Nayo alwala na dawo nayi raka'atanul fijir na zauna ina lazumi da hannu saida aka tada sallah kana nima na tashi na tada Sallah.
Ina gamawa na duba dakin ko ina babu alkur'ani nace a fili;"kila ba musulma bace Hajiya ta rika shiyasa tayi mata butulci tunda gashi ba Qur'ani a cikin daki, dan nasan musulma bazata iya zama daki babu Qur'ani ai bun kunya ne gareta"
Sai kuma nayi tunani nace kila kuma ta tafi da abunta bari safiya tayi na amso daya daga cikin na Hajiya.
Haka na zauna na fara tilawar na Kai har safiya ta waye.
Naji masu aikin Hajiya na aiki a tsakar gida.
Na mike zanje gaida Hajiya.
Ina zuwa bakin kofata mukayi kicibis zata shigo cikin dakina.
Na duka har kasa na gaida ta tace;"Haba Nana aini kamar Uwace anzama daya basai kinyi wahalar dukawa ba".
Nayi murmushi ta nuna man wani Abu tace;"ga wadirof nan akwai kaya ki duba a ciki naga bakida kiba wadan na sukayi maki saiki fidda kamin nadawo zan karo maki wasu wadan da sukayi maki yawa kuma ki ajesu waje daya idan nadawo kiban dan kada a tara maki tsumma"
Cikin murna nace;"lah Hajiya kibar su kala biyu ma sun isheni basai kin sawo man wasu ba"
Tace;"a'a nafison ki fito kiyi kyau, duk da kyaun ki ko wane irin kaya kikasa kyau suke maki ko tsumma ne bare sabbi, tunda nike bantaba cin karo da mai kyaun ki ga kuruciya shiyasa komi kikeso zaki samu"
Washe baki nayi nace;"Hajiya Nagode"
Tace;"bakomi yanzu za'a aiko maki da abinci idan bai maki ba ki fada akawo maki wani"
Ta juya ta fita na mike na buda inda ta nunaman nafara fiddo kayan duk babu kalar da nasani ganin kayan nike wasu iri ban taba ganinsu ba.
Atamfa a ciki kala hudu ne sai leshi daman bantaba daura leshi saide nagan shi jikin Yaya maimuna diyar Inna.
Cikin murna nike kallon leshin kara tabawa nike a hankali nace;"Yau nice zan saka leshi?"
Kara tabawa nike ina juya nace bama kalar nasu Yaya maimuna ba wannan yafi kyau.
Kayan sunada yawa sosai inagama fiddowa na mike zan gwada leshin doguwar rigace amman ga mamaki ba kalar dinkin garin mu ba wannan tun daga sama har kasa fadin su guda kallo nike cikin mamaki.
Ina kallon ta saiga Hajiya ta shigo cikin shiga Mai kyau sai kamshi take tana tamnar cingam ga gilashi a idonta hannunta rike da jikka Mai kyau.
Sakin baki nayi Ina kallon ta tace;"Na shirya zani cefane kasuwa kin gwada kayan ne, dan nasan kala nawa zan kara".
Cikin sauri nace;"yanzu zan gwada".
Tace;"saka black and maroon din les din hannunki abu ga farar fata nasan zai maki kyau sosai gashi yanada tsada"
Banson yadda zan saka ba dan mamaki nike ai wannan rigar idan nasaka ta zata matseman jiki kila ko numfashi ban iyawa.
Ta mikowan wani Abu tace;"ga towul nan cire kayan ki kisaka".
Na amsa nayi hanyar bandaki tace;"ke ina zaki bade cire kaya ba to aini macece ko zindir kina cire kaya a gaba na".
Na dukar da kai saboda ban iyawa.
Karatun Baba na tuna akan tsiraici.
Taya zan fada mata komu mata haram ne kallon tsiraicin juna.
Tace;"lalle kanki na cikin kwali tafi ki chanza watarana a gaba na zakiyi zindir"
Nayi gaba na shiga banda cikin raina nace;"Allah ya rabani da nuna tsiraici na ga kowa"
Na cire kayana na daura wannan Abun naga duk cinyoyi na a waje.
Nadade saida naji tana cewa;"lafiya Nana naji shiru"
Kana nayi shahada na fito ina matse kafafuna.
Dan karamin tsoki tayi tace;"nifa banason kauyan ci wallahi zanyi fama kenan?"
Ta mikaman tace;"Ina bireziyar ki?"
na dukar da kai saboda kunya saida ta maimaita kana nace;"A garin mu sai anyi aure ake sakawa "
Ta kalleni naga gabana take kallo na, naji babu dadi kafafuna har kyarma suke.
Ni kaina kwanakin nan naga gabana yayi girma sosai ya ciko shiyasa kullun gidan Inna da Hijab nike yawo dan gabana har yafi na Ma'u sosai kuma basu Dade da yin haka ba.
Wani wuri ta buda saiga bireziyoyi da yawa da wando sun fito ta dauko guda.
Tace;"saka"
Nace;"ban iyaba bansan ya ake sakawa ba"
Ta matso kusa dani ta dauraman tace;"kinga yadda nayi gobe ke zaki saka da kanki"
Na daga kai ita ta nunaman nasaka rigar.
Tace;"zage zip din"
Nace;"ban iyaba"
Tace;"lalle ba karamin daji kika fito ba"
Tazo ta saka man Zip na kalli kaina rigar ta matseni tun daga sama har kasa kirjini sun fito sosai sunyi sama kusan rabi duk a bude.
Tace;"yi tafiya nagani zaki iya yin tafiya cikin street gwon"
Ina takawa naji kamar rigar ta barke na juya naga wajen kafata ne a baya duk ta bude har kusan kinyata.
Nace;"bayan rigar ya barke ana ganin jikina"
Tayi murmushi tace;"haka dinki yake wallahi ban taba ganin wadda kaya suke ma kyau kamar ki ai duk kyawun ki dakika saka kayan nan sai naga ada banga komi ba tobarai na fiddo ki gari, kuma cikin ki cikin Nonu wanki yake shigewa shiyasa bazamu zuddashi yanzu ba sai ya fito kana amman da wahala yayi girma sosai tunda a Nonuwan ki yake shigewa, namayi mamaki dana ga har ya danyi tudu, kilade ba guda bane"
Nayi shiru kunya duk ta isheni miyasa wasu matan basujin kunyar fadin wani abu kai tsaye.
Kunya fa tana daga cikin imani....
Hajiya ta tsunke man tunani tace;"saka wannan nagani naga dakika saka street gwon kamar ke kikayi kanki, saka English wears nagani dan nasan wane zan siyo maki da yawa, amman basai kinje toilet chanza kaya ba"
Nace;"to"
Wasu riga da wando ne taban a tunani na kasan kaya ake sakasu.
Nasaka wandon da kyat ya matseni fiye da rigar dana cire, taban wata riga saman kafadar ta a bude nasaka.
Ihu tayi tace;"lalle sai an ringa layi a Restaurant dina Allah na gode maka jari a hannu wallahi nayi tafiyar sa'a yarinya tamkar ita ta kera kanta"
Nide sakin baki nayi ina kallon ta bangane mi take nufi ba.
Tace;"daga gobe garin nan zai fara cika duk yaran manyan kasar nan da iyayen su zasu shigo Bauchi dan haka damu da Hotel zamu sha ciniki kinga kenan Allah ya kawo ki lokacin da ya kamata dan ko makaho ya laluba ki saiya dawo gidan chin abinci na balle masu ido"
Ta rikitaman kwakwalwa narasa fahimtar ta toni ina ruwana da wasu yaran manya
Ta juya ta fita cikin farin ciki.
Na tashi na maida kayana na zauna saiga wani yaro ya kawo man abinci harda dafaffiyar kaza da soyayyan kwai.
Abinci ne iri-iri masu dadi aka ajeman ga lemu bana kwalba ba shi akwali yake ga sanyi.
Nayi murmushi na fara chii.
**************
Koda ya tashi da safe jikin shi ya saki yayi sallah ya zauna yana fitowa parlo ya iske kayan Breakfast ya zauna ya fara chi.
Jin abincin yake tamkar madachi saboda yadda yakejin zuciyar shi.
Magani ya gani a gefe yasan Momy ce yayi murmushi bai tsaya duba na komi minene ba ya balla yasha ya mike ya koma daki.
lumshe ido yake saboda yadda yake jin bacci.
Koma wa yayi ya kwanta bacci ya dauke shi.
************
Na gyara dakina hadda abubuwan kamshi na fesa naje nayi wanka na dawo duk cikin kayan banga wadan da zan saka ba sai wata doguwar riga bata da matsewa na saka na zauna naji shiru nayi kewar littattafai na.
Haka nayi cikin daki Hajiya bata dawo ba sai yamma ta iso da kaya masu yawa.
Na fita muka gaisa tace;"ga tailanan ya auna ki dan inason ya kawo kayan da wuri akwai wasu sabbin riga da wando dana siyo maki saiki saka gobe".
Kallona tellan keyi irin kallon da Lado keman yana hada miyau yana lasar labban shi matso kusa dani yayi.
Cikin raina nace"wai Hajiya karuwan ci take nufin nayi kenan??....kode ba haka take nufi ba nakasa gane inata dosa"
Jin mutum ya matso kusa dani yasa nayi saurin kallon shi.
Washe baki yayi yace;"Hajiya lalle zaki sami kaya ai koni da zaki taimakaman kiban ita kwana daya da har shekara ta kare kyauta zan maki dunki kuma dunkuna masu kyau wadan da idan mace ta saka su sai namiji ya kalla"
Zaro ido nayi ina kallon Hajiya dake murmushi tace;"wannan kalar manya ce kajii tana da tsana sosai"
Kallon gabana yake yace;"konan za'a huta"
Na runtse ido hawaye suka zuboman ina farin ciki zan huta ashe yanzu nafara fuskan tar rayuwa.
Jin hannu a gaba na an damki gabana nayi saurin bude ido.
Telan da Hajiya ta kawo ne.
Jinayi tamkar zuciyata zata fashe banson lokacin da wanka mashi mari ba.
Kallo na suke su duka cikin mamaki Hajiya ta zaro ido.
Tana kallo na ranta a bace.
Mamaki nike a gaban ta fa namiji zai ketaman mutunci to miyasa ta chanza fuska?
Tsawar da tayine ya maidoni daga duniyar tunanin dana shiga.
Jikake tas!! Karar marin da tayi mani.
Jinayi kaina na juya jawa nayi gaba nayi baya na sulale kasa.
Tush!!!
Qurrah
[2/28, 7:43 AM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *_JARABTAR MU*_
*_Written by-Qurrah✍🏼*_
*Page-47-48*
*Word Counter 2969*
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Addu'ar Fita Daga Bandaki.*
غُفْرَانَكَ. Ghufranak.
Ya Allah! Gafararka (na ke nema)
DEDICATED TO.....MY SISTERS😘
Page-47-48
_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_
----------------Kara na saki mai razanar wa.
Wani irin zafi naji a ƙasana na runtse ido nace; "Hajiya ki taimakaman ciwo"
Da Hajiya da tailanta suka kalli juna tailan yace; "Hajiya taho ga shawara na samu".
Tace; "Shehu ban son jin komai game da yarinyar nan tabar man gida, dan iskanci haihuwar ta nayi da zan rike ta inbata chi da sha da sutura sannan na mata duk abinda take so kenan a banza zanyi shi".
Jan hannun ta yayi suka shiga ɗaki tana ta bala'i yana bata hakuri.
Suna shiga ya kalli Hajiya yace; "Hajiya yarinyar nan karama ce yanzu dole taji tsoron iskan ci tunda baki san abinda iyayen ta sukayi mata ba kila korarta suka yi kinga yanzu kenan bazai bata sha'awa ba tunda kince man ciki gareta kuma shege ne"
Hajiya ta kalle shi tace; "to me kake nufi inta ajiyar ta ina kiyonta ita da abinda ke cikinta?"
Yayi murmushi yace; "Ina nufin ki biyo mata ta baya"
Tace; "kamar ya kuma ta baya?"
Yace; "yanzu muje ki kaita asibiti a duba ta ki kyaleta ta raini cikin ta kuma haihu, sannan kafin nan ina son ki nuna mata gata ki kashe mata kudi kamar ke kika haifeta"
Cikin bala'i ta zaro ido tace; "na lura dan kana kwaɗayin yarinyar nan ne yasa ka ruɗe, kana kallon taɓa ta fa za kayi shikenan ta mareka, to ina ga na kaita kwana da wani Allah kaɗai yasan me zata yi".
Yace; "lallai Hajiya duk barikin naki baki gama gogewa ba to bari kiji, ina nufin duk abinda kika sai mata yana nan a rubuce tana haihuwa ki miƙa mata takarda kice ta biyaki cikin wata guda koki dauke mata yaro ko yarinya, wallahi hankalin ta sai ya tashi uwa da Ɗah babu abinda ba zata iya yi ba, ko kuma ki ce ta nemi kuɗin idan kuma ba haka ba, to zaki kai yaran Ɗan nata office din 'yan sanda zaki kaita a kulle kisa a gwada ko kwana guda tayi wallahi da gudu zata bi layi".
Shewa tayi tare da guda suka kashe ita da Shehu tela tace; "zan baka ita ka rage yunwa amman kwana guda idan komai ya kankama".
Dariya sukayi yace; "ya kamata ki maido su Teema Baby da Sady ai sunyi nadama kinsan Teema ba dama, kuma idan taga yanda suke jin dadi kinsan fa zuciya yadda take kuma suna jan ra'ayinta a hankali kila da sai ta zudda cikin da kanta tabi layi".
Hajiya tayi shiru tana tunani tace; "kafa kawo shawara mai kyau" muje mugani mu kai ta asibiti.
Ina nan kwance riƙe da mara ina gujin wahala.
Da mamaki naji muryar Hajiya tana cewa; "Innalillahi Nana tashi muje asibiti, Allah yasa wani abu bai faru ba".
Ta kama ni muka fita Shehu ya bude motar Hajiyar ta sakani baya muka yi hanyar asibiti.
Ido a lumshe saboda yadda nike ji.
Kawai farkawa nayi na ganni kwance bisa gado da wata igiya a hannu na.
Hajiya tace;"sannu kin farka daman ƙarin ruwan ya kare bari na kira likita yazo ya cire maki".
Daga kai nayi ina kallon ɗakin mai kyau cikin raina nace komai yasa Hajiya ta hakura??.
Ina nan sai gata da wani likita.
Yace;"yar gidan Hajiya kin tashi ko?"
Ni dai kallon shi nike nakasa magana.
Yace; "Hajiya yarinyar nada kyau sosai kunyi saurin yi mata aure, Allah ya taimaka cikin bai zube ba amman tabi a hankali banda daukar kaya masu nauyi banda aikace-aikace Allah ya sauketa lapia".
Hajiya tace;"Doctor ina son wata alfarma ba mu taɓa irin wannan aikin da kai ba, so nike ka zudda cikin ta huta".
Cikin sauri nace; "Nikam ina son abuna, babu kyau zubdawa kuma mutuwa ake".
Na idasa maganar da kuka likitan kallo na yake sosai yace; "Hajiya ita 'yar wannan yarinyar BARIKI ta fito ko FADE aka yi mata , ai kamar bata kosa ba yanzu haka tausayin ta nike".
Hajiya tace; "Kai ko aita kosa wai kaga yadda ake aure a kauye, sannan cikin jikinta shege ne kila fade akayi mata".
Jin jina kai yayi yace; "Hajiyar kibar cikin nan tunda tana son abunta kada asamu matsala kinga har tana ambaton mutuwa sannan cikin ya fara girma, inda dai lokacin da yake ƙarami to da za'a iya zubawa, sannan kuma zubda ciki ai sai Jamil".
Hajiya tace; "shikenan ba matsala ai kamar gobe ne".
Yace;"to shikenan ga magunguna tasha, saura awo kuma".
Hajiya tace; "kada ka damu komai kai zaka taimaka ai".
Ya kalleni yace; "kada ki damu ni bana zubda ciki Dr Jamil ke zubar da ciki kuma an chanza mashi asibiti, yanzu ni zaki dinga ganii har ki haihu sunana Dr MUBARAK M NASIR zan taimaka naga kin haihu lafiya insha Allah".
Hajiya tace; "bani number Dr Jamil".
Yace; "Banda number shi amman zan saman maki kafin ku dawo"
Tace; "nagode"
Mika mata takardar hannunshi yayi ya juya ya fita daga dakin.
Tace; "idan kina iya tashi muje gida to ki tashi, dan nasan kin samu karfi ruwan da aka saka maki".
Nace; "Eh Hajiya marar ta saki, kamar babu ciwo"
Ta kamani tace;"sannu kinji Allah ya baki lafiya kinji ki haifaman jikoki".
Naji dadi amman naji kunya.
A cikin zuciyata ina jin farin ciki idan na taba cikina naji ya taso.
Na rasa meyasa yau nike son cikin kamar ba cikin shegeba sai wani jin dadi muke.
Kama hannu na tayi muka isa inda motar ta take na shiga gaba ita kuma ta zagaya tazo ta tuka.
♦♦♦♦♦
Koda ya tashi daga bacci yaji ya dan samu saukin ciwon Kai.
Message ya tura a waya sai ga Sanii ya shigo cikin sauri.
Toilet ya nuna mashi Sani yace;"Allah ya kara haske da farin ciki a Rayuwar magajin sarki mai A dalci idan ka gama akwai fura a parloun kasa, saƙo ne daga Gimbiya Rahama Maman MANAL".
Duk kuncin da yake ciki bai san lokacin da murmushi ya kubce mashi ba lokaci guda fuskar shi ta chanza zuwa murmushi.
Ya ɗaga ma Sani kai, Sani ya shiga ya hada mashi ruwan wanka tare da saka kayan kamshin da suka saka toilet din kamshi.
Ya shiga wanka yayi ya fito ya iske kayan da aka tanadar mashi .
Ya saka yazo bakin mirror yana kallon gashin kanshi da yake son gyara wa.
Cikin sauri mai mashi gyaran kai ya iso ya fara yana gamawa aka saka mashi wasu cover shoes kalar kayan ne ya saka mashi.
Yarima ya mike ya fito.
Yana sabkowa a parlon kasa yaga Rahama zaune da diyarta.
Cikin sauri ta aje diyar tazo ta rungume shi tace; 'i miss you so much Bro".
Murmushi yayi ya cire ta daga jikin shi ya nufi kujerar data aje diyar ta.
Cikin sauri ya dauketa fuskar shi da murmushi yayi kissing dinta a koshi ya mannata a kirjin shi yana sakin ajiyar zuciya.
Rahama dake tsaye hawaye sun cika mata ido ta iso ta hada su ta rungume tace;"Ina rokon Allah ya baka yara masu Albarka ya saka farin ciki a rayuwar ka na har abada, MANAL tace tayi fushi ba ka zo ganinta da wuri ba"
Murmushi yayi yace;"lokacin Dad baida lafiya amman tana raina a koda yaushe".
Kama hannunshi mai rauni tayi tace;"Bari na zuba maka fura daga Abie"
Ta sake shi ya zauna bisa kujera rungume da MANAL.
Ta zuba mashi fura ta mika mashi.
Ya amsa yace;"thank you"
Tayi murmushi yana son Rahama a cikin kannansa yana son Rahama sosai dan lokacin ita ta koya mashi yadda ake kalaba har yakema MANAL itama MANAL din tafi sabawa da ita akan kowa.
Bayan ya gama sha tace;"Su Momy sunyi Abuja wajen Mother's day gobe kuma sister's day amman a Katsina za'ayi shi, please Yaya Anuu ka taimaka kaje ko Deena ne".
Baiko kalle ta ba sai ma ɓata fuska da yayi yace; "tashi kibar nan".
Tace;"bazan karaba Yaya kasan a koda yaushe ina tare da kai kayi hakuri ".
Shiru yayi yana ma Jaririyar Hannun shi wasa yana mika hannun shi tana rikewa.
Ganin baida lokacin ta tace;"Zan wuce"
Yace;"me kike jira?"
Tace;"MANAL"
Shiru yayi yana kallon diyar yace; "zan kawo ta idan tayi kuka".
Tayi dariya tana hanyar fita tace;"Kulsoom ta huta mijin ta ya iya reno"
Tana gama fadin haka tayi saurin fita tana dariya.
Murmushi yayi ya cigaba da abinda yake.
Sosai yake kula da yarinyar kamar zai maida ta ciki, daya ga ta fara alamun kuka sai ya fara mata rawa da waka.
Duk kalolin wakokin da yakema MANAL yake mata.
Har saida tayi bacci Sani ya kira ya bashi wata takarda yasawo mashi madara kalar wadda ya ringa ba MANAL din shi tare da nuna mashi wani gado na yara, ya fadi mashi a MALL din da za'a sameshi, da mayukan wanka duk ya rubata mashi kalar da yake so.
Ba'a fi one hour ba sai ga Sani dasu baki daya.
Babu abinda Anuwar bai iya ba indai game da Jaririya ne.
Dare nayi yayi mata wanka ya sakata a gadonta.
Saida Ammie ta aiko kusan sha biyu na dare aka bada ta.
♦♦♦♦♦
Tunda muka dawo take ta ji dani kamar ba ita ce ta mare ni ba, kulawar da take nuna min har tafi na baya naji daɗi sosai .
Kwance nike ina jin bacci hankali na kwance.
Ga kayan marmari da Hajiya ta sawo man har saida na rage, ga kuma gasasshen Nama mai yawa shima.
Haka Hajiya taita jii dani a cikin kwanakin nan.
Ina jin hayaniyya sosai na masu sayen Abincin Hajiya.
Amman ban taɓa zuwa shagon taba kuma akwai kofa daga cikin gidan zuwa shagon ban fita saidai naji hayaniyya ko kofar daki nabar fita saidai a kawo man abinci a daki na.
Kuma hakan bai damu Hajiya ba sai ma cewa da take na zauna likita yace sai na kula banda aiki.
Ina jin dadin yadda Hajiya ke nuna ma cikina kauna.
Yau mun tashi safiyar Jummu'a tun kafin asuba ta waye naji motsi ina lekowa naga yaran Hajiya maza na aiki.
Sai aikin abinci ake nace kodai biki akeyi ne.
Nayi sallah nayo wanka yau ma kamar kullum saida nayi tilawar hadda dake cikin kaina saboda babu Qur'ani a ɗakin.
Ina gamawa na hau gado na kwanta.
Na dade ina bacci hayaniyya ce tasa na tashi.
Naje na wanke bakina da abinda Hajiya taban na wankin baki.
Na bude abincin da aka ban kamshin ya bugi hancina.
Na zauna naci nasha ruwa ga lemun kwali mai sanyi.
Shiru nayi ina tunanin wannan wane irin kirki ne ga Hajiyar nan tunda nazo gidanta ban taɓa cin abinci ba Nama ba kuma Naman mai yawa ga lemun kwali.
Hajiya ta shigo yau adonta yafi na kullum tace; "zan kawo maki sabbin kaya ki saka yau da gobe saboda zaki dinga fita saboda jikin ki ya dinga saki, zama waje daya yana iya haifar ma cikin nan matsala, Amman idan kina motsa jikin za kiji sauki kuma ko wajen haihuwa zakiji saukin ta".
Nayi saurin yin murmushi nace;"Nagode Hajiya Allah ya saka maki da Alkhairi"
Tace; "ba komai yanzu zan aiko maki dasu doguwar rigace yanda zakiji dadin kayan babu matsi"
Nace;"to Hajiya wai biki kuke ne?"
Tace;" a'a babban dan sarki kuma ɗa ga president shine ake bikin shi garin ko ina cike yake shiyasa muke cikin chiniki, shiyasa tun kafin asuba muka tashi muka saka sanwar abinci bakiji kide-kide ba"
Nace;"Allah sarki ba kuda nisa kenan?"
Tace;"Eh babu nisa sosai nan ai bayan gidan ne wajen kofar shigar bayin gida"
Nace;"Bayin suma tasu kofar damaban"
Tace;"Eh daga baya akayi ta sabon ginine akayi masu duk saboda auren"
Najin jina kai cikin Raina nace kowa ne bawa da tashi rayuwar wani ta talaka wani mai kudii gamunan dai nima nayi hamdala nace;"Allah na gode maka yina musulmai da kayi shi kaɗai ma ya isheni abin alfahari Allah kayi mana rabo a gobe kiyama".
Jin shiru yasa Hajiya tace;"Bari in aiko ki tashi ki kara wanka zuwa la'asar sai mu fita, daga yanzu zamu dinga fita da yamma kullum har ki haihu kodan lafiyar ki, kinga har wajen gidan Sarki sai mu dinga zuwa yauma chan wajen zamu mu kalli wasannin gargajiya Yau har Yarima saiya fito ya zaga gari shiyasa Yau kamar sallah take a gare mu"
A hankali na maimaita;"Yarima....."
Na mike naje nayi wanka hakanan naji ban son fita saboda yanzu cikina ya fito ina jin kunya Amman ba zan iya yima Hajiya gardama ba.
Ina fitowa na iske Hajiya ta mikoman wata riga ta less mai shegen kyau tace;"gashi nan Bubu ce yadda zakiji dadi babu takura".
Na amsa na saka tace;"Masha Allah ta koyi maki kyau ga turarruka nan ki saka, kinga Man da zakiyi amfani dashi saboda ke hasken ki yayi dai-dai basaikin saka wani mai ba kuma gaki da ciki kiyi sauri ina jiran ki ina shago".
♦♦♦♦♦
Ba ruwan shi da mutanen gidan ko Mai Martaba a masallaci suke gaisawa bai zuwa part dinshi.
Ammie kuma mutane sunyi mata yawa saboda gidan cike yake tun laraba har zuwa yau jummu'a.
Tun safe ake kawo mashi MANAL sai dare azo a dauketa hakan yasa baidamu da abinda akeyi ba kullum yana nan yana hidimar MANAL shi kaɗai a part ɗin shi sai idan yana bukatar wani Abu kana yasa akawo mashi.
Jawad ne kanin shi ya shigo cike da fara'a a fuskar shi yace;"Ina Angon Kulsoom yake gani na iso tare da Daddy"
Yana rungume da MANAL ya gama bata madara dinta, goge mata madarar dake gefen bakin ta yake.
Baiko kalli Jawad ba sai cigaba da abinda yake yayi.
Jawad bai damu ba yazo kusa dashi ya fada bisa kujera yana kiran;"Wash nagaji kamar dai nine angon, Ango yana dakin shi yana hutawa ni kuma ina chan bani Abuja bani Katsina"
Anuwar bai kalle shi ba yace;"waya saka ka?"
Dariya yayi yace;"kayan da kasa nayi order ne na kawo maka yau jummu'a ya kamata ka saka su dan zamuyi hawa gobe daurin aure Daddy yayi maku dinki"
Kallan shi yayi yace;"banso malam ina ruwan ka da kayan da zan saka, nace maka zanyi kwalliya ne"
Jawad yayi dariya yace;"kasani ko wadda ka sayesu saboda ita ta gani , saboda nasan tana hawa social media kuma photunanka na yau da gobe babu inda ba zasu je ba, wai ka kalli Vedion shagalillikan da aka sha a Abuja da Katsina ko ina maganar shi ake ka duba yanzu a Twitter ko Facebook ko IG kai ko ina maganar bikin ak,matsalar guda babu Ango kowa yana son ganin ka kaga yau sai farar fatar nan tayi duhu saboda yadda za'a dinga daukar ka da Camera ka kaga zaifi ka saka kayan"
Wani kallon Anuwar yayi ma Jawad yayi tsaki ya cigaba da wasa da MANAL.
Jawad yace;"Na rantse maka sai ta ga photan nan kuma sai ta yaba, kayan a fili sunfi kyau wallahi"
Anuwar yace;"Naji zan saka kodan Daddy amman bana son shegen surutun nan naka tafi nagode"
Jawad ya mike yana dariya yace;"sai mun hade zuwa an jima"
Ya bar part din yana dariya.
Kiran hadiman shi yayi suka zo suka hada mashi ruwan wanka,ya kira aka dauki MANAL, yayi wanka ya saka kayan.
A bakin mirror yazo ya tsaya lalle kayan sun mashi kyau yace;
Ina ma ace wadda aka saya saboda ita tana nan ta gani nasan zata yaba"
Murmushi yayi yana kallon mirror Allah ya jikan su baki daya.
Fitowa yayi part din Abie ya nufa yasan Daddy yana chan.
Ta baya yabi saboda bai son hayaniyya yana zuwa ya shiga kai tsaye.
Daddy da Abie suna zaune da sauran iyayen shi sun sha kwalliya suma sosai.
Ya dukar da kai kasa yana kwasar gaisuwa.
Su duka suka amsa cikin fara'a.
Daddy yace;"lalle wannan kwalliya ta daban ce Ango ya kamata wadda akayi dan ita tagani".
Su duka sukayi dariya kowa da abinda yake cewa shi dai kanshi a kasa.
Hakanan Yau kodan tana jummu'a kuma ya dade bai zagaya ba, hakanan yaji yana son fitar.
Daddy yace;"Nan zaki yi sallah ko, dan har angama kwalliyar dawa kan tun dazun Sallah muke jira ayi".
Yace;"To Dad".
Daddy yace;"Anya Yau ba'a wani abu a kasa ba? naga Yau kana dokin zagaya kodan duk dokin auren ne"
Ya ida Maganar yana murmushi.
Murmushi Anuwar yayi haka nan ya tsinci kanshi cikin farin ciki tunda ya saka kayan nan ko miyasa??
Ohow....
♦♦♦♦♦
Ban iya kwalliya ba saita kauye shiyasa banyi ba mai ne kawai na shafa sai farar hoda sai Man baki.
Hajiya ta shigo tace;"har nagaji wallahi so nike kiyi sauri mu fita musamu wajen zama inda zamu fi kallo, amman har yanzu baki ida ba"
Nace;"Hajiya Dan kwalin ne babba ban iya daura shi ba".
Tace;"fito waje ga 'yan mata nan su daura maki".
Na fito gidan cike da mata da maza su duka suka kallo ni.
Duk sai naji babu dadi jinayi kamar na koma.
Na kalli Hajiya naga tana kiran wata da zata fita hankalin ta na chan.
Anya kuwa zan iya zuwa??
Mutanen dake cikin gidan Hajiya sune suka ni ruɗewa ina ga na shiga taro, Kai bazan iyaba komawa zanyi daki.
Bazan iya fita ba amman kuma lafiyar jiki na kuma fa, to ko dai na tafi ko kuma nayi wata dubarar????
Qurrh
*_JARABTAR MU*_
*_Written by-Qurrah✍🏼*_
*Page_49-50*
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Zikiri Bayan Gama Alwala.*
أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَـهَ إِلاّ اللهُ وَحْدَهُ لا شَريـكَ لَـهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمّـداً عَبْـدُهُ وَرَسـولُـهُ.
Ashhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, wa-ashhadu anna Muhammadan abduhu warasooluh.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a tare da shi; kuma ina shaidawa cewa Muhammadu bawansa ne.
kuma
اَللَّهُـمَّ اجْعَلْنِـي مِنَ التَّـوّابِينَ وَاجْعَـلْنِي مِنَ الْمُتَطَهِّـرِينَ.
Allahummaj-alnee minat-tawwabeena waj'alnee minal-mutatahhireen.
Ya Allah! Ka sanya ni a cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni a cikin masu tsarkaka.
15.
سُبْحَـانَكَ اللّهُـمَّ وَبِحَمْدِكَ أَشْهَـدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَـيْكَ .
Subhanakal-lahumma wabihamdika ashhadu an la ilaha illa anta astaghfiruka wa-atoobu ilayka.
Tsarki ya tabbata gare Ka ya Allah tare da yabo gare Ka. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafarka kuma ina tuba gareKa.
DEDICATED TO.....MY SISTERS😘
Page_49-50
_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_
--------------Hajiya ta waigo ta ganni ina tsaye na kasa ko motsi.
Tace; "a'a Nana ke muke jira fa, taho Zuby ta daura maki mu tafi ".
Dukar da kai nayi kasa a hankali na karasa inda su Hajiya suke.
Hajiya tace; "banson wannan ɗari-ɗarin da kike yi da jama'a ya kamata ki saki jikin ki, ki saba dasu koba da mazan ba koda matan ne kaɗai".
Na kara dukar da kaina a kasa ina wasa da ya tsuna nace;"to shikenan Hajiya zan gyara insha Allah".
Bisa ɗaya daga cikin kujerun robar dake a tsakar gidan ta na zauna.
Wacce ake kira da Zuby ta amshi kallabina, tana ta wata karairaya tana chin cingam tace;"Yarinyar Hajiya ki tsaida kanki waje guda na yi maki dauri mai kyau"
Nidi na kasa magana na daga kai kawai.
Ta matso kusa dani turaren jikin ta ko kaɗan banason shi haka nan na daure na tsaya.
Mun dauki dan lokaci sannan tace angama.
Saboda ban saba ba sai naji duk an daure man kai na takura ga kallabin yayi man nauyi, amman ban nuna hakan ba saboda yadda Hajiya take kokari a kaina.
Hajiya tace; "wallahi har ta kara kyau"
Zuby ta juyar da ido tamkar tana gaban saurayin ta tace;"ai wannan Hajiya da kyawun ta saboda koya ta fito sai kyawun ta ya fita, shiyasa banyi farin cikin zuwan ta nan ba, dan kinsan yaran kauye basu iya waye ba".
Hajiya tace;"Ya isa haka Zuby wannan ba kalar ku bace, wannan ɗiya ta ce bata kalar harkar ku taimako ne zanyi".
Cikin sauri duk wa'inda ke wajen suka kallo mu.
Zuby zata yi magana Hajiya ta daga mata hannu tace;"muje Nana sauri muke"
Wani farin ciki ne ya ziyarci zuciya ta hakan yasa na fita ina murmushi.
Hajiya tace;"Ki kula sosai da duk inda muka je, saboda wajen manyan mutane ne kada ki saki baki kina kalan su kiyi murmushi kinji, dan nasan ke komai sabo ne a wajen ki, kada ki fiye yawan kallon su kinji sannan idan zaki yi magana ki kwantar da murya, duk da daman ke baki da karfin murya".
Nace;",to shikenan Hajiya zan kiyaye".
Tamkar ranar Sallah haka naga mutane suna farin ciki kusan duk wanda zaka gani yayi kwalliya.
Abin ya ban mamaki kawai saboda auren mutum guda baki daya gari ya sauya.
Tun kafin mu isa get din bayin gidan wato sabon get din da aka bude na hango mutane babu wajen zama duk wajen ya cika sosai.
Hajiya tace;"Mu zagaya tsohon dan nan ya cika, daman munzo nan saboda nasan zaifi saukin mutane chan tun dazun nasan ya chika amman muje mugani".
Nace;"Hajiya nagaji muje mu zauna chan tunda kinche wanchan yafi cika, ko kije zan tafo idan na gama kallon nan"
Hajiya tace;"ina zanbar ki ke kaɗai da wannan ciki haka, baki da kuzari yadda ya kamata kuma idan Yarima zai fito turereniyar ganinshi kesawa a dunga ture wasu saidai duk inda zani naje dake, idan ba haka ba kamin ma ki mike wani ya taushe ki, muje kawai".
Nace;"Hajiya wallahi zan kula da kaina sosai na maki alkawari kuma nima zan biyo ki dana gama insha Allah".
Hajiya dai bata soba hakanan ta tafi ta barni, na riga da nagano nufin ta wannan get din babu manyan mutan da take nufii yawanci duk yara ne da manyan yaku bayi.
Ban damu da abinda suke ba, Hajiya na wucewa na matsa na zauna bisa wata kujera cikin wata runfa ina kallon mutanen dake wajen kowa ne yana sabgar gaban shi, wasu na rawa wasu na kallo kidan da ake kallar na garinmu ne na gargajiya.
Ganin mutanen yasa zuciya ta wasai ni kaina da bani wani abu nike ba amman na rage kewa ne wannan.
Murmushi nike ina kallon su, Inna ta Fado man a rai na girgiza kai, ranar Sallah ana kide-kiden nan a kofar gidan mai gari kowa zaije kallo ban dani, amman yau gani ga kidan.
Hawayen da suka gangaro min nasa hannu na goge lalle nayi kewar Babana yanzu kowa ne hali yake ciki??
Nayi zurfi sosai a cikin tunanin gidan mu tare da kewar su.
♦♦♦♦♦
Tare da Daddy ya fito Daddy na rike da hannun shi ko ina kamshi ke tashi ana ta zuba masu flowers masu kyau da kamshi.
Murmushi yake Dad ma murmushi yake, inda Abie yake zaune suka nufa shima Abie fuskar sa dauke da murmushi.
Yana isa zai duka Abie ya mikar dashi tare da rungume shi.
Jawad ne ya iso da Khalil suma cikin shiga ta alfarma kalar na sarauta.
Abie ya saki Anuwar yayi saurin kama hannun su yace;"ka tafi wajen Dad dinka yara na sun iso ina kukabar Walid?"
Daddy yace;"kafin a gansu Ɗana ake fara gani, taho Anun muje ka hau dokin ka an riga da angama komai mutane na jira kaji My son"
Murmushi yayi ya daga Kai.
Jawad yace;"ga Walida nan zuwa Abie muma muje angama hada namu, wai muzamu ta kema Yaya Anuu baya inji Daddy".
Daddy yayi murmushi yace;"daga taimako idan baku so kuyi zaman ku fita da Anuu dina ai matsayi ne ma".
Abie yace;"ku kyalesu kaji Jawad kuje ku hau amman ba take mashi baya za kuyi ba, shima daga kun taimaka mashi"
Nan de sukayi dariya Anuu yaje ya hau dokin yana murmushi.
Tun daga kwalliyar dawakan su zaka gane wanene Anuwar adon nashi ya fita daban dana saura.
A karamin get zasu fara fita su zagaya sai su iso babban get nan zasu dawo.
Hakan yasa suka nufo get din.
Anuwar banda kallon jama'a babu abinda yake sai su Jawad dake ta daga hannu.
♦♦♦♦♦
Zaune nike ina tunanin su Baba sosai hankali na ya dauku.
Wani irin kuwa da ihu da mutane suka yi yasa na dawo daga duniyar tunani.
Ganin ana ta gudu ana matsawa ga 'yan sanda sai turowa baya suke yasa ni tunanin ko me ke faruwa...?
Ban ida tunanin da nike ba naji wani kiɗi tare da wata busa.....
Kiɗin da busar jinsu nayi har tsakiyar kwakwalwata wani irin yana yi na jini ciki.
Kaina na rike dake sarawa.....
Rufe ido nayi ina karanto addu'o'i tare da toshe kunne na saboda yadda busar da kidan ke shiga cikin kunne na.....
Wata irin kara na sakii...!!
Jinayi mutane sun fado kaina an tausheni ihu nike ina kara amman ba Wanda ya damu dani sai takeni ake.
♦♦♦♦♦
Karar da Yarima yaji yasa tsigar jikin shi tashi.
Tare da saurin toshe kunnen shi.
Har yabar wajen kunnen shi a toshe saida aka wuce kana ya saki ajiyar zuciya.
Tunani yake wai meyasa duk inda yaje sai yaji wani abun da zai tuno mashi MANAL wannan irin karar tace.
Haka dai yayta tunanin abubuwan dake faruwa tun da yaje Katsina aka samu matsala, tun daga haduwar shi da yarinyar nan Mai fura komai ya chanza kodai Aljana ce da gaske??
Kuma ai tana da iyaye lalle sai ya bisu yaji komai game da ita, koda bata raye
♦♦♦♦♦
Wani karfafen namiji ya dagoni yana dagoni jini ke zubar min.
Biyu-biyu nike ganin shi saboda yadda na galabaita.
Hajiya ganin baki maza da mata kuma kalar wa'inda take son taga Nana dasu, hakan yasa ta kagara ta iso wajen da take tun kamin Yarima ya iso wurin ya har mutse.
Tsaki kawai take tun dazun ganin lokaci ya kusa Yarima ya kusa isowa Nanah bata zoba yasa tace ma mutanen da take tare dasu bari ta dawo.
Tana zuwa ta hango wani dauke da Nana daya daga cikin masu aikin gidan Sarki dan akwai Uniform a jikin shi mota taga za'a saka ta a guje ta isa wajen.
Aza hannu tayi kai dan a tunaninta ta rasu.
Tace; "wayyo Allah shikenan Nana ta mutu daman hankali na bai kwanta ba da barin ki ke kaɗai a wajen nan"
Waigo wa yayi yana kallon ta yace;"Diyar kice".
Daga kai tayi tana matsar kwallah
Yace;"yi sauri mukaita asibiti shiga mota mutafi".
Cikin sauri ta shiga mota basu zame ko ina ba sai wani hadaden private Hospital mai suna MANAL.
Tace;"Malam banda kudin kawo ta asibitin kudi"
Ya dan waigo yace;"Kada kidamu a MANAL ba'a amsar kudin ku na Yarima ne kyauta ake komai".
Kallon shi tayi cikin mamaki tace;"amman ai a garin nan nike ban tabajin haka ba"
Mutanan kauyen nan na kusa da ita aka bude mawa ta dade ta kusa shekara biyar anan.
Tace;"nasan ta dade dan ina ganinta ko a labarai dan duk Nigeria ance babu asibiti mai kyawunta, amman meyasa yayi ta anan kuma mutanen kauye kaɗai a tunani na 'yan gidan kadai ake dubawa?".
Yace;"Hajiya mun iso bari a fidda yarinyar ayi ta lafiyar jikin ta kana"
Cikin sauri aka amshe ta akayi ciki da ita.
Hajiya ita dai ta kagara taji wannan labarin tasan komai na gidan sunan MANAL ne a jiki, to amman meyasa akayi anan, shin waima wacece wannan MANAL bata mutu ba amman meyasa sunan ta ya kasa bacewa labarin ya rikice mata tasan MANAL 'yar gidan ce kuma asibitin 'yan gidan kaɗai ake dubawa meyasa hadda mutanan kauye?? gidan basu da alaka da wannan kauyen to amman miyasa suke son kauyen??
Gashi ma ana ginin lambu kusa da asibitin kamar kasar waje idan ka shiga ciki.
Ita ta manta da ciwon Nana tunanin ina zata samu cikakken wannan labarin take.
Shi kuma wanda suka zo ganin tana ta zagaye wajen a tunanin shi duk damuwar ciwon diyar tane hakan yasa ya matso yace;
"Hajiya kiyi hakuri zata farfado insha Allah, sunana Sanii anan kauyen nake amman a gidan Sarki nake aiki shiyasa ma na kawo ku nan yadda za'a kula da ita".
Hajiya tayi murmushi tace;"mun gode bawan Allah".
Doctor ne ya fito daga cikin dakin da aka shigar da ita.
Hajiya tace;"lah! Doctor Mubarak daman kana aiki anan".
Yace;"Eh Hajiya"
Ya fada cikin sauri yace;"Hajiya akwai matsala yarinyar nan na bukatar jini sosai idan ba haka ba abinda ke cikin ta da ita kanta akwai matsala za'a iya rasasu"..
Wata Nurse ce ta iso cikin sauri tace;"Doctor akwai matsala babu jininta jininta O- ne".
Cikin sauri ya kalle ta tare da cewa;"Innalillahi...! Yanzu ya za'ayi kenan?"
Sani ya matso yace;"Lafiya Mubarak kayi mana bayani"
Yace;"wallahi jininta wahala yake cikin mutum dari baifi mutum goma ko biyar ke dashi ba, ni wallahi mutum guda nasani dashi".
Cikin sauri Hajiya tace;"waye?? Doctor Mubarak ka taimaka mana gata ga abinda ke cikin ta ka rokan mana shi".
Ajiyar zuciya yayi yace a hankali kamar mai rada;"Yarima Anuu....."
Shiru yayi dan yasan abinda ba zai yiyu bane.
Sani yace;"Kana nufin Yarima Anuwar kenan?"
Daga kai yayi, shima Sanin shiru yayi.
Cikin sauri Hajiya tace;"Dan Allah Sani ka taimaka mana, kaje ka fada mashi halin da muke ciki ka tausaya ma marainiyyar Allah gata ga abinda ke cikin ta".
Mubarak yace;"Sani kataimaka Anuwar aboki nane amman ka fini kusan ci dashi nasan da wahala amman nima zanyi nawa kokarin yarinyar nan twins ne a cikin ta, tunda suka zo last time nayi mata scanning nagani shiyasa nace ma Hajiya bana zubda ciki ban fada maki ba saboda ganin baki murna da cikin, ganin kina bukatar zudda ɗaya ina ga nace biyu ne".
Sani yace;"kana nufin 'yan biyu ne cikin ta".
Daga kai yayi Sani yace;"Bari naje wajen Mai martaba shima da wahala na ganshi Yau saboda baki sun mashi yawa, idan ban ganshi ba zanje wajen Fulani mahaifiyar Anuwar duk da itama ganinta akwai wahala ne a yau".
Mubarak yace;"Sani kayi kokari akwai matsala zan mata wasu alurai kamin lokacin da zaizo zan mashi Message dan nasan bai daukar Call".
Sani ya juya ya fita Hajiya tayi tagumi, lalle yarinyar nan har wahalar yau tana cikin list din kudin da zata biyani.
Doctor Mubarak ya juya ya koma ciki.
♦♦♦♦♦
Baki daya fuskar shi babu annuri a tare da ita.
Haka suka gama zagaya suna isa ya sabka yayi part dinshi cikin sauri.
Su Jawad suka kalli juna miyasa lokaci guda ya chanza shida aka fito ana murmushi tare dashi amman suna dawowa duk ya chanza.
Yana isa part dinshi ya kori kowa yace kada a sake a bude mashi daki kowa ke neman shi har zuwa gobe yana bukatar hutu.
A bisa bed dinshi ya fada rufe kunnuwan shi ya toshe baya son karar da yaji har yanzu yana jinta cikin kanshi.
Rufe kunnuwan shi yayi, jin ana debe mashi ta kalma yasa ya dawo hayyacin shi.
Jawad ne ya cire mashi takalmin kafar shi.
Cikin bacin rai yace;"Miya kawo ka part dina banace bana bukatar kowa ba kowa?? bana son ganin kowamiya kawo ka shigoman part??"
Ciki tsawa! yayi maganar tare da zare ido.
Jikin Jawad sai kyarma yake baitaba ganin Anuwar cikin wannan yanayin ba yanzu fa suka fita yana murmushi kuma tare sukayi zagaya babu wanda ya bata mashi saima so da kauna da ake nuna mashi..
Bai ida tunanin shi ba yaji ya daka mashi tsawa! yace;"Fita! fita! fita nace".
Cikin sauri ya mike yayi wajen Anuwar yaje ya kulle ko Ina ya dawo ya fada bisa gado yana toshe kunne.
Cikin sauri yayi toilet sakar ma kanshi yayi ruwa yana maida numfashi.
Koda Sani ya iso yayi iyakar kokarin shi Amman Mai martaba bai ganuwa gashi Daddy yana tare dashi manyan matakan tsaro aka saka a part din Mai martaba sojoji ne gasunan tsaye kamar wajen yaki saboda Dad yana ciki ga manyan mutane na kasa Nigeria dana kasashen ketare.
Part din Ammie ya nufa tareshi akayi ba'a barin maza zuwa wajen, gashi duk an chanza masu tsaron gidan duk ba wadan da yasaba dasu bane ballen tana ace sunsan matsayin shi wadannan ko Hausa basuji.
Part din Momy 'yan matane su Nifra ne a ciki Momy na part din Ammie.
Nan ma matakan tsaro ya iske inyamurai basujin yaren shi.
Da'ace zaiga Walida da da sauki zama yayi kusa da part din ko Walida zata fito.
Har dare ya fara ba Walida.
Ya mike yayi masallaci yayi salloli ya dawo part din Anuwar kamar nan shugan kasar yake yafi ko ina matakan tsaro.
Haka yayita yawo babu kowa cikin yaran gidan sai mutane ko ina anata raye-raye da kide-kide bayin gidan duk gasunan saboda an chanza ma'aikata.
Zuwa yayi bakin kofar part din Yarima ya zauna nan bacci ya dauke shi.
Saida ya dauki lokaci kana ya fito kaya ya chanza ya dawo bakin window ya tsaya kokadan baijin bacci.
Saida dare yayi sosai kana ya kwanta.
♦♦♦♦♦
Hajiya dake zaune Doctor Mubarak ya fito yace;"Hajiya ga daki nan ki shiga ki kwanta kamin gobe da safe nayi mashi Message bai dubaba na kirashi bai dauka ba amman nasan Sani zaiyi iyakar kokarin shi dan yanada mutumci, Kuma Yarima yanada tausayi idan har yaji abinda ke faruwa tozaizo nan insha Allah".
Tace;"to shikenan nagode Mubarak"
Saida Hajiya ta leka dakin da Nana take kwance ta hango ta ko motsi batayi, kana ta shiga dakin daya nuna mata, saboda Sani kawai yasa take wahalar nan da tuni tayi gida babu mai kara ganinta tanason jin labarin nan saboda tasan labarin MANAL amman batason wannan ba, batason miya suke son gefen ruwan nan ba ko minene dalili??
A jiyar zuciya tayi tare da tsoki yarinyar nan tasa tayi asarar costumers.
Haka ta kwanta bisa gado mai kyau ta juya sai bacci.
♦♦♦♦♦
Bai runtsa ba har akayi asuba.
Yaune safiyar daurin aure kuma karfe Tara Daddy yace zasu airport koma yayi ya kwanta saboda bai sami bacci.
♦♦♦♦♦
Doctor Mubarak ne ya tada Hajiya.
Ganin yanayin sa yasa ta murmuje ido yace;"Hajiya kiyi wani abu mana yarinyar nan zata iya rasa ranta duk nayi magana asibitocin garin nan babu shi idan kinsan akwai mai kalar jinin ni zan saya nasan kina hudda na mutane da yawa".
Hajiya tace;"Mubarak Koda ina hudda da mutane tambayar su zanyi kalar jinin su basan mai Shiba koni bansan kalar jinina ba balle na wasu"
Yace;"Bari naje gidan da kaina Allah yasa bai wuce daurin aure ba"
Mubarak ya fita cikin sauri yabar Hajiya zaune.
Tana murguda baki anya yarinyar nan Alkhairi ce a gareta??
Anya ba korarta zatayi ba idan ta warke zata iya daurewa tayi wahala cikin watannin da suka rage Anya tana iyawa??
♦♦♦♦♦
Jin ana tadashi yasa ya bude ido.
Ganin Dad yasa yayi saurin bude ido.
Dad yace;"ka kyauta Anu saura one hour jirgin mu ya tashi amman ace kai bacci kakeyi kowa ya fita a tunanin mu kana nan kagama shiryawa to mungode yauma kabamu kunya ka tuzar tamu a idon jama'a zargin da yan garin ke maka ya tabbata kenan mungode kaji Anuwar"
Daga haka ya fita rai bace yabar dakin tashi yayi ya shiga toilet Jawad ya hada mashi ruwan wanka.
Koda ya fito an ajemashi kaya yana sakawa Jawad ya shigo ya saka mashi takalmi ya mika mashi hula hannunshi ya kama ya saka mashi agogo.
Duk abinda ake Anuwar sai bata rai yake duk abinda yake saboda ganin ran Dad ya baci yasa yake sauri.
Baifi fourty minutes ba ya fito tare da Jawad.
Yana fitowa aka rufa mashi baya.
Kai tsaye wajen motoci yayi, yana zuwa zai shiga mota yaji muryar Sani yana kiran shi cikin dagawar Murya kuma Anuwar yau yace ba Yarima ba.
Juyawa yayi yaga Security sun hanashi matsowa sun rikeshi.
Abin mamaki ya bashi daga masu hannu yayi Sani ya iso a guje ya dukarsa.
Kafafun shi ya kama yace;"Anuwar ka taimaka kayi ceton ran mutane da yawa, Kai kade ne zaka iya ceton ran yarinyar nan da abinda ke cikin ta"
Kallon Sani yake bai gane miyake nufiba, da yayi ceton rai shida ba Doctor ba minene nashi a ciki?? Idan kudi yakeso ai kwai Hospital kuma yasani.
Dai-dai lokacin da Doctor Mubarak ya iso.
Ya kalli Anuwar nan yake mashi bayani abinda ke faruwa.
Shiru Anuwar yayi bazai iya barin ayi asarar rai ta dalilin shi ba amman kuma Dad da Abie da sauran mutane fa??
Kallon agogon hannunshi yayi ya zaro ido....
Qurrah
*_JARABTAR MU*_
*_Written by-Qurrah✍🏼*_
*Page-51-52*
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Zikiri Yayin Shiga Gida.*
بِسْـمِ اللهِ وَلَجْنَـا، وَبِسْـمِ اللهِ خَـرَجْنَـا، وَعَلَـى رَبِّنَـا تَوَكَّلْـنَا .
Bismil-lahi walajna, wabismil-lahi kharajna, wa'ala rabbina tawakkalna.
Da sunan Allah muka shiga, kuma da sunansa muka fita kuma ga Allah kadai, Ubangijinmu, muka dogara.
DEDICATED TO.....MY SISTERS😘
Page-51-52
_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_
----------------Cikin sauri yayi yun kurin shiga mota.
Doctor Mubarak yace;"Prince yarinyar nan karamar yarinya ce kuma twins ne a jikin ta marainiyya ce sannan kasan O- wahalar samu ne dashi, idan bakai ba wallahi ban san wani dashi ba sai matar ka data rasu, nasan da tana da rai na tabbata yadda take da tausayi kuma take son taimako tun tana yarinya da yanzu ta bayar, nasan halinku iri daya ne amman meyasa zaka chanza daga halin data mutu tabar ka dashi".
Kallon shi Anuwar yake ga Security tsaye ga time na tafiya.
Mubarak yace;"time din idan akayi sauri zai isa".
Ɗa ga mashu hannu yayi sannan yayi nuni daya shiga mota.
Prince ya shiga mota aka rufe Mubarak zai shiga Security suka nuna mashi motar bayan Prince.
Ya koma suka shiga shida Sani suka wuce.
Cikin mintuna kaɗan suka isa asibitin koda suka isa babu Hajiya.
Basu damu ba cikin sauri suka isa Lab aka gama abinda za'ayi aka ɗibi jinin Prince, koda aka gama saura ten minutes jirgi ya tashi cikin sauri Prince ya juya yabar asibitin.
Ina bude ido naga jini na shiga a jikina lumshe ido nayi ina tunanin jinin waye ake sakaman? nan na tuna irin yadda busar gidan Sarki da kidan gidan suka fara tashi, ashe sune suka ruɗani to komai yasa naji wannan yana yin da naji akan Busar ohow??
Wata ma a'ikaciyar gidan asibitin ce tace;"Sannu ya karfin jikin ki?"
A hankali na motsa baki nace;"da sauki"
Mikewa tayi ta fita, kallon jinin dake shiga jikina nike yau itace rana ta farko da aka sakaman jini to jinin wanene wannan ke gunada a jikina??.
Bude kofar aka yi na kai dubana ga kofar likita ne ya shigo cikin sauri ya iso inda nike ganin nasan likitan ya sani zaro ido tare da taɓa cikina koya zubar man da ciki ne??.
Shine likitan da Hajiya tace azubar man da ciki yace bai zudda ciki, to ko dubara yayi man?? Tunda wannan ba kalar waccen asibitin bace.
Ganin yadda nike kallon shi ga hannuna a bisa cikana ina shafawa yace;
"Cikin ki yana nan lafiya kalau kinji, daga yanzu anan zaki ringa zuwa awo kinjii?"
Na daga kai cikin jin kunya nace;"nagode sosai".
Hajiya ce ta bude kofar ta shigo tana rike da kuloli na abinci cikin wani kwando.
Sannu da zuwa yace tare da mikewa.
Tace;"yawwa likita bokan turai, sannu da kokari wajen ceto rayuwar ta".
Yace;"ai babu komai Hajiya ga magunguna nan asibitin kyauta take komai".
Tace; "Ah! Lalle mungode Allah yabar zumunci"
Yace;"Ameen"
Nan ya nuna ma Hajiya magungunanta ya juya yabar mu.
Hajiya tace;"Ya jikin naki".
Nace;"da sauki Hajiya sannu da kokari nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi"
Hajiya tace;"ai Yarima ne abin godiya shida ya ceto ranki, jininshi ne aka saka maki nayi mamaki daya bada jinin nan, saboda shi jinin mulki ne da sarauta lalle kina da sa'a a rayuwa ace jinin Yarima a jikin ki, ban taba tunanin haka zai yiyu ba gaskiya dan koshi ya bada iyayen shi zasu hana amman ke kinyi sa'a sosai"
Na kalli jinin da ke tafi jikina naga saura kaɗan ya ida shigewa jikina nayi murmushi nace;"lalle kam Hajiya Doctor Mubarak yayi kokari kuma kema saidai na biki da addu'ar Allah yayi maki sakayya ta Alkhairi".
Hajiya tace;"Umm"
Daga haka bata kara magana ba.
♦♦♦♦♦
Suna isa airport su Daddy har sun shiga ana shirin rufe jirgi kana Yarima ya iso.
Yana zuwa ya shiga kusa da kujerar Daddy ya zauna duk da cikin jirgin duk Family din sune Maza yan daurin aure.
Ganin audiga a hannunshi yasa Dad yace;"Subhanallah Anuu me ya sameka ne?"
Yayi saurin riko hannun ya cire addugar jini ya fito ya goge.
Baice ma Dad komai ba, hakan yasa Dad ya saki hannunshi.
Shiru a tsakanin su bamai magana sai yan uwa da keta fira suna janshi wai makararren Ango shidai yayi murmushi kawai.
Suna isa Katsina tun daga airport mutane ne har suka isa fada garin cike yake sosai.
Suna isa aka kaisu masabki Daddy ya kira daya daga cikin Security yana tambayar shi mike faruwa ne, nan take ya fadama Daddy.
Shiru Daddy yayi yana kallon Anuu, Abie sai sabgar gaban shi yake baki sun mashi yawa baida time din Anuwar din ma.
Daddy yaja hannun Anuwar wani daki suka shiga ya kulle dakin yace;"Anuwar ka faɗa man gaskiya Aljanar nan data aure ka ta kara biyo ka ko?? Itace kaje kaba jini ko saboda duk duniya ita kaɗai ke saka ƙin bin umarnin mu itace ke saka baka ganin kowa a yanzu sai ita, ka fada man itace ta biyo ka Bauchi ko?".
Yadda Daddy yayi maganar kasan yana cikin damuwa sosai.
Anuwar ya dukar da kai yace;"Nidai Dad jiya da muka fito zagayen fada naji kalar kararta ina nufin kalar kukan ta, kuma ita wadda naba jini 'yar uwar Sani ce tana da mijinta hadda ciki gareta na twins sannan jininta O ne, kasan dagani sai MANAL ke da shi duk nan kusa shine nagani da ayi asarar rai gwara na taimaka mata nima sai Allah ya taimaka man wata rana".
Shiru Daddy yayi yana nazarin magan ganunshi.
Anuwar yace;"wallahi Dad tun jiya nake cikin kunci, amman tunda na bata jinin nan na jini cikin farin ciki zuciyata tayi sanyi sosai kaga ikon Allah ko, wallahi daban bata jinin nan ba da yanzu ina cikin kunci".
Kama hannayen Dad yayi yace;"kamar ta manzon Allah yace "ku gusar da bakin ciki da damuwa dayin Sadaka, kaga jinin nan ba kudi na amsa ba sadaka ce nayi dan Allah Please Dad Understand me"
Murmushi Dad yayi yace;"naji dadin kalaman ka na baya lalle Allah yana tare da kai kana da zuciya mai kyau, yanzu muje time din zaman ka ango yazo muje a daura"
Murmushi Anuwar yayi suka fito tare da Daddy banda bushe-bushe da kide-kide Babu abinda ke tashi a gidan sai kirari da akema Ango.
A fadar Katsina aka daura auren Anuwar AbdulAziz Imam da Kulsoom Muhammad Imran, jama'an da suka hallacci daurin auren ba'a magana na birni dana kauye.
Ana gama daurin aure su Dad da Anuwar suka juyo zuwa Bauchi.
Koda suka iso kai tsaye Anuwar ya wuce part dinshi saboda ya gaji sosai.
Ya kasa gane tunda ya bada jininnan yake cikin farin cikin da ya da ɗe baiyi shiba lalle ceton rai na daban ne, Babu abinda yakai aikin Alkhairi dadi.
A haka ya yini har dare shi kaɗai sai lokacin yaga message din Momy Amarya tana part din Ammie ya bude nashi.
Sani ya kira ya hada mashi ruwa yayi wanka kana ya kalli Sani daya aje mashi abinci yace;"ka rufe wayar ka kabar gidan nan sannan ka rufeman part dina, dan ma kada a ganka ace ka bude bana bukatar kowa a yanzu ina bukatar kadaici".
Cikin grimama Sani ya amsa da to yayi yadda yace.
Abincin da aka zuba mashi ya faraci yana fara'a ya dade baici abinci kamar Yau ba.
Momy sai kiran shi take yaki dagawa.
Zai kashe wayar kiran Dad ya shigo
Cikin sauri ya dauka;"ka bude part dinka a shigo da amarya"
Yace;"Dad kafa san ina cikin farin ciki, shine hadda kai za'a saka baki dan a takura ni a kai ta wani part din kona kusa dani a ajeta".
Dad yace cikin bacin rai;"tunda kaba Aljanar ka jini ba, tun dazun na tambayi Sani yace shi taimako yayi bai san ta ba, ta riga data shiga jikin ka shiyasa ita ke saka ka wannan farin cikin to Allah ya fita, ka tashi ka bude tun kamin na iso, yanzu wajen Mai martaba nayi asan mafita tunda saboda ita ka kema Kulsoom wulakanci gwara adau mataki".
Daga haka ya kashe waya.
Tashi yayi yaje ya bude kofa ya dawo ya haye sama ya kulle ko ina tun daga palour har zuwa bedrooms din shi na sama".
Yauma kamar kullum zama yayi ya fara zana mai fura rike da sandarta a hannu tana tsalle, bai san kallar fuskar ta ba hakan yasa yayi mata kalar fuskar MANAL tunda kalar tafiyar su guda.
Yana jin motsi a kasa amman bai motsa ba ya cigaba da abinda yake.
♦♦♦♦♦
Bayan jinin ya kare aka sallame mu muka koma gida.
Yauma aka kawoman abinci kala-kala masu dadi.
Naci naje nayi wanka na fito na shirya.
Hajiya ta shigo taban magani na sha nayi sallolin da ake bina sai naji jikin yayi man dadi.
Haka na zauna har dare babu abinda ke damuna hankali na kwance tunda ciki na yana nan.
Nace a fili,Nagode maka Yarima insha Allah zan kai maka abinda na haifa nayi maka godiya nayi wannan alkawarin sannan zan maka kyauta indai zaka karɓa, zoben dake kusa dani cikin a kwatin shi na dauko ina kallo nace zan maka kyauta da wannan zoben insha Allah nasan mai daraje ne zoben zaiyi kyau dakai nayi murmushi na lumshe ido.
♦♦♦♦♦
Yana gamawa ya manna mata kiss Jin ana buga kofa da karfi yasa ya mike cikin zafin rai.
Yana budewa yaga Ammie da Momy ya dukar dakai ya basu hanya.
A mamakin shi hadda Kursim a bayan su tana lullube da fuska ba'a ganin fuskar ta amman ya gane ta.
A parloun suka zauna Ammie ta fara magana cikin ɓacin rai;"Wai kai Yarima meyasa komai naka sai ka nuna ma mutane basu isa da kai ba, kowa baya da kima a idonka babu mai saka sai Aljanar yarinyar nan ko?? yanzu muke jin labari ga Dad dinka Aljana ta aure ka to bari kaji idan kai tana yaudarar ka tomu munfi karfinta, ga Kulsoom nan bata zama a kasa idan ka isa ka yanka ta"
Momy tace;"Haba Anu kaga duk ka bata ma iyayen ka rai saboda yarinyar data mutu Maman ta da bakin ta ta fadi dan Allah kamanta da ita idan ma Aljana ce ke maka yawo da hankali insha Allah za'ayi maganin abin kaji?"
Daga kai yayi shima ranshi bace.
Har sun mike Ammie tace;"wallahi duk idan ka raba dakin kwana da Kulsoom ka nemi wata uwar bani ba".
Ware manyan idon shi yayi yana kallon Ammie cikin mamaki wai meyasa sun ƙi fahimta ta ne never shi babu aljanar data aure shi daga Allah ne.
Ta juya suka bar dakin, ya bisu da kallo.
Mikewa yayi yana kallon Kulsoom yayi daki tabiyo shi baya baice mata komai ba yana zuwa ya kwanta.
Yaja bargo ya rufe jikin shi, duk abinda yayi abaya akan MANAL Ammie bata taba bata Rai ba sai Yau.
Jin an hau gadon yasa yayi saurin juyowa!
Kulsoom ce ta cire lifayar dake jikin ta wadda ta shigo da ita, Night wear ne a jikin wata 'yar kamar riga mai kama da net komai ana gani na jikinta red color sai gashin ta mai santsi da tsawo tana gyara shi tana daure shi waje daya.
Kallon ta yake sosai tamkar ba hallitta ya gani ba yadda ya kura mata ido.
@Qurratou
*_JARABTAR MU*_
*_Written by- Maryam Qurrah✍🏼*_
*Page-53-54*
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Addu'ar Shiga Masallaci.*
أَعوذُ باللهِ العَظيـم وَبِوَجْهِـهِ الكَرِيـم وَسُلْطـانِه القَديـم مِنَ الشّيْـطانِ الرَّجـيم،[ بِسْـمِ الله، وَالصَّلاةُ] [وَالسَّلامُ عَلى رَسولِ الله]، اللّهُـمَّ افْتَـحْ لي أَبْوابَ رَحْمَتـِك .
A'uzu billahil-azeem wabiwajhihil-kareem wasultanihil-kadeem minash-shaytanir-rajeem,
[bismil-lah, wassalatu] [wassalamu AAala rasoolil-lah] , allahumma iftah lee abwaba rahmatik.
Ina neman tsarin Allah mai girma, da na fuskarsa mai alfarma, da na mulkinsa dadadde, daga shaidan tsinanne. Da sunan Allah, tisara da Aminci su tabbata ga Manzon Allah. Ya Allah! Ka bude mini kofofin rahamarKa.
DEDICATED TO.....MY SISTERS😘
Page-53-54
_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_
----------------Kallon mamaki yake mata ita wacece da har zata hau mashi bed waima su kwana a waje daya, tunanin abinda zaiyi yake dan bai taɓa kawo hakan a ranshi ba.
A tunanin Kulsoom kyawun tane da surar jikin ta suka dauki hankalin shi hakan yasa zuciyar ta fal take da farin ciki.
Ƙara gyara kwanciyar ta yi tare da kwantar da kai a jikin shi zata yi magana.
Cikin sauri ya miƙe tsaye cikin ɓacin rai, hakan yasa ta kasa magana tana nazarin yana yin shi.
Inda take ya nufo itama ta sabko daga bisa gadon tare da miƙewa tsaye.
Kallon juna suke shi da ita ganin yadda fuskar shi take yasa tasha jinin jikinta.
Hannu ya kai ya riko nata ya jata cikin sauri har kusan faduwa tayi ya bude dakin yana rike da hannunta yana ja.
Sabkowa suka yi da ita kasa wani korido sukabi ta gansu wani part komai nashi Pink and purple suka wuce parlon suka shiga wani daki nan ne taga katon bedroom da Baby bed guda biyu daya daga cikin gadajen ya jefa ta ta faɗa.
Shi kuma ya zauna bisa dayan gadon tare da dafe kai.
Kulsoom data bige ta tashi a hankali tana duba hannunta daya bige.
Tasowa tayi tace;"Prince me ya kawomu Baby room? Dan Allah ka fadaman meyasa baka sona? Menayi maka meyasa ban taɓa maka wani abu da zai burgeka ba, na aure kane dan ina son ka, koda ba zaka soni ba kaban dama a matsayina na matar ka, ka fada man abinda zan maka na burge ka??".
Kallon ta yayi yace;"Daki guda Ammie tace mu kwana daga yau nan zamu ringa kwana ga bed din nan, wannan kuma naki ban son kara jin komai daga bakin ki, ya isa zan maki duk abinda kike so a matsayin ki na matata saboda ban son shiga haƙƙin kowa saidai gado ne ba zamu haɗa ba".
Hawayen dake makale suka zubo mata, kowa ne Ango da Amarya a irin wannan suna farin ciki banda su.
Ganin baida lokacin ta yasa ta miƙewa taje ta kwanta bisa gadon ta.
Su duka bacci ya kasa daukar su ko wannne da abinda yake saƙawa a zuciyar shi har dare yayi nisa.
♦♦♦♦♦
Rungume zoben nayi har bacci ya dauke ni yana a kirjina, zuciya ta babu damuwa ko kaɗan sai farin ciki.
Ina tashi da safe nayi Sallah kamar kullun na mike na fito.
Yan aikin Hajiya maza suna ta aiki, ganin ɗakin ta a kulle yasa na juyo na koma daki.
Qur'ani nake bukatar karantawa haka nan na zauna ganin bani komai yasa na koma na kwanta.
Koda na bude ido na iske an ajeman kalaci kamar kullun yauma hadda soyayyar kaza.
A koda yaushe ina ma Hajiya addu'a akan na mijin kokarin da take yi a kaina, tunda nazo nake cin abu mai dadi ba tare da ta goran taman ba saima lallaɓani da takeyi.
Gashi jikina da abinda ke cikina komai lafiya kalau muna samun kulawa, lalle Hajiya ya dace ta zama Uwa ga gareni.
Ina cikin tunani naji karar takalmi na daga kai.
Wata 'yar siririya matashir budurwa na gani da jikkar kaya mai kafafu tana jaye da ita.
Kallona take nima kallon ta nike, na tashi zaune.
Ba laifi tana da kyau baƙa ce amman fuskarta tayi jawur ta fita daban da kafafunta da jikinta, tana da tsayi sosai gashi bata da jiki ko kaɗan dan na fita ƙiba.
Cingam ne a bakinta tana taunawa tace man;"Sannu baƙuwa kece Nana ko?".
Mamaki nake saboda yadda ta fadi sunana kai tsaye, kuma a tunani na ai itace baƙuwa tunda ni ta iske.
Nayi karfin hali nace;"Eh sannu da zuwa"
Murmushi tayi ta aje akwatin hannunta, tazo kusa dani bisa gado tace;"Wash, nagaji sosai yau banyi bacci ba".
Nace;"sannu"
Daga kai tayi tana cire wasu takalma masu tsini sosai.
Mamaki nike taya zaka iya tafiya da wannan takalmin, ganin ina kallon takalman yasa tayi murmushi tace;.
"Ko kina son sune? Naga kina kallon su kila sun burge ki ko?".
Nayi murmushi nace;"A'a mamaki nake yadda kike tafiya dasu".
Tayi murmushi tace;"ai bana saka takalmi sai irinsu saboda suna da tsada kuma Hajiya ke sai mani su, duk karshen wata tana mana siyayya".
Na jinjina kai cikin mamaki!
Saiga yaro ya shigo matashi zai girmeni cikin masuyi ma Hajiya aiki dauke da abinci.
Ta saki fuska tace;"Abu nawa na kaina kana nan dan gidan Hajiya"
Shima murmushi yayi yace;"gidan duk babu dadi Teema da baki nan amman nima nasan yanzu zan farajin yayyafi aljihu na zai cika".
Murmushi tayi tace;"kada kadamu mutumi na ga wannan kafin naje kwana yau zan bude maka bakin aljihu".
Ganin kudin da ta bashi yasa na zaro ido.
Ya amsa yana Mata kirari ya fita.
Tace;"yadai kinga na bashi kudi, yaron Hajiya ne akwai amana almajiri ne tun yana yaro yake wajen Hajiya har ya girma baida muna funci, idan kina son aike ba tare da da Hajiya ta sani ba to idan kika bashi baki da matsala dan zaiyi komai hankali kwance".
Girgiza nayi cikin raina nace kenan dai ba Amana
♦♦♦♦♦
Yana tashi yabar dakin lokacin Kursim na bacci.
Sama ya hau ya iske an masu komai hadda abinci an jera a dining table.
Wanka yaje yayi ya dawo ya shirya ya dauki waya yau itace rana ta farko daya kira Dr MUBARAK kuma tare suka yi primary da secondry.
Bugu daya na biyu ya dauka.
A dayan bangaren MUBARAK yayi sallama.
Anuwar ya amsa yace; "yarinyar da na ba jini Sani yace marainiyya ce kenan bata da kowa kuma ina uban yarinyar ? yace man kamar ya mutu".
Doctor Mubarak yace; "of course mijin ta ya mutu ya barta da ciki na duba naga twins ne, a lokacin wata matsala ta samu har jini ya fita kuma bata da wadataccen jini zata iya rasa ranta shiyasa muka ne meka gashi jinin ku kala guda ne".
Ajiyar zuciya yayi yace; "Zan ƙara ma account din Hospital din kudi da ita da sauran masu bukata a kula da duk wata mai ciki waɗanda basu da galihu idan ta haihu ka fadaman".
Dr yace;"kada ka damu insha Allah ranar da zata haihu zakaji".
Suka yi ban kwana ya aje wayar.
Lokaci guda tausayin yaran da za'a haifa ba uba ya shiga zuciyar shi.
Wace kalar rayuwa zasu yi kenan??.
Bude kofar room din shi a kayi ya dago a hankali Momy ce.
Murmushi yayi ta iso inda yake tace;"Annu dina ka tashi lafiya?? ina son yanzu ku fito kaida Kulsoom jama'a na jiran fitowar ku, nima satar kafa nayi nazo na fada maka, dan nasan halin ka ba zaka fito ba, kayi sauri ku fito tare kaga ran Ammien ka jiya ya baci".
Bata fuska yayi yace; "Momy tunanin wasu Baby's ne da za'a haifa nike ina tunanin me zan masu ne basu da gata inaso na zama gatan su domin na samu tasu ladar".
Momy tace;"to kada kadamu muyi maganar anjima".
Ya miƙe ya fito Momy na riƙe da hannun shi.
Kulsoom na kasa tasha ado da India gwon tayi kyau sosai.
Suna sabkowa Momy ta kama hannun Kulsoom ta saka cikin na Anuwar ta sakar masu murmushi.
Kulsoom tayi murmushi tace;"thank you so much Momy".
Murmushi Momy tayi tabar wajen.
Tsoki Anuwar yayi yana buƙatar abar shi yayi tunani mana.
Kulsoom ta kalli hannayen su tayi murmushi tace;"Ina kwana" Bai kalleta ba bare ya amsa.
Suka fito part din su tun daga nan keda jama'a ana guda ana saka kamshi ta ko ina tashi yake.
Part din Ammie suka nufa.
Suna zuwa aka fara kirari da kide-kide, gidan cike kamar yau ne ranar biki tsoki yake amman babu maiji Sai Kulsoom dake kusa dashi tana murmushi hannunsu haɗe dana shi.
Suna shiga suka iske Ammie da mutane.
Murmushi tayi suka isa inda take su duka suka duka.
Dagosu tayi tanuna masu waje.
Kai da kaga Ammie kasan taji daɗin yadda taga Anuwar da Kulsoom.
Anuwar na zama ya saki hannun Kulsoom.
Inda Ammie take yayi, yana zuwa ya dan duka wajen kunnen ta yayi mata rada yana murmushi.
Hakan yasa kowa dariya, Ammie ma murmushi tayi.
Juya yayi zai fita yana murmushi.
Rahama ce ta shigo kuyan gun bayan ta suna rike da Manal.
Bata fuska yayi tana gaida shi bai amsa ba ya wuce ya amshi Manal din yace mata;"idan baki iya renonta ba sai kin ba wasu ba kibar man ni nayi".
Murmushi Rahama tayi daman ta gane nufin shi.
Ya rungumi MANAL yabi ta baya yayi part din Mai martaba.
A zuciyar shi yana fatan samun tashi.
Yana zuwa ya iske Abie ya dawo daga yima baki ban kwana kai tsaye dinning table ya nufa.
Yana zuwa ya zauna yayi breakfast.
Daukar Manal yayi yana mata wasa.
Abie yace;"baka da lokaci na sai diyar ka ko?"
Murmushi yayi yace;"Abie naga kamar kana wani abu ne".
Yace;"ai na tsaida komai zanga magaji na"
Yana maganar yana murmushi.
Murmushi Anuwar yayi yace;"akawo man fura nasha"
Mai martaba yace;"yau kayi rashin sa'a hidimar biki tasa Sani bai kawo ba kila sai gobe"
Bata fuska yayi yace;"Abie ina son nashata zuwa anjima nima na saba fa ya za'ayi?"
Abie yace;"Bari na kira Sani ya kawo maka ai sana'ar ka kenan kullun tanayi"
Cikin sauri Anuwar yace;barshi Abie zan saka akaini yanzu daman ina son naje asibiti da lambu daman Dad yace naje naga yayi kuma kaga kusa da gidan tane".
Abie yace;"to shikenan, a dawo lafiya"
Ya mike da MANAL a hannu Abie yace ya bashi ita, ya mikama Abie ita, shi kuma ya fita.
0 comments:
Post a Comment