Tun dasukai magana da neges tasakawa jekadi ido sosai akan motsinta takai har bibiyarta tafarayi Amma sbd jekadin ta iya takunta fiyeda tunani lailan Bata taba samun damar sanin komai dangane da wani baqin yanayi ko sirri atareda jekadin ba harta fara sarewa daga bin daddaqin na jekadi sbd Sam ba dabiarta bace Dan ita ta dauki kanta tanada abinyi hakama ba girmanta bane tsayawa irin wainnan labe laben ga abun duniya yafara sakota gaba sbd yanzu rayuwarta ta wayi gari kowa baya tareda ita tun daga kan mijinta har yayanta su danginta ba'a magana sbd ta Jima da watsar dasu dama mahaifiyarta ta Dade da rasuwa mahaifintane kawai shima tsufa yacisa sosai har baya gane kowa sai anfada Masa wannan waye shiyasa batada lokacin kowa saina Gina rayuwarta sbd gidansu kaf kowa yazamo wani hamshaqan kansu duk da ita kadaice mace sai tana alaqanta kanta da matsayinsu suda suke maza bazata taba yadda itama ta zauna tana amfani da alfarmar wani ko sunansa so take ta Gina kanta da kanta ta yanda za'a fadeta da matsayin datake dashi badai da matsayin wani datake a qarqashinsaba shiyasa ta rufe ido ta watsar da 'yayanta da komai Amma yau ta wayi gari ko 'yan aiki batadasu sai guda biyu kacal da ganinsuma baqin ciki yake sanyata sbd Kamar Saida aka zabo wainda suka fi Muni da rashin kakkamtuwa aka Aiko matasu batada 'da,
batada miji, batada gidan kanta bare matsayin kanta ko sunan Wanda zatace a qarqashin alfarmarsa take batada Dan Haka gabaki daya yanzu Jin take kamar ta rasa nustuwa da tunaninta Bata iya tunanin komai kanta ya toshe zuciyarta bayan kwashe kwashen tunane tunanen duniya dasuka kusa haukatata Babu abinda takeyi tarasa wazata zauna dashi ko masifa tayi ta rage abinda takeji bare.
Tunanin 'yarta afia ne yafado Mata Rai take taji idanuwanta na neman cikowa da hawaye ta hadiye tana miqewa zuwa bakin window ko zataji sanyi sanyi Amma takasa Saida hawayen suka tsinke Mata ta zauna bakin windon tana fashewa da wani irin kuka Mara sauti tana buqatan mutum atareda ita Wanda zai dubeta ya saurari damuwarta.
Afia take tsananin buqata ayau din sbd ta Dan duk duniya yanzu 'yartace kawai me iya rarrashinta ta rungumeta ta saurari duk haukar dazata iya fada da wadda zata iyayima kaf duniya yanzu 'yartace kawai me iya Mata wannan bayan ita ko maleek tasan bazai taba kallonta da idon sauki Kona mutunciba
Dan Haka hankalinta yaqara tashi tana jinta cikin mummunan yanayi na baqin cikin rayuwarta da Kamar tayi hasara.
Ta Jima Yana boyayyan kukan daya Gama kumbura idanuwanta da fuskar datake masifar ji da ita sunyi jajir sunyi suntum duk da hakan bataji wani sauki ko sassaucin komaiba ta miqe ta nufi toilet jiki amace ba kwari ta wanko fuskarta tareda yowar alwala Dan ko wankan batada karfin Yi tafito ta goge fuskarta ta tayarda sallar ishai da akai tun dazu bayan tagama akaro na farko bayan tsawon lokaci yau ta daga hannu tana rokon Allah sassauci da mafita sbd ada ganin tagama samun komai na rayuwa yasa sallah data zama Dole kawai takeyi Amma adhkar da sauran adduoi gurin ubangiji basa gabanta sbd duk abinda takeso tagama samu.
Agurin take zaune tana tsiyayar hawaye ta gefen fuskarta batareda ta iya tashiba takai hannu ahankali ta dauki wayarta ta Nemo sunan afia akaro na farko bayan tsawon lokaci taji qaunar 'yayanta na dawo Mata sbd haryanzu tasan kome zata zama arayuwa 'yayantane kawai bazasu taba iya guduntaba musamman afia datake kaunarta fiyeda komai saidai takasa duba kaunar da yarinyar ke Mata sai yanzu take ganewa Dan kuwa a yanda takeji yanzu ko 'yayanta abata ta zauna dasu zataji saukin duhu da kuncin da zuciyarta ke ciki.
Numbern afia takira tayita ringing No answer harso biyar take jikinta yasakeyin sanyi hannuwanta sukai sanyi ta juyar da kanta ahankali tana kallon qasa kafin ta daga wayar ahankali ta shiga gurin saqo ta rubuta mata" _Kiyi hakuri afia_
Tura Mata tayi tareda ajiye wayar tana rufe idanuwanta zuciyarta na wani irin nauyi da kunci.
Jekadi jin tsarin na barin padima tareda tattalata tasamu lafiya amaida gida yasata sauya nata tsarin itama nabin umarninsa tafara bawa padima magani tareda kulawa da goge Mata fatarta data Gama konewa tana shafa Mata magani akai akai Wanda take padiman tafara dawowa hayyacinta Dan hartana Dan iya bude Baki Kuma tana iya zaunawa sai hakan yasaka jekadi sake bada himma sosai cikin kwana biyu padima tafara dawowa mutum sosai a ranar da padiman tafara iya bude Baki sbd tsananin farin ciki jekadi ta fita ta kebe tasake Kiran Mr Omar ta sanar dashi komai alokacin suna hanyar tahowa gizah suna cikin jirgi Amma Basu riga sun tashiba Dan Haka baida damar ganin maleek sbd Yana first class Dan haka yabari harsu Isa tukuna.
Dayake da daddare ne sosai jekadi ta fito tayi wayar adaidai lokacin lailah Tana zaune taji motsi me girma ta window din dakinta Kuma Kamar harma da mutum tagan gilmawarsa saita tashi zaune dakyau tana kallon windon zuciyarta na Dan harbawa Amma takasa riqewa ta miqe tsaye ta nufi windon tana Dan daga manyan dogayen labulayen windon saitaga kaman sake gilmawar mutum Kuma idan idonta ya gani kamar da kyau jekadi tagani.
Kallon hanyar tayi tana dawowa cikin dakinta zuciyarta na gargadarta da bin jekadin saidai Kuma wata zuciyar tana ingizata ga zuwan ta rintse ido tana komawa ta zauna saidai Kuma takasa nutsuwa tanason bin jekadin
Ta miqe da sauri tareda daukan wayarta ta fito sanyeda slippers tabi hanyar baya ta fice daga sassanta tabi inda jekadin tabi tana tafe tana waige waige har tayi Dan nisa saitakasa gane inda jekadin tabi tafara waigawa koina tana dubawa saikuma tsoro yashigeta ta juya da sauri zata juya saiga jekadi ta fito ta wata hanya tabi hanyar Nayan sassan maleek tana tafiya cikin nutsuwa sbd kada tabar qarar sawu.
Da fargaba da mamaki me tsanani take kallon jekadin tareda rintse idanu tabude mamakinta na neman komawa tsoro sbd kayan dake jikin jekadin bashine kayan data ganiba ajikin jekadin data wurga ta windontaba Kuma tabbas Bata Isa ace yanzu yanxu ta sauya kayanba.
Kodai idanuwanta ne ke Mata gizo kokuma wanine ya wurga ta windon ba jekadiba?
To idan wanine waye?
Meyasa yayi irin shigar jekadin?
Girgiza Kai tayi da sauri cikin tsananin tsoro dason tabbatarwa tabi bayan jekadin cikin sanda tana Nemo camerar wayarta tareda kashe hasken flashlight sbd idan ba tabbarwa tayi da wacece jekadin acikinsu hauka zata iya kamata Dan haka a sidade sidade tabi bayan jekadin tana waiwaye cikin tsananin tashin hankali sbd Jin kamar Kuma Ana binta itama san'da san'da abayanta.
Wata boyayyar kofar dataga jekadi ta fita yasata zare idanuwa cikin mamaki da tabbatarda zancen neges kenan dai da akwai wani Abu da maleek ke boyewa¿Aikuwa yau saitaga ko menene to Amma Kuma ta Yaya tunda jekadi rufe gurin zatayi..
Tunani tafara ta yanda zata samu Isa cikin dakin Kota halin qaqa taga abinda kila zai dawo da aurenta da maleek Dan Haka bazata Bari wannan damar ta wucetaba.
Waige waige tahau Yi cikin sauri Idonta ya fada kan wani qaton katako Wanda batama tsaya mamakin ganinsa a guri irin wannan ba ta dauka da sauri ta lallaba taqarasa bayan jekadi dake kokarin rufe kofar da mukullin ta waje bata tsaya wata wataba ta daga katakon ta buga Mata akai bada karfi ba sbd Jin bazata iya da qarfinba sbd kadata illatata sai kawai ta tureta gefe ta Fadi ta qarasa dakin da gudu ta tura kofar ta fada ciki tana dubawa.
Faduwar da jekadi tayi ganin lailan ta nufi cikin da gudu yasata miqewa da sauri tana Kiran sunanta saidai kafin tayi wani yunkuri wani mummunan duka ya sauka akanta me tsananin azaba take ta sulale agurin ta zube a some jini na fita ta goshinta batareda taga Wanda yayi Mata dukan ba.
Lailah kuwa ganin mace a kwance cikin dakin cikin wani yanayi na Kamar majinyaci yasata takowa ahankali zuciyarta na harbawa cikin tsananin mamaki da tsoro ta iso har gabanta zata Kai hannu ta tabata padiman ta bude idanuwa ahankali baccin daya fara daukanta na sakinta ta zubawa lailah idanuwanta ahankali tana kallonta da mamaki Jin motsi abakin kofar shigowan yasa padima kallon bayan lailah mamakin ganinsa nasata kaikata Kai tana kallonsa dakyau ahankali ta bude Baki tace"
AMED????
Da sauri lailah ta juya zata waiwaya wani mugun duka ya sauka a tsakiyar kanta batareda ta waiwayo ba ta yanke jiki ta Fadi agurin sama sama tanajin padiman nasake maimaita amed har idanuwanta suka rufe numfashinta na daukewa.
******
Ruwan sanyin dake sauka kan fuskarta zuwa jikinta masu tsananin sanyi ya sanyata fara numfasawa tana motsa idanuwanta dasukai tsananin nauyi tafara budesu ahankali ahankali tana rufewa tana budewa sbd hasken dayayi Mata yawa harta budesu duka suka sauka kan mutanen dake zagaye da ita tafara Binsu da ido daya bayan daya kafin ta tsayar dasu akan fuskar maleek da yayi Mata kallo daya ya dauke Kai
Ta juyar da kanta gefe taga manyan jami'an tsaro tsatsaye agurin take ta zabura da sauri tana miqewa zaune tana sake kallon mutanen dake gurin ga qarin mamaki da firgicin ganin safiyace tas idanuwanta suka sauka kan mutum kwance miqe sambal anrufesa da farin kyalle har fuska Wanda ke nuni da gawar mutum ce,ta hadiye wani mugun yawu daga bakinta daya bushe kyam Nan take tana miqewa tsaye kanta na sarawa ta dafe kan tana Jin wani tashin hankali na shigarta sbd jekadi tasan tabari agurin jiyan da daddare bayan ta tureta, wani sabon tashin hankali da faduwar gaba me qarfi tashiga kardai wani Abu yasamu jekadi Dan dukan da turewar datai mata???
waiwaye waiwaye tafara tana neman rikicewa jikinta take yafara rawar tashin hankalinda Bata saka Masa ranaba ta nufi maleek da sauri tanajin ma ta wartsake daga ciwon da kanta keyi me tsanani ko gabanta Bata gani saidata Isa gaban maleek zatayi mgna idanuwanta suka sauka gefensa daya da jekadi ke tsaye sunkuye da Kai goshinta duk jini daga gani itama tana cikin tsananin tashin hankali
A haukace lailah ta waiwaya ta kalli gawar dake rufe agurin taji qafafunta na sagewa tayi baya zata Fadi macen dake sanye cikin uniform na hukumar qasar ta tareta tana riqeta dakyau da alamar dama ita ake jira.
Ta fizgo da qarfi tana kallon maleek bakinta na rawa cikin tsananin tashin hankali tace"
Wanene???
Me yake faruwa anan?
Kallo daya yayi Mata ya juya yana sauke siririn numfashi sbd gabaki daya al'amarin ya sauya acikin qanqanin lokacinda basuyi zatoba.
Kallon gawar padima yayi akaro na hudu Yana tunanin yanda 'yar uwarta zata iya handling wannan mummunan al'amarin Sam an shammacesa a guri mafi mufi Dan kuwa yanzu acikin jekadi da lailah baisan wazai fara wankewaba duk da dukkanin shedu lailah suka nuna ita tayi kisan sbd baro baro jakadi ta fada cewar lailah ce tazo ta bugeta ta Suma itama lailan ta nuna hakan ta Yaya za'a fitarda lailah daga wannan ta bangare daya ta Yaya NURU zataji wannan mummunan labarin?
##MAMUH#
Kasa hakuri lailah tayi cikin sabuwar qaramar haukar dake Shirin kamata agurin take tafara kwacewa tana kallon maleek da sauran mutanen dake gurin cikin tsananin ihun dukkanin jikinta na rawa take cewa"
Meyasa zaku tafi Dani?
Bani nakashetaba wlh,
Dan Allah ki tsaya nayi muku bayanin abinda yafaru wlh tallahi bani bace
Dan girman Allah maleek kace su barni kasan bazan taba iya aikata wannan mummunan abin ba
Ba halina bane,
Dan Allah ki sakeni wallahi bani bace ku tambayi jekadi Dan Allah maleek karka Bari su tafi Dani....
Tana ihun tashin hankali dukkanin jikinta Babu inda baya wani irin mazarin tashin hankali da ficewa hayyaci musamman data tabbatarda tabbas kisa akai Kuma itace ake nufin tayi kisar kenan kasheta za'ayi itama tabar duniya da 'yayanta
Tunanin hakan ke saka haukatarda kwanyarta tafara fizgewa tana kokarin zuwa gurin maleek dake tsaye batareda ya dago ya kalletaba sbd kunyar hakan da baqin cikin hakan dake cinsa koba komai ita din uwar 'yayansace matarsa ta farko wadda koman lalacewarta za'a kirata da matarsa ta farko har qarshen rayuwarsu.
Dayake har bakin kofar sassansa qatuwar baqar motar jami'an tsaron take suna Isa aka sanyata aka rufe tana wani irin kuka da neman ceto daga maleek tana rantsuwar ba ita din bace har muryarta tafara dishewa musamman daya zamto kallon karshene takewa koina Dan tasan hukun kisarta bazai dauki delay ba tunda komai a bayyane yake tasake sakin wani mahaukacin kuka tana buga kanta da tint windon motar da qarfi tana kuka tana Kiran sunan maleek cikin dukkanin bada imaninta ga shikadaine zai iya cetonta
Haka aka janyo jekadi itama aka saka cikin motar aka rufe Kafin
Ja motar suka wuce sai alokacin maleek ya dago ya kalli Mr Omar dake tsaye a gefe tsaye kansa sunkuye cikin yanayi na tsananin jimami idanuwansa suka kada sukai jajir ya dago Yana kallo 'yan motar asibitin dasuka Kira suka matso Dan daukar gawar su wuce da ita saiga shelar sanrwar tahowar NEGES da kansa zuwa sassan Dan tuni abinda yafaru ya karade gizah saidai Babu Wanda yasamu iko ko damar shigowa sassan hakama Babu Wanda yasamu masaniyar shin wanene aka kashen daga jami'an tsaron da Mr Omar yakira sai motar asibitin da jami'an tsaron sukazo dasu Dan daukan gawar sai Anneti data iso sassan cikin tsananin tashin hankali tana zubda hawayen ganin wannan mummunar qaddararriyar ranar ace kisa acikin gizah Kuma daga sassan maleek qari da Dadi tsohuwar matarsa da jekadinsace cikinsu daya ya aikata wannan mummunan Abu me duniya zatayiwa MALEEK kallo?
Gashi Anki bude gawar bare asan wanene aka kashen.
Neges na zuwa cikin tsananin jimami da tashin hankalin wannan mummunan al'amarin ya kalli MALEEK Yana bayyanarda damuwarsa da rashin Jin dadinsa akan al'amarin yace"
Ina me jajanta maka wannan al'amari
Saidai nayi maka alqawarin hukunta duk Wanda aka tabbatarda shine yayi kisan a tsakaninsu biyun Dan kuwa wannan al'amari babbane dazai iya tana darajarmu gabaki daya da ikonmu Dan Haka komai zai tafi abisaga adalci da doka wannan alqawarinane.
Sai alokacin maleek ya dago ya kallesa da idanuwansa dake bayyanarda zallar bacin Rai da wani irin zafi na iko da mulki dake yawo jininsa ahankali ya bude Baki cikin kamewa yace"
Godiya maleek yake Kuma Ina fatar zaka tuna wannan alqawarin naka Dan cikakkene jinin delas basa alwawarinda basa cikawa Ni nayi maka alqawarin tayaka cika wannan alqawarin za'a tafiyar da komai bisaga adalci da doka.
Jinjina Kai neges yayi Yana danne abinda yakeji gameda maleek din ya sassauta kallonsa zuwaga gawar da aka dauka za'a shigar ambulance ya waiwaya ya kalli yakoob Yana cewa"
A tabbatarda gawar kafin su tafi da ita.
Matsowa Mr Omar yayi Ya tarewa yakoob hanzari Yana sauke Kai cikin tsananin girmamawa ga neges Yana sassauta harshe da cewa"
Allah yaqarawa neges girma
Ina neman afuwar rashin barin abude gawa irin wannan agabanka sbd darajarka fifitacciyace dabazai yiyu irin wannan abudeta a gabanka sbd dukkanin suturarta a yage take Wanda ya nuna alamar Tasha dama da makashinta kafin samun nasararsa
Ni zanyi shedar tabbarda gawar aduk lokacinda buqatan hakan ta taso agurin Sharia.
Cikin jinjinawa yace"
Shikenan hakan yayi Allah ya kyauta Amma duk da hakan Ana buqatan tabbarwan.
Matsawa mr Omar yayi tareda bawa yakoob hanya ya wuce Dan ya tabbatar din saidai Yana Kai hannun zai bude jami'an tsaron dasuke jiran ambulance su tafi tare suka dakatar dashi cikin yanayi na dokar aikinsu da girmamawa ga neges shugaban yace"
Allah yaqarawa neges girma Babu Wanda zai sake taba gawar Nan ayanxu sbd Babu abinda mukai bincike akansa zamuje da gawar lab muduba komai ayi aune aune daga lokacin ne bayan angama komai zamu bayar da gawar ayi Mata janaixa daganan ne kowa zai iya tabawa Amma yanxu muna bawa neges matuqar hkr
Saidai idan hankalinka yafi kwanciya da kwakwariyar shedane zamu iya cewa tunda maleek yagani hakan zai gamsar da Kai.
Numfashi boyayye neges yasake Yana jinjina Kai tareda kallon maleek cikin yanayi na kulawa da damuwa yace"
Duk yanda za'a ayi kada abari media suji wannan mumman labarin ayi komai a sirrance tunda hukumarma a sirrance suka shigo suka fice.
Motar asibitin tafara wucewa daukeda gawar kafin akabar jamian tsaro uku da sauran securities din maleek a bakin sassan na maleek sbd shima Yana cikin wainda hukumar zata tsare sbd komai a qarqashin bangarensa yafaru Dan Haka an saka tsaro a sassansa babu inda zashi zai zauna aciki bame Shiga sai mr Omar kawai aka bawa dama shima abincin kawai zai ringa shiga dashi yafito sai zuwa headquarter aduk lokacinda aka buqaci ganinsa harsai antabbatarda cikin su biyun lailah ce ko jekadin ce tayi kisan.
Da hakan zancen yasake qamari hankalin jama'ar gizah yayi mumman tashi musamman Anneti tana tsananin buqatan ganinsa saidai ba dama Haka Takoma sashenta cikin tsananin tashin hankali da damuwa tana daga hankalinta da rokon Allah sassaucin wannan mummunan masifar har lailah take roqawa sassauci sbd ita uwace tasan wannan Abu wani babban al'amarine daga ubangiji kowa na neman doki daga garesa Dan Haka kowa zata rokar Masa.
Ta bangaren Mr Omar Yana fitowa gizah tareda maleek cikin sirrantacciyar mota sai motar jamian tsaro da securities dinsa fitowarsu gizah kenan ga tarin dibbin mamakinsu 'yan media ne birjik suka yo kansu tareda zagaye motocinsu suna jeho tambayoyin dasuka kusan hargitsa tunaninsu su dukan Dan kuwa bayani ne akan cewa"
Shin me maleek zai iya cewa akan tsohuwar matarsa da jekadinsa dasuka taru suka kashe 'yar uwar matarsa?????
Tsit sukayi dukkaninsu Mr Omar na dagowa ya kallesu kafin ya 'dan waiwayo ya kalli MALEEK dake duba wayarsa hankalinsa kwance ya girgizawa Mr Omar din Kai take Mr Omar yabawa motar wuta sukai cikinsu da gudu sukaita kansu suna tsananta wutar al'amarin a social media da cewar tsohuwar matar UBAYD MALEEK M KALEEB tayi hadin gwiwa da jekadinsa gurin kashe yayar matarsa a Daren jiya.
Ganin yanda abin ke ruruwa Kamar wutar daji yasanya Mr Omar Kiran mum Sarah da gaggawa ya Bata umarnin duk wani Abu daya shafi kallon news ko wayoyin NURU da afia duk ta lalata kada tabari su samu news na abinda yake faruwa.
Ta bangaren iyayensu nu NURUn kuwa Abu Kamar hadin Baki Koda gari ya waye labarin ya baza duniya babusu Babu Wanda yasan Ina suka bace bat a dare daya ga 'yan kawo rahoto da 'yan jaridu daketa yawon gidansu sunason ganawa dasu akan al'amarin Amma babusu sai hakan yaqarawa tashin al'amarin girma sbd take aka fara kokarin Bata sunan MALEEK da cewar shine ya batarda iyayenta Dan boye laifin tsohuwar matarsa da jekadinsa.
Headquarter dasuka Isa wasu sabbin rubuce rubucen report aka shigar musamman akan ta Yaya 'yan jaridu sukasan macece aka kashe Kuma Yar uwar matarsa sbd Babu Wanda yasan gawar waye dagashi sai mr Omar ko jamian tsaro Kai tsaye ya hanasu duba gawar aka barta akan se Yan asibiti sungama nasu aikin tukuna
Kuma 'yan asibitin ma mutum biyune Kuma a asibitinda Babu Wanda yasan da ita aka aikasu to tayaya zancen yafita zuwaga 'yan media.
Suna dawowa gida ya shige sashensa ya zauna tareda sauke ajiyar zuciya ahankali tareda rufe idanu ya bude ya kalli gefenda Mr Omar yake tsaye Kai tsaye yace"
Kayi komai kaje da kanka ka taho dasu at any cost kada wannan labarin ya samesu harsai sun iso.
Dan dagowa Mr Omar yayi ya kalli MALEEK yace"
MALEEK anan din aikin Nan barinsa nada hadari.
Kaje komai Yana yanda ake son shi.
Angama Inshallah maleek.
Ficewa yayi Kai tsaye yakira Yana booking tickets Allah ya taimakesa washe gari da asuba jirjgin zai tafi Dan Haka Kai tsaye ya wuce ba wani delay.
Sai tsakiyar dare sosai ya Isa gidan Bai samu shigaba ta waya ya sanarda mum Sarah ta sanarda NURU da afia su shirya gizah zasu.
Da mamaki suka kalli juna lokacinsa mum Sarah ta sanar dasu saqon
NURU ta kalli wayarta da jiya ta wayi gari taganta a farfashe ta waiwaya ta kalli afia da tata ma tafi ta NURUn tashi aiki cikin sanyin murya tace"
Kina tunanin lafiya komai yake?
Sauke ajiyar zuciya afia tayi tana Dan duba agogo tace"
Inshallah lafiya."tafada hakan ne Dan bawa kanta qwarin gwiwa da bama NURUn positive answer Amma tun jiya takejin kanta cikin tsananin damuwa musamman dataga miscalls na mum dinta data kirata Bata kusa wayar na silent tunda ta karanta massage dinta taji tana kewar soyayyar uwa saidai Kuma zuciyarta na tunatarda da ita amfani mum dinta keson Yi da ita kawai tunda take nemanta.
Babu wani dogon musu sukahau shiru tsaf suka shirya hankulansu a tashe Babu me nutsuwa daurewa kawai kowannensu keyi Dan qarfafa Dan uwansa.
Sai washe gari da asubar fari jirginsu ya daga suka wuce Basu isaba sai cikin tsakar dare har lokacin 'yan jerida na daddabe boye a wajen masarautar gizah suna jiran rahoto
Dayake Mr Omar yasani saida sukazo gate din Yan jaridar na tasowa yace driver yayi cikinsu da mota duk da hakan sama sama afia taji dayan na jeho tambayar data sakata kallon waje da sauri inda Yan jaridar ke kokarin biyo motar askarawan securities din makeken gate din shiga masarautar suka taresu da sauri suka koma maboyarsu suna jiran sa'a.
Afia jitayi tana gigicewa da abinda kunnuwanta suka ji cewar
Tsohuwar matar maleek tayi kisa
Kenan shine dalilin daukosu da gaggawa ba shiri?
Rawa jikinta yafarayi ta dago idanuwanta nacikowa da hawayen tashin hankali ta bude Baki zatayi magana daidai tsayawan motar bakin sashensu a fixge tasamu damar fizgo maganar daqyar ta bakinta tace"
Mum tayi kisa?????
Da sauri NURU ta waiwayo ta kalleta gabanta na mummunan faduwa
Saidai ganin afian na kallon Mr Omar da idanuwanta da take sukai jajir yasa NURUn juyowa tana kallonsa da jiran amsarsa Dan kuwa take jikin NURUn yaso fin na afia daukan rawa Dan kuwa a yanda tasan lailah kila maleek ne kawai Wanda zata iya kashewa sbd kishi da baqin cikin abinda yayi Mata batasan lokacinda bakinta Yana rawaba ta furta"
Wa aka kashen???
Sauke Kai Mr Omar yayi cikin tsananin jimami da kasa fadar komai akan tambayoyinsu Wanda yasakasu tabbatarda maganar kenan Haka take abindaya faru kenan.
Take hawayen afia suka balle duk inda hankalinta yake Yana tsananin tashi
Mr Omar yayi saurin fitowa ya budewa afia kofa suka fito har NURUn tsabar rudewa ta manta da sashenta za'a qarasa da ita.
Afia tayi ciki da sauri ko gabanta Bata gani sbd tashin hankali wani takeson tambaya taji shin da gaskene kokuwa gizo maganar tayi Mata,
NURU kuwa sagewa dukkanin kafafuwanta sukai ta nufo cikin tana daga kafa daqyar farhat datai bacci saidai bayinda suke shigarda kayansu afian suka shigo da ita
Tana shigowa palon daidai lokacinda baiwar da afia ta dakawa tsawa tana cewa"
Ki fadamun abinda ke faruwa a cikin delah gizah nace..""taqarasa fada cikin tsananin karajin daya tsorata baiwar a firgice tace"
Kisa akayi a...a..sassan MALEEK.
Innalillahi'wainna ilaihirrajiun" shine abinda afia tafara maimaitawa cikin tsananin fita hayyacinta tana girgiza Kai da sauri da sauri.
NURU kuwa Jin sunan maleek a maganar yasa jiri dibarta Saida mutum biyu sukai saurin tarota dama Mr Omar yasakasu kiranta Dan qarasawa da ita Bata masaukin suka fito da ita ko ganin gabanta batayi sosai kokai dake aiki jikinta ya tsaya harta shiga mota aka ja Bata saniba,
Suna Isa bakin masaukinta mr Omar ya bude Mata kofar Motar
gabaki daya Bata lurada wani sashene aka kawota dabam ba asalin nataba Dan tafiyar kawai takeyi batasan inda take jefa qafa Haka Mr Omar ke bude Mata kofofin palukan dasuke wucewa har zuwa na karshe daya bude ya dakata ta shige ya janyo kofar ya juya ya koma Yana ficewa daga sassan gabaki daya.
Hankalinta baya jikinta saidata takunta yafara nisa cikin palon taji iskar numfashinta ya sauya da qamshin dayake shiga hancinta ta dakata ahankali tareda dagowa ta kalli inda take tana waiwayawa gefen damarta numfashinta saidaya kusa daukewa sbd bazatan yanayin datashiga ganinsa zaune kan kujera sanyeda jallabiya brown fuskarsa na fidda wani irin zatin kwarjini Yana kallonta da fararen idanuwansa dake zube tas akanta...ta rufe ido ahankali ta bude ta tabbatarda shi dinne
Zuciyarta da gangar jikinta sunkasa hakura ta nufesa da wani irin gudu dake bayyanarda dukkanin sirrin zuciyarta akansa idanuwanta na cikowa da hawaye,
Yana ganin hakan ya miqe tsaye ahankali daidai isowarta ta fada jikinsa yayi sama da ita kamar yarinya qarama Yana kallon idanuwanta da hawayenta suka tsinke take suna gudu kan fuskarta ya sauketa tareda matseta jikinsa ahankali Yana kallon kyakkyawar fuskarta da fararen idanuwanta dake fidda hawaye sosai
Ya dauke gira daya Yana sake boyayyan murmushi tareda kamo fuskarta da tafin hannuwansa biyu Yana kallon cikin idanuwanta data dago ahankali tana kallonsa itama har lokacin idanuwanta hawayen sun kasa tsayuwa
Ahankali ya matso da fuskarsa dab da tata yakai bakinsa kan kunnenta Saida ya sauke wani numfashin daya sanyata dauke wuta cikin sirrantacciyar muryar da Bata taba jiba a hankali yace"
Kukan menene wannan??
Rintse idanuwa tayi da qarfi tana sake qanqamesa kirjinta na mannuwa da nashi yayi baya Ahankali Yana dafe kan kujerar dake bayansu Yana riko numfashinsa dake neman sauyawa ya lumshe ido tareda budewa ya kallon idanuwanta zuwa hancinta dayayi ja sbd kukan datake
Ya zura hannunsa daya zuwa bayanta ya riqo qugunta Yana sake Kai bakinsa kan kunnenta can qasa yace"
Kina tsoron mutuwana ne??....
Wani sirirn kuka ta fashe dashi Jin abindaya fada sbd har lokacin Bata gama fitowa da mummunan tashin hankalin tunanin rasashiba
Ya kamo hannunta suka zauna Yana kallon fuskarta tareda tallafo fuskar da hannuwansa Yana cikin yanayi na kulawa yace"
Ok shikenan ya Isa haka,
Ban mutu ba,Babu abindaya sameni ok?.
Rungume kanta yayi Yana shafa bayanta ahankali Yana zuwa kanta hartagama kukan tafara sauke ajiyar zuciya sai alokacin shima ya sauke boyayyar ajiyar zuciya tareda lumshe fararen idanuwansa yanajin nutsuwa na shigarsa sbd kukan nata ya wargaza duk wata nustuwarsa dama tunanin komai.
Saidaya tabbatarda tadawo hayyacinta tagama samun nutsuwa ya dagota ya kalli fuskarta datai qasa da ita sai alokacin takejin kunyar kanta ta Dan juyar dakai tana Jin sanyi da nutsuwa na dawo Mata.
Hannunta cikin nashi suka nufi bedroom dinsa da komai ya nuna yakuma bayyanarda Nan din ne asalin turakar sarki Dan kuwa duk wani Abu dake tsare a dakin me adon zaibane(golden) sai makeken gadonsa dako rabinsa ya ishesu su biyun hadda saurama
Sai wasu dogayen labulayen windunansa dasukafi Kama da kofofi sbd girmansu ta waiwaya inda madubinsa yake ya cinye kusan Rabin bangon gefen dayake ta tsaya gaban madubin tana kallon kanta cikin nutsuwa da nazartar rayuwa sbd wato Babu Wanda yasan me ubangiji ya tanadarwa rayuwarsa agaba.
Ta cikin madubin suka kalli juna ta sauke kanta ahankali tana juyawa daga kallon madubin ta taka ahankali tabar gabansa ya riqo hannunta Yana dawowa da ita baya gabansa wannan karon kallo daya yayi Mata ya dauke Kai sbd kokarinsa kada ya tashi a banza Dan kallonta kawai na canja Masa tsarukansa da dama.
Zamewa tayi ahankali tareda nufar toilet dinsa tashige ta rufo kofa tareda sauke ajiyar zuciya me sanyi tana rufe ido cikin sanyi tace"
NURU why did you loose your control¿
Ta Jima ahaka tana sauke numfashi harsaida tadawo nutsuwarta gabaki dayanta kafin ta zare kayanta ahankali ta daure gashinta tsakiya ta yanda bazai jiqeba tayo wanka ta janyo towel dinsa blue ta dauro ta fito.
Kwance tasamesa a tsakiyar gadon takasa kallon gefen ta nufi madubinsa turare kawai tashafa ta juyo tarasa abinyi sbd sallah takeson Yi
Dole doguwar rigarta ta Dora kan towel din tayi sallolinta tana idarwa ta miqe ta zare rigar ta waiwaya takallesa a sace taga kaman yayi bacci saita sulalo ahankali ta hau gadon ta kwanta gefensa tana fuskantarsa ta zubawa kyakkyawar fuskarsa idanuwanta tana sauke ajiyar zuciya a boye, ta gangaro da idanuwanta kan dogon hancinsa da duk farhat shi ta dauko
Ta lumshe idanuwanta lokacinda taji hannunsa na sauka jikinta ahankali ta cikin bargon dasuke rufe dashi
Daga hakan Bai qare komaiba sukai bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
##MAMUH#
************
Washe gari latti ta farka daga bacci
Ta motsa ahankali tana bude idanuwanta gabaki daya tana duba kan makeken gadon data ganta ita kadai bayanan, ta tashi zaune tana gyara daurin towel din data kwana dashi tana miqewa tsaye tana kallon kofar toilet saidai Jin Babu motsi ta tabbatarda baya cikin dakin ta nufi toilet tayo alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta miqe ta koma ta kwanta sai lokacin tafara tunanin maganar kisar da akece mum dinsu afia tayi
Ta tashi zaune tana shiga sabuwar damuwar tausayin afia da farhat musamman afia da sai yanzu take tunanin halin datake ciki,
Yaya zata iya daukan wannan mummunan al'amarin sbd tasan yanda Afia takejin mahaifiyarta cikin ranta wannan al'amari abune me tsananin wahala da azabar dauka Dan Haka afia na tsananin buqatanta akusa da ita gaskia.
Tashi takuma Yi tareda saukowa kan gadon ta janyo kayanta na jiya ta maida jikinta tareda fitowa Palon tana gyara rufar kanta da qaramin gyalen datazo dashi daure akai
Babu kowa palon da Alama dai fita yayi gaba daya Dan Haka Kai tsaye ta nufi kofa ta fice kofa kofa ta palukansa harta Kai kofar ficewa gabaki daya ta fito
Dayake safiyace sosai Sosai Babu mutane tsit koina sai securities din maleek dake koina tafiya daya biyu saika gansu bayi ma na can kowa na aikin gyara da aikin abincin uwayen dakunansu kafin su tashi tasamu ta 'dan rufe fuskarta tana Dan sauri sauri harta Isa sashen Babu Wanda ya ganta tana shiga ta zare rufarta tareda nufar ciki Kai tsaye daga Palo bedroom din afian ta wuce ta shiga hankalinta na tashi dajin shiru a palon.
Zaune take kan dadduma tunda tagama sallah Bata tashi daga gurinba idanuwanta sun kumbura sosai sai fuskarta datai jajir ta dago ta kalli NURUn da duk hankalinta yasake tashi ganin yanayin afian take idanuwanta suka ciko da hawaye ta qaraso da sauri ta rungumeta da tsananin sanyin murya da kulawa tace"
Sorry baby.
Sai yanzu afia tasamu me lallasarta tunda wannan baqin labari ya sameta ta zube jikin NURUn tana sake sabon hawaye tana son magana tana kasawa sbd nauyin Baki dana zuciya
NURU ta girgiza Mata Kai tana tsoyayo hawaye ahankali tace"
Karkice komai kiyi shiru Ina Nan
Gani tareda ke.
Shiru sukai ahaka tsawon lokaci NURU na shafa bayanta ahankali ahankali tana Dan lallashinta tareda tunatarda ita tana tareda ita komai zaizo da sauki inshallah har afia din tasamu Dan sauki tanata sauke ajiyar zuciya akai akai.
Miqar da ita NURU tayi suka nufi gado ta zaunar da ita tareda Dora Mata kafafunta kan gadon ta ja bargo ta Dan rufe Mata Rabin jikinta ta kalleta da nata idanuwan dasuka sauya cikin kulawa da sanyi tace"
Bari nasa akawo Miki wani Abu kici
Jikinki ba qwari.
Fita tayi zuwa Palo takira masu aikin sashen tace akawo abinci Mara nauyi sosai da tea me zafi Sosai na lemun tsami da Zuma.
Da sauri cikin tsananin girmamawa suka amsa da to suka juya da sauri Dan ciko umarninta ita Kuma ta juya Takoma dakin taqaraso ta zauna gefen afia tana shiga nazari da tunanin asalin abin dayake faruwa kokuma yafaru sbd haryanzu takasa sanin takamaimai abindaya faru zancen guntu guntu kawai ta samunsa
Ta kalli afia ahankali tanason taga Bata cikin halinda zata iya tambayarta wani abun a yanzu
Gashi dad dinsu afian ma batajin zata iya tambayarsa Dan kuwa tambayar maleek kaman rashin girmamawa ne garesa saidai shi ya tambayeka Dan Haka bazata iya tambayarsaba saidai ko jekadi, idan tafita Takoma sashenta zata tambayi jekadi komai inshallah idan harta dawo daga delah daga Kai padima gida.
Da kanta ta bawa afia tea da 'dan flat filled bread guda daya ta taimaka Mata Takoma ta kwanta cikin kulawa tace"
Kiyi bacci kina buqatan hutawa Kona awa biyu zuwa uku ne ke likitace kinsan kina buqatan hutu kafin kisamu nutsuwar yin wani tunanin ok?
Lumshe ido tayi tana gyada Kai
NURU ta juya tana cewa"
Zankoma Nima nayi wanka naci abinci.....riqe hannunta daya afia tayi tana kallonta da idanuwanta dasuka sauya take suna neman cikowa da hawaye ahankali ta bude Baki tace"
Karki barni Ni daya NURU wlh ina buqatan wani atare Dani sbd zuciyata da shedan na ingizani kaman na kashe kaina na huta da wannan rayuwar,
Bana tareda soyayya ta uwata danake tsananin buqata da kwadayin samu Amma bantaba samuba tun Ina qanqanuwata mahaifiyata Bata taba zaunawa tabani soyayyar uwaba,
Mahaifina haryanzu Banda masaniyar ko fushin dayake Dani ya sauka Dan haryanzu bansamu ganinsaba bare yasan halindanake ciki,
'yar uwata ta jini yarinyace qarama da banama fatan taji abindayake faruwa,
Kakanni na mulki da rayuwar mulkice kawai agabansu banida kowa saike Dan Allah ki zauna taredani.
Kallonta NURU keyi cikin yanayi na damuwa da tausayi jikinta nayin sanyi tadawo ta riqo hannun afia din ta tayar da ita zaune tana cewa"
Muje can sashena zakifi samun nutsuwar hutawa farhat ma na can jekadi na kulawa da ita inshallah..
Da sauri afia ta dago ta kalli NURUn bakinta na rawa da mamaki tace"
Jekadi Kuma????
Ganin yanda Afia din ta firgita da Jin jekadi yasa NURUn Dan dakatawa da Mata kallon mamaki tace"
Lafiya dai ko??
Girgiza Kai afia tayi da sauri tace"
Mum da jekadi sune abin yafaru dasu ta Yaya jekadi zata dawo??...
Mummunar faduwa gaban NURU yayi tana yiwa afia kallon tashin hankali jekadi aka kashe kenan ko me???
Innalillahi wainna ilaihirrajiun..
Juyawa tayi tana neman ficewa afia tayi saurin biyota ta riqota tana cewa"
Ta Yaya akai Baki saniba bayan kin kwana a sashenki kinkuma ga bakiga jekadin ba,
Shin tadawo ne?
Gabaki daya NURU kasa amsa tambaya daya tayi sbd toshewar Kai
Harga Allah jekadi tamkar uwa ko Kaka take agurinta wadda takejinta Kamar jininta sbd a rayuwarta bayan iyayenta jekadi tafara nuna Mata qauna tamkar ta jini Dan haka bazata iya daukar zancen mutuwar jekadi Kai tsaye daga sama ba tana buqatan cikakken bayanin abinda yake faruwa ta dago jajayen idanuwanta ta kalli afia da itama itan take kallo cikin zaquwar Jin da gaske jekadin tadawo tace"
Kimin bayanin abinda yake faruwa
Acikin duhun komai nake akan al'amarin, shin meya samu jekadin da mum dinki Ni komaima bansaniba
Meyake faruwa"" zuwa lokacin hankalinta yafara mummunan tashi sbd Jin take al'amarin toko yayane ya shafeta sbd yanda rashin nutsuwa da tsoro dayake shigarta.
Afia ma sake rikicewar tayi tana kallon NURU zatai magana saita fasa ta koma ta janyo jallabiyarta me hula ta saka ta fito ta fice sbd dad dinta kawai zata iya gani yanzu kanta neman kuncewa yakeyi ta tsaya gaban NURU data kasa cewa komai tace"
Muje sashen naki Ina buqatan ganin Mr Omar Dan Allah.
Da ido NURU kawai ke binta sbd ita idan tashiga shock kasa komai takeyi Kamar Mara tunani Haka takama hanya suka Isa sashenta tun a palon ta tsaya tana kallon sauran masu aikinta dake tsatsaye suna jiran isowarta tun jiya Bata isoba gari na wayewa sukai ayyukansu suka Gama suka sake dasa jiran isowartata
Ko gaisuwarsu Bata samu amsawa Kai tsaye ta kalli Akira wadda take matsayin babbarsu idan Jekadi Bata Nan tace"
Akira menene yafaru akan matsalar mum dinsu afia??
Shiru Akira tayi tana sauke Kai Suma tuni kowa ya sauke Kai
Akira ta Dan dago cikin shakkun tsoma Baki cikin al'amarin sbd babban gargadi daga mr Omar na kada Wanda yafadi Wanda aka kashe din wa NURU Koda Wasa.
Sake maimaita tambayarta tayi wannan karon da 'dan daga murya
Akira ta sake sauke Kai ahankali cikin tausasa harshe tace"
Kisa akai a sassan maleek a Daren shekaran jiya, Matar MALEEK ta farko itace ake zargin tayi kisan sai jekadi da aka tafi da ita itama sbd ansameta a gurin da abin yafaru.......
Kai tsaye NURU tace"
Waye aka kashen???
Tsit sukayi Akira na sake sauke kanta
Qasa cikin nutsuwa tace"
Babu Wanda yasani tukuna.
Shiru sukayi dukkaninsu daga NURUn har afia sbd tashin hankalin da mamakin al'amarin.
Zamewa afia tayi ta sulale kan kujera ta zauna tana rasa tunanin Yi
NURU ta zauna kusada ita tareda kallonta cikin tausayawa da sanyin yanayi tace"
Kaddarace wannan ki dauka daga ubangijine Kuma Inshallah zata samu kanta idan har batada hannu aciki
Sbd dad dinku bazai taba barinta cikin wannan halin ba komai zaizo ya warware Inshallah.
Kasa dagowa afia tayi tana sauraren abinda NURU take fada Mata Wanda hankalinta baya Kai tayi zurfi cikin tunani ta dago ahankali ta kalli NURU da jajayen idanuwanta tace"
Idan ta tabba cewan itace ta aika wane hukuncine zai hau kanta a shari'ancen Court??
Shiru NURU tayi tana kallonta cikin tsananin tausayawa kafin ta Dan dauke Kai cikin sanyi tace"
A shari'ancen musulunci shine Wanda ya kashe da gangan a kashesa,
A shari'ancen kotu ma idan dukkanin shedu sun bayyanarda yayi kisan da gangan ne ba bisaga qaddara ko dalilin Kare Kai ba ko dalilin ceton Rai to tabbas kisa ce ta Kai tsaye zata hau kansa....
Saurin dafa afian tayi ganin tana neman fita hayyacinta cikin sauri tace"
Dukkanin wannan kadaki yanke ko daya sbd bakisan akan me kisar ta afkuba kika tayine Dan kariyar Kai ko bisaga kaddara kadaki cire Rai daga sauqin ubangiji kiyi kokari kiriqe jarumtar fuskantar komai Inshallah ba hakan bane Ina Mata fata.
Miqewa NURUn tayi Jin tahowar farhat dake kiranta tun daga cikin bedroom ta juya ta kalli kofar dakin kafin ta dawo da kallonta kan Afia a natse tace"
Ina zuwa Bari nadubo ta.
Wucewa tayi zuwa dakin dake gefen nata Wanda aka tsarashi da komai na yara domin farhat din tana shiga ta qaqalo murmushi tana kallon kallon farhat din data shirya cikin riga da wandon asalin yadin qasar na sarauta me kyau ta qaraso gurinta tana cewa"
Heyy sweetie you look more pretty.
Cikin Jin Dadi ta qaraso gurin NURUn tana fadawa jikinta suka juyo zuwa palo tana cewa"
Aunt jiya Ina Kika kwana Kika barni Ni kadai?
Siririn Murmushi NURU tayi tana kawar da zancen tareda Dan dagowa ta kalli inda afia data bari Palon tana fatar Bata jiyo zancen da farhat din tafada ba ta kamo hannun farhat din suka nufi gefen da dining yake ta miqawa Akira hannunta tana cewa"
Kije da ita taci abinci Ina zuwa.
Komawa bedroom dinta tayi tayi wanka cikin sauri ta shirya cikin doguwar royal gown ash ta fito Akira dake jiran fitowarta ta gyara tsayuwa suka nufi sashen Anneti Dan sai yanzu tunanin zuwa Kai Mata gaisuwa ya shigeta musamman tasan tanacan cikin damuwar al'amarin itama tabar afia zaune agurin tana saqa da warwarar yanda zata tarbi al'amarin wa mahaifiyarta sbd ko kowa ya yadda da ita ta aikata hakan bazata taba yadda da mum dinta zata aikata hakan ba.
Koda aka sanarwa Anneti qarasowar NURU gurinta sai farin ciki ya shigeta taji ta Dan samu nutsuwa da saukin abindayake cin ranta ta fito daidai shigowan NURUn data qaraso har gabanta ta durqusa har qasa ta gaisheta cikin girmamawa
Da farin ciki Anneti ta dagota tareda nuna Mata gurin zama tana amsawa cikin kulawa tace"
NURU ya kike?
Kina lafiya dai ko?
Alhmdlh"tafada cikin nutsuwa tana Dan dagowa bayan sun gama gausawar tace"
Ashe abin daya faru kenan¿Allah ya kawo mafitar wannan al'amari tareda tsare gaba.
Ajiyar zuciya Anneti tasake tana gyara zama ahankali cikin bayyanarda 'yar damuwarta tace"
Allah ne kawai masanin wannan al'amarin Amma dai koma Yaya yake
Allah ya fitar da kowa yakawo mafita
Musamman shi maleek da abin yafaru a qarqashinsa Wanda yasa Yan jaridu keta fidda labarai marasa Dadi akai
bana fatan hakan yazamo matsala agaresa, ki kula dashi sosai kibashi kulawa Dan Yana cikin tsananin damuwa na tabbata.
Shiru NURU tayi dukkanin jikinta nayin sanyi da wannan sabon bayanin data samu.
Boyayyan numfashi ta sauke tanajin tsananin buqatar son ganinsa Dan Bata lurada cewa halinda yake ciki ba kenan tun jiyan da bazata baro gurinsa ba gashi yanzu batada ikon maida kanta batareda ya nemi ganintaba.
Miqewa tayi jiki Sanyaye ta fito Takoma tanajin danuwarsa na lullubeta tana shiga Kai tsaye daki ta wuce tafara tubewa ta saka Kaya marasa nauyi tayo alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta kwanta tareda lafewa kan gadon tanajin kaman zazzabi na neman shigarta.
Baccine yafara fizgarta cikin tunanin datai nisa daga sama sama taji Ana Kiran sunanta ta bude idanuwanta ahankali dasukai nauyi sbd kanta daya fara ciwo tuni, ta dishi dishi taga kaman jekadi take gani gabanta ta bude idanuwanta gabaki daya tana waresu akanta.
Jekadi data fahimci NURUn Bata gasgata ita bace saita Dan murmushi ahankali tana cewa"
Allah qarawa MUSHRAn maleek kyau da lafiyar bacci.
Da sauri ta tashi zaune har batasan lokacinda tafada jikin jekadin ba ta rungumeta da qarfi idanuwanta na cikowa da hawayen farin cikin ganinta da tausayinta tace"
Alhmdlh Masha Allah jekadi kindawo kindowo.
Farin cikine yakama jekadi ta zame tana kallon NURUn wadda Allah ne ya hada kauna tsakaninsu tun farko ta kalli idanuwanta dasuka ciko da hawaye tace"
Karkiyi kuka Allah zakiyiwa godia Allah yaqaro haske a rayuwarki kinji,share hawayen ki gyara fuskanki maleek ke buqatan ganinki tareda afia.
Sai alokacin ta tunoda lailah ta kalli jekadi cikin sanyi da tausayin afia dayake sake kameta tace"
Mum din afia fa??
Ajiyar zuciya jekadi tayi tareda dagowa a natse tace"
Tana hannun hukuma haryanzu sbd anyi bincike an tabbatar itace saidai haryanxu takasa tsayawa ta nutsu tayi bayaninda zai taimaketa.
Shiru sukayi dukkaninsu NURU na jajanta abin cikin ranta da yanda Afia zata dauki abin.
Ficewa jekadi tayi tana cewa tana jiranta a Palo itakuma ta nufi toilet ta wanko fuskarta ta fito ta Dan gyara ta sauya Kaya zuwa doguwar jallabiya maroon ta fito tana qamshin turaren _bosslady_ dayake fita ajikinta ahankali Bata saka sosaiba sbd kada taqarawa afia damuwa akan tata hakama Bata shafawa fuskarta komaiba duk sbd afia Dan batason saka Mata damuwar wani tunanin daban.
Data fito kallo daya jekadi Tai Mata tana karanto Mata adduoin tsari daga sharrin ido Dana Baki sbd ko Yaya NURUn tafito ita din kyanta me sanyi ne.
Afia kuwa Batada wani kwanciyar hankalinda zaisa tayiwa NURUn kallon tsaf itama dai tayi kokari ta shirya kanta suka fito jekadi na gaba suna baya sai su Akira dake take nasu bayan har zuwa bakin sashenshi kowa ya dakata daganan daga jekadi saisu suka qarasa ciki a palo na biyu suka taddashi zaune Yana sauraren bayaninda mr Omar keyi Masa hankali kwance Yana sanye cikin wani coffee brown kaftan dasuka fiddo da qyallin da fatarsa keyi kwarjininsa yana sake bayyana tareda cika idon me kallonsa
Yana Jin shigowarsu Bai waiwayoba saima takardun daya bude Yana karantawa na sakin jekadi da akai a yau din
Mr Omar kuwa sauya bayanin dayakeyi yayi da kallon gefensu NURU da cewa"
Barka da shigowa.
Da Kai NURU ta amsa Masa ahankali tana satar kallon gefen maleek din kadan Wanda Bai nuna ya San da shigowar tasu ba
Afia kuwa Batada karfin amsa Masa
Zama sukayi kafin ya dago ahankali ya zubawa NURU idanuwansa dasuka sata saurin cafko numfashinta daya tashi barin jikinta sbd kallon tajisa ajikinta sosai, ta dago fuska ahankali ta kallesa ya juyarda kallonsa kan Afia tausayin 'yar tasa na kaunarta na sake shigarsa sbd yanason 'yayansa fiyeda yanda ake gani
Ya bude Baki Kai tsaye cikin kulawa da kamewa yace"
Afia maleek yaya?kina lafiya dai ko?
Shiru tayi Idanuwanta nason cikowa da hawaye ta dago ta kallesa tana hango kulawa da kaunarta gurin dad din nata sai hawayenta suka gangaro ta girgiza Masa Kai ahankali tana cewa"
Bana cikin nutsuwa dad.
Dan gyara zama yayi Yana ajiye takardun hannunsa ya sake kame muryarsa yace"
Mum dinki itace damuwarki right?
Gyada Kai tayi tana sauke Kai kalar tausayi.
Afia idan kinmin alqawarin Zaki kwantarda hankalinki ki nutsu kodan karatunki da bawa Taki rayuwar mahimmanci ki daina biyewa tunani irin na mum dinki then namiki alqawarin Babu abinda zai samu mum dinki zata fita cikin case dinnan lafiya Amma Zaki Bata shawaran ta tafi ta inganta rayuwarta ta wani hanyar kin saurari abinda nake fada right??
Dagowa tayi ta kallesa da hawayen dake gudu akan fuskarta ta gyada Kai tana cewa"
Yes Dad namaka alqawari Inshallah dagani har ita zamu cika wannan alqawarin.
Daukan takardun gabansa yayi ya bude tareda karban biro a hannun Mr Omar yasaka hannu cikin takardun tareda rufewa ya miqawa Mr Omar yace"
Ka sameta tabaka sunan lawyernta shine zai qarasa aikin yakai takardun can zasu saketa kada abari 'yan media su sani ko kadan infact dagacan a haura da ita tabar qasar gabaki daya.
Da sauri afia ta qaraso gabansa tana Masa godiya cikin tsananin farin ciki tace"
Imran ne lawyern mum zankirasa zaizo ayau Inshallah dad.
Sunan Imran data ambata yasa NURU kallon afian ta sauke kanta.
Fita afia NURUn ma ta miqe zatabi bayanta jekadi zata dakatar da ita maleek yayi Mata kallon ta barta ta wuce.
Bayan fitarsu ya kalli Mr Omar yace"
Ayi Mata takardun ganin likitan tabin hankali kada a taba barin afia tasan mum din Tata tasamu tabin hankali sbd shock din wannan al'amarin
a fitar da ita abar Mata gidan Vegas tazauna can taringa ganin likita akai akai har Allah ya yaye Mata
Afia Kuma iyakacinta da ita airport.
Allah yaqarawa maleek tausayi da adalci.
Sai maganar Dan jaridar daya fara wallafa cewan 'yar uwar.....'dan shiru yayi Wanda yasa Mr Omar da jekadi kallon juna suna Dan murmushin dasu kadai sukasan ma'anarsa
Mr Omar ya karbi zancen da cewa'
Za'a shigarda bayyananniyar qarar shariar sama akan Wanda yafara wallafa labarin ankashe 'yar uwar mushrah sbd haryanxu bayan mu da hukumar dake hannunka babu Wanda yaga asalin gawar ta Yaya yasan wacece aka kashe hadda alaqarta da mushrah,
Dan Haka inda bayanin yafara fitowa zai fada.
Ahankali maleek ya gyada Masa Kai Yana cewa"
Daga gobe kada abarsu fitowa kowa ta zauna a sashenta a tsananta tsaro a hanyoyin bangaroransu sbd komai zai iya faruwa idan aka fallasa zancen qarar Dan jaridar sbd kada asan inda yasamu zancen.
Juyawa sukai suka fice suka bar sashen nasa sbd wayar dazai fara da kaleeb.
Sbd tsaro Koda afia Takoma sashenta doka aka bayar kadata sake fitowa sai gobe Dan Haka ita Bata damuba take tasaka aka kawo Mata sabuwar waya dayake tana tareda layinta na qasar saita Sanya ta nemi numbern Imran.
Cikin tsananin damuwar halinda suka samu labarin abindaya faru cikin tsananin damuwa yake tambayar afian Yaya case din ke tafiya sbd case ne na masarauta babu me halin Shiga danma sunyi mamakin da hukuma tashiga zancen Dan masarauta irin delah gizah sune suke hukuncin komai daya shafesu da kansu Amma Kuma ace MALEEK dakansa ya bawa hukuma damar shigowa ciki duk da hukumarma tasace sai abinda yace suke amfani dashi.
Cikin nutsuwa afia tace"
Ni yanxu duk wannan bana tunaninsa yanxu sbd ya amince zai sa asaki mum a sirrance tabar qasar Dan Haka kana buqatan isowa cikin gaggawa gobe ka isarda takardun abaka ita ku tafi
Dan Allah kamun alqawarin zaka kularmin da ita sbd nasan yanzu tana cikin tsananin hali na tashin hankali.
Dan shiru yayi Yana cewa"
Bazai yiyi nazo gobe ba sbd Kar takardun nikadai lawyer bazan iya zuwaba Dole sai munje tareda wani lawyern Wanda zai duba takardun dazanje dasu agurin dama wannan Dole 2 lawyers ne suke zuwa Dan Haka Ina buqatan time Zan nemo wani lawyer din Wanda zai bamu time dinsa yazo taredani.
Shiru afia tayi cikin tsoro da tashin hankali tace"
Baza'a iya jiraba damace dad yabawa mum Dan Allah kazo kawai an zamu samu wani lawyer din.....
Shiru tayi cikeda nazarin abin data tuno na cewan NURU ma lawyernce
Wani sanyi ya lullubeta ta maida wayar kunnenta tana cewa"
Kazo NURU is here nasan zataje tareda Kai Inshallah zanyi mgn da ita.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 44_*
_*LAVENDER RESTAURANT..*_
_(Palace of mouthwatering food/delicacies)_
_IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_
_*TO KU MATSO...! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA HABE DAKE.._*
_*UNCLES, DADDIES, BROTHERS., NEWLYWED HUBBYS..! KU ZO KU YIWA ‘YAYAN KU, MATAN KU DA KANNEN KU RAJISTAR WANNAN HARKA TA KOYAN GIRKI.._*
_*Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental,snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k NE. phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61_*
_*ZA’A FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA YAU._*
_*GIRKE GIRKE GUDA 30😫😨AKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS, TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI🥂WATA DAYA CHAS ZA’AYI ANA KOYAN GIRKE GIRKEN. _*
_*KU SAKE KARANTA WANNAN BONUS DIN👇🏾RIGIJI GABJI_*
_*Nigeria @ 61 _*
_*COOKING COMPETITION!!!_*
_*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar_*
_*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS GA WANDA KE NESA_*
****************
Shiru Imran yayi Jin sunan NURU data ambata Yana nazarin abin cikin ransa sbd baya fatan samun wani kebantaccen lokaci dagashi se NURU Dan bazai iya riqe zuciyarsa ba,bazai iya danne kansa daga Mata tambyarda yaketa son Jim amsarta daga gareta Dan Dan kuwa zuciyarsa takasa amincewa ta yarda ba auren tilas neba akaiwa NURU Dan batada gata,
Yanason ji daga bakinta cewar ta aminnce da auren kokuwa haryanzu tana sonsa Dan a shirye yake daya qararda duk abinda shida mahaifinsa suka mallaka Dan ya kwatar Mata yancinta a warware aure abarta da Wanda ta zaba Dan Haka wannan alqawarinane duk suka hadu harsuka samu damar magana yanada burin sanin raayinta akansa da aurenta Duk da Haka baiso haduwarsu tazo ta wannan hanyarba Dan shi me kishine bazaizo NURUn taje irin wurin Nan ba duk da aikintane Amma baida niyar barinta Koda shine ya aureta ta ringa shiga irin wainann cases din.
Numfashi ya sauke tareda boyayyar ajiyar zuciya ahankali kafin ya bude Baki yace"
Ba damuwa zan bincika tafiyar inshallah zanyi kokari ko cikin Daren nan ne na taso ko gobe tunda safe kifada Mata.
Aje wayar yayi Yana sauke ajiyar zuciya da numfashi atare Yana rufe idanuwansa da Basu Gama dawowa daidaiba tun ciwon dayayi ya warke
Ya miqe tsaye Yana jefar da wayarsa kan kujera sbd wasu feelings dinsa da afia ke Shirin tado Masa kokuma Tama tado Masa shi akan soyayyar NURU data fara koyawa kansa dangana.
Afia kuwa tana aje wayar taji hankalinta ya Dan kwanta sbd tanada tabbacin mum dinta zata samu damar fara wata kyakkyawar rayuwar koba a gidan dad dinta ba tana Mata fatan samun rayuwa kwanciyar hankali da nutsuwa tareda sauyawa Dan kuwa wannan al'amarin daya faru babban darasine gareta.
Tana buqatan mgnar da NURU gashi ba waya hannun NURUn sai kawai ta fito da kanta zata nufi gurin NURUn tasamu tsaro a bakin sashinta tareda umarnin ba fita koina sai gobe.
Da mamaki ta kalli Wanda yake shugaban tsaron tace"
Daga Ina umarnin yafito?
Sauke Kai yayi cikin nutsuwa yace"
Daga gurin MALEEK.
Siririn numfashi ta sauke tareda hakura ta juya Takoma batareda tace komaiba sbd daga yanxu umarnin dad dinta abune me girma a rayuwarta da bazata iya tsallakewaba badan alfarwar da yayiwa mum dinta kawai ba hadda tabbatarwa datai shine komai nata samun mahaifi kamarsa sai antona.
Dawowa tayi ta nufi bedroom dinta Kai tsaye ta tube sai alokacin tasamu damar qwarin watsawa jikinta ruwa tanajin al'amarin ya warware Mata Inshallah.
Acikin Daren ranar Mr Omar yayi qwalailar bincikensa tareda yonasi wani jami'in tsaron maleek suka gano jaridar data fara wallafa labarin
Suka zurfafa binciken daya nuna Kai tsaye jaridar ta fitarda labarin ne tun qarfe shida na safiyar ranar alhalin ba'a Kuma maganar kisan Bata bayyanaba sai qarfe takwas na safe ma su maleek suka Isa gurin Kuma Basu Kira hukuma ba sai qarfe Tara hakan ke nuni da labarin yasamu masu jaridar ne kamar ma tun cikin Daren da abin yafaru kenan kafin afkuwar abin ma.
Da wannan aka Isa gidan jaridar Kai tsaye aka kama shugaban companyn zuwa headquarters Kai tsaye Maleek yabada umarnin rashin sassauci ga binciken mutumin Wanda dam jira suke su Kuma jamian tsaron suka hau gana Masa azabar data sakashi saurin bada bayani Nan take cewar wani ne acikin Daren yakawo Masa information din saidai baiga fuskarsa sosaiba.
Kallonsa commissioner din yayi Yana jinjina Kai yace"
Me kagani Wanda zaka iya tunawa game dashi Wanda zai taimaka Mana nemosa da kanmu?
Wahalallen numfashi ya sauke Yana hadiye yawunsa dasuka gama gauraya da jinin dukan da akai Masa yace"
Idanuwansa zuwa saman hancinsa sbd Yana sanyeda baqin nose mask.
Ajiyar zuciya commissioner ya sauke tareda Mr Omar Wanda dama Allah Allah yake su samu bayani me kyau dazai bada hujja me ma'ana ya kalli commissioner Yana cewa"
Zansaka aturo Mana Wanda zai Mana sketch yanzun Nan kafin safe nakeson agama inshallah.
Juyawa yayi ya fice commissioner yasa aka maida managern aka rufe Kafin a me sketch din yazo.
Daganan Kai tsaye Maleek Mr Omar yakira ya sanar Masa komai
Shiru MALEEK yayi na 'yan mintuna kafin ya Dan motsa tareda bude Baki yace"
Kaje da kanka gurin tareda wani me sketch din gurinta itama ayo na idanuwan Wanda yakai Mata meriz sai ahada agani Dan nasan mutum dayane sbd tabbatarwa.
Bayan Mr Omar ya tabbatarda anfara zana fuskar Wanda managern gidan jaridar yagani tukuna cikin tsakiyar Daren ya wuce delah Ana fitowa sallar asuba Yana sauka ya wuce Dan aiwatarda dayan aikin.
Qarfe takwas na safe afia ta Isa sashen NURU Kai tsaye bedroom dinta ta nufa har lokacin NURUn na bacci ta tashi ba saidai kasa hakurinda afia tayi yasa ta tada ita ahankali tana Kiran sunanta.
Bude ido NURUn tayi ahankali tana kallon afia dake tsaye tana kallonta cikin kulawa tace"
Sorry na tasheki
Ina tsananin buqatan taimakonki ne Dan Allah.
Da mamaki NURUn ta tashi zaune tana tattare gashinta ta dauki band gefen gadon ta daure gashin tana yaye bargonta tace"
Lafiya dai Ina ko??
Ajiyar zuciya afia ta sauke tareda juyawa ta nufi sofa ta zauna tana kallon NURUn tace"
Ki kimtsa tukuna sai muyi mgnar.
Zuro qafafunta qasa tayi tareda miqewa tsaye sanye cikin kayan bacci riga da wando masu santsi farare tas sun lafe jikinta ta nufi toilet tashige tana waiwayen afia akan tunanin ko wani abun yakuma faruwane.
Brush kawai tayi takasa wanka sbd hankalinta yafara tashi akan tunani da wasi wasin lafiya.
Tana fitowa Palo ta fito inda afia din Takoma ta zauna tana Dan kallon tv sama sama Amma hankalinta nakan yanda NURU zata karbi zancen saidai tasan yanada wuya takasa Mata wannan alfarman tunda aikintane.
Zama NURU tayi kusada afia din tana kallonta dukkanin hankalinta akanta tace"
Gani menene??
Numfashi afia tasake sauke akaro na biyu tana kallon NURUn cikin nutsuwa da nuna damuwarta da mahimmancin da maganar take dashi agurinta tace"
Maganar mum dinace yau nazo neman alfarma dama taimako agurinki,
Kinsan yanda nakeson mahaifiyata dakuma yanda nasamu wannan sassaucin yazo gareta, Dan Allah ko Zaki min alfarmar cika sauran formalities na karbota a matsayinki na lawyer duk da nasan Baki Gama zama cikakkiyar lawyer din ba Amma dai kinada damar zuwa.
Akaro na farko yau Ina roqonki wata alfarma Ina fatan Kuma Zakiyi sbd Ni Dan nasan abinda mum tayi Miki Bata cancanci ki taimaka din ba Amma Kuma Ina roqonki kiyi sbd Ni da farhat.
Tsit NURU tayi tana dauke wuta sbd Bata taba tunanin wannan maganar ba bama ta taba kawo tunanin shiga cikin wannan al'amarin ba gaba daya
Musamman na mum din afian Wanda shigarta kamarba bazai yiyuba sbd ba ita ke ikon kanta ba hakama ita tayaya zata iya zuwa Kai tsaye wannan aikin?¿
Kasa cewa komai tayi ta dago ta kalli afia batamasan me zata ce Mata ba Dan neman alfarma agurinta da afia tayi kamar abune da bazata iya cewa aa ba hakama Kuma tanajin shakkar amincewar sbd batamasan ta Yaya zata sanar da Wanda yake ikonta zancen.
Ganin Shirun NURUn yasa afia shiga damuwa takira sunan NURUn tana cewa"
Bazaki iyaba right???
Zubawa afian ido NURU tayi tana sake shiga tunanin rasa abin cewa ta girgiza Kai ahankali ta bude Baki tace"
Afia Babu alfarmar dazaki roqa gurina nakasa Miki matuqar Bata sabawa ubangiji bace saidai ta Yaya za'a sanarwa dadynki Kuma Kinga.....
Katseta afia tayi da cewa"
Dad dakansa jiya gabanki yabada damar komai gameda case din mum din wannan maganar ta sirrice yanzu idan nace zamu dauko lawyer daga waje then komai zai iya sauyawa
So please NURU ki amince dan Allah dad Bai taba dakatar damuba ko hanamu harkan data shafi karatu bare yanzu aiki Dan Allah ki yarda Ina roqonki.
Dagowa NURU tayi takalli afian tareda Dan sauke ajiyar zuciya tace"
Na amince Amma sai dad dinki ya amince Zan nema izininsa.
Shiru afia tayi tana kallon NURUn tana nazarin abin data fada din saidai tunda ta amince batada zabin daya wuce itama amincewa da bayanin tace"
Thank you.
Miqewa tayi zata fice ta dakata da cewa"
Anjima Imran zai iso inshallah saikuyi mgna.
Ficewa tayi tabar NURUn zaune mamaki na kasheta Jin da Imran zasu tafi kenan.
Faduwa gabanta yayi sbd tunani biyu dasuka shigeta take,
Na farko ta Yaya zata fadawa MALEEK maganar zuwan harda qarin Imran ne abokin aikin,
Ma biyu tayaya zata iya fita daga ita sai Imran bazata iyaba sbd tasan Imran din sai yayi kokarin tado Mata da maganarsu data wuce wadda hakan baya cikin abindata shirya dawowa dashi.
Bangare daya afia nason daureta da jijiyoyin jikinta.
Daqyar ta iya tashi daga Inda afian ta barta ta nufi bedroom tafada toilet jekadi dake jinsu batace komaiba ta juya ta fice daga sashen Kai tsaye ta nemi numbern Mr Omar ta fada Masa komai yace idan yadawo zai sanarda maleek.
Qarfe goma Sha biyu na ranar Mr Omar ya sauka a airport na gizah na dawowarsa Dan yagamo abinda yaje Yi Kuma adaidai lokacin Imran jalal ya sauka a airport din cikin sa'a suka hadu dukkaninsu motar masarauta tazo daukansu shi Mr Omar drivern maleek yazo daukansu shikuma Imran drivern Anneti afia tasaka yazo daukansa.
Kallon kallone yashiga tsakaninsu Mr Omar ya saki wani murmushi Yana miqawa Imran din hannu yana kallonsa yace"
Barka da zuwa Barr Imran jalal and all the best.
Miqa Masa hannu Imran yayi Yana cewa"
Thank you Mr Omar.
Murmushi Mr Omar yasake sakewa Yana Dan kallon gefen Imran din yace"
Kai kadai kazo??
I mean nasan kasan kana buqatan wani lawyern ga aikin.¿
Sai alokacin Imran yasaki murmushi Yana kallon Mr Omar din yace"
Aikina ne Kuma nasan da hakan shiyasa lawyern da nake buqatan muyi aikin tare tana Nan Dama
Fata dai kawai idan zaka iya jimirin ganin hakan.
Wani irin Murmushi me Fadi Mr Omar yasake Yana sake cewa"
Good luck with that too."ya juya ya wuce Yana sake sakin murmushi yashige mota aka jashi sukabar Imran din a tsaye Yana bin motar da kallo kafin ya sauke numfashi me zafi yashiga tasa motar da akazo daukansa suka wuce Suma Yana Jin tamkar zuciyarsa nason karbuwa da qiyayyar Mr Omar sbd koyaushe shine yake shiga hancinsa da kudundune Amma sbd qiyayya bata cikin abindayake Bari Yana shigarsa yasa yake yaqar hakan Yana dannewa sbd ya dauki qiyayya wani aikin wahala da kake dorawa kanka yazo Kuma ya ringa wahalar dakai ka rasa focus da sukunin rayuwa karshe ka wargaza kanka agurin qiyayyar wani.
Kai tsaye dukkaninsu masarauta suka nufo cikin sa'a kusan atare motocinsu suka iso Mr Omar ya wuce Kai tsaye sashen maleek daukeda sketch din dayazo dashi daga delah shikuma Imran afia ce da kanta ta bada umarnin kaisa sashen baqi na musamman kafin ya huta suyi mgn.
##MAMUH#
0 comments:
Post a Comment