Suna bude ido tace"Ku tashi kuyi alwala kuyi sallah." Saddiqa ta sauko da sauri ta bude akwatin kayansu makilin da brush ta dauka ta fita domin daura alwala.....Cikin tsawa ta kalli Mussadiq kamar shi yayi mata laifin tace"Kai ba zaka tashi ba sai na gaggaura maka mari ko."! Yaron ya tashi a furgice yana kallonta! da hannu ta nuna masa 'kofar fita tace"Kaje kayi alwala gari ya waye." sakkowa yayi daga katifar shima ya dauki abun wanke baki ya fita.
Hijab ta zura ta gyara dadduma ta tayar da sallah, Tana idarwa ba tayi wata adduar kirki ba ta sake daukar wayar tana dubawa, har yanzu dai babu amsa! Tsaki ta dinga ja zuciyarta na wani irin tafarfasa! babu shakka Abbah Abbas da gaske yake! tasan yaga text d'inta kunya ta hana shi bata amsa shiyasa ya shareta.
Numbar Salim ta laluba ta shiga kira. sai dai wayar a kashe take dan bai tashi ba ballanta ya kunna wayar......Mi'kewa tayi ta koma bakin katifar ta zauna had'e da cire hijab din jikinta, Numbar Abbah Abbas din ta sake nema ta 'kara tura masa wani text in kamar haka.
_Abba ina jiran amsa nasan dai kaga text d'ina dan Allah ka bani amsa shin kaine ka nemi aure na? ko kuma su Baba malam ne suka baka ni."?_
Tura masa tayi ta tsirawa wayar ido tana adduar Allah yasa yayi mata magana.............Shi kuwa Abbah Abbas yana kwance Halisa na matsa masa a jikinsa yana lumshe ido baccin da ya tara kwana da kwanaki ne yake damunsa, tinda Halimatu ta rasu bacci da nutsuwa suka 'kaurace masa, mutuwar Halimatu babban gi'bi tayiwa rayuwarsa, gani yake ma ba zai ta'ba samun mace tagari kamar ta ba, Yayi yun'kurin auran Naja'atu ne ba dan komai ba sai dan yasan ita d'in tarbiyyar Halimatu ce yana kwadayin ta zama matarsa domin hausawa suna cewa gida bai 'koshi ba to ba za'a bawa dawa ba, bayan haka kuma yana tausayawa 'yan 'ya'yansa sosai saboda yanxu suna bukatar mai kula dasu sun saba da mamansu sosai dole idan suka dawo gidan suka ga babu ita su shiga damuwa, amma duk rintsi idan suna kallon Naja'atu a gidan kuma a matsayin matarsa to zasu samu sassauci a tare dasu.
Babban abinda yake d'aga masa hankali acikin al'amarin shine! yanda zai tunkare su da maganar! Salim da Naja'atu gabadayan su bai san abinda zai ce musu ba, Salim bashi da Uban da yafi shi, hakan nan itama Naja'atu bata da uban da yafi shi, tabbas da zai iya hakura da ya hakura ya kyalesu sunyi auransu, amma ba yajin zai iya janye kudirinsa ba dan komai ba sai dan samun walwala da farin cikin 'yayansa guda biyu, saboda ya riga ya sani cewar babu wata mace da zai aura ta ri'ke masa su tsakani da Allah! shiyasa yake ganin auran Naja'atun shine yafi alkairi a garesu baki daya.
'Dan juyawa yayi ya d'auki wayarsa ya bud'e text din ya sake bud'awa domin ya sake karanta sai yaga wani ya sake shigowa, Ya bude idonsa sosai yana karantawa! Murmushi yayi wanda yasa Halisa kallonsa da sauri tace"Allah yasa alkairi ne naga kana murmushi." Kallonta yayi yana kokarin rufe wayar dan ganin tana le'ko da kanta tana so ta ga abinda yakewa murmushin, a hankali yace."Alkairi ne insha Allahu." Tace"To Allah ya tabbatar mana dashi, mikewa tayi ta fita daga dakin tana fad'in "Bari na shiga kicin na shirya abin karin kummalo." Ya bita da kallo Ba tare da yace mata komai ba, ajiyar zuciya ya sauke bayan fitar ta daga d'akin, tabbas idan Halisa taji wannan babban al'amarin akwai tashin hankali! ya riga yasan halinta da mugun kishin tsiya! uwa uba kuma tsakaninta da Yarinyar basa jituwa ko kadan yanzu yanda zai tunkareta da maganar yake tunani.......Kira ya shigo wayar dake hannunsa, koda ya duba numbar Naja'atun ce yayi serving da My doghtar! kamar kada ya daga sai kawai yayi 'kundumbala ya d'aga wayar yana d'an gyaran murya, kafin ma yace wani abu yaji shashshekar kunanta a kunnasa.
Jikinsa ne yayi sanyi ya sassauta murya irin yanda yake mata idan tana irin wannan kukan yace."Dota ya akayi kuka da sassafe kiyi shuru muyi magana ko."!! hanci ta sha'ka! zuciyarta sai tafarfasa take tace"Abba tun jiya na turo maka da text baka bani amsa ba kuma nasan ka gani dan girman Allah ka bani amsar abinda na tambayeka ko na samu zuciyata tayi sanyi."""" Jim yayi kafin yace."Kinga ni ban ga text d'inki ba ballanta na baki amsa amma kome kika rubuta min a text din ina sauraranki yanzu ki fad'a min."
Cikin rawar baki tace"Jiya bayan kasa Salim ya kawo mu gidan Baba Malam shine naji suna wata magana wacce tasa raina ya kusa futa daga jikina, ashe wai kai ba kaine ka haifeni ba , sannan babban abinda ya furgita ni yasa na shiga cikin halin damuwa da tashin hankali wai kaine da bakin ka kace musu su baka ni na zama *MADADIN* matarka da ta rasu, shine nake ganin kamar sune suke so suyi wannan had'in da bai dace ba! ai abun kunya ne ace wanda nake amfani da sunansa ako ina a matsayin mahaifina aji shine kuma zai aureni ina zan saka raina idan hakan ya tabbata."!! Cikin sar'kewar murya ta 'karasa maganar........Shuru yayi kawai yana jin saukar numfashinta a kunnansa bakinsa yayi masa nauyi gabad'aya ma ya rasa me zai ce mata.
Murya na rawa tace"Abbah wannan shurun da kayi yana nuna min cewar da gaske ne maganar daga bakin ka ta fito!!! Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! kaico da wannan furucin naka! Abbah! dan girman Allah ka janye wannan maganar da kayi, na rantse da Allah ba zan iya zaman aure da kai ba ni a matsayin Uba na dauke ka."
Tana wani irin kuka take masa maganar, Yaji jikinsa duk ya mutu! Gumi ne ma yake tsatstsafo masa kamar ba safiya ba, da kyar ya iya cewa" To naji maganar ki zanyi shawara a kai idan da akwai yuwuwar na hakura dake zan samu su malam d'in na fad'a musu duk shawarar dana yake, ki daina kuka haka kada ki janyowa kanki wani ciwon na daban." Tace"To Abbah ni da daina kuka ai sai naji maganar wannan auran ta rushe sannan zan daina kuka."!! Mamaki ya kama shi, da jin maganarta sai ma ta bashi dariya yayi kad'an kafin yace."Naja'atu me yasa bakya son na zama abokin rayuwarki."? Taji wani irin fad'uwar gaba jin abinda yace. Tace."Abbah Please ba girman ka bane dan Allah kada ka 'kara yi min wannan maganar kai ubana ne *Salim* kuma shine abokin rayuwata." Kishi ne ya kama shi jin abinda tace kawai sai ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba.
Ajiyar zuciya ta sauke bayan kashe wayar tasa, ta juya tana kallon Bayanta, Saddiqa da Mussadiq sun futa daga dakin tun d'azu! taji dad'in hakan, sai ta mike itama tabi bayansu dakin Baba Talatu.
Suna zaune a kusa da Baba Malam suna karyawa da kunu da kosai ta shiga da sallama a bakinta, a hankali ta tsuguna kusa da Baba Malam tana gaishe shi ya amsa cike da kulawa yana d'an nazarinta ganin idanunta sunyi jawur! yasa yace."Ya kwanan kuka."?
'Kasa tayi da kanta! Baba Talatu tace"Kina so ki janyowa kanki damuwa da ciwo da kinyi halin Halimatu da ba kiyi mana gardama ba, Halimatu komai muka umarceta dashi tana mana biyayya dai-dai gwargwado amma ke tun jiya ake magana daya dake, idan kika bujirewa umarninmu baki kyauta mana ba kuma baki kyautawa 'Yar uwarki ba, a yanzu babu abinda za kayi kisa ta farin ciki illah ki zama *MADADIN TA* Ki tallafi abinda ta bari gasu nan suna kallonki." Ta nuna su Saddiqa dake zaune.
Shuru tayi ta kasa magana ba wai dan bata da abin cewa ba kawai dai bata son suyi ta sa'insa da iyayenta.....Baba Malam dai shuru yayi ya dauki kofin kununsa yana sha yana had'awa da kosan sa dake cikin wata silba dake gabansa.
Saddiqa ce ta zuba mata kunun ta ajiye mata a gabanta sannan ta mi'ka mata abun da 'kosan ke ciki tace"Yaya Naja'atu gashi nan ki karya kema." Kallonta tayi sai taji zuciyarta ta tsinke! sosai yaran suke bata tausayi Saddiqa ta damu da ita sosai koda can bata son taga 'bacin ranta, tabbas a wannan lokacin ne ya kamata tayi mata sakayyar abun alherin data dad'e ta nayi mata.
Domin Saddiqar taji dadi yasa ta dauki kofin kunun tana kur'ba a hankali tana had'awa da kosan dake gabanta, Baba malam na gama karyawa sai ya dauki redion sa ya mike yana kallonta yace."Idan kun gama kun kintsa ku shiga gidan Alhaji dake dasu Saddiqa ku gaishe dasu." A sanyaye tace"Inasha Allah." takalmansa dake bakin kofa yasa ya fita daga gidan hannunsa ri'ke da redionsa.
Suna gama karyawa sai sukayi wanka suka shirya tsaf! Naja'atu da Saddiqa suka shirya cikin kaya iri daya hatta da d'inkin jikin atamfar iri daya ne komai iri daya Abbah Abbas ke musu baya bambamta su sai da gurin d'inki na Naja'atu yana d'ara na Saddiqa da wani abun, milk din hijabi toyobo ne a jikinsu ya sauka har 'kasa! Suna kokarin fita daga gidan da nufin shiga gidan Alhaji Sama'ila, Shi da Salim suna kokarin shigowa cikin gidan.
'Kamshin turaransa ne ya tabbatar mata da cewar shine Kafin ma tayi wani yunkuri sun shigo Shine a gaba Salim na take masa baya, Yana sanye da farar shadda kar 'Dinkin tazarce har kasa, da adon surfani a wuyan rigar da hannunta kansa sanye da farar hula mai ratsin 'baki! a zahiri idan ka kalleshi ba zaka ce ya kai shekarun da yake dasu ba, za'afi tunanin shekarunsa ba sufi 43 zuwa 45 ba, Abbah Abbas mutum ne dan gayu mai yawan ado da kwalliya, kuma ma'abocin kamshi shiyasa kullum baka ganin tsufasa, dan idan yace ya kai matakin shekara 50 a duniya da yawa wasu ba zasu yarda ba, sai dai kuma masu nazari da tunani idan sukayi masa kallon tsanaki a zasu fahimci cewar ya kai shekarun da ya fad'a d'in.........Da gudu Mussadiq yaje ya rungumeshi yana fad'in ''Oyoyo Abba." Yana d'an murmushi ya bashi hannunsa tare da fadin"Barka da Asuba magajin Abbah." Mussadiq na dariya ya rike hannun mahaifin nasa suka gaisa sosai........Saddiqa na murmushi tace"Abba ina kwana ka tashi lafiya."? A nutse ya d'aga kansa yana kallonsu ita da Naja'atun Yace."Lafiya lau na tashi Ina zakuje da sassafe haka."? Yana kallon Naja'atu yayi maganar."!
A kanta a kasa ta gaishe kafin tace"Zamu shiga gidan Alhaji ne mu gaisa." Yace."To babu damuwa nima yanzu zan shigo gidan.'' Kokarin ratse ta yake ya shiga cikin gidan, tayi saurin bashi hanya, tana sunkuyar da kanta, gani tayi yau fuskar sa babu walwalar da ya saba yi mata koda yake ai dole dama ya kasa sakin jiki da ita saboda yasan abinda yayi.
Ta kalli Saddiqa tace"Kuje gani nan zan biyo bayanku." Saddiqa ta kalleta tana kallon Salim da yayi wani kici-kici da fuska yana kallonta ya wani zuba hannuwansa a cikin aljihun jins din dake jikinsa.....Saddiqa jikinta sanyi yayi ganin yanda Naja'atun ta wani d'aure mata fuska! sai taja hannun Mussadiq suka fita daga gidan
Salim ya tsira mata ido bayan fitar su Saddiqa yace."Me kike fahimta ne daga gurin wannan Dattijon."? Cikin sanyin jiki da sarewa da al'amarin tace"Ni wallahi har yanxu na kasa gane inda ya dosa, dazu dai munyi waya dashi na ro'ke shi akan ya janye kudirinsa yace."zai yi shawara idan ya yanke magana zai fad'awa Baba malam abinda ake ciki."
Cikin 'kunar zuciya Salim yace."Jikina baya bani cewar Mutumin nan zai hakura dake My Princess shin idan ya kasance shine ya samu damar mallakar ki ya zanyi da raina watakila ma ina jin shikkenan 'karshen rayuwata ne yazo." Cikin wata iriyar siga yayi maganar yana matsawa kusa da ita.
Hawaye ne suka 'kwace mata tace"My Prince ka daina wannan maganar dan Allah insha Allah Allah ba zai bashi nasara ba, Ni bani da wani miji sai k..........Maganar ce ta ma'kale a bakinta sakamakon zuwansa gurin! Ya kallesu sunyi wani daf da junansu kamar zasu rungume junansu, kana kuma kallon yanayin su zaka fahimci suna cikin mayen son junansu a lokacin kome zasu iya aikatawa! Tsawa ya buga musu yana kallon Salim din Yace. "Kai meye haka ka tsaya daf da ita rungumeta zakayi ko me."?
Salim yayi gaggawar barin kusa da ita yana sosa kansa irin na kunya yace."Kawu kasan sau tari nakan shiga wani yanayi idan yarinyar nan na kusa dani, dan Allah Kawu kayi wani abu akan al'amarin aurena da ita."
Kallon shashasha yake masa kafin yayi 'kwafa ya kalleta tana ra'be a jikin bango tana goge fuska! Kamar zai ce wani abu sai kuma ya fasa, ya kalli Salim din rai a 'bace! yace"Shige muje." Salim ya shiga sosa kansa yana d'an kallonta ta 'kasan ido ya fita daga gidan, shima ba tare da ya sake kallon inda take ba ya fita ranshi a 'bace! wani irin kishi ne yake damunsa a zuciyarsa ganin abinda ya wanzu tsakaninta da Salim..
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!))_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_Kungiyar Masu Nazari Da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~~~~~~~
*9*
Cikin sanyi jiki da mutuwar jiki ta fita daga gidan, koda ta fita kai tsaye gidan Alhajin ta nufa tana tafiya kanta a kasa ga wani irin fad'uwa da gabanta yake, tana tunanin idan ta shiga gidan da wane irin ido zata kalli mahaifiyar Abbannasu matar data dauka a matsayin kakarta suke wasan jika da kaka da ita, yau an wayi gari wai itace take nema ta zama surukarta akwai kauna da fahimta a tsakaninta da Hajiyar tana ganin idan Abba Abbas din bai janye 'kudirin sa ba zata nemi taimakon matar tunda mahaifiyarsa ce watakila idan tayi masa magana ya janye.
Tana shiga gate din gidan, ta hangi Abba Abbas din da Abba Alhassan 'kaninsa da kuma Salim d'in a tsaye a jikin wata mota suna magana, Tun daga nesa take kallonsu Abba Abbas din! Tsaki! taja a zuciyarta ta kalli Salim dake kusa dashi, humm yaushe ma za'a had'a! Salim saurayi mai tashe mai jini a jika gashi dan gayu dan kwalisa, babu abinda yake burgeta a dashi sai 'kayatacciyar fuskarsa mai dauke da siririn saje wanda yayi masa kyau sosai tana bala'in son Salim saboda kyawunsa kuma ya iya kwalliya mai burgewa, shi kuwa Abba Abbas ya wani bar gashin fuska (gemu ) ya cika masa fuska duk da cewa a gyare yake hakan bai burgeta ba, babban abinda yake 'kara sawa ta sake jin tsanar auransa, shine tsali-tsalin furfurar data fara fito masa a gashin fuskarsa(gemu) Ai abin dariya ne ma ta nunawa kawayenta shine mijinta, gaskiya ita kam ba zata iya auransa ba, a tsarinta tafi son ta auri Saurayi wanda zasu mori 'kuruciyarsu amma auran Abbah Abbas babban nak'asu ne a tattare da ita
*(Humm! Waye ya fad'a miki haka Naja'atu.")*
A nutse ta iske inda suke tsaye kamar munafuka ta dinga 'boye fuskarta tana gaishe da Abbah Alhassan ya amsa fuska a sake yana d'an kallonta a fakaice hakika yarinyar na burgeshi mutuka tana da hankali da nutsuwa kuma babu shakka idan d'an uwansa ya aureta yayi dace da samun mace tagari.
Abbah Abbas kuwa kokarin shiga mota yake yi bai ko kalleta ba dan har yanzu haushinsu yake ji ita da Salim d'in.......Simi-simi ta wuce cikin gidan, Abbah Alhassan ya shiga motar ya zauna kusa da d'an uwansa, Salim yaja motar suka nufi kasuwa.
Hajiya Abu na zaune a 'kasan kafet Saddiqa da Mussadiq na gefanta suna mata wasa kamar yanda suka saba idan sunxo gidan ita kuma sai biye musu takeyi ta ri'ke hannun Mussadiq tamau! wai sai ya bata kud'in shara na shekara biyu! Yaron sai dariya yake mata yana cewa ta sake shi zai tambayi Abbansu ko nawa take so za'a bata. Ita kuwa tayi kici-kici da fuska kamar gaske tace ita sai ya bata zata cika masa hannu idan kuma bai bata ba sai ta cire masa kayan jikinsa a bakacin kudinta......Saddiqa sai dariya take musu, Mussadiq na ganin Naja'atu ta shigo yace."Yawwa Yaya Naja'atu kizo ki cece ni a gurin tsohuwar nan tana so ta karya min hannu." Hjy Abu tace'' Kina zuwa nan sai na murd'e miki hannunki dan dukkanin ku zan iya daku."
Naja'atu tasa dariya tana k'arasawa gurin tace"Lallai Hajiya 'karfi ne dake haka duba kin murd'ewa yaro hannu ki fad'i nawa ne kudin sai a biya ki." Tace."Ai ba zaku iya biya na ba." Tace"To dan Allah sakar masa hannu ya tuba." Tana dariya ta sake shi tace"Ja'iri ashe ba wani karfi ne dashi ba." Yace."Hajiya aike tsohon 'kashi ne dake ni kuwa sabo ne shiyasa da kika ri'ke ni na kasa kwacewa." Gabadayan su suka sa dariya har da ita.
Naja'atu ta zauna a nutse tana gaisheta! Ta amsa cikin kulawa tana kallonta tace"Dama kuwa ina neman ki amma ki fara zuwa ku gaisa da Alhaji yana sama sai kizo mu tattuna magana kinji 'kawata." Naja'atu ji tayi gabanta ya fad'i !!! to wace magana zasu tattauna da hajiyan? tabbas ta tsuniyar gizo bata wuce ta 'koki! sai
Tayi kokarin kauda damuwar fuskarta tana kokarin mikewa tace to shikkenan bari naje mu gaisa da Alhjin."
Sama ta hau inda dakin Alhaji Sama'ila yake, nan ta tarar da Hajiya Rabi a dakin tana gyare-gyare suka gaisa cikin mutunci kafin ta shiga dakin da yake ciki............Tayi kusan minti goma a ciki kafin ta sauko 'kasa suna zaune a inda suke suna hira koda ganin zuwanta gurin sai sukayi shuru Saddiqa ta dinga bin fuskarta da kallo ganin kamar ta sauko da damuwa a tare da ita............zama tayi kusa da Hajiyan cikin tunanin mafita tace"Hajiya gani to na dawo." Hajiya Abu ta gyara zamanta sosai ta bude bakinta kenan za tayi magana, Yaya Ramlatu ta shigo bakinta dauke da sallama. Amsawa sukayi gabadayan su, Ramlatu na ganin Naja'atu kusa da Hajiya sai ta 'bata rai! tayi kici-kici da fuska dan koda Naja'atun ma ta gaisheta bata amsa ba sai gaisuwar su Mussadiq ta amsa! Naja'atu jikinta yayi sanyi ta sunkuyar da kanta kasa tana jinta tana tambayar su Saddiqa ina Abbansu suka ce ya tafi kasuwa!
Yaya Ramlatu ta kalli Mahaifiyar ta tace"Hajiya wata magana naji daga bakin Salim dazu da safe yake fada min shine nace to bari nazo naji shin da gaske ne abinda ya fad'a wai Abbas zai auri waccan yarinyar ta zaune." Tana nuna Naja'atu da hannu tayi maganar.
Hajiya Abu a nutse tace"Eh kwarai kuwa hakane Salim bai miki karya ba! Abbas zai auri Naja'atu insha Allah sai ta zama *Madadin* 'Yar uwarta ko babu komai wad'annan yaran zasu samu walwala da farin ciki."tafada tana nuna su Saddiqa.
Yaya Ramlatu ta zabga salati tana tafa hannu tace"Haba Hajiya da hankalinku da komai zaku bari wannan al'amarin ya faru? Yanzu shi Abbas din ko kunya baiji ba zai auri yarinyar da ya ri'ke ta a matsayin 'yar sa, yarinyar da kuma ya san Salim ne ke neman auranta shine kuma zai had'a takara dashi! a gaskiya wannan abu bai tsarantu ba! gwara tun wuri yayi wa kansa fad'a dan wallahi idan ya sake ya auri wannan yarinyar to duniya sai ta zage shi saboda ya aikata abun kunya, kuma baiyi wa Salim adalci ba."
Hajiya Abu tace"Kece kike ganin kamar hakan bai dace ba amma *MADADI BA HARAM BANE* Dan ya ta mutu a mayar da kanwa d'akinta ba laifi bane! Kuma naji kina cewa duniya zata zagi Abbas a kan me? duniya zata zageshi? naga ke da kanki kika nuna bakye so 'Danki ya auri yarinyar to me yasa kuma yanzu zaki zo da wata magana, idan Salim mai hankali da tunani ne ya dace yayi wa Kawunsa adalci ya hakura da yarinyar ya bar masa kodan marayun 'yayan dake gabansa."
Yaya Ramlatu tace"A'ah!! ni ban hana Salim auran yarinyar nan ba wallahi a duk lokacin da zamuyi maganar auransa yakan ce dani Abbas din ne yake cewa ya dakata tukkuna zaiyi magana da iyayenta, sai kuma yanzu kawai daga ya rasa matarsa ya 'kwace masa budurwa ai hakan sam bai dace ba."
Hajiya Abu tace"To ai sai kiyi tayi dan tuntuni an riga an gama magana insha Allahu kafin nan kafin sati uku za'a daura auran Abbas da Naja'atu insha Allah."
Wani irin kuka ne ya kufcewa Naja'atu! da sauri duk suka juya suna kallonta! had'a kanta tayi da gwiwa tana kuka sosai da sosai! Yaya Ramlatu tace"To hajiya gashi nan dai kin gani zahiri yarinyar nan bata son wannan al'amari dan dai ba zata iya fitowa ta fada muku bane! a wannan zamanin ba'a yiwa yaran yanzu auran dole kada ku tauyewa yara hakkinsu, ni a ganina Abbas ya hakura kawai ya barwa Salim shine maslaha."
Hajiya jikinta ne yayi sanyi ganin irin gursheken kukan da Naja'atu keyi tana kokarin tayi magana Alhaji Sama'ila ya sauko daga sama!
Ganin Naja'atu na kuka sai hankalinsa ya tashi ya zauna kan kujera yana tambayar abinda ke faruwa, Yaya Ramlatu ta shiga warware masa duk abinda yake tsakin Salim da Naja'atun da irin soyayyar da suke.
Alhaji Sama'ila yayi shuru yana nazarin maganar, shi duk abinda akeyi bai san da maganar Salim a ciki ba, to gaskiya idan hakane shi Abbas din shine ya dace ya hakura da yarinyar duba da cewar maganar Salim din ta dad'e kuma shi ya san da ita bai fad'a ba saboda biyan bukatarsa, wannan ba adalci bane, a matsayin sa na wanda suka dauka a matsayin uba a garesu to bai dace yayi musu haka ba, dole ya janye maganar auran yarinyar ya kyale yara suyi auransu.
Ya kalli Naja'atu a nutse yace."Daina kuka Naja'atu ki kwantar da hankalin ki insha Allah ba zaki auri Abbas ba tunda bakya sonsa zamu baki wanda kike so insha Allahu."
Jin abinda Alhajin yace yasa Saddiqa ta fashe da kuka!! ta had'a kanta da gwiwa tana shashsheka! tofa gida ya zama na makoki mutuwa ta dawo sabuwa dan Saddiqa rungume Mussadiq tayi tana fad'in "Mussadiq mutuwa tayi mana tonan silili kowa sai gudun mu yake ana neman kai damu! meye laifin Ubanmu da ba'a sonsa! Ubangiji Allah ya zama gatanmu." Hajiya Abu ta rikice da kuka ta kama yaran ta rungume a jikinta tana fad'in "Babu wanda ya isa yayi neman kai daku! Kuma insha Allahu Naja'atu zata tare a gidan ubanku."
Yaya Ramlatu jikinta ne yayi sanyi ganin mahaifiyar tata na kuka.........Bayan alhajin ya fita Hajiya Abu ta goge fuskarta tana kallon Ramlatu tace"Kin kyauta kan abinda kikeyi kullum burin ki ki tayar min da hankali bakya kaunar na zauna lafiya yanzu meye amfanin wannan abun da kika zo kikayi ashe kinfi kaunar d'anki a kan d'an uwanki? meye Abbas beyiwa d'anki ba amma da abunda zaki saka masa kenan! kinzo kin saka marayu kuka da damuwa suna cikin damuwa a maimakon ki taya su alhini sai kizo ki sake saka musu wata damuwar to sun gode da abunda kikai musu."
Yaya Ramlatu ta share guntin hawayen fuskarta a sanyaye tace"Hajiya ban san al'amarin zaiyi miki zafi haka ba dan Allah kiyi hakuri idan ranki ya 'baci kuma insha Allahu zan umarci Salim ya janye maganar auransa da yarinyar Allah yasa haka shi yafi alkairi."
Jin abinda tace ne yasa Naja saurin kallonta hawaye na tsere a fuskarta shikkenan magana ta 'kare! jiki a sanyaye ta mike ta fita daga palon.
Salim na driving maganar dake damusa nata cin zuciyarsa, ya dan kalli Kawun nasa dake bayan mota shi da 'Kaninsa suna magana, Yace."Kawu ina da magana da kai."! Babu walwala a tare dashi yace."Ina sauraranka." Da kyar iya cewa "Dama kan maganarmu ta kwanaki ce." Kamar be san komai ba yace."Wace irin magana kenan."? Salim cikin dakewar zuciya yace."Maganar Naja'atu mana a cikin 'yan kwanakin nan gabadaya zuciyata ta kasa daurewa sai nake ganin kamar akwai wani abu da zai faru dan Allah ina so kaje ka nema min auranta kamar yanda kayi min al'kawari a kwanakin baya."
Shiru motar tayi babu wanda yayi magana, Abbah Alhassan mamakin maganar da Salim din yayi yake ashe dama soyayya ce a tsakanin Salim da Yarinyar? to me yasa dan uwan nasa yasan da soyayyar dake tsakaninsu ya bijiro da bukatarsa.
Shuru Abba Abbas yayi ba wai dan bashi da abin cewa ba, sai dan ganin cewar shi a gurinsa a bin kunya ne ace yana maganar aurensa da Salim d'in, yafi so yaron yaji maganar a bakin wani idan yaso ya gane ruwa ba'a sa'an kwando bane....
Shurun da yayi tasa jikin Salim yin sanyi, tabbas yanzu ya gazgata maganar Naja'atu cewa Abba Abbas din da gaske yake ba gudu babu ja da baya.
Yaji wani irin d'aci! a ma'kogwaronsa! dishi-dishi! yake gani a idonsa tsabar bakin ciki da 'bacin rai! Ga wani masifar kishin Kawun nasa dake sasakar zuciyarsa! Wai yau an wayi gari wanda yake tunanin shi zaiyi masa wakilcin aure shine yake kassaya dashi.........Shi kuwa Abbah Alhassan ganin 'Dan uwan nasa bai ce komai ba yasa yaja bakinsa yayi shuru haka suka isa kasuwar kowa na sa'ke-sa'ke a zuciyarsa mussaman Salim da yake jin shigar zazzafan zazzabi a jikinsa.
Yaya Ramlatu na fita daga gidan Alhaji Kai tsaye unguwar gwangwazo ta nufa gidan d'an uwan nata........Halisa na zaune a palo tana kallo Yaya Ramlatu ta shiga da sallama a bakinta......Halisa ta mike tana mata barka da zuwa taje ta kawo mata abinci da ruwa da lemo kana ta zauna suna gaisawa.
Yaya Ramlatu sai da ta cika cikinta ta 'koshi tukkuna, ta kalli Halisan tace"Kin san gagarimar maganar da nake tafe da ita kuwa."
Halisa taji gabanta ya fadi! a sanyaye tace"Ban sani ba Yaya sai kin fad'a."
Murmushin takaici Yaya Ramlatu tayi kafin tace"Kina zaune da baki a bud'e har kin samu damar zama kiyi kallo ana can ana shirya miki kasassa'ba."!! Halisa miyau ya dauke daga bakinta tace"Yaya Ramlatu dan Allah fad'a min abinda ke faruwa."
Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace"Mijinki Abbas nacan yana neman auran budurwa 'yar cikinsa, auran cuta da ha'inci Auran da duniya za tayi turr! dashi."!
Halisa ta zabura! ta dafe kirjinta gabanta na wani irin buguwa tace"Aure kika ce Yaya Ramlatu.""? Tace"Kwarai kuwa." Tafada tana tabbatar mata da gaskiyar magana
Wani irin gumi ne ya shiga tsiyaya daga jikin Halisa! "Aure!aure! kalmar ma ba babu dadin ji a kunnanta, wato duk ladabi da biyayyar da take masa da nuna masa kulawar da Halimatu take masa bai sa yaji sha'awar aure ya fita daga ransa ba? ashe duk abinda takeyi masa na kulawa a banza take mutuwar Halima ko sati biyu ba'ayi ba amma har ya fara kokarin aure, shin wai dame ta gaza ne a gurinsa......wasu hawayen takaici da bakin ciki ne suka shiga sauka a kumatunta.....Yaya Ramlatu tace." Ai ba kiyi kuka ba ma tukkuna sai kinji yarinyar da zai aure."! Bakinta na rawa tace."Wacece."? Kai tsaye Yaya Ramlatu tace"Naja'atu ce.'' Sai tayi kasa'ke tana kallonta tunani takeyi wacece ma Naja'atu! dan a lokacin gabadaya kwakwalwarta ce ta toshe ta mance a inda tasan mai irin sunan."
Yaya Ramlatu tace''Kina mamaki! ko da jin wacce mijinki zai aura bari na 'kara tabbatar miki da maganar, Abbas zai auri Naja'atu kanwar matarsa Halimatu yarinyar da ya ri'keta tun tana 'karama yayi mata komai tamkar 'yar cikinsa! shine yanzu zai maye gurbin 'yar uwarta da ita." Halisa ta dinga jin hajijiya tana daga xaune! rintse idonta tayi tana tunano siffofin Naja'atu a idonta!!! a gigice ta bude idonta ta zabura ta mike tsaye tare da cewar "Wallahi ba zaiyi wuba !! ba zan yarda da wannan cin amanar ba! Ni Abbas zaiyi wa haka? me nayi masa a duniya zai had'ani kishi da yarinya 'karama 'yar cikina! kutumar uban nan kayyasa!! sai ta zube kasan kafet ta fashe da wani mahaucin kuka tare d'ora dukkanin hannuwata a kanta.
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*10*
Wani irin kuka Halisa takeyi tamkar wacce aka aiko mata da mutuwar iyayenta, ta d'ago kanta tana kallon Yaya Ramlatun fuskarta gaje-gaja da hawaye tace"Yaya Ramlatu ina zan saka kaina da wannan abun kunyar! shin wai me yake damun d'an uwanki ne? Ya rasa wacce zai aura sai 'yar cikinsa yarinyar da ya ri'ke tamkar shi ya haifeta amma saboda tsabar abun kunya yace zai aureta tsofai-tsofai dashi zai auri 'yar 'karamar yarinya babu shakka wannan karon komai zai faru tsakanina dashi sai dai ya faru dan na rantse da Allah ba zan bari ya tozartani ya had'ani kishi da matsiyaciyar yarinyar nan da na riga nasan matsayinta a zuciyarsa ba."
Ya Ramlatu ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in "Ai shiyasa nima dana ji labarin hankalina ya tashi sosai! Kishi da irin jinin Malam Baba ai bala'i ne wane irin daurin gindi ne Halimatu bata samu ba a gurin Abbas din, ai wallahi kece abar tausayi mutukar kika bari ya auri yarinyar nan to ki rubuta ki ajiye auran ki ya 'kare tsakaninki da mijinki."
Yaya Ramlatu ta 'kare maganarta cikin karfafa maganar ta gami da 'kokarin 'kara ingiza zuciyarta.
Goge fuskarta tayi tace"Yaya Ramlatu ai na fad'a miki wallahi tallahi sai dai ya za'ba ko ni ko yarinyar nan dan ni ba zanyi kishi da Yayarta ba itama nazo nayi da ita ba, wannan karon duk abinda yake ji dashi dai-dai nake dashi zai dawo gidan ya same ni.''
Yaya Ramlatu ta dauki lemo ta kur'ba tace"To ai dik da haka ba zama za kiyi ba dole ki d'an nemi taimako dan baki san irin shirin da iyayen yarinyar suke a kan al'amarin ba, dan wannan tsinannan Malam Baba mugun mutumi ne babu irin surkullan da bayayi." Halisa tace"Yaya Ramlatu ni yanzu gabadaya ma banda kuzarin zuwa gurin wani malami da sunan taimako nifa gabad'aya auran Abbas ya fice min daga rai ya dawo ya sake ni." Ta'karasa maganar cikin rawar murya. Yaya Ramlatu tace"A'a ba za'ayi hakaba ke yanzu idan kika kashe auranki saboda wannan yarinyar ai kin cutar da kanki! kada kice ya sake ki kawai idan ya dawo ki daga masa hankali ke macece kin san hanyoyin da zaka hanashi nutsuwa da kwanciyar hankali gefe guda kuma zamu sa malamai su taimaka miki insha Allah sai zuciyarsa ta karye yaji sha'awar auran ya fita daga ransa da kansa zaice ya fasa."
Halisa tayi shuru tana tunani! Yaya Ramlatu tace"Dole ki futo da kudi aje a taimaka miki ni gaskiya bazan so ki bar dakin ki ba, ki zauna kici ubansu daga shi har yarinyar idan Allah ma ya kaddara sai ta shigo gidan sharri kad'ai ya isheta.
Halisa taja ajiyar zuciya tare dayin 'kwafa, tace"Maganar ki haka take Yaya Ramlatu bari na kawo miki dan abinda ke hannuna dan Allah kiyi min kokari akan al'amarin." Yaya Ramlatu tace"Kada ki damu zan shiga na fita insha Allahu maganar auran zata rushe ke idan ma Allah ya kaddara auran to wallahi ba zamu k'yalesu suji dad'in rayuwa ba." Halisa ta gyada kanta tana dan jin sassauci acikin zuciyarta, bedroom dinta ta nufa, minti biyar ta fito hannunta rike da kudi 'yan dubu dubu. Ta mikawa Yaya Ramalatun da fadin "Dubu ashirin ne zuwa gobe sai ki aiko a kar'bi dubu talatin din zanyi duk yanda zanyi na dauki key din gurin da yake ajiyar kudi na dauka."
Yaya Ramlatu ta mike tana gyara yafan mayafinta tace"Nima daga nan zan wuce gidan *'Yar shagamu* (wata hatsabibiyar 'kawar Ramlatun ce)Ta cigaba da cewa......"akwai wani malami da mukayi hirarsa kwanaki da ita tace ya iya aiki idan dare baiyi ba zamuje idan kuma dare yayi to da sassafe zamu buga sammako dan kada muje mu tarar da mutane." Halisa taji wani sanyi a ranta tace"Yaya Ramlatu nagode kawarai da kaunar da kike nuna min hakika ina alfahari dake a cikin 'yan uwan Abbas kina nuna min kaunar da mahaifiyarku ma bata nuna min."
Yaya Ramlatu ta dafa kafadarta tace"Kada ki damu cikin ko wane irin hali ina tare dake, maganar Hajiyarmu kuwa dama can tafi kaunar Halima a kanki saboda gidan Malam Baba sun riga sun gama dasu daga ita har Alhajin, dan baki ga yanda suke murna da wannan al'amarin ba, Hajiya har da kuka tana 'kokarin yi min baki akan nace auran Abbas da yarinyar bai dace ba, shine fa take kuka har dayi min gorin abinda Abbas din keyi wa Salim."
Halisa ta shiga girgiza kanta, cikin 'kunar zuciya tace"Ai ba sai kin fad'a mun ba dama tuntuni na san Hajiyarku bata sona ko lokacin Halimatu tafi nuna kulawarta a kanta, to kinga kuwa dole taso wannan al'amarin ni na rasa me nayi mata ta tsaneni."
Yaya Ramlatu tace"Wallahi duk sharrin daga gidan Malam Baba yake gabadaya fa sun gama da zuciyoyin jama'ar gidanmu nice kadai na gagaresu." Halisa na jin d'aci a ma'kogwaronta tace"Insha Allahu sai mun karya alkadarinsu."
To sallama sukayi da juna inda Yaya Ramlatu take sake tabbatar mata da cewar yanzu idan ta fita gidan *'Yar Shagamu* zata nufa domin su tattauna yanda al'amarin tafiya gidan malam zai kasance.
Koda Naja'atu ta koma gidan Malam kai tsaye dakinsu ta shige taje ta kwanta kan katifa, ta dinga kuka tana birgima kan katifar! sai sambatun surutai take da kiran sunan Halimatu wai ta mutu ta bar baya da 'kura mutuwarta tana nema ta zame mata barazana ga rayuwarta...........Sautin kukan tane ya cikawa Baba Talatu kunne da sauri ta fito daga kicin ta nufi dakin, nan ta tarar da ita sai burgima take kan katifa tana dukan kanta da kanta kamar wata mahaukaciya sai surutai takeyi da fad'in in dai aka daura mata aure da wani ba Salim ba to sai ta kashe kanta ta kashe wanda aka aura mata......Baba Talatu ta shiga dakin hankalinta a tashe ta birkitota wani wawan mari ta kifa mata a fuskarta tana wani irin huci!! Rintse idonta tayi ta mike zaune hannunta kan kuncinta idanunta a rufe amma hawaye ne kawai yake zurara.
Murya na rawa Baba Talatu tace"Naja'atu idan baki kashe kanki kin kashe Alhaji Abbas ba bakya kaunar Allah! Wai shin ke d'in wace irin yarinya ce butulu mai manta alkairi! yanzu da abinda zaki sakawa da wannan bawan Allahn kenan? wannan wace irin 'kiyayyace kike nuna masa 'karara? meye bai miki ba? ki sani idan da mutuwa bata ratsa tsakaninsa da matarsa ba ke baki isa ya kalleki ba ballanta yace zai aure ki dan saboda baki dace daki auri nagartaccen namiji kamar wannan ba! meye laifinsa? meye kuma illarsa!? Muna tsaka da alhani gami da rad'ad'in mutuwar 'yar mu mai biyayya kina nema ki d'ora mana ciwo! ashe bamu isa dake ba? ashe kuma Halima bata cancanci sakayya al'kairi a gurinki ba? Idan kin auri mijin Halimatu babu wanda zai kai ki Jin dad'i itama kuma zata samu farin ciki alkairin da kikayi mata kin auri mijinta bayan babu ranta kin tallafi 'yayanta! to wallahi duk sanda na kara jin kinyi wani mummunan furuci kan wannan bawan Allahn sai ranki ya 'baci! sai na fad'awa Magaji duk abinda kike yi tunda ni da malam kin raina mu bakya ganin mutuncin mu."!! Baba Talatu ta kare maganarta cikin tsantsar 'bacin rai gami da jin takaicin abinda 'yar tata takeyi.
Baba Talatu fita tayi daga dakin ranta a 'bace! hakika yarinyar bata ta'ba 'bata mata rai ba irin yau! ita rasa gane meye abin gudu a game da wannan auran da suke kokarin had'awa, a iya tunaninta da tsinkayen ta tana ganin kamar gata sukayi wa yarinyar har indai sun had'ata aure da mijin 'yar uwartata dan hausawa na cewa Naji dad'i shine gari ba nasa baba........Baba Talatu na fita daga d'akin ta zame a hankali ta kwanta kasan ledar dakin tana takure jikinta ta cigaba da kukan rashin mafita, a lokacin ji take yi dama Allah zai dauki ranta ta huta daganin wannan masifar.......... Koda Saddiqa da Mussadiq suka shiga dakin suka sameta a kwance tana kuka! Mussadiq ne kawai ya tsaya a kanta yana mata magana ita kuwa Saddiqa saboda tasan ko kukan me takeyi yasa ta juya ta fita daga d'akinta ranta a 'bace! hakika tana jin ba'kin ciki da takaicin irin 'kiyayyar da take nunawa mahaifinta, shiyasa itama ta soma jin haushinta akan irin abinda takeyi kan al'amarin.
Mussadiq ya 'karaci maganarsa ko kallonsa ba tayi ba haka ya fita daga dakin jikinsa duk a sanyaye! haka suke shiga damuwa koda can idan sun ganta tana kuka ko rashin lafiya daga su har mamansu da Abbansu duk su damu duk da bashi da wayo sosai shima ya fahimci cewar Antin tasu bata 'kaunar zaman aure da babansu........Zama yayi kusa da Saddiqa tana gyarawa Baba Talatu wake suna hira jefi-jefi ya kalli Baba talatu da fad'in "Baba me akayiwa Yaya Naja'atu take kuka."? Baba Talatu tace." Kyaleta Mussadiq ka fita daga sabgarta kaji ko." Mussadiq yayi shuru jikinsa duk yayi sanyi.........To Har aka idar da sallahar azuhur Naja'atu na kwance a daki tana juye-juye zazza'bi me zafi ne ya rufe ta wanda ya hanata mikewa taje tayi alwala tai sallah.
Saddiqa ta shiga dakin domin yin sallah ta kalleta itama ta kalleta babu wanda yace komai a tsakaninsu, Saddiqa ta gyara dadduma ta tayar da sallaharta, koda ta idar mikewa tayi ta fita daga dakin ba tare da tace komai ba, to sai hakan da tayi ya bata mamaki sosai! kuma ya nuna mata cewar yarinyar fushi take da ita, jikinta ne yayi sanyi sosai ta rinste idonta murya na rawa tace"Ba laifi na bane laifin zuciyata ne Saddiqa bana 'kin mahaifinku sai dan zuciyata ta riga ta gama makancewa da kaunar Salim, a dai-dai lokacin da muke sanya rai da bukatarmu zata biya a dai-dai lokacin kuma za'a kawo mana cikas a rayuwarmu ha'kika rayuwarmu nida Salim na cikin kalubale mai girma mutukar akace baza'a daura mana aure da juna ba."
Muryar Mussadiq taji a kanta, tayi saurin bude idonta tana kallonsa......Mussadiq duk yaji abinda take fad'a ya fahimci wata maganar wata maganar bai fahimce ta ba, Yace."Yaya Naja'atu ki tashi kiyi sallah kici abinci mu tuntuni munyi sallah munci abincinmu.
Hannunsa ta ri'ke ya zauna kusa da ita murya na rawa tace"Mussadiq bani da lafiya zuciyata na daf da tarwatsewa."!! Da sauri yaron ya d'ora hannunsa saman goshinta yana fad'in "Yaya Naja'atu kanki ne yake ciwo ? sannu bari na kira Abbanmu a waya ya kawo miki magani." Girgiza kanta tayi tana kokarin mikewa zaune tace"Mussadiq wannan ciwon nawa Abbanmu shine ya haddasa mun shi dan Allah kace dashi yayi hakuri ya k'yaleni." Mussadiq ya dinga kallonta cikin mamaki yace."Yaya Naja'atu Abbanmu ba zai cutar dake ba kiyi hakuri ki aureshi ki zauna dashi."! Taji wasu hawaye na kokarin kufce mata, wai kowa sai yace tayi hakuri ta zauna dashi to wai ta yaya zata iya zama dashi alhalin bata sonsa kuma a matsayin Uba take kallonsa, abunfa da wahala wai (gurguwa da auran nesa) mikewa tsaye tayi a hankali ta fita daga dakin, Shi kuma Mussadiq din ya dauki wayarta ya nemi numbar Abban nasu ya shiga kira.
Koda yaga Numbar Naja'atu na kiransa bai 'ki dauka ba, sai dai babu walwala a tare dashi yayi sallama! sai kawai yaji muryar Mussadiq yana fad'in "Abbanmu nine Mussadiq na kira ka da wayar Yaya Naja'atu." Murmushi yayi yana jin wani farin ciki yace."Na gane ka Magajin Abbah Ina fatan lafiya ina Naja'atun take."? Mussadiq yace."Yanzu taje yin sallah bama ta da lafiya sai kuka takeyi tana cewa wai dan Allah ka 'kyaleta."!! Shuru yayi yana nazarin maganar yaron daga bisani yace."To shikkenan kace mata na kyaleta tunda bata son Allura ba zan kawo likita yayi mata ba." Mussadiq yace."Ba wannan ba Abba naji tana cewa kada ka aure ta ita tafi so ta auri ancle Salim Abbanmu tunda bata so ta zauna tare da kai ka kyaleta ta auri wanda take so."!! Abbah Abbas ya jima yana mamakin maganar yaron, kuma yana mamakin abinda yarinyar take yi na rashin kyautawa! wato yaran take zaunawa dasu tana nuna musu a zahiri bata kaunar Ubansu har tana bawa 'Dansa sa'ko ya bashi! ranshi ya 'baci sosai da sosai! sai kawai yayi 'kokarin bagarar da maganar ta hanyar fad'in "Ina Saddiqa take kace mata nace ku shirya gobe zan aiko Salim ya dauke ku xaku koma makaranta ranar Monday." Yace."Tom zan fad'a mata Abbah." Yace." Yawwa ka gaishe min da Baba Talatu da kyau." Yace." Za taji Abbah." Kashe wayar yayi ya shiga nazarin irin iskanci da wulakancin da yarinyar ke masa, zai iya hakura da duk irin cin fuskar da za tayi masa amma kuma ba zai lamunci ta dinga cin fuskar 'yayansa ba, hakan da take yi zai sanya ransu ya 'baci! su shiga halin damuwa da maraicin mahaifiyarsu.
To da wannan 'bacin ran ya shiga gidansa......In da yaje ya tarar da tashin hankalin Halisa dan ko zama bata bari yayi ba tabi shi d'aki! ta shiga zazzaga masa rashin kunya gami da farfad'a masa duk maganar da tazo bakinta kana kuma tace" Sai dai ya za'ba ita ko Naja'atu dan wallahi ba za tayi kishi da Ya tayi da kanwa ba.
Babu Abinda yace mata ya shiga bandaki domin yin wanka zuciyarsa tamkar zata tsaga kirjinsa ta fito dan tsananin 'bacin rai!!!! Koda ya fito samunta yayi a kwance 'kasan ties tana kuka had'e da wata iriyar fuffuka tana burgima 'kasan ties kamar mai iskokai! Ya shirya tsaf ya tsallaketa ya fita ya barta a dak'in! Bin hanyar da yabi tayi da kallo hawaye na sharara ta mi'ke zaune tana cizon tsaya wato Abbas ko gani yayi zata mutu ba zai tanka mata ba kenan ballanta ya fada mata magana mai dad'i! aikuwa a zuciye ta mi'ke tsaye! tana rangaji! da had'a hanya, ta nufi kicin d'inta.
Yana zaune gurin cin abinci yaga fitowarta kallo ya bita dashi yana jan tsaki a fili ya shiga bude kwanonin abincin da ta jera kamar gaske! wayam! babu komai a ciki amma saboda tsabar iskanci da iya shega na Halisa ta shirya tevur kamar ta shirya lafiyayyan abinci......Takaici ne ya kamashi ya tsirawa hanyar data bi ido, kawai sai ya hangota ta fito daga kicin d'in hannunta ri'ke da shar'be'biyar wu'ka sabuwa dal da alama daga cikin kwalinta ta cire, kai tsaye ta durfafo inda yake jikinta na tsuma da rangaji! take fad'in "Wallahi yau koni ko kai a gidan nan Abbas na gaji da wannan abun da kake min ni ka sake ni ma na huta da ganin wannan takaicin auran wannan yarinyar da zakayi masifa ne a gare ni da kai baka sani ba sai sanda nayi maka illah a rayuwarka sannan zaga gazgata maganata." ..........Mufida ta shigo palon tana sanye da uniform na makaranta ta hango abinda ke faruwa, a guje ta jefar da jakarta tayi kan mahaifiyar tata dake dumfarar mahaifinta da dalleliyar wu'ka! tana nema ta caka masa! " Cikin karaji!! tace" Mommy meye haka? me za kiyi? Wayyo Abbanmu ka gudu."!! Tafad'a tare da zuwa ta rungumeshi tana jansa wai ya gudu. Shi kuwa yana tsaye turmin danya bai razana ba, wato wai-wai d'in da yake ji a gari a na cewar mata na kashe mazajen su idan za'ai musu kishiya abun yazo kansa, jira kawai yake ta 'karaso da wukar yaci ubanta! Halisa ido a rufe ta 'karasa inda suke Mufida na kuka tana jansa da fadin "Abbah mu gudu kada ta caka maka wu'ka Abba me kayi mata n...........Gani tayi ya kama duka hannuwan Mahaifiyar tata ya murd'e da iyakacin karfinsa Wu'kar ta su'buce ta fad'i 'kasan gurin! Ya kai mata wani lafiyayyan mari! da bayan hannunsa, wani 'karamin jini ne ya fito daga hancinta, kafin ma ta dawo hayyacinta ya sake kifa mata wani a d'aya gefan, sai kawai yaga ta yanke jiki ta fad'i ta shiga turje turje tana taune harshenta..........Aljanunta ne suke ka da ita a gurin ta dinga turje-turje tana taune harshenta farar kumfa nata fitowa daga bakinta, Halisa na 'karyar aljanu ashe dama tana dasu da gaske! sosai take burgima a gurin tana ta wasu gwalantu wanda ba wanda yake ganewa a cikinsu, Mufida ta nufe ta tana kuka zata ta'ba ta, ya hanata Yace." Je ki cire uniform din'ki idan ta gaji da iskancin da take zata tashi."
Tsakanin Uwa da D'a sai Allah tace"Abbah duba fa kaga abinda take wannan abun ba 'karya bane dan Allah kayi wani abu kai."
Tsayawa yayi tsai yana nazarin Halisan da abinda takeyi Eh kwarai kuwa wannan abun da take yasha bambam dana ko yaushe dan haka sai ya umarci Mufidan ta kawo masa ruwa a kofi, da sauri ta taje ta dauko masa, ya kar'ba ya shiga tofa ayatul'kursiyu da fala'ki da nasi 'kafa bakwai bakwai kana ya iske inda take, ruwan tofin ya guntsa a bakinsa ya shiga fesa mata a jiki, sai da yayi haka sai uku tukkuna sannan ta daina burgimar da take yi ta daina gwalantun surutan da take yi jikinta ya shika sosai tayi lakaf gumi duk ya jika mata jiki, Mufida na kuka taje ta rungumeta tana kiran sunanta................
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*12* Cikin wani mawuyacin hali Halisa ta tashi duk jikinta yayi mata mugun tsami! ga wani irin ciwo da kanta ke mata, da kayar ta rarrafa ta shiga dakinta ta zauna bakin gado tana ri'ke kanta, a maimakon tayi addua kawai sai ta fashe da kuka tana fad'in mugwayen kalmomi a kan mijin nata saboda kawai yace zai yi mata kishiya shine take addua Allah yasa ya samu karayar ariki komai nasa ya lalace! Allah yasa ya taulace ya zama wanda bashi da cin yau bare na gobe insha Allahu kuma Naja'atu sai ta zame masa masifa a rayuwarsa, tana kuka take wannan surutan tamkar wata mahaukaciya, Cikin wannan yanayi suka shigo gidan shi da yaran gabad'aya dan dubara yayi wa Baba malam yace zai tafi dasu Mussadiq saboda zasu koma makaranta, baba malam baiji dadin haka ba dashi da Abba Magaji sun fahimci cewar abinda Naja'atu tayi musu ne yasa yaji sha'awar dauke yaransa.......Kai tsaye Dakinsa ya nufa yana so ya samu nutsuwa sosai kafin ya tunkari Halisan dan ya fahimci dole sai ya karyar da kansa mussaman yanzu da ya dauko nauyi 'yayansa ya d'ora mata.........Mufida da Saddiqa Mussadiq suka nufi bedroom din Halisan nan suka tarar da ita ba yanda take sai sambatun surutai take da alama dai har yanzu mutanan nata basu gusa daga jikinta ba, Mufida taje ta zauna kusa da ita tare da dafata tana kiran sunanta.........Saddiqa da Mussadiq a bakin kofa suka tsaya saboda dama can sun san halin masifar Halisan ba kaunarsu take ba sai taga Abbansu take yi musu magana da wasa da dariya, shiyasa suka kasa 'karasawa, Halisa ta juyo tana kallon 'Yarta Mufida ganin su Saddiqa a tsaye a bakin kofa yasa ta mike tsaye a furgice tace"Ku dan Ubanku waye ya kawo ki gidana maza ku fuce mun daga d'aki shegu tsinannu 'yayan asara."! Saddiqa da Mussadiq suka zabura! a tsorace suka fita daga d'akin sukaje suka nemi kujerar palo suka zauna jikinsu sai rawa yake dama can Saddiqa da Mussadiq suna masifar tsoron Halisa Naja'atu ce take musu maganinta.......Mufida na goge hawaye tace."Mommy ya kike zaginsu su Yaya Saddiqa ne fa 'yan uwana." Wani irin bahagon mari ta kifawa yarinyar tana huci! tace"Zanci Kutumar ubanki wallahi shegiya munafuka ni zaki fad'awa su d'in 'Yan uwanki ne? Wallahi duk ranar da kika 'kara kiransu da sunan 'yan uwanki sai naci ubanki." Mufida tana kuka tace"To mommy me yasa kika tsanesu bayan mamansu ta mutu dan Allah ki daina yi musu abinda kike musu babu kyau."! A fusace! ta sake gaura mata wani mari tana wata irin fuffuka tace"Tashi dan babanki mara mutunci ki bar min dakina ko kuma yanzu na sumar dake." A gigice! yarinyar ta mike hannunta dafe da kuncinta ta fita daga dakin tana kuka, wanda yayi dai-dai da fitowarsa daga daki yana sanye da jallabiya ruwan toka, Ganinsu Saddiqa sunyi muzu-muzu a zaune yasa jikinsa yayi sanyi ya kalli Mufida dake dafe da kunci tana kuka, yace."Menene? Cikin rawar murya tace"Mommy ce ta mare ni tace na fito mata daga d'aki. Ba tare da yace."Komai ba ya kama hanyar dakin Halisan, Har yanzu tana zaune gefan gado ta had'a tagumi babu maganar sallah a tare da ita, cikin nutsuwa ya shiga dakin bakinsa dauke da sallama, Kallonsa ma ba tayi ba ballanta ta amsa masa sallamarsa, gefanta ya zauna yana kokarin ri'ke hannunta ta fizge a fusace! ta mike tsaye tana nunashi da hannu tace"Kaga dan girman Allah ka fita ka bani guri naji da abinda ke damuna baka da abinda zaka ce dani." Yaji zafin maganarta amma sai ya danne ya mike ya iske inda take, Rungumeta yayi a jikinsa yayi amfani da wata murya wacce ya tanade ta dan rarrashinta, yace."Haba Halisa wai duk me yayi zafi ne kike nema ki zautar da kanki akan abinda bai kai ya kawo ba! Menene abin damuwa dan nace zan auri Yarinyar nan Naja'atu? idan kin kwantar da hankalinki kin ri'ke girmanki sai kinfi daraja da kima da martaba a idona! Shin wai baki ga yanda Halimatu ta sadaukar da rayuwata a kaina ba, bana shakka ko tantama Halimatu yanzu tana gidan aljanna saboda ta rabu dani da iyayenta lafiya, kuma ta mutu hanyar haihuwa, har na gama rayuwata ta duniya bazan ta'ba mantawa da Halimatu ba, a kwanakin baya kin soma kwaiwayon hali da d'abi'unta amma tashi guda zaki watsar da abin da kika fara na alkairi, wallahi auran Naja'atu da zanyi ba zai sanya ni na daina kaunarki ba, kin san dai kece macen dana fara furtawa kalmar so, ko Halimatu ma kece kika jawo na aureta, to itama Naja'atun ina so ki sani bani ne nace inaso ta zama *Madadin 'Yar uwarta ba* Iyayenta ne suka nemi haka dan ko yanzu sai da na fada musu cewar maganar auran su barta suka nuna sai anyi So inaso ki kwantar da hankali ki samu nutsuwa ki kula dani da yarana gasu nan na kawo miki su ni kuma insha Allahu zan baki mamaki zan nuna miki ni d'an halak ne auran Naja'atu ba zai sa na juya miki baya ba." Shuru tayi jikinta duk yayi sanyi da kalamansa tace"Nifa ban hanaka aure ba wallahi ko budurwar zaka aura to kaje ka aura amma banda yarinyar nan bana kaunarta saboda bata ganin girmana." Yace."Na fad'a miki fa cewa kece uwargidana duk ragamar mu tana hannuki har ita Naja"atun idan tazo a 'karkashin ki take sai abinda kika tsara a gidan shi za'ayi." Jin wannan maganar tasa yasa ta sauke ajiyar zuciya tace"Nifa wallahi nasan dadin baki ne kake mun yarinyar nan na zuwa zaka manta dani, dan haka gwara tun kafin tazo na san inda dare yayi min dan bana tunanin zan zauna da ita a karkashin inuwa guda." Yace."In banda abinki ba gidanku daya ba to me zai dame ki da ita ko wacce na gidanta idan wannan da kike ciki bai miki ba sai na sauya miki wani." Tsaki taja tace." bazan yarda ba wallahi sai dai ka had'amu gida daya dan bazan amince a cutar dani ba." Yace."To shikkenan duk abinda kike so shi za'ayi, Zan sa a gyara miki side d'inki dake gidana na *'Danbare* ina fata hakan yayi miki." shuru tayi tana zum'bura baki, Ya saketa yaja hannunta suka zauna a nutse yace."Ki fad'a mun duk abinda kike so na siya miki na fad'ar kishiya komai tsadarsa zan siya miki." Tace"Sai nayi shawara tukkuna." Dariya ta bashi amma beyi ba yace."To shikkenan inaso na baki kudi kije ki had'o mata lefe kuma kema ki had'a naki hakan yayi miki." Dadi ne ya rufe ta tace"To Hakan yayi amma inaso ka sanja min mota." Yace."An gama ranki ya d'ade! amma dan Allah daga yau sai yau kada ki sake aikata abinda kika aikata a d'azu! rashin hankali ne kawai kije ki dauko wu'ka kina so ki kashe ni! kina tare da shed'an a lokacin idan da tsautsayi sai ki aikata aikin dana sani ki 'kare rayuwarki cikin uku'ba kuma ki mayar min da yara marayu." Hanci ta sha'ka! cikin takaici tace"Haba ai wallahi idan ma nayi maka rauni ban huce bacin raina ba, kana kallonta ina magana ka tsalleke ni ka tafi ai dole zuciya ta ta tunzurani a kanka." Yace."Tom yanzu dai duk magana ta wuce Gobe insha Allahu bayan sakkowar sallahr juma'a za'a daura auran amma ina tunanin ba zata tare ba sai nan da sati biyu." Halisa gabanta ya fad'i tace"Da wuri za'a daura auran ashe."? Yace."Baba Malam ne ya yanke hukuncin haka." Cikin tsabar bakin ciki da takaici tace"Aikin banza aikin hofi 'kwad'ayayyen tsoho mai son abin duniya ai dama dole ya gaggauta yin abun kodan bukatarsa ta biya." 'Bata rai yayi yace."To yanzu zamu 'bata dake kuma bana son wannan d'abi'ar taki ta zage-zage da rashin ganin girman manya." Cikin fusata! ta mike ta nufi toilet tana surutai da 'kananun maganganu, kallo ya bita dashi, Al'amarin Halisa dai sai gyaran Allah, yaji dadi sosai da ya shawo kanta cikin ruwan sanyi *(Tabbas haka maza ya kamata su dinga rarrashin matansu idan zasu 'kara aure, sau tari wasu mazan sune suke ingiza zuciyoyin matansu ga aikata abinda ba shikkenan ba, idan ya kasance zaka 'kara aure to yana da kyau ka dinga nuna kulawarka a kan matarka ta gida, kuma banda kiran wayar amarya a cikin gidan dan hakan ma na iya janyo muku samun sa'bani a tsakaninku*) Mikewa yayi ya fita daga dakin yana dan jin sassauci a cikin zuciyarsa tunda ya gama da matsalar Halisa yana ganin duk abinda zai biyo baya mai sauki ne.
Yana fitowa palon ya gansu a zaune duk sunyi tsuru-tsuru Mussadiq ma gyangyadi yake, Ya kalli Saddiqa data had'a tagumi hannu bibbiyu har yanzu zuciyarta na jin ciwon abinda Naja'atu tayi musu a d'azu duk da take yarinya wacce bata gama mallakar hankalin kanta ba ta gane ba 'karamar 'kiyayya Naja'atu keyi wa Abbansu ba, sai ta dinga tunanin to wai meye aibunsa da har zata dinga 'kinsa da kuma zaginsa, sam bata ta'ba tsammanin haka daga gareta ba...... a nutse yace."Saddiqa kuje ku kwanta kinji ko, dukkaninku ku daina damuwa ku saki jikinku a gidan nan gidanku insha Allah ba zaku samu wata matsala ba." Saddiqa murya na rawa tace"To Abbah." Ya sunkuya yana d'an tashin Mussidiq ya tashi yana mutsika ido, ganin Abbansa yasa ya bude idonsa sosai, Abba Abbas d'in ya rike hannunsa ya mike tsaye.........Shi da kansa ya rakasu d'akin dama gado uku ne mai dauke da madaidaiciyar katifa da pillo da bargo, Mufida ta gyara nata ta kwanta, Abbah Abbas da kansa ya shimfidawa Saddiqa da Mussadiq sabon bedshirt ya gyara musu sosai sannan suka kwanta, Ya tsaya kansu yayi musu addua sosai kana ya fita daga dakin tare da kulle musu kofa.............To bayan barin Abbah Abbas daga gurin Malam Baba shima Abbah Magaji sallama yayi masa kancewar kafin ya shiga gidansa zai tsaya ya siyi dik abinda za'a bukata gurin daurin auran, Malam yaji dadin hakan yace."Dashi kafin ya tafi ya shiga gidan Alhaji domin ya sheda masa abinda ke faruwa, koda Alhaji yaji bayanin da Abbah Magaji yayi masa sai ranshi ya 'baci! ya za'ayi sun riga sun gama magana da Abbah Abbas din kan cewar ya janye maganar auran yarinyar kuma dan yaga baya gurin zai sauya magana, yaji haushin hakan ya dauki laifi kacokan ya d'orashi kan Abbah Abbas d'in, Dan 'kin tsayawa ma yayi ya saurari bayanin da Abbah Magaji ke masa, ya sauko daga samansa, kai tsaye futa yayi daga gidan, Abbah Magaji na binsa a baya........Malam Baba yayi mamakin fusatar Alhajin kasancewar yasan shi d'in mutum ne mai saurin fahintar abu da kuma sau'ka'kawa cikin ko wane al'amari.......Da 'kyar Baba Malam da Abbah Magaji suka fahimtar dashi ya gane cewar ba laifin Abbas din bane sune suka tursashi......Alhaji Sama'ila yayi shuru yana ta nazarin al'amarin, daga bisani kuma addua yayi da fatan alkairi tabbas tunda Allah yayi haka to babu alkairi a cikin auran Naja'atu da Salim d'in,......Shine ya sake 'karfafawa Abbah Magaji, cewar yayi 'kokarin tana dar duk abinda ake bukata a gurin daurin aure tabbas babu makawa gobe auran Naja'atu da Abbas sai ya d'auru.........Sai misalin goma da rabi sukayi sallama da juna kowanne ya shiga gidansa cikin fatan alkairi ga junansu.........Baba Malam kafin ya kwanta sai da ya sanar da Baba Talatu abinda ake ciki na irin hukuncin da suka yanke cewar Za'a daura aure gobe dan jan lokacin bashi da amfani, Baba Talatu taji dad'in hakan sosai kuma tayi fatan alkairi dangane da al'amarin.....Naja'atu dake takure kan shimfidarta a lokan rumfar luf!! tayi kamar mai bacci tana sauraran maganganunsu, sai da taga sun shiga daki, da niyar kwanciya sannan ta mike a hankali ta dauki wayarta dake kusa da ita ta mike ta fita daga dakin ........Daya dakin ta nufa tana shararar da hawaye, xaman 'yan bori tayi tana toshe bakinta domin kada sautin kukan da take ya fita suji, wayar ta kunna hannunta na kyarma ta shiga laluben numbar Abbah Abbas d'in, tana jin idan bata zageshi ba zuciyarta na iya bugawa.........Yana zaune a palo shi kadai da Loptop a gabansa yana duba sa'konnin abokan kasuwancinsa na 'kasashen waje, Kiran wayar ta ya shigo wayarsa dan duban wayar yake hankalinsa na kan typing din da yake cikin loptol din, koda yaga numbar Naja'atun baiyi gaggawar dauka ba, ya janye idonsa ya cigaba da abinda yake Naja'atu! ta dingi kiran wayar tamkar zata kashe masa dodon kunne dole ba yanda ya iya ya daga wayar tare da gyaran murya babu wasa a cikin muryarsa yayi sallama....
'Dif! tayi gabanta na wata irin fad'uwa! sakamakon jin sautin muryarsa mai cike da kwarjini da rashin wasa yasa ta mance abinda yasa ta kiransa a wayar sai mazari jikinta yake tana sha'kar hanci had'e da sauke ajiyar zuciya irin na wanda yaci kuka ya 'koshi........'Dan gyaran murya yayi a karo na biyu yace."Dota ya akayi ne dare yayi baki bacci ba."......Murya na rawa tace"Me yasa ka san ni 'yar kace kake shirin aurena."? Shuru yayi yana nazarin maganarta, Yace."Eh abinda yasa nake kiran ki da Wannan suna (Dota) saboda nasan a matsayin shekaruna da Allah ya bani haihuwa da wuri dana haife ki kamar ki ko wacce ta fiki so ina ganin babu laifi dan na kira ki da wannan suna."!A hasale! tace." To tunda dai da bakin ka ka fad'a cewa a matsayin shekarunka da Allah ya baka haihuwa zaka iya haifeta ko wacce ta fini me zai sanya ka zubar da k'ima da mutunka a gurina ni da ka 'rike kamar 'yar cikin ka, ka sani ba da badan mutuwa ta ratsa tsakanin ka da matarka ba da kowa yana maka kallon matsayin uba a gare ni." Murmushi yayi wanda har sai da taji sautinsa a kunanta Yace."Nifa ban haife ki ba ki daina kirana Ubanki yanzu sunan da yafi kamata ki kirani dashi shine Mijin ki dan gobe idan Allah ya kaimu iwar haka kin zama matata"! Taji tamkar ta d'ura masa ashar! sai dai ta daure taja wani matsiyacin tsaki! mai 'karfi! da fad'in "Amma dai anji kunya wallahi."!! Kit! ta kashe wayar tana wani irin huci!!! Abbah Abbas ya dinga bin wayar da kallon mamaki! Yau shi yarinyar nan take jawa tsaki har tana kokarin zaginsa, Kasa hakura yayi ya sake kiran wayar! A fusace! ta d'aga ta bud'e baki za tayi magana, ya buga mata wata masifaffiyar tsawa! da fad'in " Dan Ubanki ni kike zagi ashe baki da mutunci dama."!? Jikinta ya shiga karkarwa domin tsawar da ya buga mata bata ta'ba saninsa da ita ba, kashe wayar tayi gabad'aya ta kwanta tare da takure jikinta tana kuka mai tsuma zuciya, ta kirasa a waya domin ta farfad'a masa magana mai zafi 'karshe shi ya fad'a mata maganar data ya mutsa mata tunani har da zagin Ubanta..........Abbah Abbas ya ajiye wayarsa a fusace! ya rufe loptop din ya mike ya nufi bedroom d'in Halisa........... *Sorry kuyi hakuri waya ta ta d'an samu matsala wallahi zaku ga yanayin typing din ba irin yanda na sababa........Ina ro'kon Ubangiji Allah ya kawo mana zaman lafiya a wannan 'kasa tamu ta Najeria Ubangiji Allah ka bamu nutsuwa da daidaito a tsakaninmu amin.........MY FANS KADA MU MANTA DA SALATIN ANNABI A WANNAN RANA MAI ALBARKA SANNAN KUMA MU DAURE MU KARANTA ABINDA YA SAWWA'KA DAGA CIKIN SURATUL KHAFI.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*13*
Ranshi a 'bace! ya aje loptop din kan wani tevur ya nufi toilet alwala ya daura ya fito ya hau kan dadduma ya tayar da sallahr nafila, raka biyu yayi ya daga hannunsa sama yana rokan Allah ya za'ba masa abinda yafi alkairi a rayuwarsa, kwata-kwata ji yayi auran yarinyar ya fice masa daga rai! a sabili da irin iskancin da wulakancin da take masa da shida 'ya'yansa bai ta'ba tsammin faruwar hakan daga gurinta ba yana ganin barin auranta kamar shi yafi alkairi don baya so da girmansa da komai yarinya k'arama tazo tana fada masa maganar da duk ta gadama, mikewa yayi daga kan dadduma yaje ya kwanta kusa da Halisa, ya d'an janyo ta jikinsa,
Bude idonta tayi ta wani fizge jikinta tana jan tsaki! Al'amarin sai ya bashi mamaki! ganin cewar d'azu suka gama magana da ita kan cewar komai ya wuce amma saboda ya ra'bi jikinta tana fizgewa, bai yi zuciya ba ya sake kai hannu zai janyota ta mike zaune tana 'bata fuska tace"Nifa ba zan sake amincewa da bukatarka ba sai na yankewa kaina hukunci tukkuna dan gaskiya ni maganganunka na dazu basu shige ni ba."
Ya mike zaune yana kallonta cikin d'umbin mamaki! yace." Wane irin hukunci zaki yankewa kanki bayan wanda muka yanke d'azu na dauka yanzu dani dake mun zama d'aya, ashe duk maganar da mukayi dake dazu ta banza ce." Tace."Kawai ka rabu dani na cigaba da tunanin mafita ni ba zan sake amincewa bukatarka ba kaje idan an daura auranka da 'karamar yarinya sai ka sauke bukatarka a kanta." Cikin tsabar takaici yace."Halisa ban ta'ba ganin mara hankalin mace irin ki ba wallahi kin girma amma har yanzu kin 'ki hankali 'Yar cikin ki Mufida ta fiki nutsuwa."
Tace."Duk dai abinda za kace a kaina kace ba zan amince da kai ba wallahi sai yarinyar nan ta shigo gidanka naga irin zaman da zakayi da ita."
Murmushi takaici yayi cikin sigar 'kuntatawa yace."Zanyi zama da ita irin na ma'aurata kuma ba zaki hana ni na ji dad'ina da ita ba." A fusace! taja tsaki! da fad'in "Kana tare da kunya kuwa duk ranar da 'yayanka su kaga ka kwana a d'akin wacce suka d'auka a matsayin yaya a gurinsu, sai ka tanadi abinda zaka fada musu."
Girgiza kansa kawai yayi ya dauki rigarsa yasa a jikinsa ya sauka daga bed din hanyar fita ya nufa jiri naso ya kayar dashi, gabad'aya ji yayi duniyar tayi masa zafi ko ina babu sassauci tabbas sai yanzu ne zai fara kukan rashin matarsa da yayi, a da baiyi kukan rashin Halimatu ba sai yanzu da Halisa da Naja'atu suke gwara kansa a bango....
'Bangaran Naja'atu kuwa yanda taga rana haka taga dare daga zarar ta tuna da cewar gobe za'a daura mata aure da Abba Abbas din sai gabanta ya fad'i ta hau takure jikinta, ta jima tana sa'kawa da kwancewa da tunanin mafita a gareta, tana so gari ya waye ta kira Salim a waya ta sheda masa hukuncin data yanke.......Aikuwa tana idar da Sallahr asubahi ta shiga kiran wayar Salim din inda akaci sa'a yau ya tashi da wuri, ya dauki wayar cikin mayaudariyar miryarsa yace.."My Princess kin tashi lafiya."? Murya a 'kasa tace"Lafiya kalau my prince." Ya wani narke murya irin yanda yake mata yana kashe mata jiki yace."My Prince jiya kwana nayi da tunanin ki da begen ki har mafarki nayi dake muna kwance a gado d'aya kina bani kulawa."
Ta rintse idonta hawaye na zuba tace."My Prince Abba Abbas naso ya yanke mana jin dad'inmu bana tunanin zan iya mallakawa wani da namiji kaina sai kai! bana sha'awar kowa sai kai soyayyar ka kawai nake muradi! amma ina tunanin mafarkina dakai ba zai tabbata dan ganin yanda magauta suke 'kokarin kassara mana rayuwarmu." Mikewa zaune yayi yace."My princess ki fad'a mun yanzu a wace matsaya aka tsaya dangane da maganar auranki da Abbah Abbas din.
Tace."Komai yazo karshe My Prince jiya da daddare Baba Malam naji yana fad'awa Baba Talatu cewa gobe bayan sallahr juma'a za'a daura aurena dashi, wannan dalilin yasa na yanke hukuncin guduwa daga garin gabadaya su neme ni su rasa."
Salim ya shiga goge gumi ma'kogwaronsa ya bushe sosai, yace."Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! abinda ya iya fad'a kenan, murya na rawa yace."My bani da kuzarin yin magana yanzu saboda na shiga rud'u da tashin hankali jin wannan maganar taki, zan kira ki anjima kafin nan nayi nazari kan hukuncin da kika yanke."
Kashe wayar yayi ya zauna yana tunani.......Ashe dai dattijon nan da gaske yake sai ya dasa masa 'kunci da ba'kin ciki! to kuwa in dai ya kasance cewar ya samu nasara a kansa gurin auran Naja'atu to shi kuma zaiyi amfani da damar sa, a gurin ita Naja'atu duk wani abunda yake bukata a gurin yarinyar ba zai same shi ba sai ta zame masa mafisa wanda da kansa zai gaji ya saketa, koda ya saketa shi ba auranta zaiyi ba yana so ya kawai ya dasa masa 'kunci da 'bacin rai kamar yanda ya dasa masa a zuciyarsa.
Mikewa yayi ya shiga cikin gidan...Yaya Ramlatu na kicin tana kokarin kunna wuta, taga shigewar d'an nata, sai da ta kunna wutar ta d'ora ruwan kunu kan murhun, sannan ta bi bayansa, koda ta shiga dakin gani tayi ya takure kansa hade da dafe kansa, Kafin ma tayi magana taga yana hawaye.
Tace."Salim lafiya me yake faruwa."? Cikin tsabar bakin ciki yace."Yaya 'Dan uwanki bashi da kirki ya kasance mutum mai son kansa, ya cuce ni ya cutar da rayuwata kuma ya yaudare ni da yasa na amince masa na daukeshi a matsayin uba ya ha'ince ni, yarinyar dana 'kwallafa raina a kanta yau xa'a daura masa aure da ita, ba zan ta'ba mantawa da wannan mutumin ba."
Yaya Ramlatu ta dinga mamakin maganar tace."Kai waye ya fad'a maka yau za'a daura auransa da Naja'atu da har kake wannan maganar......A fusace! yace."Ita yarinyar ce ta fad'a min yanzu ta kirani a waya tana kuka tare da sheda min hukuncin data yanke kancewar zata gudu daga garin gabadaya."
Shuru Yaya Ramlatu tayi takaici da bakin ciki kamar ya kasheta, lallai Abbas bai da alkawari kamar dai yanda Salim din ya fada hakane Abbas yafi son kansa akan kowa bai duba soyayyar dake tsakanin Salim d'in da Naja'atun ba sai da ya shiga ya fita ya raba tsakaninsu......Tace."To shikkenan sai ka hakura ka fawwala wa Allah tunda Allah yasa ya samu nasara a kanka, maganar Naja'atu zata gudu ta bar gari bata taso ba dan idan hakan ya kasance to kowa zai d'ora zarginsa a kanka, dan haka kace mata baka amince ba, dan bana son abinda zai janyo min 'bacin ran iyayena."
Yace."Idan ya kasance Naja'atu ta tare gidan Kawu Abbas wallahi tallahi nayi al'kawari sai na 'kunsa masa ba'kin ciki da takaici kamar yanda ya 'kunsa min, tunda dai Naja'atu ni take so ai magana ta 'kare zuciyarta tana hannuna shi kuma yana tare da gangar jikinta."
Yaya Ramlatu tace"Duk wani iya shege da rashin arziki da zaka yi masa ban hanaka ba, kaje kayi domin shima yaji idan da dad'i abinda yayi maka d'aurin aure suje suyi babu inda zanje." Yace."To dama me zaki je kiyi a gidan gabad'aya ma da Alhajin da ita Hajiyan basa kaunarki da suna kaunar ki ba zasu bari haka ya faru ba, sunfi kaunar Kawu Abbas d'in saboda yana da kud'i." Yaya Ramlatu ta dinga girgiza kanta takaicin da ba'kin ciki dik ya cika mata zuciya.
Da asubah da kafin ya tafi massalaci sai da ya shiga ya tashi yaransa domin suyi sallah, koda ya fito daga dakin nasu bai ko kalli dakin Halisa ba dan har yanzu haushinta yake ji yana ganin duk wani kokari da ya kamata yayi a kanta yayi zai dauke mata wuta gabad'aya dan ba zai cigaba da rarrashinta taba tana masa iskancin da taga dama.
Bayan ya dawo daga massalaci ya koma dakin nasu nan ya tarar dasu sunyi sallah suna zaune Saddiqa da Mufida suna magana, dukkaninsu suka shiga gaishe shi ya dinga amsawa cikin nutsuwa da kulawa, ya kalli Saddiqa a nutse yace." Saddiqa ki shiga kicin ki dafa muku tea da abinda kike ganin zaki iya." Tace."To Abbah." Mikewa tayi tana kokarin cire hijab d'inta shi kuma ya fita daga d'akin, Kai tsaye d'akin Halisa ya nufa domin ya dauki loptop dinsa.
Tana kwance kan bed din ta tsirawa rufin dakin ido, da alama ma ba tayi sallah ba, Ko kallon inda take baiyi ba ya dauki loptop dinshi ya kama hanya ya fita daga dakin, Halisa tabi bayansa da kallon ba'kin ciki tamkar ya tarwatsa mata zuciyarta..............Saddiqa na tsaka da aiki a kicin taji an buga mata uwar tsawa! "Ke dan Ubanki waye ya baki dama ki shigo min kicin."!? Jiki na rawa tace." Abbah ne yace na dafa mana tea da indomee." Da hannu ta nuna mata 'kofar fita da fad'in "Fice ki bar min kicin 'yar iska munafuka masu gadon mugun abu." Saddiqa hawaye ne suka tawo mata, tayi saurin mayar dasu tana kokarin fita daga kicin din Halisa ta kai mata ran'kwashi a kanta tana zaginta. Da sauri ta 'karasa ficewa daga kicin din hawayen da take ta kokarin mayarwa suka zubo.......Ganin yarinyar ta fito a firgice yasa ya kalleta yana tambayar ta menene."? Tana share hawaye tace"Babu komai." Tsawa yayi mata da fad'in "Ba zaki fad'a min menene ba."? Tace." Anti ce tace na fice mata daga kicin." Yace."Zoki zauna anan." Kusa dashi ya nuna mata, taje ta zauna tana goge fuska, cikin tausasawa yace."Kiyi hakuri ki daina kuka kinji ko." 'Daga kanta tayi tana goge hawaye, laptop din dake cinyarsa ya ajiye kan kujera ya mike ya nufi kicin din, Halisa na tsaye tana feraye doya ya shiga ya sameta......Babu walwala a tare dashi yace."Me yasa kika hana Saddiqa ta had'a musu abun kari."?
Juyowa tayi dan ba tasan ya shigo kicin din ba, ganin fuskarsa a murtuke yasa itama ta murtuke tata fuskar tace"Ai sai ka tsaya ka gani idan nayi ban basu ba sai ka bata umarnin tayi musu meye wani zaka ce ta shigo min kicin."!! Girgiza kansa yayi bai ce mata komai ba ya juya ya fita daga kicin d'in, sam bai dauka Halisa za tayi abinci ta bawa yaran ba dan ganin irin rigamar da sukayi ita dashi jiya shiyasa ya umarci Saddiqan ta shiga kicin domin ta samar musu da abinda zasu ci........Suna zaune shida yaran Yaya Ramlatu tayi sallama ta shigo, turus tayi ganinsa zaune a palon, shima cike da mamaki yake binta da kallo, har ta'karaso ta zauna kan kujerar dake fuskantarsa, Yaran ne suka shiga gaisheta ta dinga amsawa tana washe bakinta.
Cikin nutsuwa ya gaisheta ta amsa tana ta dariya kamar wacce ta shigo gidan da abin arziki, Tace."'Dazu Salim yake sheda min cewar anjima wai za'a daura auranka da Naja'atu hakane ko." ? Yace."Eh insha Allah bayan an sakko daga sallahr za'a daura anan massalacin jikin gidan Alhaji."
Tace."Allah ya sanya alkairi yasa haka shi yafi alkairi, amma banji dadi ba da baka fad'a min ko a waya ba sannan daga can gidan Alhajin ma babu wanda aka turo domin ya fad'a mun sam ba'a daukeni a bakin komai ba, ace maganar daurin auren ma sai a bakin Yarinyar mukaji dan da asussuba ta kira Salim tana kuka tana fad'a masa cewar za'a daura auran kuma idan an d'aura to zata gudu ta bar gari a neme ta a rasa, wannan maganar ta tayar min da hankali sosai saboda nasan yarinyar nan ta gudu to da kai da Salim zaku shiga cikin masifa, dalilin da yasa na umarci Salim din maza ya kira ta a waya sheda mata cewar bai amince da 'kudirin data dauka ba, Kuma nace ya fad'a mata cewar shi tuni ya cire ta a zuciyarsa, dan haka ta daina tunanin guduwa a kansa ta zauna a gidan mijinta tayi zaman aure mai tsafta."
Abbah Abbas ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Yaya Ramlatun yace."Dukkanin abinda ki kaga yana faruwa to dama can haka Allah ya 'kaddara zai faru, ko a mafarki ban ta'ba tsammanin wai zan auri yarinyar nan ba, sai dai kuma babu yanda Allah baya tsara al'amarinsa, mutuwar Halimatu ta janyo min sha'awar auran yarinyar domin ina ganin yarinyar tarbiyar tace kuma zata zame min *MADADIN TA* ta gurin kyawawan halaye da sauransu, sai dai kuma ashe ba haka al'amarin yake ba , Allah shine ya hallici Halimatu ya kuma Hallice Naja'atu a bigire d'aya, sai kuma ya bambamta musu halaye, Halin Halimatu daban Halin Naja'at daban, A jiya mun zauna da Alhaji mun tattauna magana kan cewa na janye bukatata tasan auran yarinyar, zan kuma shige gaba gurin ganin Salim ya mallaketa, a lokacin da naje wa da Baba Malam da maganar shi kuma ya nuna bai amince ba, yace yarinyarsa bata da miji sai ni saboda ni yayi ra'ayin bawa auran 'yarsa, dik yanda naso na fahimtar dashi ya kasa fahimta, haka nayi musu sallama na dawo gida ina fatan Allah yasa hakan shine alkairi a gare mu baki d'aya.
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*14*
Yaya Ramlatu zagin Baba malam kawai take a cikin zuciyarta amma a Zahiri dariyar ya'ke tayi tace"To ai shikkenan ni a gurina da kai da Salim din duk d'aya ne, kuma na zaunar dashi nace masa ya cire yarinyar daga cikin ransa gabadaya domin kai ba tsaransa bane ballanta ya had'a neman aure da kai."" Abba Abbas yayi murmushi yace."Kwana biyu ma bana ganinshi a kasuwa ko kiransa nayi a waya baya d'auka nasan duk akan hakane." Tace."Ai yanzu komai ya wuce na nuna masa dama can kai kafi cancanta daka auri yarinyar." Murmushi yayi yana girgiza kansa, gaskiya bai tsammaci zai zauna da Yaya Ramlatu haka suyi magana ta fahimta ba yaji dadi sosai da sosai data fahimce shi.
Yaya Ramlatu a gidan ta karya kummalo suka shiga daki ita da Halisa, suna 'kulle-'kullensu, Halisa ta fad'a mata duk yanda sukayi da mijin nata da maganar zai bata kudi ta had'o lefe kuma zai sanja mata mota bayan haka kuma yace ta fadi duk abinda take so zai bata kudi ta siya.....Jin haka yasa Yaya Ramlatu tace"Kinga aikin malam ya fara yi ko ai dama na fad'a miki sai Abbas ya dawo tafin hannunki sai yazo yana miki rawar jiki, dan haka ki daina d'aga hankalin ki kan auransa da yarinyar nan nasan idan muka ri'ke Malam mai al'mutsutsai! a hannunmu to bukatar mu zata biya dama kuma babban burin ki shine ki mallaki Abbas a hannu ina ganin nan da 'kan'kanin lokaci zaki mallake shi da duk wani abu nashi tunda har ya bud'e bakinsa yace miki dashi da duk wani wanda yake 'kar'karshinsa a 'kasan ki suke to kinga kuwa ai sai ki godewa Allah ki sake tanadar kudi masu kauri domin tukwici ga malam bisa ga aikin alherin da yayi miki." Halisa tace."Nifa Yaya Ramlatu sai nake gani kamar dan zai yi aura ne yasa yake kwantar da kansa ba wai asiri ne yayi tasiri a kansa ba, ki duba fa ki gani tsayin shekaru nawa muka dauka muna yawan bin malam tun Halimatu na raye asiri baya tasiri a jikinsa, sai yanzu."
Yaya Ramlatu ta 'bara rai tace"Kada ki sake wannan maganar, wato duk kokarin da nake miki bakya gani sai kin 'karya ta ni! kin 'karya ta aikin malam to babu ruwana wallahi idan kika lalata a aikinki, kada ki sake cewa na taimaka miki, inaso ki sani ko wane malami da irin kalar aikinsa, wani da ruhainai yake aiki wani kuwa da turawan aljanu yake aiki wani kuwa da ba'ka'ken aljanu yake aikinsa, to shi mai al'mutsutsai da ba'kaken aljanu yake aikinsa, idan kin san ba'kar wuyar da muka sha nida 'Yar shagamu kafin mu je zauren malam d'in sai kin tausaya mana, amma kin samu aiki yayi shine kike 'karyata wa to wallahi babu ruwana."
Halisa ganin ran Yaya Ramlatu ya 'baci sai ta shiga bata hakuri tace"Ba wai ina karyatawa bane nasan kina kokarina akaina kiyi hakuri dan Allah." Yaya Ramlatu tace"Koda can ma ba wai asirin ne baya tasiri a jikinsa ba yana tasiri sai dai yana saurin karyewa ne saboda yawan addua da zama da alwala dashi mijin naki yake, amma nasan wannan aikin da akayi masa zai dade kafin ya bar jikinsa."
Halisa ta sauke ajiyar zuciya da fad'in "To shikkenan insha Allahu zanyi kokarin ganin na kauda duk wani abu dake raina dangane da auran, ammafa nace ban yarda ya raba mana gida ba dan ina ganin kamar za'a cutar dani, sannan kuma wa 'yan nan 'ya'yan nasa daya kawo min sam bana son ganinsu wallahi."
Yaya Ramlatu tace"Eh kina da gaskiya gwara ya had'aku a gida d'aya duk da nasan ba wani d'okin auran yarinyar yake ba amma hausawa nace wa amarya ko mahaukaciya ce dole ayi d'okinta, dan haka tana tarewa ya kwashe yara ya kai mata dama ai saboda ta zama *Madadin* Uwarsu ya aureta."
Halisa tace"Yace idan an d'aura auran sai bayan sati biyu zata tare." Yaya Ramlatu tayi shuru tana nazarin maganar tace"To shikkenan sai ki hakura ki ri'kesu kafin lokacin amma ban amince ki zalince su ba tunda basu ne sukayi miki laifi ba." Cike da mamaki Halisa ke kallon Yaya Ramlatun wato idan ta fahimta tana so ta nuna mata cewar ita tana 'kaunar 'ya'yan d'an uwanta, Halimatu da Naja'atu ne bata kauna! To idan hakane kuwa 'kiyayyar da take musu ba takai har zuciyarta ba tunda ba zata bari a zalinci jininsu ba.
To Duk abinda Allah ya tsara ya hukunta sai ya kasance dama haka al'amarin yake mutum baya ta'ba tsarawa kansa rayuwa sai irin wacce Allah ya tsara masa, Abba Abbas da Naja'atu ko a mafarki basu ta'ba tsammanin zasu zauna a inuwar ma'aurata ba, sai gashi Ubangiji ya zartar da ikonsa a kansu, Sai gashi a yau jama'a masu yawa suka sheda daurin auransu, kowa sai fatan alkairi yake gami da fatan zaman lafiya, Alhaji Sama'ila da Baba Malam da Abba Magaji bakin su ya'ki rufuwa sai gaisawa suke da jama'a Abba Magaji na raba goro da alawa fuskarsa tamkar gonar audiga........Shi kuwa ango fuskarsa kadaran kadahan yana ta mi'kawa abokanshi hannu suna gaisawa suna taya shi murna da fatan alkairi yana amsawa fuska d'auke da murmushi.
Cikin gida kuwa, Naja'atu kasa gane kanta akayi ta rufe d'aki! da sakata, sai kuka take tana kiran mutuwa tazo ta dauketa, Baba Talatu da 'yan uwanta da suka cika gidan hankalinsu ya tashi suka dinga buga 'kofa suna kiran sunanta, tana jinsu tayi shuru sai ihu! take tana birgima 'kasan d'akin.
Baba Talatu ta fashe da kuka tana fad'in "Wannan yarinya tana so ta jawo min abin kunya a idon jama'a innalilihi wa'ina ilahi raji'un! Daki ta shiga ta zauna gefan gado tana share hawaye babu shakka Naja'atu ta fita zakka a cikin 'yayanta.......Abba Magaji ne ya shigo gidan ya gansu tsaye a kofar d'akin! Gashi sai gunjin kukan Naja'atun yake ji daga cikin d'akin, Ya karasa gurin da sauri yana tambayar ba'asi.........Baba Larai wacce ta kasance Yaya ga Baba Talatu itace tayi masa bayani duk abinda ke faruwa, Ya shiga bubbuga kofar yana kiran sunanta, tana jinsa taki kulashi.
Cikin rarrashi yace." Naja'atu bude kofa kinji ko duk kinsa hankalinmu ya tashi yi hakuri ki bude kofar zanyi magana dake.......Cikin dashashshiyar murya tace"Sai dai ku dau'ko gawa ta amma wallahi bazan bud'e 'kofar nan ba."
Abba Magaji ya kalli kofar 'kofa ce irin tada mai k'wari tabbas jijjige ta aikine babba amma yana ganin hakan shine mafita, yana kokarin fita Baba malam na kokarin shigowa ganinsa a fujajan! yasa ya tsaya tambayarsa, Baba malam ransa ya 'baci sosai babu shakka Naja'atu ta shirya tsaf! domin ta tozarta shi a cikin unguwa, nan ya umarci Abbah magajin ya samo matasa majiya karfi suzo su jijjige 'kofar......Gidan ya shiga ya tarar da jama'a sai surutai suke kowa na fad'in albarkacin bakinsa, har da masu cewa dama a warware auran tunda yarinyar bata so.......Baba malam ya tsaya a bakin tagar dakin ya daga labule yana le'kanta da kiran sunanta, duk da tasan shine bai sa ta amsa masa ba, juya baya tayi ta cigaba da kukanta...........Abba Abbas na tare da Dan uwanshi a bakin gate din gidan alhaji suna magana, kawai yaga abokin nashi tare da zaratan maza majiya 'karfi harda Salim a ciki zasu shiga gidan Malam......Ya bisu da kallo cikin mamaki! Jikinsa ya bashi da akwai abinda ke faruwa..............Sai da suka fara sassa'ke 'kasan 'kofar da (diga) sannan suka sanya mata karfi! aikuwa a take suka cire ta.........Mi'kewa tayi tsaye! cikin firgici! tana rarraba idonta a kansu, ganin sun shigo dakin har Baba Malam d'in yasa ta takure jikinta a bango tana rawar jiki, Abba Magaji ya nufe ta a zafafe! da alama jibgarta zaiyi Baba Malam ya hanashi, a fusace ya bar dakin, su kuwa jama'a 'yan zuwa taya murna sai fad'ar albarkacin bakinsu suke a kanta........Baba Malam yace."Magana dai duk ta 'kare kowa yaje ya cigaba da sabgarsa aure tunda an daura babu zancan a warware shi.
Dakin ne yayi shuru na tsayin minti biyar kafin yayi gyaran murya a nutse ya kira sunanta."Naja'atu.'' Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya, ya kalleta cikin yanayi na damuwa yace."Kina so jama'a su zage ni a unguwa ko? ashe a matsayina na mahaifinki ban isa na nemi alfarma a gurin ki kiyi min ba! kin shirya tozartani a cikin unguwar ko, ba'a ta'ba samun labarin yarinyar data fujirewa umarnin iyayenta a cikin unguwar nan ba sai ke! wato tun munayin abun nan a cikin gida sai ki janyo hankalin jama'ar dake waje sun gane cewa tilas mukayi miki ki auri mijin 'yar uwarki, Kina ji da kunnan ki irin surutan da jama'a keyi a kanki, kina so duniya ta zage tayi tur! dake kan 'kin bin iyaye meye aibun Alhaji Abbas da kike masa wannan 'kiyayya! idan da al'kawari da amana Abbas bai cancanci haka daga gare ki ba, to saboda haka ni wannan itace magana ta ta karshe a tsakanina dake, an daura auraki da Alhaji Abbas to kada naji kada na gani, mutukar kin daukeni a matsayin uba to ina so ki zauna da wannan bawan Allah zama na amana kamar yanda 'yar uwarki ta zauna dashi, idan aka kai ki dakin mijinki aka samu matsala ta 'bangaranki to babu shakka zan yafe wa duniya ke babu ni babu ke har abada."!! Kallonsa kawai take tana shararar da hawaye bakinta sai rawa yake tana so tayi magana amma ta rasa ma ta ina zata fara.......Baba malam ya mike ya fita daga dakin ya barta cikin zullumi da tararrabi gami da neman mafita.
Salim kuwa suna fita kai tsaye inda su Abba Abbas suke ya nufa, Yana so ya fara dasa masa 'bacin rai a zuciyarsa........Ba tare da wani damuwa ba ya shiga sheda masa abinda Naja'atun tayi ta kulle kofa tana cewa sai ta kashe kanta tunda ba'a aura mata wanda take so ba, dalilin da yasa kenan suka shiga gidan suka 'balle 'kofar har da cewa data ganshi zuwa tayi zata rungumeshi Yayanta Magaji ne ya hanata, Salim ya wani 'kasan'kantar da kansa yace."Wallahi ni Kawu tuntuni na hakura da yarinyar nan tunda naji maganar auranka da ita naji ta fita daga raina saboda nasan kai ba mutumin da zan had'a takara dashi bane, to amma kullum sai ta dame ni da kiran waya babu dare babu rana, ko dazu sai da ta kira ni da safe tace zata gudu daga gari nine na hanata nace idan kaunar da take min gaskiya ce to ta nuna ta a kanka, dan na nuna mata a yanzu dai kai ka fiye min ita sau dubu, tunda ta zama mallakina ka nake daukarta a matsayin antina."
Wannan al'amarin yayi masifar d'aga masa hankali mussaman idan ya tuno da maganar runguma sai yaji wani sabon 'bacin rai na taso masa bai ta'ba d'auka 'kiyayyar da yarinyar nan ke masa ta kai haka ba, wato da tuni ta gudu da badan Salim din ya hanata ba, babu shakka dole ya tsaurara matakan tsaro a kanta.
Baba Malam kam yana fita ya samu Abbah Abbas din da maganar lallai yau da daddare yake so Naja'atu ta tare a dakinta tunda an daura aure to maganar aja wani lokaci bai taso ba........Abba Abbas din ya nuna masa cewar ba wai ya'ki maganarsa bane yana so yayi d'an gyare-gyare a gidan, shiyasa yace sai nan da sati biyu.....Baba malam fafur ya'ki yarda da maganarsa Yace bai amince da wani gyara ba za'a kai Naja'atu ta zauna a d'akin 'Yar uwarta a yanda yake.
Abbah Abbas baya son yayi ta jayyaya dashi sai kawai ya amince da hakan.
Sai da yayi sallahr isha'i a 'Kofar na'isan sannan ya nufi gidan nashi, Halisa ana zaune a palo anci kwalliya cikin wani uban less tayi ado da gold hannu da wuya da kunne, tayi kyau dai-dai gwargwado, suna zaune ita da yaran suna kallo amma kallo daya za kayi wa su Saddiqa ka gane a tsorace sukayi ko motsin kirki sun kasa yi, shigowar Abban nasu yasa suka sauke ajiyar zuciya suna masa sannu da zuwa....Ya amsa musu yana kokarin shiga dakinsa.
Halisa ta mi'ke tabi bayansa, yana tsaye yana kokarin cire babbar rigar shaddar dake jikinsa, Halisa aka 'karasa kusa dashi kamar ba ita ba ta taimaka masa ya cire rigar ta ninke rigar ta ajiye gefan gado aka wani kalleshi ana fari da ido cikin kissa tace"Ango kasha 'kamshi."! Dariya ta bashi amma beyi ba yace."Nayi miki kama da ango a haka."? Murmushi tayi tana ta'be bakinta tace"Sosai kuwa gakanan sai 'kyallin goshi kake." Yasa dariya yana kallonta yace."Ba haka ango yake ba ango zaki sameshi cikin walwala da farin ciki komai nasa sabo amma ni duba ban ma sa sababbin kaya ba fa, kuma yaushe zanyi 'kyallin goshi bayan har yanzu na kasa samun kwanciyar hankali dake."
Wani fari tayi da ido tace"Zaka samu kwanciyar hankali dani idan baka tauye min hakkina ba ni kuma zan baka kulawa wacce tafi ta da." Yace."To naji maganarki kuma ina rokan Allah ya bani ikon kwakwanta adalci a tsakaninku, nima inaso ki dauke kanki kan dukkanin abinda zai faru a nan gaba inaso ki ri'ke yarinyar nan bisa gaskiya da amana, kece babba dan haka ki ri'ke girmanki ni kuma zan baki mamaki sosai ba zan ta'ba juya miki baya." jin furucinsa yasa taji wani farin ciki ya cika mata zuciya, Toilet ta shiga ta hada masa ruwa yaje ya wanka ya fito ya shirya cikin sabuwar jallabiya milk sannan suka fito tare, Halisa sai wani ririta shi take, ta hada masa abinci da yaji magani ya zauna yaci da bisimillah a bakinsa.....Sai bayan da ya kammala cin abincin ne ya sheda mata cewar Naja'atu zata tare a dakinta yau dan abinda mahaifinta yace kenan....Cikin 'kokarin danne bala'in kishin da ya taso mata tace"To yau kana nufin acan zaka kwana kenan."? Kai tsaye yace mata "Eh." sunkuyar da kanta tayi ba'kin ciki kamar ya kasheta, Yace."Idan kina ganin kema zaki zauna a haka ba tare da anyi miki gyara ba gobe kina iya komawa." Tace"A'a ni bana gaggawa na fiso ka sanja min kujeru da labulaye da kayan gado duk wani abu da babu a can inaso ka samin kafin na tare."
Yace."Kada ki damu insha Allah cikin satin da zamu shiga za'a kammala komai."
To sai kusan goma da rabi ya bar gidan, Halisa ji take kamar ta dawo dashi amma ba yanda ta iya dole ta hakura ta kyaleshi ya tafi ta nufi dakinta cikin takaici da damuwa.
Naja'atu taci kukanta ta 'koshi bayan 'Yan kaita sun watse! tsoro ne ya cika mata zuciya gidan ya dinga yi mata gizo gani take kamar zata ga Yayarta, motsin kirki ta kasa yi sai makyarkyata take ita kadai a takure a d'aki! kamar mujiya duk ta tsargi kanta......Mi'kewa tayi cikin tsoro taje ta murzawa 'kofar d'akin key ta barshi a jiki dan bata so ma idan ya shigo gidan ya shigo inda take, takurewa tayi kan bed tana kuka had'e da kiran sunan Allah, 'Yar uwarta kawai take tunawa tana zabura!
Abbah Abbas ya shigo gidan cikin motarsa, gurin parking ya nufa, yayi parking din motar yana fitowa maigadi ya 'karaso ya mika masa hannu suka gaisa, maigadin yace."Alhaji Ashe ka daura aure to ubangiji Allah ya sanya alkairi ita kuma Hajiya Allah ya jikanta da rahama. Abba Abbas ya amsa cikin kulawa kana yayi masa sallama ya nufi cikin gidan........Ko'ina shuru sai hasken tarwai a palon, kujera ya samu ya zaune yayi shuru yana jin wani irin yanayi a jikinsa! Gidan da yayi rayuwa da Halimatu yau shi zaiyi rayuwa da kanwarta Yarinyar da bai ta'ba tunanin zai aureta ba......Ya kai minti ashirin zaune a palon kafin ya mike cikin rashin kuzari ya nufi d'akin da yake tsammanin tana ciki.....
A hankali Ya murd'a handile d'in d'akin yana so ya bud'e kofar sai yaji ta a rufe ya murd'a sosai nan yaji alamun key a jiki! Dan buga 'kofar yayi da hannunsa.......A furgice! ta mike zaune tana zare ido! Ya sake buga kofar dakin had'e da kiran sunanta! jin muryarsa yasa taja tsaki! ta koma ta kwanta.
Cigaba yayi da kiran sunanta yana d'an bubbuga kofar a hankali............Ta sake mi'kewa zaune murya na rawa tace"Waye."? Ajiyar zuciya ya sauke jin muryarta hankalinsa ya kwanta da yaji tabbacin tana cikin gidan, Yace."Bud'e kofar ki kar'bi abinci kici.'' Kai tsaye tace"Bana ci." ta koma ta kwanta! Tsaye yayi a bakin 'kofar d'akin yana d'an tunani Ya sake dan buga kofar hade da kiran sunanta.
Tace"Abbah dan Allah ka kyaleni kayi tafiyarka wai dole sai naci abinci ni bana bukatar duk wani abu da zai fito daga hannunka." Yace."To naji bud'e kofar ina so nayi magana dake."
Tsaki taja tace"Ni ba zan bud'e maka 'kofa ba kawai kayi tafiyarka.'' Ajiyar zuciya ya sauke yace."Okey shikkenan yanzu dai kin bani dama na koma inda na fito ko? kai tsaye tace"Eh hakan sai yafi min kwanciyar hankali." Girgiza kansa yayi ya matsa daga jikin 'kofar, ledar dake hannunsa ya ajiye kan center teble ya juya ya fita daga palon, yana fita ya fito da key daga aljihunsa ya kulle kofar palon kai tsaye ya nufi inda motarsa take.......
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*15*
Kai tsaye da ya fita daga gidan Naja'atu gidansa na gwangwanzo ya nufa domin bashi da inda zaije in ba nan din ba, maigadinsa na gidan ya bude masa kofa ya shiga da motarsa ya gyara Parking a nutse ya fito daga motar ya nufi cikin gidan, shuru palon da alama itama Halisan ta dade dayin bacci, kai tsaye bedroom dinsa ya nufa dan ganin kamar hakan shine maslaha koda ya shiga dakinsa bai jira wani abu ya zare jallabiyar jikinsa, yai saura daga shi sai singlet da gajeran wando ya kwanta kan gadonshi tare da rufe jikinsa da bargo, cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya dauke shi.......Komai gajiya da dad'in bacci asubah nayi yake tashi saboda tsabar sabo da yayi da tashin asuba jikinsa har bashi yake lokaci yayi, karfe hudu da kwata ya tashi ya nufi toilet a gurguje ya daura alwala ya fito ya zura jallabiyarsa, dadduma ya hau yayi nafila(raka'atanilfijir) yana idarwa yayi addua yanda ya sawwa'ka kana ya mi'ke ya fita.......Dakin Halisa ya nufa domin tashinta, ya tarar da ita tana sharar bacci, tsayawa yayi a kanta yana dan bubbuga bed din da kiran sunanta, Halisa firgigit ta tashi zaune tana kallonsa, cike da mamaki tace" Yanzu ka shigo gidan ne."? Girgiza kansa yayi yana kokarin fita daga dakin yace."Ai anan na kwana lokacin dana shigo kinyi bacci ki tashi kiyi sallah.'' Ya bud'e kofar dakin ya fita.
Halisa ta shiga mamakin maganarsa to anan ya kwana garin ya akayi haka ta faru? to ko dai yarinyar nan tayi masa tsiya ne? murmushi tayi ta mike farin ciki kamar me a zuciyarta ta nufi toilet cikin zuciyarta tana fad'in "Lallai wannan babbar dama ce a gurina.........Wajejen biyar da minti goma ya shigo gidan ya nufi dakin yaransa, nan yaga suna ta bacci basu tashi ba, tashinsu yayi yace suje suyi alwala suyi sallah. Ya fita daga d'akin, Halisa kuwa wanka tayi sannan tayi alwala ta fito tayi sallah a gurguje ko adduar kirki ba tayi ba ta mike daga kan daddumar, wata matsiyaciyar rigar bacci ta dauko bata da maraba da tsirara tasa a jikinta ta fesa turare kusan kala goma a jikinta, ta dauko maganin mata na matsi ta lakata a hannunta kafin tasa a gabanta sai da ta tofa maliki yaumi dini (Subahanallah) sannan ta cusa maganin a matantakar ta, ta mayar da maganin inda take 'boye shi, hijab d'inta ta zura a jikinta ta nufi dakin maigidan.........Abba Abbas na zaune a kan Sofa yana dan duba wayarsa ta shigo dakin, 'kamshin turaranta ya cika dakin, fuskarsa a sake ya amsa mata sallamarta, tazo ta zauna kusa dashi tana gaishe shi ya amsa a nutse yana tambayarta kwanan yara Tace" Sun kwana kalau! Hijab din jikinta ta cire ta ajiye gefe, Ya tsira mata ido yana kallonta, gani yayi ta dawo 'yar yarinya domin rigar irin mai maida tsohuwa yarinya ce Halisa akwai breast sosai gasu manya manya gashi bata wani shayar da yawa ba shiyasa basu zube sosai ba, gabakidaya ji yayi hankalinsa ya tashi, dama daurewa kawai yake, idananunsa suka kad'a sukayi jawur, Ta sake matsawa jikinsa tana masa magana kasa-kasa, wai tambayarsa take mai yasa bai kwana gidan amarya ba.....Abbah Abbas da ya soma fita daga nutsuwarsa kai tsaye yace."Kulle 'kofarta tayi shine dalilin da yasa na dawo nan." Ta'be bakinta tayi ba tace komai ba ta shiga shashshafa jikinsa, hannunta ya ri'ke suka mike kai tsaye bed suka nufa..........Halisa ta baje hajar ta sosai ta sakar masa jiki yayi abinda yake so da ita tana taimaka masa da sabbabin salon data tanade su dan samun damar mallakarsa, abinka da jarumin namiji ji yayi Halisan ta kasa isar sa gabad'aya yaji kamar an 'kara mata ni'ima da d'adi! gashi gabanta ya tsuke ya cika sosai sai zubar da ruwa yake, abinda bayayi a ranar sai da yayi sambatun surutai Abbah Abbas komai dad'in sex baya ta'ba yarda yayi wannan sambatun da iface-iface! a ganinsa duk shashancin ne meye abin ihu! sai dai yayi ta sauke numfashi yana sakin ajiyar zuciya........Basu saurarawa junansu ba sai kusan tara saura na safe, yara har sunyi wanka sun shirya sun fito palo sun zauna amma babu break fast.......
'Bangaran Naja'atu kuwa bayan fitar Abbah Abbas din daga gidan, sai ta shige cikin bargo ta kud'indine jikinta tana addua, daga zarar ta rufe idonta fuskar 'yar uwarta take gani, gashi bargon dake lullube a jikinta sai kamshin turaran Halimatun yake, cikin fitar hayyaci ta cire bargon daga jikinta ta mike da sauri ta bud'e kofa ta fita, kan kujera ta takure jikinta tana kuka, nan ma ta dinga ganin gilmawar Halimatun tana jin sautin muryarta a kunnanta.
Hannu ta dora a kanta, tana kuka da fad'in "Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! na shiga ukuna!! ta mike a sukwane ta nufi dakin Abbah Abbas din cikin ikon Allah tana murd'a kofar dakin ta bude shiga tayi da gudu ta kulle dakin taje ta kwanta kan bed dinsa, ta rufe jikinta da bargonsa tana ta rawar jiki da addua hawaye kuwa kamar an bud'e famfo, haka ta kwana tana firgita da zabure-zabure, da asubah tayi sallah a dakin ta bude kofa ta fito kai tsaye kofar fita daga palon ta nufa, ta dinga murdawa kofar ta'ki bud'ewa zubewa tayi bakin kofar ta had'a kanta da gwiwa tana ihu!!
Abbah Abbas yayi mamaki tsayin lokacin da ya dauka yana tara da Halisa dan haka a gurguje ya samu yayi wanka ya shirya a gurguje ya fito palo ya same su suna break fast dan Halisa data fito Umarni ta bawa Saddiqa kan ta shiga ta dafa musu ko indomee ce...
Yaran na ganinsa suka shiga gaishe shi ya amsa fuskarsa cike da walwala, Ya kalli Mufida da fad'in " Ina Mommyn ki."? Tace."Ba ta dade da shiga dakinta ba." ba tare da yace wani abuba ya kama hanyar fita, gabadayansu suka ce Abbah adawo lafiya.'' Ya amsa musu a lokacin da yake kokarin fita.
Lokacin da taji kamar ana 'kokarin bud'e 'kofar dakin zabura! tayi ta mi'ke tsaye hawaye duk ya bushe fuskarta ga jijiyoyin kanta da suka tashi alamun taci kuka ta koshi! kofar ta tsirawa ido gabanta na dukan uku-uku......Abbah Abbas ya bud'e kofar palon ya shigo..........Da gudu taje ta rungumeshi ta fashe da kuka tana makyarkyata a jikinsa! hannu guda yasa ya dafe bayanta yana bin palon da kallo! Ba yau Naja'atu ta saba ri'ke shi ko ta rungumeshi ba, a duk sanda xata r'ike shi ko ta rungume shi a lokotan baya baya jin komai a cikin zuciyarsa da jikinsa, amma yau ji yayi jikinsa na wani irin rawa mussaman da yaji tudun breast d'inta a cikin kirjinsa ajiyar zuciya ya sauke mai zafi! ya d'an cire ta daga jikinsa, yana kallon fuskarta yaga duk tayi wujiga-wujiga ga alamun furgici nan a tare da ita! gyaran murya yayi kafin yayi magana, Yace."Dota wato har yanzu baki daina kuka ba ko ki fad'a min abinda ke damun rayuwarki."! Hanci ta sha'ka tana sake shigewa jikinsa da rarraba ido a palon murya a dashe tace."Abbah Yaya Halimatu ce tazo tana yi min magana dan Allah ka taimaka min ka rabani da wannan rayuwar da nake cikinta ka mayar dani gida gaban iyayena wallahi ba zan iya zama a gidan nan ba ka taimaka min Abbah rayuwata na cikin garari da tashin hankali."! Tana rirrikeshi take wannan maganganun
Hannunta ya ri'ke ya dan sassauta muryarsa sannan yace."Ki kwantar da hankalin ki Dota wanda ya mutu baya dawowa kawai kinsa tsoro acikin zuciyarki shiyasa kika kasa samun nutsuwa a gidan.....Shuru tayi tana goge fuskarta, yaja ta suka nufi bedroom dinshi, koda suka shiga dakin sai yaga shimfidar gadonsa a hargitse ga bargonshi a 'kasa, ya kalleta cikin nazari yace."A dakin nan kika kwana ne."? Hawaye suka wanke mata fuska tace."Eh ko ina tsoro ake bani shine na shigo nan na kwanta to anan din ma ban daina firgita ba." shuru yayi yana bin dakin da kallo, kafin yace."Babu wani abin tsoro a cikin gidan nan ke kanki kin sani lafiya lau mukayi rayuwa a ciki ina ganin kamar kin sanya tunanin Halimatu a cikin ranki shiyasa kike furgita ina so ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki san da cewar wanda ya mutu baya dawowa, fargaba da damuwar da kika sanya a ranki duk itace ta janyo miki firgita."
Girgiza kanta tayi tana ri'ke hannunsa tace"Abbah ba zan iya zama ba dan Allah ka mayar dani gidanmu ka dubi halin da nake ciki ka tausayawa rayuwata." Ya dinga kallonta yana mamakin maganarta ya tausayawa rayuwarta to wane irin tausaya mata zaiyi bayan wanda yake mata, Yace."Yanzu dai je kiyi wanka tukkuna naga alama ma kamar baki karya ba ko."? Daga kanta tayi tace"Ba zan iya shiga dakin ba tsoro nake ji." Kai tsaye yace."To sai kiyi a toilet dina." Tace"To kayana na dakin ai." Yace."Bari na dauko miki." Fita yayi daga dakin, ta dinga zazzare idonta tana bin dakin da kallo, shi kansa dakin nasa tsoransa take ji, tana tsaye ya shigo hannunsa rike da riga da zani na atamfa super ire-iren kayan da yake d'inka musu, ya ajiye kan bed yace."Baki shiga wankan ba." Hanyar toilet din ta nufa salo-salo! ya bita da kallo mai tarin ma'anoni! bayan shigarta toilet din ya dauki bargon dake kasa ya mai dashi kan bed din ya xauna gefen bed din hade da kunna wayarsa yana dubawa, kawai yaji ihun ta daga cikin toilet din kafin ma yayi wani yun'kuri ta fito a guje jikinta duk kumfar sabula ta dauro towel dinsa yana kokarin fad'uwa daga jikinta, ya mike a gigice yana tambayarta ihu! take tana nuna masa toilet din, Ya rike hannunta yana tofa mata addua tangadi ta shiga yi tamkar 'yar maye ta tafi luuuu! zata fad'i! ba tare da 'bata lokaci ba ya ri'ke ta sosai a jikinsa, cikin tashin hankali da damuwa ya nemi gefen bed ya zauna da ita rungume a jikinsa, ji yayi jikinta na wani irin kyarma! yana rawa kamar wacce take cikin zazzabi mai zafi! babu shakka a firgice take, adduoi ya shiga tofa mata a jikinta yana me tsirawa fuskarta ido, a fizge suna dan kama da Halimatu kad'an, nan ya shagala da kallonta dan gani yayi tana nema ta rikid'e ta koma masa Halimatu.......Lokacin ne kuma ta dan samu nutsuwa ta bude idonta tana ambatar kalmar innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Ta mike da sauri ganinta kwance lakadan a jikinsa ga towel din jikin ya sa'bule! brest dinta duk a waje! Da sauri shima ya gyara yanayin sa amma dai duk da haka kana kallonshi sai gane ya hau network, Yayi dan gyaran murya as'usul Yace."Sannu ki dinga yawaita addua ina ganin tunda kin firgita da zaman side din nan zan sa a gyara miki Side din da ya kasance nawa sai ki koma can." Gyara towel din jikinta tayi ta mike daga jikinsa, kayan ta dake kusa dashi ta dauka tana so tasa tana jin kunyarsa, Yace."Ya zaki sa kayan bayan duk ga sabulu nan a jikinki." Cikin rawar Murya tace"Ba zan iya komawa toilet din ba, dan ina wanka naji kamar ana kiran sunana." Ya dinga kallonta abin na bashi mamaki! Mikewa yayi ya rike hannunta yace."Muje na raka ki kiyi wankan." Ma'kale kafad'a tayi tana komawa baya! Yace."Zan tsaya har ki gama fa kuma bazan kalleki ba." Hawaye ta share tace''Na hakura da wankan."Ya girgiza kansa da fad'in "A'a ai bai dace ba kina amarya ki zauna da datti ba zakiyi ba'ki fa." Kallonsa ta dinga yi tana mamakin maganarsa, Tace."Abbah ni d'in amaryar waye."? Ya nuna kansa da hannu da fad'in "Amaryata mana." Taji wani irin ciwo da takaici a cikin zuciyarta, hawaye suka kece mata tace."Kaico da wannan kalmar taka Abbah! Kaico da wannan maganar dake fitowa daga bakin ka, ni ba amaryarka bace 'Yar ka ce." Tana gama maganar ta ta cire hannunta daga cikin nasa ta fita daga dakin, gabadaya ma ji tayi ta daina jin tsoron akan ta zauna a dakinsa yana kiranta da amaryarsa gwara ta fito koma meye ya cutar da ita....
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~~~~~~~~ *16* Ya jima a dakin yana sa'kawa da kwancewa kafin ya fito palon, inda ya sameta a takure a kan kujera har yanzu bata daina zubar da hawaye......Saboda jin haushin maganar data fad'a masa yasa ya kama hanyar fita dan baya so ya zauna a gidan zuciyarsa ta tunzira shi a kanta, dan ya lura koda 'kuruciya a tare da ita to da akwai iskancin dan iskancin ma yafi yawa a tare da ita, gabad'aya ya lura ta raina shi kuma ta daina ganin girmansa, wannan d'abi'un da take masa na 'bata masa rai sosai da sosai! Yana dab da fita yaji ta ri'ke masa hannu, ya juyo fuskarsa babu walwala yana kallonta yace."Me zanyi miki kuma."? Cikin rawar murya tace"Dan Allah zan bika dik inda zakaje kada ka barni ni kad'ai wallahi ba zan iya zama ba." Shuru yayi yana kallonta na minti biyu kafin yace."Jeki dauko hijab din'ki." Da sauri ta saki hannunsa Hijab dinta dake kan kujera ta d'auka tasa ya nuna mata 'kofar fita da hannunsa, da sauri ta fice tana sauke ajiyar zuciya, kwana d'aya tayi a cikin gidan jin ta take tamkar a cikin 'kaya, kulle 'kofar palon yayi yazo shigeta ya nufi motarsa....Bin bayansa tayi da saurin gaske, ta ma rigashi bude motar ta shiga ta zauna tana zazzare ido, sai da ya gama magana da maigadinsa sannan ya shiga motar, yana zama tace."Jakar kayana na manta ban dauko ba kuma tana d'akin Yaya Halimatu.'' Ya kalleta cikin rashin walwala yace."To meye amfanin daukar jakar kaya ke a tunaninki ina zan kai ki."? Tace."Na dauka zaka mayar dani gidan Baba Malam." Girgiza kansa yayi yace."Ba can zan kaiki ba zan kai ki gidan Halisa ku zauna da yara zuwa dare sai mu dawo gidan tare." Fashewa tayi da kuka tace"Dan Allah ka daka mu dawo ni wallahi akan na zauna gidan nan gwara na zauna a gidan Anti Halisan yafi." Yace."Kina ganin zaki iya zama a gidan."? Da sauri tace"Eh zan iya." Ba tare da yace komai ba ya bud'e kofar motar ya fita, cikin gidan ya koma ya shiga, jakar kayanta dake dakin Halimatu ya dauko mata ya fito.Ganinsa dauke da jakar kayanta yasa ta sauke ajiyar zuciya,tana ganin gwara ta zauna a gidan Halisa akan ta zauna ita kadai a wannan uban gidan wanda ake bata tsoro, bayan mota yasa jakar, ya shiga ya zauna ya tada motar ya fita daga cikin gidan........Tana ganin sun hau kan titi ta sauke ajiyar zuciya wacce ta sanya shi dan kallonta da gefan ido, ya dauke idonsa tare da maida hankalinsa gurin draving din da yake.............Motar tayi tsit! na kusa minti goma kafin yayi gyaran murya a nutse ya ambaci sunanta! ta kalleshi tare da amsawa, Yace."Ina so inyi miki wata tambaya bana son ki munafurce ni ko kuma ki 'ki fad'a min gaskiya." Tayi shuru tana wasa da yatsun hannunta, Yace."Me yasa bakya so kiyi rayuwar aure dani."? Kallonsa tayi ya gyada mata kansa a nutse yace."Amsa nake so ki bani bance kuma ki bani amsar da zata 'bata mun rai ba." Tace"Saboda na dauke ka a matsayin mahaifina shiyasa nake ganin kamar haramun ne nayi rayuwar aure da kai." Yace."Waye ya fad'a miki haka? shiru tayi Ya cigaba da cewa" Aure a tsakanina dake ba haramun bane Naja'atu, dan na ri'ke ki kin girman a hannuna hakan ba zai hanani na raya sinnar ma'aiki dake ba mutukar Allah ya kad'dara hakan a tsakanina dake, mutane nawa ne sukayi irin wannan auran na *MADADI* kuma auran yayi albarka, inaso ki sani da badan mutuwa ta raba tsakanina da Halimatu ba to da babu abinda zai sanya ni naji sha'awar auranki, na kwadaitu da auranki ne dan ina ganin kamar zaki maye min gurbin matata ta gurin kyawawan halaye gami da sadaukarwa, ashe ba haka abin yake ba, Allah yasa kun fito ke da Halimatu ta tsatso daya amma kuma halin kowa ya bambanta, shin meye aibuna da bakya so kiyi rayuwar aure dani? ko kina ganin ba zan iya dauke miki dukkanin bu'katunki ba ne? Shuru tayi kanta a kasa tana ta nazarin maganganunsa, Ya cigaba da cewa....."Nasan babu irin sa'ke-sa'ke da zuciyar ki ba tayi miki a kaina, kina ganin kamar nazo da son zuciya a cikin al'amarin a matsayina na babba ba yaro ba na aure ki, kina ganin tamkar na cutar da rayuwarki ne tunda na hanaki auran saurayi wanda ya dace da rayuwarki ko ba haka bane".? Kasa magana tayi, Ya cigaba da cewa" Nasan kin san da cewar Annabi Muhammad (slw) ya auri Nana Ayshatu tana 'yar shekara tara, yayin da shi kuma yake da shekara Hamsin, to kuwa idan hakane aurena dake babu haramci a ciki tunda wanda akayi duniya dominsa ma ya auri 'yar 'karamar yarinya wacce bata kai matsayin shekarun da kike ba a yanzu, ina ganin ni na aikata sinna mai kyau tunda nayi irin abinda Annabi ya aikata."......Naja'atu duk jikinta yayi sanyi da maganganunsa, Ya cigaba da cewa" Inaso ki san da cewar abinda kike tunanin wani saurayi mai tashen balaga zaiyi miki a zamantakewar aure to Matashin mutum kamata dan kimanin shekara hamsin zaiyi miki abinda yafi wanda kike tunanin shi saurayin zaiyi miki." ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa" Mafi akasari 'yan matan yanzu abinda ke damunsu kenan.... ((('kalubale gare ku 'yan mata masu tashe saboda ku na zauna nayi wannan littafin, dan akwai masu 'karamar 'kwa'kwalwar da za suce su baza su auri tsoho ba sai saurayi, toh wallahi bari na fad'a muku a wannan zamanin ba'a tsayawa za'ben miji, idan kikace xaki tsaya za'be-za'be to zaki tsufa baki yi aure ba, idan magidanci mai mata yazo auranki idan har anyi binkice mai kyau a kansa an gane cewar yana tsaye a kan gidansa da kula da iyalinsa to ki lalla'ba ki shiga daga cikin, idan kin tsaya kince ke sai saurayi to zaki iya auran saurayin kuma ki kasa samun biyan bukatarki, Samarin yanzu duk 'yan bana bakwai ne kuma mafi akasari auran sha'awa suke daga zarar bukatarsu ta biya shikkenan zaki fuskanci kalubale, bance duka aka taru aka zama daya ba amma dai abinda yake faruwa na fad'a, idan kuwa kika auri wanda ya dan kwana biyu to shi yasan menene aure saboda ya dade a cikin inuwarsa zai ri'ke ki da kyau kuma duk wata soyayya da kike tunanin saurayi zaiyi miki to sugar Dady d'in da kika raina zaiyi miki wacce tafi ta saurayin domin shi tsohon hannu ne a harkar😁)))) Abba Abbas ya cigaba da cewa" Abinda yake damun su kenan sai suce su baza su auri tsoho ba dan suna ganin kamar idan sun auri mai shekaru baza su more kuruciyarsu ba, wanda kwata-kwata ba haka bane sunyiwa abun mummunar fahimta ne, inaso ki zauna kiyi tunani mai kyau a kan wannan maganganun da mukayi dake, Na farko ni ban haife ki ba, ballanta ki dinga ganin kamar kin aikata haramci dan kinyi mu'amular aure dani! Na Na biyu kuma wad'annnan abubuwan da kike yi sun soma isata idan baki gyara ba to zan dauki mataki a kanki, ni ba yaro 'karami bane ballanta ki dinga yi min iskancin da duk kika ga dama, a yanzu ni ina a matsayin mijinki ne ba Ubaba kamar yanda kike dauka a da to yanzu ba haka bane! Wallahi! duk ranar da na sake jin kin fad'i wata mummunar magana a kaina da aurana sai na 'bata miki rai! na dauka kuruciya ce ke damunki sai kuma daga baya na gane rashin arziki ne, to ni ba lusarin namiji bane ke zaki fadawa kowa hakan tunda kin taso a gidana kinga yanda nake zamantakewar aure da mataye na, suna bani girma suna mutuntuni babu wacce take fad'a min bakar magana ko kuma taja min tsaki! dan haka nake gargadinki ki kiyaye aikata abinda zai janyo miki 'bacin raina."
Tun kafin ya gama maganarsa ta rufe fuskarta cikin hijabi tana kuka, shima tunda ya gama maganarsa bai sake cewa komai ba ya cigaba da draving dinsa, daf da zai shiga cikin unguwar ne kira ya shigo wayarsa, koda ya duba sai yaga numbar Halisa a nutse ya daga wayar, Tace"Abban Mufida ya kuma ka fita baka karya ba."? Kai tsaye yace."Naje duba Naja'atu ne yanzu ma dai ganin zuwa tare da ita ta kasa zaman gidan." Da sauri tace."Kamar yaya."? Yace."Idan nazo zanyi miki bayani." Kashe wayarsa yayi dan ganin kamar zata 'kara masa wani 'bacin ran! Yana ta jin shashshekar kunanta sai damunsa take kawai dai yayi mata shuru ne yasan dole idan ta gaji zata daina........Halisa kuwa kasa'ke tayi da waya a hannu shin me hakan yake nufi da zai dauko mata yarinya ya kawo mata gida! cika tayi ta batse ta hard'e a kan kujera tana jiran zuwansu.........
Saboda yasan zai samu matsala daga gurinta yasa ya shiga gidan fuskarsa a murtuke dan baya so tayi masa rashin arziki ya lura ba tayi maraba da zuwan Naja'atun ba......Mussadiq na ganin Naja'atu tare da Abbansu ya tashi a guje yaje ya rungumeta, Allah sarki yaro kenan har ya mance abinda tayi musu, tsugunawa tayi ta rungumeshi tana sumbatarsa a fuska, Abba Abbas kuwa bai tsaya ba kai tsaye dakinsa ya nufa, Halisa ta mike ta bishi tana huci!! Dama ya tsammaci shigowarta, ya tsira mata ido yana kallonta ganin yanda idonta yayi jajawur lokaci guda, Ri'ke 'kugu tayi tace"Nifa bangane ba meye amfanin kawo ita gidana naga harda jakar kayanta." Yace."Eh kamar yanda na fad'a miki a waya hakane tana jin tsoron zaman gidan ita kadai shine dalilin da yasa na daukota na kawo ta ta zauna nan kafin na yanke hukunci." Murya na rawa tace"To ba sai ka kai mata su Saddiqa su taya zama ba, meye sai ka kawo min ita gida." Yace."Ina tunanin ko ta ganta tare dasu Saddiqar ba zata samu nutsuwar da ake bukata ba." Tace"To naji a'ina kake shirin ajiyeta." Cikin jin haushin titsiyen da take masa yace."A duk inda nayi ra'ayi gidana ne ai." Ganin ya fusata! yasa ta dan sassauta tace"Sai dai a gyara mata d'aya sashen ta zauna dan ni bana jin zan iya zama tare da ita." Yace."Ai dama ba'ace dole ki zauna da ita ba tunda ita tafi so ta zauna anan ke yanzu zanyi duk yanda zanyi cikin satin nan a gyara miki inda zaki zauna a can gidan." Girgiza kanta tayi tana 'kas-'kas! da cingum! din bakinta tayi wani murmushi tace"Ba zai yiwu ba! ai na fad'a maka ba zan amince da wannan rabe raben gidan ba, nima ina nan babu inda zanje." Daga mata hannu yayi yace."To magana ta 'kare kada nan gaba kice min zaki koma can dan ba zaki koma wallahi." Tace."Ai duk inda kake ina nan idan ka tattara ka koma can nima zan tattaro nawa nawa na biyo bayanka." Shuru yayi mata ya zauna gefan gado, ta juya ta fita tana fadin "Bari na kawo maka kayan break din." Tana fita ta gansu zaune a kujera sun kewaye ta har da Mufida sai murna sukeyi tamkar sunga wata sabuwar hallita, ita kuma sai murmushi take musu.....Halisa taja tsaki cikin tsawa tace"Ke Mufida me kike anan zo nan ki taya ni 'aiki." Yarinyar ta mike da sauri! Halisa ta nuna mata hanyar kicin tana fad'in "Bana son shashanci ni kun wani zauna kuna dariyar banza." Naja'atu dasu Saddiqa suka bita da kallo tana kokarin shiga kicin tana surutai.........Bayan shigewar Halisan, ta kalli Su Saddiq tana nazarinsu, kwana biyu da bata gansu ba sai taga kamar sunyi rama ta rike hannun Mussadiq tare da fad'in "Kayi rashin lafiya ne."? Girgiza kansa yayi yace." Yaya Naja'atu kema kin dawo nan kenan na dauki akwatin kayan ki na kai miki dakinmu."? Kanta ta d'aga masa idanunta na kawo ruwa, da sauri yaron yaje ya shiga jan jakar kayan Saddiqa ta mike taje tana taimaka masa, Naja'atu binsu tayi da kallo hawaye ya zubo mata tausayi yaran suka bata, tana ganin ko dan saboda su zata dinga adduar Allah ya sanya mata dangana domin ta zauna tare da dasu.......Halisa ce ta fito daga kicin hannunta ri'ke da tire jere da kayan tea ko kallon inda Naja'atun take ba tayi ba tayi ba ta nufi dakin maigidan, Naja'atu ita dai binta da kallo kawai take..........
Yana zaune 'kasan kafet ta shiga dakin, ajiye tiren tayi ta zauna tana kokarin had'a masa tea din yace."Ki bawa Naja'atu abinci dan bana tsammanin taci wani abu tun jiya." Kallonsa tayi kamar za tayi magana kuma sai ta fasa, ta hada masa tea kana ta zuba masa farfesun kayan cikin rago wanda yaji magani! ta mike ta fita daga dakin...........Saddiqa ta kalla tace"Ke Saddiqa ki shiga kicin ki girka muku abinda zaku ci dan ni ba baiwar kowa bace."! tana gama maganarta ta shiga dakinta......
Saddiqa ta mike da sauri tana kallon Naja'atun tace."Don Allah Yaya Naja'atu kada ki kulata." Murmushin takaici tayi tace."Jeki yi aikin ni ba'a gabana take ba ballanta na tanka mata." Saddiqa ta sauke ajiyar zuciya ta wuce kicin din, mikewa tayi ta nufi dakin su Saddiqar nan ta tarar da Mussadiq yana ta jera mata kayanta a cikin wardorbe dinsu, Tace"Mussadiq daka bar kayan ma a jakar da yafi." Yace."Ai akwai guri a wardrobe din shiyasa nake shirya miki kayanki a ciki." Zama tayi tana bin dakin da kallo, gado uku ne kananu irin na 'yan boarding....Mussadiq yace."Yaya Naja'atu zan baki gado na ki kwanta kafin Abbanmu ya kawo miki naki." Tace"To nagode Mussadiq." ya mike da sauri yana fad'in "Bari ma naje na fada masa." Kallo ta bishi dashi har ya fita daga dakin....Dakin Abban nasu yake kokarin shiga Halisa ta hangoshi tsawa ta buga masa da fad'in "Me zaka shiga kayi."? Yace."Zan fad'awa Abbanmu ne cewar Yaya Naja'atu bata da gado." Cikin tsawa! tace"To sarkin iyayi da rawar kai ai ya fika sani." Abbah Abbas din ne ya fito daga dakin nan Halisa ta gyara yanayin fuskarta Tace."Gashinan wai yana so ya shiga yayi magana da kai shine nace masa kana cin abinci sai ka fito tukkuna." Ya kalli Mussadiq din a nutse yace."Menene."? Mussadiq yace."Abbah Yaya Naja'atu bata da gadon kwanciya amma kayanta sun samu guri a wardrobe d'in mu." Murmushi yayi yace."Gaskiya Magaji kana son Yaya Naja'atu sosai kada ka damu zansa a kawo mata gadonta itama." Murmushi yaron yayi yace."Nagode Abbah." Cike da farin ciki ya nufi dakin nasu yana so yaje ya fad'a mata abinda Abban nasu yace..........Abbah Abbas fita yayi daga gidan ya tafi sabgoginsa sai yamma likis ya shigo unguwar kuma bai shiga gidan ba sai bayan sallahar isha'i, Halisa yau ma ta cancad'a kwalliya kamar itace amaryar tana zaune a palo ita da yaran suna kallo kamar jiya, ita kuwa Naja'atu ta kasa zama a palon tana d'aki ta takure kanta sai neman Salim take a waya bata shiga.....Hannu bibbiyu Halisa ta kar'be shi, ta bashi abinci yaci kamar koda yaushe ya dawo palon ya zauna nan yaga babu Naja'atu a gurin, Ya kalli Mussadiq da fadin "Ina Yaya Naja'atu." Mussadiq yace."Tana dakinmu nace ta fito muyi kallo ta'ki." Kai tsaye yace."Je ka kirata." Yaron ya tashi da sauri! ita kuwa Halisa shan kunnu tayi ta wani tamke fuskarta....Da hijab a jikinta suka fito ta zauna kan kujera kanta a kasa tace"Abbah Sannu da zuwa." Ya amsa yana nazarinta yace."Me kike a daki ke kad'ai bayan kowa na palo." Shuru tayi, Ta kalli Halisa a nutse yace."Inaso nayi magana daku a dakina." Mikewa yayi ya nufi dakinsa." Halisa ta mike tabi bayansa, ita kuwa Naja'atu gyara zama tayi dan bata fahimci maganarsa ba, Minti biyar da shigar Halisa dakin nasa Kira ya shigo Wayarta koda taga numbarsa sai gabanta ya yanke ya fad'i! ta dauki wayar Yace."Ki shigo dakina zanyi magana daku." a raunane tace"To." Kashe wayarsa yayi, Halisa kam sai jijjiga kafa take ta cika ta batse sai wani 'kas-'kas take da cingum din bakinta, Ya kalleta cikin 'bacin rai yace."Malama ki cire wannan cingum din na bakin ki." Ta daina 'kas-'kas din tayi ta dauke kanta......Da 'kyar ta iya mi'kewa ta nufi d'akin nasa yayin da yaran suka bita da kallo, Saddiqa dai duk tafi su hankali ta gane Yanzu Yaya Naja'atu dai-dai take da Anti Halisa a gidan to dan ta shiga dakin Abban nasu ba abun mamaki bane.......
0 comments:
Post a Comment