😍
Daga d'an nesa yakejin kamar ana k'wala masa
kira, hakan ya dakatar dashi daga bud'e motarsa
da yakeyi. Hango Najeeb yayi yana k'arasowa
cikin d'an gudu gudu, tun daga nesa yake hango
sa kamar yana cikin damuwa. Sai da ya k'araso
dab da shi sannan Najeeb yace
"Wai tafiya zakayi da wuri haka? Wurinka nazo
fa."
Faruk yace
"To, kuma gashi har na rufe office zan wuce
gida, amma idan maganar batada tsawo mu
shiga daga ciki."
Najeeb yace
"No batada wani tsawo sosai, no need ma mu
shiga daga ciki muna iya tsayawa a nan."
Faruk yace
"Ok kafin nan ya gida ya k'anwata da fatan ana
kula min da ita sosai?"
Najeeb yace
"Haba mana kai kason yadda nakeson Anisah
ay, dole ma na kula da ita. Yawwa wata magana
nake ji daga gida cewar zaka k'ara aure, shin
gaskiya ne ko ba gaskiya bane ba?"
Faruk yace
"Wannan magana gaskiya ne, haka take."
Najeeb yace
"Amma ka bani mamaki Faruk, ta yaya zaka
k'ara aure yanzu? Daga yin aurenku, baka bari
nan gaba kad'an idan ma zaka k'ara sai ka
k'ara. Haba Faruk..."
Faruk yayi murmushi yace
"Najeeb kenan, gani nayi fa ba haramun bane
k'ara aurennan, sannan ba wata bare bace zan
aura 'yar gida ce."
Najeeb yace
"Nasani mana, amma baka ganin Jidda bata
dace da kai ba?"
Faruk sai ya kama dariya yace
"Ta yaya?"
Najeeb yace
"Haba Faruk, yarinyar nan kasani sarai batajin
magana, kullum cikin yawo take, gata ta tara
k'awaye a gida, baka ganin yadda su Dada ke
fama da ita? Kai baka tunanin ta zame maka
matsala a gidanka da kai da iyalinka nan gaba?
Kuna zaman lafiya kaje ka jajibo ma kanka
masifa har gida...?"
"Wa'iyazubillahi! Haba Najeeb ka daina kira min
masifa a gida, insha Allah babu abinda zai faru
sai alkhairi. Kuma da kake batun Jidda bataji
zan gyara ta, kai kanka zakayi mamaki."
Najeeb ya kad'a kafad'a alamun oho yace
"Well it's your choice not mine, don't say I
didn't warn you to."
Faruk yace
"Yawwa kuma nagode da shawara, zamu iya
tafiya?"
Najeeb yace
"Of course, ni zan tafi sai anjima a gaida gida."
***
A gajiye ya shigo gidan, tana zaune kan kujera ta
zaman mutum uku, hannunta rik'e da remote
tana chanza channel d'in da take muradin kallo.
Tunda ya shigo yake binta da ido, a tsawon
rayuwarsa bai ta6a ganin Meenah cikin irin
wannan ado haka ba.
Wani dark blue leshi ne a jikinta mai yarfin
golding, ga wasu duwatsu dake rauraya daga
gaban rigar, d'inkin an mata wanda ake cema da
peplum sai skirt da ya kamata, d'aurin
d'ankwalin kuwa kamar don ita akayi shi, tana
sanye da 'yan kunne da sark'a kalar kayanta,
yadda kasan wata matar shugaban k'asa ko
wani gwamna saboda yanayin shigarta ya nuna
hakan. K'amshin gidan ya had'u ya gauraye
dana sanyin ac, hakan ba k'aramin dad'i yayi
masa ba.
Bata ankara ba sai ganin mutum tayi tsaye a
gabanta, murmushi ta sakar masa mai saurin
fizge zuciya a yayinda ya mayar mata ba 6ata
lokaci, sannan kuma ta tashi a hankali ta
k'araso inda yake tana mai tafiya cike da
nutsuwa. Shi dai yana tsaye yana binta da idanu,
ta amshi briefcase d'insa tare da kama
hannunsa tace
"My soul lafiya ka dawo da wuri haka?"
Ya dube ta cikin kulawa yace
"Wallahi kuwa na gaji ne, sannan yau bawani aiki
sosai."
Tace
"Ok muje kayi wanka ko abinci zaka fara ci?"
Ya girgiza kansa alamun a'a yace
"Bari inyi wankan dai zai fi, sai inci abincin daga
baya."
Hannunsa take ja yana biye da ita har d'akinsa
sannan ta shiga ta had'a masa ruwan wanka
kamar kullum, bayan ta fito ta taimaka masa ya
rage kayan jikinsa, sannan ta fice ta bashi wuri
ya kimtsa.
Bayan sun gama cin abinci ne suna zaune a
parlor suna hutawa Meenah ta soma magana.
"My soul don Allah na tambaye ka?"
Ya gyara zamansa yana fuskantarta yace
"Eh Allah yasa nasani."
Tayi murmushi tace
"Daman... nace ina kake ganin za'a samu 'yar
aiki?"
Yace
" 'Yar aiki kuma? Me za'ayi da ita?"
Tace
"Mami daman keso, ni bansan inda ake samu ba
shine nace bari na tambaye ka."
Hajir ta fad'o masa a rai, take kuma ya fara
murmushi ganin wata dama ta samu da zaiyi
amfani da ita kuma bazai bari ta wuce shi ba.
Sai yayi saurin cewa.
"Haba indan wannan ne kar ki damu, Mama na
da masu aiki, so samowa bazaiyi wahala ba, zan
mata magana."
Cike da jin dad'i tace
"Kai nagode sosai my soul."
Ya d'an tsunkuli gefen kumatunta yace
"Anything for my baby."
****
Washe gari a office yasa aka kira masa Hajir,
tana zuwa yace ta zauna, bayan ta zauna ya
soma magana.
"Kamar yadda nayi miki bayani jiya zamuyi
magana, to shine yanzu zan miki bayani. Da
farko wani aiki zakiyi min, sannan don Allah ina
buka'atar had'in kanki Hajir."
Hajir tayi dariya
"Insha Allah sir."
Yaji dad'i yace
"Da farko ina so ki chanza identity d'inki gaba
d'aya."
Cikin rashin fahimta tace
"Bangane ba?"
Yayi ajiyar zuciya yace
"Ma'ana ina so ki tashi daga Hajir, 'yar gayu,
mai ilimi, mai kud'i ki koma Atika bak'auya,
marar ilimi, marar kud'i sannan kuma 'yar
k'auye sannan Atika 'yar aiki, amma kar ki damu
aikin naki bazai dad'e ba, sannan zansa a linka
miki albashinki fiye da yadda ake baki."
Da mamaki tace
"Naji bayaninka, amma zan iya sanin dalili?"
Yace
"Yawwa, dalili kuwa shine, information nake
buk'ata daga wurinki dangane da labarin dana
baki jiya, dangane da mutuwar iyaye na. Abinda
nake so dake zakije a matsayin 'yar aiki. So
aikinki yana buk'atar hak'uri, dauriya, jajircewa,
da fatan kin fahimta?"
Tace
"Na fahimta sir, kuma insha Allah baza'a samu
matsala ba. Na farko taimako zanyi, duk da ban
ta6a cin karo da aiki irin haka ba, amma na
maka alk'awarin zaka same ni mai cika
alk'awari. Sannan insha Allah zaka same ni mai
hak'uri da kuma dauriya."
Yaji dad'i sosai ya cigaba
"Alhamdulillah, da farko zan d'an baki wasu
kud'i kije kasuwa ki siyo 'yan atamfofi ki kai ayi
miki d'inkin 'yan k'auye, sai ayi ta wanke su har
su k'ok'e, daman ba masu tsada bane hakan
bazaiyi wahala ba. Na biyu idan kin zama ready
sai ki sanar dani sai nasa a kaiki inda zaki fara
aikin. Na uku duk wani abu da kikaji ya zamanto
kin rubuta shi inda hali ma ki mani vnote, ko kiyi
duka biyun. Sannan zan siya miki k'aramar waya
marar tsada ki saka sabon sim card yadda
bawanda ya sanki da layin don kar a samu
matsala. Aikinnan Hajir yana buk'atar lura da sa
ido, ko wane motsi nata akanki, duk abinda kikaji
ki rubuta ki kuma yi recording. Da munsamu
muka had'a duk wani information da zamu
buk'ata shikenan, sai na fad'a miki yadda
za'ayi. Kar kiyi wani abu da zata gane ke ba 'yar
k'auye bace, kar ki kuskura ki nuna kin iya
turanci, kuma ki mata biyayya duk abinda ta saki
kiyi. Shine kawai abinda nake buk'ata a wurinki."
Ta saki ajiyar zuciya tace
"Tabbas bazan baka kunya ba sir, insha Allah na
maka alk'awarin taimaka maka wurin gano
abinda kakeson ganowa, yanzu dana tashi daga
nan zan wuce kasuwa sai na siyo abubuwan da
nake buk'ata, ka bani nan da kwana biyu, zan zo
sai ka kaini wurin aikin."
Yayi murmushi mai bayyana hak'ora yace
"Kai naji dad'i sosai wallahi, Allah ya bada sa'a,
zan rik'a turo maki da kati lokaci zuwa lokaci,
duk sadda kike buk'atar wani abu sai ki kirani. Ki
tafi da babbar wayarki saboda recording d'in sai
ya zamana kin 6oye ta yadda baza'a gane ta ba.
Sai ki rik'a fiddo k'aramar kina amfani da ita. To
make it more successful zaki iya rik'ayin wayar
k'arya kamar kina kiran iyayenki kuna gaisawa a
can k'auye."
Tace
"Babu matsala insha Allah."
Yace
"Yawwa."
Nan ya fiddo cheque ya rubuta mata kud'i masu
tsoka sannan yayi mata godiya ta tafi.
AUREN FANSA 31
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain we touch the heart of
readers_*
PML
🌹31 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Komai tsab tuni ta kammala, ita da gida sun
d'auki haske da k'amshi. Ta dafa masa Chinese
rice with vegetable soup, sai salad. Bayan ta
gama sai ta fad'a wanka ta kammala ta fito,
yau ranar farko data bud'e 6angaren English
wears, ta fiddo wani shegen tight wando kalar
ash gashi marar tsawo da riga dark pink mai
k'aramin hannu. Ta dad'e tana shawarar ta saka
su, daga k'arshe dai tayi shahada ta sa duk da
tana jin kunya amma dole ta yakice ta wuri
d'aya. Bayan ta saka kayan sai ta taje kanta da
mayuka masu k'amshi tayi parking d'inshi da
pink ribbon daga can tsakiya sai jelar ta sauko
bisa gdon bayanta. Tabi da turaruka masu dad'i.
Ta gama shiryawa da kusan minti goma
idanunta na kan k'ofa har ta gaji da kallo, ta
jawo laptop nata da Baba ya siya mata itada
Zarah ta soma daddannawa, bata ankara ba sai
taji charab an kamo ta. Ta mik'e zumbur cike da
tsoro, sai data juyo suka kalli juna yayi
murmushi.
"Ashe kinada tsoro haka baby?"
Ta zum6uro baki abinda ke birgesa tace
"A'a ba tsoro naji ba."
Yace
"Tsoro kika ji mana, bayan na gani da ido na."
Tayi dariya tace
"Sannu da zuwa."
Yace
"Yauwa."
K'irr! K'arar door bell ta shiga dodon kunnensu,
ya dube ta yace
"Koma ciki Bala direba ne zai shigo da kaya."
Tayi ciki bata k'ara fitowa ba, ta wuce ta had'a
masa ruwan wanka, da kanshi ya lek'o yace fito
muyi fira. Tayi dariya tace
"Kai dai ka shigo ka watsa ruwa kaji dad'i."
Yace
"Angama baby."
Da taimakonta ta zare masa komai, ya shiga
toilet, ta fiddo masa singlet da gajeren wando.
Yana fitowa kuma yace
"Zo ki shafa man mai." Da mamaki kuma ya
dubi kansa wanda baisan ya furta hakan ba. Ta
sunkuyar da kanta k'asa tace
"Uhm bari naje na gyara dinning."
Da sauri ta fice inda shi kuma ya cigaba da
kallon k'ofar data bi, ajiyar zuciya ya saki ya
shirya tsab ya fito.
Suna tsakar cin abinci wayarsa ta fara ringing,
ganin Jidda yasa gabansa ya fad'i, cikin sanyin
jiki ya d'auka sannan ya dubi Meenah data tsare
shi da idanu. Yace
"He...llo."
"Hello ya Faruk a gaskiya fushi nake da kai."
Yayi yak'e yace
"Menayi?"
Tace
"Har yanzu ko kazo wurina ko? Daman nasan
baka sona."
Yace
"Ba haka bane zanzo..."
"To yaushe?"
Ya kalli Meenah har yanzu shi d'in take kallo.
Sai ya mik'e sum sum ya shiga kitchen.
Zuciyarta ta sosu, ko ba'a fad'a mata ba tasan
da mace yake waya. Macen ma wadda zai aura,
bata ankara ba hawaye suka zubo mata, jin
alamun tafiya yasa tayi saurin goge hawayenta
cikin dakewa ta k'ak'alo murmushi tana dubansa
a lokacin da yake zama kan kujera. Ya d'an
murmusa yana kauda fuska cike da kunya.
Sai da suka gama cin abincin ne ya mik'e yana
aduba agogon hannunsa. K'arfe 8:44pm. Kallon
Meenah yayi yace
"Zan fita bazan jima ba zan dawo."
Tace
"Yanzu? Ina zakaje?"
Yayi yak'e yace
"Ahh karki damu bawani dad'ewa zanyi ba."
Da sauri ya koma ciki ya sake shiri cikin light
brown yadi mai matuk'ar taushi, har hular kansa
kalar kayan, yayi kyau sosai. Kiss yayi mata a
kumatu yace
"Sai na dawo baby."
Haka tana ji tana gani ya fita, sai k'amshinsa da
ya bar mata a hanci, wanda ta tabbatar wurin
budurwa zaije. Kuka ya k'wace mata ta yi
d'akinta da gudu ta fad'a kan gado. Zuciyarta na
tafasa kamar ruwan zafi.
***
Tsaye take a gaban madubi ta ci ado na k'in
k'ari kai kace zataje tarbar matar gwamna,
sanye take da wani french lace kalar ja da adon
silver a jikinshi. Wardrobe nata ta bud'e, ta fiddo
wani kwalli da turare da wata laya da k'awarta
Luby ta bata.
"Wallahi idan kikayi amfani da kayannan Jidda
kin gama da Faruk, sai yadda kikayi dashi,
sannan ba abinda zai sa a gaba sai ganin ya
mallake ki a matsayin mata, don haka ki
tabbatar kinyi amfani dasu a daren da zai zo.
Sannan wannan kuma a abinci zaki barbad'a
masa ko lemo da zarar yasha yazo hannu!"
Wannan shine maganar da Luby ta fad'a mata a
lokacin da tazo ta kawo mata kayayyakin.
kwallin ta shafa ta fesa turaren, sai wata laya da
akace ta rik'e a hannunta gam kar ta saki har
sai ya tafi. Bayan ta kimtsa wayarta ta fara
ringing, ganin mai kiran yasa ta saki murmushin
mugunta sannan ta d'auka cikin kashe murya
tace
"Hello my dear."
Yace
"Gani nan parlon Dada, da mun gama gaisawa
zan iso main parlor ki jira ni a can."
Tace
"Angama honey."
Kashe wayar yayi ba tare da ya k'ara magana
ba.
Dada ne yake shigowa, bayan ya k'araso ya
zauna nan suka gaisa. Dada yace
"Ya gida ya iyali?"
Yace
"Alhamdulillah."
Dada yace
"Tunda nace ka nemi yardar matarka baka k'ara
zuwa ba ko?"
Yace
"A'a Dada wallahi aiki ne yasa ni a gaba, nayi
magana da ita ay ta yarda ta amince."
Dada yayi murmushi
"To kaga ka sauke nauyi, Allah ya tabbatar da
alheri."
Yace
"Amin Dada, yanzu ma wurin Jiddar nazo mu
fahimci juna."
Yace
"Madallah, babu matsala."
Daga haka ya mik'e ya fice.
A sadda Jidda ta fito Faruk na zaune kan kujerar
zaman mutum biyu yana latsa waya, tun kafin ta
k'arasa ya k'ura mata ido har ta iso yana
kallonta.
Ta dube shi sosai ta zauna kusa da kujerarsa
don ya shak'i k'amshin sosai tace
Sannu da zuwa."
A kasalance ya amsa a take yaji wutar sonta na
ruruwa a ransa kamar ana kunna ashana. Ta
dube shi sai taga ya tsare ta da idanu tace
"Yaya Faruk ina wuni ya gida?"
Ya kad'a kai tare da lumshe idanu, ji yake kamar
ya kamota ya rungume, ita kam sai matsar layar
takeyi tare da wani kad'a jiki tana wani fari da
ido. Ya sake dubanta sai yaga tayi wani kyau ji
yake kamar ba wacce tafita kyau...
Ta katse masa tunani da cewa
"Bari na kawo maka abin motsa baki."
Yace
"A'a da kin barshi ma bana jin yunwa."
Tayi wani fari da ido tace
"Ayi haka? Ay ko ruwa kasha kaida ba bak'o
ba?"
Sai wani kashe murya takeyi. Yayi murmushi
yace
"To kawo min ruwan dai ya isa, amma kar ki
dad'e don ban gaji da kallonki ba."
Tace
"To yanzu zan dawo."
Ta mik'e cike fa yauk'i da yanga ta tafi, shi
kuwa sai binta yake da ido har ta shige kitchen.
Ya lumshe idanu kafin ya bud'e jira kawai yake
yaga ta fito ko zaiji sanyi a ransa....
MSB💖
AUREN FANSA 32
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
*_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_*
P.M.L
Alhamdulillah duk wani masoyina da ya damu
dani nagode sosai Allah ya saka da alkhairi!
Naga sak'konnin gaisuwarku na kuma gode da
kulawa Allah ya bar zumunci ameen. 😘
Haka masu kirana da turo man sak'ko don jin
lafiyata kuma nagode sosai Allah ya bar
zumunci.😘😍
Wannan page d'in naku ne members na AUREN
FANSA FANS, thank you so much for everything!😍🌹
🌹32 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Duka duka batafi minti ashirin ba ta dawo
hannunta d'auke da tray mai d'auke da lemo a
cikin glass cup da aka riga aka zuba, gefe kuma
kwalin lemon 5alive ne. Tafe take tana faman
smiling tana kashe ido, tafiyar ta kuwa kamar
tana tsoron taka k'asa, fuskarta cike da fara'a
da nishad'i kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar
da hakan.
Da isowarta sai ta rissuna a hankali ta ajiye tire
d'in, sannan ta dawo ta zauna a kusa dashi tace
"Ya Faruk ga ruwa kasha."
Kallonta yake bako kyaftawa zuciyarsa tana
ayyana masa abubuwa da dama game da ita.
A hankali ta mik'o masa lemo tace
"Bismillah."
Bai iya mata musu yakeji koda kuwa yaso hakan,
don haka sai ya kar6a ya fara kur6a kad'an
kad'an, kuma a hakan suna ta6a fira.
"Kamar yadda na fad'a ma Dada cewar nazo mu
daidaita kanmu to kema haka zan sanar da ke,
don haka me zakice game da hakan? Duk da
kuwa na dad'e da sanin sirrin da ke ranki shiru
kawai nayi, amma duk da haka ina so naji ta
bakinki, kin shirya aure na ko kuwa?"
A cikin ranta mamaki take yadda tashi d'aya ta
sato zuciyarsa a tafin hannunta! Lallai indai
kuwa hakane komai zaizo mata da sauk'i tunda
har ya kamu da wuri haka. A fili kuwa
murmushi tayi tace
"To yadda za'ayi ka samu Dada da maganar don
maganar tana hannun manya, amma tambayar
amsar ka itace, eh na yarda kuma na shirya
aurenka ya Faruk."
Yayi murmushi
"Kina so na kenan?"
Ta gyad'a kai cike da farin ciki, yayi murmushi
yace
"To ba matsala ay, kuma gaskiya bana son aja
lokaci mai tsawo, in zan samu ne ma nan da sati
biyu yayi min, amma da yake zanyi gyaran inda
zaki zauna ana iya sashi nan da wata d'aya."
Tace
"To duk yadda kace ni yayi min."
Da zai tafi ya fiddo kud'i masu tsoka ya bata,
yace
"Kya sa kati da wannan, sai munyi waya."
Ta kar6a tace
"Nagode."
Sukayi bankwana ta shige d'aki, tana zuwa ta
kira Luby, ta kwashe labarin komai ta fad'a
mata, ta sanar mata ya bata kud'i masu tsoka.
Luby tayi shewa
"Duniya sabuwa, kinga a nan kenan kin harbi
tsuntsu d'aya da igiya biyu."
Jidda tayi dariya tace
"A gaskiya nagode Luby bansan ya zanyi ba idan
baki ba, kin taimaka min sosai."
Luby ta k'yalk'yale da dariya tace
"Somin ta6i ne ay, ya Faruk sai ya raina kansa,
sai ya dawo kamar zai maki sujjada"
Jidda taji dad'i tace
"Nagode 'yar uwa sai munyi magana gobe."
Sukayi sallama ta kwanta rigingine tana tunanin
ranar da zata mallaki Faruk a matsayin mijinta.
Koda ya koma gida bai iske Meenah a parlor ba,
kuma sai yaji bai wani damu ba, d'akinsa ya
wuce kansa tsaye yayi wanka ya kimtsa cikin
kayan bacci ya hau gado ya kwanta, sam ya
kasa bacci sai tunanin Jidda da ya addabe shi,
wayarsa ya d'auko ya kira ta amma har ta
tsinke ba'a d'auka ba, ya sake kira a karo na
biyu nan ma sai da ta kusa tsinkewa ta d'auka.
"Hello ya Faruk..."
Ya lumshe idanu kafin ya bud'e, sannan yaja
ajiyar zuciya yace
"Kar dai har kinyi bacci na tashe ki?"
Tayi murmushi
"Eh na fara sama sama dai, da fatan ka koma
gida lafiya?"
Yace
"Lafiya lau, gani nan ma har nayi shirin bacci."
Ta mik'e da sauri daga kwance da take tace
"La ya Faruk kuma shine ka kira ni? Idan
amaryarka ta farka taga kana waya dani fa?"
Yayi murmushi
"Kar ki damu bazata farka ba, besides tama san
da maganarmu so kar ki damu."
Tayi wani shu'umin murmushi tace
"To shikenan ya Faruk sai da safe."
Ya 6ata rai
"Kar dai har mun gama firar?"
Tace
"Eh."
Yace
"Gashi ban gaji da jin muryarki ba."
Tayi dariya
"La ya Faruk, nima haka, amma bacci nakeji
yanzu.
Yace
"To shikenan sai da safe."
Tace
"Allah ya kaimu love you."
K'itt! Ta kashe bata jira ya bata amsa ba. Ya
sagale wayar a kunnensa ya kasa cirewa. Haka
ya kwanta da tunaninta har garin Allah ya waye.
Kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da tana
cikin matsananciyar damuwa, banda idanunta da
suka rikid'e suka koma ja alamar rashin bacci da
kuma kukan da tayi a daren jiya.
Sanye take da wani navy-blue atamfa d'inkin
riga da skirt sai wani yalolon gyale data gyala a
saman kanta. Kwata kwata yau batada kumari
haka take jinta wani iri tunda ta tashi batada
walwala.
Tsaye take a kitchen tana faman had'a masa
kalaci mai rai da lafiya. Sai da ta kammala
komai ta jera saman dinning sai ta koma ta
kimtsa kitchen d'in.
Tana tsakar yi ne taji alamun tafiya, hakan ya
dakatar da ita gami da fitowa daga kitchen d'in.
Sanye yake da uniform d'in aikinsa wato komai
in black tun daga sama har k'asa, ta k'ara
dubansa a karo na biyu gami da yin murmushi.
Maimakon ya maida mata murtani sai ya fara
k'ok'arin gyara zaman belt d'in wandonsa.
Hakan ba k'aramin k'ona ranta yayi ba gami da
bata mamaki tsantsa.
Ta daure tare da had'iye 6acin ranta ta k'araso
inda yake tsaye tace
"Ina kwana?"
Bai motsa ba ya amsa
"Lafiya."
Ta dai daure tace
"Naga kana shirin fita baka karya ba."
Sai a sannan ya d'ago yana dubanta amma
fuskarsa babu annuri ko kad'an kamar wanda
aka aiko ma da sak'on mutuwa. Yace
"Azumi nakeyi."
Tace
"To... wane iri naga yau ba Monday ba kuma ba
Thursday ba?"
Ya k'ule da tambayarta sai ya kalle ta kad'an
yace
"Dole sai wannan ranakun Allah ya halasta
azumi? Mutum yana iya yi ko yaushe don samun
lada."
Ta k'ak'alo murmushi tace
"Haka ne kam, Allah ya bada lada."
Yace
"Amin, ni zan wuce sai dare zan dawo yau."
Tace
"To a ina zaka sha ruwa?"
Yace
"Zan siya abinci, don yau aikin da ke gabana da
yawa da k'yar zan samu dawowa wannan
lokacin yau."
Tace
"To."
Har yayi hanyar waje sai kuma ya dakata tare
da karkatowa kad'an yace
"Gobe za'a fara gyaran gida, za'a k'ara fasa
d'aki da parlor da kitchen daga can baya."
Bata tanka ba don ta gane inda maganar ta
dosa, shi kuwa gogan daga haka kawai sai yasa
kai ya fice don shi ko ganinta bai son yi yau,
Jidda kawai yake tunani.
Yana fita ta fashe da kuka mai tsanani don ko
maganar auren da ya tarkato bata d'aga mata
hankali irin yau da taga yadda ya chanza mata.
***
Yana office yana shirin fita don an kirasa wai
akwai wani kisa da akayi a wani gida, zasu je
bincike. Yana tsakar tattara mahimman
abubuwan da zai buk'ata aka shigo da sallama.
Ya amsa tare da bada izinin shigowa, sai dai a
yadda ya tsaya yana kallonta cike da mamakin
sauyawar da tayi kamar ba Hajir ba, gaba d'aya
ta zama bak'auya sak!
Sanye take da wani tsanwar atamfa ta k'ok'e
sosai, d'inkin k'auyawa riga da skirt, sai
d'ankwalin daban, fuskarta harda d'ige d'igen
kwalliya. Hakan ba k'aramin dariya ta basa ba.
Sai da yayi mai isarsa sannan ya dakata yana
kallonta yana tafa hannu.
"Bravo! Lallai kinyi k'okari Hajir, aww na manta
Atika ashe. Aikinki yayi kyau, are you ready?"
Tace
"Yes sir."
Yace
"Good, d'auko kayanki inada wani aikin da
zamuje muyi yanzu, amma ina iya kaiki gidana
da zarar na dawo sai mu kaiki gidan da zaki
zauna."
Tace
"Haka ma yayi sir."
Kayanta ta d'auko dake cikin ghana most go
tabi bayansa.
Da sallama suka shiga, tana zaune a parlor tana
karatun wani novel, ganin Faruk ya shigo yasa
ta dakata gami da amsa sallamar tasa. Tare
suka shigo da Hajir, bayan sun zauna Faruk ya
soma magana.
"Meenah wannan 'yar aikin da kika ce a samo
miki ce, sunanta Atika, yanzu ina sauri zan koma
aiki, so zan barta nan sai na dawo sai mu kaita
ko?"
Taji dad'i sosai suka gaisa da Hajir a mutunce
sannan tace masa.
"Ay naji kace yau zakayi dare a wurin aiki, why
not ka bari na kaita da kaina ko ya ka gani?"
Ya mak'e kafad'a alamun oho yace
"Hakane tunda kin iya mota ki d'auki d'aya daga
cikin nawa sai ki kaita, ni zan koma."
Ta masa a dawo lafiya ya fice. Meenah ta kalli
Hajir tace
"Don Allah ki tashi daga k'asa ki koma kan
kujera."
Hajir ta koma kan kujera tana ta faman
murmushi. Meenah tayi murmushi tace
"Ko kefa, bari na k'arasa abincin rana kici sai na
kaiki ko?"
Hajir tace
"To nagode."
Meenah tayi murmushi ta mik'e ta shiga kitchen.
BELLO
‹ › Home
View web version
Monday, 7 August 2017
Maryam Saidu at 08:23
AUREN FANSA 33
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
Kuyi sorry Fans muna fama da matsalar rashin
wuta🤗
🌹33 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Bayan ta kammala abincin suka ci sai ta zarce
zuwa gida don kai ta, Bilki bata zargi komai ba
sai ma murnar samun mai taya ta aiki dama
Zarah keyi to zata fara zuwa makaranta ga
bikinta da za'a sanya.
Nan aka gabatar mata da ayyukan da zata rik'a
yi tun daga su shara, wanki, wanke-wanke, girki
da sauransu.
Kafin ta tafi sai da shiga wurin Baba da ke
zaune parlor yana kallon news, ganin Meenah ta
shigo ya sanya yayi murmushi, ya bita da kallon
k'urilla a lokacin da take zama kan carpet.
"Baba ina wuni?"
Ya gyara zamansa yana kallonta yace
"Lafiya lau Amina, ya gida ya kuma mai gidan
naki?"
Tace
"Duk lafiya lau Baba yana wurin aiki."
Yace
"Madallah, naji zancen zai k'ara aure hakane?"
Ta had'iye miyau mai d'aci tace
"Hakane Baba."
Yace
"Kinsan komai muk'addari ne daga Allah Amina,
kar ki d'aga hankalinki ki jure, ki zamo mace mai
hak'uri da biyayya kinji? Allah ya za6a maku
mafi alkhairi, ya bada zaman lafiya."
Tace
"Amin Baba nagode, daman zan wuce gida
yanzu."
Yace
"To ki gaida mijin naki, da fatan baki buk'atar
wani abu?"
Tace
"A'a Baba."
Yace
"Kuma zaku tafi jami'ah, ku kula sosai, karatu
kukaje yi shi zakuyi Allah ya taimaka."
Tace
"Insha Allah Baba, amin."
Sukayi sallama ta tafi gida.
K'arfe goma saura ya shigo gidan, tana zaune
tana karatun alk'ur'ani, daga bakin k'ofa yaja ya
tsaya yana sauraron muryarta tana karanta
suratul Mujadala, yayi tsaye shi bai shigo ba
haka ma shi bai fita ba, take kuma ya tsinci
kansa cikin nutsuwa don karatun yana masa
dad'i.
Sai data kai aya sannan ya shigo, ganinshi ya
sanya tayi saurin mik'ewa ta isa garesa gami da
amsar brief case d'insa, tayi murmushin da bai
kai zuci ba tace
"Sannu da zuwa."
"Yawwa." Kawai yace ya wuce zuwa ciki, ranta
ya sosu ta dai daure ta bishi ciki a lokacin data
shiga taji alamun watsa ruwa. Sai kawai ta fito
ta zauna parlor tana kallo abinta.
Shiru bai fito ba har kusan sha d'aya ta wuce,
ga ita kuma tana kunyar binshi d'aki yanzu kada
ya fassara ta, sai kawai ta mik'e ta tattara
abincin tasa fridge ta wuce d'akinta.
Gaba d'aya ta kasa bacci sai uban tunani, ko a
mafarki akace mata Faruk zai mata haka bazata
yarda ba. Ganin hakan bashi ne mafita ba ya
zama tilas ta kai kukanta ga Allah don shine zai
share mata, toilet ta fad'a ta d'auro alwalla ta
fara sallah tana kai kukanta ga Allah.
Tana wurin har akayi sallar asuba, hakan yasa
tana gama sallah kanta ya fara yi mata
barazanar ciwo, ta lalla6a ta kwanta ba'a d'au
lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita.
Cikin baccin ne taji kamar ana ta 6arar da
abubuwa, a gigice ta farka tana salati, duba
lokaci tayi k'arfe 11:41am lallai tasha bacci.
Hijabinta ta d'auko ta sauko daga gadon, tana
lek'owa taga mutane maza suna ta aiki a gidan,
gabanta ya yanke ya fad'i, maganar Faruk ta
dawo mata a cikin kanta.
"Gobe za'a fara gyaran gida, za'a k'ara fasa
d'aki da parlor da kitchen daga can baya."
Dafe kanta tayi da ke juya mata sannan ta fara
bin bango ji take kamar zuciyarta zata fad'o
k'asa.
Note ta gani a bisa drawer d'inta hannunta na
kyarma ta d'auko ta warware ta ta soma
karantawa...
"Na tafi office, kamar jiya yau ma azumi nakeyi
kar ki wahalar da kanki yin wani girki sai dare
zan dawo, idan masu aikin nan sun gama da na
yau ki shiga d'akina ki d'auko 5k ki basu zan
kirasu na masu bayani."
Wani k'ululun bak'in ciki ne ya tokare mata
mak'oshi, ta daure tayi ta maza ta maida note
d'in ta ajiye a inda ta d'auka, ta rasa dalilinsa
na shan ruwa a waje, at least ko bai dawo da
wuri ba ay ya kamata ya ci abincin data girka
masa komai dare, amma ta lura kamar baya son
cin abincin ne gaba d'aya a nan.
Da k'yar ta sha ruwan tea ta koma d'aki ta
kwanta, k'arar aikin gidan ne ya ishe ta shi
yasanya ta kasa baccin kirki.
Allah ya taimake ta Zarah tazo zasuje
makaranta registration, tayi ta murna ta kirasa
don shaida masa amma bai d'aga ba sai kawai
ta aika masa da sak'o.
Cikin sa'a kuwa suka kammala komai suka
dawo gida, Zarah tsabar haushin gyaran inda
kishiyar yayarta zata zauna yasa ko gidan bata
iya shiga, daga waje sukayi bankwana ta tafi
gida.
Yanda ya umarce ta hakan tayi don kuwa k'arfe
shiddan yamma suka gama, ta shiga ta d'auko
masu kud'in ta basu suka tafi.
Haka kullum sai sun zo da safe su gama k'arfe
shidda, da yake ana sakin kud'i sai gashi ginin
har ya mik'a sosai.
A zamantakewar auren Meenah kuwa babu
abinda ya chanza gaba d'aya Faruk ya chanza
mata kamar bashi ba, bai damu da ita ba bare
cinta, shanta da kuma lafiyarta.
Abincinta ma baya ci ko tayi masa, tun yana
bata excuse har ya fara fitowa 6aro 6aro yana
ce mata bazai ci ba. Ga abu kad'an fad'a da
masifa, nan da nan sai ya hau fad'a ba dalili.
Nan kuwa yana can ya tare wurin Jidda, wani
lokacin can yake da anyi sallar isha'i har goman
dare. Kuma komai ta bashi ci yakeyi, gaba d'aya
ya sussuce ya rikice.
Hakan yasa aka sanya bikin sati uku masu
zuwa, don ya kusa kammala aikin gidansa saura
kad'an ya rage, haka aka tattara aka sanya bikin
aka had'a dana su Zarah da Nabeel.
Shi kuma ya cigaba da had'a lefe da kuma
akwati biyu na kayan fad'ar kishiya da zai kai
ma Meenah.
AUREN FANSA 34
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
🌹34 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Meenah kuwa duk wani abu bazata fasa yi masa
ba, har girki sai tayi koda kuwa bazaici ba, ga
tana k'ok'ari wajen ganin ta kai zuciyarta nesa
don gudun fitina, sauk'inta ma yanzu shiryen-
shiryen bikin Zarah ya fara kankama hakan yasa
ta rage yawan shiga damuwa, don kuwa tana
gida kuma bata cika dawowa ba sai yamma.
Karo na farko da ta fara shiga gidan Aneesha
tunda sukayi aure, bayan ta shirya cikin green
d'in material d'inkin doguwar riga sai ta gyala
gyale marar kauri sosai. Da sallama da shiga
gidan, Aneesah na kitchen tana fama da girki taji
sallama ta lek'o, murmushi tayi tace
"Bismillah shigo."
Bayan ta zauna Aneesah ta shiga kawo mata
lemo da kayan motsa baki, yau duk kunya ta
kama Aneesah ganin itace k'arama kuma ko sau
d'aya bata shiga gidan ba. Meenah tayi
murmushi tace
"Baki gane ni ba ko?"
Aneesah tace
"Nagane ki mana, matar ya Faruk ce nasanki."
Meenah tace
"Allah sarki ya gida?"
Tace
"Lafiya lau."
Shiru ya biyo ba, na 'yan mintina sai suka kafa
ma tv ido ana wani film. Meenah ta katse shirun
ta hanyar mik'a mata kati
"Daman Iv na kawo maki na bikin sister d'ina."
Aneesah tayi murmushi tace
"Allah sarki, Allah yasa alkhairi yasa munada
rabon gani."
Tace
"Amin ni zan koma."
Aneesah tace
"Haba tun yanzu? Na d'auka sai kin ci abinci
tukunna."
Meenah tace
"Kai haba, bamuda nisa ta yaya zan cinye ma
amarya girkin angonta?"
Aneesah tayi murmushi cike da kunya tace
"Kai a'a wallahi ba haka bane."
Meenah tayi dariya tace
"Kedai wasa nake miki, idan na dawo next time
zanci insha Allah."
Aneesah tace
"To ina zuwa."
Ta mik'e ta shiga ciki, can ta dawo hannunta
d'auke da leda tana murmushi tace
"To ga wannan."
Meenah tace
"La harda wahala haka?"
Aneesah tace
"Ba wata wahala wallahi."
Meenah tace
"To nagode ni zan tafi."
Aneesah tace
"Nima zan shigo, ay kina WhatsApp ko?"
Tace
"Eh inayi."
Aneesah tace
"Zamu rik'a gaisawa insha Allah, nagode sosai
wallahi."
Meenahtace
"Babu komai wallahi."
Sukayi bankwana ta tafi, tunda Meenah ta tafi
Aneesah ke raya kyawunta da kirkinta, sai taji
haushin kanta da meyasa bata ta6a shiga sun
gaisa ba, amma ta k'udiri a ranta zasu fara
zumunci daga yau.
****
Meenah sun soma lectures, yanzu damuwarta ta
ragu sosai, kuma tayi sa'a yana bata mota idan
zata tafi.
Ranar litinin da daddare sai ga Faruk ya shigo
da akwatina guda biyu, tunda Meenah ta ganshi
tasan na menene, don haka bata nuna
damuwarta ba ko kad'an, sai ma fatan alkhairi
da tayi masa.
Hakan ba k'aramin mamaki ta basa ba, kuma
sai ta bashi tausayi, nan ta bubbud'e akwatina
ta gani bayan ta gama ta tashi ta shiga ciki. Ya
dad'e zaune ranar farko da ya ji auren ya fita a
ranshi kuma.
Mik'ewa yayi cikin sanyin jiki ya bita ciki, tana
kwance a d'aki tayi ruf da ciki idanunta a
lumshe, hakan ya k'ara bayyanar da zara zaran
eye lashes nata. Ya dad'e tsaye yana kallonta
kafin ya tako a hankali yatsaya yana k'are mata
kallo. Sanye take da 'yar k'aramar vest pink
color sai tasa pink dogon wando, harta ribbon
d'in kanta pink ne, daga gani ba bacci take ba
amma kuma tak'i bud'e idanunta.
"Meenah..."
Ta bud'e idanunta a hankali ta sauke bisa
fuskarsa da yake kallonta kafin ta amsa da
"Na'am."
Sai kuma ya rasa abin cewa, ya sosa kai yace
"Dama zuwa nayi naji ko kina lafiya."
A ranta tace
"Sabon salo sai kace damuwa yayi da ni bare
kuma lafiyata."
A fili kuwa cewa tayi
"Lafiya lau."
Shi yadda take sharesa d'innan yaji ba dad'i,
yayi missing kula da shi da takeyi, amma yanzu
ko kallonsa bata son yi, magana ma da k'yar
take amsa masa. Da yanzu ta tambeyesa ko
yana buk'atar wani abu, amma yanzu ta daina.
"Ko kana buk'atar wani abu ne?"
Yayi sauri yace
"A'a, sai da safe."
Tace
"Allah ya kaimu."
Ta rufe idanunta alamun bacci, ya dad'e tsaye
yana kallonta kafin ya fita daga d'akin a
sanyaye.
Yana shiga d'akinsa ya iske miss calls ba iyaka
daga Jidda, kiranta yayi bugu d'aya ta d'auka.
"Haba my dear ina ka shiga inata kiranka?"
Yace
"Sorry na shiga wanka ne."
Yace
"Ok daman kud'in da zan siya anko ne na 'yan
mata baka bada ba..."
Yace
"Kud'in anko kuma?"
Tace
"Eh da kud'in k'unshi."
Yace
"To fah har nawa?"
Tace
"Gaba d'aya dubu 500 ne!"
Yace
"What? Dubu 500? Gaskiyar magana ko banida
su, bazan iya baki dubu 500 ba."
Tace
"Haba mana my dear, wai nan fa na maka
sauk'i."
Yace
"Dubu 100 zan baki, idan baki so good and fine."
Tace
"Wai wannan fad'an na menene daga
tambayarka kud'i?"
Yace
"Jiya jiya kika tambayeni dubu 200 na baki,
shekaranjiya dubi 50, yanzu kuma dubu 500, to
banida su."
"Don Allah kayi hak'uri ka bani, daga yau bazan
k'ara tambayarka wasu kud'in ba."
A fusace yace
"Ke kar ki raina min hankali fa! Na riga nace
bazan baki ba, don haka sai da safe."
K'it ya kashe wayar, cike da jin haushinta, gaba
d'aya haushinta yakeji. Yau ko baccin kirki ya
kasa, haka yasa ya mik'e ya lek'a d'akin
Meenah tana kwance tana bacci peacefully, ta
masa kyau sosai, sai dai dole ya koma d'akinsa
ya kwanta amma ina ya kasa bacci, sai gabansa
dake ta fad'uwa ya rasa dalili.
Washe gari sai ga 'yan jere, nan sukayi ta
hidimarsu ita kuma Meenah ko fitowa ma batayi
ba, tana d'aki tana jinsu suna ta aikin jerensu,
har dare suna nan basu gama ba, har washe
gari sai da suka dawo da safe suka k'arasa
wanda basu idasa ba.
Itama Meenah jeren Zarah suka tafi the next day,
hakan ba k'aramin dad'i yayi mata ba.
Biki nata matsowa yau saura kwana biyu a
d'aura aure....
AUREN FANSA 35
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
🌹35 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Washe gari aka kai lefen Zarah akwati bakwai da
kit, yayinda aka kai ma Jidda akwati takwas da
kit.
An fara gudanar da shagalin biki a wadace, sai
dai matsalar Jidda d'aya da ta masa maganar
kud'i sai sunyi fad'a, sannan idan har suna tare
yana nuna mata so da k'auna marar iyaka
amma da zarar sun rabu shikenan ko kiranta
baiyi sai dai ita ta kirasa. Hankalinta ya fara
tashi haka kuma ta soma tunanin ko maganin ya
fara dena aiki ne?
Ranar da akeyin event d'in Jidda anyi kwalliya ta
gogaggun 'yan matan nan, ta had'u har ta gaji
duk da ba wani kyau gareta na azo a gani ba.
'Yan matanta kansu da ka kallesu kaga
gagaggun 'yan mata masu ji da kansu, Luby best
friend d'in amarya ita nata ashobin ya banbanta
da na sauran ya kuma fi tsada da kyau.
Suma kuwa su Zarah na can suna shan tasu
hidimar, da yake bazasuyi abubuwa da yawa ba,
kuma bikin nasu yafi tsari da kyau.
K'arfe biyar da rabi Faruk ya iso ya kira wayar
Jidda, can sai ga ta fito itada k'awayenta su da
yawa kamar wata tawaga.
Bayan sun iso aka fara gabatar da events cike
da kwanciyar hankalin, Luby ita ta fara bud'e
wurin da rawa yadda kasan ba kowa wurin haka
take tik'ar rawa ba ko kunya.
An gayyato amarya da ango don taka rawa, shi
kam ango kunya ta hana shi rawa sosai ba, ita
kuwa amarya bako kunya sai wani rausaya
takeyi kamar ba amarya ba. Faruk sai yanzu
yake k'ara gane halin Jidda, bai ta6a tunanin
haka take ba. Sai yanzu ya fara tunanin aurensu
shida Meenah komai cikin tsari haka akayi shi.
K'arfe sha d'aya aka tashi taron, ya ajiye Jidda
gida shima ya nufi nasa gidan.
Washe gari ya tashi yana ta hidimar d'aurin
aure. K'arfe biyu daidai dubban mutane suka
shaida auren Jidda da Faruk sai Zarah da
Khaleel.
Dad'i Meenah takeji Zarah kusa da su za'a kawo
ta, bayan an gama aka zarce 'yar walima da
Faruk ya had'a masu.
****
Tana zaune kan gado taji ana maganar an
d'aura aure, haba kanta ya k'ara girma ji take
kamar a mafarki, mutumin da take ganin shine
class d'inta yau ta malleke shi a matsayin miji,
wani murmushi tayi tare da lumshe idanu, Luby
ta daka mata duka a baya tace
"Banza keda wa kike murmushi ke kad'ai?"
Ta dube ta tace
"Ina tunani gami da yin mamaki wai yau nice na
zama matar ya Faruk ya zama mallakina fa
kenan?"
Luby tace
"Ke ni ba wannan ba, kinsan mutumin nan yana
da mata, kuma kinsan yadda yake k'aunar ta
kawai suddabarunki ne yake aiki, baki gudun
maganin ya bar aiki mu shiga uku mu lalace? Ke
nifa na fara ji miki tsoro kar ya wulak'anta ki,
sannan yasan babu, baki gudun labari yasha
banbam?"
Ras ras! Gabanta ya yanke ya fad'i tace
"Haka ne fa, ko da yake ay kin min tanadi mai
kyau kar kiji komai."
Luby tace
"Keni sheyasa nake son auren yaro wanda
baisan dawon garin ba, amma masu mata ay
sun san komai."
Haka aka cigaba da shagalin biki, jikin Jidda yayi
mugun sanyi saboda gudun abinda zaije ya
dawo tsakaninta da angonta.
K'arfe tara da rabi motoci suka soma layi a
k'ofar gidan su amarya, bayan fad'a da nasihohi
daga Mama da Dada har Faruk sai da yasha
fad'a sosai da nasiha.
Uwar gida kan gida Meenah tana zaune a
d'akinta ta ci ado tsayawa fad'ar kwalliyarta ma
6ata baki ne. Gud'a ta matan da suka rako
amarya itace ta fara yo sallama, Meenah ta
danne kishinta sosai ta k'ak'alo murmushin dole,
amarya tana rik'e a hannun wata mata.
Kansu tsaye d'akin amarya suka nufa, 'yan kawo
amarya, k'ofa ce kawai zatayi linking d'inka
zuwa d'ayan 6angaren na sashen Jidda.
Masu kawo amarya suka shiga zagaye gidan don
kashe kwarkwartar ido. Suka gama kallon komai
sukayi niyyar tafiya gida.
Washe gari akayi walima k'arfe biyar na yamma
Hajiya Lami ta rik'o hannun Jidda ta nufi parlon
Meenah, sukayi sallama Meenah ta amsa. Hajiya
Lami ta ce
"To ga amarya nan don Allah ku had'a kanku ku
zauna lafiya, yanzu an bar haukan kishin nan
zaman lafiya shi kowa ke buk'ata.
Tayi murmushi
"To Allah ya taya mu rik'o."
Suka tashi suka maida amarya d'akinta bayan
iyayen sun kama gabansu, d'akin ya rage daga
amarya sai 'yan matanta wad'anda ke zaman
jiran ango.
Luby tace
"Kar fa kiganta kamar mutuniyar kirki ki raga
mata, idan tace miki kul ki ce mata cas cas!
Kinji na fad'a miki."
Nan sukayi ta zuga ta har akayi isha'i.
K'arfe takwas, tara, goma, shiru ba ango ba
alamunshi, har dai sha d'aya ta wuce
Luby tace
"Nidai zan tafi gida na gaji da jiran ango."
Haka suka tarkata suka tafi, Sai dai ta dinga
binsu da ido don batada bakin magana da kuma
tana son jin dalilin rashin zuwan ango duk da
tanadin da tayi masa, haushi kamar zai kashe
ta.
"Kar dai yana wurin waccan tsinanniyar?"
Gabanta ya fad'i, ta hau sak'e sak'e, tayi ta
kiransa yana rejecting, daga k'arshe ya tura
mata sak'o kamar haka:
"Kiyi hak'uri ki bar kirana yau bazan shigo
wurinki ba."
Ta rud'e ta gigice gashi maganin idan aka wuce
yau shikenan ya kare!
Ta hau salati tana cigaba da kiransa amma ina
sai ma ta kira taji ta a kashe.
Safa da marwa takeyi daga k'ofa zuwa gado,
tana tunainin mafita a gareta, don akwai had'ari
muddin ango baizo gareta ba a daren yau ba!
AUREN FANSA 36
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
🌹35 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Washe gari aka kai lefen Zarah akwati bakwai da
kit, yayinda aka kai ma Jidda akwati takwas da
kit.
An fara gudanar da shagalin biki a wadace, sai
dai matsalar Jidda d'aya da ta masa maganar
kud'i sai sunyi fad'a, sannan idan har suna tare
yana nuna mata so da k'auna marar iyaka
amma da zarar sun rabu shikenan ko kiranta
baiyi sai dai ita ta kirasa. Hankalinta ya fara
tashi haka kuma ta soma tunanin ko maganin ya
fara dena aiki ne?
Ranar da akeyin event d'in Jidda anyi kwalliya ta
gogaggun 'yan matan nan, ta had'u har ta gaji
duk da ba wani kyau gareta na azo a gani ba.
'Yan matanta kansu da ka kallesu kaga
gagaggun 'yan mata masu ji da kansu, Luby best
friend d'in amarya ita nata ashobin ya banbanta
da na sauran ya kuma fi tsada da kyau.
Suma kuwa su Zarah na can suna shan tasu
hidimar, da yake bazasuyi abubuwa da yawa ba,
kuma bikin nasu yafi tsari da kyau.
K'arfe biyar da rabi Faruk ya iso ya kira wayar
Jidda, can sai ga ta fito itada k'awayenta su da
yawa kamar wata tawaga.
Bayan sun iso aka fara gabatar da events cike
da kwanciyar hankalin, Luby ita ta fara bud'e
wurin da rawa yadda kasan ba kowa wurin haka
take tik'ar rawa ba ko kunya.
An gayyato amarya da ango don taka rawa, shi
kam ango kunya ta hana shi rawa sosai ba, ita
kuwa amarya bako kunya sai wani rausaya
takeyi kamar ba amarya ba. Faruk sai yanzu
yake k'ara gane halin Jidda, bai ta6a tunanin
haka take ba. Sai yanzu ya fara tunanin aurensu
shida Meenah komai cikin tsari haka akayi shi.
K'arfe sha d'aya aka tashi taron, ya ajiye Jidda
gida shima ya nufi nasa gidan.
Washe gari ya tashi yana ta hidimar d'aurin
aure. K'arfe biyu daidai dubban mutane suka
shaida auren Jidda da Faruk sai Zarah da
Khaleel.
Dad'i Meenah takeji Zarah kusa da su za'a kawo
ta, bayan an gama aka zarce 'yar walima da
Faruk ya had'a masu.
****
Tana zaune kan gado taji ana maganar an
d'aura aure, haba kanta ya k'ara girma ji take
kamar a mafarki, mutumin da take ganin shine
class d'inta yau ta malleke shi a matsayin miji,
wani murmushi tayi tare da lumshe idanu, Luby
ta daka mata duka a baya tace
"Banza keda wa kike murmushi ke kad'ai?"
Ta dube ta tace
"Ina tunani gami da yin mamaki wai yau nice na
zama matar ya Faruk ya zama mallakina fa
kenan?"
Luby tace
"Ke ni ba wannan ba, kinsan mutumin nan yana
da mata, kuma kinsan yadda yake k'aunar ta
kawai suddabarunki ne yake aiki, baki gudun
maganin ya bar aiki mu shiga uku mu lalace? Ke
nifa na fara ji miki tsoro kar ya wulak'anta ki,
sannan yasan babu, baki gudun labari yasha
banbam?"
Ras ras! Gabanta ya yanke ya fad'i tace
"Haka ne fa, ko da yake ay kin min tanadi mai
kyau kar kiji komai."
Luby tace
"Keni sheyasa nake son auren yaro wanda
baisan dawon garin ba, amma masu mata ay
sun san komai."
Haka aka cigaba da shagalin biki, jikin Jidda yayi
mugun sanyi saboda gudun abinda zaije ya
dawo tsakaninta da angonta.
K'arfe tara da rabi motoci suka soma layi a
k'ofar gidan su amarya, bayan fad'a da nasihohi
daga Mama da Dada har Faruk sai da yasha
fad'a sosai da nasiha.
Uwar gida kan gida Meenah tana zaune a
d'akinta ta ci ado tsayawa fad'ar kwalliyarta ma
6ata baki ne. Gud'a ta matan da suka rako
amarya itace ta fara yo sallama, Meenah ta
danne kishinta sosai ta k'ak'alo murmushin dole,
amarya tana rik'e a hannun wata mata.
Kansu tsaye d'akin amarya suka nufa, 'yan kawo
amarya, k'ofa ce kawai zatayi linking d'inka
zuwa d'ayan 6angaren na sashen Jidda.
Masu kawo amarya suka shiga zagaye gidan don
kashe kwarkwartar ido. Suka gama kallon komai
sukayi niyyar tafiya gida.
Washe gari akayi walima k'arfe biyar na yamma
Hajiya Lami ta rik'o hannun Jidda ta nufi parlon
Meenah, sukayi sallama Meenah ta amsa. Hajiya
Lami ta ce
"To ga amarya nan don Allah ku had'a kanku ku
zauna lafiya, yanzu an bar haukan kishin nan
zaman lafiya shi kowa ke buk'ata.
Tayi murmushi
"To Allah ya taya mu rik'o."
Suka tashi suka maida amarya d'akinta bayan
iyayen sun kama gabansu, d'akin ya rage daga
amarya sai 'yan matanta wad'anda ke zaman
jiran ango.
Luby tace
"Kar fa kiganta kamar mutuniyar kirki ki raga
mata, idan tace miki kul ki ce mata cas cas!
Kinji na fad'a miki."
Nan sukayi ta zuga ta har akayi isha'i.
K'arfe takwas, tara, goma, shiru ba ango ba
alamunshi, har dai sha d'aya ta wuce
Luby tace
"Nidai zan tafi gida na gaji da jiran ango."
Haka suka tarkata suka tafi, Sai dai ta dinga
binsu da ido don batada bakin magana da kuma
tana son jin dalilin rashin zuwan ango duk da
tanadin da tayi masa, haushi kamar zai kashe
ta.
"Kar dai yana wurin waccan tsinanniyar?"
Gabanta ya fad'i, ta hau sak'e sak'e, tayi ta
kiransa yana rejecting, daga k'arshe ya tura
mata sak'o kamar haka:
"Kiyi hak'uri ki bar kirana yau bazan shigo
wurinki ba."
Ta rud'e ta gigice gashi maganin idan aka wuce
yau shikenan ya kare!
Ta hau salati tana cigaba da kiransa amma ina
sai ma ta kira taji ta a kashe.
Safa da marwa takeyi daga k'ofa zuwa gado,
tana tunainin mafita a gareta, don akwai had'ari
muddin ango baizo gareta ba a daren yau ba!
Maryam Saidu at 06:16
AUREN FANSA 37
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
🌹37 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
A zuciye ta shige ko gabanta bata gani sosai,
tana shiga suka d'ago suka dube ta sai sukayi
ido hud'u da Faruk, wani tsananta ya sake dira a
zuciyansa ga wani zafi yana ji a k'irjinsa, yanzu
a yadda yakeji baya jin son wata 'ya mace a
duniya in ba Meenah ba, ya kalli inda Jiddar ke
tsaye da rik'ak'en k'ugu tana kad'a jiki kamar
wata mazari. Wayancewa yayi ya jefo mata
tambayar rainin hankali
"Jidda ya gida?"
Ta yamutsa fuska gami da yin fari da ido tace
"Lafiya."
Yayi murmushi kad'an yace
"Kina son wani abu ne? As you can see I am
busy here."
Tambayar ta bata haushi sosai ta kuma 6ata
mata rai ainun, ta dube shi tace
"Inada buk'atarka ko ka manta matsayinka
gareni?"
Yace
"A'a ina sane, kije zanzo muyi maganar."
Ta cika tayi fam tace
"Babu inda zanje, wai shin ya Faruk wane irin
aure mukayi? Na k'iyayya ko na soyayya?"
Yace
"Bafa haka bane, nace ki dai je zanzo, idan kuma
kina da buk'atar wani abu ki fad'a min."
Tayi shiru tana tunani, ta dubi Meenah da ke
tsaye kamar abin bai dame ta ba, sai tayi
mamakinta sosai, ta d'auka Meenah macece mai
sauk'in kai har ma tayi tunanin zatasa baki a
cikin maganar ko don ta taimaka mata, to me
hakan ke nufi?
Kawai sai Jidda ta fita da gudu daga d'akin tana
dana sanin zuwan da tayi da kuma zubar da
class d'inta da take da shi a gaban kishiya da
kuma mijin da bai damu da ita ba. Sai dai ta
k'udiri gana ma Meenah wuta, har sai ta gane
matsayinta a gidan, a shirye take don ganin
hakan ta faru kuma sai ta fi kowa farin cikin
ganin hawayenta!
Washe gari da safe Meenah na kitchen tana
had'a kalacin safe Jidda na la6e tana jiran ta
gama don ta san abinda ta shirya mata!
Sai da Meenah ta kammala abincinta soyen
dankali ne da sauce d'in k'wai, ta zuba ma
Faruk nasa a plate da na kowa sai ta koma
d'akinsa don sanar masa ya fito ya ci abinci.
Tana ganin ta shige sai ta fito cikin sand'a ta
bud'e abincin Faruk ta zazzaga ma sauce d'in
uban yaji sannan ta zazzaga ma dankalin gishiri
mai yawa. Tafiya taji ya sanya ta koma d'akinta
a guje tana dariyar mugunta don yau zatayi
kallon fad'an da Faruk zaiyi ma Meenah. Sai
murna takeyi.
Meenah ta shigo d'akinta ta kalle ta tace
"Ki fito kici abinci ko."
Tayi 'yar dariya tace
"Yanzu kuwa."
Da d'an tsalle tsalle ta fito daga d'akin sannan
kuma ta nutsu tabi bayan Meenah.
Kowa ya nutsu kan dinning zasu fara cin abinci,
Faruk ne zai fara cin abinci har ya fara d'ebo
dankalin kawai kwatsam Meenah ta lura da
d'igen d'igen yaji a gefen plate d'insa sannan ga
abincin ya chanza kala ya zama jawur, take ta
fara tunanin yadda akayi hakan ta faru, sai ta
kai dubanta ga Jidda yanayinta kad'ai ya isa ya
tabbatar ba wanda ya aikatan hakan sai ita.
Cikin dabara ta kwa6ar da lemon da ke cikin cup
a gaban faruk, hakan ya dakatar da shi daga cin
abincin da zaiyi wanda saura k'iris ya kai
bakinsa.
"Subhanalillah garin yaya hakan ta faru?"
Meenah ta mik'e da sauri tana cewa
"Kayi hak'uri wallahi ban lura ba, bari na goge."
Cikin dabara ta janye abincin Faruk ta matsar
kusa da abincin Jidda ta shiga kitchen ta d'auko
tsumma ta soma gogewa, ta faki idon Jidda ta
sauya abincin dana Faruk sai ta tura na Jidda a
gaban Faruk da sauri.
Bayan ta gama ta dawo ta zauna tace
"Sorry please, kaci abincin mana."
Yace
"Ay da kin bari sai da aka gama kika goge."
Tace
"Hakan yayi ay kaga yanzu sai aci abincin cikin
kwanciyar hankali."
Ya d'ebi abincin ya kai bakinsa, Jidda nata
kallonsa tana dariyar mugunta sai dai me? Bata
ga komai ba sa6anin abinda tayi tsammani, ta
shiga rud'ani, ta kalli plate d'inta sai taga na
Faruk ne aka chanza mata, ta kai dubanta ga
Meenah taga tana mata kallon irin ya kika ga
nayi k'ok'ari ko?
Meenah ta k'ura mata ido tana murmushi, Faruk
ya d'ago ya dubi Jidda yace
"Ya naga bakya cin abincin ne? Kici mana yayi
dad'i."
Meenah tayi murmushin mugunta tace
"Eh kici abinci Jidda, yayi dad'i sosai."
Ta fad'i haka har yanzu bata bar murmushin ba,
ba yadda ta iya haka ta d'ebo ta kai spoon a
bakinta, take taji wani irin yaji da gishiri ya
had'an mata, ta dinga taunawa da k'yar tana
hawaye tana gogewa don kar a gane.
Faruk ya kammala cin abincinsa ya mik'e yana
fad'in
"Zan tafi aiki, sai na dawo."
Meenah tayi murmushi tace
"Sai ka dawo, amma bari na gyara maka zaman
rigarka."
Yayi murmushi yace
"To."
Ta gyara masa sannan ta fita raka sa bakin
mota, suna fita Jidda tayi toilet da gudu tana
faman tari da kakarin amai, sai da ta d'auki
lokaci mai tsawo tana wanke bakinta sannan ta
fito tana faman goge bakinta da har yanzu bai
bar mata yaji ba.
Kaci6us tayi da Meenah a bakin k'ofa ta hard'e
hannayenta duka biyun tana murmushi. Ganinta
yasa ta d'an dafa ta tace
"Meyafaru?"
Jidda ta kwa6e mata hannu cike da masifa tace
"Muguwa! Azzaluma kawai."
Dariya ta su6uce mata tace
"Muguntar me nayi? Sannan kuma zalunci me
nayi?"
Jidda ta dalla mata harara sannan tace
"Wallahi kin bani mamaki Meenah, nayi tunanin
ke macece mai sauk'in kai ashe ba haka bane?
Ashe haka kike?"
Meenah ta dawo tana fuskantarta ido cikin ido
da hannayenta a hard'e sannan tace
"K'warai ina da sauk'in kai idan aka bini ta
sauk'in kai, sannan kuma ina da wuyar sha'ani
idan aka bini bata lalama ba, Jidda kar kiyi
tunanin kina ganina kamar bansan abinda nakeyi
ba, to da hankalina sannan kallonki nake tar!
Nasan ke wacece sannan nasan wane irin zama
ya kawo ki, a dah nayi niyyar muyi zaman lafiya
dake, amma tunda na gano sirrinki da kuma
k'udirinki na son rabani da Faruk na sake taku.
Wallahi baki isa ba, kinyi kad'an kice zaki rabani
da Faruk, nasani ta yadda kika k'waci
soyayyarsa ta k'arfi da kuma ta magani, anma
kisani duk abinda aka d'ora shi ba bisa tirba ta
gaskiya ba to labari ne."
Jidda ta daka mata tsawa
"Ke Meenah! Yafa isheki haka, shiru shiru fa ba
tsoro bane gudun magana ne, kar ki nemi ki
fad'a min magana yadda kikeso fa."
Meenah tace
"Ni ba fad'a zanyi da ke ba, amma kisani zan
fad'a zan kuma k'ara fad'a ke baki isa ki rabani
da Faruk ba, saboda yana yi min true love ne
babu boka babu malami, soyayyarmu had'in
Allah ce, kuma banga ta yadda zaki raba abinda
Allah ya had'a ba, duk naji conversation d'inku
keda k'awarki sannan a shirye nake nayi fighting
back don ganin baki rabani da Faruk ba."
Jidda tace
"Haka kika ce?"
Meenah tace
"Haka nace."
Jidda tace
"Shikenan mu zuba, niko bama Faruk ba har
gidannan sai na raba ki dashi, ta yadda idan kika
fita har abada bazaki dawo ba."
Meenah tace
"In kin dama ki rabani da duniyar nan gaba
d'aya bama gidan ba, sannan kisani babu abinda
kika isa kiyi min sai abinda Allah yayi min,
sannan ina so ki sani k'arya fure take bata
'ya'ya!"
Jidda tace
"Zaki gani."
Meenah tace
"Zanga alkhairi."
Daga haka ta sa kai ta fice zuwa d'akinta, inda
ta bar Jidda tsaye kamar gunki in banda cizon
yatsa babu abinda takeyi, gaba d'aya idanunta
sun sauya daga fari zuwa ja, cikin sanyin jiki ta
koma d'akinta tana mai mamakin Meenah da
kuma maganganun data fad'a mata a yau.
BELLO
‹ › Home
View web version
Saturday, 26 August 2017
Maryam Saidu at 06:17
AUREN FANSA 38
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
🌹38 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Daddare bayan sallar maghrib Faruk ya kirawo
su a babban parlor yana son magana dasu.
Bayan sun iso ya fara magana kamar haka.
"Abinda yasa na tara ku a nan shine, na farko
ina so ku sani shi aure ba abin wasa bane,
sannan ban k'ara aurennan da wata manufa ba
sai alkhairi, kamar yadda kuka sani ana yi wa ko
mace kwana biyu ko uku, don haka na ware
kwanaki biyu zan rik'a yi wa ko wacenku, ranar
girkinki ya zagayo zaki kar6i girki, saboda
Meenah ba baiwa bace da zata rik'ayi maki girki
sai dai kici. Sannan banison raba abinci, idan
girkin d'aya ne to zata dafa ma duka gidan
abinci, da fatan kun fahimta?"
Meenah tace
"Mun fahimta."
Yace
"Yauwa daman shine maganar."
Jidda ta k'ule meye na ci mata mutunci a gaban
Meenah?
***
Da safe Faruk na d'aki yana shirinsa zai fita aiki
Jidda ta shigo sai faman zum6uren baki takeyi,
ya kalle ta ya kawar da kansa tare da cigaba da
abinda yakeyi, ta matso kusa dashi tace
"Ya Faruk ina son magana da kai."
Ba tare da ya kalleta ba yace
"Ina jinki."
Kai tsaye tace
"Mota nakeso ka siya min."
Ya dakata daga abinda yakeyi ya juyo yana
kallonta cike da mamaki yace
"Mota fa kika ce? Anya kina da hankali kuwa?"
Tace
"Da hankalina ai itama d'ayar matar taka tana
hawa mota, ni bana hawa, don haka ance kayi
adalci a tsakaninmu nima sai ka bani mota."
Yayi ajiyar zuciya yana fad'in
"Jidda, Jidda, a gaskiya rigimarki ta fara isata,
idan kina maganar mota dana bawa Meenah ina
kikaga tana zuwa inba makaranta ba? Ke kuwa
ba zuwa makaranta kike ba saboda bakici Jamb
ba koba haka ba? Don haka tunda bakya zuwa
makaranta ni ba motar da zan baki, da dai kina
zuwa ne wannan is understandable sai na d'auki
d'aya daga cikin motocina na baki kema kina
zuwa makaranta, don haka kar na k'ara jin
wannna maganar a bakinki ma."
Ta juyo cike da masifa tace
"Ni gaskiya baka kyauta min ba, kawai don nace
ka bani mota sai ka min gori? Ni gaskiya ka
bani mota tam."
Yace
"Bazan bada ba zo ki k'wata, ko ita Meenah ba
rok'a na tayi ba ni naga dacewar hakan na bata,
don haka kema idan naga ya dace na baki zan
baki."
Ta fara jijjiga jiki tana masifa
"Kawai don nace a bani mota shine mene? Naga
dai motocinnan kana da su to meye don ka bani
d'aya?"
Yayi tsaki yace
"Ke kinga tashi ki fita ki bani wuri, mota kuma
zo ki k'wata sai muga ta tsiya, sakaryar banza
wadda batasan ciwon kanta ba, kullum ke kenan
rigima daga kice wannan sai kice wannan? Haka
kikaga 'yar uwarki nayi ne? Haba!"
Tashi tayi ta fita tana wannan cika tana batsewa
ita a dole an 6ata mata rai, shi kuma Faruk tsaki
kawai yakeyi har ya kammala shirinsa.
Haka ta koma d'akinta zuciyarta na rad'ad'i ta
dubi agogo k'arfe bakwai da minti hud'u
7:04am, Faruk mamaki yake bata kafin suyi aure
kamar zai maida ta cikinsa, amma sunayin aure
komai ya chanza mata, gashi bata son sanar da
Luby halin da take ciki gudun kar ta mata dariya
sheyasa ma ta bar abin a ranta.
BAYAN KWANA BIYU
Bayan kwana biyu kuma ta samu Faruk ya lafa
mata tunda har yana kwana d'akinta kuma yana
kulata, don haka sai ta fara jijji da kanta a
gaban Meenah, wai ita nan ta fara samo kansa.
Meenah ta kira Faruk a waya ta tambayesa
zataje gida kuma ya barta, don haka ta shirya
tsab direba zai aje ta, don yau ma Zarah zataje
gida itama, ta fito parlor nan ta iske Jidda nata
faman shan kankana duk ta 6ata wurin, Jidda
badai k'azanta ba.
Jidda ta d'ago ta dube ta a shek'e ta ta6e baki
sannan tace
"Fita zakiyi ne?"
Meenah tace
"Gida zanje."
Jidda ta bushe da dariya sannan ta dubi Meenah
tace
"Haba Malama ke dai fad'i gaskiya, ashe duk
k'aryar banza ce kikace kissa tafi magani, tunda
gashi zaki fita neman maganin kema? Sai dai kin
makaro don kinga yanzu Faruk ya k'ara dawowa
hannuna kuma, kuma kisani na riga nayi miki
nisa sannan a sannu zan tantance miki da
magani da kissa wane yafi tasiri, kuma yanzu
kika soma ganin chanji don nayi alk'awarin sai
kin bar gidannan kika k'aryata ni, to muje dai
zuwa, don haka kema kinbi sahu ay sai mu goga
ni da ke."
Meenah tayi murmushin da ya k'ara bayyanar da
kyawunta tace
"Ko shakka babu ni na fad'a miki kissa tafi
magani tasiri kuma zaki gani, babu boka babu
Malami, nayi alk'awarin nuna miki tasirin da
kissa take da shi, ki fara k'irga daga yanzu na
baki kwana bakwai kima fara lissafi tun daga
yanzu, sannan banga ta yadda kina k'azanta
zaki iya zama da miji lafiya ba ko wannan kad'ai
ya isheki, ni na tafi sai na dawo."
Tasa kai ta bar gidan, Jidda ta sake bushewa da
dariya tana wani huro chewing-gum d'in da ke
bakinta tayi k'wai tace
"Da sannu dai zan ci ubanki sai kin gwammace
kid'a da karatu."
****
Gaba d'aya Meenah ta dage da addu'a ba dare
ba rana, sannan ga extra kula tana masa da
kuma kaucewa duk wata hanya da zata sa su
samu sa6ani, lalla6a sa takeyi kamar k'wai,
shiyasa ma take ganin chanji sosai.
Yau da rana abinda yake so tayi masa wato
waina da miya, ta masa zo6o mai dad'i da
kunun aya tayi masa tasani sarai yafison
abubuwan gargajiya akan tarkacennan. Yana
cikin cin abincin ne Jidda ta shigo ta wani kashe
d'ankwalin ture kaga tsiya tana taunar chewing-
gum, da sauri ta janye plate d'in tana ma Jidda
wani irin kallo. Tace
"Baby ban yarda da abincinnan ba, ka daina ci
kazo na had'a maka wani."
Meenah ta mik'e tace
"Sai dai ki jira zuwan ranarki."
Faruk yace
"Kinga Jidda don Allah ki wuce ki bamu wuri
banason tashin hankali."
Cike da mamaki ta kalle shi tana kad'e kai tace
"A gaskiya bazakaci abinnan ba, saboda sam
ban aminta dashi ba."
AUREN FANSA 39
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
🌹39 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Meenah ta dube shi tace
"My soul bai isheka ba abincin ko?"
Ya gyad'a mata kai, ta mik'o masa hannu ya sa
nasa cikin nata tace
"Zo muje na had'a maka wanda yafi wannan,
babu mamaki k'ila tana son cin wannan ne."
Baiyi gardama ba yabi bayanta suka nufi
sashenta, tana tsaye da plate a hannunta suka
fice, galala take kallonsu har suka fice, babu
shakka Meenah ta yi gaba a halin yanzu ta barta
baya, dole ne ma ta d'auki mataki akan haka.
Ta fito daga sashen cin abinci (dinning) ta nufi
sashenta.
Zaune take abin duniya ya ishe ta, ta sak'a
wannan ta warware, daga k'arshe ta mik'e ta
fito daga d'akin tana cizon hannu. Shiru babu
motsin kowa, da alama suna cikin d'akin Faruk,
haushi ya turnik'e ta kamar zata fashe.
***
Dawowarsa kenan daga gidan, rashin ganin
Meenah bata tarosa ba ya tabbatar tana
makaranta don tace masa yau zatayi test har
biyu.
Yana shigowa yaci karo da Jidda daga bakin
k'ofa sai faman washe baki takeyi.
"Sannu." Tace dashi tana taunar chewing-gum,
yayi tsaki yace
"Yauwa." Ya sa kai zuwa d'akinsa yana Allah
wadaran da mace marar tarbiyya.
Yana zaune bakin gado yana cire safarsa ta
shigo sai wani cika take tana batsewa. Zama
tayi gefensa tace
"Ya Faruk magana nazo muyi."
Yace
"Yanzu Jidda daga dawowata sai ki tare ni da
wata magana kuma, ay kya bari in huta dai ko."
Tace
"Nidai ka bari na fad'a maka."
Ya dakata yace
"Ina jinki."
Tace
"Ay dai kace kai baka tauye hakkin iyalanka ko?"
Yace
"Haka ne."
Tace
"Yauwa, to tunda baka tauye hakkin iyalanka so
nake ka barni na tafi Dubai, na karanta Fashion
and Design."
Ya karkato yana dubanta yace
"Da igiyar wa?"
Tace
"Da igayarka mana."
Yace
"Kinga Malama banson zancen banza, ta yaya
kina matar aure kawai don rashin hankali sai ki
tafi wata uwa duniya da sunan karatu, ke bari
ma kiji ni ba irin mazan nan bane da mata ke
juya su yadda suka ga dama ba, don haka
wallahi sai na sa6a maki kika k'ara yi min zance
makamancin wannan."
Cike da shagwa6e tace
"Haba don Allah ya Faruk, wai ni meyasa kake
min haka ne? Saboda Allah ita Meenah ay ka
barta tana karatu sai ni zaka hana ni."
Yace
"Ita Meenah ba kina ganin cikin garinnan take
ba? Yau ga zancen banza zancen wofi, ke nafa
gaji da rigimarki haba! Mutum kullum da abinda
zaice daga wannan sai wannan to wallahi na
gaji."
Kawai ya tashi ya bar mata d'akin.
Ita kuwa sai tasa kuka tana ta magana ita
kad'ai.
****
Ranar wata Juma'a Luby tazo gidan, nan suka
baje suna fira. Jidda ta dubi Luby tace
"Luby gaskiyar magana nayi dana sanin wannan
aure, banida tantama alhakin Meenah ne ke
bibiyata, ke tunda nazo gidannan ban ta6a
tsintar farin ciki ba daidai da rana d'aya ba,
nikam na gaji wallahi auren ma ya fita raina,
mutumin nan sai shegen kulle baya bani abinda
nakeso, ga abin takaici wai Meenah yanzu tayi
min in mata batada tsoro ko kad'an, ke wallahi
aurennan na gama shi sai ya sake ni."
Zumbur Luby ta mik'e tana salati tace
"Yanzu Jidda abubuwa nata faruwa shine
bansani ba? Baki iya fad'a min? Sai da abubuwa
suka jagule miki suka fi k'arfinki shine zaki
sanar da ni yanzu ko?"
Jidda tace
"Kiyi hak'uri Luby wallahi na d'auka zan shawo
kan abin ne."
Luby tace
"Aiko sai mun d'auki fansar abinda tayi miki,
bata isa ba, wacece ita? Ke kin bani kunya kinfa
girme ta, amma kin zauna tana juya ki."
Jidda tace
"A'a Luby ke kinsani sarai mu da magani mukayi
aiki, ita fa? Ay ba d'aya bane ba ma."
Luby tace
"Shikenan, amma kar kiyi saurin karaya, aure
kuma yanzu kika soma shi, yo mekenan idan
kika tafi tun yanzu, ay ko baki warci wani abu
ba ni kya wabto mani, kuma ke ina son da kike
masa? Ko dama k'aryar banza ce?"
Jidda tace
"Luby don bakisan irin wahalar da nake sha ba,
babu fa yadda muka iya saboda matarsa tayi
mana zarra."
Luby tace
"Wallahi k'arya takeyi! Kedai ba kina amfani da
kwallin da turaren ba?"
Jidda tace
"Wallahi ina yi, kedai Luby munzo inda aka kere
mu."
Luby tace
"Yanzu akwai wani abu a wurinki?"
Jidda ta girgiza kai
"Babu komai sai tarin wahala da takaici."
Luby tace
"To zan san matakin da zan d'auka, zan dawo
anjima ko gobe."
Washe gari da sassafe ta dawo, ta d'auki Jidda
amma sai da suka shirga ma Faruk k'arya
sannan ya barsu da k'yar, shima akan kar su
dad'e.
Suna tafe a mota Luby tace
"Kar ki damu k'awata, zan kai ki inda za'a share
miki hawaye."
Jidda tace
"Ina kenan?"
Luby tace
"Me kike ci na baka na zuba, kedai ki tsaya ki
gani."
Luby ta koro ma Barmuje bayani, yayi 'yan
tsubbace tsubbacensa zuwa can yace da Luby
"An 6ata aiki ay, saboda tun farko sai dana
fad'a miki kar ya wuce daren farko baiyi tarayya
da ita ba, amma ina bakuji ba, sannan kuma sai
da ya fara yin tarayya da uwar gidanki akanki,
don haka aikinki bazai ta6a yin tasiri ba! A
yanzu komai ya wargaje saboda uwar gidanki
tana da rik'o da addini sosai, a gaskiya kafin
wani abu ya kamata da wuya. Ina tunanin kawar
da ita ne kawai zai baki damar mallakar mijinki
don haka sai kisan abinyi."
Suka kalli juna itada Luby tace
"To yanzu meye abinyi?"
Barmuje yace
"Akwai maganin da zan baki, zaki zuba mata a
wani abun sha, kamar koko, fura da sauransu,
wannan abin da kike gani guba ce data sha ita
da duniyar nan sai dai a lahira."
Luby tace
"Akwai wata hoda da ka bani jiya, inaga kamar
zata fi yi mata amfani."
Yace
"Tabbas! Zaifi sauk'i sai dai zan k'ara
gargad'inki da kada ki kuskura ki shak'i hodar
nan don idan kika shak'a.... hahaha to kema
zaki bak'unci lahira, idan kuma baki mutu ba...
haha! To zaki wahala a nan duniyar sai kin
zamo abin tausayi."
Luby tace
"Zata kiyaye ma."
Da haka suka baro dajin da Barmuje yake, suka
dawo gida.
Luby tace
"Yanzu dai ga maganin nan, kuma kinji gargad'in
Barmuje wallahi kibi a sannu."
Jidda tace
"Haba kar ki damu komai zai tafi yadda akeso."
Luby tace
"In ta mutu ki sanar dani, zan had'a mana grand
party."
Jidda tace
"Ay dole ne ma wannan."
Suka k'yalk'yale da dariya gami da tafawa.
Daga haka sukayi bankwana Luby tayi gida cike
da murna.
****
Meenah na kwance a d'aki tana baccin rana inda
Jidda ta lalla6o da hodar a hannunta, Jidda ta
huro mata hodar tayo baya da sauri, sai dai
mey? Memako Meenah taji wani abu sai ma ita
Jiddar ta kurma uban ihu sakamakon jikinta dake
mata rad'ad'i. Meenah ta farka tana salati
sannan ta fito da sauri ganin meke faruwa.
Jidda ce a tsakar parlor tana kurma ihu tana
soshe soshe, Meenah tayo kanta tana tambayar
lafiya? Ture ta Jidda tayi, sannan tayi d'akinta
da gudu ta fad'a toilet tayi wanka da ruwa masu
sanyi sosai. Sai dai babu wani sauk'i data
samu. Ta kasa zaune ta kasa tsaye, kuka kawai
takeyi, ga sam ta hana Meenah ta ta6a ta, sai
surutai takeyi marassa kan gado.
Hijabinta ta saka ta fito parlor a lokacin Meenah
na sallah d'akinta, aiko da sauri ta fito ta tafi
gidansu.
Mama na d'aki tana sallah ta shigo tana kuka,
sai tirje tirje takeyi, bayan Mama ta sallame ta
juyo tace
"Ke lafiya..."
Bata k'arasa magana ba Mama taja baya cike da
tsoron ganin fuskar Jidda kamar ba tata ba,
Mama ta fito da gudu tana salati tana fad'in
"Wacece ke?"
Jidda na biye da ita tana dariya tana cewa
"Ni ce, nice naje wurin boka nida Luby muka
anso magani zamu kashe Meenah."
Mama tasa salati tana fad'in
"Jidda. Meya kaiki? Mekika zama? Innalillahi wa
inna ilahir raj'iun! Jidda."
Jidda tasa dariya, sai ta susa kai, ta susa jiki
tana zum6uro baki tace
"Wai laifina ne? Kaji man Mama, nifa kawai
d'ora ni akayi akan turbar nabi kuma."
Ana haka Dada ya dawo, shima cike mamaki
yake tambayar lafiya. Mama ta kwashe komai ta
fad'a masa abinda Jidda ke cewa.
Dada yace
"Da alama fa kamar hauka takeyi ko?"
Mama tace
"Nima shi nagani."
Suka sa salati, Dada yace
"Duniya budurwar wawa Jidda, Allah ya shiryeki,
Hajiya kamo ta ki kai ta d'aki ki rufe kafin mu
san abinyi."
Tace
"To."
Ta kamo Jidda, tana tirjewa da k'yar suke tafiya,
Jidda taci kwalar Mama tana dariya tace
"Ina zaki kaini? Iye?"
Mama tace
"Muje d'aki ki kwanta."
Jidda tasa dariya, can kuma tasa kuka, can tasa
dariya, sai kuma tasa kuka, ta jawo hancin
Mama ta matse tace
"Daman haka boka yake? Laifin duk na Luby ne
saboda ita ta kaini tun farko, saboda ban ta6a
zuwa ba ay ko?"
Mama tana kuka tace
"Eh muje."
Mama ta sha wahala don da k'yar ta kai ta d'aki
ta rufe, sai dai taji ana bubbuga k'ofar ana ihu,
can taji dariya, can taji surutai, can kuma taji
ana cewa
"Boka, boka, Barmuje sunansa."
Mama tayi tsaye tana kuka, tace
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Jidda kinga
halin da kika jefa kanki ko? Kinzo kiyi wa wata
asiri ya dawo kanki, duniya ina zaki damu? Ka
haifi d'a amma baka haifi halinsa ba. Allah ka
shirya shine kawai abinda zan ce miki Jidda,
Allah kuma ya yaye miki."
Dada ya kira Faruk ya sanar masa yazo yana
nemansa yanzu yanzu.
Ba'a d'auki lokaci ba ya iso, Baba ya kwashe
komai ya fad'a masa, Baba ya d'ora da cewa
"Ina so idan ta warke ka sallame ta, baka
buk'atar cigaba da zama da ita, tunda har kamar
Jidda tasan tayi kisa ay kaga zama da irinsu ba
amfani.
Faruk yace
"Allah ya kyauta, Allah kuma ya bata lafiya."
Baba yace
"Amin."
Faruk yace
"Bari na dubo ta, daga nan sai na nemi asibitin
da za'a kaita."
Baba yace
"To kabi a hankali, don jikin ba dad'i."
A hankali ya tura k'ofar d'akin tana zaune
dirshen a k'asa tana kwa6a sabulu da toothpaste
cikin wata roba, ya kalle ta duk ta shafa ma
kanta, ya zauna a bakin gado yana kallonta cike
da tausayi, wannan wace irin rayuwa ce? Wai
Jidda tasan taje wurin boka? Ya kalli Dada dake
tsaye a bakin k'ofa sannan ya maida dubansa ga
Jidda da ke shafa sabulun a jikinta.
Ya gama kallonta yayi mata adduo'i sannan ya
tashi ya fita.
Ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba ya je ya nemo
asibitin da za'a kaita, daga nan aka kwasheta da
da k'yar daga gidan. Faruk ya sanar ma sauran
'yan uwanta suma sunyi jimami sosai, daga
k'arshe sukayi mata fatan shiriya da samun
lafiya.
***
0 comments:
Post a Comment