*CHAPTER 1*
Ahankali yasanya hannu a handle ɗin ƙofan yamurɗa yashige, tana tsaye a gaban tanƙamemen gadonshi me tsananin kyau da burgewa, ganinsa ba ƙaramin tsorata ta yayi ba har batasan sanda tazaro ido waje ba tana kallon shi, shima ɗin ita yake kallo cike da mamakinta ganin yanda tafirgita lokaci ɗaya da ganin shigowar sa, hakan yasaka yatsaya yana kallonta na tsawon mintuna uku kafin yaɗauke kansa yaci gaba da takowa ciki cike da tafiyansa na ƙasaita, kai tsaye wajen gadon nasa yanufa ya'aje briefcase ɗin sa da rigan aikinsa asaman gadon, kana yataka yashige cikin toilet, tana ganin shigewan sa tasaki wani wawan ajiyan zuciya me ƙarfi har da sanya hannu tana dafe ƙirjinta, dasauri tanufi hanyan fita tafice, kai tsaye inda ɗakinta yake tanufa jikinta har yana rawa, sosai tatsorata da ganin da yayi mata, fatan ta ɗaya kar yaɗaura ayan tambaya a kanta, kuma ta gode Allah da be ganta tana wani abun ba da yau kashinta ya bushe.
Kusan 20mint yaɗauka acikin toilet ɗin kafin yafito ɗaure da tawul a ƙugunsa, ɗaya kuma ya ɗaure sa saman kansa, jikinsa duk ruwa ke ɗiga, haka yaƙarisa tanƙamemen Mirror ɗin sa wanda aka cika gaban da kayan shafa kala da iri, zama yayi bayan da yawarware towul ɗin kansa yafara goge suman gashinsa da yake baƙinƙirin me yawan gaske, sai da yagama goyewa tas yabusar dashi kafin yasoma shafa wasu Expensive Lotions akan Black skin ɗin sa me kyan gaske, sai da yagama tas yagyara gashinsa yashafe shi da mayuka masu saka gashi ƙyalli da taushi, bayan ya gama tashi yayi yanufi wajen sip ɗin kayan sa yabuɗe yaciro wata farar riga me gajeren hannu da wuyan V, sai farar Three qweater me manyan aljihu, sai da yashirya tsaf yakoma gaban mirror yafesa tsadadden Parfumer's ɗin sa me daɗin ƙamshi, yaƙara kallon kansa ba ƙarya ya haɗu sosai duk da shi ɗin me kyau ne, wayoyinsa yaɗauka yafito palow yana tafiya yana dannawa har yaƙariso saman luntsuma-luntsuman kujerun yazauna, ya ɗan jima yana latsa wayan kafin ya'aje yaɗau remote yafara sanja channels, akan CCTV NEWS yatsayar yasoma kallon labaran da ake yi, shi ba kasafai yake kallon fina-finai ba, yafison kallon labarai ko wrestling, Ringing tone ɗin wayan sa ne yasaka shi ɗauke idanuwan sa akan plasma ɗin yamaida kan wayan, kallo ɗaya yayi ma wayan yaɗauke kansa yaci gaba da kallon shi, sai da akayi mishi 2missed call be ɗaga ba, ana 3 ɗin ne yasa hannu yaɗau wayan ganin dai ba fasa kira za'ayi ba, kuma sosai kiran yake damun sa, hakan yasaka yayanke shawaran yaɗauka
"Ya dai?"
Yafaɗa hakan cikin cool voice ɗin sa yana me jingina bayan sa da jikin kujeran, jin muryanta ya doki kunnunsa yasaka shi lumshe idanu yana buɗewa
"My Ib da fatan ka isa gida lafiya?"
Ataƙaice yace "lafiya".
Shiru ne yagibta a tsakanin su, hakan yasaka shi sake lumshe idanu yana jiran tasake magana, itama daga ɓangaren ta so take yayi mata wata maganar ko da irin tambayar da tayi mishi ne, cikin sanyin murya tace
"Dama na kiraka naji ko ka isa gida lafiya ne, sai anjima.."
Be bari ta aje numfashi ba ma yakashe wayan yana ajewa yaci gaba da kallon sa, sai kuma yaƙara ɗauka yalatsa yanemo wata Number yakira
"Kizo".
Daga haka yakashe yasake ajewa, 3mint sai gata ta buɗo wani ƙofa ta shigo, ahankali tanufo sa taduƙa agaban sa tace
"Gani Sir".
Idanun sa akan t.v yace
"Kihaɗa min tea kikawo min".
"Tom". Tace dashi tana miƙewa dasauri tanufi hanyar kichen, har ta kama ƙofar zata buɗe taji muryan sa ya ratsa cikin kunnuwanta
"Lubna".
"Na'am Sir". Tace hakan lokacin da tajuyo tana kallon sa
"Kibar shi kawai".
Yana faɗan haka yamiƙe tare da wayoyinsa yanufi ɗakin sa, sai da taga shigewar sa tasaki ajiyan zuciya, shiru tayi tana tunani kana cike da sanyin jiki takoma inda tafito
Be jima ba yafito riƙe da keeys ɗin mota, ya sauya shigan sa cikin wata Farar t.shirt me dogon hannu da zanen cat 🐈 agaban rigan, sai dogon wando pencil blue colour, ƙafansa da Combat kalan wandon da ratsin fari, yana saka wrist watch a hannun sa yabuɗe ƙofan yafice, directly compound ɗin gidan yanufa yanufi wajen da yake aje cars ɗin sa, acikin wata kyakkyawar farar Mota yashiga yaja slowsly yanufi bakin Gate, gateman na ganin shi yataso yabuɗe masa yafice, ahankali yake tafiyar hakan yasaka ya ɗau tsawon 30mint kafin yadangana ga wata tanƙamemen Gate, abuɗe yatarda Gate ɗin hakan yasaka yatura hancin motansa ciki, kai tsaye inda ake ajiye Motocin gidan yanufa yatsaya daidai setting wata Black cars, atare suka fito yayinda suka kalli juna suka sakar ma junan nasu murmushi, bayan ya rufe motan yataka yanufi wajen shi, tafawa suka yi suka cafke hannayen su
"Ya Bro".
"Manya-manya iyayen mu, sai yau zan ganka?".
Cewar Sameer yana kallon sa da murmushi a face ɗin sa
Ɗan shafa kansa yayi yace
"Uhmm Bro kenan Bara ka gane bane, aiki ne yayi min yawa fa".
"Na sani ai ba sai ka faɗa ba, ku da kuke manyan mu".
Smile kawai Khalil yayi be ce komi ba
"Ok muje ciki nima yanzu isowa ta kenan".
Tare suka jera suka nufi hanyar da zai sada su da main Palow, Kai da ganin su kasan jini ɗaya ne su sabida tsananin kamannin su, sosai komi nasu yakasance ɗaya har ta da skin ɗin su, tsawo ne kaɗai Khalil yafi Sameer dashi, yayinda shi Sameer ɗin matsakaici ne kuma yana da ɗan ƙiba sosai.
Suna shiga da sallama matar dake zaune saman sofa ta'amsa musu, kallo ɗaya zakayi mata katabbatar da ita ce mahaifiyarsu bcoz tsananin kamannin da suke da juna, sai dai ita fara ce sosai saɓanin su da suka biyo Mahaifinsu
"Mom".
Suka faɗa atare suna nufar inda take, Sameer har da ƙarawa da sauri yaje yayi Hugging ɗin ta yana sakar mata kiss a goshi, sannan yasami wuri gefenta yazauna yana ɗaukan Apple ɗin dake gaban ta cikin plate, sai da yagutsira yace
"Mom Afternoon".
Lokacin da shima Khalil yaƙaraso yazauna ɗaya side ɗinta suka saka ta atsakiya, atare tashafo kansu tana murmushi tace
"Welcome My twinsies, nayi kewarku kwana biyu, musamman ma kai Autana".
Taƙarisa maganar ta tana kallon Khalil da shima yakarkace kai yana kallonta, ƙara shafo kanshi tayi tana faɗin
"Ya aiki?"
"Alhmadulillah Mom".
Sameer yace "Mom ni fa?"
Kallon shi tayi, da ido tatambaye shi mene?
"Naga kina kallon sa ne kina tambayansa banda Ni".
"Oh to ai sai kajira nagama dashi ko? Ko kai ba Babba bane?".
Ɓata fuska yayi yace "kullum haka kike cewa ai, dole sai kin nuna banbanci a tsakanin mu".
"Kaima ai ban hanaka zuwa inda akafi sonka ba, sai kabari dai nagama tambayan Autana kafin nazo kanka".
Murmushi yayi yace "Mom kenan, wanda kika damu dashi ɗin ma ba take yake yi ba, ina nan zaune ai zan ganku a rana".
"Ee dai nasan haushi kake ji don nafi nuna masa kulawa".Cewar Mom tana dariya
Lokacin ne Khalil yaɗago kansa daga latsa wayan da yafara yi, yakalli Sameer yaharare shi yana ɗauke kai, waro ido Sameer ɗin yayi yace
"Mom harara na yake yi fa".
Mom tace "to ai kaine kamatsa mishi Ni banga laifin shi ba ai".
"Mom ni yunwa fa nake ji".
Cewar Khalil yana langaɓe kai
"Oh sorry My Son, bari insa akawo maka, me kake so?"
"Mom koma menene kukayi zanci, bazan iya jiran adafa min wani ba".
"Okey". Mom tace hakan tana ƙwala kiran ƴar aiki
Sai da tazo tafaɗa mata tahaɗo ma Khalil abinci takawo masa nan, sannan takalli Sameer tace
"Kai fa?"
"No Mom.. ni sai da aka cika min ciki kafin nafito, kidai ji da wannan sanƙamemen da yaƙi aure yatsaya ɗaura ma mutane ɗawainiya".
Mom tace "me kake ci na baka na zuba.. kuma wlh kadena takura masa ko yanzu nakora ka inda kafito".
Dariya yayi yace "oh Mom wasa nake wlh, shi da ma yake da zuƙeƙiyar budurwa sai ma kin ganta Mom".
Khalil da yake ɗan tsakuran abincin da aka kawo masa ɗago kanshi yayi yana kallon Sameer yace
"Mom karki yarda da maganar sa wlh".
"A'a bar Ni yafaɗa min, Ni da nakeson inga kayi aure? Kaji bani nasha inajin ka, aina take ne yarinyan?"
"Uhmm awajen aikin su mana Mom, sai kin ganta ma Mom ta bala'in dacewa da ɗan naki, yanda tahaɗu haka tadace da sunan ta, Bilkisu me gadon zinare".
Washe baki Mom tayi tace "masha Allah.. kace na kusa samun suruka kenan? To Allah yanuna min nidai wannan ranan".
"Ameen Mom ai nima na ƙosa ranan tazo".
"Son yaushe zaka kawo min ita naganta?"
Ɓata fuska Khalil yayi yace
"Mom nima ba wani sonta nake ba itace take sona".
"To ai kaima a sannu zaka so ta karka damu kaji". Mom tafaɗi hakan tana shafa kanshi
Dariya Sameer yayi yace "hmm Mom ke kin yarda dashi ko? Ni da nakama su suna zance, kullum kikaje fa office ɗin sa sai kin gansu tare".
Buga abincin Khalil yayi saman table yamiƙe tsaye zai tafi, dasauri Mom tariƙe sa tana faɗin
"Sorry son karka tafi, bari shi in kore sa".
Juyawa tayi tana kallon Sameer har da ɗan ɗaure fuska tace
"Kama hanya katafi".
Dariya yayi yace "to Mom amma baki bani abinda yakawo ni ba".
"Ok yanzu ne kasan da tambayana? Kaje sai anjima zan haɗa sai kazo ka amsar mata, tunda dama kaƙi kadawo da ita nan kai wahala yasama".
Sameer yace "Mom to me zatazo tayi miki anan? Tunda acan ɗin ma ina kula da ita".
"To kema Mom kibar masa matar sa mana, inace shi ɗin likita ne kuma yafiki sanin yanda zai kula da ita".
Khalil yafaɗi hakan yana kai spoon bakin sa, sai kace bashi ne yayi maganar ba".
Mom tace "rufe min baki, tun kafin a haife ku gaba ɗayan ku nake kula da masu ciki, koda shi likita ne bazai fini sanin yanda zai kula da ita ba, ku kanku babu wanda yataimake Ni lokacin da nake da cikin ku har sanda nahaife ku kuwa".
"To fa Mom ke da ɗan gaban goshin naki kuma har kun soma ɓatawa?" Sameer yace hakan yana gumtse dariyan sa
Atare suka banko mishi harara yayi saurin tashi yana sakin dariya, yayinda yaɗaga hannayen sa sama yana faɗin
"Babu ruwana nayi nan".
Yafice da sauri, duk kansu sai da suka murmusa kana sukaci gaba da ɗan taɓa hira a tsakanin su, duk da Khalil baya wani amsa mata wayansa kawai yake latsawa, be wani jima ba shima yayi mata sallama yatafi.
[8/30/2020, 9:09 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 2*
Ahankali yatura kan motan sa cikin gidan nashi, yaƙarisa parcking space yatsaya, yaɗau 3mint kafin yabuɗe motan yafito, tun sanda yatunkari Compound ɗin gidan yahango bayan ta tana zaune ƙarshen farandan, ga duk kan alamu bata ma san da shigowan sa ba, har zai wuce sai kuma yatsaya yana kallon ta duk da baya ganin face ɗin ta sai bayanta but yasan da akwai abinda ke damunta, shi mutum ne da yake saurin gane damuwar mutum, sau tari aɗan kwanakin nan yana ganin ta cikin wannan hali, sai dai yasan ba hurumin shi bane shiga abun da babu ruwansa, yanzun ma har yafara takawa zuwa wajenta sai kuma yaja yatsaya kana kuma yajuya yashige cikin Palon sa, dai-dai lokacin da ita kuma tasanya hannunta tagoge hawayen da suka zubo kan fuskarta, sosai in kakalle ta zaka hango tsantsan damuwa a tattare da ita, ahankali tamiƙe tanufi cikin gidan, direct kichen tanufa tafara aikin ta, ta ɗau tsawon minti 30 kafin tagama girkin tazuba cikin coolar taje tajera su kan dainning table dake cikin ƙayataccen palon, bayan ta gama tsayawa tayi awajen tayi shiru tana kallon ƙofan ɗakin sa, ta daɗe ahaka sai da taji idanunta sun cicciko da hawaye kafin taɗauke idanunta dasauri tanufi hanyan ɗakinta, akan gadon ta tafaɗa tasaki kuka me tsuma ran me sauraro, ita kaɗai tasan me ke damunta, kuma tasan babu wanda zai iya cire ta daga cikin matsalan da take ciki sai rabbi, domin ita kanta batasan ta ina zata fara aikin da aka sanya ta ba, sai da tayi kukan ta ma'ishi kafin tamiƙe tashige toilet dan ɗauro alwala.
Tunda yashiga ɗakin sa yacire kayan jikinsa direct yashige toilet, ya ɗau tsawon lokaci kafin yafito, yasoma shirya wa cikin sauri, ƙananan kaya yasanya riga sky blue me gajeren hannu wanda tamatse masa Arms ɗin sa, kana yasaka Black trouser, sosai yayi kyau cikin shigan nasa, flate cover shoes yasaka baƙi yafito yanufi masallaci, da tazara sosai da inda gidan sa yake zuwa masallacin, bayan yayi sallan direct gida yanufa yashige ɗakin sa, wani ƙofa yabuɗe yashige, cikin ɗakin kamar Labrary yake, anan yake karatun sa yake duk wani bincike abinda yashafi aikinsa, akan Hill chair yazauna yajawo lapton ɗin sa dake saman table ɗin yabuɗe yasoma aikin sa.
Wajen ƙarfe 06:00pm tafito daga ɗakin ta tanufi kan dainnig table ɗin, gani tayi babu abinda aka taɓa awajen, aran ta tunani take yi ko be dawo bane? Bata da masaniya, dan haka tayanke shawaran fita taduba motan da yafita da ita, koda tafita ta hangi motan yana nan a inda yake, ga kuma sauran nan da alama dai yana gidan, komawa tayi jiki a sanyaye tashige ɗakin ta, dama tafito da ninyan tagirka mishi abincin dare ne.
Sai da yaji an kira sallan magriba kafin yatashi yafito, direct toilet yanufa yaɗauro alwala yafita masallaci, be dawo ba sai da akayi sallan isha'i, koda yashigo gidan kan dainning yanufa yazauna, yahaɗa ma kan sa Black tea yasha, bayan ya gama yaɗan ci abincin kaɗan yatashi yashige ɗaki, sai da yayi wanka yasanya sleeping dress yafeshe jikinsa da farpume's ɗin sa sannan yazauna gefen gado, briefcase ɗin sa dake ajiye asaman gadon yajawo yaciro wata Black Computer, buɗe wa yayi yasoma aiki, sai da ƙarfe 11:00pm yayi kafin yarufe yakwanta lokacin tuni dama barci yasoma cin ƙarfin sa, yana shafa addu'ar da yayi ko minti 5 be ƙara ba barci yatafi dashi.
......... ............ .........
Washe gari ƙarfe 07:00am Brr. Khalil yagama Shirin sa, yayi shigansa cikin suit black colour, ta cikin kuma white ne, ya sanya socks and black cover shoes, ya gyara gashin kansa sai ƙyalli yake yi gunun sha'awa, gaba ɗaya in banda ƙamshi babu abinda yake tashi ajikin sa, briafcase ɗin sa yaɗauka yafita da sauri ko kallon dainning ɗin da Lubna tagama jera masa break fast be yi ba yafice, ɗaya daga cikin motocin sa kalan sky blue yashiga yaja yafice bayan da Gateman yawangale masa Gate.
Yana fita Lubna tafito daga cikin Toilet ɗaure da showel ajikin ta, kai tsaye inda kayanta yake a sif tanufa taciro wata baƙar doguwar riga me ƙyalƙyalin kwalliya tasaka, tana cikin shafa lotions bayan da tazauna gefen gadon ta taji wayanta yasoma Ringing, dasauri takalli wayan sai da gabanta yafaɗi ganin wanda ke kiran, jikinta na rawa taɗau wayan takara a kunne, bata kai ga cewa komai ba taji muryan sa yana faɗin
"Da fatan kin aikata abinda muka saki?"
Cikin rawan murya tace
"Ban samu dama ba har yanzu".
"Kina so kice min har yanzu babu wani ci gaba?"
"Ee, har yanzu be bani.."
Katse ta yayi cikin kakkausan murya yace
"Kin san abinda zai biyo baya, karki manta Mahaifiyarki da ƙannin ki.."
Sai kuma yakece da dariya
"Uhmm kinsan sauran, kuma kinsan bazan tsaya jiranki har lokacin da time zai ƙure mana ba, dake na dogara.."
Daga haka yadatse kiran batare da yabari tasake magana ba, ahankali ta'aje wayan cike da sanyin jiki, kasa ci gaba tayi da shafa man sai ma tashi da tayi tafara zagaye ɗakin tana me cike da tunani, so take tasamu mafita amma har yau zuciyarta tagaza barin ta, tsananin tausayin sa take ji aranta duk da ita zata cutu, wani ɓangare na zuciyanta tace
"Haba Lubna kifarka daga mafarkin da kike yi, karki manta fa babu abunda yahaɗa ki dashi, kuma kimanta da wata alaƙan dake tsakanin zuciyarki dashi, ki ceto Mahaifiyarki da ƙannin ki daga halaka, idan har kinyi hakan babu cutarwa a wajen shi, kuma hakan shine dai-dai".
Wannan tunanin yasaka tayi saurin fita tadoshi ɗakin sa cike da tunani kala-kala.
[8/30/2020, 9:14 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 3*
Har ta kama handle ɗin ƙofan zata murɗa sai kuma tayi saurin saki tajuya dasauri tasauke idanunta kan tanƙamemen agogon dake manne can saman bango, ƙarfe 07:25am hakan yasaka tasauke ajiyan zuciya don tasan babu shi yariga ya fita, ahankali tamurɗa tashige tasoma dube-duben drowers da sif ɗin sa, ta daɗe tana dube-dube cikin ɗakin bata ga komi ba, ƙarisawa tayi jikin ƙofan da yake shiga yayi aikin sa tare da aje duk wasu muhimman abubuwan sa, tana taɓa ƙofan kamar ko yaushe a kulle yake hakan yasaka tajuya jiki a sanyaye tasoma gyaran cikin bedroom ɗin, bayan ta gama tawanke toilet sannan tafito palow, nan ma sai da tagyara ko ina kafin tanufi ɗakin ta.
.... .... ..... .... .... ....
Nocking ƙofan da akayi ne yasaka shi ɗan tsakaitawa daga aikin da yake cikin Computer
"Yas come in". Yabada umarni yana ci gaba da aikin sa
Ahankali taturo ƙofan tashigo, sai da tajingina da ƙofan tana ƙare mishi kallo na 30soconds kafin daga bisani tasoma takowa cikin office ɗin tanemi kujera tazauna inda aka tanada don baƙi, shiru tayi taci gaba da kallon sa batare da tayi magana ba, sam bata gajiya da kallon shi sabida sosai take mutuwar ƙaunar shi, komi nashi me kyau ne ba inda yake da makusa, ya haɗu ne tako ina duk da kasancewar shi baya da farar fata but skin ɗin sa irin golden colour ɗin nan ne me shaining, yana da kyawun fuska wanda yake zagaye da ɗan siririn saje baƙi siɗik gunun sha'awa, idanuwansa farare ne ƙal kamar zaiba, yana da dogon hanci har zuwa ɗan madaidaicin bakin sa me ban sha'awa da ƙananun lips, shi ma'abocin barin suma ne me tarin yawa, don haka koda yaushe sai dai kaganshi yayi gyaran fuska ba dai yayi aski ba, yana da tsayi sosai da faɗin chest kuma yana da ɗan jiki don baza'a kira sa siriri ba.
"Wai lafiya kika tasani gaba kike kallona?" Muryan shi takatse mata tunanin ta da take yi a kansa
Ɗan firgigit tayi tana sauke ajiyan zuciya kafin tasaki yalwataccen murmushin da yaƙara ma face ɗin ta kyau, cikin sanyin murya tace
"Koda yaushe bana gajiya da kallon ka ne My Ib, Burina ako yaushe kakasance mallakina ni Ni kaɗai, ina Son ka da yawa My Ib, har yaushe ne zan ta jiranka kayarda dani a matsayin wacce zata zama abokiyar rayuwanka? Yaushe ne nima zaka nuna min ƙauna kamar yanda nake tsananin ƙaunarka da begen ka? Yaushe zaka tausaya min kaji ƙaina kagane babu wacce tafini ƙaunarka a faɗin duniyar nan?".
Duk maganar da take yin nan idanuwanta na kansa batare da ko kaɗan ta ƙifta su ba, hakan yasaka har ƙwalla suka taru cikin idanun suna shirin zubowa
Sai lokacin yaɗago kanshi yasauke idanunshi cikin nata, dai-dai da lokacin da wasu siraran hawaye suka ɗigo saman kuncin ta, tsira mata idanun sa masu matuƙar kaifi da kyawu yayi na ɗan wani lokaci kafin yaɗauke kai yaci gaba da aikin sa, cikin sweet voice ɗin sa yace
"Bilkisu wai yaushe ne zaki fahimce ni nima? Kigane nifa bazan iya ɓata time ɗina kan wani soyayya ba".
Ɗan tsakaitawa da maganan yayi kafin yace
"Please ki dena ɓata lokacin ki akan wanann batun, yanzu ki koma kije kiyi aikin ki, ina Son yau ki kamalla komi ki kawo min".
Lumshe idanuwanta tayi tabuɗe su akan shi, duk maganganun da yafaɗa bakin sa kawai take kallo, sosai take jin daɗi idan yakira sunan ta don ji take yi kamar yafi kowa iya faɗan sunan
Nocking door ɗin akayi yabada umarnin shigowa, abokin sa Brr. Tahir ne yashigo, ita kuma Bilkisu tatashi tafice batare da tasake cewa komi ba, inda tatashi yazauna yana sakin murmushi yace
"Guy ya naga ta fita kuma? Kar dai ace laifina ne na katse muku jindaɗin ku?"
Brr. Khalil ɗago kan sa yayi yasauke mishi wani kallo kafin yace
"Wai meyasa kai in bakayi tsegumi kamar mace bane baka jindaɗi?"
Barr. Tahir dariya yayi yace
"To menene na tsegumi kuma? Akan kai da Billy ne zan yi tsegumi? Uhmm gaskiya ce fa kai na kula baka son ta ko kaɗan, Ni wlh na rasa meyasaka yarinyan nan tanace akan dole sai tasame ka, meye amfanin tsayawa wajen da ake wulaƙanta ta, ga waɗanda suka dace da ita suke son ta tsakani da Allah but taƙi su tana tusa kanta inda bazata taɓa karɓuwa ba".
"Ok na gane, kafito fili kawai kace min kai kana ciki ba wai katsaya kana faɗamin baƙa ba".
Brr. Khalil yafaɗi hakan yana yatsina fuska
"Ohh sorry abokina wasa fa nake maka, Ni dama nasan kana son yarinyan nan, kawai halinka ne yasaka bazaka iya nuna mata ba, but ni dai shawaran da zan baka Please and please Ib kadena wahal da yarinyan nan katausaya mata,
Tsaki Brr. Khalil yayi yana kau da kansa yaci gaba da aikin sa, shi kuma Brr. Tahir murmusawa yayi yace
"Uhmm kai dai gaskiya ne baka so abokina amma ni banga makusa kan Billy da har zaka ƙi ta ba, yakamata kadawo tunanin ka kasan masoyin ka Ib".
"Please kafita kabani waje kana damuwana da banzan surutunka".
Brr. Khalil yafaɗi hakan yana ɗago kan sa fuskarshi a ɗaure
Dariya Brr. Tahir yayi yace
"Babu inda zan fita wlh, idan har kaga na fita to lokacin tashin ka ne yayi".
Harara yabanka mishi yaja ɗan siririn tsaki still yaci gaba da aikin sa
"Wai ya maganar Alhaji Mubarak ne? Me ake ciki yanzu? Yakamata fa musan abin yi tun kafin lokaci yaƙure mana". Cewar Brr. Tahir kenan yana ɗan gyara zaman sa
Kamar bazai ce komi ba, sai can kuma yabuɗi baki ahankali yace
"Muna da enough time ai insha Allahu komi zai zo da sauƙi, zuwa nan da nest week ma zan je Eygpt ɗin".
Jinjina kai Brr. Tahir yayi yace
"Gaskiya Shari'a da irin su Alhaji Mubarak hatsari ne dashi, yakamata kakula Ib kasaka idanu da kyau, kafin lokacin zasu iya yin komi don kawai su hanaka samun nasara, but naga alaman kana ɗaukan abun kamar da wasa ne".
"Hmm babu abunda zasu iya yi, kai dai kazuba idanu kagani duk wani take-taken su ina sane dashi, kuma bazasu taɓa samun nasara ba, da yardan Allah sai nayi nasara sai na ƙwato mata haƙƙin ta, insha Allahu ta sanadiyar Nazeefa sai na kawo ƙarshen Alhaji Mubarak da duk kan mabiya bayan sa".
Brr. Khalil yafaɗi hakan yana kallon Brr. Tahir ɗin
"Gaskiya ne, Allah dai yabaka sa'a, yanzu ya take? Ina fatan tana samun lafiya?"
Ɗan jingina kan sa yayi saman kujeran da yake yana lumshe idanun sa kafin yagyaɗa masa kai sai kuma yace
"Ina son namaida ita asibiti ne domin ina son aƙara duba ta da kyau, zamanta gida babu amfani".
"Hakan yafi dacewa ai, amma baka ganin kakaita asibitin da Sameer yake? Inaga shima zai fi kula da ita".
"Nima nayi tunanin haka, sai dai kasan Dr. Hashim yace "abarta agidan hakan zai fi sirri, sannan kasan Big bro ba aikin sa bane, tun farko shi yace dani in nemi Dr. Hashim zai fi bata kulawa, kuma sosai take samun lafiya ba kamar da ba".
Gyaɗa kan sa Brr. Tahir yayi cike da gamsuwa, daga nan hira suka ɗan taɓa zuwa lokacin tashi aikin nasu kafin suka fito ko wanne yahau motan sa yatafi.
Kamar ko yaushe ahankali yake jan motan sa, yanzun ma hakan yake yi kamar baya son tafiya, ta cikin mirror ɗinsa yahango wata baƙar mota tana binshi, da farko be wani damu ba don a tunanin sa ko bashi take bi ba, sai yatsaya yana kallonta ta cikin mirror itama motan packing tayi can nesa dashi, tsawon minti 5 be tada motan ba itama haka motan tana nan yanda take, ahankali yataka yaci gaba da tafiya batare da yaƙara speed ɗin motan ba, yana yi yana kallon motan da taci gaba da bin sa, sai da yayi nisa sai kuma yasake tsayawa itama motan taja tasaya.
[8/31/2020, 8:20 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 4*
Gani yayi kuma Motan tayi revers tajuya da gudu ta tafi, ahankali yasauke ajiyan zuciya yatada nashi motan yaci gaba da tafiya, agaban wani ɗan madaidaicin gida yatsaya, har ya buɗe ƙofan zai fita wayan sa tafara Ringing, dakatawa yayi yakalli wayan dake ajiye a gefe, ganin sunan BILKISU ya fito asaman screan ɗin yasanya shi jan gajeren tsaki yafice tare da rufo ƙofan, direct gidan yanufa yashiga da sallama a bakin sa, matar dake zaune bakin ƙofanta ta'amsa mishi cike da fara'a tana faɗin
"Maraba lale Ibrahima sannu da zuwa".
Tana maganan ne tana janyo tabarma dake kusa da ita
"Zauna mana anan".
Cire black Combat ɗin dake ƙafan sa yayi yasamu waje yazauna yana faɗin
"Ina yini Baaba?"
"Lafiya lau Ibarahima, yagida ya aiki? Da fatan kowa dai yana lafiya ko?"
"Alhamdulillah Baaba".
"Ai jiya naji ka shiru bakazo ba, ince dai lafiya?"
Ɗan gajeren murmushi yasaki yace
"Lafiya lau Baaba, ban samu daman zuwa bane shiyasa, da fatan babu wata matsala baku nemi wani abu ba?"
"A'a wlh Alhamdulillah, Nazeefa ce dai ma tafarka ajiyan take neman ka, kuma daga baya sai barci yaɗauke ta, koda tafarka kuma yau bata tambaye ka ba ko magana ma batayi ba".
Ajiyan zuciya yaɗan saki kana yace
"Ina ga yau zan tafi da ita, Nagode sosai da taimakon ki Allah yasaka, ga wanna babu yawa".
"Ikon Allah bawan Allah baka gajiya? To Nagode Allah yasaka, ai babu komi yiwa kai ne, ita kuma Allah yabata lafiya".
"Ameen". Ya'amsa ataƙaice yana miƙewa
Itama tashi tayi tana faɗin
"Shiga tana ciki ai".
Be ce komi ba yashiga, yarinya ce da bazata gaza 16yrs ba a kwance akan katifa, fara ce sol sai dai shatin kwarmin idanunta yaɗan yi baƙi-baƙi kaɗan, barci take yi hankalinta kwance, ahankali yamatsa kusa da ita yasanya hannayen sa yaɗauke ta cak ajikinsa yafito, har waje Baaba Talatu tarako shi tana ta saka mishi albarka tare da godiya ga ɗawainiyan da yayi mata
A back sit yakwantar da ita kana yashiga yaja motan ahankali kamar yanda yasaba, shiru yayi yana nazarin abinda yakamata yayi, ta cikin mirror yake kallon ta duk da baya hango ta sosai, but jefi-jefi yakan kai idanun sa kanta.
A bakin Gate yadakata yayi hon, ba daɗewa aka wangale mishi gate ɗin yatura hancin motan ciki, a packing space yatsai da motan, sai da yaɗan yi minti 3 kafin yabuɗe motan yafito da ƙafan sa, wayoyin sa yaɗauka yashigar dashi cikin aljihu kana yafito yabuɗe bayan mota yana ƙoƙarin fito da ita, ahankali tabuɗe idanuwanta tasauke kan kyakkyawan face ɗin sa, hakan yasaka taɗan saki murmushi ahankali tace
"Yayana".
Shima murmushin yasakar mata yaɗan ja jikin sa daga ɗaukan ta da yayi ninya yace
"Nazeefa.. kin tashi?".
Gyaɗa masa kai tayi still tana murmushi
"Ok fito ahankali muje ciki, yau na dawo dake gida na, anan zamu ci gaba da zama kinji?"
Nan ma gyaɗa masa kai tayi kafin tayunƙuro tatashi tafito daga cikin motan, ahankali take kallon cikin gidan kafin tamai da idanuwanta kan sa, murmushi yasakar mata kana yariƙo hannun ta suka taka ahankali suka nufi cikin gidan, a main palow suka tsaya yanuna mata kujera yace
"Zauna anan".
Ba musu tasami waje tazauna tana ci gaba da kallon Palon don ba ƙaramin burge ta yayi ba, sosai yatafi da imanin ta, tsarin Palon da kayan cikin kan shi abun burgewa ne da sha'awa, fridge yanufa yaɗauko faro water yadawo yazauna gefen ta, miƙa mata yayi ta'amsa tana sakar masa murmushi, shi kuma wayan sa yazaro cikin aljihu yaɗan latsa yakara a kunne
"Ina kike?"
"Ok kizo palow Ina jiran ki".
3minute tafito cikin ɗakin ta, har gaban sa taƙarisa taduƙa tace
"gani Sir".
"Kikai ta ɗakin ki daga yau zakici gaba da kula da ita, zuwa anjima kiyi ma drever magana yakai ki super makert duk wani abun da take buƙata kisiyo mata".
Ita sai lokacin ne ma takalli wajen da Nazeefa take zaune, a ranta tana tunanin "to wacece ita awajen shi?"
Batakai ga ƙarisa zancen zucin nata ba taji muryan sa yana ma Nazeefa magana
"Tashi kibi ta ciki".
Babu musu tatashi, itama Lubna miƙewa tayi takama hanyan ɗakin ta Nazeefa na biye da ita abaya, da ido yabi su da kallo har suka shige kafin yasauke ajiyan zuciya, tashi yayi yanufi cikin ɗakin sa, wanka yayi yasauya kaya cikin ƙaraman t.shirt fara da yellow ɗin Three qweater, yafito palow yanufi saman dainnig yasami waje yazauna, tea cup yahaɗa yafara sipping yana latsa wayan sa, tsawon mintuna ashirin yaɗauka awajen kafin yamiƙe yanufi cikin ɗakinsa, be fito ba sai da aka kira sallan magriba kafin yaɗauro alwala yasanya jallabiya fara sol yafito yanufi masjid, sai da aka yi isha'i kafin yadawo, yana shigowa yatarda Nazeefa zaune saman kujera ta ƙudundune jikinta tana kallo, shigowan sa yasaka taɗago kai tana kallon shi, kujeran dake gefen ta yasamu yazauna yana kallon ta
"Sannu da zuwa yaya".
Tace dashi tana gyara zaman ta dakyau
"Yauwa.. kinci abinci?"
"Eh Yaya".
"Ok."
Shiru yagibta a tsakanin su na ɗan wani lokaci kafin yaɗago da kansa daga duba wayan sa yana kallon ta yace
"Kije kikwanta dare yayi, ki kira min Lubna".
tace "to".
Tamiƙe tawuce ciki, Lubna ce tafito taƙariso kusa dashi
"Kihaɗa min Coffee".
Amsa mishi tayi kawai tawuce cikin kichen, shima tashi yayi yanufi ɗakin sa, ko 2mint be yi ba yafito riƙe da briafcase ɗin sa, yana zama itama tafito tamiƙa mishi takoma ciki, ahankali yasoma aikin sa cikin Computer yana yi yana sipping ɗin Coffee ɗin, har wajen ƙarfe 11:00pm yana nan zaune cikin Palon be gama abinda yake ba, can yaji ihu cikin ɗakin su Lubna, ɗan tsakaitawa yayi daga latsa Computern da yake yi yana kasa kunne.
[8/31/2020, 8:26 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
_wannan shafin naku ne masoya Littafina, ina jin daɗin yanda kuke nuna ma Book ɗina ƙauna, thank you._ ❤️
.
*CHAPTER 5*
Tashi yayi yanufi ɗakin yabuɗe yashiga, duhu ne ako ina hakan yasaka yalaluba makunnin wutan ɗakin yakunna ko ina yagame da haske, akan ta yasauke idanun sa tana zaune saman gadon babu inda jikinta baya rawa, gefen ta yakalla yaga Nazeefa na kwance sai sharan barcin ta take yi ko motsi batayi ba, maida kyawawan idanun sa yayi akanta da itama tazuba nata cikin nashi sai ɓari take yi, ahankali kamar baya son magana yace
"Menene kike ihu cikin dare? Lafiyan ki ƙalau kuwa?"
Cikin rawan murya tace
"Mafarki nayi".
Tsare ta da idanu yayi yana nazarin ta, gaba ɗaya tsoro da firgici ne yabayyana a fuskarta, ɗan numfashi yaja sannan yace
"Wani irin mafarki ne haka da yabaki tsoro?".
Sharto gumin fuskanta tayi still cikin rawan baki tace
"Am uhm Mafarki nayi ak..akan Mamana".
"Kina son kije gida kenan?"
Yaje ho mata tambayan tare da ci gaba da faɗin
"Sai in saka drever yakai ki yanzu in kinaso".
Dasauri tagirgiza mishi kai tana faɗin
"A'a".
"Ok koma kikwanta, kitabbatar kinyi addu'a tukun".
Daga haka yajuya yafita bayan yakashe wutan ɗakin, ahankali tasulale takoma takwanta tana jin hawaye na sulalo mata a fuska, cikin raunin murya tace
"Dan Allah karku kashe min su, zan yi duk abinda kukeso".
Sai kuma tasaka hannu tashare hawayen fuskanta tana tuno fuskar sa a yanzu da yashigo, take wasu hawayen suka shiga sintiri saman fuskanta ahankali tafurta
"Ina matuƙar ƙaunar ka".
....... ....... ......... ......
Shi kuwa koda yakoma cikin Palon aikin sa yaci gaba da yi, be fi 20minutes ba yatashi yashige ɗakin sa, sai da yayi wanka yashirya cikin kayan barci farare sol yafeshe jikinsa da turare sai zuba ƙamshi yake yi kamar wanda yayi wanka dashi, kwanciya yayi yayinda fuskar sa ke kallon cilling ɗin ɗakin, yaɗaura kan sa saman dantsen hannun sa yayi matashi tare da lumshe idanun sa, ahankali yabuɗe idanunsa yana ƙure cilling ɗin ɗakin da ido, tunani yake yi cikin ransa, ya daɗe ahaka batare da yaji barci yazo mishi ba, ganin haka yasaka shi tashi yanufi Toilet yaɗauro alwala yazo yatada sallah yafara jero nafiloli, sai da yadaɗe yana Sallah kafin yasoma jin barci yatashi yahau gado yayi addu'a yarufe idanunsa, ba jimawa kuwa barci yasure sa.
.
****** ****** ******
Tsaye take a bakin titi tana jiran keke napep, tana sanye da uniform ɗin makaranta, riga da wando farare, sai ɗan ƙaramin Hijab kalan ruwan goro, sosai kayan suka yi mata kyau kuma suka ƙara fito da zallan yarintan ta da kyawun surar ta, school bag ɗin ta dake rataye a kafaɗan ta tazamo shi cike da gajiyawa, sosai ranan wajen yake dukan ta, tun ɗazu tana tsaye amma har yanzu bata sami abin hawa ba, gashi har abokan tafiyanta sun watse ita tana nan tsaye ba yau ba gobe, yatsina fuskarta tayi taɗan ɗaga face ɗin ta tana kallon ƙwallelen ranan da yasake fantsamo wa, bata kai ga sauke kanta ba taji hon ɗin mota a gefen ta, dasauri tasauke kanta taɗaura idanunta saman motan dake tsaye ɗan nesa da ita, cikin socond ɗin da be wuce 3 ba takalli motan taɗauke kanta, wanda ke cikin motan ne yafito ɗan kyakkyawan sauri ne yatunkaro inda take
"Assalamu alaikum". Yayi mata sallama yana kallon fuskarta da yake a yatsine
Bata kalle sa ba taɗan yamutsa fuska tana motsa ƙaramin bakin ta, hakan yasaka yaɗan saki murmushi yace
"Baiwar Allah da fatan dai ba laifi nayi ba da ban samu an amsa min sallama ba? Duk da nasan be dace natare ki anan ba, amma kuma babu yanda na iya ne tunda bazan iya bari kisuɓuce min ba".
Kallon sa tayi fuskanta a yatsine ga duk kan alamu hakan ya zame mata jiki ne, batace komi ba sai gyara zaman jakan ta da tayi tana kallon hanya
"Baiwar Allah ko dai ke kurma ce?" Yasake tambayan ta still yana kallon ta
Ahankali tagyaɗa masa kai tana ɗan kwaɓe fuska kamar zata yi kuka
"Ayya sorry rashin sani akace yafi dare duhu, kiyi haƙuri but ina son insan sunan ki gashi kuma ina son narage miki hanya, to ya za'ayi yanzu?"
Cikin sanyi da muryanta me daɗi tace
"Ce maka akayi ina buƙata?"
Sai kuma tayi saurin kallon sa tana ɗaura hannu abaki tare da zaro idanu waje tace
"Na manta".
Don ko kaɗan tamanta da yanzu tayi masa ƙaryan ita kurma ce, shi kuwa da yasaki baki yana kallon ta be san sanda yatuntsire da dariya ba yace
"Kai Allah Nagode maka, kinga lokaci ɗaya Allah ya kamaki, sai yasaka ki kika manta kika yi magana, Uhm babu rabon ki wahalar dani kenan, kuma banda abinki ai ƙarya be kamace ki ba, ko kadan bakiyi zubi da masu faɗan magana wanda ba dai-dai ba shiyasa na'amince dake nan take".
Murmushi kawai tayi tana jin kunya na kama ta, ba haka taso ba, taso in yagane ita kurma ce yatafi yabata waje amma kuma sai gashi asirinta ya tonu
"To yanzu dan Allah kitaimaka kifaɗamin sunan ki, kuma dan Allah karki ƙi tayina muje nasauke ki gida kinga akwai rana kar yayi miki illa, kamar ki kyakkyawa be kamata kina tsaye rana na gasa ki ba, ko ba haka ba?"
Ɗan taɓe baki tayi tace
"Ni fa bansan meyasaka kake faɗamin waɗannan kalaman ba, kuma bansan meyasaka kakeson taimako na ba, meyasa zaka damu idan rana tagasa ni? Baka tunanin nafison hakan ne shiyasaka nazaɓi tsayuwa anan ɗin?"
Murmusawa yayi yace
"Ai banga aibu ba idan har nataimake ki, kuma kinsan da cewa duk namiji idan har yaga mace ahanya yanemi yataimake ta to akwai abinda yake so wajenta ne, kuma kema kinsan da haka sai dai in bazaki faɗa ba".
"Zai fi kyau dai kasanar dani da bakinka, tunda nasan da cewa Maza kala da iri ne kuma ko wannen su da abinda ke kawo su wajen yarinya, to kai kuma bansan menene yakawo ka ba".
Ɗan numfashi yaja yana kallon ta cike da burgewa yace
"Tunda kinfi son sai nafaɗa miki dalla-dalla to shikenan, Ni sunana Yazeed tunda Ni kinyi min ruwan sunan ki, kuma abinda yatsai dani wajen ki so da ƙauna ne, tun sanda naƙyalla idanu na naganki naji zuciyata ta kamu da matsananciyan ƙaunarki, kuma wlh ba da wasa nake miki ba, ina son kibani dama Dan Allah na nuna miki irin yanda kika shiga zuciyata kika mamaye min ita acikin mintuna ƙalilan kinji dan Allah".
Ɗan gajeren murmushi tayi kana tace
"Ayya Malam Yazeed Nagode da ƙaunarka gare ni, sai dai ina tunanin ka makaro domin Ni ɗin nan da kake gani tuni na zama mallakin wanin ka, ina faɗa maka wannan maganan ne don kar nawahal da kai".
Murmushi yasaki cike da rashin yarda yace
"To shikenan amma dai kizo muje nasauke ki mana, dan Allah karkice a'a plz ƴar kyakykyawa".
Batasan sanda tasaki murmushi ba takalle sa tace
"Uhm kana son kayi min daɗin baki ko?".
"Ai gaskiya nafaɗa ƴan mata, ko makaho yashafa yasan akwai kyau anan".
Taɓe bakinta tayi tace "to muje".
Gaba yayi yabuɗe mata gaban motan tashige, shima yazaga yashiga yaja motan, sai da yadaidaita motar tasa asaman kwalta ɗin kafin yace
"Har yanzu dai anƙi sanar dani sunan Gimbiyan, sai faman rowa ake min" .
Murmushi kawai tayi ataƙaice tace
"HALWA".
"Wow nice name, Gaskiya sunan yadace dake sosai, Masha Allah suna me daɗi".
"Ko?"
Yace "eh mana, ko bakisan da haka bane?"
Batayi magana ba sai murmushi da tasaki me sauti, daga haka yayi ta jan ta da surutu ita kuma tana amsa mishi wasu kuma iyakan tayi murmushi kawai, har bakin layin gidan su yakaita tace "ya aje ta nan".
Bayan yayi packing ɗin motan yajuyo yana kallonta yace
"To bakiso nakai ki har ƙofar gida ne?"
Ɗan kallon sa tayi tagyaɗa masa kai
"Meyasa to?"
"Babu komi". Ta'amsa mishi ataƙaice
"Uhmmm ko dai bakiso nahaɗu da saurayin ki ne?"
Turo bakin ta gaba tayi sai kuma tataɓe shi tace
"Ba laifi bane hakan ai tunda na sanar da kai dama".
Murmushi yayi yace
"Gaskiya ne, to yanzu bani Numbanki mana tunda kinga ban sauke ki har gida ba, kar kuma yanzu in kin tafi shikenan na rasa ki".
"Hmm tunda har kakawo ni nan ai kamar kakawo Ni gida ne, babu wanda zaka tambaya anan wajen be kai ka gidan mu ba idan har kafaɗa masa suna na, kuma gidan mu ai ba ɓoyayye bane, kana cewa gidan Malam Ayuba za'a kawo ka".
Yazeed yace "to NUMBAN kuma fa bazan samu ba kenan? Please". Yaƙarike maganar yana ɗan marairaice fuska
Cike da ƙosawa tace "bani da waya, sai anjima nagode sosai".
Tabuɗe motan tafito, shi kuma yana ɗaga mata hannu tare da faɗin
"Sai kin ganni kenan ko?"
Kawai gyaɗa masa kai tayi tawuce abin ta, shi kuma yaja motan sa yatafi fuskarsa cike da nishaɗi.
Da sallama tashiga gidan, matar dake zaune tana tatan koko ta'amsa mata tana faɗin
"ƴan makaranta an dawo?"
Cike da gajiyawa taƙarisa kusa da ita tazauna saman turmi tace
"Eh wlh Umma, kin ganni sai yanzu".
Umma tace "gaskiya ne kinsha hanya, ga uban rana da ake ƙwalla wa ai yau ko da gani kin gaji".
"Uhmmm Umma bari ke dai, wlh yau nasha wahala ga wuyan abun hawa da ban samu da wuri ba". Cewar Halwan tana tashi ta'aje jakan ta saman turmin tanufi wajen randan ruwa tabuɗe tana ninyan ɗiba
Umma tace "karki sha wannan ruwan, je ɗakina kiɗauko fure water yanzu na'aiki yara suka siyo min".
"To Umma".
Ɗakin tashige sai gata tafito riƙe da fure water'n ahannu tana faɗin
"Umma ya jikin Zainab ɗin?"
"Alhamdulillah dasauƙi sosai, zazzaɓin ya saukar mata ai, tana nan kwance cikin ɗaki inaga ko barci take yi ne?"
"Ok bari in shiga in ganta".
Ɗaukan jakan ta tayi tashige ɗakin Zainab ɗin, kamar yanda Umma tace kuwa tana kwance tana sharɓan barci duk tayi ɗai-ɗai saman katifan ta sai baza hanci take" bakin gadon tasamu waje tazauna tatsiyaya ruwan ahannun ta tazuba mata a fuska, jin sanyi ya ratsa mata fuska atake tabuɗe idanunta da suka ƙanƙance suka yi ja tana maida su tana rufewa
"To kasa tashi haka barcin ya isa, don nasan ba tun yanzu kike yi ba".
Ɗan yamutsa fuska Zainab tayi taƙara ware idanunta tana kallon HALWA kana tatashi zaune tana sakin hamma, cike da kasala tace
"Har kin dawo?"
Halwa tace "eh na dawo, ya jikin naki? Umma tace "kin samu sauƙi ko?"
"Eh dasauƙi sosai, dama wlh don kaina ya matsa min ne da babu abinda zai sa naƙi zuwa makaranta". Zainab ɗin tafaɗi hakan tana zamewa takoma takwanta
"Gaskiya gwara da kika zauna ɗin don yau babu abunda akayi, Monday ma za'a fara test, amma fa ina faɗamiki show ya wuce ki".
"Dan Allah fa? Ke da mutumin naki?"
Harara Halwa tasakar mata tana yatsina tace
"Banson iskanci fa Zainab, wlh yanzu sai mu ɓata idan kika sake kiran min ɗan iskan nan, mtwww".
Taja tsaki tana ɗaure fuska tare da huro hanci
Ita kam Zainab dariya tayi tace
"Sorry ƙawalliya roman jaɓa wasa nake miki fa, kinsan ni dake bamu haka, bani labari to me yafaru?"
"Ai kuma baki isa ba wlh tunda kika taɓo ni nafasa baki labarin, kinga Ni tafiya ma zanyi dama na biyo ne don naduba jikin naki, tunda yanzu na ganki garas to kinga tafiyata".
Tashi tayi tasaɓa jakan ta a kafaɗa tafice, Zainab na kiran ta amma ko waige batayi ba, tana fita taga Umma har yanzu bata gama tatan ba tace
"Umma na tafi".
"To har zaki tafi? Ina jiran in sauke Dambu nasawo muku kuma?" Umma tace hakan tana kallon Halwa
"A'a Umma kibar sa kawai yau banjin tsayawa ne".
"To shikenan kigaida gida, kigaishe min da Maman naku".
"To zataji".
Daga haka tafice
[8/31/2020, 8:29 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 6*
Shiga tayi cikin gidan nasu da sallama a bakin ta, Mama da fitowar ta kenan daga ɗaki riƙe da kwano ahannu ta'amsa mata tana kallon ta, ƙarisowa Halwa tayi tana kallon Maman nata da tasami waje saman tabarma tazauna tace
"Mamana sannu da gida".
"Yauwa ƴata takaina, kin dawo?".
"Washh.. nagaji wlh Mama".
Halwa tafaɗa tana zama gefen Maman
"Ai daga ganin yanayin ki nasan da haka, da fatan dai ba wahalan mota ce tatsai dake ba?"
"Shine wlh Mama, kuma sai nabiya gidan su Zainab na je duba jikinta".
Mama kallonta tayi tace
"To ya ya jikin nata? Ta samu sauƙi dai ko?"
"Alhamdulillah Mama jikin nata ya warware ai sosai, Umma ma na gaishe ki".
"Tom Ina amsawa, naso ma in shiga in gaishe ta Allah be yiba, sai ki tashi kije kiɗau abincin ki yana ɗakin ki, don nasan tunda kika langaɓe anan sai kizauna kiyi ta zuba bazaki ci ba, kuma nasan da yunwa atattare dake".
Dariya Halwa tayi tace
"Wlh Mamana shiyasa nake ƙara son ki sabida ƙaunar da kike nuna min, uhm ai yau bazan iya wasa da abinci ba sabida yanda naji hanjin cikina suna kaɗawa, bari dai inje in ɗauko".
Tamiƙe tsaye tana kwaɓe hijabinta, Mama kuma taɓe baki tayi tace
"Da dai bansan halinki bane, yanzu sai ki jagula kibar shi nan".
Halwa shigewa ɗaki tayi tana ɗaga murya tace
"Mama banda yanzu dai, kibari kigani har ƙari ma sai kinyi min".
"To bansan surutu kimaza kiɗauko kizo nan kizauna kici".
Fitowa tayi riƙe da coolar ahannun ta da wayanta, zama tayi tana tanƙwashe ƙafafunta tasoma danna wayan tana faɗin
"Mama har yanzu Yaya be dawo ba?"
"Ni ban ganshi ba, sai ki neme sa ta waya kiji inda yatsaya". Cewar Mama tana ci gaba da ɓare maggi
Wayan takara akunni tasoma buɗe coolar'n, hannu tasaka tasoma kai loman abincin dai-dai lokacin da aka ɗaga wayan nata tace
"Wai yaya ina kaje ne har yanzu shiru baka dawo ba?"
"Sorry my Dear, Ina nan kusa naje wajen abokina ne, amma yanzu zaki ganni".
Ɗan shagwaɓe murya tayi tace
"To kayi sauri kaji?"
"Ok karki damu my dear, Yayanki yakusa dawowa".
Daga haka sukayi sallama ta'aje wayan gefe, taci gaba da cin abincin tana yi tana zuba ma Mama surutu, ita kam sai Umm take ce mata, Mama da tagama ɓare maggin miƙewa tayi tashige kichen, lokacin ne Nura yayi sallama yashigo, ɗago kanta tayi dai-dai lokacin da ta'afa shinkafan cikin baki tana kuma amsa mishi sallaman
"A'a yi ahankali mana karki ƙware, wannan loma haka sai kace abincin zai gudu".
Nura yafaɗa hakan yana dariya bayan da yaƙaraso kusa da ita yasami wuri yazauna, ɗan yatsina fuska tayi sai kuma tasakar masa harara tana faɗin
"To aina kaga na zuba loma yaya? Ko bakaga yanda naɗibo bane?"
Ɗan sakin murmushi yayi yana ƙare mata kallo yace
"Na gani mana, ba gashi kin ciko hannu ba kamar wanda take gudun shigowan wasu don halin rowa, nasan fa halin ki Sarkin rowa ce".
Ture abincin tayi tana ɓata fuska, cikin shagwaɓa tace
"Mama kin gansa ko?"
Daga kichen ɗin Mama ta'amsa mata da faɗin
"Ni kin ganni babu ruwana kunfi kusa, karki sako ni cikin zancen ku".
Nura dariya yasaki yana mata gwalo, ai ko kawai tasakar masa kuka
"Kai wai me tayi maka ne Nura daga zuwanka zaka sa ta kuka? Bansan haka fa tam". Cewar Mama kenan tana leƙo kai waje
"Wlh Mama Ni ban mata komai ba kinsan halinta ai bata raina abun kuka, to kiyi shiru mana beuaty daga wasa? kinga nakama kunni na ma".
Dena kukan tayi tana turo baki gaba tace
"Ai kuma mun ɓata tunda Ni kace ma me rowa".
Haba ƴar ƙanwata abar ƙauna ta, kiyi haƙuri kiyafe ma yayanki, ban sakewa wlh kinji? Matso da kunnin ki ma kiji wata magana?"
"Me zaka faɗamin?" Tafaɗa tana kallon sa
Murmushi yayi mata yana kashe mata ido ɗaya yace
"Kalaman da kikafi so mana" ko in aje kayana baƙya buƙata?"
"Ina so mana yaya". Tafaɗi hakan dasauri tana matso da kunnen ta kusa dashi
Magana yaraɗa mata tasaki dariya tana janye kunnen ta, ɗage mata giran sa yayi yace
"To muje mana".
"To bari in sauya kaya, kaje kajira ni a zaure sai ka'aiko yaro ko?".
"Eh haka zamuyi". Nura yafaɗi hakan yana miƙewa dasauri
Itama tashi tayi tashige ɗaki, Mama da tafito daga kichen tabi Halwa da tashige ɗaki da kallo, kana tamaida idanunta kan Nura da yasaka takalmin shi yana shirin ficewa waje tace
"To yanzu kuma me kuka shirya ne na ji kuna ƙus-ƙus?"
Dariya Nura yayi yace
"Zance zamuyi mana Mama, amma yau a zaure zamuyi, zan aiko yaro yakira min ƴar taki, dan Allah karki hanata fita".
Kama haɓa Mama tayi tabi shi da kallo don takasa cewa komai, shi kuma fita yayi yana faɗin
"Sweety kiyi sauri fa, karki shanya Ni kuma don nasan shegen nawan ki".
Babu jimawa kuwa Halwa tafito riƙe da ɗankwali da Hijab ahannu, tsayawa tayi tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwalin
Mama tace "eh haƙiƙa yaran nan dagaske kuke yi, yau kuma gaba ɗayan ku kenan haukan taku tamotsa?"
Halwa dake shirin magana sai ganin yaro tayi ya shigo yana faɗin
"Wai Halwa tazo inji Nura".
Ƙarisa saka Hijabin ta tayi tana faɗin
"Kai kace gata nan zuwa".
Sai takalli Mama tace
"To Mama Ni nafita".
Bata jira jin ta bakin Maman ba tafice dasauri, girgiza kanta kawai Mama tayi tana murmushi tace
"Allah yashirya ku, yaran zamani baku da kunya wlh, ai bari Baban naku yadawo sai ya ji komi".
.
****** ****** *****
Shigowan ta kenan ɗakin taji wayan ta na ringing dasauri taƙarisa taɗauka tana karawa a kunni
"LUBNA kenan". Cewar Mutumin da yakira ta yana sakin dariya
Shiru tayi tana sauraron shi, sai dai babu inda jikinta baya rawa, har zuciyanta na wani irin tsalle kamar zai faso ƙirjinta
"Har yanzu dai kin ƙi aikata abinda muka sakaki ko? Da alamun kina son kirasa kowa naki ne".
Kallon inda Nazeefa take akwance tayi wanda sai sharɓan barcin ta take yi ta ƙudundine jikinta cikin bargo, cikin ƙasa da murya tace
"Dan Allah kuyi haƙuri har yanzu Ban samu nasara bane, wlh kullum sai nashiga nayi muku bincike amma baya barin komi".
"Kina dai wasa da rayuwan Mahaifiyarki da ta ƙannin ki, domin muddin bakiyi abinda mukasa ki ba zaki rasa su, tun yaushe muka baki aikin nan amma kullum magana ɗaya kike faɗa? To ki saurare ni da kyau, akwai wata yarinya da yakawo ta gidan nan kitabbatar da kin fito da ita cikin gidan nan, zan aiko yarana su ɗauke ta".
Cikin rawan murya Lubna tace
"Meee? Nazeefa?"
"Yess ita, ita nake so naɗauka, kijira umarni na".
Ƙitt yakashe wayan, yayinda ita kuma taciro wayan daga kunnen ta tana kallon Nazeefa
"Menene alaƙan su da wannan yarinyan? Me tayi musu? Me suke so da ita?"
Dasauri tamatsa bakin gadon tazauna tana ƙare mata kallo, sai kuma taji kawai hawaye na zubo mata, kifa kanta tayi saman gadon tasoma rera kuka mara sauti
"Meyasaka waɗannan mutanen suka shigo rayuwanta? Me tayi musu ne? Meyasaka sai ita ne zasu zaɓa? Meyasa basuyi tunanin bazata iya aikata duk wannan aikin ba musamman ma akan shi? Tabbas tana da rauni bazata taɓa iyawa ba".
"Waye zai fitar dani cikin wannan ƙangin?"
Tafaɗi hakan lokacin da taɗago kanta idanuwanta sharkab da hawaye
"Allah gani gare ka kataimake ni".
Kallon Nazeefa tasake yi kafin tamiƙe ahankali tashige toilet.
.
.
_shin su waye waɗannan mutanen ne?_
_Meyasaka suke takura ma Lubna?_
_meye alaƙan su da Nazeefa?_
🤷🏻♀️ 💃💃💃💃💃💃
[8/31/2020, 8:31 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖️ *FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 7*
Ahankali yake taka motan kamar koda yaushe, wayan sa dake ajiye ne tasoma ringing, hannu ɗaya yamiƙa yaɗau wayan bayan da yaduba yaga me kira, picking call ɗin yayi tare da saka ta a speaker 🔊 yamaida ya'ajiye
"Hello Bro".
Daga can Sameer yace
"Kana ina da Allah?"
"Yanzu gani na taso wajen aiki zan koma gida".
Sameer yace "yauwa kazo kaɗauke ni Please, motata ce tasami matsala an tafi da ita, ina office Ina jiran ka".
"Ok ganinan".
Juya kambun motan yayi yasauya hanya, minti 15 yakawo shi babban asibitin da Sameer yake aiki, bayan yayi packing fitowa yayi yashiga cikin asibitin, direct office ɗin Sameer yazarce, yana shiga yaganshi zaune yana cike wasu takardu, hannu yabasa suka gaisa sannan yasami waje yazauna
Sameer yace "just give me 10 mint don Allah yanzu zan ƙarisa sai mutafi".
"Babu Matsala". Khalil ɗin yafaɗa yana gyara zaman shi kan kujeran yalumshe idanun sa
"Ka gaji ko?"
Ɗan yamutsa face ɗin sa yayi ba tare da ya buɗe idanun sa ba yace
"Sosai ma, barci kawai nake ji wlh yanzu".
Ɗan kallon sa Sameer yayi yace
"Wai ya maganar tafiyan ka ne? Har yanzu banji kace komi ba?"
Idanuwan sa yabuɗe yana kallon Sameer ɗin yace
"Zuwa Friday zan tafi".
Jinjina kai yayi yace
"But Yakamata kayi taka tsantsan kasan Alhaji Mubarak ba ƙaramin mutum bane, don bani da shakka duk abun da kake shirya wa ana sanar masa, Ni yanzu maganar ma da nake so nayi maka kan Nazeefa ce, Yakamata kaciro ta daga wannan gidan kakaita wajen Mom hakan zai fi".
Khalil yace "ai jiyan nan naɗauko ta namaida ita gida na, inaga can zata zauna".
"Kana ganin babu Matsala?" Cewar Sameer
Gyaɗa masa kai kawai yayi
"Ok amma dai Yakamata kaƙara masu gadi, don nafi tunanin in har tana gidan ka zasu fi sanin haka, sannan kuma kaga kai tafiya zakayi Yakamata kaduba shawarata".
Shiru Khalil yayi naɗan wasu sokonni kafin yace
"Ok Bro".
Daga haka hira suka soma duk dai akan case ɗin Alhaji Mubarak, kafin Sameer yagama suka tashi suka fice, har gidan sa yasauke sa Sameer ɗin yace
"Baza ka shiga ba?"
Girgiza kan sa kawai yayi yace
"No kagaishe min dai da auntyna, sai wani lokacin zan shigo".
Ɗan taɓe bakin sa kawai Sameer yayi yace
"Kunfi kusa ai".
Kafin yabuɗe motan yafice, shi kuma yaja ahankali yatafi, a bakin Gate yadakata yadanna hon aka buɗe masa yashige, bayan yayi parcking motan yabuɗe yafito riƙe da briefcase ɗin sa a hannu, yafara tafiya cikin ƙasaita yanufi cikin gidan, hannun sa yasaka yabuɗe ƙofan yana ɗan motsa bakin sa yashige, tana tsaye wajen dainning table tana jera abinci taɗago kanta takalle shi, saurin sauke kanta tayi ganin sun haɗa idanu, cike da sanyin murya tace
"Sannu da zuwa".
Gyaɗa mata kai kawai yayi yana ci gaba da kallon ta, ahankali yasoma takowa cikin Palon kafin yace
"Ina Nazeefa?"
"Tana ciki tana barci".
"Tasha maganin ta?" Yasake jeho mata tambayan still yana kallon ta
Lokacin itama taɗago kai taɗan saci kallon sa dasauri taɗauke kanta tace
"Tasha".
"Ok ki tashe ta taci abinci".
"To Sir".
Wucewa ɗakin sa yayi, ita kuma tabi sa da kallo tana jin tsananin ƙaunar sa na ƙara shigan ta, ɗauke kanta tayi bayan da yashige tana sauke ajiyan zuciya, tasan da cewa babu yanda za'ayi tasame shi, yafi ƙarfin ta tako ina koda a mafarki ne, haƙiƙa zuciyanta tayi ganganci da takamu da ƙaunar wanda be san ma tana yi ba, tasan da cewa zuciyarta ba ƙaramin yaudaranta take yi ba da har taso uban gidan ta a matsayinta na ƴar aiki. Ci gaba da jera dainning ɗin tayi kafin tagama tashige ɗaki
Shi kuwa yana shiga ɗakin sa kayan jikin sa yasoma ragewa kafin yashige toilet, be daɗe ba yafito yasaka farar singlate da Black Three qweater yafaɗa saman gado, sosai yake jin barci kuma gashi yana jin yunwa, sai dai bazai iya tashi yaje yaci abinci ba sabida tsananin barcin da yake ji cikin idanun sa, ai kuwa yana kwanciya babu daɗewa barci yaɗauke shi
Ba shi yatashi ba sai 05:04pm, yana buɗe kyawawan idanun sa yaɗaura kan agogon dake manne jikin bango, dasauri yamiƙe yana salati, direct toilet yawuce agurguje yayi wanka yaɗauro alwala yafito, jallabiya kaɗai yazira ajikin sa yashimfiɗa dadduma yagabatar da sallan asar, lokacin da ya'idar ne yaji wani yunwa na ƙwaƙwulan cikin sa, ɗan shafa cikin nasa yayi yana lumshe idanu kafin yabuɗe su yamiƙe tsaye, gaban sif ɗin sa yanufa yaciro kayan da zai sa, kafin yakoma gaban mirror yasoma shafa Lotions, sai da yagama sannan yasaka kayan sa, riga da wando ne, rigan kalan maroon ne me hoton kan sarki, daga saman ta an rubuta THE KING da black colour, haka ma wandon sa Black jeans ne, sai yazira room slippars yafeshe jikinsa da turare sai tashin ƙamshi yake yi, wayoyin sa yaɗauka yanufi palow, babu kowa ciki yanemi kujera a ɗaya daga cikin kujerun dainning yazauna, buɗe coolar'n gaban shi yayi yaga farar shinkafa ne zalla da yankakken hanta a sama, be da sha'awan buɗe sauran, plate kawai yaɗauka yaɗibi abincin yarufe, sannan yabuɗe coolar'n dake kusa da wancan ɗin yaga miya ce na jajjage wanda yaji kifi sai tashin ƙamshi yake yi, zubawa yayi yasoma ci ahankali yana yi yana latsa wayan sa
Nazeefa ce tafito daga cikin ɗaki sanye da doguwan riga ja me kwalliyan furanni, ta yafa gyalen kayan tana tafiya ahankali kamar wacce ƙwai yafashe mata a ciki, saman kujerun Palon tanemi wuri tazauna tana kallon shi, cikin sanyin murya tace
"Yaya ina wuni".
Sai lokacin yaɗan ɗago kai yakalle ta naɗan wani lokaci kafin yamaida idanun sa kan wayan sa yaci gaba da abin da yake yi, can kuma ya'amsa mata da
"Lafiya".
Shiru ne yabiyo baya, sai kuma tagyara zamanta tana kallon shi, gaba ɗaya hankalinta da tunanin ta yana gare shi, komi nasa yana matuƙar burgeta, to meyasa? Take tatuno sanda suka fara haɗuwa yataimake ta duk da bata cikin hayyacin ta, wani kyakykyawan murmushi tasaki tana jin zuciyarta na mata sanyi da daɗi, memakon tariƙa kukan maraici sai dai ko kaɗan yanzu ji take yi tamkar bata rasa komi nata ba, duk sanda tatuna fuskar sa tana ji ne kamar tafi kowa Sa'a a duniya
"Wannan wani irin yanayi nake ji haka? Meyasaka nake jin sa daban da sauran maza?"
Zuciyarta tayi mata wannan tambayan, batakai ga lalubo amsan ta ba taji muryan sa me tsananin daɗi a cikin kunnen ta yana faɗin
"Kidena yawo da yawa saboda aikin dake cikin ki, kiriƙa tambayan Lubna duk abinda kikeso bana son yawan fitowa nan in ba da ƙwaƙwƙwaran dalili ba".
Nazeefa gyaɗa masa kai tayi, sai kuma ta'amsa mishi ganin baya kallon ta yayi maganan
"To Yaya".
Tafaɗa cike da sanyin murya kafin tatashi tasoma tafiya don komawa ɗaki, ahankali take takawa har tashige, tana shiga Lubna takallo ta sai kuma taɗauke idanun ta taci gaba da tunanin ta, itama Nazeefa samun waje tayi gefen gadon tazauna tana tunanin Brr. Khalil, daga ƙarshe tazame takwanta tana rufe idanuwanta, tashi Lubna tayi tafice zuwa kichen don ɗaura abincin dare, koda tafito idanuwanta akan shi suka sauka, sosai yau yayi mata kyau duk da ko yaushe shi ɗin me kyau ne, amma yau sai takasa ɗauke idanunta akan sa har sai da tagama ƙare masa kallo kafin tashige kichen
Ahankali yamiƙe yanufi ƙofan fita, a Compound ɗin gidan yatsaya yajingina bayan sa da bango yana lumshe idanuwan sa tare da sanya hannun sa ɗaya cikin aljihun wandon sa, shiru yayi yana sauraron bugun zuciyan sa yana tunani, ya jima awajen har sai da yaji kiran sallah kafin yanufi inda me gadi yake yayi alwala anan, tare suka jera da me gadin da sauran ma'aikatan biyu suka nufi masallaci, shi dama ba ma'abocin girman kai bane ga masu aikin sa, wani lokacin ma in yasami time wajen su yake zuwa suyi ta mishi hira shi kuma yana kallon su, duk da baya magana amma sosai yake fahimtar su, wani lokacin har yaɗan dara in suna bashi labari me daɗi, acan suka baro shi sai da yayi sallan isha'i kafin yadawo gida, Direct saman dainnig yanufa yahaɗa tea yasha, ko minti 10 be yi ba yatashi yakoma ɗakin sa, acikin ɗakin da yake aikin sa yashige, kujera yasamu yazauna yajanyo lapton ɗin sa yasoma aiki ciki, minti 5 da soma aikin nasa yamiƙe yafita, briefcase ɗin sa yaɗauko yadawo yazauna, Computer yaciro da wasu ducuments yaci gaba da aikin sa, sai da ƙarfe 12:017pm yayi kafin yadakata yarufe lapton ɗin da Computer, tashi yayi yana miƙa cike da gajiyawa yafice yanufi Toilet, alwala kaɗai yayi yafito yasauya kaya zuwa kayan barci yakwanta tare da kashe fitila.
.
_to nima bari in dakata anan, karku manta da_
*Like*
*Comments*
*Vote*
*Share*
_ina yin ku masoyana_ 💃💃💃💃💃
[9/1/2020, 10:12 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 8*
Tafiya suke yi suna sanye da uniform, fitowan su kenan akan hanyan su tazuwa school, Halwa take bata labarin haɗuwan su da Yazeed jiya, ita kuma Zainab zai ɓaɓɓaka dariya take yi har da riƙe ciki
"Ke kiyi fa ahankali karki jawo mana mutane nan". Cewar Halwa kenan tana kallon Zainab
"Ƙyale ni in dara, wlh kin bani dariya, hhhhh wai ke adole ga kurma, kai wlh banji daɗi ba da bana nan akai wannan draman, kawai lokaci ɗaya Allah yatoni asirin ki".
Sai takuma kwashewa da dariya, Halwa bige mata kafaɗa tayi tana faɗin
"Ke fa tsiyata dake ba'a zancen arziƙi dake, yanzu sai kihau ma mutane wannan haukan naki, mtswww".
Taja gajeren tsaki tana ɗaure fuska, sai lokacin Zainab taɗan sassauta dariyan da take yi tace
"Wooo kurma ta Yazeed yi haƙuri ban sakewa".
Wani irin kallo tayi mata tace
"Gyara kalaman ki, kidena danganta ni dashi, kinsan dacewa ni ɗin mallakin Yaya Nura ne shi kaɗai, to dan Allah kidena bana so".
Taɓe baki Zainab tayi tace
"Nafi kowa sanin haka ai, amma babu yanda Allah baya lamarin sa, yanzu sai kiga an sauya d.."
Saurin bige mata baki Halwa tayi tana faɗin
"Kull.. karki soma, wlh in kika ƙarisa sai an ji mu dani dake, Allah ni nakula ma kamar baƙin ciki kike min, to ta Allah ba ta ki ba, insha Allahu sai na zama mallakin Yaya Nura na sai dai kimutu".
Zainab dariya tayi tace
"Hmmm yi haƙuri ƙawalli na dena, in kinso ma gobe aɗaura miki aure dake dashi, ni wlh bata shafen ba".
Halwa tace "to ai ko bakice ba, ni inda za'abi ta shawarata wlh kafin muƙarisa wannan makarantan kawai aɗaura mana aure, domin ni a tsarina bana son nagama secondary batare da nashiga daga ciki ba".
Baki Zainab tariƙe tana kallon ta
"Lallai Halwa kin ƙosa da yawa, amma bansan haka ba sai yanzu, to gaskiya Yakamata su Mama suyi saurin miƙa ki tun kafin aji sautin kiɗan ya sauya".
"Ni da ma zaki taimaka min da yafi, kije kisanar mata tunda su har yanzu sun kasa sanin haka, wlh Zainab ina faɗamiki auren wuri daɗi ne dashi, kema dai ki aje wannan aƙidan naki kawai mu jone ayi mana tare ko ma huta, ko ba haka ba?" Cewar Halwa tana kallon Zainab tare da ɗage mata gira
Girgiza kai Zainab tayi tace
"A'a ke dai da kikaga zaki iya sai kiyi tayi, wai ma duka-duka nawa muke da har zamuyi aure, just 18years fa kenan, kinga ke kin riga da kin lume a soyayyan Yayan ki bazaki gane ba, amma ni bar ni sai na zaɓa Wanda naga ya dace dani, kuma wanda yafi kwantawa da ra'ayina".
Halwa tace "ni fa nasan halin ki, be wuce kice me kyau kike nema ba, to me zai hana nahaɗa ki da Yazeed wlh zaku dace sosai, domin ya haɗu tako ina kamar dai yanda kikeso".
"Haba dan Allah?"
"Wlh kuwa sai ma kin ganshi, nima ba ƙaramin burge ni yayi ba, sai dai kinsan tuni zuciyata ta riga ta makance ga wanin shi, babu wanda nake gani da zaifi min Yaya Nura na".
Zainab taɓe baki tayi tace
"Na kula fa kamar ma kinfi son sa akan shi, ke dai baki da zance sai ta wani Yaya Nura, uhmmm Allah dai yanuna mana ranan, amma ni gaskiya ba yanzu zanyi aure ba, sai na yi nisa a karatuna".
Daidai lokacin da wata keke napep tazo wucewa Halwa tatare tana faɗin
"Ameen inda gaske kike, kuma ko me zakice sai dai kice".
Zainab batace komi ba in banda dariya da tayi, napep ɗin suka shige yaja suka tafi, a cikin motan ma hiran suke tayi har yakawo su, bayan sun sauka Halwa ce talaluba cikin jakan ta taciro gudan ɗari tamiƙa masa, har sun soma tafiya sai wata mota tasha gaban su, atare suka tsaya suna kallon motan, wani ingarman saurayi ne yafito, yana sanye da ɓakin singlate da farar wando Three qweater, jikin sa duk zanen tatue ne kai da gani kasan irin ƴan iskan nan ne waɗanda suke tsula tsiyan su cikin gari, wani shegen aski ne akan sa oho ni na manta sunan sa ma, wuyan sa duk sarƙoƙi ne har guda biyar, tun sanda yafito yazuba ma Halwa idanu yana wani irin murmushi tare da ɗage mata gira, ita kuma sai taɗauke kanta takama hannun Zainab zasu kewaya su wuce, wuf yashige gaban su yana ci gaba da bin ta da wani mayataccen kallo yace
"Babyna babu magana?"
Ko ɗago kai bata yi ba illa sake riƙo hannun Zainab da tayi tana son sauya hanya, yasake shan gaban ta yana cewa
"Wai Baby bakiyi missing ɗina bane? Meyasaka kike min haka ne? kinsan da cewa ina matuƙar ƙaunarki da sha'awanki why bazaki bani dama ba?" Yaƙarike maganar sa yana matso da fuskar sa kusa da nata still yana murmushi me ma'anoni da yawa
Ɗan ja da baya tayi tana yamutsa fuska kana tabi shi da banzan kallo, batace komai ba dai tajuya da ninyan barin wajen gaba ɗaya sai ji tayi ya janyo mata Hijab, kiiiii sai gata tadawo gaban sa, yasanya hannu yariƙo hannun ta yana faɗin
"Common Baby sai yaushe zaki waye ne.."
Marin da tasauke mishi a fuska ne yakatse mishi maganar shi, sakin ta yayi yadafe kuncin sa da hannayen sa biyu yana kallonta cike da tsantsan mamaki, ba shi ba har Zainab sai da tatsora ta da marin da Halwa tayi mishi
Muryan Halwan ne yakatse musu mamakinsu su duk ka biyun
"Wlh koda wasa kasake ɗaukan banzan hannunka me datti kaɗaura shi akaina sai nayi maka mafiyin wannan, banza ɗan iska".
Tajuya zata tafi yayi saurin sake tare ta, cikin tsananin ƙunan rai kamar wanda zai kai mata duka wanda har sai da taɗan tsorata da ganin yanayin sa yace
"Ni kika mara Halwa? Ni Ko?"
Ɗan girgiza kan shi yayi yana sakin murmushin gefen baki yaci gaba
"Zan nuna miki waye Haris, wlh sai kinyi nadaman zuwanki duniya, sai nayi miki abinda har kimutu bazaki taɓa manta ni a rayuwanki ba tunda har kika iya cire hannu kikayi min abinda ba'a taɓa min ba, kijira kika me zai biyo baya".
Yana faɗin haka yajuya dasauri yabuɗe motan sa yashige, har motan shi yayi nisa bata ɗauke idanunta kan shi ba, sosai tatsora ta da ganin yanayin sa, ita tasan waye Haris, ba ƙaramin tantirin ɗan iska bane batasan me zai biyo baya ba kamar yanda yace "tajira zata gani" amma kuma ko kaɗan batayi nadaman marin da tayi masa ba, inda tana da ƙarfin da zatayi mishi mafiyin haka to wlh sai tayi masa
Zainab ce takatse mata tunanin ta da faɗin
"Mun shiga uku Halwa me kikayi haka? Haris fa kika mara? kuma kinsan ko shi waye a garin nan, wlh sai yaɗaure kaf dangin mu babu wanda ya'isa yafiddo mu, meyasa dan Allah kikayi wannan ɗanyen aikin? Kinsan fa ba yau yasaba miki irin haka ba".
Kallon ta Halwa tayi cike da jin haushin maganan ta tace
"Kenan kinaso kice min in barshi ya taɓa min jiki a banza? Kinsan halin sa ɗan iska ne idan har ban taka mishi birki ba gobe ma sakewa zai yi, yaje yayi duk abinda zai yi ta Allah ba tashi ba, mtswww ke kike jin tsoron sa".
Tana faɗin hakan tawuce tabar ta nan, biyo bayan ta itama tayi tana kiran sunan ta, ita ko bata kula ta ba tabuɗe Gate ɗin tashige, babu wasu mutane cikin school ɗin sai ƴan tsiraru, Direct class ɗin su da yakasance s.s3 suka wuce.
.
_To fa me zai faru?_🤔
*Comments & share plz*
[9/1/2020, 4:35 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 9*
"Mom wai yaushe Dad zai dawo?"
Shafo suman kanshi tayi tace
"Inaga sai gobe zai dawo, amma kaneme shi ta waya mana".
"Ok".
Mom tace "ɗazu Sameer yake sanar dani jibi tafiyan ka ko?"
Gyaɗa mata kai kawai yayi yana gyara zaman shi
"Ok Allah yakaika lafiya, kadai ta addu'a banaso kana wasa da addu'a, kasan aikin nan naka akwai maƙiya sosai dole sai kariƙa neman kariya wajen Allah, nima ina nan ina tayaka, Allah yamaka albarka yasa kafi haka Autana".
Murmushi Khalil yayi yace
"Ameen Mom, dama Ina so ince miki zan dawo da Nazeefa wurinki sai tazauna anan".
"Ok ai babu damuwa kadawo da ita, dama nan ɗin yafi dacewa kakawo ta, yanzu katashi muje kaci abinci tunda an gama".
Be musa mata ba yamiƙe yanufi wajen dainning ɗin, itama biyo shi tayi suka zauna a jere sannan tayi saving ɗin sa, yasoma cin abincin ita kuma tana masa hira, shi kuma sai dai yasaurare ta da kunni kawai wani lokacin kuma yana gyaɗa mata kai.
******
Shigowan ta sau biyu cikin ɗakin tana ganin ta kwance, sai dai ta kasa aiwatar da abinda tazo yi ɗin, yanzun ma har zata koma sai kuma tayanke shawaran kawai zuwa, ahankali tatako tazo bakin gadon tasami waje tazauna, shiru tayi don ta rasa ta ina zata fara, ba kasafai suke magana ba tun kwana biyu da zuwanta cikin gidan, daurewa tayi dai ahankali takira sunan ta
Nazeefa da idanuwanta ke kulle sai dai ba barci take yi ba, hakan yasaka tabuɗe idanunta tabi Lubnan da kallo, sai tasakar mata murmushi tace
"Na ganki shiru ne tun ɗazu, shiyasaka nace ko zakizo kiraka ni zanje gidan mu kar in fita in barki ke kaɗai".
Itama murmushi tayi mata sannan tatashi zaune tace
"Ai babu damuwa anty, muje in rakaki, dama zaman ya ishe ni haka".
Murmushin samun nasara Lubna tayi tatashi tana faɗin
"To muje ko".
Miƙewa Nazeefa tayi taɗau hijabinta dake ajiye saman gadon tasaka, tabi bayan Lubna da har tasoma tafiya zata fice a ɗakin, ahankali take takawa sai dai tafiyan ta ba normal take yin sa ba sabida aikin dake cikin, hakan yasaka take ɗan duƙawa kaɗan, fitowa sukayi daga cikin gidan suka tunkari bakin Gate, har suka ƙarisa babu kowa, shima me gadi ya zagaya baya, don haka kai tsaye suka tunkari ƙofan Lubna tabuɗe suka fice
Daga can nesa wata baƙar mota ce aka faka, ba'a ganin cikinta ko kaɗan, tunda suka fito Lubna tahango motan don haka Direct wajen suka nufa, ita dai Nazeefa sai bin bayanta take yi tana yi tana kalle-kallen tsarin wajen, gaba ɗaya layin gidajen masu kuɗi ne kamar g.r.a haka layin yake.
.
_shin me zai faru?🤔 Ina Lubna zatakai Nazeefa?_
_ku bini asannu don jin me zai faru._
*More comments more post* 💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
[9/2/2020, 1:47 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 10*
Har sunyi rabin wajen motan sun kusa isowa sai ga motan Khalil ta shanyo kwana, ahankali ya'iso wajen su yatsai da motan yana zuge glass ɗin motan, tsananin ruɗewa Lubna tayi har batasan sanda tazaro idanu waje ba tana kallon shi kamar yanda shima ɗin yake bin su da kallo, sai da yagama ƙare musu kallo kafin yasauke idanunshi kan Lubna wacce tagama tsurewa yace
"Me yafito daku nan?"
Gaba ɗaya ta rasa ma me zatace sai duƙar da kanta da tayi tana jin ƙirjinta na bugawa kamar zai faso waje
"Kushiga mota". Yace dasu yana ɗauke kan shi daga kallon su
Nazeefa ce tafara buɗe gaban motan tashige, ita kuma Lubna jikinta na rawa tabuɗe baya tashige, jan motan yayi slowsly yanufi gida, sai da yayi hon har sau biyu kafin Gateman yabuɗe masa, kutsa hancin motan yayi ciki ya'isa har packing space, bayan ya tsai da motan gaba ɗayan su suka fita sukayi cikin gidan, yayinda shi kuma yatsaya cire wayan sa dake chagi yafito, Direct wajen me gadi yanufa, tun sanda me gadi yahango shi yanufo shi dasauri yana faɗin
"Ranka yadaɗe Barka da zuwa, sannu da dawowa".
Fuskar shi aɗaure yace dashi
"Meyasaka kabar Nazeefa tafice cikin gidan nan?"
Me gadi da mamaki yacika shi yace
"Nazeefa kuma ranka yadaɗe? Ai banga tafita ba, wlh bansani ba ranka yadaɗe".
"Kenan wasa kake yi da aikinka ko? Ina kaje har tafita cikin gidan nan baka sani ba?"
"Wlh ranka yadaɗe wlh bansan tafita ba, kuma wlh babu inda naje in banda zagayawa da nayi".
Khalil soka hannun sa yayi cikin aljihu yana kallon sa yace
"Kakula da aikinka bana son wasa, idan har kana min irin haka tabbas zamu sami matsala ni da kai".
"To ranka yadaɗe insha Allah, ayi haƙuri bazan sake ba".
Be sake cewa komai ba yajuya yatafi, yana shiga cikin Palon babu kowa Direct ɗakin su yanufa, yabuɗe yashiga yana bin su da kallo har yanzu fuskar shi a ɗaure, yayinda su ma kallon shi suke yi suna zaune tsamo-tsamo saman gado musamman ma Lubna da tagama tsorata da yanayin shi
"Meyasaka kuka fita cikin gidan nan? Ina zakuje?" Yayi tambayan yana kallon Lubna da idanuwansa masu kaifi da burgewa
Cikin rawan murya tabuɗi baki tace
"Uhm dama.. dama zamuje gidan mu ne".
Wani kallo yayi mata me cike da ma'anoni sannan yace
"Kar in ƙara ganin kun fita cikin gidan nan, idan har gida kikeso kije kifaɗamin zan saka drever yakai ki, kuma ke kaɗai zaki fita karki soma janta kufita tare, kina jina?" Yaƙarike maganar da kakkausan murya
Atare suka gyaɗa mishi kai, har Nazeefa da itama tagama tsorata dashi domin bata taɓa ganin shi ahaka ba, shi mutum ne me sauƙin kai ba kasafai yake nuna fushin shi ba
Juyawa yayi yafice yanufi ɗakinsa, akan gado yazauna yasoma cire Combat ɗin ƙafan sa da socks ɗin sa, sai da yagama yacire farar suit ɗin dake saman farar rigan ciki ya'ajiye, ahankali yazuge necktie ɗin wuyan sa yacire gaba ɗaya ya'ajiye, agogon hannun sa yacire itama ya'ajiye sannan yakwanta yana lumshe idanun sa, yayinda ƙafafunsa ke ajiye a ƙasa gangan jikin sa kaɗai ke saman gadon, tunani kawai yake yi cikin ran sa har be san sanda time yaƙure masa ba, miƙewa yayi ahankali yanufi cikin Toilet, wanka yasoma yi kafin yaɗauro alwala yafito, Direct gaban mirror yanufa yazauna, sai da yawarware shawul ɗin dake kan sa sannan yasoma goge kan, bayan ya gama yabusar da kan da handrayer sannan yasoma shafa Expensive lotions ɗin sa, har gashin kan sa sai da yashafe su da mayuka masu tsananin ƙamshi da ƙara taushin suma, yaɗau kumb yataje gashin yagyara shi yayi matuƙar kyau, kana yamiƙe yanufi sif ɗin sa, wata farar riga me gajeren hannu yaciro sai blue jeans yasaka, da alamu dai shi ma'abocin son fararen kaya ne, wrest watch ɗin sa da Combat ɗin ƙafan sa duk farare ne yasaka, sai da yagama gyara jikin sa yafeshe ko ina na jikin sa da farpume's ɗin sa masu ƙamshin daɗi kana yaɗau wayan sa da car keey yafito, fita yayi yanufi wajen motan shi yashige yaja yana danna ma me gadi hon, ba ɓata lokaci yabuɗe masa yafice, sai da yatsaya bakin masallaci yafita yayi sallan asar kafin yakoma yaja yatafi
A bakin gidan Brr. Tahir yatsaya yaɗau wayan sa yakira sa, babu jimawa shima yafito yashiga cikin motan yaja suka tafi, a wani madaidaicin gida suka tsaya wani mutum yafito daga gidan yayi musu jagora suka shige ciki, tattaunawa sukai tayi akan aikin su har wajen magrib suna tare, sai da sukayi sallan magriba da isha'i kafin suka rabu, har gida Brr. Khalil yasauke Brr. Tahir kafin shima yakamo hanya zuwa gidan shi.
Koda ya'isa kai tsaye ɗakin shi yawuce, yacire kayan jikin shi yabar wandon da singlate yafito palow, a saman sofa yazauna yana ɗaukan remote yakunna t.v, sai kuma yatashi yanufi kan dainning yahaɗa tea me zafi yadawo yazauna, yana sipping tea ɗin idanunsa na kan t.v, ahaka har yashanye sannan yatashi yamaida cup ɗin saman dainnig, kashe kallon yayi yakashe komi na na'ura dake cikin palon yanufi ɗakin sa, wanka yayi yasauya kayan barci, yazauna bakin gado yasoma aiki cikin computer ɗin shi, wajen ƙarfe 11:56pm yagama sannan yakwanta.
........ ........ ..........
*WASHE GARI*
Ƙarfe 03:10pm yatashi daga aiki, ya fito cikin office ɗin sa yana rufewa itama Bilkisu tafito daga office ɗin ta, har tagama rufe nata office ɗin shi be gama ba, sai tatsaya tana kallon shi har sanda yagama yajuyo sukai ido huɗu, dasauri yaɗauke kan sa yasoma takawa yana barin wajen, itama biyo bayan shi tayi har zuwa inda ya'ajiye motan sa, yana ninyan buɗe motan yatsinkayi muryan ta abayan shi
"Dan Allah kasauke ni agida mana, yau banzo da tawa motan bane, kuma gashi ana jirana Uncles ɗina sun zo daga garin mu".
Juyo da kansa yayi yakalle ta sai kuma yataɓe baki yabuɗe motan sa yashige, hakan yasaka itama tazagaya dasauri tabuɗe gaban tashiga, be ce mata komi ba yakunna motan yaja suka fice, shiru cikin motan babu wanda yayi magana, sai dai ita tana yi tana satan kallon shi, sosai yayi mata kyau yau ɗin cikin shigan sa da yasaba yi koda yaushe, suit ne kalan ash da ƴar cikinta milk colour, haka komi da yasanya sun kasance milk ne har ta da Expensive wrest watch ɗin da yaɗaura a hannun sa
A bakin Gate ɗin gidan su yatsai da motan, ita kanta batasan an kawo ba sai da taji tsayuwar motan, kallon gidan su tayi sai kuma takalle shi don bata zata zai iya gane gidan nasu ba duk da zuwan sa sau ɗaya ne, tun farkon fara aikin su tare lokacin tanemi yarage mata hanya, cikin sanyin muryan ta me daɗi tace
"Nagode.."
Sai kuma tayi shiru tana wasa da hannun jakan ta, ɗan ɗago kanta tayi takalle sa idanuwanta na cikowa da hawaye tace
"Har yanzu dai bazan daina nuna maka ƙaunar da nake maka ba, ina ƙaunarka Ib, ina ƙaunar ka sosai, ni kaina bazan iya juran yanayin da natsince kaina aciki ba shiyasa nakasa ɓoye ƙaunar da nake maka, don Allah koda sau ɗaya ne tak a rayuwa kafurta min kana sona ko zuciyata zata sami sukuni, Allah ne yaɗaura min ciwon son ka kuma kai kaɗai ne zaka iya min maganin ta, har yanzu har gobe bazan gaji ba Ib, ina matuƙar matuƙar ƙaunarka".
Tana kawo nan azancen ta tayi shiru tana jan numfashi, sai kuma tabuɗe ƙofan tafice, idanuwan shi yaɗago yabi ta da kallo, tafiya take yi tana share hawayenta da gefen gyalen ta har tashige cikin gidan nasu, kafin shi kuma yaɗauke idanun shi yana sauke ajiyan zuciya, ya sani duk acikin ƴan matan da suke nuna masa ƙauna ba wacce takai Bilkisu, yasan da cewa ita ɗin ta daban ce cikin mata, tana da hankali da nutsuwa, gata kyakkyawa babu abunda tarasa, sai dai ko kaɗan shi soyayya bata burge shi, tunda yake be taɓa son wata ɗiya mace ba, be san ma ya ake soyayya ba, shi dai kawai yasan da cewa mata suna matuƙar bashi tausayi, sosai yake jin ta cikin ran shi sai dai bazai iya yin abinda take so ba
ahankali yaja motan sa yaci gaba da tafiya, zuciyan sa cike fal da tunanin ta.
.
*Comments*
*Vote*
*Share*
[9/3/2020, 2:24 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 11*
A Compound ɗin gidan sa yayi packing ɗin motan, tsawon mintuna 5 yaɗauka kafin yabuɗe murfin motan yafito, ahankali yake tafiyan nasa cike da salon burgewa har yakai bakin ƙofan main Palon yabuɗe yashiga yana motsa bakin sa, babu kowa ciki sai ƙaran T.v plasma da yacika cikin Palon sai aiki yake yi shi kaɗai, Direct ɗakin sa yanufa yashige yarufo ƙofan, asaman gado ya'ajiye briefcase ɗin sa, yazaro wayoyin sa dake aljihun wando yazube su akan gadon, sannan yacire links ɗin rigan sa yakuma cire agogon hannun sa yabuɗe drower yasaka, zama yayi saman gadon yaɗau wayan sa yalatsa yakara a kunni
"Kihaɗa ma Nazeefa kayanta kice tajira ni a palow".
Abinda yafaɗa kenan yatsinke kiran ya'ajiye wayan, tashi yayi yanufi Toilet yasillo wanka yafito ɗaure da towul ajikin sa, duk jikin sa ruwa ne ke ɗiga haka yanufi gaban mirror yazauna a stool, shiru yayi yana kallon kan shi a madubi, kyakykyawan surar jikin sa yake bi da kallo na tsawon lokaci kafin yaɗauke idanun sa, sai kuma yamayar da idanun nasa yana ƙare ma beauty face ɗin sa kallo, ya daɗe ahaka shi kan sa be san meyasaka yake kallon halittan nasa ba, amma dai yasan da cewa shi kan sa yana tsananin burge kan sa, komi nasa me kyau ne musamman ma ƴan manyan idanuwan sa masu ɗaukan hankali farare ƙal dasu, da yawa ƴan mata suna nuna masa matuƙar ƙauna kamar su cinye sa, tun yana ƙarami haka yataso me farin jinin jama'a kowa son sa yake yi ba mazan ba ba kuma matan ba, shi ba mutum bane me yawan shiga abun da babu ruwan sa kuma ba me yawan magana bane shiyasaka wasu suke ce mishi me girman kai, kuma ba haka bane sai dai in baka zauna dashi ba, anan ne zaka fahimci halin sa sosai yake da kirki da sauƙin kai.
Ajiyan zuciya yasaki yasoma shafa Lotions ajikin sa, bayan ya gama sai yaɗau kumb yataje suman kan sa yakwanta luf sai shaining yake yi, kai da gani kasan sosai kan yake shan kuɗi wajen gyara, miƙewa yayi yanufi sif ɗin sa yaciro kayan sa, sanya wa yayi yana gyara wuyan rigan tare da ɓame bottles ɗin, yadi ne fari ƙal tamkar tissue har singlate ɗin da yasaka ciki ana gani, sun bala'in ɗaukan golden skin sa, sosai sukai mishi kyau, sai da yafeshe jikin sa da farpume's ɗin sa sannan yasaka Black cover shoes a ƙafafun sa, yanufi gaban gadon sa yaɗau wayoyin sa da mukullin mota yatako yabuɗe kofa yafita
Dasauri taɗago kanta takai duban ta gare sa, haɗa idanun da sukayi yasaka hawayen dake maƙale a kurmin idanun ta daman zubowa, saurin ɗauke kanta tayi taduƙar dashi ƙasa, sosai tashiga damuwa tun sanda Lubna tasanar mata da abinda yace, duk da batasan ina zai kai ta ba but ko kaɗan bata son rabuwa dashi, bata son tayi nesa dashi, a ɗan zaman da tayi na kwana uku rak cikin gidan sa yafiye mata sauran tsawon shekarun da tayi a duniya, zaman ta gidan sa tamkar wani haske ne cikin zuciyarta
Muryan sa da yadoki kunnin ta shi yadawo da ita duniyar da taburma
"Tashi muje".
Abinda yafaɗa kenan yayi gaba, itama kuma ahankali tamiƙe tajanyo trollyn kayan ta tabi bayan sa, lokacin da ta'isa jikin motan har ya shige ya bar mata Boot abuɗe, ɗaya daga cikin ɗan aikin gidan shi ya'amsa trolly ɗin yasaka a Boot ita kuma tabuɗe gaban motan tashiga, keey yayi ma motan yaja ahankali yafice daga gidan, cikin motan ma babu wanda ke magana cikin su, Nazeefa kaɗan-kaɗan take ɗago kanta takalle shi tana sharan hawaye, tuƙin sa yake amma duk yana lura da ita, kuma akan idanun sa ɗazu hawayen ta yazuba, ahankali cikin cool voice ɗin sa yace
"Lafiya kike kuka?"
Tambayan ba kaɗai yashige ta ba don batayi zaton yasan tana yi ba, ɗago kai tayi takalle shi, sosai yayi mata kwarjini da cika idanu, sauke kanta ƙasa tayi tana ɗan saka yatsa tashare sauran hawayen nata, bata iya buɗe baki ba bare tabashi amsa, hakan yasaka tayi shiru don batasan me zatace ba, shima ɗin be sake tambayan ta ba, sai can kuma da sukayi nisa yace
"Ko dai ciwon ki ne ke miki zafi?" Yafaɗa maganan kamar me raɗa yana kallon ta
Sai da taɗago kai takalle sa sannan yakau da kanshi, cike da sanyin murya tace
"A'a, bana son rabuwa da kai ne yaya".
Jin maganan yayi ta ɗan duke shi, hakan yasaka yasake kallon ta sai kuma yaɗauke kai yamaida ga titi
"Kidena damuwa Nazeefa ba wani waje zan kai ki ba, wajen Mahaifiyata zan mayar dake zaki fi samun kulawa, ke yarinya ce yakamata ace akwai wacce zata riƙa kula dake, zaman ki gidana akwai takura da yawa, ki kwantar da hankalinki nasan kina tunanin ko mun rabu kenan".
Ahankali tagyaɗa masa kai tana ƙara share sauran hawayen nata da suka zubo mata, sosai taji zuciyar ta tayi sanyi, sai dai tafi ƙaunar zama agidan sa fiye da wani waje
A bakin Gate ɗin gidan yatsaya yayi hon kafin aka buɗe masa yashiga, bayan yayi parcking fitowa sukayi, sai da yabuɗe Boot yaciro mata trolly ɗin ta kafin suka nufi cikin gidan, Mom na zaune a palow suka shigo da sallama, amsa musu tayi tana kallon su, sai kuma tasaki murmushi tana faɗin
"Bari in cinka baƙuwa ta, ƴata Nazeefa sannu da zuwa".
Ita Nazeefa kallon Mom kawai take yi cike da burgewa, sosai taga kamannin Khalil a fuskarta duk da skin ɗin su ba ɗaya bane, take kuma taji sauran farin cikinta ya dawo mata da ganin matar, muryan Khalil ne yakatse mata tunanin ta
"Mom ai dama kinsan da zuwan ta, ba wani cinka da kika". Ya faɗa maganar ne lokacin da ya'isa gare ta yazauna agefen ta, ƙara sakin murmushi Mom tayi tace
"To ai bansan ta a fuska ba dai, tunda rowanta kake ta min sai yanzu da kaga daman kawo ta, kinji ƴata ƙariso taho kizauna anan".
Kanta aƙasa tataho ahankali cike da kunyar matar tazauna agefen ƙafarta
"Ah kin zauna a ƙasa kuma? Taso kizauna anan mana, tashi maza".
Babu musu kuwa tatashi tazauna agefen ta, yayinda suka saka Mom ɗin a tsakiya, cikin sanyin murya tace
"Ina wuni Mama".
"Lafiya lau Nazeefa, ya jiki da fatan yanzu kinji sauƙi sosai ko?"
Gyaɗa kanta tayi sai kuma tace
"Alhmadulillah dasauƙi".
"Allah yasawaƙe, kinga yanzu kin dawo gidan mu, ina fata zakiji daɗin zama dani? Kizauna anan tamkar ƴata daga yau kin zama ƴar gidan nan kema".
Murmushi kawai Nazeefa tayi tana wasa da yatsunta
"Bari in saka anuna miki inda zaki zauna ko? Kisaki jikin ki kinji daga yanzu na zama mahaifiya gare ki".
Gyaɗa kanta tayi tana jindaɗi aranta, sosai matar tayi mata, gata mace me fara'a ko kaɗan ba ƙyama a ranta, nan Mom tayi kiran me aikinta, tana zuwa tace "tatafi da Nazeefa takai ta ɗakin da tasanya ta gyarawa, bayan sun tafi ne takalli Khalil da tun soma maganar nasu yaciro wayansa yana latsawa tace
"Kai masha Allah, yarinyan gata kyakykyawa, daga gani tana da hankali da nutsuwa, da alama dai zanji daɗin zama da ita, har naji tashiga raina sosai wlh tamkar ƴata ta cikina".
Ɗan ɗago kan sa yayi yakalle ta, sai kuma yamaida idanun sa kan wayan yaɗan latsa ta kaɗan yasaka cikin aljihun gaban rigan sa yace
"Ni zan tafi Mom, ba zama zanyi ba ina da wani aiki kinsan gobe ne tafiyana, ina son inje wani waje ne". Yaƙarike maganar yana miƙewa tsaye
Mom tace "to shikenan, amma dai zaka dawo ko zuwa anjima ne don muyi hira, bana son katafi bamu sake haɗuwa ba kaji ko?"
Murmushi yasaki me kyau da burgewa, yaduƙo gaban ta yasakar mata kiss agoshi yaɗago yana kallon ta yace
"Mom ai dole ne nadawo muyi sallama, idan ma ban sami dawowa yau ba da safe zan dawo kinji".
Itama murmushi tayi tace
Ok Autana, kasan yanzu ma drever yatafi ɗauko Dad ɗin ku a airport".
Ɗan waro idanu yayi yace
"Dagaske Mom?"
Hararan sa tayi tana jan kumatun sa tace
"Da ƙarya".
Dariya yayi yace
"Sorry Mom, bari in zauna to in jira sa".
"A'a tashi katafi, kai da baka da lokaci, katafi zuwa anjiman in kadawo sai kazo ko kuma goben kamar yanda kace".
"Ok Mom ni na tafi, ki miƙa masa gaisuwa ta kafin nadawo, kice masa kuma ya'ajiye min tsarabata da kyau zanzo in amsa da kaina, kar yasoma yaba Bro".
Dariya sukayi gaba ɗayan su, sai da yasake mata kiss a goshi kafin yafice yana faɗin
"Mom byeee".
.
******* ******* ****
Ƙarfe 05:11pm. Halwa ce zaune bakin ƙofa tana yankan ƙunba wani yaro yashigo gidan yace
"Wai ance Halwa tazo?"
Ɗago kai tayi takalli yaron sai tamayar da idanunta kan yankan ƙunban da take yi tace
"In ji wane?"
"Wani ne a mota".
Shiru tayi taci gaba da abinda take yi, yaron kuma yatsaya yana kallon ta, daga cikin ɗaki Mama tace
"Wai inace dake akeyi Halwa?"
"Mama ƙyale shi yatafi, kai kaje kace bata nan". Tafaɗi hakan lokacin da tasake ɗago kanta takalli yaron
Har ya juya zai tafi Mama tace
"Kai yaron nan yimaza kaje kace gata nan zuwa".
"To". Yaron yafaɗa yana rugawa waje da gudu
"Kitashi kiwuce kitafi da Allah bansan wulaƙanci".
Zumɓuro baki tayi kamar Maman tana ganin ta tamiƙe tashige ɗaki sai magana take yi ƙasa-ƙasa, Mama kamar taji me take cewa tace
"Ke kenan kullum koran samari, inace dai dole sai an ɗaura miki aure da Nuran shine kin zama mallakin shi? Kaji min shashashan yarinya haka ake yi".
Halwa da tafito daga ɗaki riƙe da gyale a hannu tace
"To Mama meye amfanin fitan nawa tunda inada wanda nake so?"
"Kinci gidan ku, ai babu yanda Allah baya sanja ƙuduran sa, kuma fitan ki ai ba zai hana kisami wanda kikeso ba, Ni wulaƙanci ne bana so wlh, in kin fita sai kice mishi kar yasake dawowa ba shikenan ba?".
Yafa gyalen tayi kan doguwar rigan ta na atamfa me ruwan toka da akai mishi sirki da ja da milk, slippers tasanya tafice batare da tabi takan Mama dake ta surutu ba.
[9/3/2020, 7:51 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 12*
Tana fitowa suka haɗa idanu da Yazeed da yake jingine jikin motan sa, tun sanda tafito yasoma murmushi har ta ƙari so wajen sa da sallama a bakin ta, amsa mata yayi still yana murmushi yace
"Barka da fitowa gimbiyar Mata kyakykyawar yarinya".
Murmushi tayi tace "fatan kazo lafiya?"
Yace "tun sanda dai muka haɗu dake ban sake jin lafiya ajikina ba, har kuwa fitowar da nayi daga gida nazo gare ki, but yanzu da nagan ki agabana sai naji kamar an kwaso duk lafiyan mutanen duniya ne an ɗaura min ni kaɗai, kinga kuwa yanzu zan iya ce miki lafiya ƙalau kenan".
Murmusawa tayi tana kallon shi tace
"Na kula dai kai ɗin nan kana da son wasa da yawa".
Shima murmushin yayi yace
"Gaskiya ne ƴan mata, to fatan kina lafiya kema? Ya su Mama da kowa da kowa? Kinga ban zo ba sai yau ko? Wlh kwana biyun nan aiki ne yayi min yawa, amma baki ji yanda na azabtu ba da rashin ki, ji nake kamar na shekara ɗari tare dake, sosai nashiga damuwa Burina kawai nazo nasake tozali da kyakykyawar fuskar nan taki".
Ita dai batace komi ba sai murmushi da take yi
"Ƴan mata da fatan dai za'a bani matsuguni acikin zuciyar ki, wlh sosai nakamu da ƙaunar ki, ina fata dai babu wanda yariga ni?"
Halwa tace "ai tun farko kamar in ban manta ba sai da nafaɗa maka ni ɗin mallakin wani ne, sai dai in baka haƙuri Malam Yazeed domin ma fitowan nan da nayi nazo ne nasanar maka an riga da anyi min miji".
Cikin fuskar damuwa yace
"Dan Allah wai dagaske kike yi?"
"Wlh dagske nake maka, ina da mijin aure kuma nan ba da daɗewa ba za'a sanya mana ranan aure ni dashi".
Cike da rashin jin daɗi Yazeed yace
"Yanzu shikenan wani ya rigani? Shikenan kina nufin zan rasa ki? Wlh Halwa sosai na kamu da ƙaunar ki a lokaci guda, yanzu kuma bansan ya zanyi in cire son ki cikin zuciyata ba".
Cike da tausayin sa saboda sosai tayarda dashi kuma ta ga tsantsan gaskiyar sa a fuskar sa tace
"Kayi haƙuri a sannu zaka manta dani ai, dama baka daɗe da sani na ba, don haka insha Allahu nan ba da jimawa ba zaka neme ni karasa ko tuna ni bazaka sake yi ba".
Ɗan murmushin gefen baki yasaki yace
"Kayya a naki fahimtar kenan Halwa, wlh bakisan yanda nake jin ki cikin zuciyata bane zai yi wuya nacire ki sabida ƙaunar da nake miki ya wuce tunanin ki, ni kinga ban iya saka abu cikin rai ba, kuma zan faɗamiki gaskiya ta kece macen da nafara so nafara kulawa a matsayin wacce nake ƙauna, taya kike tunanin lokaci ɗaya kuma zan inya manta ki?"
Girgiza kan shi yayi sannan yace
"Nagode sosai da faɗamin gaskiya da kikayi, Nagode da baki bar ni nasha wahala ba kinji?"
Gyaɗa masa kai kawai tayi
"To yanzu sai yaushe kuma? Ko bazamu sake haɗuwa ba? Yakamata muyi zumunci don Allah kibani numbanki".
Bata musa ba tace "ok babu damuwa".
Takaranto mishi numaban kafin tace
"Ni zan shiga gida, sai wani lokacin kuma".
Yace "to Nagode sai kin ji ni a wayan kenan, kigaida su Mama".
Kanta kawai tagyaɗa masa tajuya zata tafi, kawai tayi tuntuɓe da dutse hakan yasaka tayi taga-taga zata faɗi shi kuma yayi saurin taro ta, dai-dai lokacin da Nura yashanyo kwana yagansu ahaka Yazeed ya riƙo ta, kuma sun ƙame ahaka suna kallon juna, wani irin baƙin ciki ne yatokari zuciyar shi, take yaji kishi ya kama shi, tsayawa kawai yayi yana kallon su har sanda yasake ta suka yi magana ita kuma tashige ciki, take yaji zuciyar shi tana faɗin
"Daman yaudaran ka take yi abinda take aikatawa kenan, yau Allah ya toni asirin ta".
Take kuma yatuna da abinda yafaru jiya, nan yaharhaɗa abubuwan nan da nan yaji zuciyar shi na tafarfasa, aransa yace
"Tabbas dole nayi tunani akan maganar ka, wannan dama ce tasame ni".
Daga haka yasoma takowa yanufi gidan nasu, yana shiga suka haɗa idanu da Halwa dake tsaye bakin ƙofa tana magana da Mama da har yanzu take cikin ɗaki, murmushi tasakar mishi tace
"Yaya har ka dawo?"
Ɗan dai-dai ta fuskar sa yayi shima yasakar mata murmushin yanufo ta yana faɗin
"Kinga na dawo da wuri ko?"
"A'a Yaya, amma dai Allah yasa an dace?"
Mama da tafito daga ɗaki itama tace
"Da fatan dai an sami abinda akaje nema?"
Shiru yayi na ɗan wani lokaci, yayinda duk kan su suka zuba mishi idanu suna jiran amsan shi, sai kuma yasaki murmushi yace
"Yau dai an dace, na sami aiki insha Allah komi ya wuce".
"Alhamdulillah".
Atare suka faɗa hakan, Mama har da shafa hannu saman fuskarta, yayinda Halwa tasaki fara'a tana me cike da farin ciki da jindaɗi
Sallaman Baba yakatse Mama dake faɗin
"Masha Allah. Allah Ubangiji yasanya alkhairi".
Amsa mishi sallaman suka yi, yaƙariso yana kallon su yace
"Ya naga kunyi cirko-cirko daku, wani abun ya faru ne?"
"Malam ɗan ka yau yasamu aikin dai da yadaɗe yana shan wahala, yau an dace".
Fara'a Baba yasaki yace
"Ah masha Allah, da kyau Allah yatabbatar da alkhairi".
"Ameen duk kan su suka amsa, kafin Mama tace
"Bari in kawo maka tabarma Malam".
Ɗaki tashige taɗauko tashimfiɗa masa yazauna, itama tazauna gefen shi yayinda Halwa tazauna kan dokin ƙofa tana cire gyalen jikinta tajefa ɗaki, Yaya Nura ma zama yayi a saman kujera ƴar zuƙune dake wurin
Baba yace "ina tayaka murna, yau dai gashi ranan da muke jira tazo, to Allah yataimaka yasa kafara a Sa'a".
Gaba ɗaya suka amsa da "ameen" Baba yaci gaba da cewa
"To yanzu fa an sami abinda ake nema sai kuma aure kenan?".
Duƙar da kai Nura yayi, ita kuma Halwa wani farin ciki ne yasake kama ta jin maganar Baban
Mama murmusawa tayi tace "gaskiya ne Malam tunda babu abinda za'a jira".
Baba yace "to insha Allahu nan ba da daɗewa ba za'a tsai da ranan auren, kuma ba wani daɗewa za'ayi ba tunda dama kana aikin ka, mun dai fi so ne kakama na gwamnatin hakan zai fi, tunda gashi an samu shikenan magana ta ƙare zuwa gobe insha Allahu ko jibi za'a tsai da ranan".
Sosa kai Nura yayi yamiƙe yana faɗin
"Bari inje wajen abokina".
Dariya Mama tayi tace" ko dai kunya ne zai kora ka?"
Dariya shima yayi yace
"A'a Mama akwai dai abinda zanyi can ne, ni na tafi". Yafaɗi hakan yana ficewa dasauri
"Ɗan nema za ma kadawo ne, ke kuma me kike jira, ko ke kunyan bata kore ki bane?" Mama tafaɗi hakan tana mayar da idanunta kan Halwa
Itama tashi tayi da gudu tashige ɗaki tana dariya
Baba yace "ahh ya haka kibar ta mana tazauna, kunyan wa zataji bayan mu ne iyayen ta?"
Dariya Mama tayi tace "bari dai in kawo maka ruwa kashare waɗannan yaran duk gulma ne irin nasu".
Koda takawo mishi ruwan hira sukaci gaba da yi duk akan maganar samun aikin Nura, da kuma saka ranan su.
.
.
_shin wani abu ne yafaru jiya da har Nura yatuna?_
_Wanene yafaɗa masa maganar da har yace zai yi tunani akai?_
_wani ma magana ce?_
_JIKAR LAWALI CE_ 😉
[9/3/2020, 10:48 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 13*
*WASHE GARI*
ƙarfe 02:45pm. Drever'n Brr. Ibrahim Khalil yatafi kai shi airport, suna isa ba ɓata lokaci jirgin su yaɗaga dasu zuwa ƙasan Egypt.
_Sai muce Allah yaba da sa'a BARRISTER_🤒
....... ....... ........ .....
Kuka take yi sosai kamar ranta zai fita, tun sanda yafice gidan tazauna anan palow take ta rizgan kuka, sosai take cikin damuwa abubuwan duk sun haɗe mata, har yau takasa samun mafita, ta kasa samun nasara akan abinda aka saka ta, gashi yanzu mutanen nan sun sako ta gaba, sosai suke mata barazana, gefe ɗaya kuma zuciyarta ta azalzale ta da ƙaunar mutumin da besan tana yi ba, haka kawai take jin baƙin cikin tafiyan nan nasa, shikenan bazata sake ganin sa ba sai sanda yadawo? kuma batasan ranan dawowarsa ba, sai kuma tasake fashewa da kuka tuno mahaifiyar ta da tayi, yanzu da waɗannan mugayen basu ɗauke taba da tuni takoma gida, acan zata zauna har yadawo, "take tatuna sanda yakira ta yana zaune a palow tazo tazuƙuna gaban sa, sai da yagama latsa wayan sa kafin yaɗago kai yakalle ta yace
"Gobe zan yi tafiya, zaki iya komawa gida har sanda zan dawo, kiriƙe wannan ko zaki buƙaci wani abun".
Yamiƙo mata wasu maƙudan kuɗi, ahankali tasaka hannu ta'amsa tana jin zuciyarta babu daɗi, godiya tayi masa, sannan yabata umarnin "tafiya"
Shiru tayi tana ajiyan zuciya, rufe idanuwanta tayi tana sauraron bugun zuciyarta
"Meyasaka ban faɗamasa halin da nake ciki ba da yatambaye ni zuwa gida? Wataƙil yataimake ni, ya zanyi da waɗannan mutanen".
Take tasake tuno wayan da sukayi yanzu fitan shi, mutumin da yake kiran ta, shine dai yasake kiran ta yana tambayan ta, "ance zai yi tafiya, ko tasan ina zashi?"
Runtse idanunta tayi wasu hawaye na sulmiyo mata tuna amsan da tabashi
"A'a bansani ba, bansan ma zai yi tafiya ba".
Mutumin be ce mata komi ba sai yakashe wayan, da alamun kamar wani abun ne yataso shiyasaka yakatse kiran batare da sun gama magana ba, sake runtse idanun ta tayi zuciyarta na ci gaba da bugawa, tasani dole zai sake kira, amma batasan me zai biyo baya ba idan har sukasan ya tafi?
"Wataƙil ma su zo da kansu suyi binciken abinda suke nema".
Tafaɗi hakan afili tana buɗe idanuwanta, ɗaura kan ta saman kujera tayi tarufe idanunta tana ci gaba da tunani kamar yanda yazame mata jiki yanzu.
.
****** ****** *****
"My dear tashi muje kiraka ni".
"Ina yaya?" Tatambaye shi tana kallon shi
"Ke dai kitashi kiraka ni, zan amso sabon ɗinki na ne, kuma daga nan sai mu yawata kinsan mun daɗe bamu fita ba".
Washe baki tayi tace
"hakane Yaya, bari to in sauya kayan jikina".
"Ok" yace da ita yana zaro wayan sa a aljihu yasoma dannawa
Ita kuma tashige ɗakinta dasauri, tasoma sauya kayan jikinta, wata black and peach colour material me taushi taɗauko daga cikin kayan ta, riga da sket ne sunyi kyau sosai tasaka ajikinta, hakan yasaka kyawun kayan suka sake fitowa sosai sabida yanda yahaɗe da kyan ta, sai da tashafa powder tazizara lipstick a baki sannan tasaka hijabin ta sky maroon da iya kacin sa gwiwa, babu ɗankwali akan ta sai gashinta da tatufke a can ƙasan ƙeyan ta, kasancewar hijabin me hula ne don haka ba'a ganin gashin kanta, flate shoes tasaka kalan baƙi da kwalliyan tuntu asaman me ruwan zamba, fitowa tayi tana faɗin
"Yaya na fito, muje to".
Ɗago kan sa yayi yana ƙare mata kallo, sai yasaki murmushi yace
"Baby kinyi kyau, kinga yanda yarintan ki yasake fitowa?"
Fari tayi da idanun ta tace
"Dagske yayana?"
"Dagaske mana Dear".
"Ina kuma zakuje haka?" Cewar Mama da tafito daga ɗaki tana kallon su
"Mama raka ni zatayi, zan amso ɗinkina".
"To kar dai kudaɗe, nima fita zanyi zuwa sunan Asabe, saura kuma kuje kuzauna inta jiran ki baki dawo ba".
Nura yace "Mama bazamu daɗe ba ai, sai mun dawo"
Gaba yayi itama Halwa tabi bayan shi tana faɗin
"Mama sai mun dawo".
"Adawo lafiya".
Tafiya suke yi a ƙasa suna yi suna hiran su cike da nishaɗi, kallon ta Nura yayi yace
"Ko dai mutaka a ƙasan ne? Naga kamar tafiyan na miki daɗi?"
Ɗan waro idanunta masu kyau tayi tace
"A'a Yaya tare mana dai napep, akwai rana fa a gari".
"Ok my dear, dama bana son Kisha wahala, gwara dai mutari napep duk da nan kusa ne".
Lokacin sun iso bakin titi wani me keke napep dake fake ɗan nesa dasu, yatuƙo yaƙariso wajen su yana faɗin
"Tafiya ne?"
Nura ɗan kallon sa yayi suka haɗa ido yace
"Eh bakin kasuwa zaka kai mu?"
"Ok kushiga kuɗin ku saba'in ne".
"Ai mun sani". Cewar Halwa tana turo baki gaba
Murmushi Nura yayi yace
"Ke dai da neman magana kike, menene laifin sa anan don yafaɗa miki kuɗin sa?"
"Ai Yaya babu wanda be san kuɗin haka bane, tunda ba yau suka saba kai mu ba, wannan fa doka ce da suka saka kuma kowa yasan da hakan ba sai sun sake maimaita mana ba". Ta faɗi maganar ne tana shigewa cikin napep ɗin
Me napep ɗin yace
"Baiwar Allah kiyi haƙuri ni baƙo ne ai, nayi tunanin ko baku sani bane".
Taɓe baki tayi takalli Nura da shima yashigo yazauna a gefen ta tace
"Yaya daga nan mubiya cikin kasuwan mana zan siya kayan kwalliya, nawa sun ƙare".
"An gama ranki yadaɗe, komi ma kikeso sai kisiya tunda Allah ya kawo mu ko?"
Murmushi tasaki cikin jindaɗi tace
"Eh Yayana, Nagode sosai, ina jindaɗin yanda kake kula dani".
"Babu komi ai, ke ɗin ƙanwata ce kuma Matata insha Allahu".
Dariya tayi tana jin farin ciki a zuciyarta, daga nan hira suka soma yi, yayinda me napep tuni yasoma tafiya dama, gab da zasu kawo wajen da za'a sauke su napep ɗin tatsaya
"Oh shitt.. dan Allah kuyi haƙuri bari in duba naga me yafaru".
Nura yace "ai babu komi, bari musauka anan kawai tunda babu nis..".
Be gama faɗin abinda yakeson faɗa ba yaji ya shaƙi wani abu cikin hancin sa, ko sceonds biyar basu sake ba gaba ɗaya suka ɓingire cikin motan daga shi har Halwa har suna gwara kai, murmushi me napep ɗin yasaki yajuya yagyara zaman sa yatada keke napep ɗin yaci gaba da tafiya.
.
_Tofa 🤔 me kuke tunanin zai faru?_
0 comments:
Post a Comment