Balkisu Na daf da kammala brkfst dinta sai ga Hafeez yafito daga cikin d'akinsa sanye da farar jallabiya d'akin Balkisu yayi niyyar zuwa har yanufi hanya kmr ance yajuyo sai hango Balkisu yayi zaune cikin falo, wata irin sassanyar ajiyar zuciya yayi wanda hakan yajawo hnkli Balkisu tajuyo, Hafeez tagani tsaye sakar masa murmushi tayi tana fadin Yaya har kafito?
A hnkli Hafeez yaqarasa cikin falon tsare Balkisu yayi da idanunsa sannan yace Balkisu inakikaje ne tundazu dana farka nanufi d'akinki amma bakya ciki? Kuma nalura dake acikin kwanakin nan kina yawan fita ina kike zuwa?? Balkisu shiru tayi gabadaya tarasa amsar da zata bashi.
Ganin bata da niyyar cewa komai yasa Hafeez yanemi waje yazauna qara kallon Balkisu yayi fuskan nan ba alamar wasa yace "ke badake nake mgn bane kinmin shiru?
Balkisu gabanta ne ya shiga dukan tara tara bama uku uku ba sbd kalaman da bakinta ke qoqarin furtawa batasan yadda yayan nata Hafeez zai d'aukesu ba, a hnkli tad'ago kanta tadubi Hafeez da raunatattun idanuwanta cike da faduwar gaba Balkisu tafara mgn cikin sanyin murya
"Yaya kagafarceni amma yazama dole ne intunkareka da wannan mgnr dukk da bnsan da wacce irin siga zaka kalli batuna ba, Hafeez yayi murmushi gabad'aya jiyayi Kansa yakulle domin kuwa yasan cewa qanwar tasa da wani abu mai muhimmanci take tafe, tunanin haka ne yasa Hafeez yadubi Balkisu cikin sigar lallashi yace oyaa qanwata go on ke nake saurare kifadamin dukkanin damuwarki namiki alqawarin zan magance miki ita matuqar bata fi qarfina ba.
Da sauri Balkisu tace yaya insha allahu baifi qarfinka ba, sannan zanfadamaka damuwata amma matuqar zaka biyamin buqatartawa nikuma nayimaka alqawarin zanyimaka dukkanin wani Abu dakake so matsawar bai keta addini ba, Hafeez ya jinjina kansa ganin cewa qanwar tasa seriou take mgn yasa yayi saurin cewa OK jst tell namiki alqawarin biyamiki dukk wata buqatarki matuqar bai keta addini ba. Balkisu tayi murmushi tace yayana bai sa6a addini ba asalima addini ya horemu da aikatashi kuma bayan haka idan har ka aikata hakan nikuma xankasance cikin farinciki har abada.
Jin Balkisu tace haka yasa Hafeez yace "okay sanar dani inajinki matuqar zaisaki farinciki.
Balkisu tace "tunda kamin alqawari zanfadamaka sannan karkayi tunanin in nafadamaka zaka bijirewa buqatartawa, cike da qaguwa Hafeez yace "go on kenake saurare.
Miqewa tsaye Balkisu tayi gamida tad'auke dubanta ga Hafeez a hnkli tace yayana inasone Dan Allah ka janye BURINKA nacewa bazaka tabayin aure ba, sbd ina buqatar ganin wata diya macce a cikin gdan nan matsayin matarka hakan zaisani farinciki matuqa Kuma.....! Kafin Balkisu taqarasa abinda take son fadi tuni Hafeez yataka mata burki ta hanyar daka mata tsawa keeee!! Balkisu rufemin bakinki awajan kinsan mekike fada kuwa? Ina mai gargad'inki dakiyi saurin janye wannan buqatartaki kicanja wata domin ina tabbata miki cewa wannan din bata samu shiga ba.
Da qarfi Balkisu ta fashe da kuka kmr wacce aka aikowa mutuwa, Hafeez kam gabad'aya jiyayi hanklinsa yatashi domin azahirin gaskiya bayajin zai iya biyama qanwartasa wannan buqatar domin kuwa tsakani na da macce sai idanuwa "cewa Hafeeez" wannan kuka da Balkisu keyi gabadaya yatada hnklin Hafeeez da sauri ya qarasa gareta yace "kiyi shiru plsss bnson kisawa kanki ciwon kai, Balkisu tajanye hannunta daga riqon da Hafeez yayi mata
Shiru Hafeez yayi ganin qanwartasa fushi take dashi yasa ya sassauto murya a hnkli yace "plsss Balkisu u have to understand cewa bana son aure bana buqatar kasancewa da kowa, nan gaba kad'an aurenki zakiyi hakan ma kawai ya isheni da zarar kinfara hayayyafa yaranki sun isheni sani farinciki sannan idan kinduba Bal....dasauri Balkisu tadakatar dashi cikin muryan kuka tace yaya wannan ba reason bane sbd kaikanka kasan cewa bani da saurayi hasalima baka bari Na kula kowa toh wakake tunanin zai aure ni har wadannan BURi naka sucika Wanda ka lissafo ynxu?
Da sauri Hafeez yace nima sanin kanki ne cewa banida wacce nakeso waxan aura waxan so? Dasauri Balkisu tace wlh yaya believe me idan nacemaka nasamo maka mata nagartacciya Na yarda da tarbiyyan yarinyar akwai nutsuwa da hnkli attare da ita, dasauri Hafeez yakauda knsa hace "a ina kikasanta?" Balkisu murmushi tayi gamida cewa tabbas Yaya zaka Santa amma baxan fadama ko ita wacece ba har sai ka amincewa buqatata, Yaya Hafeex karkamanta cewa kaine uwata Kaine ubana Ashe kenan dama akwai watarana da uba zai kasance yabar yarsa cikin maraici da quncin rayuwa?
Jin Balkisu tace haka gabadaya hankli Hafeez yatashi, dasauri ya 6ullo mata ta wata hanya yace "naji I will accept ur condition sai dai Inaso kisani cewa hakan zaifarune idan har yaxamto cewa kema kinsami mijin aure sannan xan amincewa buqatarki"
Dasauri Balkisu tajuyo a firgice tace "Yaya wakake tunanin zai soni har ya aureni?"
Jisukayi anbud'e labulen falo a hnkli yaqarasa ciki hannayensa sanye cikin aljihunsa cikin sassanyar muryansa yace gani.
Muje zuwa donji wanene yashigo musu gda kai tsaye gamida amsa cewa shine zai auri Balkisu.
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣2⃣
A tare suka juya gabad'aya, Dr Muh'd suka gani tsaye murmushi ya sakar musu da sauri ya k'arasa ciki yace "am swry ban muku sallama ba afuwan Assalamu alaikum" miqawa Hafeez hannu yayi sukayi musabaha, can kuma falon yayi shiru nad'an wasu daqiqa gabad'ayansu kowa da abunda yake tunani cikin zuciyarsa' Dr Muh'd ne ya katse shiru ta hanyar cewa "tabbas Hafeez najima inason Balkisu a zuciyata sai dai na 6oye ne sbd ganin cewa baka bawa kowanne d'a namiji damar tunkarar taba, a haqiqanin gsky soyayyar da nakeyima Balkisu tawuce dukk inda kake tunani domin soyayyar Balkisu tayi tasiri acikin xuciyata Wanda hakan yasa nakasa ganin kowacce irin macce da daraja a idanuna, sannan a kullum sai nayi niyyar tunkarar ka da zancen amma sai zuciyata ta haneni.
Shiru Hafeez yayi gami da dafe kansa gabad'aya jiyayi hnklinsa ya tashi domin kuwa a ynxu shi Kansa yasan bai da tacewa kasancewar Dr Muh'd abokine ga gareshi yasan koshi shi waye yakuma san halinsa Sannan yasan waye zuri'arsa.
Balkisu kam dukk kunya ta isheta gabad'a jitayi kmr qasa tabud'e tashiga.
Dr Muh'd ne yace "abokina idan ka amince min inaso kabani auran Balkisu, Hafeez kam jiyayi kmr ya d'aura hannu aka, da sauri ya qirqiro murmushin dole ya dubi Dr Muh'd cikin sigar zolaya Hafeez yace ashee kai ragon likita ne maitsoran macce? Dr Muh'd yace la! la!! la!! Ae ni ba Balkisu nake tsoro ba yayan Balkisun nake tsoro, gabad'aya dariya sukayi Hafeez yad'an bugi kafad'ar Dr Muh'd yace kai dai bawani.
Dr Muh'd yakoma cewa "nidai babban yaya kai nake saurare kabani Balkisu? Hafeez yad'anyi murmushin yaqe sannan yadubi gefen da Balkisu ke zaune tayi shiru ta duqar da knta tana wasa da yatsun hannunta, sannan yasake maida dubansa ga Dr Muh'd yace "of cox y not da bazan baka ita ba amma nifa karkayi tunanin zanma qanwata dole" bari ynxu intashi inbaKu waje kud'an tattauna idan kunfahimci juna ta amince toh falillahil hamdu inkuwa har bata amince ba toh bana tunanin nima zan amince ko nayimata dole".
Hafeez nafadin haka ya tashi yakoma daga cikin d'akinsa dan basu waje sud'an tattauna
A hnkli Dr Muh'd yatashi daga inda yake yakoma gefen Balkisu cikin tattausar muryansa yad'an duqa daf da ita yace "toh Balkisu miye ra'ayinki agame da tayina ko ince buqatata? Balkisu kam dukk kunya ta isheta qara duqar da kanta qasa tayi,murya na rawa kmr wacce zatayi kuka tace " a'a ni ina ganin baidace na amsa tayinka ba domin kuwa wani 6angare na sashin zuciyata nasanar dani cewa kawai tausayina ne aranka da kuma son taimakamin ganin cewa Yaya Hafeez yayi aure matuqar nima nayi.
Da sauri Dr Muh'd yace ko kusa Balkisu karki kawo wannan gur6ataccen tunanin cikin zuciyarki, wlh soyayyarki ta gsky ce acikin jini da 6argona yakamata ace tuntunima kinfahimci hakan wlh Balkisu believe me when I said banta6a son wata d'iya macce ba kmr ki ina miki wani irin so Wanda ni kaina yana bani tsoro plss kitaimakawa zuciyata nan yashiga yimata magiya
Ganin yadda ya marairaice fuska kmr zaiyi kuka yasa Balkisu tace "to shikenan na amince ku gama mgn da yaya Hafeeez tana fadin Haka ta tashi da sauri tashige d'akinta gami da banko k'ofa direct gadonta tafad'a tanajin wani irin nishad'i marar misaltuwa na shigarta.
Abangaran Dr Muh'd kuwa hannu yad'aga sama yana jero adduo'i na farinciki da nuna tsantsar godiyarsa ga ubangiji, yana gama addu'ansa d'akin Hafeez yanufa yayi knckn Hafeez ya amsa yes shigo jiki narawa Dr Muh'd yashiga cikin d'akin wani irin farinciki da nishad'i yake ji nashigarsa da sauri ya rungumi Hafeez yace " yes abokina adduar danajima inayi yau Allah ya amsamin Balkisu ta amince ynxu amincewarka kawai nake jira.
Murmushi Hafeez yayi cikin zolaya yace congrat namaka murna, ynxu kabari idan muka gama tattaunawa da ita Balkisun zankiraka awaya muqarasar da mgnr, Dasauri Dr Muh'd yace "wacce mgn za'a gama ae ynxu angama komai tunda madam ta yarda ynxu kawai izininka nake nema sbd ina so inturo magabata na, Hafeez kam jiyayi gabansa yafad'i da sauri yace olryt karka damu I will giv u a call let
Cike da zumud'i cikin fara'a Dr Muh'd yabar gdan.
Hafeez kam gabad'aya yashiga damuwa jiyayi wani irin rashin sukuni ya ziyarcesa Dan haka da sauri yanufi d'akin Balkisu dan yanuna mata cewa shikam bai amince da wannan chakwakiyar ba.
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [3:11AM, 7/27/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣3⃣
A hanzarce Hafeez yanufi d'akin Balkisu don ya nuna mata rashin aminciwarsa akan wannan tsarin deal din da takawo mai cike da rud'ani, a hnkli ya murza kofar d'akin jin bud'e take yasa yashige d'akin kaitsaye turuss ya tsaya cike da mamakin ganin Balkisu cikin wani yanayin dabai ta6a ganinta ba.
Balkisu kwance take ta kife cikinta ta yayin da tad'an d'aga kafafunta tana lilasu earpies ne a kunnenta tana merming waqa cike da nishad'i" soyayyaa tayi mamaya tayi charaf ta chafkemin zuciya nasamu saurayi madubin duba inata murna" murmushi Hafeez yayi gabad'aya ji yayi jikinsa yayi sanyi a hnkli yafice daga cikin d'akin batare da tasani ba, falo yakoma yazauna gabad'aya tunanin mafita Hafeez Yake nemawa kansa amma dukk hnyar dayabi sai yaga cewa ya tauye dukk wani farinciki na qanwartasa, kan Hafeez yagama kulewa gabad'aya jiyayi bashida wata mafita ko dubara domin kuwa BURIN HAFEEZ shine yaga tilon qanwar tasa cikin farinciki dan haka komai xai iyayi dukk runtsi dan ganin ya inganta farincikin Balkisu.
Take anan Hafeez yakira layin Dr M yasanar dashi cewa yanason ganinshi zuwa gobe, Dr M yayi farinciki dajin wannan kira dan haka addu'a kawai yyi yana maifatan Allah yakaimu goben.
Abangaran Balkisu kam wani irin sabon yanayi taji nashigarta kasancewar dukk wunin ranan nan suna maqale da juna awaya ita da gwarzon likitan nata.
** ** **
Balkisu ce zaune cikin motarta tana zaman jiran dawowar Meena daga talla kasancewar yau Monday ta je skul shiyasa bata samu damar zuwa wajan Meena da wuri ba sai ynxun.
Balkisu ta6ata kimanin awa biyu zaune cikin mota sai zabga uwar hamma takeyi, agogon dake d'aure bisa tsintsiyar hannunta take dubawa qarfe daya saura a hnkli tasauqe wata irin ajiyar zuciya, kmr ance d'ago kanki ae kuwa chan tahango Meena tafe da bokatin alalarta.
Dasauri Balkisu taja motarta cikin sauri taqarasa wajan Meena a hnkli tayi parkn motarta daf da Meena, zuge glass din motar tayi a hnkli cikin rashin karfin gwiwa takira sunan Meena, da sauri Meena tajuyo ganin Balkisu ce mai kiran nata yasa tayi saurin niyyar barin wajan, da sauri kuwa Balkisu tafito amotarta gamida shan gaban Meena cikin raunatacciyar muryanta tace Meena plss ki dakata kisaurareni koh da sau d'ayane daga wannan baxan sake takuramiki ba namiki alqawari, zuwa ynxu gabad'aya Meena tagama tsorata da Balkisu jiki na 6ari Meena tace Dan Allah baiwar Allah ki kyaleni haka naroqeki da sauri Meena ta ratsata gefenta da nufin ta wucewarta, cikin sanyin jiki Balkisu tace "olryt Meena kije karki saurareni amma na tabbata kinfi kowa muradin son ganin mahaifiyarki tafito a gidan kaso, da sauri Meena tajuyo fuskarta d'auke da mamaki qarara.
Murmushi Balkisu tayi tace " yes Meena nasan komai a gameda lbrinki babu wani 6oye 6oye ynxu daya rage a tsakaninmu, wlh kiyarda dani banida niyyar cutar dake hasalima nidake nakeson muhad'a kai mutaimaki juna, Meena tamaimaita abinda Balkisu tace mutaimaki juna??
Kmr ya mutaimaki juna? Balkisu tace "kwarai kuwa,kuma hakan nidake gabad'aya zai amfanemu, Murmushi Meena tayi tace " anya kuwa kinyi dogon nazari akan wannan maganar taki? Balkisu tace ae ynxu kece zanbaiwa damar yin tunani akan mgnr danaxo muki da ita.
Meena ta gyara bokatin alalarta ta fuskanci Balkisu tace" okay fadi mgnr naji Allah yasa zan iya" Dafa kafad'arta Balkisu tayi cike da qarfin gwiwa tace no karki damu insha allahu hakan bazai gagareki ba.
Balkisu tadubi Meena tace inba damuwa inason kizo mushiga daga cikin mota ta hakan zaifi sirri, dasauri Meena tad'ago tadubi Balkisu, Balkisu tamaqe kafad'a tace yadai ko dai har ynxu baki gama yarda dani bane? Meena ta girgiza kanta tace a'a ba haka bane mujee.
Cikin motar Balkisu suka shiga Meena jitayi wani irin sanyi yaratsata a hnkli tadubi Balkisu tace inajinki kiyi sauri kada namakara. Balkisu tadubi Meena sannan tad'auke dubanta daga gareta tafuskanci gabanta, Sannan takira sunan Meena bayan Meena ta amsa sannan tasake cewa kinsan menake so dake? Meena ta girgiza kanta tace a'a sannan Balkisu tajinjina kanta a hnkli tasauke idanunta akan Meena tace "so nake ki auri yayana, da sauri Meena ta gwalo idanu waje gamida dafe kirji tace mekikace? murmushi Balkisu tayi domin batayi mamakin ganin Meena tayi shock dajin buqatarta ba, Balkisu tajinjina mata kai tace tabbas abinda kikaji shinafad'a inaso ki auri yayana domin inason ganin sauyi da farinciki a tattare dashi, da zaran kinyimin haka nikuma nayi alqawari konawa ne zankashe domin na d'aukaka qara ganin cewa Mahaifiyarki tafito daga gdan yari, sannan inaso karki manta cewa nasan komai agamedake basai kinyimin wani dogon bayani agameda matar babanki ba namiki alqawarin zanji da komai kedai kawai nabaki nan zuwa gobe kije kiyi tunani
Gobe da yamma zandawo domin naji shawaran dakika yanke. Balkisu nafadin Haka tabudewa Meena qofa cikin sanyin jiki Meena tafice daga motar yayin da Balkisu kuma ta wuce tanufi gda nan tabar Meena tsaye cikin tunani.
Note: akan masu complain cewa banason yin typn da wuri inaja muku rai, wlh sam bahaka bane karku manta fa cewa nabaku uzurina plss kumin afuwa insha allahu zanqoqarta nagode.
®NWA
[11:54AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣4⃣
Cikin daren ranar Meena kasa runtsawa tayi, babu abinda take tunawa sai ranar da tafara had'uwa da yayan Balkisu irin yadda yanuna mata kyankyami da tsantsar tsana qarara a fuskarsa, dan haka tasan tabbas a zaman auransu xata cutu sai dai kome xainuna mata xa ta iya shanyewa sbd lura da tayin da bashine da kansa yaxo neman auranta ba hasalima qanwarsa yaturo to komiye dalilinsa nayi haka? Nan fa tafara jeroma kanta tambayoyi wnda ita kanta batada amsarsu.
A ynxu kam gabad'aya tunanin Meeena yatafi akan yadda rayuwarta zata kasance a hannun wanda bai ko kaunar ganinta gashi kuma a wani 6angare tana buqatar mahaifiyarta kusa da ita, Dan haka ta gama yanke shawaran amincewa auransa don tasamu damar taku6utar da mahaifiyarta daga gdan kaso.
Da wannan shawaran aranta har bacci 6arawon yayi awon gaba da ita.
** ** **
Washe gari
kafin kowa ya tashi a gdan Meena tariga kowa tashi kmr yadda tasaba, bayan ta idar da sallah ne tafara ayyukanta kafin qarfe 6 kuwa Meena tagama ayyukan ta tsaf, ruwan sanyinta tad'iba tashiga bayi ta watso ruwa, bayan tafito ne tadauki tallan kunun gyad'anta tanufi chan Bolori primary skull inda chan ne Meena zata had'u da Balkisu.
A bangaran Balkisu kuwa ita ma sauri kawai take tayi sbd bata son ta had'u da Hafeez kasancewar tasan sai yayi ta jero mata tarin tambayoyi akan wacce take son had'ashi aure da ita, gashi ita kuma basu gama mgn da Meena ba Dan haka bata da kwakkwarar amsar da xata bashi, hakan ne ma yasa tayi tunanin tad'aga appointmnt dinsu wnda tace su haduwa da yamma tamai dashi zuwa da safe.
Kafin Hafeez yafito kuwa tuni Balkisu tafice a gdan, Bolori primary skul chan tanufa a niyyarta dama intaje tasa yara sunemo mata Meena tunda dama nan ne wurin sana'arta, Balkisu nashiga skul din ba tawani sha wahalan neman Meena ba hangota tayi zaune ta rafka uban tagumi.
Meena! Meena!! Kmr a mafarki taji ana kwala mata kira dasauri tayi firgigit ta juya, Balkisu tahango zaune cikin motarta dasauri Meena tamiqe tanufi wajanta.
Murmushi Balkisu ta sakar mata sannan suka gaisa da junansu daga bisani tayi mata ixinin shiga cikin motar, a hnkli Meena tabud'e murfin motar tashiga.
Jan motar tayi cikin nutsuwa suka bar gefen makarantar chan wata anguwa suka nufa, sai da Balkisu ta tabbatar sund'anyi nisa sannan tayi parkin, Da murmushi d'auke a fuskar Balkisu ta dubi Meena tace "toh Meena kmr yadda kikaji nace miki zanxo domin naji shawaran dakika yanke toh gani nan na iso gareki don jin shawarar da kika tsaida shin kin amince kuma kinshiryawa auran yayana??
Meena ta sadda kanta qasa hawayene kawai keta kwaranya cikin sanyin murya tace na amince da auransa matuqar xankasance tare da mahaifiyata. Balkisu tajinjina kai tace dakyau amma kinsan dalilina nason ki auri yayana? Meena ta girgiza kai alamar a'a
Ajiyar zuciya Balkisu tayi sannan tamaida dubanta ga Meena gabad'aya idanun Balkisu sunrine izuwa ja! Cikin natsuwa takawo lbrin rayuwarsu tasanar da Meena, nan Meena tashiga jinjina al'amarin cikin zuciyarta tana mai tausaya musu sai dai kuma yadda taji lbrin Hafeez ta tabbata cewa kawai tad'auko ma kanta dala ba gammo ne amma kuma inta tuna mahaifiyarta sai taji wani irin kwarin gwiwa na shigarta.
Balkisu tadubi Meena tace tabbas na yaba da kyawawan d'abi'unki da yadda kika iya maida mgn ga masu hali irin na yayana hakan yasa na tabbata cewa zaki iya dawo min da Yayana normal kmr yadda yake a lkcin baya.
Murmushin yaqe Meena tayi sannan tadubi Balkisu tace "Allah dai yabani ikon cikamin alqawarinki sbd naga kinsa hope dinki akaina sosai, Balkisu tad'anyi yar dariya tace "Meena kikwantar da hnklinki kedai kawai kisa aranki daga gobe zuwa jibi muna iya xuwa a kowanne lkci gdnku dan neman auranki sannan inaso kada kifadawa kowa wannan mgnr har sai komai yakankama, cike da jin kunya Meena tace insha allahu.
Meena har tabud'e kofar motan da niyyar tafita Balkisu takira sunanta, cikin natsuwa Meena tajuyo.Balkisu tace " aff namanta intambayeki yau mekike sai dawa ne? Meena tace kunun gyad'a ne.
Balkisu tad'anyi murmushi kmr yadda hakan yaxama jiki agareta sannan tace" gabad'aya kunun na nawane? Meena tace na d'ari biyar ne zaro dubu biyu tayi ajakarta tamiqawa Meena sannan tace gashinan kiyi sadaka dashi haka har zuwa gobe kiyi manejin wannan bnfito da kud'i bane.
Da farko Meena tanuna kin amincewarta sai da Balkisu tad'an lallamota sannan tasamu ta ansa.
Direct gdan mallan Zakiru Balkisu tanufa don cika alqawarinta kmr yadda tafada mishi cewa dukk halin da ake ciki agame da Meena xataxo tasanar dashi (mgnr lectures kam yau bbu ita)hakanan ta juya akalar motarta izuwa gdan mallan Zakiru.
®NWA
[1:14PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:37AM, 7/29/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣5⃣
(Very sorry readers nayi mistake din numbr nasa 23 sau biyu makin nasa 24 nayi mistk ynxu 25 xamu tashi)
Kamar kullum yau ma ya kasance mallan Zakiru na nan cikin Zaurensa yana bitar karatu alqur'ani, da sallama Balkisu tasa kai cikin zauren tare da neman izinin shiga, cikin nutsuwa Mallan Zakiru yakai qarshen aya sannan ya rufe qur'anin ya ajiye agefensa, cikin sakin fuska yayi mata Iso
Mai d'akinsa mallan Zakiru yashiga yakira dan takawo masa taburma, Inna takawo taburman tana qoqarin shimfid'awa Balkisu tayi saurin amsa ta shimfid'a tabarman, bayan ta xauna sannan suka gaisa sannan Inna, ficewa Inna tayi tabasu waje kmr yadda tasaba in mallan yayi baqi bata zama.
Balkisu tadubi Mallan Zakiru fuska d'auke da murmushi kai dagani kasan tana cikin farinciki, "tace Baba kmr yadda na sanar dakai cewa dukk yadda ake ciki a game da Meena zansanar maka wato naafad'a mata inasone ta auri yayana ynxun nan muka gama mgnr da ita sannan ta amince zata aureshi nikuma nayi mata alqawarin bayan bikinsu zanfito da mahaifiyarta a gdan yari.
Mallan Zakiru yyi murmushin jindadi yace "Masha allahu' Allah sarki Aminatu allah ya sanya alkhairi, Balkisu ta amsa da ameeen daga bisani Mallan Zakiru yadubi Balkisu fuska d'auke da damuwa yace "amma kmr yaushe ne kike xaton zaku turo magabatan ku don neman auran Aminatu?
Balkisu tace "toh baba muna so mu tsaida ranan ne tukun, mallan Zakiru yajinjina Kansa sannan yace toh wacce shawara kika yanke agameda tunkarar Yagana don niman auran Aminatu?
Balkisu tace Baba karka damu inaso ne in angama ajiye mgn d'aya zamu turo qanin mafaifinmu sbd in.... kafin Balkisu ta qarasa abinda take son cewa Mallan Zakiru yace "Sam kada kiyi haka sbd dukk cikin garin nan bbu wnda baisan waye mahaifinku ba nikuwa nafi kowa sanin cewa muddin Yagana tagano cewa Aminatu gdan masu hali zatayi aure toh fa baxata amince ba.Sbd dukk wata hanya da tasan zatabi don ganin cewa ta lalata wannan auran toh fa zatayi Kuma babu wnda ya isa yadakatar da ita, Dan haka inaso kibar komai a hannuna sannan kitabbatar da cewa cikin qanqanin lkci zakusa lkcin auran don gujewa fitina.
Balkisu tad'anyi jimm! Sannan tadubi Mallan Zakiru sannan tace amma Baba kana ganin ta wacce hanya zamu bi? Mallan Zakiru yyi murmushi yace zansamo wani daga cikin kauyanmu inyimata nuni da cewa shine Wanda yakeson ya auri Aminatu amma fa dukk wani wakili ko waliyi Na ango zaifito ne daga 6angaranku. Nan Mallan Zakiru ya tsatssara ma Balkisu matakin da zasubi don gujewa sharrin Yagana
Kwarai da gaske Balkisu taji dadin shawarwarinsa ae kuwa nan tayi taxu bawa Mallan zakiru godiya, tana mainuna jindadin taimakonsa gareta.
** *** ** ***
Qarfe hud'u Na yamma na bugawa Dr Muh'd na isa gdnsu Balkisu don cika umarnin Hafeez kmr yadda yabuqaci ganinsa.
Hafeez kam yau through out bai ko fita bakin get ba yana nan cikin d'akinsa yana sana'ar tashi wato tunani, kwan kwasa k'ofar dayaji anayine yadawo dashi daga duniyar tunanin da yatafi, a hnkli yamiqe batare da yace komi ba yanufi k'ofar bud'ewa yayi Dr Muh'd ne yagani tsaye cikin dakakkiyar shaddarsa mai kyan gaske sai wani zuba qamshi yakeyi, Hafeez yadubi Dr Muh'd har yaso yabashi dariya sai kuma yabasar hannu yamiqa masa suka gaisa sannan Hafeez yace dashi yaje Falo yad'an jira gashinan zuwa
Dr Muh'd kam cike da zumud'i ya nufi falo yazauna dan jiran Hafeez
Toilet Hafeez yashiga ya sakarwa kanshi ruwa yajima a haka daga Bisani kuma ya silla wankansa, qananan kaya Hafeez yasaka blue riga da baqin wando dukk da cewa Hafeez baifiye son qananan kaya ba amma yau su yaji yana muradin sawa turare mai dadin gaske ya fesa sannan yafice a d'akin.
Falo ya nufa kaitsaye yana shiga kuwa ya tarar da Dr Muh'd na nan zaune yana jinran fitowarshi, murmushi Hafeez yayi ya girgixa kansa.
Bayan sund'an tattaba hira sama sama' Hafeez ya dubi Dr Muh'd jiki a sa6ule yace "amm abokina wato dalilin da yasa nace kazo ina neman ka yau shine inason inji daga gareka shin kashirya auran Balkisu? In kashirya wa auran inaso nan zuwa gobe kaje chan sabon fege gdn uncle Ma'aruf kasanar dashi dukkan wani jawabi dakake tafe dashi akan auran Balkisu.
Hafeez nafad'in haka ya sadda kanshi qasa cike da damuwa da qunar zuci, dasauri Dr Muh'd yamatsa kusa dashi a hnkli ya dafasa yace "tabbas abokina nasan kana cikin damuwa da alhenin rabuwa da tilon qanwarka amma kasani zaman Balkisu a gurina tamkar tana hannunka ne insha allahu nayimaka alqawari baxan ta6a cutar da qanwarka ba, zan riqeta amana tamkar kaine awajan sbd inason Balkisu sosai inayimata so Wanda baxan iyaganin abinda zai cutar da ita ba.
Da sauri Hafeez yarungume Dr Muh'd yana kukan farinciki sannan yace "nagode maka abokina sannnan inaso kasa aranka cewa Balkisu amanace a hannunka sannan inaso idan zaiyuwu a d'aura auranku cikin wani sati if possible"
Dasauri Balkisu taqaraso cikin falon fuskan nan sha6e sha6e da hawaye cikin muryan kuka tace haba Yaya Hafeez aure na nikad'ai nakeji kana mgn banji kana mgnr naka auran ba, karka manta da alqawarinmu sbd nariga nasamo ma nagartacciyar mata Wanda nake da hope din cewa zata kularmin da yayana yadda yakamata.
Rasss! gaban Hafeez yafad'i, shidai bai San mieyasa Sam baya qaunar yaji anyi mishi mgnr wata d'iya macce ba, balle kuma harta kai ga mgnr aure.
Jiki a sanyaye Hafeeez ya maida dubansa ga Balkisu yace "wai wacece wannan yarinyar dakike son Na aura wacece ita a ina kika santa ya akayi kikasan tana da nagartaccen hali meyasa kike son tilastani nayi aure?' a jere Hafeez ya watsoma Balkisu tambayoyi?"
®NWA
[1:15PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:52AM, 7/30/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣6⃣
D'ago Jajayen idanunta tayi Wanda suka rine sbd kuka, a hnkli ta sauk'esu akan Hafeez, wani irin kukane ya sake kubce mata Wanda ita kanta batasan dalilin yinsa ba, cikin dishashiyar muryanta tace "Yaya Hafeez karka ta6a tunanin cewa auran wacce nakeson had'aku zai zama cutarwa ko danasani a gareka wlh kayarda dani cewa nafi amincewa auran Meena atattare da kai" Meena!! Hafeez yamaimaita sunan da sauri k'urawa Balkisu idanu yayi gabad'aya sai yaji tabashi tausayi, gashi akan wannan Meenar da ta dage dole ne yaga cewa yadaure ya aurenta mutuqar hakan zai sata farinciki da walwala.
Dasauri ya miqe tsaye daga zaunen da yake jawota yayi jikinsa ya rugumeta nan yashiga bubbuga bayanta cikin sigar lallashi, cikin murya qasa qasa Hafeez yace kwntar da hanklinki Billyn mama na amince zan auri dukk wacce kika kawomin ita matsayin matar aure, amma sai dai I have one request 4 u, k'ura mishi idanu Balkisu tayi alamar shi take saurare dasauri ya janye jikinsa daga nata sannan yaci gaba da mgn "na amince zan auri yarinyar da kikeson kawota cikin rayuwata sbd inada yaqinin cewa bazaki ta6a had'ani da wacce bata dace da rayuwata ba, sai dai kuma inaroqonki plss kada kitilastamin zuwa d'aurin auren sbd hnkli da kwakwalwata bazasu iya jurar ji ko ganin cewa wai yau nike aure ba plss kisamu komawaye ya wakilceni sannan dukk abinda kikaga yadace kawai kiyi nabar miki wuqa da nama" Hafeez nafadin haka yayi sauri yabar falon cike da d'acin rai.
Jikin Balkisu gabad'aya yayi wani irin sanyi, a hnkli Dr Muh'd yaqaraso gareta cikin muryan lallashi mai nuna tsantsan tausayi ga masoyiyar tashi, nan fa ya xage damtse yayi ta tausar zuciyar cikin hikima da kwarewa, sai gashi kuwa cikin qanqanin lkci ta manta da komai.
A Bangaran Hafeez kuwa d'aki yashiga ya kulle kansa ji yayi gabad'aya duniyar tamasa xafi.
** ** ** ** **
Kmr yadda Mallan Zakiru yayi ma Balkisu alqawari haka kuwa akayi yaje can qauyansu yasamo wani matashin saurayi dake aikin faskare.
Abangaran Dr Muh'd shima yaje yasamu ya gana da qanin mahaifinsu Hafeez, wato uncle Ma'aruf, uncle Ma'aruf kam bayan binciken daya qarayi akan hallayan Dr Muh'd yasamu kyakkyawan yabo hakan yasa ya amince domin yafi kowa farinciki dajin lbrin. Dan haka cikin qanqanin lkci aka sanya lkcin bikin Hafeez da Balkisu
Mallan Zakiru da kansa yaje har wajen Yagana yasanar da ita cewa d'an uwansa ne Wanda yaxo daga qauyansu yaga Meena yakuma nuna cewa yana son auranta, Yagana tayi farin ciki jin ancemata daga noma sai faskare sune aekinsa koshi faskare da noman aekatau dinsu yakeyi ana biyansa dan haka kenan su Meena za'a sha noma wani irin farin ciki ne ya lullu6eta datagama wannan tunanin, Dan haka batare da 6ata lkci ba tanuna amincewarta.
Mallan Zakiru yyi matuqar farin ciki da hakan domin kuwa hakarsu daf take da cimma ruwa.
Komai ya kankama yan'uwa da abokan arziqi anfara hallara, gwaggwanin su Balkisu da mamaninta dukk sunzo nan suka fara gyara diyar tasu Balkisu tafito fasss da ita baqaramin kyau tayi ba.
Bangaran Yagana da yarta kuwa kullum basu da aiki sai gori da kyarar Meena wai tarasa Wanda xata jaju6o musu sai d'an kauye kauyan ma futuk nan fa zasu taru suyita dan gware tama kai.Meena kam ko uffan bata cewa dasu domin ita tunaninta a kullum bai wuce yadda zata kasance a wani gda a matsayin matar wani ba,sabuwar rayuwar da zata shiga kullum shike addabar tunaninta.
Plan din Mallan Zakiru da Balkisu komai Na tafiya yadda suke so da taimakon ubangiji.
RANAR DAURIN AURE
Ranar juma'a da misalin qarfe biyu na rana bayan ansauqo a masallaci aka d'aura auran HAFEEZ ABDULLAHI SHARIFF tare da AMINATU SULEIMAN akan sadaki dubu hamsin, inda kuma suka sake garzayawa aka sake d'aura auran BALKISU ABDULLAHI SHARIFF tareda DR.MUHAMMAD SHU'AB GASHU'A an d'aura auransu akan sadaki dubu d'ari.
***
Dubu uku Mallan Zakiru yacira daga cikin sadakin Meena yakaiwa Yagana yace gashinan wannan shine sadakin Aminatu, zokaga farinciki awajan Yagana nan fa ta sokare kud'in a ha6ar zaninta
A cewar Yagana tunda Meena takala futuk ta aura to miye zata siyamata tunda dai d'an kudin da Meena kesamowa yaqare a kudin hayarta dan haka baxata siyamata komai ba.
Da misalin qarfe hud'u na yamma Mallan Zakiru ya je gurin Yagana wani tsadadden material da sarqa da yan kunne da takalmi da kyale set komai yayi match kayan sun matuqar haduwa, Balkisu ce ta aikomishi tace yabawa Meena idan anzo d'aukar amarya tasanya ajikinta. Hakan yasa Mallan Zakiru yakawo kayan dan ciki alqawarinta.
Yagana naganin kayan dake hannun Mallan Zakiru dukk tabi tawani rud'e, miqa mata kayan yayi yace "Yagana ga wannan kayan daga hannun mijin Aminatu sukafito yace dan Allah atabbatar da tasa wannan kayan zuwa an jima sannan kisanar mata cewa kartabari kokadan kayan sulalace sbd arosu yayi daxarar ta isa gdnshi ciresu xatayi yamaidasu inda ya aro, wata irin dariyar k'eta Yagana tafara dukk farinciki yabi ya lullu6eta.
Hakanan akayi shagalin biki a bangaran Balkisu da Dr dinta, sa6anin Hafeez wnda ya kulle kansa cikin d'aki.
Misalin qarfe tara na dare wasu irin manya manyan motoci tsadaddu ne sukayi fakin a k'ofar gdansu Meena, da sauri wata gwaggonsu Hafeez tashiga gdan Cikin shiga ta kece raini dukk da kasancewar dare ne amma shigar da tayi kallo d'aya zakayimata kasancewa an narka daloli.
Yagana kam tabawa Aminatu kayan tasa baqaramin kyau sukayi mata ba, ganin tayi kyau abinta yasa Yagana dukk haushi ya isheta nan tashiga dangwarar kanta tanayimata gori sai wani kusheta takeyi.
Ana cikin hakane Gwaggon Hafeez Hajiya Nana tashiga domin tafiya da Meena.
Ae kuwa gabad'aya kan Yagana yad'aure shuru kawai tayi tana kallon ikon Allah azatonta dukk wad'annan manyan matan suma hayarsu akayi, al'amarin bai qara tsinkar da Yagana ba sai da tabisu zuwa waje taga wasu irin dan qara dan qaran motoci Wanda sune suka zo d'aukar amarya Meena. Yagana tanaji tana gani aka sanya Meena cikin mota sakeke tayi da baki cike da mamaki domin ita takasa gane wannan Al'amarin jitayi andafata da sauri ta juya Hajiya Nana ce cikin sigar lallashi take lallama Yagana domin ita a tunaninta Yaganan tana cikin alhenin rabuwa da diyarta ne, nan taciro dubu hamsin tamiqawa Yagana. Cikin mota takoma sukaja take anan sukabar cikin unguwar.
Yagana na ganin haka ko gyale babu a jikinta balle takalmi haka tanufi gdan Mallan Zakiru cike da masifa domin kuwa bakin nan nata taf yake da tambayoyi Wanda babu mai amsamata su sai Mallan zakiru.
®NWA
[1:15PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:47AM, 7/30/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣7⃣
Jiki Na 6ari haka Yagana ta shiga gdan Mallan Zakiru ko sallama babu ta afka musu cikin gda, dai dai lkcin Mallan Zakiru yafito daga bayi hannunsa riqe da buta yana kiran mai d'akinsa ta kawo mishi abinci, Mallan Zakiru sai ji yayi ance "toh algungumi munafiki azzalumi mai sai da yaran mutane" da sauri Mallan Zakiru yajuyo danganin mai mishi wannan alkaba'iran Yagana yagani tsaye ko mayafi babu balle takalmi ta wani riqe qugu sai huci take kmr zakanya, murmushi Mallan Zakiru yayi domin kuwa bai yi mamakin ganinta ba don yatsammaci haka.
Mallan Zakiru yadubi Yagana yace "toh ynxu kuma Yagana wanne laifi nayi haka da har nacancanci ki biyoni gda da masifa?
Yagana ta gyara tsayuwa cike da masifa tace "ae kuwa kace dani haka tunda ka gama rainamin hankli wato ashe sai da Meena kayi? Kafadamin suwa kasayarwa da ita a nawa kasaidata? Mallan Zakiru yayi murmushi cike da dattijantaka yace "akan naira dubu uku kacal kuma suma kudin suna hannunki, kinga kenan ashee bani kad'ai naci ribar sai da Aminatu ba.
Nan fa Yagana tabud'e murya tana tadajijiyoyin wuya ita alafurr adawo mata da Meeena, Mallan Zakiru kam yau dukk jiyayi lamarin Yagana ya kai mishi mak'ura wata uwar tsawa yabuga mata wnda tayi sanadiyyar shiga natsuwarta.
Sheqeqe Yagaña tayi tana bin mallan Zakiru da kallo cike da mamaki, Mallan Zakiru yadubi Yagana cikin tsananin fad'a yace "wlh kedai tirrr Allah wadai da hali irin naki Yagana wlh ina mai tabbata miki cewa kiyi gaggawar canja halinki kiji tsoran haduwa da mahallicinki domin kuwa a kodayaushe lkci yana iya kuremiki.
"Dama mai kika d'auki kanki? Kind'auka cewa ke kadaice kike da kwakwalwa da tunanin yadda zaki cutar da wani toh kisani dama irin wannan lkcin nakejira, najima inatunanin ta yadda za'ayi Na ku6utar da Aminatu daga hannunki sai gashi Allah maji roqon bawansa ya amsamin addu'ata da najima inayi akan yabani ikon da zankubutar da Aminatu sai gashi yakawomin hnya mafi sauqi, kuma bari kiji infad'amiki Aminatu dai na gdanta ma'ana gdan mijinta bakuma zanfadamiki inda take ba balle kije kitada musu qayarbaya sbd jahilci irin naki.
Gwalo idanu waje tayi tadubi mallan Zakiru tace "Zakiru nice jahilar"? Mallan Zakiru yajinjina kansa yace"kwarai kuwa" Nan fa Yagana ranta yaqara 6aci cikin tsananin fada tashiga nunashi da d'an yatsa tace "wlh kajira kaga abinda xai biyo baya wlh dani kake mgn" Mallan Zakiru yace "ae shi sharri kare ne kuma mai shiyake bi insha allahu babu abinda xan gani sai alkhairi, kuma indai aminatu ce tayi aure a babban gda gdan dasuka san darajar mutum, gdan da inhar keda zuri'arki zasuyi shekara goma kuna tara dukiya bafa zaku iya sayen koda karen gdan ba, balle kiyi tunanin zuwansa" Mallan Zakiru nafadin haka Yagana tayi kwaf ta kad'akai tafice a gdan cikin tsananin fuskata.
"Mtsssw aikin banza kawai yarinya kin grma bakisan kingirma ba, baki da wani aiki sai tunanin kanki da ahalinki nawa rayuwar duniyar take da zaki d'auki son duniya kid'aurawa kanki" Inna dai natsaye bata ce komai ba, sai bayan da komai yalafa sannan suka zauna yake bata lbrin dukk abin da yafaru.
Innah taji dad'i sosai da jin wannan lbrin.
** ** ** ** ** ** **
A bangaran Amarya Balkisu kuwa gabad'aya famlyn ango sun hallara don d'aukar amarya, amma Balkisu tace sam batasa Xancen ba, ita bbu inda zataje har sai ankawo Meena cikin gdan ta sadata da yayanta sannan, babu irin lallashin da basuyi ba amma furrr taqi amincewa a dole suka hkra suka zauna zaman jiran isowar matar Hafeez.
Ba'awani jima ba kuwa sai ga yan d'aukan amarya sun iso, hakanan Hajiya Nana ta lullu6e fuskar Meena akashiga da ita cikin gdan, Bayan sun gama bud'arsu da shewarsu ne Balkisu tazo da kanta taja hannun Meena suka shiga d'akinta don suyi mgn.
Meena kam tun isarsu gdan babu abinda take sai kuka daga ita har Balkisu babu mai ba wani hkri, dakyar Balkisu tasamu tayi controlling din kanta sannan tashiga roqon Meena da ta kular mata da yayanta nan Balkisu tashiga fad'awa Meena abinda Hafeez yafiso da wanda baya so.
Meeena kam sai kuka takeyi kmr ranta zai fita, hakanan Balkisu tagama fad'amata dukk abinda yakamata sannan takama hnya har zata fita sai tajuyo tace "Meena Dan Allah kikasance mai juriya da hkri kmr yadda nasanki sannan ynxu da zarar hidimar bikin nan taqare xancika miki naki alqawarin" tanafadin haka tashare hawayenta tafice a d'akin.
D'akin Hafeez Balkisu tanufa nan ma wani sabon kukan tasha, wannan karon hadda Hafeeez shima yazama tamkar wani qaramin Yaro sai kukan yakeyi, Balkisu ta d'ago da jajayen idanunta tadubi Hafeez tace "plsss yaya ka kula da Meena kmr yadda kake kula dani hakan zaisani farinciki, girgiza mata kai kawai yakeyi batare da yace komai ba.
Dakyar Anty munnawara matar uncle ma'aruf ta 6an6are Balkisu daga jikin Hafeeez, sai kuka sukeyi gabad'ayansu.
Hakanan Hafeez yanaji yana gani akatafi da Balkisu gdan auranta.
Wani irin k'unci yakamaji Wanda hakan yasa ciwon xuciyarsa ya tashi dakyar yasamu yasha magani ya kwanta.
Meena kuwa Hajiya Nana takaita asalin d'akinta Wanda ya kasance mallakinta, d'akin kam ya matuqar had'uwa da tsari komai tsaf tsaf nacikin d'akin.
Hakanan kuwa Meena tanemi gado ta kwnta wani irin karkarwan d'ari tashigayi ga knta da yake tsananin sara mata sbd ciwo, nan tadunqule waje d'aya ga wani irin azababben tsoro daya dinga shigarta kmr ta shid'e.
®NWA
[1:15PM, 10/15/2016] My Nabss: [12:57AM, 8/1/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣8⃣
Dukk addu'ar da tazo bakin Meena ita kawai take karantowa, runtse idanuwan tayi sosai bata ko k'auna bud'esu sbd tsananin tsoro, yayin dashi kuma gogan nata ke d'akinsa kwance yanata sharar bacci sakamakon magungunan daya d'irkawa cikinsa.
A bangaran Meena kam dak'yar tasamu itama baccin yayi awon gaba da ita daf da asuba, dan haka bata wani samu ishashen bacci ba, hakanan ta daure ta nufi toilet alwala tad'auro sannan tazo tagabatar da sallah.
Bayan ta idar da sallah ne tarafka wani uban tagumi cike da damuwa,
Misalin qarfe takwas na safe Meena ta tashi tanufi falo sbd wata irin yunwa da taji ta gallabeta har wani irin duhu duhu take gani dakyar tasamu tafita koh Allah zaisa ta samu abinda tasawa cikinta.
Koh da fitar Meena Daniel tagani yanata zirga zirga tsakanin kitchn da dinning area, shiru tayi tana binsa da kallo domin ita dai batasan ko waye shi ba.
Meeena na nan tsaye kmr wadda aka shuka, Daniel ne yasake fitowa daga cikin kitchn a karo nabiyu hannunsa dauke da flask din ruwan zafi kmr ance ya waiga sai ganin Madam yayi a tsaye kmr wata marar gaskiya, ae da sauri ya ajiye flask din ya qaraso gareta cike da grmamawa yace gud murng madam, kintashi lpy? Cike da mamaki Meena ta amsa lpy kalw, sannan Daniel yace ni sunana Daniel nine ke kula da store room Na gdan nan da kuma kitch, gyad'a kai kawai Meena tayi hankalinta dukk yana wajen dinning area ita dai burinta tasamu abinda taci.
Ganin hakane yasa Daniel yace am swry 4d disturbn u madam, d food is ready da sauri yaqara kan dinning din nan yafara bud'e mata abubuwan da ya girka kala kala, Meena kam riqe baki tayi cike da mamaki tadubi Daniel tace "Daniel dukk suwaye zasuci wannan abincin? Daniel yace "madam boss ne yace ake girka enough abinci yadda kowa zaici ya qoshi", Cikin zuciyar Meena tace uhumm boss kodai runbu irin wannan almubazzaranshi haka.
Sinasir da miyan allayahu shine kad'a Meena taga zata iyaci Dan haka d'aukan plat kawai tayi Daniel ya taimaka mata tazuba abincin, d'aukan plat dinta tayi ta koma falo domin jitayi bazata iya zaman dinning table dinba, zamatayi sosai tafara bawa cikinta haqqinsa.
Hafeez kam yau baqaramin makara yayi ba wurin tashin sallah sai qarfe bakwai da rabi ya farka a gaggauce yashiga toilet yadauro alwala, yana gama idar da sallah yakoma toilet din yayi wanka yazo yasake shiryawa tsaf abinsa, sai wani sauri yaketayi kmr wanda xaitashi sama yau dai Hafeez ko za6en kayan sawanshi bai tsayayi ba sbd yau bashida niyyar wuni acikin gda balle abokan wasanshi suzo su sami damar takura mishi, Qarfe takwas da rabi nayi Hafeez har yagama shirinsa.
Meena kam har tagama cinyye sinasir dinta, wani qatoton qashi ta tsaya gwaigwaya sai faman ko kuwa takeyi dashi, tana cikin wannan halin ne sai ga Hafeez yafito daga d'akinshi cikin sauri sbd baya so ya hadu da wannan Meenan da Balkisu ta d'aura mishi nauyin da bazai iya cikawa ba.
Hafeez nafito wa cikin harban falo wata yarinya yagani tayi zaman dirshan tanata faman ko kuwa da qashi, wani irin abune ya tsaya awuyan Hafeez domin shi arayuwansa yatsani yaga anacin abinci da hannu balle kuma ita wannan ga dukkan alamu dambe takeyi da qashi.
A fusace Hafeez yanufi falon yana xuwa yace "ke dabbar ina ce miye hakan? Wacece ke ? Wannan wanne irin qazanta ne?"
Meena kam batayi tsammanin da mutum tsaye kusa da ita ba, tsawa kawai taji andoka mata Wanda ya mugun razana ta har qashin hannunta ya su6uce ya fadi😂 da sauri taduqa tad'auki qashinta tamiqe tsaye gamida juyowa domin Meena kam tuni tagane mekiranta da dabba sunan, shi din ne kuwa tagani tsaye fuskan nan a turbune babu alamar wasa acikinta.
Wani irin shock Hafeez yashiga ganin wannan fitsararriyar yarinyar agabanshi domin kuwa har abada baxai manta wannan face din ba, da saurinshi kuwa ya zaro idanu cike da mamaki yace "ke wat ar u doing here? Meya kawo ki cikin gdana? Meena kam quramishi ido tayi gabanta sai bugun tara-tara yake, nan fa Hafeez yafara kiran Daniel! Daniel!! Daniel!!! da qarfi Hafeez ke kiranshi kmr wanda yaga dodo agabansa. Dagudu Daniel yaqaraso yace "yes boss am here" Hafeez yanuna Meena da hannu yana kallon Daniel yace "Daniel who's dis girl?" Daniel ya yadubi Meena wacce ke tsaye hannu riqe da qaton qashinta wani yawu Daniel had'iye cike da tsoro domin shi baisan wacce irin amsa xaibawa boss din nashi ba, dominshi a tunaninsa koma wacece ai shi zai fisa saninta... Daniel!!! Da qarfi Hafeez ya koma kiransa cikin fushi yace "I'm not tlkn to u"? Who's dix girl? Daniel ya sadda kai qasa yace boss I think she is ur wife, amma nibensashi ba fa.
Meena kam tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, Hafeez yadubi Meena up and dwn yace cabb badai wannan abar itace matata ba?
Meeena naganin Hafeez xai wuce gona da iri kawai ta ratsa tagefenshi tawuce kitchn ta ajiye plat din sannan ta wanko hannunta.
Dasauri tanufi d'akinta ta banko kofa, ganin tashiga cikin d'akin nan ya tabbarwa kansa cewa lallai wannan yarinyar itace wadda aka had'ashi da ita? Tabbb juyawa Hafeez yayi izuwa d'akinshi take yaji yafasa fitar da yayi niyyar yi.
Dakinsa shima ya shiga da sauri.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:53AM, 8/1/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣9⃣
Kai da kawowa Hafeez ya dingayi cikin d'akinsa gabad'aya jiyayi Balkisu tagama 6ata mishi rai sbd tarasa wacce zata hadasa dashi sai wannan fitsararriyar yarinyar wata qazama da ita yar qauye.
Wani irin haushin Meena yadinga ji, jiyayi kmr yaje yarufeta da duka.
Abangaran Meena ma haka abun yake d'akinta tashige tana zuwa tafada kan gadonta,nan tafara kuka wani irin haushin Hafeez da tsoransa ne suka tsayamata a cikin xuciyarta lkci d'aya cikin ranta tace "wato dai shi wannan uban masifan bashi da aiki sai cewa mutun dabba qyaattt" Meena tayi kwafa cike da jin haushinsa tace ae kuwa zan nunamaka halin dabbancin.
Tun daga wannan ranar Meena ta umarci Daniel da yake kai mata abinci cikin d'akinta, dan haka yasa ynxu kwata kwata Meena da Hafeez sunbar had'uwa dukk da cewa suna gda daya.
** ** ** **
BAYAN SATI DAYA.
Tuni Balkisu tad'auka qarara izuwa babbar kotu dake cikin jaharsu, da taimakon Dr Muh'd Balkisu ke gudanar da komai batare da sanin Meena ba.
Sai da akayi sati guda currr ana abu d'aya shari'ace aka gudanar inda Mallan Zakiru yazo takanas har kotu shida wasu sauran mutanen cikin anguwarsu, suka bada shaidan cewa lallai Yagana itace ta kashe d'anta.
Sbd irin kudin da Balkisu tanarkawa yan'sanda shiyasa sukaje har gdan Yagana suka suka titsa qeyar ta izuwa police station, nan fa suka shiga yimata horo na azaba kala kala akan lallai ta amsa laifinta na kisa, dakyar Yagana ta amsa laifinta ganin tana shirin shurawa zuwa lahira.
Bayan Yagana ta amsa laifinta ne kotu tayanke mata hukuncin d'aurin rai da rai a gdan yari tare da horo maitsanani kasancewar yadda tayi wasa da hankli hukuma.
Balkisu tayi farinciki da samun nasarar da sukayi, hakanan akafito da baba Rabi dukk ta wani tsufa ta rame ta d'an canja kammanu.
Sunanan tsaye mallan zakiru dasu Balkisu, yansanda sukazo wucewa da Yagana hannuta saqale da ankwa ana qoqarin wucewa da ita gdan yari. Dasauri Mallan zakiru yatsaidasu nan fa yayi tayiwa Yagana tuni akan abubuwan dasuka faru yace" ynxu dai gashinan kinga qarshenki (Allah yashiryi masu halin sonkai irin Na Yagana)
Baba Rabi kam sai godiya take ta jerowa Balkisu, daga bisani ne Baba Rabi ta dubi Balkisu tace "baiwar Allah ko zan iya sanin koke wacece"? Balkisu tayi murmushi cike da farinciki tace "baba karki damu zanfad'a miki koni wacece amma da farko inaso ki kwntar da hnklinki kinatsu sbd nima yarkice kmr Meena"
Da sauri baba Rabi tadubi Balkisu tace yan nan kinsan aminatu ne Dan Allah tana ina? Kiwa Allah kifadamin koke wacece INA aminatu Na dan Allah kitaimaka ki kaini gareta, Balkisu tace Baba kwantar da hanklinki ynxuma wajan Meena zankai ki yanzu insha allahu zakiga Meena, wani irin hawayen farinciki ne ya lullu6e Baba Rabi.
Kofar wani katafaran gda Baba Rabi taga anyi parkn, cikin girmamawa Balkisu tace "Baba fito mushiga daga ciki", kurawa Balkisu idanu Baba Rabi tayi tana yimata wani irin kallon tuhuma cikin ranta tace "anya kuwa banyi kuskuren amincewa da wadannan mutanen ba, bansani ba ko masu yanke kan mutane ne" tana cikin wannan tunanin ne taji muryan Balkisu tace "Baba karkiji komai wlh babu abinda zamu miki kizo muje nakaiki wajan Meena" jiki a sanyaye haka nan baba Rabi tarufawa Balkisu baya suka shiga cikin gdan.
"Salamu alaikum! Salamu alaikum!! Anty amarya Meena" cewar Balkisu dai dai lkcin da suke qoqarin shiga falon.
Meena kam nacikin d'akinta tana d'an wasu gyare-gyaren ta juyo kmr ana sallama, kuma kmr muryan Balkisu tajiyo domin dai ita tasan cewa bata kai matsayin da Hafeez zai mata sallama ba. Dan haka da sauri ta tashi tafice a d'akin da sauri tanufi falo.
Da gudu Meena ta isa falon don tarbon Balkisu, Tursuuu Meena tayi ta tsaya cike da mamaki galala tayi da baki domin abinda taganewa idonta (tsawan shekara tara da suka shige Meena bazata taba mance wannan nagartacciyar fuskar ba) fashewa tayi da wani irin kuka mai tsanin ban tausayi.
Zaku jini anjima don jin cigaban lbrin, nagode.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [9:07AM, 8/2/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣0⃣
Wani irin farin ciki ne marar misaltuwa ya lullu6e Meena da gudu taqarasa wajan Baba Rabi, rungume junansu sukayi a tare suna ta kuka, Balkisu da Dr Muh'd kam suna daga gefe sai murmushi sukeyi.
Daga Meena har Baba Rabi anrasa mai lallashin wani, kuka sukeyi gwanin ban tausayi, dakyar Baba Rabi ta share hawayenta nan fa tashiga Shafa fuskar Meena ta ko ina sai mamakin girmanta takeyi, yayin da itama Meena sai kallon ta takeyi jiki take kmr ta manne a jikin Baba Rabi.
Bayan sun natsu sun zauna Meena ta umarci Daniel da yakawo musu drinks, cike da bin umarninta yakawo drinks kala kala yadiresu musu shi. Sai da suka d'an samu suka sharuwa sannan Meena tadubi Balkisu tayi ta zabga mata adduo'i nafatan alkhairi tare da yimata godiya, Balkisu sai murmushi takeyi.
Ana cikin hakane Dr Muh'd yatashi yace "shi zai koma office" nan yayi sallama dasu yafice Balkisu har wurin mota tarakashi daga bisani takoma cikin gdan.
Meena kam ana nan liqe da Baba Rabi dan jitake kmr wani zai k'wace mata ita, Balkisu dai sai dariya take mata.
Meena tadubi Baba Rabi tace 'Amma' (sunan da Balkisu ke kiran Baba Rabi dashi knan) Baba Rabi tadubi Meena tace "Naam Aminatu" Meena ta shagwa6e fuska tace Amma kintafi kinbarni cikin wahalalliyar rayuwa naga rashin gata naga tozarta naga walaqanci naga.....dasauri Baba Rabi ta toshe mata baki tace "haba Aminatu minene kike fad'a haka yakamata ace kin yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau a matsayinki na muslma, sbd wannan halin da muka tsinci kanmu jarabawace ta ubangiji dukk abunda Allah yarubuto cikin k'addararka to tabbas babu makawa sai tasameshi" Dan haka karki wanisa damuwa aranki ko kice zaki dinga tuna baya hakan bashi da kyau, ynxu ita wacce kike son yin mgn akanta ae gashinan taga qarshen sakamakonta.
Balkisu ta jinjina kai tace tabbas Baba wannan haka yake, Baba Rabi ta gyad'a kai tace toh kinga in hakane kuwa bai kamata kidinga tuna abinda yariga yawuce ba, Na ma gode Allah dayasa nasameki da ranki cikin k'oshin lafiya gashi har kinyi aurenki a gdan mijinki kinga wannan ma wata baiwace ta ubangiji Dan haka ki gode masa kiqara gode masa a koda yaushe Allah yana tare da mai gaskiya sannan yana bayan masu hakuri.
Da sauri Meena tafada jikin Baba Rabi taqanqameta tana kuka, cikin zolaya Balkisu tace wlh anty amarya in baki daina wannan kukan naki ba xand'auki Baba mutafiyarmu, dasauri Meena ta dubi Balkisu ta d'an turo baki cikin shagwa6a.
Baba Rabi tanumfasa tace "miye naga kina turo baki ae da gaskiyar Balkisu sbd a yau insha allahu inaso naje garinmu nasadu da dangina. Balkisu ta gyara zamanta ta fuskanci Baba Rabi tace "Baba sai dai fa kiyi hkri koda zakije garinku to ba yau ba sbd muma muna buqatarki kusa da mu, sannan kada kidamu ba'anan zaki zauna ba akwai gdan da muka ajiye miki na mussaman a Famfamari, Riqe ha6a Baba Rabi tayi cikin nuna jindadi da farinciki ta waro idanu tace dukk nikadai? Irin wannan d'awainiyan anya kuwa baiyi yawa ba?
Balkisu tace haba dai Baba wanne irin yawa kuma kema fa tamkar mahaifiya kike agaremu dukk abinda zamu iya yiwa mahaifanmu to zamuyi miki dukk da cewan Mahaifan namu basa raye" Baba Rabi ta goge hawayen dake kwaranyo a mata a fuska, nan tashiga sawa Balkisu albarka gamida yimata ta'azziyar rashin da sukayi.
Babban tashin hnkli Meena tashiga yayin da taga Ammanta na qoqarin fita a cikin gdan, kuka takeyi sosai ita fa lallai sai tabisu. Balkisu tace haba Meena miye hakan? Sai kace wadda Baban guduwa zatayi, kiyi hkri mana tunda Yaya Hafeez baya nan kibari idan yadawo xai kaiki shi da kansa.
nan fa Meena tace batasan zancen ba.
Dole Balkisu takira Hafeez tasanar dashi cewa tanaso zasu d'an fita wani waje tare da Meena, batare da 6ata lkci ba Hafeez yace Allah kiyaye.
Cike da farinciki Balkisu tad'aukesu a mota suka nufi Famfamari inda gdan Baba Rabi yake,
Wani d'an matsakacin plat house ne mai kyan gaske, falo daya da d'akuna uku da toilet da kitchn sannan kowanne bed room da toilet dinsa.
Masha allahu gda yayi kyau da tsari, Baba Rabi dai sai godiya take tana sama Balkisu albarka.
Bayan sun gama gyara ko ina Na gdan Balkisu tace da Meena ta shirya tayi dropn dinta a gda ita zata wuce gdanta tad'aura abinci.
Nan ma dakyar Meena ta yarda suka tafi cike da kewan Ammanta.
Akan hanyarsu takomawa gda Balkisu tadubi Meena tace "toh anty amarya nacika miki dukkan wani alqawari naki inaso nima kicikamin nawa kikular min da yayana tamkar yadda uwa zata kula da d'anta. Dammm!! Gaban Balkisu ya buga a hnkli ta kalli Balkisu jiki a sanyaye ta gyad'a mata kai gamida cewa insha allahu.
Balkisu tayi murmushinta mai sanyi, dai dai nan suka iso kofan gdan, Meena tayi sallama da Balkisu jiki a sanyaye haka tabud'e get din tashiga, motar Hafeez tagani ajiye wurin parkn motoci wato hakan nanufin yadawo? damm! Taji gabanta yabuga sbd alqawarin da tayiwa Balkisu ne yafad'omata.
0 comments:
Post a Comment