Kwanaki biyu kenan da dawowarsa,qarfe sha daya saura na safe ya shigo sassan hajjan,a lokacin abba babba abba yusuf da abban tsakiya duka suna falon hajjan,zahra na kitchen tana wanke kwanukan data hada musu breakfast,don tun safe sukazo suna ta lissafi,na haqqin Allah da za'a fitar cikin kudin hajja da ake juya mata,lokacin fiddawa yayi.
Tunda ta gama ta zuba masa nasa a fulasan da ake zuba masa kamar koda yaushe,kwanaki biyu kenan tun randa ruwan saman ya tareta hajjan bata sake bari taje din ba,saidai ta bayar a kai masa kamar yadda ya fada,ita kam zahra nata idanu ne,saboda tasan halin hajjan,katafila ce sarkin aiki,takan kowa take bi idan aikinta ya tashi.
A ladace ya cire takalmansa ya qaraso gabansu ya tsugunna,daya bayan daya ya gaidasu,yaji dadin samunsu a tare,tunda yaje bai samesu a sassansu ba dama
"A kawo maka abincinne?" Hajja ta tambayeshi,tunda ta lura kwana biyu wani shareta yake,tun ranar nan,itakam ko a jikinta,tunda tasan koma meye qarshe shi zaifi kowa mora
"A'ah...zanyi magana idan za'a kawomin din....magaa nakeso muyi dama" abbansa ne ya daga kai ya dubeshi yana ninke takardar daya gama rubutu akai,abba yusuf ne ya amsa
"To Allah yasa lafiya" qasaitaccen murmushin nan nashi na gefan baki yayi sannan yace
"Lafiya lau abba.....cikin yarjewar ubangiji inason satin nan da zamu shiga in sha Allah mu wuce umara,nida hajja da abba na.....da kuma mama" Wani farinciki ne ya bayyana sosai saman fuskar hajja,burinta a duniya kenan ta koma qasa mai tsarki,duk da cewa taje har sau biyu,hajji daya umara daya,amma wajene da babu musulmin da bazaiso ya dawwama ma a can ba,lallai ba shakka haidar din wata kyautar Allah ce cikin iyalinta,soyayyar da yake mata mahaifi da mahaifiyarsa kai dama ahalinsa gaba daya abarso a sameta ce cikin zuciyar kowanne daga cikin dangi,don samun dorewar qaunar juna da danqon zumunta.
Kowanne a parlour din son barka yake gami da sanya masa albarka,tare da yaba wannan namijin qoqarin sa yayi
"naso ace na qara da abban tsakiya da abba yusuf,to amma kudin hannuna sun qare,ba zasu isa ayi komai na mutum biyu ba,amma in sha Allah sune a lissafina na gaba" nunawa sukayi babu komai,su da dan uwan nasu duka abu dayane,sannan suna da yaqinin da yardar Allah shi mai kai kowa ne cikin dangi idan da halin yiwuwar hakan.
Sun dan jima anan suna tattaunawa cike da farinciki,kafin daga bisani suyiwa hajja sallama kowa ya nufi wajen neman kudinsa,sai falon ya rage daga hajjan sai haidar din,sai kuma zahra dake kitcehn tana dora abincin rana kawai don idan ta zauna ta huta gaba daya,inna gaje ciwon qafa ya hanata zuwa aiki tun shekaran jiya.
Kira hajjan ta qwalawa zahra tace ta fito da abincin haidar,ta zata kai masa za'ayi,batayi tunanin yana falon ba don haka ta fito gaba gadi haka abunta,wata straight gown ce a jikinta,wadda tayi mata das a jikinta.
Da kallo ya bita bayan ta gaidashi ta aje masa abincin ta koma,suna hada ido da hajja ya hade rai tsam sannan yace
"Yanzun haka take yawo anan?"
"To uban mutane,sai akayi yaya?ni bama wannan ba,tafiyar nan da zahra'u ya dace ayita,don baka je dakin Allah haka ziqau ba,kabar kyautar da yayi maka a gida ba" kallonta yayi ya soma zuba abincin yau da kanshi ba tare daya nema wani ya zuba masa ba
"Yanzu dai babu kudi hannuna,saidai nan gaba idan Allah yayi" hade ranta tayi sosai
"Eh na sani ai ubana.....ni zan biya mata da kaina,saboda haka a sama mata komai da komai,idanma za'a dage tafiyar sai lokacin data samu to a dage din" baice mata komai ba,dama kuma tasan halinta ba zaya tanka ba,don haka taci gaba da sabgarta kawai,tana ta kiran 'yan uwa daya kamata su sani tana gaya musu batun biya mata umarar,abun mamaki kuma don iya qarfa qarfa irin na hajja sai take hadawa da zahra kan harda ita za'a tafin,shidai yana zaune yana cin abinci yana kuma kallon ikon Allah,zahra kuwa na kitchen bata ma san wainar da ake toyawa ba.
Sai da ya gama cin abincinsa sannan ya miqe ya fice,dole zaiyi maganin hajja,zai kawo qarshen wannan mulkin mallakar nata,zata ga nasa qarfin ikon akan aurensa,don haka tun a motarsa driver na jansa ya kira anty alawiyya.
Bayan sun gama gaisawa tayi masa godiya da addu'ar qaruwar aziqi kan umarar da ya biyawa iyayensu saiyayi mata maganar da ita ta sanya ya kiratan
"Kaya nakeso a hadamin,irin wanda ake hadawa amare a akwati" dariya ce taso kubce mata amma ta danne,don kada tayi dariyar ta jama kanta jagwal,duk da cewa ita ke gaba dashi
"Ohkey.....lefe kenan....kaman na nawa?,kuma akwati nawa?"
"Akwati bakwai is okey,nayi hidima da kudaden hannuna....amma banison kaya low quality please,designers kumadd high quality"
"In sha Allah babu matsala"
"Please su zama ready kafin na dawo"
"To shikenan....babu damuwa" saiya yanke wayar ya aje gefa,ya maida idanunsa kan titunan da suke wucewa.
23/10/2021, 08:50 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 40
Wayar ya sake jawowa,wata number ya sake laluba,wanda suke masa aikin ginin filin da ya siya a nan,yadan jima da siyan filin,tun farkon fara aikinsa ya hada albashinsa ya siya,hakanan da kadan da kadan ake aikin gininsa,yadda zaifi masa sauqi bazai wahala ko ya kashe kudi masu yawa ba lokaci guda,zuwa yanzu ginin yayi nisa qwarai,don abinda ya rage ma sauran abubuwan da ba'a rasa bane,da farko yayi niyyar ma ya kammala gidan ya saida,amma da yayi tunani sai yaga,bashi da mazauni kenan duk sanda yazo ganin gida saidai a cikin gidansu,auren da aka daura masa da zahra yasa ya fasa saidashin kwata kwata,saboda koba zahra ba dama dole zaiyi aure,idan kuma yayi auren zai dawwama zuwa gidansu ya zauna?,dole yana buqatar muhalli.
Da kamfanin yayi magana,ya shaida musu abinda yake da buqata cikin gidan,suka gaya masa kudinsa da zaya bayar,yayi musu alqawarin turawa zuwa qarshen wata,a sannan suna can basu dawo ba kenan a yadda ya lissafa,yana saka ran kuma kafin su dawo din an kammala komai,saiya aje wayarsa yana ci gaba da lissafe lissafensa cikin ransa,zuciyarsa fes,yana jin wata nutsuwa da sukuni suna ratsashi.
******** **** ********
Bai sakewa hajja zancan tafiyar zahran ba,kamar yadda bai amshi kudinta ba,tayi tunanin waskewa yakeson yi,saita matsa da mita da qorafi,sai ranar daya sameta zaune ya miqa mata komai da komai na tafiyar zahran da aka kammala bayan an dage tasu tafiyar da sati daya.
Kwalla ce ta qwacewa hajjan,abinda bai taba zaton gani daga idanunta ba,duka shida zahra dake zaune a gefanta suka zuba mata ido,jikinsu duka yayi sanyi
"Allah yayi maka albarka,ubangiji yaci gaba da gin riqo da hannayenka,Allah ya kula maka da rayuwarka,yadda kake taimakon al'ummar annabi kake kula da iyayenka da 'yan uwanka....Allah yayi maka kyakkyawan sakamako,haidar....kaida zahra Allah shine shaida....kaf cikin jikokina babu wadanda suka shiga raina kamar yaku,hakan ya sanya nan duniya tun kuna da qanana bani da burin daya wuce Allah ya hada kanku kuso juna ku zama miji da mata,sai wani al'amari me daure kai ya soma gudana a tsakaninku,amma hikima ta ubangiji da baya maida addu'ar bawansa,sai gashi ya kawo hadin aurenku ta fuskar dani kaina ban tsammata ba.....haidar....ga zahra nan,a yau zan baka amanarta...ka riqe amanar zahra,kai da ita duka nasan halayenku...hakan ya sanya nake da yaqinin dukkanku kun dace da junanku,zaku gasgata abinda nake fada din,zahra,haidar yayanki ne kuma mijinki,ki bishi ki masa biyayya,ki masa biyayya kamar yadda musulunci ya tanada,Allah ya albarkaci rayuwarku" cikin sanyin jiki dukkansu suka amsa da amin,saita miqawa zahra passport din hannunta
"Zaki tafi umara tare damu,mijinki ya biya miki" kamar a mafarki taji fitar furucin daga bakin hajjan,saita daskare a zaune tana jujjuya passport din,yau itace zata qasa me tsarki ta qarqashin ya haidar din?,mutumin da take masa kallon mara qaunarta,wanda bayason yaga suna farinciki da walwala?,mutumin da take kiranshi da mara ALKIBLA?,mai baudadden hali,wanda sam ALKIBLARSU bata zo daya ba,ashe ta sanadinsa zata je taga ma'aiki?sai qwalla ta cika mata idanu,ta sake matsawa kusa dasu muryarta na rawa saboda farinciki
"Na gode,Allah ya saka da alkhairi,ya qara budi,ubangiji ya biya da jannatulfirdaus" idanunsa ya lumshe yana jin dadin muryarta hade da dadin addu'ar data yi masa ya amsa da
"Amin".
"Wannan kadanne daga alkhairinsa,alkhairin nasa kuma da zaya shiga rayuwarki matuqar kika ci gaba da bin maganar magabatanki,matuqar kika ci gaba da daukar zancansu da muhimmanci,na taba gaya miki,haidar ba irin sauran maza bane gama gari,tun a shekarun quruciya na gama karantar halayyarsa tsaf,tun kafin na haifeki nake sha'awa inama ina da diya da idan ya girma zan bashi ita?,yana da boyayyun nagartattun halaye da dabi'u,yana da sauqin kai da sanyin hali,yana da tausayin mace.....amma dukka ba kowa ke iya karanta da gane hakan ba,saboda matuqar zaka mu'amalanceshi daga nesa,to tabbas zaka masa fassarar mai ra'ayin riqau,mai kakkausan hali,mara tausayi ne,mai zafi da saurin fushi,eh aliyyu yana da ra'ayin riqau akan gaskiya,yana da kafiya kan abinda yasan shine dai dai,yana da fushi idan yasan an sabawa dai dai ko doka,yana da rashin tausayi akan azzalumin mutum mara imani,amma matuqar baka da irin wadan nan siffofin,zakaji dadin zama da haidar fiye da kowane dan adam.....zan baki tips na zama da haidar din,a matsayinki na diyata,ni kuma uwa a gareshi da tasan halayyarsa,ba don ki mallakeshi ba,sai don ki masa biyayya ku samu zaman lafiya da qauna me dorewa" wadan nan sune lafuzzan umminta a sanda take shaida mata batun tafiya da ita bayab ta miqa mata passport dinta ta sanya masa albarka,zama ummin tayi ta dinga zayyana mata abubuwa masu matuqar amfani a rayuwarsu,har zahran ta dinga mamaki da kunyar hakan,saidai ta lura ummin ko a jikinta,saboda ta sani tana gyara rayuwar diyarta ne,tana kuma inganta rayuwar haidar dinta,aikine da takejin ya wajaba a kanta a matsayinta na uwa
*_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT KANO_*
Da motoci hudu duka aka dunguma aka tafi rakiyarsu filin jirgin saman don wucewa qasa me tsarki,suna ajesu sukayi bankwana dasu aka maida motar gida,dama daya ta abba yusuf ce,daya ta abban tsakiya,zasu wuce kuma kasuwa ne abinsu,sauran biyunne na haidar,mustapha yaja daya,ya shamsu da suke tare da ya sadiq sukaja daya suka koma gida da sauran yaran gidan da aka taho dasu.
Gaba daya wani irin nauyi takeji,surukutar abba babba da mama takeji tana mamayarta,ko hira ake bata iya magana cikinsu,dama shi haidar din ba wani gwanin magana bane,sau tari wayarsa tana hannunsa ne yana faman danne danne,wanda baya wuce duba labarai,ko duba saqonni da suka shafi aikinsu.
Yana ankare da yadda ta kasa sakewa din,nutsuwar data sakeyi ta bashi mamaki,kusan tun tale tale yasan zahra cikin yaran gidan,tayi shuhura wajen aikata laifi da samun kariya daga wajen hajja da a wancan lokacin yake ganin daure mata qarqashi kawai takeyi,abinda ya janyo rashin jituwarsu kenan,yaci alwashin shi bazai bari ta buwayi kowa ba,duk da girma ya sake canzata qwarai,amma a yau din ta sake canzawa,wata kamala ta musamman ke kwaranya tun daga fuskarta zuwa jikinta.
Qafarshi daya dora daya kan daya ya sauke bayan ya gama karantarta,ya duba agogon hannunsa,akwai sauran lokaci kafin a nemi passingers din,don haka ya miqa a nutse yana daukar hularsa dake ajjiye gefe ya soma takowa inda suke.
Ita ta fara ganinsa,a sace take kallonsa,tunda suke da shi ba zata iya tuna sau nawa ta taba ganinsa da qananun kaya ba,yau sai gashi sanye da wata dakakkiyar shadda gezner gray colour,sabuwar dal,sai maiqo take da daukar idanu,wani irin annurin kyau yake fitarwa na musamman,gaba daya kamanninsa sun canza kamar ba Aliyyu haidar sojan nan ba,batasan yaganta,batasan tunda ta fara kallonshin ya ganta ba sai da yazo dab da ita,ba tare da su abba suna gani ba yadan ranqwafa ta gefan kunnenta kamar xai dauki wani abu
"Idan kinaso kawai kice kinaso,kada ki wani damu da jan ajin nan naki" saiya miqe ya barta daskare cikin tsananin jin kunya da nauyi,yayin daya bar mata sauran turarensa tana shaqa wanda ke qara sanyata cikin wani yanayi nason kasancewa dab dashi
"Waini babu inda zan samu ruwa ne,ishirwa fa nake ji tunda muka fito daga gida" hajja ta fada,sai haidar din yace
"Akwai.....muje a duba mata" yayi maganar yana duban zahra,a hankali ta miqe,tayi gaba yabi bayanta.
Slow ta fara tafiya bayan sun fito daga wajen,don a jikinta takejin qare mata kallo yake tsaiwar da yayi daga baya,rage hanzarinta da tayi yasa ya cimmata,saiya jera da ita,suka ci gaba da takawa a hankali kuma tare,saidai kamar wadansu masu shirin film,lokaci lokaci saisu waiga kallon juna,kowanne saiya kama dan uwansa,sai kuma kowa ya dauke kansa,saidai shi haidar yana maida kansa gefe daya ne ya murmusa,komai nata ya gama fallasa kanshi,wai amma dole saita ja masa aji?,saiya samu kansa da wassafa yadda zai qure jan ajinta da kuma kunyarta,qaramar dariya ta kubce masa.
Kafin su qarasa provision din haushi duka ya cikata,ta dinga jin ba dadi saboda yadda ake binsu da kallo,abun haushinma yadda duk 'yammatan da zasu gifta sai taga sun bishi da kallo,yau aiport din a dan cike take,alamun akwai yawan matafiya kenan a ranar.
"Kai....nasma,kinga sojan nan,wanda ke zuwa gidan general hamza" daya daga cikin fararen 'yammata uku sanye da baqar abaya ta fada qasa qasa tana tabo ta kusa da ita,wanda hakan ya faru a kunnen zahra wadda ke tsaye daga qofar provision din tana jiran fitowar haidar da ya tsaya biyan kudin ruwa da lemon da suka siya,wani abu ne ya takore wuyanta,ta juya a hankali tadan kallesu,dogaye ne don sun fita tsaho,hakanan farare ne ba kamar ita da take chocolate ba,hannun kowacce tsadaddar waya ce,wadda aka kira da nasma ta bada attention dinta inda haidar din yake tsaye,saita fidda ido
"Wow....wallahi shine,don Allah heedaya,yau ko ya za'ayi mu samu number dinsa please" daya ce ta zaro idanu
"Waye zai tunkari wannan?,ban taba gaya miki yadda muka taba yi dashi ba,tsinannen girman kai ne dashi,kulashi shine great mistake da zakuyi,ku nema number dinsa dai ta wata hanyar daban,koda cikin gidan general ne"
"Gidan general ba kowa sai matarsa,duka yaransa sunyi aure,ita kuwa ban tsammanin tana da number dinsa"
"Quiet sis....gashinan fitowa fa" dayar ta fada,duk sai sukayi shuru har zuwa sanda ya fito din,ya qaraso inda zahra take,wadda kishi ya cikawa qirji,ranta ya dinga suya.
Jerawa yayi da ita,kuma ta tabbatar yammatan nan sun bisu da kallo,a hankali ta saka hannunta ta lalubo nashi,saita hade tafukan hannunsu waje daya ta matse gam,taqi kuma duban fuskarsa.
Mamaki ya kamashi dajin faruwar hakan,saiya bi hannuwan nasu da kallo,laushi da dumin tafin hannunta yana ratsashi,ya dinga qoqarin lalubar qwayar idanunsa taqi bashi dama,har sai da sukaje kusa da inda su hajja suke sannan ta fara qoqarin zame hannunta,shi kuma yace baisan zance ba,hakan yasanya ta dakata da tafiyar da sukeyi,ta juyo tana dubansa,matsowa yayi gab da ita zai hade tazarar dake tsakaninsu,taja baya da sauri,cikin salon marairaicewa ta shagwabe masa tana masa inkiya dasu hajja da ido
"Idan kika sake lasa min zuma a baki ko?hmmmm....." Saiya gyada kao ya zare hannun nasa a hankali,ya soma yarfar dashi,kamar wanda wani abu ya maqale masa.
Cikin jirgi ta kasa ta tsare,saboda ta lura ashe jirginsu daya da 'yanmatan,number din set dinsu dama daga nashi sai nata,don haka harda qirqirar baccin qarya saman kafadarshi.
Bai fahimta meke faruwa ba sai daga baya,cikin ranshi ya dinga dariya sosai,shikam zuwan yammatan ma kamar taimakonsa yayi,saiya tallafeta sanda take kwance kafadar tasa yana tayata,ta dinga zare ido a boye tana tsoron kada fa ta wuce gona da iri.
Hotel me kyau suka sauka,dab da harami,don daga window dinsu suna iya hango masallaci,su shida harda wata 'yar qawar hajjan da suka hadu a jirgi,itama umara ta kawota
"Daki daya mas'ud da halima su zauna daki daya,daki daya kaida zahra,nida rabi mu zauna a daki daya" hajja ta tsara yadda zasu zauna,duk da mama najin nauyi amma haka suka amsa,hakanan itama zahran nauyinsu takeji,ga haidar kuwa sai yaji nutsuwa,yaji har ransa hakan yayi masa,amma saiya basar bai nuna ba saboda yasan tsiyar hajjan,don haka kowa shida kayanshi ya wuce dakinsu.
Dakine madai daici mai kyau,wanda yake dauke da duk abinda xasu iya buqata a kwanakinsu,itace qarshen shigowa don tuni haidar shi ya shigo,tana ajjiye qaramar jakar hannunta taji ya riqe mata hannu,dubansa tayi,ya kafeta da idanunsa har wani lumshewa sukeyi,saiya matsa hannun da qarfi har sai data dan saki qara
"Badon hajja tace haka ba,da bazaki ce komai ba kenan ko?,saiki bita gotai gotai ki dinga kwana a bayanta?" Kasa amsa masa tayi,saboda wani nauyinsa kunya da qimarsa data dadu a idanunta,da kansa ya sakar mata hannun yadan ja da baya sannan ya dauke idanunshi,order din abinci yayi musu sannan ya wuce bandaki.
Cikin kwanaki biyu suka gama ibadar umara,sai sauran ziyarce ziyarce da suka biyo baya,sun ziyarci gurare masu yawan gaske wadanda suke da alaqa da tarihin musulunci,manyan gurare da suke da tarihi da kuma alfarma.
Sosai imani qaunar Allah da manzansa suka sake shigarsu,a kwanakin ibada sukayi ba kadan ba,hakanan tsakanin haidar da zahra kowa ya tsinci kansa da yin addu'a cikin zuciyarsa kan katari da kyakkyawa kan tarayyarsa da dan uwansa,dukkaninsu babu wanda yasan dayansa yana addu'a dominsa.
A kwanakin da suke cikin ibadarsu duk da suna daki guda kowa yana kwancinsa,da sun dawo daga masallaci ko xiyara kowa zaiyi wanka ya samu wajen kwanciya,kusan duk kwanciyarsa a qasa yakeyi,yabar mata gadon,yayin data dinga jin nauyin hakan,duk sanda ta daga idanu ta ganshi kwance saman carfet sai taji kamar bata kyauta ba,a hankali ta tsinci kanta yana burgeta matuqa,baya ga soyayyarsa data shigeta ba tare data ankara ba,ta yi mata shigar burtu.
A wannan tafiyar ta sake gasgata zancan mahaifiyarta,duk abinda ta fada dangane da haidar din haka yake,yana lura da damuwar kowa cikinsu,baga mamanshi ba,baga hajja ba,baga abba babba ba,baga ita ba,kullum kwanan duniya saiya tabbatar babu me buqata ko matsala a cikinsu,bugu da qari ta fahimci yadda yasan addininsa yadda ya kamata,duk da ta sani cewa sam gidansu basa wasa da karatun addini,amma kuma bata tsammaci samun sani da fahimtar addini har haka daga wajen soja ba,ta manta cewa suna suka tara,iya zamansu bataga yayi fada ko fushi ko sau daya ba,kamar ma walwalarsa aka qara yawanta,ya qarfafesu dukkansu sun ribanci abunda suka je aiwatarwa,basu sake ba sai da suka gama ziyararsu kaf inda zasu iya zuwa,sannan suka soma kuma yawon ganin gari.
Ranar farko da suka dawo daga tafiyar ganin gari da sukayi,miqaqqiyat tafiya ya kaisu wani waje,a gajiya suka dawo,don a qafa yace zasu taho,yana yi yana kwasar hajja,don ma Allah yasa yana ganin idanun mamanshi da abbansa suna kwabarsa,haka ya sanyasu tafiyar qafa yace kowa ya wasa jininsa,hajja kam ta dinga masa mita,saiya dinga dariya yana cewa
"Cikin irin tafiyar da muke wannan ba komai bace,kamar kaje qofar gida ka dawo ne" sai suka hada ido da zahra,wadda ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah yau haidar din ke dariya?,saiya waske ya dauke fuska,wanda ta fuskanci kamar haka halayyarsa take,ya iya waskewa mutum.
A hanya suka ga wani kantin saida kayan qwalam da maqulashe,zaka iya siya ka tafi dashi,zaka iya kuma zama kaci a nan,hajja kam cewa tayi bata shiga,zasu tsaya a waje ita da mama,don dama shi abba babba tashi tafiyar daban,ya hadu da abokan kasuwancinsa a can tun zuwansu,don haka shi tare dasu yake,su hajja ne haidar din ke jagorantarsu,ganin haka yasa yace zahra ta biyoshi suje su siyo,su suka samu abun xama nan suka zauna su kuma suka wuce ciki.
Kamar kowanne lokaci ta gefan idanu suke satar kallon juna,jallabiyya ce a jikinsa irin ta maza harda hirami,ita kuma baqar abaya tayi rolling daya lullube mata fuskarta da rabin hancinta.
Ita ta dinga dauka musu abinda take ganin zasu iyaci,hannunta ya cika saita rasa inda zata sanya,tana waiwaya ta ganshi gefanta riqe da kwando,suka hada idanu saiya saki qaramin murmushi ya miqa mata kwandon,ta zuba a ciki,ga mamakinta binta kawai yaci gaba dayi tana zaba tana zubawa,kai kace yaro ne da uban gidansa har suka gama.
Wajen biyan kudin akwai dan layi,saiya duba daura dasu yace ta zauna anan kada ta gaji,idan ya biya zai mata magana ta taso su tafi,murmushi ya subuce saman fuskarta,mutum ne shi mai nuna kulawa qwarai,tana sane da yadda yakema mamanshi duk safiya,dama ba'a maganar hajja,duk wanda ke qarqashinsa yana samun kulawarsa yadda ya dace.
Dukka hankalinta na kansa a fakaice,yana tsaye kusa da wani balarabe suna hira,tana mamakin yadda yaji larabci har yake iya mayarwa yadda za'a fahimta tun zuwansu,kwatsam ta hangi wata matashiyar balarabiya ta iskosu,saita tsaya tsam,tun daga sanda ya waiwaya ya ganta,zuwa sanda taga alamun hira yakeyi da ita,fuskarshi da fadada da fara'a wadda ta qara masa kyau sosai.
茦irjinta ne taji ya quntat sosai,saita miqe tana cire earpiece din kunnenta dai dai sanda yake juyowa shida yarinyar suna kallonta,yana kallo ta miqe daga gurin ta fice da hanzari,zuciyarta na mata zafi,tana hango yadda ya sake mata fuska sosai kamar ba haidar data sani ba.
"Ke lafiyarki kikema mutane tsaki?" Hajja ta tambayeta sanda ta isa inda suke,shaf ta manta data isa dab dasu,kishi kawai ke nuqurqusar zuciyarta
"Eh mun gama siya,na barshi a can zai biya kudin,wajenne akwai layi"
"Ai dama....su da basu rabo da siye siyen irin wadan nan abeba蓷en".
Tunda ya fito har suka qarasa hotel a tsume take,taqi ma koda kallonsa bare ta nuna tasan da wanzuwarsa,cikin ransa hakan ke masa dadi gami da burgeshi,ko banza yasan ya gama kama zuciyarta TABBAS! baya ko shakka kan hakan.
Shima baice ba har zuwa sanda ya dawo daga dubasu mamansa,ya tabbatar basu buqatar komai kafin ya kwanta.
Sam bata tsammaci dawowarsa da wuri ba,saboda tasan yanayin awa daya a qalla idan yaje musu sallama kafin ya dawo,itama yau gajiyar da sukayi ne ya sanyata bata kuma fita ba,saita shige wanka ganin ya fita,donta samu ta shirya a nutse,tunda yawanci idan yana nan saidai ta shirya cikin hijabi,fitar tasa ne ya sakata fitowa daga wanka daga ita sai towel a daure a jikinta,ta kuma tsaya gaban mirrow tana shafa turarukan da take amfani dasu,sannan ta ware gashinta daya jiqe da shower tana son yadan sha iska kadan kafin ta maida ta kulle,dai dai lokacin daya turo qofar dakin kunnensa maqale da waya yana amsawa.
A badini ta tsorata,amma a zahirance saitaqi motsawa,saboda batason ta motsa ma ya dauka ta damu dashi,gwara ta nuna masa haushinsa takeji koda ba zaya fahimta ba,don haka taci gaba da tsaiwa gaban mudubin tayi kamar batasan ya shigo din ba.
Kamar wanda aka jonawa wutar lantarki a jikinsa haka ya dinga ji,karon farko kaf rayuwarsu daya taba ganinta a haka cikin irin wannan shigar,take aka zare masa dukkan wani kuzarinsa da lakar jikinsa,saiya juya a hankali yana maida qofar tare da katse wayar da yakeyi,duk da bai gama isar da saqon da yake isarwar ba.
23/10/2021, 08:50 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 41
A hankali ya isa bayanta ya tsaya dab da ita,sai a sannan tsoro yadan darsu a ranta,amma ta dake taci gaba da tsaiwa,tsaiwarsa tasa har jikkunansu na gogar juna,ya daga tafin hannunsa ya dora saman kafadarta yana kallon fuskarta ta cikin madubin,saita motsa zata matsa,yayi hanzarin saka daya hannun nasa ya tsaidata tsam a wajen,sauko da hannun nasa yayi a hankali daga kafadarta zuwa dantsanta har yatsunta na hannu kamar me mata shafar mai,saiya hade yatsuntsu waje daya sannan ya saki qaramin murmushi
"Me yasa ko yaushe kike son nuna baki so,kuma baki damu ba,bayan nasan qaryane,kina so,kuma kin damu dani" idanu ta waro dukka yana kallonta ta cikin mudubi,duk da jikinta rawa yake saboda kusancinsu da tafiyar tsutsar da yake mata a hannayenta amma hakan bai hanata magantu ba
"Ni.....ni bana sonka,kuma ba damuwa nayi ba,koma meye kayi rayuwarka cefa"
"Kishi zalla"ya fada a sarari sannan ya birkitota ya zamana suna fuskantar juna,dukka hannayenta ya kama ya riqe cikin nasa,yana kuma kallon qwayar idanunta
"Rayuwar mu dai mrs pretender.....am tired....na gaji da wannan jan ran ranki ya dade,na gaji da jira,sai yaushe zaki yarda zuciyarki nason dan uwanki aliyyu kamar yadda ALIYYU KE SONKI!,sai yaushe zaki yarda kin damu da haidar kamar yadda HAIDAR YA DAMU DAKE?,sai yaushe zaki fuskanci ke dashi duka kun hau ALKIBLA DAYA ta soyayyar junanku?....idan ke kinqi fada,kina jamin aji ko?....." Ya tambaya yana sakar mata wani murmushi da babu abinda yake qara mata face saukar mata da kasala,da kuma wani mugun sonshi
"Kin cancanci kija ajinki ZAHRATY.....amma yau kam haidar dukka wata jarumtarsa ta qare,duk dauriyarsa ta tafi,abinda ya jima yana boyewa,abinda ya jima yana binnewa,abinda ya jima yana tunanin ya mutu babu shi yau ya raya kansa da kansa......." Saiya dora kansa saman kafadarta duk da cewa ya fita tsaho,yadan rusuna ya rage tsayinsa,ta yadda hakan zai bashi damar rungumeta sosai cikin jikinsa,laushin fatarta na 蓷ai 蓷aita tunaninsa,yana jin kamar bakinsa bazai iya qarasa furta abinda yakeson fada ba saboda nauyi da yayi masa,kamae me rada,kamar wadda ake zanawa kalaman tun daga saman zuciyarta zuwa qwaqwalwarta haka ya dinga amsar kowanne furuci me cakude da harafi dake fita daga bakinsa
"Ina sonki....soyayyar da qauna ce tafi rinjaye da qarfi a cikinta,qaunar kuma da ba daga zuciya kawai take ba,ta ratsa jini qasusuwana da kuma tsokata.....qauna irin wadda ke cakude da numfashina da kuma raina,wadda babu yadda za'ayi ta fita daga jikina....saidai ta hada harda numfashina" kalaman da bata tsammaci samunsu daga wajensa ba,shi din daya kasance cikin sahun maza da dukkaninsu ta basu sunan MAYAUDARA kuma marasa ALKIBLA,cikin mazan kuma ya kasance mai baudadden hali,mara uzuri mai zafin zuciya da fada,yau shine rungume da ita kamar zai karya qasusuwanta yana gaya mata yana sonta?,shine rungume da ita kamar zai maidata cikinsa yake fasa mata sirrin zuciyarsa?,bata gama wannan tunanin ba taji numfashinsa na sauya yanayi
"Kina sona zahra?" Ya tambayeta kai tsaye sanda ya cusa kansa tsakanin wuyanta,saita kasa bashi amsa saboda yawo da yake da harshensa a wajen
"Uhmmmm.....ki amsa min mana" ba zata iya magana ba,saboda abinda yake aikata matan tuni ya sanya qafafunta sun fara rawa
"Ohkey.....bari na dasa miki sabon harsashin da zaki fara sona koda baki shirya ba" daga haka ta nemi haske a dakin ta rasa,yasa hannunsa tuni ya kashe dukkan qwan lantarkin dake dakin wanda yake kusa da madubin da suke tsaye,sai qaramar futilar gefan gado wadda me dim light,gaba daya ya dagata yayi mata masauki saman gadon dake dakin shima ya daga qafafunsa da yajisu kamar basu taba sanin meye qarfi ko kuzari ba ya haye saman gadon.
Saukar numfashinsa saitin kunnenta ya sanyata rintse idanu,bugun zuciyarta ya qaru sosai,qamshinsa ya cika mata hanci,jikinta yayi wani rauni lokacin daya fara aike mata da saqonni,ta rasa duk wani kuzari nata,ya saukar mata da kasala sosai,sai taji yasa hannunsa yana qoqarin zare towel na jikinta.
Da sauri ta damqe hannun nasa tana girgiza kai,duk daba cikin haske bane amma yana iya ganin motsawar kan nata,da wata irin raunanniyar murya yace
"Nooo......nooo zuhra...." Yana mirgina kansa hagu da dama shima,yadda ya soma komawa ne yake bata tsoro,tana tsoro sosai,don ba zata manta abinda yaso faruwa rannan ba,sake maidata jikinsa yayi tsam,saidai wannan karon cikin zafin nama yake ci gaba da aike mata da zafafan saqonni,masu rikita dukkan wani mai lafiya,da sanyashi cikin shauqi,saqonnin da suka kusa sanyata fita daga hayyacinta,cikin qaramin lokaci ya zautata,ya fidda duka wata zalama da qwarewa tasa,ya nuna hazaqa da fikirarsa,harya rabata da towel din ba tare da tasan anyi hakan ba,bata fara hawa saitinta ba sai da taji za'a maimaita irin na ranan nan,a sannan ne ta ankara da wayo kawai yayi mata,ta kuma lura da wautar data tafka,sai ido ya raina fata,ta razana sosai,taso ta sake bore,saidai inaaa.....ya hanata wannan damar,don koshi a sannan baijin yana da control na kansa da kansa bare ya yiwa kansa birki,bai sassauta ba,hakanan bai qyaleta ba har sai daya samu isa duniyar ma'aurata,duniyar dake maida biyu su zama daya,duniyar zahransa,duniyar data sanyashi a ranar sunansa da nata ya cika.
*_BAYAN WANI LOKACI_*
Kuka take sosai amma shi murmushi ne ke fita saman fuskarsa duk da yana jin kukan yana sukar zuciyarsa sosai,ya sani akaran kansa cewa bai raga mata ba ko dis,amma ya ya iya da ranshi,zai iya cewa ba laifinsa bane,tana maqale da ita kamar wanda aka ce masa za'a qwaceta,zallar sonta sabo fil yake kwarara cikin ranshi,kamar ya ciro zuciyar tasa gaba daya ya bata kyautarta,ba irin lallashin da baiyi mata ba,gashi har sha biyu da rabi na dare ta hanasu barci,shi da kansa ya gasata sosai,sannan ya barta tayi wankan,data gama shiya taimaka mata ta fito,amma wajen shiryawa fir taqi yarda,sai baya ya juya mata yana dariya ciki ciki yabarta ta shirya da kanta,ko a yanzunma da take kwance cikin jikinsa sai daya mata fin qarfi tukunna,baisan me zai sanyata tayi shuru ba,duk da ya lura irin shagwabar da takema hajja yau take sauke masa,shagwabar da abaya idan yaga tanayi yake aike mata da saqon harara ko tsawa,sai gashi yau yasa hannu bibbiyu ya amsa
"Kona kira miki hajjan?" Ya fada qasa qasa,da sauri ta maqale kafada,saita cusa kanta cikin qirjinsa tana sassauta kukan nata,ita kam waya aiketa da wata hajja?,tazo ta tijarasu kota titsiyesu da tambayoyi?.
Cikin salon qwarewa da dabara hannunsa saman sumar kanta ya dinga kashe mata jiki,har wani bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,wanda cikin baccin ajiyar zuciya ta dinga saki,sai daya tabbatar baccinta yayi nisa sannan ya sauketa a hankali,ya dora mata kanta saman pillow ya rufa mata duvet,sannan ya soma gyara mata sumar kanta yana kallon fuskarta,fuskar zahransa,murmushi ya subuce masa daya tuna tsiwa irin ta zahran,amma yau bakinta yayi laushi sosai,duk da cewa dama ta jima da canzawa,abubuwan da suka faru dazun suka dawo masa,rakin data dinga yi,magiyarta da ban hanqurin data dinga masa tana cewa ba zata qara ba,shi kuma yana tambayarta ba zata qara me ba,dukkansu shida ita ya tabbatar mahaukata suka zama tuburan,ita ciwo ya isheta,shi kuma duniyar data jefashi ne yasa ya kasa fahimtar komai.
Sallah ya sauka yayi yana miqa godiyarsa ga Allah,ya sani cewa ubangiji ya gama masa komai,sai kuma neman taimakonsa kan bauta masa da tsare haqqoqinsa,sannan ya kuma ya shiga lamarin xamantakewar aurensu,ya bashi ikon da zai riqeta bisa doron shari'a,kan gaskiya amana tausayi da kyautatawa.
Tana bude idanunta dashi ta soma tozali,ya sanyata a gaba yana qare mata kallo,saitayi rub da ciki da sauri tana boye fuskarta,yana murmushi shima ya haye bayanta,ya aza mata nauyinsa yana cewa
"Good morning zahraty amarya" sosai ya bata kunya bayan wadda takeji,nauyinsa takeji sosai,musamman idan ta tuna waye ya haidar a wajensu,amma gashi dare daya ya sauya komai a tsakaninsu,kamar bashi ba,kamar wani aka canza musu dashi,bata taba ganin fuskarsa a yanayin data ganta ba tsakanin jiya da yau.
Sai da yayi da gaske sannan ta miqe ta fuskanceshi,ya dinga tsokanarta,ya hanata sakat,ita kuma kunyarsa kamar qasa ta tsage ta shige ciki haka ta dinga ji,bai qyaleta ba yaci gaba da bibiyarta duk inda ta saka qafa cikin dakin,saidai bai fiya magana ba,amma ayyukansa na gaya mata komai,shi ya hada mata ruwa ta sake wanka,ya gyara dakin da kansa,don yace harsu tafi babu masu sharar da zasu sake shiga musu dakin,tayi mamakin yadda ya iya aiki da kansa,ashe dama a baya rashin ganin dama ne?,ko kuma sune basu fuskanceshi ba,itakam mamakin sauqin hali irin nasa take,komai nashi a sauqaqe yake yinsa,babu zafin nan,babu izzar nan da suke zatan masa ita.
Wayarsa ce tayi qara,ya qaraso ya daga,hajja ce take kira,bayan sun gaisa sai tace
"Lafiya na jiku shuru yau?"
"Eh...itace bata jin dadi sosai,ta sha magani ne,tana kwance" duk da ranta ya bata wani abu amma sai bata nuna ba,kawai tace
"Ayyah,qila tafiyar jiya ce da haka kawai ka kwasa mutane....ni dinma qafata ciwo take sai dana shafa magani,to Allah ua sawwaqe,ya bada lafiya"
"Amin amin" yana dubawa yaga harta kashe wayar ma,sai ya saki murmushi suka hada ido da zahra,itama murmushin kawai tayi,addu'a dama take kada Allah yasa asirinsu ya tonu wajen hajjan,sai gashi bata gane ba
"Ko zakije ku gaisa?" Ya fada yana kashe mata ido,kafada ta maqale,tasan bata isa taje ta fito ba hajja bata gano komai ba,don ko tafiyarta tasan ta sauya.
Wuni sukayi sur cikin dakin ba tare da shi ko ita sun fita ba,sai yayi amfani da wannan damar,ya dinga lura da ita tare da dasa mata sabuwar qaunarta cikin zuciyarta,bai yarda sunyi nisa da juna ko raba mazauni ba,ya sanya nata sabo dashi da saboda jikinsa,tun tana kakkaucewa harta sallama.
Washegari shi da ita kadai suka fita wani waje,bayan sun biya sun gaida su hajja,yadda ta dinga sussunne kai da jin nauyinsu su duka ya alamtawa hajja me afkuwa ta afku,duk da ba haka taso ba,taso sai bayan anyi taron biki an kaita amma ba abun damuwa bane,tunda already matarsa ce.....da fatan alkhairi ta bisu sanda suke ficewa,saita lura mama ma idanunta yana kansu fuskarta na nuna farincikin dake qasan zuciyarta.
Karo kusan na hudu kenan tana hada ido dashi sanda suke zaune saman table din daga ita saishi,waje ne me kyau,wanda kallonshi kawai ya isa ya sanya zuciya ta debe kewar dake damunta,gabanshi shi babu komai face ruwan roba,sanda aka kawo menu ita ya zabarwa abubuwan da za'a kawo mata,wanda kusan duk abubuwan kwadayi ne,yatsunsa ya sarqafe kawai cikin na juna ya zuba mata idanu yana kallon duk wani motsi nata,kyau take qara yi masa,qaunarta yakeji har babu iyaka.
Karo na qarshe da suka hada idanu tadan kwabe fuska kamar mai shirin yin kuka,murmushi ya sakar mata yana girgiza kansa,gyara zamansa yayi still dai baibar kallonta ba,a hankali yace
"U r my first love" cikin mamakin furucinsa ta dakata daga kai ice cream din data debo bakinta ta zuba masa idanu alamun son qarin bayani,kai ya gyada mata
"Yes u r"Saita samu kanta da tattara dukkan hankalinta a kanshi,cike da mamaki take dubanshi
"Tun lokacin da aka haifeki na fara sonki,a lokacin da nike tamkar 蓷a a wajen ummi,duk da na fara samun qanne a lokacin,amma sanda aka haifeki ji nayi sai a lokacin na samu qanwa,a sannan ni kadai kike yarda dani baya ga ummi kaf fadin gidan" yana fadin haka saita tuna sanda hajja ke bata wannan labarin,amma a lokacin ta zata hajjan na fada ne kawai saboda taji dadi a ranta,kota rage kaifin jin haushinsa da rashin jituwar dake tsakaninsu
"Sannu a hankali kina qara gama inajinki cikin zuciyata da gangar jikina,hakan yana yiwa ummi dadi,amma takan kwabeni kan...nayi a hankali,kada kulawar da nake baki tasa ki sangarce,saina fara sanya lura da nutsuwa,a sannan sai na lura da kin fara tabara saboda gata da kike samu daga wajen hajja itama,duk gidan kece ta gaban goshinta fiye da kowa,saboda sunanta da kikaci,sannan kuma cikin jikokinta kinfi kowa wuni wajenta,tunda jima sashenta shine wajen zamana a yawancin lokuta.
"Lokacin da kika fara girma a sannan na zama saurayi" saita kalleshi,murmushi ya subuce mata,saboda fadar hakan da yayi ya tuna mata da abubuwa masu yawa,ta kuma gane dai dai lokacin da yake nufi din,shima murmushin ya sake mata mai sanyi sannan yaci gaba
"A lokacin na fuskanci kaf cikin sa'anninki da tsararrakin kin fisu tsiwa.....kafiya...rashin tsoro da kuma taurin kai,kuma kamar hakan ya faru ne saboda kulawa da hajja ke nuna miki,kinsan dalilin da yasa na aje soyayyarki?,wanda ya zama musabbin da har yau babu wanda yasan ina sonki?" Kai ta girgiza a hankali cike da daukin son jin ci gaban labarin
"Abu na farko da ya sanya naji ya cancanci na ajeshi shine ummi....ummi na nuna miki qauna da soyayya qwarai,hakanan ta azani a matsayin yaya a gareki,wanda ya isa da duk lamuranki,ya isa ya yanke hukunci cikin rayuwarki fiye da sadiq.....sai nayi tunani a karan kaina,matuqar naci gaba da sonki har aka kai sanda zaki sani koki fahimta....to ya zamana babu me tsawata miki kenan kan kiyi koki bari?,idan har na aureki kenan babu sauran wanda zai dinga taka burki akan al'amuranki?,komai zakiyishi yadda kike so?,hakan zaiwa ummi dadi?,ko kuma zaifi mata dadi idan naci gaba da tsaiwa kan rayuwarki ne?.....hukuncin na aje din shi nafi ganin dacewarsa,saboda haka na ajjiye dukkan wata soyayyarki da nakeji a cikin raina,na shiga treating dinki kamar sauran,na kuma qara matsa lamba fiye da baya,abunda ya kuma sawa naji na gamsu da hukuncin da na yiwa kaina,sabon suna da suka miki inna wuro,uwar masu gida ko?,hakan na nufin kiyi abinda kikeso,sannan lokaci qalilan daga dan fara tasawarki samari suka yiwa rayuwarki caaaaaa.....naso hajja a lokacin ta yarda da tsarin da naso kafawa a kanki amma fur taqi,saboda tana ganin na fiya matsantawa,bana duba maraicinki.....kinsan wani abu?" Saita girgiza kai a hankali,labarin da yake batan yana mata dadi sosai
"A duk sanda wani yazo ya kuma yaudareki ya gudu.....na fiki jin ciwon faruwar wannan,nakan jima ina jin raina yana baci,duk da nakanji kishi,nakanji bacin rai duk sanda kike tsaye da wani da sunan saurayi,to amma sai zuciyata ta gayamin,tunda ka aje soyayyarta ka zabi bata kariya,dole zuciyarka taqi ji taqi gani,dole ka daure ka zama jajirtacce,ka fuskanci dukkan wani qalubale,na karbi wannan magana,na kuma sake jaddadawa kaina hakan,dalilin da yasa na karbi zahra takwararki kenan,na soma nazartarta da halayyarta....."sai yadan tsaya yana aje numfashi idanunsa kan zahran yadda ta nutsu tana saurarensa tana kuma fahimtarsa
"Am sorry to say....tana da haquri....tana da sanyin hali,uwa uba nutsuwa da kamewa,sannan kuma sunanku daya,wadan nan dalilai sune kadai suka sanya na miqa mata wuyana,saboda nasan wadan nan halaye zasu dai dai da tawa dabi'ar da halayyar,zatona da hasashen saiya zama gaskiya,ta fahimceni fiye da yadda na zata,ta kuma banbance abinda nakeso da wanda bana so,a hankali sai zuciyata ta fara samun nutsuwa da sukuni,na kuma gamsu zahran ta dace dani,saidai duk da haka baki fita daga zuciyata ba....sau tari nakan tura mata saqo wanda a zahiri sanda nake rubutashi dake nake,saidai nasan cewa koda baki sani ba kai tsaye,kuna karbar wayarta,kuna kuma shiga inbox nata,idan akayi katari kika karanta to kamar na rage wani nauyi dake zuciyata,na kuma isar da saqona,don yawancin lokuta tana gayamin yadda kike nuna zallar mamaki idan kikaci karo da daya daga cikin saqonnin dana tura matan.....bazan boye miki ba....nayi missing zahra'u,na kuma shiga tashin hankali na haqiqa sanda na rasata,har nakejin ma kamar bani bane....kamar zan zauce....na jima....na jima ina dorawa kaina alhakin mutuwarta,saboda ta rasu ne a sanda naje makaranta ganinta,da wani yammaci,na dawo daga gwambe,na tsaya ta wudil ganinta,saboda munyi waya tun ina hanya.
"Sanda na shiga makarantar na sameta shuru,kamar irin anyi hutu dalibai sun kokkoma gida,to amma nasan ana tsaka da zangon karatu ne,ba lokacin hutu bane,waya na daga na kirata da zummar bata mamaki,don batasan da zuwa na ba,na gaya mata inda nake tsaye,cike da zumudi da mamaki tace gata nan fitowa,saina maida wayar aljihuna ina duban inda nake tsayen,wajene mai yalwar bishiyoyi dogaye da kuma tarin ciyayi mai tsaho,tunda nake zuwan mata makarantar lokaci zuwa lokaci bamu taba tsaiwa a wajen ba sai ranar,ina cikin karantar yanayin wajen naga bullowarta ta gefena,kamar kowanne lokaci cikin hijabinta,tana tafe tana murmushin ganina,saina bata dukka hankalina harta qaraso.....
"Me ya faru yau naga makarantar taku yau so silent" tambayar dana fara mata kenan
"Wallahi tun jiya da aka samu fitowar macizai ne,sai kowa ya tsorata ya lazimci zaman daki,don yau ko lactures ma ba'ayi ba" kai na jinjina sannan nace
"Amma da kin gayamin da bazan shigo ba bare na fiddoki daga daki" dariya tayi
"To na godewa Allah da ban gaya maka ba bare ka haramta min ganin fuskarka....komai muqaddarine ai daga ubangiji,koda ina daki duk abinda ya qaddara zai sameni saiya samenin"basai na gaya miki sauran abinda tace min ko nace mata ba...saboda tsaro ba don tsoro ba" ya fada yana murmushi,itama murmushin tayi tana girgiza kanta,idanunta a kanshi,ajiyar numfashi yayi
"Yau soyayya ta sani dogon magana.....a taimakamin da ruwa" hannunta ta sanya ta bude masa gorar ruwan sannan ta ajjiye masa,ya dauka a nutse ya soma sha,yana sha yana ajewa yashaqi numfashi har ya gama,ya aje robar yana sauke numfashi tsahon minti daya sannan ya dora.
"Bari na samo maka abun sha a wani kanti nan" ta fada ta soma takawa,da hanzari na tsaidata
"A'ah....ni ganinki kawai nazoyi,bana buqatar ci ko shan komai" kafada ta maqale
"Ban yarda ba....saboda nima irin karamcin nan naka nakeso na koya,saboda haka saina samu ladan baqona" daga haka ta soma takawa ta cikin ciyayin nan tayi gaba,a cikin zuciyata inason tsaidata amma kamar wanda aka daurewa baki na kasa,inasin ince kada tabi ta wannan ciyayin amma na kasa fada mata,inason ince mata ta tsaya na rakata amma dukka kamar wanda aka daurewa baki duk na kasa fada,ashe ajali ne,ajali ne ya kirata,don batayi wani nisa da idanuna ba naga gilmawar wani abu ta bayanta,na fuskanci maciji ne,idan nayi magana kuma zata iya rudewa,don haka na fara takawa da wani irin hanzari da zafin nama,dai dai sanda ta waiwayo tana kallona,sai fuskarta ta nuna mamakin ganina ina tahowa inda take da mugun gudu,bansan ya akayi ba saijin ihunta nayi ta durqushe cikin ciyayin.
Sanda na isa na sameta riqe da qafarta,ta hada gumi sharkaf tana juye juye,dana dauke hannunta saiga inda macijin ya sareta nan,na bata taimakon daya dace,na riqeta zuwa asibitinsu na cikin makaranta,saidai abun haushin abun takaici basu da allurar kashe gubarsa,raina ya baci sosai,amma ban tsaya biye musu ba,saboda kada bata lokaci ya jawo asarar ran da naketa gudu,na sanyata a mota kawai muka wuto zuwa kano.
"Irin gudun dana dinga tsalawa ni kaina nasan Allah ne kawai yayi motar ba itace ajalinmu ba nida ita gaba daya,tana cure waje daya set din gaba taba murqususun ciwo da azabar dafin daya zuba matan,hankalina rabi ga titi rabi a kanta,qarin abun haushin asibiti manya guda biyu mukaje suma basu da allurar a dai dai lokacin ta qare,sanda muka dauki hanya zuwa asibitin mu a sannan ta kalleni,launin idanunta yana canzawa
"Kayi haquri ya haidar....kayi haquri,kuma naga ranka ya baci,duk abinda Allah ya shiryawa bawa bai isa ya tsallake mishi ba" saita maida kanta ta kwantar,kalamanta suka dagan hankali,na tsaya gefan hanya sanda naga yanayin jikinta ya saki gaba daya.
Nasan a sannan ta mutu don zuciyata tana gaya min haka.....amma idanuna a rufe suke,saina tashi motata da mugun gudun da yafi na dazu na nufi asibitin,saidai abinda nake tsoro dai shi aka gayamin,zahra ta rasu,dafin yaci jikinta yakai inda ba'a so yakai......"saiya tsaya da bata labarin yana duban yadda hawaye ke zuba a idanunta,a wancan lokacin sam batasan yadda mutuwar zahra ta kasance ba,kawai dai tasan saran maciji ne,hakanan tana ganin haidar yaqi daukan qaddara ne kawai,amma data kwatanta mutuwar masoyi ko aboki gaban idanun abokinsa sai taga abun ba mai sauqi bane,dole ya shiga irin yanayin daya shiga din,kasa jurewa tayi,sai tayi qasa da kanta kuka na kubce mata.
23/10/2021, 08:50 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 42
Murmushi ya saki,sannan ya taso daga inda yake zaune,yaja kujera dab da ita ya zauna har gwiwarsa na gogar tata,hannunsa ya sanya ya dago fuskarta gaba daya,saiya girgiza mata kai alamun
"A'ah"yatsansa guda daya ya sanya ya dinga dauke mata hawayen,murmushi kwance saman fuskarsa,har sai daya goge duk wani hawaye da yayi saura,saiya hada goshinsa da nata suna musayar numfashi,qamshin turarensu na gauraya da juna
"A wancan lokacin kinyi fushi....kin nuna kishi saboda ganina da wata balarabiya.....wadda nake ganinta da muni sosai idan na hada da kyakkyawar fusakarki,da kuma yadda zuciyata ta rayu da sonki......ta samu dukka fara'ata ne da kulawa saboda yabonki da tazomin dashi,ta shaidamin tunda taga shigowarmu taji mun burgeta.....tana son qawance dake,dalilin da yasa ta biyoni kenan har kika ganmu tare....saidai kuma a yanzun gashi kina kuka saboda wata da na taba so na baki labarin mutuwarta...me yasa bakiyi kishin xahra ba?" Ta rasa amsar da zata bashi,amma dole duk me imani yaji a yadda zahra ta rasun ya tabashi,ta riga data wuce zahra ba zata taba dawowa ba,kishi da ita tamkar abun nan da hausawa ke kira da ihu bayan hari ne.
Murmushi ya saka yana cewa
"Na fahimta....amma har yau kinsan ban samu makwafin zahra ba?" Cikin mamaki ta zare fuskarta daga nashi tana duban idanunsa,saiya dage mata dukka girarsa
"Eh....ban sake samun wadda tacemin ALIYYU HAIDAR INA SONKA BA,ban sani ba ko baqinjini gareni?" Dariya sosai ya bata,yanayin yadda yayi maganar ma abun dariya ne,sai tasa hannu ta toshe bakinta,yayin daya harde hannayensa a qirji yana qare mata kallo,dariyarta kadai ta sanyashi farinciki shima,gami da saukar masa da nutsuwa
"Aikam saidai idan har shin haidar din ne baiso a gaya masa ba,a iya sanina akwai daruruwa ko ince dubban mata dake ta dakon randa xai basu dama su furta wannan kalma a gareshi....." Tararta yayi ta hanyar watsa hannayensa,kamar zai saki kuka yace
"Ni dukkansu ban gansu ba,bansan da zamansu ba,zahran hajja kawai na sani,kuma ita kadai nake jira da dakon randa zata gaya min hakan....." Itama bata barshi ya qarashe ba yaji saukar kalaman kamar ruwan sama saman zuciyarsa
"Ya haidar kadai nakeso....shi nake qauna har abada" idanunsa ya ware cikin mamaki yana dubanta
"Say it again please"馃檹馃徑,duk kunya saita cikata,ta maida kanta wani sashen tana murmushi,sai ganinshi tayi ya koma inda ta maida kan nata
"Please....inason na sake ji" wani qwarin gwiwa ya bata daga cikin idanunshi,saita kalleshi sosai
"Ina son ya haidar,ina sonka...ina sonka" gaba daya ya tattareta cikin jikinsa,ya manta ma suna waje ne,sai data ankarar dashi,ta tabbatar da a 9ja suke da tuni sun tara 'yan kallo,da qyar yayi controlling kansa,ya komqa ya zauna dab da ita,muryarsa cike da wani irin softness ya kamo hannunta ya riqe tsam cikin nasa sannan yace
"Hakan yana nufin....kin mallakamin rayuwarki?,kin zama ni na zama ke?,zakici gaba kuma da kasancewa tawa har abada,munyi amanna wa juna zamu rayu da juna duk rintsi duk kin yarda da wannan?" A kunyace kan irin salon kalaman dake fita daga bakin yayan nata,da salon kallon da yake mata ta gyada masa kai,saiya girgiza kai
"Banison body language.....pls ki gayamin da bakinki"
"Amince.....na amince ya haidar" lightly yayi kissing saman hannunta,ya rasa da wacce kalma zai sake magana,kawai sai yaci gaba da riqon hannunta cikin nashi yana kallon kayarsa kamar za'a qwaceta,har sai da tayi waving hannunta saman fuskarsa
"Bansan me zance miki game dani ba,abu daya zuwa biyu kawai bakina zai iya gaya miki,da kanki zaki dinga bawa kanki amsar irin mijin da kikayi katari dashi,sannan ina miki albishir din cewa......zaki shiga sahun matan da sukafi dukkan mata sa'ar miji a duniya" daga haka ya miqe yana riqe da hannunta,itama saita miqe suka soma takawa cike da wani irin xallar farinciki dake yawo dasu a duniyarsu.
Kwan daya tak suka qara suka fara shirin dawowa,ya bata dama ta siya dukkan abinda take da buqata,siyayya me yawa da batasan me za'ayi dasu ba.
Kamar yadda suka tafi tare haka suka dawo,sun tadda 'yan Tarbarsu danqam suna jiransu,family ne mai cike da hadin kai da qaunar juna,babu wani bambanci da xaka gani tsakaninsu.
Tun a airphort din ta ankare da yadda 'yan gidan nasu keta gulmarta ita da ya zakin,saboda duk inda yayi yana maqale da abarsa,baya jin kunya ko nauyi sam,motsi kadan nata idanunsa da hankalinsa yana kanta.
Da zasu tafin bai bar kowa ya shiga tashi motar ba,zahran ta rasa dalili amma yayi fuska,ta sani dukkansu shakkarsa suke,saboda haka ba wadda ta iya tunkararsa,sai hafsat data rage bata samu waje ba,tayita zagaye tanason tace ya dauketa,amma ta kasa,sai zahran ce ta dubeshi
"Please ya haidar....maman khairat ce bata samu waje ba" ta fada cikin marairaicewa,wani kallo ya watsawa hafsat din ta window,ba shiri ta fara qoqarin juyawa tabar wajen,amma sai zahran ta yaficeta ganin baice komai ba.
Bai tanka musu ba har aka fara tafiya,basuyi nisa da airport din ba ya bawa driver umarnin ya tsaya,saiya fidda kudi tana ajema hafsat din fuska a tsuke
"Sauka ki tari napep ki hau....." Kallonshi duka suyi cikin mamaki,saiya hade rai tsam,zahra ta dubeshi a shagwabe
"Yayaaaaa"
"Shshshshhh...ba gida muka nufa ba,so take muyita yawo da ita?" Mamaki ya kamata,toba gida suka nufa ba ina suka nufa kenan?,tana ji tana gani hafsat din ta sauka ta tari napep su kuma sukaja motarsu suka wuce,sai tayi kicin kicin ita ala dole fushi take dashi,bai tankata ba,data kalli fuskarsa ma sai taga walwalarsa yake abinsa.
Tanata zuba ido tana ganin yadda suka shiga unguwar,mamakin wajen wanda zasuje take,daga dawowarsu daga doguwar tafiya irin wannan.
Bata samu amsar tambayarta ba har sai da suka tsaya qofar gidan,mai gadin madaidaicin gate din ya bude musu suka shige madaidaiciyar harabar gidan da zata iya cin motoci uku zuwa hudu ba tare da sun takura ba,da kansa ya fita,ya zagaya inda take zaune ya bude mata motar,fuskarsa dauke da murmushi yace
"Bismillah" dubansa tayi tana maqale kafada tare d zumbura baki,Ranqwafowa yayi saman kanta yana murmushi
"Beautiful.....wannan bakin naki...." Sai ya saka yatsunsa biyu ya kama labban nata ba tare daya qarasa fadar abinda ke bakinsa ba,janye bakin tayi da sauri saboda yawon daya fara da yatsunsa saman labban nata
"Ranki ya dade.....ina miki barka da shigowa gidan aurenki" ya fada murya can qasa kamar meyin rada,da sauri ta daga ido tana kallonshi
"Ya haidar....kada kayi haka,shi yasa ka hana kowa shiga motar mu....hajja fa" yatsansa ya dora saman lips dinsa yace
"Shshsshhhhh....banason kiran sunan kowa ba,bansan kowa ba sai ke,nan din duniyarmu ce ni dake,kema kuma zaki manta da kowa da komai soon" ba tare data shirya ko ta ankara ba taji gaba daya ya sunkuceta,ta Maqaleshi sosai,saboda ji da take kamar zata fadi
"Karki damu,a hannun soja kike" ya fada yana murmushi,saita maida masa martani itama ta maida kanta qirjinsa ta kwantar,tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri,sai ta daga kanta cikin mamaki ta dubeshi,murmushi ya sake sakar mata
"My heart beat ko?,kada ki damu,sonki ne da zumudin kasancewa tare dake" wani farinciki taji yana ratsa zuciyarta,tanajin alfahari da kasancewarsa mijinta yana mamaye ruhinta,qaunar hajja ta sake fadada a ranta,tabbas ita din ba qaramar masoyiya bace,me yasa kaf cikin jikoki da 'ya'yan 'yan uwa bata zabi kowa ba sai ita?,ita kadai ta dauka ta mallakawa mutum mai tsada da daraja irin aliyyu?,a hankali a hankali take fuskantar komai,kamar yadda ta taba gaya mata cewa zata gane,zata fahimci gatan datayi mata,bata da bakin gode mata,bata kuma da abinda zatace mata face addu'ar gamawarta da duniya lafiya.
Tana daga hannunsa take qarewa gidan kallo tun daga hanya har shigarsu falo,ba'a cika masa kayan alatu na qarya da barnar kudi ba,amma ya qayatar matuqa ya kuma bada ma'ana,parlour,two bedrooms with toilets a qasa,dining area,kitchen,store da wani toilet din a falo,saman benan gidan ma falo ne da bedroom biyu,kowanne shima da toilet,gaban kowanne daki akwai qawataccen corridor da zai baka damar ganin gaba da bayan gidan,akwai dakuna daga bayan ainihin ginin gidan guda biyu masu falo daya da bandaki,sai wajen ajiye motoci matsakaici ha matsakaiciyar haraba don shan iska.
Dubansa tayi sanda taga yana aje kayansu a dakin daya direta
"Ina nawa bedroom din?" Wani kallo ya mata mai kwantar da zuciyar masoyi,saidai fuskarsa a dan hade take,saiya zare rigar shaddar jikinsa,jinsa yake gaba daya a takure,don bazai iya tuna rabonshi da saka manyan kaya ba,banda wannan tafiyar da hajja ta tubure kan lallai bashi ba saka fingilallu kuma damammun kayan yahudu,bayan garin ma'aiki zashi.
Sai daya qaraso dab da ita ya dagata tsaye yana riqe da qugunta da hannu daya,daya hannun kuma yana warware rolling din doguwar rigar dake kanta
"Banason na raba komai da matata,nafison komai namu mu dinga sharing....bawai saboda babu wadata ko ikon siya ba,a'ah.....inason mu samu kusanci qauna da shaquwa matabbaciya.....irin wadda a tarihin masoya kaf na duniya babu masoyan da suka samu shaquwa da fahimtar juna irin tamu" yakai qarshen zancan sanda yake fidda mata doguwar rigar jikinta,saiya zamana daga ita sai under wear da vest,kaman maye haka ya bita da kallon qurilla,yadan ja baya kadan ta yadda zai samu damar kallonta da kyau,saiya miqa hannunsa i zuwa muhallin dako yaushe yake tsone masa idanu,ya kumayi tafiyar ruwa da nutsuwarsa,gocewa tayi tana dariya,a 'yar tarayyarsu ta qididdigaggun kwanaki,ta gama fuskantar shi din mutum ne da yake qaunarsu,suka kuma matuqar tafiya da hankalinsa,cikin zafin nama ya bita zai cafko yana cewa
"Oh....no,don Allah,kada muyi haka dake pleasessssssss" dai dai nan ya samu nasarar kamotan,ya mannata da jikinsa yana sauke qatuwar ajiyar zuciya,tsayin minti guda kafin yace
"Duk sanda nake tare dake,nakan manta wanene ni....ashe dai da gaske kedin aljannar duniyata ce,don Allah....ki rayu dani,mu mutu tare" martani ta maida masa ta hanyar rungumeshi tsam itama,yadda takeji cikin zuciyarta bazai misaltu ba,a hankali take rada masa wasu kalamai cikin kunnuwansa,kalaman da suka sake rura wutar dake ruruwa cikin zuciyarsa,suka kuma sanya ya daina gane komai,cikin qaramin lokaci suka qwace dukka hankali da nutsuwarsa,wanda hankalin da nutsuwar basu dawo masa ba,har sai data kaishi wata duniya ta daban,duniyar da kullum yake bege da muradin tabbata a cikinta matuqar da zahran ne.
Kwance saman qirjinsa wanda tuni bacci yayi awon gaba da ita,yayin da shi kuma yayi nisa cikin duniyar tunaninta,duk da tana tare dashi amma baya gajiya da tunaninta,bai taba zaton cewa qaunarta a zuciyarsa tayi nisa har haka ba,bai taba tunanin zuciyarsa zatayi nisa da zurfi cikin soyayya har kamar haka ba,ashe ubangiji sonshi yake da rahama daya sanya matsaloli tsakaninta da manemanta a baya,ashe tanadinsa ce ubangiji yayi masa,shi yasa yake rusa dukkan wata alaqarta da wani.
Qarar da wayarsa tayi ita ta katse masa tunaninsa,sai daya miqa hannu sosai sannan ya iya lalubota,saboda fadawa da tayi gefan gado,yana duba sunan yaga hajja ce,saiya sauke zahran yaja mata bargo ya lullube mata jikinta,ya zura qafafunsa qasan gadon sannan ya amsa wayar
"Wai ina kuka tsaya ne haidar?,baka duba lokacine?,kusan awa uku?,hafsa tace a hanya kuka sauketa,kuna ina ne?" Ya bude baki zaiyi magana sai yaji muryar tasa a dakushe take,don haka ya danyi gyaran murya
"Banason qaniya....ka bude baki kayimin magana"
"Muna gidanmu.....,gobe ko jibi zamu shigo mu sake yi muku ban gajiya"
"Gidanku?,wanne gidan naku"
"Gida na na gaida gida dubu" salati hajja ta saki tana sallallami,jin haka sai kawai ya datse wayar,yama kasheta gaba daya,ya tashi ya lalubo wayar zahran itama ya kasheta,ya hadasu gaba daya ya watsa cikin sif sannan ya wuce bandaki yana murmushi qasan ransa,yasan za'asha daru da rigima,tana can qila ta tadawa kowa hankali,shikam bazai dauki wannan gantali da aure da hajjan keta yi musu ba,ana masa wasa da hankali kamar zahran bata gama zama mallakinsa ba.
Kamar kuwa yadda yace din,kwanansu uku cikin gidan su kadai,babu abinda suke banda morewa amarcinsu,gami da sake dasawa juna sabo da shaquwa mai qarfi a tsakaninsu,cikin kwanakin zahran tayi mugun sabo da soyayyarsa,wadda ya dinga koyar da ita salo salo cikin dabara da tsabar qwarewa,sau tari takan saki baki tana tambayar kanta
"Da gaske ya haidar ne wanann?" Duk inda ta motsa yana maqale da ita,tare suke komai,girki gyaran gidan,wanke wanke,kai hatta ma wanka bai bari ta shiga ita daya,idan ko ta sake tayi ita kadai to tayi aikin banza,don sai ta sake,suna aikin yana tsokanarta,wasan guje guje sam batasan a inda ya koya ba,ya qware a sosai a tsokana,idan mamaki ya cikata ta saki baki da ido tana kallonsa,saiya hure mata ido da iskar bakinsa,wani lokacin kuma saiya hade bakinsu waje guda,yace bari ya rage mata mamakin da takeyi,saiya tsotsi lips dinta iya son ranshi sannan ya saketa,ya dubeta yace
"Kairukum kairukum li ahlihi,wa'ana kairukum li ahly. 禺賷乇賰賲 禺賷乇賰賲 賱丌賴賱賴 賵丕賳丕 禺賷乇賰賲 賱丌賴賱賷,annabi yace mafi alkhairinku shine mafi alkhairinku ga iyalansa,sai annabi da kansa yace nine mafi alkhairinku ga iyalina,yana taya iyalansa dukka ayyukan gida da kika sani....ni din waye da bazanyi koyi da wanda akayi duniya da lahira saboda shi ba?" Maganganunsa sunyi matuqar burgeta ba kadan ba,da gaske ne duk wanda ya hukunta wani mutum bisa wai wai ko kuma kallonsa da yake daga nesa ba tare da ya mu'amalanceshi ba,zai aikata babban kuskure,ashe kalar abinda umminta keta mata kwadayi kenan?,lallai uwa uwa ce,a kowanne hali makomar rayuwar ahalinta na nan cikin ranta,komai runtsi komai wuya,Aliyyu miji ne 蓷aya da 蓷aya,mai tarin nagartar da kaso mafi yawa daga cikin mazan yanzu suka rasa irinta
(Idan baki samu ba,saiki roqi Allah ya gyara miki dabi'ar naki mijin,ya zama me koyi da sunnar ma'aiki,idan kuma kin samu,saiki godewa Allah,kuma kada kiyi wasa da damarki,koki wofantar da baiwar da Allah yayi miki,idan budurwa ce ke....kina da sauran dama,ki fidda so ko burgewar dukkan wani qyale qyalen duniya daga ranki,ki tsayawa sallar dare,kiyita gayawa ubangiji da roqarsa ya zaba miki miji na gari,ba mai arziqi ko kyau ba,miji na gari ya wuce dukkan wani irin nau'in miji daya mallaki dukiya kyau mulki ko sarauta,miji na gari shine abu mafi tsada da daraja cikin rayuwar diya mace kaf!!!,da zarar kin dace dashi,tofa matar du wani mai mulki kudi kyau ko sarauta saidai ta biyoki a baya,matuqar itama ba katari tayi da irin naki mijin ba,ubangiji ya wadata qannenmu 'yan uwanmu da 'ya'yanmu da nagartattun maza馃げ馃徑馃げ馃徑馃げ馃徑,dama daukacin matan musulmi gaba daya).
Cikon kwana na hudun suka shirya wajen sha biyu saura suka nufi gida,duk a kunyace take,saboda batasan da wacce fuska zata kalli jama'ar gidan nasu ba,musamman mama da umminta,har gwara hajja an saba gauraya.
Sai da suka shiga kowanne sashe suka gaidasu sannan suka wuce sassan hajja,ga mamakinta ba wanda ya tsokanesu ko ya tada maganar,bare ya nuna yasan me ya faru,suna sallama sukaci karo da akwatuna masu azabar kyau blueblack guda takwas cas,kowacce shaqe da kaya a cikinta,wasu daga cikin 'yan uwan hajja ne suka gama kalla,da alama tafiya zasuyi ma,don har sun miqe.
Ango da amarya suka kirayi sunansu dashi,itadai ta murmusa ta gaidasu cikin kunya,yayin da aliyyu ya fuske cikin salon miskilancin nan nasa,sai zahran ta dinga satar kallonsa ta gefan ido,ya zama aliyyun nan sak dake basu tsoro cikin gidan,suna hada ido ya kashe mata idonsa daya,ya mata nuni data rage kallonsa,yana taba zuciyarsa,saita janye idanun nata tana sakin murmushi,dai dai nan suka hada ido da hajja wadda ta gama sallama da baqinta suka fice
"Sannunku marasa kunya feqaqqu....bari na fara da babban rasa kunya beran tankan.....kaga....hade girar gefe da gefanka ba zasu tsoratani ko su hanani cima mutunci ba.....da zaka daukemin yarinya ka kaita gidanka da kanka anyi biki ne?,ko ce maka akayi ma ciniki ya fada ne?,ance maka ta gama zama taka?,aro ne na shekara daya shine zaka zaqewa mutane....." Tana tsaka da bambaminta ya miqe yana cusa wayarsa aljihun wandonsa
"Don Allah ki hutama ranki.....don ciniki ya dade da fadawa....ki godewa Allah da bata shigo tana miki amai bama....idan sadakinne ya miki kadan ki fadi dame kikeso a qara yawanshi" baki ta kama tana zare ido,yana ganin haka yasan ya soma maganin rigimar hajjan,saiya juya ya fara takawa zai fita daga falon,ba tare daya ma kalli kayan lefen da yasan shi ya bayar aka hadashi ba,duk da yaga akwati daya ta dadu akwai,har zai fita saiya waiwayo,xahra nata danne dariyarta,hajja na tsaye inda take tana binsa da kallo
"Kuma ga amanar matata nan....quda idan ya tabata saina ciki tara"
"Haidar....aliyyu,dani kake maganar" ta fada cikin daga murya sanda yake ficewa daga falon,cikin ransa tana qyaqyacewa da dariyar abinda ya yiwa hajja.
Guri ta samu tana zama tana hade ranta tsaf,duk da cewa zallar farinciki ne qasan ranta me tarin yawa,already sun riga sun gama magana dasu abba babba kan abarsu tunda har sun hada kansu sunma wuce gidansu,shi dama taron biki al'adace kawai,tunda an qulla auren yadda musulunci yace,kuma jama'a sun shaida shikenan
"Gafara kika tsareni da ido mara kunya....ja'ira kamar ba kece nan kamar zaki mutu ba saboda mun aura miki shi,ashe lambu lambu kikayi,qiris kike jira" wannan karon dariyarta kubcewa tayi,sai kuma tayi saurin mazewa
"To tunda nafi qarfina aina haqura na zauna ko?,badai za'a ce banyi biyayya ba" murmushi ne ya qwacewa hajjan itama,tasa hannu tana daga kayan,don ita duk yadda ake kallon lefan bata samu gani ba saboda gajiyar tafiya da take tare da ita,sai yanzu tadan samu ta warware.
Zahra dai bata sanya hannu ba har hajjan ta gama kalla tana daga gefe a zaune,har saida hajjan da kanta tace ta matso ta gani mana,saita girgiza kai alamun a'ah,hakan saiya burge hajjan,duk da cewa an riga da an zama daya,amma har yau akwai abubuwan da zahran ke kunyar yinsu,ba kamar 'yammatan yanzun ba,da wata ma randa za'a kawo lefan tana gidansu,masu kawowa ko qofar gida basa gama kaiwa take tsallen albarka ta fito aci gaba da gani da ita,tana gani tana comment,tana hanawa a tattaba mata wasu abubuwan,Allah ya kyauta.
*_BAYAN KWANAKI BIYU_*
Walima gagaruma haidar din ya shirya a sabon gidan nasu,ranar walimar aka taho mata da akwatunan lefanta,saiya zamana kamar itace a madadin yinin biki,sosai aka ci aka sha,aka gabatar da wa'azi da nasihohi ga mata kan zamantakewar auratayya,wadda ta ratsa zukatan mata da dama,dangi sosai suka halatta,gidan yayi cikar kwari,saidai anyi taro lafiya an kuma watse lafiya.
Rayuwa suka ci gaba da gudanarwa mai cike da tsantsar soyayya da qauna ta kwatance,idanu ko wanxuwar wani a waje baya hanasu nunawa junansu zallar son da sukewa juna,mutane da dama na mamakin haidar din,saboda kowa ya sanshi da miskilancinsa ya sanshi,sai gashi lokaci daya zahra ta sukurkutashi.
Tako wanne fanni yana jin zahran ta cancanci ayi mata kowanne iri so,don dan xamansu da 'yan satittika yasa ya gama fahimtar wacce irin macace ita,ta dauki dukka halayen umminta wajen biyayya wa miji da iya kula dashi,wani irin salo da yake da tabbacin wasunsu ta samosu ne daga wajen hajja,wanda sau tari akwai lokuttan da zai samesu suna hira da ita,tana bata labarin yadda mata ada ke biyayyawa miji ba irin matan yanzu ba.
8:30 pm
A nutse take kai kawo tsakanin kitchen da parlour tana shirya masa abinci,duk inda ta gifta idanunshi yana kanta,shigar da tayin ta dauki hankalinsa matuqa da gaske,duk sanda xata gifta saita bar masa qamshinta,bai taba zaton mata nada son turare haka ba sai da zahran ta kasance matarsa.
Plates ne na qarshe data ajjiye,sai itama ta samu waje tana niyyar xama,hannunsa ya miqa mata yana lumshe ido,ba bata lokaci ta saka hannu nata cikin nasa,hakan ya bashi damar jawota jikinsa,yayi mata mazauni saman cinyarsa,hannayensa ya sanya dukka yana yawo dasu saman jikinta,bata hanashi ba,saboda tasan abinda yafiso kenan,saima ta kwantar da kan nata saman kafadarshi,lungu da saqo na jikinta yake bi yana sansana,tsahon wani lokaci sannan ta kira sunanshe cikin wata lallausar murya
"Hubby na...."
"Makaranta fa....exam ta kusa" shuru ne ya biyo baya,har sai daya kammala abinda ya soma din,saiya dubeta da lumsassun idanunsa da suka jirkice suka qara qanqancewa
"Bana jin xan qyaleki ke kadai xahraty.....zamu tsara komai mu fuskanci komai tare,zamuyi karatun jarrabawa tare,zan kaiki ki dinga zanawa muna dawowa gida tare....nasararki nasara tace,amma da zarar kin kammala,zamu koma abuja,zan koma bakin aikina,yanzun hutun aikin da mukajeyi nake mora,sai kuma yazomin a daidai,Allah ya sanyawa hutun albarka....na mallaki xahrata a cikin sa,ta xama haidar....haidar ya zama zahransa" murmushi tayi,ta juyo gareshi,ta saka hannayenta duka biyun ta saqalo wuyansa,fuskarta dab da tashi
"Na gode sosai da wannan sadaukarwa daka yimin....ina fata ni da kai zamu dawwama a haka,na gode sosai" ta qarasa fada tana hade fuskarsu waje daya,sai kuwa ya sake kai mata cafka,cikin sauri ta zame tana cewa
"Abinci yallabai.....ayimin afuwa a fara cin abinci" ta fada tana saluting nashi kamar yadda sukewa manyansu,idanunsa ya lumshe a kanta sannan ya budesu yana fidda murmushi,yana so tana kuma burgeshi duk sanda ta tsaya gabanshi haka ta qame tayi saluting nashi,bai taba ganin kyau ko burgewa a irin wannan gaisuwar ba sai da zahranshi ta fara yi masa irinta,shima maida mata yayi yana murmushi,har ta zauna bai dauke idanunsa daga kanta ba.
Kamar yadda ya fada din kuwa tare suka tsara komai,kamar yadda yake kama mata aikin gida haka yake tayata karatun jarrabawar,bata taba tunanin haidar din gifted bane,mai matuqar ganewa tarin basira da kuma dabarun koyar da karatu,bata taba marmarin karatu ba,bata taba jin karatun jarrabawa me dadi ba,wanda babu ginsa ko qasawa a ciki ba sai wannan karon,yasan tarin abubuwa game da abinda ta karanta din,idan tace ta gaji yasan yadda zai mata ta samu relief su dora daga inda suka tsaya,su huta suyi bacci su tashi suci gaba,yace so yake ta fita da sakamako mai kyau wanda zata bar tarihin cikin makarantar,kamar yadda shima yabar tarihi cikin tashi makarantar daya gama.
*_BAYAN WASU KWANAKI_*
Yana tsaye daga saman dining yana hada musu tea shi da ita a cup biyu,yanayi yana duba agogo,a shirye yake tsaf cikin wata dakakkiyar shadda sabuwa fil ruwan zuma,wanda saida aka sha daru shida zahran tashi kafin ya yarda ya sanyata,shiri ne na tafiyarsu jarabawa a rana ta farko,ya sake daga kansa yana duban hanya,sai gata ta fito dauke da plate a hannunta,sanye take da wani lafiyayyen lace itama ruwan zuma,dinkin riga da plain zani,sabida yace bai yarda ta saka skert ba.
Duban fuskarta yake sosai,tana tahowa inda yake din tana yatsina fuska
"Yau wani laziness kikeji hubby,kodai exam dince tun kafin a fara take bugunki?,karki fa damu,ina da zato mai qarfi a kanki,kisa a ranki an gamata kawai" ajjiye plate din tayi a gabansa,ta hade hannayenta waje guda 馃檹馃徑
"Bani da haufi tsoro ko shakka indai sojana yana kusa....mutumin dake iya kula da qasarsa ma bare ni mutum daya?,....na yadda da kaifin basirarsa,hakanan inda malami ne shi xaiyi wuya a sami malami kamarsa kaf qarninsa kuwa,koda bayan mutuwarsa ne da shekara dari" wani kallo ya kafeta dashi,yana jin kamar ya hadiyeta,gwana ce wajen iya tsara kalaman da zasu tafi da hankalin dukkan mai hankali,ya rasa amsar da zai bata illa tukuicin lallausan murmushinsa,wanda ya jima yana shaida mata ya tanadeshi ne kawai saboda ita,ta kuma yarda da hakan dari bisa dari,don takanyi mamakin yadda yake komawa zakin gaske a gaban duk wata mace koma bayanta,hatta da qannensa shakkar nan tasa tana cikin zukatansu
"Kawai dai qwan nan ne,tunda na fara soyashi zuciyata ke tashi...." Ta amsa mishi tambayarsa ta farko sanda take daukar cup din tea din daya miqa mata,idanu ya kuma zura mata yana karantarta sanda take kurbar tea din,har sai data lura,saita dage masa girarta dukka biyun,alamun tambayar lafiya?
"Anya ko hubby....anya ban jefa qwallona a raga ba?" Ido ta fiddo tana aje cup din
"Bana tunanin haka.....haba watanmu nawa sojana....kawai ko a gida banson qarnin qwai,kuma ko xanci ma saina yanka wadatacciyar albasa akai nake ci" kafadunsa ya dage yana bude plate din chips da qwan data aje masa
"Ohkey....amma ko chips din ai kyaci ko?" Fuska ta kyabe cike da shagwaba tana maqale kafada
"Nifa qamshinsu ya gama cikamin ciki.....saidai ka taimaka ka siyamin meatpie a wannan gurinnnnn" dariya taso bashi,tunda ya taba siya mata meatpie din ta maqale masa,saiya maqale kafada shima
"Naqi wayon,saidai idan kin yarda nima....." Qarshen zancan ya furta mata qasa qasa,sarai ta gane abinda yake fada,saita sakar masa kukan shagwaba,ta dauke hand bag dinta dake gabansa ta sauko daga dining din tana diddira qafa,dariya sosai yakeyi shima,ya aje abincin ya biyo bayanta.
Har suka je suka dawo yana tattalinta,suna gama exam din ta zagaya inda ya zauna zaman jiranta ta sameshi,bata yarda kowa ya biyota ba,ya gama ganeta amma tana togewa,kishinsa take hakan ya sanya bata hada kowa dashi.
Da taimakon Allah da kuma agazawar haidar din ta kammala jarrabawar cikin babbar nasara,babu qunci ko takura ko wahala mai yawa,wanda dalibi ke tsintar kansa a duk yayin jarrabawa,wanda tasan cewa sirrin hakan na tattare ne da dafawar haidar din.
Ta yadda da cewa samun masoyin gaskiya babban dace ne a rayuwa,hakanan rashin sa'a a soyayya kada ya sanya mace ta yanke tsammani da samun haske kuma mabudin yayewar dukkan matsalarta,abu daya ake buqata shine,ki sake hankalta a yayin da duk wata qaddara ta sameki ko kika aikata kuskure,kiyi qoqarin zama me kamewa,ki ninki zurfin dora abubuwanki saman sikeli da mizani fiye da ko yaushe,sannan ki zafafa da addu'a,babu ji babu gani,babu daga qafa babu hutu.
Imani da qaddararta da tayi,ta karbeta hannu bibbiyu,ta kuma tsarkake zuciyarta,ta riqe mutuncinta da mutuncin gidansu,ta kuma yi biyayya ga magabatanta shi yasa Allah ya dubeta yayi mata musaya mafi alkhairi,ba shakka yaudara nada zafi da ciwo,tana da qarfin da zatayi barazana ga rayuwar wanda aka yiwa ita,saidai kuma girman ubangiji ya shafe komai,qudirarsa da alkhairinsa kan bayinsa yawa ne dashi,koda yaushe ko godewa ubangiji bisa kowacce irin nau'in qaddarar daya tsagawa rayuwarka,tayi maka dadi ko bata yi maka ba,wannan shike nuni da cikar imanin bawa.
Randa sukayi paper din qarshe ta dinga jin jikinta sama sama,haka dai ta daure akayi sallama da qawaye da abokan karatu,ko cikin mota ma cikin seat ta lafewa haidar din,daya tambaya tace babu komai gajiya ce,bai gasgatata ba amma ya qyaleta,saboda ya lura kaman batason magana ne,zatonsa bai tabbata ba sai da suka bude falo zasu shiga,saita tafi luu zata fadi ya tarota,ya qarasar da ita saman kujera yana mata sannu,gaba daya ya rude cikin qanqanin lokaci,ruwa ya bata mai sanyi tasha,sai numfashinta ya koma normal
"Sannu"
"Lafiyata qalau" tayi qarfin halin fada,saboda zallar damuwar data hanga tattare dashi
"No hubby....baki da lafiya" don kada tayi masa musu kota bata masa lokacima yasa bai tsaya sauraren kalaman bakinta ba ya dauketa cak sai bandaki,ya ajjiyeta sannan ya tara mata ruwan wanka
"Ki wanka na baki minti goma,zan shirya na kaiki kiga likita" saiya fiddo mata towel soson wanka da sabulun wankan ya aje mata,sannan yaja mata qofar ya rufe,saiya wuce daya bandakin shima.
Idanu ya zuba mata sanda ta gama shirin ta fito,saiya riqe hannunta sosai
"Duk yadda kika kai ga boyemin baki da lafiya hubby bazai boyu ba,kin manta ne,ni dake ruhi daya ne yake rayuwa a gangar jiki guda biyu?" Murmushi ta sakar masa,saiya karata da jikinsa suna takawa a hankali yana sake gaya mata wasu kalaman da suka sanyata sakin ajiyar zuciya a jejjere.
A qalla ya kusa minti talatin zaune shida ita cikin motar riqe da hannayenta yana jero mata kalaman nuna zallar qauna da godiya a gareta,tun lokacin da likitan ya shaida masa tana dauke da juna biyu gaba daya yayi wani irin rudewa,ko a yanzun ma hawaye zahran ke futarwa,saboda kalaman da yake amfani dasu a kanta sun girmi kanta,kalamaine da take da cikakken yaqinin ba kowacce mace bace Allah yake mata baiwa da samun mijin da zai furta mata su ba
"Gobe as early as possible zamu wuce abuja...thank god kin gama abinda ya zaunar damu,kinji kuma yace kin da buqatar cikakken hutu,so zan buqaci hajja kawai ta bamu baba gaje mu wuce da ita....but...banda fadar dalili,don i sure tsaf hajja zata hanani tafiya dake" dariya sosai ya bata data tuna da hajjansu,hajiya hajja,ayi tsiya ayi dadi,tana sonsu tana tattalinsu,amma idan tsiyarta ta tashi har su saita dandana musu.
Kamar yadda ya tsara kuwa tun a daren ya gama hada musu abinda yasan suna da buqata,ba wasu kaya bane masu yawa,tunda komai a kwai a can,ya kira hajja yace baba gaje ta shirya gobe zata rakasu abuja,ta fara masa tambayoyi yace ta bari idan yazo gobe zasuyi magana,ranar kusan kwanan zaune yayi,rabi bacci rabi idanunsa biyu,duk sadda ya farka saiya tuna cewa wai shima ya kusa zama uba?.
Qarfe bakwai a gidan tayi musu
"Wai tafiya abujan na meye haka saikun daukemin gaje kuma?" Zahra ce ta marairaice fuska
"Haba hajja,can dinfa babu dadi wallahi xaman shuru" waiwayawa tayi ta dubeta
"To ba sai ya barki nan ba,ya dinga zuwa?" Baki zahra ta tura
"Habba hajja...a'ah wallahi,ni mijina zanbi"
"Na shiga uku ni fatsima.....yau naga abinda yafi xare tsayi.....innawuro ni kike gayawa haka kanki tsaye." Ilham da husna me zasuyi in banda dariya,baba gaje dake tsaye a gefe tana tayasu,shikam haidar dama bai shigo ba yana wajensu abba babba suna gaisawa,daga can ya tsaya wajen ummi don bincika me dame take da buqata,duk da bata rasa komai,amma bakan baisa ya daina hidima gareta ba,kwata kwacin yadda zaiyima gidansu.
Yana shigowa kuwa tace
"Kama hannun matarka ku ficemin,Allah ya kiyaye hanya,nikam yanzu kunfi qarfina,Allah rabamu qalau" yasan wata tsiyar aka tufka sai baice komai ba banda dariya da yake dannewa,amma ya godewa Allah da hajjan bata harbo jirginsu ba,haka suka fice bayan sunwa kowa sallama.
Shida ita a baya suka zauna,don bazai iya juriyar awanni suna waje daya amma ba ita a gefansa ba,baba gaje da driver suna gidan gaba,hakan ya baiwa zahra damar kwanciya sosai bisa jikinsa,don sam bata jin qwarin jikinta,shi kuma ya tattarota cikin jikin nasa sosai,ya gyara mata yadda zata fi jin dadin kwanciyar.
Tun basuyi nisa ba kiran hajja ya shigo wayarshi
"Anya lafiya zahra'u kuwa take?,ni sai da kuka wuce naga yanayinta baiyimin ba" cikin dakiyar nan tasa yace
"Lafiya take hajja....wani abu ya faru ne?"
"Um um....amma kawai sai nakega kamar me yaron ciki....koma meye ne ka kula da ita da kyau,sannan idan akwai wani abu da baku gane mishi ba kayi hanzarin dawomin da ita gida....kana jina?"
"In sha Allah hajja"
"Allah yayi muku albarka,ya albarkaci rayuwarku,ya tsare dukkan abunqi"
"Amin amin,Allah ya qara girma da shekaru masu albarka" ya fada cikin jin dadi,har kullum yana ganin girma da qimar tsohuwar,saboda zallar qauna da take nuna musu shi da soulmate dinsa.
Zuwansu da baba gajen ba qaramin ma'ana yayi ba,domin itama ta hangi abinda hajjan ta hanga,duk da basu gaya mata ba,don haka bata barin zahran tayi komai,komai na gidan ta dauke shi,ita kanta zahran ba qaramin dadin zama da baba gajen takeyi ba,tana debe mata kewa,hakanan duk randa ta tashi jikin babu dadi zata gaya mata wani abu da zatayi wanda zaisa taji sauqi da qwarin jikin nata.
Ta fannin haidar kuwa ta samu dukkan wata kulawa taimako da qwarin gwiwa a matsayinta na mace mai haihuwar fari wadda batasan yadda abun yake ba,shi kansa bai barinta tayi wani abu da zai wahalar da ita,ta kowanne fanni ta zama 'yar lele ta gaske.
Hajja batasan da zaman cikin ba,sai sanda ya samu hutu na sati guda,yace su shirya suje kanon su roqi hajja tabar musu baba gaje,a lokacin cikin nata ya shiga wata na uku,kuma ga duk mutum mai saurin tsinkaye da daukar haske zai fahimci akwai ciki tare da zahran,tayi wani kyau,hakanan ta sake cika,fatarta ta qara haske,sau tari haidar kan sanyata gaba da tsokana,ya hanata sakat,bini bini yana shafa fatarta,idan tayi qorafi sai yace
"Ke dince ki qara wani kyau,fatarki kamar atafa,karfa nan gaba na soma kasa gane hanyar fita daga gida,ko naje nayi shirme gaban manya ki jawomin hukunci" saita tureshi tana tura baki,sabida ita gani take kamar tsokanarta yake,don rannan daya goyata ya zagaya da ita cewa yayi ta sauka,ta fara ninka nauyinta,sai data dinga masa kukan wasa sannan kuma ya lalace wajen lallashi da bata haquri,ire iren yanayin rayuwarsu kenan,idan ka ganshi a cikin gida saika rantse da Allah ba ALIYYU MAS'UD DABO bane,sojan nan daya kasance dodon 'yan ta'adda da marasa gaskiya dake cikin qasar nan,idan ka ganshi a waje sanye da kaki ba zaka ce zaka sameshi a haka cikin gida ba.
*_BAYAN WATA TARA_*
Tsaye suke cikin dakin hajja,taja rungume cikin jikinsa saidai ya rungumeta ne ta bayanta saboda tsinin cikinta wanda ya dora dukka hannayensa biyu akai,yana jin yadda yaron cikinta ke motsawa,kai kace zai fasa cikin ne ya fito,bai dauke hannun ba har sai daya tsagaita da motsin,suka saki ajiyar zuciya shida ita a tare,sannan ya juyo da ita suna fuskantar juna.
Tausayinya yakeji fiye da kima,koda can shi mutum ne mai tsananin tausayin mace,macen ma ace mai juna biyu,yau saiga abuj cikin gidansa,a jikin mace mafi soyuwa duk duniya a wajensa baya ga iyayensa
"Banda hajja ce hubby duk duniya babu wanda ya isa ya sanyani na wani kawoki wankan gida" murmushi ta saki,ta sanya hannunta tana shafan kwantaccen gashin fuskarsa da ko yaushe yake qara masa kyau da kwarjini
"Kasan dai hajja ta fimu damuwa da kwanunanmu....sannan tun ban dade da shiga third trimester dina ba tace ka dawo dani gida,yanzu idan baka kawoni ba zataga cewa kamar bata isa damu bane,bayan ina da tabbacin cewa tayi hakanne saboda amfanin kanmu" fuskarta ya riqe tsakiyar hannunsa,ya matso da ita dab da tashi,cikin softness yace
"Hubby....inason in zama mutum na farko da zaya dauki 'yarshi" yatsanta ta dora saman lips dinsa tana cewa
"Shshshs.....point of correction.....soja nakeso na haifa,jarumi kamar kai....mai kuma kama dakai" dagowa yayi yana murmushi,ya kama hannayenta duka ya riqe cikin hannunsa
"Little zahra ni kuma nakeso.....kuma inaji a jikina itace"
"Ok....ok,ba anyi yarjejeniya ba akan a bari har sai ranan?,duk wanda yayi wining zai zaba abinda yakeso mutum ya bashi..."
"Yes hubby" ya fada yana lakace hancinta,saita jefa masa harara
"Ka takurawa hancin nan nawa" dariya sosai ya saki yana cewa
"Ya qara kyau ne,kamar na dauke kayana na tafi dashi" tasan cewa girma ya qara fiye dana da,amma ba zai taba fitowa ya gaya mata hakan ba,saidai kullum idan ya dameshi da cewa hancinta yayi qato ko yayi muni sai yace mata suyi musanye da nata,ko ta bashi kayanshi yana so shi a haka.
Rigima ta soma yi masa kan ta gane dariya yake mata saboda tayi muni,lallashin duniya taqi shuru saboda bai daina dariyar badai,har sai da hajja tazo ta tankada qeyarsa sannan aka samu salama.
Tana zama saqonsa yana shigowa wayar tata
_zan qara kwana daya ko Allah zaisa ina da rabon ganin baby na,but please kada ki sanarwa kowa_
Idanu ta zaro cike da mamakinsa,muhimmin taro suke dashi da mr president a jibi amma yace bazai tafi ba,saita koma daki ta kirashi tana son tayi convincing dinsa kan ya tafi saboda muhimmancin taron amma fur yaqi,dole ta rabu dashi,ya daddogara ta dawo falo saboda ciwon mara da baya da yaketa tsunkulinta.
A falon tayi kwanciyarta suna hira da hajja,jifa jifa tana cije lebe idan aka mintsineta,saita dinga mamaki,don bata taba ciwon mara haka mai naci ba kamar nayau,ana mintsinarta amma da tayi daya biyu uku a rana shikenan sai washegari,amma nayau din yaqi barinta batasan dalili ba.
Ciwon bayan da taji yana yawa saita koma daki da niyyar kwanciya ko zai ragu,saidai tana shiga kamar an dado ciwon ne,tayi tayi ta zauna ta kasa qafarta ta riqe gam,dole ta dinga qwalawa hajja kira,sai gata bagatatan ba shiri.
Tuni ta fahimci haihuwa ce,ta aika umaima ta kira mata mamarta matar abban tsakiya,ta sanya ilham kuma ta shiga tsohon dakin zahran ta dauko kayan da aka ware don tafiya asibiti.
Kafin ilham ta dauko kayan maman umaima ta qaraso ciwon ya ta'azzaran mata,ta kasa tafiya bare akai ga batun zuwa asibiti,don haka hajja tace adan dakata ko zai lafa mata sai a tafin,saidai ina,gaba kawai ciwon yakeyi,wanda harta kasa jure masa tana neman taimako,baba gaje da kuma hajjan su suka riqeta lokacin da suka fahimci haihuwar tazo gadan gadan,cikin ikon Allah da taimakon addu'a cikin mintunan da basu wuce uku ba kukan jariri ya karade sassan hajjan gaba daya.
Kusan tare suka saki ajiyar zuciya ita da hajjan,farinciki mara misaltuwa ya sauka a zukatansu gaba daya,hajjan ce da kanta,duk da tsufa ta dauke yaron daketa watsal watsal cikin qazantar da suka fito tare yana canyara kuka,ta kasa daurewa saidata rungumeshi cikin jikinta qwalla na gangarowa daga idanunta
"Alhamdulillah....alhamdulillah" shine kawai abinda yake fita daga bakinta,sannan ta qarasa dab da zahran ta dora mata yaron saman cikinta tana shafa sumar kanta
"Sannu takwarata,sannu da qoqari,barka da arziqi" saita lumshe idanunta cikin matuqar jin kunya,gefe guda na zuciyarta farinciki na mamayeta,idanunta kan fuskar yaron,fuskar da ko ba'a wanketa ba ta bayyana kamar ya Aliyyunta daya dauko,sak shi,kamar kaki yayi ya aje,take wata qauna irin wadda ubangiji S W T yake dasawa a zukatan bayinsa tsakanin uwa da 蓷a ta fara kwaranya a zuciyarta.
Kafin kace meye wannan labarin haihuwar ya zaga gidan,tuni aka soma gyaran zahran da jaririnta,cikin qasa da awa guda tayi wankanta da ruwan dumi,an goge yaron da kyau,an gyara mata dakin hajjan yadda zai dace da yanayin jaririn,hajjan tasa an dora mata kunu bayan ta soma da bata tea mai uban kauri da bournvita saboda ruwan nono.
Sau wajen biyar yana attempting bude gidan nasa ya shiga sai yaja tsaki ya fasa,yayi imanin koda ya shiga baqiqqirin gidan zai masa,bazai ma iya zama ba,saboda babu fitilar gidan,daga qarshe kamar wanda ake umarta,yaji kawai zuciyarsa ta yanke masa ya koma gidan hajjan ya wuni da zahran,idan yaso idan dare yayi ma ya bude tsohon dakinsa na gidan yayi kwanciyarsa,duk da babu komai yanzun a dakin sai katifa,ya tabbatar sai yafi samun relief akan ya kasance tana nesa dashi.
Tunda ya doso gidan yaji gabansa yana faduwa,sanda shamsu ya bude masa qofar gidan ya ga kamar yanason magana dashi,amma bai tsaya ba sai daya isa inda suke aje motocinsu,yana kashe motar kuma yayi sassan hajjan.
Sanda ya shigo yayi dai dai da lokacin da jaririn ke kukan neman nono,baba gaje na kan zahran tana gwada mata yadda ake feeding yaro,tana ta dariyar rashin sabo irin na zahra
"Saiko kin dage,don na fuskanci me gidan nawa acici ne".
Tuntube ya kusa ci da filallukan falon hajjan saboda yadda zuciyarsa ta bashi amsar zahransa ce ta haihu yana qaryatata,banda ingarma ne kuma tsayayye da faduwa zaiyi qasa warwas,ko takan hajjan dake masa magana baibi ba yayi inda yaji kukan na fitowa wato dakin gadon hajjan.
Kyakkyawan gani kuwa idanunsa suka masa,zahransa rungume da kyakkyawan baby cikin jikinta tana shayar dashi,idanunta a runtse da alama ta jin zafin yadda yake tsotso ne,tashi guda tayi wani mugun kyau,fatarta kamar an qara mata sinadaran kyau,baisan ya isa garesu ba saida yaji muryar baba gaje dake fita tana cewa
"A barshi yasha sosai kafin a cireshi,ruwan maman sai yafi saurin zuwa,idan kin gama saiki magana zaku asibiti su sake tabbatar da lafiyarki"
Qamshinsa ne kawai ya sanar mata da zuwansa,saita bude idanunta a hankali daga runtsesun da tayi,take suka hada idanu,saiya miqe hannunsa a hankali ya riqe hannuta sosai,yasa daya hannun yana shafar fuskarta,ya kasa furta kowacce kalma,idan ta lura da kyau qwalla ce ta cika idanun nasa,itama dubanshi take murmushi na fita a fuskarta,a hankali taji ya qwato kalmar
"Alhamdulillahi rabbil Aalamin,Alhmdlhillazi bi ni'imatihi tatimmus salihat" ya dinga jerowa,saiya matsa gab da ita ya manna mata wani dogon kiss a goshinta kamar xai hada da numfashinsa,sannan yayi kissing bayan hannunta,ya sake matsawa a hankali ya bude fuskar yaron yayi bismillah ya tsugunna yayi kissing goshinsa shima,ya dago a hankali suka hada ido,murmushi yaqi yankewa daga fuskarsa
"Sannu hubby....sannu zahraty" addu'a ya shiga jero mata na fatan alkhairi ita da iyayenta,wanda hakan har sai daya kusa sanyata kuka,sannanna hankali ta zare maman daga bakin yaron wanda tuni yayi bacci ta miqawa haidar din shi
"Ma sha Allah,littale zahra kinyimin kara mai yawa" dariya ya bata,cikin dariyar tace
"Duba dai,little haidar ne" idanu ya fiddo,sai kuma ya narke fuska
"Yanzu fisabilillahi saida kikamin wayo dai....shikenan....Allah ya raya little baba sa'id" sosai maganar tazo mata a bazata,haidar da gaske yake sunan abbanta ya sanya mata?,ya lura da irin kallon da take masa,saiya jinjina kai yana murmushi tare da bata qwarin gwiwa
"Eh,sa'id sunanshi,Allah ya albarkaci rayuwarsa,yasa kuma ya dauko halayyar abba qarami(shine sunan da suke gayawa mahaifin xahran sanda yana raye)" bata iya daurewa hawayen daya cika mata idanu ba saida suka zubo
"No....yau ba ranar kuka bace,ranar farinciki ce,muma mun zama iyali,mun fara aje iri,kimin alfarma karki bata mana ranarmu" yakai qarshen xancan yana rungumeta cikin jikinsa ita da jaririn gaba
"Allah ya faranta maka yadda ka faranta min,ubangijin al'arshi ya kula maka da rayuwarka yadda ka kula da tawa,ya zama jinka ya zama ganinka,ya kuma zama garkuwarka" idanunsa a lumshe yana jin wani yanayin mai cike da sa'a da nasarar rayuwa,gami da katari da macen aure ta gari yana tsumashi
"Ameen mace ta gari"
"Au koke koken rashin son auren dole kuke ko kuwa?" Suka tsinci muryar hajja na shigowa,saiya saketa,suka daga kai suna dubanta,ta wani hade rai da gaske taqi dariya
"Me kuka wani tsareni da ido....zuwa nayi karbar takardar zahra'u,don naga alama idan na qyale wata shekarar za'a maimaita abinda ya faru yanzu"
"Kamar ko kin sani,don saita haife mai sunanki ma.....nida hubby kuwa mutu ka raba.....mutuwa ce kawai zata shiga tsakaninmu,inma zaki murmushi Allah gwara kiyi" ya fada ko ajikinsa dariya ta subuce hajjan,don itama farinciki da take ciki tasan bazata iya boyeshi ba,duk sai suka tayata darawa suna tuna rigima irin tata
"Komai zanyi inayinsa ne saboda rayuwarku,na godewa Allah da ya nuna min hadin kan ahalina gabanin mutuwata".
Haidar na murmushi yace
"Bamu da abinda zamu saka miki dashi hajjanmu sai fatan gamawa da duniya lafiya,kije ki tadda mijinki cikin aljanna madaukakiya kuci gaba da rayuwa"addu'an fatan alkhairi sosai ya dinga jera mata zahra na amsawa da amin,zuciyar hajjan fari qal kamar tasu ta fita tabar dakin,bayan ta tunawa zahran ta shirya ta fito haidar din ya kaita a sake tabbatar da lafiyarta,ta fita tana sake godewa Allah kan tarin baiwa da ni'imomi da yayi mata.
*_TAMMAT BI HAMDILLAH_*
_Kada ki sake,kada ki bari damuwar wani d'a namiji ta hanaki sukuni,kada ki bari damuwar wani saurayi daya yaudareki tasa ki tsaida taki rayuwar cak,bayan shi yana can yana tashi rayuwar_
_rabu dashi,manta dashi,nuna masa bashi da muhimmanci cikin rayuwarki,kamar yadda ya nunawa duniya hakan a kanki_
_kada ki manta,idan dubu sun qika....dubu ke sonka suke kuma jiranka_
_sau tari abinda kake so saiya zamana ba shine alkhairi a tattare dakai ba,abinda kake gudu kuma shine alkhairi a tare dakai ba tare daka sani ba_
_zama mai hankali ta hanyar zurfafa tunaninka,kada ka yarda ka yankewa wani dan adam hukunci ba tare daka mu'amalanceshi ba,kada ka yarda ya fadi halin wane bayan baka zauna dashi zama na gaske ba_
_koda yaushe ka zama mai kyautata zatonka ga mutane,sai gobenka tayi kyau_
_MAZA kuji tsoron Allah,nasan bazan aureki ba,to bazan soma tsayawa zuwa zance wajenki ba,kona bata lokaci kan layin waya ina qona miki kati ko ina qona nawa katin ba,ina bata miki lokaci,ina dauke hankalinki daga kula maza 'yan gaske masu niyyar aurenki ba,KADA KU MANTA KAI YAYA NE,WATARAN KUMA UBA NE!,ZAKA HAIFA KO A HAIFA MAKA!,AKWAI KUMA HISABI,ALLAH BAYA QYAKE HAQQIN WANI AKAN WANI TUN NAN GIDAN DUNIYA_
*_muna miqa saqon godiya da jinjina a gareku masoya kuma makaranta litattafan zafafa,wadanda a kullum basa gajiya da sanya kudadensu su siya rubutunmu,ubangiji yabar qauna_*
*_muna neman afuwan wanda muka batawa,ko wanda muka yiwa ba dai dai ba,ko labarinmu ya batawa,ko bai masa yadda yaso ya kasance ba,dukkanmu ajizai ne,duk inda ajizi yake kuwa saiya nuna ajizancinsa_*馃檹馃徑
*_kurakuran dake cikin rubutunmu muna fata Allah ya yafe mana,ya bamu ladan dake ciki_*
*_ubangijin ya sadamu a rubutu na gaba,ya bamu aron rai da lafiya,yaci gaba da riqo da hannyenmu,ya kuma bamu damar rubuta abinda al'ummar annabi muhammadu zasu amfana dashi_*
*SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA,ASHHADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'A TUBU ILAIKA*馃檹馃徑馃檹馃徑馃檹馃徑馃檹馃徑to
0 comments:
Post a Comment