Muna zaune sai ga Hajiya ta shigo muka gaisa ta kalli Teema tace;"ki taso muje ayi maki allura ko a saka maki roba kada gobe kidawo kice man kina da ciki, ki dauko man wata wahalar kuma".
Teema tace;"muje kin sami number Dr Jamil ne?".
Hajiya tace;"ban samu ba sai munje wajen Dr Mubarak na amshi number, kiyi sauri dan sai munje gefen gari yana asibitin gidan Sarki kiyi sauri".
Tace;"Hajiya aini a shirye nake muje"
Ta miƙe ta saka ta kalman ta masu tsini ta saka wani dan karamin gyale iyakar shi wuya, har sun kai bakin kofa Hajiya ta waigo tace; "Muje Nana mana ko kema kinga garii, kinga gidan ba kowa zakiji ba dadi".
Nace;"to Hajiya"
Na dauki Hijab ɗin da nike Sallah har kasa na saka.
Da silifas nazo gidan, tuni Hajiya taba almajirai su, taban wasu takalma masu tudu kaɗan marassa nauyi.
Suna saka ban tsaya shafa komai ba na bisu.
A motar Hajiya muka shiga, muka nufa asibitin.
♦♦♦♦♦
Da mota guda ya fita daga shi sai driver.
Har suka isa hankalin shi yana a waya yana kallon videos din da Kulsoom tayi mashi a Spain.
Saida suka daɗe kana ya ganshi a kauyen.
Gidan su Sani a gefen gari yake shi kaɗai kusan ma duk haka gidajen garin su Sani suke, garin akwai sha'awa kauye ne amman yayi kyau saboda ko ina noman rani ake garin yayi tsanwa gaskiya garin ya burgeshi.
Murmushi yayi ya motsa cikin sauri driver yazo ya bude mashi ya fito yana kara kallon yadda garin ya burgeshi daga gidan su Sani kana kallon Lambun shi.
Turawa yayi akayi mashi Sallah akace ya shigo.
Gidan ƙasa ne amman ko ina a tsabtace yake ga kamshi da gidan keyi ita kanta matar tsohuwa ce amman jikinta a tsabtace sai kamshi take na kalar turaren su.
Zama yayi bisa abinda akayi mashi shimfida.
Suka gaisa cikin girmamawa yace;"Inna fura nazo samu".
Tayi murmushi tace;"aida ka fada ma Sani da tuni an kawo maka basai kazo ba, shi yace kada nayi akwai ragowar ta gidan ku saboda haka ni nabari sai gobe sai nayi domin kuna cikin hidima, amman bari yanzu na kawo maka konawa kake so yanzu na gamata".
Yayi murmushi sai gata da Fura cikin kwarya.
Ta aje a gaban shi tace;"Allah yasa ta isa"
Yayi murmushi yace;"ta isa haka ba ni kaɗai ba har ma Mai martaba zai samu, ina yaran Sani ne?"
Tace;"Aiko sun bar nan matar ta matsa tafi son cikin gari sosai da yaƙi ni nace nidai su tashi ai duk ɗaya ne tunda ba nisa yanzu ni kaɗai ce, sai idan jikoki na sun zo".
Ya jinjina kai ya fiddo kudi masu yawa ya aje mata a gaban ta.
Tace;"Dan Allah kabar su ina ganin Alheri da yawa daga Mai martaba Ina godiya sosai hakan ma nagode kabar shi Allah dai ya baka abinda kake so ya kuma kare ku kaida zuri'ar ku"
Yayi murmushi yace;"Ameen amman bana maida abinda na fitar daga aljihuna naji Dadi nima da karramawa".
Nan ta dauka tana godiya wani Yaro ne ya shigo yace;"Inna mai fura kinyi bako wai Liman daga Katsina"
Cikin sauri Yarima yakai duba ga yaron dake magana.
Ya maimaita;"Liman daga Katsina.....?"
*Qurratou*
*JARABTAR MU*
*Written by-Qurrah✍🏻*
*Page-57-58*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Addu'ar Sujadar Tilawar Alƙur'ani.*
سَجَدَ وَجْهِي ِللَّذِي خَلَقَهُ وَصَوَّرَهُ وَشَقَّ سَمْعَهُ وَبَصَـَهُ بِحَوْلِهِ وَقُوَّتِهِ تَبـارَكَ اللهُ أَحْسَـنُ الخـالِقيـن.
Sajada wajhee lillathee khalaqahu washakka sam’ahu wabasarahu bihawlihi waquwwatih {tabaraka Allahu ahsanu alkhaliqeen}.
Fuskata ta yi sujada ga wanda ya halicce ta, kuma ya tsaga ji da gani a gare ta, da iyawarsa da kuma karfinsa, Allah mafi gwanintar masu halitta, Ya girma, kuma alherinsa ya yawaita.
اَللّهُمَّ اكْتُبْ لِي بِهَا عِنْدَكَ أَجْراً، وَضَعْ عَنِّي بِهَا وِزْراً، وَاجْعَلَهَا لِي عِنْدَكَ ذُخْراً، وَتَقَبَّلَهَا مِنِّي كَمَا تَقَبَّلْتَهَا مِنْ عَبْدِكَ دَاوُدَ.
Allahummak-tub lee biha AAindaka ajra, wada 'annee biha wizra, waj'alha lee 'indaka zukhra, watakabbalha minnee kama takabbaltaha min 'abdika Dawood.
Ya Allah! Ka rubuta mini lada saboda ita (sujadar), ka kankare mini zunubi saboda ita, ka sanya ta ta zamo taskar arziki gare ni a wajen ka, kuma ka karbe ta daga gare ni kamar yadda ka karbe ta daga bawanka Dawuda.
DEDICATED TO.....MY SISTERS😘
Bissimillah Rahmanir Rahim
Page-57-58
--------------Ihun da nayi ne ya jawo hankalin mutanen wajen.
A guje Hajiya da mutane suka shigo man daki, dan a tunanin Hajiya haihuwa ce tazo.
Tana shigowa ta ganni zaune ina hawaye idona a runtse.
Su duka suka yi tsaye suna kallo na, Hajiya ta nuna masu da hannu dasu fita, suka juya su duka suka barni daga ni sai Hajiya.
Ta iso inda nake zaune ta zauna tace; "Haba Nana me kike ma kuka ne? Ko mun maki wani abu ne?".
Na girgiza kai ina goge hawayen dakebin fuskata, amman na kasa tsaida su saboda yadda rayuwa ke tafiyar man daga wannan sai wannan.
Hajiya ta goge man hawayen, sannan ta kama hannu na tace; "kiyi hakuri nasan kina jin ciwon abun da ya faru a zuciyar ki, nasan ba halin ki bane fyaɗe ne wani yayi maki, amman kiyi hakuri komai zai wuce".
Na ɗaga kai nayi ina kara goge hawaye na.
Ta kara damkar hannuna tace cikin nuna jimami da damuwa a tare da ita tace;
"Wannan ba komai bane ba, zaki iya komawa budurwar ki koda kin haihu".
Na kalle ta cikin mamaki!
Ta ɗaga kai alamar tabbatarwa tace; "yaran da kika haifa su zasu tona maki asiri, amman ina da shawara me zai hana muje mu yadda su kafin asuba a kofar gidan marayu, ko kofar gidan Sarki".
Cikin mamaki da razana na kalleta tare da mikewa tsaye jikina har kyarma yake saboda jin magan ganunta.
Kamani tayi tace;"zauna naga hankalin ki ya tashi wallahi banyi tunanin maganar zata yi maki muni har haka ba kawai shawara ce na kawo, naga haka yanzu ake".
Cikin dasashiyar murya nace;"Bani ɗaya daga cikin azzaluman uwaye masu daukar alhaki, taya zan raini ciki wata tara sannan na yada abinda na haifa nasan tun a duniya Allah bazai barni ba, nayi laifi kuma na ƙara wani laifin, ina son abun koda kowa zai gujeni zan zauna da yarana ina son su a haka".
Hajiya ta riƙe ni tace;"Babu komai na fahimta Nana kada kidamu, yanzu kwanta dare yayi nisa".
Daga kai nayi na zame na kwanta tare da ajiyar zuciya.
Hajiya ta mike ta kashe man wutar ɗakin sannan ta fita.
Na zame na kwanta tare da ƙara goge hawaye na, daga haka bacci ya daukeni.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Kulsoom dake tsaye tana hawaye abin duniya ya isheta ashe kallon juya ake mata gashi har an fara naima ma Anuwar aure tamayi kishi da mai fura ina ga ƴan matan zamani kalar ta.
Juyawa yayi a fusace ya hau sama.
Bin shi tayi cikin sauri koda ta isa har ya rufe kofar dakin.
Buga kofar take amman shiru ta gaji ta juya daki.
Jikin ta har kyarma yake ta dauki wayar ta ta kira Hanan.
Nan ta bata duk labarin abinda ke faruwa.
Su duka hankalin su a tashe yake nan Hanan ta bata shawarwari sun dade suna waya kana Kulsoom ta kashe tayi toilet ta dade tana wanka cikin ruwan kamshi, sannan ta fito ta zauna a gaban mirror.
Kusan duk wani turare dake a gaban mirrorn dakin ta saida tasaka shi, kana ta dawo a gaban wadirof tana duba rigar da zata saka, duk yawan night wears din da ke a akwai a ciki, amman ta rasa wacce zata sa sai chan taga wata ta dauka pink color ce wani tunani tayi sai tayi murmushi a hankali ta furta;
"MANAL best color"
Mikewa tayi ta sakata taje bakin mirror ta kalli rigar ita kanta tasan tayi mata kyau gyara gashin tayi ta tubke shi waje daya.
A hankali take takawa kamar mai jin tsoro har ta isa kofar dakin shi.
Turawa tayi a hankali ga mamakin ta saita jishi a bude shiga tayi.
Tana shiga suka hada ido yana bisa gado yana kallon wayar shi tasan abinda yake kallo, da alama kwanta zaiyi dan sleeping dress ne a jikin shi.
Tunda suka hada ido bai kara kallon taba sai aje wayar da yayi ya zame ya kwanta tare da jan blanket dinshi.
Ta iso cikin fargaba da faduwar gaba ta hau gadon jin baiyi ko motsi ba yasa ta zame ta kwanta a bayan shi.
Blanket ɗin daya lullube itama shita ja ta lullube jikin ta dashi.
Nan ma taji baiyi magana ba, ganin ta samu dama yasa ta matsa kusa dashi tare da rungume bayan shi tsam.
Yana jin duk abinda take amman bai hanata ba saboda zuciyar shi a gajiye take dole ne yayi ma iyayen shi biyayya, runtse ido yayi jin kamshin jikin ta mai daɗi ya bugi hancin shi yasa ya bude ido a hankali.
A lokacin Kulsoom ta shagaltu da yimasa wasa shafa shi take tana kara manne mashi amman shi kamshin turaren jikin ta yakeson shaka.
Ganin bai tsaidata ba yasa ta cigaba da abinda take.
Juyowa yayi ya dagota ta dawo a gaban shi.
Wani farin ciki ne ya ziyarci zuciya ta lalle yau zata yi nasara lalle akwai kyauta mai tsoka ga Hanan.
Tafara tura mashi sakon ni tun yana turewa har ya dena, ta shagaltar dashi, da kalar salonta.
Hankalin Kulsoom bai kwanta ba a daren har saida Anuwar ya kusan ceta.
Duk data wahala amman zuciyar ta dauke take da farin ciki jinta tayi wata ta daban.
Anuwar maida numfashi yake tare da runtse ido yana tuna Jummu'ar shi ta karshe a Katsina.
Mikewa yayi yaje ya gyara jikin shi ya dawo ya fara sallah, koda ya kalli bed dinsu Kulsoom tayi bacci, bai koma ba har saida akayi asuba ya fita masallaci, koda ya dawo babu Kulsoom Kuma a chanza bedsheet din an saka turare a dakin.
Bisa gado ya koma ya kwanta tare da mafalkai iri-iri sai wajen ten ya farka.
Yana tashi toilet ya nufa ya iske an hada mashi ruwan wanka.
Yana fitowa ya iske Kulsoom zaune bisa gado ga kayanan ta aje kallo guda yayi mata ya dauke kai daga kallon ta.
A gaban mirror ya tsaya yana goge jikin shi da towul din hannun shi.
Tasowa tayi ta iskeshi hannu ta mika mashi ya bata towul din.
A hankali yace;"No need"
Bata fuska tayi tare da langwabe kai kamar zatayi kuka ta kara mika hannu tare da shafa shi cikin salo.
Bata yayi tare da tsoki, maimakon taji haushi sai tayi murmushi.
Ta amsa ta goge mashi sumar shi ta gyara mashi gashin.
Nuna mashi kayan dake saman gado tayi ta juya.
Shiru yayi yana kallon kayan tashi yayi yaje ya dauka ya saka.
Ya fito daga dakin yayo kasa yau yarasa wane kalar yanayi yake ciki.
Farin ciki ko akasin haka, yana fitowa babu motsin kowa a cikin dakunan.
Haka ya sabko ya iske Kulsoom.
Tana ganinshi ta mike taje inda yake ta kama hannun shi tana murmushi kai tsaye bisa dining table ta nufa.
Taja mashi kujera ya zauna, duk abinda tasan yana so ta zuba mashi ta tura a gaban shi.
Ya dago suka hada ido ta sakar mashi murmushi ya juyar da kanshi yace;"thank you"
Murmushi tayi suka faraci suna gamawa ya mike tabi bayan shi dan tasan inda yayi.
Kai tsaye part din Ammie ya nufa.
Yana zuwa bata parlo ya wuce bedroom dinta tana bisa bed dinta, ɗaya daga cikin masu aiki tana shirya mata wadirof dinta.
Yana shigowa matar dake tsaye ta sunkuya ta gaida shi cikin sauri tayi hanyar fita.
Ammie tace;"Lantana ina zaki? Nina baki umarnin fita dawo ki ida aikin ki".
Cikin girmama ta dawo kai a kasa ta fara maida kayan.
Karasowa yayi inda Ammie take zaune ya zauna har ya zauna bata kalle shi ba.
Kulsoom ce ta shigo Ammie tayi murmushi tace;"Lantana bamu wuri".
Ran Anuwar yayi matukar baci shi ya shigo an hana wata kuyanga fita amman Kulsoom tana shigo ance ta fita me Ammie ke nufi??
Lantana na fita ta kalle shi tace; " tashi kabar man daki tun kafin nayi maka wulakanci".
Sun kuyar da kai yayi lokaci guda fuskar shi ta chanza ranshi ya baci sosai.
Ammie bataji dadin haka ba amman tana ganin hakane daidai da Anuwar wannan shine sabani na farko da suka fara fuskan ta.
Ya mike yabar masu dakin kai tsaye hanyar fita yayi.
Sani ya kira yace yazo ya fidda shi.
A gefen gari yaje ya zauna cikin Lambun da Dad yayi mashi.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Yauma kamar kullun zaune nake abin duniya yayiman yawa narasa mafita saina maida lamari na ga Allah dayaya yeman abinda ke damuna.
Hajiya tana iyakar kokarin ta akaina da cikina.
Ina zaune naji muryar namiji na sallama.
Na daga kai nace;" shigo"Dr Mubarak ne da Hajiya suka shigo, cikin mamaki nake kallon shi.
Murmushi ya sakar mani na dukar da kaina a kasa nace;"sannu da zuwa"
Yace;"yakike jin jikin? Babu matsala?"
Na daga kai, Hajiya tace;"Bari na barku ku gana ko"
Murmushi Dr Mubarak yayi ni kuma kaina yana a kasa.
Tana fita ya matso kusa dani ledar daya shigo da ita ya bude ya fiddo wani abu cikin wata roba babba mai Fadi ya bude ya miko man.
Naki amsa yace;"to bari na baki a baki konayi maki dore idan kikaki karba"
Na zaro ido cikin mamaki
Ya daga kai ya matso dab dani nan naji gabana yana faduwa lokaci guda na fara zufa.
Ganin zai tabani da gaske rikeni zaiyi ya sakaman a baki yasa nayi saurin amsa.
Nasaka a baki na ina tamna dadin abin yasa har lumshe ido nake.
Abin kamar biskit amman ba kalar na kauyen muba wannan daban yake tunda shi a cikin robama aka sakashi namu kuma a leda.
Saida nakusan cin rabi kana nace na koshi.
Murmushi yayi ya fiddo man wasu daga leda su kuma a cikin gwangwani suke yace na ringaci.
Na daga kai nace nagode ya mike tsaye yana kallona, kallon da yakeman bansaba da irin shiba hakan yasa na dukar dakai gabana yana kara faduwa.
Yace;"Nana nizan tafi bazaki man rakiya ba?"
Nace;"a'a sai anjima nagode"
Murmushi yayi ya duko dai-dai fuskata munajin hucin juna yayi murmushi ya shafa gefen fuskata da gashi ya kwanta yace;"ki kula da kanki"
Kasa motsi nayi saboda jin hannun shi nayi tamkar garwashin wuta aka azama, sai zufa nake gabana yana kara faduwa.
Ya juya yana murmushi yabar dakin.
Hajiya tana bakin kofa ta labe tana kallon mu tana ganin yayo hanyar fita tayi saurin fadawa dakin ta.
Yana fitowa ya kira Hajiya ta fito tana washe hakora tace;"har kungama gaisawa"
Yace;"kinsan Nana batada sakin jiki shiyasa nabarta zan kawo mata kayan da zata dunga ci saboda ta samu kuzari da wadataccen jini a jikinta kinga jininta wahalar samu yake"
Tace;"to mungode Dr Allah ya saka da Alkhairi"
Yayi hanyar fita Hajiya tayi tsoki ta bata fuska dai-dai zai fita lokacin teema ta shigo tabishi da kallo.
Tana shigowa tace;"Hajiya miyakawo Dr Mubarak a gidan ki?"
Tsoki tayi tace;"zai bataman plan wallahi Raina duk a bace inagafa Nana yakeso idan ko hakane zan dauki mataki dan bazan bari ya bataman shiri ba nayi wahalar banza kenan"
Teema tace;"to mizakiyi kinsan fa yanada power kinsan dan waye?? Iyayen shi a Abuja suke ba dan Bauchi bane zai iya kai masu Nana basusan komi a kanta ba"
Murmushi Hajiya tayi tace;"Nasan komi akan shi Baban shi ba boyayyen mutum bane, lalle idan sainayi wani abu a kai sai Mubarak yabar Bauchi kana aikina zai tafi dai-dai"
Tayi murmushi tace;"nasan abinda zanyi"
Ina daki banda faduwar gaba ba abinda nake miyasa naji haka game da Mubarak, amman miyasa shi wanchan daya tabani banji zafi irin wannan ba??
Haka nayita tunani har dare yau abincin gwangwani na yini chi.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Furar gidansu Sani ya yini sha sai dare ya koma gida.
Yana isa ya wuce a part dinshi.
Bedroom dinshi ya nufa ya yana zuwa yayi wanka ya fito ya saka kayan bacci ya hau ya kwanta.
Yanajin motsin shigowar Kulsoom har ta hau gadon.
A jikin shi ta kwanta baice mata komi ba a haka sukayi bacci.
A haka rayuwa ta cigaba tsakanin shi da Kulsoom a bangaren Ammie ko gaisuwar bata amsa sai wani bi shima ciki-ciki shi kuma Abie baisan abinda ke faruwa shiyasa babu abinda ya shiga a tsakanin su.
Suna zaune shida Kulsoom a parlo yana waya da Dad.
Ya kalleta yaga tana ta chanza fuska sai ya mutsa fuska take.
Mikewa tayi tsaye yaga ta rike kanta.
Cikin daga murya tace;"Anuwar kamani zan fadi juwwa nake gani"
Cikin sauri yayo kanta ta zame a jikin shi.
Wayar hannun shi yayi saurin kiran Doctor ya kamata ya maidata bisa kujera.
Cikin lokaci kadan saiga Doctor Mubarak ya shigo cikin sauri.
Yana zuwa yafara duba Kulsoom.
Saiga Walida tashigo taga Doctor Mubarak juyawa tayi cikin sauri saigata sun dawo itada Ammie.
Sun isowa Doctor Mubarak ya gama yimata tambayoyi yayi mata gwajin abinda yake zargi dagowa yayi yana murmushi yace;"My Friend congratulation"
Ammie tace;"Mubarak ciki gareta?"
Ya daga kai yana murmushi.
Walida tayi ihu ta fita a guje tana cewa wallahi nizan ma Abie na Albishir.
Anuwar ma murmushi yake yana kallon Ammie, cikin sauri Ammie ta rungume shi.
Nan fa wayar shi ta fara kara Dad ne ta Ammie ma Mom ce.
Kulsoom ta manta da wata kunya lokacin guda ta fara murmushi tanajin ta wata sabuwar duniya yau itace dauke da cikin Anuwar.
Lokaci guda farin ciki ya mamayeta tana murmushi tana shafa cikin.
Ammie ta kamata sukayi daki Anuwar da Mubarak suka fita.
Yanadawo daga raka Mubarak dakin shi ya wuce.
Zaunawa yayi yana wani tunani a hankali yace;"kenan idan yarinyar nan bata mutu ba itama zata iya haifaman Baby?? So guda na kusanci Kulsoom haka itama nakasa yadda da gaskiyar su zan nemota dakaina inde tana raye"
Mikewa yayi yana tunanin taya zaifara.
Sani zai kira shizai shirya mashi komi shizai koya mashi kalar rayuwar kauye shizai kawo mashi kayan da zaiyi ammfani yadda zaiyi mu'amallah da yan kauye batare dasunji tsoron shiba
Wata zuciyar tace;"miyasa bazaka yadda da kaddara ba yarinyar data mutu miyasa kake wasi-wasi"
Shawarar kiran Sani ita ya yanke, idan yaje da kanshi hakan zaisa ya samu natsuwa.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Yanzu Doctor Mubarak shine ya zama abokin firata kusan kullun da yamma yana wajena.
Hajiya bata taba nuna bacin rai kota gajiba kila dan yana bata kudi.
Tunda ya tabani naji zafi bankara bari ya tabani ba.
Yau hakanan na tashi banjin dadin jikina daman na shiga watan haihuwa na inji Mubarak.
Jin cikina ya motsa yasa na cije lebe.
Haka nayini inajiran shigowar Doctor Amman shiru.
Na mike ina tafiya da kyat saboda nauyin cikin falon Hajiya nayi sallama na shiga.
Tana zaune tana kallo tayi murmushi tace;"uwar biyu lafiya ko muje asibiti?"
Nace;"Hajiya daman likita ne bai zoba lafiya de?"
Teema dake shigowa tace;"yabar Bauchi kuma bazai kara dawowa ba"
Murmushi nayi nace;"banson wannan wasan aida nabishi"
Hajiya tace;"Jiya bayan yabar gidan nan Mahaifiyar shi taje asibiti da kanta ta tafi dashi wai karatu zai karo a waje sainan da shekara ukku zai dawo"
Innalillahi! Shine abinda na ambata tareda da aza hannu akai lokaci guda hankali na ya tashi.
Jinayi duniyar taman duhu saboda koba komai mun sava zaman shi dani yana rageman kewa.
Daki na koma cikin sauri na fada bisa gado.
Ban fada dai-dai hakan yasa cikina juyawa.
Wani irin azababben zafi naji nayi wata irin kara ganin jini na zuba.
Nace;"innalillahi jini!! Yanzu idan ya zube wazaiman hanyar samun jinin wanchan?"
Ganin yana fita yasa nayi wata irin kara!!
MARYAM ANKUDII (QURRAH)
*JARABTAR MU*
*Written by-Qurrah✍🏻*
*Page-59-60*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Addu'ar Sujadar Tilawar Alƙur'ani.*
سَجَدَ وَجْهِي ِللَّذِي خَلَقَهُ وَصَوَّرَهُ وَشَقَّ سَمْعَهُ وَبَصَـَهُ بِحَوْلِهِ وَقُوَّتِهِ تَبـارَكَ اللهُ أَحْسَـنُ الخـالِقيـن.
Sajada wajhee lillathee khalaqahu washakka sam’ahu wabasarahu bihawlihi waquwwatih {tabaraka Allahu ahsanu alkhaliqeen}.
Fuskata ta yi sujada ga wanda ya halicce ta, kuma ya tsaga ji da gani a gare ta, da iyawarsa da kuma karfinsa, Allah mafi gwanintar masu halitta, Ya girma, kuma alherinsa ya yawaita.
اَللّهُمَّ اكْتُبْ لِي بِهَا عِنْدَكَ أَجْراً، وَضَعْ عَنِّي بِهَا وِزْراً، وَاجْعَلَهَا لِي عِنْدَكَ ذُخْراً، وَتَقَبَّلَهَا مِنِّي كَمَا تَقَبَّلْتَهَا مِنْ عَبْدِكَ دَاوُدَ.
Allahummak-tub lee biha AAindaka ajra, wada 'annee biha wizra, waj'alha lee 'indaka zukhra, watakabbalha minnee kama takabbaltaha min 'abdika Dawood.
Ya Allah! Ka rubuta mini lada saboda ita (sujadar), ka kankare mini zunubi saboda ita, ka sanya ta ta zamo taskar arziki gare ni a wajen ka, kuma ka karbe ta daga gare ni kamar yadda ka karbe ta daga bawanka Dawuda.
DEDICATED TO.....MY SISTERS😘
Bissimillah Rahmanir Rahim
Page-59-60
------------A bayan Part ɗin shi yace ma Sani su hadu wani dan wajen hutawa da akayi.
Yana sabkowa bakowa har Kulsoom ɗakin ta a kulle yake ya fita.
Yana zuwa ya iske Sani a wajen zaune yana jiran shi.
Zama yayi suka gaisa kallon Sani yayi yace; "ina son ka fadaman taya zanyi mu'amallah da mutanen kauye ba tare dasun gane daga inda na fito ba, ina son na chanza kamanni na nakoma kalar su"
Cikin mamaki yake kallon Anuwar kuma da alamar fuskar shi babu wasa a tare da ita.
Cikin girmamawa Sani yace;"Duk abinda Yarima Anuwar yake so shi za'ayi yanzu"
Murmushi Anuwar yayi yasa hannu aljihu ya fiddo kudi masu yawa shima debosu yayi bai san konawa bane ya mikama Sani.
Sani ya zaro ido yace;"Allah ya taimaki Yarima Anuwar ai kudin sunyi yawa, ko kwata ba za'a kashe ba a cikin su".
Kallon Sani yayi yace;"Na kira wayar Mubarak bata shiga kila yaje wani waje ne, ina son yarinyar nan da yace yar uwar shi ce aje ayi mata sayayya dasu saboda ya fadaman wannan watan zata haihu kuma tunda yabar gidan nan nake kiran wayar shi bata shiga zuwa anjima zan kira Mom din shi koyaje Abuja dan haka kaje kayi mata komai".
Sani yace;"Yallabai ai ban san taba, Doctor Mubarak yasan ta kuma yau da safe da naje asibiti ance yabar asibitin su tin jiyama suka ce yabar asibitin".
Mikewa yayi tsaye yace;" ina son mu fita a tare, saboda ko yau saida Doctor Mubarak yazo amman taya za'ayi ace yabar hospital ba tare da Dad ya sani ba, kuma yau da yazo gidan baiman maganar ba, akwai wani abu kenan".
Koda suka fito, hospital din suka nufa dan Jin minene dalilin barin Doctor Mubarak asibiti.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Su Hajiya suna shigowa suka ga abinda ke faruwa tace; "Teema kamata na fidda mota haihuwa ce tazo haka jininta na fita akwai matsala".
Hajiya ta fita cikin sauri Teema ta kamani muka fito ina hawaye jini na kara zubowa, ga radadi inaji saboda yadda naji ana motsi a cikin nawa.
Koda muka shiga motar Hajiya ban kara sanin inda kaina yake ba.
Teema tace;"Hajiya ya naga kinyi asibitin gidan Sarki bayan Doctor Mubarak bainan sauran Doctors din wasu mafa turawa ne basu jin Hausa".
Hajiya ta kalli Teema tace;"ke zaki biya mata kudin gado da abubuwan da za'a bukata dole ne mukaita chan su san yadda zasu yi da ita dan nikam wallahi nagaji, ta miƙe ta biyaman kudina duk jarina ya kare a kanta, banda kajin da taci kuma dan iskanci abincin gwangwani takeci koni bancin shi, to bare ita tashin kauye".
Shiru Teema tayi har suka isa suna zuwa aka amsheta aka shiga da ita dakin haihuwa.
Suna zaune a bakin dakin Nursing ta fito a uzurce dai-dai lokacin da su Anuwar suka shigo.
Tace;"Alhamdulillah ta haihu yaran ta suna lafiya Baby girl and Baby boy saidai ita rayuwar ta akwai matsala dan babu jini a tare da ita kuma bamu san inda zamu samu kalar jinin ta ba, saboda yanada wahalar samu wanchan karan daman Doctor Mubarak ya samo shi wajen Prince".
Nurse din na juyawa taga Anuwar a bayan ta yana kallon ta su duka hadda su Hajiya aka kai kasa.
Sister Fatima ita kaɗai ce ba hausa a cikin Nursing din, anan take aiki tun farkon budewa Mubarak ya kawota.
Anuwar yayi gaba cikin sauri ta mike tabi bayan shi.
A office din Doctor Mubarak ya zauna ta shigo ta duka ta gaida shi ya amsa yace;
"Wacece ta haifi yara har biyu batare da anma Dad magana ba? Kuma wane kalar jini ne da ita"
Cikin sauri tace; "O negative (O-)"
Kallon ta yayi cikin sauri yace;"Ba sister din Mubarak bace".
Dukar dakai tayi tace;"Eh haka yace, kuma yanzu yabar garin tun jiya Mom din shi take nan tazo tafiya dashi yaƙi yarda amman yanzu ya bita yace two days zaiyi yadawo".
Ajiyar zuciya yayi ya mike tana biye dashi Lab ya shiga Sani na bayan shi da ido yayima Sani nuni, Sani shiya ce a debi jinin Anuwar dan yasan abinda yake nufi.
Cikin mintuna kaɗan aka debi jinin Anuwar cikin sauri Sister Fatima tayi waje a guje.
Sani na biye dashi a tunanin shi gida zasu sai yaga ya koma office din Doctor Mubarak.
Zama yayi saiga Sister Fatima ta dawo, yace; "ina son ganin yaran sannan ya kamata a fadama Dad".
Tace;"ai Doctor Mubarak ke magana da Dad kuma yanzu bainan".
Yace;"zan mashi magana ku dauki address din inda yarinyar take zaune".
Cikin sauri ta fita lokaci kaɗan sai gata da yara an saka masu kaya masu kyau daya a hannunta daya a hannun Hajiya.
Suna shigowa tun kafin su iso inda yake yayi saurin mikewa, saboda yadda yaji zuciyar shi ta buga, ya lumshe ido yasan yana kaunar yara da yawa, shiyasa zai kula da Kulsoom kodan ajiyar su kuma zaije garin su yarinyar nan, a dai-dai lokacin ne suka ji karar jiniya.
Bude ido Anuwar yayi yace;"Dad?"
Cikin mamaki! Dai-dai lokacin da sister Fatima ke mika mashi Baby boy din hannunta.
MARYAM ANKUDII {QURRAH}
*JARABTAR MU*
*Written by-Qurrah✍🏻*
*Page-6162*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Karatun Tahiyya.*
اَلتَّحِيَّاتُ ِللهِ وَالصَّلَوَاتُ والطَّيِّبَاتُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ أَيُّهَا النَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِكَ الصَّالِحِينَ. أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَرَسُولُه .
Attahiyyatu lillahi wassalawatu wattayyibat, assalamu AAalayka ayyuhan-nabiyyu warahmatul-lahi wabarakatuh, assalamu 'alayna wa'ala ibadil-lahis-saliheen. Ash-hadu an la ilaha illal-lah, wa-ashhadu anna Muhammadan 'abduhu warasooluh.
Dukkan nau'in ban girma ya tabbata ga Allah, da kuma salloli da kyawawan kalmomi. Aminci ya tabbata gare ka ya Annabi, da rahamar Allah da albarkatunsa. Aminci ya tabbata gare mu, da kuma ga bayin Allah salihai ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne.
DEDICATED TO.....MY SISTERS😘
Bissimillah Rahmanir Rahim
Page-6162
----------------Ya maida hankalin shi ga abinda Sister Fatima ke mika mashi.
Lokaci guda zuciyar shi tafara bugawa akai-akai.
Bissimillah yayi kana ya amshi yaron.
Wani irin faduwar gaba ya ziyar ce shi, copy dinshi ya gani a lokacin dayake jariri a wani picture dake parloun Abie.
Ya dago kai dai-dai lokacin da Dad ya shigo.
Murmushi yake shima Anuwar murmushi yake Dad yace;
"Surprise! Surprise...!"
Murmushi yayi yace;"Dad how do you know...."
"Shiiiiiiii, My son nasan inda zaka iya zuwa ina zuwa akace bakanan ko gida ban shigaba nayo nan, Mom dinka na gida tana jiran ka Congratulation My son"
Kallon Dad yake shida ba haihuwa akayi mashi ba amman Family House dinsu duk sun rude ko ina maganar ciki akai, murmushi yayi yamaida kallon shi ga yaron dake hannun shi yana murmushi lokaci guda yaji muguwar kaunar yaron.
Dad ya amshi diyar dake hannun Hajiya datayi mutuwar tsaye dan jinta take kamar a mafarki yau gata ga President sai murza ido take anya hakan zaiyiyyu yau silar Nana tayi ido biyu da abinda saide a tv take ganin shi, duk Barikin ta ko Governor bata taba ganiba a fili.
Kallon yarinyar Dad keyi lokaci guda yaji kaunar yarinyar saboda kusan komi na halittar su kalar na MANAL ne ya maida kallon shi ga gashin kanta daya kwanta.
Daddy yayi nisa a tunani sai Anuwar yace;"Dad wata marainiyya ce ta haifesu yar uwar su Doctor Mubarak ce chan dangin Mom dinshi na kauye wai diyar Yayan Mom dinshi ne, kuma Dad wai Mom dinshi tazo ta tafi dashi yarinyar na bukatar taimako fa"
Da Sister Fatima da Hajiya suka fita.
Maida numfashi Dad yayi yana kallon yarinyar dake hannun shi abubuwan da suka wuce suke dawo mashi ranar daya amshi MANAL a Spain a hannun shi, manna yarinyar yayi a kirji yana sakin ajiyar zuciya.
Jikin shi duk ya mutu yace a hankali;" zan masu komi a matsayin uban"
Cikin sauri Anuwar yace;"No Dad nima inaso na samu ladan su, ni zan dauki matsayin maihaifi tunda nima na kusa zama Uba, kai kuma Dad a matsayin kakan su dan kafara tsufa"
Ya ida maganar yana ma Dad gwalo tare da murmushi.
A hankali Dad ya lumshe ido yace;"Alhamdulillah Yau gani ina wasa da yaro na na kalli fuskar yarona na ganta cikin farin ciki, daji dadin zama kakan su sosai inason su sosai, tunda suka sakaman Anuu dina farin ciki".
Murmushi Anuwar yayi ya kara rungume yaron a kirjin shi zuciyar shi na kara bugawa akai-akai duk dakika guda kara son yaron yake.
Dariya Dad yayi yace;"kasaka a kira dangin ta abasu abinda za'a basu dare yayi mutane na jiran ka akwai walima da za'a shirya gobe"
Daga kai yayi wallahi jinshi yake kamar bazai iya barin yaran ba.
Sani ne ya shigo bayan sun gaisa da Dad Anuwar yace a kira Hajiya.
Hajiya ta shigo ta zube kasa tana kwasar gaisuwa.
Dad yace;"Kece wadda kuka kawo matar data haifi yara biyu"
Cikin sauri ta kara dukawa tace;"Eh nice uwar rikon ta"
Idon Anuwar yana ga yaron ya kasa dauke ido tunanin yadda zai badashi yake baiko Jin abinda suke cewa.
Yana dagowa yaga Dad yasa ambata kudi masu yawa murmushi yayi Dan yaji dadin kyautar.
Dad yace;"tashi mutafi dare yayi nisa, nima banson rabuwa da Amarya ta"
Yana kallon yarinyar hannun shi yana murmushin.
Murmushi Anuwar yayi amman ya kasa motsi ko kadan saboda baisan rabuwa da yaran.
Dad ya gane haka sai yace;"tunda kaine Uban yara kasaka masu suna mana, kuma akwai kayan dana ajesu saboda jikina na wajen Kulsoom amman yanzu sai abasu zan siyo maka wasu"
Murmushi Anuwar yayi yaji dadi sosai, daman Dad yayi dan yaji dadi.
Ya Mika ma Hajiya yarinyar yace;"Anuu kayi masu suna"
A hankali yace;"Farhan and farhana"
Murmushi Dad yayi yace;"sunci sunan su saboda su farin ciki ne ga kowa insha Allah"
Anuwar ya mike da Farhan a girji yana kallon shi kiss yakai mashi a koshi ya mikama Sister Fatima yace;"a fadama Momy dinsu sunan su saboda shiya dace dasu Sani zai jagoranci komi"
Yaron ana mikama Sister Fatima ya aza kuka cikin sauri Anuwar ya matso ya amshe shi yayi, sai kuma yaron yayi shiru su duka dariya sukayi sis Fatima tace;
"Yaro bayason Dad dinshi ya tafi, yasan hannun Dad dinshi"
Yana a kafadar shi har yayi shiru jin shiru suka duba sukaga yayi bacci.
Ya mikama Sis Fatima Dad ya kama hannun shi yana kallon yaron yana bacci har suka fita.
A zuciyar Dad kokari yake su fita kada Anuwar ya amshi macen dan akwai matsala dan kila tarewa zaiyi a gidan su yarinyar saboda yadda yaga kamannin su da MANAL.
Suna zuwa suka shiga mota sai gida.
Mamaki abin ya bashi yadda yaga gidan ana kide-kide ko Ina da haske mutane kamar ba dare ba kamar ana wani biki.
Kallon Dad yayi cikin mamaki.
Murmushi Dad yayi yace;"sai an kwana biyu ana murnar samun jika daga Anuwar sannan idan angama Kulsoom zata zabi kasar da zatayi rainon cikin ta har saita haihu"
Lokaci guda farin cikin daya ke a ciki ya kau.
Yace;"Dad akwai masu bukatata yaran nan uwar su marainiyya ce suma sannan Doctor Mubarak yabar gari Mom dinshi ta tafi dashi ina tunanin karya yayiman yarinyar dangin Dad dinshi ce dayake Mom dinshi basa shiri da dangin Dad dinshi na kauye please Dad kabar ni na taimaka masu"
Dad ya kama hannun Anuwar yace;"na maka alkawari duk wata zan basu kudin da zasu bukata bazasu nemi wani abu su rasaba"
Shiru yayi amman shi bazai iya barin garin nan ba.
Suna zuwa bai tsaya ban kwana da Dad ba ya bude yayi fitar shi.
A part dinshi ya nufa yanzuma babu kowa dakin.
Sama yahau ya kwanta tashi yayi yaje bakin window wayar shi ya ciro ya kira Sani yace gobe tun da safe yake bukatar kayan nan.
Zama yayi yaji baya iya jurewa jin kaunar yaran yake ta ko Ina.
Soyayyar yaran tasa ya manta da wani abu cikin Kulsoom, daya runtse ido yaron yake gani.
Da kyat ya samu ya runtsa.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Ina bude ido dare yayi nisa, na hango yara guda biyu kowane bisa wani gado na jaririrai ga jinin da ake karaman.
Murmushi nayi nace;"Alhamdulillah"
Sai kuma na tuna da Baba yanzu da yara biyu zan koma mashi.
Hawaye ne suka zuboman bisa fuskata nan nafara kuka hadda shasheka.
Sis Fatima dake bacci ta mike tace;"yawwa Nana kin tashi sannu, lah! Kukan mi kike?"
Ta matso kusa dani tace;"kece matar da tafi kowa sa'a a asibitin nan, ba'a taba haihuwar da Prince yazo ba sai wannan sannan albishirin yaran ki yan baiwa ne sunada Sa'a Prince shine zai masu komi kuma shiyayi masu suna hadda President kamar a mafalki dan haka ki godema Allah wallahi har bansan yadda zan maki bayani ba"
Na goge hawaye na ina kallon yaran sis Fatima tace;"Prince a matsayin shi na Uban yara ya masu suna Farhan da Farhana"
A hankali na maimaita Farhan Farhana...?
Murmushi nayi ina karajin kaunar mutunan a raina, to miyasa ya saka masu wannan sunan?? Yayi farin ciki da haihuwar su kenan??
A haka na kalli jinin shi da saura kadan ya ida shigewa nayi murmushi.
Lumshe ido nayi na kwanta.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Tunda safe ya shirya yaje part din su Abie a chan ya iske Dad.
Suka gaisa yace;"Dad zanje Abuja wajen Mubarak naji lafiya yabar asibitin"
Kallon shi Abie yayi yace;"kwana nawa zakayi ?"
Yace;"kwana biyu"
Dad yace;"Amman bakai kade zakaba ko?"
Yace;"Dad banason zuwa da kowa dagani sai Sani zamu tafi, kaga gidan su Mubarak zan sabka, kuma iyaka chan daga airport sai chan"
Abie yace;"kenan banda kai za'ayi walimar da Mom dinka ta hada maki"
Dukar dakai yayi yace;"Eh Abie a gafar ceni"
Daga kai sukayi Dad yace;"Sai munyi waya"
Sukayi bankwana yaje part din Ammie sukayi hadda Kulsoom haka na Momy suka fita shida Sani.
Kai tsaye a asibiti suka shiga suna shiga sukaga yaran a hannun Sis Fatima da wata Nurse.
Amsar su yayi yana murmushi Sis Fatima tace;"Bari na dauko Camerar asibiti ayi maku pictures saboda tarihi wallahi ban taba ganin yaran da sukayi kyau da Uba kamar yau"
Murmushi Anuwar yayi cikin sauri ta shiga office din Doctor Mubarak sai gata da Camera kika mashi su tayi sunata kamshi an masu wanka cikin kayan da Dad ya kawo masu.
Kallon yarinyar yayi yaga kamannin su daya da MANAL tana yarinya.
Kallon yarinyar yake tana wasa na hannunta wani irin bugun zuciya yakeji murmushi yarinyar tayi maida kallon shi yayi ga yaron.
Rungume su yayi baki daya a kirjin shi, duk abinda ake Sis Fatima na daukar pictures dinsu.
Sun dade haka kana ya bada yaran.
Amsar Camerar hannun ta yayi ya kalli Sani sutafi.
Suna tafiya amman zuciyar shi naga yaran nan, murmushi yayi yana tuna inda zashi.
A gidan su Sani suka yada zango.
Bayan sun gaisa da Inna Sani ya bashi kayan daya umarce shi.
Daga kayan yayi yana kallon su tare da mamaki baita ganin kalar suba.
Ga wasu takalma da yake tunanin taya zaisasu a kafar shi tsoro yakeji kada su jima kafar shi rauni.
Saka kayan yayi kallon kayan yake a jikin shi ya rasa taya zai iya zama dasu a jikin shi na wani lokaci.
A hankali ya saka kafar shi cikin wasu takalman roba gasu rufaffi ne.
Yana saka kafar shi yaji takalman na cizon shi hakanan ya daure.
Sani ne yayi Sallama yace ya shigo yana shigowa yace yanzu zasu airport din?
Kallon shi Anuwar yayi yace;"A mota zamuje Katsina"
Zaro idoo Sani yayi ya kara shigowa ciki yace;"Shugaba fa yana a gari koda bamu tare da Security zaisa a saka mana ido, to mizai hana muje airport aganmu muhau jirgin Abuja sai dare muhau na Katsina mana"
Kallon Sani yayi lallai maganar shi ce zata dauka dan yasan Dad baison ko kofar gida ya fita ba tare da Security.
Jin jina kai yayi Sani kayan shi ya maida tareda alkyabba.
Ya fito airport suka nufa kuma maganar Sani suna isa airport suka iske Security ko ina a airport din.
Jin jina kai Anuwar yayi yace;"lalle Dad"
Haka sukabar garin Bauchi zuwa Abuja suna zuwa nan ma suka iske Security a cike.
Gidan su Mubarak suka nufa, suna zuwa babu kowa sai masu aikin gidan wai sunbar kasar baki daya
Baidamu ba sai yamma suka bar gidan su Mubarak suna fitowa ko Ina sojoji ne a gaban gidan da alama biyo su sukayi.
Tsoki Anuwar yayi Kiran Babban su yayi yace ways sakashi nan yace Dad ne, kudi masu yawa ya basu yace suje su huta bayason ganin kowa a tare dashi.
komawa airport sukayi sukabar garin Abuja sai Katsina.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Koda na tashi da safe akaban labarin abinda ya faru.
Shiru-shiru ba Hajiya sai chan da yamma sai gata itada teema.
Yadda naga Hajiya sai kara washe baki suke ka abinci tayo iri-iri.
Sister Fatima tace;"idan kuka gama za'a iya salamar ku sannan zaku bada Address saboda Sani za'a ba.
Hajiya tace;"To shikenan ai yanzu zamu wuce"
Nan na sabko daga bisa gadon Hajiya ta goya macen Namijin a hannu.
Teema ta dauko kayan, muna zuwa Sister Fatima tace akwai kayan yaran.
Na aza a cikin laida sai naga anata zuba kaya a bayan mota.
Muna zuwa gidan su Hajiya aka azaman ruwan wanka.
Bayan Hajiya taman wanka na fito na saka kaya na, na zauna ina zaune Ina shayar dasu saiga Hajiya da Teema sun shigo.
Hajiya tace;"inason zamuyi magana dake mai mahimmanci dake yanzu"
Teema tayi sauri tace;"Hajiya..!"
Da karfi cikin mamaki sai abin yaban mamaki.
Hajiya wani kallo tayima Teema tare da cewa;"idan zaki bataman plan zan iya biyan ki kibar gidana bana bukatar ki ki tsaya matsayin ki"
Jin kalaman Hajiya sannan ga Teema tana kallon Hajiya cikin mamaki yasani nima mamaki.
Tomi Hajiya take nufii??
Wace magana ce??
♦♦♦♦♦♦♦♦
Suna isa Katsina ana magrib kai tsaye masallaci suka nufa sukayi sallah wani Shago Anuwar ya shiga ya chanza kaya.
A tunanin Sani Hotel zasuje ko gidan Sarki.
A bakin titi suka fito Anuwar sai kallon mutane yake yau itace rana ta farko daya shiga irin wadan nan mutanan.
Taxi ya tara ya shiga yace Batagarawa zasu.
Al'ajabi da mamaki ne suka ishi Sani.
A bakin wani Shago Anuwar ya sayi fitila.
Yace ma mai shagon;"malam dan Allah nankusa akwai fura mai dadi"
Maishagon yace;"Allah sarki yanzu babu fura dan yan furar sun koma garin su dan yan kauye ne ke tallar furar"
Cikin sauri yace;"ya sunan kauyen da ake kawo furar ne?"
Yace;"kauyen dake gaban mune nan Tudu"
Sukayi sallah Anuwar ya fito sukayi sallar isha'i.
Bayan sun fito hanyar kauyen yayi babu kowa sai daji.
Suna nan tsaye saiga wani yaro tafe da Amalanken shi.
Anuwar ya tsaidashi yace;"ina zamu samu motar zuwa Tudu?"
Yaron yace;"ai mota guda ce ta Manii kuma sai gobe da yamma. Yau yariga daya wuce"
Kallon yaron yake cikin mamaki.
Yaron yace;"ta Tudu zanbi kuzo na rage maku hanya"
Kallon shi Anuwar keyi cikin mamaki tareda zaro ido.
Yace;"mutane na hawa ne?"
Cikin sauri Sani yace;"to yaro Mungode ya sunanka?"
Yace;"Jabe"
Sani yace;"Amman ai kamar babu waje ko buhun huna sun rufe wajen"
Yaron yace;"kada kudamu haka nike dauko yayyena ada daga kauyen har birni tallar fura hadda kayan su, to bare kuda baku da Kaya"
Anuwar dayake kallon taya zai hau wannan abun ai saiya jimashi ciwo ko mota bayason yawo balle wannan abun.
Amman jin maganar Jabe yasa yace cikin sauri;"wane waje a birni?"
Yaron yace;"bakin wata baranda tana kallon makaranta"
Cikin sauri Anuwar yayi sujada a kasa sannan ya dago yace;"Alhamdulillah Sani gidan su nake nema"
Sani yace;"gidan su?"
Anuwar ya daga kai yana kallon Jabe dake mamakin ance gidan su ake nema.
MARYAM ANKUDII {QURRAH}
*JARABTAR MU*
*Page-63-64*
*Written by-Qurrah✍🏻*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Zikiri Bayan An Yi Sallama Daga Sallah.*
أَسْـتَغْفِرُ الله (ثَلاثاً) اللّهُمَّ أَنْتَ السَّلامُ، وَمِنْكَ السَّلامُ، تَبارَكْتَ يَا ذَا الْجَلاَلِ وَالإِكْرَامِ.
Astaghfirul-lah (3) Allahumma antas-salam waminkas-salam, tabarakta ya zal-jalali wal-ikram.
Ina neman tsarin Allah (sau uku).
Ya Allah! Kai ne Aminci, kuma daga gare Ka Aminci ya ke, alherinKa ya yawaita; ya ma'abocin girma da alheri.
لاَ إلَهَ إلاَّ اللَّهُ وحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، اَللَّهُمَّ لاَ مَانِعَ لِمَا أَعْطَيْتَ، وَلاَ مُعْطِيَ لِمَا مَنَعْتَ، وَلاَ يَنْفَعُ ذَا الْجَدِّ مِنْكَ الْجَدُّ .
La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, wahuwa ala kulli shayin qadeer, allahumma la mani'a lima a'tayta, wala mu'tiya lima mana'ata, wala yanfa'u thal-jaddi minkal-jad.
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki na Sa ne (Shi kadai) kuma yabo na Sa ne (Shi kadai), kuma Shi ne Mai iko kan komai. Ya Allah! Babu mai hana abin da Ka bayar kuma babu mai bayar da abin da Ka hana, kuma wadda ba ta tsirar da mai wadata daga gare Ka.
لاَ إلَهَ إلاَّ اللَّهُ, وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللهِ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَلاَ نَعْبُدُ إِلاَّ إِيَّاهُ, لَهُ النِّعْمَةُ وَلَهُ الفَضْلُ وَلَهُ الثَّنَاءُ الْحَسَنُ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ.
La ilaha illal-lah, wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, wahuwa ala kulli shayin kadeer. la hawla wala quwwata illa billah, la ilaha illal-lah, wala na'abudu illa iyyah, lahun-ni'matu walahul-fadl walahuth-thana-ol- hasan, la ilaha illal-lah mukhliseena lahud-deen walaw karihal-kafiroon.
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki na Sa ne (Shi kadai), kuma yabo na Sa ne (Shi kadai), kuma Shi ne Mai iko a kan komai. Kuma babu dabara babu karfi sai da Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; kuma ba ma bautawa kowa sai Shi. Ni'ima tasa ce, kuma falala tasa ce, kuma kyakkyawan yabo nasa ne. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, muna masu tsarkake bauta (daga shirka) a gare Shi, ko da kafirai sun ki.
سُبْحَانَ اللهِ، وَالْحَمْدُ ِللهِ، وَاللهُ أكْبَرْ. (ثلاثاً وثلاثين) لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ.
Subhanal-lah walhamdu lillah, wallahu akbar (33). La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamdu, wahuwa 'ala kulli shay'in qadir
Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma godiya ta tabbata ga Allah, kuma Allah Shi ne mafi girma. (Sau 33). Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, (Shi kadai), kuma Shi ne Mai iko kan koma.
Ana karanta wadannan surorin (kowace daga ciki har izuwa karshenta) bayan kowace sallah; amma bayan sallar Asuba da Magariba ana karanta su sau uku.
بسم الله الرحمن الرحيم{ قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ*اللَّهُ الصَّمَدُ*لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ *وَلَمْ يَكُن لَّهُ كُفُواً أَحَدٌ}
Bismi l-lahi r-rahmani r-rahimi.
Kul huwa l-lahu ahad, Allahu s-samad, Lam yalid wa lam yulad, wa lam yakun lahu kufu'an ahad.
{قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ * مِن شَرِّ مَا خَلَقَ *وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ * وَمِن شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ * وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ }
Bismi l-lahi r-rahmani r-rahimi.
Kul a'udhu bi-rabbi-l-falaq, min sharri ma khalaq, wa min sharri ghasikin idha waqab, wa min sharrin n-naffathati fi-l-'uqad, wa min sharri hasidin idha hasad.
بسم الله الرحمن الرحيم {قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ * مَلِكِ النَّاسِ * إِلَهِ النَّاسِ *مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ * الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ * مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ}
Bismi l-lahi r-rahmani r-rahimi.
Kul a'udhu bi-rabbi n-nas, maliki n-nas, ilahi n-nas, min sharri-l-waswasi-l-khannas, al-ladhi yuwaswisu fi suduri n-nas, mina-l-jannati wa n-nas.
Bayan kowace sallah sannan a karanta Ayatul Kursiyyu.
{اللّهُ لاَ إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لاَ تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلاَ نَوْمٌ لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلاَّ بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلاَّ بِمَا شَاء وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ }
Allahu la ilaha illa huwa-l-hayyu-l-qayyum. La ta'khudhuhu sinatun wa la nawm, lahu ma fi s-samawati wa ma fi-l-ard. Man dha l-ladhi yashafa'u 'indahu illa bi-idhnihi. Ya'alamu ma bayna aydihim wa ma khalfahum. Wa la yuhituna bi-shay'in min 'ilmihi illa bi-ma sha'a. was'a kursiyyuhu s-sama-wati wa-l-ard. Wa la ya uduhu hifzuhuma, wa huwal-l-aliyyu-l-azim.
Allah, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye, Mai tsayuwa da koma. Gyangyadi ba ya kama Shi, wala barci. Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin kasa nasa ne. babu mai yin ceto a wurinsa sai da izininsa. Yana sane da abin da yake gabansu (watau al'amarin duniya) da abin da yake bayansu (na al'amarin lahira). Ba sa sanin wani abu daga iliminsa, sai abin da Ya so. Kursiyyunsa (watau gadonsa) ya yalwaci sammai da kasa, kuma kiyaye su (sammai da kassai) ba ya yi masa nauyi. Shi ne kuma madaukaki, mai girma.
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، يُحْيِي وَيُمِيتُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ.
La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, yuhyee wayumeet, wahuwa 'ala kulli shayin qadeer
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Muli nasa ne (Shi kadai), kuma yabo nasa ne (Shi kadai), yana rayarwa, kuma yana kashewa, kuma Shi ne mai iko a kan komai (sau goma bayan sallar Magriba da Sallar Asuba).
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ عِلْماً نَافِعاً وَرِزْقاً طَيِّبَا، وَعَمَلاً مُتَقَبَّلاً.
Allahumma innee as-aluka ilman nafi'an, warizqan tayyiban, wa'amalan mutaqabbalan.
Ya Allah! Ina rokonka ilimi mai amfani, da arziki kyakkyawa (watau na halal), da aiki wanda za a karba. (bayan sallama daga sallar Asuba).
DEDICATED TO.....MY SISTERS😘
Bissimillah Rahmanir Rahim.
Page-63-64
--------------Miƙo man wata takadda Hajiya tayi tace; "inaso ki natsu ki karanta wannan rubutun dake a jikin takar dar nan".
Murmushi nayi ina juya takardar dana amsa nace; "Hajiya aini rubutun aj'mi kawai na iya karantawa banyi boko ba ko kaɗan saboda Baba Liman ne".
Murmushi tayi tace; "Baban ki yana Liman kika kwaso mashi cikin shege a gida?
Tab lallai kam dole ki gudu dan abin kunyar yayi yawa".
Kallon Hajiya nake cikin mamaki lokaci guda ta chanza miyasa?? Matar da kullum ƙoƙarin kwantar man da hankali take yau kuma ta chanza fuska sannan maganganunta sunyi man muni.
Na kalleta nace; "Hajiya idan wani abu nayi maki ki yafe man wallahi ban san nayi ba kuma ki fada man zan gyara".
Tsoki tayi ta miƙe tsaye fuskarta babu alamun wasa ko sauki tace; "duk abinda na kashe maki ne a cikin takar nan ko sabulun wankan ki yana cikin list din takardar hannun ki, wasu kaji da lemuka da kika chi kika sha duk suna ciki ina so ki biya ni, daman nayi hakurin ki haihuwa ne sai ki biya ni, ko kina tunanin ina da Imanin dazan taimaka maki ne?? to kibar wannan tunanin ina son kudina a cikin sati guda ko na batar maki da yaran ki ke dasu har abada".
Farhana ce a hannuna maganganun Hajiya suka sa saura kaɗan ta fadi Teema tayi saurin kamata jinayi numfashi na yana niyar daukewa saboda ko a mafarki ban taba tunanin haka ba.
Har ta juya ta fita saita dawo tace; "ohh! Naman ta baki san yawan kudin ba ko?? Dubu dari biyu ne da hamsin, kada ki mantadaga baya abincin gwangwani kika koma cii".
Daga haka ta juya ta fita, kasa kuka nayi jinayi lokaci ɗaya duk abinda ya faru baya ya dawo man wai daman mutane kalar su guda kenan??.
Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo man Teema ta dafani tace;.
"Ina da shawara"
Nayi saurin kallon ta!
Daga kai tayi tace; "zaki iya biyan Hajiya cikin wata guda nizan maki hanya".
Kallon ta nake cikin mamaki taya za'ayi na iya aikin karfin da zai kawoman waɗannan kuɗin da ko ganinsu ban taɓa yiba.
Tace;"Inaso kije dakin Hajiya kice kin yadda idan kika gama wanka yaran ki sunyi kwari zaki biyata kudinta ta hanyar da take so".
Na kalli Teema nace; "wace hanya Hajiya ke nufi?"
Murmushi tayi tace; "tana so tayi neman kudi dake saboda kina da kyau sosai, tasan zaki kawo mata costumers, ke bari na fada maki gaskiyar al'mari".
Nan Teema ta fadi man plan din Hajiya tunda ta fara bani labarin nake hawaye har ta gama tace; "yanzu mafita ta rage gareki".
Teema tace; "ga shawara zan baki kibi hanyar da Hajiya tace kibi, wallahi kinji na rantse zakiji dadi fiye da daa, kuma sannan yaran ki zasu tashi cikin gata dan mai reno za'a dauko maki ta kula da su iyakar ki shayarwa".
Duk maganganun Teema basa gabana saboda bazan iya dauka ba, ganin babu alamun daukar maganganunta yasa tace;
"Bari na takaita maki labari wallahi har kasar waje sai kin fita, zaki shiga cikin manyan yan matan garin nan, saboda kyawun ki dan kusan kullum sabbin kaya zaki saka, sannan ba haka zata barki ba saita wayar dake sannan hakan zai sa ke ma ki zama Hajiyar kanki, kullum kina bisa jirgi wannan Alhajin ya dauka idan kuka dawo wani zai dauka har Umra sai an samu mai zuwa dake, ita kuwa ko wannan wayar ta zamani iPhone din nan da ƴan mata ke rikewa kema sai tazo hannun ki a cikin sauƙi, yaran ki zasu zamto wasu taurari dan nasan duk idan kika fita sai kinyo masu siyayya gasu cikin ƙoshin lafiya".
Kallon ta nayi ina hawaye zuciyata tamkar ta fashe saboda bakin ciki.
Teema tace;"kiyi tunani zuwa safe, fiye da abinda na fada maki zai iya faruwa".
Na goge hawaye na ina maida numfashi nace; "Bazan butulce ma Ubangiji naba na aika abinda yayi hani dashi, zina fa Ubangiji Allah yace kada ku kusanceta, kusantar ta haramun ne, ko kalaman batsa kayi ka kusan ci zina balle aikata ta, shin Teema kinsan abinda kuke so na aikata ko kunsan girman laifin ta kuwa wajen Ubangiji? Manzon Allah (S.A.W) yace:Mai zina ba zaiyi zina ba, yayin da yake zina, sai an cire masa imani, Haba! Miyasa mutane muke zaman kanmu ne.
Wallahi Teema zina wata babbar musifa ce da bala'i da dukkan sharri, Zina itake ruguza al'umma, ita ke rushe mutunci, Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake samun dukkan sharri kamar haka: Raunin addini, Raunin akida, Karancin imani, Rashin kwarjini, Duhun zuciya, Fushin Allah, cikawa babu Imani, Karancin kunya idan nace zan maki bayanin kowane wallahi har safiya ta waye ba zamu gama ba dole na tsagaita.
Koda ƙaranci kunya zan dauka ke kinsan yanzu mutanen mu kunya tayi karanci maganganun batsa da shigar banza sunyi yawa ga al'ummar mu, kuma wannan duk sanadin Zina ne, zan dauki duk wata wahala ta rayuwa amman bazan sabama mahalicci naba, kila rayuwata a kunci da wahala zata ƙare amman zan daure kowa ne bawa da kalar Jarabtar shi ni tawa kenan".
Goge hawayen da suka zuboman nayi jikin Teema ya mutu hawaye itama ke zubar mata tace;.
"Ina ma yaranki murna koda basu zo ta hanyar aure ba amman sunyi dacen uwa ta gari, ina ma nima nazama kamar ki,irin kune iyayen da yaransu ke alfari dasu, zan taimaka maki insha Allah, ban taɓa jin na tozarta ba sai yau ban taɓa tunanin barin gidan Hajiya ba sai yau, Nana ina tsoro kada na mutu yanzu mizan cema Ubangiji na".
Na kalleta nace;"Ubangiji mai karbar tuban bayin sane".
Teema tace;"ki tashi yanzu na dauki hankalin Hajiya ki debi kayan ki da kike so dana yaran ki waɗanda aka baki a asibiti ki gudu dan Hajiya akan kudi zata iya komai ko batar maki da yara tana iyawa".
Na daga kai na tashi na goya Farhana, Farhan kuma yana hannu na, na ɗaukar masu kaya kala biyu kowanne Teema ta zabar man na dauki zoben daman dashi kaɗai nazo Teema ta sakaman a jaka wata yar karama.
Taban kudi naira dubu tace sune da ita.
Nace;"idan Hajiya tabi bayana fa?"
Tace;"ba zata bi bayan kiba dan zan cemata ta saida kayan yaran ki masu tsada ne, ni bamma taɓa ganin kalar suba sun isa kudin da take bin ki, ko kuma sunyi in kuma ba hakaba to nima zan tona asirin abinda yasa ma nace ki gudu ina tsoron kada ta cutar dake ko yaran ki".
Najin jina kai na dauki jakar da hannu daya, dayan kuma Farhan yana a kafaɗata.
Tare muka fito da Teema ita ta shiga parlon Hajiya ni kuma na fita ina zuwa kofa a bude na tura na fita.
Titin babu kowa nabishi ina tafiya naji karar mota bayana na juya na matsa daga titin.
Har sun tafi suka dawo mutane biyu ne, kalar kayan gidan Sarki garesu dan akwai haske a titin hakan yasa naga kayan su.
Daya yace;"Ina zaki baiwar Allah dare yayi wace unguwa kike mu ajeki, munan Gubi zamu Allah yasa hanyar mu daya".
Nace cikin sauri;"Eh ai chanzani"
Daya ya fito ya amshi jikar hannu na ya saka mota yace na shiga na zauna.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Murmushi yayi yace;"Sani taya ake hawan wannan abun?"
Cikin sauri Sani yace;"Bari na gyara maka wajen da zaka hau".
Cikin sauri yaje ya ture buhun-hunan yace;"Allah ya taimaki ji......"
Bai ida ba Anuwar ya ɗaga mashi hannu yace;"ka kirani da Anuwar kada ka kara wannan maganar".
Duƙar da kai Sani yayi, yayi sauri zai kai kasa Anuwar yayi saurin dago shi, Jabe dai kallon su kawai yake.
Sani ya nuna mashi yadda zai hau yakai hannun shi zai kama Amalanken yayi saurin cire hannun na shi tare da kallon wajen.
Ajiyar zuciya yayi ya runtse ido ya kama ya hau tare da sakin numfashi.
Sani yaje kusa da Jabe yace ya bashi shi zai jasu, Jabe baiyi gardama ba saboda yanzu tsoron su yake dan mamaki yake ace mutumin kauye yana tsoron Amalanken wai bai iya hawa ba ko dai wulakanci ne.
Haka suka fara tafiya Jabe da Sani sunata fira, chan Jabe yace;"Amman kamar duk rigar ku yafi kowa kyau ko?
Sani yayi murmushi yace;"eh"
Yace;"muma muna da Nana mai fura suna kama itama duk kauyen su tafi kowa kyau"
A haka har suka isa gidan su Jabe.
Koda suka sabka Anuwar duk ya galabaita zufa ta ko ina a jikin shi.
Kallon wurin da suka zo yake yana maida numfashi Sani yace;"Allah ya taimake ka bamu da ruwan da zaka sha"
Dai-dai lokacin da Baffan su Jabe ya iso da tabar ma a hannu tare da Jabe.
Cikin sauri Baffa ya shimfida yace;"sannun ku da zuwa Jabe yace baki nane"
Sani yace;"yawwa sannu dai"
Suka zauna bisa shimfida Jabe ya aje ruwa cikin wani koko.
Sani yace;"mun gode"
Sani yace;"daman wajen ka muka zo akan wata diyarka mai tallar fura".
Baffa yayi shiru yace;"yarinyar nan ba diyata bace, amman kawar diyata ce tare suke zuwa tallah sannan mahaifin ta abokina ne, ga gonar shi gatamu munyi zaman mutumci".
Ajiyar zuciya Anuwar yayi yace;"inane gidan su?"
Sani ya mike yace;"zanje na kewaya bandaki"
Ya mike yabar wurin Anuwar ya gane nufin shi murmushi yayi, saboda hankalin Sani yasan babu abinda yake ji.
Bayan tafiyar Sani Baffa yace;"labarin yarinyar babu dadi, ta fada a cikin kuncin rayuwa tayi rayuwar kunci, bari na baka labarin abinda nasani akan rayuwar ta".
Nan Baffa ya fara ba Anuwar labarin abinda ya faru tun daga farko har karshen guduwar ta.
Dafe kai yayi yana cewa;"innalillahi! Daman akwai azzaluman mutane irin matar nan? To yanzu wane gari Baban ta suka koma??"
Baffa yace;"Bayan yadawo yarinyar ta gudu bansan abinda matar tace mashi ba yaje wajen diyata ko tasan inda take kota fada mata saboda itace Aminiyar ta, tace mashi tace zataje Bauchi wajen wata mata, a lokacin ya koma Bauchin koda yaje tace bata zo ba, haka ya dawo daga karshe de diyar nan ana tunanin ta halaka dan har yau babu wanda yace ya ganta cikin yan kauyen su".
Dukar dakai yayi yana jin zuciyar shi tamkar ta fito duk wahalar nan shine sila yanzu idan bata raye fa?
Bazai taɓa yafe ma kanshi ba.
Anuwar yace;"ya fadama garin da suka koma?"
Yace;"Eh ya koma asalin garin su yanzu yana Dan-musa a chan ya koma da zama"
Anuwar yace;"zamu samu motar garin yanzu?"
Yace;"a'a akwai nisa kabari gobe muje, amman baka fadaman kai waye ba ko cikin dangin Maman tane?"
Shiru Anuwar yayi ya mike tsaye yace;"saida safe"
Baffa yace;"ga daki nan zuwa safe sai mu shirya?"
Sani ya kira yazo suka shiga dakin.
Wani irin sanyi ne ake a garin.
Wani daki suka nufa babu ko kyaure a daki ga sanyi anayi sosai.
Shiga suka yi sai gadon kara, da wata molakakkar katifa dake shimfide a bisa gadon karan.
Sani yayi saurin gyara gadon ya shimfida ya gaggen zanin gadon dake kai.
Sani yace;" ko kana bukatar wani abu?"
Girgiza kai yayi yaje bakin gadon ya zauna.
Sani yayi shimfida a kasa zai kwanta Anuwar yace;"kazo ka kwanta anan bazan yi bacci ba"
Ya mike duk sanyin da akeyi yabar dakin.
Gidan ya fito cikin sanyin nan.
Zuciyar shi tacika da kunci da nadama da addu'ar Allah yasa yarinyar tanada rai, yunwa ko bacci babu guda wanda yakeji.
Jinshi yake tamkar ya jawo daren.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Daya daga cikin su yace;"baiwar Allah halan auren kine ya rabu aida kinyi hakurin har zuwa safe a dinga kai zuciya nesa, Kuma ma baccin abin kuruciya da kika fito ina zaki samu mashin anan dare yayi, muma sakon sarki ne zamu amso ammanta yau Sani benan bai amso ba, sai yanzu aka tina dabaki hadu damuba"
Na jinjina kai saboda na rasa ina zani ina zan dosa.
Muna isa sukace ina zamu ajeki mu gidan Rabi Mai fura zamu kinga bayan gari fadi gidan da zaki"
Nace;"ai kusa damune konan kuka ajemu yayi"
Sukace;"to"
Muna zuwa suka ajeni anan na.
Nayi masu godiya nasamu bayan katan ga na boye bayan sun shiga Jim kadan sai gasu sun fito suka hau motar su suka juya.
Suna barin wajen na fito daga inda na boye nazo kofar fidan dai-dai lokacin da tsohuwar tazo budewa.
Subhanallah!
Shine abinda ta fada dan bataji takon tafiyata ba saide taganni.
Tace;"yarinya daga ina haka cikin wannan daren gaki da yara?"
Nace;"ki taimaka man dan Allah na kwana zuwa gobe nabar maki gidan"
Ta amshi yaron hannu na tace;"shigo"
Na shiga ta kulle gidan.
Tayi gaba nabi bayan ta har dakin ta.
Gado ne mai rumfa sai wani a gefe sai kujera mai chin mutum biyu, dakin de kalar dakin kauye ne amman yayi kyau sai kamshi yake.
Tace;"zauna ga kujera Nan"
Na zauna tareda kwance goyo na ta aje Farhan bisa gado ta fita sai gata da languna masu kyau tuwo da miya.
Ta aje a gabana ta kawoman ruwa cikin kofin silver tace;"kawo wannan kici abinci"
Na mika matashi na sabko bisa leda na zauna nafara cin abincin.
Saida na gama na fita na kwanke hannu na dawo har ta kauda kayan danaci abincin tace;"miyasa kika fito gidan ki a yanzu da danyen jego?"
Nace;"Banida kowa"
Shiru tayi tana kallo na ta girgiza kai tace;"uban yaran fa"
"Bansan shiba"
Kallona take cikin mamaki tace;"Allah ya kyau, yanzu dare yayi zaki iya kwanciya kuma zaki iya zama anan"
Nace;"Inna akwai matsalar zamana"
Nan nabata labarin gidan Hajiya nace;"kada ta biyoni"
Tace;"to shikenan daga yanzu zaki zauna anan babu wanda zaisan kina nan kuma tsakanin mu da gari akwai dan nisa"
Nace;"Nagode"
Tace;"yaushe kika haihu?"
Nace;"Jiya"
Ta daga kai naje gadon da ta aje yaran na kwanta.
Can tsakar dare Farhana ta farka tana kuka na bata Nono Amman bata daina ba ita ta amsheta tana jijjigata har tayi bacci a kafadar ta.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Duk sanyin nan akanshi ya kare kana ya koma ciki yayo alwala yaje cikin daki yayi sallah.
Zama yayi yana tunanin kada Dad ya tsananta bin cike akan shi fa, dauko Camera yayi yana kallon pictures dinsu na jiya a asibiti, murmushi yayi ya manna masu kiss yace;
"I miss you so much"
Duk duniya yaran kade zasu iya saka shi murmushi a yadda yakeji.
Jabe ne ya shigo ya aje masu koko da kosai ya gaidasu.
Sani yazo ya mika ma Anuwar ya kalli abinda aka kawo mashi.
Sani yace;"Ga abinci Dan Allah kaci kodan lafiyar ka rabon ka da abinci tun Break din jiya"
Ya amsa shima yasan yanajin yunwa Amman jin labarin yarinyar yasa ya manta da yunwa.
Daukar kofin silver yayi ya kafa a bakin shi ya kurba.
Cikin sauri yayi waje a guje zubar dashi na kalkalin amai.
Sani yazo ya kawo mashi ruwa ya kuskure bakin shi suma babu dadi kamar ba ruwa ba kamar an saka gishiri.
Sani yace;"konaje Batagarawa na siyo maka break da ruwa"
Kirgiza kai yayi yace;"bazan shaba wannan din de su zan sha muje na chi abinda suka kawo"
Suka koma daki ya runtse ido ya kafa kai yasha kokon ya dauki kosai yana tamnawa tamkar yana tamna magani haka yakejin kosan.
Sani ya girgiza kai yana tunanin wannan wace yarinya ce Anuwar ke nema ya jefa rayuwar cikin wahala?? Kallon kafar shi yayi yaga tayi jawur lokaci guda hawaye suka kawo ma Sani lallai wannan So jarabta ne a rayuwar Anuwar.
Tashi yayi yabar dakin saboda bazai iya kallon yadda Anuwar ya chanza ba lokaci guda harda rama yayi.
A gaban gida Anuwar ya iske Sani.
Saiga Baffa yace;"zakuyi wanka domin ni na shirya"
Anuwar ya sosa jikin shi dake mashi kai-kai yace;"zanyi idan bazamu takura kuba"
Baffa yayi murmushi yace;"Babu komi shigo"
Anuwar ya shiga Baffa yasa aka kaimashi ruwa ya nuna mashi bandaki.
Sani de idone nashi tun yana al'ajabi har ya dawo tausan Anuwar.
Anuwar yana shiga kafafun shi suka fara kyarma dan bandakin akwai tumakin su.
Cikin sauri ya fito yace;"muje"
Ba musu suka tafi Sani yace;"inazamu samu motar dazata fidda mu"
Baffa yayi murmushi yace;"ai a kafa zamu tafi"
Zaro ido Sani yayi yace;"to ai ko a Amalanken mutafi dan akwai nisa"
Baffa yace;"to bari na kira Jabe"
Gida ya koma sai gashi tare da Jabe.
Amalanken suka hau Anuwar banda kallo babu abinda yake, sai tunanin daman akwai mutane masu irin wannan rayuwar??
Kuma suna jin dadin rayuwar.
Dai-dai gidan su Nana Baffa yace;"kaga gidan mahaifinta na nan kauyen"
Kallo Anuwar yabi gidan dashi har suka wuce.
Suna zuwa Batagarawa suka hau motar Katsina.
Suna zuwa Katsina suka shiga tasha babu wanda ya damu da Anuwar tun ya dukar da kai har ya dan saki jiki.
Suna zuwa suka hau mota,motar nada tsawo sosai ga mutane aka amshi kudin motar.
Anuwar yaga yadda za'a tutsa su ya zaro ido yana kallon mutane.
Sani yace;"mutum nawa za'a saka anan?"
Mai motar yace;"Kai Malam wannan wace tambaya ce kasan mutum hudu ake sawa nan inda kuke saura mutum guda kenan"
Sani yace;"a barmana duka sit din baya guda biyu"
Cikin sauri Anuwar ya kalle shi yace;"a haka zamu zauna"
Mamaki Sani yace kudin kejara guda yaso abada nashi shida Baffa kujera daya, amman taya za'ayi su zauna a matse Anuwar??
Haka suka zauna har mota ta cika suka fita.
Lokaci guda Anuwar ya tsohe hancin shi jikin sai zufa ke zuba.
Sani zaiyi magana Anuwar ya daga mashi hannu.
Haka sukaita tafiya shikan shi Sani da yasaba wahalar kauye amman yau jinshi yake a wahalar ce.
Sunyi tafiya mai nisa sosai kana akazo wani gari mai dan girma.
Nan sukaga mutane sun fara sabka a tunanin su nanne Dan-musa su duka hamdala sukayi.
Sai sukaji wani yace;"naji kunce Dan-musa zaku a ajemu nan mu hau mota basai anje Tasha ba"
Su duka suka kalli juna Baffa yace;"eh nan Dutsam-ma ne yanzu zamu hau motar Dan-musar"
Anuwar na fito kayan shi duk sunyi dauda sun ya mutse gashin kamshi ya ya mutse duk ya rame.
Maida numfashi yake kafar shi jini ya taru ya kwanta.
Jikin shi kaikayi yake mashi da kyat yake maida numfashi.
Kallon shi mutunan da zasu tasha yake yace;"amman ku bakine dan Dan-musa aka haifeni ba wanda bansani ba?"
Sani yace;"Eh yau zamu fara zuwa"
Yaron yace;"Haba shiyasa dan har ma aikatan su nasani dayake karatu nake duk weekend saina koma"
Jin jina kai Sani yayi shine Anuwar yana gefe yana maida numfashi har juwa yake gani.
Yaron yace;"mutsaya nan gefen hanya yanzu mota na zuwa har Dan-musa"
Suka tsaya yaron yace;"Shikam dan uwanka na kama da Anuwar dan President din mu amman shi ance bai zama kasar ko jiya saida muka kalli bikin shi a Facebook maganar aketayi ba'a taba bikin da aka kashe ma kudi a Nigeria kamar nashi ba, kai gaskiya kuna kama idan na dauki photon ka na'aza a Facebook sai annemoka"
Kara kallon Anuwar yayi yace;"Kai shine kode mafarki ne"
Kamin Anuwar yace wani abu yaron ya dauki photon shi.
Dai-dai lokacin da wata katuwar matattar mota ta tsaya a gaban su yaran motar yana cewa;
"Dan-musa, Dan-musa"
Anuwar ya kalli Sani cikin mamaki.
Yaron yace;"kunga ga mota nan tazo, muje"
Sani yace;"Yarima..."
Bai idaba yaron yayi saurin kallon su, shima Yarima ya zaro ido Sani kuma ya tushe baki.
0 comments:
Post a Comment