Al'ameen da yake zaune a kan kujera yana kallonta yace..."ke dai yanzu kina son wannan abin dayawa".
Sai da ta sauke empty roban a bakinta sanna ta amsa mishi da..."wallahi yayana in bansha ba jina nake ba dai-dai nake ba kuma sai in rinka jina... "Turo k'ofan da akayi tare da sallama shiya dakatar da maganan da take.
Altine ce ta shigo d'akin d'auke da katon tray da warmers akwai ta ajiye a kan rug dake tsakiyan d'akin tare da gaishe su,amsa mata sukayi fuska a sake.
Fita ta k'arayi ta dawo da wani madaidaicin tray mai d'auke da tea flasks da plates da cups ta ajiye ta fice tare da rufo musu k'ofa.
Kama hannunta yayi suka sauka k'asa inda Altine ta jera musu kayan breakfast.
Al'ameen shi ya fara bubbud'e warmers d'in yana dubanta yace..." Me zaki ci in zuba miki?"
"Zuba min pepper soup d'in saboda bakina yafi son Abu mai yaji".
Zuba mata yayi a plate ta fara ci,shi kuma chips ya zuba suna ci suna hiransu.
Al'ameen yace..." Babyna wai kin fad'awa su Umma rashin lafiyarki kuwa?"
"Um-um " tace tana tura katon tsoka bakinta.
"mesa baki fad'a ba?" Ya bukata.
"Zan k'ira wayan Fateema anjima in fad'a mata sai ta gayawa Umma".
" Fateema kenan sarkin rawan kai bansan meya hanata zuwa gidanmu ba"yace yana murmushi.
Bata fuska tayi tace..." Hmmm tana son zuwa amma Abba ya hana dan ba abinda ya tsana kaman fita anguwa daga makaranta sai gida".
Gyad'a kai yayi yana ajiye tea cup dake hannun shi yace..." Abba yana da gaskiya cos 'ya mace sai da kula".
Bayan sun k'are cin abincin,k'wanciya yayi a cinyarta suka bud'e sabon shafin love.
Ameera tana wasa da gashin kanshi tace..."yayana ka manta maganan Alhaji ne?"
"Wanne magana kenan?" Ya tambaya yana b'ata fuska kaman mai tunani.
Dariya tayi tana ture kanshi akan cinyarta tace..."kasan abinda nufi tashi ka tafi office ".
Tashi yayi ya zauna suna facing juna ya rik'o fuskanta da hannayen shi yace..." Kora ta kike ko Babyna?"
Zaro ido tayi tana kallon shi tace..." Na isa in kore ka....."bata samu daman k'arasa maganan ba sakamakon had'a bakinshi da nata da yayi.
Sun jima a haka har yana k'okarin zarcewa Ameera ta k'wace kanta da k'yar tace..." Ka manta a gidanku muke?in Hajiya ta shigo ta same mu a haka fa?"
Yana gyara riganshi yace..." Ni nasan ba wanda zai shigo nan koda k'wana zamuyi a cikin d'akin nan".
Rau-rau tayi da ido cikin shagwab'a tace..." Yayana ka manta meya kawo mu nan ko sai kasa Hajiya ta koremu".
" hmmm wai ke wayo ko?gashi daga zuwa gidan Hajiya kin warke".
Ajiyan zuciya tayi tana kallon gefe tace..." Yayana ina su Aunty dash Fa'iza?"
Had'a rai yayi kaman wanda aka gayawa sak'on mutuwa yace..." Muna zaune lafiya shine kike son b'ata min rai ko?"
Matsowa tayi ta d'ora kanta akan kafad'an shi tace..."ba haka nake nufi ba kayi hak'uri dan Allah".
Rungomota yayi ta gefe ya fara magana..."ki yafe min Ameera akan abubuwa da suke faruwa a gida bansan me yake faruwa dani ba musamman in a gaban Lateefa ne sai in rasa ina kaina yake ga kuma wani shakkarta da nake ji ko kallonki bazan iya yi aganta ba,wannan abu yana matuk'ar damuna.ina son in kika k'ira Umma tazo ki fad'a mata su taya mu da addu'a nima zan fad'awa su Hajiya".
Hawaye na sauka a kan fuskarta tace..."abu d'aya muke fuskanta yayana Umma tana zuwa zan fad'a mata ta gayawa Abba ya taimaka mana da addu'oi".
Suna cikin magana Ya Sa'ad ya shigo yana yiwa Al'ameen tsiya wai Baban twins.
Shiko sai dariya yake yana amsawa da Allah yasa ya fad'a a bakin mala'iku.
Bai jima ba ya duba Ameera tare kad'a kan Al'ameen suka fita tare.
Bayan tafiyansu ne Ameera tayi dialling number Fateema,bai dad'e yana ringing ba ta d'aga tare da tambayan waye
"Ke dallah Teema nice fa" Ameera ta amsa mata a d'ayan b'angaren.
Ihu Fateema tayi cikin murna tace..." Sisto kece wayyo I missed u ina wayar ki take kika kirani da wannan?".
Dariya Ameera tayi tace.." Ke kar ki cika min kunne,wayar Al'ameen ce. meya hanaki zuwa in kinyi missing d'ina da gaske?kuma ko a waya in ban kira ki ba,ba kya kirana".
Marairaice murya Fateema tayi tana... " ya kike magana kaman baki san halin Abba ba?yanzu abin nashi ya kara gaba dan cewa yayi in muna yawan zuwa gidanki mutane zasu ce mun zuba k'afa a gidanki sabida k'wad'ayi munga mijiki mai kud'i,shiyasa baki ganni ba ".
" toh shikenan ki bawa Umma wayan " .
Fita tayi zuwa tsakar gida inda Umma take zaune tana gyara gyad'an miya,mik'a mata wayan tayi tace Ameera ce ta k'ira.
Karb'a Umma tayi bayan sun gaisa Ameera take fad'a mata abinda ya faru, nan tayi mata Allah ya sauwake tare da alkawarin zasu zo gobe su dubata ita da Fateema.
Cikin tsanin farincikin zata ga Ummarta ta tashi ta fito parlour wajan Hajiya kuma har tana aiyanawa a ranta matsalarta ya kusa karewa dan tasan Abba yana ji zaiyi wani abu akai.
*part thirty one*
A parlour ta iske Hajiya da wata bak'uwarta suna hira,durkusawa tayi har k'asa ta gaida bak'uwar sannan ta samu waje a kasa ta zauna.
Hajiya ta b'ata fuska tana dubanta tace..."ya zaki zauna a k'asa ki hau kan kujera ki zauna".
Batayi gardama ba ta hau ta zauna, ganin yanda Hajiya ta b'ata fuska.
Bak'uwar tana murmushi tace..." Hajiya bak'uwa kikayi ne bangane ta ba".
" asama'u kenan amaryar d'an auta nane baki gane ba?"Hajiya tace itama tana murmushin.
Wacce aka k'ira da Asma'un ta k'ara fad'ad'a fara'ar fuskanta tace..."Allah sarki itace wacce mukayi bikin k'wanakin baya ko?"
Kamin Hajiya ta bata amsa ta cigaba..." Ke yanzu kinga laifina ya za'ayi in gane ta tunda shi Al'ameen d'in kanshi rabon shida gidana sai ince yafi shekara goma bare matansa".
" kada ki damu zai kai miki su ku yini insha Allah " Hajiya tayi assurance d'inta.
Ameera dai tana jinsu bata ce komai ba saida Hajiya ta gabatar mata da matan a matsayin k'awarta ce tun suna secondary school.
Kasa sakewa tayi tare dasu dan haka bata dad'e da zama ba ta tashi ta koma d'akinta ta k'wanta.
Sai bayan shiganta ne Hajiya takewa Asma'u bayani game da Ameera,nan ta taya su murna tare da addu'an Allah ya raba lafiya.
Bayan sallahn azahar misalin biyu da rabi saiga Al'ameen ya kasa zaman office ya dawo gida.
Koda Hajiya ta fara mishi fad'an meyasa ya dawo lokacin tashi baiyi ba,marairaice fuska yayi yace zazzabine yake son rufe shi shiyasa ya dawo.
Sannu ta shiga jera mishi tace..." Ya sha paracetamol ya k'wanta ya huta.
Karb'an maganin yayi yana Jan k'afa shi a dole ga mara lafiya ya wuce d'akin Ameera.
Dariya Hajiya tayi tana girgiza kai tace..." Wai ni zaiyiwa dabara".
Sallama yayi ya tura k'ofan ya shiga,baki bud'e Ameera take kallon shi har ya maida k'ofan ya rufe.
Ajiye brief case d'inshi akan kujera yayi ya juyo yana kallon yanda ta sake baki tana kallon shi ga abinci a gabanta ta bud'e da niyan zubawa amma ta kasa.
Gabanta yazo ya tsuguna yasa hannun shi ya rufe mata bakin yace..." Rufe bakin mana 'yan matana".
D'an had'a rai tayi tare da kawar da kanta gefe tace..." Haba Yayana yaushe ka bar gidan nan da zaka k'ara dawowa,na lura so kake Hajiya ta kore mu a gidanta mu huta".
Rungumota yayi ta baya tare da kissing d'in wuyanta yace..."haka ake taran miji Babyna tunda baki saba gani a gida by dis time ba ai kamata yayi ki tambaye ni ko lafiya,ko kin manta tare muka fara laulayin ne in tuna miki?"
Kunya maganar shi ta karshe ya bata ta rufe idonta da hannu tana dariya,cakulkuli ya fara mata shima yana taya ta dariyan.
Saida suka gama wasannin su,sannan ta zuba musu abincin suka fara ci.sai zuba yajin daddawa da Hajiya ta aiko mata take tana ci har tana lumshe ido.
"Kasa yajin kaji yafi dad'i wallahi" tace tana k'ara zubawa a gabanta.
Girgiza kai yayi yana..." Um-um ci kayanki da alamu me kada'i Hajiya ta aikowa".
A ranan ma ba bai bar gidan ba saida Hajiya ta kora sannan ya tafi gida badan ranshi yaso ba.
Da washe gari misalin sha biyun rana Umma da Fateema suka iso gidansu Al'ameen duba Ameera.
Albarkacin hutu na k'wana 2 da tasamu a gidan Hajiya yasa tayi d'an dama-dama,raman da tayi shi kuma sun danganta shi da zazzabin da take.dan haka Umma bata kawo komai a ranta ba.
Hannu bibbiyu Hajiya ta sauke su,nan da nan Altine ta cika gabansu da kayan sanyi dana marmari.
Ameera dad'i kaman ya kashe ta yau taga Ummarta.
Bayan sun gaisa Ameera taja hannun Fatima zuwa d'akinta dan su d'an taba hira,suka bar Umma tare da Hajiya suna hira
Haka baje suna yi can Fateema tace.." Naji jiya kina complain akan zuwa gidanki Wallahi Ameera kullum ina son zuwa amma Umma da Abba suke hanani wai gaki da abokiyar zama kuma mutane zasu ce Dan kin auri mai kud'i shiyasa muka zuba k'afa gidanki tunda muna jinki a ways aiya wadatar".
"Ni dai tunda ita Umma tunda ita ba zuwa take ba ai ya kamata ke kina zuwa koda sau 1 a wata ne,amma zanyiwa Umma magana ana barinki".
Cikin jin dad'i Fateema tace..." Good sister".
Ameera tunda suka shigo d'akin take yunkurin fad'awa Fateema abinda yake cinta a rai amma ta kasa daga tayi niyya sai taji bakinta yayi nauyi,hak'ura tayi suka cigaba da hiransu.
Bayan sallahn azahar Umma ta shigo d'akin Ameera su d'an zanta kamin su tafi,nan ma Ameera tayi-tayi ta kasa fad'awa Ummanta komai tana ji tana gani sukayi mata sallama suka tafi.
Kuka tayi sosai bayan tafiyansu har saida taji kanta yana ciwo kaman ya rabe 2 sannan ta rarrashi kanta tayi shiru.
Tana magana cinkin ranta.. Wannan wani irin rayuwa ce ace ke da gidan mijinki ki koma tamkar baiwa?ita da za'a shawarceta sai tayi zamanta an an yafi mata zama a can,nan Hajiya tana kula da ita kaman k'wai ga uwa uba samun kulawan mijinta da take samu a koda yaushe sab'anin gidanta da ko ganinahi batayi sai dai ya saci k'afa yazo ya dubata tsakiyar dare.
K'iran sallahn la'asar da taji anayi yasa ta mik'e ta fad'a bathroom tayi wanka tare da d'auro alwala.
Saida ta tsaya ta d'an tsara make up dan bata son Al'ameen ya fahimci halin da take ciki.
Ta idar da sallahn la'asar amma bata tashi akan pray mat d'in ba tana zaune tana tunani Al'ameen yayi sallama ya shigo.
Suna had'a ido suka sakarwa juna murmushi.
" ya jikin Babyna?"ya tambaya a lokacin da yake zama a bakin gadon yana facing d'inta.
"Alhamdullilah da sauki " ta amsa mishi lokacin da take zama kusa dashi," ya aiki zance koya office zance?"
" huuh all d same ba sauki dan yanzuma gudowa nayi saboda aiki ya min yawa".
Haka rayuwar Ameera tayi ta gudana a gidan Hajiya dan yau satin ta d'aya da zuwa taji sauki sosai kuma ta murmure kaman ba ita ba .
Bayan sallahn la'asar as usual Al'ameen ya dawo daga office suna zaune suna hiransu Hajiya ta aiko tana k'iransu.
Ba b'ata lokaci suka iske ta a parlour tana zaman jiransu,waje suka samu suka zauna.
Hajiya ta tattaro hankalinta gare su kana tace..." Ameenu ina son yau d'in nan Ameera ta koma gida tunda taji sauki saboda bana son Lateefa ta fahimci abinda yake faruwa".
Kirjin Ameera ne ya buga da karfin gaske jin furucin Hajiya, ta saci kallon Al'ameen taga yayi k'asa da yana son sanar mata halin da suke ciki shima ya kasa cewa komai.
Hajiya ta juyo ga Ameera tace..." Ina son ki kula da kanki sosai in kin koma gida,kada ki kuskura kiyi sakacin da zata gane cewa juna 2 gare ki,ina son ki yawaita saka Mayan hijabai saboda wasu dalilai.kin fahimce ni ko? "
Kasa motsa labb'anta tayi saboda nauyin da suka mata dan haka da kai ta amsa mata.
Al'ameen shima kasa magana yayi,tace..." Kai ka tafi yanzu anjima da daddare zan kawo ta da kaina".
Amsawa yayi ya tashi jiki a mace ya koma d'akin Ameera dan d'auko hulan da car keyn shi.
Ameera bata motsa daga inda take ba Hajiya tace..." Tashi kije ki fara had'a kayanki kamin lokaci yayi".
Mik'ewa tayi sum-sum kaman wacce k'wai ya fashewa a ciki tabi bayan shi.
Hajiya taso ta fahimci wani abu amma ganin basuyi mata bayanin komai ba yasa ta kawar da zargin da yake ranta.
Pls masu korafi kuyi hakuri kubi novel din a sannu zaku gane wani sako name son isarwa.
[3/26, 7:05 PM] Nabeelah Shu'aib: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀
*~UKUBAR KISHIYATA
😭😭😭😭😭😭
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part thirty two*
Yana zaune a bakin gado yasa hannayen shi duka biyu ya rike kanshi dasu yana kallon k'asa.
Bud'e k'ofan da Ameera tayi shiya dawo dashi hayyacin shi daga duniyar tunani da ya fad'a,suna had'a ido kowannensu ya kakalo murmushi yake na son kawar da damuwa ga junansu.
Tsayawa tayi a bakin k'ofa ta hard'e hannayenta a kirji tace..." Ya naga ka zauna bayan kuma tafiya ya kamata kayi?"
Da hannu ya mata alama tazo,zuwa tayi a hankali ta zauna a gefen shi,kamo hannayenta tayi duka 2 ya rike cikin nashi yana kallonta da idanuwansa da suka rine da fari zuwa ja yace..." Ameera bana son komawarki gidan can nafi son ki zauna a nan ko in saya miki gidanki daban yanda zaki zauna cikin k'wanciyar hankali har Allah ya sauke ki lafiya,I tried to tell Hajiya amma bansan meyasa ba na kasa fad'a mata komai " ya karasa maganan cikin matukar damuwa.
Murmushi kwance a kan fuskanta take dubanshi tace..." Karka damu yayana tunda Hajiya tace in koma zan koma mu zauna nasan nan da d'an lokaci komai zai daidaita".
Har yanzu fuska ba fara'a yake kallonta ya fara magana..."gaskiya na riga na yanke hukunci baza ki koma gidan nan ba ".
Cikin muryan rarrashi da k'wantar da murya tace..." Kayi hak'uri in koma saboda kada Hajiya taga kaman mun tsaba umarninta,beside na fad'awa Umma na tabbatar zata taya mu da addu'a "haka tacigaba da tausan da kalamai da tasan zai k'wantar mishi da hankali har saida taga ta sama mishi natsuwa tare da danne nata damuwan,
ko kad'an bata yarda yaga wani abu a fuskan ta ba illah murmushi dake tashi a kyakkyawar fuskarta
Bayan fitarsa ta kama hada kayanta tana mai zubar da hawaye saboda tausayin kanta da Kanta take ji, dama ya ta kare kuma bare ace lateefa taji labarin juna biyu gareta? girgiza kai tayi ta cigaba da had'a duk wani abu nata.
Bayan sallahn isha'i Hajiya tasa ta a gaba suka kama hanyan gidanta zuciyarta sai dukan 3-3 yaje,a mota Hajiya sai k'ara jaddada mata ta kula da kanta har suka isa gidan .
A parlour suka iske Al'ameen da Lateefa suna kallo,hannu 2-2 Lateefa ta karbe su harda rungume Ameera a gaban Hajiya wai tayi missing d'inta.
Hajiya bata bar gidan ba saida ta had'asu tayi musu nasiha mai ratsa jiki wanda Lateefa yake shiga 1 kunne ya fita ta 1.
Bata wani dad'e ba a gidan ta mik'e dan ta koma gida, suma duk suka mik'e dan yi mata rakiya " koma ki huta Ameera keda baki gama warwarewa ba" Hajiya tace mata.
Ba tayi gardama ba ta koma ciki dama tana tsoron zama cikinsu bata san wani rashin mutuncin zasuyi mata ba bayan tafiyan Hajiyan.
Lateefa kuma ta k'asa take hararar Hajiya a zuciyarta tana zanyi maganinku duka.
Direct part d'inta ta wuce cikin sauri ta bud'e k'ofa ta shiga ta mayar ta rufe tare da jingina a jikin k'ofan,wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata data tuna yanzu wani hali zata shiga.
A nan ta zube tasha kukanta na tausayin kanta da kanta ta more da kyar ta rarrashi kanta ta mik'e zuwa cikin bedroom d'inta.
Wanka kawai tayi ta haye gadonta ta kwanta zuciyarta a cunkuse.
Da washe gari da sassafe ta tashi ta nufi kitchen kaman yanda ta saba,dama Lateefa tun cikin dare ta sanar da masu aiki dawowar Ameera kuma ta umarce su da su sakar mata aiyukan gidan.
Duk da Lateefa ta hana su bai hana Rabi fitowa dan taya taba saboda har cikin zuciyarsu suna tausaya mata sosai.
A zaune ta same ta a cikin kitchen d'in tana firen dankali, Ameera da saurinta ta karaso cikin kitchen d'in tana cewa "haba Rabi ba kya gudun laifina ya shafe ki?"
D'an tsagaita firan Rabi tayi ta d'ago tana kallonta fuskarta cike da fara'a tace..." nasan suna bacci a wannan lokacin balle inji tsorin zasu fito su same ni anan,dan haka ki k'wantar da hankali ki ba abinda zai faru sai alkhairi".
K'arasa shigowa ciki tayi tana jin hawaye na taruwa a idonta,kusa da ita tazo ta durkusa tace..." Nagode Rabi da taimakon da kike min a gidan nan,dame zan taimaka miki yanzu dan mugama da wuri?"
" d'auko d'anyan kifi a friji ki wanke min kamin in gama firan"tace tana cigaba da aikinta.
Murmushi kawai Ameera tayi ta juya zuwa deep freezer ta bud'e ta d'ebo su yanda tasan zasu ishi gidan .
Wanke su ta farayi a sink d'in cikin kitchen,k'arnin kifin ne ya fara damunta sosai har ya haddasa mata tashin zuciya lokaci d'aya,duk dauriyanta amma saida amai ya kwace mata ba shiri.
Rabi dake firan dankali bata san lokacin da tayi cilli da wukan hannunta ba tazo da gudu ta riketa tana yi mata sannu.
Da'kyar ta samu ya tsaya,wanke fuskanta tayi tare da kuskure bakinta tana maida numfashin wahala.
Akan kujera Rabi ta zaunar da ita tace..." Zauna anan bari ni zan karasa aikin".
Jingina tayi da kujeran ta lumshe ido saboda yanda take jin cikin ta yana wani irin murd'a.
Lemun tsami Rabi ta d'auko mata a frdge ta bata tace..."ki sha wannan zaki ji saukin tashin zuciyan.
Bata musa ba tasa hannu ta karba ta fara shan lemun.
Rabi kuwa duk Rabin hankakinta yana kanta,tana aikinta kuma ta na juyowa tana kallonta fuskarta d'auke da murmushi sakamakon ta riga ta gane cutar Ameera. Dan Rabi ba karamar mace bace a kalla zatayi 37 years a duniya.
Cikin ikon Allah Ameera taji saukin tashin zuciyan amma hakan baisa ta daina shan lemun ba saboda dad'i yayi mata sosai dan kwata-kwata bata jin tsamin saima wani zaki-zaki da taji lemun yana yi mata.
Suna aikinsu suna hira sai gashi sun gama cikin k'ank'anin lokaci.
Bayan sun zuzzuba a warmers Rabi tace..." Toh bari in tafi kar su shigo".
Godiya Ameera tayi mata sannan ta kama hanyan fita, har ta kai bakin k'ofa ta juyo fuskanta d'auke da fara'a tace..." Hajiya ina taya ki Murna ".
Da wuri Ameera ta waigo tana dubanta cike da fargaban me zata ce mata ta tako a hankali zuwa gabanta tace..." Murnan meye Rabi kike tayani dashi?"
Rabi bata daina murmushi ba tace..." Hajiya ga dukan alamu juna 2gareki".
Zuciyarta ne ya buga da karfi,ashe dai ana ganewa da ake cewa ta boye?
Baki na rawa tace..."yanzu kowa ya gani zai gane?"
Rabi ta fahimci damuwar da take ciki dan tace... " ki k'wantar da hankali ki ba mai ganewa a gidan nan tunda ba wacce ta tab'a haihuwa a cikin su balle su lura da canzawarki,ni kaina amai da kika yi a gabana shiya tabbatar min da hakan sai dai ina baki shawaran ki guji Inda suke ki nisance su sosai dukda dama ba wata alaka bace tsakaninku kinji?Allah zai kare ki daga sharrinsu kuma Allah ya sauke ki lafiya".
Nauyayyen ajiyan zuciya ta sauke tare da sakin fuskarta tace..."nagode Rabi Allah ya saka da alkhairi".
Komawa tayi cikin kitchen dan k'arasa sauran aikin ita kuma Rabi cikin sauri ta koma part d'insu na masu aiki.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀
*~UKUBAR KISHIYATA
😭😭😭😭😭😭
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part thirty three*
Kan dinning ta shirya musu kayan breakfast d'in sannan ta koma d'aki duk abin duniya ya isheta saboda yau tun tashinta bata sha mutumin taba wato fresh milk.
Duk da tasan fridge d'inta babu komai a ciki amma hakan bai hanata bud'ewa ba ko zata samu wani abun,ga mamakinta fridge d'in cike yake da fresh milk harda ice cream.
"Allah sarki Yayana" tace lokacin da ta d'auki roba 1 ta koma kan kujera ta zauna tana sha,tana jinjina mishi tasan shine kad'ai da wannan aikin kila dare yabi ya tanada mata abinda yasan tana matuk'ar bukata.
Tana gama sha ta d'auko burmemen hijabinta dogo har k'asa amma mai hannu ta saka ta fito parlour.
Suna kan table suna breakfast ta same su,durkusawa tayi har k'asa ta gaishe su.
A wulakance Lateefa ta amsa,Al'ameen ko d'agowa baiyi ya kalleta ba balle tasa ran zai amsa.
A tsawace Lateefa tace..." Ke dan ubanki ban hanaki zuwa inda mijina yake ba?sai ana magana ki kama sunkuyar da kai sai kace wata mutuniyar arziki"ta karasa maganan tana harararta.
Tsum- tsum Ameera ta mik'e tayi hanyan part d'inta.
Wata tsawar ta kuma daka mata..."ke ina zaki tafi kuma bayan ban gama dake ba?ki wuce part d'insu Fa'iza ki gyara musu kamin su dawo daga sch".
Al'ameen yana jinsu amma ko d'ago da kanshi ya kasa balle yayi yunkurin hanawa.
Part d'insu Fa'izan ta wuce ta bud'e parlour ta shiga, gani tayi duk sunyi kaca-kaca da parlourn komai a warwatse.
Cikin k'ank'anin lokaci ta kimtsa ko ina ya zama fes.
Cikin bedroom ta nufa shima da nufin kimtsata,tana bud'e k'ofan bata san lokacin da ta k'wala wata irin razanannen kara ba sakamakon abinda idonta ya gane mata.
Ihun da tayi shi ya dawo dasu cikin hayyacinsu ,a razane suka rabu da juna suka juyo suna kallonta.
Jikinta gaba 1b'ari yake,Fa'iza,Shamsiyya da wata sabuwar k'awarsu mai suna Binta ta gani tsirara akan gado suna murkususu.
Shamsiyya ta wawuro towel ta d'aura a lokacin da take saukowa daga kan gadon,ta nufo Ameera da ta kasa motsi ta sandare waje 1.
Wani gigitacen mari ta fara d'auketa dashi tana nunata da yatsa tana huci ta fara surfa mata ruwan bala'i.
Kan kace me sauran ma sunyi joining,nan suka taru suka nad'a mata na jaki.
Haniyarsu ce ta cika gidan har Lateefa taji ta iso wajan tana tambayan ko lafiya?
Shamsiyya tayi caraf tace..."Aunty ace karuwancin yarinyan nan yayi nisa kuma ta rasa inda zatayi sai gidan nan?"
"Ni Ku gaya min me yake faruwa nace?" Lateefa ta k'ara tambaya cike da k'osawa.
Binta ta matso gaba tace..."Aunty wanka fa muke yarinyan nan tazo tana lekamu".
Salati Lateefa tasa tana tafa hannu ta juyo ga Ameera tasa k'afa ta hamb'areta ta fad'i k'asa.
Bata tsaya yin tunani ko la'akari da me zaisa su many an 'yan mata shiga wanka tare ba.
Ta cigaba da bala'i..."dama kana ganin idonta zaka san tayi nisa a harkan lesbian, toh wallahi ba a gidan nan ba sai dai kije can ki nemi abokan shashancinki".tana magana bugunta sai da sukayi mai isarsu sannan suka k'yale ta dan Kansu.
Da k'yar ta iya jan jikinta dake mata ciwo ga uwa uba mararta daya kulle ji take kaman zai balle saboda azaba.
K'wanciya tayi cikin azaba da rad'ad'i tana ta juyo kuma tana tunanin alak'arta da Fa'iza da irin abubuwa da take mata,sai yanzu ta fahimci manufarta.
Godiya ta shiga yiwa Allah da bai bata nasara a kan ta ba har tasan wacece ita,ta gwammace ta dauwama a *UKUBAR* Lateefa da ta kasance a irin wannan halin.
Haka ta cigaba zancen zuci har baccin wahala ya d'auketa.
Har bayan 12pm Lateefa bata ga gilmawar Ameera ba yasa ta k'walawa Rabi k'ira tazo gabanta ta durkusa,nan take tambayarta ko Ameera tana kitchen?
Amsa mata tayi da... " a'a ban ganta ba Hajiya".
Wata k'atuwar ashar Lateefa ta lailayo sannan tace..." Tab lalle yarinyan nan ta rainani in har ban gyara mata zama ba,wata rana sai taci tuwo akaina".
Tana gama fad'an haka ta mik'e a fusace tayi part d'in Ameera, Rabi tabi ta da ido tana girgiza Kai cike da jimami.
A kan tiles ta same ta zube tana baccin wahala,ga fiskan nan ya kumbura suntum.
Ba imani balle tausayi Lateefa tasa hannu ta wanka mata lafiyyar mari kan kumburaren fuskanta.
A razane ta mik'e tana muzurai,suna had'a da Lateefa ta zube a wajan tana bata hak'uri amma hakan bai hana Lateefa zazzaga mata bala'in data k'waso ba.
Tasa kyarta tayi har kitchen d'in tana balbale ta da masifa kuma tace maza ta d'aura musu abincin rana.
Ko d'ago da kai ba tayi ta kalleta ba har ta gama ta fice.
Goge hawayen fuskarta tayi,ta fara kiniyan d'aura girgin.
Rice and stew tayi niyan girkawa dan haka duka 2 ta d'aura su lokacin d'aya,tana soya kayan miyanta da tasa kayan kamshi harda curry a ciki.
Ka min ta gama soya miyan saida tayi amai har sau 2 saboda yanda take jin curryn yana hawa mata kai.
D'an k'walin kanta ta cire ta rufe hancinta dashi,d'ayan hannunta kuma rik'e da lemun tsami tana tsotsa.
A haka ta gama musu girkin ta jera musu akan dinning sannan ta wuce part d'inta dan yin wanka.
Ruwan d'umi ta had'a ta gasa jikinta dashi,k'wanciya tayi lamo cikin ruwan tana jin dad'inshi ga mararta ma har yanzu bai daina ciwo ba.
Tana fitowa daga wankan mai kawai ta shafa tasa wata jallabiyar ta ash colour babu zancen k'walliya saboda an haramta mata shi a gidan.
Hijabi ta d'aura akan jallabiyan tayi sallahn azahar.
Tana idarwa tayi hanyan kitchen saboda wata zababbiyar yunwa da take ji,tana addu'an Allah yasa sun rage mata.
Allah ya taimake ta dan ta samu sun rage dayawa.
Sai dai kuma ba zata iya cin miyar ba saboda warin curry.
A plate ta d'ebi white rice tasa man gyad'a tare da marmasa maggi kad'an akai,albasa da attargu tasa a turmi ta d'an jajjagasu shima ta juyesu akan white rice d'inta ta zauna ci.
Sosai abincin tayi mata dad'i sakamakon sunfi shiri da abinci mai yaji yanzu dan haka taci dayawa.
Tana gamawa kuwa ta kama kiciniyar d'aura na dare,saboda tasan tana k'wanciya bacci zatayi azo ana masgarta a banza.
Bayan dawowarta daga gidan Hajiya kaman da wata 2 Fateema da ya kumbonsu suka zo mata yini kuma Allah ya taimake ta ranan Lateefa bata nan sun fita watsewarsu ita da Salees d'inta su Fa'iza ma basa nan dan haka lafiya lau suka wuni suna tafi.
A k'wana a tashi ba wuya dan yau cikin Ameera ya shiga wata na 7 kenan,amma duk gidan ba wanda ya sani in ka cire Al'ameen da Rabi.
Cikin ikon Allah cikin yabi jikinta da yake Allah ya mata baiwan diri da na Fulani dan haka su suka rike mata cikin .
Wata safiyar Wednesday Ameera tanan goge-goge a parlour,Mamarsu Lateefa tayi sallama ta shigo.
Lateefa cike da murna ta tare ta.
Ameera dak'yar ta kai k'asa ta gaisheta.
Fuska ba yabo ba fallasa ta amsa suka wuce part d'in Lateefa .
Ameera ajiye dustern hannunta tayi ta shiga kitchen dan had'owa Mamar Lateefa ruwa da abin motsa baki.
Cikin dauriya take komai sakamakon nauyi da cikin tayi mata.
Katon tray ta cika shi da drinks da snacks ta nufi part d'in Lateefa dashi.
Hirarsu suke suna k'wasan dariya kaman wasu k'awaye,Ameera tayi sallama ta shigo.
Tafiya take a hankali harta k'ataso tsakiyan parlour ta ajiye tray akan center table dake tsakiyan parlourn.
Tsiyaya juice d'in tayi a glass cup tazo gaban Maman Lateefan ta mik'a mata tare da k'ara mata sannu da zuwa.
Mik'ewa tayi da k'yar ta fice, duk akan idon Maman Lateefa ta k'asa cewa komai.
Bayan fitan Ameera ta juyo ga 'yarta tace..."wacece wannan ko sabuwar 'yar aiki kika samu?"
Dariya Lateefa tayi har rana rik'e ciki tace..." Mama kenan wannan Ai itace amaryar Al'ameen amma kinga yanda na maidta mai aikin gidana duk wani aikin gidan nan ita take yinsu na hana masu aiki...."
" me dallah dakata shasha"ta katse ta cikin tsawa.
Lateefa sororo tayi ta na kallon Mamanta ita kuma ta cigaba ..."Ai kuwa kece mai aikinta nata dan kina gab da zama 'far kallo a cikin gidan nan,ke da nake ganin ba wacce ta tako k'afana cikin 'yan matan da Allah ya bani sai me Ashe kuwa ba haka bane".
Turo bani Lateefa tayi tace... "Haba Mama keda na d'auka zaki tayani farincikin ina jiya kishiyata amma sai ki hau yi min fad'a akanta?"
Tsaki Mama tayi tace..." Baki da idone Lateefa, ba k'ya ganin abinda yake jikinta wannan kishiyar taking?"
Zaro ido tayi ta na kallon Mama tace..." Bangane ba,Mama me kika gani a jikinta?"
"Bud'e kunnenki kiji duk yanda akayi yarinyan nan ciki ne da ita".
[3/31, 3:03 PM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀
*~UKUBAR KISHIYATA
😭😭😭😭😭😭
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part thirty four*
Wata irin zabura Lateefa tayi ta mik'e tsaye tare da d'aura hannayenta duka akai tace..." Na shiga 3,dan Allah Mama da gaske kinga ciki a jikinta?"
" k'irata ki gani da idonki"Mama ta bata tabbaci.
K'wala mata k'ira ta farayi da dukkan karfinta.
A tsorace Ameera ta shigo ta zube a k'asa tace..." Gani
Aun..."
Katse ta tayi cike da karaji tace..." Mik'e daga tsugunen nan munafuka".
Yunkura tayi ta mik'e tsaye da k'yarta tana kallon yanda duk ta hargitse.
Wawuro hijabinta Lateefa tayi zata cire mata,Ameera tayi saurin rik'ewa tana..." Aunty ki hak'uri,me nayi ne?"
Lateefa bata ma jin me take cewa babban burinta ta cire wannan hijabin da bata rabuwa dashi dan ta tabbatar da maganan Mamanta.
Da karfin tsiya ta samu nasaran cire hijabin, ai kuwa cikin tagani ya d'an fito kaman an kifa k'warya.
Lateefa bata san lokacin da hijabin ya sub'uce ya fad'i a hannunta ba.
Mama tace..." Yanzu kinga zahiri ko?"
Wani mahaukacin mari ta d'auketa dashi wanda yasa har ta kifa a k'asa.
Binta tayi ta cigaba da dukanta tana taka cikin da k'afa tana sumbatu kala-kala kaman wata sabuwar kamu kana ganinta kasan bata cikin hayyacinta.
Mama da k'yar ta samu nasaran janye ta gefe tare da zaunar da ita akan kujera tana ta haki.
Ameera kuwa tuni ta fice daga parlour da rarrafe dan tsira da ranta.
Mama ta dubeta taga har yanzu bata dawo hayyacinta ba sai huci take,kamo hannunta tayi ta girgizata tace..."ke ki nutsu ki dawo hayyacinki kiji abinda zance miki,ba haka ake yi ba in kin kashe 'yar mutane fa?da sannu ake bin komai duk da kema kinyi sake sosai a zamanta a gidan nan da haka bata faru ba.karki damu tunda kina dani yanzu zan baki shawaran yanda cikin zai bare cikin sauki".
Sai a lokacin ta samu daman sauk'e nauyayyen ajiyar zuciya tare da gyara zama tace..."ina jinki Mamana ya za'ayi?"
"Aiki zaki k'ara mata yafi na yanzu,dan 'yan aikin nan da take ba masu wuya bane.abinda nake so sake shine duk kayan ku na wanki da guga ita zaku tarawa,ke harda sharan wannan tafkeken gidan naku ciki da wake karki tausaya mata kiyi haka zuwa sati 1,in baki ga wani cigaba ba kimin waya balle nasan za'ayi nasara saboda da alamu cikin k'arami ne".
Rungumeta Lateefa tayi tana murna da godiya mama tace..." Haba sai kace baki sanni ba?ba zamuyi sake gidan hutun ya sub'uce mana ba".
Nan suka cigaba da hirarsu wanda kusan gaba d'aya akan yanda zata Lateefa zata musgunawa Ameera ne.
Sai bayan a zahar tayi shirin komawa gida bayan Lateefa tayi mata goma na arziki ta rakota har parking lot.nan take fad'an har zata koma bataga su Fa'iza ba.
Nan Lateefa take shaida mata sun tafi rabon katin auren k'warsu Binta wanda za'ayi nan da 2weeks.
Sak'on a gaishe su ta bari wajan Lateefa tashiga mota driver ya maidata Gida .
Komawa cikin gida tayi tana ayyana sabon rashin mutuncin da zatayiwa Ameera.
Kayan sawanta dana Al'ameen sun kai kusan set 30 ta fito dasu tana kwalla mata k'ira.
Tana jan k'afa ta fito daga part d'inta zuwa cikin parlour inda Lateefa take jiranta ,tana shirin tsunguna taji an watso mata fuska.
"K'washe kayan nan kije ki wanke minsu tas sannan ki jira su bushe ki goge su duka a yau and bana son machine wash dan yana b'ata min kaya dan haka use ur hands and wash them" tace tana watson matso mugun kallo dan bata ki ace ta shak'eta su mutu ita abinda yake cikinta ba.
Tsungunawa tayi da k'yar tana tattara kayan saboda tunda Lateefa ta tattaka mata ciki take cin mararta yana mata wani irin zogi.
Haka ta fita dasu can compound d'in gidan zuwa bakin tap dan wanke su.
Mai wankin gidan yana ganinta ya taso da gudunshi da niyan karb'a amma ta dakatar dashi tace ya barsu ita zata wanke su da kanta.
Jikin shine yayi matuk'ar sanyi dan haka ya rasa bakin magana yaja gefe yana kallonta harta kai bakin tap tana shirin fara wankin da hannu kaman yanda aka umarceta .
Wajen maigadi yaje yana maida mishi zancen.
Girgiza kai yayi cike da jimami yace... "Yarinya 'yar k'arama da ita amma matan ba d'igon imani bata dashi take azabtar da 'yar mutane".
Driver yace..." Nifa laifin maigaidan nake gani tunda shi ya kamata ya tsawatar mata amma ya kasa".
Mai gadi ya girgiza kai yace..." Kai dai bari wannan lamari sai Allah tunda yasha sayo mata abubuwa yana bani ajiyarsu sai can cikin dare zai dawo ya karba".
"Hakane kam wannan abu sai Allah" inji mai wankin.
Ameera tana can tana tikan wankin tana zubar da hawaye tana kuma nadaman kin amicewa da shawaran Al'ameen na bata da yace zai saya mata gidanta daban taki gashi tunda ta dawo abin k'ara gaba yake.
Dan mugunta irin na Lateefa wasu kayan ma a wanke suke ta had'a dasu.
Haka ta gama ta shanyasu gaba d'aya akan igiyan shanya,sannan ta koma cikin gidan tace tagama.
Harara tabita dashi idon nan kaman zasu fad'o k'asa tace..."wallahi inna Cuba kayan nan naga jik'a-jik'a kika min,hmmm.." Yatsunta 2 ta had'a ta Mirza sukayi k'ara kana tacigaba" kema kinsan sauran ba said na fad'a miki ba tashi ki bani waje".
Harta ta tashi zata tafi tace..."yauwa sak'wara nake son ki mana duka gidan hard a masu aikin gidan nan".
Kasa magana tayi kawai kitchen d'in ta wuce kai tsaye ta d'auko manyan doya guda 3 ta kama fira, bayanta mararta duk sun rike sai azaba take ji,ga yunwa da take ji dan rabonta da abinci tun safe.
A haka ta had'a musu lafiyayyar miyan egusi da yaji ganyan ogu da cry fish ga naman rago,gidan sai kamshi yake.
Bari d'aya kuma doyanta data d'aura da d'an gishiri ya nuna.
Turmi da tab'aryata ta d'auko ta fara kirb'awa,tanayi tana tsayawa sakamakon azaba da cikinta da bayanta ke mata.
Haka Rabi ta shigo ta sameta ta Mike sharkaf da gumi.
Da sauri Rabi ta k'arasa tana..." Hajiya kawo in kib'a miki amma wannan rashin imanin yayi yawa ,Allah ya saka miki Hajiya wallahi koba dad'e koba jima Allah ba zai barta ba karshenta ba zai tab'a k'yau ba".
Zubewa tayi a k'asa tana juyi akan tiles d'in kitchen, Rabi tana kirb'awa amma hankalinta gaba d'aya yana kan Ameera sai hawaye take tana mata sannu .
Cikin ikon Allah kamin Rabi ta gama taji ciwon ya lafa,dan haka tazo tasa hannu ta fara tayata yin malmala suna zubawa a warmers.
Rabi tana hanata amma taki tace taji sauki shiysa.
Bayan sun kammala ta koma wajan kayan dan gogesu ta tatar da mai wankinsu yana aikin gogr mata su.
Nan ta nemi ya bar mata ta k'arasa yace bakomai taje bakomai zai k'arasa mata.
Bata koma cikin gida ba gudun kada Lateefa ta ganta ta shiga 3,dan haka can garden d'in gidan ta wuce ta samu waje ta zauna.
Sai bayan 9 ya gama gugan ta k'waso kayan ta shigo cikin gida, bakowa a parlor,wucewa tayi dasu d'akinta ta ajiye da safe ta bata.
Wanka ta farayi sannan tayi sallahn isha'i,da rarrafe ta k'arasa kan gadonta ta k'wanta tana maida numfashi.
Ko 30 mins batayi da k'wanciya ba taji cikinta ya fara wani irin murdawa na yunwa.
Ba shiri ta tashi ta nufi kitchen dan samawa cikinta wani abu.
Duk dube-dubenta bata samu komai ba a kitchen d'in,tana son d'aura ko indomie ne amma tana tsoron a kamata a kitchen a nad'a mata na jaki saboda tasan wannan shirin Lateefa ne dan in bata son taci abinci a gidan Sai tasa a k'washe abincin akai can layi ko kan soak away azubar.
Dawowa tayi d'akinta ta k'wanta,bata jima da k'wanciya ba taji motsin mutum a parlour ta.
Bata motsa ba daga kwacenta saboda tasan mutum 1 ne mai shigo mata d'aki a irin wannan lokaci.
Yanda ya ganta ya matuk'ar razana shi,da sauri ya k'araso ya hau kan gadon tare da sa hannu ya d'agota yana tambayarta meya sameta.
Da hannu ta nuna mishi cikinta da bayanta.
Kwantar da ita yayi ya fita da sauri zuwa parlour,ya samo mata ibomol cikin first aid box ya dawo ya same ta kaman yanda ya barta.
Tambayanta yayi ko taci abinci?ta amsa mishi da bata ci ba.
Fita ya k'arayi zuwa kaman 15mins Sai gashi ya dawo da plate a hannun shi cike da indomie sai tururi yake da alamu yanzu ya dafa shi,d'ayan hannunshi kuma rik'e da wani k'aton shopping bag ya ajiye a k'asa ya hau gadon.
D'agota ya jinginar da ita a jikinshi sannan ya fara bata abincin abaki,nan da nan ko ta cinye shi tas..
Ledan da ya shigo dashi ya b'ude,cake ne da sauran snacks zallah a ciki,shima ta hau ci hannu baka hannu k'warya,kallonta yake cike da tausayi saboda mutum yana ganin yanda take abinci zaka san yunwa ya gama cinye ta.saida taci mai isarta sannan ya bata maganin tasha.
K'wantar da ita yayi yana lapping d'inta kaman 'yar jinjira har baccin mai dad'i ya k'washeta.
Shi bai bar d'akin ba saida yaga baccinta yayi nisa sannan ya fita ba dan yaso ba ya ayyana abubuwa a ranshi.
[3/31, 11:33 PM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
😭😭😭😭😭😭
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*part thirty five*
Washe gari bata farka ba sai wajan karfe shida da rabi na safe.
Garau ta tashi ba ciwon mara dana bayan da take ji jiya,wanka tayi tare da alwala tayi sallah sannan ta fito aika-aikacenta da yanzu ya zame mata jiki.
Rabi ta iske a kitchen tana girki harta kusa kammalawa.
Da murmushinta ta k'araso tana mata sannu da aiki.
Bayan sun gsisa Rabi take tambayarta ya jikinta?
"Da sauki wallahi dan yau na tashi bana jin ciwon komai" tace tana murmushi.
"Alhamdulillah Allah ya k'ara lafiya ya raba Ku lafiya" inji Rabi.
Ta amsa da "Ameen".
Hannu tasa suka k'arasa aikin tare suna hira abinsu,dan yanzu Rabi ita zame mata tamkar k'awa.
Da ita kad'ai zata zauna tayi hira cikin k'wanciyar hankali.
Yau sati 1 kenan Lateefa take gallazawa Ameera dan cikin jikinta ya b'are amma shiru ba labari,sai ciwon mara da baya da kusan suka zame mata jiki amma tana shan ibomol da Al'ameen ya ajiye mata su a d'aki harda paracetamol sai taji sauki.
Ganin ba canji yasa Lateefa tayi shawaran k'iran Mama dan su canza shawara.
Can cikin bedroom d'inta ta shiga sannan ta k'irata,bayan sun gaisa take fad'a mata cikin yana nan bai zub'e ba.
" kada ki tada hankalinki ki turo min d'aya daga cikin k'annenki tazo in bata wani magani dana tanadar miki, da zarar ta sha cikin nan ba zai k'wana a jikinta ba"Mama tace mata cikin rarrashi.
Dariya tayi na jin dad'i tana jin ba wanda ya kaita sa'an uwa na gari.
"Yanzu zan turo Shamsiyya tazo ta karb'a".
Mama ta katse ta da ..." Yau zata zo bazaki bari sai gobe ba? Naga yanzu yamma tayi".
"Hak'urina ya kare Mama na k'osa inga babu cikin nan ajikinta dan haka zan iya jurewa zuwa gobe ba"tace tana huci kaman wata macijiya.
Suna gama wayan tayi dialling number Shamsiyya tace tazo bedroom d'inta ta sameta.
Cikin minti biyar ta shigo tace..."gani Aunty".
" zariya zan aike ki akwai sak'ona a wajan Mama ki karb'o min kuma pls karki k'wana duk yanda zakiyi ki dawo yau".
Shamsiyya tace... " toh ba zan k'wana ba saboda muma muna nan muna shiye-shiryen auren Binta".
Lateefa tace..."oh ashe auren ya matso ko?"
"Eh saura 5 days, bari inyiwa driver magana muje mu dawo da wuri" tace tana mik'ewa.
Dakatar da ita Lateefa tayi tace..." Kije ke kad'ai ba tare da driver ba saboda sirri ne ".
" shikenan Aunty saina dawo".tace tare da ficewa daga bedroom d'in.
Wani maganin gargajiya Mama ta bata cikin goran faro ta kawo.
Cikin tsananin murna Lateefa tasa hannu ta karb'a ta ajiye a gefenta sannan ta fara k'walawa Ameera k'ira.
Ameera tana jan k'afa ta shigo parlour saboda yanda cikin nata kullum yake k'ara girma da nauyi.
Maganin ta mik'o mata tace..." Gashi maganine shanye ki bani roban".
"Magani kuma Aunty? Lafiyata k'alau fa" tace tana shirin mik'ewa ta bar wajan.
Murmushin mugunta tayi tace..."wato bazaki sha girma da arziki ba ko?Ku rik'e min ita in bata".
Kamin ta rufe baki Fa'iza har ta iso inda take tana janta cike da mugunta dama yanzu ba wanda ya kaita jin haushin Ameera tunda ta kasa cimma burinta akanta.
Shamsiyya tazo tayi joining suka rirriketa,Lateefa ta taso da roban maganin a hannunta.
Cikin tashin hankali Ameera ta fara mata magiya kan taji kanta ta k'yaleta amma Lateefa ko d'igon imani babu a ranta balle tausayi burinta kawai shine taga ta b'atar da abinda yake cikinta ko hankalinta zai k'wanta.
Murmushine shimfid'e a fuskanta harta k'araso gaban Ameera tace..." Kada ki damu 'yar k'anwata,wannan magani da kike gani zai taimaka miku sosai wajan haihuwa kinsan ina ji dake bana son ki sha wuya shiyasa kika na nemo miki maganin da kaina".
Tana gama fad'an haka ta matse mata baki ta fara d'ura mata maganin su Fa'iza suna tayata suna dariya.
Basu k'yaleta saida taga goran ya zama empty sannan suka k'yaleta.
Gaba d'aya Ameera ta galabaita ta fita haiyacinta ido jawur take kallonsu,har yanzu basu bar mata dariyan ba.
Daddafa kujeru tayi ta mik'e da kyar tayi hanyan part d'inta tana layi,a ranta kuwa tana ayyana karshenta yazo bata cire d'aya cikin biyu maganin mutuwa ta d'ura mata.
Ba yanda zatayi sai dai taje ta jira mutuwarta.
Tana shigowa parlournta taji mskoshinta yacika da wani irin bauri da d'aci wanda ya haddasa mata tashin zuciya lokaci d'aya.
Da gudu tayi bathroom kamin ta k'arasa ta kece da amai mai tsanani kaman zata amayar da kayan cikinta.
Aman bai tsaya ba saida ta komai na cikinta ya fita sannan ya tsaya.
Shower ta sakarwa kanta sannan ta fito ta k'wanta akan gadonta tana kuka tana mik'awa Allah lamarinta a haka har baccin wahala yayi gaba da ita.
Pls manage dis.kuma masu complain akan Ameera Ku kara hakuri.
[4/1, 8:34 PM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀
*~UKUBAR KISHIYATA
😭😭😭😭😭😭
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*part thirty six*
Lateefa tana k'wance a parlournta ajan 3 seater cike da nishad'i take danne-danne a wayarta,kana ganinta zaka san tana cikin farinciki.
Number Aina'u tayi dialling tasa a kunnenta,fuskarta cike da annuri take cira ta d'aga wayan.
"B'atan hanyan kikayi ko kuma ince sai yau kika tuna dani?" Aina'u tace bayan ta d'aga wayan.
Dariya mai cike da farinciki ta k'washe dashi tace..."Besty yau ina cikin farinciki shiyasa na kiraki ki tayani farinciki "
" a haba! Meya faru ?bani insha mu taya juna murna"
"Hmmm Aina'u wai ashe wannan yarinyan munafurta ta take".
Cikin sauri Aina'u ta katseta tace..." Wace yarinya kuma?"
Lateefa saida taja numafashi tace..." Wannan tsinannaiyar Ameeran nan mana ashe ciki ne da ita".
Zumbur Aina'u ta mik'e daga zaune dafe da kirji tace..." Me kika ce Lateefa,ya akayi kikayi wannan saken har hakan ta faru?"
K'ara gyara k'wanciyarta Lateefa tayi sannan ta bata amsa..." Bar shegiyar yariyan nan b'oye cikin tayi ban tashi sani ba saida Mama tazo gidan nan ta ganta,dan munafurci kullum hijabi take jurmuk'awa..."
Da sauri Aina'u ta katseta..."yanzu wani mataki kika d'auka ko shine abin farinciki da kika k'ira ki gaya min?"
" ke dad'ina dake gajan hak'uri"Lateefa tace mata tana dariya.
"Uhum ina jinki,zuciyata ce take tafasa shiyasa kika ga na kasa hak'uri" Aina'u tace mata.
Lateefa saida ta k'ara dariya sannan tace..." Bazan iya k'watanta miki tashin hankali dana shiga ba a wannan lokacin,idona rufewa yayi na hauta da duka ta ko ina.da k'yar Mama ta k'wace ta,tace min ba haka make ba ta bani shawaran kara mata aiki masu wuya zuwa sati,nayi ta d'aura mata amma ba nasara shine yanzu ta aiko min da wani jiko muka d'ura mata wanda Mama ta tabbatar min ba zata k'wana dashi a jikinta ba.farinciki ne ya cika ni shiyasa na kiraki ki tayani murna".
Dariya mai kama da shewa Aina'u tayi tace..." An gaishe da Maman Mu,sai yanzu naji hankaluna ya k'wanta,yanzu tana ina?"
"Tana can d'akinta tana fama da kanta"Lateefa ta bata amsa.
Aina'u tace..." Bari in k'ara miki wata idea nima,ki kula da takunta da zarar kinga ta fara labour sai kiyi amfani da wannan chance d'in ki k'arasata kowa ya huta.kuma ba wanda zaiyi doubting d'inki dan kowa cewa zaiyi ta mutu a wajan haihuwa".
K'yalk'yalewa tayi da dariyan jin dad'i tace..." Gaskiya yayu Besty shiyasa nake ji dake".
Sallama sukayi ta ajiye wayan bayan Aina'u ta k'ara mata evil ideas .
Fa'iza da Shamsiyya sun saka Binta a gaba suna ta kuka wiwi wai a dole sunyi rashin masoyiya.
Binta tazo ta rungumesu tana rarrashinsu tace"haba Ku daina bata hawayenku kusan auran nan zanyi ne Kawai ba dan ina so ba kawai saboda matsayinshi yasa zan aure shi ku tuna fa major general ne fa? kunga akwai naira da zamuyi abinda muka ga dama bayan haka kuma alakarmu tana nan ba abinda zai canza kunsan nima ba zan iya rayuwa ba ku ba dan kun zama jinin jikina".
"Shamsiyya tace..." Are u sure?"
" off course yes"ta tabbatar musu.
Cike da farinciki suna shiga shasshafata tare da sauran abinda ba zan iya tsaya in gani ba balle in d'auko muku.
Ameera bata tashi a baccin wahala da take ba sai wahan 8:39pm.
Tana farkawa tajita jakam a jik'e.
Cike da tashin hankali tayi yunkurin mik'ewa amma ta kasa,ji tayi kaman an kulle mata mara.
Komawa tayi ta k'wanta.
A tsorace tasa hannunta a hankali karkashinta inda take jin danshin.
Hannunta har rawa yake saboda tsaban fargaban me zata gani.
Wani ruwa mai yauk'i ta gani had'e da jini yana bin k'afanta.
Kuma ne mai karfi k'wace Mata mata,ta rasa wani irin tunani zatayi.
A duke tana bin bango har ta shiga cikin bathroom zama tayi dirshan akasa tana kallon ikon Allah,jinin dai ya tsaya amma ruwan bulbulowa yake kaman an bud'e famfo.
Bata san ma ta ina zata fara ba shiyasa tayi zamanta,sai kusan 9:45 ta samu ya tsagaita zuba,da k'yar ta mik'e tayi wanka ta fito tare da canza kayanta ta k'wanta tana jiran hukuncin Allah.
Azaba take ji kota ina ga abin cikinta nata da yake k'ara damunta da motsi.
Juyi take tana hawaye ba mai taimakonta,sai bayan karfe biyu da rabi na dare sannan ta samu wani wahalallen bacci ya d'auke ta.
Tana ta zuba ido ko Al'ameen zai shigo amma har tayi bacci ba labarinshi.
Koda same da ta tashi ciwon da take ji ya d',an lafa saidai ruwan ne bai tsaya ba...
Zamanta tayi cikin bedroom d'inta ko parlournta bata lek'a ba balle tayi gigin fita aiki.
Tana nan zaune ta fara jin motsi a parlournta,zuba ido tayi tana jiran taga ko wayene saboda tasan Al'ameen ko kallonta bai isa yayi ba balle har ya kaiga shigowa part d'inta.
Zuru tayi tana kallon k'ofan shigowa bedroom d'inta.
Turo k'ofan akayi aka shigo.
Lateefa ta gani tsaye a bakin k'ofan da murmushi akan fuskarta.
Tsoro k'arara ya baiyana akan fuskan Ameera ganin Lateefa yau har cikin bedroom d'inta, ta san dai alkhairi ba zai tab'a shigowa da ita ba sai dai akasinta .
K'arasowa tayi gabanta tana kallon ta har yanzu da murmushinta.
"Ya jikin 'year k'anwata?" Tace lokacin da take tsugunawa a gabanta .
Da k'yar bakinta ya iya cewa "da sauki".
" ina da ina ke miki ciwo"ta tambaya still wit her smiling face.
Da hannu ta nuna mata cikinta da bayanta.
Matsowa ta k'arayi gabanta taxa hannu ta danna mata mara da iya karfinta har saida tayi k'aran azaba tace..." Nan ko?"
"Sannu kinji,ina son in kika ji ciwon ya k'aru ki min magana mu tafi hospital ko?"
Gyad'a kai tayi kawai dan batada bakin magana.
Mik'ewa tayi tare da nufan hanyan fita.
D'an dakatawa tayi ta waigo tace..."ina parlour in kina nema na".
Tana fad'an haka tasa kai ta fice.
Wayarta ta lalubu da yake gefenta da niyan k'iran Ummanta ko Al'ameen dan su san halin da take ciki sai dai Nash ashe wayar ba kota flashing.
Cilli tayi da wayan a tsakar d'akin har komai na wayan ya tarwatse saboda haushi wayar ma ya bata.
Daga bata kuma taga in wayar tana kunne kila Al'ameen ko Fateema wani ya neme ta a cikinsu.
Yunkura tayi da niyan d'auko wayarta dan ta had'a amma ta kasa motsa koda kafartane .
Hak'ura tayi ta kwanta tana jiran mutuwarta .
Motsi ta kara ji a parlournta kuma yanzu cikin sand'a.
Hakan ba k'aramin taxa mata hankali yayi ba,kar dai Lateefa ce ta k'ara dawowa dan ta k'arasata.
Zubawa kofa ido tayi tana jiran taga mai shigowa.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀
*~UKUBAR KISHIYATA
😭😭😭😭😭😭
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*part thirty seven*
K'ofan taga an turo a hankali wanda ya k'ara mata tsoro da fargaba da take ciki.
Rabi taga ta lek'o da kanta itama a tsorace.
K'arasowa tayi da sauri ganin Ameera a yashe a tsakar d'akin tana..." Subhanallahi 'yar nan jikin ne haka?ni dama tunda safe da ban ganki ba hankalina yaki k'wanciya.ina son shigowa in dubaki amma tsoron Hajiya ya hanani shigowa,yanzuma wannan mutumin nan da suke yawan fita tare shiya zo suka fita shiyasa nayi amfani da wannan daman na shigo dan duba lafiyarki.ashe haka jikin ya k'ara tsanani?"
Ameera kawai sauraronta take dan bakinta ya kasa furta komai.
Rabi tace..." Yanzu ina yake miki ciwo?"
Da k'yar ta bud'i baki tace..." Rabi cikina bayana zai karye,Rabi zan mutu ki k'ira min Ummata"
"Ba zaki mutu ba Hajiya alamun nak'uda nake gani a tare dake, Sai dai kaman lokacin haihuwar da saura.ko kuma jirani ina zuwa" tana fad'an haka ta fice da saurinta.
Bata tsaya a ko ina ba sai wajan Baba mai gadi,tana zuwa bata b'ata lokaci ba ta sanar dashi halin da Ameera take ciki.
Nan da nan yacewa Rabi ta kawo ruwa ya mata addu'a in dai haihuwa ce toh da izinin Allah ba zata dad'e ba zata haihu,in kuma wani abinne daban shima da izinin Allah zai zo mata da sauki.
Da gudu Rabi tayi cikin gida tazo da ruwa a cup ta mik'a mishi.
Shima kamin ya tazo yayi Alwala yana jiranta.
Tana bashi ruwan ya zauna ya fara addu'oi yana tofawa a cikin ruwan.
Ya d'auki lokaci mai d'an tsawo kamin ya gama ya bata yace...
"Gashi in kinje ki zaka k'ankara a ciki yayi sosai a bata tasha da bismillah.
Godiya Rabi tayi mishi sannan ta koma cikin gida da saurinta,saida ta saka k'ankara yayi sanyin sannan ta kaiwa Ameera tasha.
Abinci ta kawo mata ta tilasta mata taci kad'an.
Zama tayi kusa da ita tana mata hira samama,zuwa kaman 40 mins Ameera harta manta da wani da take ji,suka kama hira sosai harda dariya.
Rabi taji dad'in yanda taga ta watsake haka tace.." Uhum Hajiya hiran ba zata k'are ba kuma tunda naga ciwon ya d'an lafa bari inje in d'ora girki".
Sai a lokacin Ameera ta tuna ashe fa bata da lafiya..." Rabi wallahi na daina jin komai wani irin magani kika bani nasha?"
Baba Bello ne ya miki addu'a a cikin ruwa na kawo miki,ko a kauye mutane suna tururuwa wajan karb'an ruwan addu'a a wajanshi kasancewar k'auyenmu d'aya dashi shiyasa na sanshi".
Ameera tace..."Allah sarki Baba,Rabi dan Allah ki fara mik'a mishi sak'on godiyata kamin inje da kaina".
Yunkura Rabi tayi ta tashi tana.." zaiji insha Allah".
Tana fita Ameera itama taja jiki ta tashi ta fad'a bathroom tayi wanka dan ta k'ara jin dad'in jikinta.
Rama salloli da ake binta ta farayi sannan ta kimtsa ta fito kitchen wajan Rabi wacce harta kusa gama aikinta.
Kallonta Rabi ta tsayayi saboda mamaki can tace.." Haba Hajiya ya zaki fito?aida zamanki kikayi saboda na kusa kammalawa".
Murmushi Ameera tayi tace.."aiko da wanke-wanke zan taya ki".
"Barshi ki koma d'aki kada tazo ta iske ki anan, kuma karki bari tasan kin samu sauki kiyi k'wanciyarki ki na k'wana 2.ina tsamanin matsalar da ya sameki yana da nasaba da aikin wahala da kikeyi".
Ameera bata musa mata ba ta amsa da " toh " ta koma part d'inta.
Rabi tana gama girki ta zubawa Ameera a warmer ta kai mata har bedroom.
Bata fita a d'akin ba saida ta tabbatar da Ameera taci ta koshi sannan ta k'washe kayan ta fita tana k'ara jaddadawa Ameera tayi k'wanciyarta kuma tayi yanda tace mata dan tasan yanzu duk yanda akayi Lateefa tana kan hanyar dawowa,sabida duk tsiyarta bata yarda Al'ameen ya rigata dawowa.
Rabi tana fita idonta ya kai kan wayarta da yake tarwatse a tsakiyar d'akin.
Da sauri ta d'auka ta had'a shi ta kunna tana Allah sarki Yayana nasan ya neme in bai samu ba.
Kunna wayar tayi ta ajiye a gefenta tana kallon yanda a in cikinta ya isheta da motsi,hannu ta kai tana shafawa da murmushi a fuskarta.
Wayanta ne ya katse mata abinda take,wayar ta jawo tarw da receiving call din.
Sallama tayi tana murmushi kaman yana ganinta.
Lumshe ido Al'ameen yayi tare da ajiyan zuciya tace..." Haba Babyna kin kusa zautar dani yau,kinsan zan kiraki Dan inji lafiyarku shine kika kashe min Waya?kodai wani laifin nayiakayi min irin wannan horon mai tsanani a haka?"
Bata katse shi ba harya kai aya sannan ta bashi amsa da..." Ko d'aya Yayana ai kai haka laifi a wajanmu just dai na manta ne ban kunna way an ba".
Nan suka cigaba da hiransu kaman basu da wata matsala a rayuwa.
Lateefa cikin sauri take driving cos a yanzu babban burinta shine taje taga wani hali Ameera take ciki.
Yau kwata-kwata bata so ta motsa ko nan da can ba saboda tana son yin amfani da shawaran Aina'u tana fara haihuwan ta karasata kowa ya huta.
Sales shiya hura mata wuta a Waya kan dole taje su had'u wai yayi missing d'inta,da taso yi mishi gardama amma ganin ranshi ya back yasa ta hak'ura tabi shi badan komai ba sai dan bata son bacin ranshi.
Tana shigowa cikin gidan direct part d'in Ameera ta nufa tana aiyana abu iri-iri a ranta.
Da d'an fargaba ta tura k'ofan ta shiga.
Ameera suna cikin waya da Al'ameen taji motsin mutum a parlournta.
Kashe wayan tayi gaba d'aya ta tura shi can kan gado sannan ta rungume cikinta da hannu 2 tare da runtsr ido ta fara murkususu.
Lateefa saida taji zuciyarta ta bada *DUM* ganin har yanzu da sauran ranta kuma nataccen cikin nata yana nan bai b'are ba.
Sai dai ta wani side d'in taji sanyi a ranta tunda da alamu bata ciki. hayyacinta.
D'an dariya Lateefa tayi na jin dad'i sannan tasa kai ta fice.
Ameera bata juyi da murkushe-murkusen ba said a ta tabbatar da Lattefa ta sannan ta mik'e zaune Rana murmushi saboda taji dadin shawaran Rabi.
Lateefa tana fita part d'inta ta wuce.
Bayan ta rage kayan jikinta ta zauna a bakin gado tare da kitan Mamanta.
Bayan sun gaisa Lateefa ta bata abinda ya faru tunda daga ranan da suka mata maganin har zuwa yanzu da ta fito a d'akinta.
"Ba wacce maganin nan ciki ya zauna a jikinta,ba dai kince bata cikin hayyacinta ba?" Mama ta tambaya.
Lateefa ta bata amsa da "eh"
Mama tace..."ki bata kwana 2zai zube ".
Cikin jin dad'e Lateefa tace " shiken nan Mama nagode"
" INA k'anenki ne yau kusan kwana 4ban jisu a Waya ba"
"Suna can wajan shiye-shirye bikin kawarsu"
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀
*~UKUBAR KISHIYATA
😭😭😭😭😭😭
(Its all about love and betrayal)
*Story by*
*UMMEE YUSUF*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*part thirty eight*
Suna gama waya da Mama ta fad'a bathroom hankali k'wance tayi wankanta tare da tsantsara make up ta zauna jiran Al'ameen ranta fari sol.
Al'ameen bai samu daman shiga part d'in Ameera ba sai wajan karfe 2 na dare.
Tana tsakiyan baccinta ya shigo.
Yaye bargon yayi shima ya shiga ya k'wanta tare da k'ara lullube su.
Jawota yayi jikin sosai ya rungume ,sai faman shinshinata yake kaman wani sabon maye.
Bud'e ido tayi ta ganshi mak'ale da ita,kara shigewa jikin shi tayi dan sunyi missing d'in juna.
Al'ameen dama kaman jira yake ya shiga aika mata da sak'oni,shi bai barta ba sai suka farantawa juna rai.
Daga nan suka shiga hirarsu cikin k'wanciyar hankali, bai bar d'akin ba sai da ya tabbatar da ta koma bacci sanna ya koma part nashi.
Haka Ameera tacigaba da zamanta a cikin d'aki ko parlourta bata fitowa sai dai taci tayi wanka ta kwanta.
Lateefa bata daina mata sintiri a d'aki ba,wai ko zata ga tana labor ta k'arasatan.
Ameera itama tana jin motsinta zata fara murkususun k'arya,ba zata daina ba har sai ta fita.
Wannan abu yana yiwa Lateefa ciwo ace yau kusan sati da bata maganin amma ciki yaki ya zube,kuma da zarar tayiwa Mama complain sai tace ta k'ara hakuri zuwa k'wana 2n da Lateefa bata son ji dan haka tayi niyyan d'aukan mataki da kanta.
Yau Saturday yazo dai-dai da ranan d'aurin auren Binta da mijinta Major General Ibrahim Hassan.
Su Fa'iza sun kai sati da tarewa a gidansu Binta kasancewarsu manyan k'awaye.
Lateefa tayi shirinta tsab na zuwa bikin,tasha ky'au cikin purple shaddanta with purple veil in short komai purple tayi amfani da shi.
Sai dai Kasan zuciyarta ba bikin bane dalilin fitanta,so take daga can ta wuce su had'u da bestynta ta bata shawara akan Ameera da d'an cikinta dan yanzu ta gaji da ganinta haka gara ayita ta kare.
Ameera tana jin fitanta ta fito main parlour tayi zamanta dan rabonta da fitowa tun ranan da Lateefa da kannenta suka d'ura mata magani.
Lateefa bata wani jima a gidan bikin ba ta wuce Neman Aina'u.
Numbernta tayi dialling kusan 3 missed call ta bata kamin ta samu ta daga wayan tana magana da k'yar tace" Besty ya akayine?".
A zuciye Lateefa tace.." Wai a ina kika ajiye wayan ina ta kira baki d'aga ba?"
Hak'uri Aina'u ta bata tace tana tare da Alhajinta ne yanzun amma ta bata nan da 15 mins zata fito Sai su had'u a at home restaurant.
Ba b'ata lokaci Lateefa taja motantan sai can,sai dai bata fito ba ta zauna a cikin motorn tana jiran isowarta.
Kaman yanda ta fad'a ba tafi 15 mins tana jiranta ba ta iso wajan cikin adaidaita sahu.
Fitowa itama tayi suka shiga ciki tare da samun wuri suka zauna.
Suna zama Aina'u tace.." Kinga ni yunwa nake ji,kiyi mana order abinci".
Tabe baki Lateefa tayi tace..."ke kike ta abinci saboda dani matsalata daban ta kawo ni nan amma kiyi order duk abinda kike so akawo miki".
Abinci mai rai da lafiya tasa aka kawo mata ta fara ci.
Aina'u ba tayi magana ba sai da tayi kusan rabin abincin sannan ta d'ago da kai tana kallon Lateefa data zuba mata na mujiya tana kallonta.
"Menene matsalar taki Hajiya?"
Sauke tagumi tayi tare da sauke ajiyar zaciya tace..." Kema kinsan baya wuce maganan yarinyan nan cos ita kad'aice matsalata a yanzu".
Aina'u batayi magana ba sai da ta gama shanye juice d'in da ta d'ora a bakinta sanna ta fara maganan.
"But I think mun gama da chapternta tun last week,ko wani abine ya bullo bayan shi?"
"Shi d'inne Aina'u,taki haihuwan balle in samu daman aikata abinda nayi niyya.ga cikin shima yaki lalacewa sai dai kullum tana d'aki tana murkususu".tace cike da damuwa.
Tunda ta fara Aina'u take kallonta,bata katse ta ba sai da ta kai aya sannan tace.." Wallahi kina bani mamaki yanzu ,Lateefa kaman ba kece mai bani shawara ba da komin saukin abu yanzu sai ki kasa samun bakin zar....."
Katse ta Lateefa tayi da..." Ke ni dan Allah ki bar surutun nan ki bani shawara insan abinyi dan ni kaina ya kulle na rasa wani irin tunani zanyi".
Aina'u saida ta numfasa tace..." Abune mai sauki Besty tunda kina da kudi,abinda zakiyi gobe ki samu private hospital mai k'yau ki kaita a matsayin kin kaita haihuwa daga nan ki samu babban doctor ki lallab'ashi ya mata alluran da zata shek'a kowa ya huta".
Zaro ido Lateefa tayi tana kallonta tace..."Aina'u so like asirina ya tonu?wani doctor zaka kaiwa wannan babban al'amari ya saurare ka?"
Aina'u cikin k'wanciyar hankali take cin naman kaza dake gabanta tace..." Dad'ina dake saurin karaya,a duniyan nan wa zaik'i kud'i?millions zaki bashi nasan tabbas da gudu zai share miki hawaye nima zan shigo goben sai mu kaita tare,kada kiji wani abu saboda inaji a jikina matsarki tazo karshe".
Haka tayi ta bata shawara tare da karfafa mata guiwa harta amince sannan suka rabu akan sai gobe ta iso.
Sai bayan 5:39 Lateefa ta dawo gida, ko ta kan Ameera ba tabi ba tana jiran wayewar gari su aikata barza'u.
Ameera cikin baccinta ta fara mafarkin tana jin wani azaba a mararta tun tana daurewa har ta fara juyi na azaba.
Wani irin juyi taji cikinta yayi wanda yayi sanadiyar farkawanta ba shiri,kuma sai a lokacin ta tabbatar ashe ba mafarki bane a zahiri take ji ga jikinta duk ya b'aci kaman na lokacin da Lateefa suka d'ura mata magani.
Addu'a ta farayi tana hawaye tana cewa a ranta inama ace rana ne da Baba mai gadi yayi mata tofi ta sha ko zata daina jin wannan azaban.
D'ago kai tayi tana kallon wall clock dake manne a d'akinta taga 1:30 na dare.
Tun tana hawaye tana add'uoi har hawayen suka kafe bakin ma ya mutu murus saina zuci da take.
K'ara kallon agogon tayi taga 2:00 ne kawai.
Cikin wani wahalalen murya tace " wayyo Ummata ki yafe min nasan yau mutuwa zanyi.
Gumi duk ya wanke mata jiki kaman ba a.c a d'akin.
Ita kanta ta tabbatar ciwon yau da take ji ya nika wanda da take ji da nikin ba nikin.
Har karfe uku da rabi tana nan zaune ko k'wanciya ta kasayi balle wani abu wai shi bacci gashi yau Al'ameen bai shigo ba da ya taimaka mata.
A lokacin ne kuma taji fitsari ya cika mata Mara.
Yunk'ura tayi da niyan tashi amma ta gagara da haka da rarrafe ta k'arasa bathroom danyin fitsarin amma abin mamaki ta kasa tsugunawa.
Zamanta tayi dirshan a cikin bathroom d'in tare da mimmike k'afa.
Yunkura tayi da niyan fitsarin amma taji wani abu daban da bata san dame zata k'watanta shi ba yazo ya danne ta ga wani azaba da tunda tazo duniya ko labarin shi bata tab'a jiba take ji.
Fasa fitsarin tayi tana yarfe hannu ta rasa ina zata saka ranta taji sanyi.
Sau uku tana gwadawa amma sai ta kasa na hud'une taji wani nishi mai karfi yazo mata wanda saida ta toshe baki da hannu dan ji take kaman ta k'wala ihu saboda zaba.
Maimakon taji tayi fitsari sai jin wani abu daban tayi ya fad'o harda kuka.
A firgice ta kalli wuri yaro ta gani fari sol dashi.
Mamaki da tsoro ya hanata tab'a yaron.
A wautarta bata San cewa labor take ba ta d'auka irin ciwon nan me da take yi yana lafawa.
Zuba mishi ido tayi tana kallon yanda yake tsotsan hannu tare da bin bulb light dake bathroom d'in.
Sababbin azaba ta fara ji tana juye-juye,ba'a d'auki lokaci ba ta sankato da baby girl.
Cikin ikon Allah tare da mabiyan suka fad'o ta fara cancara kuka.
Motsi mutum taji a cikin d'akinta wanda ya haddasa mata tsoro da fargaba.
Motsin na kara kusanto bathroom d'in yayin da zuciyarta me kara lugude.
Ba kowa take tsoro ba illa Lateefa,cikin daren nan ta same ta da yaran nan komai zai iya faruwa.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀
*~UKUBAR KISHIYATA
😭😭😭😭😭😭
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part thirty nine*
Knocking k'ofan bathroom d'in taji anyi wanda saida hanjin cikinta ya kad'a saboda tsoro.
Murya k'asa-k'asa taji yace..."Babyna are u alright? "
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi sannan ta saita muryanta da ya dashe tace..."Yayana kaine a wannan lokacin?"
"Mafarkai nake tayi akanki shiyasa na kasa daurewa nazo in duba lafiyarki".
Murmushi tayi jin furucin shi tace..." Ka shigo mana".
"Me kike yine a cikin bathroom at this time har kike cewa in..." Maganan ce ta mak'ale mishi a mak'ok'oro ganin Ameera zaune da 'ya'ya 2 a tsakanin k'afanta.
Da sassarfa ya shigo ciki jikinshi har b'ari yake.
Idon shi cike da kwalla ya tsuguna kusa da ita.
Hannun shi yana karkarwa ya kai yana shafasu cike da so.
Juyowa yayi yana kallon Ameera da hawaye shame-shame a fuska dan yama kasa magana.
Girgiza mishi kai tayi tana murmushi,kasa daurewa yayi ya jawota jikinshi ya rungume yana kukan farincikin k'yautar da Allah ya bashi,yau shekara goma sha hudu da wani abu da yin aure bai samu haihuwa sai yau.
Wani sabon k'aunarta yake jin yana ratsa ko ina na jikinshi.
Da k'yar Ameera ta k'wace kanta tace.." Yayana ya isa haka,kaji ana kiran an k'ira sallah tashi ka tafi massalaci".
Girgiza mata kai kawai yake yana k'ara matse ta a jikinshi.
"Pls ka tafi zaka makara a jam'i don't worry we will be fine".
Da k'yar ta samu ya sake ta ya nufi hanya fita,har ya kai bakin k'ofa ya dawo yace..." Kin iya yanda ake yankan cibi?"
"Ban iya komai ba amma ka bani Waya in k'ira Umma dan ta iya har gida ake zuwa ana kiranta tana taimakawa masu haihuwa".
Bata gama rufe baki ba ya fita da gudu ya d'auko mata wayan ya bata.
Wajan da yaran yaje India suke k'wance suna tsoson hannu.
Shafa gashin Kansu dake k'wance har wuya ya shiga yi,dariya ce ta tsubuce mishi wanda baisan lokacin da yazo mishi ba ji yake kaman ya maida su ciki yake jin.
Dawowa yayi ya k'ara k'amk'ame Ameera yana mata godiya tare da kissing d'inta ko ta ina.
Da sud'in goshi Ameera ta samu ta kora shi massalaci dan har an tada iqama lokacin.
Number Fateema tayi dialling,a lokacin Umma ta shigo tashinta yin sallah.
Ido ta zaro tana kallon Umma tace..." Umma Ameera ce fa".
"Ameera kuma da asuban nan,lafiya kuwa?"Umma ta tambaya da damuwa k'arara akan fuskarta.
" wallahi bansani ba nima"ta amsa itama cikin damuwa.
"Yi maza ki d'auka inji ko lafiya ".
Fateema tana d'agawa tace..." Aunty lafiya kuwa?"
"Lafiya lau" Ameera ta bata amsa sannan ta cigaba ..."ina Umma?"
"Gata nan,ko in bata wayan?"ta tambaya.
Amsawa tayi da a bata d'in.
Mik'awa Umma tayi tace" ke take nema".
Karb'a Umma tayi tasa a kunnenta tace..." Ameera lafiya kira da asuban nan?"
Gaisheta ta farayi,Umma ta amsa cikin kotsawa dan ita ba gaisuwarce a gabanta dalilin k'iran take son ji.
"Umma in kinyi sallah Ku taho yanzu".
A rikice Umma tace..." Inzo yanzu lafiya?"
A kunyace tace... " Umma ban iya yanke cibi bane kuma....kuma..."sai tayi shiru.
A take damuwar kan fuskarta ya koma fara'a tace..." Masha Allah!! tun yaushe kika haihu?"
Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba .
Umma tace.." Toh gamu nan zuwa amma kamin zuwan Mu ki samu towel ko zani ki lullub'e su saboda iska".
"To Umma sai kun iso" nan sukayi sallama ta ajiye wayan.
Umma ta juyo tana kallon Fateema da take dariya alamun taji zancen ba sai an mata k'arin bayani ba.
Had'a rai Umma tayi tace..."ba washe baki zaki tsaya yiba,yi maza ki yi sallah Mu tafi".
Da gudu Fateema ta d'auki buta tayi bayi.
Al'ameen yana idar da sallah ya dawo wajan 'ya'yanshi ya saka su a gaba yana kallo.
Saida tace mishi Umma da Fateema suna hanyan sannan ya hak'ura ya tafi part d'inshi.
Ya fita bai jima ba su Umma suka iso.
Umma ganin jikoki har 2 a lokaci 1 yasa ta kasa rufe baki sai sannu take ta hero mata.
Yanke musu cibi Umma tayi tare da musu wanka ta nannad'esu cikin d'an k'walin Ameera kasancewar ko wando ba'a saya ba.
Itama mai jego Umma ta had'a mata ruwa mai zafi sosai tayi mata wanka tayi fes da ita kaman ba ita ta haiho yara 2 nan ba.
Fateema kasa ajiye su tayi, tana rungume dasu saii jijjigasu take.
Suna zaune suna hira Rabi ta shigo dan dubata.
Turus tayi tana kallon su cike da al'ajabi tace..." Ikon Allah mu da muke cikin gidan ma bamu san anyi haihuwa ba,har kuda kuke nesa kunji kun iso?"
Umma ta dubi Ameera tace..." Dama 'yan gidan naku basu san kin haihu ba?"
Girgiza kai tayi tare da sadda kai k'asa tana murmushi.
Ladi tana k'arasowa ciki tace.." Da mun sani ai anan zaki same mu Hajiya".
Hannu tasa ta karb'i d'an dake hannun Fateema tana kokarin zama ta hango wani jaririn akan gado.
Fara'arta ne ya k'aru tace..." Dama wai 'yan biyu ne?"
Dariya Umma tayi tace..." Wancan kishiya ce shiyasa kika ganta a yashe".
Dariya suka k'washe dashi dukkansu,Rabi tace.." Ungo mai gidanki dan ni k'awata zan d'auka"
Nan ma dariyan suka saka.
Saida suka tab'a hira mai cike da bark'wanci sannan Rabi ta fita zuwa kitchen dan had'owa mai jego da bakinta abin kari ta kawo musu sannan ta fara had'a na masu gidan
Al'ameen tunda ya koma part d'inshi ya kasa zaune balle tsaye sai zagaye d'akin yake yana ta buga waya yana fad'awa 'yan uwa da abokan arziki.
Jinshi yake kaman anyi mishi albishir da gidan aljanna.
Sallahn nafila ya rinka jerowa yana mik'a godiyarshi ga Allah na nuna mishi wannan babban rana a rayuwarshi.
Wanka yayi ya shirya dan tafiya office.
Lateefa yau bata samu baccin safe ba dan ta k'wana da maganan da sukayi da Aina'u a ranta.
Tana zuwa parlour taga kan dinning wayan ba komai.
Bud'e murya tayi ta fara k'walawa Rabi k'ira.
Da sauri Rabi ta iso gabanta ta zube a k'asa tace..." Gani Hajiya".
"Wani irin rashin mutunci ne yasa har yanzu baki gama breakfast ba?" Ta tambaya tana harararta.
Rabi kai na kasa tace..." Kiyi hak'uri Hajiya gidan ne da baki shiyasa".
"Baki,wani irin baki kuma ya ban gansu ba?"
"Suna can sashin Amarya" ta bata amsa.
Zuciyarta ne ya buga da karfi can kuma wata zuciyar tace..."ko Allah ya takaita mata wahala ta shek'a cikin dare.
Atake taji wani dad'i ya ziyarci zuciyarta,tana murmushi tace..."meye ya faru a part d'in nata?"
" *HAIHUWA* tayi Hajiya"Rabi ta bata amsa.
0 comments:
Post a Comment