---------------Murmushi yayi yace;"Kada ki damu Mummy naga duk kin ruɗe, please Mummy ki fahimce ni wallahi ba Aljana bace Mummy mutum ce har mahaifinta na gani munyi magana a shekarun baya, Mummy bansan ya a kayi ba na manta da ita yanzu Mummy ina buƙatar taimakon ki idan muka koma Nigeria daga ke sai Ammie ne zaku iya fahimta ta, Mummy ki taimaka man, saboda tafiyar ta na kama data MANAL idan suna gudu hakan yasa na saka mata fuskar MANAL".
Ƙara riƙe hannun shi tayi tace;"Na yadda da kai Anuu amman kasan matsalar guda ce, ba zan goya maka bayan ka ƙara zuwa wannan kauyen ba, kai ko Katsina ban amince kaje ba, saidai abu guda zan maka ina so ka saka Sani yaje garin su yarinyar yaji minene labari sunji labarin ta idan babu labarin ta to taimako guda zan maka tunda kace baka san fuskarta ba cikin dare abin ya faru, kuma basu da hoton ta ina da wata dubara".
Cikin sauri yace;"Mummy fada man ina son ganinta, Mummy yarona ko yarinya ta sun isa girma sun fa girmi Hamrah".
Tace;"kwantar da hankalin ka, abin mai sauki ne"
Kallon Mummy yake yana jiran me zata ce
Mummy tace;"Mahaifinta Sani zai je ya taho dashi, idan suka zo sai ya fadi maka kamanninta kana zanawa idan ka gama zana fuskarta, sai a saka a media a saka kudi ga duk wanda ya kawota za'a saka kudi masu yawa, nasan zaka iya saboda kwarewar ka a zane, kaga MANAL ta taimake ka data saka ka karanci zanen".
Cikin murna yace;"Mummy hakan yayi sosai nagode"
Tayi dariya tace;"yanzu wannan photon MANAL ne kazana ba wata Mai fura kayi wayo, Matan duniya sun kusa koma maka MANAL naga alama"
Murmushi yayi yace;"ai duk matan duniya babu mai kyawun ta, itama Mai fura kalar tafiyar ta nace, tasamu wani kasone a zuciyata shiyasa na aza mata fuskar MANAL dan zata fi mata kyau, amman nasan MANAL dina ta fita kyau"
Mummy tayi dariya tace;"lallai kam na yadda tasamu waje a zuciyar ka amman kana nufin duk saida ranka da kayi bata kai MANAL ba?"
Murmushi yayi yace;"kinsan a cikin mata akwai Special one"
Dariya Mummy tayi tace;"lallai kam yanzu dare yayi bari naje, kasan gobe da wuri zamu tafi ko? Ka shirya zan saka Sani yazo tarbar ka dan kasan da gaske nake idan ka huta kwana biyu sai mu aika Sani lokacin an gama walima hankali ya kwanta".
Murmushi yayi yace;"to shikenan Mummy"
♦♦♦♦♦♦♦♦
Tsaye nake ina dakan fura bayan dalibaina sun fita.
Farhan yana zaune waje guda, daman shi wasa baida meshi ba, sannan baida fada ko kaɗan baida fita tun suna yara da wahala kaji kukan shi maganar shi ma a hankali yake yinta ga natsuwa da hankali bai damu da shiga yara ba.
Sai Farhana sarkin yan jan fada da wasa, ga fada da surutu kamar aku haka take a bangaren surutu, kusan ko ina ansan ta ga shegen yawo wanibi sai Inna ta fita neman ta.
Wasu lukuta a cikin yan matan wata makaranta ake ganota, Farhana ita ke ce masu gidan su ana fura suzo su siya, Inna har maganin baki ta bata dan itama tsoron surutun Farhana take ga shegen wayo.
Farhana tace;"Ummie gaskiya nima ki si ya man kayan wasa su Bintar gidan Malam liti suna dasu na kasa, Innarta tace ta siya mata kema ki siyaman, tukane da ɗiyar bebi"
Inna dake zaune tana tanka ɗe tace;"kada ki damu sarkin yan wasa indai kina barin zuwa gidajen mutane saboda wasa zan siya maki"
Tace;"Wallahi Inna na daina, idan na ƙara zuwa ki daure man kafafu, Inna hadda takalma masu tsini kalar na Sallah a sayo man a Kasuwa".
Inna tace;"to shikenan Allah ya kaimu ranar Kasuwa kawun ki Salisu na bashi ya siyo maki".
Tsalle ta fara tana cewa;"Nima na kusa samun kayan wasa"
Tsalle take sosai tana murna nidai saidai nayi dariya.
Yaya Sani ne ya shigo yana washe baki bayan mun gaisa yace;"Inna gobe akwai Fura ta musamman muna da Babban bako".
Cikin ɗoki Inna tace;"Wanene zai zo garin namu, kada dai ka ce man Yarima?".
Yaya Sani yace;"Yarima ne dakan shi hadda iyalan shi, zasu shigo, shiyasa gari ko ina gyara ake, hadda gidan Lambu yanzu aka kirani aka ce naje nasa kuyangi su gyara mashi gidan Lambun shi, shine ma na biyo, yanzu zanje na dauko masu aiki".
Inna cikin murna tace;"Kai masha Allah, ai wannan ba komai bane ba, ko Nana na zuwa ta gyara dan Yarima akwai son tsabta gashi Nana ta iya gyara ita ya dace taje daman ta kusa gamawa, bari sai na amshi aikin Yarima babu sanya yanzu za' ayi mashi".
Sunan Yarima kaɗai aka ambata Amman nabi na roɗe chan naji Inna tace;"Nana yi maza ki tashi ki ɗauko mayafi ki tafi".
Cikin sanyin jiki nace;"to"
Har na jefa ƙafa ta ɗaya a cikin ɗaki naji Yaya Sani na cewa;"Inna kin san Alhaji Yakubu ya matsaman akan maganar Nana tun lokacin da yaganta taje barkar matar Salisu".
Cikin ɗakin na shiga tare da tsayawa dan inji me zai ce.
Yace;"ko yanzu da zan shigo na ganshi waje wai zai maki sallama tunda na kasa mashi hanya shi aure yake so da gaske, nace yayi hakuri yau mun fara hidima na zuwan Yarima yayi hakuri har hankali ya kwanta sannan ayi koma meye. Zaman yarinyar nan haka ba zai yi yuba ba miji duk da duk tsawon shekarun nan bata fita, amman kinga gashi ta samu miji to kinga ya kamata taje d'akin ta, yara kuma koni ina rikasu balle kina da rai, kinga idan hankali ya kwanta sai mu tafi tare da ita wajen dangin Mahaifinta koda zasu yi wani abu dole a ne me su tunda aure dole saida su, kinji abinda nike tunani na dakatar dashi har zuwa hankali ya kwanta sai ayi abun a tsanake"
Inna tace;"hakan yayi Allah yayi maku albarka nima yanzu hankali ya karkata da Nana taje dakin ta da kuruciyar ta zama haka bazai yiyuba, sannan duk yadda dangin Baban ta suka kita dole yanzu muje wajen su dan su san tana raye ai sun isa su manta hakanan, inma basu amshi yaran a matsayin dangin suba ku kun ishesu ko bayan Raina"
Wasu hawaye ne suka zuboman na goge na rasa dami zan saka masu Inna lallai sun isheni dangi, saide Mahaifina Koda yaushe yana raina nima ina bukatar ganinshi.
Inna ke gwalaman kira tana cewa nafito muje.
Goge hawayen nayi na saka Hijab dina na fito kaina a kasa nace;"sai mundawo"
A zauren muka iske Farhana na wasa da diyar kara da Farhan yayi mata.
Allura ce a hannun shi yana zirgawa riga yake mata.
Cikin sauri nace;"Farhan miya hadaka da allura? Miyasa ka daukar ma Inna kaya?"
Lokaci guda ya rude yace;"kiyi hakuri Ummie Farhana keson kayan wasa shine nayi mata diyar kara ina dinka mata kaya kuma wallahi bazan batar ba"
Kara bata fuska nayi nace;"mikoman"
Ya mike zai mikoman reza ta fado daga bisa jikin shi.
Cikin sauri nace;"Subhanallah!! Miyasa bazatayi hakuri ba tunda Inna tace zata siya mata, yanzu hadda reza kuka dauko idan kuka yanke fa?"
Yaya Sani yace;"Farhan bani kada ka kara yanzu idan na fita zan nemo inda ake saidawa zan siyo mata kaji, kubar amfani da allura ko reza kada su yanke ku kunji"
Daga kai yayi Farhana sai zare ido take dan duk rashin jinta tana tsoron duka.
Yaya Sani yace;"kuzo muje ku raka Maman ku gidan Lambu"
Su duka suka taso da murna.
Muka fito tafiya kadan ta kaimu a gidan.
Muna shiga ya budema dakunan yace zaije ya dawo.
Tsayawa nayi kallon wajen gidan katon wajene an shibka kayan itace ga wajen zama wajen ya hadu dagani har yara kallo muke.
Muna shiga dakin muka zamo tamkar wasu wadan da basu taba shiga burni ba, komi na dakin ya zamo mana sabo sai kallo muke.
Farhana tace;"Ummie na zauna dan Allah bisa nan"
Ta nuna kujera nace;"a'a Farhana abinki yayi yawa ku zauna a kasa"
Bata fuska tayi tace;"Ummie ba ance Baban mu bane, munaso mu zauna bisa, sun burgemu"
Ban tsaya bata amsaba saboda naga abinta yayi yawa wai gidan Baban sune.
Ina fita wannan dakin naga kuma wani waje, wajen wani katon wurine ruwa ne a tsakiya cikin katon kwami, saman a bude kana kallon sama, wajen ya hadu sai daukar ido yake.
Ciki na kara shiga naga wasu kujeru da tebir a gaban su da wani madubi kamar na zinari wurin yayi kyau nan ne naga dakuna ukku ina budewa naga gadone a ciki.
Na shiga na fara gyarawa hadda ban daki mai kamar daki saboda kyau sai daukar ido yake.
Ina gamawa na fito naje dayan dakin shima gado ne na gyara shima hadda ban daki duk na chanza masu zanen gado.
Dakin dake kallon wadan nan nashiga ina jefa kafa gabana ya fadi saboda jin kamshin turaren da bazan taba mantawa.
Kallon dakin nike komi nashi mai ruwan hoda ne, kallon dakin nike ina wani tunani haka kawai naji dakin da kalar sun birgeni.
Dakin an cika shi da abin wasan yara gado biyu kala daya duk kananu na wasan yara sai wajen aje kaya hadda wajen aje takalma, hadda ta kalman yara maza da mata.
Dakin duk yafi daukar hankali na.
Karar bude kofatane ya dawo dani daga duniyar tunanin dana shiga.
Su Farhana ne suka shigo da alama wani abu sukayi.
Dan aguje suka shigo ganin yadda dakin yake yasa sukayi turus suka saki baki suna kallon dakin.
Farhana ta washe baki tana kallon manyan kayan wasa, da takalma masu tsini da takeso.
Cikin murna tayi inda suke, wata katuwar diya ta runguma wadda ta kusa girman ta.
Cikin sauri naje na jayeta daga jikinta.
Nace;"Miya kawo kunan ne? Yanzu idan suka iske ki da kayan su bazan hanasu dukan kiba, tashi ku tafi gida idan baku zama a dakin farko"
Farhan yace;"daman saida ta zauna bisa kujera shine nazo na fada maki, ta biyo ni"
Farhana ta fara alamun hawaye tace;"Ummie kiyi hakuri wallahi inason gidan nan nide kibar ni anan ku koma gidan Inna Kawu Sani fa yace gidan Baban mune kuma kowa ai gidan Baban su yake zama, nima zan zauna gidan Baba na"
Farhan ganin Farhana na kuka yabi ya rude, kokadan baison kukan ta shiyasa ko fada ta jawo shike shigan mata.
Kama hannunta yayi yace;"kinga yanzu gidan babu kowa Kawu yace saida daddare zasu iso ko gobe da safe muje na fada maki wata dubara"
Kama hannunta yayi suka juya ni kuma nayi murmushi dan dariya sukaban Wai gidan Baban su, aikina na cigaba na gyara dakin sosai dan da alama nan yake zama dan naji da zan chanza zanen gado yadda yadda yake kamshi.
Har yamma muna gidan saida na gyara ko Ina.
Tunda su Farhan suka fita ban kara jinsu ba nasan sunyi zuciya harmade Farhan sarkin yan zuciya da kafiya gashi da hikima, duk yadda Farhana ke fitima daya jata na rasa miyake fadamata saitayi shiru yanzuma nasan gida ya jata sukayi.
Nagaji sosai dan nasaha aiki sosai.
Ana kiran magrib Yaya Sani yazo sai sannu yakeman, nace na gama na wuce gida.
A gajiye na isa gida ina zuwa nayi Sallar magrib nayi Isha'i sai bacci, daman Inna ke kula da sunci abinci da wajen kwanciyar su.
♦♦♦♦♦♦♦♦
A Abuja suka Sabka Dad yace abari saida safe aje Bauchi.
A Babban parloun Dad yaga photon shi da twins, mamaki yake haka parlaour din Mummy.
Mummy tace;"duk wanda yaga photon nan sai yayi magana, a parloun Dad dinku da wani dan jarida ya dauki photon duk inda kayi a social media maganar ake wai Yarima Anuwar ya haifi yara biyu"
Murmushi yayi yana kara kallon photon son yaran ya karu inama ace nashine part dinshi ya nufa zuciyar shi cike da farin ciki yaran nasa shi farin ciki sosai.
Ko a Abuja tsakanin Anuwar da Kulsoom babu wani abu sai Hamrah dake surutu a tsakanin su tana koma part din Mummy ya koma dakin shi ya kulle.
Safiya nayi ya shirya a parlo suka hadu suka gaisa.
Suna gama breakfast wajen karfe koma suka nufi airport sai Bauchi.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Tunda suka tashi naga sunata farin ciki da dauki har Farhan da bai cika nuna farin ciki ba amman shima Yau fuskar shi sai fara'a yake.
Da wuri mukayi aikin fura, narasa gane masu su suka zuba ruwan wanka zasuyi Inna tace ita zata masu.
Na dauko masu kaya su saka sukace kayan sallar su zasu saka kallon su nike sai wani doki da farin ciki suke.
Nace;"akan mi zan baku kayan Sallah kubari sai gobe jummu'a na fiddo maku kunji"
Su duka suka bata fuska Farhana sarkin yan kuka har ta fara.
Inna ta shigo tace;"lafiya take kuka, daman fada muke dake, jiya kin saka su kuka"
Nace;"Inna babu abinda nayi masu wai yau Alhamis fa amman shaddar su ta sallah wai zan saka masu nace suyi hakuri sai gobe masallaci"
Inna tace;"jiya da kika korosu sukazo suna kuka kin hanasu zama gidan Baban su, da Sani yazo da yamma suka fada mashi shine yace su shirya zaizo ya dauke su suje tarbar Baban su, tunda kika kuresu, dan haka ki saka masu kayan su"
Kallon su nake Suma ni suke kallon Inna tace;"Bari hararan man jikoki bari nazo na saka masu da kaina daman jiya fushi nayi dake shiyasa ko abincin dare ban maki magana ba da baki chiba dan mi zaki koresu, yaro ai ba'a rabashi da kayan wasa, yanzu haka kayan baki daya yau za'a chanzasu da kinbar su sunyi wasa ba shikenan ba"
Shigowa tayi ta dauko masu kayan su na Sallah shadda ce iri daya suka saka sai murmushi suke.
A daukoma Farhana ta kallar manta na Sallah masu tsini har yanzu bata iya tafiya dasu ba tana tafiya tana faduwa amman tafison su, da Sallah ta aza kuka saida Yaya Sani ya siyo mata su.
Na rasa miyasa suke kaunar wannan??
Cikin Raina nace;"kodan ya taimaka mana da jini sai kuma nace ai kusan komi nasu shiyayi shi da kudin shi mukayi, kodan an ambace shi da sunan Baban su ohow"
Ihun sune ya dawo dani daga duniyar tunani.
Murna suke ga Kawu Sani muka gaisa.
Yace su tafi su tafi suna murna yau ko ban kwana basuyiman.
Lallai son da sukema Yarima yayi yawa har sun manta da basuyiman sallama saboda doki.
Inna ta dafani tace;"mikike tunani haka?"
Nace;"bakomi Inna"
Tace;"kode dan kinga kalar son da sukema Yarima ne? Nima nayi mamaki yadda idon su duk ya rufe kinsan wani Allah yana hada jinisu tosu tun suna jarirai Allah ya hada nasu yanzu idan suka ga Yarima nasan hankalin su zai kwanta"
Murmushi nayi ina kallon yatsuna ni kaina ba suba na kasa gane kallar kaunar da nike mashi.
♦♦♦♦♦♦♦♦
A airport din Bauchi suna sabka waje ya cika Security basu bari a isa inda Anuwar yake.
Su Farhana mutane sun hada sun hango Yariman saboda yadda wajen ya cika.
Sai tsalle take amman ta kasa ga takalman ta masu tsini, Sani na rike da ita ta fizge ta fara bi ta kalkashin mutane.
Sani na Kiran ta amman saida ta Isa tana isa Anuwar na shiga mota.
Hawaye ne suka zubo mata saboda duk ta gurje har takata anyi.
Sani ya riketa yace muje gidan su yanzu.
Cikin sauri tabi bayan shi, sai kara boye hannunta da ta gurje take.
Suna isa gidan ma a cike yake.
Suna rike da hannun su ya nufi part din Mai martaba dan yasan yana nan.
A part din Maimartaba ba'a bari kowa ya shiga.
Anuwar suna shiga yace;"Mummy zan shiga ciki part din Ammie nasan ta ajeman fura"
Dad yace;"Amman ya kamata kaci wani Abu a nan"
Abie yace;"kasa a kawo mana nan"
Ya mike Hamrah tace;"Dad zanje nima"
Kama hannunta yayi suka fito.
Suna fitowa yaga Sani tsaye da Yara cikin rana, Security din dake tsaye bakin kofa yayima magana.
Sani na tsaye Security ya iso yace abarshi ya shigo part din.
Suka biyo bayan shi, suna kusa isowa ya kurama yaran ido gaban shi ya fadi saboda yadda yaga namijin baki daya kamar d'an shi, wani photo nashi ya tuna ranar da yafara hawa doki kamar photon haka yaga yaron.
Farhan da Farhana suka kalli juna Farhanaa ta fizge hannunta daga hannun Sani ta ruga a guje tayi inda Yarima...
Farhan ya biyota a guje yana cewa;"ki tsaya kibi a hankali baki iya tafiya da takalman nan ba, wannan abinba ba kasa bace, ki tsaya kada ki kafadi"
Haba ko kamin Farhan ya iso ita harta isa zata hau wasu mata kalen bene guda ukku dake tsakanin ta da Yarima kuma wajen daga gani zaiyi zulbi cikin azama da takalman ta masu tsini tayi wajen haba tana dariya tana kallon Yarima da yayi mutuwar tsaye ya kasa motsi aiko tayo baya jim ta fado bisa Farhan daya zo dakatar da ita.
Su duka sukayi baya suka saki kara suka gangaro suka fadi kasa.
Cikin zafin nama Anuwar ya saki Hamrah yayo kansu.
Kan Farhan ya bugu jini ke zuba.
Ya dagosu ya rumgume su bisa jikin shi yana jijjiga wa.
A hankali suka bude ido hawaye na bin fuskar su sukace;"Ba...ba"
Suka kalli juna sukayi murmushi suka duka suka rufe ido.
MARYAM D'ANKUDII {QURRAH}
*JARABTAR MU*
*Written by-Qurrah✍🏻*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Addu'a Yayin da Mutum ya juya a cikin kwanciyar Barci.*
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ الوَاحِدُ القَهَّارُ، رَبُّ السَّمَوَاتِ وَاْلأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا، الْعَزِيزُ الْغَفَّارُ.
La ilaha illal-lahul-wahidul-qahhar, rabbus-samawati wama baynahuma, al'azeezul-ghaffar".
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, makadaici, marinjaye, ubangijin sammai da kasa da abin da ke tsakaninsu, mabuwayi, mai yawan gafara.
DEDICATED TO.....MY SISTERS😘
Bissimillah Rahmanir Rahim
Page-73-74

[4/2, 8:10 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*
*Written by-Qurrah✍🏻*
Page-75-76

*Addu'ar wanda ya Razana a cikin barci, Da wanda Ya Kasa Barci.*
أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ غَضَبِهِ وَعِقَابِهِ، وَشَرِّ عِبَادِهِ وَمِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ وَأَنْ يَحْضُرُونَ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat min ghadabih,wa'iqabih, washarri 'ibadih, wamin hamazatish-shayateen, wa-an yahduroon.
Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga fushinsa, da ukubarsa, da sharrin bayinsa, da kuma wasuwasin shaidanu, da kuma kada su zo mini (a cikin al'amurana).
DEDICATED TO.....MY SISTERS😘
Bissimillah Rahmanir Rahim
Page-75-76
---------------Wata irin kara Anuwar yayi ya dauki Farhana dake saman Farhan.
Sani cikin azama ya dauki Farhan yabi Anuwar da yayi part din shi.
Hamrah ce tsaye tana kiran sunan Anuwar tana cewa;"Dad....Dad" amman da alama kojin ta baiyi ba.
Suna zuwa a bedroom dinshi na sama ya nufa, ya aje Farhana bisa gado yayi saurin juyowa ya amshi Farhan.
Ya kwantar dashi ya lalubi wayar shi.
Dr Ashraf ya kira yana aje wayar shi, cikin sauri ya dawo ya zukunna yana kallon su, Farhan ya jawo ya rungume a jikin shi yana goge mashi jinin dake a jikin shi.
Dr Ashraf ne ya shigo cikin sauri.
Anuwar ya mike Dr Ashraf ganin yadda Anuwar ya rude jikin shi har kyarma yake hakan yasa Dr Ashraf yace yaba su waje.
Tsoki yayi ya fita a bakin kofar ya tsaya yana kaiwa da komowa.
Sani shine tsaye yake yana mamakin yadda Anuwar ya rude shida keda halin ko in kula da mutun.
Ganin yadda hadaden yadin jikin shi Milk color duk ya baci da jini gashi ya kasa natsuwa.
Mamaki abin yake duk son da yake ma diyar shi guda daya tak da Allah ya bashi amman tana kuka tana kiran shi da alama ma rudewa tasa baiji ba.
Dr Ashraf ya fito Anuwar bai tsaya yaji bayani ba yayi ciki da sauri.
Dr Ashraf ya kalli Sani yace;"yaran sun bugu amman na masu abinda ya kamata na masu allurar bacci sai dare zasu tashi nayi hakan dan su samu hutu"
Sani yace;"Mun gode likita Allah ya saka da Alkhairi"
Yana shiga ya iske Anuwar ya azasu bisa jikin shi suna bacci yana shafa kansu.
Ya kalli Sani yace;"Bana bukatar kowa inason hutu"
Sani ya juya ya fita cikin sauri.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Zaune nike dalibai na mani tambaya amman hankali na wajen Yara na da basu dawo ba, ban iya tambayar Inna daman Yaya Sani yace zasu dade gashi yau tambayar sunyi yawa.
Shiru nayi ina jin dadin tambayar sun kare chan naji wata tace;"Malama idan zaka rama azumi na farillah zakayi ranko kenan ba dole sai kayi shi a jere ba koko dole a jere zakayi?"
Na daga Kai na kalleta nace;"Mafi yawan cin Mallamai sun tafi akan cewa ba dole bane sai kayi shi a jere ba, saboda fadin Allah(SWT):
Wanda ya kasan ce daga cikin ku bashida lafiya ko a halin na tafiya to sai ya biya adadin a cikin wasu kwanuka na dabam.
Haka an ruwaito hadisi daga Abdullahi binu Umar(RTA)
Manzon Allah (SWA)yace;
"Wanda yake da ramuwa na azumi idan yaso yayi su a jere idan yaso yayi su a rarrabe"
Allah shine masani akan komi.
Zan mike kenan wata ta jefo tambaya na daure na maida hankalina wajen ta tace;"Malama mijina zai iya kusantata bayan jinin haila na ya dauke amman banyi wankaba?"
Nace;"Mallamai sun yi maganganu ukku karkashin wannan mas'alar kamar haka:
1-Imamu Malik da Imamu shafi'i da mafi yawan Mallamai(Allah ya musu Rahama) sun tafi a kan baya halatta yayin da jinin hailar ya dauke ya kusanci iyalin shi har sai tayi wanka Daga cikin dalilan su fadin Allah (SWT):
Kuma kar ku kusan cesu har sai sunyi tsarki idan sunyi wanka sai kuje musu daga inda Allah ya umurce ku.
Nace;"maganar na tsayi gobe zan ida maki insha Allah"
Nayi addu'ar tashi nayi daki Ina zuwa na fada saman gado rashin dawowar su ta dameni ina tsoron kada suce a chan zasu zauna ko Farhana ta bata a burni dan naga garin da girma ga Farhana da son yawo.
Inna ta fahimci halin da nake ciki tace;"kada kidamu suna tare da Sani kila sai bayan Isha'i zasu dawo dan wani bi sai lokacin yake dawowa ballai yau da sukeda baki a gidan"
Nayi murmushi bance komi ba saboda kunya danaji
Zama tayi kusa dani tace;"d'azun munyi maganar ki Sani"
Nan tafadaman yadda sukayi saboda batasan naji ba.
Tace;"kifadaman minene ra'ayin ki zama haka baiyi "
Na dukar da kai nace;"Inna banida zabi sai naku kun mani komi a rayuwa zaku iya iko a kaina"
Inna tace;"ba haka bane yanzu matsayin jawara kike kinada yan ci akan abinda kikeso ko mu iyayen ki addini ya baki dama"
Shiru nayi hawaye suka cikaman ido.
Da fadi tayi tace;"Sai kinyi hakuri a rayuwa sai kiga kinso abu ba Alkhairi bane rayuwar mutum kiyi addu'a Allah ya fitar maki da wanda zuciyar ki keso idan ba alkhairi bane idan kuma alkhairi ne Allah ya kawo maki mafita da wuri"
Saurin kallon Inna nayi ya akayi tasan inason wani?
Kamar tasan abinda nike tunani tace cikin murmushi;"Nanah kina matukar son Yarima haka yaran ki abin na daure man kai sosai, zakiyi mamaki ya akayi nasani ko? nasan haka tun shekarun baya tun yara suna kananu, lokacin da Sani yazo yace matar Yarima zata zo a bayyane kika bayyana kishin ki a lokacin nayi mamaki amman daga baya saina bar mamaki saboda shi So babu inda bai fadawa shiyasa ko wannan maganar taki naji Dadi da Sani yace a dagata zuwa su Yarima su koma addu'a yanzu ita ta rage maki"
Ajiyar zuciya nayi na kasa kallon Inna saboda kunya ashe daman tasan sirrin zuciya ta.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Baici komi ba tunda suka iso yana nan yana gadin su su farka gashi sai bacci suke hankali kwance, rufe wayar shi yayi domin baison damuwa, duk sallolin shi anan yayi su.
Yana gama magriba ya taso yazo bisa gadon ya zauna yana kallon na mijin da ke bacci ya tsun hannun shi ya kallah irin nashi ga fuskar su iri daya hatta jikin su, yaron karkarfane kamar mahaifin sa shiba ramamme ba shiba mai kiba ba haka yake, yarinyar ya maida kallon shi wajenta komi nata kalar na MANAL runtse ido yayi ya bude ya rasa mike damun shi.
Gyara mata gashin kanta yake a hankali saboda kada ta tashi.
A hankali ta bude ido suka hada ido murmushi tayi, shima murmushi yayi yun kurin tashi take cikin sauri ya kamata ya zaunar da ita.
Kallon shi tayi tace;"Ba..ba"
Murmushi yayi yana kara gyara mata gashin ta da ya zubo gefen fuskarta.
Farhan ne ya fara motsi su duka suka maida kallon su wajen shi.
Shima bude ido yayi a hankali yana kallon saman dakin kana ya fara kallon dakin.
Farhana tace;"Yaya Farhan kaga Baban mu, Yau muma mun samu Baba munada Baba su Hamisu dasu Indo su Binta bazasu kara mana goriba kalli ka gani Baban mu yafi nasu kyau"
Mamakin magan ganunta yake yarinyar yadda take maganar duk ta rudashi irin maganar MANAL komi nata kallar na MANAL.
Jin an taboshi yasa ya katse tunanin da yake yayi saurin kallon su.
Rike mashi hannu tayi tace;"Dan Allah Baba kada ka maidamu gidan su Inna Yau munaso mu kwana da Baban mu muma, kuma ka dauko Maman mu mu dinga kwana a tare daku a daki daya haka Baban su Hamisu keyi masu, sai sunyi Bacci suke kaisu daki dan Allah ka dauko Ummien mu"
Ta ida maganar tana hawaye cikin sauri yasa hannu yana goge mata tace;"to kayiman alkawarin zaka maido Ummien mu da Innar mu"
Yadda tayi maganar ji yayi kamar mafarki yake gani yake kamar MANAL ce lokacin da take ce mashi yayi mata alkawarin zai zama mai zane saboda ya zanata.
Kara rike mashi hannu tayi cikin sauri yace;"zan maidota insha Allah, yanzu ku taso ku wanke baki muci abinci"
Tashi sukayi suna kallon dakin sun saki baki sun kasa tafiya.
Hannun suya rike su duka Farhana tace;"Baba ina takalma na masu tsini na Sallah ne kuma sukade gareni masu tsini suma saida nayi kuka aka siyaman, sannan Ummie tace idan na batar bazata sake siyaman ba"
Zu kunnawa yayi dai-dai tsawonta yace;"zan siya maki da yawa gyale Ummie dena kuka kinji"
Tare suka sabko kasa waya ya kira Sani sai gashi Farhana tace;"Kawu a dauko mana kayan mu ni bazan koma ba gaskiya"
Dariya yayi yace;"Aiko saina fadama Inna ince bakison zaman gidan ta"
Tace;"ai bazan zauna anan ba saida Inna"
Dariya yayi ya zuba masu abinci ya tura a gaban su ya sakama Yarima ya zuba mashi fura ya aje a gefe.
Farhana ta kalli Sani tace;"Kawu kaga gidan Baban mu duk yafi gidan su Indo kyau kuma Babana yafi nasu Indo kyau"
Dariya yayi yace;"Farhana sarkin yan surutu to bari kiji Baban naki baison surutu, kuma Ummien tace idan za'aci abinci ba'a magana"
Zaro ido tayi tace;"baison surutu kamar Yaya Farhan shima wayyo ni Farhana nayi shiru kada ya koremu, Baba idan na kara surutu ka dinke man baki daman Ummie tace sai an din keshi kozasu samu sauki na"
Dariya ta bashi yayi murmushi yace;"to kici abincin kana kinji"
Ya kalli Sani yace;"gobe zakaje Katsina namanta tunda muka iso ban fada maka ba, wajen Baban yarinyar nan idan kaje zamuyi waya, jirgi zakabi zuwa Katsina idan kaje zansa a dauke ka kutafi garin"
Sani yace;"to shikenan baida matsala sai nayi sabko ai, Allah ya kara nasara"
Bayan sun gama su Farhana an koshi ta kalli Baban ta da zai kai fura a baki tace;"kullun Ummien mu keyin fura amman Yau Inna tayi ta"
Murmushi yayi baison surutu Amman na yarinyar bai damun shi.
Sani yace;"tashi mutafi gida hakanan nasan Inna nacen na jiran ku"
Anuwar yace;"kace ma Inna tabar su anan har kadawo daga Katsina jibi kenan saisu koma"
Sani yace;"to shikenan Allah ya kara girma da nasara muna godiya sosai"
Jin haka Farhana sai murna take.
Har Sani ya kusa fita tace;"Kawu kace Inna ta saiman tukunyar kasata da takalmi mai tsini kada ta manta zata ba Kawu Salisu ya siyo a kasuwa hadda diyar bebi"
Su duka saida sukayi dariya.
Kamasu yayi suka mike toilet dinshi ya shiga dasu.
Yau da kanshi yayi masu kwanta yabasu tuwol suka daura yace su jira
Suna nan zaune suna kallon daki sai gashi da kayan bacci sai kamshi suke.
Farhana tace;"Baba kaima kanason kamshi Ummien ma tanason kamshi sosai"
Murmushi yayi ya saka Mata kayan ya sakama Farhan dake tsaye.
Bisa gado yace suje su kwanta.
Bisa gado daya suka kwanta yaja masu bargo.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Tun ina jiran Yaya Sani har abin ya fara ban tsoro Innama haka.
Wayarta da Yaya Sani ya siya mata tace na dauko na kira shi na dauko na kira na mika mata.
Ganin tana murmushi yasa hankali na ya kwanta sun dade kana sukayi sallama kallo na tayi fuskarta dauke da murmushi tace;
"Kinji yadda yara sukayi da Sani wai basu dawowa saide mu koma tare tun safe suna tare da Yarima"
Nan Inna ke fadaman abinda Sani ya fada mata nima dariya nayi.
Hankali na ya dan kwanta amman nayi kewar su.
Inna tace;"zamu sha kewa saboda gobe yace sabko zaiyi Yarima ya aike shi wai bazasu dawo ba sai jibi"
Shiru nayi ina tunanin taya zan barsu har jibi.
Haka nayi bacci cikin kewar yara na.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Koda asuba tayi suna bisa kirjin shi suna bacci.
Yana mikewa Farhan ya mike Anuwar yace;"Farhan koma kayi bacci Mana"
Farhan yace;"lokacin Sallah yayi Baba"
Shiru Anuwar yayi ya shiga toilet yayi alwala ya kama Farhan ya nuna mashi inda ake alwala lafiya kalau yayi alwala.
A tare sukayi Sallar yaron yana yin komi cikin natsuwa Yarima kallon shi kawai yake.
Suna gama Farhana ta tashi tace;"Yaya zanyi Sallah"
Abin mamaki ya bashi hadda ita da yake gani bataji.
Farhan ya gaida Anuwar ya mike ya kamo Farhana.
Al-qura'ani Anuwar ya dauko yana karantawa zuba mashi ido sukayi.
Farhana tace;"Baba mun iya karatu Ummie ta koya mana amman Yaya ya fini iyawa sosai"
Kallon su yayi yace;"Farhan yiman karatu naji"
Nan fa ya farajin karatu cikin kira'a Mai dadi ga muryar yaron akwai dadi.
Ya dade yanayi kana Anuwar yace;"duk wa ya koya maka wannan karatun haka har ka iya"
Farhanaa tace;"Ummie mana ita ke hanamu bacci bayan asuba"
Haka sukayi mashi karatu har safiya ta waye tun da safe aka aje masu Breakfast yanzu ma sukayi wanka ya saka masu kaya masu kyau Farhana sai murna take tana kara kallon kayan.
Wajen karfe goma yace;"su zauna zaije ya dawo suka zauna ya kunna masu tv"
A part din Ammie ya zauna suna gaisawa tace;"ai jiya Hamrah Tasha kuka wai kafison wasu yara akanta tana maka gama baka waigo ba"
Murmushi yayi yace;"tana Ina nayi kewarta tazo na bada hakuri"
Yana tare da Hamrah part din Ammie sun gaisa da Kulsoom yanata fira da Hamrah yana bata hakuri.
Ammie tace;"Nina ce Kulsoom tabari sai angama Walida saita ta koma part dinku dan nasan yanzu idan takoma baka barin ta fitowa dan ba kunya ta ishekaba"
Murmushi kawai yayi
Sai wajen karfe daya yace mata zai fita sai dare zai dawo haka suka rabu.
Part dinshi ya dawo ya iske su Farhana anata kallo ko motsin kirki batayi ta kurama TV ido murmushi yayi ya iso.
Wayar shi tayi kara ya duba cikin aljihun ya dauka yace;"to shikenan ku taho a tare zuwa goben jirgin safe ne da wuri zaku iso sai kunzo"
Ya maida wayar yana kallon su sai farin ciki suke.
Lokacin Sallah yayi a tare sukayi Sallah furar jiya ce ya ida shanye wa su kuma ya zuba masu abinci.
Haka suka yini Farhana sai surutu take zuba yana mata dariya.
Yauma a daki guda suka kwana.
Safiya nayi kamar jiya haka suka tashi.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Yau da dokin dawowar su na tashi shiyasa da wuri nayi fura na fidda ta gidan Sarki Yaya Salisu ne yazo ya dauka.
Nayi wanka na koma na zauna na kagara su dawo gani nake kamar sunyi wata basu nan.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Yau ana kawo fura aka kawo mashi ya zuba ya sha gaban shine ya Fadi.
Ganin ya tsaya da Shan furar yana kallon furar yasa Farhana dake bisa cinyar shi tace;
"Baba furar da dadi ne Ummie na keyin ta kullun ai nafada maka da shekaran jiya ne kawai Inna tayi, toya kaji furar da dadi"
Shiru yayi ya aje furar yana karema Farhana da Farhan kallo gaban shine ke faduwa.
Wayar shi tayi kara ya dauka yace;"Masha Allah ka kaishi ma sabki ya huta ganinan zuwa"
Ya mike cikin sauri yayi part din da Liman yake.
Farhana da suke zaune ta mike zata fita Farhan yace;"Farhan yace ba an hanaki fita ba"
Murguda baki tayi tayi waje daman dan taga kofa a bude ne.
Farhan ya mike ya biyota chan ya hangota tana tsaye gaban wata yarinya ya nufi wajen.
Yana zuwa yaga yarinyar tasa hannu biyu ta inziga Farhanaa ta Fadi.
Cikin zafin nama shima ya ingiza yarinyar ta saki kara ta kiran;"Mom..Mom"
Kulsoom ce tafito tana ganin abinda ya faru Hamrah a kasa tana kuka Kuma ta gurje cikin sauri ta iso.
Tace;"Kai waye da zaka shigo gidan nan ka dakan man diya"
Mari ta kai mashi ta kara mashi a dayen ban garen amman ko gezo baiyi kamar bashi ta maraba.
Farhana ya mikar tsaye dake kwance a kasa abin mamaki ya bata.
Su Mummy da Ammie da sukaji kukan Hamrah suka fito Suma mamaki suke
Kulsoom tace;"ka bata hakuri kasan ko wacece ka ture harta ji rauni babu wanda ya taba mata fada ballai ya tureta hartaji rauni dan haka kabata hakuri"
Ta ida maganar cikin daga murya yaron ko motsi baiyi ba.
Ammie tace;"Ina akasamu wanna yaron mai kalar zuciyar Yarima rabona da naga wannan Izzar tun Yarima yana Dan shekara shidda a duniya jinin waye wannan yaron ina aka same shi"
Farhana tace;"mu diyan Yarima ne"
Mummy da Ammie cikin sauri suka karaso Mummy ta iso gaban Farhana ta duka dai-dai tsawonta tace;"Innalillahi!! MANAL ce aka kara haihuwa ko kuma nima na rude kamar Anuu"
Ammie dake gaban Farhan tace;"kila de 'ya 'yan aljanu ne nima Yarima ne sak a gabana lokacin da yake yaro"
Cikin sauri ta budi security din dake tsaye bakin kofa tace;"kayi maza ka kira su Mai martaba kiran gaggawa"
MARYAM D'ANKUDII {QURRAH}
[4/4, 8:26 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*
*Written by-Qurrah✍🏻*
Page-77-78

*Addu'ar Da Wanda Ya yi Mafarki mara kyau zaiyi.*
أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ ثَلاَثٍ مَرَّاتٍ.
a'uzu bi-l-lahi mina shaytani r-rajeem (3)
Wanda ya ga abu mummuna a mafarki, to sai ya yi wadannan abubuwan:-
- Ya yi tofi ta gefen hagunsa sau uku.
- Ya nemi tsarin Allah daga shaidan da kuma sharrin abin da ya gani, sau uku.
- Kada ya gaya wa kowa wannan mafarkin.
- Ya juya daga kwibin da ya kasance yana kwance a kansa.
Idan ya so, ya iya tashi ya yi sallah.
DEDICATED TO.....MY SISTERS😘
Bissimillah Rahmanir Rahim
Page-77-78
---------------Farhanaa tace;"Wai Yaya mu 'ya 'yan aljanu ne?"
Kallon ta yayi cikin azama ya damki hannun ta yace da karfi;"mu gudu"
Aiko cikin sauri Farhana ta bishi da Ammie da Mummy suka tsaya kallon su duk sun rikice cikin sauri Kulsoom ta juya tayi wajen Security din dake bakin get din shigowa part din Ammie.
Suna ganinta a guje sukayo wajen ta cikin sauri haka yaba su Farhana damar fita.
Cikin tsawa tace;"ku kamo yaran da suka fita yanzu-yanzu kada abari subar gidan nan akamo man su"
Suka juya sukabi su Farhana a guje.
Anuwar bayan sun gaisa da Liman yasa aka kawo mashi abinci.
Komawa yayi ya zauna yana jiran ya gama.
Liman ya kalli Sani yace;"bazan ciba saboda nasan Fura na nan na jira yazo mugama abinda zamuyi mu tafi chan"
Sani yace;"Baza ai hakaba nan gidan aka baka masabki Yarima bazai bari ka tafi bakaci komi ba dan haka bari na kira wayar Inna a aiko maka yanzu"
Liman yayi murmushi yace;"to shikenan yazo muyi kaga kamin a kawo man mun gama tunda yace ba'a daukar lokaci"
Sani ya juya yaje inda Anuwar yake zaune ya fada masu yadda sukayi.
Anuwar ya mike ya isa inda Liman yake.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Ina zaune aka kira wayar Inna na mika mata.
Bayan ta aje tace;"tashi Nana kiyi maza ki dauko mayafi yau babban bako garemu a gidan Sarki, ki kai mashi fura da kin fita zaki samu abin hawa"
Na mike cikin sauri nace;"to Inna ai a shirye nake"
Saboda yarana yasa nace haka nayi kewar su sosai inaso na dauko su.
Tsaye nayi cikin daki Ina murmushi yau zanga Yarima kenan, wani abu na tuna cikin sauri nayi wajen kayana na dauko zoben nan ina murmushi nace ya dace da wannan babu abinda zan saka mashi dashi amman kyauta koya take tanada amfani, shekara kusan biyar kenan inason nayi mashi kyau murmushi nayi na saka shi a Babban d'an ya tsana saboda idan Inna tagani hanani zatayi.
Inna ta zuba fura na mike tsaye na saka Hijab dina tabani kudin mota na fita.
Ina fita nayi bakin titi duk sainaji daban saboda ban fita ko kadan.
Ina bakin titi rike da sabuwar kwaryar Inna a hannu na saiga mai adai-daita sahu yazo.
Yana zuwa na fadi inda zani muka tafi.
Kara kallon garin nike duk ya chanza rabona da shiga Bauchi tun da nabar ta.
♦♦♦♦♦♦♦♦
Farhan yaja Farhana suka boye bayan wata mota dake gefen wani daki, suna kallon yadda Security din wajen kebin dogon titin gidan da kallo babu yara sai lekawa suke wurare .
Farhana sai zufa take tace;"Yaya dan Allah kayi hakuri nasaka wahala wallahi haka nace mata muga diyar hannunta ta araman na taba shine tace wai Allah ya kyau ta taba yarinyar kazama kamar ni diyarta, shine nace niba kazama bace shine ta turani na fadi, wallahi ba laifina bane"
Jin motsin mutum yasa sukayi shiru suka kara labewa.
Anuwar na zaune yana fada mashi yadda fuskar ta take.
Saboda shape din fuskar su guda da MANAL hakan yasa yake zanen shi cikin kwanciyar hankali.
Yadda shape din girarta take ta kusa hadewa saboda cika da tayi da idanunta girman su dai-dai dana MANAL sun dan ciko su basuyi yawa ba su basuyi kadan ba sai dogon hancin ta.
Sani na tsaye yana kallon ikon Allah.
Anuwar na gama zanawa ya dauki photon yana kallo rude ba dai-dai yayi zanen ba kusan kamar su guda da Manal dan Manal dinshi na yarinya wannan na babba.
Sani yace;"amman wannan kamar Nanar Inna maman yan biyu"
Cikin sauri Anuwar ya kalle shi.
Jin shiru Security bai dawo ba yasa su Mummy suka fito dai-dai lokacin da Abie da Daddy suka iso nan su Mummy suka basu labari kuma yara sun bace.
Daddy yace;"ayi sauri a bincike ko ina na gidan a binciko su" dan danan aka fara neman yara Daddy yace yaron mayyar yarinyar nan ne.
Suna zukunne kusa da motar da aka dauko su Sani daga airport gefen dakin dasu Anuwar suke ciki.
Hannun farnana daya fito daya daga cikin security din ya taka.
Wata kara ta saki wadda saida Farhan ya rude yayi zumbur yayi bisa titin gidan saboda rudewa.
Security din dake tsaye suka bishi yayi hanyar babban get din gidan.
Dai-dai lokacin da Nana ta shigo get din ai yana hangota yayi wajen ta yana ihu, itama hangen shi tayi ana binshi.
Mamaki take lafiya ko laifi yayi cikin sauri tayi wajen.
Yana zuwa inda take yayi bayan ta ya boye yana kiran sunan Farhana.
Cikin tashin hankali tace;"ka fadaman miyasamu Farhana laifi tayi?"
Daga kai yayi ya jikin shi sai kyarma yake.
Security din take tsaye gabana suka zagaya suka fizgo Farhan dake bayana wani irin ihu yake nabi na rude lokaci guda na fara Kuka ina binsu ina cewa kuban d'ana da alama basujin abinda nike cewa.
Hanko Farhana nayi tana ihu a hannun wani nayi wajen a guje kamar ma haukaciya ina isa ta ganni ta fara ihu tana cewa;"Ummie zasu kashe mu Ummie wai sun ce mu yaran Aljanune Ummie kada su tafi dani"
Rudewa nayi na hango Farhan sunyi nisa.
Wani irin Ihu nayi nayo wajen Farhana dake mikoman hannu.
Anuwar dake tsaye karar TV yasa basajin komi chan yaji irin ihun daya tabaji.
Liman yayi shiru Sani yace;"kamar muryar Nana"
Cikin sauri suka fito dai-dai lokacin da nasaki kwaryar hannu nayi wajen Security ina kuka Ina son ban bare Farhana a hannun shi.
Cikin tsawa Anuwar yayi ma Securityn magana ya saki Farhana bata tsaya kallon suwaye ba.
Ta kama hannun Farhana tabi hanyar da aka dauki Farhan a guje.
Dai-dai lokacin da ta hangi mutane tsaye an aje Farhan a gaban su.
Chan ta nufa a guje rike da Farhana.
Tana zuwa ta iske an saka Farhan a gaba kowa na kallo.
Tana isa wajen taji an kwala mata kira tayi saurin juyawa saboda muryar da taji.
Tana waigowa taga Yaya Sani da Baban ta da wani matashi daya kura mata ido.
Kuka take sosai kamar ranta zai fita ta isa inda suke.
Bakin ta na kyarma tace;"Ba...ba"
Yace;"Na'am Na...na"
Wani irin ihu tayi wadda hakan yasa duk mutanen dake wajen hankali su ya dawo kanta.
A gefen Anuwar take hakan yasa tayi baya-baya zata fadi ta fada a bisa kirjin shi
Rumgume ta yayi ya zugunna kasa tana bisa jikin shi, Daddy da Abie dasu Mummy da Ammie dasu Kulsoom sukayo wajen.
Kulsoom ta kalli mace a bisa jikin Anuwar yana girgiza ta.
Farhana da Farhan sukayo kanta suna cewa;"Ummie kitashi kada su tafi damu zasu cutar damu, Ummie sunce mu yaran Yarima bane Ummie kitashi mu koma wajen Inna tunda bamu da Baba, mun hakura Ummie bazamu kara neman Baban mu ba"
Jin kalaman su yasa zuciyar shi tsinkewa cikin azama ya d'ago mata hannu domin yaji tana da rai, hakan yaba duk wanda ke wajen damar kallon zoben dake d'an yatsan ta Babba.

0 comments:
Post a Comment