Rumtse idanunshi yayi da ƙarfi dan bai taɓa jin hakan ba,
Wani irin tsuma fatan saman idanunshi suka farayi, kamar shi yake juya su.
Kanshi ya jingina da marfin motar can ƙasan maƙoshin sa, ya fara mai-mai-ta.
"Hasbunallahu wani'imanwakil, innalillahi wa innailaihi rajiun. Subahanallahi Alhamdulillah".
Shiru PA yayi tare da ratsa gefe, yana mai kallonshi.
Tsawon daƙiƙu 3 suka ɗauka a haka, kana ya yunƙura ya miƙe tsaye tare da ambaton sunan Allah.
Bayan ya fita ne kuma PA ya maida marfin motar ya rufe.
Kana Driver'n'shi da gwamnatin kasar ta bashi, da ƴan tsaron shi suka fito suka mara mishi baya.
Yayinda PA dinsa ke gefenshi.
Saida Suka shiga har cikin iya inda matafiya ne zasu shiga.
Kana sukayi musabaha duk suka juya suka tafi.
Shi kuwa da Usman PA Suka nufi cikin farfajiyar jirgin kasan cewar an fara cikiyan matafiya.
A can ɗaya sashin kuwa. Riyyam-nsra ne, tsaye gaban Mammynsu.
Yayinda Zayton ke manne da kanta bisa kafaɗarshi, tana rau-rau da idanu alamun zubda hawaye.
Cikin yanayi na rauni da taraddadi Mammy ta kalli Riyyam-nsra cike da jaddawa ta kamo hannunsa ta riƙe da ƙarfi ido cike da hawaye tace.
“Kasan manufar tafiyarka, itace burinmu da farin cikin rayuwata.
Ka kuma sani ina tsoron duk abinda zai rabani da kai.
Riyyam ka sani, kaine GARKUWAta nida ƴar uwarka.
Lallai tabbas munada ciwo a zuciyarmu.
Ina tsoron kada garin gyaran gira in rasa ido.
Kada ban samu baɗiniba in rasa zahiri."
Cikin ƙarfin hali da jarunta yace.
"Mammy babu abinda zaki rasa, in sha Allah ƙari zaki samu. Da izinin ubangiji.
Babu wani abu na duniya da zai miki hijabi da mallakinki".
Cikin zubda hawaye Zayton tace.
"Mammy kin ganshi ko, shi baya tsoro, kada yaje yayi abinda zamu rasashi".
Hannunshi yasa ya share mata hawaye tare da cewa.
"Koda zaku rasani sai kun samu madadina".
Da sauri Mammy tace.
"Kamin al'khairi cewa, zaka kiyaye shiga hurumin da ba naka ba, kayi iya abinda ya kaika ka dawo".
Hannunshi ya ɗaura kan nata tare da cewa.
"Nayi al'ƙawari Mammy na".
Rungumeshi tayi shida Zayton ɗin jin anata neman matafiya".
Kanshi ta shafa tare da sa mishi al'barka.
Kana shi yayi ciki, su kuma sukayi baya.
Yana rataye da jakarsa bisa kafaɗa,
yayi matuƙar kyau cikin shigarsa ta matasan zamani.
Kamanninsa da Rayyern sun ƙara bayyana matuƙa, kasan cewar irin shigar Rayyern ɗin yayi.
Wayarshi ya zaro, ya fara ɗabi'ar tasu ta Tiktokers viewing ya farayi, yana jujjuyawa ƙasan jirgin.
Tare da fara, mgn da Hausa.
“Assalamu alaikum Al'ummar Nigeria".
Sai kuma ya haura ya ajiye wayar bisa steps din marfin jirgin, kana ya dawo baya, ya fara takowa a hankali yanayi yana ɗan rawa, da tsalle.
Mafi akasarin mutanen dake bayansa matasane, shiyasa suka tsaya suna murmushin calikancinsa.
Yana isa gab da wayan second ɗin daya saita na video na cika.
Dan haka yasa hannunshi ya ɗauki wayar kana ya kutsa kai cikin jirgin...
Zaune yake bisa kujera no 23 acan sama VIP, kusa da jikin windown jirgin.
Yayinda Usman ke bayanshi.
Wasu files ya zaro cikin briefcase ɗinsa, tare da biro, a hankali ya sunkuya ya fara buɗe takardun, yana sa hannu a cikinsu ɗaya bayan ɗaya.
Shi kuwa Riyyam-nsra tafiya yakeyi yana ɗan dudduba no ɗin kujerun.
Yana isa kusa da Rayyern ya tsaya tare da cewa.
"Yesss! Kunga ga maƙocina, sarkin aiki har a jirgima aiki yakeyi".
Bai ɗagoba kuma baici gaba da rubutun da yakeyi ba sai ƙirjinsa dake bugawa.
Jakarsa ya zare a kafaɗarsa ya sakata a mazaunin ta.
Wanda haka yasa saida ya matso kusa da Rayyern.
Yatsun sawun yaron ya zubawa ido cike da mamakin ganin yatsun iri ɗaya sak da nashi yatsun Har nails dinsu.
Da sauri ya ɗan ware idanunshi.
Ganin wani ɗan ɗigon tawadan Allah kan tsakiyar farcen babbar yatsar Riyyam-nsra.
A hankali ya ɗan motsa kafafunshi dan sai yaga kamar ƙafarsa ce.
Shi kuwa Riyyam-nsra zama yayi bisa kujerar dake manne data Rayyern, tare da sauƙe numfashi kana ya lumshe idanunshi saboda wani irin masifeffen bugu da zuciyarsa keyi.
Yayinda gaba ɗaya cikin jirgin kuma kowa ya zauna mazauninsa.
Tsit kowa ya nitsu.
A hankali Riyyam-nsra ya buɗe kwayar idanunshi sabida,
Jin alamun an rufe marfin jirgin kana jirgin ya fara ƙugin tashi.
Shi kuwa Rayyern har yanzu idonshi na kan kyawawan sawun Riyyam-nsra.
A hankali Riyyam-nsra ɗin ya juyo ya kalli gefen da Rayyern ɗin yake.
Da sauri ya ɗan sunkuyo da kanshi ganin inda Rayyern ya fuskanta.
Janye sawunshi yayi tare da cewa.
"Salamu alaikum".
Da sauri Rayyern ya juyo sabida muryar yaron sak muryar ƙaninsa Ramadan.
Yana juyowa shima Riyyam-nsra yana juyowa ya fuskanceshi.
Wani irin zabura Riyyam-nsra yayi tare da zazzaro idanunshi waje, kana ya yunƙuro zai tashi.
Da sauri ma'aikaciyar jirgin dake bayanshi ta nufoshi da sauri tana cewa.
"Hey Are you okay? please sit down!!”
Ta ƙare mgnar da ɗan sauti sabida lokacin jirgin, yake raba tayoyin shi na gaba da ƙasa, anfi buƙatar kowa a zaune.
Shi kuwa Riyyam-nsra wani irin masifeffen kaɗuwa al'ajabi mmki da tu'jjudine suka rufeshi, gaba ɗaya jikinshi rawayake.
Cikin buɗe baki ya nuna Rayyern da yatsarshi manuniya kana ya nuna kanshi.
Da sauri ma'aikaciyar ta sake cewa.
"Please I say sit down!."
Jin hakanne da kuma ganin yanda yake baya baya.
Yasa ya koma bisa kujerar ya zauna.
Cikin kaɗuwa da wani irin fuska mai cike da mmki yace.
"Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, daya haliccemu da kamanni iri ɗaya."
Shiru Rayyern yayi yana mai kallonshi da gefen ido.
Bai iya shiga sabgar da ba ta saba, a rayuwarsa baya taɓa sa kansa a lamarin da bai shafeshi ba.
Da sauri ya juyo jin Riyyam-nsra na cewa.
"Ina ma Mammy na ta ganka.
Allah mai iko.
Inama ace jirgin nan bai tashi ba, da na roƙeka da girman Allah da Manzonsa muje Mammy na taga mai tsananin kama dani."
Sai kuma ya kalli sajen Rayyern cikin tsananin farin ciki, so, ƙauna, bege, yace.
"In sha Allah nima daga yau zan fara tara saje irin naka".
Sai kuma ya matso kusa da Rayyern tare da dago wayarshi.
A hankali Rayyern ya ɗan juyo kwayar idanunshi kan fuskarshi ganin alamun zai manna kanshi bisa kafaɗarsa.
Fuskarshi ya tsuke tare da tsareshi da ido.
Da sauri ya kwaɓe fuska tare da karkata kai cikin turo baki yace.
"Na tuba".
Sai ya ganshi lammanim ƙaninsa Ramadan sak da yayi haka, dan haka Ramadan kanyi mishi duk sanda ya tsareshi da ido.
Ido ya ɗan zubawa lips ɗin shi yana cewa.
"Please kayi haƙuri hoto zamuyi zan nunawa Mammyna ne, zata so ganinka".
Ya juyo da nufin zaice a a.
Kawai sai yaji Riyyam-nsra ya ronƙofo kanshi da kyau.
Ya manna kansa bisa kafadarsa.
Yana murmushi yayi musu selfie.
Sai ya zama suna kallon juna.
Kafaɗarshi ya ɗan manna da nashi dan jin bugun zuciyarsu ya dai-dai-ta yana harbawa a tare a tare, dib-dib.
Sai kuma ya zuba mishi ido ganin ya taso ya zauna ya juyo ya fuskanceshi da kyau.
Hannunshi ya miƙa mishi tare da sallama.
Dole ya bashi hannu ya kuma amsa sallama tunda horaswar Musulunci ne.
“Sunana Zakariyya amman Riyyam-nsra nakeso a kirani, ni ɗan ƙasar Ethiopia nanne, ban taɓa zuwa Nigeria'n ba sai yau.
Dalilin abokina Nasiru Ahmad zanje.
Kai kuma fa?".
Fuska ya kuma kwaɓewa ganin ya janye hannunsa bai kuma ce mishi komai ba.
Cikin yanayin shagwaɓa yace.
"Please dan Allah gaya min".
A nitse ya juyo ya kalli yaron da yakeji.
Sonshi da ƙaunarshi na ratsa mishi jinin jiki da zuciya, haka nan yaji wani aminci na musamman a kan yaron.
Cikin tattausan muryar da irinta yakewa Ramadan mgn yace.
“Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara".
Ruggumeshi Riyyam-nsra yayi tare da cewa.
"Nice name. Please Zan iya ce maka Yaya?”
Kai ya jujjuya mishi alamun a a.
Da sauri yayi rau-rau da idanunshi tare da cewa.
"Dan Allah fa, to me zan ce maka".
A taƙaice yace.
"Hamma Rayyern".
Wani irin murmushin jin daɗi yayi tare da cewa.
"Hamma Rayyern".
Sai kuma ya gyara riƙon da yayiwa wayarsa da tun tuni yake musu video.
Kusan a tare suka sauƙe ajiyan zuciya lokaci da jirgin ya gama ɗagawa, yayi sama ya rabu da ƙasar Ethiopia.
A hankali ya ɗan juyar da kanshi kana yaci gaba da aikin da yakeyi.
Da sauri ya kuma kalli Riyyam-nsra da ma'aikaciyar jirgin nan tazo tana ce mishi lfy kuwa, ɗazu yake ta rawan jiki ta ƙare mgnar cikin yanayin saninsa da son suyi hoto tare.
Murmushi yayi tare da nuna mata Rayyern kana yayi ƙasa da murya yace.
"Yayana ne zai zaneni wai na cika surutu".
Murmushi tayi tare da kallon fuskar Rayyern kana tace.
"Ka cika rawar kai, ba kamar yayanka ba."
Sai kuma ta ɗan kalli Rayyern tare da cewa.
"Sir a rinƙa yi mishi faɗa yaron nan baya jin mgn a TIKTOK".
Kai ya gyaɗa mata ba tare da ya kalleta ba.
Hoto sukayi da Riyyam-nsra kana tayi gaba.
Usman PA kuwa yana can baya.
A hankali jirginsu yayi ta keta gajumare, yana ratsa sararin samaniya.
Tafiya ta nisa kowa sabgogin gabansa yakeyi.
Amman banda Riyyam-nsra gaba ɗaya ya shigewa Rayyern shigewa mai tarin yawa.
Ya kuma kasa yakice yaron.
Duk yadda yayi sai yake jin zuciyarsa mai raunice a kan yaron.
Wani irin son yaron yakeji har cikin ƙahon zuciyarshi.
Ga mamakinsa ko yanayin cimar da suka fiso iri ɗaya ne.
Domin tunda Riyyam-nsra ya shigo bakinsa bai zauna banza ba, sweet da chocolate ya cisu iri daban-daban.
Ya lura yaron bakinsa bai zama shiru.
Hoto kuwa yayi musu sunfi hamsin video kuwa sun kai goma.
Haka sukaci gaba da keta hazo...
A nan gida Nigeria kuwa gidan Alhaji Idi Saleh Dakata.
A hankali Jannart ta fara motsi, alamun farkawa daga baccin da allurar ya sa tayi na tsawon.
Awanni biyu da rabi.
A hankali ta fara motsa fatar idanunta da sukayi mata nauyi.
Dai-dai lokacin kuma Barrister ya turo ƙofar ɗakin tare da sallama.
A hankali Mom dake zaune gefenta ta amsa mishi.
"Wa alaikassalam, Barrister ka dawo".
Cikin kula ya gyaɗa mata kai tare da ƙarasowa bakin gado.
Ido suka zuba mata cikin tausayawa, ganin hawayen dake bin gefen idanunta suna sauƙa har cikin kunnenta.
A hankali Mom tasa tafin hannunta ta fara share mata hawayen.
Ba tare kuma da ta buɗe kwayar idanun nata ba, ta fara sakin Shessheƙan kuka.
Zama Barrister yayi a bakin gadon, tare da kamo hannunta ya riƙe, cike da tausasawa da kulawa yace.
"Sorry Jannart kiyi haƙuri ki dena, kuka dukkan abinda yayi tsananin zaiyi sauƙi".
Jin muryar ƙanin mahaifin nata, mafi kulawa a gareta ne.
Yasa ta buɗe Idanunta, tare da yunƙurawa, zata tashi zaune.
Da sauri Mom ta tallabota, ta zauna tare da jingina bayanta jikin allon gadon.
Gyara zama Barrister yayi tare da kallon Mom yace.
"Mom Abdul a kawo mata wani abu ta ɗan ci".
Da sauri Mom ta miƙe tare da cewa. "Toh". Ta nufi hanyar fita cike da kekyawar niya da zuciya.
Shi kuwa Barrister ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da juyowa ya kalli Jannart data gaza tsaida hawayenta.
Murya can ƙasan maƙoshi ta fara mgn.
“Abba ƙirjina yana ciwo! Kaina yana bugawa, tunani ya hanani samun sauƙi, na gaza gano Yah Junaid wanne irin ɗan uwane a duniyar nan.
Anya kuwa Abba Yah Junaid yana da cikekken hankali da sanin haramcin babban fasadin da yake son ai katawa gareni."
Sai kuma hawaye shar-shar, suka soma zubo mata ta kasa ƙara sa mgnar.
Shi kuwa Barrister cikin tsananin tashin hankali da kaɗuwa da firgici mai birkita tunanin iyaye na gari yace.
“Me kike nufi Jannart wanne irin fasadi kuma?".
Murya na rawa ta kalleshi cikin rauni tace.
"Abba Yah Junaid fa fyaɗe yake son yamin, a lokuta ma banbanta, yana ƙudirin yi min Fyaɗe, idan na ƙi amince mishi ne, yake yunƙurin kasheni.
Abba cewa yakeyi fa zai kasheni in ban amince da shiba.
Ya kuma ce muddin na gayawa wani zai kasheni.
Wlh Abba zai kasheni.
Abba ya zanyi? Ina zan shiga a rayuwata in samu sauƙi, Ɗan Allah Abba ka rabani da gidan nan in ba haka ba Yah Junaid zai kasheni kuma Daddy ba zai hanashi ba".
Ta ƙare mgnar cikin tashin hankali.
Da ya ta azzara nitsuwar Barrister Kabir saleh Dakata.
Wata iriyar fitinenneyar zufa ce mai zafi ta soma tsastsafo mishi.
Cikin tuno abubuwa da dama na rayuwar duniya, ya kamo hannunta tare da fuskantar ta da kyau kana yace.
"Jannart! Jannart!! Jannart!!!".
Ya kirata sau uku duk da amsa mishi da takeyi.
Cikin yin ƙasa da murya yace.
“In sha Allah, Junaid bazai kashe kiba, da izinin ubangiji sai kin rayu, rayuwa mai Al'barka domin ke ayace, kuma izinace sannan taƙin shaida mai ƙarfi".
Hannunta ya kuma riƙewa cikin irin sona uba da ɗiyarsa yace.
“Jannart zaki rayu cikin aminci.
Domin Ubangijin daya raya Annabi Musa acikin gidan Fir'auna cikin lfy da aminci.
Shiya rayaki a gidan nan cikin lafiya da aminci.
Ya rigada lokacin ya ƙurewa Magautan, bazasuyi nasaraba, dan sunyi nasararsu tun shekarun baya sun gama nasara, yanzu nasarar tamu ce.
Gsky zatayi halinta, in sha Allah zanci gaba da zame miki jigo. Kuma zan nema miki GARKUWA, cikin gaggawa kafin su juyo garemu".
Shiru tayi tana jin kalaman ƙanin mahaifin nata, sai dai ta kasa sama musu mizanin da zata aunasu ta ajiyesu ta fahimci manufarsu.
Gogewar hausarta batayi surfin ta Ƙanin mahaifin nataba.
Cikin ruɗanin da kalamanshi suka saka mata tace.
"Abba ni na gaji da zaman gidan nan, dan Allah ka sake roƙon Daddy ya bakani ko zai yarda, in koma gidanka."
Cikin sauƙe nannauyan numfashi yace.
"Jannart sake roƙar tashi tamkar wasa da rayuwarki ne, kamar dai kusanto da a ...".
Da sauri ya haɗiye ragowar mgnar sanin ƙwaƙwalwarta bazata fahimci zancen nasa ba.
Ita kuwa cikin sanyi ta zuba mishi ido.
Dai-dai lokacin kuma Mom ta shigo da tray a hannunta, cup ɗin tea ne mai kauri, sai soyayyan irish da ƙwai.
Cikin nitsuwa tace.
"Abba to..".
Hannu ya ɗan ɗaga mata tare da cewa.
"Ya isa da yamma zan dawo muyi mgn Jannart kada ki kuma yin kuka".
Ya ƙare mgnar yana miƙewa tsaye.
Kai kawai ta gyaɗa mishi kana ta bishi da ido har ya fita.
Bayan ya fita Bathroom ta shiga, ruwa ta ɗan watsa, bayan tayi brosh kana ta fito.
Ba laifi ta ji sauƙin sosai numfashin ta ya dai-dai-ta.
Tea ɗin kawai ta iya sha.
Kana ta koma ta kwanta dan Alllurar bata ida saketa ba.
Can cikin bacci taji wayarta na suwa.
"Mahmoud".
Tace tare da amsa kiran.
Nan yake shaida mata cewa.
Dr Rayyern Mai-nasara yana hanyar dawowa Nigeria tun safe jirginsu ya taso.
Zuwa azahar zasu sauƙa Abuja.
Kuma yau ɗin zasu shigo Kano cikin alamun bacci tace.
“Toh ya akayi kuma lbrin ya sauya Mahmoud ba sai jibi ba kace?”
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Uhumm kin kuwa san waye Dr Rayyern, mutun yana nan tamkar Wahainiya gane shirinsa ko manufarsa fa wuyane dashi.
Ke dai in kin samu dama kiyi ƙoƙarin zuwa Airport da yamma wata ƙil a dace, zan turo miki hotuna Yah Usman PA Yayan Abokina Deen wanda yayisu a bayan motocin Dr Rayyern ɗin so sai ki ɗauki number's ɗin motocin ta wannan hanyar zaki iya samun damar bibiyarsa".
Cikin sanyi tace.
"Toh Ngd matuƙa".
Daga nan sukayi sallama.
Salman ta kira yana ɗagawa yace.
"Ya jikin namu?".
Cikin sanyi tace.
"Da sauƙi waya gaya maka?".
“A'isha Lawal ce ta gaya min tace ɗazu data kira Mom ce ta ɗaga wai jikinki ya tashi."
Ayyah tace a taƙaice kana ta mishi bayanin da Mahmoud ya mata ta ƙara da cewa.
"Ka shirya da yamma muje Airport ɗin bari in turoma hotunan".
Toh yace kana sukayi sallama.
Ƙarfe biyu dai-dai jirginsu ya sauƙa cikin international Airport Abuja.
Bayan wasu ƴan daƙiƙu, aka fara fitowa.
Mutun kusan 21 suka fito.
Kana Rayyern ya sako ƙafarsa ta dama kan matakalan forko.
Wani irin sassanyan numfashi ya shaƙa a hankali tare da zuƙan iskar ƙasarshi abin sonshi da al'faharin shi.
A hankali ya fara takowa yana sauƙa cikin haiba.
Da sauri ya ratayo jakarsa a kafaɗa tare da biyoshi a baya da gudu.
Usman kuwa shima jakarsu ya ratoyo kana ya biyoshi a baya.
da sauri ya matsoshi.
Juyowa yayi jin an riƙe mishi hannun damanshi.
"Hamma Rayyern daga nan wanne state ɗin zaka tafi".
Ya rasa gane meyasa zuciyarsa ke bawa yaron amanna ko dan kamar da sukeyi ne.
Sam bai shiryawa amsa mishi ba kawai yaji lips ɗinshi sun furta.
"Kano".
Wani irin tsalle yayi tare da cewa.
"Yesssss! Nima Kano zan tafi ai".
Cike da mamaki Usman ya nufosu har yana tuntube tare da cewa.
"Sir wannan fa?".
Juyowa yayi ya kalli Usman da salon.
Baya son shisshigi.
Shi kuwa Riyyam-nsra da sauri ya dawo kusa da Usman hannu ya bashi tare da cewa.
"Ni ƙaninsa ne".
Baki buɗe Usman ya bishi da ido.
Daga nan masallacin cikin Airport ɗin suka wuce, ganin azahar tayi har lokacin yaso zarcewa.
Suna idar da salla Usman ya miƙe da nufin fita ya samo abinci.
Dan yasan ubangidan nasan bazai buƙaci abinci yanzuba.
Juyowa yayi ya ɗan kalli Riyyam-nsra tare da cewa.
"Bishi kuje Restaurant".
Kai ya jujjuya tare da cewa.
"Bana jin yunwa".
Kai kawai ya gyaɗa mishi.
Nan suka zauna har la'asar tayi.
Bayan an idar da sallane kuma, suka koma ciki.
Domin shiga jirgin da zai wuce Kano.
Ƙarfe huɗu da rabi dai-dai jirginsu ya tashi daga birnin tarayyar Nigeria zuwa Kano ta dabo tumbin giwa.
A nan cikin Kano kuwa.
Jannart ce zaune cikin motar, Salman kana shi kuma yana gaba gefe.
Baba Ado dake jansu.
Yayinda sauran garadan dake tsaronta, suke hangame da baƙi a zatonsu tana can cikin ma'aikatar nasu, dan sam basu lura da lokacin da ta fitoba, koda yake Salman ne ya bawa Baba Ado key kana ya jawo motar har zuwa bakin mashigansu ya kawo mishi.
Shiyasa suka fita, basu ganeba.
Kai tsaye filin jirgin sama na malam Aminu Kano suka nufa.
Sosai kuwa Jannart tayi kyau acikin shigar pallazo da kuma tight shirt din dake jikinta, wanda ya bayyana lafaffen cikinta, kasancewar kuma rigar nata na d’an bayyana nipples dinta ne, yasa ta daura wata Navy blue fashion top akan shigar ta ta, wanda tsawonsa ya kawo har guiwanta, Yayinda ak’afanta take sanye da wani navy blue hill shoe, na company’n gucci mai kyau da tsada da uban tsini, akanta kuwa wani had’add’en medium vail ne wanda ya sauko harkan kirjinta.
Sam akan fuskarta babu wani kwalliya sosai, saidai kuma hakan bai hana zallar kyawun fuskarta bayyana ba, Yayinda small lips dinta suka sha peach lipstick, acikin jikinta kuwa wani sassanyan k’amshi ne yake tashi.
Suna shiga cikin Airport ɗin sukayi paking a Airport parking.
Kana suka wuce suka nufi cikin.
Bayan isarsu da kamar 5 minute, jirginsu Rayyern yayi sauƙar angulu.
Bayan yan daƙiƙu ne kuma matafinyan suka fara fitowa.
Da sauri Usman ya matso kusa da uban gidan nashi, cikin yin ƙasa da murya yace.
“Sir in kira driver?”
Shiru yayi ganin ya ɗan kaɗa mishi yatsarshi manuniya.
Shi kuwa Riyyam-nsra da sassarfa yake biye da Usman a baya.
A haka har suka fito asalin filin da matafiya kan zauna su jira masu tarbarsu.
Kanshi ya ɗan ɗago ya kalli taron mutanen, yatsarshi yasa ya ɗan gyara zaman farin glass ɗin dake idonshi.
Gefen lips ɗinshi na ƙasa ya ɗan kamo ya ɗan tauna a hankali.
Da sauri kuma ya ɗan juyo ya kalli bayanshi.
Inda ya hango Riyyam-nsra can baya yana ɗan tahowa yana waige waige a alamun shi yake nema.
Gabanshi ya nunawa Usman tare da yin mgna can ƙasa.
"Ƴan jarida ne, zanbi nan, in sun tsareka kaji dasu."
Yana faɗin haka, ya ratsa yabi yar siririyar hanyar dake gefen damanshi.
Shi kuwa Usman ya nufi hanyar fitan.
Jannart kuwa da sauri cikin tsananin razana ta koma bayan Salman tare da yin ƙasa da kanta murya can ƙasa tace.
"Innalillahi Salman gacan Hakim abokin Yah Junaid idan ya ganni zai gaya mishi."
Sai kuma ta zaro ido jikin tashin hankali ta dafe kirjinta tare da cewa.
"Na shiga ukuna tare suke da Yah Junaidu ma gashi can bayanshi".
Da sauri Salman ya ɗan kalli gabanshi kana ya juyo.
Gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi sabida hango Hakim Da Junaidu sun nufosu gadan-gadan.
Jujjuyawa tayi.
Ganin wata ƴar siririyar hanyar ne gefen hagunta, wacce nan Rayyern yabiyo.
Da sauri ta sunkuyar da kanta ta ratsa cikin ƴar hanyar ta ɓacewa ganin su.
Nannauyar ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauƙe, tare da ci gaba da tafiya cikin yar siriyar kusurwar.
Tana tafiya tana wai-waye da juyawa tana kallon bayanta.
Shi kuwa Rayyern, cikin ɗan sassarfa yake tafiya.
Saboda so yake kafinma Usman da Riyyam-nsra su fito, ya shiga taxi ya tafi.
Tafiya yake yana dai-dai-ta kan files da takardun da yayi ta aikin rattaɓa musu hannu a cikin jirgi.
Haka yasa bai lura da gabansa.
Ita kuwa Jannart tafiya take tana wai-waye shiyasa bata ganin gabanta.
Jin kamar takun wani a bayanta ne kamar ana boyota, kuma yasa ta ƙara saurinta.
Dai-dai lokacin kuwa Rayyern ya iso gab da ita.
Jin ana ce. Ke! Ke!! Yasa ta juya da nufin zata arta da gudu.
Sai kawai ta jita jikin mutum sunyi karo.
Goshinta ya bugi gemunshi da azaban ƙarfi.
Take files da Takardun hannunshi suka watse.
Yayinda ita kuma tayi tangal-tangal ta koma baya zata faɗi ƙasa, da sauri ta rumtse idanunta tare da sakin sauti mai cike da tsoro, hade kuma dasa hannunta da nufin dafe ginin dake wajen, dan kare kanta daga faɗuwa ƙasa.
Kawai sai ta kamo kwalan rigarshi ta gefe ta cikin da kuma Suit ɗin dake saman da ƙarfi.
Pet-pet haka boturan jikin rigar duk suka ɓalle, kab suka watso ƙasa, hakan yasa gaba ɗaya rigunan jikinshi suka buɗe.
Cikin wani irin masifeffen takaici yasa hannunshi ya fisge hannunta dake shaƙe da gefen kwalar rigarshi.
Ya yarfa hannun tare da zuba mata wani irin masifeffen....!
Kuyi hakuri rashin jina da wuri.
Rayyern da ban Riyyam-nsra da ban ai sunayenma ba iri ɗaya bako.
Free PAGE ne wannan.
By
*GARKUWAR FULANI*
By
*GARKUWAR FULANI*📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*TUBALI*
PAGE 5
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FREE PAGE NE*
*Littafin TUBALI na kuɗine, ki biya 500 in saki a ƙaramin group, ko kuma ki biya 1000 in saki Special Group, wanda cikin mako biyu kacal zamu ƙare part 1. Ki turo kuɗin ta asusuna na GTBank, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan numben whatsApp na 09097853276. Ki saya ki karanta cikin salama ba tare da hakkina a kankiba, in bazaki sayaba ga littatafai nan birjik kamar jompa a Jos sai ki samu na kyauta ki karance salim alin*
Kallo mai cike da tarin takaici ya watsa mata, rikitattun idanunshi cikin nata kwayar idanun kasan cewar suna fuskantar juna.
Wani irin azabebben zogi lips ɗinshi sukeyi sabida yadda ta bugi gemunshi da goshinta, har hakan yasa lips ɗin suka haɗe da kyawawan haƙorinsa.
Zut-zut haka yakeji suna zogi.
Da raɗaɗi, wani irin tafasa zuciyarshi takeyi tare da harbawa, files ɗin campany'nsa da yake da matuƙar mahimmanci da suke watse a ƙasa ya zubawa idanu.
Wani irin mugun kallo ya kuma watsa mata duk a cikin abinda baifi 5 second ba.
Idonshi ya kai bisa hannunta dake shaƙe da kwalar rigarsa ta gefe.
Hannunshi na dama yasa ya damƙo hannunta da azaban ƙarfi, kana ya yarfashi.
Wanda sanadin fizge hannun nata da yayi kuma wayarshi, kirar iphone 12 pro max dake cikin al'jihun rigarsa ya faɗo ƙasa.
Kana ita kuwa Jannart wani irin masifeffen karkarwa jikinta keyi.
Yayinda kuma gaba ɗaya hankalinta kecan baya.
Sabida masifar tsoron Yah Junaid da ta tabbatar muddin ya ganta sai ya kusan kasheta.
Haka yasa gaba ɗaya ma hankalinta baya kanshi, bare taga ta'adin da ta aikata mishi.
Tangal-tangal tayi lokacin daya yarfa hannun nata, da sauri ta dafe ginin gefenta tare da gyara tsayuwarta, cikin rashin sa'a ta sauƙe ƙafarta ta hagu kan glasss ɗin fuskar wayar tashi, da tsinin takalminta mai masifar ƙarfi.
Saurin yin ƙasa da kansa yayi, sakamakon jin ƙaran sautin fashewar glass din wayarsa, wanda take dauke da screen mai tsada.
Idonshi ya rumtse da ƙarfi.
Yana mai jin tamkar ya shaƙe wuyanta sai tayi sanyi.
Sam Ba ɗaruruwan kudin wayar yake tunawa ba, muhimman abubuwansa dake cikin wayar yake tunawa wanda yasan tabbas zai iya rasa wani abun.
Ita kuwa Jannart da sauri ta sunkuyo jin ta taka wani abu kuma tsantsi ya ɗebi ƙafarta.
Da sauri ta janye ƙafar tata cikin wani akasin kuma, ta sauƙe tsinin takalmin nata, kan tattausan ƙafarsa dake cikin tattausan takalmin fata,
dai-dai kan farcen babbar yatsarshi ta kafa tsinin takalmin tare da sake iya nauyi ta.
"Auchhhhhh!!". Ya sake wani irin sauti tare da rumtse idanunshi da ƙarfi, hade kuma da taune lips ɗin shi na kasa dake ta zogi tun buge shi da tayi.
Ƙara rumtse idanunshi yayi sabida wani irin,
masifeffen azaba da yaji tun daga tsakiyar kanshi har cikin ƙoƙon ranshi, kana ya iso kan babbar yatsar tashi.
Da sauri ta kuma janye ƙafarta, tare dayin baya kaɗan tana mai wai-wayen bayanta, alamun sam hankalinta baya gabanta sai baya.
Wani irin kallo ya zubawa tarin ɓarnar da tayi mishi,a lokaci ɗaya ta lalata mishi abubuwa da yawa, har lfyarshi bai tsiraba
Ta nuƙurƙusashi tamkar wanda yayi karo da tirela.
Wani irin nannauyan numfashin ta sauƙe ganin Salman ne ke biye da ita a bayan yana ce mata ke ɗin.
Da sauri Salman ya iso garesu.
Ganin yadda suke tsaye cirko-cirko.
Rayyern ya kalla cikin nitsuwa,
tare da fahimtar karo sukayi, cikin sauri yace.
"Innalillahi karo kukayi, bawan Allah kayi haƙuri."
Ya ƙare mgnar yana sunkuyawa files din ya fara tattarewa, yana mai cewa.
"Subahanallahi, wayarka duk ta dare, Jannart garin ya akayi haka".
Ita dai Jannart sai numfashin tsoro take sauƙewa, ta gaza cewa komai sabida ganin wani irin mugun masifeffen kallon da yake watsa mata, sai yanzu idonta ya kai ga ta'adin da tayi mishi.
Da sauri tayi ƙasa da kanta dan bata da jarumtar da zata iya jurar kallon nan daga kwayar fitinennun idanunshi.
Yatsun ƙafarshi ta tsurawa ido ganin yadda suke tsuma alamun tsananin azaba, ga kuma jini da take tsastsafowa.
Dib-dab-dib-dab haka taji zuciyarta na bugawa a 170.
Salman kuwa cikin yanayin damuwa ya miƙowa Dr Rayyern Mai-nasara Takardun da wayar cikin yanayin jin ba daɗi yace.
"Dan Allah da Manzonsa kayi haƙuri bawan Allah".
Idonshi ya rumtse da ƙarfi tare da miƙa hannunsa ya amshi takardun da wayar.
Sabida Salman ya gama dashi, tunda yace.
"Dan Allah da Manzonsa yayi haƙuri, to ya zame masa wajibi kuma dole yayi haƙuri sabida wannan shine mafi ƙololuwar al'farmar da mutun zai nema a wurin musulmi yayi mishi, wannan shine kalaman da Abban sa ke cemasa a mafi akasarin lokuta.
Amman badon haka ba yaso ya yarfawa wannan birkitacciyar yarinyar mari ɗaya rak, taji salon yadda tafin shi yake, so yayi ya yarfa mata mari da hannun hagunshi wanda yasan tabbas sai ta saki fitsari sabida ya lura bata iya bada haƙuri ba, kuma bata da nitsuwa.
Wani irin juyowa yayi ya watsa mata wani irin kallo da fuska a murtuƙe,
"Mchewwwww ". Yaja mata wani irin tsaki tare da yin kwaffa kana ya juya yayi gaba ba tare da yayiwa Salman mgn ba.
Cikin kaɗuwa Salman yace.
"Jannart ya akayi haka, kinga asarar da kikayi mishi kuwa, nasan tabbas duk yadda akayi kece da laifin karon tunda kin hango mala'ikan ɗaukan ranki, kina gudu kina rawan jiki kina wai-waye kinzo kin mishi ta'adi.
Kin kuma san kuɗin wayar nan da kika fasa mishi sarai amman ko a jikinki.
Sannan kin tsaya kinyi shiru, wannan wanne irin tsorone kijeyiwa Junaid?”
Ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe, tare da lumshe idanunta a hankali cikin nutsuwarta da ta fara dawowa tace.
“Allah ya bashi haƙuri, wlh Salman na rasa ta ina zan fara bashi haƙuri ne, kagafa wani irin kallon da yakemin tamkar zai shaƙeni ya kasheni, tsoronshi naji.
Sannan kuma duk tsorona kada Yah Junaid ya ganni, wlh in ya ganni a nan kuma bance zanzo nanba bisa aikina sai ya kusan kasheni, duk allurarsa ta sojoji a kaina zai direta."
Cikin takaici Salman yace.
"Shike nan ai mun rasa damar farko, dan yanzu dai da wuya in Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara bai wuceba tun tuni, matsalar ba sanin fuskarsa akayi ba bare ace da mun ganshi zamu ganeshi.
Dama dole bincike zamuyi da numbers din motocinsa, da aka bamu zamu ganeshi mubi bayanshi muga gidansu. Kinga har lau dai tsoron Junaid yana hanaki nasara.
Har nima ta shafeni."
Cikin takaici tace.
"Toh ya zanyi?".
Kwaɓe fuskarsa yayi tare da juyawa yayi baya.
Itama kuwa juyawa tayi tabi bayanshi.
Riyyam-nsra kuwa, ɓat RAYYERN da Usman PA suka ɓacewa ganinsa.
Gaba ɗaya ya gama zagaye wurin babu su ba dalilin su.
Wani irin masifeffen kuka yakeji tun daga can ƙasan maƙoshi sa yana taso mishi.
Saboda lokaci daya yaga samu ya kuma ga rashi.
Kana layinshi bazaiyi aiki a nanba bare ya kira Mammy ya sanar mata halin da yake ciki.
Hakan yasa yake jin wani irin ƙuncin rai.
Gefe ya koma ya zauna bisa kujera, tare da maida kanshi ya jingine yana mai jin wasu irin zafafan hawaye na tsastsafo mishi.
Da sauri Salman ya nunawa Jannart Riyyam-nsra tare da cewa.
“Ikon Allah Jannart ga mutuminki".
Juyowa sukayi suna kallonshi.
Shidinma kuwa Idanunshi da sukayi ja ya buɗe yana kallonsu.
A hankali Jannart tace.
"Kai ba shi bane, sai dai ko ƙaninshi".
Da sauri Riyyam-nsra ya miƙe tsaye tare da rataya jakarshi bisa kafaɗa.
"Assalamu alaikum".
Yace yana miƙawa Salman hannu.
"Wa alaikassalam".
Yace tare da bashi hannu.
Sukayi musabiha, cikin sanyi Jannart tace.
"Ayyah dan Allah ka cewa yayanka yayi haƙuri, ban sani bane".
Cikin fahimtar cewa. Rayyern suka gani suke cewa yayanshi, ya ɗanyi murmushi cikin hikima yace.
"Ta ina kuka haɗu ina yake.
Ni ya ɓace min ne nasan kuma shima ni yake nema yanzu".
Da sauri Salman yace.
"Ikon Allah ta nan yayi, to amman ba zuwa za'ayi a ɗaukeku ba".
Da sauri ya nufi inda Salman ya nuna mishi yana mai cewa.
"Dan Allah kuzo ku nuna min inda yayin".
Cikin nitsuwarta tace.
"Wani aiki mukazo yi nan Airport ɗin kai dai kawai kayi nan ɗin zaka ganshi."
Salman ne ya ɗan harareta irin hararar da har yau bata gano manufarsaba,
Bayan Riyyam-nsra yabi tare da cewa.
"Na nawa kuma aikin yau dai ai mun rasa damar sai dai mubi mataki na gaba, kuma dan Allah fa yace so muje mu nuna mishi."
Dole tabi bayansu.
Gaba ɗaya harabar wurin Airport parking din babushi babu alamarsa.
Kana sun dudduba gefe-gefen duk bashi, cike da gajiya da son komawa gida Jannart tace.
"Kai to ka tare taxi mana ya kaika gida".
Dafa motarsu yayi tare da kwaɓe fuskarsa kana yace.
"Ai baƙone ni, mu baƙine daga Ethiopia, wani aikine Hamma na yazo yi, shine mukazo tare".
“Toh ka kirashi a waya mana".
Cewar Salman.
Dafe kai yayi tare da cewa.
"Toh ai dole sai na sai layin nan ƙasar taku nasa.
Shiru sukayi baki ɗayansu,
Can dai Jannart tace.
"Toh yanzu ya zakayi".
Cikin danne tarin damuwarsa yace.
"Ku taimaka ku kaini na sayi layi.
Sannan sai in nemi masauƙi".
Haka kuwa akayi Salman ya amince bayan sun kaishi, ya sayi sim card layin Mtn, yayi register.
Tuni lokacin biyar ta gota,
A hankali suka fito bakin shagon.
Cikin kula da alamun kallon akwai inda Salman ya sanshi yace.
"Toh ƙanina yanzu ina zakaje ne?".
Jingina kansa yayi da jikin motar kasan cewar, CRV ce tanada tudu.
Idonsa ya lumshe tare da fara wassafo dajar shigar dake jikin Rayyern.
Kama daga Suit ɗinsa agogon hannunsa takalmansa zoben yatsarsa, uwa uba wayarsa.
Da kuma irin takardun da yaga yana ciccikewa da matsayin inda suka zauna.
Cikin sauƙe numfashi ya ɗago kansa tare da gamsuwa da tunaninsa yace.
"Ku taimaka ku kaini hotel mai kyau, wanda yake anguwar manyan mutane.
In na isa na samu layi na ya hau zanyi mishi text ta Email ɗinsa".
Da sauri Jannart tace.
“Toh ni dai Salman ka medani kafin ka kaishi."
Murmushi Salman yayi tare da cewa.
"Toh ai sai mun wuce ta inda yake so ɗin ba yace unguwar manya ba, mu kaishi hotels ɗin Nasarawa GRA kawai".
Juyowa tayi ta kalleshi kana tace.
“Uhum kafa san abubuwan wuraren tsada garesu ko, sannan kai kana ma da kuɗin ƙasar nanne?."
Murmushi Riyyam-nsra yayi tare da cewa.
"Yess ina dasu, nayi canji tun a ƙasata, kuma in ma bazasu isaba ai zasu amshi transfer ko?."
Kai ta gyaɗa mishi tana kallon tarin kamanninsa da wanda tayi karo dashi.
Bayan sun shiga motar ne.
Baba Ado yaja.
Salman na gaba kusa da Baba Ado shi kuma yana gefenta.
Cikin hausarsa da bata isasshen inganci yace.
"Hotel mai kyaufa".
Gyara zama Salman yayi tare da cewa.
"Kada ka damu. *Nasarawa GRA* itace unguwar da ta tara kaf manyan masu kudi na Kano,babu wani babban mai kudi ko ɗan siyasa na Kano da ya isa yake ji da kansa dama sauran jahohi da basu da gida a. Nasarawa GRA hatta Government House ma anan yake.
Sannan a cikin GRA din akwai manyan layuka da sunayensu
*Lamiɗo Creasend* da kuma *Ahmadu Bello way* da kuma sauran ƙana nan layuka.
Kana akwai manyan Hotel's din da suke Nassara GRA akwai *Tahir Guest Palace*
da kuma *Ni'ima Hotel* da *Green Park* da *Liyafa Hotel* duk wadannan suna cikin Nasarawa GRA ne, kuma manya ne sosai ana ji da su suna da tsada da kuma kyau da inganci, zaka samu duk abinda kakeso a ciki.
Yanzu sai ka zaɓi wanne zan kaika, kaga dare ya fara yi mana."
Numfashin ya ɗan sauke cikin jin daɗi da gamsuwa da bayanin unguwar da suka shigo ɗin, daga shiga unguwar kasan ta manya ce.
"Muje Taheer Guest palace hotel".
Riyyam-nsra ya faɗi yana kallon gefen titin garin.
“To Alhamdulillah gashi ma mun kusa.
”Salman yace yana mai karya kwanan shiga layin da hotel ɗin yake.
Suna shiga bayan yayi parking, Suka sallameshi suka tafi.
Salman na cewa.
"To sai zuwa gobe zan kiraka in sha Allah inji ko ka gane ya'yan naka. Tunda na amshi number taka ta ƙasarmu".
Toh yace tare dayi musu godiya.
Suna fita Suka nufi ma'aikatar su ta Arewa 24. Tafiya ce mai ɗan tazara tsakani.
Hakane yasa Baba Ado yake gudu.
Mintuna kaɗan suka isa.
Suna isa suka samu su Sunday a tsaye ƙiƙam to babu salla bare salati sai tsaron Jannart in wata tayi a biyasu makudan kud’in, da su kansu har yau basu gano manufar tsaron da ake bata, fiye da shi kanshi Alhaji Idi Sale Dakata'n ba, ko kanshi bai bawa wannan tsaron ba haka babban ɗan sa dasu Abdul, to ko dan ita macece shiyasa.
Cikin hikima Baba Ado yayi parking jikin motarsu.
Kana suka fita suka shiga cikin ma'aikatan jim kaɗan Jannart ta fito.
Suna ganin ta fito suka mara mata baya.
Tana shiga mota Baba Ado yaja.
Kana yaja suma sauran suka bishi a baya ganin. Yaja ɗin.
*Dr Rayyern*
Wani Irin karkarwa ƙafarsa keyi, sosai yatsar ke fidda jini.
A haka ya tsaida ɗan taxi ya shiga, ba tare da yace komaiba, mai taxi ɗin yaja.
Bayan sun fita Airport ɗin sun miƙa hanyar cikin gari.
Kanshi ya jingina da jikin kujerar, wani irin masifeffen zafi yakeji zufa na tsastsafo mishi tako ina, sabida zogin da yatsarsa keyi, ga lips ɗinsa dake raɗaɗi kana ga zuciyarsa dake tafarfasa.
Sosai mai taxi ɗin ya dai-dai ta motar tasa bisa titi, a hankali yace.
"Sir ina muka nufa?".
Shiru yayi tamkar bai jishi ba sabida zogin fashewan farcenshi da yatsarsa su suka buwayeshi.
Sai da ya kuma tambaya kana cikin taune lips ɗinsa yace.
"Nassarawa GRA".
Toh yace kana yaci gaba da driving.
Tabbas da AC cikin motar amman bai gamsar dashi haka yasa yaketa haɗa zufa.
Suna shiga cikin tsakiyar anguwar Driver'n ya kuma juyowa ya ɗan kalleshi a hankali yace.
"Sir ta ina zamu ɓullo?".
A takaice yace.
"Ahmadu Bello way".
To ya Kuma cewa kana sukaci gaba da tafi kan kyakkyawan titin mai faɗi da wadatan tsabta.
Tafiya yakeyi a hankali.
Yanayi yana ɗan kallon tabka-tabkan gidajen dake shumfud’e na gani na faɗa tamkar abirnin India.
"Kayi hannun dama". Dr Rayyern Mai-nasara ya faɗa mishi a hankali.
To yace tare da ratsa wa damanshi.
Wow yace lokacin da suka fito kan ɗan madaidacin titin, da wani irin tamfatsetsen gida mai tsananin kyau na al'farma yake forkon layin.
“Yayi tsaya a nan".
ya kuma tsinkayo muryar Dr.Rayyern.
Juyowa yayi ya kalleshi kana ya juyo ya kalli tamfatsetsen gidan, na al'farmar da in ya kintata nanne gidansu.
Cikin ransa yake tasbihi ga Allah.
Tare da juyowa ya kalli shi kana a mutunce yace.
"Mai gida in shigar da kai ciki mana, naga tun kan ka shiga yatsarka na zubda jini".
Wani irin taɓe fuskarsa yayi,a rayuwarsa babu abinda ya tsana sama da haka, mutun ya shiga harkar sa, sam shi a tsarinsa babu ruwansa da shiga sabgar da bata shafeshi ba, sai dai kuma yana matuƙar son tausayawa sabida shi mai tausayine.
Cikin dakekkiyar murya yace.
"No ba matsala.
Bani da canji ko zaka bani Account number ɗinka inyi maka transfer'n in ba matsala?".
Da sauri mai taxi yace.
"Okay Sir".
Kana ya fara karanto mishi ac no ɗin.
Wata ƙaramar waya ya zaro a al'jihun rigarsa ta ɗaya gefen.
Ya ɗan lallatsa jim kaɗan ya medata al'jihun.
Cikin tsananin jin daɗi mai taxi ya kalli text ɗin Alert daya shigo masa na dubu ashirin.
Cikin jin daɗi yace.
"Ngd matuƙa Allah ya ƙara buɗi ya jiƙan iyaye".
"Amin".
Yace kana ya sako ƙafarsa waje, a hankali ya takata.
"Shehyytt". Ya ɗan fidda sautin sabida ƙafar tayi tsami, tuni yatsar ta kumbura.
Bayan ya fito ne kuma mai taxi ɗin yaja motar ya tafi.
Shi kuwa Rayyern a hankali tare da d’an ɗingisa ƙafar tasa ya nufi bakin kekyawan gate ɗin.
Kan yatsarsa manuniya yasa ya ɗan ƙonƙosa jikin ƙofar.
Da sauri wani kekyawan buzu dake zaune bakin ƙofar ya miƙe tsaye, tare da zuwa ya ɗan tura wani abu, kana ya leƙa da ido ɗaya.
Da sauri ya meda abin ya rufe tare da sakin murmushi cikin tsananin jin daɗi ya ja ƙofar ya buɗe yana mai cewa.
"Masha Allah, Dr. ya dawo".
Da sauri wani kekyawan matashi dake fitowa daga can cikin gidan cikin ya nufi baki gate ɗin cike da farin ciki.
Yana cewa.
"Alhamdulillah, Abba! Abba!!! Mamy ga Hamma Rayyern ya iso".
Ya ƙare mgnar yana mai rungume Dr Rayyern da ya shigo.
Yayinda wasu mutanen suka taso da sauri suka iso garesu.
"Dakta Barka da isowa lfy".
Shine abinda suke haɗa baki wurin faɗa da alamun shaƙuwa da so.
Duk da alamun akwai driver' a ciki da kuma mai bawa fulawa ruwa sai kuma mai wankinsu da guga,
Sai Baba Mauɗo wannan buzun da alamun mai gadinsu ne, shi.
Wani ɗan guntun murmushi yayi tare dasa hannunshi ya shafa kan wannan kekyawan matashi daya amshi takardun hannunshi yace.
“I miss you so much my Ramadan".
Kana ya bawa Baba Mauɗo hannu cikin kulawa da girmamawa tare dasu Ari sukayi musabaha.
Anutse yayi gaba Ramadan na biye dashi a baya.
Yayinda Su kuma suka koma wurin aikinsu, suna me farin cikin dawowar Dakta wanda yayi kusan mako huɗu baya nan.
Suna ratsa farfajiyar gidan da a ƙalla zai ɗauki motoci 7 zuwa 9 kuma ko wacce bazata matsi ko gogi ƴar uwarta ba.
Gaba ɗaya gidan zagaye yake da dogayen bishiyoyin na mijin gwanda, sai sirran Ayaba dake ƙasansu a jere da ƴan guntayen dabino.
Kana daga can baya kuma wani ɗan ma dai-dai-cin Garden ne mai masifar kyau, wanda yake cike da itatuwa da tsirrai masu sanyi da ƙamshi.
Kana daga farfajiyar gidan akwai wani baranda mai kyau da faɗi, wanda yake da steps.
Ata ƙasanshi gefen bishiyoyin an jera fararen kujerun silver hakama a ciki.
Kana tura ƙofar zaka riski wani hamshaƙin falo mai ɗan karen girma, Dan fadi da girmawa kuwa AC ma biyu ne aciki.
Ta gefen hagun falon gab da bakin ƙofar shigowa kuwa, wani ɗan madaidacin Bathroom ne.
Sai kuma gefen hagu, wani corridor ne mai fadi.
Kana shiga wurin zaka ga steps ɗin hawa sama masu faɗi.
Can gefen Bathroom din kuma ta gaba, wani kekkyawan Dinning area ne mai dauke da table mai kujeru takwas, sai wani Fridge mai suffar show glass Wanda ke cike maƙil da kayan sha.
Sai gefenshi kaɗan washing hand baby ne.
Kana ta kanshi ƙofar kitchine ne mai girma, wanda yake ƙawace da Kitchen cabinets and drawers masu masifar kyau, komai na ciki blue color and white ne.
Daga cikin kitchen din kuma ƙofar store ne.
Daga cikin store kuma akwai ƙofar baya, inda wasu igiyoyin shanya ke jere da kuma inda suke ajiye kamarsu dankali, doya, al'basa, da dai ire irensu.
Daga Kitchine din kuwa akwai wata ƙofar da zata ratsa ta cikin wani corridor, mai ɗauke da ɗan madaidacin falo mai 3 Bedroom,s and bathrooms. Sai ɗan Dinning area ƙarami.
Can gefen dama kuwa inda benen yake, kana hawa sama kan steps din, kana iya hango cikin falon ƙasa.
Tafiya kaɗan zakayi ka riski wani babban falo mai masifar kyau da tsaruwa.
Can gefe kuma wani kekkyawan Dinning table ne shirye cikin Dinning area mai sarƙafe da labule mai zirin-zirin igiyoyin dake sarƙafe da duwatsu masu daraja sheƙin Diamond.
Kana sai wani Fridge shima kamar show glass kana gefenshi kuma Show glass ɗinne mai shirye da cups, plates, spoons, mug's da dai sauransu.
Sai Kitchen dake gefe da store kamar na falon ƙasa.
Kana sai Bedroom guda biyu, wanda basa kusa da juna dan a tsakanin su Dinning area da kitchen da store suke.
Akwai wata baranda mai kyau ta bayan ɗaya Bedroom ɗin inda nanne ɗakin Dr.Rayyern ɗayan kuma na Ramadan.
Ƙasan benen kuma akwai wata ƙofar wanda kana shiga zaka samu wani side ne kuma irin na saman sak, koman su iri ɗaya.
Sai can gefen kitchin ɗin falon ƙasan kuma akwai wani kofa wanda room and parlour ne mai kyau da Bathroom a ciki.
Daga gefe kuma can akwai ɗaki ɗaya inda masu aiki zata iya zama, amman bbu mai aikin a gidan.
Can waje kuma akwai BQ, Boys Quaters.
Gefen BQ ɗin kuma wani part ne mai kyau matsakaici a rufe yake su kansu Dr Rayyern da Ramadan Basu san menene a cikin wannan Part ɗin ba.
Tsarin gidan dai masha ALLAH.
Bisa wannan babban baranda mai steps biyar zuwa shida suka hau. Kana suka buɗe kofar babban falon.
Ramadan na mai kiran Abba! Abba!! Yana buɗe kofar suka hango Abba da Mamy, suna sauƙowa daga steps ɗin Dinning area, Wanda ta nan zasu fito side ɗinsu.
Wani kyakkyawan mutum ne mai matsakaicin shekaru, mai jini a jiki da tarin cikar haiba da kamala.
Ganin Rayyern dinne kuma yasa shi sakin wani irin yalwataccen murmushi, tare da buɗe hannayenshi dake cikin gariyar jikinsa.
Da sauri Dr Rayyern ya ƙarasa gabansa.
Rungumeshi yayi tsam a jikinsa tare da sauƙe ajiyan zuciya.
Mamy kuwa gefe ta zauna bisa kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, cikin haiba da tarin son ɗan nata tace.
“Babana wato Abba kawai kayi missing ko".
Da sauri ya saki Abba yana murmushi mai cike da farin cikin ganinsu yace.
"Na isa Mamy, bakiji me bahaushe yace ba."
Da sauri tace.
"Me yace".
Ta ƙare mgnar tana yiwa Abba kallon tsokana.
Matsowa yayi kusa da ita, hannunta ya kamo ya ɗaura tsakiyar kanshi tare da yin ƙasa da murya yace.
“Uwa mafi uba koda uban sarki ne".
Dariya mai cike da so tayi mishi.
Abba kuwa gefenta ya zauna tare da tsareshi da ido.
Ƙeyarshi ya ɗan sosa cikin sanyi yace.
“Abba bani ne na faɗa bafa, Malam bahaushe ne ya faɗa".
Ramadan ne yayi murmushi yana mai jin daɗin, yaga Hamman nashi yana gaban iyayensu, dan nanne kaɗai zakaga fara'arsa ka kuma ji yayi doguwar mgn Especially in da Abba ne.
A hankali ya zauna gaban Abban nasu, tare da miƙar da ƙafarsa dake masifar mishi zogi.
Ita kuwa Mamy Dinning area ta nufa.
Plate ta ɗauƙa cikin show glass din, kana ta buɗe Fridge.
Chocolates da sweet ta cika cikin plate ɗin.
Kana ɗayan kuma tasa Apple da inibi. sai kuma goran ruwa da cup a ɗaya ta shiryasu, bisa tray'n kana ta nufo falon.
Da sauri Ramadan ya matso kusa dashi, tare da zubawa ƙafarsa ido cikin mmki yace.
"Innalillahi Hamma Rayyern meya samu ƙafarka?”
A hankali ya miƙar da ƙafar tare da motsa ta.
Da sauri Mamy ta ƙasaro, Abba kuwa sunkuyowa yayi ya kama ƙafar cikin tashin hankali, ganin yadda yatsar ta haye ta kumbura ga jini har yanzu zuba yakeyi.
"Rayyern, meya sameka? Meya faru?".
Yayi tambayar a rikice.
Kanshi ya ɗan sunkuyar ya kalli ƙafar tasa, kana a hankali yace.
"Wata mahaukaciya ce ta takani".
Yayi mgnar cikin salonsa na rashin iya ƙarya.
"Wacece ita a ina kuka haɗu?".
Abba ya kuma tambaya.
"Ban santaba, just kawai dai I know mental problem ce, kuma a Airport muka hadu.”
Ya bashi amsa, adan takai ce yana mai cije labb’ansa, wanda kuma hakan alamace dake nuna cewar kafar tanayi mishi zafi sosae.
Ramadan kuwa da sauri ya miƙe, ɗakinsa ya haura da sassarfa, dan ƙaramin akwatin taimakon gaggawa na likitoci ya ɗauko.
Yana sauƙowa ya zauna daɓas a gaban Dr.Rayyern ɗin, kamo ƙafar yayi tare da fara bashi taimakon gaggawa dan jinin ya tsaya.
Cikin mmki Ramadan yace.
"Sorry Hamma har nail dinka ya fashe, amma Mahaukaciya a airport how? then why akabarta ta shiga airport din?”
“Uhmmm” yace dan azaban zafin da yakeji.
Da sauri suka ɗago kansu baki ɗayansu.
Shi Dr.Rayyern TV dake like jikin ginin ya zubawa idanu.
Tamkar zai mannasu jikin fuskar kekyawan Dattijon nan Malam Mai-nasara da aka hasko a tashar Sunnah TV.
Ahankali ya janye ƙafarsa daga riƙon da Ramadan yayi mishi.
Tare da juyawa ya maida hankalinshi ga TV, yayinda shima Ramadan hakan yayi.
Abba da Mamy kuwa idanu suka zubawa Rayyern ɗin.
Wani irin kallo Abba yakeyi mishi mai cike da ma'anoni.
Cikin haɗe fuska yace.
"Kai Ramadan tashi ka kashe tv’n nan".
Juyawa sukayi baki ɗayansu suna kallonshi.
Fuskarshi dake haɗe ne yasa Rayyern yin ƙasa da kanshi, cikin sassayan sauti murya can ƙasa yace.
“Please Abba kayi haƙuri wa'azinshi nada daɗi".
Cikin tsawa yace.
"Ramadan kashe min TV nan".
Da sauri Ramadan ya miƙe jiki na rawa ya kashe TV’n.
Shi kuwa Rayyern cikin wani irin rauni da biyayya, ga mahaifin nashi da bin umarnin shi da neman izininshi yace.
“Abba kayi haƙuri".
Fuska a haɗe yace.
"Ramadan zokayi mishi aikin daya dace.
To yace kana yazo ya wonke mishi yatsar yayi mishi dreesing ɗin wurin da duk abinda ya kamata.
Yana gamawa magriba nayi.
Dole suka miƙe sukayi al'wala kana suka nufi masallaci.
Jannart kuwa.
A hankali ta kutsa kanta cikin falon nasu.
Tazo tsakiyar falon kekan tayi kiciɓis da...!
In sha Allah zuwa dare in na samu caji zakuga PAGE 6.
Littafin TUBALI na kuɗine .
By
*GARKUWAR FULANI*📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*TUBALI*
PAGE 6
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
*FREE PAGE ne*
*Littafin TUBALI na kuɗine ki biya ki darinki biyar kacal in saki a ƙaramin group wanda bonus ne ga dana na, dan in na gama ya zama Complete 1k ne, saukine yanzu ga Masoyana, asalin kuɗi nai 1k ne, Special Group kuma su post nasu zaifi yawa. 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo shaidar biyanki ta whatsApp 09097853276. Kada ki bari garabasar ta wuceki, kice sai an gama, Hajia in kuma kinada zakuwa da turo 1k a saukake cikin makonni bibbiyu zamuke gama part-part*
Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki👩🏻🦰 da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci😄iya kudinka iya shagalinka💃kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR)
Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza.
kada kubari abaku labari😍 munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai🏨 da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR 👩🏻🦰da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki.
Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm🪞🎁🛒🛍️🤝🏻
Da Yah Junaid, wani irin masifeffen tsorone ya rufeta wanda yasa ta fara ja da baya.
"Dan ubanki sai yanzu kika dawo? Ina kikaje kika tsaya? Tukun nama ƙarfe nawa ne ƙa'idar tashi aikinki?"
Ƙara matsota yayi tare da buga mata tsawa.
"Shegiya ƴar iska badake nake mgn bane kina jina kinyi shiruba".
Cikin rawan murya tace.
"Uh uhm dama gidan Baba Kabir nake".
Ta ƙare mgnar tana komawa gefen Mom da yanzu ta iso.
Cikin haɗe fuska tace.
"Yarinyar nanfa ba isasshen lfy ne da itaba".
Juya kai yayi ya watsa mata wani irin masifeffen kallo tare da cewa.
"Toh uwar shisshigi".
A hatsale Mom tace.
"Toh ubana, anyi Shisshigin aikin banza".
Ta ƙare mgnar da kama hannun Jannart sukayi ciki.
Shi kuwa kwaffa yayi tare da bin bayan Abdul da yazo ya wuce su, bai ce musu ko ƙalaba.
Riyyam-nsra ne kwance bisa tattausan gadon ɗakin hotel ɗin daya kama.
Tuni yasa sim card ɗin sa na Mtn har ya zauna ras a wayar.
Kana yasa katin daya saya tun wurin sayan layin.
Mgn yakeyi da Mammy.
Yana mata bayanin haɗuwarsa da mutumin nan da suke kama.
Harma da haɗuwarsu da su Salman, kana ya ƙara da cewa.
"Mammy al'ummar Nigeria suna da kirki, suna da mutunci da mutunta baƙo, naga karamcinsu tun a cikin jirgi.
Mammy ina son su ina son ƙasar."
Cikin sauƙe numfashi tace.
"Yesssss! Riyyam akwai masu kirki, da amana da kawaici.
Amman kuma akwai maha'inta azzalumai macuta, ka kula da kanka kayi taka tsantsan."
Cikin gamsuwa yace.
"Toh Mammy in sha Allah zan kula".
Daga nan ta bawa Zayton sukayi ta hira yana mai gaya mata yadda ƙasar take.
Zaune suke a falon gidan Dr Lukman.
Cikin tawagarsu ta gamayyar kamfanonin jihar da kuma likitoci.
Dr Lukman keyi musu bayanin cewa.
"Dr Rayyern Mai-nasara ya dawo a yammacin yau, kuma Alhamdulillah dama akwai taron da gwamnatin jiha zatayi damu likitoci a gobe da safe, shine babban dalilin dawowarsa.
Toh muna tashi a taron zanyi ƙoƙarin tahowa dashi campany'n Alhaji Idi Sale Dakata, muyi taron jan ra'ayin nashi a can".
Cikin gamsuwa sukace eh hakan yayi.
Kana sukaci gaba da tattaunawar.
Ab’angaren Dr Rayyern Mai-nasara kuwa, kusan atare suka shigo cikin gidan shida Abba da kuma Ramadan, wanda yanzunne dawowansu daga masallaci, domin koda suka yi sallah’n magriba basu fito daga cikin masallacin ba, har saida aka sallame salla’n Isha.
Kaitsaye cikin babban falon gidan suka nufa, Yayinda zuciyar kowannensu ke cike da sanyi da kuma salama, musamman ga yanda iska mai dadi ke kad’awa tana ratsa kowani hudan gashi na jikin d’an Adam mai rai.
Haka suka shigo falon Abba na gaba, sai Rayyern dake take masa baya, wanda yayi na k’arshen shigowa kuwa shine Ramadan, wanda yake d’an shafa screen d’in wayar dake rike a hannunsa.
Ganin shigowarsu ne kuma yasa Mamy dake, tsaye agaban had’add’en dining table d’insu wanda aka k’awatasa da wasu fitinannun royal chairs, ta saki sassanyar murmushin dake bayyana tsananin k’aunarta ga ahalin nata, murya asake tace.
“Masha Allah! Our dinner is ready.”
Jin hakan da sukayi dinne kuma yasa kasu sakin murmushi, tare da wuce wa dining area din kai tsaye.
Ramadan kuwa kulolin da Mamy ta miƙo kishi ya amsa dasu plate and spoos da gorunan ruwa mai sanyi.
Kana ya juya ya fita, dan kaiwa su Baba Mauɗo nasu abincin cikin kamala da mutuntaka ya kai musu kana ya dawo.
Shikuwa Rayyern da tun fitowarsu daga masallaci, yake tasbihi acikin zuciyarsa, kaitsaye gaban had’add’en fridge’n mai kaman show glass d’in dake dining area din ya nufa, yana isa kuwa ya bud’e murfin fridge’n, tare da d’ansa kansa ya zaro babban ledan chocolate na diary milk , wanda ya d’au sanyi sosai.
Maida murfin fridge’n yayi ya rufe, tare da juyowa ya zauna akan d’aya daga cikin kujerun dining table d’in, wanda aka cika saman babban table d’in, da kayan cima kala kala, more especially fruits.
Ahankali ya b’are ledan, tare da kai chocolate d’in bakinsa.
Fitinannun idanunsa masu d’auke da long eye lashes ya lumshe, adaidai lokacin da yaji d’and’ano da kuma zak’in chocolate din ya mamaye harshen sa, wanda hakan yasa shi sake tura chocolate din abakinsa, tare da soma taunawa ahankali, yana maijin wani irin sanyi aransa, Tabbas aduk sanda yake cin abunda yakeso, yakanji wani irin gamsuwa na musamman, musamman madai duk wani abu mai zak’i, kwarai yanason zak’i sosai da sosai.
Abba da Mamy dake zaune kuwa idanunsu kawai suka zuba masa, musamman ma Abba da bayajin dad’in, yawan shan zak’in da Rayyern d’in keyi, always shan zak’i sai kace karamin yaro.
Shikuwa Rayyern da har yanzu idanunsa ke lumshe, hakanan yaji ajikinsa cewa akwai k’wayoyin idanun dake kansa, wanda hakan yasa ahankali yad’an ware oily eyes d’insa, masu matuk’ar kyau da daukar hankali.
Karab sukayi ido hudu da Abba, hakanne kuwa yasa shi d’an gyara zamansa, tare kuma da yin k’asa da kansa, saboda acikin 2 second din ya fahimci wani irin kallo Abban, nasa keyi masa.
Zare chocolate din dake bakinnasa yayi, tare da ajiyewa agefe.
Ganin hakanne kuma yasa Mamy da Ramadan yin murmushi, shikuwa Abba plate d’in dake dauke da crispy microwave Patatoe chips, and salad, da kuma onion sauce ya turowa Rayyern d’in gabansa.
Tare da cewa.
“Maza kacinye wannan.”
Plate din da Abban nasa ya turo masa ya kalla, tare da d’an zaro idanunsa, kana lokaci guda kuma ya sanja mood dinsa izuwa shagwab’a, akasalance cikin kuma muryarsa da bakowa kejinta ba yace.
“Abba duka wannan zan ci?.”
“Eh duka kuma yanzu nakeson kaci.” Abba ya fad’a cikin tsare gida.
Ahankali ya saukar da idanunsa k’asa, saboda yanda yaji tone din Abban nasu, yasan abun is seriously.
D’aukan plate d’in abincin yayi tare da fork ahankali, yakai abincin bakinsa bayan yayi bismillah.
Bai kuwa wani ci abincin sosai ba, ya d’ago kansa ya kalli Mamy dake cin abincinta itama.
Cikin muryarsa dake bayyana rashin sabonsa dayin magana mai yawa yace.
“Please Mamy na k’oshi da abincin nan ki bani tea.”
D’agowa Abba yayi ya kalleshi, still kuma cikin tsare gida yace.
“A’a fa yau sai kacinye abincin nan tas, saboda haka babu wani tea din da za’a baka.”
Maraitattun idanunsa yad’an lumshe, cikin kuma yanayin dake bayyana tsananin biyayyarsa ga mahaifinnasa yace.
“To Abba amma dan Allah abani tea sai in had’a, na tabbata abincin zaifi shiga...”
Yanayin yanda ya k’are maganar yana karyar da wuyansa gefe ne, yasa Abban sakin murmushi, cike da k’aunar d’an nasa yace.
“Shikenan to na yarda ka had’a da tea d’in.”
Jin haka yasa Mamy tashi ta soma kokarin had’a masa tea, kamar yanda ya buk’ata.
Shikuwa Murmushin jin dad’i yayi, saboda dama shi yafison ko yaya idan zaici abinci, ya zamana yana mixing abincin da abu mai zak’i, gashi kuma dama shi.
Sam baya da yawan cin abinci, sometimes idan yaci chocolate d’insa ya d’aura da bootle water, yakanji sa dai-dai.
Had’a masa tea d’in acikin mug Mamy tayi ta mik’o masa, koda ya karb’a bai wuce 3 sipping yayi ba, ya d’ago kansa ahankali ya kalleta.
Cikin yanayi da salon maganarsa yace.
“Ayyah Mamyna sugar baiji ba dai, please ki karamin.”
Idanu Mamy tad’an zaro cikin yanayin mamaki tace.
“Rayyern Shugar 3spoon amma kace baiyi maka ba, kai dai kam shan zak’i ya zama maka jiki.”
Ta kare maganar tana mai k’ara masa Shugar one spoon acikin tea d’in.
Murmushi kawai yayi, batare daya kuma cewa komai ba, ya maida kansa ya cigaba da sipping tea din, sai time to time yake daukan patatoe daya yakai bakinsa, nan ma kuma gudun kada Abba yayi masa fad’a ne.
Saida yasha kusan rabin tea d’in, kafin ya d’ago da kansa ahankali ya kalli Ramadan dake cin abinci.
“Ramadan ya hospital d’in, ina fatan komai yana tafiya dai-dai ko?.”
Ramadan kuwa Jin abunda Hamman nashi ya tambaya ne, yasa shi dakatawa da cin abincin, tare da cewa.
“Alhamdulillah Hamma Rayyern komai yana tafiya yanda ya kamata, bayan wannan tafiyar taka ma Ya Sulaiman yana zuwa, tare mukeyin duk wasu abubuwan da suka dace.”
Idanunsa ya d’an lumshe ahankali tare da jinjina kansa, Tabbas dama yasan koda bayanan, Sulaiman da Ramadan zasu gudanar da komai yanda ya kamata kana ga sauran Doctor's ɗin, kasancewar dukansu Doctors ne way’anda suka san aikinsu, kuma kowannensu da irin k’warewarsa.
Hiran hospital d’in da kuma irin manya manyan ayyukan da sukayi, alokacin da bayanan Ramadan d’in ya shiga yi masa.
Yayinda shi kuwa ahankali yake d’an jinjina kansa, alaman gamsuwa, saboda zuwa yanzu bakinsa ya dan fara gajiya da motsawa.
Abba da tun d’azun ya kafesu da idanu baya ko k’yaftawa, murmushi ne kawai ke bayyane akan fuskarsa.
Yayinda yake yiwa yaran nasa, wani irin kallo mai d’auke da tsananin k’auna had’i da soyayya, Tabbas yanaji aransa cewa yaransa GARKUWA ne, sannan koda bayan ransa da izinin Ubangiji,
Zasu ƙarasa ginin TUBALI’n da aka fara ginasa zasu karasa ida ginasa da yardar Allah, akullum a kuma koda yaushe yana alfahari dasu, Tabbas ako ina zaiyi al'faharin cewa.
Yay’an nasa jajirtattune kuma masu k’wazo, Lallai watarana Tabbas zasu cimmawa abunda suke so yana jin gamsuwa mai tarin yawa na riƙo da amarsu da Allah ya bashi da basu gamsasshiyar tarbiya.
Jin da yayi hirar tasu ta tsaya ne kuma, yasashi Kallon Rayyern tare da cewa.
“Rayyan ya tafiyar taka? Ina fata ansamu abunda akeso ko!?.”
Kai Rayyern d’in ya jinjina tare da bud’e bakinsa anutse yace.
“Alhamdulillah Abba, duk wani abu da muke nema na samu, dama kayan amfanin companies dinmu ne naje sayawo, to kuma ba abunda ban samu ba, nayi ordering Insha Allah kuma soon zasu sauk’a nan Nigeria.”
Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwa, kana yace.
“To kaida kaje US kuma sai gaka a ethiopia’n harda karb’an wani kambun karramawa.”
Murmushin daya bayyana fararen haƙoransa yayi, cikin kuma sakewa da mahaifinnasa yace.
“To Abba ai acikin Airport na hadu da yarannasu harna taimaka musu, shine fahimtar likitane Ni yasa dole aka wuce dani k’asarsu,
Jin dadin ceton ahlin masu muƙamin ƙasar ne yasa sukamin wannan karramawar.”
“Masha Allah Allah Ubangiji yaci gaba da taimakawa.”
Abba da Mamy suka had’a baki wajen fad’ar hakan.
Ramadan kuwa daya kammala cin abincinsa, mik’ewa tsaye yayi tare da d’aukan wayarsa dake kan table d’in, cikin kuma yanayin nuna kulawa ga Hamman nasa yace.
“Yauwa Hamma Rayyern bari na amso maka maganin rage zogin ciwo acikin pharmacy d’inmu.”
Kai kawai Rayyern din ya jinjina, Yayinda shi kuma Ramadan yasa kai ya fice daga cikin falon.
Koda ya fito daga cikin gidan nasu direct Mai-Nasara’s Pharmacy Nig LTD ya nufa, kasancewar kuma pharmacy din bashi da wani nisa da gidansu, hakan yasa bai wani b’ata lokaci ba ya dawo.
Shida kansa ya d’auko bottle water marar sanyi, tare da b’are maganin ya bawa Hamman nasa yasha.
Bayan Rayyern din yasha maganin ne kuma, ya mik’e tsaye ahankali tare da kallon su Abban nasa, aladabce yace .
“Abba ni zanje na kwanta, dan inajin gajiya sosai ajikina.”
Kai Abba ya jinjina masa tare da cewa.
“To Allah ya tashemu lafiya.”
Da “Ameen.” Ya amsa kafun yayiwa Mamy da Ramadan saida safe, kana kaitsaye ya nufi sashinsa, da k’ofar shiga cikinta ke Cikin babban falon a nitse yake tattaki bisa steps ɗin haurawa saman.
Ahankali ya murd’a handle d’in had’add’Iyar k’ofar, tare da tura kansa ciki.
Wani irin sassanyan k’amshin room freshener daya shak’ane kuma yasashi lumshe idanunsa, wanda suke d’auke da wani yanayi na musamman.
Tabbas shi mutum ne maitsanin son k’amshi, wannan yasa aduk sanda yaji k’amshi sai zuciyarsa tayi sanyi.
Ahankali ya bud’e idanun nasa, tare da soma bin kekyawan falon da kyawunsa ya zarce tunanin mutum da kallo.
Duk da kuwa cewar babu yawan tarkace acikin falon, amma yanayin tsarin falon da kuma kayan dake cikinsa, na millions din kud’i ne ya ƙawatashi.
Domin kuwa acikin falon wasu irin had’add’un Roma complete sofa’s ne masu masifar kyau da tsada, wanda sukayiwa tsakiyar falon k’awanya, Yayinda aka cika samansu da wasu irin trow pillows new design, babban abu mafi d’aukar hankali ajikin sofas din kuwa shine, yanda aka k’awata su da wani irin abu mai kaman royal glasses, da kuma ado na musamman, kasantuwar design din Golding ash ne kuma, yasa har wani d’auke ido adon sofas d’in keyi.
Yayinda daga k’asan sofas din kuwa aka shumfud’e wani had’add’en Ash colour Austin carpet, mai tsananin taushi da laushi, domin kuwa saboda tsabar laushin carpet d’in, har k’afan mutum kan iya nutsewa idan ya taka.
Yayinda aka d’aura wani had’add’en glass Roma table akan tsakiyar carpet d’in, wanda kuma shine ya k’ara k’awata kyau da had’uwar falon, musamman wasu beautiful roses masu kalan gold da aka d’aura asamansa.
Acan b’angaren dama kuwa, wani irin makeken tv plasma ne black na companyn Samsung mai matuk’ar kyau da tsada, saboda tsabar girman TV din kuwa, ba a iya mannashi a bango ba, kan wani had’add’en Royal tv stand aka ajiyesa, daga gefe da gefensa kuwa aka zuba wasu glass roses masu kyau da tsada, wanda da zaran dare ya rufa suda kansu, suke bada deference colours na light.
Still kuma had’add’un dark and golding ash colour, plain curtains d’in dake sak’ale jikin kowacce door da kuma windows d’in dake cikin falonne, suka k’ara bayyana had’uwar falon, domin kuwa curtains ne masu shegen tsada da aminci, wanda aka k’awata su da had’add’en decoration na d’aukar hankali, Tabbas ko daga iya curtains d’in dake cikin falon ka tsaya, kasan an kashe matuk’ar kud’i, balle kuma aje ga kwalliyar wallpaper din, da akayiwa gaba d’aya jikin bangon falon da ako ina zai amsa sunansa falo.
Har lau kuma acikin falon nasa tafiya kad’an zakayi, ka iske wani had’add’en dining area’n da aka k’awatasa da decoration na classic curtains masu kalan grey, sai zazzafan Angel dining table mai d’auke da 6chairs, grey da kuma gray colours, Tabbas ko a iya wajen falon Rayyern ya amsa suna, ya kuma cika hamshak’in falon dake dauke da tsadaddun furnitures.
Daga gefen dining area din kuwa wata koface, wanda da’alama kuma nanne kitchine d’insa.
Sai kuma wasu kofofi guda biyu dake cikin falon, 2 bedrooms wanda kitchen and dining area ke tsakiyarsu.
Sassanyar ajiyar zuciya ya sauk’e a dai-dai lokacin da ya gama, k’arewa had’add’en falonnasa kallo, komai nead babu wani alama ma dake nuna cewar, yakai 4 to 5 weeks baya cikin dakin, kasancewar duk kwanan duniya Ramadan na shigowa yana gyara duk abunda ya d’anyi kura.
Rigar suit d’in dake jikinsa ya zare ahankali, tare da ajiyeta akan sofa, ahankali cikin takun dake bayyana gajiyarsa ya nufi d’aya, daga cikin 2 door d’innan da suke d’an nesa da juna.
Sauk’e hannunsa akan k’ofar dake b’angaren dama’nsa yayi, wacce takasance itace bedroom d’insa.
Koda ya tura kansa acikin dakin kuwa, wani daddad’an kamshi da kuma sanyin AC ne ya bugeshi, still ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa, musamman da yaga yanda aka k’awata, original royal bed d’insa da soft bedsheet mai kyau.
Kamar dai yanda yaga falon nasa nead, haka ma komai dake cikin dakin, babu wani abu na kushewa acikin bedroom d’in, saboda nan ma wasu royal furnitures ne aciki masu masifar kyau, tamkar dai agidan sarauta haka d’akin nasa yake, saboda komai kama daga kan bed, drawer, dressing mirror, gothic chairs duk masu kalan gold ne, sai kuma curtains din cikin dakin da suka kasance milk colour.
D’an sunkuyawa yayi ahankali ya zare takalman dake k’afarsa, batare kuma daya jira komai ba, ya soma kokarin zare long sleeve din dake jikinsa, bayan ya cire rigar ne kuma, ya k’arasa gaban wani medium glass wardrobe, wanda acikinsu ne yake ajiye duk wasu abubuwan buk’atansa marassa nauyi, kama daga kan towel, bathrobe, short neakers, dadai sauransu.
Wani nead bathrobe ya d’auko tare da warwarewa ya zura ajikinsa, saida ya gama daure igiyoyin bathrobe din kuma, kafun ya zare wandon suit din dake jikinsa.
Kaitsaye bathroom d’insa ya wuce, Lallai ko acikin bathroom dinansa nasha kallo, domin kuwa hatta wajen da mutum zai tsaya yayi wanka na glass ne, daga cikin gurin kuma kana iya ganin komai na cikin toilet d’in, ga wani had’add’en jakuzzie mai daukar hankali wanda cikinsa, ke cike da tsabtataccen ruwa.
A yanayin yanda yakejin kansa a matuk’ar gajiye ne kuma, yasa bai wani bata lokaci wajen yin wankan nasa ba, bayan ya kammala wankanne kuma ya dauro alwala, kasancewar haka ya sabarwa kansa, baya tab’a kwanciya babu alwala.
Ahankali ya murda handle din bathroom din ya fito, hannunsa rik’e da wani towel, Yayinda gargasan jikinsa kuwa ke jik’e da ruwa, sunyi wani irin kwanciya lub, wanda kuma hakan shiya sake bayyana hasken fatarsa.
Cikin yanayin nutsuwar daya zamar masa sabo, ya tsane duk jikinsa, tare da karasawa gaban dressing mirror ya shafa mai ajikinsa, bayan ya kammala shafa maid’inne kuma, yabi jikinsa da wani men body spray mai kamshin gaske.
Yana kammala duk wani abu da zaiyi kuwa, ya k’arasa gaban wardrobe dinsa, tare da ciro wani sabon towel ya daura akan waist d’insa, yayi hakanne kuma saboda sometimes yafi jin dadin bacci, idan babu wani kaya mai nauyi ajikinsa, kamar dai towel yanajin dadin bacci da towel sosai.
Numfashi ya fesar adai-dai lokacin da yayi amfani da wani remote, wajen yin off na hasken wutan dake cikin dakin.
Anutse ya haura saman tattausan gadonsa, tare dakai hannunsa ya kunna two bedside lamp din dake gefen gadon.
Ai kuwa yana ajiye kansa akan pillow, yaji sautin kiran waya na tashi daga gefensa, hannunsa yasa yadan dafe kansa akasalance, saboda Allah Yasani kwata kwata at this time bayason damuwa. Idan ya gaji bacci kawai yake so yayi, domin da hakanne kawai zaiji he’s okay.
Kallonsa ya mayar ga inda Ramadan ya ajiye masa wayoyin nasa uku, wato samsung da kuma iphone d’insa wacce, mental problem dinnan ta dazu ta kwankwatsa masa da tsinin takalmin ta, wanda dududu yasan kudin takalmin nata bai wuce 10 to 12k ba, amma gashi tazo tayi masa asaran dubu daruruwa sai kuma yar karamar woyar.
Jawo wayoyinnasa yayi ahankali tare da ture iPhone d’in gefe, ya dauk’i Samsung S21 ultra din da take ta ringing, ganin sunan Sulaiman na yawo akan screen d’in wayarne kuma, yasa shi picking call d’in.
Koda ya amsa sallamar da Sulaiman din keyi masa kuwa shiru yayi, sai shi Sulaeman d’inne, daga can
b’angaren yace.
“Ya akayi nak’ikk’ira d’ayan layinka akashe, sai yanzu na samu wannan? Ykk fatan dai kana lapia, sarkin rainin hankali shine harda wani cemin ba yau zaka dawo ba, kai dai kam Rayyern naga randa zaka daina miskilanci.”
Idanunsa ya d’an lumshe, tare da sauke ajiyar zuciya, kana agajarce yace.
“What’s up ai gani nadawo ko?.”
Kai Sulaiman ya girgiza domin kuwa idan da sabo ya saba da halin Rayyern Mai-nasara.
“Nothing nakiraka na sanar dakai kada ka manta, gobe ne fa taron likitoti da za’ayi hope zaka je ai?.”
Sulaiman ya fad’a da kulawa.
“Insha Allah.” Still ya fada yana me gyara kwanciyarsa.
“Okay to saida safe kurman dole, mitsss mutun baya gajiya ma da shirun.”
Sulaiman ya fad’a yana me katse kiran.
Rayyern kuwa ahankali ya zare wayar daga kan kunnensa, tare da fesar da wani irin numfashi.
"Ashyhhhhh". wanda kuma yayi hakanne saboda zogi da yakejin yatsar k’afarsa nayi masa, duk da kuwa yasha magani, amma dai har yanzu yakanji k’afar nad’anyi masa zogi.
Labb’an bakinsa ya cije da d’an k’arfi tare da rumtse idanunsa, lokaci daya ya soma tuna yanda yarinyar tayi masa babban b’arna, kuma wai dan saboda tsabar raini, ko hakuri ta kasa basa dan girman kai, sai wuki-wuki da ta soma yi masa da mayun idanunta.
“Mchewww.” Yayi tsuka abayyane tare da cewa.
“Da wani dan bakinta kaman na tsuntsu, dama irin wayannan ƴan yaran. Sam ba kai daya garesu ba.”
Yakai karshen maganan yana sake gyara kwanciyarsa, tare da sakin kowanni irin tunani ya kama ambaton sunan Allah Acikin ransa, da haka bacci ya d’auke sa, yau ko samun daman duba system d’inshi baiyi ba.
Taheer Quest Palace.
Riyyam-Nsra ne kwance akan makeken bed din dake cikin d’akin hotel d’in daya kama.
12:30 am kenan amma har yanzu wayarsa kirar iphone 11pro ne ke rik’e ahannunsa, Yayinda yayi kwanciyar nan irinta rub da ciki, gaba d’aya hankali, tunani da kuma nutsuwarsa ya badasu ne ga wayar tasa, Inda yake ta receiving DM da kuma comments na mutane, akan videos d’in daya sake d’azu na shigowarsa Nigeria, inda mutane da yawa kanyi masa message akan cewar, suna matuk’ar son su had’u dashi, ciki kuwa harda y’an mata masu tambayarsa awanni masauk’i yake, domin acewarsu zasu kawo masa ziyara, burin mutane da yawa shine su had’u dashi suyi videos, wasu kuwa zallan kyawunsa ne yake rud’arsu, wanda hakan yasa suke bayyana maitarsu afili, ko kunyar kai da addininsu basaji, amatsayinsu na musulmai, kuma yaya mata, wanda kowa yasani Mace nada matuk’ar daraja, amma Ina wasu matan kam haka suke watsar da kansu kamar shara a bola.
Shikuwa Riyyam nsra ayau ya sake tabbatarwa da kansa cewar, mutanen Nigeria nada matuk’ar mutumci da kuma iya karrama bak’o, sannan da yawansu suna nuna masa k’auna k’warai.
Bayan ya gama amsa DM na mutane ne kuma yayi posting videos d’insa, wanda yayi musu shida Rayyern, Yayinda a k’asan videos d’in yayi godiya da irin karamcin da Rayyern d’in yayi masa, wayyo Allah ai kuwa kaman jira mutane suke, suna gama watching na videon ya fara samun new comments and DM, wanda shi kansu bazai iya amsasu duka ba, Yayinda mafi yawancin mata kuma suka sake haukacewa, nanfa kowacce ta fito ta fara maganganu kala-kala, harda masu tambayarsa wai dan Allah ko zai had’asu da kyakkyawan yayanshi.
Shidai ya gani amma baiyi reply ba.
Bakin shi ya dan zumbura gaba tare da cewa.
“Wayyo wannan Hamma Rayyern ɗin ya kashemin kasuwa fa, ji duk an shareni sai mgnarsa ake,”.
Ya kare mgnar da murmushi
Ana Cikin hakanne kuma saiga k’iran Nasir Ahmad ya shigo cikin wayar tasa.
Koda ya d’aga hira suka sha inda Nasir Ahmad ya dinga yi masa fadan cewa bai Kirasa ba, da kuma mai yasa zai sauka a hotel, saboda da ace yakirasa da bazai taba bari ya sauka a hotel ba.
Hakuri Riyyam din ya basa, daga nan kuma suka ci gaba da hirarsu, ananne Nasir din ke tambayan a Riyyam hotel din daya sauk’a, bayan ya fad’a masa cewa a Taheer ya sauk’a ne kuma sukayi sallama, inda Nasir din ya shaida masa cewar, Gobe Insha Allah zaizo nan Taheer Guest Palace din, ya d’aukesa su tafi gidansu...!
Uhummmmm, akwaifa abu a wanga littafin, fatana dai Allah ya bamu aron rai da lfy, mu gama lfy, amman kam ku shirya karatu da murmushi a fuskokinku🤝🏻🥰
0 comments:
Post a Comment