a bakin k'ofa, tana sanye da brown and cream
atamfa d'inkin riga skirt, tayi kyau sosai, da
sauri ta taro sa ya k'ura mata idanu yace
"My baby ya akayi ne?"
Yaushe rabon da taji sunan nan a bakinsa har
ma ta manta, tayi murmushi tace
"Jidda ce tun d'azu banganta ba, ko da saninka
ta fita?"
Ya kwashe labarin komai ya fad'a mata, tace
"Ikon Allah kenan, amma Jidda bata yi wa kanta
adalci ba, amma sai inga duk bai kai na saki ba
my soul."
Ya kamo ta suka dawo parlor suka zauna yana
kallonta sosai yace
"Rabuwa da Jidda shine mafi alkhairi a garemu
my baby, saboda a gaskiya bazan iya cigaba da
zama da ita a matsayin matata ba, besides ba'a
son raina na aure ta ba."
Ta dube shi cike da mamaki tace
"Bangane ba my soul."
Yace
"Wato akwai wata rana na fito zan tafi aiki sai
naji Jidda na magana da mahaifiyarta tana ce
mata ita ba wanda takeso sai ni, a nan naji
Mama na ta rarrashinta akan tayi hak'uri tunda
ni ba sonta nakeyi ba, tun daga wannan lokacin
sai na karaya nake ganin kamar ban kyauta ba,
abin yana ta damuna sosai, a ganina abinda
kawai zanyi na faranta ransu shine na bijiro da
maganar auren Jidda, a tunanina sun mani
komai a rayuwa bai kamata d'iyarsu tana sona
nak'i ta ba."
Meenah ta kamo hannunsa tana murmushi tace
"A gaskiya kayi tunani mai kyau kuma ka kyauta,
sai dai daman tun farko kayi min bayani da sai
nafi fahimtarka my soul."
Yace
"Naso yin hakan my baby, amma a lokacin sai
na rasa dalilin da yasa na kasa fad'a miki
gaskiya, kuma wallahi bansan yadda akayi ba
sai dai naji ance wai matata ce, abin zai baki
mamaki is like bansan abinda nakeyi ba, kuma a
lokacin Jidda tayi amfani da magani wajen jawo
hankalina gareta, nidai kawai idan ta warke zan
sallame ta, taje can ta nemi wani daidai da ita."
Tace
"Bazan iya saka yin abinda baka so ba, duk
abinda kaga yafi dacewa kayi ni kuma zan baka
goyon baya d'ari bisa d'ari my soul."
Ya kamota ya rungume a k'irjinsa gami da
lumshe idanu yace
"Sheyasa nake sonki my baby."
Tace
"Nima haka, yanzu muje kayi wanka kaci abinci
ko, na dafa maka abinda kafi so."
Cike da jin dad'i yace
"Allah my baby?"
Tace
"Wallahi kuwa."
Yace
"Shikenan muje, don yau ma kece zakiyi min
wanka da kanki."
Ta tashi tana fari da ido tace
"Muje."
Ta wuce yabi bayanta.
****
Yana zaune a office d'insa aiki yasha gabansa
wayarsa ta fara ringing, ganin Hajir ya sanya ya
dakata ya d'auka.
"Hello Hajir."
Tace
"Hello Sir ina wuni?"
Yace
"Lafiya lau, ya dai?"
Tace
"Aikinka na kammala komai Sir, yanzu ya
za'ayi?"
Cike da jin dad'i yace
"Da gaske kin had'a komai da komai?"
Tace
"Yes Sir komai ya kammala."
Yace
"Wow Weldon Hajir, a gaskiya nayi matuk'ar
farin cikin jin haka, yanzu abinda za'ayi, ki
shirya zuwa gobe zan shigo gidan, dana kiraki
sai ki fita daga shigar Atika ki koma Inspector
Hajir d'inki. Sauran bayanin zan kiraki. Yanzu
wani d'an bincike nakeyi akan wad'anda suka
turo domin kashe iyayena, nama kammala don
har na tura a kamo yaran, don muna
buk'atarsu."
Tace
"Yayi haka sir, sai Allah ya kaimu goben."
Yace
"Amin, thank you."
Daga haka sukayi sallama, Faruk yayi
murmushin jin dad'i sosai.
****
Kiran farko na sallar asuba a kunnensa akayi,
domin ba bacci yake ba, saboda tsabar farin
cikin kalar matar da Allah ya bashi, shi kwata
kwata bai k'ara tabbatarwa ba sai yau,
tambayar kansa yakeyi anya kuwa akwai wanda
ya kai shi sa'a?
Ya lalubi bed side lamp sannan ya dube ta tana
bacci, numfashinta yana fita a natse.
Kyakkyawar fuskarta nata annuri, yayi ta kallonta
baya ko kyaftawa har sai da idanunsa suka
kawo ruwa sannan ya dawo hankalinsa, ya
sunkuyo a hankali ya manna mata light kiss a
goshinta, ya numfasa, Allah kad'ai yasan tarin
son da yake mata. Da k'yar ya lalla6a ya sauka
daga gadon ya shiga toilet yayi wanka ya fito da
alwalarsa, ya shimfid'a sallaya yayi nafilfili har
alfijir ya fito, sannan ya nufi masallaci.
Yanda ya barta haka ya dawo ya same ta, yayi
tsaye a gaban gadon rungume da hannayensa
yana kallonta.
"Wai lallai baby an gaji."
Ya zauna gefenta ya tallabo kanta sannan yace
"Meenah... Meenah..."
Ta bud'e ido a hankali tabi shi da kallo har idon
ya washe gaba d'aya. Yace
"Ki tashi kiyi sallah, ko gajiyar ce ta hana ki
tashi?"
Ta runtse ido tana k'ok'arin tashi, yayi
murmushi kawai ya d'aga ta cak sai toilet, ya
tarba ruwa masu d'umi ya saka ta ciki, ita kuwa
idonta har yanzu a lumshe yake, yana tsaye yace
"Haba ragguwa sai kace first time dai."
Tayi murmushi kurum, daga haka ya fita ya bata
wuri don ta kimtsa.
Tsawon minti 20 tafito, ya matso yana dariya.
"Ragguwa kawai ni tuni naje masallaci na
dawo."
Ta wuce shi tayi shirin sallarta tana jin wani irin
nishad'i marar misaltuwa. Kwanciyarsa yayi, ta
gama sallarta tayi adduo'inta gami da mik'a
godiyarta ga Allah da ya karkato mata da
hankalin mijinta gareta tana fatan su dauwwama
haka har k'arshen rayuwarsu. Sai kuma ta tuna
Jidda ko a wane hali take yanzu? Ta dad'e tana
mata addu'ar samu sauk'i, tana gamawa sai
kawai ta maida kanta bisa sallayar tana lazumi.
Ya d'ago yana dubanta yace
"Ya zaki kwanta a nan?"
Tace
"Haka nan."
Yace
"To kodai?"
Ta k'udundune fuskarta da hijabi ta k'yale shi,
cicci6o kanta yayi ya d'ora bisa jikinsa yace
"Tashi mu koma kan gado."
Tayi shiru tana kallon kyakkyawar fuskarsa, yace
"Allah yayi miki albarka my baby."
Taji dad'i sosai ta amsa da
"Amin my soul."
Ya cigaba da fad'a mata dad'd'an kalamai masu
rikita lissafi, ganin haka yasa na tashi na baro
d'akin, sai dai fatan Allah ya kawo k'azantar
d'aki..
AUREN FANSA 41
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
🌹41 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
A hankali ta bud'e idonta juyi d'aya tayi ta
hango shi bakin wardrobe da alama wanka ya
fito yana shirin fita, duba agogo tayi k'arfe
8:30am, zumbur ta mik'e tana mamakin abinda
ya haddasa masa makara yau, zaune ta mik'e
tana kallonsa yana k'ok'arin d'aura agogo a
hannunsa, ta sauko daga gadon ta kamo
hannunsa tana cigaba da sa masa.
"Yau ka makara my soul."
Jin yayi shiru ya sanya ta d'ago tana dubansa
da mamaki, damuwa ta gani k'arara bayyane a
fuskarsa wanda idanuwansa ma sun nuna hakan.
"Meyake damunka my soul?"
Yace
"Babu komai, kije kiyi wanka yau tare zamu fita,
sannan ki sanar da Zarah ta tamabayi mijinta ya
bata izini zamu fita tare da ita."
Tayi shiru tana tunani can kuma tace
"Lafiya?"
Yace
"Koma me kenan zaki gani nan da lokaci kad'an,
kedai kawai ki kirata ki sanar da ita."
Tace "To." Sannan ta wuce tana tunanin
dalilinsa nace mata haka.
Tayi wanka ta sanya bak'ar after dress, tea
kawai suka sha inda a waje sukayi kaci6us da
Zarah inda take shaida musu da mijinta zasu tafi
yace zai kaita, haka ma Anisah tazo a daidai
sadda zasu shiga mota, itama ta shaida musu
mijinta zai kaita, nan kuma kowa ya fara shirin
tafiya.
A mota babu wanda yayi magana ko wane da
tunanin da yakeyi, ta kai dubanta ga Faruk da
alama ya zurfafa cikin tunanin, ta ta6o sa tace
"My soul wai meke faruwa haka ne? Sannan duk
ina zamuje da su Anisah?"
Ya karkato kad'an ya kalle ta sannan ya maida
kansa ga titi yace
"Ki gafarce ni my baby."
Tace
"Akan me fa?"
Yace
"Kawai ki yafe min akan abinda zai faru yau."
Cikin rashin fahimta tace
"Me zai faru yau?"
Bai kai ga bata amsa ba wayarsa tayi ringing, ya
d'auka yace
"Hello Usman."
Usman yace
"Muna hanya ka turo mana address d'in."
Yace
"Muma muna hanya, zan turo maka sai mun
had'u d'in."
Ya kashe kiran ya tura masa address d'in.
Meenah da zuciyarta fal damuwa tace
"Kaji my soul, wai meke faruwa?"
Yace
"Kiyi hak'uri zaki ga koma menene."
Ganin ya d'auki hanyar unguwarsu ya sanya
tace
"Daman gida zamu shine kak'i sanar dani?"
Ya d'anyi murmushin k'arfin hali a zuciyarsa
yace
"Nasan yau zanyi breaking heart d'inki my baby,
amma abinda zanyi ya zama dole in ba haka ba
hankali na bazai ta6a kwanciya ba."
Ya kalle ta yaga ta zurfafa cikin tuanani, yayi
ajiyar zuciya a lokacin da ya karya kwanar
layinsu Meenah.
Ganin motoci a k'ofar gidansu ya sanya ta d'an
razana kad'an gami da zaro idanu waje, ya
kalleta ya kawar da fuskarsa gefe, yasan kota
masa tambaya baisan abinda zai ce mata ba.
Yayi parking ya fito daga mota, yana d'an kalle
kalle, ganin ba motar Usman ya sanya yasan bai
iso ba, amma motoci hud'u sun iso na abokanan
aikinsa, su Zarah duk sun iso inda take ta
tambayar abinda ke faruwa. Amsa d'aya take
samu wato,
"Nima bansani ba."
Su Najeeb ne kad'ai suka san abinda ke faruwa
saboda ya sanar musu daman.
Ya d'auki waya ya kira Hajir ya sanar mata yana
k'ofar gida. Tace she's ready tun d'azu. Nan
suka cigaba da tsara plan d'in nasu.
Ita dai Meenah bata k'ara magana ba illa dai
gabanta da ya tsananta bugu.
A 6angaren Bilki kuwa tunda ta tashi da safe
k'awarta ta iso akan yau zasu walimar bikin
d'iyar wani sanata da za'ayi a cikin garin Abuja,
Baba kuwa yana d'akinsa yana wanka zai fita,
shiryawa tayi cikin wani dank'areren leshi mai
matuk'ar tsada sai k'yalli takeyi, wayoyin da ke
hannunta sun kai kala uku kuma manyan wayoyi
masu tsadar gaske, ta fito parlor sai zuba
k'amshi take kamar shagon saida turare, kaci6us
tayi da Hajir sanye cikin bak'ar after dress tayi
tsaye a bakin k'ofa idanunta manne cikin bak'in
glass wato no respect.
Suka ja suka tsaya Bilki ta kalle ta daga sama
har k'asa tace
"Ke Atika meye haka? Ina aikin dana saki zaki
zo kiyi wa mutane tsaye a ka haka! Matsalar
d'an k'auye kenan ka wayar da shi sai daga
baya ya nuna yafika wayewa. Mts."
Laila tace
"Gaskiya kam da alama don wannan yarinyar
'yar rainin hankali ce, ke Malama ki bamu wuri
zamu wuce."
Hajir ta kalle su da chewing-gum a bakinta sai
hannunta dake hard'e tace
"Wacece Atika don Allah?"
Bilki tace
"Ahh! Kiji min neman magana fa, yo wacece
Atika 'yar aiki in ba ke ba? Kaji min yarinya zata
nemi ta maida ni k'aramar yarinya."
Laila tace
"Gaskiya wannan ta samu wuri da yawa. Da nice
ke da tuni na sallame ta don bazan iya ba, zan
iya farfasa mata jiki."
Bilki tace
"Eh gaskiya ne, ke Atika! Ki wuce kije ki d'ora
girkin rana kafin mu dawo."
Hajir ta kallesu a wulak'ance tace
"I'm sorry to say Hajiya, amma bazanyi ba, sai
dai idan kece zaki je ki d'ora."
Suka fara salallami suna tafa hannu, Laila tace
"Wai bazaki gaura mata mari ba, ni wallahi
sheyasa kikaga bani d'aukar 'yan aiki saboda
bansan wadda zan kwaso ba, ya za'ayi ki zauna
kina fad'a tana fad'a? Ki d'auki mummunan
mataki akanta mana."
Bilki tace
"Lallai kin k'oshi da sadda aka kawo ki kamar
zakiyi min sujjuda amma yanzu kin k'oshi kin
mik'e k'afa ko? Lallai sannu Atika, to wallahi
kizo ki kwashi kayanta ki bar min gida munafuka
kawai."
Hajir tayi murmushin mugunta tace
"Daman yau zan bar miki gida Hajiya kar ki
damu."
Bilki tayi tsaye ta rasa ma me zatace sai tafa
hannu kawai takeyi.
Minti goma tsakani Faruk ya doka sallama, Bilki
ta washe baki tace
"Ah kinga surukinmu ne yazo, sannu da zuwa
Faruk."
Ya shigo yana k'are ma gidan kallo, yana d'aga
kwalar rigarsa yace
"Ki gyara kalamanki Hajiya ba Faruk zakice ba,
Inspector Faruk Adam Ishaq zaki ce."
Suka kalli juna itada Laila, Laila ta rad'a ma
Bilki a kunne
"Adam Ishaq fa yace, me hakan ke nufi kenan?"
Hajir tayi murmushi ta cire after dress d'inta
ta dawo kusa da Faruk tace
"Sunana Inspector Hajir ba Atika ba."
Bilki tace
"Ke kamar ya keba Atika bace, to wacece ke?"
Meenah da Zarah da Anisah suka shigo ganin
Ikon Allah a daidai nan Baba ya sauko yana
gyara hular kansa ganin mutane da hayaniya ya
sanya yaja tsaya yana tambayar lafiya?
MSB💖
BELLO
‹ › Home
View web version
Friday, 8 September 2017
Maryam Saidu at 14:37
AUREN FANSA 42
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
Ina yi ma d'aukacin musulmai barka da sallah,
da fatan munyi sallah lafiya? Allah ubangiji ya
maimaita mana Amin thumma Amin! ❤️
Wannan page d'in nakune Faty Ladan, Hauwee
Bash, Asma'u Ammani, Hafsat Kabeer, Farida
Bature, Feedn, Machika, and Aisha Basheer dama
sauran wad'anda ban ambata ba, nagode da
k'aunar book d'innan da kukeyi.😘
Fatan alkhairi ga Auren Fansa Fans😍Allah ya bar
zumunci.❤️
🌹42 🌹
Cikin girmamawa Faruk ya isa inda Baba ke
tsaye ya gaishe shi ya amsa masa yace
"Meyake faruwa ne haka a nan?"
Faruk yayi murmushi yace
"Yanzu zaka fahimci komai Baba."
Faruk ya koma inda Hajir ke tsaye yace
"Hajir ina so ki bani wayar nan dana baki zan
duba wani abu."
Hand bag d'inta ta bud'e ta fiddo ta mik'a
masa, ya maida dubansa ga Bilki yace
"Ina so ki nutsu ki kalla."
Tace
"Bangane abinda ke faruwa a nan ba, don Allah
ayi mana bayani mana."
Faruk yace
"Abinda nake k'ok'arin yi kenan ay."
Wayarsa ya zaro daga aljihu ya kira bugu d'aya
aka d'auka yace
"Usman bud'e motata ka d'auko min system
d'ina tana nan daga bayan seat, sai wasu
wayoyi amma ba'a jiki suke ba suna nan a gefe
sai ka d'auko mun su duka."
Bansan me Usman yace ba naji dai Faruk yace
"A'a motar a bud'e na barta kawai ka bud'e,
yanzu yanzu muna jira don Allah."
Baba yace
"Wai lafiya haka Faruk? Har yanzu ban fahimci
inda ka sa gaba ba."
Faruk yace yana k'ok'arin maida wayarsa aljihu
"Yanzu zaka fahimta Baba."
Bilki kuwa kamar ruwa ya cita haka kurum
gabanta ya tsananta bugu, don har wata kyarma
take duk da batsan abinda ke faruwa ba.
Usman ne yayi sallama hannunsa d'auke da
laptop da wayoyi, Faruk ya kar6a inda ya aje ta
a saman center table d'in dake ajiye a parlor
d'in, yayi ta had'e had'ensa ya jona nan ya
had'a can, cikin minti kad'an wani video ya
bayyana a saman screen d'in laptop nasa. Ya
juya ta setin da kowa ke tsaye ya danna play.
Hoton farko video Bilki inda take waya da Laila a
gameda makircin da suka had'a, maganar yadda
take kwasar dukiya da shawarwarin da Laila ke
bata akan yadda zata dage wajen cigaba da juya
dukiyar.
Next scene kuwa hoton Laila ne da Bilki suna
zaune cikin d'aki suna maganar yadda suka
kashe Hajiya Reema da Alhaji Adam, take Bilki ta
fara zufa itada Laila, wannan abu ya basu
mamaki ya akayi aka d'aukesu hoto haka?
"Waye ya d'auki wannan videon?" Ta fad'a
jikinta na kyarma, Baba kuwa kallonta kawai
yana salati, inda Zarah da Meenah ke tsaye suna
kuka suna mamaki.
Scene na gaba kuwa yana d'auke da video d'in
Laila da Bilki inda Laila ke narrating yadda akayi
kisan da kuma shawarar su cigaba da 6oye
sirrinnan, har Bilki ke nuna mata tsoronta kar
wata rana asirinsu ya tonu. Laila tana nuna
mata asirinsu a rufe yake babu mai ji.
"Wallahi bani na kashe su ba, wallahi Laila ce ta
kawo wannan shawarar."
Bilki ta fad'a tana kyarma, Laila tace
"Dana baki shawarar wa yace ki d'auka don
haka kina da laifi kema."
Bilki tace
"Nidai wallahi kin cuce ni Allah ya isa wallahi."
Laila ta buga tsoki tace
"Aikin banza, yo Allah ya isarki me zatayi min?"
Faruk ya cigaba da displaying duk wani abu da
aka d'auka na Bilki da Laila, tare da voice notes,
Baba da zufa ta jik'e shi jagab, ya kalli Meenah
da Zarah yaga yadda suke kuka, sannan ya juya
ga Bilki da take borin kunya suna chachar baki
itada Laila suna ta k'ara bankad'e asirinsu da
kansu.
"Tun farko ina zaman zamana kika kawo
wannan shawarar kika ce mu kashe su..."
"Dana kawo shawarar nace dole kibi ne? Kema a
lokacin kina jin haushin Alhaji Adam, akan ya
samu kujarar da kikeso mijinki ya mallaka ko
nayi k'arya?"
Bilki tace
"K'arya kike munafuka algunguma, abin naki
harda sharri kuma? To wallahi..."
Maganarta ta katse ne sakamakon wani zafafan
mari da Baba ya d'auke ta dashi, har sai data ga
gilmawan wuta sannan ta nemi ji da ganinta ta
rasa na wuchin gadin.
Dafe kuncinka tayi cike da azaba kafin kuma ta
ankara ya k'ara d'auke ta da wani wanda yafi
na farko zafi, kyarma ta fara yi inda hawaye ke
ambaliya a saman fuskarta, ya d'aga hannu zai
k'ara wanke ta da wani marin cikin azama
Meenah ta rik'e masa hannu gam gam tana
kuka, tace
"Kar ka k'ara mata wani Baba, ka rabu da ita
don Allah."
Baba ya fara k'ok'arin k'wace hannunsa yana
nuna Bilki yace
"Ashe ke mutuniyar banza ce bansani ba?
Shashasha marar mutunci! Ashe ke muguwa ce?
Makira! Anya kinada imani kuwa? Kin bani
mamaki ban ta6a zaton haka daga gareki ba..."
Sai ta fara borin kunya tana fad'in
"Yo har abin kunya ya wuce daga gareka? Kai fa
kana zaune da mutum ka kasa gaya mata
iyayenta na asali tsabar rufa rufa!"
Baba yace
"Ki min shiru a nan, anya kina da hankali kuwa?"
Tace
"Ras nake, yo tunda aka tona min asiri na wa
zan iya rufewa kuma? Ai wallahi sai na fasa
k'wan! Ke Amina! Kalleni nan Alhaji bashi ya
haife ki ba! Haka nima ba nice na haife ki ba!
Kije ki tambaye shi inda iyayenki suke."
Gaban Meenah yayi mummunar fad'uwa, dafe
k'irjinta tayi a yayinda hawaye suke kwarara a
fuskarta, Baba take kallo tace
"Ni 'yar tsintuwa ce ko?"
Faruk kuwa tsaye yayi cike da mamaki a yayinda
k'walwarsa ta tsaya cak da aiki....
AUREN FANSA 43
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
Dedicated to First Lady 😍
PML You are the best Allah ya bar mu tare👌🏼😉😌
🌹43🌹
Cikin wani irin yanayi yace "What?"
Bilki kuwa k'ara d'aga murya takeyi tana fad'in
"Ke Amina ba mu muka haife ki ba."
Laila tana ta d'an zunguranta akan ta bari ina
bata ma saurareta ba. Baba ya sunkuyar da
kansa yana mai tsananin jin haushin Bilki, ko
kusa bai so Meenah tasan matsayin ta ba, a
ganinsa hakan zai iya haifar mata da damuwa
sosai, da yawan tunani, duk da yasan sanin
matsayintan ba wani abin bane don kuwa
cikakiyyar 'yar sunnah ce, hakan yasa ya tattaro
nutsuwarsa yana kallon Meenah data tsareshi da
ido kamar yau ta fara ganinshi, yace
"Kar ki damu zan sanar da ke komai, Faruk
kammala aikinka sai mu tattauna."
Da k'yar Faruk ya tattara nutsuwarsa amma
gaba d'aya hankalinsa naga Meenah da kuma
son jin in da gaske ne zancen Bilki.
Police guda biyu ke tsaye a waje Faruk ya kirasu
suka shigo, da hannu kawai ya basu order
wanda su kad'ai suka san me yake nufi, sara
masa sukayi sukace
"Yes sir..."
Fita sukayi ba'a jima ba sai gasu sun dawo da
matasan maza majiya k'arfi su kusan biyar
masu k'iran 'yan daba, ko su Zarah sai da suka
tsorata da ganinsu, sai wani huran hanci sukeyi
suna zare idanun kamar kura taga nama. Take
jikin Laila ya fara 6ari don kaf d'insu ta ganesu,
haka zalika ita kanta Bilki sai ta fara salati tana
bada hak'uri da neman gafara.
Faruk yace
"Wad'annan sune wad'anda kukayi assigning
suka aikata kisan da hannunsu, suka kashe min
iyayena..."
Take tsikar jikinsa ta tashi idanunsa suka kawo
ruwa, ya kai dubansa ga Anisah yaga tana kuka
itama, duk sai ta basa tausayi a ransa yace
"Ke kenan da bakida wayau a lokacin bare kuma
ni."
Bilki tace
"Ni dai bansansu ba. Billahi bansan ko su waye
ba."
Baba ya daka mata tsawa
"Yi mana shiru a nan! Ko so kike sai na sa an
harbe ki ne da bindiga? Ga laifi an kamaki dumu
dumu amma kina k'aryatawa?"
D'aya daga cikin 'yan daban suka ce
"Tabbas nine wanda Hajiya Laila ta kira take
sanar dani irin aikin da za'ayi musu, sannan
sukayi min alk'awarin mak'udan kud'i idan na
aikata abinda suka sani, ita kuma Hajiya Bilki ita
bani umarnin kisan tace idan ban aikata ba to
tabbas ni zatasa a kasheni, haka sukayi min ko
wanensu zai bani dubu d'ari biyar biyar idan
aikin ya kammala. Don haka na samu abokanan
aikina na sanar musu yadda zamuyi aikin. Ko
bayan faruwan haka sai da suka mallaka min
gida da mota wai a cewarsu farin cikin abinda
nayi musu ne."
'Yan sandan suka matso kusa da su Hajiya Laila
sukace
"You're under arrest for the murder of Hajiya
Reemah and Alhaji Adam, you have the right to
remain silent, because anything you said will be
used against you in a court of law."
"Don Allah ka gafarce ni, ku yafe min abinda
nayi."
Ta matso kusa da Meenah tace
"Ki yafe min irin cin zalin da nayi miki a baya,
nasan kin sha wahala a wurina ki yafe min."
Baba yace
"Kamar yaya?"
Zarah ta matso tana share hawaye tace
"Baba, tunda na taso nake ganin yadda Meenah
ke fuskantar wulak'anci, mugunta da kuma
zalunci a wurin Mami, bugun yau daban na gobe
daban, ga sata aiki kamar jaka, abinci kuwa data
gama wannan sai a sata wani, wanke wanke,
wanki, wankin toilets, shara, goge goge, duk
Meenah ce keyi. Sannan bata cin abinci sai ka
kusa dawowa, haka zata wuni da yunwa ga
uban aiki, da ka kusa dawowa zata korata tayi
wanka taci abinci yadda bazaka gane ba. Ko
nayi yunk'ura fad'a maka sai Mami ta hana, ko
tace zata zane ni muddin na sanar da kai..."
Baba yace
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Bilki ashe
yadda na d'auke ki ke ba haka kika d'auke ni
ba? Tun farko dana san haka kike da ban d'auki
amanar maraininiyar Allah na baki ba, amma
kisani akwai ranar hisabi kuma Allah sai ya
mata sakayya..."
"Na tuba Alhaji, ka yafe min..."
"Bilki kije na sake ki saki d'aya..."
Kowa sai da ya zabura jin sakin da Baba ya
yiwa Bilki, sannan ya bita da nasiha da fatan
zata gane kuskurenta, haka aka saka musu
ankwa itada Laila aka jasu suna tirjewa da
maganganu suka fice.
Faruk gaba d'aya jikinsa yayi sanyin abinda yaji,
wai Meenah marainiya ce?
"Me nayi? Na d'auki alhakin baiwar Allah." Ya
fad'i a cikin ransa.
Duk da daurewarsa sai da k'walla suka zubo
masa, ya share sannan ya bi bayansu Bilki inda
Anisah ma tabi bayansa, suka bar gidan. Suna
fita Meenah ta kifa kanta a hannun kujera tayi ta
kuka kamar ranta zai fita, Zarah na ta aikin
rarrashinta inda itama kukan takeyi, Baba yaja
su suka shiga cikin d'aki yana ta faman
rarrashinsu.
*****
Daddare kowa ya nutsu a parlor amma daka kalli
kowa kasan ba a cikin nutsuwa suke ba.
Baba ya maida dubansa ga Meenah yace
"Dalilin da yasa ban ta6a fad'a miki ba shine, na
farko baniso kiyi kukan maraici, na biyu baniso
ki shiga damuwar rashin iyaye, don kinsan
yawan damuwa ga yaro ba abu bane mai kyau,
amma ina mai baki hak'urin 6oye miki da nayi
duk da nasan you have the right kisani."
Nan ya kwashe labarin komai ya fad'a mata, su
waye iyayenta da kuma yadda akayi ta dawo
hannunsu da zama. Sannan ya d'ora da cewa
"Duk da nasan banyi niyyar fad'a miki ba amma
wallahi ji nake kamar an sauke min wani nauyi
da ke bisa kaina, Meenah bana fad'a miki
maganar nan ba don ki shiga damuwa ba, a'a na
fad'a miki ne bisa tirsasawa da akayi min, sai
dai ina rok'onki da kada ki d'ora damuwa a ranki
don Allah, sannan ki cigaba da yiwa iyayenka
addu'ar samu rahama daga Allah, inda suka tafi
muma zamu iske su wata rana."
Ya fad'a da guntun k'walla a idanunsa. Meenah
ta share hawayenta tace
"Wallahi Baba ban ta6a sanin cewar bakai ka
haifeni ba saboda babu alama, duk wani gata ka
min shi, sai dai nace Allah ya saka da alkhairi,
amma kasani har yanzu bazan daina ganinka a
matsayin mahaifina ba saboda kaima mahaifina
ne saboda yaya kake ga mahaifiyata don haka
duk d'aya ne, kuma insha Allah na maka
alk'awarin cire damuwa a raina."
Yace
"Alhamdulillah, ke kuma Fatima kema kar ki
shiga damuwar ganin mahafiyarki da aka kama,
ki cigaba da yi mata addu'a."
Tace
"Insha Allah Baba."
Faruk da ke zaune jikinsa sanyi k'alau yace
"Baba inada magana idan an bani dama."
Baba yace
"Bismillah mana."
Faruk ya sunkuyar da kansa saboda nauyin
maganar amma kuma dole ne ya fad'i, don ya
samu su yafe masa.
Yace
"Baba, ka gafarce ni, nayi kuskure babba."
Sai kuma yayi shiru, Baba yace
"Kuskure kuma Faruku? Na me?"
Ya kalli Meenah yaga shi d'in take kallo, sannan
ya maida kansa k'asa yana wasa da zoben
azurfar da ke hannunsa yace
"Wallahi Baba da zan auri Meenah ba sonta
nakeyi ba... daman don na d'auki fansar abinda
akayi wa iyayena ne sheyasa na aureta..."
Ras! Ras! Gaban Meenah ya yanke ya fad'i, ya
d'ago ya kalleta yaga idanunta sun kad'a sunyi
jawur! Tana masa kallon mamaki had'e da
tsana...
"Meenah nasan nayi kuskure a nan amma
wallahi..."
Da gudu tayi ciki tana kuka mai sauti...!
Zarah ta bi bayanta da gudun itama tana k'wala
mata kira...
AUREN FANSA 44
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
http://MaryamSBello.blogspot.com
🌹44🌹
A bakin gado Zarah tayi arba da ita ta kifa kanta
tana kuka kamar wacce aka aiko ma da labarin
mutuwa, a hankali ta k'arasa gami da zama
gefenta ta d'an dafata sannan ta kira sunanta
cikin sigar rarrashi.
"Meenah..."
A hankali ta d'ago da jajayen idanunta tana
kallon Zarah a yayinda hawayenta suka cigaba
da zuba ba k'akk'autawa, Zarah ta sa hannunta
ta share mata hawayen tace
"Haba Meenah, meye haka? Meye abin kuka a
nan? So kike sai wani ciwon yaje ya kama ki a
banza? Don Allah kiyi shiru ku fahimci juna keda
mijinki."
Meenah tayi murmushin da ya fi kuka ciwo tace
"Zarah, a halin yanzu ba zaki gane halin da nake
ciki ba saboda bake bace aka yaudara ni ce aka
yaudara, ke kina can zaune lafiya da mijinki kina
sonsa yana sonki, ni kuwa fa? Ashe wanda nake
matuk'ar so kamar raina ashe yaudara ta
yakeyi? Mutumin da zan iya sadaukar wa
rayuwata domin farin cikinsa, mutumin da nake
da burin samun zuri'ah ta gari da shi, mutumin
da nake kallo a matsayin masoyina na hak'k'ika
ashe shi ba haka yake kallona ba, ya cuce ni! Ya
cuci rayuwata, yayi min wasa da feelings ba
kad'an ba, wallahi Zarah namiji mugu ne, namiji
bashida tabbas! Allah wadaran namiji!"
Zarah tace
"Haba Meenah! Ki saurari kanki ki daidaita
tunaninki, yes na yarda Faruk bai kyauta miki ba,
kuma baiyi amfani da hanyar da ya dace ya
d'auki fansa ba, amma tunda yayi admitting a
gabana dake da Baba kinsan yayi namijin
k'ok'ari, ina so ki sani ba ko wane mutum bane
zai iya haka ba, ya kamata ko nan kiyi
respecting decision d'insa, kuma ko rantsuwa
nayi bazanyi kaffara ba ya na matuk'ar sonki a
yanzu, kuma ya gane kuskurensa."
Ta mik'e tsaye tana huci
"Sonsa na banza, bana so ya rik'e kayansa,
kuma nidai na gama zama da mayaudarin
mutum kamar Faruk, bazan koma gidansa ba!"
Zarah ta mik'e tana kallonta galala kafin tace
"Are you kidding me? In ma wasa kike ki daina
tun wuri, Meenah kamar yadda na fad'a miki da
farko zan kuma maimaitawa, Faruk yana sonki
ko ki yarda ko kar ki yarda, koda can baya sonki
to yanzu Allah ya d'ora masa. Don haka kiyi
tunani."
Baba ne ya aiko kiransu, suka mik'e jiki a
sanyaye suka fice, a parlor suka iske Faruk kallo
d'aya zakayi masa ka tabbar da hankalinsa a
tashe yake, tunda suka shigo ya kafa mata ido
ita kuwa ko kallon inda yake batayi ba, suka
samu wuri suka zauna k'asa, Baba ya fara
magana.
"Da farko dai ina so nayi muku nasiha akan
zaman duniya, gaba d'ayanku nan musulmai ne,
kuma shi musulmi a duk inda yake ana so ya
zamto mai hak'uri da kuma juriya da kuma
imani, tabbas Faruk baka kyauta ba a wani
6angaren, amma kuma ina so ke Aminatu kiyi
hak'uri na tabbata yanzu Faruku yana sonki
bada wasa ba, kuma tunda ya fito fili ya fad'a
miki bai kamata kuma ki juya masa baya ba.
Don haka ina so kiyi hak'uri ki d'auki k'addara,
kuma komai na duniya mai wucewa ne, ki rik'e
mijinki kiyi masa biyayya don shine gatanki
duniya da lahira."
Meenah tace
"Nagode Baba, amma ni gaskiya bazan koma
gidansa ba, ya sauwak'e mini kawai."
Ba Faruk kad'ai ba hartta Baba sai da ya razana
da jin kalaman Meenah, Faruk sunkuyar da
kansa kawai yayi yana jin tashin hankalin da bai
ta6a ji ba.
Baba yana kallon Meenah yace
"Aminatu, kalamanki basuyi min dad'i ba, don
banyi zaton kamar ki mai ilimi da aiki da shi zai
furtawa mijinki haka ba, amma ina so ki sani
saboda gaba duk wani 6acin rai in zaizo miki to
kisan irin kalaman da zaki furta. Mijinki dai
mijinki ne. Sannan zancen ya sake ki ma bai
taso ba, idan ma ya taso sai kiyi tunani wa
kuma zaki aura? Maza majoritin mu halinmu a
rufe yake, kafin kuma ki gane halin sai kin zauna
da mutum.
Aminatu duk rintsi kiyi hak'uri ki zaunawa
aurenki, kedai ki cigaba da add'ua, duk wani
hargirsi idan ya taso a tsakaninku kok'ari zakiyi
wajen ganin kun zauna kun warware
matsalarku."
Ya gyara zamansa ya d'an yo gaba daga
jinginar da yayi, yayi ajiyar zuciya ya cigaba
"Kin bani kunya Meenah, ban ta6a tsammanin
haka daga gareki ba, ni kome Faruk yayi na yafe
masa, don haka kiyi k'ok'ari ki yafe masa kema.
Ki tashi ki fara shirin komawa d'akinki, Allah yayi
maku albarka ya kwa6e muku duk wata fitina."
Ya kai dubansa ga Faruk yace
"Allah ya jik'an iyayenka ya gafarta masu, ga
matarka nan sai a kiyaye gaba, ka kula da ita da
kuma kanka, kasan dai matsayinta yanzu, don
haka ka rik'e ta amana Allah yayi maku
albarka."
Yace
"Amin Baba, na gane kuskure na kuma insha
Allah hakan bazata sake faruwa ba, nagode
sosai insha Allah zan kula da Meenah, zan kuma
rik'e ta bisa amana da gaskiya."
Cike da farin ciki Baba yace
"Amin, zan shiga daga ciki na d'an kwanta."
Sukayi sallama ya fice.
Zarah ita da mijinta su sukayi mata rakiya har
gidanta da misalin k'arfe biyar da rabi na
yamma, suna nan har akayi sallar isha'i bayan
sunci abinci suka fara shirin tafiya, Zarah ta
k'ara yi mata fad'a sannan ta bita da nasiha,
sukayi sallama dasu suka shige gida suma.
Bayan ta shigo ta maida k'ofar ta rufe, yana nan
tsaye bakin k'ofa yana faman murmushi, ta
kauda fuskarta tace
"Ya dai?"
Yace
"Bacci nakeji my baby, amma inaso na fara yin
wanka kuma ke nakeso kiyi min da kanki, kinsan
na gaji da yawa rabona da bacci mai dad'i har
na manta."
Ta so ce masa bazatayi ba amma tuno da
nasihar Baba ya sanya bata musa ba ta bishi da
"To."
Ta kunna masa ruwan zafi da taimakonta ya
watsa, ta taimaka masa ya shafa cream mai
k'amshi shi kuwa duk wani motsinta akan
idonsa yake. Ta kammala ta tafi tayi wanka ta
fito sanye da kayan baccinta masu kyau da
kuma firgita tunani, sai zuba k'amshi take ya cije
lips d'insa na k'asa yace
"My baby, kullum k'ara chanza min kikeyi,
yanzun ma sai naga kinfi ko yaushe yin kyau."
Duk da taji dad'in kalaman nasa haka bai hanata
turbune fuska ba tana cigaba da linke kayansa
da ya cire yanzu.
Yayi murmushi ya mik'e ya jawo ta ta fad'o bisa
k'irjinsa yana kallonta cike da so da k'auna
marar misaltuwa, ita kuwa k'ok'arin k'wace
kanta ta shiga yi wanda ta kasa saboda irin
rik'on da yayi mata....
AUREN FANSA 45
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
# *WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-
FANS-459256761123035
# *http://maryamsbello.blogspot.com
_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan
neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon
zuwa Ameen_❣️
🌹45 🌹
Ya d'an yi tsai yana dubanta, ta kawar da
fuskarta gefe, yace
"My baby, ki tausaya min ki kula ni, idan har
kika za6i ki guje ni to wallahi rayuwata tana
cikin matsala, nayi laifi tabbas kuma na gane
kuskure na har ma na bada hak'uri, to meyasa
bazaki yafe min ba? Allah ma muna masa laifi
ya yafe mana bare mu mutane? Wallahi ina
k'aunar ki, da zaki bani dama da na nuna maki
hakan Meenah..."
Shirun dai ta kuma yi, yace
"To in bazaki yi magana ba, kiyi hak'uri ki saki
ranki, kin hak'ura?"
Ya shafi fuskarta yana mai juyo da ita, take tayi
k'asa da k'wayar idonta.
"Kinji ni baby? Ki tuna matsayina a gareki, na
baki hak'uri kiji tausayina don Allah Meenah. Da
me zanji? Kina fushi dani kink'i hak'ura, ke
kad'ai fa guda nakeda a halin yanzu, ina zansa
kaina Meenah? Please please! Tuba nake, na
tuba bazan k'ara ba, kar6i wannan takardar ki
gani abin farin cikin da ya same mu."
Ya zura mata takardun cikin hannunta, ta kalla
shek'ek'e ba tare da ta karanta ba ta mik'a
masa yace
"Yanzu har kin duba baby?"
Ta gyad'a masa kai, yace
"To me kika gani?"
Tace
"Oho!" Kalmar data ambata a ciki kenan ashe ta
fito fili, yayi murmushi yace
"Daman wannan takardar k'arin ilimi ne aka tura
ni na tsawon shekara biyu wanda zanyi shi a
k'asar ingila, shine nake neman shawararki
saboda karatunki."
Har ranta taji dad'in alherin da ya same shi
wanda ta tabbata yaga hakan a fuskarta
Sai kawai ta ce masa
"Na taya ka murna, sai dai duk yadda ka tsara
yayi min."
Yayi murmushi yace
"Alhamdulillah naji dad'i, sai dai inaga kamar
zamanki a nan don ki k'arasa karatun naki yafi,
amma zan rink'a waiwayanki, bawai natafi har
sai na kammal ba ne, a'a zan rink'a ziyartarki,
donma in banda ina son kiyi karatun da k'afata
k'afarki, yanzun ma idan kinfson mu tafi taren
sai mu ajiye shi gaba kya yi shi."
Ba tare da ta kalleshi ba tace
"Babu damuwa, kaje zan zauna."
Yayi murmushi yace
Ay da yake yanzu level 3 zaki shiga kinga dana
dawo kin kammala insha Allah, kinga dana dawo
sai mu baje soyayyarmu yadda ya kamata."
Tace
"Allah ya taimaka."
Haka yayi ta lalla6a ta kamar k'wai, sai wani
riritata yakeyi yana yi mata kalamai masu
tausasa zuciya har ya samu ta d'an sauko daga
dokin data hau har ma tana d'an kula sa.
Washe gari ne yayi shirin aikinsa, bayan ya
kimtsa ta raka shi bakin motarshi yace mata yau
da wuri zai dawo yaci abincin rana ta masa
amala da miyan ku6ewa d'anya, ta bishi da
"To." Da fatan dawowa lafiya.
Yana tafiya ta tashi tayi wanka ta kimtsa gidan
sannan ta hau mota tare da kud'in da ya bata ta
nufi kasuwa, ta siyo garin amala da k'ashin rago
da ku6ewa, tana dawowa ta fad'a kitchen ta fara
kacaniyar dafa abinci, k'arfe d'aya da rabi daidai
ta gama 1:30 pm, tana gamawa ta fad'a wanka
ta fito ta shirya cikin wata atamfa dark blue
d'inkin riga da skirt d'inkin ya zauna dabas a
jikinta.
Amma shiru ba alamunshi har wajen uku, ta
d'auko wayarta ta shiga neman layinsa nan ma
bai d'auka ba. "Oh God!" Ta fad'a tare da jefar
da wayar ta mik'e bisa doguwar kujera, sama
sama bacci ya ringa fisgarta tana k'in yi don
bata son baccin yazo.
Can wayarta ta fara ruri ta mik'e zumbur ta
d'auka yace
"Baby zan aiko a d'aukar min abincin nan don
meeting zamu shiga yanzun nan, idan nace sai
na dawo kafin na koma zan makara."
Tace
"Sai ka turo bakomai."
Ta mik'e ta had'a shi cikin basket, ta kira d'an
almajirinta Yusha'u tace
"Koda bacci zai d'auke ni idan wani yazo ka
d'auko basket bisa dinning ka mik'a masa."
Yace
"To Anty."
Ta koma tayi kwanciyarta. Itace bata tashi ba
sai k'arfe hud'u har da 'yan mintina, tashinta
yayi daidai da k'wank'wasa k'ofa, ta mik'e
zaune daga kwanciyar tana gyara d'aurin
d'ankwalinta, sannan ta mik'e tayi tattaki izuwa
bakin k'ofa gami da bud'ewa.
Wata budurwa ce sai dai ko ba'a fad'a mata ba
tasan yarinyar tana cikin matsala babba.
Ta bata izinin shigowa, ta koma kitchen ta had'o
mata kayan lashe lashe da tand'e tand'e, ta
koma ta zauna suka soma gaisawa a mutunce,
Meenah tace
"Baiwar Allah sai dai ban gane ki ba, sannan
meya faru da ke haka naga jikinki duk ciwo
haka?"
Maimakon budurwar tayi magana sai kawai ta
durk'usa har k'asa tare da fashewa da wani irin
kuka mai tsanani.
Meenah ta razana tana tambayar lafiya? Da
k'yar budurwar ta tsagaita daga kukan da takeyi
sannan ta fara magana cikin sanyin jiki.
"Mu talakawa ne tu6us, wanda har cin yau
yakan gagare mu, Allah yayi ma mahafina
rasuwa da jimawa, sai mahaifiyata, mahaifiyata
ita take fafutukar nema mana abinci da kuma
kud'in makaranta, ba irin aikin da batayi ba,
haka muka cigaba da rayuwa mahaifiyata itace
komai na, sai dai a kwana a tashi na had'u da
hatsabiban k'awaye wanda suke hure min kunne
har na biye musu na kai kaina a halaka!"
Ta share hawayenta ta cigaba.
"Nazo na fara fita lokacin dana ga dama na
dawo lokacin dana ga gama, tun mahaifiyata na
fad'an tana duka na har ta gaji ta bini da
addu'a, gashi bana jin maganarta, nabi na raina
ta ban d'auke ta a bakin komai ba, tasha yi min
kuka akan abubuwan da nake mata amma ni ko
a jikina, na had'u da samari 'yan k'arya suna
min wayau suna kaini hotel su bani kud'i, daga
nan idanuna suka ida bud'ewa gaba d'aya, bana
ji bana gani, sutura kuwa sai wadda na cire duk
akan idon mahaifiyata, har ta kai ta kowa
mahaifiyata bata iya fita unguwa, data fita za'a
fara nuna ta ana gulmarta.
Kwatsam wata rana sai na had'u da Jidda..."
Thursday, 14 September 2017
Maryam Saidu at 23:38
AUREN FANSA 46
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-
FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan
neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon
zuwa Ameen_
🌹46🌹
Da mamaki Meenah tace
"Jidda kuma? Meye mahad'inki da ita?"
Budurwar tace
"Nasan zakiyi mamakin idan na sanar da ke ni
ba kowa bace face Lubabatu wacce aka fi sanin
da Luby..."
Meenah ta mik'e tsaye a razane tace
"Luby? Kece haka?"
Luby da kanta ke k'asa tace
"Eh nice! Nice Luby aminiyar Jidda, ki zauna Zan
k'arasa bayani na."
Ta k'i zama still tana kallonta da mamaki, Luby
ta sake d'agowa tace
"Ki zauna don Allah ba don ni ba."
A hankali ta koma ta zauna tace
"Ina jinki." Luby ta cigaba
"Kamar yadda na fad'a miki a baya cewar na
had'u da Jidda a wurin bikin wata 'yar
makarantar mu da akayi, duk da ba ajinmu d'aya
da Jidda ba amma a ranar muka k'ulle muka
zama best friends. Nice sanadin lalalacewar
Jidda, ni na d'ora ta bisa gur6attaciyar hanyar
ita kuma ta bi, a tare muka cigaba da harkar mu
ta bin maza da sauransu. Nidai yanzu ba komai
ya kawo ni ba illa nazo neman gafararki, ba don
ni ba don Allah ki yafe min, nayi kuskure amma
yanzu na gane kuskure na, ki gafarce ni..."
Meenah tace
"No kar ki damu ni banida rik'o, kuma na yafe
maku, Allah ya tsare gaba, sai dai garin yaya
kika ji wannan ciwon haka a hannu?"
Ta kai dubanta ga hannun dake nad'e da
bandage gaba d'aya tace
"Wannan a ranar muka samu sa'insa da
mahafiyata akan ina so na fita da misalin k'arfe
takwas na dare, a lokacin mahaifiyata ta tashi
tace ita sam bazan fita ba, niko na dage akan
sai na fita sai dai ayi wacce za'ayi, na fad'a
mata maganganun sannan nayo hanyar waje, sai
dai daidai bakin k'ofa mahaifiyata ta tako da
sassarfa tana fad'in, Lubabatu idan kika sa k'afa
kika fita ban yafe maki ba, daga haka kawai ta
juya ta koma gida, ni kuma kawai naja tsuka na
fice abina ba tare da na damu ba. A ranar hotel
muka kwana bayan mun gama abinda mukeyi
muka zarce club, muna can har asuba, sai da
gari ya fara haske sannan muka fito don
komawa gida. Sai dai me? Muna kan hanya nida
saurayin nan nawa muna jin kid'a muna rawa a
mota ba tare da mun ankare ba muka yi had'ari,
shi saurayin nawa take ya cika ni kuwa asibiti
aka wuce dani rai a hannun Allah, sai dana
kwana bakwai ban farfad'o ba, bayan na farfad'o
naji likita na cewa sai an yanke min hannu, nayi
kuka nayi kuka, nayi bak'in ciki, nayi nadama ba
kad'an ba. A ranar nayi Allah wadarai da son
abin duniya gami da bijire wa iyaye, nidai cewa
nayi ban yarda ba, daga nan akayi wa hannuwa
na hotuna (Scan) kusan kala uku, gashi banida
kowa dole ni likitan yake tunkara da maganar.
Yace min k'ashin hannun ya lalace da yawa, ya
ratattake k'ashin, wato sai an yanke su, ido waje
na zaro nace
"Duka hannuwa na?"
Yace
"Eh to, zai iya yiwuwa dukansu amma gaskiya
hannu d'aya yafi samun dameji wanda idan aka
d'auki lokaci zai iya ru6ewa, zamuyi iya
k'ok'arinmu muyi miki 'yan dabaru a shi d'ayan
hannun, idan Allah ya taimaka sai ya zauna.
Sannan abu na biyu wurin yin 'yan bincikenmu
mun gano kina d'auke da wannan cutar wato
cutar H.I.V AIDS."
Luby ta d'an dakata saboda kukan da yaci
k'arfinta, haka itama Meenah sai da tayi
hawayen, Luby ta cigaba.
"Wani abu naji ya sokeni a k'irji kamar an sara
mani mashi, kuka nakeyi tamkar raina zai fita,
gaba d'aya duniyar da abinda ke cikinta sun fitan
min a rai, likita ya zayyano min kud'in aiki wato
gaba d'aya miliyan biyu harda rabi, kaina ya
d'auki chaji sosai, nace su sallameni na tafi na
samo kud'in aikin sai na dawo. Suka sallame ni
nayi gidanmu, na tarar da mahaifiyata tana
ganina ta razana tana tambayar meyasame ni,
na koro mata bayani, tayi ta min fad'a tace ita
ba ruwanta dani don haka na tafi na nemo kud'in
da kaina daman na saba neman kud'i, ta koro ni
na fito ina kuka. Babu wadda ta fad'o min rai
kamar Jidda, nasan ko bata bani kud'i ba zata
taimakeni da shawara, sheyasa na taho nan."
Meenah ta kalli Luby kallo na k'urilla sannan
itama ta koro mata nata bayanin.
"A gaskiya Luby idan har kud'in aiki kike nema
sai dai kije ki nemi taimako kamar su gidan
radio, wurin manyan k'asa, sannan Jidda da kika
zo nema bazaki same ta ba, saboda Jidda dai ta
haukace."
A razane tace
"Ta haukace kuma?"
Meenah tace
"Eh ta haukace, a ranar da kuka je wurin boka
amso maganin da zaku sa min ta saka min ya
koma mata, tun daga wannan ranar ta fara
hauka tana tona muku asiri, yanzun ma zancen
da nake miki ana can ana hadaniyar fidda ta can
k'asar waje neman magani. Luby wato ita
daman duniya haka take, duk yadda ka d'auke ta
haka zata zo maka, tabbas kin tafka babban
kuskure a rayuwarki, waya ce miki iyaye abin
wasa ne? Musamman uwa, kin wulak'anta
uwarki ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Kin bi
boka ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Kinyi
zina ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Shekara
da shekaru kina shayar da mahaifiyarki gubar
6acin rai, ke ba yarinya ba ak'alla zaki kai
shekaru ashirin da shidda yanzu a yadda nake
kallonki, yaci ace yanzu kina gidan mijinki kina
bautar Allah amma kin tsaya shashanci,
shekarunki sun kai ace kinyi hankali ki gane halin
da duniya ke ciki, abinda yafi miki kije ki rungumi
mahaifiyarki ki nemi gafara, ki mata biyyaya
sannan ki gyara rayuwarki tun kafin ki koma ga
mahaliccinmu. Ina so ki maida komai kamar
tafiyar ruwa ki kuma tari gaba, ki yarda da
kaddara mai kyau ko marar kyau, wallahi Allah
gafurur Raheem ne, kuma insha Allah nima zan
taimaka miki da wani abin, cikin gadon
mahaifina zan baki wani abu sai ki k'ara cikin
kud'in aikin da za'ayi miki."
Ta bud'e baki cike da mamaki sai kuma hawaye
suka fara wanke mata fuska.
"Meenah, nagode! Nagode Allah ya saka da
alkhairi, Allah ya k'ara bud'i, Allah ya jik'an
iyaye yayi mana gafara, bani da bakin da zan
gode maki, na bibiyeki da sharri ke kuma kin
saka min da alkhairi, haka rayuwa take daman
ko wannan ya ishemu ishara."
Meenah tayi murmushi
"Kar ki damu, bakomai wallahi ai yiwa kai ne,
wannan ba wani abu bane."
Tana kallo Meenah ta mik'e ta shiga d'aki, ba'a
jima ba ta dawo hannunta d'auke da paper, ta
zauna tana mik'a mata.
"Gashi."
Tasa hannunta mai d'an lafiyar ta kar6a tana
kuka, Meenah tace
"Yanzu shiga ta na kira Faruk, na masa bayani
shine yace na k'ara miki shima ya bayar." Luby
ta duba tace
"Har dubu d'ari uku? Kai nagode Allah ya k'ara
bud'i."
Meenah tace
"Wannan ba abu bane ba babu damuwa, Allah ya
k'ara tsare mana imaninmu, ya tsare mu daga
fad'awa halaka, Allah ka shirye mu ya ganar da
mu."
Luby tace "Amin ya Rabbi."
Luby bata tafi ba sai da Meenah ta bata abincin
rana tana mai k'ara mata fad'an ta nemi yafiyar
mahaifiyarta, a haka ta bar gidan tana mai
jinjina al'amarin.
BAYAN SATI BIYU
****
Ranar wata talata, tana zaune taji horn d'in
motarsa, ta mik'e cike da mamakin ganin ya
dawo da wuri, ta lalla6o ta fito don tun jiya bata
jin dad'i. Ta k'arasa wajensa sai fara'a yakeyi
yana mata murmushi itama tana tayasa duk da
batasan dalilin farin cikin nasa ba. Ta kar6o
jakarsa suka jero har parlor ta dire jakar ta
d'auko masa ruwan sanyi a fridge ta tsiyaya
masa ta bashi.
Bayan ta zauna tace
"Lafiya ka dawo da wuri yau?"
Ya kuma dubanta yace
"Lafiya lau, tafiyar nan ce ta taso wai jibi jibin
nan zamu tafi, kin tuna maganar da mukayi a
baya ko?"
Tace
"Eh na tuna."
Yace
"To itace yau abin ya ida tabbata."
Tace
"Masha Allah, yanzu jibi zaka tafi?"
Yace
"Insha Allah."
Tace
"Zaku dad'e kenan?"
Yace
"Da shekara biyu zamuyi amma yanzu insha
Allah bazai wuce shekara d'aya ba mun juyo,
kuma in mun dawo zamu iya samun chanjin aiki
da kuma k'arin girma. Yanzu ma so nake naje
na shaida masu Dada maganar kuma ke nakeso
ki raka ni."
Ta d'an yamutsa fuska tace
"To amma fa ni bana ma jin dad'i."
Ya zaro idanu yana k'are mata kallo, yace
"Kodai abin arzik'in ne ya samu?"
Tace
"Me kenan?"
Yaja hancinta yace
"Kinfini sani, amma banga ta zama ba tashi
zakiyi mu tafi asibiti a auna ki don a tabbatar."
Kafin ma tayi magana ya zura mata hijabinta
pink color tare da jawo hannunta suka nufi
mota.
Ba k'aramar murna Faruk yayi ba da yaji daga
bakin likita cewar ciki ne da ita har na kusan
wata biyu, tun da suka shiga mota yake washe
hak'ora kamar gonar auduga.
‹ › Home
View web version
Thursday, 14 September 2017
Maryam Saidu at 23:39
AUREN FANSA 47/END
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-
FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan
neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon
zuwa Ameen_
🌹47 🌹🔚
A ranar sukaje wajen Dada, ya dad'e yana sa
masa albarka tare da fatan dacewa, sannan ya
ce lallai lallai sai ya bashi takardar Jidda don
data warke ya mik'a mata, yasan dole zata koyi
hankali. Haka Faruk ya rubuta ya mik'a ma
Dada, haka ma Mama tayi masa fatan dacewa
da sanya albarka. Daga nan suka wuce gidansu
Meenah ya shaida ma Baba, Baba ya bishi da
doguwar addu'a ya sanya masa albarka.
Sai dai tun ana gobe zai tafi hankalinsa ya tashi
bai ta6a tunanin daidai da kwana d'aya zaiyi
nesa da Meenah ba gashi har za'a shafe watanni
bai ganta ba, yana shigowa d'aki a lokacin tana
kwance kan gado ya zauna gefenta yace
"A gaskiya Meenah bazan iya tafiya na barki ba,
kawai kiyi hak'uri ki shirya mu tafi tare." Ta juyo
tana dubansa tace
"Nidai jeka ka barni, ina nan gida Nigeria bazan
iya binka ba a yadda nake jina d'innan."
Ya tur6une fuska ya shiga zayyano mata
matsalar da zai shiga idan bata bishi ba, har da
cewa tayi differing semester d'in mana idan suka
dawo sai ta gyara. Da k'yar ta lalla6a sa yayi
hak'uri ya barta, amma idanunshi sun kad'a
sunyi ja, haka itama ta wuni tana kuka har bacci
yayi awon gaba da ita. A daren ranar Meenah
taga tarairaiya kamar wata k'wai, ya dad'e yana
shayar da ita zuma kafin kuma suyi bacci mai
dad'i.
Washe gari ya fara shirin tafiya, kafin ya tafi sai
da ya nemo mata wata mata dattijuwa da zata
zauna da ita har ya dawo, haka suna ji suna
gani sukayi bankwana har airport ta kaishi, sai
data ga tashin jirginsu sannan ta dawo zuciyarta
na k'una ta rasa meke mata dad'i.
Haka ta kwana tunaninsa har ciwon kai ya
sauko mata wanda kafin safe zazza6i mai zafi
ya rufe ta, sai da tayi ta shan magaunguna
sannan ta samu taji sauk'i.
Shi kuwa gogan naka yana sauka masaukinsa
dama ya siya sabon sim, yana sawa ya kirata,
bugu biyu ta d'auka.
"Hello."
"Baby ya nake jin muryarki can k'asa ko jikin
ne?"
Ta lumshe idanu tace
"Eh to zazza6i ne yake d'an damuna amma da
sauk'i."
Ya rude ya shiga mata tambayoyi.
"Kinsha magani? Yanzu meke miki ciwo? Ya kike
ji yanzu?"
Tayi murmushi
"Wallahi yanzu kam bana jin komai sai kasala,
so ya hanya? Ya kuma gajiya?"
Yace
"Alhamdulillah, gani nan na sauka masaukina
yanzu zanyi wanka sai na kwanta na huta."
Tace
"Ai gara kayi bacci kam, sannu."
Yace
"Yauwa baby, kema sannu."
Sun dad'e suna fira kafin suyi sallama, kowane
yana jin kewar d'an uwansa.
Meenah ta cigaba da karatunta cikin kwanciyar
hankali, kullum cikin missing Faruk takeyi sai dai
kullum suna mak'ale a waya suna fira basa
gajiya da junansu.
Sun cigaba da zumuncinsu itada Zarah kusan
kullum suna ziyartar juna, haka ma Anisah wacce
ke fama da tsohon ciki itama tana k'ok'ari wajen
ganin tana zumunci dasu Meenah.
****
BAYAN WATA BAKWAI
Meenah na zaune a parlor tana cin guava kamar
a mafarki taji horn, ta yunk'ura da k'yar ta lek'a
ta window ganin motar haya ya sanya ta fara
mamakin ko waye?
Bata gama mamaki ba sai data ga ana fiffido da
akwatina daga boot, gabanta ya fad'i batayi
tsammanin ganinsa yanzu ba, yayi wani kyau
yayi k'iba sai k'yallin hutu yakeyi. Ga k'asumbar
nan tasha gyara sai walk'iya takeyi.
Ta lalla6a ta fito bakin k'ofa daidai nan ya
k'araso yana murmushi, take ya ware
hannuwansa duka biyun alamun ta iso gareshi.
Ta dafe cikinta daya turo gaba tare da sunkuyar
da kanta k'asa, yayi murmushi tare da takowa
daf da ita sannan ya rungume abarsa tsam tsam
kamar za'a k'wace masa ita don ma tulelen
cikinta ya hana shi ya rik'e ta sosai.
Ya sumbace ta a goshi yana dubanta yace
"Wow! Baby cikinnan fa yayi miki kyau sosai."
Ya k'arasa yana kashe mata ido d'aya, tayi
murmushi, ta zum6uro baki cikin shagwa6a tace
"Shine zaka taho ban sani ba?"
Yayi dariya
"I'm sorry baby, just wanted to surprise you
daman."
Hannunta ya rik'o suka k'arasa ciki, ta taimaka
masa ya rage kayan jikinsa yana ta zolayarta
wai yanzu ta zama k'atuwa ko tafiya da k'yar
takeyi, ita dai sai dariya takeyi. Bayan ya huta
kuma ya shiga bubbud'e akwatina yana fiddo
mata tsarabarta, kaya ne mak'il akwati guda na
kayan baby wanda babu abinda babu a ciki, kaya
masu kyau da tsada, sai akwati guda nata
wanda ya k'unshi leshi, atamfa da su kayan
bacci da kayan kwalliya da sauransu, tayi murna
tayi ta masa godiya ba adadi.
A ranar dukkansu sunyi kwanan farin ciki da
kuma kewar juna.
Washe gari sai ga Jidda itama ta warke ras,
tazo neman gafara kuma duk sun yafe mata,
tace ta samu mijin aure, sun taya ta murna da
fatan alkhairi inda har Faruk yayi mata
alk'awarin bata tasa gudumuwar.
A kwana a tashi ba wuya wurin Allah yau Allah
ya sauki Meenah da misalin k'arfe biyu na dare,
Faruk yana tare da ita har ta haifi santalelen
d'anta k'ato mai k'oshin lafiya, bayan an gyare
shi tas aka mik'a ma Faruk shi sai kallonsa
yakeyi cike da sha'awa, ya sumbati kumatun
Meenah yace
"Wane suna zamu sa masa?"
Tayi murmushi tace
"Duk sunan da kaga ya dace dashi ka sa masa."
Yayi masa hud'uba da sunan mahaifinsa wato
Adam amma za'a ringa kiransa da Khalifa.
Ranar suna anyi taron suna lafiya kuma ya
k'ayatar mai jego tayi fes da ita tana sanye cikin
wani golden lace sai k'yalli takeyi kamar wata
amarya.
Mai jego da d'anta sun cigaba da samu kulawa
sosai a wurin Faruk, ga yalwatar arzik'i
musamman da akayi masa k'arin girma kud'i
sun zauna masa sosai, hakan yasa Meenah ta
bashi shawarar ya gina masallaci ya kuma ringa
bada tallafi a gidan marayu, ba k'aramin dad'i
shawarar nan tayi masa ba, yayi tasa mata
albarka yana jin dad'i.
A haka har sukayi arba'in inda ta cigaba da
karatunta a lokacin ne kuma ita Zarah ta haifi
d'iyarta mace sun sha suna babyn taci sunan
mahaifiyar Nabeel wato Sadiya, za'a ringa ce
mata Nasreen.
A yanzu su Meenah har sun kammala karatunsu
suna jiran result.
****
Zaune take tana shayar da Khalifah Faruk ya fito
daga d'aki da alama bacci ya tashi, yana zuwa
ya rank'wafo yana sumbatar kanta, yace
"Zo muje na baki wani abu."
Ta mak'ale kafad'a alamun a'a tace
"Nak'i wayon, nasan dalilin da yasa ka kirani."
Yayi murmushi yace
"A'a fa result d'inki zan nuna miki."
Da sauri ta aje Khalifah ta mik'e tsaye tana
murmushi tace
"Da gaske? Mu je nagani."
Ya wuce tabi bayansa suna shiga yasa ma k'ofar
key yana dariya k'asa k'asa, tace
"La daman wayau zakayi min ko? Ni gaskiya ka
bud'e min na fita."
Yace
"Nak'i, ga key d'in zoki k'wata."
Ta nufo sa ta fara k'ok'arin k'wace key d'in
aikuwa ya damk'e ta yace
"Wana kama?"
Ta fara kukan shagwa6a tana fad'in.
"Wayyo my soul, mun bar Khalifah shi kada'ai a
parlor fa kar yayi kuka."
Yace
"To tsaya mu nema masa k'anwa sai ki tafi."
Tace
"Nidai a'a."
Yace
"Aiko baki isa ba."
Ya fara k'ok'arin zage mata zip da k'yar tayi
nasarar k'wace kanta tana ta faman dariya sosai
sannan ta d'auki pillow ta jefe shi da shi har
yanzu bata bar dariya ba. Nufo ta yayi ya chafke
ta yace
"Zan baki punishment, kina jifan mijinki."
Kafin tayi magana ya had'a bakinsa na nata....
ALHAMDULILLAH!!!
Alhamdulillah da Allah ya nuna min farkon book
d'innan da k'arshensa lafiya! Darasin dake ciki
Allah ya bamu ikon d'auka, kuskuren da ke ciki
Allah ya ka yafe mana.
Godiya ta musamman ga dukkanin masoya na
da wanda na sani da wanda bansani ba kusani a
duk inda kuke ina k'aunarku.
Fatan alkhairi ga duk wani mai karanta novel
d'ina, Allah ya bar zumunci Amin.
Daga k'arshe ina mai bak'in 😭😭cikin sanar da
masoya na cewar zan dakatar da rubuta 😭😭😭novel
zuwa wani lokaci bisa wasu dalilai wanda basai
na fad'e su ba da fatan masoya na zasuyi min
uzuri zasu kuma fahimce ni, nagode da k'aunar
da kuke nuna mun nima kusani ina k'aunar ku a
duk inda kuke.😘
0 comments:
Post a Comment