Wani uban tsawa yadaka mata yace "keee!! Zonan nan" Meena sai da tad'an figirta a hnkli ta juya akalarta izuwa falo, Hafeez ya watsa mata wata uwar harara cike da jin haushinta yace ke gdanku ba manya ne? Kina ganin mutane baxaki gaishesu ba ko ba akoya miki bane? Meena ta turo baki a hnkli tace INA wuni, mtssw Hafeez yayi tsaki yace " bansani get out wuce kiban waje" Meena ta juya da sauri tashige d'akinta tana gunguni.
A hnkli Hafeeez yace "Mtssw village girl gal kawai"cike dajin haushin ganinta yanufi d'akinsa.
•° •° •° •°
Yau ya kasance weekend Hafeez na nan gda sai wasu aikinsa yakeyi a system insa, zaune yake a falo sanye da farar jallabiya gabad'aya ya maida hnklinsa akan aikinshi.
A bangaran Meena kuwa a kullum bata da wani tunani da yawuce taya zata fara jawo hnklin wannan uban yan girman kan yakarka to izuwa gareta har tasamu tabashi kulawan.
Cikin tunanin da takeyi ne wata dabara tafad'o mata dasauri ta tashi tanufi falo, dama cikin shirinta take tsaff, cikin natsuwa Meena ke tafiya har ta isa cikin falon Hafeez tagani zaune yanata aiki a hnkli taqarasa gareshi tace "assalamu alaikum" dasauri Hafeez ya d'ago kanshi Dan ganin wacece keyimishi sallama.
Meena yagani tsaye gabansa sanye da wasu material riga da siket sun matuqar amsar jikinta tayi kyau abunta "koshi Hafeez cikin ransa sai da ya yaba wannan shiga" amma a zahiri sai cewa yayi wa'alaikissalam, nan kuma yatsaya sheqeqe yana kallonta cike da nuna isa yafara kusheta yace ke kuma fa miye hakan zaki zo kitsaya akan mutane?
Dasauri kuwa Meena ta zauna cike da sanyi tace "ina kwana" Hafeez ya amsa ciki ciki yace "lpy" Meena taqara da cewa sannu da aiki Hafeez yad'ago kanshi ya watsa mata wata uwar harara batare da ya amsa mata ba ya maida kanshi sannan yaci gaba da aikinsa, Meena na nan tsugunne Chan tasake cewa "amm kayi brkfst kuwa"? Hafeez yakawo iya wuya wani irin haushi yaji tabasa ina ruwanta da cikinsa, kallonta yakomayi ya watsar da yinta yacigaba da aikinsa.
Meena takawo iya wuya danne zuciyarta kawai takeyi dan haka dasauri ta tashi tabar gurin, d'akin ta takoma cike da jin haushin wannan izza da mulki na Hafeez.
Hafeez na nan zaune Daniel ya had'o kayan brkfst akan tire yanufi d'akin Meena dashi, yana zuwa yafara kwankwasa k'ofar d'akin a hnkli, da sauri Hafeez yajuyo dan ganin mai k'wank'wasa kofan d'akin Meena, Daniel yagani tsaye hannunsa d'auke da abinci da sauri Hafeez ya taso dai dai lkcin Meena tabud'e kofa.
Wani irin takaici ne ya turnuqe Hafeez "cikin zuciyarsa yace lallema yarinyan nan yaushe ma tawaye da har zata fara bada umarni ana kawo mata abinci?sannan ma tarasa Wanda zata sa ya kaimata abinci sai Daniel da irin wannan shiga nata" Meena ce ta katse masa tunanin da yakeyi, jiyayi tace sannu Daniel har ka kammala Daniel yace "yes madam" hannu tasa zata amshi abincinta Hafeez yadakawa Daniel tsawa yace "oyaa maida abincin nan kitchn" jiki na rawa Daniel yajuya da abincin ixuwa kitchn kmr yadda boss din nasa ya umarce shi.
Juyawa yayi gurin Meena fuskan nan a turbune ya nuna tada hannu yace "ke yar qauye bari kiji kinyi kad'an kidinga bada order a gdan nan wai dan akaimiki abinci daga yau irin rana tayau bana so in qara ganin Daniel kofar d'akinki danufin wai yakai miki abinci kinajina koh? Kije da kanki kid'ibawa kanki inba haka ba kixauna da yunwa" har Hafeez ya juya xai tafi sai kuma yadawo ya dubi Meena duba na walaqanci yace "ke yar qauye inaso daga yau kezakina shiga kitchn da kanki kidafa abinci, take anan kuma yashiga kiran Daniel!
Jiki na rawa Daniel yaqaraso yace "yess oga" Hafeez yadubi Daniel yace as 4rm today inaso karka qara bin umarninta nacewa ka kawo mata abinci' Hafeez yariqe kunnensa yana mainuna alamar warning ga Daniel sannan yace "and then daga ynxu ita zata ke dafa abincinta" Daniel yace okay oga.
Hafeez nafad'in haka yajuya yabar wajan, Meena tsayawa tayi tana binsa da kallo cikin xuciyarta tace "jibeshi da anyi magana yawani cewa mutum d'an kauye qyaatt" juyawa tayi cikin d'akinta tad'auko hijabi tanufi kitchn dan tasamu abinda tasawa cikinta domin kuwa Meena intaji yunwa bata wasa da abinci.
Sumi sumi tanufi kitchn don tad'aura wani abun,...Hafeez na nan zaune ta ratsa ta gefensa tawuce, juyowa yayi yana kallonta tsaki yayi cikin xuciyarsa yace "village gal"
Kitchen Meena tashiga nan tafara laluben abinda zata dafa, tana cikin tsaka da dubawa ne taga hango kwalin indomie da sauri ta janyo kwalin tad'auki indomie biyu nan ta kunna rishow kasancewar bata iya amfani da gas ba.
Take anan Meena tafara dahuwar indomie dinta wnda taji albasa da attaruhu, ae fa nan gda ya kaure da qamshi Hafeez kam mayen indomie take anan yajiyo qamshi na dukan hancinsa wani irin yunwa yaqarajin tashigesa kasancewar dama baiyi brkfst dinsa ba.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:00PM, 8/3/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣2⃣
Dasauri Hafeez yamiqe yanufi kitchen din, dai dai lokacin ne kuma Meena ke qoqarin juye indomie dinta a plat, yawun Hafeez ne yatsinke sai wani had'iyar yawu yake (sbd Hafeez na mutuwar son indomie shiyasa ma kullum gdan baya rabuwa da kwalayen indomie) Cikin natsuwa Meena ta bud'e fridge din dake ajiye cikin kitchen tabud'e tad'auki exotic mai sanyi sannan taduqa tad'auki indomie dinta.
Hafeez bai tsammaci fitowar Meena a lkcin ba jiyayi kawai sunyi karo da juna, dasauri Meena tace "subahanallahi" wani irin takaicine Yakama Hafeez ganin cewa ita kad'ai ta dafawa kanta indomen, duba jikinsa Hafeez yashigayi ko allah zaisa yaga inda ta6ata masa jiki yasauqe haushinsa akanta, amma sai dai anyi Sa'a babu inda jikinsa ya6aci,dan haka dubanta ya shigayi kmr wacce tayi wani abun.
Meena kam tsaye tayi tanabinsa da kallo, Chan Hafeez yaqufula yace "ke yar qauye wannan wacce irin qaxamar dahuwa ce kikayi jibi yadda kikawani zabga tarugu sai kace wata maiyya.
Meena tazaro ido waje tace "nice mayya Kuma?"batare da Hafeez ya kulata ba yace "common get out" Meena taratsa ta gefenshi zata wuce tana gunguni Hafeez yace "magana kike ne?" Meena ta manna masa ta wucewarta, Hafeez yayi tsaki yace qyatt yar qauye kawai sai wani faman big head kike xanyi maganinki very soon. Nan yashiga kwalawa Daniel kira!
A bangaran Meena kuwa d'akinta ta wuce kaitsaye dukk haushi ya isheta mgnr Hafeez ce kawai ke mata yawo a kunnenya, kwafa tayi cike dajin haushi tace "tabb wato ni Hafeez zaicewa Maiya? Wlh sai yagane kurensa sai na mai dashi yazama mayen shima in yaso mahad'e muzama mayun mu biyu,..Meena sai faman cin indomien din ta takeyi wnda taji kayan had'i, tanaci tana masifa ita kid'ai a d'aki.
•° •° •° •°
Washe gari.
Meena tunda safe bayan ta idar da sallah tanufi kitchn dan tasamu abinda tad'aura, mgnr Balkisu ce tafad'o aran Meena lkcin da aka kawota inda Balkisu ke sanar da ita abunda Hafeez yafiso yayi brkfst dashi wato soyayyan kwai da tea, dariyar mugunta Meena tayi, nan tashiga farfasa kwai wnda xatayi amfani dashi ta jajjaga tarugu mai yawa ta yanka albasanta tazuba maggi da kayan kamshi ta zuba cikin kwan ta bubbugashi sosai yabi jikinsa, nan tahau suyan kwan, daga gefe kuma tad'aura ruwan zafin tea dinsa Wanda tazuba lipton da citta suga da kalinfari da barkono sosai, ae fa nan qamshi ya karad'e gdan.
Hafeez sai da ya tabbatar da cewa yayi wanka sannan ya shirya tsaf abinsa cikin shaddarsa sky blue sai hularsa wadda tayi matchn da kayansa, agogon hannunsa yad'auka yasa sannan yafesa turare yanufi hanyar fita, bud'e kofan nan da Hafeez zaiyi yaji kamshin ya doki hancinsa da sauri yaqarasa cikin falon ko da yaduba dinning area yaga anshirya komai tsaf tsaf kmr yadda aka saba, cikin hanzari yanufi dinning table yaxauna tare da duban agogon hannunsa qarfe takwas da rabi yana ganin haka yayi saurin zaro wayanshi dake aljihunsa, wata nmbr yayi dialing cikin natsuwa yake mgn yace "yes mansur am on ma way just giv me 15 to 20 mint a will b thr soon" yana gama wayar ya hau bud'e brkfst din ruwan zafin tea din yafara zubawa kadan cikin cup sannan yadibi kwan nashi cikin plat, wani irin kamshi mai dad'i ne yake ta doke hancinsa.
Sai da ya tabbatar da ruwan xafin yad'an huce dai dai yadda zai iya sha sannan yajawo kusa dashi, plat din kwansa yasa agaba dasauri yadebo mai yawa yaddana a bakinsa yafaraci a hnkli yad'an lumshe ido sai da kwan yakai qarshe Hafeez yaji wani irin azababben zafin barkono ya ziyarci harshensa dasauri yafurzar ya dauki cup din tea dinsa ya kurba ko zaiji d'an ji dama, ae fa nan Hafeez ya miqe tsaye idanunsa sukayi jajir harshensa yadinga fiddowa waje sbd tsabar azaban da yakeji ko mgn yakasa(kasancewar Hafeez bayason abuda yaji SBD ulcer)
Meena dake la6e tana kallonsa sai kwasar dariya take abunta, kara leqawa tayi don taga yadda yake daka tsalle ae kuwa tana sa kai sukayi ido biyu da Hafeez.
NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:10AM, 8/4/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣3⃣
Hafeez nahad'a ido da Meena yatabbatarwa kansa cewa itace tahad'a masa wannan muguntan, dan haka a fusace yayi kanta sai dai Hafeez baisamu daman qarasawa gareta ba sbd wani irin abu da yatsaya a zuciyansa nan da nan yanemi hnklinsa yarasa jagwaaf yafad'i qasa gamida riqe kirjinsa yanata mutsu-mutsu a kasa. Abu dai kmr wasa wasa tun Meena na yar dariyarta har dai talura cewa Hafeez da gaske yake, ae da gudu Meena taqarasa inda yake kwnce nan tashiga jijjigasa tana kiran sunansa.
Gabad'aya idanunsa suncanja kala Hafeez yajigata sosai zuciyarsa wani irin suya take masa.
Meena ta lura abin nashi dagaske ne ba wasa dan haka dagudu tashiga kiran Daniel, Daniel yazo da hanzari ganin ogan nasa cikin wani hali hakan yasa yafahimci cewa ulcer dinshi ne yatashi dagudu Daniel yashiga d'akin Hafeez yad'auko maganinsa nan ya qoqarta yasamu yabashi maganin yasha.
A hnkli Daniel yasamu yad'aga Hafeeez dakyar yataimaka mishi ya kaisa d'akinshi. Hafeez jiyayi tsanar Meena taqaru a xuciyarsa.
A bangaran Meena kuwa jitayi gabad'aya jikinta yayi sanyi, sai ynxu takejin kwata kwata bata kyauta ba nadama tashigayi marar iyaka.
Tunda wannan abu yafaru kuwa Hafeez bai qara bin tankan Meena ba, yar kulatan ma dayakeyi suna rigima kwata kwata ynxu ya daina.
Mgnr abincinsa kuwa Daniel kedafa mishi kmr kullum.
• • • • • •
Meena abin duniya dukk ya isheta Hafeez ko kallon indatake baya son yi jiyayi gabad'aya yatsaneta, shiyasa da zarar gari yawaye yake Allah Allah yafice a gdan.
Yayin da ita kuma Meena ke tunanin hanyoyin da zatabi dan taga cewa ta kyautata masa, Hanyar farko da Meena tafarabi shine da zarar Hafeez yafita zuwa office dinshi a wannan lkcin ne take shiga d'akinsa ta gyara ko ina ta wanke toilet tattara under wears dinsa ta wanke masa, haka kullum Hafeez idan yadawo sai yaga komai Na d'akinsa very neat.
Ana cikin hakane Daniel ya samu Hafeez yasanar dashi cewa yanaso zai zaije enugu can garinsu domin gudanar da bikin kirisimeti, Hafeez yayi mishi izini sannan yad'auki kudi mai tsoka yabawa Daniel.
Lkcin da Daniel zaitafi garinsu har qofan d'akin Meena yaje yayi sallama da ita, nan itama tayi mishi fatan adawo lafiya.
*DA YAMMACI*
A yammacin ranar ne Meena tashiga kitchen tad'aura tuwon semo da miyan d'anya ku6ewa, Meena taxage sosai tadafa abinci mai kyau da tsari dukk dan taburge Hafeez.
Bayan Meena tagama girkinta ne takoma d'akinta toilet tashiga ta silla wankanta sannan tafito tashirya tsaf abunta cikin wata jar atamfarta mairatsin ash kala, atamfar taimata kyau sosai, simple mark up tayi sannan tanufi falo taxauna ta kunna Tv.
Horn din motar Hafeez Meena taji, dasauri tamiqe taleqa window' Hafeez din ne kuwa ta hango yayinda yake qoqarin fitowa a mota, dasauri takoma maxauninta.
Murd'a kofan falon yayi yashiga batare da ya lura cewa akwai mutun a falon ba, dasauri Meena ta taso da fara'arta tayi mishi sannu da zuwa batare da Hafeez ya kulata ba tasa hannu tana qoqarin ansar briefcase dinsa, wani irin takaici Hafeez yaji baisan lkcin daya tunkud'e ta ba tafad'i. Hafeez ko ajikinsa haka yatsallaka Meena yawuce.
Dinning area yamaida dubansa yaga cewa tahad'a masa abincin dare tsaki yaja mtssssww stupid, Hafeez nafadin Haka yanufi d'akinsa.
Jikin Meena yayi sanyi sosai a hnkli ta tashi a wurin tashiga d'akinta, saman gadonta tahau tarafka wani uban tagumi nan tashiga yin tunani kala kala akan yadda zatabi da hafeez nan dai tayanke shawaran zata jure komai dan ganin tacikawa Balkisu alqawarinta kmr yadda tacikamata nata.
Magri nayi Hafeez ya d'aura alwalarsa yawucewarsa masallaci, bayan sun idar da sallah restaurant yanufa kai tsaye yacika tumbinsa, dukk da cewa yasan Meena tayi girki amma Sam baijin iyacin girkinta koda wasa.
__•__•__•__°__°__°__•__•__•
A kullum Meena tana qoqari sosai wajan kula da Hafeez, ta gyara mishi d'aki tasa roomfrshnr ta wanke toilet dinsa tagyara mishi kayansa, sannan tayi mishi girki kullum dukk da cewa Hafeez bayaci amma Meena dai dai da rana d'aya bata fasa abubuwan da takeyi ba, tsawa da gyara turi da masifar Hafeez baya hana Meena ta kyautata masa.
Meena ce zaune a falo tanajiran shigowar Hafeez, sai jin tayi telephone Na qara (wato landline wnda kowa xai iya d'auka, kasancewar Meena batada waya) dasauri Meena tamiqe ta isa wurin da telephn din ke ajiye tad'aga wayan kmr yadda taga Hafeez nayi, sallama tafarayi sannan suka gaisa
Take anan Meena tagane muryan Balkisu ne nidai naga Meena sai murmushi takeyi daga bisani kuma naji tace mekikace daqarfi!! ?? Gabadaya naga hankli Meena yatashi dasauri tajefar da wayan tanufi d'akinta.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [11:47AM, 8/4/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣4⃣
A rikice naga Meena tafito daga d'akinta sanye da hijab dasauri naga taja kofan d'akin ta rufe sannan tanufi hanyar waje a hanzarce, bakin titi tanufa kai tsaye da alamar tana jiran abin hawane.
Kmr wucewan minti biyar Meena na nan tsaye bata samu abin hawa ba, sai ga Balkisu nan cikin motarta tun kafinma taqarasa tagane cewa Meena ce tsaye bakin titi.
Dasauri Balkisu tayi parkn din motarta kusa da Meena, zuge glass din motar tayi lkcin ne Meena tafahimci cewa Balkisu ce, ae kuwa da hanzarinta taqarasa cikin motar.
Bayan tashiga cikine Balkisu tafashe da yar dariya tace "a'a Anty amarya inazaki haka badai kice mgnr da mukayi bane dukk tafirgitaki haka ba?" Meena tayi wata irin sassanyar ajiyar zuciya tace "haba Balkisu mai xai hana hanklina baxai tashi ba karki manta fa cewa basan garinsu mahaifiyata ba ynxu idan ta tafi tabarni batare da nabita naga dangina ba mai kike tunanin xaifaru? Gsky nidai xanbi Amma na xuwa garinsu, Balkisu tadubi Meena da murmushin nan nata tadafa kafad'arta tace "haba kekuwa Anty amarya ae baki bari naqarasa miki abinda nake son cewa ba kawai naga kinkatse call din shiyasa kikaga nafito a hanzarce".
Ynxu koh da ace bin Baba Rabin zakiyi hakanan zakitafi batare da izinin yayana ba ko kuwa hakanan zakije hannu siddan babu kayan sawa balle tsaraba?
Meena ta sadda kanta qasa tace "wlh dukk na rikice ne sbd bana fatan abinda xaisa nasakeyin nisa da mahaifiyata" Balkisu tace "hakane amma ae ba yau bane tafiyan nata sai jibi ne fa Dan haka muje namaidaki gda ki kwantar da hnklinki zanfad'awa Yaya mgnr tafiyan naku amma inaso kema kisameshi dakanki kifad'a masa, toh kawai Meena tace.
Hakanan Balkisu ta mai da Meena gda sai faman zolayanta takeyi.
** ** **
Hafeez ne zaune awani tafkeken Restaurant yana cin abincinsa hnkli kwance, daga gefe kuma inda ya ajiye wayansa tashiga ruri! A hnkli Hafeez yajawo wayan 'luvly Sister' sunan da Hafeez yayi saving nmbn Balkisu shine ya baiyanna agaban screen din wayansa da sauri yad'auka gamida sawa a kunnenshi, bayan sun gaisa ne Balkisu ke sanar da Hafeez mgnr tafiyan Meena wnda zasu ita da mahaifiyarta, Hafeez yace "olryt Allah yakaimu lkcin" Balkisu tace ameen nan suka d'an ta6a hiransu daga bisani kowannensu ya ajiye waya.
Abangaran Hafeez kam shiru yayi hakanan kuma sai yakejin kmr babu dadi, can dai kuma ya hori xuciyarsa tama daina damuwa da wannan yar qauyan ae ma inta tafi kahuta, inba ma tsabar rainin wayo ba Balkisu nake aure ko ita ae kamata yayi taxo da kanta taneme ixinina wato tanaji ita watace tafi qarfin takawo kanta knan?, hakanan Hafeez yayi tasaqawa da kuncewa a cikin xuciyarsa. Har dai yagama cin abincinsa sannan yanufi gda.
Yau ma kmr kullum Meena tayi masa abinci ta ajiye dukk da tasan cewa baci xaiyi ba, haka nan bayan shigowarsa cikin gda har bakin kofa tabisa dan ta tarbeshi amma gayen nata ko kallon inda take baiyi ba, balle yanxu dama cike yake da haushinta akan qin xuwa da batayi da kanta tafara tambayarshi ba.
Inda sabo kam Meena tasaba da irin abubuwan da Hafeez ke mata wanda zuwa ynxu kam har sun fara daina damuwarta.
Misalin qarfe tara na dare Meena tashiga bayi tayi wnka sannan tad'airo alwala, kayan bacci tasaka masu sauqin nauyi hakanan tajawo xani tad'aura saman sleepn drss din sannan tasanya hijabinta ta gabatar da nafilfilunta kmr yadda tasaba, bayan ta idar da sallah ne ta yankewa xuciyarta shawaran cewa gwnda taje a daidai wannan lkcin tasanar da Hafeez mgnr tafiyanta inba haka ba da safe koh da zata tashi olrdy ya fita.
Hakanan ta gama yanke shawaran ta, ta amincewa zuciyarta, Dan haka d'akin Hafeez tanufa kai tsaye a hnkli tashiga knckn kofar,...sai da Hafeez yagama jan ajinsa kasancewar yasan babu wnda xai kwankwasa mishi kofa adaidai wannan lkcin sai Meena shiyasa sai dayagama jan ajinsa sannan yace yes come in! A hnkli Meena ta murd'a kofan d'akinta shiga.
Hafeez tagani zaune bakin gado dagashi sai farar vest da boxsas yanata aiki da system inshi, da sallama tashiga cikin d'akin, Hafeez ya amsa mata sallamarta batare da yad'ago ya kalleta ba.
Meena taduqa har qasa ta gaida Hafeez,..Hafeez kuwa ko kallo bata ishesa ba amaimakon ma ya amsa gaisuwansa datayi sai cemata yayi yes inajinki fad'i abunda yakawoki kinga aiki nakeyi.
Meena ta had'iye wani yawu dakyar yawuce sannan ta sadda kanta qasa sbd jitayi gabad'aya Hafeez yayi mata wani irin kwarjini, cikin nutsuwa Meena tace "dama Amma nane xatayi tafiya xuwa gda shine nake so na bita" Hafeez yace "dakyau yar qauye xa'aje qauye kenan? Meena dai batace masa komai ba sai wasa kawai take da d'an yatsanta.
Wani murmushin takaici Hafeez yayi sannan ya d'auko wata waya LG yamiqa mata yace ga waya nan inkinje kiyi amfani da ita, Meena ta amsa tayi godiya sannan Hafeez yad'auko bandir din kudi yan dari biyar biyar ya watsawa Meena cike da gadara yace gashinan wannan akaiwa tsohuwa nasan zata buqata.
Mgnr Hafeez ta matuqar 6ataran Meena amma sai ta danne xuciyarta miqewa tayi cike da d'acin rai takalli Hafeez ta kalli kud'in har dai Meena tayi niyar sakar mishi mgn sai kuma nan da nan ta taushi zuciyarta, ajiye masa kudinsa tayi a qasa dai dai qarfarshi taficewarta a d'akin.
Binta Hafeez yayi da kallo cike da mamakinta
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:27AM, 8/5/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣5⃣
Balkisu da kanta taje wani babban super market tahad'owa Baba Rabi tsaraba masu kyau na amfani, su sabulun wnka wanki turaren shafawa kwalayen biskuit da dai sauransu, hakanan ta kwasa tayi gdan Baba Rabi dasu ta kai mata. Baba Rabi tayi farinciki sosai da irin yawan hidimar da Balkisu keyi da ita, nan tayi tasawa Balkisu albarka gami da nuna farincikinta.
Washe Gari.
Tunda asuban fari bayan Meena ta idar da sallah batasamu ta kwanta ba sai da ta tabbatar da cewa tayi dukkan wani aikinta kmr yadda tasaba, agogon dake liqe jikin bangon d'akinta ne yabuga qarfe 6:30 a gaggauce Meena tafad'a toilet tayi wanka kasancewar tasa qarfe 7:00 Hafeez ke fita, gashi yau tanason tawuni gdnsu dan tasan irin shirye shiryen da yakamata suyi ita da Ammanta.
Wata dakakiyar shadda lemon green wadda akayiwa aiki dazare orange, riga da siket ne su Meena tad'auko tasa (woww ni kaina munay sai dana yaba wannan shiga) dukk da ba wata kwalliya Meena tayi sosai ba amma tai matuqar kyau, nan tad'auko takalmi orange gyale orange.
Motsin Hafeez taji yana qoqarin fitowa daga d'akinsa dasauri taduba agogo taga 6:57 a hanzarce ta zura wata qatuwar Hijabi tanufi waje.
Ki6iss sukayi da juna Hafeez ke kokarin fita yayin da Meena tafito a d'akinta dasauri tace Yaya!!
Mamakine qarara ya baiyanna a fuskar Hafeez jin cewa Meena ke kiransa da Yaya dukk da cewa bata fiye kiran sunansa ba, sannan a iyazatonsa yana tunanin tayi fushi da shi sbd abinda yayi mata jiya daddare.
Tsayawa Hafeez yayi batare da ya juyo ba, a hnkli Meena taqarasa kusa dashi tace "ina kwana" Hafeez ya amsa a takaice Lfy, Batare da nuna damuwa ba Meena tace "Dan Allah sonake kamin izini xanje gdnmu nawuni acan sannan inba damuwa inaso ka ajiyeni a gda.
Hafeez har yayi niyyar cewa wani abu sai kuma yafasa, juyowa yayi yakalleta sama da wasa sannnan yace olryt nabaki nan da minti d'aya inbaki shirya ba xan wucewata.
Ae Hafeez nacewa haka dasauri Meena ta miqe kafinma Hafeez yabar falon tuni tashige d'akinta hijabin dake sanye jikinta tacire tasanya gyalenta sai takalminta da tasa tad'auki wayarta a gaggauce tarufe d'akinta da kofar falo, kasancewar ita da Hafeez kowa nada nashi mukullin.
Hafeez ne zaune cikin motarsa yana jiran fitowan Meena, hango ta yayi tafe sanye da gyale dasauri Hafeez yasake kallonta dakyau wani irin abu yaji ya d'arsu a zuciyarsa wanda shi kansa baisan miye ba wani irin kishi yaji domin kuwa ko da ace maqiyin Meena ne yaganta to tabbas dole ya yaba mata sbd tayi masifar kyau, cikin zuciyar Hafeez yace "lallai yarinyan nan ta rainamin hnkli ba ynxu naganta sanye da hijabi ba? Wato dan zata fita shine hadda wani sa gyale.
Hafeez naganin Meena taqaraso ya watsa mata wata uwar harara, wanda hakan yasa Meena tasha jinin jikinta, a qufule Hafeez yace kee wato baki shirya fita zuwa anguwan ba shine kikayi westin tym dina?
Meena tadubi kanta sama da qasa sannan tasake duban Hafeez tace "wlh yaya na shirya" Hafeez yadaure fuska yace kina nufin da gyalen nan zaki fita? Meena tafahimci abinda Hafeez yakeson cewa wato bai da tsarin son iyalinsa su sa gyale, dasauri Meena ta koma cikin gda tasanyo hijabi dukk da cewa hijabin sam baiyi matchn dakayan jikinta ba hakanan tasanya abinta domin ita dai buqatarta kawai ta jita ajikin Ammanta.
Gdan baya Meena ke qoqarin bud'ewa dasauri Hafeez yace ke yar qauye wakike ajiye drivanki look inbaki shirya tafiyan ba nixan wucewata ko ancemiki banda abubuwan yine, jiki a sanyaye Meena tabude gdan gaba taxauna Hafeez yaja motan sukafice a gdan.
Sanin datayi Hafeez baisan gdnsu ba shiyasa tadubeshi cikin sanyin muryanta tace "famfamari zamuje wurin masallacin juma'a, ko uffan Hafeez bai ce mata ba hakanan yaja motarsa yanufi anguwan da tafad'a mishi.
Sunxo dai dai kofan gdan ne Meena tace sun iso tsayawa yayi a hnkli daga gefen hanya, Meena tasa hannu zata bud'e kofan Hafeez yace "ke tsaya yar kauye karki 6allamin murfin mota, zura hannunsa Hafeez yayi yabud'e mata kofan sannan yace, nabaki nan da awa biyar kikoma gda kinji abinda nace?"
Ran Meena ya6aci sosai amma talura Hafeex neman rigima yakeyi shiyasa kawai ta gyada masa kanta tafice a motar.
Meena taji dadin kasancewa da Ammanta sosai wnda har hakan yasa tashagala tamance da umarnin Hafeez.
Qarfe 2 dai dai Hafeez yakoma gda amma still Meena bata dawo ba, wani irin haushi Hafeez yaji ganin cewa yadawo gda babu Wanda ta tarbeshi dukk da cewa baya kulata amma yau din sai yaji babu dadi.
Wani irin tunani ne yazowa Hafeez lkci d'aya wanda yad'imautashi, dasauri ya zari car key dinshi yafice a gdan, gdansu Meena yanufa kai tsaye sbd tunawan dayayi cewa matuqar Meena tace zata koma gda tofa motan haya xata hau, tunanin Hakan ne yasa ya gaggauta zuwa yad'auko ta da kansa.
Hafeez na danna kan motarsa cikin kwanar gdansu Meena nan ya hango abinda yad'aga masa hankali.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:23AM, 8/5/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣6⃣
Hafeez Meena ya hango tsaye a kofar gdansu ta tsaida mai adai-daita sai faman murmushi takeyi mishi yayin da suke mgn ita da mai adaidaitan, wani irin kishi Hafeez yaji, nan fa jikinsa yafara kyarma a guje yashiga cikin layin ko gabansa ba ya iya gani mai kyau, Hafeez na pake motanshi kafinma yakasheta a hanzarce yabude murfin motan yafita batare da ya kashe motan ba.
Gadan gadan Hafeez ya nufi kan mai adai daita, mai adai daita na cikin tsaka da ciniki da Meena sai ji kawai yayi anshaqo wuyansa ta baya ana dukansa ta ko ina.
Dasauri Meena tafasa ihuu! Tana roqon Hafeez da yabar abinda yake yi, Hafeez kam kojin ta bayayi gabad'aya jiyake kmr ya kashe mai adai daitan sbd haushi,. ihuun da Meena takeyi ne yajawo hnklin mazan anguwar dakyar suka samu suka kwaci mai adai daita a hannun Hafeez.
Idanun Hafeez gabad'aya sun rine sunkoma ja sbd tsananin kishi, a tsorace Meena tafara ja dabaya sbd gabad'aya Hafeez tsoro yabata sai wani irin huci yakeyi tamkar zaki cikin dawa, gawata uwar harara dayake jeho mata.
Da gudu tashiga gdansu dai dai lkcin ne Baba Rabi takejiyo hayaniya daga waje dole tamiqe tanufi hnyar waje don ganin mekefaruwa, Meena ce tashigo gdan da gudunta sai faman waiwayen bayanta takeyi.
Hafeez kam mutanen cikin anguwar sai tambayanshi sukeyi mai wannan bawan Allah yamasa? Kota Kansu Hafeez bai biba yanufi motarshi ya kasheta yarufe sannan yanufi cikin gdansu Meena din.
Meena rungume Amma tayi dukk tsoro yacikata sai wani faman haki takeyi kmr wacce tayi gudun 3kilomita, Baba Rabi sai faman tambayarta takeyi Aminatu lpy kuwa meyaparu waye ya biyoki? Meena kasa mgn tayi sai faman kallon hanyar shigowa gdan takeyi a tsorace "domin atunani Meena hadda ita Hafeez zai hada"
Hafeez ne yashigo gdan sallamarsa, Baba Rabi ta amsa mishi sallaman yayin da ta kura mishi ido tanajiran yafad'i da wacce yazo domin atunanin Baba Rabi shine Wanda ya biyo Meena,(domin kuwa Baba Rabi ko a hoto bata ta6a ganin Hafeez ba) Hafeez har qasa yaduqa ya gaishe da Baba Rabi, Baba Rabi ta amsa "lafiya kalaw" Lkcin ne Meena tayi wata irin sassanyar ajiyar xuciya sannan tace "Amma wannan shine Hafeez yayan Balkisu" Baba Rabi ta fad'ad'a murmushinta sosai tace "Allah sarki kayi Hkri Sam ban shaida ka ba, nan tayi mishi iso ixuwa cikin gdan, A falo Hafeez yazauna Baba Rabi da kanta takawo mishi abinci tuwon semo da miyar allayahu zallah, drinks takawo mishi da ruwan sanyi.
Baba Rabi da Meena kitchn suka koma suka fara had'awa Hafeez juice din kwakwa, Hafeez kam yunwa yakeji sosai dan haka bude kulan yashigayi tuwon semo yagani anyi malmalanshi ansa leda tsaf sai kuma miyan allayahu wnda taji manja, malmala d'aya Hafeez yad'iba yasa a plat bayan yazuba miyan allayahun nan fa yahauci, kafin Hafeez ya ankare tuni yagama da malmala guda"woww vry nyc Hafeez kawai ke fad'i yana lasan baki😋"
Meena ce tashigo Hannunta d'auke da jug din juice din kwakwan, duqawa tayi tad'auki glass cup a kusa dashi batare da ta kalleshi ba tashiga zuba mishi.
Kura mata idanu Hafeez yashigayi kmr yajawota kusa dashi haka yakeji, Meena nagama zuba mishi juice din ta tashi tabar falon a hanzarce.
Hafeez jiyayi kmr baxai iya tashi awajan ba sbd wani irin qoshi dayayi, rabonsa da cin abinci kmr haka har yamanta, murmushi kawai Hafeez keyi shi kad'ai yasan abinda yasashi murmushin.
Meena ce tashigo cikin falon wannan karon ba Hijabi, filas din da Hafeez yagamacin abinci dasu shine Meena tashigo danta kwashesu, Hafeez kam sai binta yake da kallo tamkar wata baquwa, Hafeez kam sai mamakin knsa yakeyi yadda ya lura cewa Meena naqoqarin zautar dashi lkci d'aya mamakin kansa yashigayi sosai wnda har Hafeez yakama tantamar anya kuwa shine? (LOL)
sai da Meena ta gama kintsa falon sannan Baba Rabi tashiga falon suka sake gaisawa da Hafeez, Baba Rabi tasake da Hafeez sosai sai jansa take da fira, wanda shikuma Hafeez gabad'aya kunya tagama cikasa kasa sakewa yayi da Baba Rabi, bayan sund'anta6a hira sama sama ne Hafeez yaciro kudi Wanda shi Kansa baisan iyakarsa ba yace wa Baba Rabi gashinan tayi tsaraba, dafarko Baba Rabi qin kar6a tayi tace a'a ae Balkisu tayi musu hidima sosai dan haka baxata kar6i kudinsa ba, gabad'aya Hafeez jiyayi daraja da kimar tsohuwar taqaru a idonsa, dakyar dai Hafeez ya samu ya lallama Baba Rabi ta Amshi kudin,....daga bisani Hafeez yace da ita shi xai wuce gda dama yaxo ne dan yayi mata Allah yakiyaye hanya, Baba rabi nan tayi tasa mishi albarka tana mai nuna jindadinta sosai.
Hafeez nafitowa Meena tasa Hijabinta tad'auki wayarta sukayi sallama da Amma, a hanzarce tarufawa Hafeez baya a tare suka fice a gdan.
Gaban Meena sai dukan uku uku yakeyi gabad'aya taqisakewa sai faman takure kanta takeyi.
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:50AM, 8/6/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣7⃣
Daga Hafeez har Meena ba Wanda yace da wani uffan haka har suka isa gda, Hafeez nayi parkn Meena tayi sauri tafice a motan, tsuki Hafeez yayi cike da haushinta, a filin gdan Hafeez yayi parkn din motanshi baiko sami damar sakata ma ajiyarta ba, a hanzarce yarufawa Meena baya.
Meena da sauri tabud'e kofan falon sannan tanufi d'akinta, isar take nan takama kofan da niyyar tabud'e sai jitayi Hafeez yace "kee! Tsaya anan Meena ko waigawa takasa tsaye tayi bakin kofar kmr wadda aka shuka.
Hafeez nazuwa a fusace ya manna Meena ajikin Bango, take mata babban yatsanta yayi naqafa da qarfi Meena tasaki Yar qara, Hafeez yace "aikin banxa ashe kina mgn?, Meena ganin Hafeez ya kura mata ido ko kiftawa baiyi yasa tasadda kanta qasa, Hafeez gyad'a kai yayi yace "dakyau hakan Yatabbatar min da cewa baki da gaskiya sannan inaso kifad'a min uban waye yabaki izinin tare mai adai daita har kitsaya dashi kina masa dariya? Meena wacce sai mutsu mutsu takeyi tanason kwace kanta daga riqon da Hafeez yayi ma hannayenta gashi ya taka mata babban d'anyatsa yaqi sakewa, Meena kamar xatayi kuka tace nifa badariya nake mishi ba, kawai tambayarsa nayi anawa xaikain.....kafin Meena taqarasa abinda take son cewa Hafeez yadaka mata tsawa yace ni ba wannan natambayeki ba cewa nayi meyasa kike masa dariya?
Meena tayi rau rau da idonu tace Dan Allah yaya kayi hkri baxan sake ba.
Hafeez yace no ba laifinki bane laifina ne sbd kin raina ni ko? Meena ta girgixa kanta tace "a'a
Hafeez yace okay toh yayane? Wato hakan ma yananufin cewa idan kukaje garin naku haka xakiyi behaving? Kina tare masu abin hawa kina musu dariya? Toh bari kiji inkikasa wasa a tafiyan nan wlh sai nace babu inda zaki, sannan sbd tsaban kinrainani wato nabaki awa biyar akanki dawo gda shine kikayi xamanki sbd tsabar kinnrainani ma shine kike ganin kinfi qarfin kid'aga waya ki kirani kice xaki koma gda.
Meena tace "wlh ba haka bane nadauka kana gurin aikin kane shiyasa nayi tunanin komawa da kaina, a firgice Hafeez yaqara matse ta da bango wnda gabad'ayansu sunajin numfashin juna, Hafeez yamatso da kanshi daf da fuskar Meena yace" an gaya miki cewa aiki na yafiki muhimmanci ne ko kuwa bakisan cewaa..shiru Hafeez yayi ya kasa qarasa abinda yake son cewa.
Sake mata hannu yayi sannan yanuna ta da yatsa yace toh bari kiji ban amince ko da kinyi wannan tafiyan ki ke yawaita hawan motan haya ba ko kice xakisawa mutane gyale, can kuma Hafeez ya kufula yace ke daga yau ma nayi canceln sa gyale a gareki, inkinga kinsa gyale toh daga ke sai nine acikin gdan nan kinajina ko?
Da sauri Meena tace ehh!
Hafeez ya gyara tsayuwansa ya kalli Meena dakyau sannan yace in kunne yaji jiki yatsara, d'akinshi ya wuce yabar Meena tsaye.
Huuhh!! Shine abinda tace kawai tashiga d'akinta
A gajiye takwanta bisa gadonta tadafe goshinta, cikin zuciyarta tace "hmmm Yaya kenan dama nakawo haka araina sbd naga take takenka kwana biyun nan sokake ka hanani wannan tafiyan shiyasa kake tsiro da rigima kala kala nikuwa nasan halinka dan haka a ynxu dai baxan biye maka muyi ta rikici ba, balle kasamu galaban hanani yin wannan tafiyan.
Kiraye kirayen sallahn la'asar din da akeyine yasa Meena tayi hanzarin tashi tanufi toilet tad'auro alwala.
Abangaran Hafeez kuwa wani irin abune yatsaya mishi arai nan yafara jerowa kanshi tambayoyi wai mema yasa nadamu da lamarin wannan yar qauyen ne mema zaisa naji kishinta ohh my god kar fa najawa kaina raini agun wannan bakauyiyar yarinyar (nidai Munay dariya nayi, nace araina babu mai amsa maka wannan tambayoyinaka sai munturo maka JUMAYMA Yar bincike ta bincika mana kai LoL)
Hakanan Hafeez yayi ta faman sintiri cikin d'aki shi kad'ai yarasa abunda ke mishi dad'i domin gabad'aya jiyayi bayason abinda zaisa Meena tayi nisa dashi. Tunani barkatai Hafeez yayi tayi har dai shima yajiyo kiran sallahn yatashi yad'auro alwala yanufa masallaci.
** **
Bayan dawowar Hafeez a masallaci haka kawai ya tsinci kansa da son xaman falo, kasancewar Meena nacikin kitchen, shiyasa ya zauna yana kallon dukk wani shiga da ficenta.
Haka nan Hafeez yayi xaune har Meena tagama kirginta ta jerasu a dinning table ta wucewarta d'akinta domin ta shirya kayan da zata tafiya dasu gobe.
*Washe Gari*
Tunda asubar fari Meena ta tashi kmr yadda tasaba tad'aura abin brkfst ta jerawa Hafeez a dinning area, sannan tashiga toilet ta silla wankanta, tana fitowa tashafa versiline sai powdr Meena bata yarda tayi wata doguwar kwalliya ba domin talura a yan kwanakin nan Hafeez na matuqar nuna kishinsa akanta Wanda ita kuma hakan yan burgeta yana kuma bata tsoro, wata atamfarta tad'auko tasa sannan ta sanya hijabi har gwiwa.
Travelling bag dinta tajawo ixuwa falo, sannan tanufi sashen Hafeez ta kwan kwasa mishi kofa.
Hafeez nacikin d'akinsa yafito a wanka kenan yaji kmr ana buga kofa, jallabiyansa ya jawo yasaka sannan yaje ya bud'e kofan.
Meena yagani tsaye cikin shirinta na tafiya ga kuma nan jakar kayanta a gefe, haka kawai Hafeez ya tsinci kansa da fad'uwar gaba. Jiki a sanyaye hafeez yadubi Meena yace "har kinfito? Meena tace eh! Ina kwana Hafeez yace lpy Lou.
Mamakine Yakama Meena don yau ko ince ynxu taga wani irin canji atattare da Hafeez komai yakeyi tamkar Wanda bashi da lakka ajiki haka nan ya kama jakar Meena yasa a booth din motarshi.
Har gdan Baba Rabi yakaita, Hafeez yashiga sungaisa da Baba Rabin sannan yamusu Allah kiyaye hnya.
Bai wani jima ba a gdan yayi sallama da Baba Rabi, Meena har tayi xamanta domin bata da niyyar mishi Rakiya, sai da Baba Rabi ta doka mata harara sannan ta tashi tabi bayansa.
Xakujini anjima don jin ci gaban lbrin, ynxu banda caji ne. Tnxs oll😘
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:06PM, 8/6/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣8⃣
Wurin Motarsa kai tsaye Hafeez yanufa yayin da Meena tarufa masa baya, bud'e motan yayi ya xauna batare da ya rufe ba, hakan ne yabawa Meena dama bud'e daya site din itama tazauna.
Wata irin nannauyar ajiyan zuciya Hafeez yayi sannan yamaida dubansa ga Meena yace "idan kukayi tafiyan sai yaushe zaku dawo? Meena wacce ke wasa da gefen hijabinta kai duqe tace naji Amma nacewa sati d'aya xamuyi mudawo, dammm! Gaban Hafeez yafad'i amma sai yayi saurin dakewa yace olryt" shiru sukayi gabad'ansu na d'an wani lkci, can dai Hafeez yace "amm Balkisu takirani ta sanar dani cewa drivan Dr Muh'd ne xaikiku can Gwazan ko? Meena tace eh shine..
Ciro kudi Hafeez yayi sannan yamiqawa Meena yace gashinan susha mai a hanya, kar6a tayi sannan tayi mishi godiya, Hafeez ya maida kallonsa ixuwa wani gefe batare da yakalli Meena ba yace "i hope kinji gargad'in danayi miki cewa banda sa gyale " Meena tace insha allahu zankiyaye hakan.
Murmushin jindadi Hafeez yayi yace "vry gud of u"Meena dai batace komai ba. A dan gaggauce Hafeez yace ni xanwuce kada nayi latti Allah tsare hanya, Hafeez sai tsintar knsa yayi dacewa "ki kula da kanki Meena"
Insha allahu shine abinda Meena tafad'a sannan tafice a motan, sai da Hafeez ya 6acewa ganinta sannan tashiga gda.
Hafeez na isa cikin falo gabad'aya sai yaji dukk gdan yamasa fili babu Meena ba Balkisu, wata irin kewa ce tadinga shigarsa Wanda hakan yasa Hafeez yanufi dinning area yaxauna kawai sai tsintar kansa yayi yanacin abinda Meena ta girka masa
Hakanan Hafeez yagama cin ferfesunsa sannan yazuba kunun gyad'a yafara sha yana lumeshi idanu, cikin ransa sai tunani yakeyi haka dama Meena ta iya girki bansani ba Oh my God!! Hafeeez yabud'e cikinsa sosai yakwashi girki.
Bayan ya kammalane yanufi d'akinsa domin ya shirya zuwa office.
** ** **
Balkisu da kanta ta tura Habu driva yad'aukisu Meena, hakanan suka kama hanya, cikin ikon Allah sun samu isa garin gwaza lafiya.
Yan'uwa da abokan arziqi kowa yayi farin cikin ganin Baba Rabi, haka nan su Baba Rabi sun sami tarbo mai kyau awajan yan'uwansu (kasancewar iyayen Baba Rabi sunjima da rasu, a hannun kawunta ta taso) Khadija yar gdan kawu Usman tun zuwan Meena gdan nan Allah ya had'a jininsu khadija tayi farin ciki sosai da xuwan Meena(kawu Usman shine kawun Baba Rabi) yaransa guda biyar mata hudu daga ciki dukk sunyi aure sai khadija auta.
Meena ma tajidadin kasancewa da Khadija sosai, gashi sunkasance sa'anin juna, khadija tabawa Meena wata hud'u shiyasa inkagansu atare tamkar wasu twns,
Tun zuwansu gwaza Meena kullum tana tare da khadija tana d'aukan lesson domin kuwa khadija akwai wayo da son gayu shiyasa kullum Meena na tare da ita tana koyan wasu abubuwan.
Abangaran Hafeez kuwa fushi yake da Meena wanda ita batasan ma yanayi ba,..fushi yakeyi sbd Meena bata kirashi tasanar dashi sun Isa lafiya ba, sai abakin Balkisu yakeji. Kullum Hafeez wayanshi na kusa dashi yana jiran call daga Meena amma shiru kakeji, da xarar Hafeez ji kira yashigo wayansa da hanzari xai jawota yaduba a tunaninsa Meena ce takira, Hafeez nason kiran Meena a koda yaushe amma girman kai yahanashi aikata komai.
*Bayan Sati Daya*
Dakyar Hafeez yaga wucewan sati dayan nan domin kuwa jinsu yake tamkar shekara d'aya wani irin farin ciki Hafeez yake ji idan ya tuna cewa Meena yau zata dawo kmr yadda tafad'a mishi, hakanan Hafeez yatsinci kansa da fita waje yana sadaka sbd farinciki.
A gajiye Hafeez yakoma gda falo ya kwanta domin yahuta, baifi wucewan minti biyu ba yafarajin bacci na fisgarsa, kmr daga sama yaji wayansa Na ringing da farko har ya share har ta tsinke baid'aga ba sai da aka sake kira a karo na biyu sannan yasa hannunsa ya lalubo wayar d'aukan kiran kawai yayi batare da yaduba sunanan ba.
Cikin muryan bacci yace "hello" a bangaran Meena tace Assalamu alaikum, lkci d'aya Hafeez ya fahimci mai mgn firgigit ya miqe ya xauna dasauri Hafeez yace Meena kece?
Meena tace eh Yaya nice dama nabugo insanar maka cewa akwai wani biki da zamuyi anan bazan samu damar zuwa yau ba inaso zanqara wani satin sbd in.....kafin Meena taqarasa abinda take son fad'i tuni Hafeez ya katse wayan.
Wani irin numfashi Hafeez keyi cike da tashin hnkli sbd tsabar takaici baisan lkcin da yayi wurgi da wayansa ba yace "ohhh no Meena baki Isa ba I cnt tollrt it any more idan baxaki iya dawowa da kanki ba nizanje nadawo dake, tsawan wannan satin dakikayi bakisan halin damuwar dakikabar ni aciki ba, am vry eager to c ur cute face Meena.
Hafeez nafad'in haka yanufi d'akinsa da sauri car keys dinsa ya Zara yadawo yadauki wayansa afalo ya fice a gdan.
Hafeez na kan hanya yakira Dr Muh'd yace yanaso Dan Allah yabashi aron Habu driva zai rakashi izuwa wani waje, Dr Muh'd yace okay Abokina ba damuwa.
Asibitinsu Dr Muh'd Hafeez yanufa yad'auki Habu driva yace dashi yanaso yarakashi garin da yakaisu Meena a yau din nan. Cike da bin umarninsa Habu driva ya harba motansa izuwa garin gwaza.
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:54AM, 8/7/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣9⃣
Kasancewar Habu driva yasan gdan kawu Usman hakan yasa suka nufi gdan kai tsaye.
Meena ce zaune tsakar gda ita kadai ta rafka uban tagumi tunani ne sosai aranta addua kawai takeyi kar Allah yasa Yaya Hafeez yace baxa tasamu daman tsayawa bikin nan ba,
Meena tayi nisa sosai cikin tunaninta sai jiyayi andafata a hnkli tadago kanta, Khadija tagani tsaye, ae kuwa bashiri tasakar mata murmushi, cike da kulawa Khadija ta duqa daf da Meena tace sister anya lpy kuwa? Wani murmushin yaqe Meena tasakeyi sannan tadubi Khadija tace "sister lpy Lou mekika gani?" Khadija tace a'a naga kinxauna ke kadai kin zuba uban tagumi ko dai kina tunanin Shine? Dasauri Meena tace haba dai khadija wlh ba haka bane kawai nadamune sbd inason natsaya bikin Hamza (hamza qanin Kawu usman ne) Khadija tayi murmushi sannan tadafa kafadan Meena tace "kema bnda abinki banace ki kira mijin naki kisanar masa cewa kina son yabaki damar qara wasu kwanakin ba?.
Meena tashare kwallar dake qoqarin zubo mata tace "wlh sister na jarabba hakan hasalima dana fadamishi bai ce dani qala ba kawai yakashe wayansa.
Khadija tace ohhh wlh kina damuwa da abinda baikamata ace kindamu ba, kikasani ko ntwrk ne ko rashin caji kibari anjima kisake tryn. Murmushin yaqe Meena tayi tace oky.
Khadija tace yauwa kokefa, nan taja hannunta tace tashi ma muje kasuwa daxu Baba yabamu kudin sayen anko yakumacemin haddake dan haka kisaki ranki kitashi mutafi.
Jiki ba kwari hakanan Meena ta tashi tashirya suka tafi kasuwa.
Su Meena ko minti uku basuyi da tafiya kasuwan ba sai gasu Hafeez sun kunno kai cikin anguwar.
Dai dai kofar gdan Habu yayi parkn, kafinma yace da Hafeez wani Abu tuni Hafeez din yafahimci cewa nan ne gdan.
Fitowa sukayi daga cikin motan sannan suka sami yaran dake wasa kofan gdan suka aiki daya daga cikinsu akan yaje yace wai ana sallama da Meena
Yaron kuwa dagudu yashiga cikin gdan kmr yadda aka umarce shi, yana zuwa yace "wai inji wani mutumi awaje yace ana sallama da Meena"
Amma nadaga cikin d'aki tajiyo muryan yaron da sauri tafito waje tace da yaron "waye ke sallama da Meena?" Yaro yace shima baisani ba, Baba Rabi tace da yaron yatsaya nan tashiga ciki tad'auko hijabi tace da yaron suje tagani.
Koda fitar Baba Rabi izuwa waje Hafeez tagani tsaye jingine da mota, dasauri taqara wajansu tana musu sannu da zuwa, Hafeez kam sai waige waige yakeyi inda xai hango Meena.
Baba Rabi tace "sannunku da zuwa Hafeez kai ne tafe? Hafeez yayi murmushin yake yace wlh kuwa Baba nine, Baba Rabi tace toh sannunku da zuwa kushigo daga ciki.
Dakin Kawu Usman Baba Rabi tasauqe su Hafeez, bayan sunqara gaisawane baba Rabi takawo musu ruwan sha.
Sannan tace da Hafeez yad'an jira kadan Meena sunfita ita da yar'uwarta, shiru Hafeez kawai yayi, tunanin inda Meena taje a wannan yammacin kawai yakeyi.
Abangaran Meena kuwa suna can kasuwa wajen siyan anko, bayan sungama ne Meena tace sister inaso kikaini inda ake siyan gyale da hijabi, haka nan Khadija takaita gurin da tabuqata, Meena tasaima kanta hijab kallan ankon nasi sannan tasaima Khadija Gyale itama kallan ankonsu.
Haka nan suka gama siyayyansu cike da farinciki suka koma gda.
Mai taxi na ajiye su Meena fitowan nan da zatayi idanuwanta sukayi tozali da motar Hafeez, rass!! Gabanta yafad'i, amma sai tadake domin tana tantama kmr ba motansa bace, hakanan suka kwashi kayansu suka nufi cikin gda.
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [3:57AM, 8/7/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode4⃣0⃣
Suna shiga cikin gdan da sallamarsu kafin sunemi waje suzauna Baba Rabi tace "kee! Aminatu daga xuwa kasuwa kuje kudawo shknan sai kumaida gari naku kuje kuyi xamanku, Meena tace Amma wlh ba haka bane mund'an tsaya siyan wasu abinne shiyasa mukadan jima.
Baba Rabi tace toh ae kunkyauta sai kitashi kije d'ankin Kawu Usman kinyi baqo, dasauri Meena takalli Baba Rabi tace "Amma baqo kuma"? Baba Rabi eh kawai tacemata tabar wajan.
Khadija tadubi Meena tace sister tashi kije natabbata babu wani namijin daxaixo yanemiki har ayimishi izinin zuwa d'akin Kawu face mijinki, plss tashi ki kintsa kijeki.
Kafin Meena tace wani Abu Khadija taja hannun Meena izuwa d'akinsu, nan ta tsara mata kwalliya mai kyan gaske Khadija da kanta tabud'e akwatin Meena taza6o mata wasu riga da siket masu kyau tace tasasu. Batare da Meena ta musawa Khadija ba hakanan tadauki kayan tasa, sai da tashirya tsaf sannan tasanya hijab tanufi d'akin kawu usman.
Qamshin turaren Meena ne yadoki hancin Hafeez, dasauri yad'ago kansa Meena yagani tana qoqarin xama bisa kujerar da yake zaune.
Meena wacce gabanta yatsananta Faduwa cikin siririyar muryanta tace sannu da zuwa Yaya ina wuni? Hafeez ya kura mata idanu ko qiftasu bayayi, shiru yayi tamkar baxaice komai ba , can dai yace Meena ba wannan ne yakawoni ba "Habu driba kam tun shigowar Meena yabar d'akin" Meena tayi shiru tana sauraren Hafeez taji da wacce yaxo.
Hafeez ya matso daf da Meena yace zuwa nayi domin inaso kimai maitamin abinda kikace lkcin da kika kirani awaya d'axu.
Shiru Meena tayi takasa cewa komai sai faman wasa takeyi da d'an yatsanta,, Hafeez yaqufula sosai yace ko bakyajina ne nace kimaimaita abinda kikafad'a daxu. Cikin tsananin faduwar gaba tafara mgn tamkar ta mai in'en "tace umh uhm dama cewa nayi inaso kabani dama domin na samu halartan bikin Hamza.
Hafeez yace okey dukk satin da kikayi anan basu isheki bane,? Meena tayi shiru! Hafeez yace kibani amsa mana ko kuma baki san cewa kinbar mijinki shi kad'ai cikin wani hali na kewa ba?
Kewa?? Shine abinda Meena tamai maita cikin xuciyarta, Hafeez yace toh bari kiji nazo intafi da mamata kuma ayau din nan komin dare xamu bar Gwaza mukoma Maiduguri, Meena tad'ago kai fuska a maraice tace "Dan Allah yaya kayi hkri kabarni ko kwana biyu ne inqara.
Cike dajin haushinta Hafeez yace kinsan Allah bari kiji wlh ko awa d'aya bazan bari kiqara ba, kuma kitashi ynxun nan kije kihado kayanki inajiranki a mota.
Hafeez nafad'in haka yatashi yabar d'akin, a tsakar gda ya tarar dasu Baba Rabi.. nan yaduqa har qasa yayi musu sallama yace "Baba ni zan wuce ynxu" Baba Rabi tace haba Hafeez baka tsoron kuyi dare a hanya, murmushi yayi sannan yace Bakomai insha allahu, nan yayi musu godiya yafice a gdan yakoma cikin motarsa yana zaman jiran fitowan Meena.
Abangaran Meena kuwa dagudu ta tashi takoma d'akinsu Khadija sai faman kuka takeyi, Baba Rabi nazaune cikin d'aki taga wulgawar Meena dasauri ta tashi tabi bayanta.
Ko dashigarta ta tarar da Meena na kuka tana had'a kayanta, Baba Rabi tadubi Meena tace "ke kuma miye kikewa mutane kuka?" Meena wacce kuka yaci qarfinta tafashe dawani sabon kukan tace " Amma Yayane yace yaxo tafiya dani bayan Kuma nafadamishi cewa muna da biki.
Baba Rabi wani uban tsaki taja tace "mtsww aekin wofi kawai yoo dama inkika zauna bikin kawu Hamza uban mexaki tsinana toh kisani dukk wani abu marar muhimmanci dakike tunani yafi miki bin umarnin mijinki domin kuwa bikin Kawu Hamza kodake ko bake xa'a daurashi dan haka kirufewa mutane baki tun baki tarawa kanki jama'a cikin d'akin nan ba.
Meena kam gabad'aya takawo iya wuya wani irin takaicine ya sarqe ta, dasauri tashirya kayanta tsaf tayi sallama da kowa kafin Khadija tadawo tayi saurin ficewa tabar gdan (khadija na gurin Sa'idu tailor ta kaimusu kayan ankonsu dinki)
Fushi Meena tayi sosai dan haka tana xuwa tasa kayanta a booth tabud'e gdan baya tazauna.
Hafeez naganin haka yafito daga gaban mota yadawo baya inda Meena ke zaune, kowa na gdan yafito yayi musu Allah kiyaye hanya.
Batare da Bata lkci ba sukabar cikin garin gwaza, suka kama hanyan Maiduguri.
0 comments:
Post a Comment