skirt d'inta, duk da kayan dake jikinta sun mata
kad'an hakan bai hana ta yin kyau ba, ji tayi an
rungume ta ta baya, tasan baya wuce aikin
Zarah.
"Auch! Haba mana Zarah so kike ki k'arasa ni
ne?"
Zarah tasa dariya, tace
"To sarkin fad'a, yanzu dai maida wuk'ar albishir
nazo miki dashi." Meenah ta juyo da murmushi
saman fuskarta tace
"Ina jinki."
Zarah tace
"Fari ko ja?"
Meenah tace
"Fari k'al ma kuwa."
"Baba yace nayi WAEC d'ina yanzu idan naci mu
tafi university tare!"
Zarah tace cike da murna. Meenah farin ciki ta
rasa ina zata sa ranta, dama ta dad'e tana
addu'ar su tafi university tare da Zarah, sai dai
tasan Baba ne ya hana yace bazatayi ba sai ta
kai SS3, amma yanzu ko ya akayi ya yarda?
Meenah tace
"Amma ya akayi ya yarda?"
Zarah tace
"Wallahi ikon Allah, kuma fa ba tambayar sa
nayi ba, shi da kansa ya kirani yace na shirya
yin exam tare da ke."
Meenah cike da murna tace
"Lallai ikon Allah, Allah yasa kici."
Zarah ta rungume Meenah tana murna tace
"Amin sisi."
"Kai meye kun cika ma mutane kunne da
hayaniya?"
Cewar Bilki daga bakin k'ofar d'akin tana tsaye,
fuskarta ba yabo ba fallasa.
Sukayi tsit, ta kuma daka musu tsawa
"Ba da ku nake ba?"
Zarah tace
"Da... dama, Baba ne yace za... zan iya tafiya
university tare da Meenah..."
Take ta washe baki kamar ba ita ba, tace
"Allah d'iyar Baba? Yaushe ya yarda?"
Tace
"D'azu kafin ya tafi wurin aiki."
Bilki tace
"Alhamdulillah, yayi daidai Allah ya bada sa'a sai
ki dage, tun kafin ace bakida k'ok'ari, ko kuma
ace wasu sun fiki."
Ta k'arasa tana ma Meenah wani irin mugun
kallo. Duk sun san abinda take nufi kuma hakan
ya sosa ransu.
"Ke! Meenah zo ki matsa man k'afa ta."
"Mami zan taya ta."
Wani kallo ta watso mata na irin kika k'ara
magana sai na kakkarya ki sannan ta fice.
Meenah ta dafa ta tana fad'in.
"Don Allah Zarah daga yau ki daina cewa zaki
taya ni idan tasa ni aiki, wallahi fad'a kike ja
man duk sadda kika fad'i haka."
"Uhm." Kawai Zarah tace, daga haka Meenah ta
juya da sauri zuwa sashen Mami.
Da sallama ta shiga, zaune take kan wata
kujerar hutawa ta baje k'afafuwanta ma'ana ta
mik'ar dasu saman kujerar, tana faman danne
danne a wayarta k'irar iPhone 7plus, tana zuwa
ta durk'usa har k'asa tace
"Gani Mami."
Sai data samu tsarabar harara sannan tace
"Meya tsaida ki tun d'azu nake zaman jiranki?"
Bata ce komai ba kanta na k'asa dai.
"Sai anyi magana kiyi sum sum da kai kamar
mutuniyar arzik'i..."
"Kiyi hak'uri Mami, wallahi ban tsaya yin komai
ba nan na taho."
Tayi tsaki gami da mik'o mata k'afa.
"Ni matsa man k'afata, kuma saura kiyi mani
mugunta irin na rannan wllh sai na yi maganinki,
don yau sai dai a kaiki asibiti don sai nayi miki
lis!"
A hankali take matsa mata cikin lalla6awa, sai
kuma ta sakar mata k'wanya a kai.
"Ke bakida hankali ne? Ya zaki dinga mani abu
kamar susar k'adangare?"
Sai ta hau yi da d'an k'arfi, nan ma ta kai mata
wanda yafi na d'azu zafi.
"Yau ga muguwa! Zaki 6alla min k'afa ne?"
Ta rasa yadda zatayi, mistake kad'an sai taji
k'wanya mai shegen zafi a kanta.
Da daddare tana kwance ita dai abin duniya yabi
ya dame ta, zuwa yanzu ta yarda ta amince ba
Mami ta haife ta ba, ta yarda Baba ne babanta
amma sam ta kasa yarda Mami ce ta haifeta.
To ina mahaiyarta? Ta rasu ne ko tana raye? Ko
kishiyar Mami ce? Kullum ire-iren wad'annan
tambayoyin sune suke mata yawo a cikin kai,
kuma har yanzu ta rasa amsa. Daga k'arshe ta
yarda ta amice mahaifiyarta ta rasu kuma
kishiyar Mami ce kawai. Wasu zafafan k'walla
suka zubo mata, ita kam batasan dad'in uwa ba,
bata san ya ake ji ba idan mutum na tare da
mahaifiyarsa.
Sama sama tayi bacci gudun makara saboda ga
aikin gida ga kuma shirin makaranta.
Da asuba ta mik'e bayan ta gabatar da sallar
asuba tayi wanka, ta yi aikin gidan kamar
kullum, ta had'a kalaci, d'aki ta wuce ta sanya
uniform d'inta da basu samu guga ba, bayan ta
gama shirinta tsab ta fito don ta karya, tana
bud'e kular abinci sai ta ganta wayam! Nan ta
hau dube dube amma kaf ba komai a ciki.
Mami ce ta sauko cikin kayan bacci da d'aurin
gaba tana zuwa tabi Meenah da mugun kallo, ta
wuce kitchen. A ranar haka nan ta hak'ura da
kalacin daman sun makara, sauk'inta ma Baba
ya basu kud'in makaranta da batasan ya zatayi
ba.
***
BAYAN KWANA BIYU
Da sallama ya shigo office d'in, yana zaune yana
fama da aiki kamar kullum, d'ago da fuskarsa
yayi yace
"Shigo mana Usman."
Sai da ya kammala abinda yakeyi sannan ya
maida dubansa ga Usman dake zaune d'auke da
wata babbar brown envelope.
"Yalla6ai daman akan aikin da kasani ne, to
Alhamdulillah na kammala maka komai shine na
kawo maka ka gani."
Da sauri ya d'ago yana duban Usman yace
"Da gaske ka kawo duk abinda nake buk'ata?"
Usman yana murmushi sosai yace
"K'warai kuwa gasu."
Ya sa hannu ya zazzaro wasu hotuna guda biyar
ya dire a gabansa, sannan ya fiddo wani dogon
paper mai rubuce rubuce a samanta....
AUREN FANSA 17
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Dedicated to Kiddies friends 4ever, thanks for the
support you are special to me! Love you guys❤️
๐น17 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
D'aya bayan d'aya yake duba hotunan dake baje
a gabansa, sai daya d'auki lokaci kad'an yana
analyzing ko wanensu duk Usman yana kallonsa.
Sai da ya gama sannan ya d'ago yana kallon
Usman yace.
"Nagode, sai kayi min bayaninsu."
Usman ya gyara zama yace
"Yalla6ai ka duba wannan takardar na rubuta
komai amma duk da haka zan maka bayani da
baki.
"Da farko hotunan nan sai da nayi k'wak'waran
bincike akansu kafin nazo nan."
Hoto d'aya ya d'auko ya mik'a masa.
"Wannan sunansa Alhaji Hamza Umar, haifaffan
d'an garin Katsina ne kafin ayi masa transfer
zuwa nan Abuja. Wannan kuma matarsa ce
Hajiya Bilkisu, yaransu biyu kacal duka mata.
Babbar itace Amina wadda suke kira da Meenah
ga hotonta nan, sai k'aramar wadda babu wani
tazara a tsakaninsu mai suna Fatima Zarah. Duk
wad'annan hotunan sai da nayi bincike na gano
account name d'in d'iyarsa mai suna Zarah duk
a nan na kwaso hotunansu, ita Meenah a nata
account d'in babu hoto ko k'wara d'aya, hartta
handle d'insu yana nan a rubuce a jikin takardar.
Sai ita d'ayar mai suna Hajiya Layla ita tana
Kaduna da zama da mijinta mai suna Alhaji
Sambo, sai d'iyarta k'wara d'aya mai suna
Yasmeen."
Gwauron numfashi Faruk ya sauke a lokaci guda
kuma ya d'auko hotunan yaran nasu da akayi
masa nuni dasu yana ta kallonsu yana juya
hotunan. Aje hotunan kuma yayi yana kallon
Usman tare da d'ora hannayensa saman table
d'in yace.
"Good job, so anything else?"
Usman ya cigaba
"Yes, makaranta d'aya suke zuwa mai suna
Turkish, ita babbar tana k'ok'arin kammala
karatun nata ne while ita k'aramar wato Zarah
tana SS2 a yanzu. Duk weekend suna zuwa
Katsina wurin mahaifiyar Hamzan mai suna
Hajiya Fatima.
Idan suka je kamar misali ranar Juma'a zasu
dawo ranar Lahadi, amma yanzu bincike ya nuna
mani cewar sunyi akalla sati biyu basuje ba,
sakamakon jarabawa da d'iyar Alhaji Hamza
take shirin zanawa ta fita daga secondary.
Alhaji Hamza yakan d'auki yaranshi su fita
yawon shak'awatawa duk ranar Alhamis da
daddare."
Ajiyar zuciyar ya sauke yana kallon Usman ya
kuma cewa
"Anything else?
"Yawwa, ka tambaya ina da ina suke zuwa, to a
zahirin gaskiya yaran Alhaji Hamza basa fita
yawo, daga makaranta sai islamiyya, amma
daga nan basu cika zuwa ko ina ba. Amma kayi
hak'uri a 6angaren Hajiya Layla sai na k'ara
bincike don bansamu wani information sosai ba,
na dai gano cewar tana yawan fita Dubai saro
kaya."
Faruk yace
"Nagode, ka manta ka sanar dani aikin da sukeyi
fa."
Usman yace
"Sorry sir, Alhaji Hamza ma'aikacin banki ne,
amma matarsa bata aiki tana harkar kasuwanci,
wanda naji ance tana da gidajen mai, shaguna,
mall, tana da k'aton shagon saida saide, da
sauransu.
Haka zalika Alhaji Sambo shi d'an kasuwa ne
kuma yana aikin gwamnati."
Ya saki ajiyar zuciya yace
"Nagode da taimakon da kayi min duk da akan
aikinka ne amma ni ka taimake ni ba kad'an ba,
so nagode Allah saka da alkhairi."
Usman yayi dariya
"Haba yalla6ai menene na godiya? Ni keda
godiya ay."
Faruk yace
"Bakomai Usman zaka iya tafiya."
Daga haka ya amsa da "To." Sannan yayi masa
sallama ya fita.
Yana fita ya saki murmushin da shi kad'ai yasan
mana'arsa.
Murd'a k'ofar akayi aka shigo, Najeeb ne, da
murmushi Faruk yace
"Ka shigo mana."
Bayan ya zauna ne Najeeb ya soma magana
"Ka bani mamaki Faruk, ban ta6a tunanin haka
daga gareka ba..."
Gaban Faruk yayi mummunan fad'uwa, yace
"Me akayi?"
Najeeb yace
"Yanzu daman abinda kake shiryawa kenan baka
sanar dani ba? Inda banji me kuke cewa ba da
bazaka ta6a fad'a min ba ko?"
Faruk yace
"Ko kad'an ba haka bane, naso ace sai na gama
duk abinda ya kamata sai na sanar maka..."
Najeeb yace
"To tunda yanzu naji sai ka fad'a min komai."
Faruk yayi dariya yace
"Akan dai maganar nan ce ta kwanakin baya."
Najeeb yace
"Maganar iyayenka ko?"
Faruk yace
"Eh ita, so wani d'an bincike nasa aka yo mani
akan mutanen kuma an kawo."
Ya k'arasa yana mik'a masa hotunan.
Najeeb ya duba bayan ya gama yace.
"Ok to menene next move naka?"
Faruk yayi murmushin nasa da ya saba yi masu
ma'ana daban daban yace
"Zan sanar da kai komai, yanzu muje muyi
sallah mu dawo."
Najeeb yace
"Ok muje."
A tare suka mik'e suka fice daga office d'in.
***
Yana shiga d'akin nasa ya jiyo k'amshin turaren
wuta mai dad'i, ga sanyin ac gaurewa da d'akin.
Yasan baya wuce aikin Jidda, don ya lura tunda
suka dawo take faman d'wainiya dashi, bakin
gado ya zauna ya shiga cire takalminsa da safa,
bai kai ga gamawa ba ta shigo d'akin nasa,
hannunta d'auke da tray d'in ruwa da lemon
kwali 5alive, a d'an k'aramin table ta ajiye ta
d'ago tana kallonsa cike da kunya, tace
"Sannu da zuwa yaya."
Yace
"Yawwa sannu da aiki."
Tace
"Yawwa, kana buk'atar wani abu?"
Ya d'an karkato gami da kallonta yace
"A'a nagode."
Daga haka ta fice daga d'akin a yayinda shi
kuma ya fad'a toilet don watsa ruwa.
AUREN FANSA 18
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น18 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
***
Kwanci tashi babu wuya wurin Allah har su
Meenah sun gama zana exams d'in k'arshe.
Ranar da suka gama Baba yayi musu kyauta
mai tsoka sannan ya musu alk'awarin tafiya
Katsina hutu. Murna a wurin Meenah ba'a
magana, daman tafison can saboda can tafi
sakewa tayi abinda takeso, babu mai takura
mata.
Haushi Bilki kamar zata fashe, daman duk sadda
zasu je Katsina hutu sai hankalin Bilki ya tashi a
cewar ta mai mata ayyukan gidan bata nan.
Akan dole takeyi har sai sun dawo.
A tsarin hutun sati biyu zasuyi inji Baba, don
haka tun ranar Meenah ta fara shirin tafiya. Ta
wanke kayanta ta goge.
Ranar da zasu tafi tunda asuba ta tashi, bayan
tayi wanka ta d'auko cikin sabbin kayanta na
wata sallah ta saka, blue atamfa d'inkin riga da
skirt, tayi kyau sosai.
A lokacin data sakko k'asa ta iske Baba da
Zarah suna karyawa, yana ganinta yace.
"Maza zo kici abinci mu kama hanya."
Da saurinta kuwa ta taho tana murmushi.
Bayan sun kammala, Hassan mai gadinsu ya
shigo ya fara fitar musu da kayansu yana
sakawa boot.
Bilki ce ta sauko tana yak'e, tace
"Badai tafiyar bace?"
Baba yayi dariya yace
"Itace yanzu zamu kama hanya ma."
Ta had'iye 6acin ranta tace
"Wai tun yanzu Alhaji?"
Sai da yayi murmushi yace
"To idan bamu tafi yanzu ba sai yaushe zamu
tafi? Katsina fa ba nan ba."
Tace
"Hakane kam, to Allah ya tsare ya kaiku lafiya."
Yayi murmushin jin dad'i yace
"Amin."
Bayan gama ban kwana, Alhaji ya d'auki hanya
zuwa Katsinan Dikko.
Sai can yamma suka isa, da gudu su Meenah
sukayi ciki suna zuwa suka haye 'yar tsohuwar
dake zaune tana hutawa a parlor.
"Kai kai zaku 6alla ni ne?"
Sai kuma tayi murmushin jin dad'i
"Ahh Aminatu da Fatsima ne? Saukar yaushe?"
Meenah tace
"Yanzun nan muka iso, ina wuni Goggo?"
Tace
"Lafiya lau, ina Baban naku."
Meenah tace
"Yana waje yanzu zai shigo."
Bata rufe baki ba ya shigo.
"Lale maraba da Hamza."
Yayi dariya tare da zama k'asa yana kai gaisuwa
zuwa ga mahaifiyar tasa.
"Mun same ku lafiya?
Tace
"Alhamdulillahi, ya aiki?"
Yace
"Alhamdulillah, ya k'arfin jiki?"
Tace
"Sai godiyar Allah."
Yace
"Allah k'ara lafiya, daman yaran suka kammala
makaranta shine na kawo suyi maki sati biyu,
naga sun kwana biyu basu zo ba, ni kuma gobe
in Allah ya yarda zan juya."
Tace
"Kai masha Allah! Allah ya bada sa'a."
Suka amsa da "Amin."
BAYAN KWANA BIYAR.
Kamar kullum bayan Meenah ta sanya kayan
baccinta riga da wando kalar dark pink, tana
shirin kwanciya Zarah dake kwance tana latse
latse a wayarta ta ajiyewa wayar gami da kiran
sunanta.
"Meenah..."
Ta kalle ta gami da yin murmushi tace
"Na'am Zarah."
Jingina Zarah tayi jikin bangon gadon da take
kwance tace
"Meenah wai meyasa kika k'i sauraron wannan
mutumin? Nafa lura kamar sonki yake da
gaske."
Take annurin fuskarta ya 6ace 6at! Ta d'aure
fuska tamau gami da gyara zamanta kusa da
Zarah.
"Wane mutumi kenan?"
A iya sanin Zarah babu wanda ke takura mata
kamar wani wanda ke yawon matsa mata wai ya
had'u da ita a Instagram!
"Haba mana Meenah, kinfa san wa nake nufi."
"Ay ni bai furta man cewar yana sona ba..."
Ta fad'a gami da jawo wani novel na turanci mai
suna Behind the clouds ta soma bud'ewa tana
k'ok'arin karantawa.
Zarah tayi ajiyar zuciya tace
"Bafa kyau wulak'anci, ki daure ko yaya ne ki
sauarare shi."
Meenah ta ajiye littafin tana mai kallon Zarah
tace
"Zarah duk duniya banida aminiya sama da ke,
ke kanki kinsan cewa soyayya bata cikin ra'ayina
a yanzu, ban iya bama bansan ya take ba, ban
kuma san ta ina zan fara ba, nifa tun farko
sheyasa nace miki kar ki bud'e min irin
wad'annan abubuwan kika k'i ji Zarah, yanzu ga
irin ta nan, daman abinda nake gudu kenan."
Zarah ta kalle ta da mamaki tace
"Me kike gudu?"
Meenah tace
"Samarin zamani mana, 'yan k'arya mayaudara,
ina tsoron ayi min wasa da feelings d'ina,
sheyasa ma kikaga ina tsoron yin soyayya..."
"Ay ba duka aka taru aka zama d'aya ba, idan
kikayi sa'a sai kiga kin samu mai sonki da
gaske..."
"Zarah da kinyi hak'uri kin k'yale ni bazan iya
yin soyayya yanzu ba..."
Ta fad'a tana k'ok'arin cigaba da karatunta
ranta idan yayi dubu to ya 6ace.
"Bazan tilasta miki ba, amma ina rok'onki ki
bashi chance idan kikaga alamar mayaudari ne
basai ki rabu dashi ba? Menene a ciki? Ni
wallahi haka nan kawai yake bani tausayi kullum
cikin damuwa yake da ke, ina laifin me sonka?
Koda bai furta miki kalmar so yanzu ba, to na
tabbata zai furta maki nan bada jimawa ba!
Haba Meenah bansanki da wulak'anci ba..."
Ta d'aga mata hannu
"Ya isa Zarah, naji na amince zan bashi chance,
shikenan?"
Zarah tayi murmushi
"Shikenan, kiyi karatunki sai da safe."
Tayi murmushi
"Allah ya kaimu lafiya."
Gajiya tayi da karatun ta d'auko wayarta gami
da duba lokaci. K'arfe 12:53am, ajiye littafin tayi
tana k'ok'arin kwanciya message ya shigo ta
wayarta.
Tasan bai wuce d'an k'wak'war nan, ta fad'a a
cikin ranta gami da sakin d'an guntun tsaki.
Dubawa tayi.
"Hello."
"Hey."
"No answer?"
"How are you dear?"
"Hmm."
"Are you sleeping?"
"Please talk to me mana."
Da k'yar tace
"Hi."
Yana kwance yana latse latse a laptop nasa
message nata ya shigo, ya ware manyan
idanunsa cike da mamaki, murmushi yayi ya
rubuta mata.
"Thank God! Naji dad'i da kika man reply, i
thought na maki wani laifi ne?"
"A'a bakomai..."
"So ya kike? Kin dai hanani number ki ko?"
"Hmm."
"Bakomai kina min rowan jin muryarki mai dad'i
ko?"
"A'ah..."
"To ki bani mana, idan ba rowa ba."
Yau yaci albarkin Zarah, don haka sai kawai ta
tura masa number d'in.
Minti biyu tsakani...
Kwance take lamo, zuciyarta na mata sak'e
sak'e. Bata ankara ba wayarta ta fara ruri,
bak'uwar number ta gani. Da k'yar tasa hannu
ta d'auka....
AUREN FANSA 19
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น19 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Tun kafin ta kai ga d'auka haka kawai ta tsinci
kanta da fad'uwar gaba, ta kira sunan Allah don
neman nutsuwa cikin zuciyarta. Cikin ikon Rabbi
kuwa ta samu nutsuwa sai dai kafin ta d'auka
tuni wayar ta katse. Ajiyar zuciya tayi, sai dai
tana katsewa wani kiran na shigowa.
"AssalamuAlaiki yake ma'abociyar kyau, kwarjini
da kuma nutsuwa."
Abinka da rashin sabon waya da maza, tuni ta
rasa nutsuwarta, da k'yar ta amsa masa
"Wa'alakumsalam."
"Yau dai na taki sa'a tunda har aka d'auki
wayata sannan aka d'aga lokacki d'aya, lallai ni
mai babban sa'a ne. Ko ba haka ba 'yan mata?"
Ta k'ara kiran sunan Allah a karo na biyu,
saboda rashin sabo da kuma muryar mutumin da
bata san ko waye ba, sai dai me? Jin muryar
takeyi kamar ana busa sarewa, bata ta6a jin
murya mai dad'i ba irin ta wannan mutumin
ba...
"Ya kikayi shiru Princess?"
Gabanta ya yanke ya fad'i, wai wannan mutumin
kamar aljani? Da yayi mata magana sai gabanta
ya fad'i.
"Nidai muryar nan taki ko dai zan biya ne don na
lura tana tsada..."
"Ina wuni?"
Yayi murmushi, har tana jiyo sautin yana bugun
dodon kunnenta, sannan a take tsikar jikinsa ta
tashi tayi wani yarr!
"Kina lafiya?"
"Lafiya lau."
"To masha Allah, zan d'an baki dan gajeren
labarina, bana so ki zo kina ce min bakisan ko
da wa kike waya ba... ko ba haka ba?"
Tace
"Uhm."
Yace
"Yauwa, da farko sunana Faruk Adam, shekarata
26 kacal a duniya, iyayena sun rasu gaba d'aya
tun ina k'arami, yanzu daga ni sai k'anwata
muka rage, ina zaune gidan wani uncle d'ina a
garin Abuja. Mahafiyata shuwa ce while babana
fulani ne. Yanzu dai na kammala karatuna ina
aiki. To kinji kad'an daga cikin tarihin rayuwata,
ko zan iya jin naki?"
Tace "uhm, Allah ya jik'ansu."
Yace
"Amin, ina jinki fa."
Da k'yar ta iya tattaro nutsuwarta wuri d'aya ta
soma magana mai cike da nutsuwa.
"Sunana Amina Hamza, mahaifina d'an garin
Katsina ne amma yanzu aiki ya kai shi Abuja, na
kammala karatuna na fita daga secondary ina
jiran admission zan tafi university. Mu biyu ne
kad'ai a gidanmu daga ni sai k'anwata mai suna
Fatima."
Yayi murmushi
"Allah sarki Allah ya taimaka, to baki fad'a min
shekarunki ba?"
Tace
"16."
Yace
"Wow, lallai ashe dai da sauranki yarinya."
Tayi murmushi mai cike da kunya.
Haka suka 6ata wannan daren Faruk na janta da
fira, tun tana d'ari d'ari har ta d'an saki jikinta
tana bashi amsa, idan akayi labarin dariya suyi
dariya, daga k'arshe ganin har uku na dare ya
sashi yayi mata sallama akan zai kirata da safe.
Koda ta kwanta kasa bacci tayi, muryarsa kawai
takeji cikin dodon kunnenta kamar yanzu yake
mata magana.
Daman bata sallah sheyasa ma bata tashi da
asuba ba. Bacci takeyi har kusan goma da rabi
na safe.
Juyi d'aya tayi akan gado tayi tozali da wayarta
kamar had'in baki sai kuma ta fara ruri. Ganin
number d'in jiya ya sata sakin murmushi ba
shiri.
A kasalance ta d'auka gami da yin sallama.
"Good morning! Rise and shine, raina ya bani
yanzun nan kika farka daga bacci, ko da yake
laifi nane dana hana ki bacci da wuri tun jiya
ko? To ayi min afuwa. Bazan sake ba."
Cikin ranta tace
"Wannan sai kace aku ko gajiya baiyi da
magana?"
"Ina kwana?"
Yayi murmushi
"Lafiya lau da fatan princess d'in tawa ta tashi
lafiya?"
Ta langa6ar da kanta gami da lumshe idanu
tace.
"Alhamdulillah, thanks."
Yace
"Yauwa, to yanzu abinda ya kamata kije kiyi
wanka sai kici abinci."
"To." Kawai tace gami da yi masa sallama ta
kashe wayar. Ganin Zarah tsaye bakin k'ofa ya
sa gaban Meenah ya yanke ya fad'i. Zarah ta
k'araso tana dariya
"Love in the air, yanzu don Allah bakiji dad'i ba?
Amma ace mutum ya takura ma kansa da
rayuwar kad'aici haba!"
Murmushi tayi ta sauka daga kan gadon tace
"Bari nayi wanka."
Tana jin Zarah na d'aga murya tana fad'in
"Wai don dai kar ayi maganar zaki wani shige
wanka."
Murmushi kawai tayi.
Wunin ranar zungur a d'aki tayi shi, har dare
bata fito ba, ba abinda ke tashinta daga gado
sai shiga toilet.
Washe gari kuma haka ta tashi sukuku. Zarah ta
rasa gane kan yayar tata.
Haka dai komai ya cigaba da gudana a tsakanin
Meenah ta Faruk, wuni sukeyi mak'ale a waya,
zuciyarta ta aminta da shi lokaci guda, ta yarda
ta amince shi d'in takeso. Tun da ya turo mata
hotunan sa taji yayi mata, lokaci guda ya sace
zuciyarta ya kuma tafi da imaninta gaba d'aya,
har ta soma cewa cikin ranta
"Anya ba surk'ullensu na fulani yayi mani ba?"
Wata rana da daddare yana ta kiranta ya sanar
mata gobe zaizo wurinta, daman sunyi zaizo
Katsina, idan yazo zai shigo su gaisa. A lokacin
da yake ta kiranta tana bacci kuma wayar a
silent take.
Washe gari da safe sai ta iske message d'insa
ya turo mata.
"Just to say good night! With you in my
mind... ?"
Sai tayi murmushi ta tura
"In both the soul and mind...."
A lokacin da ta tura masa sak'on bai gani ba
saboda yana cikin jirgi don tahowa Katsina!
AUREN FANSA 20
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Dedicated to each and every reader, you always
support me, and i am grateful for that! Thanks
alot!❤️
๐น20 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Awa biyu tsakani ya diro cikin garin katsina,
yana isa airport ya ciro wayarsa ya buga ma
Meenah waya ya sanar da ita isowar tasa. Zarah
bata gama shan mamaki ba sai da Meenah ta
shiga kitchen don girka masa lafiyayyen abinci
mai rai da lafiya. Coconut rice da miyar kaji, gefe
kuma Russian salad ne, sai drinks kala kala.
Banda su snacks da aka tanada. Goggo da
k'amshi ya cika mata hanci ta fito daga d'aki ta
lek'o tana fad'in.
"Kai lafiya me kuke dafawa?"
Zarah tayi dariya tace
"Ay Goggo surukinki ne zaizo, shine fa su
Meenah ake ta shiri haka."
Meenah ta sunkuyar da kanta tana murmushi,
Goggo tayi dariya tace
"Ahh lallai kice munada babban bak'o, ay gara
dai yayi yazo ko zamu huta hakan nan."
Bata gama komai ba sai da k'arfe bakwai harda
rabi. Kasacewar yace mata da anyi sallar isha'i
zaizo.
Tana gama wannan aikin ta shiga wanka ta fito
ta shirya cikin wani lace ruwan zuma (coffee
brown) da light pink a jikinshi, d'inkin riga da
skirt. Da taimakon Zarah ta d'aure d'ankwalin
kayan irin na zamin da ake kira mai steps. Ga
d'ankunne an sa kalar kayan. Tana gama fesa
turare wayarta ta hau ruri da alama Faruk ya
iso. A karo na farko taji ta gigice, kasancewar a
yau zata ta6a fuskantar wani d'a namiji a
rayuwarta da idanun soyayya. Bayan ta d'auka
ya sanar da ita isowar tasa cewar yana bakin
k'ofa. Ba yadda batayi da Zarah ba akan ta
shigo dashi tak'i, harda zolayarta wai ay ba
saurayinta bane ita. Hakan yasa ta d'auki waya
ta tura masa da message akan yasa a shigo da
shi bakin k'ofa (main entrance).
Tana bud'e mishi k'ofa suka bi juna da kallo mai
kwantar da zuciya, kafin kuma dukkansu su saki
murmushi mai d'auke da wani 6oyayyen sirri.
Mamaki takeyi akan yadda yafi kyau a fili akan a
hoto...
Ta kauce ta bashi hanya ya shigo, yanan sanye
da shadda marar nauyi kalar sky blue sun kama
jikinshi, idonshi mak'ale cikin farin glass wanda
ya k'ara fito da cikar kamalarshi na cikakken
namiji, wanda boko ya zauna masa sannan kud'i
ma suka zauna masa had'e da hutu, ga kuma
uwa uba kyau, ba abinda ke tashi a wurin kamar
k'amshin turarensa mai sanyaya zuciya.
Meenah fa tayi nisa a kallonsa yayi murmushi ya
soma karkad'a mata key d'in motarsa, taji kunya
sosai ta wuce ciki kanta k'asa, yabi bayanta.
Suka zauna kan kujeru parlon Goggo, da k'yar ta
ce
"Ya hanya? Ya kuma gajiya?"
Yayi k'awataccen murmushin dake fizge zuciya
yace
"Alhamdulillah, ya gida ya hutu?"
Tayi murmushi still bata d'ago kanta ba tace
"Komai alhmdulillah, yasu Anisah?"
Yace
"Suna can lafiya lau, ina Goggo da Zarah?"
Kafin tayi magana Zarah ta fito da k'aton tray
mai d'auke da lemo kala kala da cups d'in glass
guda biyu. Sai data dire bisa center table d'in
dake parlor sannan ta zauna suka gaisa a
mutunce, yace
"Ga Zarah nan kenan? Itace sweet sister d'inki.
Sannu Zarah ya kike? I've heard so much about
you, gaskiya sister nan taki tana ji take."
Zarah tayi dariya
"Haka ne, nima ina ji da ita ay."
Tana gama fad'an haka ta mik'e tsaye ta fice.
Ba'a juma ba kuma ta dawo d'auke da wani tray
d'in mai d'auke da kuloli guda biyu, plate biyu
sai kuma bowl na snacks da salad. Bayan ta dire
sum sum ta fice saboda yadda taga sun kasa
6oye soyayyar da ke zuciyoyinsu a gabanta.
Ta lek'o don zuwa kitchen had'o tea, daman ita
Zarah al'adarta ce duk dare sai tasha ruwan
lipton (green tea) kafin ta kwanta, nan ta hango
su suna cin abinci a plate d'aya, sai kuma
sukayi mata kyau, kuma sun mugun dacewa da
juna, abinda Faruk zai nuna ma Meenah shine
haske fata don shi fari ne nesa ba kusa ba,
Meenah kuwa bak'a ce (chocolate color). Suna
cin abincin suna kallon juna, fatar bakinsu kuwa
kad'an take motsi daga lokaci zuwa lokaci. Ta
koma d'aki tana mamaki sai kace ba Meenah ba,
gaba d'aya ta fad'a tarkon so.
Kafin ya tafi ya d'auko kyauta gift d'in turare da
agogo ya bata, amma sam tak'i kar6a, sai da
yayi da gaske har yana neman yin fushi sannan
ta kar6a tana godiya sosai.
Soyayya tsakanin Meenah da Faruk kullum abin
dad'a gaba yake cike da salo na ban mamaki,
basu iya yini d'aya basuyi waya ba, haka ma
kullum yana kan hanyar zuwa wurinta.
Tabbas zuwa yanzu soyayyar da Meenah ke ma
Faruk bata misaltuwa, abin mamaki Faruk ya iya
tafiyar da soyayya yadda ya kamata ya kuma
son hanyoyi daban daban na yadda zai jawo
hankalinta gare shi, ga yaci sa'a wannan shine
karo na farko data fara sanin yadda ake soyayya,
sheyasa a halin yanzu duk wanda zata so zata
soshi ne da dukkan zuciya da kuma ruhinta.
Faruk ya riga da ya saye zuciyarta farat d'aya,
ko irin kalaman da yake furta mata kad'ai ya isa
ya saye zuciyar Meenah, don haka sheysa bai
sha wahalar yiwa zuciyar Meenah kamun kazar
kuku ba!
Batada wani tunani sai na Faruk, batada wani
ra'ayi sai nasa, sannan batada wani buri sai na
mallakarsa a matsayin mijinta na abokin rayuwa
na har k'arshen rayuwarta ba.
AUREN FANSA 21
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น21 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Bayan kwana biyu da safe sai ga Baba ya diro
garin wai da niyyar d'aukar su Meenah,
hanakalin Meenah ya tashi don tasan da k'yar
idan Mami zata barta tayi soyayya ba, tasan dai
Baba baida matsala, amma Mami take ji. Aikuwa
tana sanar da Faruk cewar gobe zasu koma
Abuja yace shima zai tattara ya koma daman ya
gama abinda ya kawo shi, sai ya koma zai
cigaba da kawo mata ziyara.
Washe gari kuwa suka tattaro suka dawo gida.
Duk da hankalinta a tashe yake hakan baisa taji
ko d'ar a zuciyarta game da son da takeyi wa
Faruk Adam ba. A ganinta shi d'in yasan menene
so, yasan darajar abinda yakeson, ya kuma iya
tafiyar da shi ta hanyoyi daban daban, ya iya
tarairaiyar mace da bata kulawa yadda ya
kamata. Sheyasa son da take masa shi yake
k'ara bata k'warin gwiwar fuskantar Mami.
Suna dawowa kuwa kusan kullum sai yazo, har
dai ya zama d'an gida, yadda taga Baba ya
amshi Faruk hannu bibbiyu ya sanya dole taja
bakinta tayi tsit, kuma kullum yazo Zarah ke
raka Meenah fira, hakan yasa ita kanta Mamin
ta rasa gane wurin wa yake zuwa, amma tana
fatan wurin Zarah yake zuwa, don a yadda take
gani mutum ne mai kud'i sosai.
*
K'arfe takwas na dare kamar kullum Faruk ya isa
gidansu Meenah, kasancewar ya zama d'an gida
tsakanin Baba da Mami.
Bayan sun gaisa da Baba, a lokacin Baba yana
da niyyar fita, haka ma Mami tana sama tana
fama da lissafin kud'in kasuwancinta.
Yana nan zaune yana jiran Meenah. Aikuwa sai
gata ta fito tayi kyau kamar kullum cikin material
mai taushi silver da ratsin bak'i a jikinshi, d'inkin
doguwar riga, d'inkin bai kama jikinta ba. Tun
daga nesa suke sakarma da junansu murmushi
mai sanyi. Ta zauna a kujerar dake fuskantarsa,
centre table ne mai bak'in glass a tsakiya wanda
aka d'aura kayan marmari cikin tray kala kala a
cikinsa, irinsu Apple, grapes, banana, orange,
pear da sauransu. Zamewa yayi ya zauna k'asa
gami da rausayar da kai yace.
"Barka da hutu!".
Dariya ya bata sosai saboda yadda yayi
maganar, tace
"Alhamdulillah, muna ta sha kam."
Yayi shiru zuwa wani lokaci sannan yace.
"Zuwa yaushe kike ganin za'a aurar da ke?"
Ita dariya ma ya bata tace
"Aure ay lokaci ne... sai lokaci yayi sannan."
Ya langa6ar da kai yace
"Haka ne, amma ni ko yanzu aka bani ke zan
kar6a hannu bibbiyu, zan nuna maki k'auna ta
ban mamaki, sai dai bansani ba ko ke zaki so ni
kamar yadda nake son ki... sannan ina so idan
Allah ya kaimu zan sanar da iyayenki cewar
aurenki zanyi..."
Ta lumshe idanu cikin wata sabuwar k'auna
dake k'ara mamayarta, ta kuma k'ara lallu6e
mata zuciyarta, tace
"Kar kayi tantama a kaina ya Faruk, soyayyarmu
had'in Allah ce, i respect you and your values..
Faruk d'in da nake so bana ganin kowa sai shi,
bana jin k'aunar kowa sai shi... haka ma banida
buri a yanzu sama da mallakarka a matsayin
mijin aurena na har abada..."
Sai bayan ta furta hakan kuma kunya ta kamata
had'e da mamaki, yadda ta zauna tayi ta zuba
kamar pampo, amma daga baya sai take ganin
kamar su6utar baki tayi. Sai tayi saurin cewa
"Nidai fatana ka rik'e soyayya ta, kada kaci
amanata, ka yarda dani, idan kayi min wannan
to ni kuma nayi maka alk'awarin baka dukkan
kulawa."
Sai ya rasa abin cewa kuma, murmushi tayi ta
sauko k'asa ta shiga yanka masa kayan
marmarin yana sha.
***
Bilki ta soma tsarguwa da yawan zuwan Faruk
cikin gidansu, da yawan ke6ewa da sukeyi shida
Meenah akan Zarah suna fira. Ga wata sabuwar
al'ada da Meenah ta 6ullo da ita na yawan
kwalliya wadda ta gama lura don Faruk take
yinta. Ta gigice ta shiga damuwa sosai, neman
k'arin bayani takeyi tasan Zarah bazata ta6a
fad'a mata ba saboda an ta6o 'yar uwarta haka
bata ganin aibunta, su koda wani abin ne ba'ajin
ta cikinsu kashewa sukeyi su rufe babu mai ji.
Ko fad'a sukayi baya wuce yini d'aya idan kuwa
sun dad'e to kwana d'aya ne sun shirya sun
kuma manta komai. Don haka taga babu mafita
illa ta tunkari Meenah tayi mata bayanin abinda
take zargi.
K'arfe tara na dare ta raka Faruk ya tafi, tana
dawowa ta taradda Mami tsaye gefen gadonta
ta hard'e hanyayyenta wuri d'aya tana huci.
"Mami....?"
Ta dube ta sosai daga sama har k'asa tace
"Amina....!"
Bata amsa ba illa ta dube ta a yadda take
kiranta cikin wata irin murya. Sai kawai ta jeho
mata tambaya
"Meke tsakaninki da Faruk?"
Ta sunkuyar da kanta k'asa, batayi magana ba,
sai da Bilkin ta daka mata uwar tsawa mai gigita
k'wala.
"Bada ke nake magana ba?!"
Cikin sark'ewar murya tace
"Da...ma yace yana...so...na tun muna Katsina,
kuma daman gobe ne Faruk d'in yake niyyar
sanar daku muna son junanmu... mun yanke
shawarar yin au..."
Ji kake tassa!!! Mami ta d'auke ta da wani irin
wawan marin da har sai data ga giftawar wuta,
ta nemi ji da ganinta ta rasa!
AUREN FANSA 22
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Dedicated to Mrs Fawwaz, Sadnaf, Momyn
Sultan, my sakwara, Maman Khady, Jannatuwa,
Faridat Musa, Rufaida Yusuf. One luv guys❤️๐
๐น22 ๐น
http://MaryamSBello.blogspot.com
Bilki ta soma magana cikin fushi.
"Kin bani mamaki Meenah, yanzu har yaushe
idonki ya bud'e da kike neman k'wace ma 'yar
uwarki saurayi? Ke ko kunya bakiji ace 'yar
uwarki tana son wani kema kina sonsa? Fatima
fa k'anwarki ce Amina, ay na d'auka ke mai
d'auka ce ki sadaukar mata da wani idan ta
kama, amma wai ke! Kece mai k'wacewa
Meenah."!
Ta share hawayenta cikin tsantsan mamakin
Mamin tasu, muryarta na rawa ta soma magana.
"Mami Faruk bai ta6a cewa yana son Zarah ba,
ni yake so tun asali, ko ita Fatiman ba sonsa
take ba, ni bansan ina kika ji cewar saurayin
Fatima ne ba, idan ma kina tunanin cewar
saurayin Fatima ne to ki daina tun wuri." Sai
kuma ta juya mata baya gami da had'e
hannayenta wuri d'aya tace
"A baya kinsha k'wace min kyauta a makaranta,
amma gaskiya yanzu bazan yarda a k'wace min
Faruk ba, hak'uri zakiyi ki sa mana albarka!"
Sai kawai Bilki tasa salati, yau tana fad'a
Meenah na fad'a.
"Lallai wuyanki yayi k'wari ya isa yanka, akan
nace kin k'wace wa 'yar uwarki saurayi kike
neman ki fad'a min magana Meenah."
Ta fad'a tana nuna kanta.
"Bafa saurayi na bane Mami."
Duk suka d'aga ido tana tsaye bakin k'ofa
idanunta sun kad'a daga fari zuwa ja! A hankali
ta k'araso cikin d'akin tana share hawaye tace
"Akan me zaki mare ta akan maganar da bakida
tabbas a kanta? Mami! Ki sani Meenah 'yar
uwata ce ta jini, ta yaya kike tunanin zata
k'wace min saurayi? To bari kiji abinda baki sani
ba, Faruk saurayin Meenah ne bani ba, ko don
kinga ina zuwa muna fira dashi kikayi tunanin
saurayina ne?" Tayi murmushi tace
"To ba haka bane, ni kawai mun saba ne
sheyasa kikaga ina fita amma lokuta da dama
ay tare da Meenah muke zuwa, duk randa kika
ga naje ni kad'ai to Meenah ta tura ni akan in je
kafin tazo." Ta kalli Meenah dake hawaye wani
na bin wani, tasa hannu ta share mata tace
"Daina kuka 'yar uwata, kiyi hak'uri da abinda
Mami tayi miki, sannan kisa a ranki Faruk naki
ne ke kad'ai kinji?"
Suka rungume juna suna kuka.
Haushi ya kashe Bilku kafin kuma sum sum ta
fice daga d'akin cike da kunya!
A wannan daren Bilki batayi bacci ba, yadda
taga rana haka taga dare.
Washe gari Meenah taga fushin Bilki fiye da
yadda ta saba gani, da Zarah take sabgoginta,
itama sai ta kama kanta a d'aki tak'i fitowa
tana karance-karancenta. Sai dai zuciyarta cike
take da tsoron Mamin, data tuna marin da tasha
jiya sai gabanta ya fad'i.
*
K'arfe goma na safe Faruk yazo, Bilki na zaune
parlor tana chanza channel, tun daga jin
sallamarsa tabi ta d'aure fuska yadda bata ta6a
yi masa ba. Yana zuwa ya zube k'asa yana
gaishe ta, sai kawai ta kafa masa ido bata amsa
ba, k'arshe ma sai ta mik'e ta haye bene zuwa
d'akinta ba tare da tace komai ba. Meenah na
daga bak'in k'ofar kitchen tana ganin komai, ita
kunya ma ta kamata ta kuma kasa k'arasowa
ciki. Sai da ta d'auki akalla minti biyu sannan
tayi ta maza ta shigo parlon kanta a k'asa.
Dukkansu sunyi shiru aka rasa mai fara yin
magana a cikinsu.
Da k'yar Faruk ya daure yayi murmushi cikin
basarwa yace
"Munyi ma Mami laifi ko?"
Ta d'an d'ago suka had'a ido, ta lumshe idanu
tace.
"Tun jiya take haka, mun rasa gane mata."
Yayi shiru cikin tunani, can kuma yace
"K'ila bata amince dani ba..."
Tayi saurin cewa
"Bakomai zata huce ne."
Baba ne ya ke saukowa daga mattakalar bene
Bilkin na biye da shi tana rik'e da briefcase
d'insa, ya hango shi a parlor zaune, da sauri ya
mik'e cikin girmamawa yabi bayansa don yaga
kamar parlonsa ya nufa daga can 6angarensa.
Baba nakan kujera Faruk na gefensa daga k'asa.
Bayan sun gaisa kamar kullum cikin mutunci da
girmama juna, can Baba yace
"Umar Faruk."
Ya d'ago da fararen idanunsa ya dube shi yace
"Na'am Baba."
"Meke tsakaninka da Amina?"
Faruk ya rud'e ya shiga inda inda saboda yadda
yaga Baban ya masa kwarjini, take kuma ya
sadda kansa k'asa.
0 comments:
Post a Comment