AMANA TA CE
By
©Rash Kardam
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassan ne ya fito daga dakinsa cikin manyan kaya, yayi shiga ta alfarma, dining yaje ya zauna hajiya fatima ne zaune tana jiran mai gidanta, bayan ya zauna ta masa sannu, ya amsa cikin sakin fuska ya kalleta yace Fatima ina Auta take, tace tana sana’arta har yanzu inaga bata farka ba, cikin kulawa ya kalli fatima yace hajiya ina fada miki kulum ki ringa kula min da Auta, cikin daure fuska tace Alhaji kulum haka kacewa yarinya duk ta san garce sakalci ya mata yawa ta girma aman kamar wata jaririya, Alhaji ya nisa yace hmm fatima akwai maganar dana ke so muyi da Auta da Ammar, ana cikin haka sai ga Ammar ya shigo cikin ladabi ya gaidasu, suka amsa da sakin fiska, ya kalli Hajiya yace Mum ina Auta tace tana daki tana sana’ar ta na baccin sage barinje na tasota, Ammar ya mike da nufin komawa falon Abba yace aaa Ammar bama haka ai kaima dana ne don ina jinka ajikina kazauna mu karya tare, ana haka sai ga Mum tafito Auta na biye da ita, yau anyi sa’ah harta yiwanka da wuri bata tsaya baccin gadonta ba, cikin zazza kar muryanta ta gaida Dad dinta da Mum san nan Ammar cikin kulawa ya amsa, kusa da Dad ta zauna suka karya bayan sun gama suka koma falo, dad ya zauna mum na gefensa Ammar na kasa tana zaune, Autar Hajiya na kusa da ita, Abba ya dago cikin muryansa mai sa sanyin jiki kalo daya zaka masa ka gane yana cikin taradadadi, Zainab ya ambata, Autar Hajiya sai da taji sunan har cikin ranta tasan dad baya kiran sunan ta haka kurum sai da dalili, ta amsa da na’am dad, Dad ya kalle ta yace Zainab ina son insanar dake wani abu, sanana inaso ko bayan raina Auta kikasance mai hakuri da biyya ga wanda zakiyi tarayya dasu san nan ki rike mutuncinki, karki sake kiyi watsi da tarbiyan da muka miki, nasan ki amma ina son ki kara rike mutun ciki, ki rike Adu’ah a duk inda kike, Zainab idonta duk ya ciko da kwala don tun da take da dad bai taba mata zance makamancun haka ba,maganar dad ne ya katse mata tunani, Ammar ya kira ya amsa, dad yaci gaba dacewa Ammar kai kadai na yarda da kai acikin wayanda mukayi tarayya, kaine ka rike min “AMANA” ta don mutane yanzu ba yarda, san nan ko bayan raina banyarda ka bar Zainab ba ga “AMANARTA” na baka kai kadai nasan zaka kula min da ita, cikin sanyi jiki Ammar yace dad mai yasa kake irin wan nan maganan Dad yayi murmushin manya yace Ammar da Zainab atare, yace kukadai zan sanar da maganan nan kusani akwai wayanda suke min barazanan kashe ni da iyali na akan dukiyata, da nanema da gumi na, nikuma naki amsamusu sabida mutuwa da rayuwa tana hannun Allah, ba wanda ya isa ya kashe wani face da izinin Allah. Cikin damuwa Auta da Ammar sukacewa suwaye dad murmushi yayi yace ka kyalesu kawai zan sanar muku amma bayanzu ba, hajiya ma tayi musu nasiha sosai, dad ya mike ya fita hajiya tayi daki Auta kuka takeyi Ammar ne ya rarrasheta sai da tayi shiru kafin ya fito harabar gidan nan sale suka fara masa kallon bansa da kuma zaka sani yau, musa kam dariya yayi sosai kafin yace mun kusa ganin karshen wan nan rigima taka da kafafa kamar gidan ubanka, an samu gidin zama sai nuna isa kamar dan gd ko ta kansu bai bi ba ya wuce dakinsa shidai yana fatan Allah ya tsaresa da sharrin masu sharri.
Dad bai dawo ba sai kusan 10 lokacolin Auta tayi bacci hira sukayi sosai da Hajiya kafin yace bari ya watsa ruwa bayan yayi wanka hajiya fatima tafito cikin kayan baccinta mai daukar hankali ta nufi dakin Alhaji sun yi hira sosai kafin suka kwanta, Misalin karfe 2 gari yayi shiru sai sai hadirin daya hadu gari yayi baki2 nan take ruwa ya tsinke sosai kamar da bakin kwarya, kowani mutum na gidansa yana bacci, wata bakar jeep ce mai bakar glas na ga tanufo gaye din gidan Alhaji Al-hassan sai da suka fito duka kwan kwasa wa mai gadi ya bude musu suka shiga, duk da ruwan da akeyi bai dame musuba kalo daya zaka musu kasan ba alkairi bane, atare dasu, sun rufe fidkokinsu da marks bakinsu da kwayan ido su da kofar hancinsu ke waje, magana sukayi tsakaninsu wanda sukazo a jeep dasu sale da musa, da alaman dai sun san da zuwansu, bayan sun gama ne, suka nufi cikin gida ko da suka shiga dakin Alhaji suka nufa suka samesi da hajiya suna tare,
Ammar ko yatashi tun karfe daya yasoma sallah nafilan da yasabayi duk dare bayan ya idar duk da ruwanda da akeyi yaji alamar shigowan mota da sauri ya leka nan yaga wasu da bakaken kaya sun rufe face dinsu duk abunda sukayi na kallonsu nan yaga sun ciro bin diga, yana kalon sun shiga ya bude kofar dakinsa cikin sanda ya kwanta a kasa yadoma tafiya da ciki kamar yanda sojasuleyi a fagen yaki cikin fulawas ya soma bi ko da yaje ta kofar baya ya shiga yayi sa’ar kofar abude take nan ya tura a hankali, daman duk wanda yashigo ta baya dakin Auta zai fara samu don haka ya tura kofar a hankali.
yaganta tana bacci, a hankali ya soma tashita, cikin ikon Allah ta mike ba gyan gyadi, ihu zata sa ya toshe bakinta yace Auta kina jina wasu mutane sun zo gidan nan da kuma da alamar wayanda dad yafa da.suna son kashesa ne, nan cikinta ya fara rawa idontaya ciko da kwalla, yace dau hijab diki mu leka muga don musan abinyi, kasa dauka tayi shi ya daukar mata ko ta kalmi bata tsaya dauka ba suka nufo falo a han kali suka leka, nan suka ga abunda ya razana su dad ne aka samasa bindiga da Hajiyasuna kara lekawa nan suka ga fuskan Baba Sani da yayansa iyaka, alokacin suka dana kuna mar bingigan tass kake ji karan harbin bindiga, nan take auta tasaki kara atake suka juyo gurin da sukaji kara suna fadin suwaye suka nufo gunsu.
Yan uwa amin afuwa za ku ga ban2 dana farkon dana soma sakewa, yanzu na dawo da lbr daga tsakiya ne amin afuwainaga hakan watakil zaifi.
Shin su Autar Hajiya da Ammar suna kubuta daga sharrin mutanen nan? bacin gashi gate din gdn a kulle.
Suwaye wayan nan mitanen?
Mai nene alakarsu da Dad?
Waye Ammar?
Don son jin amsarnan kubiyo Yar Gidan Kardamawa.
Taku akulum mai kaunarku
®WWA®
Rash .A. Kardam
[9:20PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rash Kardam
Tass kake ji karan harbin bindiga nan take Auta tasaki razananen kara, da sauri suka juyo girin da sukaji karan suna fadin suwaye, suka nufo gun, Ammar yana ganin haka yaja Auta tana turjewa ita sai taje gun su Dad da Hajiyarta, dakyar ya shigarda ita dakinta yasaka key ya kullesu, ga ruwa sai sauka yakeyi ana tsawa, nan yarasa yanda zaiyi Adu’ah ya tuno na ne man tsari daga abokan gaba ya fara karantawa, autakan sai kuka take, ana cikin haka su Kawu Sani suka iso kofar nan suka fara jijjiga kofar, Auta ko kara sautin kuka takeyi Ammar bai san lokacin daya daka mata tsawa tayi shiru don kukanta har cikin zuciyar shi yake tabasa, nan ta damke bakinta, duk ya rue yarasa ya zaiyi gashi ba hanya, kasu Baba Isiya da sani su jijjiga kofa ga harbin suketayi, kiris yarage su balla kofarnan take dabara ta fado masa da sauri yayi gun Waldrop, ya zazzagar da kayan ciki kasa da kyar ya turo ya jawo ya kawo zuwa bakin kofarya tokare, nan ya janyo dress miro shima ya tokare nan ya dafe kansa sai ga wasu zafafan hawaye:'(:'( ke zuba yana kiran sunan Allah ya kawo musu mafita.
A bakin gate kuwa mai gadi da sale suka leko ganin su Alhaji an sheka kiyama suka sheke da dariya sukace yau ina kudin ka ya dawo namu, gumus ne ya fito yace kuba mu karfe ina tunanin akwai wasu agidan nan zamu balle ko fa, don yar Alhaji na tare da wani Sai a lokaci idi yace kai:oops::oops:munyi kuskure daya da muka bar dakin Ammar bamu fara ta kanshi ba barinje na dubo shi, ko da yaje dakin ba ammar nan yace duk yanda akayi Auta tana tare da Ammar amma bazasu gudu ba, don gidan nan na rufe ba gurin tsira dariyan mugunta suka farayi, wani katon karfe suka samo wanda duka daya zasuyi wa kofar su balle, nan suka nufo cikin dakin da karfen.
Ammar kuwa adu’o’i yakeyi can ya tuna windo dakin na glass da sauri ya mike nan ya fara dube2 ba wani karfe a dakin wanda zai fasa ga shi sukuma sun kusa balle kofa duk ya kalli ko ina na dakin ba wani abu, sai can ya kalli Bedside drawer, da sauri ya dauko ya zubar da kayan ciki, ya nufi windon da karfin ya buga tare da bissmila bugu biyu yayi mai kyau wundon ya balle sosai yanda zasu wuce sai da ya leka ta baya yaga ba kowa kafin ya dauko Auta ya sanyota ta waje tasauka kenan yana shirin fita wani kwanban da bai gama balle ba ya yankeshi nan sai ga jini sosai gashi kwalbar ya shiga sosai har sai da yace washhhhh, lokacin su baba Sani suka balle kofar suka nufoshi.
®WWA®
Rash Kardam
[9:20PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Ya balle window din ya fara fitar da Auta kafin ta zo fita wani kwalban glass a jikin window din ya yanke shi ya shiga sosai, ya ji zafi harsai da yace washhhh, dai2 lokacin su baba sani suka balle kofa suka nufo shi cikin zafin nama ya dirka ga jini sai zuba ya keyi sosai, da sauri Ammar ya yakwanta a kasa ta gefen window, cikin hantsari ya fisgo Auta ta fadi kasa wanda faduwar wata ya dai2 da wani dutsi nan ta buge bakinta sai ga jini, kara tasa yayi sairin toshe mata baki, su gumus da kawu isiya suna isowa harbi suka fara amma bai kai ta inda su Auta suke ba, baba sani ne ya ciza yatsa don ya ji haushi ga window ya musu kankanta baza su iya fita ba da sauri yace ku zo mu zaga mu bisu da sauri suka fita ga ruwa haryanzu zuba yakeyi sosai.
Ammar na ganin sun bar window yayi kokarin rashi ga jiri na debansa don jininsa ya zuba sosai, ga Auta kuma jiki ba kwari, ya mike yana tan gadi ya dagata kasa tsayuwa tayijijjigata yayi da kyar sai ta sauke ajiyar hrt kafin ya mikar da ita suna mikewa suka hango motar su baba sani sun nufosu, nan ya fara janta da gudu tunda daga hayin rigasa layin waya suke gudu sai da suka wuce kantin yawo, kafin suka kara gudu dai2 zasu fita a hayin rigasa, Auta ta fadi da sauri ya dauketa ganin in yace zai miki hanya zasu kamasa sai yayi gurin wani sabon gini wanda dogayen ciyawasun bullo agun gabansa kuma katon ruwa ne wanda ya taru, nan ya kaisu gun ya tsuguna ya tare Auta da numfashinta ke shirin daukewa
abunka da rashin sabo ga razana don Auta in banda girkida take taya hajiya bata wani wahala, tasaba da rarrafen carpet tun tube da waya, baran da ta rage ita daya ma Dad da Hajiya ba irin gatan da basa mata.
Su baba sani da suka iso gurin nan suka fita ga ruwa na sauka sosai duk dube2 da sukayi basu gansu ba,
Ammar kuwa suna gurin a tsugune da ke Auta ce ta jikin garu, nan wata kuna ma ta fito sabida ruwan da ya dameta a gidanta tana fitowa kuwa kafar jidda ta hau sai da tazo kusa da gwiwanta ta danna mata cizo, har saubiyu duk da zafin da taji tayi saurin damke bakinta, Ammar na ganin haka ya kara matse bakin nan kuwa kunamar ta kara yanka mata cizo, sai murkususu take tayi, gumus da duna sukace alhaji ku tafi kawai mu zasu tsaya mu ne mesu in baku mu kawo maka gawarsu ba to zamu maka da lbr mutuwarsu, nan suka tafi da motar suka bar su gumus a gurin, sun dade suna dube2 sosai agun kafin suka soma fita,
Autakuwa wuya yayi wuya bata san lokacin da ta kwace bakinta ta saki kara da sauri su gumus suka juyo nan suka fara nufo gurin da sukaji karan,
Ammar na ganin haka ya mike yasoma jan Auta suna kara gaba kawai suka ga kato kogin ruwa ne a gabansu ga su gumus sun nufosu.
Abun gwanin tausayi nikaina Rash bansan lokacin da na fara zubar da hawaye ba.
Allah sarki su Auta da Ammar Allah ya kwace ku a hannu wayan nan Azzalumai din Ameen.
Sai dare zakuji ni
Taku a kullum mai kaunar ku
®WHW®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Ammar ya ma rasa ya zaiyi ga Auta numfashin ta na kokarin daukewa da sauri ya suguna akasa ya ajiyeta acikin tabo ga jini yana ta zuba daga hannunsa,
Gumus suka nufo su da sauri nan ya harba bindiganya sake harba wa yaji bullet ya kare cikin jin haushi yace oh ya wurgar da bindigan akasa ya nufosu ko da yazo daman Ammar na ankare yana isowa suka fara kokuwa cikin ukon Allah karfin yazo ma Ammar ya wurga shi a wan nan ruwan, aiko dan uwan gumus na ganin haka dake yana haskasu da touch light, ga shi gumus nata fanjam aruwa dake shi bai iya ruwa ba, kuma ruwan da dan yawa, da sauri yayi gun ruwan ko ta kan su Ammar baibiba ya je gun dan uwansa don ceto rayuwansa,
Ammar na ganin haka ya dauki Auta yasa gudu sai da yayi nisa ga ruwa ya soma tsagaitawa, ya samu wani rumfa ya ajiyeta ya huta, basu dade sosaiba ya auta sai hawaye:'(:'(take tayi ko da ya laluba kafarta yaji ta kubura suntum, taba kafar dayayi har sai da tayi ihu haka ya dauketa suka cigaba da tafiya.
Su gumus ansha wuya da kyar aka ciro shi don har yasoma shan ruwa, yana dawo wa hayyacinsa yake tambayar mugum ina suke yace sungudu, mtssss bahaka nasoba nan yace naga abunda ya faru kar ka sheke zuwa lahira da wuri shiyasa na cirokakai kajimin wayan nan sai kace mutuwar nima izini takeyi, mikewa sukayi gumus ya karbi wayar mugum don nasa ruwa ya bata, baba sani ya kira ya tambayesu suna ina yace yanzu zasu bar gidan Alhaji kenan sukace gasu zuwa.
ko da suka isa nan suka samu baba isiya da sani sun daure sale mai gadi da musa, don daman sunyi akan zasu daure su sabida ace barayi ne suka zo, hakan sukayi, ko da su gumus suka iso nan sukaga abunda ke faruwa dariya sukayi sosai sukace Alhaji baku da dama,
Baba sani yace ya ina fatan kun sheke su cikin sauri gumus yace ai har gawan ma sai da muka yardasu inda ba mai gani, nan kawu isiya yace aikin ku na kyau, gumus yayi murmushi yace oga sai kudin fa baba sani yace ina zuwa cikin gidan suka shiga dakin dad suka duba drawer nan suka ci karo da damin kudi sai dasukayi dariya sosai kafin suka diba nan suka fito falo, baba sani yazo cikin izgilaci yace su Al-hassan yau an sheka kiyama to ina naira kai dan taurin kai yau zamu facaka da dukiyar da kake ta kama dashi, yana zuwa kan hajiya sai da ya shureta da kafa, ke kuma yar iyeye yau munyi maganinki da yar da kuke so, harda dauko bare wanda bakusan daga ina yake ba ku fifita shi akan mu gashi yau duka bakwa nan mun kuma samu dukiyar cikin ruwan sanyi sai ya kece da dariya sosai, nan suka fita suka shiga mota suka tafi don suke su sallami su gumus.
®WHW®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Ko da sukaje gidan kawu isiya wanda tutun nufawa, ba kowa aciki kuma ba nisa sosai da gidan Alhaji marigayi, nan suka shiga ko da suka zauna nan baba sani yace yau burin mu yacika na gama wa da Al-hasan da iyalansa, kamar yanda mukayi Alkawari zamu ba ku 400k kowa zai dau 200k kenan gumus ne yace oga mungo amma munaso aba mota koda kwaya daya ne ehhh musamu na yawo a gari, ko wani aiki kuke so zamu muku cikin sauki kawu isiya yace aaa bazai yuba abun yaso ya dawo musu rikici baba sani yace ba matsala za a duba in komai ya lafa abaku, nan ya ciro 300k ya basu yace kurike wan nan kafin komai in ya lafa zamu sallame ku, gaba daya nan sukayi sallama kowa ya kama gabansa.
Da safe yan unguwa suka fito don wasu sunji karar tsayuwardon haka suka yi cirko2 gashi jiya anyi ruwa sosa, mukwabcin dad wani mai suna Alhaji Abubakar yace yan uwa yau ban ga Al-hassan a masallaci ba kuma duk rintsi in ba jinya yayi tsanani yana zuwa sallah amma yau shiru, ko lfy wani mai suna Alhj kabir yace ni jiya fa kamar an shigo unguwan nan don duk da karan ruwan sama dake zuba naji ihu san nan naji harbin bindigasun dade suna jimami kafin wani acikinsu yace kamata yayi mu shiga gidan mugani, nan suka dun guma suka shiga tun a kofa sukaga masu gadi an daure su, da sauri suka isa wajansu, bakinsu an toshe da tsumma, kunce su sukayi nan Alhaji Abubakar ya fara tambayan lfy, sun wahala yasa ba wani amsa don dauri da aka musu mai kyau ne hakan shi ya gala baitar dasu, da sauri suka nufi cikin gidan bayan sunshiga a falo suka tarar da gawan Alhaji da hajiya nan suka soma jimami masu kuka suka fara, alhaji abubakar makocin dad policene nan take ya kira ja mi’an tsaro suka fara binjike nan sukaje dakin Auta inda suka ga yanda aka baza kaya da alamar kare kansu da sukayi da kuma fasa window da akayi gashi ba auta ko da suka zaga nan sukaga jini da kuma alaman harbin da akayi ta waje, Alhj Abubakar yace cikin daya biyu ko sun kashe Zainab ko sun dauketa ko da suka dawo gd sai alokacin ya tuna da ammar nan ya nufi dakin da ke tsammanin nasa ne sallaya tagani a shin fide da alamar anyi sallah akai ki da suka fito suka nufi kofar baya nan sukaga an tura kofar anshiga duk binciken da sukayi ba wani amsa nan suka kira Alhaji sani da baba isiya suka sai da musu, ko da suka iso gidan kuka sukeyi sosai kai ka rantse basu da hannu aciki har sani na ikirarin imyasan wanda yayi kisan nan sai ya dau fansa, kawu isiya kam ko mace iyakaci yanda yake kuka. haka police suka tafi da gawarwakin don kara bincike.
Ammar da auta kuwa tafiya yayi sosai, sun shigo cikin gari kuma dare yayi sosai don asuba ya kusa, nan yasamu inda ba ayi ruwaba ya kwantar da Auta ya yagi zanin dake daure a saman kayan baccinta ya kulle hannusa sai runtse ido yakeyi alamar zafi, ya daure hannuta ya dauketa suka cigaba da tafiya sunyi nisa sosai, sai ga wani mai mota yazo wucewa nan ya tsare shi sam yaki tsaya haka ya cigaba da tafiya sai ga wani da alamar wan nan irin yan taxi masu zuwa gari zuwa gari har yaki tsayawa komai ya tuna ya dawo daukarsu, nan Ammar nace ina zan kaiku Ammar yace ban sani ba mutumin yace to ni saminaka zanje yanzu, yace muje ka ajiye mu a hanya.Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Motar suka shiga nan mutum min yace subada 1500 kudin mota sai a lokacin ya tuna basu da kokisi, innalinahi wa inna ilaihi raji’un abunda ya furta gashi sunyi nisa sosai, sun shiga jeji don sun bar cikin garin kaduna sosai, jiki ba kwari yace wa driver dan Allah ka tai make mu wlh fitowar gaggawa ne ya kama mu bakosisi ajikin mu, driver ya narko ashar yayi, aefa baka isaba zan dauko ku a bati ne ba ko sisi mai na tsada kuma niman kudi na fito, waya sani ko dan iska ne ma kai kasato musu yarinya inazaka da wannan yar gashi jikinta duk jini, kalala ta mata rayuwa, ko sayarta zakayi, nan take ran Ammar ya baci don tunda yake ba abundaya tsana kaman zargi ko kazafi, shi da ya tsani zina a rayuwansa mezaisa ya aikata cikin bacin rai yace kaii Malam ya isheka in har bazaka taimaka min ba karka min wan nan zaton, nan mutumin yace anyimaka kuma zata fita anan ba wlh sai kabani kudina, nan ran Ammar yakara baci wai shi dayake nima da guminsa ga kuma Zainab yar gata gabada baya wai yau sune a wulakance ga shi an kashe su Alhaji shikenan Zee sa ta dawo “MARAINIYA”nan take yaji hawaye:'(:'(:'( wasu na bin wasu, sai a lokacin ya kalli agogon hannusa mai kyau yace ma
driver bani da kudi amma ga agogona in zaka karba yafi karfin kudinka, driver yace nagani ko da ya karba yagani yasan zaiyi tsada dayawa nan yace to shikenan yanzu in kaiku saminaka ne ko zaku sauka anan tsabage bacin rai yace barin musauka anan, ya dauki Auta suka fita, gefen hanya ya kwantar da ita lokacin gari ya waye sosai, sai alokacin yaga kafarta ya kumbura sosai fa bakinta ma ya kumbura sosai, gashi yayi ja abunka da farar mace, gindin wata katuwar bishiya yaje ya shinfida fallen zani ya kwantar ta, ga yunwa yasoma damunsa ga hannusa yana masa zafi sosai, bayan ya kantarta, yasoma dube2 ko zaiga ruwa don yasha yakuma ji alwala.
Acikin garin kaduna kuma Alhaji Abubakar ko ince Inspector Abukar shiyatsa akan gawan su dad har akayi zana idarsu aka kaisu makwancinsu na gsky, kafin kace me lbr ya baza gari, yan uwan dad sun taru a gidan ko da Sadiya yar Baba sani taji lbr ba karamin girgita yayi ba baran da taji ance ba a ga Zee ba tashiga tashin hankali don suna shishiri sosai,
Inspector Abubakar daya koma gd ya tausaya ma yarsa bulkisu don kawar Autace sosai tayi kuka kuma nan ta dauki aniyar saita dau fansa akan duk wanda ya aikata abun, bayan kwana uku da rasuwan su Dad yan uwansa sukace su duk wanda yayi abun nam sun barshi da Allah, sirutu kala2 su ka rinkayi har saida Inspector Abubakar yaso ya ganesu, bilkisu kuwa ranan kwana na uku, tasami Abbanta akan ita ta canza ra’ayi daga kan Science courses, yanzu Law zata karanta don tazama barrister don ta nimo ma Kawarta Ameeniyar ta, hakkunta da cutar da ita da akayi, kuma tace Abba ni ajikina inajin Zee bata mutu ba ko ga yanayin statement din da aka samu kuma kaga ba aga Ammar ba nisan yana tare da ita kuma bazai cutarta ba da yardan Allah don yana da hali mai kyau, Inspector Abubakar yaji dadin maganar yarsa Bilisu wanda ake kita da futuhatul-khai, yamata Adu’an Alkairi da fatan nasara.
Su baba sani nan suka fara kiciniyan raba dukiyar dad har yaso su samu sabani da baba isiya akan wanda zai zauna a gidan dad da kyar Baba isiya ya hakura akan shi za a bashi motar dad babban ya rike.
Rayuwa kenan wai naka najikinka shiyake son ganin bayanka basa tunanin suma zasu mutu ba tsoron Allah wan nan wani irin zamani ne burin wasu mutanen su ci “Amana” yan uwa muji tsoron Allah musani Amana tana gefen siradi da Zumunci duk wanda ya karya daya aciki to yasan makomarsa, don ranan kiyama akwai wasu kugiyoyi a kasan gadan siradi duk wanda yaci amana ko ya bata zumunci ko da ya kusa karshen haye gadanne haka kugiyar zata finciko shi wasu kafin su isa duk sun yaga naman jikinsu, ‘Yasalam’ yan uwa muji tsoron Allah mu gyara rayuwar mu musan man zumunci da Amana mu kiyayesu, ya Allah kasa mudace da karshe mai kyau Ya Allah ka daura mu akan hanya madaidaiciya Ameen.
Ammar sai da yayi tafiya mai nisa kafin ya ga wani rafi nan ya rasa ya zaiyi ya debi ruwa ya kaima Auta tasha ko zata ji dama2 ga tausayinta shikam kasa sha ma yayi in har Auta bata sha ba ba zai iya sha ba, ya sanya hannumsa biyu ya debi ruruwan yanufi gunta tun kan ya isa ruwan ya zube nan yaji wasu hawaye:'(:'( sun zomasa. Yana zuwa kusa da ita ya ga sai wani irin nishin azaba takeyi kamar wai shirin mutuwa Ammar baisan lolacin da yasaki kuka kamar karamin yaro yana cewa Zainab dan Allah kar ki tafi ki barni ke kadai kika ragemin bani da uwa ba uba, gashi sun kashe mana Dad da Hajiya in kintafi ina zansa kaina kuka yakeyi sosai da sosai.
Nima Rash bansan lokacin da nasaki kukan tausayi ba. Allah sarki rayuwa juyi2 Allah ka kawo masu Auta da Amar mafita Ameen.
®WHW®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Nan yasaki kukamai ban tausayi, jijigata ringayi sai yaga tasaki ba ko alamar motsi atare da ita, da sauri ya dauketa yayi gun rafin da ita yana isowa yaga wani dan tsoho yazo diban ruwa a gora, tsohon nan, ganin halin da Ammar ke ciki yasa yace subhanallah bawan Allah mai yasa meta Ammar kasa magana yayi sai hawaye:'(:'(wani na bin wani, tsohon na ganin halin da Ammar ke ciki ya dibi ruwan goransa tare da bisimillah ya watsamata sau 2 nan take ta saki ajiyar zuciyamai karfi, muryan ta ya dishe, ga jikint ba kwari duk ya mutu, ahankali take magana sai da Ammar ya sunkuyo dai2 bakinta kafin yaji mai takecewa wayyo kafarta, ammar da sauri ya riki kafar sai a lokacin tsohon ya lura da kafan yace yasalam mugani ya rike kafar wan nan ae cizo kunamane ya daneta, yace yanzu ku biyo ni in taimaka mata, ammar ya dauketa suka bi tsohon.
A cikin garin kaduna kuwa, su baba sani sun shiga sabon rayuwa mai dadi da dukiyar da suka dade suna mafarkin samunsa, Sadiya sam nataji dadin yanda Abbanta ke zakewa akan dukiyar dan uwansa ba, tunda ba a ga Autaba kuma hakan bai tabbatar da cewa ta mutuba, abin duniya duk ya isheta, haka rayuwa ta kasance musu cikin nishadi har sun manta da wasu wai su Al-hassan da fatima da wata diyarsu Zainab bare Ammar dan kallo.
Ammar ko haka yabi tsoho nan sunyi tafiya mai nisa sosao kafin suka shigo wani karamin kauye wanda gidajen ciki baifi a kirga ba, in kazo gida daya sai kayi tafiya mai nisa kafin ka iske diga daya, ko da suka isa kofar wani diga an masa rufi da da ciyawa sai katangan kara aka dan zagaya gidan naki biyu ne a gidan sai dakunan kaji da baru yan kanana da agwagi, suna sallama wata yar tsohuwa ta fito daga dakin danake zaton nan ne gurin kwanan su, tace lale maraba baki mukayi, ganin Ammar rike da joda ga jini ajinsu duka yasa tace lfy kuwa, suwaye wayan nan, tsohon nan yace bakine da sauri ta dauko taburman sakar kaba ta shinfuda musu, ammar ya kwantar da Auta tsoho nan daki ya shiga ya dauko wani yar jakar fata, ya dauko magani da nan ya kama kafar ya matse gun cizon saiga karin ya fito nan ya sake matsewa har sai da Auta tayi kara ta kan kame Ammar sai zufa tayi, saida yacire yashafa mata magani, san nan yasa inna laure ta dafa
Musu ruwan zafi ta kawo masa kadan a kofi ya saka magani yabama Auta da kyar ta iya shan maganin tana runtse ido.
®WWA®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Bayan Auta tasha maganin, sai aka dawo kan Ammar nan shima ya kunce daurin da yayi ma ciwonsa, tsohon nan da naji inna laure nakira da malam, ya dauko wasu magun guna, ya wanke masa ciwon da wani farin ruwa, nan ya haungo karamin glass ya shiga hannun, sai da ya dauko aska ya ciro glass din, duk da Ammar na miji ne sai da na ga indonsa yayi jajazur da alamar yana jin zafi sosai, baran ciwon ya kwana shiyasa, Auta kam kasa jure gani tayi sai kifa kanta tayi tana kuka maras sauti…,
wai yau itace a kungurmin kauyen da ko wuta babu bare ruwan fanfo, kafin asauko gun kwanciya mai kyau, nan take kalaman Dad dinta ya fado mata, inda yake mata nasihan sa na karshe akan ta yi hakuri a duk inda tasamu kanta, sabida yanayin rayuwa.
Allah sarki duniya kenan wai ace su baba sani su zasu kashe iyayenta akan dukiya da son duniya, mai suka maida zumunci ne ga cin “Amana” wan nan wani irin rayuwa ne sam tausayi ya kaurace a idon jama’a basa tunawa zasu mutu su koma ga Allah, in har kayi mai kyau zaka taras, kwanciyan kabari ma akabar mutum dashi babban aiki ne bare ace ka aikata mumunan abu har akaika wutar yasalam!!… Innalilahi wa inna ilaihi raji’un duniya tazo karshe wayan nan abun duk alamun karshen duniya ne Allah ya kyauta yasa mudace da karshe mai kyau ameen.
Hawaye ke gan garimata daga idonta, tayi nisa cikin tunani, sai ji tayi ana share mata hawaye, tana daga ido taga Ammar ne, shima hawayen yakeyi sai alokacin tasamu tasaki kuka mai ban tausayi, shima kukan yasaki, an rasa mai rarrashin wani.
Malam da inna laure sun zuba musu ido sai kallonsu sukeyi, tabbas ko basu fada musuba suna cikin tsananin tashin hankali, nan take ina kaure ta fara hawayen tausayi, malam idonsa yayi ja sosai, malam kenan akwai tausayi ga taimako.
malam yace bawan Allah kai na mijine ka kasance mai juriya a kowani hali duk da bansan mai yasame ku ba aman da alama kuna cikin tashin hankali, kuyi hakuri, kusani duk tsanani yana tare da sauki, kuyi hakuri ku bar ma Allah komai, zai yi muku saukin Al’amarin, haka rayuwa take kowa da irin jaraban da ubangiji ke masa kuyi fatan Allah ya baku ikon ci, Ammar ya amsa da ameen.
Inna ta mike ta debu ruwan wanka a yar bahonta da tsage aka nane shi ta surka kafin ta kaima auta bayi, sai da ta taimaka mata kafin ta kaita bayi tafito ta barta nan ta dauraye jikinta, don ruwan da dumi sosai ya gasa mata jiki kuma ta samu dan karfi, bayan ya fito inna tasake sama Ammar ruwan ta kaimishi shima wankan yayi, bayan yafitoa wanka suka shafa mai dake lokacin da mina ne, a kwai dan sanyi kadan.
Malam ne ya hau kekensa yaje can kauyen da gabansu anan ake samu shago, yasayo musu suga, yadawo inna laure ta musu surki mai dumi sosai, don ya ware musu hanji, abinci ta dauko musu dambu tayi daman, kuma ta danyi da yawa, san nan Malam ya karamusu da nashi, aiko sunci danbun sosai don yunwa sukeji, sai da suka gama cin abincin, san nan sukayi godiya ga Allah da ya kubutar dasu, san nan Ammar ya juyo ya gode ma Malam, cikin kulawa malam yace karkada mu ni domin Allah na muku, ita rayuwa bakan wa zai tai make ka nan gaba, kuma dukiya da dan mitum, da dabba ba a musu keta, ku kara gode ma Allah ammar sai da yaji kwalla, asai ana samun irin wayan nan mutane a zamanin yanzu, Hamdalah yasakeyi ga Allah da ya ciyar dasu.
Inna laure ta gyara daya dakin nan dama da kyausa, in sunyi baki anan suke kwana, ta kwantar da yar katifar bonun da ke dakun tayi shinfidi akan gado, inna laure kenan duk da acikin kauye suke tsohuwar akwai tsabta, komai nata tsab2 gwanin burgewa, ga kamala da kyautawa.
Malam yace ga daki an gyara zamu kwana da kai inna laure kuma sai su kwana da kan warka, kafin in Allah ya kaimu waye wan gari, sai kubamu tarihin ku da abunda ya baroku da gida, Ammar yace to, Malam ya kara cewa meye suanan ka..? Amar ya nisa yace sunana Ammar ita kuma kanwata Zainab, Malam yace aaa babban suna gareta, sunan Mahaifiya ta gareta, Allah sarki Uwata zan kiraki da shi, har cikin ran Auta taji sunan da irin kauna da suka gwada musu, haka ta shiga dakin inna laure ta kwanta don huce gajiya.
®WHW®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Bacci tayi sosai akan yar katifan inna, sai magriba ta farka tayi sallah, bayan ta idar inna ta kawo musu tuwon dawa mai laushi miyar danyan kubiya yaji man shanu, sai kamshi takeyi,nan suka ci suka koshi, sai da sukayi isha’i kafin Auta ta dingisa kafarta tashiga daki ta kwanta, bata dade ba bacci ya dauketa, Ammar ma dakin suka shiga shida malam suka kwana,
Auta bata farka ba dai asuba da inna ta daga ta tayi sallah bayan sunyi sallah,
ta gaida inna ta din gisa zuwa dakinsu malam ta gaidasu ta dawo ta zauna, don ba halin taya inna girki,… Bata da lfy,
inna ta musu dumame da kunun tsamiya, nan sukaci duk da damuwan da suke sai da sukayi santi don inna gwanar iya girki ce,…
sai bayan da suka karya kafin malam ya umurci Ammar da ya basu tarihinsa dana Auta, ammar ya gyara zama nan take idonsa ya kawo hawaye, da bai zubo ba ya fara dacewa,
Sunana Ammar Saad Saraki, ni haifafen dan maiduguri ne iyayena yan mai duguri ne, kenan su Barebari ne gaba da baya, baba na ya kasance dan gidan sarkin Gwaza ne, su biyar mahaifinsu ya haife su, Uku mata biyu masa matan akwai Ya fanna, da da hajja gana da Yakura, sai wan babana sunasa hashim sai babana mai suna Sa’ad, mahaifina ya taso cikin kulawa da kaunar mahaifinsa kasan cewar yana da nutsuwa sabani yaya shi da suke uba daya wato hashim,
hakan yasa suka tsani baba na da mahaifiyarsa don shikadai ta haifa sauran hudun duk yayan kishiyarta ce Hajiya faima,…
duk tsanar da suka masa bai damesa ba ya nimi ilimin boko da na addini bayan ya kammala karatun degree dinsa ya dawo gd,
sai mahaifin sa ya masa Auren gata da mahaifiya ta, Hakimin liman kara, hajja faty mahaifiya kenan ta kasance mace ce mai kamala da kyautatawa ga hakuri da juriya ga sanin darajan dan adam, lokacin auren kudin da sarki Abdallah Saraki ya kashe ba karamin tada hankalin hajiya fatima yayi ba, nan tace ita mai yasa baza ayi auren danta ba, sarki yace a yanda bai nitsu ba shine shaye2 yar wa za a hada shi da ita,
tun daga wan nan lokacin suka dau tsan gwama suka daura ma kakata da da mahaifiya ta, duk da hakan bai damesu ba,
kwanaki sun ja yau wata 5 da auren mahaifina da umma na nan ta fara laulayin ciki, gashi yazo mata da laulayi, bata son shan ruwan fanfo sai na rija tunda suka lura da hakan, sukayi makircinsu aka bata ruwan gdn gaba daya don karta samu na sha, haka kullum sai anje nimota ta a gari don in bata sha ba tashin hankali ne, haka rayuwa tayita tafiya.
Sarki Abdallah Saraki, ya yanke shawaran sauka a mulki sai daura dana Sa’ad Saraki akan mulkin gwaza, tun daga randa sarki ya yanke hukunci, hankali hajiya fatima ya tashi, nan suka soma shiga bokaye, sai da suka san makircin da sukayi mahaifina ya dau mahaifiya suka bar garin bashi tun daga lokacin ba asan inda mahaifina yake ba, bayan tafiyan mahaifina bakin cikin yasa yagamu da ciwon hawan jini, harya makance da ganan kuma Allah ya karbi abunsa,……
Mahaifina na barin gari bai zarce ko ina ba sai kanon dabo tunbin giwa ko da mai kazo anfika,….lol…. Amma basufi yan Bauchi ba fa,
nan ya samu wani mutumin kirki ya rikesa a unguwar Dakata, haka yayi ta rayuwansa da umma na harta cikinta ya kai na haihuwa, nan laraba ta tashi da matsanacin ciwon mara nan sukayi asibiti, ana kaita ta haifi danta, tubarkala ko kalon dan batayi ba Allah ya karbi abunsa, asai masalan da aka samu lokacin tana mai duguri, maganin da aka a rijiya ta sha don karta haihu dake Allah yayi zanzo duniya sai da ta haifen lokacin ya mata illa sosai, shine sanadin mutuwarta.
®WHW®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Bayan anyi zana idarta matan da babana ke gidan ta karbe ni haka ta raineni har na girma na kai 15 yrs lokacin ina secondary school, haka zamu fita aiki mudan samo abunda zamuci sam baba na yaki aure, ana cikin haka malam suka shirya komawa garinsu, don suma mazuwa ne, yan jalingo ne, tunda suka shirya tafiya, mahaifi na yace na shirya muje muga yan uwansa,
tunda ga ranan ya nimi kudin motan tafiya muka shirya ranan asabar 12 /3/ 2012 muka tafi mai duguri tun a hanya mahaifina ya ke cemin gabansa na faduwa, ko da muka isa mai duguri, muka shiga motar gwaza, muna isa yaga masarauta ya canza nan ya samu lbr rasuwan iyayensa, mahaifiyar sa ma bata dade da rasuwa ba, gidansu ya watse nan mukayi kuka tare, daga nan yace mu wuce cikin mai duguri, washegari muna zuwa, cikin garin mun sauka a tasha, kenan nace ma baba na ina jin fitsari, nan yace inje bayan gidan tashar na tafi kenan,
kafin in dawo naji karan wani abu dammm, gurin ya dau hayaki asai bomb ne ya tashi tare da mahaifina,
Innalilahi wa inna ilaihi raji’un, abunda na furta kenan nan aka tattara wayanda suka tarwa tse ki gawan mahaifina ban samu gani ba tun daga nan na shig gararin rayuwa, kwana na 2 a mai duguri a tasha na dan samu taimakon kudi na hada da nawa, nan ji a tasha ana mitar Kaduna haka kurum naji garin ya min,
nan nashiga motar,
Kiran sallah da akayi ne ya sasu mikewa malam jikinsa yayi sanyi alamar tausayi, inna kam harda hawaye Auta kam kuka takeyi shabe2 don sai yau tasan tarihin Ammar,
Bayan sun dawo daga sallah malam yace su huta sai gobe yaji lbr Auta da zuwan ammar kaduna, nan inna ta daura musu abinci,..
ta girka musu, dan waken dawa da wake ba karamin, dadi yayi ba, don sunyi santi inna ta iya daka yaji, don harda yar bushahen namanta, takesawa acikin yaji sai yayi zakwakwai, gwanin santi,
Da la’asar haka sukayi sallah sukazo zauna malam yace zashi dibo ruwa nan Ammar yace zan bishi, suka dau jarkuna zuwa rafi, suna yar hiran duniya akan abunda ke tafiya gar suka dawo saida sukayi sawu 3 nan inna ta dafa musu ruwan zafi sukayi wanka,…
Malam suka fita zuwa wajen gd,
suna fita suka hango yan matan kauyen sun taru a dandali, tun daga nesa suka fara gulman Ammar yau malam ya samo santalelen saurayi, wan nan tafara naa ne wancan na nawane, najaat tace kai kustsaya kuga duk cikin ku kunga da wanda ya dace sai ni, dake duk suna tsoronta ba wanda ya tanka, nan malam fa Ammar sukazo suka wuces7 zuwa shagon kauyen, garin suka sayi taliya, malam kenan akwai kokari.
0 comments:
Post a Comment