman akwai fitila a hannun shi.
Tace mik'o man kudin nace.
Na warware gefen zanena na kwance daurin na mika mata kudin, dai-dai lokacin da ya iso wajena.
"Subhanalillah "ya ambata yace ke yaushe kika fita ina kika je ruwa ya dokeki haka??
"Kallo yabi Innah dashi yace "ba nace kibar aza mata tallah ba?? Kuma tallah har ta wuce cikin kauyan nan da kauyu kan kusa damu har Katsina,ina laifin konan tashar Ado takai ai za'a saya,diya mace ce kuma zamani ya sauya yaran binnin ynxn basu da tarbiya sam ga karancin kunya,idan ta kwaso wa'innan halayyan fa,kuma acikin maza zata zauna akwai hadari sosai mata cikin maza hakan yake sa mace karancin kunya "ni dai dukar da kai nayi ga kyar mar sanyi inayi.
Kuka Innah ta aza "yanzu Malam duk abinda nike ma diyar nan baka ganii? Yanzu fa fada nike mata ta kai dare wannan wace irin tallah ce har dare "lallema Innah Rakiya gori fa ta gama yi man ,amman ta chanza magana.
"Yace ba haka nike nufi ba "tace kai dai kawai dan ba Ma'u bace ita da na haifa cikin cikina "Baba yace ya isa haka muje yace danii.
Nabi bayan shi ya bani fitilar hannun shi .
Dakina na shiga cikin sauri na jawo buhun da nike saka kayana,na dauki wasu riga da zani na saka naga zanen duk ya kode ba kamar rigar ba kallon su nike,ni da Ma'u ke da atamfar masaya tayi man kenan, kuma idan nayi magana a zageni har da duka tunda ubanta ya ɗin ka.
Na saka rigar taman yawa saboda Ma'u ta fini kiba,amman tsawan mu guda.
Na cire su, dama su kaɗai ne da basu yage ba a cikin kayan nawa sai na jikina da suka jike.
Haka nan na hada riga daban zane daban.
Baba ne ya shigo da kaskon wuta a hannu.
Nayi saurin mikewa na amsa nace sannu Baba "yace yawwa Nana bari na kawo maki abinci "na daga kai.
Jim kadan sai gashi da abinci nasan na shine dan kusan kullun abincin shi nike ci ba zai ci abinci ba sai naci hakan ya kara wutar kiyayya tsakanina da Ma'u da Inna.
Ya aje a gabana "kici nasan kina jin yunwa " jikina har kyarma yake saboda yunwa,na saka hannu ina ci har na gama ya mik'o man ruwa.
Baba!!
Jin yadda na kira sunan yasa yayi saurin ɗagowa.
Nace Baba wai menene sunana kaga *NANA* laƙabi ne kamar Nanah Fatima,khadiya,Maryam,Aisha,kaga kamar Ma'u Nana Asma'u ina son na sani ko dan koyi da mai sunana.
Shiru yayi har na wasu lokutta.
Ganin yadda fuskar sa ta chanza yasa nayi saurin cewa yi hakuri Baba bazan karama wannan tambayar ba.
"Babu komi yace,idan kin gama ki iskeni daki da littattafan ki ya kamata nayi maki sadaka idan kin gama Bulugul marram kuma nayi maki kyauta,sannan akwai tambayoyin da zan maki a cikin iziyyah "na ɗaga kai.
Shiru nayi ina tunanin bazan kara tambayar mahaifina sunana ba zan cigaba da amsa NANA amman naso nasan sunana,nace kila saina kara girma kana ya fada man , nasan Baba mutun ne mai ilimi zai sa man suna mai ma'ana.
Lumshe ido nayi ina tunanin maganar wani malami cikin littafin sa,idan yace *Ana sanin* *mahaifin ka da sunanka* sauri nayi na mike na shiga Bandaki nafito nayi alwala.
Bayan nagama sallah na dauki jikata nayi dakin Baba nace yau sanyi ya hanamu karatu a zaure kenan.
Sallama nayi ya bani izinin shigowa na shiga na iske Ma'u yana mata fada,muka hada ido ta wurgo man harara,na samu gefen ta na zauna.
"Yace haka kika ga yar uwar ki nayi?? Idan zata shigo sai na bata izini sannan yau insha Allah zata gama Bulugul marram a cikin babi na karshe take "ya dago ya kalleni yace koba a zikiru waddu'a'i kike ba "na daga kai.
"Yace amman ke har yanzu arba'una kike shima har yau ba kiyi rabi ba "cikin hadisi arba'in,yar uwar ki nada sama da Hadisi dubu biyu littafin Hadisi nawa ne a kanta ba zaki iya lissafawa ba.
Ran Baba ya baci sosai yadda yake mata fada kamar zaiyi kuka.
Kuma dan naje dakin Mahaifiyar ki nace kizo muyi karatu shine zaki banko man daki har kofata ta cire to da a kaina ta faɗo fa?
Sai a lokacin naga babu kyauren dakin.
"Yace buda inda kike kuma kibiya na jiya ko kuma naimaki yadda na saba kullun sai an maidoki baya "ta bude tana tura baki"
Kallon Ma'u nike nima ta so saman rai saboda yadda takema Baba kullun sai ranshi ya baci inde zamuyi karatun "Tace na manta "shiru yayi yana kallon ta "yace ba nace kije yar uwar ki ta ringa koya maki ba?? "tace Allah ya kyau amman bai ji ba.
Ta kalleni ta wurga mani harara kamar idon ta zai faɗo, kana tace "Batanan tallah take zuwa kuma sai dare take dawowa "yace kefa??
Kai tsaye tace "Niban tallah" shiru nan ma yayi ya girgiza kai.
Ya biya mata kana na bude ya ida biya man nawa, yayi addu'a yace yanzu tunda kin gama wannan kuma kinyi mukkutarur hadis kuma kinyi Riyadus salihin yanzu saura muwadda imam Malik.
"Ma'u ce ta mike a fusace ta fita "yabita da kallo ya safke a jiyar zuciya.
Ya gama yi man tambayoyi muka yi sallama.
Duk da maganganun Inna naman ciwo akan cewa ba Baba ya haifeni ba wai ni yar Zina ce shiyasa duk garin nan babu mai Sona.
Shiru nayi ina tunanin maganar ta zata iya zama gaskiya,amman kuma kullun Baba sai yace ni ne na haife ki shiyasa nafi kowa sonki,son da Baba ke man idan bashi ya haifeni ba bazai man wannan son ba.
Amman kuma banda dangi amman shima Baba ai ba dan nan bane Inna kawai ce yar nan.
Toko minene gaskiyar labarin??
*************
Zaune yake a cikin wasu Royal din kujeru Milk colour ya lumshe ido jin karar tafiya yasa ya bude runan nun idon shi da suka kada suka yi jawur tamkar garwashi.
"Asslamu Alaikum" a hankali ya bude idon shi cikin wata kasalalliyar murya marar sauti ya amsa ya kalli mutumin nan yace.
Please Dad help me!!
Bayan ya zauna ya kama hannun shi "yace *Annuwar* mike damunka?"
Dad Abie ne yayi maganar tamkar zaiyi kuka "Abie? "wayar shi tayi kara yasa hannu ya ɗaga, bayan sun gaisa sun dade suna waya shi dai Dad hakuri yake badawa.
Bayan sun gama ya kalli Annuwar yace "Mai Martaba ya fada man komi yanzu kaine baka da gaskiya "Dad wallahi bazan iya son wata mace ba bayan Princess.
Shiru Dad yayi nawani lokaci"haba Annuwar ya kamata kamanta da ita yarinyar da tadade da rasuwa"wallahi Dady bata mutuba"Dady yace a tareda kai muka kalli videon da suka aiko inda suke chaka mata wuka"sai kuma yayi shiru saboda yadda shima abin ya soshi ranshi.
Kayi hakuri kaje wajen Kursim yarinyar mahaifin ta nada kirki kuma tana sonka kayi hakuri kaje Katsina gobe.
Dady daman kaima dake goyan bayana a koda yaushe yau kuma kabi bayan Mai martaba Why Dad??
Ba haka bane inason ka bazanyi abinda zai zamo maka takura ba ko cutar wa, shekarun ka ya kamata ace kanada iyali Mai martaba yana cikin damuwa dalilin rashin iyali,magana ake a garifa ana cewa shiyasa baka zama kasar kowa da abinda yake cewa a kan ka,a shekarun ka ace bakada iyali kaga dole a zarge ka shi kuma Mai martaba dole abin ya dameshi.
Shiru yayi bau magana ba Dady yasan halinshi shiyasa bai damuba dan yasan bazai yi magana ba.
"Yace yanzu bari naje na kwanta dare yayi zuwa gobe zanje dakaina bama maganar waya ba akan ya karama lokaci ku faminci juna kaida yarinyar"sai a lokacin ya kalli Dady yayi murmushi"Murmushi Dady yayi shikade yasan halin dan nasa tunyana primary yake tareda shi har zuwa yanzu.
Fita yayi shi kuma ya mike ya nufi bedroom dinshi zama yayi bakin bed dinshi yana bin photunan su da kallo murmushi yayi yace banji a jikina baki cikin wannan duniyar ba.
Tashi yayi yaje bakin window yana kallon cikin Villah mtsww yayi tsoki yace duk akan wannan mulkin narasaki.
Kunnen shi yayi saurin rufewa tareda da idonshi.
**********
Asuba nayi na mike naje na zubama kowa ruwa a butarsa nayo alwala nayi sallah bayan nagama addu'a sai kuma na mike naje nakaima tumakin Inna abinci na share wajen,na cika ko ina da ruwan rijiyar dake tsakar gidan mu.
Ma'u ta fito tana mika tareda hamma tasa kafa ta ture ruwan butar dana zuba mata.
Ina hada wanke wanke ta iskeni babu magana ta mikoman buta nace mizan yi da ita??
Kallon banza tayiman tace"ruwa zaki saman saboda ban alwala da ruwan sama sanyi garesu"zanyi magana Inna ta fito daga daki ta tsaya tana bina da mugun kallo"tace idan bakiyi yadda nace kamar yadda kikayi dalilin zubar hawayen ta jiya da daddare kema yanzu zaki zudda naki"na amsa na mike naje na jawo mata ruwa na mika mata.
"Ta harareni tayi gaba"na koma na zukunna ina aiki.
Alwallah take amman ba ruwanta da hagu ko dama,shiru nayi ina wani tunani wai nan yar Liman ce, gidan karatu take,tosu sauran matan garin fa ya suke ibadar su??
Inama zasu yadda su daukeni nima tamkar diya irinsu,danashiga na koya masu yadda zasuyi ibadar su,Ma'u a cikin abokanta tafi kowa ilimi haka a garin tafi kowa ilimi shiyasa dan Mai Gari kesonta.
Kaf naji anjefoman buta nayi firgigi!!
"Kada kicinye man diya bakar mayya kallon ya isa haka"ashefa Ma'u nike kallo ina duk wannan tunanin.
Cikin sauri na Ida ta mike tace"ga buhu chan Yau ma zogala zaki dafa dan ta kawo kudii jiya buhu biyu zakiyi harda Rama zaki debo gonar Baban ku ta gefen gari"Jim nayi Ina tunanin dauko buhu biyu akwai wahala"cikin tsawa tace koba zakijeba ne!!"nayi saurin dauka nafita.
Yauma ratse na kamayi banson shiga mutane dan gudun wulakan ci.
Ina isa na iske su Shatu suna wasa kawata ce bafulatana ce ga gonar su gata Baba kuma tare muke tallah ita nono ni kuma fura, baban su yanada mutunci shiyasa suke mutunci da Baba rugar su babu nisa.
"Tace lah Nana"duk duniya bayan Baba dakeso na sai ita kade ta taba nunaman soyayya shiyasa nikesonta"baki na washe nace Shatu mai nono"tace yau ban fita tallah kiwo nazo"nayi murmushi"tace muje na tayaki"tare muka dibi Zogalan da Rama,koda muka gama mungaji bakin wata bishiya muka zauna cikin gonarsu ga rana ta tafara dan goma ta kusa,kosai ta mikoman"tace gashi mucii dazun jabe ya siyoman shi a kauyan ku"na amsa naci taban ruwa nasha najini dai-dai.
Nace bari naje kada na makara zan gyara zogalan tallah zan fita"tace muje na kama maki tunda jabe na wajen shanun"Nace lah barshi na gode"tace wallahi sainaje cikin Hausar ta dabata fita,na dauki guda ta dau guda,muna tafiya muna fira har muka isa bakin kofar gidan mu,tace bata shiga nace ai nagode saboda nasan dalili.
************
A hankali ya bude idonshi jin ana huramashi ido, kan fuskar wata yar matashiyar budurwa ya sabke idonshi wadda shekarunta zasu kai goma sha biyar itada kanenta shima zai kai shekara sha biyu,dariya suke ganin ya bata fuska yasa suka kalli juna,sai suka kama kunan su cikin shagwaba suke"ohh sorry Broth Annuwar Dad ne yace kafito ayi Breakfast dakai Momy ma is waiting for you.
Hannu ya daga su duka sukabar wajen.
Kallon yakai akan photunan dake kusa dashi daya ya dauka shida wata yar yarinya jikin photun zatakai shekara tara,kiss yakai a saitin fuskar ta yace I love you My princess.
Toilet yanufa yayi wanka yazo ya shirya cikin kananun kaya ya fito.
A parlon Momy ya iskesu"Dad yace tahonan My Son"kusa da kujerar Dady ya zauna suka gaisa da Momy yamaida kallon sa ga Dady suka gaisa daga haka baice komi,abinci aka zuba mashi kalar wanda akasan yana chii.
Bayan sun gama har ya mike"Momy tace Anty Amina tana bukatar magana dakai tace kakirata"kai ya daga ya juya"tace Annuwar yau Momyn ce kake fushi da ita??
Juyowa yayi sai kuma ya tsaya"tashi tayi ta iskeshi inda yake tsaye"Dady yace inada meeting zamuyi magana anjima,shima ya fita.
Kamashi tayi suka shiga Bedroom din ta zaunar dashi.
Yace Momy please kinsan banason hayaniyya banason ayima rayuwata kutse,miyasa lokaci guda ku duka zaku juyaman baya saboda Kursim??
Inason nayi rayuwata batareda an takura man itaba inason na zauna nikade.
Shiru tayi tace"kayi hakuri Anty tace ka budewa wayar ka kuyi magana amman kayi kokarin cire MANAL a zuciyar ka"jin jina kai yayi ya wuce.
A parlo ya zauna ya runtse idoo yana tunanin tayaya zai cire Manal a ransa??
Miyasa gabana ke faduwa a duk lokacin da aka ambaci Katsina???
Qurrah
Share and comment plx
[1/28, 3:02 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*
*Writing by-* *Qurrah*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
DEDICATED TO...MY SISTERS😘
Page-3&4
*~Abin Da Ake Fada idan aka firgita~*
لاَ إِلَهَ إِلاَّ الله
La ilaha illal-lah
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.
-----------------Innahlillah kawai yake ambata, saboda yadda zuciyar shi ke bugawa akai-akai.
Wayar sa ya kunna, yana kunnawa sunan Abie ya bayyana yana kiran shi, har ta kusa tsinkewa ya kasa dauka, sai chan yayi saurin dauka yayi sallama, dayan bangaren Abie yace, "Yarima me kake nufii dani, na zama karamin mutum nace za kazo yau shi ne ka koma Abuja!?".
"Abie kayi haku.....!!".
Tsawar da Mai martaba yayi yasa Yarima toshe kunnenshi, daman Bluetooth ne a kunnen shi da shi yake waya. Runtse ido yayi yana jin zafi a zuciyar shi, wannan wace irin Jarabta ce yake so ya shiga tsakanin shi da Abie har da tsawa.
Yau ita ce tsawa ta farko a tsakanin su, kullum Abie cikin tattalin shi yake da nuna so da kauna.
Kashe waya Abie yayi, Annuwar yayi zaune bakin gado wani irin zafi mai radadi yake ji a zuciyar shi, maimakon ya saduda sai ma kara tsanar Kursim da yayi a zuciyar shi.
Maimakon sati daya, mai martaba ya maidashi wata daya a Katsina, ta yaya zan zauna inda ban sani ba har tsawon wata daya??
Gashi na tsani garin, koya aka ambaci Katsina sai naji wani irin faduwar gaba.
****************
"Wash!", nace tare da zama ina lumshe ido, na gaji sosai. Inna ce ta fito tace, "zaman mie kike anan??".
Nace; "Na gaji ne Inna".
"kin gaji inma dan dumamen da nayi kike mawa to ki daina, dan an cinye idan kin dafa zogala zan dan dan maki, shi ma dan kiji karfin yin tallah".
Na mike na samu wani buhu na joluye zogalan na gyara.
Koda na safke zogalan rana tayi nace Inna zanyi wanka, "tace wanka kuma? daman neman maza kike zuwa ba tallah ba?? shi yasa kike saidawa"!.
Nace, "wallahi Inna masu saye sunfi son mai tsafta, shi yasa ake sayen nawa da wuri".
Tsaki tayi tace, "sai kiyi sauri dan a kasa zaki, banda kudin mota". Ido na zaro cikin mamaki. "Kas.....?!!".
Kallon da tayi min yasa na kasa ida maganar, nayi saurin daukar bokiti nayi bandaki, ina fitowa naje daki na shafa mai, d'an sauran turaren da Yaya Maimuna ta kawo min na balle inda ake sawa na goge ga kayana, sunsunawa nayi na lumshe ido a duniya Ina matukar son kamshi yana sani farin ciki,Yaya Maimuna ita ce Babba wajen Inna, sai Yaya Auwalu dake neman kudi Abuja, ita Kuma Manii take aure duk zata zo turare shi ne tsarabar mu, amman Inna bata sani ba ta dade bata haihu ba sai akan Ma'u, shi yasa duk wani tanadin ta Ma'u dai komi.
Na mike na saka silifas dina da suka sha wanki suma sunyi tas.
Na fito ta miko min Fantekar zogala tace. "ki dauki ashirin kici abinchi salan ki batar man da kudii".
Nace, "wallahi Inna akwai nisa zuwa Katsina, dan Allah kiban ko na ragin hanya ne".
"Lallai ma yarinyar nan, ni zaki fada ma nisan Katsina, ba'a ba BATAGARAWA kuke tallah ba yaushe kuka shiga Katsina?? to bari kiji daga Yau kasa zaki dawo kuma ai ba cikin gari kuke shiga ba ba iyakar ku nan bakin titi ba?? Bace min da gani!".
Na nada gammo na aza fantekar, ga nauyin kaya ga tafiya ga gajiyar aikin gida, lallai kam, kowa ne bawa da kalar tasa Jarabta ni kuma matar uba, na juya nazo fita muka yi karo da Ma'u saura kadan na saki fantekar zogalan.
"Wayyo Allah Innan mu ta kona ni, ashe zogalan bai huce ba ta aza min fanteka a goshi. "nace amman Ma'u baki son gaskiya".
Inna na zuwa ta wanka min mari tace, "yar bakin ciki fuskar tata zaki kone, toh ta Allah ba taki ba!". Ma'u tace cikin kuka, "daman tace sai ta rabani da Kabiru na shi ne zata kone min fuska dan ya bar ganin kyau na". Fantekar dake kaina Inna ta sabke ta fara Jibga ta kamar kayan wanki tana cewa, "yanzu bakin ciki kike min na zama sirikar dan Mai garii?? Shegiya ai gara na kashe ki damu rasa Kabiru, gidan sarautar kike ma bakin ciki kuma sai ta shiga".
Ko da ta sakeni na wahala tace, "tashi ki tafi sai kinje tallar".
Saboda wahala idona har rufewa yake gashi ta fasa min jiki inda ta bugan da takalmi.
Da kyar na aza fantekar bisa kaina, takalmina daya ya tsinke haka nasa shi na fito ina kama bango.
Babu mai sona a cikin garin yanzu, daban ratse ma mutane ba duk inda na wuce sai ace shegiya ce, malam ya tsinto ko ya yima wata ciki, tunda shi kullum cikin yawo yake,wani yace;
"Amma yarinyar tana ban tausayi sai nayi wata shidda ban gan ta ba saboda bata shiga jama'a", dayan yace, "to wai ya aka yi aka san ita shegiya ce??".
"Matar shi ya fada ma wa, ka san wasu matan ba rufin asiri, ita kuma ta barbada gari". Duk da banda kuzari amman na kagara n abar wajen, sai wani daman diyan zina ance kyau garesu ga shedanan.
Ina wuce su duk inda na gifta da kalar nasu zancan, wasu kuma sai suce Liman bazai iya aikatawa ba sharrin matane, saboda kishi yasa take cewa haka.
Ina fita gari na samu wata bishiya na zauna saboda kaya da suka shigan man cikin kafa, ga kaina na wani irin zafi har cikin kwanyata, ga jikina wani wuri duk ya fashe zafi ta ko Ina, gashi yau garin zafi ake yi ga rana.
Wai daman haka rashin galihu yake?! Ina ma zan samu wanda zai ce yana sona nabar masu gidan su, kai hadda garin ma yanzu banda madafa sai Allah, ya Allah kayi mini magani.
Zafi tako ina nike ji, hawaye nake yi masu zafi, shin wacece ni, nima diya ce kamar saura??
Wannan wace irin duniya ce nake ciki, kayar data shige min cikin kafa duk na fidda, kana na samu leda na daure takalmi na.
Ganin an kusa a zuhur kuma Ina hangen kauyan mu yasa nayi saurin mikewa, ji nayi jikina yayi min nauyi hakanan na aza Fantekar a kaina, na fara tafiya kamar zan fadi, ina cije lebe ina runtse ido, juya wa nayi saboda kukan shanu da naji. "lah Nana!". Inji jabe dan gidan su Shatu"da kyar na dago kai nayi murmushi, "ina zaki haka jikin ki duk ciwo?".
Nace, "Katsina zanje nan BATAGARAWA kamin ka shiga cikin gari inda motocin garin mu ke tsayawa".
Yace, "Amma dai ba'a kasa ko? Me yasa baki hau babur ba? Gashi duk jikin ki da ciwuka".
Nace Jabe taimaka man ka sauke min fantekar nan, faduwa zan yi".
Cikin sauri ya sauko daga bisa amalanken shanun su, yana sabluke min naji kaina ya rike saboda nauyi"yace muje kihau Amalanken na taimaka maki bari na gyara buhun hunan ciki"na daga kai.
A ciki na zauna shi kuma yana jan Amalanken na dukar da kaina ina hawaye,inama ba'a haifeni ba a cikin duniyar nan.
**************
A hankali yake tafiyar har ya iso inda Momy ke zaune"tace Prince ina zuwa nagan ka cikin shigar manyan kaya?gashi Dadyn ku yana Meeting"zanje naga Abie.
"Zo nan!", tace tare da da nuna kusa da ita,"kallonshi take, bayan ya zauna cike da kauna da tausayi tace;
"kayi hakuri, ko wane dan Adam yana da tashi jarabawa mu kuma wannan ita ce tamu Jarabtar, kayi hakuri ka amshi Kursim a matsayin Manal, ko dan lafiyar Mai martaba, ka tausaya ma Anty Amina hakuri take amman abun na damunta, dan bata da yadda za tayi, kuma yarinyar za kaji dadin zama da ita, Lawyer ce ta mallaki hankalin kanta, kaga tana da dubaru kalar nasu na Lawyers ta san yadda zata zauna dakai, haka Dadyn ka zaiyi farin ciki nima haka".
Shiru yayi sai kuma ya kalleta yayi murmushi tare da daga kai alamar aminta.
Nifra ce ta shigo falon cikin wasu hadadun riga da wando rigar kayan kamar Suit Amman ba Suit bane.takalman ta Pink wasu higher hill masu belt ta daure kafar ta dasu sai stones din su Blact yalwataccen gashin kanta ta kamashi waje daya ya sabko har a kafa darta wani kalar hulane akan ta.
Kallo daya Annuwar yayi mata ya dauke kai.
"Momy zanje na dawo yanzu", tace amman kin san idan kuna Nigeria baku fita ko??".
"Momy daga ni sai driver zan fita bana bukatar jiniyya".
"kina hauka ne??".
"Baza ki fita ko ina ba bace min dagami".
"Please Yaya Anu said something mana".
Momy bari mufita tare zanje airport sai akaita inda zata amman ko One hour ban yadda kiyi ba".
Momy tace, "to shikenan", tsalle Nifra tayi tare da rungume Annuwar tare da manna mashi kiss a kumatu"thank you so much Broth!", raba ta yayi daga jikinshi yayi gaba tabi bayan shi.
Suna fitowa security suka rufa masu baya, motar Soja uku gaba uku baya haka suka sasu tsakiyya.
*************
Ranar dake bugun gadon bayana hakan yasa jikina naji kamar ana tsikarina, na dago daga duken da nike.
Muna kaiwa yace; "Nanah munzo", nace to jabe na nagode ina gaida Shatu".
"Zata ji yau ita kiywo ta tafi bata tallah yau sai dai gobe".
Nace, "to shikenan nagode".
Na aje fantekata inda na saba zama ni da Shatu duk sai naji babu dadi ni kadai haka jiyama ni kadai yauma.
Dan danan zogalata ta kare koda yamma tayi har na saida,na isa inda zan hau mota,sai kuma na tuna Inna tace kasa zan dawo,na juya Matii yace"yar gidan Liman mantuwa kikayi ne da zaki koma"nace a'a zanje a kafa akwai ganyen da zan dibar ma Innata a bisa hanya,yace "amman ai kwai nisa daganan kizo ko tudu na kaiki sai ki ida"nace kayi hakuri Matii yau banda kudin mota"shiru yayi yana kallona sai kuma yace bakomi muje daga yau zan dunga daukar ki inde nazo wannan tashar"nace to nagode.
Na kama na hau yauma gefe na zauna kamar kullun,bana shiga cikin yan matan Tudu,daman sunfi na kauyan mu rashin kunya.
Yauma su kade suka kama habaicin su,yau basu san ban koda lokacin su zafi da radadin da jikina keman sun isheni,zafi har cikin kaina,muna isa Tudu na sabka naje nayima Matii godiya yace bakomi,yima kaine,duk na ina cikin wahala amman naji dadin taimakon shi,saboda bainuna kyama taba,kuma dan garin mune yasan komi a kaina Amman Tudu yake zaune dan tafi kauyen mu,kauyan mu ko hanyar Mota babu saide ka yanki daji da Mota amman Tudu akwai hanyar Mota kuma sukeda Kansila.
Sauri nike cikin daji babu kowa sai karar tsuntsaye,haka naita ratse a cikin gonaki har na isa.
Ina shiga duhu ya fara sabkowa nayi sauri nabi ta baya na nufi gida.
Gabana na faduwa nayi sallama.
Baba na iske cikin gida tsaye shida Inna yana fada.
"Alhamdulillah"shine abinda ya fito daga bakin Baba"yace sannu Nana kindawo kiyi hakuri nafita ban fadi maki ba daga salar asuba na wuce wani kauye chan gabashin mu dan nasamo mashi wani magani akwai nisa shiyasa daga masallaci na wuce"nace ba komi Baba andawo lafiya??
Kallo ya bini dashi.
"Me nake gani a fuskar ki kamar sawon hannu??".
Nace; "umm daman...".
"Ai ko kila faduwa tayi fuskarta ta bugu".
Cewar innah. Nace, "eh daman dazun na buge".
"Allah ya sawaka".
Yace, daga haka bai ce komai ba. Yace, "tafi kiyi sallah sai ki aza maganin a tukunya??".
Innah tace, "Amman dai ai lafiyar ta kalau daman akwai maganin karin lafiya da baka yar kin taka ba".
Kallon ta yayi yace, "amman kinsan tana da rauni a cikin cikin ta ko".
Amman Malam shekara nawa da wannan rauni kuma bai taba tashi ba??".
Baiyi magana ba ya bar wajen.
"Miko min kudina".
Na warware zani na na bata, tace, "malam ya biyo ta gona yace na debe mashi Zogala dan haka yanzu Fura zamu yi, kwana biyu har ya tuho. "to nace tare da tunanin kirbin fura gobe ga jikina yayi tsami ko Ina ciwo yake min.
Alwala nayi tace, "ga tuwon ki chan Madafi idan awaki suka cinye kin huta".
Naje na dauko cikin wata roba, miyar ya kadan ko rufe tuwon bata yi ba.
Bayan na gama Sallah naci abinci, na aza kaina bisa gadon karan dake dakina, ina runtse ido saboda zafii.
Ina zaune naga dare yayi na mike nace bari naje dakin Baba.
Yau yana zaure saboda babu sanyi,nayi sallama na cire ta kalma na na zauna"yace kin aza magani ko dan kullun zaki ringa sha kamar ruwa har ya sallace yazamana ba daci"ciwon zai shafe insha Allah kamar baki taba yiba saboda kin girma yanzu kullun da ciwon nike kwana dan kada ya hanaki haihuwa ciwon nada matsala amman yanzu wannan maganin insha Allah shine waraka gefen cikin ki zai zama lafiya kalau"nace to Baba Allah ya saka da Alkhairi yace"Amin Allah ya kawo maki dauki a cikin rayuwar ki kisamu sauki"na mike naje na aza maganin nadawo na zauna.
Ya mikoman wata leda yace"ga kyautar ki ga kuma Sabon littafi"na amsa cikin murna nace nagode Baba Allah ya biya yasaka maka da Aljannah"Amin ya ammabata cikin jin dadi"har na bude yafara biya man saiga Ma'u da sallama kamar ansata dole"yace ke sai yanzu zaki fito"nide nayi saurin boye ledar da Baba yaban kada ta gani.
Juyar da kai tayi tace"kaina keman ciwo"baice komi ya idaman na mike nace Baba saida safe"yace ga magani na amso maki wajen Kabiru"(saurayi Ma'u dan Mai gari shikade keda kyamis shima ba karatu yayiba koya mashi a kayi).
Na amsa nace nagode nabar wajen cikin sauri ina boye laidata cikin Hijab.
Ina zuwa daki nace Wash na bude ledar,Turare ne irin na dure nayi murmushi nace kyautar turare tana faran taman rai inason kamshi,sai kuma naji wata leda daman tun chan naji kamshi shiyasa nayi saurin tashi kada Ma'u ta jiyo.
Miyau na har tsun kewa yake tun naman sallah rabona da Nama dan ko Baba ya kawo saide na hangeshi,naci na koshi na dugun kune takar dar,na fito na yadda ta bayan gida nasamu kohi naje na debo ruwan magani na nataho daki Ina jiran su sha iska,maganin da Baba yaban na balli biyu nasha,magani naji ya huce nasha na kwanta.
Duk wahalar dana sha yau amman naji raina yayiman haske.
Saide faduwar gaban dake ziyar tata lokaci zuwa lokaci narasa minene dalili?
Nayi addu'a na juya bisa gadon karana.
*************
Tunda ya iso gidan baije part din kowa ba saide abinci da aka cikashi dashi.
Ganin karfe tara na dare yasa ya fito domin zuwa part din Mai martaba.
Ko Ina na gidan bayi ne, duk inda ya gifta banda kirari babu abinda ake.
Wani abu mai kama da kaho kalar suffarshi amman na silver ne, aka fara hurawa, wannan shine shaidar yarima ya fito, kamin minti daya ta ko Ina fadawa ne ke fitowa cikin azama a jere.
Wasu na shimfida capet inda zai taka wasu na nadewa, ata kuma sai saka turaren masu dadin kamshi suke cikin lokaci kadan gida ya dauki kamshi gidan ya zama tamkar safiya.
Kirari ta ko Ina kamshi tako ina.
Har ya isa part din Mai martaba.
Fadawan dake bin bayan shi ya daga hannu suka juya, wadan dake tsaye bakin kofa Mai martaba suka fara kirari;
"Allah ya taimaki sarki na gobe mai jiran gado ., duk Al'umma nama Yarima sannu da zuwa tareda fatan farin ciki a rayuwar yarima, sarauta gado ce ba haye ba shine babba dan babba jirgi mai masoya da yawa,Mai martaba yace ayi maka iso yana farin cikin ganin Yarima a wannan lokacin!". Aka bude ya shiga, ido hudu suka yi da Mai martaba ya dukar da kansa a kasa, saboda yadda Abie yayi masa kwarjini.
A kasa kusa da shi ya zauna tare da da dukar da kai cikin muryar sa mai sanyi yace;
"Allah ya taimaki Mai martaba, tuba nike ayi min afuwa ba zan kara kuskure irin wannan ba".
"Taso kadawo inda nike ina bukatar naji dumin Yarima na".
Murmushi yayi ya hau kujerar dake kusa dana sarkin.
Cikin kulawa yace, "Na san baka ci komi ba".
"Naci", inji Yarima bayan tun Breakfast din da yayi a Abuja.
"Kayi hakuri Yarima na san kana cikin matsala, amman insha Allah Kursim zata kawo karshen matsalar". Shi ine Yarima shiru yayi amman ya san abinda ba zai yiwu bane.
"Ina jin ciwon yadda magajina ya kasa farin ciki tsawon shekara bakwai, na san kana son Manal Amman mahaifanta tama, shekarar Abdulrahman ashirin bai samu haihuwa va sai akan Manal, kaddara ta raba su kuma ya dangana haka Mahaifiyar ta, ka duba kaga tsawon shekarun da suka yi ba haihuwa kasan ko ba karamin so zasu yi mata ba, da ace Uba na sayan ran dansa da Abdulrahman ko tsiyacewa zai yi yafi son diyar sa akan komai, kaddara ce ta raba su kuma ya dangana, ina so kaima ka dangana".
Kara dukar da kai yayi.
"Yanzu an shirya komi gobe zaka wuce Katsina, kuma na san zaka ji dadin zaman garin".
"To Abie, duk yadda kace haka zanyi bana bukatar fushin ka akaina".
"Ina son ka zama mutum kamar kowa, tun da Manal tabar duniya ka rufe karatu jin dadin rayuwa bama ka zama kasar, dan kada ka shiga jama'a, dole na damu, ina son ka zama kamar kowa, da ana sayen farin ciki da tuni na siyo maka".
Murmushi yayi wanda ya dade bai yi irinsa ba, yace, "Abie ka kwantar da hankalin ka, gobe zanje amman dan Allah arage min kwanaki".
"Cikin jin dadi yace, "ba zai yiyu ba, ina so ku saba, kaga sai asaka bikin kamar sati biyu".
"To shikenan Abie yanzu sai da safe".
Murmushi Abie yayi har da hawayen farin ciki.
"Kaje Ammin ka ta ganka, na san zata yi farin ciki".
Daga kai nayi na fita ina murmushi.
Lalle mahakurci mawadaci, yau addua'r sarki AbdulAziz ta karbu.
Ta hanyar da Mai martaba yake bi yabi yaje part din Hajiya Amina.
Zaune take cikin kayataccen falon ta, waya take kuyangunta na kasa.
Sallama yayi ya shigo dauke da Murmushi a fuskar shi.
Baki Hajiya Amina ta saki tana kallon shi cikin mamaki.
Ajiye wayar hannun ta tayi, ta mike cikin azama taje gaban shi.
"Wannan shine Yarima na, ko an chanza min ne kodai mafarki ne kalar wanda na saba?"
"Allah ya taimaki Uwar gidan sarki ya kara lafiya da daukaka wannan ba Mafarki bane,Yarima dan sarki jikan sarki shine a gaban ki".
Hannu ta saka ta jawo shi tace, "muje".
Ba musu ya bita, Bedroom suka nufa, kuyangu suka bisu da kayan marmari.
Suna zama bakin gado Yarima ya daga hannu.
Kuyangun suka ce, "muna godiya kuma muna farin ciki da ganin magajin sarki a yau!". Suka bar wajen.
Hawayen dake bin fuskar Ammi yasa hannu yana gogewa.
"Ya isa haka Ammi na tuba na san na bata maki".
Saukowa tayi takai kanta kasa tayi Sujjada.
"Yanzu Yarima na zai zauna dani zaibi umarnina kamar yadda yake ada".
Daga kai yayi tareda murmushi.
Tace, "jiya kanwar ka ta haihu.Na kiraka na fada maka waya a kashe".
Me ta samune?".
"MANAL ta haifa". Murmushi yayi ya rungume Ammi.
"Ta samu matsala amman nan da sati biyu zata dawo, yanzu suna Spain a chan ta haihu".
"Allah ya raya akan sunnah".
"Amin". Sun dade har dare yayi kana yayi sallama ya nufi part dinshi.
Lumshe ido yayi tare da shakar kamshin falon shi.
Kai tsaye toilet yana nufa cikin saurin ma a'ikatan daya ya nufi toilet daya ya tsaya cire mashi alkabba.
Koda ya shiga an hada mashi ruwa a cikin bahon wanka ruwa masu kamshi shi komi nashi mai kamshi ne.
Bayan ya fito ya iske kayan bacci ya saka tareda takalma yauma bakin window yazo yayi tsaye yana tunanin zaman da zaiyi a wata masarauta.
Har dare yayi kana yaje ya kwanta tareda Addu'ar bacci.
Bayan yadawo sallar asuba ya kwanta sai wajen tara ya tashi.
Cikin sauri ya mike toilet ya shiga yayo wanka koda ya fito an chanza zanen gado angyara dakin sai kamshi dake tashi.
Kaya ya saka tareda saka Alkyab.
Ganin jikuna yayi ana fita dasu na kayan shi, murmushi yayi yanufi part din Hajiya.
Yauma kamar jiya saida akayi shelar fitowar Yarima shiyasa kamshi ta ko Ina a gidan.
Tare da mai martaba da Ammi suka yi Breakfast, bayan sun gama Ammi tace yaje part din iyayen shi su gaisa(kishi yoyinta)
Dakin Hajiya Sa'adatu ya fara zuwa ita kebima Ammi sai Hajiya Hadiza suma mamaki ne a tareda dasu amman suka boye.
Kannan shi cikin sakin fuska duk suka gaisa.
Ban kwana yayi da Ammi, mai martaba har bakin motocin da zasu kai shi airport yake, gida ya zama kamar ana wani biki,kide-kide da bushe-bushe kalar na sarauta kamshi kota Ina.
Hannu mai martaba yasa ya bude mashi murfin mota.
Murmushi yayi yace, "nagode".
Ya shiga ya kulle har suka fita yana wajen tsaye.
Lumshe ido yayi yana tunanin, saboda faduwar gaba dake ziyartar shi. Addu'a yake sai kuma yaji sanyi na shigarshi.
Lokaci guda ya ji yana son zuwa garin Katsina, har ma yana mantawa da neman aure za shi, ya rasa dalili sai kuma yaji daukin zuwa garin yake chan.
Komi zai faru a katsina??
🤭OHO😅😜
*Qurrah*
[1/28, 3:02 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*
*Writing by-Qurrah*
Page -7-8
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*~Addu'ar Wanda Ya ji Tsoron Faruwar Wani Abu Mummuna saboda Kambun Baka~*
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Idan dayanku ya ga wani abu da ya kayatar da shi ga dan uwansa, ko ga kansa, ko ga dukiyarsa, to ya roki Allah ya sanya albarka gare shi; domin kambun baka gaskiya ne.
Page -7-8
DEDICATED TO.....MY SISTERS😘
_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_
----------------Kuka nike tamkar raina zai fita,dalilin kukan da nike kaina har ya fara ciwo,wannan wane rashin kauna ne??arasa wanda za'a hadani dashi duk kauyan nan sai Lado,miyasa Inna zata man haka??nikam bari Baba yazo idan har yana sona ya kaini wajen dangin Uwata,koya suke nasan zasu soni,zanyi biyayya akan komai amman banda wannan saidai idan Baba ya furta da kanshi babu yadda zanyi,dole nayi mashi biyayya tunda Uba ne musulunci ya bashi damar ya zaba ma diyarsa Miji nagari,wata zuciyar tace "kenan yanzu idan Baba yace ki aure shi kenan yarda zakiyi?"
Runtse ido nayi kamar ina magana da wani,nace;" to ya zanyi tunda shi ya haifeni"
Nayi ta gumi ina jiran shigowar Baba.
*************
A hankali Kursim ke yin tako rigar data saka kuyangu na dauke wa,saboda jan kasa da take.
Tsaye yake ana saka mashi Alkyabba madubi aka kawo mashi,dai-dai fuskar shi ya kallah ya dauke kai,yayi hanyar fita cikin dakin,dogaran dake tsaye bakin dakin suka fara kirari,bai kula yabi hanyar da zata sadashi da lambun da aka hada dominsa,tafe yake tareda da yan jagora.
Yana zuwa ya zauna ya dagama na bayan shi hannu"godiya muke dan sarki jikan sarki"daga hannu yayi saboda baison haya niyyar suka bar wajen,sai guda da ya tsaya ya gyara mashi Alkyabba shi tareda cewa"Ina nema izini wajen shugabana zanbar wajen koda abinda kake bukata?"tare da dukar da kanshi a kasa.
Da kai yayi mashi nuni yabar wurin.
Lumshe ido yayi ya rasa mike mashi dadi,a hankali ya bude idon shi jin kamshi mai dadin gaske ya bugi hancin shi.
A kan fuskar Kursim idon shi ya sabka"murmushi ta sakar mashi irin wanda tasan kowa ne namjii tayi mashi sai ya rude"kauda kai yayi har ta iso,matan dake tare da ita suka gyara mata riga ta zauna bisa kujerar dake kusa dashi,ta daga masu hannu subar wajen "suka ce godiya muke Gimbiya sarauniyar kyau farin cikin Sadauki Yarima Annuwar" murmushi tayi da alama taji dadi suka bar wajen ta maido kallon ta ga Yarima,tana kara gyara zama.
Lumshe ido tayi cikin zuciyar ta tace, "daman nasan zanyi fama dakai Yarima" ta bude fararen idanun ta akan shi.
Tare da cewa; "Nayi farin ciki da ganin Prince dina a cikin ƙoshin lafiya, Masarautar da mutanen cikin ta suna farin ciki da ganin Prince Annuwar a cikin wannan gida,da zuciya zata bude idon ka domin kaga abinda ke ciki na tabbata da zakaji kaina kuma zaka ban gurbi na zama abokiyar rayuwar ka,zan amince ma kowa ce ukuba inde Prince zai zauna dani,zan kansan ce mai hakuri da juriyya akan abin da nikeso".
Ko motsi baiyi ba daga inda yake zaune tamkar ma baijin yaren da take magana ba, da turanci tayi maganar amman tamkar da wani yare wanda bai taba jiba,saboda yadda yana yinshi ya nuna,babu alamar yaji maganar ta,kuma yaji duk abinda tace saide tamkar dutse haka yake.
Jim tayi tana tunanin me zata ce sai kuma tayi murmushi ta bude baki zata yi magana, "umm....!!"daga hannu yayi a hankali cikin muryar shi wacce take kamar yana rada yace "Am feeling sleep" baki ta saki tana kallon shi "Take this;he said" wani abune ya miko mata kamar gift "No need tace" it is not money" ya fada.
Sai a lokacin ya kalleta yace"it is a shame that you should visit a person like me and go away empty handed".
Amsa tayi tace"thank you"baice komi ba ya mike itama ta mike"take care of your self"ya dan waigo yace"thank you"taji dadi sosai thank you da yace mata"ashe tun dazun yana jina?? lalle koba yanzu ba kalmomi na zasu yi tasiri kenan a zuciyar ka "tsaye tayi har ta dena hangen shi.
Tana juyowa suka hada ido da Hanan,tare suka sakar ma juna murmushi Kursim tace "tun yaushe kike nan kinzo ki min sa ido ko?"dariya Hanan tayi tace"muje ciki Princess akwai magana amman fa ba ido nasa maku ba yanzu nazo wajen, lokacin ku duka kun mike,lallekam naga ansha soyayya"duka Kursim takai mata tareda cewa,"banson wulakanci".
Tare suka jera suka shiga part din Kursim,kuyan gunta suka kama mata ta cire rigar, lokacin an hada mata ruwa cikin bahon wanka,shiga tayi tana sinsinar kamshin ruwan tana lumshe ido,idan ta tuna Cool voice din shi,kamar mai motsa baki,shiru tayi cikin ruwan tana hangon fuskar shi jinta take tamkar yana kusa da ita,haka tayita lumshe ido, saida taji maganar Hanan kana tayi sauri ta fito tana daure da towul,a gaban mirror ta zauna,kuyan gunta suka gyara mata kai suka fidda mata kayan da zata saka,zasu safa mata Mai ta daga hannu,suka fita.
Hanan na bisa gado na latsar wayar ta.
Har Kursim ta gama"wai kinsan wani abu inji Hanan?"girgiza kai Kursim tayi"wallahi ban taba ganin guy din da zaiyi kyau da soyayya ba kamar wannan"bata fuska Kursim tayi tare da cewa"mikika gani kenan har kin kalleman miji ko?"
Dariya Hanan tayi tace"ohh sorry my friend bamu haka da ke,kawai de wasu colour eyes na gani wajen shi,wanda kallon su kade zai iya ruda mace"Yanzu de shikenan ya isa nifa ba kyaun shi yasa nike son shiba haka kawai Allah ya hada jini na da nashi.
Kallon kawai Hanan keyi"kinsan dawa nike chart yanzu?wallahi da Ammar nike chart wanda muka hadu dashi a New York kin tuna kika hana mashi number naki,nabashi nawa wallahi sonki yake kamar mi"mtsww Kursim tayi tsoki tare da cewa.
Banison ka Hanan ki dena"i told him that a woman without a husband is like a cloth in the market,idan yayi kokari zai sameki"
"Are you in your senses?"
Kallo Hanan tabita dashi cikin mamaki daga magana duk ta rude kamar wata matar aure"please Hanan kideman haka,tun farko kinsan Annuwar nike so,jina nike tamkar matar shi"zaro ido Hanan tayi"daga mata kai Kursim tayi alamar tabbatar wa"shiru Hanan tayi,tana tunani.
Yana zuwa part din da ya sabka,cikin sauri masu aikin part dinshi suka cire mashi Alkyabba,zasuyi magana ya nuna hanyar fita,suka bar wajen.
Lumshe ido yayi yana tunanin jinshi yake tamkar wata duniya,lalle ba karamar biyayya bace yayima Mai martaba zuwa shi wurin nan.
Shiru yayi yana bukatar kadeci yana bukatar zuwa gefen garii.
Yana son zama gefen gari inda babu haya niyya.
To yanzu wazaima magana kode ya fita shikade??
Wayar shi tayi kara ya duba yaga Ammi, murmushi yayi ya daga kiran.
***************
Ina nan zaune bakin gado karana naji sallamar Baba,jiki na har kyarma yake wajen saurin fita.
Ina fita dai-dai lokacin da Inna da Ma'u suka fito,suka tsaya bakin kofar dakin Inna,ni kuma a nayo wajen Baba.
Tun kamin na iso har hawaye sun wanke man fuskata,dan nasan da wahalar gidan Lado mai jakkai,gwara ta nan gidan,a chan dami zanji da wahalar tukama yaran shi tuwo koda surfe da dakan fura koda masifar matan shi har made Uwar gidan sa yadda naji labarin tana bautar da matan shi.
Hakan yasa dana tuna sai hawaye.
"Subhanallah...!!"Baba ya fadi bakin shi har yana kyarma wajen fadi.
"Mi akayi makine diyata waya tabaki ne kike kuka haka,fadaman ko waye?"
"Aikin banza tattalin shege"inji Inna dake tsaye kofar dakin ta.
Baba wallahi bana son auren nan,kabari nasamu mai sona nima, wallahi ban son Lado,ka taima kaman Baba.
Kallon mamaki Baba yake man kamani yayi ya zaunar bisa turmin dake tsakar gidan "waya fadamaki Lado mai jakkai zaki aura?"
Cikin isa da tinkaho Inna ke takowa har ta iso inda muke tsaye tace;"nice nan nace Lado shima ya aiko da kayan baiko,saboda yayi maka magana baka amince ba,ni kuma a matsayi na na uwarta na amince,ayi rana daya ita da Ma'u "kallon banza ya bita dashi,ya kama hannu na mukayi daki na.
Ya zaunar dani bisa gadon kara na yace; "kiyi hakuri Nanah babu wanda ya isa ya aurar dake ga wanda baki so,indai ina da rai, saidai idan ke kika kawo shi kikace kina so" a jiyar zuciya nayi.
Ya mike ya fita naji hankali na ya kwanta,nayi ajiyar zuciya na kwantar da kaina bisa gadon kara.
Guf naji akayi da dan kyauren da nike rufe daki na.
Zumbur nayi na mike kada kyauren ya fado man cikin zaro idoo....!!!
Tamkar zakanya haka take maida numfashi kamar wanda tayi gudu.
Dafe girji nayi ina kyafta ido!!
Ma'u na bayan ta "ashe duk kashe din dana yi maki baki dauka ba,kenan idon ki har ya bude da zaki tsallake magana ta?? kenan kinsa naji kunya da kaina naje na nemo maki auren Lado,shine zaki watsa man kasa a ido,dan baki zauna cikin cikina ba??to bari kiji wallahi wuya saita sa kin amince da auren Lado,dan sai gidan Lado ya zaman maki Aljannar duniya,dan sai gidan nan ya zaman maki bakin gida,da kafar ki zakije neman Lado"Ma'u tayi tsaki tare da wurgo man harara
Kuka nike tamakar raina zai fita;"Inna ki taimaka man wallahi bazan iya zama gidan Lado ba,zan maki duk abinda kike so,ki taima min Inna "Kafafun ta na rike ina kuka tamkar raina zai fita.
Fizge kafar ta tayi,ta ingiza ni nayi kasa na bige kaina jikin gadon karana.
Wani irin ihu na saki, wayyo Inna na mutu...!! "bata ko waigo ba saima cewa da tayi; "yanzu kika fara ganin azaba Kuma kun kullah alaka da ita kenan" ta fita ta nata bala'i.
Dafe kaina nayi jini na zuba ga kara ya shige man gefen fuskata.
Kuka nike cikin zuciya ta nace;"zan dauki ko wace azaba akan zaman gidan Lado "na cigaba da kuka ga azabar zafi da kaina keyi,nasa hannu zan cire inda karan ya shiga,wani irin azabar zafi yasa saida nayi kara na cire ina runtse ido.
Har dare yayi ina zaune sai walkiya da akeyi da alamun hadari ne,jim kadan ruwa ya sakko,dan danan sai sanyi gashi kuma Inna ta cire man kyauren dakina gashi babu labule,hakanan na kwanta na dukun kune waje daya.
Zumbur na mike jin ruwa a jikina,dakina ne ke zuba dai-dai wajen gadona.
Kukan tumaki naji zasu shigo dakina na kara rudewa,na rakube gefe guda ina kyar mar sanyi.
Ummeeyyy.......ganin su nayi a cikin daki na.
"Innalillahi..!! wayyo Allah na ku fita kubar man daki "kuka suke suna Ummeeyyy Ummmeeeyyyy,Inna ce a bayan dabbobin.
Nace; "yawwa Inna ki zo ki korasu,su duka sun cika man daki"cikin kuka nike maganar ga dakina na zuba ga sanyi.
Tsaki tayi tace;"su fita suje gidan Uban wa??ai daman kinsan nan dakin sune,nagaji da raɓewar da suke ne,basu san ruwa na bugun su,kinga sai ku raba dakin su a gefen daya daban kema a gefe daya daban,diyar Liman wacce ta girmi auren Lado" harta juya ta fita sai kuma ta dawo "bani hitilata,tunda ba Uban ki yasaya ba,sai ki jira har yasai maki taki" ta gizge hitilar hannu na tayi tsaki tabar wajen.
Kuka tumakin Inna keyi ga babu fitila gashi yau wani irin duhu ake.
Tayaya zan kwana da tumaki daki daya??
Jikina kyarma yake dan tsoro, lokaci guda na nemi zafin ciwon dake goshina na rasa tsabar tashin hankali.
Gab-Gab kakeji cikin dakin sai kuka da suke yi ga fitsari tare da kashi, tamkar babu bil Adama a dakin,saboda yadda na lafe jikin wata kusurwa,gashi dai-dai nan ruwan ke zuba,ban damu ba saboda yafi man zama cikin tumakai kilama su sokeni da kahon su.
Amman duk da haka zuciyata fal da tsoro take,kada suji motsina.
A haka a tsaye nike har aka dauke ruwa nayi hamdala,jikina sai kyarma yake saboda sanyi.
A hankali na tsugunna dan naji tsit,sunbar kuka,nayi zukunne har bacci ya daukeni.
****************
Bayan ya gama waya da Ammi,Abie ya kirashi suka gaisa yace;"babu damuwa ko Yarima?"lumshe ido yayi yasan yana cikin takura baiko kwana ba amman jinshi yake kamar yayi shekara,saida Abie ya kara mai-maita tambayar kana Yarima yace;"Abie inason gobe na fara fita gefen gari,dan na rage kewa"murmushi mai sauti Mai martaba yayi yace;"kada ka damu zan ma surukin naka magana saiku fita da Gimbiya,hakan zaisa shakuwa a tsakanin ku"baiji dadin saka Kursim a ciki ba amman tunda yana son fita babu yadda ya iya.
Sukayi ban kwana ya aje wayar,yayi shirin bacci yayi addu'a ya juya.
Kursim tace;"lafiya kike kallona??kamar yau kika saba ganina?"maida numfashi Hanan tayi tace;"wallahi Princess tausayi kikaban dan na fahimci halin da kike ciki,ina da shawara "kallon Kursim tayi tace"inajin ki,fadaman inji".
Mikewa tsaye tayi ta iske Kursim inda take zaune"mizai hana mu bullo ma Prince ta bayan gida,ina nufin muyi amfani da abinda yake so"kallon ta Kursim keyi tace"Banga ne mikike nufi ba,kamar mi kenan?"
Murmushi Hanan tayi tace;"ina nufin MANAL mana,idan akwai wadda kike mu'amallah dashi a gidan ki tambaye shi wane irin attitude Manal keda?"
Murmushi Kursim tayi tace;"ya akayi Doctor tafi Lawyer dubara??gaskiya komi nawa ya tsaya,idanu na sun rufe"dariya Hanan tayi.
Jim Kursim tayi kamar tana tuna wani abu tsalle tayi tace;"yes I remember muntaba fira da Sister dinshi Ahalam tace Manal nada funny attitude ita kade ke sakashi dariya,sai Ammi da Abie iyayen shi"zaro ido Hanan tayi cikin mamaki!!!
Jin jina kai tayi tace;"kenan Princess zata koyi bada dariya kenan??"murmushi Kursim tayi tace;"yanzu da muna shiri da Nifra da saina tambaye ta game da Sister dinta".
Bata fuska Hanan tayi tace"wallahi banson yarinyar nan, saboda kasaitar ta da jin kanta,gata karamar yarinya,amman sai iskanci,kinga wani biki danaje na Dikko,yaron wani ambassador,ashe coursin dinta ne,wallahi tana shigowa Hall din saida aka mike nide naki tashi,ganin yadda hankalin kowa ya koma kanta yasa nabar wajen,kinga yadda diyan Governor's keson shiga kamar itace President din,shiyasa banson ta,bata ko magana saide daga hannu"dariya Kursim tayi tace;"shiyasa mina bamu shiri,kuma yadda akace sanda uwayen kema Manal ko rabin shi basuyi ma Nifra,saboda gata kamar a cinyeta shiyasa sukayi garkuwa da ita,gashi kakan ta wanda ya haifi Maman ta Major ne,ko chan Family din su Maman ta kamar su hadiye ta danso,kinga son da sukema Manal ne ya koma kan Nifra,gata ta ko ina shiyasa dole tayi wulakan ci"tsoki Hanan tayi tace"kila kuma banzar dan taga tanada kyau"
dariya Kursim tayi tareda mikewa tace"ance duk kyanta Manal tafita"
Cikin mamaki da zaro idoo Hanan tace;"Aljana ce ita Manal din??dan gaskiya duk da banshiri da Nifra amman nasan tanada kyau"
Dariya Kursim keyi tace"wallahi naga photu nan su"girgiza kai Hanan tayi tace;"dole Prince ya rude shiyasa duk wahalar make up din da akayi maki bai yababa,amman akwai dabaru da yawa da duk munin mace tayi amfani dasu Namiji sai ya rude balle kema mai kyau ce".
Agogo Kursim ta kallah tace"wai daman haka dare yayi munata fira??mu kwanta hakanan firar Yarima saita kaimu gobe ba'a gama ba"tare suka kwanta kowa ce da kalar tunanin ta a zuciyar ta.
****************
Ummeeyyy-Ummeeyyy kukan tumaki yasa nayi firgigi na bude ido anata kiran asuba.
Subhanallah!!
Na mike cikin sauri jin kaina na ciwo,gani nayi kamar lokacin dana kwanta bacci.
Banda warin kashin su tare da zarnin fitsarin su babu abinda dakin keyi,banson wari ko kadan a rayuwa ta,ni dai kamshi shine abinda nike,na toshe hancina.
Na mike tsaye jin motsi yasa suma suka mike.
Nazo zanfita sun tare kofa,duk suka rude sai kuka suke,nima yau cikin zuciya tsoron su nike,duk da tunda na budo ido a duniya nagan su,amman yau saboda sun zama abokan rayuwata babu sabon kwana waje daya yasa na rude.
Da kyar nasamu na tsallaka har na bige da bango nafadi yaraf!!
Su kuma duk sun rude, suma suka fito nayi saurin janye jikina kada su fadaman.
Kafa ta ta bugu zafi nike ji sosai,jina cikin lema yasa nayi saurin mikewa.
Zanena duk ya jike da laka,saboda ruwan jiya,ina murnar kayana sun bushe sai kuma murna ta koma ciki to dame zanje tallah Yau,su kadai suka rageman riga da zanii,masu lafiya.
Cikin sauri na koma dakin lokacin sungama fita,na toshe hancina saboda warii.
Haske ya dan fara na hango buhuna na kaya,ina zuwa na kamashi nayi saurin saki ganin kashin tumakai ne da fitsarin su.
"Innalillahi..!! Sama suka kwana kenan yanzu yazan yi??"
Dauko buhun nayi na fito bakin rijiya na zazzage kayan.
Na dauko bahon wanki kofar dakin Inna.
Nazo na jawo ruwa na zuba banji karar tafiya ba sai dai naga Inna tsaye gabana cikin tsoro nace;"Inna Ina kwana!!
Umm Daman "tsawa ta dakaman tace"kada ki kwashe ruwan rijiyar nan,kuma ki maidaman baho Ubana ya saiman ba Malam ba,kada ki sake tabaman kaya,kije korama kiyi wankin ki sarkin yan tsabta" hawaye suka zo man.
Na kwashe kayana zan bar wajen tace"narasa inda yarinyar nan ta gajii kafiya da taurin rai"bance komi ba"tace ki ratse kibi tabaya,kada kibi ta gaban massalacin da Malam ke bada karatu,idan kika bari ya ganki,saina yimaki wata azabar kuma kidawo kiyi aikin fura dan yau da wuri nike bukatar kifita tallah,dan nagaji da ganinki"nayi saurin fita.
Babu kowa saboda sanyi ruwan jiya,har nagama wanki a korama babu wanda yazo,na dauki kayana nayi gida.
Ina zuwa Baba baidawo ba na wuce nayi sallah,na gyara dakin,kana nafara aiki.
*************
Kalolin abinci ne agaban shi,amman bai kalli ko guda saima tashi da yayi ya bar wajen,bakin window ya tsaya kamar kullun hannu cikin aljihu,ina bukatar fita ya ambata a fili.
Cikin Farin ciki da shigo dakin ta tada Hanan dake rankon bacci.
Bude ido tayi tace"miya faru Princess zaki tadani,bayan kinsan jiya bamuyi bacci da wuri ba"murmushi ta saki tace"fita zamuyi gefen gari da Prince"zaro ido Hanan tayi ta murtsike ido tace"wow thank God ga opportunity kinsamu bari na fada maki abinda zakisa Prince ya rude"kusa da ita taje tayi mata rada a kunne,su duka sukayi dariya Kursim tace"kai kawata dama kece Lawyer kin san dubaru da yawa shawarar ki ta amsu bari na tashi na shirya yau bani bukatar kowa ya shiryani nizan yi da kaina"ta mike ta nufi toilet.
Shima Prince ya shirya ya fito ana masa kirari har ya iso wajen motocin da zasu fita.
Kursim ce tafe tana kamshi cikin shiga ta Alfarma tayi kyau nagani na fada,cikin purple din riga ta material ita Order tayi daga Dubai,duk kayanta order ne tayi wadan da zata saka har Yarima ya koma.
Babu magana ta mika hannu ta amshi Key din mota,ta kashe mashi ido tareda murmushi tayi nuni da ya shiga.
Ba musu ya shiga ya zauan.
Princess ta shiga Driver sit ta zauna.
Cikin mamaki yake kallon ta daman tana driving??
Tunda yake bai taba driving ba,gashi ita mace zatayi to mi hakan ke nufi dagashi sai ita kenan zasu fita??
Akwai wani abu a kasa kenan ko miye oho??
*************
Na gama aikin fura nayi wanka na saka kayana da suka bushe.
Nace"Inna na tafi"bako ta kalleni ba saima waka da takema Ma'u,wai sarauniyya kuma Gimbiya matar Kabiru dan Mai garii.
Na fita nabi ta bayan garii saiga su Shatu.
Na hau muka gaisa tace"waike kullun cikin rauni kike"nayi Murmushi tace"yau zamu shiga birni jabe zai kaimu"zaro idoo nayi nace"Birni Kuma??"ta daga kai.
Hakanan naji banson shiga birni,saidai ko dan kaunar da Shatu keman zanje.
Yau zanga mutanen Birni😅😅
Qurrah
[1/28, 3:02 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*
*Writing by-Qurrah*
Page-5-6
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*~Addu'ar Wanda Ya ji Tsoron Faruwar Wani Abu Mummuna saboda Kambun Baka~*
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Idan dayanku ya ga wani abu da ya kayatar da shi ga dan uwansa, ko ga kansa, ko ga dukiyarsa, to ya roki Allah ya sanya albarka gare shi; domin kambun baka gaskiya ne.
DEDICATED TO....MY SISTERS😘
-------------Babu ɓata lokaci jirginsu ya tashi sai katsina suna isa suka iske taro anzo tar barsu.
Babu wanda Yarima ya kallah saka makon faduwar gaba da ta riskeshi yana isowa garin yaji wani iri ya kasa gane ma kanshi zufa kawai yake.
Na bayan shine ke cewa Yarima na bada gaisuwa ga duk wanda kenan.
Har ya shiga mota suka bi hanyar gidan sarki.
********************
Yau koda na tashi na jini lafiya kalau ga karfi da nike ji a jikina.
Yauma kamar kullun har na gama wanke-wanke.
Aikin fura na fara ina daka Ma'u na zaune tana kwalliya sai ga kawayen ta.
Da girman kujerar ki matar Kabiru a gida sai dai a kirɓa a baki kisha haka a gidan Miji sai dai a kirɓa a baki ki sha.
Duk garin Dansabau babu macen da bata yin daka sai ke Ma'u diyar Liman matar Kabiru.
Wani daɗi ya ziyarci Ma'u a zuciyar ta tace " mace sai dai tayi man kirɓi nasha naba wa'inda nike so amman idan yarinya tayi biyayya kila na tausaya mata nasa ta cikin masu take man baya garin namu ne "shewa sukayi tare da guda.
Matar mai gari da girman kujerar ki "tace shiyasa nike son ku yanzu kuzo muje Tashar Ado mu kaso kudin tallar da waccen banzar ta samo jiya "daman abinda suke so kenan suka miƙe suna mata kirari kamar wata matar sarki.
Tace "yan bakin ciki sai dai su mutu ta Allah ba tasu ba "suka kara shewa suka fita.
Ina ma Ma'u zata gane bana mata bakin ciki da auren Kabiru.
Nasan bazan samu kamar Kabiru ba amman ban taba jin kyashi ko hassada akan auren nasu ba,saboda nayi imani da Allah ke bada wa ,kuma ban isa na hana abinda Allah ya kaddara ba,tome zai sani bakin ciki kuma akan 'yar uwata.
Haka na gama aiki na gaji wajen sha biyu nayi wanka na dunƙule furar ,na leka dakin Inna,nace Inna na gama sai naga babu kowa.
Nayi zaman jiran Inna jim kaɗan sai gata,tace yawwa tunda kin gama ina so in baki sabtu idan kinje.
"Kisawo ma Ma'u turaren nan dan aune na Muttala ukku" nace to "kema ki dauki Muttala guda kisai wani abu" cikin jin dadi nace nagode Inna.
Kallo take taga Ina farin ciki tace "ban yadda dake ba mikoman kwaryar nan na ƙirga furata dan naga yau nishad’i kike zaki yi min cuta ko kin samu dama ki zalun ceni "na miƙa mata tace "Allah yasa 'yar biyar ta bace kiga kalar bugun da zaki sha a gidan nan sai yafi na jiya kuma da kafa nace kije kada kihau wata mota "nace to Inna.
Koda na fita bakin gari naga Amalanken su Shatu ina isa naga Shatu ciki da kwaryar nonon ta"tace tun dazun muke jiran ki jiya Jabe yace baki da lafiya "nace ai naji sauki na hau muka tafi muna fira.
Yau zuciyata wasai nike jinta jinike kamar an man wata kyauta farin ciki nike ji a raina na rasa dalili.
Muna zuwa muka zauna a inda muke zaunawa koda yamma ta yi munsaida.
A cikin tashar Batagarawa muka shiga nida Shatu tayo sayayyar kayan su na fulani,ni kuma na siyoma Ma'u turaren aure.
"Shatu tace ba zaki sayi kamshi ba nasan kina son kamshi"
Nace Baba na ya siyoman jiya.
Muka dawo muka dauki kwaryoyin mu.
Jabe yazo ya dauke mu da Amalanken shi.
Awara muka sawo munaci muna fira.
Idan ina tare da Shatu har mantawa nike da matsala ta.
Muna zuwa Kauyan mu na dire nace sai gobe Shatu na gode.
Shatu tace gobe ki fito da wuri na daga kai.
Ina shiga gida da sallama.
Da farin ciki a tare da dani hakanan yau da farin ciki natashi.
Kaya nagani a tsakiyar gidan mu "Innah ke guda tana cewa yuriri diyata mai goshi" ga kayan nan kwalayen biskit da alawa da cingam,sai wasu a ware yan kadan Kuma ba biskit da cingam su a kasa suke na Ma'u kuma bisa tabarma.
Da murnata nace Inna wa aka kawoma kaya ne haka na Ma'u ne? "tace eh wannan na mai kashin arziki ne, sai ta nuna yan kaɗan ɗin wannan kuma na mai kashin tsiya ke da Ma'u "zaro ido nayi nace Inna aini banda saurayi" Lado mai jakkai ne ya kawo maki "innalillahi!!
Inna jaki fa gareshi kuma matan shi ukku Inna abarni na zaba kamar yadda Ma'u ta zaɓa "iyye daman mijin Ma'u kika sama ido kenan kalar shi kike so to bari kiji ke da gidan sarauta ko kudi sai dai gani sai hange har abada,da wane asalin naki za'a so ki? da shegan takar taki? dan kin samu Lado mai jakkai yace yana so "kuka na aza dan Allah ki taimaka man,wallahi ba irin mijin Ma'u nace nike jira ba kinga shi tsoho ne kuma ga mata ga yara,gashi ko abinci ba'ayi gidan shi wannan jakin shi kadai gareshi.
"Makwabta kushigo kuji bakin ciki fili shegiya na zabar miji to bari kiji idan ubanki yazo kikace baki son Lado wallahi sai na maki bakar azabar da baki taɓa jin kalar labarinta ba "kuka nike sosai na tashi na nufi daki.
********************
A Masarautar katsina ko Ina bushe bushe ake da kide kide.
A fada suka zauna Sarki ya fito suka gaisa da Yarima cikin girmamawa.
Aka kaisu masauki, abinci babu kalar da ba'a aje masu ba.
Wurin da aka kaishe ya kayatu.
Harda lambu a cikin wurin,wanka yayi ya fito lambun wurin ya mashi kyau sosai.
Zuciyar shi fes babu damuwa a tare da shi harya manta abinda ya kawoshi.
Yana wurin zaune har zuwa la'asar ya tashi yayi wanka yayi sallah.
A cikin gidan sarki kuma Gimbiya Kursim ce da kawar ta Hanan diyar Governor din garin itama daka ganka kasan wayayya ce kuma da alamun kudi na aiki a jikin ta.
Mai makeup suka dauka daga Abuja tana ma Kursim heavy Make-up ake mata tamkar wata Amarya.
Wow my dear kingan ki tamkar wacce zata je gasar kyau na duniya.
Red din rigane a jikinta wacce tayi order din shi a Dubai rigar tayi kyau kuma wacce tasa rigar itama mai kyau ce, sai abun ya zama na biyu ga kyan riga ga kyan mai riga.
Kursim nada kyau sosai wanda ba kowa ne namiji bane zai ganta ya dauke kai ba ,tana wayewa sosai kasancewar baki daya rayuwar ta a turai tayi ta .
Mai Makeup ta gama ta fita.
Wallahi wannan guy din ko dutse ne shi da baya motsi yau idan ya ganki sai yayi motsi.
Ance wata guda zaiyi?? murmushi tayi tace wallahi one week yayi yawa guy din nan sai ya haukace.
Da fata tayi tace "My dear As soon as that is done the Prince is bound to fall in love with you".
Umm murmushi Kursim tayi, tace my friend Yarima ba kalar sauran maza bane yana da wahalar sha'ani.
Duk yawan fadin Yarima da kika ji ina yi to soyayyar bangare daya ce.
"What do you mean? I don't understand your proverbs Soyayyar bangare daya".
Murmushi Kursim tayi tace ina nufin ni kaɗai ke son shi shiyasa iyayen sa suka turoshi dan mu shaku yanzu ne za'a fara soyayyar bawai an turo shi dan mu kara son junan muba.
Zaroo ido Hannan tayi tace "Wallahi kursim I can't do that akan na miji" ke dai bakisan so ba .
"Towai ya taɓa yin soyayya ko yanzu zai fara?"
Soyayyar ce tasa baya shiga cikin jama'a tsawon shekaru tara "kamar ya inji Hanan cikin Surprise", mace guda yake so tunda yake a rayuwar sa tunda aka haifeta yake sonta shi ya zama Nanny shike mata komai, har ta kai shekara tara ranar data cika shekara tara ranar aka daura masu aure da ita, kuma ranar aka sace ta lokacin babanta yana Governor akan hanyar su ta zuwa airport,wa'inda suka sace ta sukace suna bukatar ya janje takarar shi ta Governor lokacin yayi four years zai kara wasu,yace sai sun maido mashi ɗiyar shi kana ya janye,sunyi maganar da daddare koda aka tashi da safe a bakin get din Government House aka iske wani kaset aka kai ma Baban ta koda aka kunna,sun daure mata hannu tana kuka tana fadin Yaya Anuu kazo katai dani,kawai suka caka mata wuka,nan take ta mutu suka dauketa suka kaita cikin wani gulbi suka yarda ruwa ya tafi da ita ko gawar basu kawo masu ba.
Harda hauka saida Prince yayi ya dade baya kasar yana asibi,bayan ya warke sai ya fara shan giya ta zama ruwan sa wallahi Hanan idan kika ga yadda mahaifin shi ya koma sai kin tausaya ma Family,tunda wannan lokacin rayuwar sa ta chanza,da kyar mahaifin shi ya rabashi da shan giya bayan ya kaishi Saudia wajen Friend dinshi.
Akwai lokacin da ina karatu,akace Prince yazo London lokacin ana Birthday din shi,naje nakai mashi Gift bai kalli Gift din ba bareni ya kalleni.
Babu time yanzu yana jirana ina so naje naga da wace kalar fuska yazo man .
"Please My Friend ina da questions da yawa akan rayuwar Prince ki bari mu ida labarin, "sorry Hannan nasan Mom din ba zata hanaki kwana anan ba kibari na dawo na ida maki labarin Prince.
Ta mike zata fita "Hanan tace ya sunan yarinyar?"
MANAL daga haka ta juya ta fita.
Zuciyar ta cike da tunanin wane kalar tarba Prince zai mata??
Qurrah
[1/28, 3:02 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*
*Writing by-Qurrah✍🏽*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Page-9-10
DEDICATED TO......MY SISTERS😘
_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_
----------------Kallon ta yake yadda take Driving cikin kwarewa da murmushi dauke a fuskar ta.
Kallon shi tayi tana murmushi tace, "ya dai Prince, ko kana bukatar wani abu bayan fitar?". Girgiza kai yayi.
Murmushi tayi na jin dadi da alama kwalliyar yau ce tayi masa, ta san ita mai kyau ce, ta yarda da kyaun ta, ta san ko bai so ta dan komi ba zai so ta dan kyaunta.
Motsa baki yayi alamar zai yi magana, ta dan rage tafiya tana kallon shi, cikin Cool voice dinshi yace, "daman kina iya driving gaskiya bazan iya ba akwai wahala, kinyi kokari". Cikin mamaki take kallon shi.
Tunda ta taso da gata gaba da baya, amman bata dauki driving abu mai wahala ba, amman shi mamaki yake yake, wannan wane irin gata ne, ai abun yayi yawa.
Har suka isa cikin wani estate dake gefen garii.
A cikin gidajen estate ta shigar da motar, har tayi parking bai ce komi ba.
Gidan ya tsaru sosai, kallon gidan Yarima yake yana zaune cikin mota.
Fitowa tayi daga motar tayi gaba, har ta dan kusa kai wajen kofar parlon ta waigo bata ga Prince ba.
Baya ta koma yana zaune cikin motar yadda ta barshi.
"Kenan ita ma motar baya iya budewa itama wahala ce? wannan wane irin Mulki ne da izzah??".
Murmushi tayi ta bude mashi motar.
A hankali ya sauko da kafar shi kasa, ya fito yana kara shan kamshi.
Kallon gidan ya gama yi yace; "babu kyau kadaicewa da mace".
Kallon shi take daman yana da ilimi ko dai dan bai son ta ne??
Kashe ido tayi cikin shagwaba tace, "Prince gidan bai maka bane? Amman nan gefen gari muke, daga nan sai University's din Katsina sai fita gari".
Hanyar mota ya koma tabi bayan shi.
Bude mashi motar tayi ya shiga ya zauna ta rufe, ta koma ta tada motar suka fita.
***************
Yau ma kamar kullum inda muke zama muka zauna, Shatu tace, "Allah yasa mu sai da da wuri muje cikin gari kamin Jabe ya dawo".
Muna nan zaune yau kam babu kasuwa.
Gashi lokaci sai tafiya yake Shatu tace; "yau babu kasuwa saboda dan sanyin da aka tashi dashi, kin san ba kowa ke shan fura ba idan akwai dan sanyi".
Mike tayi da kwaryar Nonon ta tace, "muje".
Kallon ta nike cikin mamaki nace; "amman fa kinsan bamu saida ba, kuma kin san Inna ba tada uzuri ko kadan".
"Na sani amman duk masu sayen furar mu, sai suce yau basu sha akwai dan sanyi, kin ga idan muka shiga binni kila mu samu masu saye ko, nima so nike ki saida ko dan Inna, ki samu raunin jikin ki ya warke kamin tayi maki wani".
Cikin amincewa da murna nace lallai Shatu na sona, nima na mike da kwaryar furata nace, "muje mu gani".
Tafiya muke har muka iso wajen wata makaranta inda muka ga maza da mata, wasu na shiga wasu na tsaye, kallo na bisu da shi dan ganin su nike wasu mutane na daban.
Shatu ta fini wayewa saboda da ita ta saba shiga burni, ni ko yaune rana ta farko da na tsallako burni.
Saida Shatu ta rike min hannu saboda yadda jikina ke kyarma, ganina nayi tamkar wata duniya naje, wai dama haka Burni yake da kyau?? Ya Allah yasa muna da rabo a gidan Aljannah, dan ni da birni sai gani sai hange, lokaci guda imani ya kara rufeni, ganina wata Alkarya wadda ban taba tunanin zuwa ba.
Kasan kafata na kallah naga shi kan shi wajen tafiyar mota ankayata, shi ba kamar jar kasar garin mu ba, haka Allah ya tsara ma kowane bawa rayuwarsu, kuma wadannan haka suke rayuwa cikin jin dadi.
Shatu ta katse min tunani, "lah Nanah kinga munzo wajen gidajennan da nike baki labari a birni, gasu can kin hangosu?".
Baki na saki ina kallon ikon Allah, jikina sai kara kyarma yake.
"Ni dai Shatu mu bar wajen nan tsoron mutanen nan nike, kuma ga mota na wuce tsoron su nike saboda ba irin na garin mu bane, ace mota ma hadda mai suffar kwado".
Dariya Shatu tayi tace; "shi yasa nace mu shiga yau Burni dake, ni kam na saba gani, ke nifa hadda malamin lafiya na taba gani, na taba bin yan matan tudu tallah wajen asibiti sai ma kinga masu fararen kaya kamar ba mutane ba".
"Tab ni kam ban ma iya zuwa ni dai mu rabe yau kinga wata rumfa chan muje babu mutane".
Wajen rumfar muka yi muka sake kayan mu, Shatu tace; "to taya za'ayi mu sai da sana'a ba mutane?? Kuma kin san idan Jabe yazo bai iskemu ba sai munyi fada, kin san bashida hakuri".
Hawaye har sun kawo min, jikina har yanzu kyarma yake ga faduwar gaba.
Muna nan zaune ko sai ga wasu yan makaranta maza suka ce, "yan mata furar ku nada dadi, mu saya?". Shatu tayi saurin cewa, "Eh akwai dadi ga nono mai kyau".
Nan fa suka yi mana ciniki jin dadin furar yasa suka ce mu dawo gobe tayi dadi zamu samu ciniki anan dan nan yan makaranta ke tsaya hawan mota, har ma dai idan akwai rana, Shatu tayi murmushi tace; "To mungode zamu dawo in dai za'a barmu mu zauna anan".
Suka ce, "kada ku dama ai tsoho ne angina sabo, wajen babu jama'a amman zamu yi maku tallah sai ku biya mu!". Suna maganar suna dariya.
Ita ma Shatu dariya take tace, "mun yarda sai Allah ya kaimu gobe, sunana Shatu ita kuma Nanah yar gidan Liman". Suka ce, "lallai yar gidan Liman kin iya fura".
Ni kam banda kyarma da zufa babu abinda nike, ga maganganun Baba na man yawo akaina samarin birni basu da tarbiyya, kullum hudu barshi akan na rike mutunci na duk da yana cewa ya aminta dani bai jina a duk inda zan shiga zan kiyaye.
Daya daga ciki yace, "Shatu kina ban kawar ki mai kyau?". Nan na kara jin gabana na faduwa, dariya Shatu tayi tace, "in dai kana mana tallah asan wajen zaman mu tunda nan babu mutane".
"Kada ki damu Allah ya kaimu". Muna cikin haka abokan su suka zo suna cewa me suke anan?? Nan suka fada masu, suma suka ce a basu harda manyan yan mata.
Zaunawa suka yi nayi tunanin gida yan matan zasu da tasu, kawai sai naga suma sun zauna zasu fara sha.
Cikin mamaki nake kallon su, taya za'ayi mace taci abinci cikin maza?? Lallai yan matan birni ba suda kunya, maganar Baba ashe haka ne.
Suna sha suna fira dayar da aka kira da wani suna da ban iyaba tace; "wallahi aboki ka taimake mu daman yunwa muke ji, amma duk da haka saina rama dukan da kayi man cikin makaranta". Hannu ta daga ta kaima namijin bugu.
Ban san sanda nace; "Subhanallah...!!". Tare da runtse ido kada naga an aikata haram da idona, mace ta kai hannun ta jikin namiji.
Su duka suka juyo suna kallo na rakube waje daya, suka ce, "lafiya wani abu ya cijeta mike samunta?".
Shatu da yake ta fahimci abinda ya faru sai tayi saurin cewa; "kanta ke mata ciwo ga jimuwar nan a koshin ta, shine ta taba taji zafi saitayi kara"wayyo sannu su duka suke cewa harda ku mutafi wani wuri shima sunan sa wuyar fadi,Wai a cikin makaranta cikin sauri nace"a'a kubar shi na gode"mun dan samu ciniki duk wanda yazo wuce sai ya tsaya ganin mutane wajen,har saura guda hudu cikin kwarya ta itama Shatu Nono ya kusa karewa.
************
Tafiya suke tara inda zasu sai ta hango wani waje yayi kyau da alama wurin kamar Company ne amman gefen shi anyi wajen zama mai kyau na ma'aikata,waya tayi baban ta tace ya tambayar masu izini ga wajen da suke.
Jim kada ya kirata yace suje su zauna.
Suna zuwa aka bude mata,cikin girmamawa tayi parking ta fito,yanzu ma ita ta bude mashi ya fito.
Suka zauna ta kalleshi tayi murmushi, tana tunanin shawarar Hanan.
A kan ta sakar mashi jikinta ai na miji ne,dole zaiji wani abu game da ita,tunda kalaman ta basuyi tasiri akan shiba.
Murmushi tayi tace cikin zuciyar"lallai kam shi ba dutsi bane"sai Kuma tayi wani tunani mutunan da yace bazai iya zama da itaba ba ita kade cikin gida inaga tashiga jikin shi.
Kusa dashi ta matsa, bai ce komai ba,hannunta ta saka a cikin nashi, lumshe ido tayi.
Cire hannun shi yayi, ta bude ido, wani kallo yayi mata yasa tasha jinin jikinta, sai ma matsawa da tayi tace, "sorry". Bai ko kalleta ba.
Ta rasa me zata yi mashi??
Mikewa yayi yaje ya dan yi tafiya kadan ya tsaya.
Kallo tabi inda yake kallo.
Wasu yanmata su biyu ta hango cikin rumfa, gaba dasu sun juya baya, ba'a ganin fuskar su.
"Me kake bukata?". Lumshe ido yayi yace; "su waye a chan mi suke yi,naga su kadai zaune?".
"Naga dazun da muka wutosu kamar fura suke saidawa".
Girgiza kai yayi ya koma ya zauna.
Chan Kuma sai ya mike ya nufi wajen, tayi saurin cewa; "Prince ina zaka?".
Ba tare da ya waigo ba yace; "wurin ina son fura".
Tafiya yake bai ji amsar taba.
Ta saki baki tana kallon shi.
Me zai yi wajen masu fura???
0 comments:
Post a Comment