Suna shiga falon tashiga kwalama lami kira wacce ke kichen tafito Arude tana Fadin"Hajiya lafiya kuwa naji kiran ne daga Sama" Ummi takalleta daidai lokacin da Mu"azzam ke zama kan kujera hannuwansa duka biyu dafe dakai tace"Ina lafiya son ne yadawo gida ba lafiya"Dafe kirji lami tayi tana Fadin"Munshiga uku hajiya yallaban? Tafada duka idanunta waje.
Ni tara na shiga bama uku ba, lami,abinci zaki Taimakon dashi yaci na bashi mgani"Tafada kamar zatayi kuka da sauri lami takoma da baya tana Fadin"Yanzu kuwa hajiya..Yallabai sannu,Allah kenan yanzu yanzu da lafiyanka anjuma kuma ta kubcemaka"Tana wannan mganar tafada kichen din karime da Uwani na tambayanta lafiya takwashe komai tafada musu suma din dafe kirji sukayi idanuwa waje kafin su cikin rawan jiki su fice zuwa falon.
Koda sukaje sun iske Sani maigadi da Falalu durkushe sunatama yallabai sannu wanda ke kwance kan cinyar Ummi tana shafa kansa tana jeramai addu"o"i tana tofamai bisa kai,kamar zatai kuka kokuma ciwon yadawo jikinta nan su karime ma sukabi ayari suka zube suna jeramai sannu wanda ke amsamusu dakai kawai ammh a zahirin gaskiya jiyake dama shine su domin su basu da wata damuwar kamar yadda yake ciki,lafiyansa kalau kawai yarasa mezaicema Ummi ne, wanda hankalinta zai kwanta,to gashi bai tsiraba shiya manta yadda in yana ciwo Ummi haka zata sakashi gaba tana kuka bata sukuni sai ya samu lafiya..To yaudin ma hakane yafaru ita tadinga bashi abinci abaki Wanda yakeji kamar yana cin madaci ammh hakanan yaita Turawa yana gama ci dama tama Family doctor dinsu waya Dr Abduljabbar wanda yace yana hanya.
Koda Dr Abduljabar yazo yaduba mu'azzam kawai yace Rashin Samun hutu ne alluran barci yamai yace ya kwanta yasamu barci na good 5 hours yana tashi komai zai koma Normal,ai Ummi ta dakanta ta rikeshi har dakinta ta ciremai,takalmi da Socks taciremai caot din,ta kwantar dashi bisa gadonta tana Fadin"Oya sleep kaji dai Abunda Dr yace ko'"Yagyada mata kai yayi, sai tacigaba da cewa'Bani son katashi sai na tasheka da kaina so Rest kaji son"Tafada tana shafa kanshi.
Kallonta yakeyi kafin yariko hannunta yace"Nagode Ummi na Nagode"Yafada idanunsa sun kawo kwallah kafin yayima hannun kiss mirmishi tayi tamaidamai kiss din bisa goshi tana Fadin"Iz my duty son..Love u so much"Tafada tana kara kissing dinsa bisa goshinsa shikuma lokacin alluran tafara aiki idanunsa na lumshewa blanket tarufamai zuwa kwankwasonsa kafin ta fice bayan Ta rufomai kofa..Ajiyar zuciya ya sauke yanajin kamar ya fashe da kuka..Yazaiyi Baffa shettima zai watsama kasa a ido ko Ummi wacce ta sadaukar da fatincikinta akansh,ta sadaukar da dukkan jin dadin Rayuwarta zuwa gareshi,yasan cewa Ummi bazatataba fahimtarsa ba kilama tayi Fushi dashi Fushi na har abada..Da wannan Tunanin barci yayi awon gaba dashi.
""""Saida yashafe wajen awa shidda yana barci kafin yatashi shima din kiran sallar mangarib ne yataadashi wanda daman haka yake komai Nauyin barci wlh ana fara kiran sallah Allah ke tayar dashi..daidai lokacin daya mike Ummi ta shigo dakin Ganinsa zaune yasa Takarisa tana Fadin" Nasan daman yanzu zaka tashi shiyasa na shigo"Tafada tana zama kusa dashi wuyansa tataba zuwa kansa tana Fadin"Ya jikin hop u feel better Now, son?"Tafada murya cikin Damuwa lumshe ido yayi kafin ya bude cikin sansanyar murya yace"Naji Sauki Ummi daman Ciwon kai ne,fa kawai"Yafada yana kallonta.
Shiiiiiii.."Tace hannunta bisa bakinshi kafin tace"Ciwon kanka son Awurina ba kawai bane,bakasan tashin hankalin dana ke shiga bane duk sa"ilin dana ganka ba cikin walwalwarka ba"Tafada tana shafa fuskarsa riko hannuwanta yayi yana Fadin"Duk wanda yasamu Uwa kamar tawa Uwar hakika shi mai Sa"a ne kamar yadda nasan Nimai Sa"ane Nasamun ki Amtsayin mahaifiyata Ummi na"Yafada yana kwantar da kansa bisa kafadanta,Hannu tasanya tana shafa kanshi mirmishi take kawai ammh takasa furta komai sai shine keta maimata "ina sonki Ummi na".
Har dare yayi haka Ummi keta hidima da mu"azzam ko abinci takasaci wayyo baiwar Allah gabadaya tsausayinta yacika Mu"azzam shiyasa yafaramata barcin karya donta kyalesa yaje dakinsa ya kwanta..Ammh ina Ummi bata yarda ba Dakinta takara maidashi ta, kwantar dashi kamar wani jariri bayan ta Tofeshi da addu"a Kallonta kawai Mu"azzam keyi baida tacewa gashikuma soyake ya kebe yakira Shureim yafadamai komai ke faruwa domin kanshi fa ya kulle ya Rasa mafita.
**** ***** *******
kwana Uku mu"azzam yayi Ummi bata barinsa Fita ko"ina wai sai yagama warwarewa Ranar na ukun da kuzarinsa yatashi shima din dakyar tabari yatafi aiki sai daya tabbatarmata da cewa ya warke kuma zai kula da kanshi..Suna Fita yacema Ushe kaduna zasu sai da Shureim ya gansa kwatsam kiransa kawai yayi yacemai yana ina ?yace yana cikin asibiti "
Kallo Farko Shureim yayima Mu"azzam yasan ba lafiya yana tsakar duba patient ne ammh dole ya yanke ya turama wani Likitansu yadda kai kawai mu"azzam yayi bisa kafadansa yana fadin"Yazanyi dan"uwa ina cikin damuwa kirjina yamin Nauyi bansa yazanyi ba na shiga tsaka mai wuya"Yafada kamar zai fashe da kuka bubbuga bayansa Shureim yakeyi baiyi mgana ba sai zuwa chan yadago kujera yaja masa ya zauna karamin Fridge din dake office din yabude ya dauko Ruwa kofunan dake saman gun ajere ,yadau daya ya tsiyayamai Ruwa ya mikamai ba musu ya karba yasha Yakara mikamai alamar yakarama ba musu Dr Shureim ya zubamai sai dayakusa shanye rabi kana yadagamai hannu maida komai yayi ma"adanarsa kafin yakoma ya zauna yana Fuskartarsa kafin ma Dr Shureim yayi mgana Mu"azzam ya rigasa da cewa.
"Sun saka Ranar Dauren Auren fa"Yafada cikin wani yanayi zaro ido Dr Shureim yayi kafin yace"Kai don Allah wasa ko gaske"Wani kallo Mu"azzam yamai kafin yace"Kaga alamar wasa atare dani wlh da gaske nake jiya baffa ke fadamun nan Da two week nazo adaura Aure"Dafe kai Dr Shureim yayi yana Fadin"Innalillahi Dan"uwa Abu fa ya rikice Yazamuyi Da Ummi shine babban problem din
"kallonsa kawai mu"azzam yayi idanunsa sunyi jawur yace"Shine nakasa nemo mafita.juz tell me ya zanyi.ni kamar ma na gudu daga kasar gabadaya wlh"yafada yana dafe kansa saurin girgixa kai Dr Shureim yayi kafin yace"No bashine solution ba,yanzu Abunda za"ayi kakoma gida gobe zanzo sai mutaru mu fadama Ummi ko ya kagani"zare ido mu"azzam yayi kafin yace"Wata Ummi kaga mallam nemo wata hanya dai...Kana tsammanin Ummi taji wannan lbrin bata Yanke jiki ta fadi ba kasan ko yadda Ummi tadauki gaba mai tsanani dasu Baffa"Yafada cikin Nuna Abun ya ishesa.
Dafe kai Dr Shureim yayi kafin yace"Hajiya fa bazatayi wani Abu akai ba"dagowa yayi kafin yace"Hajiyarmu.."gyada masa kai Dr shureim yayi Dan ihu Mu"azzam yayi kafin yace"Yes gud..Ka kawo shawara kafadama hajiyar tamu yadda kukayi sai naji..Ammh wlh fadama Ummi ba mafita bane dan"uwa kafi kowa sanin Ummi kai fi daya ce"
"insha Allah komai zai Tafi daidai karka damu" shureim yafada Mikewa Mu"azzam yayi ya mikasa hannu sukayi musabaha yana fadin"Ina da wata shari"a Zan koma sai munyi waya"Damke hannunsa Dr yayi kafin yace"Kadaina damuwa plz dan"uwa anytin will be alright kaji"Gyada kai kawai yayi kafin ya fice a office din Ransa a jagule...
Koda Dr Shureim yakoma gida bai fadama hajiya ba sai da safe itakanta ta shiga rudu tadinga juya Abin Aranta kafin tace"Shureim akwai mtsala Suhaima tanajin dukkan mganata ammh akan Abunda yashafi zuru"ar moodu zuciyarta ta tsaure Abunda suka mata yasakarmata dafi mai zafi wanda mantashi sai anyi babban jihadi..Kai na ya kulle wlh Suhaima baza tataba yarda Mu"azzam ya auro diyar fadi ba bazata taba yarda ba"Tafada cikin tabbatarwa..Jikin Shureim yayi bala"in Sanyi rausayar dakai yayi kafin yace"Plz hajiya do Sometin ke kadai ce hop dinmu wlh"Kallonsa tayi kafin tace"baka son komai ba shiyasa ai shi mu"azzam din yasani shiyasa yakasa Fadamata,ammh kubar komai Ahannuna zuwa gobe in na yanke decision zan Nemeka"mirmishi yayi yace"yauwa barrister tink abount it nasan baki rasa mafita"Fulon kujera tamakamai Tana fadin"Ka maidani kakarka ko Shureim"Ficewa yayi yana fadin"Matsayinki na mutum uku ne uwa,uba,kaka kinga dole na dinga taba kowani barayi"Dahaka yafice yana dariya.
**** ***** ****** *****
*MAID*
Achan kuwa Tuni duk wani Shirye shirye ya kamkama Zahirah batasan komai ba itadai Bahna dinta yace ta tattaro kayanta zata koma gun yakura da zama murna kamar zai kasheta jiki na rawa ta hada ya dauketa yakaita gun yakura.itakuwa batare da tsayawa wasa ba ta shiga gyara yarta tata Zahirah yarinyace,shiyasa bata fahimci komai ba,ammh abun yana bata mamaki komai aka bata tasha wanka ma bada ruwan banza take ba hakama tsarki..Turaren tsugunno ko har tagaji dashi kuma Abunda yafi dauremata kai tadaina zuwa mkranta data tambayi baffa sai cemata yayi "Kada tadamu xata koma mkranta ammh ba anan garin ba"To miskilancinta yahanata kara magana..Uwa uba ga Nasihohin da yakura kullum dare take doramata kan tayi hakuri da duk Rayuwar data tsinci kanta karta bari a fahimci Rauninta, zahirah yarinyace miskila wacce mgana ba damunta yayi ko ta tambayi yakura amsa daya take bata"Mtsayinki ne zai karu yahna"daganan bata kara cemata komai Itakuma bakinta na mata Nauyin kara tambaya.
Ayayinda biki yarage Saura one week duk wanda ya kamata yaji sai yaji don Bukar ya shiryama Abun gayyah yayi sosai shida mahgana Wanda mutane dadama Sunyi mamakin wai Mu"azzam dan Suhaima wanda ba"arabu ta dadi ba za"a kuma kulla auratayyah wasu dadama sun kasa gasgassta abun wasu kuma so suke suji yadda wannan al"amari zai Faru Shikuwa Shettima ya dole kunnensa Ruf burinsa kadai yake Muradin cikawa.
•°•°•°•°•°•°••°•°•°•
""""Kokarin daura tie yake lokacin da wayar ta shigo masa Sai da gabansa yafadi dayaga, sunan BUKAR MAID Ya fito baro baro..Gabansa ya fadi har sai da wayar ya yanke yarasa Abunyi kafin ya nemo mafita wayar ta sake daukan kuwa..Cikin mutuwan jiki ya daga kiran kokafin yayi mgana yaji muryan Baffa na kwarara sallama cikin mutuwan jiki ya amsa bayan ya gaisheshi.
Baffa Shettima yace"Daman dalilin kira na karin Tuni ne Rana ita yau ne za"a daura Auren kada ka sha"afa don Allah kada kabani kunya dana"Yafada cikin karyewar murya Cikin daburcewa mu"azzam yace"Bazan baka kunya ba baffa ammh bazata tare ba ko? Saboda akwai shirye shiryen danake son gudanarwa"Bude bakin baffa sai cewa yayi "Kada kadamu da wannan Ai zahirah kanwarka ce..Babu abunda zaka wahalar da kanka ko dakin dakake kwana ka ijiyeta babu damuwa komai sai yazo daga baya..Ammh kamim alfarmar ana daura aure zaka taho da matarka nan"jikin Mu"azzam yadau rawa zufa tana yankomai yanaji baffa nata hello hello ammh kuma ya kasa mgana dakyar ya iya cewa"Shikenan Baffa Umarninka shine nawa...Allah ya kaimu'Yafada kamar zai saka ihu.
*MU"AZZAM....!* yaji muryan Ummi takirasa daga baya cikin muryan fushi da tsantsan bacin rai, a firgice ya waigo yana kallon Ummi wacce ke tsaye kikam akofar dakin nasa Fuskarta babu Annuri tana Fitar huci cikinn Fushi da bacin Rai...Ai Tuni mu"azzam yaji kansa na juyawa jikinsa yahau rawa babu Tamtama Ummi tagama jin komai yau karyansa takare.
Abunda baisani ba tun sanda yafara waya Ummi na tsaye awurin tagaji da jiransa yaxo suyi breakfast ne yasa ta biyo sawunsa hankalinsa yayi gabane shiyasa baiji karan bude kofarta ba dukkan Abunda yafada a kunnenta.
Takowa take cikin Fushi tana karisawa kusa dashi tace"Mu'azzam minaji kana fadi..Naji kana fadin in an daura aure matar bazata tare ba? kuma naji kana ambatan Baffa wani Baffan?'"Tafada cikin Tsawa tana zaremai ido jikinsa na rawa yaja baya yana Fadin"A"a Ummi tsaya kiji kada ki daga hankalinki don Allah"Tsareshi tayi ido wanda suka kada kafin tace"Zaka fadamin ko sai naci UBANKA YANZU ANAN"Tafada kamar zata dakesa.
Bai da Zabi illa zubewa dayayi agabanta yana fadin"Ki yafemin Ummi rashin gayaminkin dabanyi ba..Bani son Tashin hankalinki ne narasa mafita Ummi"Yafada kamar zaiyi kuka hannu tadagamai kafin tace"go to d point Mu"azzam wani Baffan kuma wata matar naji kana mgana akai"Tafada cikin Tsawa runtse ido yayi kafin yace"Zuwan danayi maiduguri baffa yakirani yana bani UMARNIN auren Diyar marigayiya Inna Fadi ta da rasu ta bar... " *TAS.."TAS..."TAS..* kakejin Karan tafika ta ko'ina haka Ummi ke zuba su bisa Fuskar mu"azzam Tana kuka take fadin
" IBRAHIM nizaka ci amana...Nizaka Tozarta to wlh baka isa ba, zoka Ficemin daga gida kaje bani bukatarka wlh na barma Shettima kai, daman Burinsa kenan..Zoka fice Ibrahim bani kaunar ganinka zo ka Ficemin.."
tafada cikin wani yanayi Kafin tajuya Tafara tafiya tana kuka jiri ne ya kwasheta kafin kace me ta zube kasa warwas kamar gawa cikin wani irin Rudewa Mu'azzam ya mike lokaci daya yana kwallah kara da fadin
*UMMI NA*..."yafada cikin Sauti wanda,duk wanda ke gidan sai da yaji wannan Sautin.
_*hohoho..Anzo gunfa janaf fans...Akwai badakala mai ban mamaki da tsausayi da Nadama..Kubiyoni ni zan warware muku ZARE DA ABAWA*_
*#TEAM ZAHIIRAH#* _Kutanadi Botiki na taran hawaye_😛
*#TEAM MU"AZZAM#* _kuma ku Shirya shiga cikin kuncin rayuwa,garari tareda fadawa tarko mai wuyar fita_😂
*#TEAM UMMI#* _Ku kuma ku daura damarar daukan Fansa,ba mutumci yasin no respect_😎
*Comment*
*Share*
*Vote*
*#intelligent writer's#*
*#Uwar mijina...!#*
*#Janaf#*
*#One love#*
[18/08, 14:17] 80k: _*INTELLIGENT WRITERS ASSO*🖊_
🌺 *UWAR MIJINAH..!*🌺
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)_
*ALKALAMIN:JANAF*💕
*WATTPAD:JANAFNANCY*
*DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF*
*NOT EDITED*⚒
*NO.8*
'''''''''''Lami da Uwani Dake kichen suna kokarin hada breakfast sukaji wannan ihun tare da kiran Sunan Ummi,cikin Dimautuwa suka fito falo nan sukaci karo da karime itama ta rumtumo zata shigo kichin din hannunta dafe da kirji take fadin"Lami kunji abunda naji kuwa?'Tafada tana haki.
Lami bata samu zarafin mgana ba ,sai ga Sani maigadi da Falalu mai bawa fulawa ruwa da ushe suma sun Rumtomo zuwa falon Suna tambayan lafiya ihun me sukaji haka"Karime ta nuna Saman Hajiya tana fadin"Wlh bamu Sani ba ammh kamar daga bangaren Hajiya ne fa"Basu samu zarafin mgana ba suka ga Yallabai ya fito cikin tashin Hankalin hannunsa dauke da Ummi wacce ke halinn rai da Mutuwa.
Cikin sarsarfa yake saukowa yana Fadin"Bring d car plz"Yafada cikin tashin Hankali ganin haka yasa ushe rumtumawa waje ya bude motar yallabai wanda ya fito da ita 607 kirar Piogion ,su karime ko hannu suka daura akai suna fadin"Mun bani hajiya innalillahi wa"inna Alaihirraju"un"Haka suketa maimatawa har mu"azzam ya fice da sauri.
Kokafin sufito tuni har yasakata a mota ushe yaja sani ya budemusu get sun fice cikin hanzari..Lami da karime jikinsa babu inda baya Rawa Uwani tace'Mun bani meyafaru da hajiya ne'tafada kamar zatayi kuka babu wanda ya iya cewa komai sai ma karisa da sukayi gun sani maigadi wanda ke zaune da falalu suma suna janjanta Abun haka sukayi tsaye tsuru tsuru babu mai iya cewa komai kuma sun kasa komawa sucigaba da aikin gabansu.
Cikin Abunda baifi minti sha biyar ba suka bayyana acikin babban asibintin nan *SPECIALIST HOSPITAL ABUJA* Ushe ne yayi saurin fita ya rumtuma cikin asibitin yana kiran Nurses suma cikin rudewa suka dauko abun daukan mara lafiya suka biyoshi ammh kafin kace me har sunci karo da Mu"azzam ya dauko Ummi ahannunsa,cikin Tashin hankali yake kwalama Doctor kira..Dr Abduljabar ne ke kan Duty ranar kuma daman Asibitin nan asibitinsu nan suke da fayel tun bayan dawowarsu Abujan da azama.
Ko takan Nurses din dake kokarin amsan Ummi su sanya bisa gadon jinya dake hannunsu baiyi ba,kai tsaye office din DR.Abduljabbar ya shiga yana Fadin"Dr. Save my life Ummi na "Yafada kamar zai fitar da kwallah.DR.Abduljabar dake zaune yana duba patient yayi Saurin mikewa yana Fadin" Brr.Mu"Azzam meyasamu Ummi kuma"Shima yafada cikin Tashin hankali kafin yayi mishi nunu da dan gadon dake office din yana Fadin"Drop her here"Yafada yana kokarin taimaka ma Mu"azzam din.
Patient din Dr.Abduljabar yabawa hakuri ta jirashi awaje cikin gaggawa yafara gwaje gwaje dakuma kokarin farfado da Numfashin Ummi wanda yadauke gabadaya shiko Mu"azzam yakasa zama fadi yake"plz Ummina don"t do dis To me,inkika mutu rayuwata tashiga lahaula plz wake up nayi miki alqawarin bin dukka umarninki"Yafada cikin wata irin karyayyan murya lura Da Dr.Yayi baya cikin hayyacinsa sai ya kallesa yana fadin"Brr.Cool down Karka damu Ummi zata tashi bawani abu bane seriuos kawai taji Abunda yadan Firgitatane.So Abunda nakeso dakai kabani wuri in gudanar da aiki na plz" yafada kamar yana lallashinshi kuramasa ido yayi kafin yakada kai ya juya ya fice.
Sai da DR.Abduljabar ya kwashe fin awa kana ya fito wanda Mu"azzam ke kofar office din yana safa da marwa cikin tashin hankali ya rike Dr.Yana Fadin"Dr karka cemin Ummi bata tashi ba don Allah"Mirmishi yayi kafin yadafa kafadarsa yana fadin"is ok Brr.Mu"azzam Ummi tafarfado Cikin Nasara alluran barci nayi mata..Karka damu kamar yadda nafadamaka wani abu ne taji kota gani, wanda ya matukar razanata har yayi sanadiyar sumarta ammh yanzu ta farfado komai Normal insha Allah"ajiyar zuciya ya sauke yana fadin"Alhamdulillah..."Dr.Yayi mirmishi yana fadin"Ummi baxata mutu tabar mu"azzam ba saboda dayansu bazai iya rayuwa babu daya ba..Bantaba cin karo da soyayyar uwa da 'da irinku ba anyway kuna burgeni sosai"yafada yana bubbuga kafadansa
Gyada kai kawai Mu"azzam yayi kafin yayi mgana Dr. Yace"yanzu zamu maidata dakin dazata samu hutu insha allahu zuwa yamma ko tomorrow morning zaku koma gida" Hannu kawai Mu"azzam yabasa yana Fadin"Tanque Dr Allah ya saka maka da alheri'jijjiga hannun nasa yayi yana fadin"Haba babu komai Nima Ummi uwata,Allah yakara lafiya.
Cikin abunda baifi minti goma ba har ankai Ummi dakin Hutu cikin wani kayatattacen daki mai kyau da tsari wanda sai ka rantse ba acikin asibitin yake ba,saboda yadda ya tsaru komai na bukatar rayuwa akwai shi cikin dakin..Mu"azzam yakasa barin Asibiti waya yayi wajen aikinsu yana fadin bazai samu zuwa ba Brr.Barau ya wakilcesa wajen gabatar da sharia na yau din.
Brr.Mu"azzam yakasa jirkawa ko nan da chan saboda hankalinsa bazai iya kwanciyaba sai yaga farkawan Ummi yana zaune acikin dakin kan kujeran dake gefen gafon..Hannunsa sakale cikin na Ummi wacce ke barci Numfashinta na zuwa na dawowa ga karin Ruwan da"ake mata yana shiga dis dis..Fuskarta ya tsurama ido lokaci daya idonsa yakawo kwallah ganin yadda Umminsa ta rame lokaci daya,gabadaya kansa ya kulle ya rasa mafita..Bai gama zurfafa Tunani ba yaji hanunsa dake cikin Na Ummi yafara motsi da sauri ya mike yana fadin"Ummi na...Ummi na..."yafada yana damke hannunta itakuwa Ummi sama Sama,takejin Muryan Mu"azzam idanunta sunfara budewa dishi dishi..shiko ganin tana ta mutsu mutsu yasashi ficewa da sauri zuwa office din Dr.Abduljabar yakirasa da sauri da hanzari yabiyo bayansa suka rantamo dakin koda suka shigo Ummi tafarka tana kokarin mikewaa zaune da hanzari mu"azzam ya karisa yana fadin"Ummi karfa kiji ma kanki ciwo baki da lafiya"yasa ka hannu zai rikota da dakamai tsawavtayi lokaci daya dacewa"Karka kuskura katabani Ibrahim..."Tafada cikin kaukkausan murya wacce tadan shake.
Ba Mu"azzam ba kadai ba, hatta Dr.Abduljabar cak ya tsaya da kokarin karisa kusa da ita dayake dominn Dubata Mu"azzam kuwa suman tsaye yayi yana duban Ummi fuskarsa tana bayyana damuwa karara dakyar ya iya bude baki yace"Don Allah Ummi kiyi hakuri ki yafeman..Kinga baki da lafiya kibari mu koma gida mayi mganan a tsanake"Yafada yana hada hannuwa dago kanta tayi tana kallonsa lokaci daya hawaye suka zubomata tace cikin wata murya mai cike da tsausayi"yanzu dakai za"a hada baki aci amanata ko Mu"azzam? tafada tana kallonsa da jajayen idanunta ya bude baki zai yi mgana ta dakatar dashi bayan tadagamai hannu tacigaba da cewa"Ka kyauta..Kuma nagode bisa hallacinka ..Kaje na bar ma su shettima kai, nikuma zan barka dasu zankoma kasata inda aka reneni wato gidan marayu tunda yanzu maraicin nawa yakara bayyana"Tafada tana fashewa da kuka.
Mu"azzam yakasa mgana illa zuciyarsa dake bugawa fat..Fat..Inda ace zai samu sararin kuka wlh dayaji dadi..Dr.Abduljabar yakallesu cikin mamaki kafin yabude baki yace"Brr.Mu"azzam meyake faruwa ne..? wani laifi ka aikatama Ummi duk da irin son datake maka take furta wa"innan kalaman?"Yafada cikin tsantsan mamaki.
Mu"azzam yakallesa idanunsa sunyi jawur jijiyoyin kansa sun taso Radau..Ummi ya kallah wacce keta sharban kuka kamar me yama kasa mgana sai durkushe wa yayi yana jan kafa zuwa bakin gadon Ummi yana ta so yayi mgana ammh zuciyarsa datayi Nauyi yakasa mgana hannu yasa zai riko hannu Ummi ta matsa baya tana fadin"Ka fice kabani Wuri Mu"azzam bana son ganinka"Tafada tana kuka kara matsowa yake shiyasa takara saka ihu hade da tswa tace"Ka ficeman nace IBRAHIM..Wlh indai baka fita nizan fita nabar maka dakin..KA FICE KABANI WURI NACE"Tafada cikin dakamai tsawa gani yaki motswaa yasa tafara kokarin tsinke karin Ruwan dake hanunta da Sauri mu"azzam ya mikewa yana fadi cikin rawan murya"No Ummi zan..Zan..Fita..Na fita shikenan ko"Yafada kamar wanda yarasa hankalinsa jin muryansa tafara rawa yasa Ummi kallonsa tsausayinsa na neman mata tasiri shiyasa tayi saurin kauda kai kuka na kara kwacemata.,cikin hanzari Mu"azzam ya mike yafice Dr.Abduljabar yana kokarin mai mgana ammh ina har ya fice..Dr yayi tsuru kawai domin yashiga comfuse jikin sanyin jiki ya karisa kusa da Ummi yana kallonta kafin yace"is ok Ummi..Kibar kuka hakanan kinga baki da lafiya kina bukatar Hutu"yafada cikin kulawa Kauda kai Ummi tayi batayi mgana ba komawa tayi ta kwanta kafin tace"Don Allah,Dr. biman Mu"azzam kada kabarshi yatafi cikin wannan halin don Allah"Tafada cikin kuka Mamaki ma yahana Dr.Abduljabar mgana yana tsaye Ummi tasake cewa"Don Allah Dr.."Tafada tana kallonsa saurin gyada kai yayi kafin yafice yana mamakin wannan al"amarin mai daure kai.
Koda yafito baiga Mu"azzam ba cikin zafin Nama yafice zuwa haraban asibitin yana zuwa daidai motarsa na ficewa daga asibitin dafe kai Dr.Abduljabar yayi yana fadin"oh my god..Wai meke faruwa ne'"Nifa kaina ya daure' ganin ba wanda zai bashi amsa ne yasa yasaka kai yakoma cikin asibitin bai koma dakin Ummi ba, wata Nurse ya umarta dataje ta dubata tamata alluran barci ko tasamu Natsuwa.
Shiko Mu"azzam yana Fitowa cikin tashin hankali ya karisa wajen motarsa Ushe dake cikin motan yaga fitowar oga kamar zai fadi cikin hanzari ya fito ya budemai motar yafada ciki lokaci daya yana fadin"Uche back to house.."Yafada cikin wata murya mai nemam agaji jin haka yasa sai da Ushe ya waigo yana kallonsa kafin yace"Oga..Are u alright.."Yafada yana fatan kar ace hajiya ta mutu..Ko bude ido mu"azzam baiyi ba Kuma bai da niyyar mgana shiyasa Uche juyawa yayima motar key suka fice duka zuciyoyinsu babu dadi.
Abun mamaki su karime sunanan haraban gidan nan cikin jimami jin hon yasa sani zabura ya bude get..Gani motar yallabai tasawo hancinta cikin gidan yasa suka kara tsurewa..Ushe baigama parking ba suka isa wurin da sauri Falalu shi yabudemai yallabai mota yana fadin"Yallabai ya hajiya take da jiki"ganinsu tsatsaye yasaka Mu"azzam dan sakin Fuska ammh ina ya makaro domin ma"aikatan nasa sunfi kowa lakantan Uban gidansu.
Cikin rashin kuzari yafito daga cikin motan yana kallon fuskokinsu lokaci daya yana kauda kai..Dakyar ya kakalo mgana yace"Ku kwantar d Hankalinku Ummi tana lafiya ta farfado an mata alluran barci ne kinji..."Yafada yana wucewa ,da kallo suka bisa duk da yayafada musu ammh kuma zuciyarsu ta kasa yarda da Abunda yafada musu ba.
Har yakusa shiga falon ya waiwayo yana fadin"Baba ku yi hanzari kuyi abinci mai Ruwaruwa Ushe zai daukeko keda lami da Uwani kuje ku kaima Ummi ku dubata'"Yana gama Fadin Haka yashige falon.
Karime takalli Lami tace"Wai anya yallabai lafiya kuwa" lami ta sauke ajiyar zuciya tana Fadin"gaskiya akwak mtsala"Sani maigadi yace"Koma miye Allah ya kiyaye gaba kuyi hanzari kuje kuyi abunda yace,kada ya fito kuma baku kammallah ba"Jin haka yasa suka Rumtuma cikin gidan zuciyarsu ba dadi.
Fanten wake sukamata wanda yaji hanta..Sai suka hadamata lemon kanka..Kayan Fruit suka diba kama Daga kankana,abarba Apple,lemo etc basu wani tsaya neman yallabai ba domin Tunda ya shiga ciki bai Fito ba, suna kammallawa suka hada cikin kwando suka sako mayafai Ushe na waje na jiransu suka shige mota suka Fice su falalu nabasu sakon Suyima Ummi sannu kan Suzo.
Ushe yayi musu jagora har zuwa dakin da Ummi take,tana kwance idanunta na kallon Saman dakin,Sukayi sallama suka shigo,Tana jin Sallamansu tafara kokarin mikewa Uwani ce takarisa Da sauri ta rikota tana fadin"Sannu hajiya,yi ahankali"Tafada tana sakamata Pillow abaya yadda zataji dadin zama.
Karime ta ijiye kwandon Tana ma Ummi sannu lokaci daya da lami suna mata yajiki,ushe ma dake gefe sannu yake jeramata tana amsa cikin sanyin jiki kallon su takeyi kafin tace cikin dasasshiyan muryanta"Sannunku da zuwa,daga ina kuke"tafada kai tsaye karime tace"Yauwa hajiya,daga gida muke,yallabai ne ya umarcemu da mu yi abinci mukawo miki"Jin sun ambaci Mu"azzam yasa jikin Ummi na rawa tace"My son? yana ina yanzu,don Allah kufadamin wani hali yake ciki"Tafada lokaci daya hawaye na zubomata bisa kunci.
Cikin mamaki su lami suka kalli juna kafin Uwani tayi karfin Halin cewa"Yallabai yana gida hajiya shi da kanshi yabamu Umarnin dafa miki abinci mukawo miki"Ajiyar zuciya Ummi ta saki kafin tace"Alhamdulillah.."Tafada tana lumshe ido lokaci daya tana share hawaye..Cike da mamaki su karime kebin Ummi da kallo yanzu suka samo bakin zaren,na damuwar yallabai.
Lami ne tace"Hajiya azubo miki abinci ko kuwa Fruit zaki sha"Shuru Ummi tayi kafin tace"Bar abincin nan Lami kubani Fruit kuyi maza ku koma gida,ku tabbatar da Son yaci abinci kada kubarsa ya kwana da yunwa don Allah"Tafada tana tsaresu da ido gyadamata kai kawai sukayi domin Suma kansu ya daure.
***** ****** *******
Koda Mu"azzam ya shiga ciki dakinsa ya wuce direct,yana shiga ya sulale yafada bisa gado ko takalmi bai cire ba,kansa ne yamasa Nauyi lokaci daya yaji kamar hawaye ya zubomai dazaya samu daman Yin kuka daya samu saukin halin dayake ciki,yanzu ya zaiyi?Bazai iya sabama Ummi ba kuma bazai iya Watsama Baffa Shettima kasa a ido ba,Gabadaya ya rasa inda zai sanya kansa.
Idanunsa suna lumshe ammh ba barci yake ba,kawai tsabar Tunani wayarsa dake cikin aljihu tadau kuwa cikin kasala da mutuwar jiki ya zura hannu ya ciro saboda yadda kansa yama Nauyi ko duba sunan baiyi ba domin Idanunsa sun masa Nauyi yasa yadaga kawai yakara a kunne.
"Dan"Uwa.."Shureim yafada Jin muryan Shureim yasa Mu"azzam mikewa jikinsa na rawa yace"Dan"uwa ina cikin wani hali ina bukatarka,kusa dani"Yafada cikin Tashi hankali jin yadda Mu"azzam ke mgana yasa ya mike daga zaunen dayake gaban Hajiya yace"Dan"uwa,meke faruwa ne? muryan ka tanuna kana cikin damuwa"Yafada shima cikin damuwa hajiya dake zaune gefe takalli Shureim tana fadin"Kai lafiya kuwa? meyafaru da mu"azzam din"Tafada tana kallonsa.
Shureim najin Abunda hajiya tace sai ya budemata Speaker wayar..lokacin mu"azzam Yana takan rabtafamai na abunda ke faruwa,cikin tashin hankali ya kareshe da cewa"Dan"uwa ya zanyi? Ummi tace bata son ganina,kuma tace ita kasarsu zata koma bata bukatata yanzu batason ko kallon Fuskata"Yafada kamar zai fashe da kuka cikin tashin hankali Shureim yace"Innalillahi..Ashh Abu baiyi dadi ba"Yafada yana dafe kansa.
Hajiya dake gefe wanda tagama jin komai tace"Shureim bani Mu"azzam din in yi mgana dashi"Tafada cikin kakkausan murya alaman Ranta yabaci kai tsaye ya mikata ta karba takara akunni tana Fadin"Mu"azzam Saurareni"Tafada ranta babu dadi,jin muryan Hajiya yasa mu"azzam sakin ajiyar zuciya yana fadin"Hajiyarmu UMMI ta tsaneni tace natafi na bata wuri bata bukatata, kan Abunda bani da yadda zanyi na hana Faruwansa"Tsaki Hajiya tasaki kan tace"mtsweee..Wai wata irin zuciya Suhaima take dashi ne? Ta girma ammh haryanzu bata bar sakarci ba,in ta koreka tana da wani dan ne bayan kai"Hajiya tafada ranta bace kafin tace"Ka kwantar da hankali ka yanzu Shureim zai daukoni mu taho zan ganta sai naji dalilin wannan Sakarcin"Tafada cikin dattako Mu"azzam yashiga jerama hajiya godiya bata kulasa ba ta mikama Shureim wayar tana fadin"ka shirya muje Abujan yanzu"Tafada tana kokarin mikewa,saurin yanke wayar yayi lokaci daya yana taimakamata.
Kaya kawai ta chanza,sai mayafi data sanyo,Duk da haryanzu da Sauran ciwon kafan ammh dayake motace shima Shureim yasan zuwan Hajiyan shine masalaha,shiyasa agurguje ya shirya Sukama Zulaika sallama Suka dau hanya Shureim da kanshi yake jan motan.
*Comment*
*Share*
*Vote*
*#Intelligent writer"s#*
*#Uwar mijina..!#*
*#HAFMEELART#*
[18/08, 14:17] 80k: _*INTELLIGENT WRITERS ASSO*🖊_
🌺 *UWAR MIJINAH..!*🌺
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)_
*ALKALAMIN:JANAF*💕
*WATTPAD:JANAFNANCY*
*DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF*
*NOT EDITED*⚒
*NO9*
""""Basu isa ba sai gabda la"asar Shureim, Mu"azzam kawai yakira yafada musu lambar dakin da Sunan Asibitin,kai tsaye chan Suka Nufa,Sai da Ummi tagansu kwatsam lokacin tana zaune bisa gadon ancireta mata karin Ruwa tayi nisa cikin Tunani sai jin Muryan Hajiya taji tana fadin.
"Suhaima wannan wani irin sakarci ne naji kin aikata"Cikin Firgita Ummi tadawo daga tunanin Tilon danta ganin Hajiya tsaye bisa kanta Shureim na gefe yasa tace cikin mamaki"Yaya.." yaushe agari kuma"tafada tana kakaro mirmishi Balla mata harara Hajiya tayi kafin tace"Kul karki kara cemin yaya Tunda baki daukeni da daraja ba,sau nawa zan Fadamiki Suhaima kidinga barin yaron nan, ya shiga cikin Danginshi,ke baki mantuwa kuma baki yafiya wani irin zuciyane dake da bazaki gane yanzu kinfi karfinsu ba ehe'"Tafada ranta bace Ummi ta kalli Hajiya kafin tayi mirmishin Takaichi tace"To yaya ki zauna kiji mana,kinsan mezasu min kuwa Mu"azzam fa suke neman Rabani dashi"tafada cikin zubar hawaye.
Dagamata hannu hajiya tayi kan tace"Bazan zauna ba,domin bashi nazo yi ba,nazo ne namiki fada ki chanza Tunani saboda Abunda kika aikata ko a addininki bashi da kyau,Wayace zai Rabaki da Mu"azzam danki ne fa,wanda kika dauki cikinsa wata tara kikazo kika sha wahalan Nakuda,bayan kin Haifesa kika sha wahalan Renonsa har ya kawo iyanzu,kina tsammanin ko butulu ne shi zai manta dake? balle Yaron iya biyayyah yana miki sujuda ne kawai baya miki shin bazaki godema Allah ba..,Karki manta akwai iyayan da ko mutuwa zasu yi wlh basu isa su hana ya"yan su abunda sukayi niyyah ba,shinke baki bambamta dasu ba,saboda sonki da yake yasa baya son bacin ranki, yakasa fadamiki sai dai shi yayi ta zama da damuwa bisa ransa,so kike watara zuciyarshi ta buga saboda zafafan kalamanki akanshi.."Hajiya tafada tana dakatawa saboda tagaji da tsayuwa( da dai kicii gaba da tsayuwan waya gayamaki borno gabas take😂)
Wuri ta nema ta zauna tana kallon Ummi dake kuka Shureim kuwa hajiya nafara fadanta yafice..Riko hannunta hajiya tayi tana fadin"Don Allah don Annabi Suhaima kibar Mu"azzam yayi Auren karfa ki manta ba mugun abu bane,Sunnar ma"aiki ne fa zasu dambaka,kuma in baki manta ba yanzu shettima yaga ishara da halin Rayuwa ke din dai da suka tsana, kece sanyin idanuwansu saboda keki ka haifanmusu dan" daya zama garkuwa garesu'"takareshe fada tana kallonta.
Ummi dai kuka take bilqqi da gaskiya Kafin tadago tana kallon hajiya ta furta cikin kuka"yaya diyar FADI ce fa,Kin manta yadda Fadi tayi sanadiyar wargaza farincikina duk da burina na zama da moodu har karshen Rayuwata"Takareshe fada cike da gunjin kuka,Mirmishi hajiya tayi kafin takara rike hannunta Tace"To Saime,Ita Fadin tana raye ne? ehe..Ai Allah kenan wanda ka raina shi zai maka rana wata rana"Tafada tana kallonta shuru Ummi Tayi tana kukan ta Hajiya sai bata kara mata mgana ta kyaleta tayi kukan nata.
Mikewa tayi tana gyara mayafinta kan tace"Kinga in har baki ji mganata ba wlh tallahi Shi kanshi dan "Dakike Tutiya dashi watarana ke da hannunki zaki kasheshi"Da sauri Ummi Tadago tana kallon, hajiya idanunta jajur ta furta murya adashe"Ni Hajiya..Zan..Zan kashe mu"azzam"Gyada mata kai tayi kan tace'Kwarai indai baki janye kalamanki na bakison ganinsa ba,kuma baki sama auren albarka ba, Shi zai jawo ki Sakamai damuwa aranshi har yayi sanadiyar mutuwarsa kamar yadda Fadi da shettima suka kashe moodu da Zaluncinsu"Kallonta Ummi keyi cikin nazari kafin tayi mgana Hajiya ta rigata da cewa"Karki ce komai kawai kiyi Fatan alheri..Kifara shiri Sati mai zuwa za"a daura aure kuma yataho da matarsa,ki Natsu kuma kiyi aiki da hankalinki kuma ko bakomai yar"uwansa ne"Hajiya tafada tana tafiya kafin takara cewa"Indai na isa dake..Kada naji wata mgana kuma,ki fadama Mu"azzam amincewarki ko hankalinsa ya kwanta,Ni na wuce daman Abunda ya kawoni kenan"Hajiya tafada tana kokarin Ficewa.
Ummi tace"Yaya yamma tayi ku bari sai gobe" A"a Hajiya tace kafin tacigaba da cewa"Gwara mu koma muda zamu dawo sati mai zuwa biki,Allah bamu alheri Yakuma kara lafiya"Daga haka ta fice daga dakin.
Ajiyar zuciya Ummi ta Sauke duk kalaman Hajiya basu shigeta ba, domin Tana ji aranta duk wanda yace ta zauna da Jinin Fadi ba masoyinta bane..Wlh bazata iya ganin mu"azzam ya Auri diyar Fadi har yayi mata ciki sun Haihuwa ba har abada zata tsani yaran ,wanda kuma ba fatan ta kenan ba akullum fatanta Mu"azzam yayi aure ya haifamata jikoki wanda zasu debemata kewanshi tunda shikadai gareta,ammh yanzu yaya tasaka baki wanda bazata ta taba juya baya ga bukatarta ba don Kamar mahaifiyarta take kallonta ammah har abada *BAZATA TA TABA SON JININ FADI DA SHETTIMA BA*.Kawai tabarma Ranta ayi Auren ammh har abada wanan yarinya sun kawota ne domin Itama ta dandana abunda suka dandanamata.."Da wannan Tunanin Ummi ta tsaya ammh duk da haka sai da ta koka saboda yadda zuciyanta ke harbawa in tama Tuna wai Mu"azzam dinta zai auri Diyar FADI.
Wata Nurse ce tazo dubata,kawai sai tace mata takira mata Dr Abduljabar, yana office sanda Nurse din take fadamai,Bai bata lokaci ba,ya isa ga dakin Abun mamaki,Ummi cemai tayi yakira mata Mu"azzam yazo yadauketa su koma gida ita ta warke"Hakika ko Dr Abduljabar yaji dadi kai tsaye yakira Brr.Mu"azzam yana fadamai sakon Ummi.
Mu"azzam dake kwance wani abu mai kama da zazzabi yarufesa kiran Dr.Abduljabar ya shigo wayansa jikinsa na rawa yadauka yana fadin" Dr hop dai ba jikin ummi bane yatashi?" yafada cikin Nuna damuwarsa dariya Dr Abduljabar yayi kan yace"No..Ummi ce tace kazo ku koma gida,wai ita ta warke" yafada yana kallon Ummin yana yar dariya.
Da wani hanzari mu"azzam ya mike yana fadin"Plz doc,stop dis joking kasan fa zuciyata zata iya bugawa"Dariya Dr.Abduljabar yayi kan yace"Wlh billahil azim da gaske nake,au baka yarda ba,to ga Ummi tafadamaka da kanta"
yafada yana mikama Ummi wayar karba tayi tana mirmishi tace"my son.."Cikin farinciki ai mu"azzam mikewa yayi yana rawan baki ya Furta"Alhamdulillah my Ummi is back..Ummi am on my way yanzu kinji i love u"Yafada bakinsa yakasa rufuwa, gyada kai tayi tana jin kwallah na taruwan mata tace"
""Love u too..Son drive safely kaji"Tafada muryanta yafara chanzawa sai tayi Saurin mikama Dr.Abduljabar wayar itakuma tayi saurin fadawa tiolet din dakin tana danne kukanta..Bataso likita yagani,Shiko baima lura da ita ba, ya kashe wayarsa ya maidata aljihu bayan ya kashe wayan,lokaci daya yana fita daga dakin.
Shiko Dan Marayan Allah mu"azzam jikinsa na rawa ya fito daga daki cikin Murna da farinciki lokaci daya yana latso kiran Dan"uwa bisa wayan yana picking lokacin Suna hanya Yaji mu"azzam yace"Allah Ya iyamaka abunda ka gaza Dan"uwa"
"Amin Amin.."Dr,Shureim yake amsawa yana fadin"meyafaru dan"uwa irin wannam addu'a haka"? cikin Farinciki Mu"azzam yafadamasa sa cewa Ummi yanzu ta kira yazo yadawo da ita gida.
Cikin jin dadi Dr.Shureim yace"To Alhamdulillah Dan"uwa ga duk alamu tafiya tayi kyau,hajiyarmu tayi nasaran Tankwara Mana Umminmu"Yafada yana dariya lokaci daya yana kallon hajiya wacce ke kallonsa itama tana mirmishin jin dadin Suhaima taji mganarta.
Cikin Jin dadi mu"azzam yace"Bari kawai dan"uwa ganinan zuwa mu hadu kawai"Dariya Shureim yayi kafin yace"To sai dai in zamu wuce Maiduguri dauro maka aure Dan'uwa"Yafada yana yar dariya
Cikin Rashin Fahimta Mu"azzam yace"Banga ne ba"Shureim yace"Muna hanyar komawa Abuja hajiya tace mu juya kawai"Rike baki Mu"azzam yayi kafin yace"Abuja kuma i think sai gobe"Dariya Shureim yayi yana fadin"To miye ai babu komai Tunda kwalliya tabiya kudin Sabulu angon Wani sati"Yafada yana sheka dariya Bata rai Mu"azzam yayi yana fadin"kaidai dan iska ne wlh,nidai bama Hajiyata waya namata godiya.
Shureim na dariya ya mikama hajiya wacce itama ke dariya tana fadin"Wlh nan da ko wani satin mtsayinshi zai kamo naka,yaro"Mu"azzam dake jinsu yayi dariya yace"yauwa hajiyata Proud of u Barrister mu"Yafada yana dariya,Dakuwa tamai kamar yana ganinta tace" kaniyarka nan,dan nema kawai wato karfi da yaji kaida Shureim kun maidani kakanku ko"? tafada tana dariya.
Mu"azzam yace"yo hajiyarmu ai dole kiyi hakuri babu kakannin dole kece zaki cigaba da jan ragamar kujerar"Yakareshe fada yana dariya Itama dariyan tayi kafin tafara mai nasiha dacewa"Naji dadi da Suhaima taji mganata,, duk da nasan bazata watsamin kasa a ido ba,to ammh kaima ina so in fadamaka sai kayi taka tsantsan ma"ana duk abunda yashafi Auren nan kada kadinga yawan Tuna mata,domin wlh ina tabbas din bata yafe bafa,tana Rike dashi yardarta baya Nufin yafiyarta bane..So kabi komai asannu,munanan muna mata Addu"a Allah cire Abun aranta tunda yanzu zuru"ace za"a hada mai girma"Har tagama mganarta Mu'azzam naji yana jinjina kai sai da tagama ya Numfasa yace"Naji hajiyarmu kuma insha Allahu zaki sameni mai biyayyah da Bin Umarnin Ummi bazaki ji sabanin Tunaninki ba..,Allah ya shigemana gaba"hajiya ta karba Da Amin Amin kamin suyi sallama ya datse kiran jikinsa asanyaye jin dadinsa daya Amincewan Ummi shi aganinshi indai akayi auren zama yahada guri daya to za"a samu sauki (Tab lalle mu"azzam bakasan Ummi ba har yanzu..Zama yahada ko? zaka ganinma idonka in kafara amsa gwale gwale😂)
Dama yana farfajiyan gidan ne sanda yake wayar da hannu kawai ya yafito Ushe wanda ke gun su sani maigadi suna hira,Da hanzari ya kariso yana fadin"Yallabai ina muka Nufa"Kallonsa Mu"azzam yayi kafin yace"Ina su Lami? suna chan ko ka maidosu gida ne? Cikin girmamawa Ushe yace cikin Gurbatattaciyan Hausansa'" A"a nadawo dasu tuni ma yallabai"Gyada kai kawai yayi, budemasa motan Ushe yayi yafada yana fadin"Ka hanxarta Ummi ke jirana"cikin rawan jiki Ushe yafada bangaren Direba yaja mota suka Fice bayan Sani maigadi yabude musu get suka Fice suna daga musu hannu.
Basu wani dade ba suka iso asibitin cikin Taku sa na kasaita ya fito ya nufi jikin asibitin dakin da Ummi ke ciki ya tura tare da sallama,Tana zaune agefen gado kamar mai jiran wani abu tana jin sallamansa tadago tana amsawa da hanzari ya isa gareta ya rumgomata yana fadin"Ki yafemin Ummi na don Girman Allah"Yafada yana kwantar da kanshi bisa kafadanta.
Cije baki tayi tanajin wani takaichin na yadda Shettima ya dana mata bomb kuma yatashi da ita,hannu tasaka bisa kansa tana shafa gashin kansa tana Fadin"Shiiiiiii...Karka ce komai son..Ya wuce aguna Allah ya sanya alheri a aurenka"Tafada kamar ta kurma ihu dagowa Mu"azzam yayi yana kallonta kafin yace"Da gaske Ummi kin amince"? yafada yana kallon,kwayan idonta daya ciko da hawaye.
Kauda kai tayi kafin tace"In ma ban amince ba son,zaka fasa ne bayan kaje kafad'amasa ka amince harma an sanya rana, biki yazo"Tafada cikin sanyi ammh kuma ranta abace.
Saurin Riko hannunta yayi yana Fadin"wlh Tallahi Ummi Tunda bafffa yafadamin wannan mganar Auren nan,kullum cikin zullumi nake Ummi bansan,yadda zan misalta miki ba ammh Ko alama wannan Aure bai kwantamin ba"Yafada yana murza hannunta mirmishin yake tayi tana riko hannunshi tace"It ok..Kana son yarinya ai ko"? tafada kanta tsaye lokaci daya kuma ta tsareshi da ido.
Dariya ta kusa kamasa ganin yadda Ummi ta tsareshi da ido ,dan murmusawa yayi kafin yace"Ummi wani irin so kuma,?Ai SO DAYA NE Kuma ke na baiwa shi,infact ma ni yarinya Tunda nake banta dora idanuna akanta ba"Yafada cikin halin ko inkula.
Ran Ummi fes tace"Yauwa son..Bani son, ma ko ka ganta ma kasota, don bazan bari tazama abokiyar rayuwarKa ta har abada ba..Zan samo maka daidai dakai kaji ko"Gyada mai kai kawai aransa yana fadin"Wani so? miye ma wata aba soyayyah,ai don BIYAYYA NE,kawai zan Aureta.
Hannu Ummi tabashi irin na yara tace"alkawari Fa son.."Tafada tana mai dariya shima dariyan ya soma bayan ya mikamata hannu ya sarke nata yana fadin"Cikawa Ummi na"yafada yana jijjiga hannun alamar tabbatarwa..Rumgumesa tayi tana fadin"ina matuka sonka Dana"Shima hugging nata yayi back yana fadin"Nima haka Ummi na.
_Wayyo Mu"azzam ka gama kashe kanka da kanka don kaniyarka kaga Zahiran ne,kokuwa kasan me gobe zata haifarwa..I swear kashiga list din Ummi don kasan bata mantuwa_😥
Mu"azzam ne yaje har office yama Dr.Abduljabar mgana kan cewa yazo yayi discharging dinsu zasu wuce,zuwa yayi ya dubata kafin ya rubuta wasu magunguna yabasu tare da cema Ummi data takoma ta samu barci don Allah,godiya sukayi masa kafin su Fito Ummi da kafanta har mota Mu"azzam yacire Budadden Takalmin sa ya bata,tunda lokacin da"aka kawota hankali atashe ko ta takalmi ba"a bi,Dr.Abduljabar na biye dasu yana musu dariya,da hanzari ushe yataso ya karbi kwandon abincin dasu karime suka kawo yasaka abooth kafin ya bude musu mota suka shiga Dr.Na musu fatan Allah kara lafiya lokaci daya ya juya yakoma cikin asibitin.
Hon Ushe ya danna abakin
get din,sani maigadi yazo da hanzari ya bude musu suka sulala ciki,da gudunsa yazo ya bude musu murfin motan,Ummi tafara fitowa Fuskarta cikin Fara"a Ai sani na ganinta ya washe baki yana fadin"Barkanmu da arziki Hajiya,ya jikin kuma"Amsawa tayi da "Jiki da sauki Sani ya aiki"Amsawa yayi da "Alhamdulillah.
Daga murya yayi yana kiran Falalu yana Fadin"Kazo ga hajiya tadawo"hayaniyar shiya fito dasu karime daga ciki suma cikin murna suka yamaimayeta suna mata sannu da jiki,har daki suka rakata su karime Mu"azzam ne ya Umarce su dasu dafamata wani abu taci,bayan tasha mgani tayi salollinta sai ta kwanta,cikin rawan jiki Suka fice suna matan fatan samu lafiya
Sai da Ummi ta rama sallolinta kana taci abimci Tasha mgani Awaya Mu"azzam yahadata da hajiya tana mata barka da sauka gaisawa sukayi sama sama kafin suyi sallama domin kowannensu na bukatar Hutu.
Mu"azzam dakansa ya taimakama Ummi tayi brush yarikota har bisa gadonta ya kwantar da ita..Tare sukayi addu"ar kwanciya barcin kafin su shafa tare..dakinsa yatafi yayi shirin barcinsa cikin kayan barcinsa Pjm ash colour da blanket dinsa yazo nan kasa kan capet din dake dakin ya kwanta yana kallon Ummi wanda ya barci yayi awon gaba da ita..Mirmishi yayi yana Fadin"Ummi na kenan,Allah ya barminke"Shima dai cikin lokaci barcin yayi awon gaba dashi.
•°•°•°•°•°•°°•°•°•
*MAID*
Shirye shirye fa na cigaba da kamkama A bagaren Su bukar da yakura kota kowani fanni an shirya ma Abun,bukar akwati guda yayi ma Zahirah na Fitar biki bayan uban kayan dakin dayayi mata yan Dubai.
Itakuwa Zahirah cikin lokaci tachanza fatarta tayi sulbi saboda yadda yakura ta dage babu wasa,fuskarta tayi fayau tana Fitar da Annuri,Ko"ina ta gifta wani kamshi ne mai tsaya azuciyar wanda yashakeshi ke binta duk inda tagifta..koda bikin ya rage saura kwana uku An rigaya an mata kitsonta na bare bari,yan kanakana yariyari 2step an zubomata shi har baya,dayake ba laifi tana da suma,Ga kunshinta an zubamata shima turbarkallah masha Allah.
Zahirah tafara tsarguwa da wannan Abubuwan da"ake mata koda ta tambayi yakura sai dai tamata dariya tace'"Diyata kenan ki kwantar da hankali abun alheri ne zai sameki Matsayinki ne zai karu kinji karki damu"Ko kwalliyan ne baki so adaina miki"Jin haka yasa ta girgiza kai tana dariya.
Baffa shettima yakasa boye jin dadinsa godiya kuwa yazubama Bukar ba adadi..game dako gayama zahirah yace sai an daura auren In mijinta yazo tafiya da ita,zai fadamata( Kai dai Shettima kacika son kanka da yawa yasin).
********
Ranar alhamis Hajiya Baraka ta iso ita da matar Shureim Zulaika tare shi Shureim din,wanda agobe zasu bi jirgi zuwa Maiduguri daura Aure..Ummi babu wanda tafadamawa to dawa ma take hurda zuwan hajiya yasa tama su karime mgana kan Suyi shirye shiryen abinci gobe nasu dana bakin maiduguri..
Sunji mamaki da Hajiya baraka ke fada musu gobene yallabai zaiyi aure"Abunda basu taba ji ba Ummi kuwa kauda kai tayi ranta na mata kuna,hakuri hajiya ta basu tare da cewa abun yazo agurgujene,shiyasa basu ji ba.
Abangaren mu"azzam ko baida wani shiri Brr.Barau kawai yafadamawa,sai Dr.Abduljabar,Shureim kuwa yazo da abokin aikinsa Dr.Haruna kurfi,Su kadai ne zasu tafi maidugurin gobe in Allah ya kaimu.
Ummi kuwa tayi bakan ko mganar bikin ake bata sanya baki,shima mu"azzam din koda wasa bai taba kwatanta hirar da ita ba,yana kiyayewa ammh duk wani motsinshi Tafin Hannunta yake kar take kallonsa aransa tana ayyana abubuwa dadama wanda nikaina ban sani ba.
*RANAR DAURIN AURE*
Rana bata karya saida Uwar diya taji kunya takowani bangare shirye shirye,ne ke gudana tun ma bangaren su Zahirah su abun da gaske suke don kuwa gida tuni ya cika da yan"uwa da abokan arziki..Mahgana itama tana chan danata gayyah ga kuma yakura wacce itace gayyah komai.
Zahirah tafara fahimtan wani abu domin Duk inda ta gifta amarya ake cema gashi Yakura ta shiryata cikin wani ubansu less bayan tanadeta da lifaya,.Ita kadai adaki tana tunani domin ita tunda take bata taba yin kawa arayuwarta ba ita kadai take rayuwarts..Duk wani shagali da sauri suka farashi domin Shettima yace Yakura su zama cikin shiri ana daura aure mu"azzam zai wuce da matarsa.
Abangaren Su mu"azzam kuwa jirgin karfe goma zasu shiga zuwa maid,shiyasa da wuri suka kammallah shirunsu suma anasu barayin sun safe su karime suka tsabtace gida suka fada kichen domin hada hadan abinci Hajiya kuwa na lura da ummi ko jiya batayi barci ba tarasa wannan bakar zuciya irin na suhaima,yanzu ma tana kwance ko tashi batayi ba gashi ita hartayi wanka zulaika ma ta cakare abunta tashige cikinsu su lami suna aiki dayake sun santa babu ruwanta.
goma Saura kadan Mu"azzam da Shureim suka shigo dakin Ummi wacce ke kwance cikin bargo hajiya na gefenta tana mata fada kamshin daya bugi hancin tane yasata dagowa luuu..Tayi da ido na ganin yadda mu"azzam yaci ado wata ubansu gezner brown ammh light riga da wando yar ciki,harda malummalum kansa dauke da wular zannah bukar,kafafunsa kuma cikin booth suke bayan hannunsa daure,da agogon azurfa mai kyau da kyalkyali yana daukan ido.
Fuskarsa tana Fitar da wani Annuri na dabam,anko sukayi domin shima Shureim irin shigan dake jikinsa kenan, domin shiya yimusu Ankon., Ummi na ganin suna takowa gareta tayi maza,ta maida kanta cikin blanket saboda kukan daya taho mata..Tanaji aranta shettima yagama da ita duk abunda zatayi daga baya ne..Tana ji tana gani mu"azzam yadau kwalliya zashi daurin aure..kawai sai tafashe da kuka harda shessheka wanda har ya fito sunajin sautin kukan nata.
Da mamaki suka bita da kallo kan suyi mgana Hajiya ta musu nuni da kofa da suFita kawai,mu"azzam baida zabi illa juyawa yana fadin"Ummi na ina bukatar addu"anki zamu dau hanya'Banza tayi dashi dole jiki asanyaye yabi Shureim wanda yaja hannunsa suka Fice.
Babu yarda ya iya..Yanaji yana gani ushe yakaisu Airport suna zuwa sanarwan Sunaye yafara gudana lokaci kadan aka kirasu suka shiga jirgin kafin a kammallah komai yahau sararin Samaniya ya fara lulawa MAIDUGURI.
*Comment*
*Share*
*vote*
*#Intelligent writer's#*
*#Uwar mijina...!#*
*#Janafnancy#*
_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*🖊_
🌺 *UWAR MIJINAH..!*🌺
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)_
*ALKALAMIN:JANAF*💕
*WATTPAD:JANAFNANCY*
*DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF*
*NOT EDITED*⚒
*NO 10*
"""Awa uku suka shafe a sama,kafin jirgin ya saukesu a babban Filin jirgin dake birnin na maiduguri,Mu"azzam da kansa yakira Bukar yafada masa isowarsu wanda dama tun suna gida yafada masa zasu biyo jirgi In sun kariso azo a daukesu.
Bukar da kansa yazo filin jirgin ya daukesu zuwa chan gidan nashi, daya kachame da al"umma mata da maza wa"inda suka zo daurin aure,babban Falon Na gidan Bukar nan aka saukesu wanda sukansu yan"uwan Bukar din da sukayi tozali Da mu"azzam din sai da suka raina kansu domin sunga tsantsan kyau,ilimi da kamala tareda tsantsan kwarjini da dattako.,Ba shakka zahirah ta dace da samun gwarzon Namiji haka suke fadi duk wanda ya fito daga falon bayan sun gaisa,Bukar daganshi ya shiga cikin gida inda mata ke gudanar da sha"aninsu yayi ma mahgana mgana kan akawo masu Mu"azzam abinci kafin su wuce daurin auren,Jin isowar ango yasa gidan yadau guda lokaci daya.
Kafin kace kwabo an cika gaban su mu"azzam da abinci Nau"i na dabam dabam sai wanda suka zaba,Shureim ya kalli Mu"azzam yace"Ango fa kasha kamshi,to ya ne zaka taba ne kafin mu wuce"yafada yana dagamai gira.
Tsaki Mu"azzam yayi kafin yace"Sai dai kai,domin naga kamar kafini bukata"Yafada yana Cigaba da dannan wayansa,Dariya su brr barau suka sheke dashi suna Fadin"Shima yana kukan aure so ba cin abinci"Kara darawa sukayi kafin Shureim yacire babban Rigansa yana fadin"To Ango ayi kuka lafiya,yan"uwa ku sauko muyi mu harraka kafin kuma na anjuma"Yafada yana zama lokaci daya da bubbude kulolin gabansa,Sinasir ce sai na biyu Tuwon shinkafa sai Farar shinkafa.
Sinasir suka zuzzuba da miyar Alaiyyahu wacce taji nama da manshanu suna ci suna zolayansa suna dariya,Shiko yama gefe ko kallonsu bayayi yana ta latsa waya abinsa Shureim ya kallesa yana tura sinasir abaki"Wai nace ba"Yafada yana kallon Mu"azzam wanda ya dago yana kallonsu.
Ganin haka yasa Shureim yace"Amaryan ba nan ne gidansu ba"eh sai akayi ya"mu"azzam yafada cikin dage kai,Dariya shureim yayi kafin yace"yo ko gilmawarta banji ba,balle kamshinta kasan ance yan maiduguri badai kamshi ba"Yafada yana tauna kashi Dariya Dr Abduljabar yace"Kwarai su daman, da kamshi aka sansu"Kauda kai Mu"azzam yayi kafin yace"Sai ku shiga ciki duk wacce kuka gani tana kamshi itace amaryar"Yafada yana wani hararansu dariyan shakiyanci suka shekemai dashi sunayi suna dibam garan abinci shiko yayi musu banza.
Ahaka suka kammallah kafin duk su share hannayensu da bakinsu da Tissue,babu dadewa sai ga bukar yazo yace su fito su shiga ciki su gaisa da goggonin Zahirah kafin su rankaya ,zuwa gun daura auren lokaci ya kusa,Cikin jin dadi suka mike mu"azzam na baya baya,suka iza keyarsa gaba koda suka shiga nan suka ga dangi kowacce taci adonta ammh fa sun dane jikinsu cikin,lifaya wanda ya burgesu shureim sun gaisa da kowa da kowa don kowani daki sai da suka shiga,kanwar bukar itace autansu Aisha sunanta suna cemata, Ashe ta fito da gudu da wani kasko ahannunta wanda yake cike da Rushin wuta ga turare yana fitar da hayakin kamshi tafara zagaye Mu"azzam dashi tana sakin guda,nan da nan guri ya kaure da guda da wake wakensu na chan sai abun yakoma burgesu shureim tuni suka fitar da wayoyinsu suna daukan bidiyon yadda mata suka zagaye mu"azzam kowanne rike da kaskon Turare suna mai Feshi da hayaki,tare da guda,dakyar dai suka barsa ya isa gaban mahgana wacce keta faman saka mishi albarka bayan tasaka hannunta bisa kanshi"Allah ya albarkaci Aurenku moodu da zahirah,Allah yayi ma rayuwarku albarka,Allah ya baku zuru"a tagari,Allah ya zaunar daku lafiya,ya kauda dukkan Fitina akanku..Yaasaka ace gwara da akayi"Tagama fada hawaye suna zubomata gabadayan jama"an gun suna amsa mata da Amin.
Shikanshi mu"azzam jikinsa yayi sanyi, shima din da Amin din yake amsawa su shureim na tayasa,To dakyar da mu"azzam yasamu ya fice daga gidan saboda yadda akamai cha mata suna ta kirarin Zahirah tagama dace da sun gwarzon mazaje.
Suna Fitowa suka shisshiga motoci sai Famfari gidan Baffa Shettima inda za"a daura Auren,koda suka isa guri ya cika da al"ummah sai wanda yagani lokacin Da Mu"azzam ya fito daga mota wasu sun ma dauka Moodu ne saboda kamar da suke,sai daga baya suka fahimci shine angon,Baffa shettima yaci fararen kaya da Babban riga harda rawani bakinsa kuwa yaki rufuwa,wani masallaci dake kusa dasu anan aka shiga domin daura auren wani yaya ga bukar shiya, amshi auren zahirah a inda mai gayyah mai aiki baffa Shettima ya nema ma Dansa Mu'azzam,auren zahirah kan sadaki Naira dubu dari,shaidu sun hallara kuma an nema sun bada cikin lokaci Alkwarin Allah ya tabbata Tuni yan,sheda suka hau sanarwa.
*ALKWARIN ALLAH YA CIKA AYAU MU"AZZAM MOODU YAZAMA MIJI GA ZAHIRATU LAKADAN BA AJALAN..."
Saboda Farinciki Baffa shettima Rumgume Mu"azzam yayi yana kuka kamar karamin yaro,kowa yadauka kukan murna ne ammh shi anashi barayin ba haka bane tunawa yayi da dan"uwansa Moodu uwa uba,Fadi wanda duk sun kwanta dama,rashinsu babban illa ne agareshi maraici ya lullubesa,haka yakoma ya Rumgume Bukar yana kuka yana mai godiya,shikuma yana mirmishi kawai domin yanajin sa wani iri duk da yacika ma Shettima Umarninsa,.
Jama"a kuwa dadama zunde sukayi tayi suna cewa"Dole shettima ya makale yahada Aure,yaga yaro yazama mutum ga kudi,ga dukiya ga uwa uba kyau,bayan ya manta dimbin Muzgunawa da takuran Da Suhaima ta fuskanta sanda tazauna tare dasu,dayawan su sunso suji ya Suhaima zatayi in taji wannan al"amarin(Kusan mutane baka gadonsu ammh sana da gadon bakinka).
Achan cikin gida kuwa,Lokacin da masu sheda suka sanar da an daura Aure,kannen yakura dake daki tare da Zahirrah wacce ke zaune kamar mutum mutum,tafara fahimtar meke faruwa da ita ammh abunda ya daure mata kai,in Aure za"ayi mata waza"a daura mata, ita da ko tadi da saurayi bata taba yi ba,bata gama mamaki taji sun rufeta da guda lokaci daya suna mata ambaliyan Turare mikar da ita sukayi suka Fito da ita Falo suna Fadin "Takawarki lafiya Yarinya mai babban mtsayi"Suke fada suna mata tafi da ihu gefe daya suna busa mata hayakin Turare.
Tuni zahirah taji tafara Rudewa kafafunta suna hardewa idanunta sun ciko da hawaye fahimtar haka da Yakura tayi ne ya sa ta isa garesu tana fadin"Don Allah ku dakata da wannan gudan kunsan fa yata batason hayaniya" Tafada tana rikoTa ai zahirah naji yakura ta rikota kawai sai ta fada jikinta lokaci daya ta fashe da kuka tana fadi cikin Rawan murya"Da gaske..Ne...Ni..Ni aka ma Au...Re"Tafada hawaye suna karanyomata..kallonta yakura tayi lokaci daya itama taji ruwan hawaye kawai sai taja hannunta suka fada kuryan dakin harda Rufo kofa.
Zaunar da ita yakura tayi kafin tafara share mata hawaye tana fadin"Kibar kuka yata..Kinji!Farinnciki zakiyi da godiya Allah daya daga darajanki Ayau din kika zama matar aure mai Daraja"Tafada tana kallon kwanyan idonta,Naurau Naurau tayi da ido kafin tace""Taya za"a min Aure ban sani ba? kuma ma waye na aura? tafada kanta tsaye ammh cikin sigar yarinyata
Mirmishi yakura tayi tana zama kusa da ita tace"Karki damu yanzu badadewa ba zaki ga angon ki,kuma na tabbatar in kika gansa sai kin godemana saboda zaben da mukayi miki"Tafada tana,dariya Abun mamaki itama zahirah dariyar tayi tana Rumgumota take fadin"Ammh anan gidan zan zauna ko"Tafada bayan tadago tana kallonta,shafa kanta yakura tahau yi aranta tana ayyana yarinta har yanzu na damun Zahirah
Bata bata amsa ba sukaji gida ya rude da guda ana ma ango kirari gaban zahirah ya yanke yafadi takara makalkale yakura lokaci daya jikinta na rawa..Dan kallonta yakura tayi cikin tsausayawa kafin tace"Kinji ko ga angon chan ya kariso maza tashi ki kiga wanka bari na turo yagana takara shiryaminke nasan kila shettima ya bukaci ganinki"Tana fadar haka tazame jikinta,tafice tana share kwallan data biyo mata.
waje ta fito inda Su mu"azzam suke dangi sun yamaimai mayesa suna sakin guda dasa albarka duk inda ya gifta jinjina ne domin dai duk inda Mutum yake to mu"azzam yakai Cikin dakin yakura suka shiga suna gaisawa da baki,anata saka albarka da fatan zama lafiya yakura tayi tasaka albarka tana hawaye Lokaci daya tana kallon Mu"azzam batare da kowa yaji mai tace ba tadan sunkuyo tace"Suhaima ko ta amince"Kallonta mu"azzam yayi kafin yayi kayatattacen mirmishi yace"Ta amince domin da yarda ta nazo nan"Kallon ban yarda dakai ba yakura ta mai kamar zatayi mgana sai kuma tafasa.
Har suka gama gaisawa da jama"a basu ga ko keyar amarya ba sukuma basu tambaya ba,itakuwa tana cikin daki yagana tagama shiryata cikin wata shadda green doguwar riga wacce taji aiki bayan ta yaneta da lifaya fuskarta tana ta kyalkyali da haske ga kunshinta wanda ya haskata sai zallar yarintarta ta fito fili..Koda Yagana ta jawota zuwa falo har su mu"azzam sun Fice daga gida,fitowarsa yasa suka kara sakin wani guda na ganin yadda amarya tayi kyau kamar ba ita ba.
Suko su Mu"azzam suna Fitowa shureim ya kallesa yace"Kai nifa wlh nagaji wai dangin naku basu karewa ne"Yafada yana daure Fuska,shiko Dr Abduljabar cewa yayi"Wlh ni kafafuna sunfara zafi fa..Kuma gashi bikin naga kamar ba yan mata sai matan aure"mu"azzam dake jinsu yayi musu banza don shima yagaji gaskiya yana bukatar hutu,shiyasa ya nemo bukar ta waya,Kan zasu je su dawo.
Gidansu dake maiduguri suka nufa,suna zuwa daman akwai wa"inda suka saka suna kula da gidan,Komai yana nan a muhallinsa,shashenasu dai na da dasuna matasa,anan suka yada zango,kowa ya baje yana sauke Numfashi Brr,barau yace"ammh sai gobe zamu koma ko? don wlh ban iya tafiya ayanzu haka"Harara Mu"azzam ya wurgamai yana fadin"raggo kawai hala wani aiki kayi"Yafada sanda yake kokarin fadawa tiolet.Sukowa kowa yabaje bisa gado wai sun gaji mamakinsu kawai mu"azzam yayi kamar wasu mata.
Nan suka zauna har dare basu sake fita suna ta zencen bikin yan maiduguri har Dr.Abduljabar nace shima irin na brr,zaiyi nan fa zai makale dariya sukahau yimai suna mai shakiyancinsu na abokai.
Mu"azzam da kansa yakira bukar yafadamasa cewa ashirya da amarya da mutum biyu domin sun rigaya da sunyi buking jirgin karfe tara na safe zasu tashi,jin haka yasa bukar cemai babu damuwa insha Allahu,anan ne ma sukayi mganar kayan dakinta nan mu'azzam yace abarsu sai zuwa gaba,da haka sukayi sallama suna gama waya dashi ya kira Ummi almost 7misseds call ammh bata dauka ba dole ya hakura yakoma ya kira hajiya.
Hajiya tadauka suka gaisa tana tambayansu andaura aure lafiya"Ya amsa mata da Alhamdulillah kana ya zarce da tambayan Ummi nayakira wayarta taki dauka,Ajiyar zuciya hajiya ta sauke kan tace"Lamarin Suhaima sai addu"a mu"azzam wlh tunda kuka tafi bata fito daga daki ba,nayi nasihan nagaji nadawo fada,ammh duk abanza kuka kawai take tana ma Shettima Allah ya isa"Tafada cikin nuna damuwarta na abun ya isheta.
Zuciyar mu"azzam tayi wani dam.."!Wato Ummi ta amince ne don babu yarda zatayi ammh abun na zuciyarta rausayar dakai yayi kafin yace"Hajiyarmu Ummi tana so na kamu da ciwon zuciya ne"? yafada cikin rashin hayyaci,Girgiza kai tayi kafin tace'Suhaima duk duniya bata da wani sanyin idaniyanta irin Ka,duk abunda kaga tayi tanayi don Sun bata mata,eh dole zataji ba dadi don hakika shettima da Fadi sun zalunceta ammh kuma rayuwa babu yafiya kofa Allah muna masa laifi ya yafemana ballantana mu mutane"
ajiyar zuciya mu'azzam ya sauke kan yace'aie shikenan Hajiya Randa Ummi tawayi gari na fadi na mutu sai ta duka tadauka"Yafada kamar zaiyi kuka bai bata zarafin mgana ba yace"Ashirya abinci da dakunan saukan baki gobe jirgin karfe tara, zamu biyo"Daga haka ko mgana hajiya batayi ba, ya yanke wayar ransa na masa kuna,Ranar wlh barcinsa ragaggene sallah ya kwana yi da rokon Allah ya saussauta zuciyar Ummin akan,,wannan Auren Tunda bakin alkalami ya rigaya daya Bushe.
*Washegari*
Tun wajen Bakwai suka gama Shirye shiryensu suka Nufo gidan Baffa saboda kada su rasa flight,Koda sukaje angama shirya amarya zahirah wacce tunda daren jiya Shettima ya zaunar da ita yayi mata nasiha mai kashe jiki kan ya gangaro kan cewa zata bi mijinta zuwa inda yake aiki,ai ada auren bai dameta ba ammh jin zata bar bahna dinta,da yakura da baffa,harda mahgana da kannenta sai fashe da kuka Baffan yayi ta bata baki,ai data koma daki kwanciya tayi tacigaba da kukan,yakura bata da karfin bata hakuri saboda tsausayin zahirah ne ke cinta itama kukan take aboye.
Yau din ma cikin liyafayan aka nannadeta kamshi kawai ketashi tare da ita,Zahirah taci kuka idanunta har sun kumbura saboda kuka,damuwarta daya gunwa za"a akaita gashi kuma bata son kowa ba ,duk da Baffa yace gun goggon ta zata zauna da matar Kawuntane da yarasu kuma danshi ne ya aura mata.
Lokacin da suka iso Baffa ya bukaci ganawa da dan nasa na sirri cikin wani daki suka shiga,bayan sun zauna baffa ya riko hannun mu"azzam yana cewa"dana nagode maka bisa yimin biyayyah dakayi,nakuma ji dadi matuka,ammh don Allah ina neman alfarmar "Yafada yana kallonsa.
Mu"azzam yace"Wata irin alfarma ne baffa fadeta indai batafi karfina ba zan maka ita,"Yafada kansa tsaye. gyada kai,baffa yayi kan yace"Alfarmar don Allah kada kabari laifina da ni da Fadi ya shafi rayuwar marainiyar Allah zahirah,wlh yarinyace karama tana da karancin hankali uwa uba gata yarinyace mara son tashin hankali,don Allah kamin alqawarin yimata katanga ga Fushin da zai sauka akanta na mahaifiyarka( ji baffa da karfin hali..Wannan ai shine ga bugu ga tsinke jaka)
kuri Mu"azzam yayi ma baffa yana jin kansa na masa Nauyi aransa yana fadin"Baffa da Ummi so suke su kasheshi lokacinsa baiyi ba"Damke hannu baffa yayi kafin yace"Naji baffa zanyi iya bakin kokarina duk da kasan sai ahankali kawai albarkanku da addu"anku muke bukata"Jin haka yasa baffa Rumgumosa yana godiya da saka albarka harda hawayen farinnciki,mikewa yayi ya fita da kanshi yaje har daki inda zahirah take ita da bukar da Mahgana,wacce ke kuka ta rike mahaifinta gam hannu baffa yasa yariko zahirah batare da yayi ma kowa mgana ba ya nufi dakin da mu"azzam yake.
Yana zaune mu"azzam na zaune ya zaunar da zahirah kusa dashi yana fadin"Dago fuskarki yata kiga Mijinki kuma aljannarki ina miki fatan zama dashi har karshen rayuwarki"Jin haka yasa mu"azzam yadago kai dai dai lokacin da zahirah ta bude lifyafan data rufemata fuska fes suka kalli juna lokaci daya gabansu ya amsa atare Dam"
zahirah tayi ka sake tana kallon mu"azzam kallo na rashin hayyaci tana mamaki wannan dan gayun shine mijinta,shiko mamakin tsantsan kankanta da yarintarta yake gani,to shi wannan ai reno aka basa yarinya yar ficila haka,tsaki yaja ransa yana mamakin Baffa daya mtsa sai yahada auren nan yo shi ko giyan wake yasha ai baya haikema Wannan ba sai ta mutu
Kauda kai yayi yana daure Fuska,Ganin haka yasa ta dukar dakai tana kukan zucci,nan baffa yashiga yimusu nasiha haka bukarma yazo yayi nashi kafin sufara haramar wucewa Airport don lokaci ya kusa,Wa inda zasu bi zahirah Yakura ce sai Mahgana wato matar mahaifinta saura ance duk suyi hakuri daga baya saje.
Yan kayayyakinta kadai aka daukanmata akwati daya sai Abubuwan da ba"a rasa ba,Da zahirah taga dangi kowa rumgumeta yake yana kuka ai itama sai ta burkice ta kamkame babanta tana kukan bazata ba shi yadauketa cak yakaita mota yana hawaye yace"yahna..Kibar kuka kiyi hakuri da rayuwa saboda ke macece watarana ma uwa zaki zama,ina miki fatan sassautan al"amura gareki yata,"Daga haka yajuya yana kuka,mota biyu sukayi zuwa filin jirgin wanda mu"azzam ya matsu su tafi don hankalinsa na gun Ummi.
Anfara kiran sunansu bayan angama tantancesu A first class suka zauna Zahiirah tana makale jikin yakura mahgana na gefe chan gefe kuma su mu"azzam ne suma wanda suke gulman amaryan mu"azzam din suna fadin"wannam ai kwailace yanajunsu banza yayi musu yafara karanta jarida duk da bakomai yake fahimta ba.
*SAFE LANDED..Azzamhirah*
*Comment*
*Share*
*Vote*
*#intelligent writer's#*
*#uwar mijina#*
*#JANAFI#*
*🌺UWAR MIJINA..!*🌺
_(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)_
*Alkalamin:JANAF*
*wattpad:Janafnancy*
*Dedicated to my blood Sisters JANAF*
*Intelligent writer's Asso*✏
*NOT EDITED*⚒
_*Attention:Ina wacce takeson fatarta ta murje yayi taushi da kuma fresh?ina wacce takeson idan an ganta sai an wanke hannu kan atab'ata don tsabar murjewa?maza garzayo ki sameni zan miki recommending cream bana bleaching illa zai gyara miki kalarki ne,sannan kuma muda maganin toilet infection kowani iri ne wanda mike kira da martabar mata,yasin idan baki dashi an barki agidan baya,kuma muna da man dandruff da kuma man gyara suma,if interested pls do chat me up @ 07065481260...thank u all as u patronize!!*_
*NO 11*
"""Har suka iso Abuja Airport, Zahirah na makale jikin yakura tana kuka itako,kamar ranta zai fita,tun yakura na lallashinta har takoma ta kyaleta domin bazata hanata takoka ba,kodon dacin dake ranta yafita.
Jirgin na saukesu Mu"azzam yayi ma Ushe waya kan yazo yadaukesu,Bayan kuma yakira hajiya yafadamata isowarsu,Dr Abduljabar da shima yayi ma direban sa waya kan yazo ya daukesa,cikin lokaci kadan suka kariso,motar mu"azzam ita Aka saka zahirah da yan"uwanta sukuma suka shiga ta Dr.Abduljabar.
Lokacin da Ushe ya dannah hon abakin wani babban get mai kyau da tsari baki da hanci su yakura suka saki suna kallon tsaruwa kai tun ma da suka doso anguwan,suka saki baki suna bin ko"ina da kallo lalle Duk wanda baizo Abuja ba yabar kallo,haka yakura da mahgana keta fada aransu.
Sani maigadi jikinsa na rawa ya wangale get motocin guda biyu masu kyau suka sulala cikin gidan,motocin na tsaya a parking space sai ga Su zulaika dasu karime sun fito suna rangwada guda suna ma amarya lale da zuwa hajiya baraka ce agaba taci adonta cikin wani dakakken leshi,mai kyau da tsari,Ita da kanta ta bude ma Su Zahirah mota tana fadin"Brka da zuwa Amarya ta ango"Tafada farinciki ya nuna har bisa Fuskanta.
mahgana tafara fitowa kana yakura tafito rumgume da zahirah wacce ta sunne kanta tana digan hawaye Rikota hajiya tayi tana fadin"Allah sarki Zahirah Allah yasa a kulla alheri"Tafada tana rumgumeta,Dariya yakura tayi tana fadin"hajiya baraka ashe rai kan ga rai"Hajiya baraka tariko hannun yakura tana fadin"Uhum kedai bari yakura ya bayan Rabuwa kuma"yakura ta amsa da "Sai alheri hajiya ina Suhaima.
"Hajiya tace"Tana daga ciki mu karisa "Tafada tana musu jagora ammh zahira na rumgome ajikinta su zulaika na gaba suna jera guda ta ko"ina,suko su Mu'azzam daganan, sukayi sallama da Dr.Abduljabar da Brr.Barrau suka tafi amotar Dr din Shi da Shureim da Dr.Haruna ne suka take ma su hajiya baya.
Ummi dake kwance, kan gado kowani dakika na zuciyarta bugawa takeyi,tana ji sanda hajiya kefadama zulaika cewa amarya ta iso..Gabanta ya amsa lokaci daya jikinta ya dauki rawa hawayen takaichi da bakin ciki suka zubomata ta sanya hannu ta share mata,bata gama tunanin mafita ba ,taji bude get da karan diran motoci,bata kara tsinkewa da al"amarin ba sai da taji gida ya kaure da ihu,da gudan zuwan amarya Ummi dake zaune tayi saurin mikewa Jiri na neman kadata ammh ina zuciyarta suya take tana fadin"Yanzu ke suhaima Diyar fadi zaki bari tashigo miki gida.ehe..Kinmanta yadda suka taru suka ruguza miki burinki da rayuwarki gabadaya"Jin abunda zuciyarta ke sakamata ne yasa ta nufo kofa da niyyar fita jirin daya debeta ne yasa tayi saurin dafe bango lokaci daya dadafe kanta nan ta sulale tana kuka mai cin rai tana fadin"Allah ya isa tsakanina dakai Shettima kadade kana cutar da zuciyata *WLH NI SUHAIMA NAYI ALQAWARIN DAUKAN FANSA AKAN KA,TAKUMA HANYAR DAKA,BIYOMIN,ZAN RAMA"Tana fadi tana dukan kanta da hannuwanta tana kuka kamar wata zararra.
Suna zuwa kofar shiga babban falon hajiya tayi ma zahirah rada akunni tana fadin"Ki shiga da kafar dama,zahirah bayan kinyi addu'an fatan zaman lafiya agareki"Jin haka yasa tafara karanto addu"a tana kuka kafin su shiga falon wanda daman babban falo ne mai girma da tsari wanda yake dauke da kujerun royal chair har seti biyu,golden colour wanda sukayi ma falon kwanya bayanshi sai wani kafet mai kama da auduga wanda da kasanya kafa zakaji kafarka Ta, lume aciki,sai wani tafkeken Tibin bango daya kusa cinye rabin falon daga yamma kuma wani babban dining area ne wanda yaji wani ubansu Dining table wanda akallah mutane fin goma zasu kammallu agun.
Daga gefe kuma wani korido ne wanda da ka shiga zaka ci karo da wani babban daki ciki da falo wanda cikin nan store,duk wani nau"in abinci yana ciki,sai falon inda nan ne madafi ma'ana wajen dafa abinci wanda yaji kayan wuta na amfanin yau da kullum,inka fito kuma dakuna uku ne ajere,na su karime ne duka.
in mutum yadaga kai sama kuma mattakalan bene zai ci karo dashi,kana hawa zaka tarar da dakuna biyu kachal wanda nan ne shashen Ummi mai gayyah mai aiki..Daki daya bedroom ne,kawai da tiolet daki dayan kuwa babban falo ne mai dauke bedroom da tiolet harda kichen,Ummi tana zaune ne cikin one bedroom ne mai babban falon tabarshi ne in tayi baki kamar hajiya wanda ko wannan zuwan nan ta sauka.
In ka kara saukowa kuwa akwai wani korido dayake kallon saman Ummi,dakabi nan sai sashen mu'azzam dauke da babban falo da bedroom da tiolet,indan ka fito kuma daga gefe ne sai ga wani daki shima dauke yake da falo mai 2 bedroom aciki harda kichen.
Shi Naga hajiya tanufa tasaka makulli tabude, tana fadin"To amarya ga dakinki ki shiga da kafar dama"Yakura ta rikota tana tayata addu"an kafin su sanya kai cikin dakin wanda ke tashin kamshi ko"ina agyare yake falo ne,dan madaidaici mai dauke da wasu arnan kujeru royal chairs purple ne masu kyau sai wani capert daya mamaye duka dakin wanda taushinsa ya wuce misali,wani mamaken talabijin ne ke ta aiki shi kadai sai center table wanda ke tsakiyar dakin,Yakura da mahgana sakin baki sukayi suna bin,ko"ina da kallo,basu gama kallo ba sai suka dangana da cikin bedroom din wanda shima komai na ciki purple ne, shima ya kawatu da Royal bed da wani makeken wardrope da madubi wanda ke shake da kayan ado na mata dama, kowani daki agidan agyare yake da kayan more rayuwa.
Kan gadon dayaji lafiyayyan zanin gadon aka ijiye zahirah wanda kanta ke dunkule cikin lifayanta ammh kallo daya zakamata kasan yarinyace karama ,haka suka karime ke fada bayan sun Fito daga dakin,nan fa suka shiga jera musu abinci kala kala wanda sukayi musu hajiya keta rawan jiki dasu,sallah suka farayi kafin su zauna suna cin abinci bayan hajiya tabasu wuri,Yakura da mahgana suna ta fadi zahirah tagama sa"a ammh *UWAR MIJINTA* itace babban mtsalanta.
mu'azzam kuwa,da Shureim bangarensa suka fada sukayi wanka gado suka hau suka kwanta domin sun gaji jiki na bukatar hutu,shima kafin kace me dukkansu barci ya kwashesu,shiko mu"azzam da ,zullumi yayi barci saboda rashin ganin giftawan Ummi,kuma baisamu kebewa da hajiya ba balle yayi mata mgana.
Hajiya kuwa falo suka dawo ita da zulaika,suna hiransu ammh ranta abace yake saboda abunda suhaima tayi mata,tun jiya tafita batunta saboda tun tafiyar su Mu'azzam take bata baki ammh suhaima takiji wuni tayi adaki,bata fito ba shiyasa yau din hajiya ko mgana bata mata ko dakin ma bata shiga ba,aranta tana fadin"Sai dai ki kashe kanki don ko ga amarya nan tazo"
Kamshin Turaren da sukaji ne yasa suka kalli saman Ummi ce ke saukowa cikin takun isa sanye take da wata shadda gezner, doguwar rigar golden colour,wacce taji aiki sama da kasa,ta daura dankwalin bisa kanta bayan ta tamke gashinta,wuyanta sanye da sarka zinare da kunnenta harda hannuwanta kafafunta kuwa sanye da wani Vine ne mai dan Tudu sai mayafi data yafo mai dan girma.
Fuskarta babu fara'a ko kadan duk da ba wani kwalliya tayi ba ammh kyau xalla ya bayyana,saukowa take cikin takunta na isa,hajiya da zulaika suka bita da kallon burgewa don sun shaida Ummi fa macece ta nunawa ako"ina.
Ta iso falon lokaci daya tadan saki Fuska tana fadin"Sannu da gida yaya" mirmishi Hajiya tayi kan tace"Hoho..Hajiya suhaimar shagali kin gama fushin naki kin fito'"Dariya kawai tayi tanazama Zulaika dake gefe tana gaisheta ta amsa tana fadin"Lafiya kalau zulaika ya hidima kuma,Allah ya saka da alheri"Zulaika ta amsa da Amin.
Hajiya ta kalleta tace""yan maiduguri fa sun iso dazu, mun barsu suna cin abinci ne"Tafada tana kallon Fuskanta Yamutsa fuska Ummi tayi kafin tace"uhm.."Kawai kauda kai Hajiya tayi kafin tace"Zulaika dan bamu wuri don Allah"Tashi zulaika tayi tanufi barayin su lami dake chan kichen suna shirye shiryen dora dinner.
Hajiya takalli Ummi tace"Karki sake ki fara ma Suhaima wannan ba girman ki bane, Rama cuta ga wanda baiji ba baigani ba'"Ummi takauda kai kafin ta kago mirmishin dole tace"Allah bakomai yaya..Kawai nakasa kauda abun araina ne balle har na manta" hajiya tace"Hakuri zakiyi ki kuma tuna Allah ma muna masa laifi ya yafemana to kema kiyi koyi da musulman kwarai ki yafe suhaima don Allah"
Kuri tayima hajiya da ido kafin ta muskuta tace"Shikenan yaya zan duba komai zai wuce"Jin haka yasa hajiya washe baki tace"Yauwa diyar albarka kokefa,maza tashi kije tundazu yakura keta tambayanki" da mamaki tace"Kina nufin da yakura aka zo"Hajiya tace'Eh ita da matar baban yarinyar"jin haka yasa Ummi mikewa tana fadin'bari na leka "Har ta wuce ta dawo tana fadin"af nace su mu"azzam basu dawo bane banji duriyansu ba.
Hajiya tace"Inafa tare suka iso,suna ciki kila suna watsatsake gajiya ne kinfa san maiduguri ba kusa ba"batayi mgana kawai takada kai tawuce kowani taku intayi kamar ta kurma ihu takeji yau matar shettima da diyan Fadi sune zaune cikin gidan danta kai shettima yagama cutarta ta ko'ina.
.
Da sallama tashiga falon,mahgana ne zaune afalon,tana ganin Ummi ta shigo ta mike da sauri kallonta kawai tayi ta fahimci itace suhaimar data dade tana jin lbrinta daga bakuna da dama,kwarjininta yasa mahgana saurin sadda kai tana fadin"Sa..nn..u ha..Ji.Ya"Cikin rawan murya Ummi tajuyo ta kalleta akaikace tana wani kyabe baki ko tankata batayi ba, tafara taku zuwa cikin bedroom din bayan ta sakarmata dogon tsaki,bayanta mahgana tabi da kallo aranta tana fadin'"Baki ba mara da kunya ba,bala"i yanzu ina zahirah zata iya da wannan jaraban"Tafada aranta tana kuma kama baki kamar tana jinta.
Knooking tayi akofar bedroom din yakura dake ciki tana lallashin zahirah taci abinci tace"Waye shigomana,mahgana"Bata taba zaton Suhaima bace,da siririyar sallama ta shigo dakin lokaci daya suka hada ido da Yakura,da sauri yakura ta mike tana fadin"wai suhaima nake gani haka kodai idona gezo yakeman"Mirmishin kasaita Ummi tayi kafin ta tako cikin isa da takama tana fadin"Nice dai Suhaimar dakika sani yakura ba gizo idonki,
ke miki ba, kina gidan dana Mu"azzam ne"Tafada cikin izza lokaci daya tana sauke idonta kan zahirah wacce ke zaune kan gado ta cire lifayan daga ita sai doguwar rigar shaddan dake jikinta yarintarta tafito fili kirjin nan ma yanzu yafara tasawa kura mata ido Ummi tayi lokaci daya tagano kamarta da uwarta kamar an tsaga kara ankarya Tuni fuskar Ummi ya chanza tahade rai sosai tana binta da wani kallon na zaki ci ubanki ne.
Zahirah kuwa da sauri ta sunkuyar dakai jikinta yahau rawa tuni idanunta suka ciko da kwallan tun sanda Ummi ta shigo kallon farko zahirah ta mata gabanta yafadi balle dataga yadda take kallonta Allah sarki tuni tafara hawaye da hannu tasaka tana sharewa jikinta kuwa bai bar rawa ba.
Yakura dake tsaye tana kallon Abunda ke faruwa itama cike da tsausayi take kallon zahirah kan takoma ta kalli Ummi tayi karfin hali cewa"ai nasan muna gidan danki mu"azzam ne kawai mamakin ganinki nake shekaru fa dayawa"Tafada itama bakinta yafara rawa Ummi tayi mirmishin dayafi kama dana takaichi kan tace"eh hakane kam yakura ya kwana dubu kuma"Tafada ammh still idonta na kan zahiirah.
.Yakura tace"Sai alheri shikenan kin guji maiduguri ko'Tafada da sigar zolaya,hoho ai nan da nan Ran Ummi ya baci takankance ido tace"Yakura kika ce me? na guji maiduguri "Tafada bayan ta sakarmata idanunta wa"inda suka fara chanza launi Yakura ta kalleta sai yanzu ta tuna tayi fa baram barama, Kafin tayi mgana Ummi ta kariso kusa da ita tana fadin"Ai maiduguri itace garin da duk aduniya in aka ambaceta nakejin kaina cikin bakinciki wani lokacin ma har na koka,garin da tunda nasaka kafata cikinsa ban kara farinciki ba sai da na barsa,garin da aciki aka kasheman mijina wanda naso rayuwa dashi koda bamai yawa bane.! garin da nashiga kunci da takura da halin kakaniyan rayuwa duk acikinsa,kin manta yakura kece kike tallafamin da abunda zanci aboye dani da dana,? kin manta? nace kin manta ne? tafada tana zare mata ido kuma cikin tsawa.
Yakura tayi kasake kawai tana binta da kallo Ummi ta damke hannu yakura tana fadin"Shine kuma kike tambayana na gujeku alhalin kuka fara gujeman,ku,kuka fara kyamatata,saboda mene, ni bazan nisanta kaina daku ba,kuma na nisan ta duk wani ahalina,daga rabarku ba"Tafada tana sakin hannunta lokaci daya tana sakin ajiyar zuciya kafin tajuya tana kallon zahirah wacce ta rabe jikin gado tana kuka tace.
*YAKURA KINYI KUSKUREN BARIN SHETTIMA YA YA AURAMA MU'AZZAM DIYAR FADI,HAR ABADA ZAN CIGABA DA KALLONTA AMATSAYIN MUGUWAR UWARTACE, WACCE BABU IMAMI KO KADAN ARANTA,KUMA WLH TALLAHI SAI TA DANDANI KUDANTA FIYE DA WANDA UWARTA TA DANDANAMIN DAT IZ MY PROMISE*
Tagama fadar haka tajuya afusace lokaci daya idonta na fitar da kwallan bakinciki da takaichi,yakura dake tsaye itama hawayen takeyi tace' * SUHAIMA* da karfi wanda har mahgana dake tsaye falo sai da taji cak Ummi ta tsaya yakura tatako zuwa gabanta tace"Kiyi wa girman Allah suhaima kiyiwa rayuwar marainiyar Allah duba,kada ki hukunta ta kan laifin da bata araye sanda uwarta ta aikata shi,kiyi afuwa gareta don Allah,wlh da ina da yarda zanyi danayi na hana wannan auren ammh banda yarda zanyi,illa in baki hakuri don Allah suhaima kada ki cutar da Zahirah don girman mahaliccinmu "Yakura tafada lokaci daya tana fashewa da kuka itama suhaimar cikin kukan ta waigo tana fadin"Wlh bazan iya ba yakura,da zan iya da tuni na yafe musu,ammh indai Fuskar mai kama da Fadi zata zauna dani to har abada abun zai dunga dawomin duk sanda na ganta,kiyi hakuri".
Tana gama fadin haka tafice tana kuka,haka ta wuce mahgana dake falo wanda jikinta yagama yin sanyi domin ta dan jiyo wasu maganganun sama sama,hajiya dake falo ita da mu'azzam da Shureim wanda suka dawo daga taka ma abokin aikin Dr.Shureim ya wuce cikinn Abuja zashi wani guri daga chan zai wuce gida,suka ga Ummi tafito daga dakin zahirah tana kuka mai cin rai ta haye sama da sauri ta shige daki ta bamko kofa.
Muazzam yayi sauri zai bi bayanta yana Fadin"Ummi.."Hajiya tace"Dawo mu"azzam kai kasani yanzu suhaima baza ta taba sauraranka ba'Tafada itama jikinta yayi sanyi,cikin sanyi da kasala Mu"azzam ya juyo yana fadin"Hajiya zuciyata tafara Rauni da Da abunda ke damun Ummi,bazan juri ganin kukanta koda yaushe akaina ba,zan sauwakema yarinyar nan,kawai in zasu wuce su wuce da ita kawai"yafada cikin son nuna gaskiyansa.
Hajiya ta kada kai tace"Kul kada ma kasoma hakuri dai zakuyi daga kai har ita din,domin abun bazaiyi,sauki ba yanzu,sai dai ahankali kawai"Tafada cikin sanyi itama Shureim dake gefe,yayi ajiyar zuciya yana fadin"Kai ni wlh lamarin nan har ciwon kai yake sani wlh"Mu'azzam yakallesa kawai yakada kai yabi hanyan shashensa ransa na masa kuna.
Achan bangaren su yakura kuwa Ummi na ficewa mahgana tarumtuma cikin dakin tana fadin"yakura mun shiga uku wlh ganinta ma yafi lbrinta"Tafada cikin mamaki,yakura kuwa dakyar ta iya daga kafa ta karisa ga zahirah wacce ke rakube tana zubar kwallah ta rumgumota tana Fadin"yata sai dai kiyi hakuri,domin kin shigo wata rayuwa wanda babu mai fiddaki,Shawarata gareki shine sai kin zama mai hakuri da kauda kai,biyayyah da taka tsantsan,Kibita sau da kafa don *UWAR MIJINKI CE* kuma bakomai itadin goggon kice"Tafada tana sharemata hawaye.
Zahirah tadago kanta tana kallon Yakura cikin sarkakiyan murya tace"Me..Me..Yafaru..Ne,naji tana ambatom mama na ne,metayi mata? tafada cikin Hawaye kallonta Yakura tayi wata zuciyata tace"Ki sanar da ita komai domin yanzu ne ya chanchanta ta sani'" gyara zama yakura tayi tafara bawa Zahirah lbrin duk abunda yafaru daga farko har karshe ta kareshe da cewa" Dole ki koyi hakuri da kawaichi,yahna akwai aiki agabanki"
Mahgana dake gefe tace'"Ja ma kuwa wlh"Tafada cikin damuwa zahirah data daskare zaune tanajin wani lbri mai kama da mafarki takalli Yakura hawaye sun wanke mata fuska tace"Laifiin Umma ne dana Baffa ya shafe ni ko"Tafada cikin sagewa kafin tagyada kai tace"Insha Allahu zanyi,kuma zan iya,zan zauna kodan cikama baffan burinsa inafatan koda zan dawo sai in Ummi ta gafarta musu abunda suka mata"Tafada cikin karfin gwiwa ammh hawaye sun kasa tsaya mata.Mamaki yakamasu ganin yau zahirah tayi mgana har ta wuce kalma goma lalle abun babbane,kara mata nasiha sukayita da shawarwarin domin gobe tunsafe suke son komawa zahirah dai kuka kawai take ammh kuma tana nuna karfin hali,akasan ranta kuwa data tuna kallon da Ummi ke jifanta dashi sai Taji cikinta ya murda.
*****
Ummi kuwa tana shiga daki tafada bisa gado tana kuka kamar wata karamar yarinya babu abunda take tunawa sai yadda suka zo Nigeria kamar haka tare da moodu da Khamis tana mararin rayuwa mai inganci,rayuwa da masoyinta na har abada,sai gashi fadi da shettima suka suka taru suka ruguza mata dukkan Farincikinta tunda kafarta taka gidan nan,bata taba farinciki ba kona minti daya ba,shikanshi moodun bai samu daman sakewa da ita ba,har yabar duniya,ko cikin mu"azzam rabo ne kawai daga Allah,ammh da haka zai bar duniya ko kwansa bai ijeba.
Tadade tana kuka kan ta share hawayenta Tiolet ta fada ta dauro alwala,kafin tazo tadata sallahr la'ssar domim ta gabato ammh idanun nan nata sun kumbura sunyi luhu luhu alamar tasha kuka,.
Har dare babu wanda yaji duriyan Ummi hajiya ne da zulaika keta hidima dasu Yakura ko mu"azzam tunda ya shiga daki zazzabi ya rufesa Shureim ne ya dubasa yamasa allura dayake suna da first Aid box agidan,ko sallolinsa cikin dakin yayi su gabadaya jikinsa baimai dadi abinci ma sai da hajiya ta matsa kana yaci,sai yamzu yakara tabbatarwa wlh Ummi ce mahadin rayuwarsa Fushinta kadai dafi ne agaresa.
Haka dukkan zuciyoyi suka kwana babu dadi,Ummi ta kwana kuka da nadamar ma amincewa da auren datayi ma gabadaya,shiko mu'azzam ya kwana cikin zullumi da damuwa da Halin da Ummi ke ciki,shibama ta amarya yake ba,don Tunda suka zo Ko dakin bai leka ba, ba,Itako abarayin baiwar Allah Zahirah har su yakura sukayi barci idanunta biyu,maganganun Ummi kadai kemata yawo bisa kwanya wanda ko muryanta ta tunano sai tsikar jikinta ya tashi,saboda tsabar yadda ta tsorata da ita,tanaji ajikinta karshen tane yazo domin yadda taga idanun Ummi kwata kwata babu Rahama balle ragowa.
•°•°••°
Garinn Allah na waye da wuri su karime suka kammallah breakfast hajiya ta umarcesu da sudiba sukai barayin zahira amarya,wacce suma suka tashi da wuri suka gyara kansu bayan sun gyara zahirah wacce tunda tatashi ta dasa kuka,lura datayi su yakura fa, yau nan zasu barta tareda Ummi ai sai Allah.
Itama hajiyan suna gama karyawa suka fito domin Shureim nason zuwa aiki aranar shiyasa,lokacin da suka fito zasu tafi ne hajiya tashiga har dakin Ummi ta mata sallama tareda Nasiha na nunamata kawai tayi taji,ammh kasan ranta ko sauraran hajiya batayi,har haraban gidan Ummi ta rakosu bayan hajiya ta shiga gun su yakura ta musu sallama,suma suka ce yanzu zasu tafi,mu'azzam din suke jira,hajiya tama zahirah nasiha sosai kafin tafito cike da tsausayinta aranta tana fadin"Wayyo Sun sa yar yarinnya cikin mtsala."
Su karime dasu lami harda su arakiyan, Shisshiga mota sukayi Ummi da mu'azzam suna zuba musu godiya ita da surikarta Zulaika,suna tsaye suka zuba hon sani maigadi ya wangale musu get suka fice sukuma suna daga musu hannu,Ummi dake tsaye tajuya zuwa cikin gida,mu"azzam dake bayanta sanye da bakar jallabiya yayi saurin binta ya cinmata yana fadin"Ummi na barka da safiya"
Shekeke ta kallesa kan tace"Yauwa.."Agajarce kamar bataso takuma yi saurin yin gaba ta barshi cike da takaichi yabita da kallo kafin kawai ya kada kai zuwa ciki,dakinsa ya wuce direct yaje yayi wanka ya shirya cikin ,wani yadi fari mai tsantsi wanda hatta farar singlete dinsa ana gani,bai saka hula ba yafito zuwa falon,kai tsaye dakin da"aka ijiye zahirah ya tura tare da sallama.
Dukkansu suna falo zahirah na zaune akasa sanye da farin hijabi babba ta rufe jikinta kuka take ta shirba yakura da mahgana suna tsaye da alamun Nasiha suke mata,amsa sallamar sukayi suna gaisheshi da kwana cikin girmamawa ya gaishesu yana fada musu cewa basu,ganshi jiya ba, wlh suna karisowa zazzabi ya rufesa sai yanzu yaji dama dama.
Fatan samun lafiya suka mai kan yakallesu yace"Badai kuma kun shirya ba"Yafada yana kallon akwatunsu dake gefe,yakura tace"Insha Allahu kuwa mu"azzam mai zamu jira tunda komai ya kare sai fatan zaman lafiya" Jin haka yasa ya jinjina kai yana fadin"To hakane ku fito kuyi sallama da Ummi yanzu direba zai zo yakai ku tasha yasaka ku a mota"jin haka yasa yakura cewa"Yauwa dama kuwa yanzu nake shirin maka mgana zamu kai Zahirah gunta bisa al'ada" Mu"azzam najin haka ok kawai yace ya fice wanda tunda ya shigo kallo daya yama zahiran ya kauda kai aransa yana mamakin kamar mai ciwon kuka duk sanda zai ganta tana cikin kuka,ganin ba damuwarsa bane yasa ya kauda kansa yana wani basarwa.
Yana fitowan Falo yaci karo da Ummi zaune kan daya daga cikin kujerun falon ta dora kafa daya kan daya tana,girgizawa fuskarnan tata babu Annuri ko kadan,kallo daya,mu"azzam yayi mata ya dauke kai saboda yadda gabansa yafadi yana fatan kada Ummi ta gwada hali gabansu Yakura.
Suko suna fitowa yakura rumgume da zahirah,ganin Ummi zaune yasa tace"ah kina ma nan ashe"Tafada suna karisawa akasa suka zaunar da zahirah kusa da kafar Ummi wacce ta zabura ta janye kafarta tana fadin"ah karki tabani.."Tafada lokaci daya tana matsawa mu"azzam dake tsaye yakalli Ummi ya lamgwabar dakai tako banka masa harara wanda dole yakama hanyar ficewa yana kokarin kiran Ushe da wayar dake hannunsa.
Mirmishin yake yakura tayi kafin tace"Toh Suhaima mu zamuyi harama don kinsan garinmu da nisa,ga amanar zahirah nan,kin dai san ko bata auri danki ba,yatake agurinki ko,?to mudai mun damka miki ita kowani riko kikayi mata wannan ya rage naki ke kuma zahirah kiyi mata biyayyah kinji..Uwatake agunki,ko badon kina auren danta ba,Allah yabaku zaman lafiya"
Inkunce tak Ummi ta tanka sai ma kara volume din Telebijin,datayi tanayi tana kada kafa,mahgana da yakura suka kalli juna kafin su mike jikinsu asanyaye,yakura tace"To suhaima Allah sa mugana don Allah akara hakuri zahirah dai yarinyace" Tafada cikin karaya jin sun mike yasa itama zahirah mikewa tana kuka ta malkalkalesu tana fadin"zan biku,kada ku barni anan *BAN SABA BA...!"*
mu'azzam dake tsaye bakin kofar falon tundazu yaji kawai lokaci,daya tsausayin yarinyar ya tsirgamai, barinnma yadda take ta kuka tana karsu barta anan,Ummi dake zaune ta kwalama karime kira,da hanzari karime ta fito tana fadin"Gani hajiya" cemata tayi taje cikin dakinta kan side drower zata ga kudi da wata leda ta daukomata,da hanzari karima tatafi ba jimawa sai gata da rafar kudi yan dubu dubu har guda biyu,da leda cike da kaya, duka tahada ta mikama yakura tana fadin"mungode sosai,da cika alqawari,ga wannan babu yawa,kiyi amfani dashi" yakura tace"Suhaima kuma harda,wani dawainiya"mirmishi Ummi tayi kan tace"a"a ba dawainiyyah bane,kinsan alheri danko ne baya faduwa kasa banza alherinki gareni har yau nakasa mantawa dashi.
Godiya yakura tayi mata,.mu"azzam ne yayi gyaran murya yana fadin"Direba fa ya iso,tundazu yana jiranku"Jin haka yasa karime daukan musu kayan zuwa farfajiyan gidan,ai zahirah data ga da gaske ne tafiya zasuyi ai sai ta kwakumesu tana kukan zata bisu tun yakura na lallashinta hartagaji,Ummi dake gefe takaichi ya cikata batason sadda tace"Ke..."Cikin tsawa ai da hanzari tadago jajayen idanunta tana kallonta harara ta sakarmata kan tace"Dawo ki zauna makira,ai zama yazama dole tunda kika yarda aka daura auren"Tafada tana nuna mata hannu.
Jikin zahira na rawa ta saki yakura hawaye na bin Fuskanta takoma ta zauna,suma cikin hawayen idon suka bita da kallo lokaci daya suka daga mata hannu suna fadin"sai wani lokacin yahna"da sauri suka juya barinma yakura da kuka yazomata,har suka fice daga falon ba wanda yakara waigowa,suna fitowa ansaka kayansu amota sallama kawai sukayi da mu"azzam bayan yabasu dubu hamsin gakuma kudin mota dayabama,ushe wanda yace ya tabbatar ya sakasu a mota tukun,cike da kewa da tsausayi mai girma azuciyarsu Motarsu ta fice daga gidan.
Shima yadade tsaye jikinsa amatukar sanyaye kafin yaja jiki yakoma falon,yana shiga yaga zahirah durkushe gaban Ummi ko kwakwaran motsi takasa itakuma tana ta kada kafa ita kadai tana huci,ganin haka yasa ya sulale zai shige barayinsa sai ji yayi Ummi ta kira sa" *IBRAHIM..* tafada cikin kakkausan murya.
*Comment*
*Share*
*Vote*
*Jamcy bby*
[18/08, 14:18] 80k: *🌺UWAR MIJINA..!*🌺
_(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)_
*Alkalamin:JANAF*
*Wattpad:Janafnancy*
*Dedicated to my blood Sisters JANAF*
*Intelligent writer's Asso*✏
*NO 13*
Karisowa tayi lokaci daya tana kafesa da ido,Saurin basarwa yayi da razanar da yayi yana fadin"Wlh Ummi wani fayel na manta shi ya dawo dani"Yafada yana daukan fayel din, kallonsa tayi kamar zata tanka sai kuma ta fasa kan kujera ta zauna batare da tayi mgana ba,shima ficewa yayi yana fadin"Sai na dawo Ummi na,da lebe ta amsa tana rakashi da ido.
Zahirah ko tana shiga daki tasaki ajiyar zuciya lokaci daya kuma tana sakin mirmishi data tuna sanda tayi mai Wurgi da fayel saboda tsoron Ummi kan kujera tafada tana lumshe ido tana tuno Fuskar Mu"azzam lokacin daya sakarmata idanunsu lokaci daya taji wani yanayi yana shiganta batason kallon idanunsa saboda suna rikitata ainun,kara gyara kwanciya tana lumshe ido har barci ya kwasheta bata sani ba.
Sai wajen azahar ta farka gabanta na faduwa,kada yazo Ummi ta nemeta sallah kawai tayi tafito falon,Ilai kuwa da Ummi taci karo da ita zaune afalon,cikin rawan jiki ta zube tana gaisheta Ummi ta bita da kallon mai kama da harara,kafin tace"Ke dama kina ciki tun dazu,uban wa kika barwa sauran aikin"Zahirah tayi saurin cewa"A"a sallar na shiga nayi Ummi.."Tafada zuciyarta na tsinkewa,tsaki Ummi tayi kan ta kauda kanta ganin haka yasa zahirah mikewa tawuce kichen Ummi ta bita da kallon wani takaichi na kulleta kamar tatashi ta shakota takeji gyara zama tayi tana,fadin"Allah ya isa Shettima cuta kam angma cutata.
Ranar matare dasu karime ta wuni,sai da mangriba tayi kana,ta tafi dakinta ta daura alwala tayi sallah dayake taci abinci dasu karime,kallo ta danyi kan akira issha"i tana idarwa,tabi lafiyan gado saboda tagaji sosai.
*Washegari*
washegari takama Friday ce,tun jiya Ummi tafadamai yau Zaria zata ta duba Hajiya dakuma yimata bangajiyan biki,Tun safe ta kammallah shirinta Ushe yayi ma waya kan yazo yakai Ummi dayake yau bazai Fita Office ba,har Ummi ta tafi zahirah na daki bata sani ba,domin tunda tatashi tayi sallar Asuba,takoma wani barci mai Nauyi ya dauketa wanda ta kasa tashi sai wajen 9 tafarka tana salati gabanta ko yafadi saboda Tsoron Ummi agurguje tayi wanka ta saka riga da sikat na wani less ja da baki,hijabinta ta saka ta fito falon ganin bakowa ya sakata sum sum ta wuce dakin su karime,suna ganinta suka hau gaisheta,ta amsa tana fadin"Yau na makara,Allah sa Ummi bata nemeni ba"Kallonta karime tayi kan tace"sha kuruminki Yata Yau Ummi tafiya tayi,Zaria taje tun safe"Wani siririn ajiyar zuciya Zahirah tasauke ranta yayimata sanyi sai ta ji tasamu Natsuwa,nan ta shige cikinsu suna hira.
Tashi tayi ta hau sama ta gyarama, Ummi daki kafin ta sauko tafara kokarin gyara falon tana cikin goge Tibin dake jikin bango Falon ne taji gyaran muryansa,wanda ita tuni tabada amanna ga aikin datakeyi,Saurin juyowa tayi sai taci karo dashi cikin riga da wando kaftan Deep blue kansa babu hula kafafunsa ma wani takalmi ne budadde,hannunsa sanye da agogon na kamfanin Rado,duka idanunsa ya sakarmata ayayinda duka hannuwansa ke cikin aljihun wandonsa.
Ganin ya tsaya yana kallonta yasa tayu Saurin dukawa tana fadin"Ina kwana ya Mu'azzam"Kallonta yayi cike da mamaki kan yace"Waya saka ki wannan aikin? yafada muryansa na nuna alamun baiji dadi ba,dukar dakai tayi kafin tace"Ni nasaka kaina..",tafada cikin dakewa kuramata ido yayi,tayi Saurin dukar dakai saboda yadda takejin idanunsa akanta.
Bata rai yayi kafin yatako zuwa kan kujera zama yayi yana kwalama karime kira"Baba.."Yafada cikin muryansa mai amo da burgewa,Karime dake daki ta amsa ta fito jikinta na rawa,ganin zahirah Durkushe agaban yallabai yasa jikinta yafara rawa,itama durkushewan tayi tana Fadin"Gani Ranka ya dade,Allah yasa ba laifi nayi ba"Kallonta yayi fuskarsa babu wasa yace"Baba waya saka yarinyarnan goge goge,"Yafada yana kallonta.
Daburcewa tayi tadago tana kallon zahirah wacce tayi mata wiki wiki da ido,dukar dakai Tayi kafin tace"Um...."A"a ni fa na saka kaina ko Mama"Ta katse Karime lokaci daya tana kayfamata ido,Karime tace"Eh..Eh hakane ita tasaka kanta wai tagaji da zama haka"Tafada tana dukar dakai saboda batason kallon Fuskar yallabai balle yagane tayi karya.
Shiko tuni ya ganosu,har kayftamata idon datayi yana lura dasu,mirmishin gefen baki yayi kafin yace"Ok yanzu nace ki karba aikin,ki karisa kuma daga yau kada ku sake bata wani aiki mai Nauyi,saboda batayi girman dazata dauka ba"Yafada yana basarwa Da toh karime ta amsa kafin ta karbi aikin Tafara karisawa,shiko wayansa ya fiddo yahau latsawa itako Tana gefe kanta duke tana wasa da adon leshin dake jikinta ta wutsiyar ido yake kallonta aranshi yana mamakin wayo da kuma hankalin yarinyar yasani sarai Ummi ce tabada Umrnin ta dunga yin wannan aikin ammh har ta san Tarufe bata so yaji,lokaci daya yaji Yarinyar ta burgesa matuka kuma ya yaba da hankalinta.
Sunan zaune jugum har karime tagama abunda zatayi ta fice,ganin Fitan karime yasa itama ta mike sum sum zata koma daki azatonta baya kallonta hankalinsa na bisa waya,kawai taji yace"Ina zaki? ai ban sallameki ba,dawo nan ki zauna"Yafada still idonshi na bisa wayar jikinta asanyaye ta dawo ta zauna ammh kan nan na duke,kallonta yaketa Wutsiyar ido tsaf lokaci daya ya karemata kallo doguwace siririyace bata da kiba,fuskarta doguwace mai dauke da idanunta ma tsaikaita,sai dan bakinta daidai misali babu abunda yafi burgeshi da ita sai zanenta na bare bare dake gefe da gefe kumatunta,sun mai kyau sosai har baisan ya shagala da kallonta ba,har sai da taji daga jikinta ana kallonta ta dago kanta karaf,suka hada ido,dashi,Kuramata ido yayi itama sai taji Takasa dauke idanunta akansa tanaji kamar wani abu ke zagaye duk ilahirin jikinta idanunta Tuni sukafara tara kwallah,lokaci daya taji kamar ana mata waiwayi, Saurin kauda kanta tayi zuciyarta na tsinkewa aranta tana fadin"Yana da kyau..."Mirmishi yayi still yana kallonta kan yace"Ya kewar gida,nasan kina kewan su ko" cikin sanyin murya ya furta hakan.
Jin haka yasa tadago tana kallonsa kan tadan murmusa kawai batayi mgana ba,kallonta ya sakeyi yaga tana ta mirmishi ita kadai,shima murmusawa ya sakeyi kan yace"Hop yanzu kindaina kuka ko? tunda nan din ma gida ne,ga Ummi gani kuma komai kike bukata ki tambayemu zamu yi miki kinji"Yafada idanunsa na kanta dagowa tayi ganin yana kallonta yasa ta gyadamai kai kawai tadan mirmishi.
Mamaki ya kamasa baisan sadda yace"Baki mgana ne? ko nine ake ma rowan muryan"Jin haka yasa ta girgiza kai kafin ta bude baki tace"Ina yi mana.."Tafada kamar ansata dole,Jinginar da kansa yayi bisa Cussion yana fadin"To kidaina mun mgana dakai Juz open ur mouth and Talk to me.."yafada yana lumshe ido,itakuwa bakinsa ta kurama ido tana kallon yadda yake magana,jin batayi mgana ba yasa ya bude ido karaf ko yakamata tana kallonsa,kunya yakamata ta dukar dakai tana rufe fuska da hannuwanta.
Shi dariyama take bashi,kallonta yayi yana Fadin"Kina son mkranta.."Jin abunda yafada yasata saurin dagowa lokaci daya tana washe baki,har hakoranta suka bayyana tare da dimple dinta mai karamata kyau,shagala mu"azzam yayi da kallon tsabar da kuma inda mirmishi hade da dariya yakema mace kyau,Masha Allahu kawai yake Furtama shima baisan yaushe yake kallonta ba,haka kurum yakejin dadin kallonta tana dariya.
"Makaranta..Ina so yaya,zaka sani ne"Tafada cikin nuna abun na ranta,rausayar dakai yayi kafin yace"eh mana zan sakaki indai zaki maida hankali,agida ajinawa kike? yafada yana kallonta gyara zama tayi kan tace"SS1 nake kafin acireni.."Tafada cikin Rauni,kallonta yayi kafin yace"Meyasa aka cire ki..? kallonsa tayi kafin idanunta su ciko da hawaye tace"Ba..Ba baffa bane yace nan garin xa"a kawo ni ba,kuma wai zaka sakani kowacce makranta nake so,wai haka"tafada da sigar yarinyata lokaci daya ta goge hawaye da dayan hannunta.
Gyada kai yayi yana fadin"Eh mana zan sakaki mkranta insha Allahu zakiyi karatu har ki gaji da kudina,kuma da aljihuna nayi miki alqawarin rayuwa mai inganci matukar kika kasance mai hakuri ga dukkan al"amuran da zasu gabato mana tsakanin ni dake'"Galala tamai da ido alamar bata gane ina ya dosa ba,jinjina mata kai yayi kafin yace'"Kan Ummi na,nasan kinsan komai basai nayi dogon zence ba,don Allah kiyi hakuri da dukkan abunda zata miki,na lokaci ne,kuma banison kowani yazo kinunamai abunda ke faruwa plz and plz keep d screet mu kadai kawai,duk da abunda kikayi, dazu ya tabbatarmin bazaki bani kunya ba"Yafada yana kallonta,ga mamakinsa kayatattacen mirmishi ta sakarmai kafin tace"Indai wannan ne kada kaji komai,Ummi kamar Uwa take aguri,duk abunda zatamin bana ganin laifinta,fata Allah yasa ta canza ta gane gaskiya.."Tafada muryanta tafara rawa kawai sai ga hawaye sun zubomata,Kallonta Mu"azzam yayi yana mamakin kaifin basiran yarinya at her age haka,bata Fuska yayi kafin yace"to miye na kuka kuma? ke wai don Allah na tambayeki kuka bai miki wuya ne,koda yaushe kina cikin kuka"Yafada yana tsuramata idanunsa.
Girgiza kai tahau yi,hankicif dinsa dake aljihunsa ya dauko ya mikamata yana fadin"Kinga Wipe ur Tears..Bani son kuka nan,daga yau'"Karba tayi tana share hawayen dashi kallonta yake yana ayyana abubuwa dadama,bai samu zarafin mgana ba,wayar dake hannusa ta dau kuwwa..Sunan Ummi ya bayyana kan Screen din bai tsaya,ba ya mike bayan ya dauki wayan yana Fadin"Ummi na badai kun isa ba"Zahirah jin an ambaci Ummi tayi hanzarin mikewa bata gama Fahimtar waya bace tafada daki da Sauri dauke da hanki din daya bata jikinta na rawa,itafa ko mala"ikan Mutuwa bata tsoro kamar yadda take tsoron Ummi.
Da ido ya bita yana mamaki yadda take tsorata in taga Ummi,ko taji sunanta,bai wani tsaya tsananta Tunani ba yawuce barayinsa suna cigaba da waya da Ummi,koda suka gama waya yana duba agogo yaga lokacin jumma"a har ya kusa,baki ya rike yana mamakin yadda ya biyema yarinyarnam har yana neman makara zuwa masallaci,alwala ya daura kan yasaka hulansa ya Fito,su Sani da Falalu suna ta kwasan gaisuwa,amsawa yayi cikin Fara"a kafin yafada mota,yau mazajen da kansu sukayi Driving Sani ya budemai get ya fice.
Itako Zahirah adaki murna ta cikata Ya mu"azzam yace zai sakata mkranta duk sanda ta tuna da haka sai tayi dariya ita kadai,haka kurum ta nanike ma Hanki din nan,Ta shinshinashi yafi akirga kamshin Turarensa Na Azzaro Visit,shi yakemata dadin shaka,takasa ijiyesa,saboda kada kamshi yayi nesa da"ita tana idar da sallah ta haye gado hanki din,na kan kirjinta tana shakar kamshin barcin yayi awon gaba da ita,cike da mafarkin Dan Ummi, *MU'AZZAM*
Mu"azzam bai dawo ba sai dare,koda ya dawo Tuni zahirah tadade da yin barci,yau tasamu sake,batayi aikin komai ba,su karime kota matsa basa bata,sunce ta huta tunda Ummin bata nan,abinci kadai taci tabi lafiyan gado,ammh just imaging tana rumgume da hanki din Mu"azzam😂 _Zahirah kar ki saka kanki cikin wahala,wlh Ummi zata iya kasheki ni ba ruwana_😛
Shima din a koshe yake Coffea kawai yasha yabi lafiyan gado,dayake sunyi waya Da Ummi tace hajiya ta riketa sai ta mata Weeked kana zata dawo,sai lokacin tafado mai Arai,mirmishi yayi shi kadai daya Tuna shirmenta,Fuskarta na dawomai lokacin datake dariya,da Tunaninta shima ya kwanta wanda ya rasa dalilin haka,ammh sai ya barshi a tsausayinta ne ke dawainiya dashi,da kuma yadda zai cikama yarinyar Burinta don ya lura tana matukar son karatu aranta.
****---*
Da garin Allah ya waye,Zahirah an samu sake barcinta tasha ta hantse,don Tunjiya su karime suka sanar da ita,tunda Ummi takai dare to, bazata dawo ba,shiyasa bata damu ba sai 9 ta tashi,wanka kawai tayi ta gyara shashenta,wata doguwar riganta ta saka ta Atamfa,wacce cikin kayan da Bahna dinta yamata ne,ta daura dankwalinta ta zubo da gashinta baya,Falo ta Fito tana tafiyanta cikin sanyi,mu"azzam dake kan,Dinning yana breakfasat Tun fitowarta kamshin Humranta ya daki hancinsa,ya lumshe ido yayi, kafin ya dago yana kallonta itabatama Lura dashi ba,direct ta wuce zata shashen su Karime,muryanshi taji asama yana kiranta.
*ZAHIIRAH..* cikin husky voice dinta Tsam tayi da Ranta saboda yadda Sunan yadaketa,sai taji duk duniya babu wanda ya iya kiran Sunanta irinshi,waigowa tayi Asanyaye Tadora idanunta bisa kanshi wanda yake zaune yana karyawa,yana sanye da bakin wando da wata farar Riga na kamfani Armani,gashin kansa ya kwanta yayi kuf,Fuskarsa tana Fitar da wani Annuri.
Kwarjini yayi mata shiyasa takasa karisawa,sai shine yace"Ki kariso mana.."Yafada baya kallonta cikin sanyin jiki ta kariso kusa dashi,ammh kafafunta suna hardewa kamar zata fadi,basarwa yayi yana jamata kujera yana fadin'Be carefull,Set here..."Yafada yana nunamata gun zama a dofane ta zauna tana wani sunne kai,ta gefen ido yake kallonta,kafin yace"Ba gaisuwa.."jin haka yasa tayi saurin zamowa tana fadin"Ina kwana.."Amsawa yayi da "Lafiya,ya kika kwana"Da lebe ta amsa,ganin yadda bata natsu ba shiyasa ya mike yana fadin"Ki karya.."Daga haka yatashi ya karisa Falon ya fada kan daya daga cikin kujerun falon,yana dora kafafunsa kan center table Din ,dake kusa dashi,ammh hankalinsa yana gun zahirah,yana kallon yadda take komai kamar mara lafiya,tea kawai tahada sai buredin wanda aka soya da kwai,shima din cikin sanyi takeci,kamar batason ci,yana lura da ita,Aransa yace dole ma ki zama wata lazy baki cin abinci,tashi yayi batayi Aune ba,sai ganinsa tayi akanta ya dauki Filet ya zubomata Ferfesun kaza,ya ijiyemata agabanta Filet din Buredin da kwan,ya dauka bayan ya sake lodamata,bai kalleta ba yace"Oya Eat..'Yafada ba alamar wasa bayan yaja kujera ya zauna.
Dagowa tayi tana kallonsa ganin yadda yahade Fuska yasa ta tsorata sai ta fara kurban shayin tana cusa buredin ammh idanunta fa sunkawo kwallah,lura da hakan da yayi ne yace"Ki maida hawayenki,wlh kika bari suka zuba zan saba miiki"Jin haka yasa tayi saurin maidawa tana tura buredin abaki,shima fefersun kaza taci kadan bada yawa ba,kallonsa take tama marairaice Fuska,lura da hakan dayayi ne yasa yace"Kin koshi ne..."Saurin daga kai tayi mikewa yayi yana Fadin"ok..Daga haka ya wuce shashensa ko kara kallonta baiyi ba.
Da kallo ta bisa Aranta tana mamakinsa yadda lokaci yake rikidemata,ajiyar zuciya ta sauke tana kallon inda yatashi kamshin Turarensa take shaka tana jin wani sanyi Aranta,dakyar ta iya tashi ta karisa shashensu karime suka gaisa,tana zaune suna ta hiransu har bayan azahar kafin takoma dakinta itama tayi sallar,tana idarwa tabi lafiyan gado bata tashi ba sai bayan la"asar,wanka tayi da sallah kafin tafito zuwa falon,da Mu'azzam taci karo wanda ke kwance kawai bisa kujera idanunsa suna lumshe kamar mai barci,ganin haka yasa ta lallaba zata koma daki,kawai taji muryansa cikin sanyi yace"Come back.."Cak ta tsaya tana maida Numfashi ,tafiya tafarayi kafin ta kariso kusa dashi..,"Sit.."Kawai yacemata bai ko bude idanunsa ba,jikinta Asanyaye tazauna akasa tana sunkuyar da kanta,ta dade zaune kanzil bai cemata ba,tun tana kunya kunya harta saki jiki tana kallon wani idian film da Zee World ke nunawa,shiko duk motsinta yana kallonta haka kurum take bashi tsausayi,haka suka zauna babu mai ma wani mgana ita tana kallo shiko yana kwance abunshi,har sai da aka kira mangarib kafin ya fice zuwa massllaci,itama zahirah tashi tayi taje tayi sallah,tana idarwa ta dawo falon saboda taga yadda zata kaya afilm din,shiyasa tama manta da kashedin Ummi ta haye kujera tana kallo abunta tana mirmishi,sai da akayi Issha'i kana ya shigo,haka yazo ya sameta,lalle kallo yayi ma zahirah dadi,shima nan ya zauna tare da ita,system dinshi ya dauko yahau bincike aciki,itakuma tana kallonta,Sai da 9 tayi kana yace taje ta kwanta,dole ta mike ta mai sai da Safe ta wuce dakinta.
Ko a washagarima haka ta kasance Mu"azzam yana kula da Zahirah daidai gwargwado sai gashi cikin kwana biyu harta fara sakin jiki dashi,har suna dan Fira,duk da bamai Tsayi bace,Weekend din gabadaya bai Fita ko"ina ba,inba massllaci zashi ba,yana gida kuma suna tare Da Zahirah dan zaman dasuke tare,yasa ko bata Fito ba baijin dadi sai ya aika karime ta kiramai ita,tazo ta zauna koda bazai mata mgana ba,
Yau din ta kasance lahadin karshen Sati,suna zaune Falo shi da zahirah wacce ke gefe kan kujera tana sanye da riga da sikat na wani material,shiko yana gefe kishingide kansa bisa cussion Ammh idanunsa alumshe,shi yabawa Zahirah daman kuramai ido tana wassafa kamaninsa Aranta,Ta shagala da kallonsa wanda har Ummi dake tsaye kanta bata Sani ba,sai da taji an zuba mata wani gigitattacen mari wanda Sai da ta Wutsinlo bisa kujera lokaci daya tana fashewa da kuka,Bata tsorata ba,sai da tadago ido ta zubasu kan Ummi wacce ke tsaye idanunta jawur tana huci,Mu'azzam yayi Saurin bude idanunsa yana kallon Ummi kafin ya mike yana fadin"Ummi yau..."Tas..Tas..Ta tsinkeshi da mari lafiyayyu har guda biyu,da hanzari ya dafe gun yana bin Ummi da kallo yadda take wani girgiza kamar wata mai aljanu sabon kamu.
*Comment*
*Share*
*Vote*
0 comments:
Post a Comment