Bilki suka fita don saka Meenah a makaranta.
Gobarau Academy itace makarantar da suka
nufa, da zuwansu da komai basu wuce minti
talatin ba aka kammala komai aka saka ta Pre
nursery, duba da shekarunta kuma a k'a'idar
makarantar idan yaro bai kai shekara 3 ba to
baza'a saka shi nursery ba daman. Daman 'yan
pre nursery ba'a saka musu uniform.
A ranar aka barta makaranta kuma ko kuka
batayi ba da su Hamza zasu tafi don ta samu
abin wasa sai dad'i takeji.
K'arfe 12 suke tashi don haka dole Bilki ke
d'auko ta don Hamza na wurin aiki lokacin, ba
yadda ta iya haka nan take hak'ura tana d'auko
ta d'in.
Haka rayuwar ta cigaba da gudana cikin hukunci
da hikimar ubangiji, Meenah har ta shiga
nursery. Meenah Allah ya bata k'walwa komai
aka koya mata ta iya sai dai idan ba'a koya
mata ba, kuma idan ta dawo gida ta dinga yi
kenan ko gajiya batayi.
Ba'a saka Zarah makaranta ba sai da Meenah ta
shiga nursery 2 a lokacin ita kuma Zarah tana da
shekara 3 a duniya yayinda Meenah keda hud'u.
Ranar wata juma'a akayi ma su Meenah hutu
suna zuwa gida Meenah ta fara neman babanta
don nuna mai report card nata, sai
dai rashin sa'a yayi tafiya zuwa Lagos a safiyar
ranar, tayi ta kuka tana kiran ita Baba.
Bilki tana tsaki ta ansa report card nata dana
Zarah tana dubawa, abin takaici a wurinta wai
Meenah na d'aya tayi ita kuwa Zarah na ashirin
tayi cikin su ashirin da shidda. Bilki kamar tayi
kuka don takaici. Wato Meenah dai tafi d'iyarta
k'ok'ari kenan?
"Gaskiya da sake!" Ta kalli Meenah tace mata
"Ke! Zo nan!" Meenah tayi tsaye idanunta k'wal
hawaye a duniya tana tsoron Bilki, fizgo ta tayi
da k'arfi.
"Ke dan ubanki sai da kika yi na d'aya wannan
karon ma? Kin manta bugun da nayi maki last
term kenan? Salon kija babanta ya dawo ya
zane Zarah ko? Ke ga mai k'ok'ari ko? Shegiya
mai kama da mage! Wuce ki bani wuri!" Da gudu
Meenah tayi d'aki tana kuka sosai, jawo Zarah
tayi ta rungume tace.
"Don Allah d'iyar Baba ki dage kifi waccan
yarinyar k'ok'ari kinji?" Zarah ta gyad'a kai.
Da rana ta zuba ma Zarah abinci ta shiga
wanka, Meenah na zuwa Zarah tace.
"Zo muci." Ba musu ta zauna suka fara cin
abincin tare.
Ba'a jima ba Bilki ta fito wanka tana lek'owa
taga Meenah nacin abin da d'iyarta abinda ta
tsana! Da tsawa tace
"Ke!" A firgice Meenah ta tashi tana kyarma,
Bilki ta k'ara daka mata tsawa.
"Bana hana ki cin abinci tare da Zarah ba?
Shegiya wuce ki tafi d'aki." Tayi d'aki da gudu a
tsorace. Zarah ta aje cokalin hannunta tace
"Bazan ci ba nima sai da Meenah." Daman Bilki
tasan abinda zatace kenan, tsaki taja tace
"To sai dai kar kici wallahi amma bazakici tare
da Meenah ba, kinji na fad'a miki!"
Aikuwa aje cokalin tayi tana fushi sosai ta bar
parlon. Tsaki Bilki ta k'ara yi tana k'ara jin
haushin Meenah...
***
Sauri yakeyi ya dawo gida don nuna ma iyayensa
result nasa na shedar kammala jss3 nasa. Driver
na yin parking ya fito da gudu yana murna
shigarsa keda wuya ya taradda abinda ya d'aga
masa hankali, ya kuma gigita shi a lokaci guda,
take zuciyarsa ta fara bugawa da sauri a
yayinda k'walwarsa ta tsaya cak! ta bar aiki
lokaci d'aya!!!
Iyayensa ne kwance jina jina, a yayinda wasu
mutane kusan su bakwai ke tsaye cikin
bak'ak'en kaya hartta fuskokinsu an rufe da
black mask!
Tsaye yayi ya kasa tantance a wace duniyar
yake, take kuma ya fashe da kuka yana fad'in.
"Su waye ku? Mey...asa ku...ka kashe min
iyaye?"
Direwa yayi k'asa yana kuka yana jijjiga iyayen
nasa a yayinda yake kiran Anisah! Mutumin yayi
dariya yace.
"Ka bar kuka yaro, sun tafi inda ba'a dawowa
kaima kuma yanzu zaka bisu!" Yakece da dariya
sannan ya saita bindigar daodai saitin k'irjinsa
ya harba.
A gigice ya farka duk da Ac d'in da ke aiki amma
hakan bai hana sa yin sharkaf da zufa ba. Ta6a
jikinsa ya soma yi amma baiga jini ba, ajiyar
zuciya ya sauke ya shiga yin addu'a don ba
k'aramin tsoro yaji ba.
"Wane wane irin mafarki ne haka..... ?"
Ya fad'a yana mai k'ara tunawa da mafarkin da
yayi. Zumbur! Kuma ya mik'e ya fice da gudu
don duba lafiyar iyayensa don gani yake kamar
da gaske ne....!
AUREN FANSA 10
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น10 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
"Mummy...! Mu.." A firgice suka farka daga
bacci, da mamaki suka ce
"Waye?" Kasancewar d'akin gauraye yake da
duhu fitila a kashe take, Daddy ya kai hannunsa
ya kunna bedside lamp yana kallon Faruk dake
tsaye, da sauri Faruk ya rungume mahaifiyar
tasa yace.
"Alhamdulillah! Ashe duk lafiyarku lau, wallahi
naji tsoro."
Mummy tayi murmushi don tasan ya k'ara yin
mafarki. Tace
"Faruk nasha fad'a maka mafarki ba gaskiya
bane ka daina d'aga hankalinka akan mafarki,
nasha fad'a maka bakaji."
Faruk yace
"Nasani Mummy amma meyasa a duk lokacin da
nayi mummunan mafarki sai naji gabana ya
fad'i, sannan na kasa samun nutsuwa, gani nake
kamar wani abu na shirin faruwa da mu!"
Daddy yace
"Haba Faruk! Ka zamo mai tawwakali mana, an
fad'a maka mafarki ba gaskiya bane haba! Tashi
kaje ka kwanta."
Sum sum ya tashi ya fice, Daddy ya kalli
Reemah yace.
"Wai shin kuwa yaron nan na addu'a a duk
lokacin da zai kwanta bacci?"
Reemah tace
"Yana yi, kullum sai na je na tabbatar da sai
sunyi addu'a kafin su kwanta su duka."
Daddy ya numfasa yace
"To Allah ya kyauta amma sai ya k'ara dagewa
da addu'a sosai."
Reemah tace
"Insha Allah."
***
BAYAN WATA D'AYA
Zaune yake yana karatu wayarsa ta fara k'ara,
ganin sunan Daddynsa yasa yayi saurin
d'agawa.
"Hello kaine Faruk?"
Yace
"Eh nine lafiya ina mai wayar nan?"
"Sai dai kayi hak'uri mai wayar nan ya rasu
dashi da matarsa!"
"What? Innalillahi wa'inna ilahir raj'un!"
"Ya Faruk!"
A firgice ya farka ganin Anisha tsaye gabansa
tana kakkarwa, yasa yace
"Ke lafiya menene?"
Ta fashe da kuka.
"Mummy! Ya Faruk Daddy da Mummy babu."
Yace
"Kamar ya? Ina suke?"
Tace
"Wasu mutane na nan sun zagaye Mummy da
Daddy..."
Kafin ta k'arasa ya mik'e da gudu ya fita."
Zuwansa keda wuya ya taradda abinda ya d'aga
masa hankali lokaci guda kuma ya gigice ya
shiga rud'ani! Murza idanunsa ya fara yi don
yayi tunanin wannna karon ma mafarki yakeyi,
la6ewa ya shiga yi a bakin k'ofa yana sauraren
mutanen da ke tsaye. Kusan su hud'u majiya
k'arfi.
"Hello Hajiya Laila Sunusi! Aikin da kika samu fa
an kammala abu biyu ya rage. Na farko bamuga
yaransu guda biyu da kika lissafa mana ba! Na
biyu takardun gidannan da sauran mahimman
takardun da kika ce a baki."
"Yes Ma! Ok Ma! Insha Allah na miki alk'awarin
cika miki dukkan aikin da kika
samu da ke da aminiyarki ya sunan ta ma?
Haha yes Bilkisu Ringim! Ok..."
Kamo hannun Anisah yayi yana kuka d'akinsa ya
fad'a ya kwashi wasu takardu nasa dashi dana
Anisah na makarantarsa da abubuwan da yake
buk'ata ya jefa jikka suka fito da sauri sukayi
hanyar fita. Anisah na kuka shima yana kuka
suka fito gate, gaba d'aya masu gadinsu basu
nan, security sunfi goma amma yanzu bai ga
kowa ba. Adaidaita ya samu suka wuce wata
police station, yana zuwa ya fad'a masa dukkan
abinda ya gani ya kuma ji sannan yace suzo su
ceci iyayensa kafin su mutu.
Ba 6ata lokaci suka nufo gidan sai dai da
zuwansu abin mamaki ba komai gidan asali ma
gidan a rufe yake da kwad'o sai dai gawar
iyayensa, nan akayi examining d'insu aka
tabbatar da basuda rai, take Faruk ya rasa a
wace duniyar yake, kansa yayi dip, hawaye kuwa
kamar an bud'e pampo. Sambatu kawai yakeyi
yana fad'in.
"Daman nasha yin mafarki an kashe mana iyaye!
Nace abin kamar zai faru amma ba wanda ya
kula ni..."
Duk police d'in da yayi yunk'urin tab'asa da
niyyar rarrashi turesu yakeyi suna fad'uwa k'asa,
gaba d'aya kamar ya zauce. Yama k'i nutsuwa
asan ina danginsa suke a sanar masu de abinda
ya faru. Gaba d'aya gidan ba mota ko d'aya,
motocin mahaifinsa sunfi kala takwas amma
yanzu ko d'aya babu.
Nan kuma kan Faruk ya fara juyawa kafin ya
ankara ya fad'i k'asa tim!
AUREN FANSA 11
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น11 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
A hankali ya bud'e idanunsa bakinsa d'auke da
salati, sai kuma ya fara kiran
"Mummy! Daddy! Wai da gaske ne an kashe su?
Ina Anisah? Wallahi duk wanda ya kashe min
iyaye sai na rama masu koma waye..."
"Alhamdulillah kunga ya farka ma ashe! Sannu
ya jikin?"
Kallon likitan yakeyi kafin kuma ya fashe da kuka
sosai. Da k'yar aka rarrashe shi, sannan likitan
ya zauna kusa da gadon da yake kwance tare da
dafa sa.
"Faruk, hak'uri zakayi iyayenka sun riga sun
rasu, kukanka bazai ta6a maido su ba, yanzu
addu'arka ita kad'ai suke buk'ata, kayi hak'uri
kaganni nan na maka alk'awari k'wato maka
'yancika a gurin azzaluman da suka aikata maka
wannan mummunan aikin, kar ka d'aga
hankalinka kaji ko?"
Ya share hawayensa
"Nasani doctor, iyayena basa buk'atar kukana
amma kuma ya zama dole nayi kuka, ba wanda
zai gane abinda nakeji a zuciyata abin yana min
ciwo, zuciyata tana min zafi, iyayena sune komai
na, banida kowa a garinnan sai su, don haka
dole nayi kuka saboda na rasa komai na rayuwa,
na rasa iyayena, sannan na rasa gidanmu da
dukiyar mahaifina..."
Kuka yaci k'arfinsa. Doctor ya numfasa
"Faruk kaganni sunana Dictor Ishaq Aliyu, ni d'an
garinnan ne, daga yau na maka alk'awarin
taimaka maka har sai ka samu ingantacciyar
rayuwa da kai da k'anwarka, inada mata d'aya
da yara hud'u, maza na guda biyu sai mata biyu,
kar ka damu bazakayi maraici ba Indai kana tare
dani don haka ka bar kuka ka share
hawayenka."
Faruk ya kalleshi da mamaki yace
"Da gaske doctor? Zaka taimaka min duk da
baka san koni waye ba?"
Likitan ya gyad'a kai
"Zan taimaka maka kuma zan taya ki fighting
battle d'innan har sai kayi nasara, yanzu kaga
kwananka hud'a a nan asibitin, kana buk'atar
muje gida ka huta."
Faruk yace
"Nagode doctor! Nagode Allah ya saka da
alkhairi! Ya k'ara budi."
Likitan yayi murmushin jin dad'i yace
"Amin Faruk mu tafi ko?"
Yace
"Eh, amma ina Anisah?"
Likita yayi murmushi.
"Gata can office d'ina tana bacci muje mu d'auke
ta sai mu wuce."
Ba'a d'auki lokaci ba suka iso gidan Doctor
Ishaq, gida ne tangameme na gani na fad'a da
ke Maitama, lallai shima doctor Ishaq
mahashuk'in mai kud'i ne.
Shi ya jagorance su har cikin gidan, suna shiga
wata mata dattijuwa ta fito da murmushi a
saman fuskanta.
"Sannu da zuwa Alhaji."
Ta fad'a tana k'ok'arin amsar jakarsa dake
rataye a kafad'arsa.
"Yauwa sannu da gida Malama Rukayya."
Tayi murmushi. "Ahh bak'i mukayi kenan,
sannunku da zuwa ku shigo mana."
Suka shiga suka zazzauna kan kujera.
Alhaji ya fara magana, ga yara nan, ki shiga
dasu ciki suyi wanka ki basu abinci akwai
maganar da zamuyi da ke bayan nan."
Tace
"To Alhaji."
Ta tashi sannan su Faruk suka bi bayanta. Wani
d'aki suka nufa daga gani na yaranta ne mazan,
tace ma Faruk ya shiga yayi wanka, sannan ta
fiddo masa kayan da zai saka. Hannun Anisah
taja, ta mata wanka ta saka mata kaya masu
kyau.
Kan dinning taja su ta zuba masu abinci suka ci
sosai sannan suka wuce parlor inda Alhajin ke
zaune da alama abinci ya gama ci.
Bayan sun zauna Alhajin ya fara magana.
"Ina su Yazeed?"
Tace
"Suna can waje suna buga ball."
Yace
"Jeki kirawo man su gaba d'ayansu."
Da girmamawa ta amsa ta fice.
Can sai gata yaran na biye da ita a baya.
"Dada welcome." Suka fad'a gaba d'aya.
Yace
"Thanks, ku zauna." Duk suka zauna, nan kuma
suka hau kallon su Faruk. Alhaji ya numfasa ya
fara magana.
"Hajiya kinga wad'annan yaran guda biyu?"
Tace
"Eh nagansu."
Yace
"Yauwa, wannan shine Faruk sai ga k'anwarsa
nan Anisah, shine yaron da nake kula dashi a
asibiti bayan rasuwar iyayensa."
Tace
"Allah sarki sune yaran kenan? Allah ya jik'ansu
da rahama."
Yace "Amin, so nake mu cigaba da rik'esu a
matsayin iyayensu, na farko kinga marayu ne
gasu yara k'anana, na biyu duk wanda ya
taimaki wani Allah zai taimake shi. Yara ne
kuma marayu, basuda kowa sai Allah, shine na
ga dacewa in d'auko su in rik'e don samun lada,
ko ya kika ce?"
Ta numfasa.
"Haka ne Alhaji, wallahi wannan ba wani abu
bane, insha Allah zan rik'e su a matsayin uwa a
garesu, Allah ya bamu ikon rik'e amana."
Yace
"Amin, Faruk wad'annan k'annenka ne gasu nan,
kaga wannan shine babba mai suna Yazeed,
shekarsa sha biyar sai mai bi masa Hauwa'u ana
kiranta Jidda shekararta Sha hud'u, sai k'aninta
Nabeel shi yakeda da sha biyu sai auta gata nan
Yusra ita keda shidda, don haka kuna jina
wannan 'yan uwanku ne ban yarda wani ya nuna
musu wariya ba a cikinku, kuna jina?"
Suka ce
"To Dada."
Alhaji yayi murmushi
"Faruk ga kannenka nan sai kuje kuyi wasa ko?"
Faruk yayi murmushi inda gaba d'aya suka mik'e
suka fice.
Alhaji ya ce
"Allah ya bamu ikon rik'e su amana, ya tona
asirin azzaulumai."
Tace
"Amin ya Allah Alhaji, yaran sun bani tausayi
wallahi, Allah ya bi musu hakk'insu."
Yace
"Amin amin, anjima zanje inyi magana da
manyan lauyoyin da na sani, asan me za'ayi a
kai."
Tace
"Hakan yayi daidai, yanzu makarantarsu fa?"
Yace
"Makarantarsu ba matsala bace na d'auki
nauyin karatunsu, yanzu ayi k'ok'ari a saka su
makarantarsu Yazeed."
Tace
"Haka yayi daidai, Allah ya k'ara bud'i."
Yace
"Amin Amin, bari inje in d'an kwanta kafin
anjima zan koma asibiti."
Tare suka mik'e ya fice tabi bayansa.
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น12 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
***
Washe gari aka saka su makaranta. Yanzu
abubuwan sun ma Faruk sauk'i tunda yanzu
gidan da suke basuda matsala, daidai
gwargwado suna samun kulawa sosai, sai dai
har yau hoton gawar iyayensa ya kasa 6ace
masa kai, ko rufe ido yayi sai ya gansu ya kuma
ga mutanen da suka kashe su, sannan sunayen
da aka ambata har yanzu ya kasa mantawa
hasali ma ya samu diary nasa ya rubuta
sunanayen nasu.
Ya samu shak'uwa mai k'arfi tsakaninsa da su
Yazeed komai a tare sukeyi su uku abin sha'awa
sun had'e kansu. Duk inda kaga d'aya to zakaga
d'ayan. Haka ma Anisah da Yusra sun zama
k'awaye, ita Jidda ta girmesu don haka sai dai
sama sama suke shiri, daga gaisuwa sai kuma
cin abinci ke had'a su. Duk da k'arancin
shekarun Anisah ta fuskanci Jidda nada wuyar
sha'ani sannan miskila ce ta k'arshe, sai dai
akwai kuma kirki halayen nata dai gasu nan a
baibai, mutum ce mai wuyar fassara, sheyasa ta
lura yaran gidan basu shiga harkarta, don haka
itama sai tayi baya baya kad'an.
Har yau Anisah ta kasa gane iyayensu sun mutu
har abada bazasu dawo ba, don kusan kullum
sai ta tambaya. Meyasa suka dawo nan da
zama, ina Daddy da Mummy? Yaushe zasu
dawo? Haka take tasa Faruk gaba da ire iren
wad'annan tambayoyin har idan ya rasa amsa
sai tasa masa kuka, dole sai dai yace sunyi
tafiya mai nisa kuma zasu dad'e basu dawo ba.
To tun wata rana da abin ya fara isarsa ya daka
mata tsawa yace tayi hak'uri Mummy da Daddy
basu dawowa, da farko ta tsorata amma da
Faruk ya zauna yayi mata bayani sai kuma ta
fahima, ya kuma d'ora da cewa ta dinga yi musu
addu'a kullum, aikuwa tun daga ranar bata k'ara
tambayarsu ba haka ma da ta motsa sai tayi
musu addu'a.
***
BAYAN WANI LOKACI...
Zaune suke kan dinning suna breakfast gaba
d'ayansu, Dada ne ya aje cokalin hannunsa ya
soma magana.
"Wai ina Faruk ne?"
Hajiya Rukayya da suke kira da Mama tace
"Inaga yana ciki kamar wanka ya fito."
Sanye yake cikin bak'in wando wulik pencil
trowser sai ya d'ora ash shirt marar hannu, tun
daga k'afafuwansa ya isa ka gane cewa
kyakkyawan mutum ne, don kuwa k'afar tasa
fara ce tas kalar larabawa har wani gashi gashi
ake gani a tsakankanin yatsanshi na k'afa.
Haka nayi ta d'aga kaina har na sauke su kan
fuskarsa... tabbas duk inda ake neman namiji
toh a nemi wannan mutumin, gashin kansa irin
mai cikar nan ne mai yawa sannan nannad'e
yake kamar na jarirai.
'Ya Faruk Dada na jiranka fa za'a ci abinci."
Kai! Wannan Anisah ce ta k'ara girma haka?
Lallai idan na tsaya muku bayani bazaku gane
ba, kamarta d'aya da Faruk gashinta mai kama
dana larabawa an tufke shi daga can tsakiya
amma duk da haka sai da ya zubo bayanta,
kyakyawa ce itama.
Sanye take cikin light pink dress 'yar kanti.
Murmushi yayi mai bayyana hak'ora yace.
"Ina zuwa."
Da sauri ta fice, turare ya feshe a jikinsa sannan
ya zura takalmansa ya fice.
Yana zuwa ya gaida Mama da Dada ya samu
wuri ya zauna kusa da su Nabeel. Nan aka soma
cin abinci.
Dada ne ya dakata ya soma magana.
"Faruk kamar kullum bazan gaji da ce maka kayi
hak'uri ba, wallahi har yanzu kan aiki ake ganin
an kamo wad'anda suka kashe iyayenku..."
Faruk yayi murmushi yace
"Haba Dada wallahi babu damuwa, komai lokaci
ne, insha Allah Allah zai bayyana mana su."
Dada yayi murmushi, sheyasa yake son Faruk
yaro ne mai kaifin tunani, da kuma nutsuwa da
hangen nesa. Don haka sai yace
"Haka ne, amma insha Allah za'a cigaba da aiki
Allah yasa a dace."
Suka amsa da "Amin."
Dada ya cigaba.
"Kunga yanzu kuna dab da gama makaranta, to
kamar yadda nayi alk'awari mazan zan tura su
Saudia don neman ilimi, to zan had'a da kai
Faruk kowa ya za6i abinda zaije ya karanta.
Abinda yasa kuka ga na za6i wannan k'asar
saboda nayi k'wak'waran bincike ana tsaro
sosai da yaran mutane, to kuma yaro ko yaso
koya k'i dole ya kama kansa. Amma kamar
kullum bazan gaji da jawo hankalinku ba, don
Allah ku nutsu ku tsare mutuncinku, kar kuga
bana kallonku to ku tuna Allah (S.W.A) yana
kallonku, wallahi kuji tsoronsa abinda kuka je
nema shi zakuyi, kunaji ko? Allah yayi muku
albarka sai ku dage ku fito da grade mai kyau."
Suka ce
"Amin Dada, insha Allah zamu kiyaye."
A haka suka cigaba da karyawa.
***
"Mami don Allah ki barni zan sa da kaina."
Hajiya Bilki tayi tsaki
"Ke da Allah wuce can, ki bari na sa miki."
Ta zum6uro baki.
"Assalamu Alaikum..."
Bilki ta d'ago tana k'are mata kallo.
"Wa'alaikumusalam."
Daga sama har k'asa na k'are mata kallo,
Meenah ce ta girma haka? Tayi tsawo ta k'ara
kyau, wannan ita ake kira black beauty, ga
gashin kanta duk d'ankwalin da ke kanta hakan
bai hana shi fitowa ba...
"Mami na gama wanke kayan."
Bilki ta ta6e baki.
"Kin gyara min kitchen?"
Tace
"Eh na gyara."
"Kinyi shara da wanke wanke?"
Meenah tace
"Eh nayi..."
"Kin wanke toilets?"
"Eh na wanke naki..."
"Na d'akin Zarah fa? Shifa wa zai wanke?"
Ta d'an bata rai.
"Mami home work kawai zanyi sai na wanke, an
bamu home work har biyar gashi ko d'aya ban
ta6a ba."
Ta doka mata harara,
"Sannu 'yar boko, toh bari kiji bazakiyi ba sai kin
gama min aikina tsab a gidannan sannan zaki yi
wani home work."
Tayi narai narai da fararen idanunta wadda suke
kamar an d'iga madara a ciki.
"Ke! Bansan iskanci ya ina miki magana kin
tsaya kina wani kallon mutane zaki wuce ko sai
na mauje ki!"
A zahirin gaskiya bawani assignment d'in da
zatayi, don ta riga tayi shi da asuba, daman
gudun aiki yayi mata yawa sheyasa data gama
sallah take home work ko karatu, kawai ta gaji
ne tun safe take aiki bata huta ba, daga wannan
sai wannan ko kalaci batayi ba...
"Mami zan taya ta."
Bilki ta 6ata rai
"Kiyi ki gani yadda zanyi da ke a gidannan, maza
kije kuma kar tayi nata home work d'in sai ta
gama maki naki!"
Sum sum Zarah ta fice zuciyarta cike da
tausayin Meenah...
AUREN FANSA 13
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น13 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Duk'e take tana faman wanke toilet Zarah ta
lek'o, cikin muryar rad'a rad'a tace.
"Meenah bari na taya ki."
Meenah ta d'ago tana duban Zarah tace
"A'a ki rufa man asiri Zarah, yanzu da Mami
tazo zata dake ni."
Zarah tayi murmushi
"Ay dana ji ta taho zan bari..."
"Nidai gaskiya ina tsoro ki bari kawai..."
Da sauri Bilki ta shigo d'akin, tana zuwa ta jawo
Meenah.
"Ke maza kije kiyi wanka ga babanku nan
dawowa, bar wankin toilet d'in zan k'arasa..."
Halin maman tasu na basu mamaki, sun rasa
meyasa da babansu ya kusa dawowa sai ta
hana Meenah yin ko wane aiki.
Sum sum Meenah ta fice daga d'akin.
"Mami meyasa kike sa Meenah aiki ni baki sani?
Kuma meyasa idan Baba ya kusa dawowa kike
kora Meenah tayi wanka ko
taci abinci?"
Bilki ta daka mata tsawa
"Ke! Kar ki k'ara min ko wace irin tamaya a nan
kina jina? Kema fita ki bani wuri."
Sum sum ta fita tana jinjina hali irin na uwarta.
Ba'a jima ba ya shigo gidan a gajiye, Bilki ta
tasa yaran gaba suna kallo ya shigo da ledoji a
hannunsa, da sauri Zarah da Meenah suka mik'e
suka kar6a kayan hannunsa.
Bayan ya zauna yana murmushi yace
"Kaza ce da ice cream na siyo maku kuje kuci."
Da murna suka shige ciki. Bilki tana murmushi
tace
"Yaran nan na shan gata Alhaji, kana tunanin
baiyi yawa ba kuwa?"
Alhaji yayi murmushi yace
"Bilki kenan, ay ba wani abu nake musu na
gatanci ba, bana sangarta su, haka ma bana
6ata su da kud'i ko wani abin duniya, abinci ne
nake basu wanda kuma yin hakan ba laifi bane."
Tayi murmushi
"Bakayi laifi ba kam nima dama wasa nake
maka."
Sai kuma yayi ajiyar zuciya
"Kinsan abinda ke damuna?"
Tace
"Sai ka fad'a."
Yace
"Mutuwar Alhaji Adam, su waye marassa imanin
da suka bishi har gidanshi suka kashe shi dashi
da matarsa?"
Bilki ta had'iye miyau da k'yar tace
"Nima abinda yake damuna kenan kullum Alhaji,
nasan mahassada ne kawai."
Ya numfasa
"Wai me duniyar nan keso ta zama ne? Mutane
akan kud'i ba abinda bazasuyi ba?"
"Uhm...uhm Alhaji bari na kawo maka ruwa
kasha."
Bai kawo komai a ransa ba yace
"To."
Aikuwa da daddare Meenah bata samu abincin
dare ba, wai ay taci kaza ta k'oshi bataga dalilin
da yasa za'a bata abinci ba.
Da safe Baban na fita aiki ta jibga mata uban
wankinta dana Zarah, duk da suna da mai wanki
amma tsabar mugun hali irin na Bilki sai da ta
jibga mata wankin daya fi k'arfinta. Tana gama
bata wankin ta shigo daidai bakin k'ofa taci karo
da Zarah tana fad'in.
"Mami idan Baba ya dawo sai na fad'a masa
abinda kike ma Meenah idan baya nan..."
Finciko ta taji anyi, tayi d'aki da ita tana zuwa
ta shiga tsula mata bulala, sai data zane ta tas
sannan tace
"Wannan kad'an nayi miki akan bayan kin fad'a
masa, sai jikinki ya gaya musu, zaki fad'a ko
kuwa?"
Da sauri ta girgiza kanta tana kuka.
Haka dai kwanaki sukayi ta tafiya cike da wahala
a gurin Meenah, sam batada lokacin kanta sai
aikin gida, bata samun lokacin karatu sai can
cikin dare, sheyasa gata nan wata 'yar ficit sai
tsawo amma ba kumari, Zarah kuwa wata 'yar
duma duma ga ta fara sol fatar jikinta irin ta
'yan hutun nan ce da basu san wahala ba, ita
kuwa Meenah batada k'iba sai tsawo.
***
A haka rayuwar tayi ta mirginawa, har Meenah
ta kai SS3 a yayinda Zarah ke SS2, yaran sun
girma sun zama 'yan mata, daka gansu tare sai
ka k'ara kallonsu don kuwa ko a makaranta tare
sukeyin komai, shiga aji kawai ke raba su.
Halayen nasu ne kawai ya banbanta, ita Meenah
tana da wani calm attitude, tanada nutsuwa
komai nata a hankali takeyinsa, ko
maganarta wani a hankali takeyi, ba kamar
Zarah da take abu kazar kazar ba, ita tsaye take
kamar ba mace ba, she's too lousy dai tana da
hayaniya....
Sannan uwa uba Meenah ba irin girkin da bata
iya ba, da kuma ko wane irin aiki yi take irin su
shara wanke wanke, wanki da sauransu, kuma
bata gajiya da gyara wuri koda za'a shekara ana
6ata shi, Meenah bata damu da abin duniya ko
wayar da take rik'ewa batada komai na social
media a ciki, ita dai kawai tayi waya idan ta
kama shikenan, amma Zarah akwai son harkar
social media, ga yin hoto kamar hauka, to a
wannan fannin ne halayensu suka banbanta, ga
son jiki bata iya ta6uka komai na aikin gidan
saboda haka ta taso ba'a sata tayi, sheyasa ko
gyaran d'akin bata iya ba, sai Meenah tazo ta
gyara mata...
AUREN FANSA 14
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Dedicated to Susu, thank you for everything!❤️
๐น14 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Bakajin komai a d'akin sai k'yalk'yatar dariya,
da k'yar suka dakata, Laila ce ta soma magana.
"Shegiyar gari, wato kina nan kina facaka cikin
dukiya, kina nan kina taka matsayin da kika
d'ad'e kina burin takawa, kina nan kina hawa
kud'i ki taka kud'i ki yadda kikeso a cikinsu,
lallai shawara d'aukar d'aki yau gashi mun
da'auka tayi mana amfani!"
Suka sake sa dariya, Bilki tace
"A da na bijirewa shawararki, kuma da farko na
tsorata amma yanzu abin sai wanda ya gani."
Suka sake sa dariya gami da tafa hannu. Laila
ta kuma cewa tana dariya
"Yayi daidai kin birgeni! Yanzu keda talauci sai
dai ko a lahira..."
Bilki tace
"Kada Allah ya had'ani da shi koda a lahirar ne
ma. Yanzu tsoro na kada wata rana a gano mu
ya zamuyi kenan?"
Laila tace
"Daman ay ke bugun Abuja ce, daman ke kalarki
bata k'auye bace ba..."
Bilki tayi dariya
"To kin dai gani, rabona da k'auye har na manta,
tunda muka dawo Abuja idan kin ganni k'auye
sai dole..."
"Assalamu Alaikum..."
Ta shigo d'auke da tray d'in lemo da glass cups
guda biyu sai plate d'in cincin da dambun nama.
Ta ajiye tray d'in sannan ta gaishe su, sai da
suka watsa mata harara sannan suka ce
"Lafiya."
Bilki tace
"Kin d'ora abincin rana?"
Tace
"A'a yanzu zan d'ora."
Bilki tace
"Aikin me kike da tun d'azu baki d'ora ba har
kusan k'arfe sha biyu?"
Tace
"Wanke wanke ya taru da yawa shine na..."
"Yi min shiru a nan!" Ta daka mata tsawa.
"Duka duka wanke wanken guda nawa ne da har
zaki ce yayi yawa? Sai anyi magana ki dinga
rissina kai kamar wata yarinyar kirki, zaki wuce
ki d'ora ko sai na san me zan miki!"
"Uhm... me za'a dafa?"
Tayi tsaki
"Ki dafa mana fried rice da peppered chicken, sai
ki had'a coleslaw, akwai kaji a freezer ki d'auki
guda biyu kiyi amfani dashi. Sai kinsan halin
babanku yafison tuwo, kiyi masa tuwo miyar
busassar ku6ewa."
Da k'yar tace "To." Ta fice idanunta cike da
hawaye!
"Anya bataji mu ba d'azu?" Cewar Laila cike da
damuwa.
"Ko taji me za'ayi? Ah babu ay."
Sukayi dariya Laila tace
"Haka ne fa."
Tana kitchen tana yanka kaji Zarah ta shigo tana
sanye da wando jeans sky blue sai light pink
shirt marar hannu.
"Meenah zo ki ga..."
Da mamaki take kallonta tana d'aga mata fuska
don taga idan idanunta ba k'arya suke nuna
mata ba.
"Meenah kukan me kike? Hala Mami ce? Me tayi
miki?"
Ta k'ak'alo murmushin dole tace
"Babu komai, wani abu ya fad'a min ido ne."
Zarah tayi murmushi
"Uhm baki iya k'arya ba Meenah, ni nasan wani
abu Mami tayi miki."
Meenah tace
"Bakomai amma don Allah Zarah zan miki
tambaya inaso ki fad'i man gaskiyar abinda kika
sani."
Zarah tace
"Ina jinki."
Meenah tace
"Don Allah a iya zamanki a gidannan kin ta6a ji
koda a wurin wani ne cewar tsintso ni akayi?"
Zarah ta k'yalk'yale da dariya harda duk'ewa,
Meenah ta kalleta galala cike da mamaki tace
"Meye haka wai Zarah? Ya ina tambayarki kin
tsaya kina min dariya?"
Har yanzu dariya takeyi, da k'yar ta tsagaita
tana duban Meenah tace
"Anya baki buk'atar ganin likita Meenah? Kanki
d'aya kuwa?"
Meenah ta k'ule tace
"Shikenan sai kije kiyi ta dariyar, gani kike kamar
wasa nakeyi ko?"
Zarah tace
"Daman ay wasan kikeyi, ta yaya ma zaki fara
irin wannan tunanin?"
Meenah tayi murmushi mai ciwo tace
"Dole nayi tunanin haka Zarah, na rasa meyasa
Mami bata sona..."
Da sauri Zarah ta rufe mata baki
"Kar kice haka, ay indai zaki kula halinta ne
haka, koni tana min."
Meenah tace
"Eh amma ba kamar yadda take min ba, dole ne
na fara tunanin duk yadda akayi ko tsinto ni
akayi ba'a san asali na ba, ko kuma ni 'yar rik'o
ce."
Zarah ta 6ata rai
"To yayi miki kyau, ki cigaba da fad'in haka ni
kuma daga yau na daina miki magana a
gidannan."
Meenah ta juyo da sauri
"Haba dai?"
Zarah tace
"Ki cigaba ki gani."
Da sauri Meenah tace
"La na bari, ya za'ayi na bari mu 6ata?"
Zarah tayi murmushi
"Yawwa sweet sis bara na taya ki aikin don ayi
sauri, kuma idan kika hanani yi sai na daina miki
magana a gidannan."
Ta fad'a cike da shagwa6a, Meenah tasa dariya
ta kwaikwaiye ta
"To bazakiyi ba wuce ki tafi ki kwanta."
Zarah tace
"Nak'i"
Haka suka k'arasa aikin suna zolayar juna, wasu
abubuwan sai da Meenah ta dinga koya mata,
kuma ba laifi tana fahimta.
***
"Wai bazakuyi sauri ku fito ba Jidda? Kodai a
tura driver ya d'auko su ne?"
Da sauri Anisah ta fito cikin shigar atamfa
d'inkin doguwar riga kalar blue and purple sa ta
d'ora purple mayafi.
"A'a Mama mu zamu d'auko su, nifa na gama
shiri su ya Jidda ne tun d'azu basu gama ba."
Mama tayi dariya.
"Au kin k'agu kiga yayan naki hala? Wannan irin
zakwad'i haka?"
Anisah dariya, daidai nan sauran 'yan matan
suka fito sun sha ado sunyi kyau inda dukansu
suke cikin shiga iri d'aya.
Yusra tayi dariya
"Kai Mama duk kin k'osa a dauko miki yaranki
ne haka?"
Mama tayi dariya
"Ke ni ba kakarki bace, ku wuce ku tafi haka
nan."
Da sauri suka tafi suna dariya...
Jidda ta dubi agogon dake mak'ale a hannunta,
k'arfe sha biyu harda rabi ta wuce.
"La Ibrahim kayi sauri sun kusa sauka."
Ibrahim yayi murmushi
"To ranki ya dad'e."
Tunda suka dira a airport hankalinsu ya kwanta
ganin har yanzu basu sauka ba, amma daga
inda suke suna hango jirgin yana niyyar sauka
k'asa. Duk sukayi ajiyar zuciya.
A hankali jama'a suka fara fitowa daga jirgin,
haka ma duk wanda ya hango d'an uwansa sai
ya ruga ya taro sa.
Tsaye suke kusa da kujerar zama wato (waiting
chair) idonsu k'yam saitin k'ofar jira kawai suke
suga ta inda zasu 6ullo.
AUREN FANSA 15
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น15 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Ba'a fi minti biyar ba suka kunno kai, ko
wanensu yana tura trolley nasa, tunda suka fito
Jidda ke kallonsa ya za'ayi ta mance da wannan
fuskar?
Ya chanza gaba d'aya ya zama wani babba,
k'irar jikinsa kansa abin kallo ce irin giant
d'innan, abinka ga fari sai ya k'ara murjewa ya
zama bature sak! Ta kalleshi yana murmushi.
"Sannu da zuwa yaya!" Anisah ta ruga tare da
mak'alk'ale shi, a yayinda Yusra ke mak'ale da
nata ya'yyen, sai a lokacin Jidda ta dawo
duniyar tunani.
Da k'yar ta daidai nutsuwarta tace
"Sannunku da zuwa!" Ko alama bai gane ta ba.
"Yauwa sannu... Jidda ko?"
"Wow haka muryarsa take?" Ta fad'a tana k'ara
kallonsa cike da mamaki. Tace
"Eh nice yaya."
"Wow duk kun girma..."
Suka taya su jan kayan nasu har bakin mota.
Tafiya suke amma idonta na kansa. Abu d'aya
take maimaitawa a zuci...
"What kind of change is this?"
Haka aka loda kattunan jakunansu a boot.
Koda suka shiga mota shi ya zauna gaba, daga
baya babu abinda Jidda keyi sai aikin kallonsa.
"Ya Faruk? Ya Faruk? Ya Faruk?" Wannan abu
shi take ta fad'i a ranta. Ta d'an k'ara kallonsa
ta baya, gashin kansa kad'ai abin kallo ne, ya
k'ara kyau akan wanda yake dashi da, sai
shinning yake kamar taurari a sama...
"Anya bayada iri da larabawa?"
"Wa kenan?"
Ta kai dubanta tana kallon Najeeb daya tsareta
da kallon tuhuma, tace
"Uhm uhm bangane ba."
Nabeel yace
"Rabu da ita tun d'azu na lura da yadda ta
chanza."
Tace
"Na chanza kamar ya?"
Najeeb yasa dariya.
"Kamar yadda kika fahimta."
Daga nan ba wanda ya tanka har suka iso gida.
Mama harda d'an gudunta tana fad'in
"Welcome home."
Suka shiga parlor Najeeb ya kalli matan yace
"Ku kai mana kayanmu d'aki."
Sannan ya maida kallonsa da Mama.
"Bari mu d'an watsa ruwa muyi sallah."
Mama tayi murmushi
"Eh hakane lokacin sallar azahar yayi ya kamata
ayi sallah sai aci abinci, sannunku da hanya."
Nabeel yace
"Yauwa Mama, ina Dada?"
Tace
"Yana Ireland yau satinsa d'aya da tafiya, amma
insha Allah ya kusa dawowa."
Najeeb yace
"Ok... hakane munyi waya yake fad'a min batun
tafiyar tasa Allah ya dawo dashi lafiya."
Aka amsa da "Amin"
Daga haka kowa yayi hanyar d'akinsa.
Faruk d'akinsa ya burgeshi yadda yayi tsab sai
k'amshi da sanyin ac ke ratsa dukkanin illahirin
jikinsa, bai tsaya wata wata ba ya fad'a toilet.
Yana gamawa ya saka k'aramar riga da dogon
wando.
A dinning aka hallara kowa yayi serving kansa
jollof d'in shinkafa, da pepper soup, sai kaza
gasassa sai salad.
Sun fara cin abincin ne Mama tace.
"Alhamdulillah, Allah na gode maka daka nuna
man wannan ranar, ranar da 'ya'yana suka
kammala karatunsu lafiya, fatana Allah ya
albarkaci karatunku, Allah ubangiji ya baku
sa'a."
Gaba d'aya sukace "Amin amin."
Ta cigaba
"Yanzu dai ga Likita Najeeb, ga Detective Faruk,
ga kuma Banker Nabeel, kai masha Allah! Allah
yayi albarka."
Suka ce "Amin Mama mun gode Allah ya saka
da alkhairi."
Tace
"Amin, yanzu dai ya kamata kuyi settling kowane
ya nemi mata yayi aure, shine kad'ai abinda ya
rage."
Duk kansu k'asa basu ce komai ba, itama Mama
murmushi tayi a haka suka cigaba da cin abinsu.
***
Bayan Wata D'aya...!
Zaune yake kan kujerar office d'insa yana faman
dube dube a computer d'insa, aka shigo da
sallama, a hankali ya d'aga ido ya kalli k'ofa
yayi murmushi.
"Ah Usman! Shigo mana ya zaka tsaya a bakin
k'ofa?"
Ya k'araso yana gaishe shi
"Ina wuni sir?"
"Lafiya lau zauna magana zamuyi."
Bayan ya zauna, Faruk ya soma magana.
"Wani aiki zan saka, don Allah ina so duk abinda
nake nema ka yi k'ok'ari wajen ganin ka samo
min duk wani abu zan buk'ata."
Usman yace
"Insha Allah, ay ba yau ka fara sani aiki ba,
kuma duk lokacin da kake sani abu ina k'ok'ari
waje ganin na gano maka koma me kake nema."
Faruk yace
"Haka ne, to yau ma ina tafe da wani aikin mai
matuk'ar mahimmanci a wurina."
Ya fad'a yana fiddo wani abu a cikin drawer d'in
table d'insa.
"Karanta kaga."
Da ladabi ya kar6a ya soma karantawa. Bayan
ya gama yace
"Yalla6ai amma suna ne kawai nake gani."
Faruk yayi wani d'an guntun murmushi yana
juya kujerar da yake zaune akai. Sai da ya
d'auki tsawon mintina biyu zuwa uku sannan ya
soma magana.
"Eh sunaye ne na mutum biyu, bincike nake
buk'ata akansu."
"Toh yalla6ai."
"Yawwa, i want every bit of information
regarding them. Ina buk'atar komai idan nace
komai i mean everything. Wane gari suke? Wace
unguwa? Sunada 'ya'ya? Guda nawa ne? Suna
da miji? Meye sunansa? Wane aiki yake? Ina da
ina suka fi zuwa? Wace makaranta yaransu
suke? Don't left out anything, including their
photos."
Usman ya gyara zamansa yana fuskantarsa.
"Angama amma yalla6ai meyasa kake neman
information d'innan haka? Sannan ta ina zan
samo hotunan su?"
Faruk ya mik'e tsaye tare da dawowa gaban
Usman gami da zama saman table a kusa da shi
yace
"Usman bana son shishigi, aiki na saka shi
zakayi min, kawai kaje ka kawo min abinda na
saka please banda wasa, sannan hotunansu
wannan kai zaka nemo."
Usman yace
"Hakane insha Allah zanyi k'ok'ari."
"Yauwa kana iya tafiya."
Daga haka ya fice, inda Faruk yayi murmushi
yace.
"This is my first step towards my goal, waiting
for the next step."
Yayi murmushi yana kad'a kai.
0 comments:
Post a Comment