Kyakkyawar fuskarta ta kalla zuwa jikinta ta sauke ajiyar zuciya me qarfi sbd tausayin NURUn da Kamar rayuwarta ta raunane auren sa'ar mahaifinta bayan tanada Wanda takeso daidai ita sabon jini Amma yanzu gashi auren dattijo yahau kanta duk da MALEEK yawuce duk wani tsarin Imran nesa ba kusaba Dan kuwa Kota Ina Babu inda Imran yakamo maleek bayan qananun shekaru dazai nuna Masa Wanda shikansa maleek din kyau da hutu tareda wani irin iko da sarauta dake yawo a jininsa suna boye manyancinsa matuqa sosai dan kuwa jikinsa kawai masu qananun shekarunma bazasu kaisa kyawun jikiba musamman dayake Yana geamin sosai haryanzu shiyasa jikinsa koyaushe Kamar na yara.
Ajiyar zuciya tasake saukewa tareda cire wannan tunanin aranta Dan kuwa ita yanzu tariga ta cire kanta acikin maganar komaima Dan kuwa ko lokacinda take muradin raba auren nasu bataga ta inda zata faraba dama fatanta idan mum tadawo dad zai sawwaqewa NURUn sbd wadda zuciyarsa keso tadawo to Amma ita ta ina take gano yiyuwar saki arayuwar dad dinsu Wanda ko rabuwarsa da mum haryanxu duniya Bata gama saniba bare yayi wani sakin.
Aje laptop dinta tayi gefe tareda Miqewa ta Sanya slippers ta fita zuwa kitchen Dan yin wani aikin duk da Bata iyaba Dan debewa Kai kewa batason tunanin komai yadawo Mata musamman na mum dinsu datake fatar shafewa ta manta gabaki daya.
Sai gab da magriba NURU ta farka daga baccin miqe tashiga toilet tayi fitsari da brush ta fito ganin bakowa a dakin tasan wani Abu sukeyi ta zame gajeran wandonta ta dauko wani dogo da zo har qasan gwiwanta ta fito riqeda wayarta tana duba wani email da aka turo Mata daga karatun court din dataje jiya tana dariyar mark din data samu ta nufo kicin dan tunda tafito yanayin qamshin datakeji tasan afiace a kitchen din.
Ganin uban aikin da afia din keyi tareda farhat da mum Sarah sai Fana dake tayawa yasata sakin dariya cikeda mamaki ta miqawa farhat wayarta tana cewa"
OMG meyake faruwa anan ne?
Cikin kanne dariya mum Sarah tace"
Princess na aikin abincin dinner ne.
Wani wargazajjen flat bread ta cire daga pan duk ya sauya kala sbd Kwan jikinsa duk ya kone afia tayi tana aje spoon din hannunta tace"
Alhmdlh na Gama waye zaiyi Mana testing?
Shiru kowa yayi NURU ta matsa tana sake kallon girke girken da mamaki da dariya akan fuskanta tace"
Nidai bana cikin 'yar dandanawa.
Farhat kuwa da sauri tayi bayan NURU tana cewa"
Nima bana ciki.
Kallon mum Sarah afia tayi da alamar ke fa??
Wani yawu mum Sarah ta hadiye tareda kallon Fana tace"
Saidai Fana kinsan Ni inada suga ba komai nakeciba musamman yau ya haye da yawa sugan.
Tana gama fadar hakan ta sulale ta fice daga kicin din.
Fana Kam ba damar wani zance ta matso ta diba komai daya bayan daya tana dandanawa harta Gama ta dago idonta na kallon qasa tace"
Komai yayi daidai ranki ya dade.
Da mamaki NURU ta kalli Fana daketa faman danne yunqurun amai dake taso Mata na abincin Amma ahaka sbd gudun batawa afia tace komai yayi.
Afia da kanta tajera komai a dining ta wuce tabarsu NURU ta kamawa Fana suka gyare kitchen din tsaf komai yakoma kaman ba'ayi aiki dashiba Fana ta wuce sashensu na ma'aikata NURU ta rufe koina na cikin ta fito ta nufi dakinsu tayi alwala tayi sallar magriba lokacin afia hartayi wanka ta shirya ta fito taje Tasha black tea kawai Takoma daki sbd karatu takeson yi.
Har akai ishai suna Palo suna kallon wani adventure film a Netflix daganan ta hadowa farhat _Rice Krispies_ har suka Gama suka koma daki sukai sallah sukai Shirin kwanciya Bata Bari dakin farhat ba Saida taga tayi bacci tukuna tabaro tadawo dakinsu har lokacin afia n karatu tazo ta zauna kusada ita itama tana duba wasu hardcover books na lauyoyi na _Michael Connelly THE BRASS VERDICT_
Karkata tunaninta yayi akan abincin da afia din ta dafa dake kan dining Wanda maleek zai iyaci yasa ta aje littafin hannunta tareda kallon afia da bacci bacci yafara fizgarta ta miqe ta fita Dan dauke abincin daga kan dining duk da tasan kilama ya shige zuwa yanzu.
Direct dining ta nufa ta kwashe kayan ta maida kitchen tana qoqarin barin kitchen din taji motsin bude kofar kicin din ta baya tayi saurin waiwayowa cikin sauri da Yar fargaba tace'
Waye??
Muryan mum Sarah taji daga bayanta ta kofar nata dakin tana cewa'
Fana ce zata shigo ta hadawa MALEEK tea yakira Yana buqatarsa yanzune kafin ya sauko.
Jin haka tasake ajiyar zuciya ta matsa jikin kofar tace"
Fana ki koma kawai zanyi masa.
Juyawa Fana tayi ta wuce itakuma ta juyo ta kalli mum Sarah tana cewa"
Tea kawai Koda wani Abu?
Tea kawai yace amma bansaniba ko Zaki hada Masa da wani abun.
Fara hada Masa tayi tareda dauko cake dinda tayi jiya ta jera masasu a plate ta dauko ganyen lemon daga fridge ta wanke tareda zuma ta hada tea din ta zube ta jero a tray ta fito mum Sarah na biyeda ita daukeda sauran kayan suna shiga dining room Yana shigowa itace agaba ta 'dan dago kadan cikin taushin murya tace"
Barka da fitowa.
Akaro na farko ya amsa gaisuwarta da "yawwa" Yana zaunawa kan dining ta ajiye tray din hannunta ta matso kusadashi Dan zuba Masa qamshin turarenta na _Black Opium_ ya bugo Masa cikin hanci ya dago ahankali ya kalleta
Jin idanuwansa akanta yasa ta dakatawa tana Dan juyowa suka hada ido ta sauke nata tana juyowa da sauri ta kalli mum Sarah dake gurin tun kan ta Gama juyowa mum Sarah tayi saurin aje tray din tabar gurin tana soke kai ganin abinda yake neman fun karfin mamakinta.
Mum Sarah na wucewa ta juyo tana qarasa zuba Masa tareda jawo Masa cake din ta koma kitchen ta dauko ruwa ko zaisha ta ajiye tareda budewa ta zuba a cup.
Kasa wucewa tayi saida taga yagama tana daga kicin tana hangensa ya miqe ya wuce ta fito ta kwashe kayan ta maida ta nufi daki tana miqa sbd bacci takeji yanzu Kam.
Saidata shige ya kashe wutar palon farko yashigo ciki ya wuce sama.
Washe gari suna Shirin zuwa makaranta afia ta dauko zancen padima tafadawa NURUn tana qara cewa"
Inaga zaifi idan tazo Nan taga likita gaskia sbd Sam yanda nayi Mata tambayoyi da amsoshinta akwai rikitarwa bangane komaiba gskia sosai so inaga tazo taga likita zaifi.
Kallon bansan ta yayaba NURU tayiwa afia jikinta a sake tace"
Bansan ta inda zanfara bane,
Bansan ta gurinwa zan fara ba.
Kiyiwa jekadi bayanin komai da abinda kikeso ita zata isar Miki da saqonki koina dakomai saidai kawai kiga padima ankawota.
Shiru tayi hakanan tanajin wani iri kamar zata wuce guri idan tayi hakan Amma Kuma ceton 'yar uwartane zatayi tunda tanada damar yin hakan zatayi Inshallah.
Juyowa tayi ta kalli afia tace"
Thank you,zan yiwa jekadi magana idan na Isa makaranta inshallah.
Suna Isa makaranta takira jekadi saidata jira jekadi tagama gaisuwarta ta amsa cikin bawa jekadi nata girman itama kafin ta fadawa jekadi buqatarta tason akawo Mata 'yar uwarta padima tazo Mata ganin gida.
Ba musu jekadi tace"
Angama Inshallah MUSHRA,zanje yanzu na sanarwa Anneti ta sanarwa da MALEEK sai a aika gida ataho da ita Nan daganan sai akawo Miki ita har inda kikeso.
Koda jekadi ta isarda saqon NURU ga Anneti Bata musaba tace jekadi ta isarwa da MALEEK sakon aikuwa Kai tsaye shima ta isarda sakon a waya ta hanyar Mr Omar Wanda yace anbasu dama take washe gari aka aika aka taho da padima wadda Ta taho badan iyayensu sunso ba sai Dan saqon ta hanyar kaleeb ya iso musu.
Abal ya tabbatarwada padima duk yaji wani mugun labari yasamu NURU bashi ba ita har abada hakama ammi Kuma ahaka taji takuma amince saidai ta qudurta bazatayiwa NURU komaiba kodan kalaman iyayensu saidai bazata dawoba saitasamu nata rabon na ingantacciyar rayuwa ta taho tabar amed da mugun mamaki da baqin cikin daya kaisa Shan mugun qudurirrika akan ko zaiyi yawo tsirara bazata jimaba zaimata aikinda ko wata bazata rufaba acan saita dawo saidai Kuma wani tunanin daban yasashi Kiran mahaifinsa dake cikin amintaccin NEGES yafada Masa zuwan padima Wanda shima atake yafadawa NEGES.
Kallon jekadi Anneti tayi lokacinda take miqa Mata saqon NURU na wata sabuwar madarar raqumi da akaiwa Hadi da sinadarun Karin kyan fata Da wasu abubuwan ma tace"
Wannan sakon NURU ne da hannunki kullum Zaki ringa Bata tana shansa harya qare sbd na yanke shawaran kece Zaki Kai Mata 'yar uwarta ki zauna acan sai lokacinda tagama ziyararta kudawo tare sbd dalilai na Kare maleek da iyalansa duk da 'yar uwartane Amma bamusan Yaya halayenta sukeba musamman gashi ziyarar tazo a bazata.
Yanda kikace haka za'ayi Anneti.
Miqewa tayi ta fice Tana sake miqa gaisuwarta.
Tana fitowa duk da darene sosai saitaji tana buqatan zuwa ta duba lafiyar 'yar amanar NURU Dan kuwa tamkar amanartane NURU tabata Dan haka ta nufa sashen Kai tsaye.
Tun daga nesa taga kamar wutar sashen a kashe take sai abin yabata mamaki ta Dan dakata tareda dudduba sauran sassan duk hanyoyinsu wuta a kunne.
Daga can ciki kuwa gyara tsayuwa yakoob yayi Yana kallon padima dakewa tarin darhamai da danyen zinarai daya zube agabanta kallon haramun Kamar zata cinyesu abakinta yace"
Yaya Zaki iya kokuwa??
Hadiye wani yawu tayi tareda danne kwadayinta ta kallesa tsoronta na bayyanuwa tace"
Bazan iya kisaba wlh sbd ban iyaba bantabayiba.
Wani kallon Kai tsaye yayi Mata Yana sake zuba Mata wasu akan wainnan yace"
Ba kisa zakiyiba zuba Masa kawai Zakiyi a abunsha sauran aikin anan zamu qarashi,
Idan Kika cika wannan aikin akwai alqawari me girma na cikar buri da akai Miki alqawari daga shugabana haka zalika Kuma fitar maganar daidai take da bakin rayuwarki.
Wani kallon tsoro biyu tayi Masa kayan cikinta na juyawa sbd duk balainta batakai na kashe wani ba
Waninma maleek datake 'dan yiwa kanta kwadayinsa dukda tasan da wuya ita ko bashiba burinta dai gidan mulki
Yanxu ta Yaya zata iya kisa?.
Kuma aikinma batasan na ainihin wayeba tunda yadaice shugabansa bai fada ko wayeba.
Ciro wani qyalle yayi ya miqa Mata tareda cewa wannan ki warware gashinki ki dauresa aciki idan kinje can so daya kawai akeso ki juye Masa duka a abunsha kawai Banda abinci,
Idan kinzuba kiyi flushing din kyallen.
Miqa Mata yayi ya juya ya fice Yana cewa"
Sauran bayanin idan andawo Nan zakijisha.
Fitowa yayi fuskarsa rufe da kayan bayi Mata ya wuce batareda waiwayeba ya fice gabaki daya daga gurin.
Da mamaki jekadi tabi bayan baiwar data fito daga sassan Dan Haka ta qaraso da sauri tana sake duddubawa kafin ta nufa kofar Kai tsaye tashiga
padima dataji motsi tayi saurin boye darhaman tareda janyo abincinta da bataciba gabanta tareda zaunawa ta kishingida tareda rufe idanu har jekadin tashigo.
Da rashin yarda da mamaki jekadi ke kallon koina kafin ta kalli padima Kai tsaye tace"
Waye yafita yanxu daga Nan?
Bude idanuwa padima tayi tana ganin jekadi tayi saurin miqewa tareda russunawa tace"
Allah ya taimaki jekadin jekadai.
Sake maimaita tambayarta jekadi tayi tana kallon padiman har lokacin.
Cikin girmamawa tace"
Abincine takawo sbd dazu Koda aka kawo banajin dadin cikinq nace amaida zuwa anjima adawo dashi.
Kallon tsaf jekadi Tai Mata kafin tayiwa abincin da aka kawo din ta tako ahankali tana kallon abincin takai hannu ta bude tayi Masa kallon tsaf tareda Dan Kai hannunta a kaikaice taji dumin abincin Wanda baida dumi ko kadan ta dago ta kalli padiman kallon tsaf tasaki wani murmushin bazata dayasa padiman Dan washe Baki itama tace"
Saida safe ki huta lafiya"" ta juya ta fice batareda yiwa padima sauyiba ko alamar komai.
Tana fita padima ta sauke ajiyar zuciya tareda warware gashinta tasake gyarawa kullin zama cikin yalwataccen gashinta.
Ta zaro uwar dukiyar data boye tana tunanin inda zata kaita kafin tadawo.
Zagaye tafara cikin tsananin tsoro da firgici Dan ganinta da wannan darhaman masu tarin yawa zasu iya kaita lahira, gabaki daya tsoro da tashin hankali takeji wace masifar ce wannan daga zuwanta ko Paris din Bata qetaraba ta hadu da wannan balain yanxu idan taqi Yi ance abakin ranta,
Idan tafadawa wanima abakin ranta,hakama idantace zata tona tafada gskia batasan waye ya aikoba Dan aikenma fuskarsa rabi arufe babbar masifar datafisu shine idan ta aikata tayi kisan Kai ga Wanda tasan ko gunduwa gunduwan gawarta Kare suka samuci tayi arziki to ita Kam wane tashin hankali ne wannan.
Tana hada wani mugun zufa ta dauresu waje daya tareda cusawa cikin kayanta na sawa takoma gefe ta zauna har lokacin gumi take hadawa ta Nemo numbern amed sbd sanin shikadaine abokin cin mushenta na rayuwa.
Yana ganin kiranta yasaki ajiyar zuciya sbd abinda yake jira kenan Dan mahaifinsa ya fada Masa komai Dan shine yaje gurin padiman.
Dauka yayi cikin matsewa sbd har lokacin takaice yake da ita yace"
Lafiya dai ko Kira da wannan tsohon daren.
Wani wahalallen numfashi tasaki cikin qasa da murya tace"
Amed inason ganinka a Giza komai tsanani gobe Dan Allah.
Kallon mahaifinsa yayi sbd tun Rana ya iso Giza din yau shima sbd wannan tarkon nasu ya Dan sake Bata murya yace"
Sbd me zanzo kiranki?
Kinga karki rainamun da hankali Mana.
Cikin rawar murya tace"
Dan Allah amed kazo kokuma idan bazaka samu zuwa ba ka hadani da mahaifinka wlh Ina cikin wani mummunan tashin hankali ne na..... shiru tayi tana tuno maganar da Dan Aiken yafada Mata dazu hawayen cikin idonta suka gangaro Mata ta sauya zancen da cewa"
Akwai dukiyar NURU ce a hannuna inason baka ka Adana min harna dawo sbd bazan bataba batamasan da itaba.
Washe Baki yayi Kai tsaye Yana cewa"
Ganinan tafe yanzu kuwa.
Da mamaki tace" yanxu Kuma?
Kana gizah ne dama?
Da sauri yahau gyaran zancen da cewa"
Aa inanufin zan fadawa mahaifina zaishigo ya karba ta sirrance.
Bata yadda dashiba Dan taji gargada a zancensa Amma yanxu tunda tanason kubuta daga wannan saita ciro maganin da aka Bata ta Raba biyu ta bude gaban wata sarqar daham dake cikinsu tasaka dayake qaramine saiya shige ta maida Dan locket din ta rufe tana cewa"
Idan ta 'batarmin acan tareda zamuje qasa Dan ga shaida nan nasaka acikin kayan Kuma bazaka taba ganowaba.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖
_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
*_Mamuhgee 26_*
Washe gari sakayau taji ta Dan rage tashin hankalinta sbd ta rabu da dukiyar Dan hakanan taji Kamar jakadi Bata yarda da itaba ita yanxu data tabbatarda mutuwa ba abin Wasa bace data ji tafara Jin kamshinta zuwanta gizah sbd jiya harzuwama yanxu cikin matsanancin tashin hankali takejin kanta gabaki daya kusan Rabin zumudin tafiyar yabarta tsoro da shakkun abinda zai iya faruwa gaba shine yafi komai cikata yanxu gefe daya gasu abal tana Isa sukaji wani abun yafaru ayanda tasan abal dinsu dakansa zai iya bada shedar kome yafaru itace...
Gyaran muryan jekadi ya dawo da ita zurfin tunanin data shiga ta dago ta kalleta jiki duk amace ta Dan rusuna ta gaidata
Jekadi ta amsa cikin sakewa tace"
Bismillah zamu wuce Inshallah.
Janyo Jakarta tayi suka fito daganan har sassan Anneti aka fara kaita ta gaidata cikin tsananin girmamawa da tsarguwa kafin suka fito bayan sun Isa gate na biyu Dana uku Saida aka bincike kayanta tsaf kafin suka fito main gate inda dakarun tsaro suke sunfi guda ashirin suka fice daga delah gizah zuwa airport manyan motocin tsaro biyu na bayansu har airport.
********
Yau tunda safe suka fice duk su dukansu sbd exams dasuka fara ayau din ga uwa uba ita NURU tana gama da ciwon Mara sama sama dam idan zatayi period kusan kowane wata saitayi ciwon Mara ga uwa uba Imran da kwanakin Nan tunaninsa yakasa barinta Jin cewar bayada lafiya sosai
Tausayinsa takeji har cikin zuciyarta saidai tasan matuqar ba afiace zataje ganinsaba tabita itadashi iyakaci addua.
Suna fitowa yau sbd sammako dasukayi cikin itace agaba tana gyara daurin kanta na scarf fari shikuma Yana fitowa daga geamin dinsa wasu qananun zufa dasuka fiffito Masa suna gangara daga fatarsa da tsantsinta ya hanasu zama ta dago ta kallesa wata irin mummunan kunya ta kamata tayi sauri dauke Kai kasa batasan lokacinda tace"
Gud morning ba.
Kallo daya tayi Mata daga sama zuwa qasa ta dauke kansa ya wuce Kamar bai lura dasuba afia dayake tasan halin dad dinta saitayi gaba sbd sanin jinin mulkin ya motsa akansu su 'yayansa.
NURU ma hakanan tabi bayan afia tana kashe wayarta suka fada mota suka wuce.
Sai yamma lis suka dawo Kai tsaye daki suka nufa kowa yayi wanka ko abincin kirki NURU bataciba sallah kawai tayi ta janyo laptop tareda wasu takardun tahau karatu afia ma libry ta wuce Dan ita tafi ganewa karatu acan.
Daqyar kowaccensu tayi sallar ishai sbd bacci da gajiya suka Dan sake tattaba karatun bacci yayi gaba da kowaccensu a inda take.
Sai cikin tsakiyar dare su padima suka iso Dan haka ko cikin main gidan ba'a Bari sunshigo ba sbd MALEEK na Nan Dan haka part din masu aiki suka sauka akan seda safe zasu Shiga cikin gidan.
Tunda safe sukuma su NURU suka wuce school sbd jiya bacci be barsu sunyi karatunba sosai shiyasa Koda safe dasu padima suka samu shigowa su NURU sun wuce aka sauketa dakin dake kusadana mum Sarah na jekadi ma Yana gefen nata saiya zama sun sanya dakinta tsakiya.
Kallon aljannar duniya takeyi hawaye na silalo Mata a fili tace"
Wannan wane irin masiface take bibiyata,
Amed Kaine ka cutatarda rayuwata wannan rabon ya subuce min.
Kallon dakin da aka sauketa tayi Wanda aka Kira Dana saukan baqi Wanda tasan har abada kila ko a mafarki bazata samu irinsa ba matuqar ba aikin da aka Bata tayiba dasukai Mata alqawarin cikar buri.
Shafa kanta tayi taji maganin na ciki ta sauke ajiyar zuciya tana bawa kanta qwarin gwiwan aikatawa.
Da wannan tunanin tayini tana kallon kanta a madubi sbd ko tsaron dake Nan gidan ba qarami bane tsaf zatayi ta bakin ranta ba duniyar ba lahirar Dan haka Dole Saida taka tsantsan.
Da yamma suna dawowa farhat tafara tarbonsu da gudunta tayi musu oyoyo tana sanardasu isowansu padima Wanda yasa NURU sakin wani qayataccen murmushi tana 'dan wartsakewa daga gajiyarta taqarasa ciki cikin farin ciki.
Jekadi ce tafara fitowa ta russuna cikin girmamawa tace"
Barka da dawowa ikon MALEEK na gizah.
Da murmushi ta matso tareda girmamawa itama tace"
Allah yaqarawa jekadi matsayi
Kun iso lafiya?
Ya kuka baro Anneti.
Murmushin ganinta cikin sabon sauyi jekadi tayi sbd lurada Kamar taqara Dan sakewa fiyeda da tace"
Anneti na miqo gaisuwarta gareki da sauran iyalan MALEEK gabaki daya.
Muna amsawa tace tana kallon kofar da padima ta fito fes hartayi wanka ta Sanya doguwar riga me Fadi sosai ta qarasa da Dan sauri suka rungume juna suna yare tana tambayarta su abal da ammi da meryam.
Duk suna lafiya ta amsa tana yiwa afia barka da dawowa cikin 'yar girmamawa.
Tareda padiman suka qarasa dakinsu sunata yare Wanda yasa afia keta Binsu da murmushin burgeta dasukai musamman NURU daketa nuna kulawa ga 'yar uwarta saitaji NURUn na sake Shiga ranta tace"
Baby am jealous fa.
Murmushi NURU tayi tana cewa"
Karki damu itafa tafiya zatayi tabar Miki NURU.
Padima da batasan me sukace ba farko sai Binsu take da ido kishinsu na sake ciketa musamman NURU da idan ta tuni asalinta.
Wanka sukai kowa ya shirya cikin qananun Kayan Shan iska suka baje karatu suna fira da padiman at the same time.
Har dare tana dakin suna first gida Dana ciwonta Wanda take ce musu ba laifi tanajin kaman tafara Jin sauki sbd wani magani da abal yabata.
Sai dare sosai NURU ta rakata har cikin dakinta suka zauna suna dasa sabuwar zancen gida Wanda duk yasake tadowa NURU kewar gida da iyayenta ita kuwa padima satar kallon tsadaddun kayan baccin dake jikinta takeyi Wanda itama anhadota da daya na sawar yau Amma saitakega kaman na NURUn sunfi kyau da tsada Wanda batasan cewa daga jikin NURUn ne.
Sai after 12 tafito daga dakin Takoma nasu ta kwanta tanajin farin cikin saduwa da 'yar uwarta.
Washe gari ma sammako sukayi sai yamma Amma ba sosaiba suka dawo zuwa lokacin farhat tadan fara sabawa da padima dake kokarin zama kamar yarinya itama tana Taya farhat din Wasa itadai jekadi idanuwanta na bude qyam akan komai dake wakana a gidan.
Kwata kwata su NURU basa zama sbd exams shiyasa Basu ma dauko maganar ciwon padima ba Bari sukai saisun Gama exams sunsamu lokacin kansu isashe tukuna itama padima Bata damuba Dan so take kadama su Gama exams din da wuri Dan kada a tado maganar tasamu ta aikata aikinta ta tattara Takoma Dan ita anan ko gurin zama Bata ganiba dan haryau datake batun cike sati biyu da zuwa Bata taba saka maleek a idontaba Dan haka gwara tayi wannan aikin Takoma can Giza kila nata rabon acan yake tunda anmata alqawari.
Kamar koyaushe yau gidan bakowa sai masu aiki sai ita saisu jekadi da mum Sarah datakewa laqabi da tsofin najadu.
Duk wata damar aikata aikinta Bata samuba tsanani da tsaron da ake bawa abincinsu yayi yawa shiyasa komai yafara cakude Mata musamman dataji jekadi tafara qyanqyasa zance komawarsu tunda sunyi sati biyu cikin na uku gashi ita Tama rasa uban hasarar metake idan Takoma ba wani sakamakon.
Yau da wuri NURU ta dawo sbd sauranta exam daya tagama hakama yau daya tayi Dan haka cikin walwala da gajiya take gashi tanason bawa padima lokaci su futa yawo takaita taga gari da 'yan siye siye duk da kusan so biyu suna futa da afia data samu interval na Wana biyu.
Wanka tayo ta fito sanyeda doguwar riga sukaci abincin cikin nishadi da walwala har akai magriba suka shige ciki Acan sukai sallah dakinsu suna sake fira daganan NURU ta dauko maganar ciwon padiman kafin tabata amsa ta dauko wani zancen ita padiman da haka suka kamo wani zancen har lokacin bacci yayi suka kwanta.
Washe gari NURU batada exams Dan haka suka shirya suka fita yawon shopping itada padima da farhat sai jekadi datake bayan NURU ko Nanda can Wanda yasa NURUn fara Dan tsarguwa Amma sbd kaunarta da jekadi Bata nunaba saima siyayya da akaiwa kowa suka dawo gida da yamma lis.
Kowa daki ya nufa yayi wanka da salloli kafin suka fito cin abincin dare gabaki dayansu.
Suna gamawa NURU tayi daki tasake yin wanka tareda Shirin bacci ta nufi dakin padima harzata Shiga mum Sarah ta qaraso gurinta tana cewa"
MALEEK na buqatan black lemon tea.
Fasa shiga tayi ta nufi kitchen tana cewa"
Ok mum Sarah ki tayani wanke ganyen lemon din Bari na dauko cake dinda nayi dazu da safe.
Padima najin haka ta fito tayo kitchen din tahau Taya NURU aikin suna Dan firantawa.
Saidata hada komai tafara daukan cake ta nufi dining tabar padima a kicin tadawo ta tararda padima na tayata juya tea din kafin ta qaraso ta karba jekadi tashigo kicin din NURU tace"
Yawwa nagode padima bari nadauko guri na juye.
Juye Masa tayi ta dauka takai dining daidai fitowarsa ya qaraso dining din ya zauna ta sulale ta bar gurin sbd kayan dake jikinta Koda ta isa kitchen padima Takoma daki jekadi ce kawai a tsaye tana Shan ruwa.
Bai wani Sha dayawaba sbd yau taste din ba Dadi Dan haka ya miqe yahaye sama.
Yana wucewa NURU tayi daki itama bayan tayiwa jekadi Saida safe.
Saida jekadi ta tabbatarda kowa ya shige tadawo dining room ta dauki cup dinda MALEEK Tasha tea tazuba kadan a hannunta ta shinshin taji bataji wani qamshinba dabann takoma kicin ta dauko wani cup ta zuba shayin takai bakinta tareda rintse ido ta kurba kadan
Take ta bude idanuwanta tana kallon cup din gabanta na Dan faduwa tasake kurba tea din take jikinta yafara sauyawa da yanayi kaman na zafi zafi kaikayi kaikayi tayi kicin da sauri ta Adana tea din ta fito zuwa lokacin yafara Jin kamar ana hura wuta me zafi cikin jikinta ta nufi hanyar dakinsu NURU da qyar tana dafe jikinta ta Isa kofar dakin tayi knocking so biyar ajere NURU dake korarin rufe laptop ta kwanta ta ajiye laptop din tana kallon kofa kafin ta taso sbd kada atada afia datai baccin gajiya.
Ganin jekadi cikin yanayin ba daidaiba yasata fitowa dakin gabaki daya tana rufewa tareda kallon jekadin cikin mamaki tace"
Lafiya kike jekadi?
Bakida lafiya ne?
Girgiza Kai tayi wani irin mummunan gumi dayafi kamada Ana sheka Mata ruwan zafi Dan har tsiyaya take ta bude Baki daqyar a Dan wahalce tace"
MALEEK....kije kidubo MALEEK....guba..gubar qona jini a tea.....
Arude NURU take kallon bakin jekadi kayan cikinta na juyawa tsabar kaduwa tace"
Guba...maleek kuma?....
Turata jekadi tayi tana cewa"
Kije da sauri kidubosa akwai matsala babba.
Juyawa tayi da gudu tana waiwayen jekadi akaro na farko tana hawa Daman MALEEK dukkanin jikinta na rawar tsoro da firgici itakuma jekadi Kai tsaye dakin padima ta Isa ta Sanya mukulli daga waje kafin tafada dakin mum Sarah tana fidda wani gurnani azaba da wahala.
Tana Shiga qaton palonsa na farko taga Kofa biyu daya ta palonsa na biyu daya ta dakin matarsa lailah Bata tsaya komaiba ta nufi wadda qafafunta suka jata zuwa ta bude da sauri ta fada nanma wani palon ne tana hango kofar Master bedroom dinsa ta nufa da gudu ta fada ko ganin gabanta sosai batayi.
Cak ta tsaya tsakiyar dakin sbd fitowarsa wanka kenan dagashi sai towel iya qugunsa dukkanin fatar jikinsa tayi jajir kamar anmasa duka da danqo
Hankalinta take yaqarasa hargitsewa tanabin jikinsa da kallon qafafuwanta na daukar rawar tashin hankalin ganin wannan mummunan al'amarin.
Sbd jininsa nada tsananin karfi yasa yake iya controlling tsananin azaba da radadin dayakeji na juyawa cikin jininsa ya dauke idonsa daga kallonta tareda juya Mata baya sbd rashin kayan jikinsa.
Ganin masifar tafi yawa abayansa yasa batasan lokacinda ta qaraso da guduba ta Dora duka tafin hannuwanta a tsakiyar bayansa Wanda yasa wata ajiyar zuciya me qarfi kufce Masa sbd wani sanyin saukin azabar dayaji
ya juyo gabaki daya Yana kallonta hannuwanta akan jikinsa ya lumshe fararen idanuwansa dasuka koma jajir yabudesu fes akanta.
Ba sha'awar mace yakejiba ko kadan sbd komaima bazai iyaba ayanxun sbd konuwa da tafasar dayakeji acikin jikinsa Amma haduwar jikinta da nasa ya raunana azaba da zafin dayake ji sosai
yasake ware idanuwansa akanta tareda matsowa cikin jikinta sosai tayi saurin kasa da ido zuciyarta na harbawa haryana iya gani ta saman kirjinta
Hannu 'daya yasa ya zagayota tareda matseta cikin jikinsa yasakejin wani sanyi yasake sauke ajiyar zuciya tareda Dan sassautawa yana kallon fuskarta daidai ta dago zuciyarta na harbawa da tsoro da firgici da komaima ta kallesa idanuwansa suka shiga cikin nata kusan atare suka sauke ajiyar zuciya
Ya dago hannunta ahankali Yana kallon fuskarta ya Dora kan botiran rigar baccinta
Ta maida idonuwanta ahankali ta rufe bugun zuciyarta na tsananin Tues tanaji Yana bude botiran rigar har qarshensu rigar ta zame a tsorace ta rungumesa sbd kirjinta dake bayyane qyam.
Atare suka sauke qaqqarfar ajiyar zuciya musamman shi dayaji sanyi na shigarsa ya rungumeta gabaki daya cikin jikinsa idanuwansa alumshe.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖
_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
*_Mamuhgee 27_*
Wani irin 'dumi taji Yana yawo cikin jikinta sbd akaro na farko arayuwarta da jikinta ya hadu Dana wani ba kayan komai ajikinta ga jikinsa da zafi Sosai sai qara manne jikinsu yakeyi Yana sassauke ajiyar zuciya ajere batasan lokacinda ta rufe idanuwanta ba tana sake shigewa jikinsa sosai sbd ganin kaman hakan na rage Masa Abinda yakeji,
Ahankali tazagaya da hannuwanta zuwa bayansa ta rungumesa da kyau take wani wawan jiri ya debesu su dukan ba shiri ya xebe kan makeken round royal bed din dake make da tsakiyar dakin shine a qasa itace a samansa ya lumshe idanuwansa tareda budesu daqyar ya kalleta yaga yanda idanuwanta sukai lahu alamar batada zabi sai nasa ya juyar da ita gefe ta kwance tareda sake shigewa jikinta ahankali Yana fidda wani boyayyan wahalallen numfashin tsananin azaba.
Ganin haka yasa hankalinta yatashi tasake rudewa ta qanqamesa cikin jikinta tana shafa bayansa da tafin hannuwanta ahankali ahankali tana karanto addua sbd batasan takamaimai mezatayiba ga jikinsa har lokacin da wani irin zafi.
Zameyi da sauri ta sauko gadon idanuwansa na rufe har lokacin ya dungule guri daya sbd azaba ta Sanya hannu ta zare wandon rigar baccinta tareda pant dinta cikin tashin hankali da sauri ta nufi toilet dinsa ta fada daqyar ta iya gane kan toilet din ta sakarwa kanta ruwan sanyi masu tsananin sanyi harsaida numfashinta yakusa daukewa sbd sanyi haka ta daure ta fito da sauri ta nufo gurinsa
Ya bude idanuwansa daqyar yayi Mata wani irin kallo yanajin 'yarinyar qarasashi kawai zatayi daga kwance kafin ya lumshe ido tashige cikin jikinsa sanyin jikinta na shigarsa yasake qanqameta Yana cusa kansa cikin wuyanta dake zuba qamshin turaren _Byredo_ ya sake Kai fuskarsa kan tata suna shaqar numfashin juna sosai ta bude fararen idanuwanta itama dasukai taushi ta kallesa shima ita yake kalla da nasa jajayen idanuwan tanajin hannuwansa na yawo jikinta Amma Bata iya motsawa sbd har lokacin cikin azabar ciwon yake Saida duk sanyin jikinta yashige nasa jikin itama jikinta yadauki dumin nasa yafara sauke ajiyar zuciya yanajin sauki saukin tsananin zafin dayakeji.
Tsit dakin yayi bayan sanyin AC daketa yawo a dakin Babu me motsi acikinsu musamman ita dake cikin jikinsa a nade numfashi ma ahankali take fitarwa sbd tsananin hali na kunya datakejin kanta aciki yanzu sbd ayanda taji yayi tsit tabbas sauqi yafara zuwar masa.
Tsawon lokaci suna ahaka Babu me motsi ahankali ta zame Yana jinta Amma bai motsaba ta tashi zaune ta gyara Masa rufa ta sauka gadon ahankali ta dauki kayan baccinta ta maida tareda dauke towel dinsa aqasa ta maida toilet tafito tasake taba jikinsa har lokacin da zafi Sosai sauqin kawai shine Yana iya daure ciwon yanzu Dan haka ta juya ta nufi kofa Dan zuwa gurin jekadi Koda akwai maganin daza'a bashi sbd tsananin zafin jikin yayi yawa idan Babu zata Kira Mr Omar yanxu cikin Daren nan yazo anema likita.
Saukowa tayi tana duba qaton agogon dake Palo daya nuna qarfe biyu da mintuna hudu ta nufa dakin jekadi Kai tsaye ta bude tashiga Bata gantaba.
Da mamaki cikin tsoro ta Isa kofar toilet din dakin cikin rashin nutsuwa takira sunanta harso biyar taji shiru a rikice ta bude bayin tana jefa idanuwanta ko Ina Amma bata ciki ko rufe kofofin bataiba ta fito da gudu tayi dakin mum Sarah tana bude kofar tayi saurin zaro ido tareda qarasowa cikin firgici tayo kan jekadi da jikinta haryafi na maleek yin jajir da daukar zafi ta dago arikice tace"
Mum Sarah kikawo ruwan sanyi sosai da towel da sauri.
Hannuwanta har rawa sukeyi tafara ragewa jekadi kayan jikinta tabarta daga ita sai shimi
Ta karbi towel din da mum Sarah ke miqo Mata yadau sanyi sosai sbd ruwan kankarane aka saka Masa ta ya6a Mata ajiki take sanyin yafara shigarta tafara jero ajiyar zuciya a wahalce.
Ganin hakan yasa NURU ta miqe da sauri kafafunta har rawa sukeyi ta nufi dakinsu kota kan afia dake kwance a qasa batabi ba ta zari wayarta ta fito sauri ta nufi dakin mum Sarah tana Nemo numbern Mr Omar dayake shima acikin mansion din yake Yana ganin kiranta ya tashi zaune sbd koyaushe a shirye yake kullum dare Baya wani dogon bacci sbd tsaro.
Cikin girmamawa ya dauka da cewa"
Barka da.....a yamutse ta katsesa da cewa"
Mr Omar maleek da jekadi sunci ko guba kokuma wani Abu daban kaga kawai kazo yanzu yanzu matsalan babbane, maleek... maleek..jikinsa duka yayi wani...
Ko rufe Baki batayiba taji buga kofarsa
Ta dago a tsorace ta kalli kofar palon zuciyarta na bugawa da qarfi sbd tsananin tsoro
Ta cikin wayar dake kunnenta har lokacin taji yace"
Nine abude kofar da sauri.
Da gudu ta qarasa kofar ta bude Masa dukkanin jikinta rawa yakeyi Bai dago ya kalletaba yace"
Zanduba jekadi ta jikinta zamu gano ko menene.
Da sauri tayi gaba tana cewa'
Zo zo zo kaduba suna cikin tsananin azaba,
Maleek ya....shiru tayi tana kaucewa ya qarasa gurin jekadi da sauri
Kallo daya yayi Mata yasan menene
Da sauri ya daga hannunsa daya yakai bakinta saikuma ya kasa tabbatarwa ta hakan ya dakata cikin tsananin tashin hankali yace"
Idan na tabbatar garin asirin Kona jinine Wanda zai.....
Cikin tsawar dabatasan Tai Masa ba tace"
Mekake jira ka tabbatar Mana maleek na can cikin irin halin kayi sauri kafada mana abinda za'ayi kokuma Akira Dr Damien kaduba kaga halinda suke ciki...
Sake sauke Kai yayi cikin Dan Jin nauyin zancen yace"
Bakinsu za'a laso aji idan da daci sosai.
Wani irin kallo Tai Masa itama cikin tsananin Jin zancen wani iri daga sama.
Ganin kallonda mum Sarah Tai Mata ta sauke Kai haka shima Mr Omar din yasata Shan jinin jikinta sbd hakan na nufin itace Dole zataje ta dandano musu na maleek tunda dai Babu me iya Shan na jekadi hakama maleek Dole sai ita Dan dama irin wannan masifar idan ta samu mutum Miji ko Mata ke lasa bakin idan Kuma yarone iyayensu idan tsofine yayansu.
Juyawa tayi da sauri ta fita ta nufi hanyar sama zuciyarta na bugawa a qarfafe sbd tsoro haka ta qarasa dakin har lokacin Yana kwance lullube idanuwansa arufe ganin hakan yasa ta qarasa da sauri ta haye gadon Bata tsaya wata wataba takai fuskarta dap da tasa zuciyarta na harbawa tasa hannuwanta biyu ta tallafo fuskarsa ta rufe idanuwanta ta Dora qaramin bakinta kan nashi ta zura harshenta cikin bakinsa ahankali ta laso sai alokacin ta bude fararen idanuwanta ta kallesa ga mamakinta saitaga idanuwansa a bude hancinta yake kallo.
Da sauri ta zabura tareda zare bakinta tana saukowa gadon dukkanin jikinta na rawa tayi kasa da kanta zatai mgn can qasan maqoshinsa ya bude Baki a wahalce yace"
Idan jekadi ce ko mr Omar kice abinda suke zargine Mr Omar yasan password na inda maganinsa yake
Daga haka ya maida idanuwansa ya rufe sbd azabar abinda yakeji cikin jikinsa
Da sauri ta juya daga dakin ta fice zuwa qasan har tana hada bene uku uku gurin saukowa ta iso dakin da sauri ta kalli Mr Omar muryarta na rawa tace"
Yace shine duk abinda kuke zargi din kayi sauri ka dauko antidote din yace kasan komai please please please hurry Mr Omar...
Cikin sauri sauri shima yace"
Ok ok Amma Dole saimun tabbatarda bakin nasa akwai "daci sbd ta hakan zansan idan yagamabin jininsa..
Rikicewa tayi tana rawar murya tace"
Eh"kawai sbd ita Bata wani gane daci acikin bakinsaba gabaki daya ta rude da wani irin dumi da qamshin _Vedshakti lemon mouth freshner_ data debo abakin nasa Dan haka bazata iya tantance komaiba.
Tashi Mr Omar yayi ya fice daga dakin da sauri haryana tuntube tabarsu cirko cirko a tsaye kowa kayan cikinsa na juyawa sbd fargaba.
Jin shiru shiru yasa NURU fitowa takalli agogo lokacin har qarfe uku da arbain tayi tafito Palo yafiso goma tana komawa dakin mum Sarah Jin take Kamar tayi Ari hauka ta dauko wayarta zata Danna Masa Kira sai gashi yashigo da gudu gudu ya miqa Mata Yana cewa"
Hada da ruwan zafi kikai Masa yasha inshallah zafin zai sauka gabaki daya bayan asuba saina Kira Dr Damien.,
Idan yasha zaiyi amai sosai karki basa komai bayan wannan sai bayan 2 hours.
Karba tayi tayi kicin mum Sarah na bayanta jikinta na wata irin rawa take dafa maganin harsaida mum Sarah ta matso cikin tausayi da damuwa itama tace"
Ki nutsu Inshallah maleek da jekadi Babu abinda zaisamesu.
Gyada Kai tayi kawai tana dauko cup cikin cups din MALEEK dake gurinsu daban ta zuba Masa ko a tray Bata tsaya dorawaba ta dauka ta fice da sauri tana cewa"
Mum Sarah ki zuba kiyi gaggawar bawa jekadi.
Tana Isa dakin ta ajiye cup din saidata qara sanyin AC kafin ta qaraso gadon ta aje cup din kan bedside ta kallesa tanajin nauyin yanda zata bashi sbd tagama fahimtar Dan idanuwansa na rufe bashine ke nufin Yana bacci ba.
Kafin tayi wani yunquri taga ya motsa tareda bude idanuwansa Yana tashi zaune batareda ya kalletaba ya miqa hannu daqyar
Dasauri ta dauko cup din ta matso ta miqa Masa tareda tsayawa akansa Kamar zata fasa kuka sbd Jin yanayin take har cikin ranta.
Kurbi daya yayi ya dakata sbd abinda yakeji ta matsosa sosai cikin kulawa da damuwa tace"
Yace duka za'a shanye.
Ko kallonta Bata samu damar yayiba yasake daga cup din yasha Yana rufe ido tareda shanyewa ya miqa Mata cup din da sauri Yana saukowa gadon ya nufi toilet yafara kelaya wani irin aman azaba Wanda yasata kasa hkr tabisa ciki idanuwanta na cikowa da ruwa musamman ganin Aman hadda jini sosai aciki ta rude tana dafa bayansa da har lokacin yake bayyane ba Kaya ajikinsa Dan abin kamar daurin Rai da dai towel dinsa har lokacin be kunce ba koya kunce akwai qaramin gajeran wando ajikinsa.
Saidayayi mugun amai sosai kafin taji take zafin jikinsa ya sauka gabaki daya ta zuba Masa ruwa ya wanke fuskarsa da bakinsa ta fito tabarsa aciki ta sake gyara Masa gadon da duk suka cukuikuye sbd rudewa ta dauki cup din ta fice daga dakin tun kafin yafito sbd ta lura tun cikin toilet din yadawo MALEEK dinsa.
Gurinsu jekadi ta Isa da sauri itama cikin sa'a ta tararda ta amaye komai gabaki daya ta shigo suka kamata tareda goggge Mata jiki suka kwantar da ita take baccin wuya ya dauketa sai alokacin dukkaninsu suka saki ajiyar zuciya me qarfi abinda takeji tokare a zuciyarta ya fada Mata ta dafe goshinta tana sake sakin jerin ajiyar zuciya kafin ta dago dmta kalli mum Sarah tace"
Menene yafaru bayan shigewata da daddaren?
Ajiyar zuciya mum Sarah tasaki tareda sauke Kai qasa cikin rashin sanin takamaimai na komai tace"
Bansaniba
Kawai dai abinda nasani shine jekadi tashigo dakina acikin wannan halin
Abu daya tace shine na jininta na quna.
Wani sabon numfashin takuma saukewa me zafi kafin ta bude Baki tace"
Shikenan zuwa da safe idan duk sunji sauki zamuji abinda ya samesu
Ki lura da ita Mr Omar zai Kira Dr bayan asuba.
Juyawa tayi ta fice jikinta a matuqar mace sai yanxu takejin tsamin jikin guje gujen dataitayi daga sama zuwa qasa ta nufi dakinsu ta fada kan gado tareda lumshe idanu tana godewa Allah dayasa komai ya tsaya nan Amma Kuma zuciyarta na Bata wani irin yanayi Mara Dadi na afkuwar al'amarin sbd idan har ciwon maleek ne kaman yanda yasaba to ita jekadi fa?
Gabaki dayama wannan ciwon wani babban abune na daban sbd azabar dasuka Shiga sai me qarfin jini ne kawai zai iya dauka dan kuwa taga tsananin azabar dasuka shiga musamman MALEEK.
Bude ido tayi ahankali tasake lumshewa har lokacin tanajin dumin jikinsa daya Shiga jikinta sbd ba qaramin full body contact suka samu ba Dan ita yacire rigarta shikuma dama Babu anasa jikin.
Saurin rintse ido tayi da qarfi tana cire tunanin cikin ranta ta gyara kwanciya Dan tasamu bacci ya Dan dauketa kafin asuba.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖
_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
*_Mamuhgee 28_*
Da asuba Saida afia ta tada ita sbd nannauyan baccin daya dauketa ta bude ido daqyar ta kalli afia kanta na wani irin sarawa sbd nauyi dayayi mata sbd rashin bacci da damuwar abinda yafaru cikin daren.
Tashi tayi daqyar ta nufi toilet tashiga tayo alwala tafito ta tsaya gefen afia ta tada tata sallar.
Suna idarwa afia ta ringa satar kallonta a kaikaice sbd duk wani motsin NURUn qamshin turaren dad dinta takeji ajikinta yana tashi.
Shiru tayi sbd batamasan mezatace ba Amma mamakinta anan Ina NURU ta hadu da qamshin?
Ta Yaya?
Ganin idan tayi magana Kamar ta muzanta NURUn ne yasata yin shiru ta Adana kalamanta tukuna.
Gari nafarayin haske NURU ta fito ta nufi dakin mum Sarah ta dubo jekadi har lokacin bacci takeyi saita fito ta nufi dakin padima ta tura tajisa arufe taga key din ajiki ta waje saita bude dakin tareda shiga har lokacin bacci padiman keyi ta qarasa bakin gadonta ta taba bargonta ahankali zata tasheta
Padiman tasaki wani razanannan ihu tana zabura zaune gumi duk yagama jiqata idanuwanta duk a waje take kallon fuskar NURU jikinta na Dan rawa ta sharce gumi tana saukowa daga gadon.
Da mamaki da tsoro NURU ke kallonta tace"
Lafiya padima?
Mafarki kikayine kike wannan ihun kina hada gumi haka?
Kasa kallonta padima tayi sbd har lokacin gumi takeyi cikin tsananin firgicin mummunan mafarkin datayi batareda ta waiwayo ba ta nufa hanyar toilet tana cewa"
Mafarki nayi sbd banyi addua ba na kwanta.
Bayanta NURU tabi da kallo cikin mamaki sosai kafin ta juya ta fice daga dakin ta nufi kitchen tana Danna Kiran Mr Omar.
Saidata tabbatarda ita kadaice a kicin din tace"
Gud morning Mr Omar.
Barka da tashi ranki ya dade"yafada daga can bangaren cikin girmamawa.
Shiru tayi cikin nazarin abinda zata fada Masa...shikuma Jin hakan sai ya gyara murya cikin nutsuwa da Bata tabbaci yace"
Dr Damien yazo ya duba MALEEK tun six harya wuce ma inshallah komai ya wuce.
Sake yin shiru tayi tana wani nazari kafin ta sauke ajiyar zuciya me sauti tace"
Mr menene wannan ciwon?
Shin kodai wani abun sukaci kokuma ya taba skin dinsu?
Tsit Mr Omar yayi Jin tambayar tata saidai baija shirun da tsayiba Dan kada ya Bata hope na zai amsa tambayar ya Dan sake gyara murya cikin Bata girma yace"
Ranki ya dade Inshallah allergy ne kawai Amma bana saka ran da...
Qin qarasawa yayi tareda dauko zancen itama jekadi kowane lokaci duk zasu farka lafiya Inshallah.
Ajiyar zuciya ta sauke zuciyarta na wasi wasin abinda yace na cewan allergies ne,
Wane irin allergy ne wannan me tsananin azaba.
Daga sama tajisa Yana qara saita murya yace"
Ranki ya dade idan na hali Dan Allah basai 'yayan MALEEK sunsan meya faruba,kowama Dan Allah kada yasani sai maleek ya tashi anji daga garesa shida jekadin.
To" kawai tace tana kashe wayar cikin 'yan tunane tunanen dasuke shigarta.
Kasa yin komai na breakfast tayi tabarwa Fana aikin ta wuce daki tashiga wanka tafito lokacin har afia tagama shirinta itama tahau shiri suna gamawa ko breakfast NURU batayiba afia ce kawai tayi suka wuce makaranta.
Tunda suka Isa NURU batada sukuni tunanin halinda yake ciki ya hadu da karatun exams dinta ya hargitsa Mata Kai har wani jiri jirin ciwon Kai takeji sauqinta dayane daga yau tagama exams dinta hutun gaske zatayi kafin sudawo hutu inshallah sbd tana tsananin buqatar hakan.
****
Qarfe goma Sha 'daya da mintuna shida maleek ya sauko ahankali yake tafiya cikin nutsuwa da kamewa Yana sanyeda jallabiya milk sai daukan ido takeyi sbd maiqo da laushin yadin jallabiyan.
Mr Omar dayake tsaye tuntuni Yana jiransa a palo yayi saurin sake sauke kansa cikin tsananin biyayya ya sake ja baya maleek ya wuce yabi bayansa cikin tsananin girmamawa yace"
Barka da fitowa MALEEK.
Allah yaqara lafiya da Nisan kwana tareda tabbataccen tsari da kariya.
Fitowa sukai suka nufi gym dinsa har lokacin Mr Omar na bayansa suna shiga a Dan qaramin palon dake ciki maleek ya zauna tareda Dan lumshe idanuwansa dasuke Dan nuna yayi rashin lafiya sbd sunyi haske sosai sun 'dan fada sai hakan yayi kaman yaqara Masa kyan fuska.
Cikin nutsuwa Mr Omar ya matso daga bayansa yace"
MALEEK garin meriz ne jekadi ta farka tun dazu nayi magana da ita a dakin littafai ta tabbarminda.......shiru yayi tareda sauke Kai.
Dagowa maleek yayi batareda ya kallesaba yace"
Uhum...
Sake gyara tsayuwa mr Omar yayi Yana Dan gyaran murya a raunane yace"
Jinin mushrah ce tayi wannan aikin.
Alokacin ya dago manyan idanuwansa dasuka koma fararensu tas ya dorawa Mr Omar dayayi saurin yin qasa da Kai Yana cewa"
Afuwa MALEEK Amma tabbacen zancen kenan na duba shayin da jekadin ta gabatarmin tareda tabbacin zancenta na cewa tun a gizah taga abin zargi atattare da jinin mushrah din.
Shiru dakin ya dauka tsit na tsawon lokaci maleek baice komaiba
Mr Omar Kuma jiran damar dazai cigaba da koro bayanin sauran zancen.
Ko motsi maleek yayi Mr Omar yasan manufarsa Dan haka shirun maleek din ya tabbar Masa da abinda zaiyi ya juya a nutse ya fita tsawon mintuna uku saigashi tareda jekadi da itakam ta zurma sosai ba laifi saidai jikinta lafiya kalau takejinsa Mr Omar ya rufe kofar ya qaraso yace"
MALEEK ayanda jekadi tayi bayani Babu sanin mushrah ko wani daga cikin ahalinsu gameda wannan aiki na 'yar uwarta,
Akwai banbancin halaye da ra'ayoyi me girma a tsakaninsu Wanda Kai tsaye zamuce hassada kokuma rashin wayo yasa wani daga cikin gizah yake amfani da ita batareda tasaniba.
Kallon jekadi maleek yayi cikin nutsuwa da kamewar murya yace"
Inawa jekadi ya jiki tareda barka da arzikin samun lafiya.
Cikin girmamawa me girma tace"
Godiya nake maleek hakama jekadi nayi maka sannu da jiki.
Maleek kaman yanda kasani Babu inda wannan aiki yafito sai a gizah Kuma kamar koyaushe dai zarginmu Yana yawone akan mutane da yawa musamman idan mukai la'akari da bincikenmu damuketa fama a dunkule na rasuwar mahaifinka,
Tsawon shekarun Nan Danayi a delah naqi barowa nayi bin duk wani diddiqin sirri Babu wani alamar acan ko wanenen me wannan garin na meriz yake Amma yau bayan shekaru masu tsayi garin yasake bayyana Wanda hakan na nufin garin meriz a cikin delah gizah yake.
A Daren ranar dazamu zo cikin dare Naga abin zargi a sassan baquwar mushrah Amma sbd na tabbatar nashiga najata da wani zancen Kuma tabbas hancina ya shaqi kusan qamshin meriz Amma sbd tabbatarwa naqi magana sbd tasamu damar zuwa dashi anan mu tabbatar da hujja saidai banyi zaton zatayi tsaurin aikata abinda aka aikota dinba ayimin afuwa MALEEK.
Kuma kaman yanda Mr Omar yafada hassadace me qarfi a tsananin padime da mushrah wadda ta samo asali daga cigaban aure da mushrah tasamu na MALEEK Kuma haryanzu mushrah batasan da wannan halayen na 'yar uwartaba Dan kuwa ko wannan zuwan nata inada tabbacin Babu alkhairi acikinsa sbd iyayensu takanas kaleeb yayi magana dasu bayan nayi Masa bayanin komai na ranar danaga mutum yafita daga sassanta Dan haka Ina me roqo da neman afuwan maleek akan kada yayi fushi da mushrah akan laifi mafi Muni da jininta ta aikata.
Tsit suka kumayi gabaki dayansu na tsawon lokaci maleek na nazartar abubuwa da dama acikin kansa wainda ba komai bane sai mutuwar mahaifinsa dayayi wato mutuwar azaba yanaji Yana gani duk da Yana yaro qarami lokacin Amma Yana iya tuno azabar dayaga mahaifinsa aciki,
Tun daga lokacin Basu sake ji ko ganin wani Abu daya danganci garin meriz ba sai yau sama da shekaru arbain kenan.
Tabbas zarginsu ya tabbata cewar a gizah kowanene yake Dan haka yanxu Kam aikinsu na gaske zai fara.
Dagowa yayi ya kalli Mr Omar dake jiran umarni ya maida idonuwansa kan jekadi Kai tsaye cikin kamewa yace"
Baza'a bari kowa yasan da zancenba ciki kuwa harda ita datayi aikin ki maidaita gizah idan tanacan ne za'a San waye shugaban aikin nata sbd na tabbatarda ita kanta nasan wa takewa aikiba sbd al'amarin me girmane bazasuyi saurin bayyanarda kansuba,
Amfanin wannan aikin na meriz da aka sata shine komawata gizah neman magani sbd sunyi tunanin acan ne kawai za'a samu maganin warkar Dani dagacan ne zasu qarasa niyarsu wadda baasantaba.
Gyada Kai jekadi tayi tace"
Kabar komai ahannuna kafin ka iso gizah Inshallah aikin yayi nisa
Inshallah sai Allah yacika nufin kaleeb Dan kuwa alqawarine sai anciyar da dabbobin gizah Naman duk Wanda ko da ido yataba ganin garin meriz bare ya taba.
Mr Omar ne ya matso yace"
Jekadi sai magana ta gaba itace umarnin maleek ne kada mushrah tasan abinda yafaru sai lokaci yayi hakama iyayenta
Duk abinda tayi idan lokaci yayi zatafada musu dakanta aranar qarshe da Babu gyara.
Gyada Kai jekadi tayi tana sake yiwa MALEEK fatar samun lafiya ta miqe ta fice.
Mr Omar kuwa gyara tsayuwa yayi yana sauke Kai yace"
Maleek meye ainihin wannan hukuncin na jinin mushrah da aka sanarwa jekadi.
Jininta ta aikata kuskure babba na cutatar da 'yar uwarta hassadarta tasa tasaka kanta cikin masifarda tun kafin mahaifinta yazama saurayi bare yayi auren haihuwarta.
Wayar kaleeb ya karba da Mr Omar ya miqo Masa bayan yagama yimasa bayanin komai dasuke ciki suka fara magana kowanne cikin kalar nasa ikon da kamewa ta sarautar dake jininsu kafin ya ajiye wayar.
Miqewa yayi tareda nufar kofa sai ya dakata ahankali batareda ya juyoba Kai tsaye yace"
Ka bawa jekadi muriz din damuke ajiya sbd bincike abisaga umarnin kaleeb kullum abata drop daya acikin abinsha ahaka har agama gano ainihin shugabanta duk tsanani kada abari asan muriz ake Bata sbd kaucewa basu alamar ansan dasu.
Cikin jinjina Kai Mr Omar yace"
Yanda kaleeb yace shine daidai.
Fitowa sukayi suka nufo ciki Koda suka shigo direct sama maleek ya wuce kasancewar NURU batanan hakama afia yasa jekadi da kanta ta tsare kitchen harsaida Fana tayiwa maleek din breakfast aka jere Masa Mr Omar Kuma na daga bakin kofar Palo shima ya kafa ya tsare.
Padima datake jiran Jin mugun labari na kuka ya faru agidan taji Babu komai batajin motsin kowa alamun lafiya Amma duk da hakan qin fitowa tayi tanajin hankalinta Sam be kwantaba gabaki daya gizah takeson komawa ta karbi dukiyarta da tukuicinta na aikin da aka sakata da dasa tata cin sabuwar duniyar.
Sai yamma sosai su NURU suka dawo cikin farin ciki da walwala suke duk su dukan sbd Gama exams dasukai.
Wanka nuru tafarayi ta Sanya blue pencil jeans da farar _Gaultier_ top me hannun shimi ta fito a kicinma taci abinci tanason mgn da jekadi Amma Sam jekadin taqi Bata dama qarshema ce Mata tayi allergy ne Kamar yanda Mr Omar yafada Mata.
Padima Saida NURU tadawo tafito suna fira sama sama Dan takasa sakewa Kai tsaye tacewa NURU gida zata koma.
Da mamaki NURU ta kalleta zatayi mgn jekadi ta qaraso cikin girmamawa ta kalli NURUn tace"
An kammala maganin maleek.
Da wani irin farin ciki me tsanani data danne padima ta juyo ta kalli jekadin tanajin dukkanin damuwarta ta yaye kenan yasha tea din boyewa suke baida lafiya kenan.
Miqewa NURU tayi tabar gurin tana cewa"
Padima Ina zuwa.
Murmushi me Fadi jekadi tasakarwa padime tana cewa"
Ki huta lafiya jinin mushrah.
Cikin farin ciki padime tace"
Yawwa.
Dama tanason sanin halinda yake ciki duk da tasan yanzu ko kallo bazata samu daga maleek dinba Amma tanason tabbatarwada yasamu lafiyar Dan haka ta dauki tray din ta fito kenan ta hadu da farhat tana cewa"
Aunt NURU abincin daddy ne wanna?
Gyada Mata Kai kawai NURU tayi tana cewa'
Bari na aje anan ki jirani na sanyo jallabiya saimu Kai Masa.
Jekadi dake fitowa daga kicin ta matso gaban NURUn a natse tace"
Abincin maleek ba'a barinsa ako Ina shiyasa ko jiya yasamu allergy.
Kallon kanta tayi taga shigar Sam Bata daceba da zuwa gurinsa zatai magana jekadi ta sauke Kai tana cewa"
Afito lafiya.
Numfashi me sanyi ta sauke tareda daukan tray din tana satar kallon hanyar dakunansu tafara hawa saman sbd kada afia ta fito.
Tana shiga palon farko ta tsaya kofar palonsa na kurya tana sauke ajiyar zuciya sbd gabanta dake faduwa ta kalli farhat data bude kofar Kai tsaye ta shige tayi gurinsa da gudu Yana zaune kan royal kushin yayi crossing fararen qafafuwansa da Babu takalmi sai daukan ido suke kaman baya taka kasa dasu.
Shigowa tayi qafafunta na Dan rawa ta qaraso ta ajiye tray din kan table tana dagowa maleek dinma na waiwayowa yayi Mata kallo daya ya juya sbd kayan dake jikinta.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖
_SAFIYYAH HUGUMA_
_BILLYN ABDULL_
_MISS XOXO_
_HAFSAT RANO_
_MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
*_Mamuhgee 29_*
_*YERWA INCENSE & MORE*_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: _*08095215215/09044191709*! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
**********
Harta Gama zuba Masa ta ajiye Bai Bai Kuma waiwayowa ba amfani yake da wayarsa sai farhat dayake tankawa ahankali,
Juyawa tayi zata fice batareda ya kalla inda take ba yace"
Kijira ki tafi da kayan.
Dakatawa tayi tareda sauke ajiyar zuciya boyayya sbd atlas dai yanuna yasan da shigowar mutum ba farhat kadaiba.
Juyowa tayi ahankali tadawo daga gefe ta tsaya tana Dora kallonta kan tv dake aiki Sam bama murya kusan gabaki daya Wanda ta fahimci qaidar iya muryar tv dayake buqatane ahakan.
Ganin tsayuwar Kamar zata damesa saita sulale ahankali Takoma palonsa na farko ta zauna tana kallon tsari da haduwar palon Wanda kusan komai na palon milk ne.
Juya idanuwanta tayi kan wani qaramin hoton LAILAH dake cikin qaramin milk frame tana tareda maleek din dukkaninsu cikin qananun Kaya black shi Yana zaune gabaki daya hankalinsa nakan wayar dake hannunsa itakuma ta rungumosa tana dariya fararen haqoranta tas a bayyane sunyi kyau.
Dokawa taji qirjinta yayi ta dauke kanta daga kallon hoton tareda Dan hadiye yawu tana qoqarin Wasa da yatsun hannunta.
Kasawa tayi tasake juyowa gabaki daya ta qurawa hoton ido tana qarewa LAILAH kallo.
Kyakkyawace da kyanta yake a bayyane,gata da kyawun jiki Kamar ba ita ta haifi afia ba Kamar dai yayarta,
Wayewarta ko acikin hoton a bayyane take sbd yanayin shigarta da yanda take nanuke ajikin MALEEK Wanda son datake Masa yake bayyane afili shima alamunsa da yanda hankalinsa ke kwance qarara a hoton ya bayyanarda soyayyarsa ga matarsa.
Sake dauke kallonta tayi daga hoton jikinta nayin sanyi bugun zuciyarta na qaruwa ta waiwaya gefenda kofar dakin lailah din saitaji jikinta na Gaza Mata ta miqe tabar gurin ta koma cikin palonsa wannan karon sallamarta daqyar ta fito qasan maqoshi sbd shaqewar dataji maqoshinta yayi.
Qarasowa tayi kanta a qasa ta dauki tray din ta fice batareda tabi takan farhat ba dasukazo tareba.
Tana saukowa kitchen takai kayan ta wanke da kanta ta maidasu gurinsu ta fito ta nufi daki batareda Takoma gurin padima ba.
Tana zuwa daki ta fada kan gado takwanta tareda rufe idanuwanta tana sauke ajiyar zuciyarda batasan Kota mececeba.
Har dare Bata sake fitowa daki ba Koda padima tazo ta tambayeta ce Mata kawai tayi kanta na ciwo hutu take buqata.
Padima Bata damu da hutun da NURUn tace tana buqataba ta zauna gefenta tareda kallonta Kai tsaye tace"
NURU inason zankoma gida Kuma cikin gaggawa sbd kwana biyun Nan inata mafarkai marasa Dadi na abal da ammi kaman dai da akwai babbar matsala Dan haka Ni inaga zankoma gurinsa kada ya zamto babuke akusa Babu Ni.
Tashi zaune NURU tayi tana kallonta da yanayi na damuwa tace"
Amma ai nayi waya da abal ko dazu Kuma banji alaman matsala ko wani damuwaba bayan haka meye amfanin zuwanki kema idan Baki ga likita ba akan Taki lafiyan.
Yamutsa fuska tayi tana cewa"
Kibar maganar nawa ciwon sbd bana tunanin zan tsaya ganin likita naji sauqinsa sosai Dan dama kila hadda damuwar rashinki akusa ne yasa abin yayi tsanani yanzu Dana zauna dake naji saukin komaima kawai damuwata anan iyayenmu ne kiyi tunani kema kinsan Koda damuwa abal bazai taba Bari kiganeba barema Koda na baro fa bayajin Dadi kwana biyu Yana fama da ciwon tari...
Da wata sabuwar damuwar NURU ta kalleta tana cewa"
Amma meyasa tun zuwanki Baki fadamun abal bayajin dadiba padima?
Kinga shine ya gargadeni akan kada na fada Miki Kuma ko yanzu kada kiyi Masa maganar Dan zaisan cewa nafada Miki
Nidai gida zankoma jibi kiyi Shirin duk abinda Zaki bani da Wanda Zaki karbomin daga MALEEK,
Ni bana wannan ba NURU meyesa nakeganin kaman ba zaman aureba kike a gidan nan??
Dan Babu wani alamari daya danganci aure danaga Yana faruwa dake.
Shiru NURU tayi tareda dagowa ta kalli padiman tsawon mintuna sbd batasan me zataceba tunda kusan gaskia padiman tafada, ta sauke numfashi tareda Miqewa tana cewa"
Kidaina wannan tambayar padima
Ba lallai komai ake bayyanawaba
Tunda dai akwai auren komaima ahankali za'ayi.
Miqewa padiman itama tayi tana cewa"
To dai iyayenki saisu daina dukan gaban 'yar so tana auren MALEEK na delah gizah Dan kar ayi zaton wuta a maqera ajita a masaqa.
Juyowa NURU tayi ta kalli padiman da manyan idanuwanta ta matso daf da ita harsuna shaqan juna tace"
Ko a kasuwa za'a jita ba ruwanki bane ki Kama bakinki kadaki fadawa su abal abinda zaisasu damuwa sbd padima ba ruwanki da abinda zai kawo musu bacin Rai ko damuwa.
Murmushi padima tasaki cikin isashiyar muryarta tace"
Kiji da matsalar gabanki ta zaman aikin gida da renon mijin wata Ni kibarni zanji dasu abal din naki idanma labarin yakaimusu wata Rana Dan yanxu banjin zanyi lokacin isar musu da wannan labarin inada nawa sabgogin kawai dai kishirya min komai nafada Miki gida zankoma.
Wucewa tayi ta fice daga dakin tabar NURU nabinta da kallon takaici takaici sbd halin padima dai haka yake tun suna yara saidai kwana biyun Nan datazo musu tayi tunanin tafara sauyawane shiyasa taketa kiyayewa sbd kada suyi halinsu agabansu afia subarwa kansu abin takaici.
Zaunawa tayi kan kujera tana furzar da numfashi tace"
Zanyiwa jekadi magana ta maidaki tun kafin mufara halin acikin gidan Nan tunda kinji kingani kinfasa neman lafiyar ai shikenan kije ko Dan lafiyar iyayenmu.
Da daddare har daki tasamu jekadi zata zauna jekadi tayi saurin miqewa tana cewa"
Ba girmanki bane mushrah idan kinason ganinane duk inda kike zan sameki naji bayaninki ko umarninki.
Murmushin yaqe kawai tayi sbd duk ranta a jagule yake yau din daga wannan sai wannan.
Daga tsayen ta kalli jekadi da taushin murya da zallar gajiya da damuwar komai tace"
Jekadi padima zata koma gida jibi nafadawa Mr Omar yayi muku komai na tafiyar,
Idan kunje kibata wadataccen kaso acikin wainnan dukiyar dake can na dukiyar auren......kasa karasawa tayi sbd Jin nauyin fadar kalmar aurenta
Itakuma jekadi Jin tayi shiru tace"
Yanda kikace haka za'ayi Inshallah"sbd ta fahimci abinda take fada.
Gobe ku shirya saimu fita akaiku kuyi siyayyar abinda kuke buqata.
Godiya jekadi keyi Allah yaqaro girma da kusanci tsakainki da MALEEK tareda tabbaciyar qauna.
Shiru tayi batareda tace komaiba saima sanyi da jikinta yayi ta juya zata fice jekadi tadago takalleta cikin tausayi da kaunarta saitaji bazata iyaba ta gyara tsayuwa tareda aje matsayinta na jekadi takira sunan NURUn cikin tsananin kulawa kaman yanda ta Saba a da.
Tsayawa NURUn tayi tareda waiwayowa ta juyo gaba daya damuwarta na raguwa sbd tasan jekadinta ta Da ce kafin tazama Matar maleek.
Takowa jekadi tayi tazo har gabanta takamo hannunta tajata zuwan kan kujera ta zaunar da ita kafin itama ta zauna ta fuskanceta cikin kulawa a natse tafara cewa"
NURU aure da kike gani Kona soyayyane saika dage da kulawa da naci akan wasu abubuwan sbd kusan a rayuwar aure ke mace kece zakija ragamar Kama hanyar zuwa wani mataki,
NURU kinshigo wata irin baudaddiyar rayuwar aure wadda kike buqatar juriyada kokartawa kafin kisamu matsayinki na Matar gida idan ba hakaba rayuwarki da quruciyarki zasu qare su tsufa cikin tausayi me tsanani,
Aure gidan sarauta musamman irin naki auren dayake da qalubalai da tazarori masu yawa,
Shawara daya anan itace ki maida hankali ki dage karki dage a Gina karatu kawai ki zauna kiyi nazari aurenkima kina buqatan dage Masa Dan bawa kanki suna da matsayi a gidanki sbd karki tsufa agidanki bakisan suna ko matsayinki a gurin Wanda kike aureba Dan kuwa wannan wata rayuwace da Kika shigo ba Babu fita sai mutuwa hakama akwai qalubalai agabanki Dan haka ki nutsu kiyi abinda yakamata kiyiwa kanki yaqi kema Dan tabbatarda zamanki acikin aurenki sbd auren MALEEK babban rabone agareki ki,
Kibude idanuwanki ki daina yadda da kowa da komai sai abinda zuciyarki ta nutsu dashi NURU.
Sai alokacin ta dago ta kalli jekadin jikinta duk yakuma yin sanyi ta bude baki ahankali tace"
Nagode jekadi.
Gyada Mata Kai jekadi tayi tana miqewa tace"
Ranki ya dade Zaki iya tafiya.
Miqewa tayi ta nufi kofa tana Jin gabaki daya gajiya takeji sbd sanyin da jikinta ketayi ayau din daga wannan sai wannan.
Dakin farhat ta wuce kawai sbd acan zata samu nutsuwa yanzu kawai
Tana shiga ta nufi toilet tayo alwala ta fito daidai shigowan farhat Nan suka shirya sukai sallah tare daganan tacewa farhat baccin awa biyu zasuyi kafin la'asar
Nan suka kwanta.
##MAMUH##
KUYI MANAGE.
0 comments:
Post a Comment