Da karfin guwa, ta soma zazzaga ma munay masifa wanda, wanda yasa munay sake baki don bata taba tsammanin ta iya masifa ba.
sai a lokacin taji muryan xarah na cewa munay kika bar wan nan mai kama da Aljanan, take miki rashin kunya, daga hannun munay ta kai mata mari, auta ko cikin zafin nama ta rike hannun, ido munay ta zaro sai a lokacin ma ta lura da kayan jikin ta, aiko take ranta ya kara baci tayi kam ta da niyar duka aiko auta ta damko ta, sai lokacin karfi ya zo mata nan ta shake munay, sai ga idonta ya fito alamar tafiya taji shaka, xahrah da kaltum suna ganin haka, sukayi kan auta zasu fara jibgarta sai ka ahyan ya shigo ko sallama babu, yana yar wakansa, ganin abunda ke faruwa, yayi kansu kai!! meye haka? Mts ya fisgo xahra da kaltum, kafin ya kwace munay, sai haki takeyi, auta ko jin wuyanta ya bushe ta wuce kitchen ta dauko faro mai sanyi, tana takun isa, ta zo falo ta taras yana fada wa munay, suna hada ido ta yi mata gwalo, nan munay takara harzuka sosai, kamar zata fasa ihu.
Auta bata gama gyara zama ba, taji tsayuwar motar Ammar da sauri tayi mike don bata son ahyan ya tafi ya barsu, zasu iya mata rashin mutunci, kitchen taje ta dibi rabin girki da tayi wa munay, duk da tasan ya masa yawa, amma don ta kularta, ta diba da yawa sosai, tazo ta wuce su tayi dakin ammar lokacin yana cire ta kalmi, da sallama ta shiga, kalonta ya tsaya yi don tayi kyau sosai, bai san har ta iso gefensa ba, sam ya shagala da kalonta sai da ta hada hannunta tana tafawa, kafin yayi firgit ya sauke wani ajiyar hrt, sannu da zuwa ta masa, ya amsa da sakin fuska, kalonta yayi, ya ce my sis gsky na iya zabe, don kayan nan ba karamin kyau suka miki ba, murmushi tayi tace na gode Allah ya kara budi, ameen ya ce barin watsa ruwa, tana zaune ya shiga dakinsa, sai da ya dau 10 minutes, kafin ya fito cikin kaya maras nauyi, abincin ta zuba masa, nan kamshi ya fara dukan hancinsa, aiko bai tsaya wata2ba ya fara diban abinci yana santi, sai da yaci yayi rabi sanna ya sha ruwa, yace Alhamdulilah.
Hira suka rinkayi yana bata dariya sai kyal2lewa takeyi, sai da aka kira sallah magriba kafin ta masa sai da safe, ta nufi cikin gd, sai da ta dan leka ta ga basa nan, ta nufi kitchen da hanzari ta ajiye cooler ta nufi dakinta, key ta saka tayi sallah haka har akayi isha’i ta kwanta.
Da safe ta hada breakfast ta dibi nata ta koma daki, bayan ta karya ta koma daki, bata fito ba sai karfe daya ta daura na rana lokacin munay na bacci, tana gamawa ta diba ta koma daki, bayan taci wanka tayi ta zauna tana duba littafin adu’ah. Sai kusan uku taji tashin mota tasan munay ce, tana tabbatar da ta bar gidan ta fito ta nufi kitchen ta gyara ta kama wasu ayukan.
Su mum sun isa sakoto lfy, tayi duk abunda ya kaita, da taso su kwana 2 amma sai aka mata kiran gagawa dole suka shirya don ta jirgi zasu dawo yau din nan 5 jirginsu zai sauka.
Auta ko han kali kwance take aikin ta, har da yar waka ta, ahyan ne ya shigo gd ya leka daki munay yaga bata nan, murna fal ransa ya nufi dakinsa ruwa ya watsa kafin ya canza kaya zuwa boxer da singlet ya nufi dakin auta, nan yaga fata dawo dakin ba, buya yayi a toilet.
Auta na gama aikinta ta shigo dakinta, bata rufe kofa ba turawa tayi don zata koma jimawa kadan ta dauko zobon da taha kafin yayi sanyi, kan gado ta fada, bata wani dade ba ta fara gyan2di, a hankali ahyan ya bude kofar, lokacin bacci barawo ya dauketa, kusa da ita yazo nan ya fara mata wani irin salon, “(ido na zaro ina rokon Allah ya kubutar da wannan baiwa daga hannun wan nan maras tausayin)”.
Auta kamar daga sama taji ana mata wasu abun da ya basa tunaninta, a hankali ta soma bude ido ganin ahyan yasa tasoma kokawan kwace kanta, amma ina yafi karfinta, sai kokarin rabata da kayanta yakeyi, da kyar ya samu ya yaga rigan jikinta, ganin daga ita sai bra yasa ta ja da baya ga hawaye da ke zuba, shiko sai wani dariyan mugunta yakeyi, haka har suka iso bangon dakin, ya nufota gadan2 tasaki wani razanane kara,
Wanda yayi dai2da shiigowan Ammar gidan, bai karasa parking ba sai ga su hajia mamu sun iso, auta ganin ba wanda ya jita yasa takara takarkarwa iya karfinta tasaki ihu ta fadi kasa sumamiya, shiko hakan baisa ya ci gaba da abunda yayi niyar yi ba.
aiko dukansu da ammar da su hajiya bansan wanda yafi wani gudun shiga ba, nima ina ganin haka na bisu da mugun dugu har sai da wayata ta fadi.
Mai karatu ban samu daman daukar wayata ba, nabisu don inji gurmin da za a toya, kar ya wuce ni, in na dauko zakujini a next page….lol…
Taku a kulum mai kaunarku Yar Mutan Kardam
®WISDOM
HAUSA WRITER’S
Rash Kardam
[7:56PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Da gudu suka nufi cikin gidan, duk a rude suke, ammar garin hawa stairs ya fuge kafarsa, nan take sai ga jini ya soma fita, amma ko ta kansa bai bi ba, yana isa yaga kofar arufe yayi zaton da key ne ajiki, komawa yayi da baya yayi wani duka ma dakin, sai yaga ko motsi baiyi ba kafin yasake naushin, H Mamu ta zo da sauri ta murda kofar sai gashi ya budu, duka suka shiga dakin, abunda suka gani ne yasa su suman tsaye, ammar da gudu ya kaima ahyan damka wanda shi gaba daya baya cikin hayyacinsa yana kokarin kire ma auta skirt yakeyi, ammar ya shake wiyarsa ya makasa da garu take kansa yasoma zubda jini, ran hajiya mamu ya baci idonta ya rufe, ga hawaye zai zuba yakeyi dai2 nan munay ta shigo ganin abunda ammar yake ma bros dinta yasa tafara dukansa wani naushin da ya mata sai da ta fadi gebe dan azaba kasa kuka tayi, hajiya mamu tazo tafara taya ammar dukan ahyan, sai da suka ga baya ko motsin, suka kulyalesa, kausar kam kuka take kamar ranta zai fita, ammar da gudu ya dauki auta yayi waje da ita wanda marabanta da gawa kadanne, kausar da H Mamu suka rufa masa baya, akabar munay da bros sai kuka take tayi.
Ni’IMA CLINIC, ya nufa gudu yakei kamar zai tashi sama har sai da yan hanjin cikin kausar suka kama disko, suna isa emergency suka nufa, da sauri nurses suka karfe ta suka shiga da ita, ba a dade ba na hango Mrs Adul cikin shigan kayan likita, tayi emergency, ammar ko kasa zaune yayi sai zagaya wa yakeyi, yana hawaye nan wani bakin ciki ya tokaresa, bai san lokacin da ya buga hannunsa a garu. Har sai da hannu tayi kass, kausar duk ta tsure da lamarinsa daman haka yake da zuciya, (ni rash nace hmm).
Can Mrs Abdul ta fito fiskan nan baya bo ba fallasa da sauri Ammar yayi gunta, Dr ya jikintan? Ta tashi kuwa? Atare ya jero mata wayan nan tambayan, ajiyar zuciya tayi kafin tace Alhamdulilah, bata tashiba amma zamu ce da sauki, amma meye ya razana ta haka don tayi dogon suma, amma muna sa ran farfadowanta a kowani lokaci, aziyar hrt ammar yayi, Mrs Abdul taci gaba da cewa, zamu kaita dakin hutu ba kuma mai zuwa kusa da ita don bata son hayaniya, suna tsaye akazo aka wuce da ita special room, hajiya mamu kam duk takasa cewa komai wai ace ahyan ne ya aikata haka, ina tarbiyan da tabasa duk yasa kafa yayi watsi da shi, in sonta yakeyi, mai yasa bazai fada mata, sai ayi musu aure ba? Dole in gwada wa ahyan bacin raina dole nasan abin yi, kausar kam kasa hada ido tayi da ammar don tana jin tsanar ahyan amma sun gode ma Allah da Allah yasa bai kita mata haddi ba.
Munay kuwa ganin kar dan uwanta ya mutu, yasa ta mike tana dingishi, ta nufi harabar gidan isa mai wanki ta ganin nan ta kwala masa kira, kazo ka taimaken, sanin halinta yasa ya biyo ta da sauki, sama suka haura nan tace ya kamata ahyan ahaka suka fito, mai gadi ke tambayan ta, maike faruwa? Wani mugun kalo tamasa wanda yasa dole yaja bakinsa yayi shiru, sabida sanin halinta, da gudu suka nufi T.H, suna zuwa emergency ta kaishi nan doctors sulayi caaa akansa basu dau lokaci ba suka gyara masa ciwon da yaji kuma ya farfado amma sun masa aluran bacci, sannan suka nufo munay suka fada mata san’nan ta tanadi kayan tea, don in ya farka ta fara bashi ruwa mai zafi ya sha, nan tayi godiya ta nufi hanyan gd.
Ammar ko ganin an wuce da auta ga kayan da ke cikinta duk ayage yake wani sas’san jikinta na aje, yasa ya nufi gd don ya dauko mata kayanta acanza mata, bai ce kala wa H Mamu ba don wani haushin su yakeji, fita yayi ya nufi gd a mota don yana hanzari baya son yin nisa da auta, gani yakeyi kamar za’a sake mata abunda aka mata, yana isa gd, dakita ya nufa ga mamakinsa bai ko ga su munay ba amma dake ba damuwar sa bane kuma baya son ganin su, nan ya dau mata fallen zani da karamar riga, sai hijab, yazo fita kafarsa ta gogu da takalmin auta nan yaji wani azaban zafi da sauri ya kali gun, sai alokacin yaga ciwon da yaji, bai tsaya takan ciwon ba yazo sauka daga stairs yaga munay tana tahowa sai dingishi takeyi, wani mugun kalo ya watsa mata, fuskansa sam ba ko annuri, kamar baitaba dariya ba, nan take wani tsoronsa ya dira mata azuciya.
Luv u all my fanz
Rash Kardam
[7:57PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Wani mugun kalo yamata, yanzu tsoron ammar ta ke baran da ta tuna nashin da ya mata da sauri ta dawo da baya, ta sauko sai da ta bashi hanya ya fita, sannan ta haura ta debi duk abunda zata diba ta dau poss dinta dake tana da kudi aciki ta nufi asibiti, tana zuwa ta nimi gu ta zauna ta zuba tagumi tana kalonsa, tana fatan Allah yasa ya tashi.
Ammar ko yana fita ya nufi dakinsa ajiye ki din mota, don shikam yabar amfani da abun gidansu kuma yau zaisa afara nima musu gd, don tabbas shine silan ja ma auta wan’nan abun, in da bai yarda yazo gidan nan ba da ahyan bai mata haka ba, ko da ya fita abokinsa auwal ya kira yace masa gd yake so mai dan saukin kudi, amma ba wanda yake da mutane da yawa ba, auwal yace an gama zuwa gobe zakaji “feedback” nan sukayi sallama ya nufi asibiti, yana zuwa yasamu H mamu suna inda suke sun zuba tagumi, nan yaji tausayinta, gsky tayi masa karamci gashi tilon danta na miji ta wasa abunda bata tana zaton zatayi ba, bata so kanta ba ta bama dan ta laifinsa, gaskiya hajiya mamu tacika mutuniyar kirki uwa ta gari, wacce take son yayan wasu ta kuma kula dasu tsakaninta da Allah, Hajiya mamu Allah yasaja miki ya biyaki da rikon gsky da kika mana ameen, amma bazan iya cigaba da zama’a cikin gidan ki ba, don tunda yasoma kuskuranta, nan gaba zaiyi abunda yafi haka ni daman hankalina bai kwanta dashi ba, cikin zuciyarsa yake magana, sai da yaji H mamu tace ammar sannu da dawowa, firgigit ya dawo hayyacinsa, Murmushi ya kakalo wanda yafi kuka ciwo yayi, ammar duk yaba ma hajiya tausayi lokaci daya duk ya canza kamar bashi ba, kausar tamasa sannu, ya amsa ya tambayesu ya mai jiki sukace haryanzu dai ba lbr, kayan ya mika musu yace ya kamata su je gd su huta, h mamu tace ina ae ba inda zata zata kwana da auta, tace kausar taje gd, ido ta zaro don auta bata tsira itama tanaga intaje abunda zai mata kenan bare uwansu badaya bare uba, don da aure a tsakaninsu, ajiyar hrt tayi kafin tace mum kata kafarki, h mamu dake babbace ta gano kausar kuma sai taji badadi azuciyarta danta yau ake gudu,(umm tsakanin uwa da danta sai Allah duk da taga laifinsa amma sai da taji wani iri, yan’uwa ya kamata mu na tausaya wa iyaye mu kyautata musu, don sun sha wahala ba kadan ba akan mu ya Allah kaba mu ikon tausaya musu da jin kansu, kaman yanda suka mana muna kanana Ameen).
Su hajiya mamu da kausar suka kwana a dakin masu jinya, shiko zama yayi a kofar dakin akwai chair azaune ya kwana da safe bayan sunyi sallah yaje ya sayo musu abinci, suka karya sai ga Dr ta zo nan suka gaidata, suka tambayeta ya mai jikin tace musu da sauki nan ta wuce office dinta, wayarsa ce tayi kara yana daga wa yaga auwal da sauri ya dauka, bayan sun gaisa yace my man an samu gida ku biyu ne aciki amma yace min daki2 ne in kana da tym sai kazo muje a nan dutsin tanshi ne, yace ba matsala na gode sukayi sallama ya kashe wayarsa, sai kusan 10 ya bar asibiti direct gun auwal yaje, sun duba gd ba laifi yayi gashi daki dadai ne, ko wan’ne da bayi aciki san’nan akwai kofa a tsakiya, sai ta waje ma akwai kofa kamar na falo ta wajen gidan sai yar karamar gate dake gun, kuma gidan na da kyau sai na dayan yana tsam’manin ciki da falo ne da bayi, sai kitchen da wani karamin daki na saka kaya, dake bauchi muna da arahan haya kudin ba masu yawa bane, 60k ne kawai nan yaga arahansa don inda a kaduna ne abun sai a slow, nan yace zaibada kudin zuwa jimawa san’an yasa aka kira masa almajirai ya biyasu yasa su wanke masa dakin don yau zai kwaso musu kayansu ko gobe.
Yana fita bank yaje ya zaro kudi a account dinsa don duk wata hajiya mamu na sallamansa da 30k kudin da take basa gashi yau kusan shekaran su 2 da wani abu, a gidan kunga ya dan samu wani abu, duk abunda ya kamata ayi anyi, yaje gida dakin auta ya kwaso mata kayan ta dake sif dinta wanda yasan’nata ne, shima ya dibi nasa, ya ajiye, kasuwa ya shiga ya sayo musu katifa manya guda 2, yazo ya ajiye, ya gaji likis gashi yanzu magriba ta kusa duk da yana lekasu ya tambayi lfy auta, yanzun ma asibitin ya nufa.
Munay tana zaune ta zuba tagumi, ahyan yasoma bude idonsa, yana kalon dakin da kyau, sannu a hankali ya komai yasoma dawo masa, kara yasaki yana kiran no! no! no!, ( nikam nace to no! Din na me nene ko yaso sai ya gama biyan bukatar sa ne? oho, ko haushin da mum dinsa ta gansa ne? Oho zamuji koma miye nan gaba).
Taku a kulum mai kaunar ku
Rash Kardam
[7:57PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Ahyan bakaramin damuwa ya shigaba, yau yasan mum dinsa tayi fishi dashi bai kuma kyauta ba, dole yaje ya bata hakuri, da kyar ya iya shan tea ya sha magani ya koma ya huta.
Yana isa asibiti ya gaida su H mamu, san’nan yanufi gun Dr yake tambayart cikin Zee tace d sauki, dakin ya dawo ya zauna a gefe, ya zuba ma auta ido ko kyaftawa baya yi,wayar H Mamu yayi ringin tana dagawa taga munay ce, da kamar bazata daga ba, amma sai ta dauka daga daya bangare akace, “hello mum ya kk? Mum duk abunda bros ya miki ya kamata kiyi hakuri ki tausaya masa, kizo ki ga jikinsa, a kan wan”nan yar da ba’a san asalinta ba, sai wai2 amma ki kyale dan ki wanda kikeso” wani tsawa ta daka mata nikaina sai dana tsorata, wato munay kema bayansa zakibi ko? Kuma kar in kuskura inji kin kara zaginta ni baruwana da shi, har sai ya gyara halinsa tukun mtss ta kashe, ammar har rashi saida yaji taisayinta don tacika uwa ta gari ba mai son kanta ba, sai yau yaji kara sonta a matsayin uwa, “Allah ya biyaki mum”, kausar ma jikinta duk yayi sanyi ammar yayi karfin hali yace mum kije ki dubasa da jiki, duk abunda zaiyi bazaki taba kankare alakar kuba, “hannuka baya ruba ka yanke ka yar” dan kine dan haka adu’ah shine mafita, taji dadi amma bata nuna ba sai kawar da kan ta tayi kamar bata jishiba.
Zee ce ta fara motsi kada2 sai tasaki wani kara take sukayi kanta dukansu, ihu take tana kiran sunan Allah, sai kuma ta soma cewa Ammar…. ammar….. Ammar kazo ka kwace ni zai kashe wayyo Allah na, wayyo mum kun tafi kun barni, ammar da sauri ya je ya kira Mrs Abdul da sauri sukazo allura ta mata take bacci ya sake daukarta, Mrs Abdul tace karku damu zata farka cikin hankalinta, ajiyar hrt ammar yayi godia ma Allah dr tafita ta basu gu.
Sai can dare ta farka, taga mum nan ta soma tuna mai ya faru kuka tayi sosai, mum na lalashinta, tea ta hada mata tasha ta kai mata ruwan wanka tayi taji dadin jikinta kafin tayi sallah.
Ahyan kuwa an sallamesa cike da tsoro da zullumi ya shiga gd, da farko kam yaki shiga sai da munay tashiga ta duba masa ko mum na’nan, taga batanan tukun ya shiga gidan.
Kausar jin munay na gd yasa tadawo kuma hauwa mai aiki ta dawo yau, tukun ta koma gd, ya rage h mamu ke ajikinta, gsky ta gwada musu kulawa.
Sai can yamma ammar yazo yana gun cuku-cuku neman shagon da zai dan sari kaya yazuba aciki, ya fara business da yan kudin da ya tara na albashin da yake samu.
Sai da ya gaida h mamu tukun ya yima auta ya jiki? ta amsa da sauki, sun dan taba hira kafin yace ma mum yana so zai roki gafaranta don ya mata laifi sai da ya bata hakuri kafin yasanar mata da hukunci da ya yanke, da farki taso taki akan sai dai ahyan ya bargidan, ammar ya nuna mata ilan hakan san’nan ta amince, sun na cikin hira Mrs Abdul tazo ta basu sallama, kaya suka tattara san’nan ya tsara musu napep suka je gudan sai da h mamu ta gyara ma auta daki duk da a gyare yake kafin ta musu salama akan gobe zata dawo.
Ko da ta koma gd tasamu ahyan ko kalon inda yake batayi ba, da gudu yazo ya rike kafarta yana bata hakuri tureshi tayi ta wuce idonta cike da kwalla, “a zuciyarta tausaya masa amma sai ta gwada masa kurensa”.
Washe gari sukaje da kausar suka duba auta tare da kayayaki bayan sun dade suka musu sallama suka dawo, washe gari ammar ya tattara yan kudin h mamu da ya sani da wasu ta kardunta ya kaimata yabata hakuri sam bata so ya bar yi mata business ba don yaron yana da “AMANA” amma ba yanda ta iya haka ta hakura nan ta dibi kudi mai yawa tabasa yayi godiya ya fito kenan suka tsaya da mai gadi sunyi hira sosai sai kusan 9:00 ya nufo gida ya sai musu nama da yan kayan motsabaki abakin titi mai mashin ya ajiye shi yazo shiga lugun gd da suka koma wasu yan’isa suka tsaresa harda wukakensu suka nuna kudi suke nema baiyi musu ba ya basu kudin da aka bashi, har sunce ya tafi dayan yace kai tsaya ban…..
Taku mai kaunar ku a kulum
Rash Kardam
[8:00PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Wani daga cikinsu ya ce tsaya, baiyi musu ba ya tsaya, daya daga cikinsu yace haka zamu kyaleshi baiji a jikinsa ba,ammar adu’ah ya ke tayi na neman tsari, gani basa kusa da shi kuma yana yin kwana zai shiga gidan da suka kama, fakar idonsu yayi yasa gudu don ya sadakar ko ya tsira ko su mishi illa, iya karfinsa yake gudu yazo dai2 shiga gidan kafin ya bude kofar gdn, wani daga cikin yan saran ya kai masa sara cikin ikon Allah bai same sa sosai ba, ya shiga gidan sakata.
Auta jin haya niya ta fito ita da matar gd sun tsaya cirko2, nan matan gd take bata lbr yan sara garin nan take auta ido ya ciko da kwala, yayanta ta tuna ko a wani hali yake oho nan ta fara masa adu’a kariya daga uban giji, suna tsaye agun sukaji an rufo kofa matar rayi daki da gudu sabida tsoro, auta kam ko motsi kasawa tayi da sauri tayi zaure tsaban dakiyar zuciya tana haska wa taga ammar da sauri tazo ta rike hannusa tana hawaye shiko ido ya runtse sabida safin ciwo sai mai da numfashi yake yi kama hannunsa da auta tayi yasa ya bude idonsa, han’nu da ba ciwo yasa yana goge mata hawaye suka nufi daki, dan kwalinta ta yanka biyu ta daure masa han’nu tana masa san’nu ya amsa.
3yrs leter
Garin kaduna wata kyakyawan yarinya na hango cikin farin ciki ta nufi gidan inspector Abubakar ko dana kare mata kalo naga futha ce ta kara girma sosai tadawo cikakiyar mace abun sai mai karatu ya ganta, cikin murna iyayenta suka tareta bayan yar kwarya-kwaryan malimar da aka shirya mata, sadiya ma ta hallara inda yanzu tagama karatunta ta dawo cikakiyar yar’jarida walima ya gudana cikin kayatarwa.
Baku tambayeni ya labarin pinky yar’rawan kai, hmm ku biyo ni kuji.duniya ta juya don yanzu pinky ko yar motar da take ja babu don yanzu dukiyar baba isiya ta kare ba abunda ya rage masa yanzu sai diabetes da tasa sa agaba har an yanke kafa daya gasa rai kwa-kwai mutuwa kwa-kwai, don shi tun daga duniya yafa ganin nasa saka makon bai ko ina ba matansa sun gujesa don tanzu ba abun duniya.
Baba sani kuwa ba laifi komai yana tafiya yanda ya kamata don har ya manta da wasu yan’uwansa da kuma yar’auta rayuwansa ya ke ci son ransa.
Garin bauchi kuwa ammar da auta ci gaba ya samu cikin she kara biyu Allah ya buda wa ammar ya albarkaci dukiyarsa da ya nema da guminsa yanzu shaguna 2 garesa na atamfa da shadda less masu kyau sai na takalma da jakukuna, wani abun dadi sunan auta yasake mayarwa, haka rayuwansu ya kasance cikin jin dadi da farinciki, watara na ammar suna zaune da auta take cemai tana son suje kaduna ko da ba dade wa zasuyi ba, ina son inga futha da sadiya don nasan bayan tafiyata suna cikin damuwa ina son inga wasu yan’uwa, ammar yace ina sane da haka don ba yanzu nake son zuwa ba akwai lokaci in muna raye don na dau wa kaina alkawarin matsawan ina raye sai na dau fansa masu Dad da mum kuma sai an yanke masu baba sani hukunci dai2 da laifinsu, auta har cikin zuciyarta taji dadi ta kuma kara masa fatan na sara.
5 weeks leter
Ammar ne a shago yana ta fama da jama’a cikinsa ya fara murda masa tun na daurewa abun har yasoma da munsa kafin kace me ammar ya fadi akasa cikin firgici yaron shaginsa ya dauwaya yana son ya kira auwal abokinsa ya kira auta cikin rudewa yake mata bayani akan zasu kaishi asibiti, sai da tayi magana ya ga ba auwal ya kira ba, da sauri ya kira na auwal akwai yace gani a kofar Central market din yanzu zan shigo da gudu yazo suka daukesa sai “NI’IMA CLINIC” auta cikin rudewa ta kira wayansa nan auwal ya daga tana kuka tace kuna wani asibiti ne yace suna ni’ima tace to gata zuwa, duk da bawani yawo take a gari ba mai napep tatsara ya kaita tana zuwa ta samu auwal sai safa da marwa yake a kofar emergency, nan yasoma lallabinta don kuka take sosai, ana cikin haka nurses tafito ta ba ma auwal ta kardan magani yace bari yaje ya sayo.
Dr tace tafito auta na ganinta ta nufeta tana hawaye Dr ya jikinsa, ta ce da sauki, ke ce matarsa, auta kamar ta ce aa ta dauka ba wani abu bane kawai sai tace eh nice ok!! Ki biyo ni office to tace Dr tayi gaba tana binta a baya sai da sukaje wani office ta nuna mata kujera ta zauna, sai da Dr ta cire glass din idonta, tace ya sunan ki madam tace Zainab, Dr tace zainab daga ganin ki kamar wayyayiya amma kina abu kamar baki san komai ba, ae yanzu kai ya waye, duk auta na cikin duhu sai da Dr tace mai yasa baki ba wa mijinki hakkinsa kinsan laifin ki kuwa Allah na fushi dake haka mala’iku suna tsine miki, ga shi kinsa mijinki cikin wani hali yanzu in ya fara bin matan banza fa hakki na kanki, don a yanzu haka sperm ya masa yawa don in bai samu ya biya bukatarsa ba zai iya shiga ko wani irin hali, auta sai da taji gananta ya fadi, dake Dr macece nasiha ta mata sosai, tukun tace ta je ta duba mijinta, sai a lokacin suka ga sun dade sosai kusan 1hrs tana mata nasiha kwatance dakin da aka kaisa tamata, auta jiki ba kwari ta fito ta nufi dakin.
Ammar ko bayan da aka masa allura ciwon cikin bai dade ba ya lafa, auwal a gefensa kusan 40 minutes yayi ya farka dake jinisa da karfi ko alluran bacci aka masa bai cika dadewa ba, nan auwal ya fara masa nasiha akan tunda auta yakeso ya fito ya fada mata ko yanimi wata ya aura, sai da yagama maganarsa kafin ammar ya fara magana da ni bana son takura ma zainab don banga alamar tana sona ba, abunda ya hanani sanar mata kenan kawai shakuwar da mukayi ne, ni kuma banjin zan zauna da wata mace kamar bazan iya mata adalci ba, zuciyata zainab take so, sai hawaye ya fara zuba masa amma zan bama zuciyata hakuri matsawan zainab taki amincewa na auri wata ko don gudun fadawa halaka.
Auta da ta dade da isowa tana shirin shiga taji anakiran sunanta, nan taji duk abunda suke fada kuka takeyi tana fadi bazan iya ba Ammar .
Hmmm karkuso ku gani alokaci idi na zaro don tsananin mamakin auta duk halaci da ammar ya miki cab… Ko dai mai take nufi zamuji nan gaba.
Taku a kulum mai kaunar ku.
Rash Kardam
[8:00PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Ammar abu duniya ya ishe sa, zaune yak’e a shago, ya zabga tagumi, wayar sa ce tayi kara ya duba yaga Auwal ne, ya dauka da sallama sa, daga ban garen Auwal yace” kana jina Ammar ta fiya ce ta kamani ta gaggawa zan fita zuwa waje,” kana leka min gun business dina komai ake ciki kana sanar da ni.
Ammar ya ce “ba matsala Allah ya k’are,” sai ka jini.
Hajiya Mamu ce zaune tak’e na zarin hukunci da yakamata ta yanke ma Ahyan, ta dad’e ta na tunani, kafin naga ta saki wani lallausan murmushi, wanda hakan yak’e tabbatar min da ta samu amsa ta.
Munay ce ta shigo gdn, H Mamu ta mata kalon tsaf tana na zarinta, sunan ta kira Munay zo nan, tazo ta zauna, a nats’e ta ke kalonta, Munay ina kike yawan zuwa kw’ana b’iyu?, ba kya yawan zaman gida, fada min?, “cikin zafin rai tayi maganar.”
Munay duk ta tsorata da yanayin Mum dinsu, kame-kame ta far’a yi, tsawa ta sake daka mat’a, Mum da… Ma..umm..um.. Wani mari ta sakar mat’a, kin bar fit’a. “sam ni ban yarda da tarbiya kawarki sholly ba.
Fada ta mata sosai, ta tashi ta bar Munay a gun.
Ahayn karatun sa yak’e ba wasa, duk randa zasuyi waya da “Munay sai ya mata nasiha sosai mai shiga jiki. Don shi yanzu ya fita harkan yan’matan b’ariki, ya kima ga Allah.
Auta z’aune tana nazarin abunda take ma Ammar sam wani sa’in bata ky’autawa amma ta rasa mai yasa zuciyarta ke sata hakan, abun na da munta, ga wasu muna’nan makarkan da rakeyi, wani sa’in ma ko ta f’arka, bakinta kasa furta addu’a ya keyi.
Haka rayuwan su ya kasance, ba d’adi, don yanzu “Ammar ya bar shiga harkanta,” tun daya gane bata son ganin sa bare farin cikinsa.
Sam ba zai iya mata wulakanci ba in ya tuna “Dad da Mun da AMANATA da suka bashi, sai yaji ba zai iya wulakanta ta ba.
Munay ke shirin ta na zuwa gun “Malam don yau’ne zai gama mat’a hadin mafani ta,da in ta tun kari “Ammar bazai iya mata musu ba.
Da kyar ta samu ta fito a gida ba tare da Mum ta ganta ba, ta dau hanyan Firo nane garin da bokan yake. Tayi tafiya mai nisa har ta kusa g’arin, tun daga nesa ta hango wasu mutane sun taru amma basa da yawa, basu fi su b’iyar zuwa shida ba, sai da ta iso kusa ne taga wata motar da tana yawan zuwa gidan Malam, kamar zata wuce ganin hatsari ne yasa ta d’awo da baya ta tsaya. Matar da tak’e zuwa a motar ne ta yi hatsari, ga wasu muna’nan magan-ganun da tak’e fada, ba dad’i ji. ” ni Jimma’i na kashe Farida, ni nayi asiri ma Sadiq ya bata, ni na haukata zainabu” da sau’ransu, abun ba dad’i ji.
“Munay jikinta yayi sanyi, tasoma nadamar a’bunda tak’e aikata wa. Kafin su bar guri “Matar nan ta cika tana ihu tana birgima a cikin dati.( Mata muji tsoron Allah kar ku d’auki zuwa gun boka a’ bu ne mai kyau, tun daga ranar da zaki sa ka f’arki sallah bazata karbu ba, ga azaban lahira ga haduwa da karshe maras ky’au, muji tsoron Allah mu gy’ara).
Munay ta shiga motarta, ta dawo gida cik’e da nadama, kuma yau zata fasa kwalban da “Malam yace asirin ciki kwalban, zai raba Ammar da Auta. Kuma zan nimi gafaran su, kar nima nayi irin wan’nan mutuwar.
Garin kaduna kuwa yau sun tashi da jimami don yau sunyi rashin “Baba Isiya, Allah ya karbi abunsa.( tabbas duniya ba gurin zama ban’e, ko kai ko ka so sai ka bart’a. Yan’uwa mubi duniya, a san’nu in ka d’auka da zafi, zaka ga da z’afi, rayuwa bata da guarantee).
Su “Pinky an shiga damuwa,” yanzu sai Mum dinta k’adai ta rage mata. “Ya Allah ka jarrabe mu, jarabawar da zamu iya Ameen”.
Auta ce zaune tana sauraron wa’zin Malam ja’afar Mahamud Adam, sosai wa’azin ke shigarta, gashi yana baya ni game da yawan Addu’a da amfanin zama da al’awala, duk sai taji kamar ta ita yakeyi, tunani ta far’a ” Yaushe rabon da na zauna da al’awa?, Yau she rabon da na yawaita yim azkhar?. Tabbas ko tantama b’abu shiyasa nak’e yawan ma farkai.
“Yaro ne yayi sallama, ana kiran Zainab a waje,” wai tazo yana jiranta. Wani gaushi ne ya tur’nuketa, mts tayi tsuka.
Taku a kulum mai kaunarku
Happy birthday to you Maman Abideen, i wish you long life n prosperity.
Rash Kardam
[8:00PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Auta ta d’ade a bakin k’ofar “Room”, duk “maganar da su k’ayi taji”.
Kuka ta k’eyi sosai tana fadin no!! B’azan iya ba, Ammar.
Ta d’ade a gun tana k’uka, sai da taji ‘Auwal na shirin fit’owa’, kafin ta share hawayen ta, nufi d’akin.
San’nu tayi ma Auwal, ta b’aye shi, ya’ya mai jikin? “Da s’auki’ ya bata amsa, a takaice”, jikin ta ba kw’ari, ta isa gun g’adon, idon sa a lumshe”tamkar mai bacci” kan “white chair” da ke gefen g’ado ta z’auna, sai da aka kira sallah la’sar kafin ya m’ike ta basa “pure water”, yayi al’wala.
Dake ” jikin sa da s’auki, “Alhamdulilah”, b’ayan ya d’awo daga sallah, ta basa abinci da aka k’awo musu yaci.
“Kw’anan uku, aka sallame su, duk w’ani hidima, “Auwal shi ya yi musu, har aka sallame su”.*****Kw’ana ki sun tafi, “Ammar ya daina gani fuska a gun Auta” ta d’aina shiga har kansa, duk ” Ammar ya fita a hayyacin sa, ya rame ga damuwa ta masa y’awa,” Auta ko bata ma san yana yi ba”.
Yau take “friday” ta fito gidan” Aunty Mamu ta kai musu ziyara” tun tana napep ta lura da “wani mai jar m’ota, yana binsu a b’aya, har suka iso k’ofar gidan su, tana sallaman mai napep, zata shiga g’ida, sallama ya mata”Assalamu’alaikum c’ikin murya mai d’adi” k’amar ana busa sarewa ya mata sallama”, Auta kamar zata shiga g’ida amma s’anin muhimanci “sallama” yasa ta amsa ba t’are da ta juya ba, cikin salo da hikima, ya ke mata magana, wanda sai dayasa ta juyo, hira ya soma yi m’ata, tana yar dariya, sun d’ade agun sosai, sai da yama sallama zai tafi tana juyowa, “Ammar ta g’ani ido sa c’ike da kw’alla ” abun gw’ani tausayi,” Auta ko kalo sa bata yi ba, tabi g’efen sa ta wuce, hmmm nikam n’ace “Auta kar ki mana haka”.
Soyayya ce mai k’arfi ta kulu tsakani Auta da Adam’s abun ba’a cewa k’omai, “Ammar ko ya d’awo “so silent” komai ya cakude masa, ga son Auta da ke barazana ga rayuwan sa”, abun sai Addu’a.
Munay ko duniya tayi d’adi, yanzu ta samu wata kawa mai suna Sholly ita ta k’ara bude mata ido, har kan gaban su kawai suka sani sune gun malamai, don su samu samari masu k’udi.
Ahyan k’uwa duniya ta masa kunci, sam mum ta fita a har kansa, gashi yau saura “3 days” ya koma “school” duk b’aya cikin hankalin sa, “ya’yi nadamar abun da ya aikata, yanzu a shirye yake da duk w’ani hukuncin da “Mum” ta yanke zai d’auka.
“Alhamdulilah, lfy uwar jiki b’abu mai fushi d’ake.
Nagode da kulawar ku gare ni, Allah ya bar zumunci” Ameen.
Rash Kardam
[8:00PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Yaro ne yayi sallama, aka amsa masa,yace”wai ana sallama da Zainab a waje”. Mts taja tsaki cike da takaici Auta tace”kaje kace waye ne?, yana fita takama guna-guni ita kadai, ni wan’nan Adam din ya wani takura wa mutum, mts haushi ma yake ban yanzu. Yaro ne ya sake daw’owa yace”wai inji Adam. Tace kace masa bata’nan, Yaro ya tafi bai kuma dawo’wa ba.
Auta tayi kw’anciyar ta, tana mai tuna abunda tayi ma Ammar, kw’alane ya cika idon ta, tabbas ban ky’auta masa ba, na dawo butulu, ta yaya ma hakan ta faru dani?, har na aika ta masa hakan ya zama dole in basa hakuri, don Ammar shine jigon rayuwa ta da farin ciki na. Kuka ne ya kw’ace mata, tana mai tuna iya’yenta, addu’a ta musu da fatan samun Rahman Allah.
Munay tana isa gida d’akin ta, ta shiga ta kw’anta a bakin gad’o, kuka taci mai isarta, tana danasani abunda ta ai’kata. Tace “Ya zama dole in’nimi gafar su Auta, matsa’wan in basu yafe min ba, bazan samu Rahman Allah ba, don na shuga gakki su. Kw’albar asirin ta da’uko, ta b’oye a hijab d’inta, ta nufi gurden, tana zuwa ta d’au katon dutsi, tayi bismilla ta kw’ad’a ma kw’albar, nan take wani bak’in hayak’i ya soma fita, gurin ya fara jujjuya mata, duk addu’a da tazo bakin ta yi take yi, sai da ta tsuguna kafin zuwa jimawa ta daina ji, da sa’uri ta mike ta nufi d’akin ta, al’wala tayi, ta fara sallah tana mai neman gafara gurin Allah.
Hajiya mamu duk shirin take yi ta na jiran dawo’war Ahyan zan iya masa hakuri matsawan zai bi umu’rnina da sharud’an da zan gindaya masa to zan iya hucewa.
Kausar ce ta i’so falon tace “Mum na gama duk aiki da kika sani. Ok!. Wayar ta ne ta yi ringing Ahyan ke kiranta, ba kaifi da fara’arta ta d’au sallamansa. Cikin ladabi yace “Mum ayini lfy?. lfyklau ya karatu?. Alhamdulilah!! “Mun ma gama yanzu results muke jira nan da 5days zan dawo, Alhamdulilah!! Allah yasa a ga saka mako mai ky’au, Ameen Ya Allah.
Cike da murna ya kashe wayar, yana mai tam’bayar kansa anya kuwa yau Mum dina ne ta amsa min magana?, kuma Batare da ta nuna fushinta ba. Hmm!! “Ya zama dole in yi amfani da wan’nan lokacin don in wanke laifina. Da wayan nan tunanin yayi bacci.
Ammar ne ke shago duk ya rame ya fita hayyacin sa, waya yakeyi da Auwal, sun jima suna tat’tau’nawa sukeyi sun d’anyi hira sosai, Auwal ya ce”ina dawo’owa gobe fa, don akw’ai abun da zanyi ran friday. Cikin farin ciki Ammar ya ce haba? Eh! ya bashi amsa, to Allah ya kawo ka lfy Ameen. Ya kashe wayar.
Auta zaune take ta gama yan aiki da zatayi, wanka tayi tasaka riga da skirt English wears, sun mata ky’au. Tana zaune taji gaban ta na yawan fad’uwa addu’a ta tsanata yi.
Ammar ne ya sh’igo kai da ka ga yanayinsa baya cikin hayyacinsa, tun daga sha’ago maransa ya soma murd’a masa, da ky’ar ya’iya k’arasowa cikin gd, yana shiga dai-dai k’ofar d’akin ya zube yana fidda wani-irin numfashi, da sauri Auta tayi kansa, ta rike shi tana kuka, tana cewa”Yaya na dan Allah ka tashi ban son irin wan’nan wasan, nasan na maka laifi wlh na tuba bazan sake ba. Ina sai wani rikon da yamata numfash’insh’i ya kara sama-sama, kai in ka ganshi bazaka d’au zaka dawo ka gansa da rai ba. Wani kara ta saki dai-dai lokacin su Hajiya Mamu da Kausar da Munay suka shigo gidan, da gudu sukayi dakin ganin halin da yake ciki Hajiya Mamu tace “Munay yi sauri ki juya motar nan zamu nufi asibiti da sh’i. Matan da ke gidan ita da mijinta suka sh’igo, mijin shiya taimaka a ka sash’i a mota suka nufi asibiti. Dr ranan da suka kawo sh’i ita suka samu. Emergency aka nufa da sh”i sun dad’e a kansa kafin Dr ta fito ba alamar dariya a fuskan ta tace “ma Auta da H Mamu su biyo ta office.
Sai da ta zauna ta nuna musu kujera suka zauna ta kalli Auta ta banko mata wata harara, “ke Zainab wato ba ky’ajin nasiha ko.
“Anya kina tsoron kamun Allah kuwa?.
Sh’in kin san hakki aure a kanki kuwa?. Cikin fada-fada take mata maganan.
Zainab ina tausaya miki, Auta kam in banda kuka marar sauti ba abinda takeyi. Cikin rud’u Hajiya Mamu tace” Dr ni ban fahimci mai kike nufi ba?, Ina son ki min karin baya ni.
“Dr bata boye ma H Mamu komai duk ta sanarma ta, “salati Hajiya Mamu ta saki ta kalli Auta, Zainab yaushe Ammar ya sama mijinki?. Cikin kuka tace”Mum nifa lokacin da muka kawosh’i Dr ne tace ni matarsa ce?, shine nace mata eh! ban d’auka abin da zata fada ba kenan. Ajiyar zuciya Hajiya Mamu ta saki,san’nan tayi baya ni ma Dr yanda zata gamsu.
Dr tace”na fahimce ku amma gsky Hajiya d’anki nacikin wani irin yanayi yana bukatar Aure don Sperm ya masa yawa. Baran yau abun yayi worse, kuyi iya k’oka kafin nan da 10days ku masa Aure, in ba haka ba zai iya fadawa halaka gash’i haisai da ya sumar da sh’i. Hajiya mamu tace”Dr in Allah ya yarda zamuyi iya k’okarin mu ayi Auren kafin 10days din. Right!! Allah ya taimaka ameen suka amsa.fitowa sukayi daga office d’in H Mamu tana ta nazarin wan’nan Al’amarin tanaga hadin dazata yi zai’zo dai-dai lokacin Ahyan ma ya dawo Allah yasa su bi umurni na, Ya Allah ka taimake ni akan had’in Auren yaran nan da zanyi Amern.
Taku a kulum mai k’aunar ku
Rash Kardam
0 comments:
Post a Comment