Wata rana Sailuba takaima k'awarta haj. Zakiyya ziyara anan ne take cewa "k'awata ni kuwa me zai hana ki karb'i Maryam?"
Wani d'an iskan kallo ta watsa mata tace "amma k'awata basiranki ya gude ne ko?kirasa yar da zakice na karb'a na raina da hannayena masu albarka"
"Hum k'awata kenan inbaki saniba ki sani rainon wannan yar shine zai baki duk wani abu da kike nema kuma ta hakane zaki cimma burinki akanta sannan zokiji" tajawo tayi mata rad'a, bushewa sukayi da dariya suka tafa sun jima suna kulle kullensu kafin su sallami juna.
Haka Maryam taci gabada samun kulawa daga ta ko wane fanni kamar yadda Nanne ta buk'ata haka dole Ammey ta cire kunya take kula da yarinyar ta domin ta kula abokiyar zamanta ba irin wannan matan bane da suke son jan d'an wani jikinsu.
Sai dai abinda yai masifar d'aga hankalin Amina shine sanda Maryam ta isa yaye kawai tace ita Maryam takeso abata tunda ita an tabbatar da bazata k'ara haihuwa ba, ita kuma Amina yanzune ma ta soma Kuma babu wanda yasan iyaka ci sai Allah dan Allah ya rok'ar mata ita ta temaka tayi mata wannan sadaukarwar.
Wani irin masifaffen tashin hankali ne yakawowa ziciyarta farmaki take tafashe da wani fitinannen kuka mai mugun k'arfi wanda yasa duk suka maida hankalinsu kanta yayin da Baffa yake dubanta da masifar mamaki Sailuba kuwa wani b'oyayyen murmushi take saki azahiri Kuma hawayene yake ta rige rigen fitowa daga idanunta ta bala in kalar tausayi ta taso ta durk'usa agabanta tareda rik'o hannayenta tana wani irin kuka mai cin rai tace.
"Dan girman Allah badan halina ba dan soyayyar da kikewa annabinmu muhammadur rasulillah (S A W) ki taimaka kiyimin wannan sadaukarwar na miki alk'awarin Maryam bazata tab'a sanin zafin cewa bata tareda mahaifiyar taba zan rik'eta da gaskiya da Amana zan kula da ita fiye da yadda bakiyi tunaniba kiyimin wannan temakon 'yar uwata" ta k'arashe tareda zubowar wasu hawayen Mai uban yawa.
Wani irin tausayin tane ya rufe Baffa yasawa ransa Koda wannan ce kad'ai kwansa a duniya ya baiwa Sailuba ita halak malak ko ba komai Sailuba 'yar uwarsa ce jininsa Koda baya raye ita mai rik'e masa 'yarsa ne.
Ta ko Amina wani mugun kallo ta watsawa Amina kuma tasaki wani mugun tsaki mai k'arfin gaske tace"Allah ya baki naki kema maman Maryam shine sunan data rad'a mata tun bayan haihuwar Maryam amma kisani kome zai faru bazan iya baki 'yata ba domin wannan ai zakunci ne ace an rabani da d'iyata wannan sam bazai yiyuba wallahi" ta k'arashe tana kuka bil hak'k'i domin yanayin kallon dataga Baffa yana mata shi yake nuna jin d'acin kalamanta, batareda ya k'ara duban inda takeba yacewa Sailuba
"Karki damu insha Allahu babu wani abu dazaki nema kirasa shi matuk'ar yayanki Baffa yana raye dan haka bazakiyi kuka rayuwarkiba" daga haka ya tashi ya d'auko Maryam dake d'akin uwarta tana baccinta hankali kwance ya dawo inda suke har lokacin Sailuba bata bar kukan datake ba yace.
"Gata nan na baki amanar ta ki kulamin da ita karki bari wani abun yasameta Kinga itake nan abinda Allah ya mallakamin a halin yanzu wannan kyautar ba kowa Allah yakewa irintaba nasan ko babu raina ke mai rik'e min 'yatane dan haka bana so kisawa ranki cewa bake Kika haifi Maryam ba haka banaso tasan cewa bakece mahaifiyar taba"
Cikin wata irin razananniyar k'ara Amina ta sulale awajen ta fad'o k'asa sumammiya take suka yo kanta cikin tashin hankali suna jijjigata Baffa ne ya tashi da sauri ya kawo ruwa suka shafa mata take ta kawo ajiyan zuciya, zumbur ta mik'e tana wani irin kuka mai cin rai d'akinta ta shige da gudu yayin da Sailuba ta kalleshi tace " Baffa ko mu maida mata da 'yarta kar wani abun Kuma yazo yana dasamun jifa abinda takeyi"
"Karki damu zata rage kinsan dole ne taji babu dad'i ace 'yarta guda d'aya tak an kyautar wanda bamu da tabbacin cewa tana da wani Kwan takakke bayan wannan musamman idan Kika duba irin yadda ta ringa samun cikin yana zubewa"
Ita ko Amina tana shiga d'akinta ta fad'a saman gado tana wani irin masifaffen kuka mai matuk'ar cin rai tasawa ranta kome zai faru wallahi bazata bawa wannan matar yar taba matar da bataso zuwan yarinyar duniyaba duk wani irin tuggu da ta dinga had'a mata wanda ya dinga sanadin zubewar gudan JININTA tana sane mutumin kuwa da baya son ganin kwanka sanyin idaniyarta a duniya ai baka da mak'iyi sama dashi mayafinta ta zara kawai ta fice agidan tana kallonsu har lokacin suna dining Baffa yana rarrashin Sailuba datace zata dawo mata da yarta.
Kai tsaye gidan su ta nufa tsabar rud'anin data shiga bai barta ta kula da malam dake zaune saman dakalin k'ofa ba ta shige d'akin Nanne wace fitowar ta kenan a wanka tana shirin zuwa duba surukar shamsiyya wacce ta sha ciwo Umma taje ta sake zuwa ita sai yau Allah ya nufa dake a tsarin malam baya yarda su fita rana d'aya sai dai d'aya taje d'aya ta jira.
Tagama zura hijabinta Kennan juyowar da zatayi taji fad'owa Amina jikinta tana wani irin mugun kuka mai masifar cin rai, take jikinta ya kama rawa ta rik'e ta da kyau tana tambayarta ta abinda ya same ta cikin tashin hankali domin tasan duk abinda yasaka Amina kuka to lallai abin yakai intaha.
Amina ta kwashe duk yadda sukayi da su Baffa ta fad'a mata cikin kuka ta k'ara da cewa 'Kuma Baffa yace ko kallon yarinyar kar na K'ara you amatsayin 'yata.
Wani fitinannen kallo Nanne ta kafe Amina dashi yayin da ziciyarta yake wani irin tasa tace
Taku ce maman Islam
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JINANA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 13
"Yanzun shi Baffan ne ya d'auke 'yar yabawa kishiyarki akan me shi ya haifa Miki yar ko su sukayi Miki rainon da nak'udar wallahi bazai sab'uba bindiga a ruwa" sosai Nanne ta hau fad'a ta inda suka shiga bata nan suke fitaba sosai ranta yai azabar b'aci ganin fad'an bazai fisshe taba ta finciki hannun Amina tana fad'in"zo muje gidan dole su baki yarki haka akeyin kyauta da abun wani mugunta"
Tana bud'e labulan suka gabza karo da malam dayagama jin komai tayi saurin ja baya tana had'e rai danma kar ya dakatar da ita dan daga kallon irin kallon dayake binta dashi tasan cewa yagama jin komai " muje ciki ko?"
Shine kawai abinda malam yace yana rab'a gefenta ya wuce had'e rai ta k'ara yi tana hararan bayan sa sai dai babu ikon musu dashi dan tun farko basu sabar Masa da hakan ba.
Waje ya samu ya zauna saman kujera mazaunin mutum d'aya yayin da Amina ta zauna agabansa ta sunkuyar dakanta k'asa ita Kuma Nanne ta zauna gefen gado fuskar nan babu alamun annuri ta masifar cin magani dan ma kar malam yace zai hanata zuwa d'aukar ma 'yarta mataki.
Gane take takenta ne yasa malam sakin murmushi yace "Zahra kenan Zahra'u manya Zahra'u sarkin rikici dan Allah Zahra in kin girma kisan kin girma inbanda abinki ina ruwanki da harkar yara 'yar nanfa tasace yana da iko akanta dan me Zaki goyi bayan rashin gaskiya to ban amince Miki zuwa ki zubar min da kima a inda nake da Martaba da daraja dan haka na kashe wannan maganar ke Kuma" ya fad'a yana nuna Amina karna sake hanin kinsa k'afa kin baro d'akin ki akan wani dalili mara tushe 'ya dai tasace Kuma yayi abinda yake so da ita ace danme kar naji kar na gani kinji ko" sosai malam ya rik'a yi musu nasiha har zuwa sanda yai shiru Nanne ta sauke ajiyar zuciyata tace "nifa malam bawai ina goyon bayan Amina bane saboda anbama kishiyarta yarta ba domin da ace suna zaune lafiyane to da hakan mu kanmu saiyafi Mana dad'i amma kishiyarta muguwar makirace datasan kan kissa ta mugunta" nan Nanne ta rik'a bawa malam irin labarin da shamsiyya ta fad'a mata da irin bautuwar da Amina take a siyasance a hannun Sailuba.
Ajiyar zuciya malam ya sauke yace "karku damu domin komai na Allah ne Kuma duk abinda yake damuwa hukuncin Allah ne dan haka kusa aranku duk abinda zai samu mamana daga Allah ne domin babu wani abu dayake samun bawa face da sanin Allah"
Sosai nanma ya kwantar musu da hankali sannan yayima Amina nasiha da hak'uri a duk halin data tsinci kanta hak'ik'a Allah baya barci, yace Nanne taje ta rakata Kennan Baffa yayi sallama' bayan sun gaisa da malam kafin yace komai malam ya soma bashi hak'uri abisa shirmen Amina har Saida kunya ya kama Baffa ya dinga sunne Kai yana dad'a bawa malam sannan yace adad'a bawa Amina hak'uri domin ansan anyi mata ba daidai ba amma yayi hakanne dan samun had'in kansu.
Malam yace babu komai Allah yabada wasu masu albarka.
Tunda suka dawo gida Amina tayi masifar d'auke kanta daga garesu ta daina kulasu duk wani aikin gidan ta ajeshi tsakanin ta dasu sai ido hatta kicin na falonta take shiga, sosai hakan yake sosa ran Baffa shi da kanshi yasan cewa basu kyauta mata ba sun nuna son ransu kuma zata na ganin cewa dan Sailuba 'yar uwarsa ce shiyasa ta nuna son Kai acikin al'amarin.
Da k'yar yasamu yasha kanta suka koma dai dai haka ma mama kamar yadda ta rad'a wa sailuba suka koma daidai amma Kuma bata Kara yarda tayi mata wannan uwar bautar ba.
Wata irin sangartacciyar rayuwa aka koya Maryam wani irin mugun gata ake gwada mata wanda babu wanda ta ragawa rashin kunya wa kowa sai anyi magana Sailuba tace ai yarinyace haka rayuwa taci gaba da tafiya an mugun tab'ara Maryam duk girman mutum bai wuce ta zageshiba.
Koda Nanne ta kula da yadda Amina ta watsar da Maryam da al amuranta fad'a ta Mata tace yau idan akace Maryam ta lalace kafin kowa yaji ciwon haka kece zakiji domin kece kika san zafinta ita adirenta ta ganta dan haka ita hakan bazai tab'a damunta ba domin batasan ciwontaba haka Nanne tayi ta mata maganganu tare da nuna mata illar kawar da kanta da tayi daga kan Maryam.
To Kuma duk yadda taso Jan yarta ajiki tareda nusar da ita hakan ya faskara see domin Sailuba ta wuce tunanin mai tunani akan komai musamman ta fannin makirci ta kware fiye da zaton me karatu.
Haka rayuwarta yacigaba a tab'arb'are babu kwab'a babu harara duk abinda take so shi ake mata a ta gefe guda kuma tun bayan da ta Kuma haifar yara maza guda biyu duk basu zo da raiba bata sake Koda b'atan wataba sosai abin ya dameta ga matsalar Maryam da Allah yayita da fitinar tsiya ga shegen rashin kunya ga d'an banzan tsokana abin ya masifar damunta amma sai takema yarta addu ar Allah ya shirya.
A b'angaren Sailuba kuwa tunda taga daga Kan wannan yara anja kusan shekara bakwai Amina bata k'ara Koda b'atan wataba hakan ba k'aramin faranta ranta yayiba dan haka ta watsar da duk wani nema da take akanta ta maida dukan wani asirinta akan iya Baffa shi kad'ai riba biyu ga Baffan ta ga Kuma Maryam data b'atar da duk wata hanya da zata gane cewa Amina ce mahaifiyar ta.
Lokacin da MD ya dawo ya tarar da irin tab'arb'are war da rayuwar Maryam yayi ga fitsara ga raini wa kowa ba k'aramin tashi hankalinsa yayiba ya dinga bin Ammey yana fad'an bata kyautaba databar rayiwar Maryam awajen wacce batasan ciwon haihuwaba amma sam Ammey tak,'i kula hakan tama daina sauraron say domin tasan cewa kotayi magana babu abinda hakan zai haifar sai fitina Kuma tun wataran da taga abin yana yawa tayi ma yarinyar fad'a ta zageta ta kuwa kamata ta zane ai kuwa ranar taga ruwan bala I a wajen Baffa dan rufe ido yayi ya tujareta har da mata iyaka da yarta abin ya k'ona mata rai sosai har Saida tayi zazzab'i saboda bak'in ciki shi kanshi Baffa da yaga kamar bai kyautaba yasa ya dinga rarrashin ta daga baya.
Da farko MD yaso jan Maryam ajiki amma Sailuba bata bada damar hakan ba domin da kanta ta dinga tusa tsanar Muhammad a zuciyar Maryam har taji duk duniya babu wanda ta tsani ta bud'a ido ta gani irinsa.
Tun yana daurewa halayyar tata har abin yafi k'arfinsa domin halin yarinyar ya wuce tunanin mai tunani, hakan yasa yai masifar tsanar wannan mugun halin nata yarinyar da ya ginu da tunanin yadda zai jata jikinsa ya gwada mata Koda gutsuren k'aunar da mahaifinta yake nuna masa amma ina makircin uwar rik'onta bazai bari hakan ya faruba.
Sanda Maryam ta cika shekara goma dai dai Amina ta Kuma haifo yaronta katon gaske sak Maryam har yaso yafi Maryam fari da manyan idanu, wannan haihuwa ba k'aramin gigita tunanin haj. Sailuba yayiba domin ta rigada tagama sawa ranta cewa Amina tagama haihuwa ita da k'ara haihuwa har abada, kamar yadda sabon bokan da suka sake ya fad'a Mata.
Tun kafin suna take tunanin hanyar dazata b'ullowa wannan yaron dan bata tab'a jin abinda ta tsana sama da wannan yaron ba duk iya yanda taso had a makircin ta akan yaron idanun Baffa ya rufe abinda ya k'ara d'aga hankalin Sailuba yadda atake Baffa yayiwa Amina kyautar wani kat'on gidansa na G R A sannan Kuma yaron wanda yayima hud'uba da Abdul Nassar yabashi companyns na takalma company data gama cin buri akai tagama tsara duk yadda zata yi ace anbarwa Maryam shine yau ake bama wani banza da uwar banzan lallai Baffa ya tarowa kansa
Ba k'aramin murna MD yai da haihuwar Abdul Nassar ba dan ko ba komai yasamu aboki duk da kasancewar sa mutum mara son hayaniya hakan bai hana sunyi wata irin shak'uwa da yaron ba.
Haka rayuwar Nassar yaci gaba da tafiya cikin tsantsar so da kulawar Ammey sa da Kuma bross d'in sa kamar yadda Baffa yasa su dinga fad'a masa.
Sosai Nassar yataso yaga yadda akema uwarsa cin mutunci a fakaici shima ya kuwa yace baisan wannan ba dan haka duk abinda akasa Maryam taiwa Ammey sai ya rama akan Mama tun suna had'uwa suyi ma yaron duka har zuwa lokacin da Maryam din ta fara rage wasu abubuwan domin daga yanayin yadda Ammey take tafiyar da al amuranta yasa ta gano nagarta da kyaun halin Ammey yasa ta sassauta mata duk da cewa ba wai ta dena dukabane.
Haka dai rayuwar yacigaba yayin da agefe guda MD yakasa jurewa fitsaran Maryam yasa duk abinda Masa yake kamata yayi Mata d'an banzan duka tun tana zaginsa idan ya daketa har azaba yasa ta daina sai dai tayi ta fad'a masa bak'ak'en magan ganu shima Kuma sai ta tabbatar databa da tazara mai yawa atsakaninsu ga wani tsinannen d'abi a da aka koya Mata na yawon club wanda mama takance tayi komai ba komai ubanta ya tara mata
Hakanne yasa Maryam take abinda taga dama kud'i kuwa ko nawa take buk'ata za a bata batare da bin ba asin abinda tayi daauba Kuma Koda an bata yanzun anjima ta buk'ata wanda suka fisu Bata za ai batare da wani bin diddigiba.
Hakanne yasa Ammey dauk'e kanta akansu har zuwa yanzun da Maryam ta fara jan d'an uwanta ajiki ta dai ce aun daina fad'a to bari mu gani da gaske ne ko Kuma wani shirin ne Maryam da uwarta suka Kuma yowa
Muje zuwa
Daga taku
Maman Islam
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________🔥BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 14
Cigaba
Suna shiga d'akinta Nassar yace "Adda ni nafasa game muje muyi kwallo kawai, kawai ko muyi basket kallonsa ta d'anyi tace "a a nak'i wayon saboda kasan kafini kwarewa anan ko" yace "to naji buga game d'in Allah yabawa mai rabo sa a"
"Hello k'awata akwai matsala fa wallahi ina cikin damuwa"ta d'aya b'arin haj. Zakiyya tace "mun shigesu wane irin matsala Kuma kinsanfa bana juran irin wannan k'ananun zantukan yanzun sai kisa cikina ya murd'a"
"Hmmm kedai bari k'awata wannan tsinanniyar matar Saida tasan yadda tayi ma Maryam asirin da gashi tana neman sawa Maryam tafi k'arfi na zokiga yadda take wani jan wannan shegen yaron ajiki wallahi karkiji zuciya na"
Itama Zakiyyan ajiyar zuciya ta sauke idan bata manta aikinsu na farko ba bokan ya tabbatar musu da cewa ba ko yaushe ne suke da nasara ba dole wani lokacin a jarrabisu da rashin nasara dan matar atsaye take itama bata sanya wajen addu a sannan babanta ma tsohon mugun matsafine" kujifa?
Sosai suka shiga neman mafita wanda daga k'arshe dole suka yanke komawa wajen tsohon bokan da suka daina zuwa tun tuni.
Maryam kuwa suna d'akin har lokacin suna buga wasa da Abdul sai rinto take masa da ya cinye saita ce ba hakaba tun yana hak'ura har shima yai zuciya ya tashi ta dubeshi "ina zaka?"
"Wallahi na daina wasan sai na cinye saikice ke baki yardaba kuma ke kike min rinto nadaina shike nan" yafad'a kamar zaiyi kuka tace "to shikenan k'anina zokaji wani abu" ya rank'wafo kamar zaijin ya kuwa d'auke wayarta daya gama fakonta ya haddace password d'inta, ai kuwa ya zuba da gudu ko takan Baffa da Ammey da har lokacin suke dining bai biba ya arce waje, can saiga Maryam d'in ta biyoshi tana fad'in "wallahi inbaka bani wayana ba saina fasa baka wannan abinda nace" ganin har ya fita itama tabishi da gudu yayin da iyayen suka bisu da kallo cikin sanyin rai.
Da gudu ya shige lambu itama ta rufa masa baya sam idanunta bai kula da dutsen ba sai data taka santsi ya d'ebe ta tafi zata fad'i tasaki k'aran firgita jinta ajikin mutum yasata sakin wani irin ajiyar zuciya.
MD wanda tun shigowar Abdul da gudu ya dawo daga duniyan tunanin daya tafi ganin Maryam ta biyoshi tana hayaniyan data saba indai antab'ota yasa ya maida hankalinsa kansu baisan ya akayi ya isota lokacin datayi sufa zata fad'iba shidai kawai yaganta ne kwance saman kirjinsa Maryam wacce sai lokacin ta bud'e idanunta ganin jikin wanda take tayi saurin tashi tare da sakin wani d'an uban tsaki, abinda yafi tsana a rayuwarsa ya fincikota da mugunta ta Kuma fad'owa jikinsa Saida tasaki k'ara saboda bigewan datayi da gwaiwar hannunsa, cikin b'acin rai yace "dawa kike? ni sa ankine da zakimin tsaki?"
Dubansa tayi taga har idanunsa ya sauya tasani Sarai idan tashiga hannunsa bazataji da sauk'i ba d'auke kanta tayi tana hararan gefe tace "ni ai ba dakai na keba da wancen nake" ta fad'a tana nuna dutsen daya tad'eta, duk da yanayin dayake ciki sai da abin yaao dariya yadan murmusa ya tun kud'eta daga daga jikinsa sai data kai k'asa ta na tashi kuwa ta galla masa harara da murgud'a baki tace dakai nakeyi me ka isa yimin yi yayi kamar zai kamota ta taka da gudu ta wuce cikin gidan.
Da yamma suka fito domin zuwa gidan malam gaba d'aya har Baffa wannan k'aida ne idan ya dawo sai yajema malam tare da dumbin alkhairansa mai tarin yawa.
Bayan sun gama gaisawa da malam Amina da Nassar sukayi cikin gidan yayin da Baffa ya tsaya anan suke dad'a gaisawa da malam anan malam yake tambayarsa ya kuwa lek'a Inna?
D'an sunkuyar da kansa k'asa yai yana sosawa cikin ladabi yace "ban Sami zuwaba har yanzu amma ina mata aike akai akai"
Malam yace "zancen banza kenan ance maka wai abin hannunka ne maganin matsalar ta karfa kamanta Kai kad'ai ne d'an da Allah yabata a duniya ina mai tabbatar maka tafi buk'atar ka akan duk wani abu da kake da Kuma Allah ne kad'ai yasan halin datake ciki akan hakan, dan haka nake umartarka daka daure kaje"
Shiru yayi cikin d'acin rai yarasa wannan masifa yarasa abinda yake damunsa shida mahaifiyarsa amma zuwa inda take ya gagaresa meke nan meyake faruwa da rayuwansa ne?
Maman Islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JINANA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 15
Sun jima sosai a wajen malam yana dad'a fad'a masa maganganu masu sanyaya jiki da karyar da zuciya sosai yaji babu dad'i shi da kanshi yana matuk'ar kewan mahaifiyarsa tsohuwar Allah ta ala amma ya kasa sauke hakkinta dayake kansa tsayin lokaci, har hawaye Saida yayi malam ya rik'a lallashinsa tareda nuna masa kuskurensa.
"Adda zo muje gidan su anty Halima dan Allah" hararansa tayi tace "bazanjeba ka manta dazu kasa Baffa ya hanani zuwa sayan kayan kwalliya Kaine kace na cika ta adin kud'i"
"Kiyi hak'uri dan Allah Adda na daina" da k'yar yasamu yasha kanta suka fito, yamma ce sosai ga uban hadari bak'i k'irin har tace su koma Nassar ya nace suka fito dai dai nan motan MD ya shigo sanye cikin kakinsa da alama ya dawo atafiya ne d'an tun ranan data k,wace suka had'u alambu basu k'ara had'uwa ba sai yau da murna Nassar yai wajensa yayin da Maryam ta d'auke kanta kamar bata gansa ba.
Kanta na k'asa batasan ganinsa, duk da kasancewar Nassar ya d'auke hankalin Shi da surutu amma dukkan motsinta yana ankare ta gefen ido yake k'are mata kallo yana mamakin yadda take da d'an Karen d'aukar Kai da mai da kai ba komaiba an riga an gama da ita ranan dayabar garin yanaji ana fad'a da ita akan ta zagi mai gadin kusa da su mama tana goyon bayanta akan wai da abin daya mata hakanan Maryam bazata zageshiba sai da dalili wannan abu ya bala in b'ata masa rai.
Sai dai masu Karin magana sunce hannunka baya rub'ewa ka kayanke ka yar dole zai koya Mata tarbiyyan da aka gaza bata tun farko amma yasani fitsara ne zaisha kala kala ita Kuma taci bak'ar wahala.
"Kira min Addanka Nassar" yafad'a cikin rashin sonaganar sa, sai da Nassar ya k'ara kallon MD dan mamakin aiken daya masa "bazaka bane" yafad'a cikin daka tsawa da gudu ya k'arasa "Adda kizo inji bross" wani banzan kallo Maryam ta watsawa Nassar kafin taja tsaki tace "ina wasa dakai ne dazaka zomin da wannan banzan sak'on?
To ka koma kace bazan"""""""""kafin tak'arasa taji d'all asaman leb'b'an ta da mugun k'arfi da sauri ta dafe bakinta tana kallon sa yadda yai bala in daure fuska saitaji wani irin shakkarsa ayau d'in, shikam k'ara tamke fuska yayi yace "wato ke maraya kunya ko kullum iskancinki k'ara gaba yake to ni d'in nan sai na gyara miki zama ke k'aramar mara kunyace wallahi kuma ku koma babu inda zaku fita da wannan hadarin"
Maryam wadda har idanunta ya fara ciki da kwalla ta juya batareda ta kalleshi ba har yana mamakin rashin mai da raddinta dan yasan hali saidata tabbatar takai tsakiya kafin ta juyo ta galla masa harara tace "kuma sai Allah yasakamin ban yafe ba" ya d'an taka kamar zai bita ta shige da gudu,
Murmushi ya d'an sosa kansa aransa yace wannan saitata ba k'aramin aiki bane andai riga da an cuci uwarta ne an lalata Mata tarbiyyan d'iya.
Tana shiga falon taci tuntub'e da k'afar Ammey da ta mik'e tana zaune saman kujera saura kad'an ta fad'i Ammeyn ta tarota "ke lafiya kike wannan uban gudun saikace wata wacca aka biyo?"
Maimakon amsa saita fashe da kuka Ammey ta d'ago kanta saita ga lebanta a kumbure gashi har sun d'an tsatstsafo da jini "waya dakar miki baki har ya kumbure haka?"kasa bata amsa tayi sai sabon kukan data fashe da.
Nassar ne yace "wallahi Ammey bross ne ya dakar mata baki da k'arfi saikace yasami sa ansa"
Hararan Nassar Ammey tayi tace "haka nan dai bazai daketaba da abinda tayi masa inba hakaba bazai tab'a taba"
Hararan Ammey Maryam tayi sannan taja tsaki tabar wajen dama rashin kunyar ta bawai ta dainayi mata neba in babu Nassar awajen tana d'an tab'awa da kallo duka suka bita yayin ta shige d'akinsu mama tana can gidan haj. Zakiyya ta rasa tsiyar da suke k'ullawa agidan wannan haj. Zakiyyar hakanan ta tsani matar ko gidan ta zo sai maman tayi da gaske take gaidata.
Bayan wata uku
Sakamakon jarrabawan su ya fito ba k'aramin farin cikin sakamakon Baffa yayiba haka Kuma haj. Sailuba tasa dole yasai mata mota matsayin gift d'in cinye jarrabawan datayi ko kad'an hakan baima Ammey dad'i ba amma bata da ikon magana tunda anyi mata iyaka da hakan amma kullum tana kaiwa mahalicci kukanta ba dare ba rana tana sane da cewa baya bacci tana fatan ya bimata hakkinta akan yadda ake d'ora mata rayuwar d'iya.
Haka ma muhammad baiso akaba Maryam sarkin rawar Kai motaba ta mama datake fita da itama bason ransa bane amma Baffa yace yayi hak'uri ya riga da yayi mata alk'awarin intaci jarrabawan duk abinda take so zai sai mata.
Hakama b'angaren cigaban karatunta Baffa yace ta zab'i duk k'asar datake son yin karatu' tace ita tace ita Dubai take so tana son gadon Baffa amma Islamic medicine sosai hakan yayiwa Baffan dad'i sai dai wannan karon Muhammad yayi nasara Dan cewa yayi k'anwarsa mace bazataje wani k'asa karatuba anan kusa dasu zatayi.
Wai Maryam batasan sanda ta fashe da wani mugun kuka ba tace "ai dama na dad'e da sanin cewa baka k'aunar mu nida mamana wai ma ina ruwanka da rayuwana ne da zakabi ka takura ka addabeni ni bana shiga huriminka amma ni duk kabi katakurawa rayuwata yadda ka tsane ni haka nima NA TSANEKA NA TSANEKA NA TSANEKA haka maganar ta yayi ta amsa kuwwa a kunnen tunda yake bai tajin maganar daya masa d'acin wannan ba sosai abin ya dake shi da sauri ya tashi da nufin binta Ammey ta dakatar dashi haka ma Baffa sukace ya k'yale ta yanzun tana cikin zafine.
Maryam bata san kukan rashi ba a rayuwarta an d'ora tane akan cewa ubanta yana da komai dan haka duk abinda take so zata samu hakan ne yasa tai masifar saka ranta da tafiya Dubai yayin da Mama take dad'a ingizata wannan dalilin yasa taji ta Kuma tsanar MD aranta fiye da yadda ta tsanesa abaya.
A b'angaren MD kuwa tunda ya koma d'akin sa maganar Baffa yake tayi masa Kai kawo "Muhammadu ka taimakemu kaja Maryam a jikinka ka rage wannan 'yar tsamar dayake tsakaninku domin duk duniya baku da kamar junanku Kai kafi kowa sanin haka sannan in Mai k'ara jadadda maka alk'awarin d'an uwana Hassan bazai tab'a tashi a banza babkoda k'asa ta rufe idonsa babu abinda za a fasa.
Sosai abinda Maryam d'in ta masa ayau yai masifar tsaye masa arai bai tab'a jin d'acin abinda take masa irin na yau d'in ba ya jima yana Kai kawo kafin ya samu Kiran gaggawa daga office dan haka ya shirya cikin sauri ya fice
Tunda ga ranan bai k'ara had'uwa da itaba dan ko fitowa tayi ta jangoshi komawa take da gaske bata son ganinsa wani b'acin rai take tsintar kanta a ciki duk lokacin data yi arba dashi.
Shi da kanshi ya nema mata makarantar da ransa yake so sai da ya gama mata komai sai sa hannun da yazama dole ita zatayi da kanta sannan ya kawowa Baffa komai sannan yacewa Baffa indai yana gari to shine zaina kaita ya kuma d'auko ta hakan yasa hankalin Baffa ya fara kwanciya.
Maman Islam CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
16
Koda Baffa yazo musu da maganar makarantar tsalle sukai suka dire kamar had'in baki sukace su indai abu daga hannun MD ya fito basa sonsa, ranan haj. Sailuba taga ruwan bala i wajen Baffa bata tab'a tunanin ya iya jaraba hakaba sannan a k'arshe yace matuk'ar tasaka Maryam ta bijirewa makarantar sai tasha mamakin sa badan tasoba ta lallab'a Maryam ranan Monday tayi shiri cikin tsananin fushi.
Cikin tashin hankali ta Kira haj. Zakiyya take fad'a mata yadda sukayi da Baffa da irin wutar daya bud'e mata abinda bai tab'a yimata ba tace "ni abinda yasa bana son kusancinta da wannan tsinannen yaron saboda" banji abinda tace mataba saijinai haj. Zakiyyar tana cewa"muci gabada shirinmu k'awata komai zai tafi yadda ya kamata itama Deedah can zataje dole ko bata so domin aikinmu yafi tafiya dai dai Kuma dole zasu zama k'awaye na irin mamakin nan ta hakanne aikinmu zaifi tafiya.
Haka dai sukaci gabada kulle kullensu wanda su kad'ai sukasan abinda suke shiryawa.
Zaune suke afalon suna d'an tab'a hira jefi jefi dan matuk'ar Baffa yana gari bazaka tab'a gane asalin halin Sailuba ba shiyasa Baffa yake ganin har tafi Amina son Maryam baisan irin wainar da ake toyawa agidansaba kuma bai tab'a ganewa ta kalan halayen yarinyar ba domin son dayake mata da kuma muguwar kisisinar haj. Sailuba bai bashi damar gane abinda take tafiyar dashi na rayuwarta ba domin ta toshe duk wata hanya da zai gane hakan da asirinta da kuma kissa.
Koda tagama shirin ta cikin wani bluen swiss mai matuk'ar kyau da tsada kasancewar ta mayyar kwalliya ba k'aramin ado ta tsarawa kantaba saikace wacce zata gidan biki.
Kanta tsaye b'angaren Baffan ta wuce dan har yagama shirinsa yau zai koma wannan karon China ya nufa dan shigo da wasu kaya dan haka shima cikin shiri tasame shi, ta d'an had'e rai tace "Baffa ina kwana?"
"Kin tashi lafiya merona?"
"Lafiya tace ganin shi cikin shiri tace Baffa tafiya zakayine?"
"Eh Maryam Kinga wannan karon na dad'e dayawa ga kayan dana zo dasu saura kad'an dan haka daga China zan wuce Dubai dan shigo da sauran kayan harda dogayen rigunan dana tab'a kawo miki to suma na d'an gwadasu suma naga sun tafi har ana ta cigiyarsu dan haka suma zan siyosu" sosai hakan yaima Maryam dad'i arai sai dai wannan karon bata nuna rawan kantaba tace "Allah ya k'ara bud'i da d'aukaka Allah ya kare mana ku Baffa daga dukkan abin ki dan fiyayyen halitta amen"
Sosai Maryam ta d'auko wasu daga hallayar mahaifiyar ta na yaba kyauta duk kankantar abu da kuma kyauta ga duk wanda take tareda dashi sannan bata da k'yamar wanda take ganin tafishi ko natane wannan halayyar yana matuk'ar burgesa.
"Baffa ya maganar motana kaga yau zan fara zuwa school Kuma bani da ko sisi a account d'ina mama ta rance bansan abinda mama take da kudiba ita bata ajiyeba kuma bata barni na ajiyeba saikace mai caca"
Sosai maganar ta yabawa Baffa dariya yace karki damu my dear zan bud'e miki sabon account komai da komai da sunana ATM kawai Zaki amsa duk sanda kikaso ciran kud'in sannan yanzun zan miki transfer dubu d'ari biyar sai ki kiyi amfani dashi kafin na dawo motarki kuma so nake ni da kaina na zab'o miki mai kyau da tsada" tace "Baffa ni kaga kalar da nake so ta fad'a" tana nuna masa fuskar wayarta zaro ido Baffa yayi sannan yace "wannan kikeso MAMAN malam tab' wannan koni bazan iya lale million 25 nasai mota dan fariyaba anayi wutar duniya Maryam nasai miki ta 5 million inba hakaba sai dai ki hak'ura wallahi"
Ganin bazatayi nasaraba tace to Baffa amma kud'in dakace zaka zuba min yayi kad'an kaga wancan karonma kafin ka dawo har na dawo abin tausayi"
"Naji zan k'ara Miki d'ari biyu akai" tace "na gode Allah ya tsare mana kai kaje lafiya ka dawo lafiya"
"Amen ya Allah dota" daga hakan Baffa ya sallameta bayan ya bata dubu dari a hannunta kafinma ta k'araso ta b'oyesu ajakar ta har sanda ta sakko suna falon ta d'an kalli mama tace "mama bani kud'in makaranta zan wuce"
Maman ta d'an dubeta tace"Baffa bai baki bane?"
"Ya bani sun min kad'an"
"Je cikin jakana inajin baza a rasa canjiba" da sauri ta shige d'akin ta fito tana k'irga kud'in, sannan ta dubi maman tace "mamana na d'auka duka dubu ashirin da biyar ne" jin abinda tace sai da Ammey ta d'ago ta dubeta suka had'a ido ta kuwa galla mata harara ta d'auke kanta, mama tace "to Maryam ki kula da kanki kiyi abinda yakaiki domin babu mamaki ya kasance wannan shine zai kasance gatanki anan gaba"
"Ban gane me kikeson ceminba mama banason irim wannan maganan dan Allah mama"
Irin wannan maganan ya zama dole Maryam domin da sannu zaki iya rasa wani abu mai muhimmanci arayuwarki ko mu ko dukiyar ko dukanmu"
Yanzun ba iya Maryam ce take kalloan maman tata ba harda haj. Amina dataji gabanta ya tsinke take ta hau karanto hasbinnallahu aranta yayin da Maryam tabar gidan cikin sanyin jiki.
A jikin mota ta hango MD sanye cikin kakinsa da alama shima daganan office zai wuce ganin yadda yai masifar had'e rai sai da gabanta ya fad'i amma dake itama jan wuya ce sai ta had'e nata ran tak'arasa zata bud'e bayan motar tsawan daya buga mata yasa batasan lokacin data bud'e gaban ba sai tsintan kanta tayi kawai a zaune jikinta na rawa.
Sai da ya daidata zamansa sannan ya dubeta yace "ke baki iya gaida mutane bako, ita mahaukaciyar 'yar rainon naki bata koya miki girmama manya bane?"
D'auke kanta tayi gefe tana k'unk'uni tare da hararan waje ya wani fincikota da k'arfi har Saida kanta ya bugu da gwaiwar hannunsa "me kike cewa ina wasa dake ne ko?"
Shiru tayi batare data tankasa saima hawayen daya ciko mata abinda tunda yake da Maryam bai tab'a ganina, karaya a tare da ita lallai duk abinda yasanya ta a wannan yanayin ba dan k'aramin abu bane.
Tunda yaga haka sai ya fasa hukuntatan ya tunkud'eta ta koma mazaunin ta ko kallonsa bata kumayiba har suka Isa makarantar ya fito itama ta fito har lokacin jikinta a sanyaye duk da rashin jinta sai yaji tausayin ta ak'asan ranshi amma Koda wasa bai bari hakan ya nuna akan fuskar Saba, har ta juya ya kirata ga mamakinsa saiyaga ta dawo ta tsaya a kusa dashi sosai yasan cewa da abinda yake damunta domin ya jima da sanin cewa indai tana cikin yanayin damuwa to ita d'in rak'umi da akalace sai yadda kayi da ita.
Dubu biyar yabata kamar bazata karb'a ba sai Kuma ta karb'a batareda ko kallon inda yake ba bare yasa ran zata gode tayi gaba abinta murmushi kawai yayi yabi bayanta suka jera yayin da idanu sukayi kansu duk inda suka gifta sai an kallesu an k'ara saboda tsabar kyau da kwarjinin su.
Sai da ya rakata ta gama komai kafin ya karb'i wayarta zaro ido tayi tana kallonsa nombobinsa ya saka ya kira ya d'auki nata daga haka ya mik'a mata wayanta yace "Allah yabada sa a"
Har ya shige motarsa tana tsaye tana kallonsa yana shiga ya juyo ganin tana wajen harara ya galla mata kafin yaja motar yabar wajen ajiyar zuciya tasaki tana juyowa wata matashiyar budurwa wacce batafi sa artaba tana tana k'arasowa inda take, tayi tareda mik'a Mata hannu sukayi musabaha tace "ni sunana Maryam Abdullah Abubakar kefa?"
Zaro ido Maryam tayi tana kallonta kafin tasaki wani k'asaitaccen murmushi tace "ni Kuma sunana Maryam Baffa Abubakar" itama Maryam kallonta tayi da mamaki tace mata" badai Baffa Abubakar mai gidajen mai ba?" Jinjina mata kai Maryam tayi sannan tace "shine kina wane b'angaren ne?"
Tace "Islamic medicine" itama Zaro ido tayi tace ai nidake b'angaren mu d'aya tace suka tafa tareda rik'e hannun juna suna murmushi Maryam Abdullah Abubakar tace "da alama kema sabuwace ko?"
"Eh yau na fara zuwa "
"Ni kuma jiya Kinga Ashe bani kad'ai nayi missing 2 weeks ba" Maryam tace "au ke jiyama kikazo Kennan?"
"Eh wallahi" haka dai sukayi ta hira har suka k'arasa cikin ajin.
Ranan basu hutaba daga wannan malamin ya fita wani zai shiga wuni gudana na ranan farkonta amakaranta bata da wani huta, Koda ta koma gidama agajiye take wanka kawai tayi ta fito neman abinci dan wata fitinanniyar yunwa takeji ko samun damar cin abinci basuyiba.
A dining ta had'u da Nassar shima shigowarsa Kennan dan shima nasu makarantar tun safe sai karfe shida suke dawowa shine makarantar da Maryam tagama wanda acan tayi sauka tareda sauran litattafai na addini Arabic ne da boko a had'e amma akwai mugun tsada.
Sun fara cin abincin kenan MD ya k'araso wajen sanye da kayan shan iska tree queter wando da riga mai yankakken hannu irin iya kafadan nan farare kar.
Zama yai yana opposite d'in Maryam yace "d'an zubamin abincin nima yunwa nike ji sosai" yayi hakanne ak'ak'arinsa nason janta ajiki kamar yadda Baffa ya buk'ata, kallonsa tayi da mamaki dan a saninta ko abinci yazo ci yagansu ita da mama a dining d'in ya hak'ura yau Kuma ya da ahaka sai dai ko kallonsa batayi ba taci gaba dacin abincinta.
MAMAN Islam CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 17
Kafe ta yai da manyan idanunsa yayin datai bala in d'auke kanta tayi kamar bata san da zamansa awajen ba ganin haka yasa yajanye nata abincin yafara ci shima cikin d'aure fuska.
Dagowa tayi ta dubeshi ta ko ina bataga alamar wasaba dan haka takai hannu zata d'auki ruwa shima ya dafe hannun batareda ya kalleta ba haka Kuma bai daina cin abincin saba janye hannun ta tayi ta mik'e batare data tanka Masa ba tabar wajen' bin bayanta yayi da kallo har ta shige d'akin ta, kai tsaye toilet ta shige ta d'auro alwala tazo tagabatar da sallar magriba bayan tayi addu o i sosai sannan tafara karatun alqur ani mai girma har zuwa lokacin da aka kira sallar isha sannan ta rufe qur anin tayi ta addu o'i har zuwa sanda aka shiga masallaci tabi jam 'i daga nan cikin d'akin ta duk abinta bata sanya da addu a sam bata da wasa a wannan fannin.
Nassar ne ya lek'o ganinta ninke sallaya ya koma da gudu tana kiransa amma bai dawo ba, can kamar wajen mintuna uku sai gashi ya sake dawowa da sallamar sa ya shigo ta d'ago tana mallonshi tace "da gulmane yasa ka lek'o ka koma kamar w""""""""""" ragowar maganar ne ya mak'ale sakamakon ganin wanda ya biyo bayansa take ta maida kallonta ga Nassar tana hararan sa murmushi ya mata tareda salute nata ya juya jin kiran da Ammey tayi dan haka ya wuce da d'an tsallensa.
Juyowa tayi asanyaye har yayiwa kansa zauni asaman kujeran gefen gadonta "k'araso ki zauna hira nazo tayaki" wani kallo ta watsa masa amma batace komaiba sai uban bugu da ziciyarta yakeyi sai kawai taci gabada gyaran kayanta data soma tunda safe batasan tashinasba sai jin hucin numfashin sa tayi daf da ita a d'an firgice ta juyo saura kadan ta fad'a jikinsa saboda yadda ya matsota kamar zai shige jikinta tana k'ok'arin janye jikinta yayi saurin dafe kafad'unta ya kafeta da idanunsa mai firgita masu kallonsa d'auke kanta tayi gefe tana tura baki tareda k'unk'uni "me kike cewa nida nazo muyi hiranmu nayaya da k'anwa shine zaki shareni ki hau aikin nasan ba dan Allah kikeyinsa ba"
Bata iya tace masa komaiba saboda kusancin dayake tsakaninsu hakan yasa takasa wani kwakwaran motsi har jikinta ya soma d'an rawa rawa, wani murmushi ne ya kwace masa ganin tsoro k'arara kwance cikin idanunta,sakinta yayi ya koma inda ya taso yace "zoki zauna labarin abinda ya faru a makaranta yau zaki bani, sannan me da me aka koya muku duk abinda baki gane ba Kuma ni zakizo ki tambaya"
Ita dai tsabar mamakinsa ya hanata tankawa domin tasani cewa duk duniya babu wacce yatsana sama da ita da mamanta gashi yanzu Kuma yazo yana wani shige mata anya ba wani muguntar yake shirya mataba Kai ita Kam tana kokwanton wannan shige matan da yake.
Shi Kam duk yadda yaso janta da hira takasa sakewa dashi saima shakkunsa dayake hangowa a kwayan idanunta amma babu komai shima duk da badason ransa yake biye matanba zai daure yaci gaba har sai yaga ta saki jiki dashi.
Washe gari da wuri tayi shiri ko Kari bata tsaya tayi ba duk a shirinta na tserewa MD bata son abinda zaina had'a dashi dan ta bala in tsanar say wallahi har cikin zuciyar ta, sai dai ta makaro domin tana fitowa ta hangoshi jikin motarsa a tsaye ga draiver agefensa shi Kuma hankalinsa yana kan wayarsa yana faman latsawa.
Har ranta taji sanyi dan tayi tunanin shi zaisa yakaita dan haka a nutsenta ta k'araso tazo d'an gefensa taja ta tsaya batareda ta tankawa kowa cikinsu ba mai gadin ma datake gaidawa yau dan karta gaida Muhammad yasa taki gaidashi, shi Kam ko ajikinsa saima mota daya bud'e mata yace shiga, babu musu ta shiga driver ya shiga ga mamakinta sai gani tayi ya zagayo tadayan b'arin ya shigo', d'ago kai tayi da niyyar kallonsa suka had'a ido d'age mata gria yayi "ya dai?" ya yace yana kallonta d'auke kanta tayi kamar bataji me yace ba tunda suka shiga ya maida hankalinsa Kan computer yanason k'arasa wani aiki kan ya isa office.
Yau ta riga Maryam zuwa dan da wuri ta fito yau ma kamar juya 5k yabata batason dogon magana yake had'a ta dashi dan haka yauma amsa kawai tayi ta wuce yabi bayanta da kallo har ta b'acewa ganinsa ajiyan zuciya ya sauke sannan ya juya ya shiga mota driver yaja.
Tafiya take a nutsa tana tuna maganar da sukayi da mama yanzun kafin ta fito inda take ce mata"Maryam kiyi yadda kikeso kiyi abinda kikaga dama rayuwa bashi da tabbas inke kece yau gobe wanin kine abinda yake hannunka zai iya kwacewa ya koma hannun wani sannan rayuwa takan sauya mai bud'i ya koma talaka, shi kuma talaka ya koma me k'udi dan haka kiyi amfani da lokacin ki sannan kiyi amfani da damarki dan duk lokacin daya kubce miki bazaki sake samun irinsaba" sosai maganganun maman yake tsinkar Mata zuciya tabbas tafi kowa sanin halin mama bata maganan banza tunda ta dage akan wannan akwa k'arkarfan dalilinta haka nan yauma dazata fito dubu hamsin ta bata duk da wannan ba komai bane awajen maman amma tana mamakin yadda take bata kud'ad'e akai akai har dubu d'ari biyar tana bata musamman intasan tana da wani casu ko shagalin k'awayen ta' tana tsaka da wannan tunanin wanda yai matuk'ar d'aukan hankalinta taji tayi karo da abu kafin ta d'ago dan ganin waye an d'auke ta da wani matsiyacin mari wanda yasa saida tasaki jakarta da wayarta suka tarwatse awajen amatukar fusace ta d'ago sukayi ido biyu "me na maka dazaka mareni?" tayi masa tambayar hannunta dafe da kuncin ta "ubanki Kika yimin dan uwarki hanyar ta ubankice da zaki taho kina mana rangaji har ki buge mutane"
Itama fusata tayi tace saidai ubanka dan uwarka hanyar ta inaga naka ubanne ya ginata d'an iska wawa jaki dabba kuma wallahi ina mai tabbatar maka sainaga waye ubanka ak'asar nan sanaga g"..........kafin ta k'arasa ya Kuma d'auke da wani mugun marin take jini ya balle mata ta hanci da gefen bakinta durk'ushewa tayi awajen saboda jirin daya fara kwasar ta shima tsuganawar yayi agabanta ya d'ago hab'ar ta ya kalli cikin kwayar idonta yace kije ki turo duk uban da kike tak'ama dashi"
Duk da bak'ar azabar daya gauraye mata fuska haka bai hanata "furta cewa zaka gani ina mai tabbatar maka cewa saikaga gatana wallahi zakasan ni katab'a saikayi nadamar zuwanka duniya yau" ina jira 'yan mata ya fad'a tareda barin wajen take duk mutanen da suka cika wajen suka watse basuyi mamakin d boy ba domin takadirin d'an iska ne ya addabi kowa amakarantar gaba d'aya kowa tsoronsa yake hatta da malamai ma basu da ikon hukunta KAMAL ABBA AL HASSAN d'a d'aya tilo ga mahaifinsa alh. Abba AL HASSAN wanda yasamu dukkan dama da sake yake yadda yadda dama arayuwarsa.
Saida kowa ya watse sannan Maryam ta k'araso wajen d'ago fuskar Maryam tayi yadda taga yayi kaca kaca da jini ga gefen idonta har yayi kwanciyar jini batasan sanda ta fashe da kukaba tace "ke kuwa name sake me ya had'a ki da wannan azzalumin d boy d'in wanda bashi da mutunci ko kadan jifa yadda yadda ya mayar miki da fuska?"
Bakin ciki bai barta ta ce komaiba sai wayanta data Mik'o mata bayan ta cire code "kiramin mamana" shine kawai abinda Maryam ta iya cewa daga haka ta yanke jiki awajen ta fad'i a sume, take Maryam ta Kuma rud'ewa jikinta ya kama rawa garin ta kira mata maman ta dannan no MD wanda yai save da MY LOVELY BROSS yayi hakanne dan tsokana sai akayi rashin sa a ko dubawa ma batayi ba.
Shiganea office kenan babu dad'ewa kiran yashigo saida yai matuk'ar mamakin ganin kiran nata domin yasan ba k'aramin abune zai saka Maryam kiransa zaima iya cewa tunda suke da ita bata tab'a kiransa ba, kamar kada ya d'aga sai Kuma yace baisan dalilin kiranba bari ya d'aga yaji ko wani abunne.
Memakon muryanta muryan wata daban yaji tana kora Masa abinda ya faru cikin tsantsar tashin hankali ransa ne yai wani irin mummunan b'aci take jijiyar kansa tayi wani irin rud'u rud'u tsabar azabar fushi mik'e wa yayi a fusace yana kiran waya yai waje ko takan driver bai biba ya figi motar da mugun gudu yayin dayai magana cikin d'acin rai ta waya.
Cikin kankanin lokaci ya isa makarantar har lokacin tana jikin Maryam tana faman girgizata yayinda mutanen da suka dad'a dawowa ganin Maryam ta sume wasu na bada shawarar akaita asbiti wasu na fad'in akaita gida tunda ansa mata ruwa a fuska bata farko ba.
Cikin takun izza da isa ya k'araso wajen fuskar nan tasa babu d'igon rahama ya k'araso mutane suna ganinsa sanye da kaki tare da rubutun matsayin sa ajikin wannan d'an k'arfen da suke rubuta matsayin mutum ajiki an rubuta LIEUTANANT GANERAL MUHAMMAD BAFFA ABUBAKAR kafin kice me mutanan sun watsa, bai tsaya bin ba asiba ya sab'i 'yar uwarsa Maryam ta rufa masa baya.
Daga taku har kullum MAMAN Islam CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMANA ISLAM
Page 18
Asbiti mafi kusa ya nufa da ita ransa amasifar b'ace aransa yana ayyana irin hukuncin da zaiwa wannan yaron dan yasha alwashin saiya gane kurensa tunda ya tab'a masa 'yar uwarsa.
Acan makaranta kuwa anfita da Maryam Kennan wani abokinsu ya k'araso wajen su d boy yace "abokina kaga yawan sojojin da sukazo suka tafi da wannan yarinyar kuwa?"
Wani banzan kallo d boy ya watsa masa "to sai me dan tasan wani daga cikin sojoji Allah yasa bakin bindiga tasani kafa riga kasan koni waye Man kaf k'asar nan mutum bai fi biyu zuwa uku ba suke da damar iya hukuntani dan haka zanci haba da yin yadda naga dama ni kad'ai ne awajen ubana kuma yatara min shegun so kaga dole na warwasa son raina"
"Kasan d'ayar wa daka kuwa?"
"Koma 'yar uban waye dole gobe taji tsoron bin hanyar danabi"
Man bai tsaya sauraron ba yace "yar gidan BAFFA ABUBAKAR ce fa"
Duk da cewa gabansa yayi mugun fad'uwa amma Saida yace "wane banza ne haka har girman ikonsa yakai na ABBA AL HASSAN be?" Kafin ma Man yabashi amsa moticin da suka shigo na sojoji kusan guda shida suka faka agefensu ak'alla sunkai su ashirin ko ma sama su kansu malaman makarantar tunda sukaga wannan gangamin sannan ba wani taro suke ba suka tabbatar babu lafiya.
K'arasowa sukayi inda su d boy suke wani daga cikinsu yace "waye kamal d boy anan wajen?"
"Lafiya kuke nema na ko naci ban biyaba ne har aka yo mun gayyar masu gadi haka"
Wata irin damk'a d'aya daga cikinsu yayi masa turoshi gaban sauran da mugun k'arfi har saida yai baya zai fad'i suka wani talle masa k'eya suka cakume gefen wandansa suka jashi zuwa jikin motarsu.
"Kunsan koni waye kukema wannan wulak'ancin? wallahi zakasan ni kuka tab'a dukanku sai kun rasa aikinku sai kunyi nadamar abinda kukayimin" duk cikinsu babu wanda ya tankashi har suka figi motocinsu da mugun gudu sukabar wajen take hayaniya ta kaure kowa da abinda yake fad'a wanda ya raina kuwa hakan ya musu mugun dad'i ko ba komai an karya alkadarin sa.
"Ba wani mummunan rauni tajiba b'acin raine yasa ta suma amma mun shawo kan matsalar sai dai gaskiya ku dunga kiyaye shigarta irin wannan b'acin ran dan zai iya jawo babbar matsala" wannan shine bayanin shine bayanin da Dr yaima MD.
Bayan ya fito a office d'in Dr d'akin dataken ya dawo tana zaune ta jingina bayanta da d'an k'arfen gadon har lokacin bak'in cikin abinda d boy yai mata bai gama sakinta ba sannan taci alwashin saita rama Koda hakan zai haifar da ko wacce irin fitina.
Hannu kawai taji yana yawo saman fukarta tayi saurin d'ago kanta' ganin MD tayi cikin wani irin masifaffen fushi wanda bata san yana da irinshi ba, saida yagama share mata hawayen da suke ta faman gudu sannan ya maida hannun inda yatsun d boy sukayi rud'u rud'u wajen yayi wani irin ja "me ya had'a ku da har zai kamaki yayi miki irin wannan dukan saikace wata yarsa"
Jin yanayin da yai maganar yasata d'ago ta d'an kalleshi ganin babu wani alamun wasa yasa ta kwashe duk abinda yafaru ta fad'a masa jikinsa har wani tsuma yake tsabar b'acin rai.
Mik'ar da ita yayi yabata mayafinta da takalmanta ya kama hannunta sukayi waje basu zame ko inaba sai inda yasa aka kai d boy kafin yaje yayi mugun laushi mari uku kacal yayiwa Maryam amma shi yasamu mari kala kala fiye da kala d'ari tuni kamannimsa suka sauya banda bulalar dayashi dan cewa yayi karsuyi masa dukan wasa dama yana ciki da ubansa Abba AL HASSAN wanda suke ta fafatawa dashi akan wani case da suke zarginsa.
Sanda suka shiga wajen tuni d boy ya jima da suma domin ba k'aramin jin jiki yayi ba duk da mugun haushin sa akan abinda yayi mata saida yabata tausayi ganin yanayin daya shiga balle itama mace mai matuk'ar tausayi da rauni take ta fashe masa da kuka tace ita tayafe dan Allah ya rabu da d'an mutane kar su masa illah, ganin yadda ta d'aga hankalinta yasa yace kar tadamu dama d'an gargad'i ne kawai sukayi masa dan gaba ya kiyaye yasan cewa duk matsayinsa duk abinda yake tak'ama bakowa zai tab'a ya kwana lafiya ba.
Daga nan gida ya wuce da ita lokacin haj. Sailuba ta fito haraba tanama driver magana zasu fita motansa ya ahigo sarai tasan motarsa ne yasa ta d'an dakata dan tanason masa gargad'i akan 'yarta duk da cewa Baffa ne ya bashi dukkan dama.
Ganin Maryam ce tafara fitowa daga motar yasa tai bala in had'e rai mugun kallo ta rik'a binta dashi har ta k'araso inda take tsaye ganin irin shatin marukan dake kwance saman farar fatar fuskar ta yasa a rud'e takamo fuskar da duka hannayenta tace "baby wanne azzalumin mara imaninne yayi miki wannan d'anyen aikin, wane la'anannen ne wanda bazai gama da duniya lafiya ba, nan dai ta zage tana ta zuba ruwan rashin arzik'i duk a tunanin ta MD ne yayi mata domin dama shine yake iya mata dukan dabata isar d'aukan mataki ba sai dai ruwan tujara da rashin mutunci koda taji cewa bashi bane hakan baisa tayi shiru ba sai datayi mai isarta ranan fitar dabata samu tayiba Kennan.
Ita kanta Ammey ganin irin zaluncin da akayiwa Maryam d'in sai da taji ajikinta amma bata tankaba kamar ko yaushe idone nata amma har kullum bata fasa yiwa 'yarta Adda a ba.
_________________________
B'angaren abokan d boy kuwa ana barin wajen dashi d'aya daga cikin abokansa ya bugawa alh. ABBA AL HASSAN waya ya sanar masa, take ransa yai masifar b'aci cikin tsawa yace"wane me zarrar ne yake da k'arfin gwaiwar kama d'ana wanene shi wane me tsautsayin ne lallai inason sanin wanene shi"
"Dad yar gidan BAFFA ABUBAKAR ya daka yau amakaranta shine yayanta ya turo aka kamashi" innalillahi,wa inna ilahi raji'un shine kawai abinda Abba AL HASSAN ya iya fad'a kafin ya zube saman sofa dake office d'in lallai yau Kamal ya janyo masa wata sabuwar masifar da baisan ta hanyar da zai magance ta.
MAMAN Islam CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 19
Yajima yana gabza bala e kafin ya fice daga office d'in cikin tashin hankali,kai tsaye gidansa ya nufa lokacin haj. Maimuna tana hakimce saman kujera ta d'ora kafa d'aya saman d'aya mai aikinta tana durkushe agabanta da alama wani umarnin take bata.
Tana ganin shigowarsa ta sallami mai aikin sannan "sannu da zuwa alhaji lafiya naganka tun kafin lokacin tashin yayi"
"Na gaji nagaji nagaji haba dan masifa wallahi maimuna kin haifi masifa kin haifi fitina haka kawai ina zaman zamana zai je ya d'auko min masifar da bazan iya magance taba wallahi ba ruwa d'an iskan yaro haihuwar asara t""''"""''''''' dakata malam Kaine haihuwar asarar ba d'ana ba me yai maka zaka zo kasashi gaba da masifa ai duk wannan tsinannen bakin nakane yake binsa"
"Zanci" ya lailayo wani katon zagi ya lafta mata,nanfa rigima ta balle wannan ba sabon abu bane agidan Abba AL HASSAN indai ransa zai b'aci ta ranar babu zaman lafiya.
Washe gari bayan tagama shirinta a dining ta tadda Nassar yana kari ta harareshi tace " um su acici har an fara afawa
Maman Islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 21
Haka tacigaba da karatunta cikin nutsuwa tun tana tunanin maganganun maman har tasaba ta daina saka abun aranta amma hakan baisa ta daina siyan muhimman abubuwaba aduk lokacin data ganta da wasu 'yan k'udi masu nauyi, yayinda wani irin shak'uwa mai ban mamaki ya shiga tsakaninsu da name sake d'inta dan haka bata da aminan daya wuce Maryam da Halima.
Abangaren d boy kuwa da farko saida yaci alwashin d'aukan fansa Abban sa ya taka masa burki yace"kul dan ubanka karkaja min mutuwa kwanana basu K'are ba wannan yaron da kake ganinshi bashi da ruwan mutunci ko kadan dan iskane nake bafad'a maka nagaban kwatance dan haka ka nisanci wannan yarinyar domin ba 'yar kowa bace face'yar Baffa Abubakar"
Saida d boy ya razana dajin abinda Abban nasa yace domin kaf yankin nasu babu wanda baisan waye Baffa Abubakar ba saboda tarin dukiyar da Allah ya hore masa da d'umin karamcin sa ga bayin Allah, sannan agefe guda yasha mamakin yadda take rok'on yayanta da ya k'yale shi haka duk da yadda ake fad'an rashin mutuncin yarinyar take yaji duk wani burinsa akan d'aukan fansa ya ruguje saima k'ok'arin son kulla alak'a da ita.
Agidan su Maryam kuwa babu abinda ya sauya sai tsarin yawon inda yanzun haj. Zakiyya ce take zaryan zuwar musu wanda idan suka shige d'aka har mantawa ake dasu dakehaj. Amina babu ruwanta da ahiga abinda babu ruwanta bata tab'a sanin wainar da suke toyawaba.
Yayin da MD ya diga ayar tambaya akan wannan ziyarar takawar wannan matar mara yankewa hakan yasa batareda da sanin kowa ba ya nemo CCTV camera saida yabari ranan sun fita gantalin bin malamansu da suka saba yasa aka jona aka saita komai tareda recording d'in duk abinda zai rik'a faruwa akaf gidan ta ko ina har d'akin Ammey batare datasan anyi hakanba.
Rannan MD ya kawota makaranta dake sauri yake abakin get ya sauketa sannan yace idan lokacin tashinsu yayi ta fad'a masa zaisa driver ya maidata gida yau yana da wani meeting wanda sai dare yake tunanin zasu dawo k'ala batace masaba kuma dama yasan basatace d'in ba, bai jira komaiba yaja motarsa da azabar gudu yabar wajen.
A hankali tafara takawa zuwa bakin get d'in tunda tafara zuwa makarantar shekara d'aya kenan da d'an wani abun bai tab'a ajeta anan d'in ba sai yau, ta kusa kaiwa bakin k'ofar kamar yadda ta saba koda yaushe sai ya kaita har parking space na makarantar sannan zai ajeta ya juya.
"Hey hey" taji muryan wanda bazata tab'a mantawa ba arayuwarta domin shine mutum na farko da babu wanda ya tab'a yi mata irin tozarcin da yayi mata, batasan lokacin data saki wani matsiyacin tsaki ba ta juya yayin da shi kuma yayi saurin shan gabanta da motarsa, a mugun fusace ta d'ago ta watsa masa wani mugun kallo sanda yake fitowa daga cikin motar.
Yana k'arasowa bata bari ya fad'a mata wani abuba tayi saurin cewa "wai kai wane irin mutum ne mara tunani wanda baisan darajan kansaba bare na waninsa?
Yau kuma takeni kake sonyi komai?
Wai dan Allah me yasa wasu mutanen baau da tunani ne kwakwalwarsu irin na kifine?
Yo inba hakaba ni banga dalilin gamin kifi da gada ba dazaka wani zo ka shamin gaba ina cikin tafiyana idan kuma hukuncin farko ne bai ishekaba akwai wanda sukafi wannan sai ka jira.
Duk abinda take fad'a bai katsetaba saida yabari tagama maganar ta kafin yace 'Amincin Allah yatabbata ga sarauniya kuma shugabar masu yafiya, ba wani abune yasa na tareki anan ba sai dan na k'ara neman yafiyarki abisa abinda ya faru duk da nasan cewa saboda ke wannan boss d'in yayan naki ya k'yale ni amma duk da haka ina mai kara neman afuwarki na miki alk'awarin ko kallon banza bazai k'ara had'a ni dakeba pls pls pls" ya rik'a maimaitawa yayin da tayi masifar d'auke kanta ta juya da nufin bar Masa wajen batasan ya akayiba sai kawai ganinsa tayi zube agabanta basa gwaiwoyinsa yana cigaba da rok'on yafiyar ta bai ko damu da yadda mutane suka fara taruwa awajen ba.
Zaro idanu tayi ganin yadda ya zube saman gwaiwoyinsa ga mutane da abin kallo baya musu kad'an har sun fara taruwa awajen tayi saurin cewa "meye haka dan Allah jifa har an fara taruwa anan katashi"
"Ni ba damuwana masu kallona ba damuwana kawai kice kin yafemin"
"Tashi dan Allah" ta fad'a cikin sanyin murya "zantashi ne kawai idan kince kin yafemin"
"Na yafe maka amma bisa wani sharad'i to tashi" tasake fad'a can k'asan mak'oshi da sauri ya tashi yana fad'in"na gode na gode sosai ko wane irin sharad'i ne ki fad'a na miki alk'awarin tunda dai kin yafemin" fad'a yana binta lokacin data fara takawa cikin makarantar,bayan yabawa d'aya daga cikin abokansa mukullin motarsa suna takawa a hankali yayin da ta fara ce masa.
"Gaskiya yakamata ka gyara halinka da d'abi unka ba abune me kyau ba kowa ya rik'a maka shaidar baka da mutunci babu wanda ka ragawa har akai ga matakin da kowa zai fara jin tsoronka sam wannan zalunci ne babba dan Allah ka gyara kaga ni d'innan dakake gani duk abinda kake ji dashi nafika ko ranan ma shammata na kayi banda haka bazakayi nasara akainaba sai dai ni bana shiga harkan wanda bai shiga nawaba dan haka kaga ko makarantar nan banda kawa sai A A"
"Nasani sam ban kyautaba kuma na miki alk'awari insha Allah daga yau nima babu ruwana da sabgar kowa"
" Allah yasa" ta fad'a atakaice tana wucewa department d'insa.
Yana tsaye har ta shige murya k'asa k'asa yace "tamin Allah yasa tasoni nidai tamin badan komai ba sai dan nutsuwa da ajinta Abba kayi suruka irin wacce kake so 'yar wani wanin ma wanda yai suna aciki da wajen k'asar nan"
(Su Kamal d boy daga sannu sarkin fawa lol🤣🤣🤣)
Yau kam da wuri suka koma gida dake lacca d'aya ke garesu suna gamawa babu wani jinkiri Maryam ta nemi da A A ta rakata banki tana son bud'e sabon account, da mamaki AA take dubanta kafin tace "ke kuwa name sake duk yawan asusanku wanda ba ayi miki iyaka dasuba sai kin bud'a wani?"
Bazaki gane bane sam mama bata barina da k'udi ita zata bani kuma ita zata dawo ta rance na rasa abinda mama take da k'udi duk yawan kyauta irin na Baffan mu wallahi A A Saida mama ta kureshi" haka dai suka tafi tana bata bad habits d'in mamanta wanda abin yake masifar damunta ta kuma rasa dawa zata zanta taji sanyi saifa yanzun dataji ta aminta da ita.
Har sukaje suka bud'e account kud'ad'en da Maryam ta zuba a account d'in saida abin ya bata tsoro yayin da Maryam ta dinga mata dariya daganan tace Maryam ta rakata kasuwa zatayi siyayya sai da suka fara zuwa tasiyi kayan kwalliya da turarukanta dake Maryam mayyar turarece zai wuya ka kusance takaji bata k'amshi domin ita d'in 'yar gayuce tagaban kwatance hakan yasa take da masifar farin jini Saidai halinta bai barinta shiga sabgar mutane domin bata da kirki ko kad'an.
Daga nan Kuma suka nufi wajen masu saida kayan abinci A A taga Maryam ta d'auki babban buhu na shinkafa da k'arami sannan ta d'auki taliya carton biyu haka makaroni da cous cous da semonvita irin buhunnan mai guda sha biyu shima guda biyu manja man gyad'a Maggi kanshi saida ta d'auki carton guda banda sauran spacies data d'iba ita dai A A kasa daurewa tayi tace "name sake nasandai abincin gidanku trela ake kawoshi me zakiyi da wannan abin da kike ta loda?"
"Ba damuwarki bane" cewar Maryam datakewa mai shinkafar maganan ko zasu samu motar da zai kwashe musu dukan kayan? dan adaidaita yayi musu kad'an.
"Akwai 'yar k'ur k'ura wanda shi dama aikinsu Kennan d'iban kaya sukai maka duk inda kakeso' ya fad'a yana kwalawa wani kira.
Tun tambayar da tayi mata tace ba damuwanta bane bata k'ara tofa nataba abinda ya Kuma d'aure mata kai shine ganin motar bai faka ko ina ba sai k'ofar gidansu da mugun mamaki ta rik'a kallon Maryam wacce ta d'auke kanta batare data bari sun had'a ido ba.
Suna tsaye har aka gama shiga da kayan abinci sannan ta sallami mai motar suka bi mai d'aukan kayan na k'arshe, shima ta sallame shi yayinda suna shiga suka tadda Umma da Abban Maryam da shima shigowarsa Kennan gidan aka fara shiga da kayan daya fara tunanin ko b'atan kai masu kai kayan sukayi amma yana ganin Maryam da Maryam sun shigo ya dingabinsu da kallo fuskarshi da alaman tambaya.
" Ku zauna mana Abba"
Maryam ta fad'a tana zaran buta tayi bayan gida, sam Maryam batada k'yamar mutane musamman inkana da tsabta dake it's mutum ce mai tsananin tsabta da k'yamar k'azanta, tana fitowa tayi alwala tayi d'akin Umman su A A ganin haka yasa itama Maryam tayi alwalar tabita d'akin.
Tana fitowa tanemi waje ta zauna tana gaida Umma da Abban kafin ta kalli Umman tace "nifa yunwa nake ji Umma yau bross ko kari bai bari nayi agidaba wai ya makara a office"
Kallon mijin nata tayi yayin da yayi mata alamar data bata abinda suke dashi,shi kuma ya saka takalmansa yayi waje Umma Kuma ta nufi kicin ta kawowa Maryam wake da shinkafar da suka dafa da salak da tumatur da cocomber, ta aje mata ta koma domin kawo mata ruwa sai ga Abba ya shigo da ruwan roba da lemo harda dafaffen kwai tunda yasan me aka dafa agidan.
Sam bata wani nuna bak'unta ba taja abincin taci ta k'osh har tana santi ita kam Maryam zuba mata ido tayi tana kallonta batareda data iya cewa uffan ba saida ta gama ta wanko hannunta ta dawo tasha lemon da ruwa sannan tace.
"Abba wannan kayan abincin nakane kai na siyowa dan Allah Abba kada ka k'ara zuwa kayi dako insha Allah idan Baffana ya dawo zansa yabaka jari ka fara business kaima insha Allah Allah zai dafa maka"
Rasa bakin magana Abba da Umma sukayi suka rik'a kallon Maryam da tsabar mamaki dama Maryam taji sanda yake cewa saida yai dako ranan sannan ya samo musu abinda zasuci?
Sosai Abba ya gode mata sannan yayi mata fad'an abin yayi mugun yawa tace "Abba wannan ba komai bane akan idan da ace Baffana na fad'a wa shi ya doramu akan wannan tsarin nida 'yan uwana" addu'ar da Abban Maryam ya rik'a yiwa Maryam da zuri arta harsaida yasata hawayen farin ciki itama.
Sai bayan la asar ta baro gidan ta kamo hanyar nasu gidan dake suna da tazara sosai sai yamma ta dawo maimakon Kuma ta shiga gida sai kawai ta shige gidansu MM wani class mate d'inta wanda har yau suna mutunci dashi kasancewar su unguwa d'aya.
0 comments:
Post a Comment