"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. ina ne nan?". Ta faɗi hakan ne a fili tana jin zuciyarta na tsinkewa, don tasadakar gidan cin kai ne aka kawo su
"Gidana ne".
Taji maganar ya doki kunnin ta, dasauri tajuyo tana wurwurga idanu, nan kuwa idanun ta yasauka akan sa, yana zaune saman kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana sakin murmushi, daga shi sai farar singlate da gajeren wando me ruwan ƙwai da iyakacin sa gwiwa, gefen sa kuma da akwai mutum ɗaya dake tsaye yana gadinsa, wani irin bugawa zuciyarta tayi kamar zatayi tsalle tafaso cikin ƙirjinta, take wani irin tsoro yashige ta har batasan sanda tawaro idanun ta waje ba tana kallon shi, still yana murmushi yace
"Barka da zuwa turaka ta Amarya ta, yau dai gaki cikin gidana abinda nadaɗe ina fata da buri kenan".
Ahankali yatashi yanufo ta har zuwa gaban ta kafin yadakata yana ƙare mata kallo, sai kuma yasoma zagayeta yana tafa hannun sa, wanda duk taku ɗaya da yake yi tana ji ne kamar yana tafiya da bugun numfashin ta, sai da yagama zagaye ta sannan yazuƙuna agaban ta yana kallon cikin idanun ta da tatsayar akan sa ko motsin kirki takasa yi, sosai ganin shi yayi tsananin firgita ta har tana jin komi na jikinta ya dena aiki, murmushi yasaki yana faɗin
"Yau dai na baki mamaki ko? Baki zatan zaki iya zuwa hannun Haris cikin sauƙi ba?"
Sai kuma yasaki dariya yaci gaba
"Dama nace miki zan kafa tarihi cikin rayuwan ki, zanyi miki abinda har kimutu bazaki taɓa mantawa dani ba, to ga ranan tazo, yau duk zan huce wahalan da kika bani, kin bani wahala sosai Babyna".
Yaƙarike maganar yana kai hannun sa saman fuskarta yashafo gefen face ɗinta, kafin yacire hannun dasauri yana zuba murmushi
"Ohh kince in dena taɓa ki ko?" Uhmmm saboda na taɓaki kika cire hannu kika wanka min mari ko? To yau kuma bari inga wani hukunci zaki min, kin san me?"
Yatambaye ta yana matso da fuskar sa kusa da nata, sai lokacin tasami daman motsa jikin ta, dasauri taja baya tana girgiza mishi kai, nan da nan hawaye suka cika idanun ta suka soma zubowa, cikin rawan murya tace
"Don Allah.. don Allah na roƙe ƙa kayafe min, wlh bazan sake ba dan Allah kayi haƙuri".
Dariya yakece dashi yana zama dirshan a ƙasa yace
"Da wuri haka? Taya kike tunanin mayunwacin zakin da yadaɗe yana farautan abincin da zai ci, yau ya samu sai kuma yasaki abincin yatafi?" Sam wannan ba me yiwuwa bane, yau sai nacika Burina akan ki Halwa, yau zan yi maganin ishin ruwan da nadaɗe ina fama dashi cikin raina, yau zan cire duk wata sha'awan ki dake damuna".
Riƙo hannun ta yayi yana son jawo ta jikinsa, tayi saurin ja baya tayunƙura tatashi aguje tanufi wajen Nura da har yanzu yana nan kwance, girgiza shi tasoma yi cikin kuka tana faɗin
"Yaya Nura dan Allah katashi, katashi kataimake ni dan Allah Yaya".
Dariya Haris yakwashe dashi, dai-dai lokacin da Nura yabuɗe idanu yana jin kukan Halwa yayi saurin zabura yana kallon ta, saurin shigewa jikinsa tayi tana faɗin
"Dan Allah yaya kataimake ni zai raba ni da mutuncina, dan Allah yaya karka bari yacin ma burin sa kataimake ni".
Tasake fashewa da kuka har da su majina, gaba ɗaya duk tagama tsorata, shima sake riƙo ta yayi yace
"Kiyi shiru Halwa babu abinda zasuyi miki kinji, idan har ina raye babu abinda zai same ki kidena kuka".
Muryan Haris ne yacika wurin
"Kai kuriƙe min shi da Allah".
Ai kuwa nan da nan mutanen nan gaba ɗaya sukayo kan su suka damƙo Nura suka rirriƙe shi, shi kuma Haris yafinciko Halwa dake ta faman rusa kuka kamar ranta zai fita, sai roƙon sa take yi tana faɗin
"Don Allah don girman Allah kaji tausayina karka raba ni da mutuncina, wayyo Allah don Allah kayi haƙuri kataimaki rayuwata wlh ni marainiya ce".
Dariya yake yi yana jan ta yanufi wani ɗaki da ita, Nura kuwa sai son ƙwacewa yake yi yana faɗin
"A'a dan Allah karkayi kaƙyale ta, dan Allah kasake ta".
Garam haka yaji ƙaran kulle ƙofa da Haris yayi, runtse idanuwan sa yayi yana jin wasu hawaye na kwaranya a idanun sa, tsananin tausayin ƙanwar sa ce yakama shi
"Meyasa?"
Yafaɗi hakan a fili yana sake runtse idanun sa da ƙarfi jin ihun ta dake shiga kunnin sa
...... ...... ....... ........ ....
Tana zaune saman gado ta ƙudundune jikinta cikin hijabin ta, ta haɗa kai da gwiwa tana wani irin kuka na fitan hankali, kuka take yi sosai tana sake matse kanta da ƙafafunta waje ɗaya, ji take yi ina ma Allah yaɗauki ran ta a yau ɗin, ko kaɗan bata fatan tasake minti ɗaya cikin duniyar nan
Buɗe ƙofan ɗakin akayi, Nura ne yashigo idanuwan sa ƙyarr akan ta, ahankali yasoma takowa zuwa wajen ta yana jin kukan ta na shiga masa har cikin ƙwaƙwalwa, sosai kukan nata ke taɓa masa zuciya, koda ya isa hannu yasaka yadafa kafaɗan ta, sai taɗago dasauri tana kallon sa da idanuwanta da suka gama rinewa sukayi jawur sai tsiyayan hawaye suke yi, dasauri tasaka hannu biyu tariƙo ƙafafunsa tatusa kanta ajikin sa tana sake fashewa da wani irin kuka me tsuma ran me sauraro, ahankali yaɗaura hannun sa saman kan ta zuciyarsa cike fal da tausayin ta, so yake yi yararrashe ta amma ko kaɗan yakasa buɗe baki, be san da wani kalma zai fara ba, ita kuwa sake tusa kanta take yi cikin kuka da ba'a jin muryan ta sosai tace
"Yaya.. Yaya ya cuce Ni, ya cuce ni Yaya ya gama da rayuwata, ya raba ni da martaba na na ɗiya mace, yaya ya gama dani wlh ya gama dani, wayyo Allana nashiga uku na lalace".
Kuka tasake kecewa dashi tana buga kanta saman ƙafafunsa, dasauri yariƙe ta yana tallabo fuskarta yace
"Ki dena kuka Halwa, kidena kuka dan Allah, kukan ki na taɓa min zuciyata, dan Allah kiyi shiru kitashi mutafi kinji".
Girgiza kan ta tasoma yi cikin kuka tace
"Yaya ina zani? Ina zani da wannan abun kunyan? Ina kake so naje yaya? Dan Allah yaya katafi kabar ni anan, katafi kabar ni zan kashe kaina ne, bani da sauran wani farin ciki cikin rayuwan nan, wlh Yaya mutuwa zanyi, zuciyata zata buga, dan Allah yaya kakashe ni nahuta.."
Saurin ɗaura hannun sa saman bakin ta yayi yana kallon ta yace
"Ki nutsu Halwa dan Allah, kinsan me kike faɗa kuwa? Ni Yayan ki ne kuma zan rufa miki asiri, babu wanda zai sani wlh har Mama, nayi miki alƙawari kuma zan aure ki, nasan abinda kike tunani kenan, Halwa babu wanda zai ji kitashi mutafi gida dan Allah".
Daƙyar yalallaɓa ta tamiƙe, yana riƙe da ita suka fito palow da babu kowa ciki, ɗaukan mata takalmanta yayi yace "tasanya" babu musu tasaka har lokacin hawaye take zubar wa, fitowa suka yi cikin gidan, wajajen babu wasu gidaje da yawa, don haka sai da sukayi tafiya sosai sannan suka kawo bakin titi, Halwa bata iya tafiya sai da taimakon Nura, gaba ɗaya ajikin sa take ya rungume ta ahaka suke tafiya, basu jima da tsayuwa ba suka sami napep suka hau, a ƙofar gida yasauke su suka fito suka shiga gidan, a cikin zaure Nura yadakata yana kallon ta yace
"Dan Allah kidena kukan nan karki sa Mama tafahimci wani abu daga gare ki, bansan me zance mata ba".
Gyaɗa kanta tayi tana saka hannu tasoma share hawayen ta, still kuma wasu na tsiyayowa, Nura yasoma shiga yaleƙa yaji shiru, sai yadawo yariƙo ta suka nufi ɗakinta, a saman katifan ta yazaunar da ita sannan yafita, sai da yataɓa ɗakin Mama yaji shi a kulle, ashe be kula bane labule tasaki takulle ɗakin, koda yatura yaga ƙofan ya buɗe, sai da yaleƙa ko ina yatabbatar babu ita sannan yadawo cikin ɗakin Halwa, tana nan kwance sai kuka take yi, ƙarisowa yayi kusa da ita yakira sunan ta, shiru tayi bata amsa ba
"Kitashi kigyara jikin ki Mama bata nan, Halwa karki sake Mama tafahimci akwai wata matsala atare dake kinji ni ko?"
Kuka tasake fashewa dashi tana ɗaura hannun ta saman fuskarta
"Wai don Allah kukan na menene? Inace duk dan ni kike yi kuma nace zan rufa miki asiri zan aure ki".
Buɗe idanunta tayi tana kallon shi, sai kuma tarufe idanun taci gaba da kukan ta, sam bazai gane me take ji cikin zuciyarta ba, amma tasan da cewa komi nata ya ƙare, Haris ya gama cutar ta har abada, bazata taɓa yafe mishi ba".
Miƙewa yayi yana kallon ta yace
"Ni zan fita, kidena kukan nan haka dan Allah, ki saka ma zuciyar ki salama Allah zai saka miki, kinsan baza mu iya faɗa dashi ba ya riga da yafi ƙarfin mu, kibar sa da Allah kinji My Halwa?"
Zuciyarta ne tayi mata sanyi, shiru tayi tana sake lafewa saman katifan sai ajiyan zuciya take yi
"Yauwa my dear dan Allah karki bari Mama tafahimci kinyi kuka bare tasan wani abu na damunki, yanzu bari in fita yanzu zan dawo kinji?"
Gyaɗa masa kai kawai tayi, shi kuma yafice, ahankali taci gaba da kukan ta, tasan da cewa sosai tayi dacen Yaya, wanene zai iya auren ta da wannan tabon cikin rayuwanta? Amma gashi Yayan ta mafi soyuwa cikin ran ta ya amince zai aure ta bayan yasan abun da yasame ta, tabbas yayan ta ya cika masoyin gaskiya, da ko wani namiji zai fahimci cewa ko wace Yarinya da hakan yasame ta ƙaddara ce Allah yarubuto mata, su gane cewa auren ta babban jihadi ne kuma sadaukarwa ne, da mata da yawa da suke kukan baƙin ciki sun dena.
Ji tayi ƙaunar yayan nata na sake ninkuwa cikin ranta
"Allah Sarki Yayana, tabbas kai me ƙaunata ne da bansan ya zanyi ba, wani miji zan aura da zai iya zama dani ahaka? Nagode Yayana ina matuƙar ƙaunar ka, Nagode Nagode sosai da karufa min asiri".
Tafaɗa maganar afili tana sakin murmushi kamar yayan nata na ganin ta, sai kuma can tafashe da kuka tana cewa
"Allah ya isana mugu azzalumi, bazan taɓa yafe maka ba, insha Allah sai anyi ma yaranka kaima abun da kayi min, mugu azzalumi kawai".
"Ke da wanene haka kike ta ja mishi Allah ya isa?"
.
_Toooo 🤔 me zai faru?_
_kuna ganin asirin ta zai rufu kuwa?._
[9/6/2020, 7:14 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 15*
"Ke da wanene haka kike ta ja mishi Allah ya isa?" Cewar Mama tana bankaɗo labulen
Dasauri taɗaura hannu a saman fuskarta, cikin ruɗewa tace
"Ahm Ma.. Babu kowa".
"Ya zakice min babu kowa bayan naji da kunnina kina mishi Allah ya'isa, tukunna ma me yayi miki da za'ayi ma yaran shi?"
"Mama wani ne fa yakusa yabige ni, shine sai ƙunduma min zagi yake yi, shine fa abun yanzu yake damuna".
Guntun tsaki Mama taja tana sakin labulen tace
"Shine ke kuma tunda baki da haƙuri zakizo kina taja mishi Allah ya isa? Allah yashirya ki Halwa, nima da naji ku shiru ne nafice abuna".
Ɗaki Maman tashige tana ci gaba da surutun ta, yayinda Halwa kuma gyara kwanciyan ta tayi tana sauke ajiyan zuciya cike da fargaba, rufe idanuwanta tayi tana jin wani kukan na sake zuwan mata tuna abun da yafaru da ita yau, wani irin ƙunci da baƙin ciki ne suka tokare mata wuya, take tafashe da kuka tana toshe bakin ta
"Shikenan yau an raba ta da abu mafi daraja ajikinta, wai yau ita ce wannan ƙaddara yasame ta, abinda ko a mafarki bata taɓa tunanin wannan ɓakin ranan zai zo mata ba, ya zatayi da rayuwan ta? Ji take yi kamar takashe kanta duk sanda tatuna yau wani namiji yasanta a ɗiya mace batare da aure ba
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Abinda take ta maimaita wa kenan har tasoma jin zuciyarta na mata sanyi.
.
**** **** **** ****
*WASHE GARI*
*EGYPT*
Zaune yake saman Three sitter ya harɗe ƙafafunsa yana danna Lapton ɗin sa, takardu ne birjik agaban sa sai faman aiki yake yi, yana sanye cikin fararen kaya masu taushi sosai, wandon Three qweater ne sai Rigan me kamar singlate
Tun jiya da yasauka a ƙasan yake faman aiki babu ƙauƙautawa, bincike sosai yake akan mutumin da yazo don shi amma har yanzu yagaza samun koda bayani ɗaya akan sa, sosai yake cikin damuwa ko lokacin kansa baya dashi, yanzun ma aikin yake yi but tunanin sa na wani wajen daban, wayan sa da tasoma ringing yayi saurin ɗauka domin dama abinda yake jira kenan
"Hellow Poker.."
"Ok.. ok turo min da address ɗin wajen".
Cire wayan yayi a kunne yariƙe a hannu yana kallon screan ɗin wayan, 1mint sai yaji Message ya shigo, dasauri yabuɗe yaduba sannan yatashi, cikin sauri yasauya kayan sa cikin farar riga me gajeren hannu da blue jeans, sai yaɗaura jaket saman rigan baƙi ne me belt a wajen cikin sa, jaket ɗin me hula ne sai dai be sanya hulan ba iyakan yasaka Combat a ƙafan sa Black, yaɗau wayoyin sa yazuba a aljihu yafito yarufe ɗakin, kasancewar a Hotel ne ɗakin sa yana hawa na uku ne, cikin sauri_sauri yake taka step ɗin har yasauko ƙasa, yana fita yatari taksi yashige suka tafi, a wani haɗaɗɗen club aka sauke sa yafito yabiya me taksi ɗin kuɗin sa kana yamatsa gefe kaɗan yana ƙare ma wajen kallo, tsawon mintuna 5 yaɗauka awajen kafin yajanyo hulan Jaket ɗin ya'aza akan shi yasoma takawa yashige wurin, sosai ciki yake da duhu, mutane ne birjik ciki kowa na sha'anin gaban sa, ba abinda ke tashi aciki sai daddaɗan cool music da aka sanya wasu sai cashewa suke yi, yana shigowa kallon wajen kawai yake yi har ya'isa wani hill chair yazauna yana kallon mutane, tsawon mintoci yana zaune a wajen yana nazarin inda zai ga mutumin da yazo nema, sai kawai yayanke shawaran nufan wasu matasa maza da mata dake zaune gefe can saman wasu haɗaɗɗun kujeru sai kurɓa alcohol suke yi, wata matashiyar budurwa ce taƙariso kusa dashi hannun ta riƙe da cup, kallo ɗaya zaka yi mata kagane irin waɗannan gogaggun karuwan nan ne, skin ɗin ta baƙi ne but ko kaɗan batayi yanayi da ƴan Nigeria ba coz yanayin shiganta da wayewan ta
"Hi". Tace dashi lokacin da ta'isa gaban shi
Kallon ta yayi sai yaɗauke kan sa dasauri batare da ya amsa mata ba, murmushi tayi tace
"Kana son wani abu ne? Naga tun ɗazu kazo kazauna anan kamar kana neman wani ko?"
Gyaɗa mata kai kawai yayi batare da yasake kallon ta ba
"Ok ko zan iya taimaka maka?" Tafaɗi maganar tana kurɓan Juice ɗin dake hannun ta
Shiru yayi kamar bazai ce komi ba sai kuma yace
"Ina son ganin Mr. Jay pitter ne, me wajen nan, ance min in nazo nan zan same shi".
Murmushi tayi tana gyara gashinta takalle shi dakyau, sai kuma tagirgiza kan ta tana jawo kujera tazauna taci gaba da shan Juice ɗin ta, shiru ne yagibta a tsakanin su har Khalil yana shirin tashi sai yaji muryan ta ya doki kunnin sa
"Meyasaka kake neman sa?"
Ɗan kallon ta yayi sai yakau da kai be ce komi ba, ƙure shi da ido tayi tana wani irin murmushi tace
"Daga Nigeria kake ko? Nima acan nake ai".
Taƙarike maganar tana kau da kan ta taci gaba da sipping juice ɗin ta kamar ba itace tayi maganar ba, shi kam kallon ta yake kamar me neman wani abu jikinta, mamaki ne kwance acikin ran sa domin ko kaɗan batayi kama da zubin ƴan Nigeria ba, musamman ma da yaga tana mishi turancin kamar tana wani yare, sam ba wani fahimta yake ba, murmushi tasake yi wannan karon da Hausa tayi maganar tace
"Kana mamaki ko? Uhmmm kadena mamaki sabida ni da kake ganina cikakkiyar Bahaushiya ce ƴar Nigeria, Nigrian ma a Kano, sunana Fadila kuma musulma ce ni, but anan ana kira na da baby Dil".
Ɗago kai yayi sosai yana kallon ta da tsantsan mamaki a face ɗin sa wannan karon, but yaƙi furta komi
"Kafaɗa min meyasaka kakeson ganin Mr. Jay pitter?"
"Meyasa kikeson nafaɗamiki?" Yayi maganar yana kau da kai kanta
"Sabida zan taimaka maka, bazaka taɓa samun shi anan ba, koda zaka kwana kana sintiri ne, wahala kawai zakayi, but Ni kuma zan iya taimaka maka in kaika inda yake".
Khalil yace "Please kitaimaka min ina son ganin shine sabida wani bincike da nakeson yi".
Dariya tasaki tana kallon shi cike da sha'awa tace
"Sau da yawa ina ganin irinka suna zuwa nan don neman sa, kuma tun sanda naganka nagane kai ɗan Nigeria ne kuma nasan abinda yakawo ka har kake neman sa".
Da mamaki Khalil yakalle ta yace
"Taya kika sani".
Sai da tashanye sauran Juice ɗin ta'ajiye cup ɗin sannan takalle shi tace
"Idan har kana son taimakona to mubar nan wajen, Ni kuma zan faɗamaka duk abinda kakeso kasani, har da wanda ma bakaso".
Shiru yayi yana nazari kafin yace
"Ok muje to".
Tashi tayi takalle sa tana kashe mishi idanu, tamatso kusa dashi kaɗan ahankali tace
"Kabari in nafita sai kabiyo bayana".
Hakan ko akayi, sai da tafice kafin yabiyo bayan ta, daga can nesa yahango ta tsaye tana ware hannayen ta tana yarfe su, wajen ta yanufa yana kallon ta, bata bari yayi magana ba tace
"Kasamar mana taksi mubar nan".
Sai kuma tasakar masa murmushi tace
"Ko muje musaukin ka".
Wani irin kallo yayi mata, sai tawaro idanu still tana murmusawa tace
"nan zai fi sirri, coz za'a iya samun matsala ne".
Jimm yayi kana yace
"Ok"
Daga nan yatare musu taksi suka shiga suka tafi.
[9/10/2020, 11:42 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 16*
Lokacin da suka isa cikin ɗakin sa na Hotel ɗin Baby Dil akan sofa tayi wa kan ta matsuguni, taɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tajingina bayan ta da kujeran tana kallon shi, shi kuma Direct cikin Toilet yashige, be jima ba yafito yanemi wuri kan kujera yazauna kana yace da ita
"Ina jinki, Please ina son nasan komi ga mutumin nan".
Ɗan sakin murmushi tayi still tana kallon shi tace
"Ni kuma zan sanar da kai komi insha Allahu, katambaye ni duk abinda kakeso".
Gyaɗa mata kai yayi kafin yagyara zaman sa yace
"Akwai wani Alhaji Mubarak da muke Shari'a dashi acan Nigeria, kuma tabbas an tabbatar min da Mr. Jay pitter abokin harƙallan shi ne, don haka nazo bincike kuma ina son nahaɗu dashi".
Baby Dil tace "tabbas da ka isa wajen shi babu abinda zaka samu, domin Alhaji Mubarak na hannun daman sa ne, kaga kuwa babu abinda zaka samu a wurin sa illa ma kasake jagula abin, kamar yanda nace maka xan sanar da kai komi sabida nasan sirrin su ne, a baya mutane irinka sun zo kamar kai don bincike, wasu ƴan sanda ne wasu kuma lauyoyi ne, but kai bansan menene aikin ka ba?"
"BARRISTER". Yafaɗa ataƙaice
"Ok Amma tun sanda naganka naji zuciyata ta kwanta da kai sosai shiyasa nazo wajen ka bcoz nima ina buƙatar taimakon ka".
Shiru tayi tana sauke numfashi, sai kuma tasauke ƙafan ta tahaɗe hannayen ta waje ɗaya tana kallon shi, sannan taci gaba da faɗin
"Zan soma da baka tarihina duk da baka tambaye ni ba but nasan duk abinda kake nema yana da alaƙa da abinda akai min, shekaru 7 kenan da zuwata wannan ƙasan, ko ince aka sai dani a wannan ƙasan, zaka yi mamaki idan nace maka ta sanadiyan maƙocin mu nazo wannan ƙasa, mun kasance mu talakawa ne don haka maƙocin mu yake taimaka mana kasancewar sa me kuɗi, haka kawai watarana yace inxo zai sama mana aiki awani gida, dama abinda muke nema kenan musami aikin da zamu dogara dashi ni da iyayena, kwana biyu da soma zuwana, uban gidan mu yakai ni wani gida, ni dai ban fahimci ko ina ne ba amma akawai ƴan mata irina da yawa don mun kai mu sha biyu, muna ji muna gani akai mana allura wanda bamu fahimci na menene ba, tun daga lokacin hankalin mu yagushe, ashe makocin mu ne yasiyar dani ga mutumin da yasamar min aiki gidan sa, shima kuma yasiyar dani ga wani uban gidan sa".
Shiru tayi tatsira ma waje ɗaya idanu taci gaba da faɗin
"Wannan alluran da akai mana yagusar mana da hankali, anyi haka ne don su cin ma manifan su akan mu, suna harƙallan sai da coken that's why suke samun ƴan mata sufarka cikin su azuba musu coken ɗin nan aciki, alluran da ake yi yana da ƙa'ida, yana ɗaukan iya awannin da zai kai mu ƙasan da za'a kai mu ne, don haka lokacin da akai mana hankalin mu gushewa yayi bamu sake sanin inda muke ba sai a wannan ƙasar, sun kawo mu nan an kuma mana aiki an cire mana coken ɗin, sai dai basu bar mu haka ba suka sai damu ga Mr. Jay pitter, mutum ne shi da yake safaran ƴan mata ƙasa-ƙasa wasu kuma yamai dasu karuwan sa don samun kuɗi dasu, acikin waɗanda muka taho tare gaba ɗaya yasiyar dasu a wasu ƙasashe sai ni da wata yabar mu a matsayin karuwan sa, tun sanda natsinci kaina a wannan ƙasa nake kuka ina roƙon su da sumai dani ƙasata, sai dai aikin gama yariga da yagama su mutane ne da basu tsoron Allah, daga farko da sukaga ina musu taurin kai har nayi yunƙurin guduwa haka sukai ta gana min azaba, but duk da haka ban sa ran wataran zan ƙi guduwa ba, sai dai duk wani hanya da yakasance zan bar ƙasar nan sun toshe ta, ataƙaice dai zan faɗa maka babu yanda za'a yi nabar ƙasan nan batare da sanin su ba, haka nahaƙura naci gaba da zama dasu nima har lokacin da nasaba, nima nadawo nagoge azahiri namanta da komawa ta gida, sai dai abaɗini abin na nan araina, aduk sanda natuna da iyayena sai nayi kukan baƙin ciki, ina tunanin awani hali suke na rashina, shiyasaka har yanzu ban fid da raina zan koma ba".
Muryan ta da yasoma rawa ne yasaka ta yin shiru, sai da tashare hawayen fuskarta kafin taci gaba
"Shi kuma Alhaji Mubarak tare suke harƙalla da Mr. Jay Pitter, yana kawo masa ƴan mata sosai, duk wani aikin da Mr. Jay yake yi tare suke yi dashi, nasan shi sosai domin yana yawan zuwa nan ɗin, kuma insha Allahu duk wani sirrin su zan iya nemo maka inhar kayi alƙawarin zaka mayar dani ƙasata, ina son nakoma gun iyayena, kataimake ni don Allah, sosai naji zuciyata ta aminta da kai". Taƙarike maganar tana fashewa da kuka
Brr. Khalil kallon ta kawai yake yi cike da tausayin ta, sosai tabashi tausayi kuma yana ji aran sa insha Allahu sai ya taimaka mata, dama wannan daman yake nema wanda zai kawo ƙarshen masu safaran mata, koda iyakan Alhaji Mubarak da mutanen sa yakawar tabbas yasan ba ƙaramin Jihadi yayi ba, ko ba komi za'a rage yawaitan mugaye irin su, ajiyan zuciya yasauke yana tuno Nazeefa
"Yanzu shikenan da itama nan za'a kawo ta? Yarinya ƙarama, kai amma waɗannan mutanen basu da imani, Allah kaɗai yasan iya adadin yaran da suka kawo waɗanda ma basu kai ta ba".
Numfashi yaɗan ja yana kallon ta yace
"Kiyi shiru Fadila, insha Allahu zan taimaka miki kibar wannan ƙasan, zaki koma ga iyayen ki in Allah ya yarda nayi miki alƙawari".
Kallon shi tayi da idanuwanta da sukai jazur tayi masa murmushi tace
"Nagode sosai".
"Babu godiya tsakani na dake, ke dai ki aiwatar da duk abinda zan saka ki".
Daga nan yasoma bata bayanai akan abinda yakamata tayi masa, sun daɗe suna tattaunawa kafin tatafi, shi kuma tashi yayi yashige toilet yayo wanka tare da ɗauro alwala yafito, shirya wa yayi cikin farar jallabiya da dogon wandon jeans yashimfiɗa sallaya yayi sallah, sannan yamiƙe yaɗau tellphone ɗin dake ɗakin yakira Receptionist yayi odan abinci, yana zama babu jimawa akayi nocking door ɗin yaje yabuɗe ya'amso yadawo yazauna yasoma ci, abincin yake ci sai dai hankalin sa baya wajen yana nazari, wayan sa dake saman gado tasoma ringing hakan yasaka yaɗan kalli wajen kafin yasauke ajiyan zuciya, yamiƙe yanufi inda wayan take yaɗauka, ganin Bro ɗin sa ne babu ɓata lokaci yayi peacking call ɗin yana zama
"Hello My Bro".
"Hi ɗan ƙanina ya kake?"
Ɓata fuska Khalil yayi yana shafa goshin sa yace
"Bro bana so".
Dariya Sameer yayi yace
"Sabida me um ɗan ƙanina?"
Shiru yayi yaƙi magana
Still dariya Sameer yasake yi yace
"I'm sorry dama tsokanan ka nake, ai yanzu kai big boy ne tunda kafara aje yara, kasan fa Hakima ta haihu".
"Dagaske Bro? Yaushe? Me tahaifa?" Yayi masa tambayoyin ajere yana miƙewa yakoma wajen abincin sa
"Yanzu babu daɗewa, ai nayi tunanin Mom tariga ni sanar maka, namiji tahaifa".
"A'a tun safe da mukai waya bamu sake ba, Allah yaraya shi Yaya, ina fata ni za'a yi wa takwara ko?"
Sameer yace "tabb kai awa?"
"Ni a Dadyn sa, Please Bro kasan munyi alƙawari dani da kai, duk wanda yahaihu cikin mu zamuyi ma junan mu takwara".
"A'a to ai bance maka na fari ba, ni Dad zan ma takwara sai dai kabari tasake haihuwa lokacin ma kayi naka auren, kaga sai su tashi tare ko?"
Ajiyan zuciya Khalil yayi yace
"Dama haka zakace ai, kafison Dad dani, shikenan sai kayi ta sakawa".
Dariya Sameer yasaki jin yanda Khalil ɗin yayi maganan cike da shagwaɓa, cikin dariyan yace
"Haba autan Mom Kar kayi fushi tunda nace zan saka, kuma kasan da cewa ni dama na wurin Dad ne, dole na fifita shi akan ka, amma fa ina son ka sosai fa, daga shi sai kai a zuciyata".
Murmushi Khalil yayi yace
"Uhmm naƙi daɗin bakin, ai dama Mom ta sanar dani kuma yanzu na yarda, yanzu ni dai kagaishe min da me jegon da kyau da kyau tare da My Son".
"Ok zasu ji, ya aikin naka? Dafatan komi yana tafiya normal?"
"Alhamdulillah Yaya, Ina samun duk abinda naje nema".
"To Allah yataimaka yabaka Sa'a".
"Ameen Bro, katura min photon Baby ta WhatsApp in ganshi".
Sameer yace "ok yanzu kuwa".
Daga nan sallama suka yi, yaci gaba da cin abincin sa yana latsa wayan sa.
[9/12/2020, 1:32 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 17*
*WASHE GARI*
*NIGERIA*
Da sallaman ta tashigo gidan, Mama dake zaune tana gyaran lagwani ta'amsa mata tare da faɗin
"A'a maraba da Zainaba"
"Mama ina wuni?"
"Lafiya lau, ya Umman taki?"
"Tana lafiya, tace in gaishe ki".
"Ina amsawa, ya wajen su Zaituna, ina fata kina leƙata?".
Murmushi Zainab tayi tace
"Eh Mama ina zuwa sosai".
"To madallah haka akeso, kishiga ƙawar taki na ciki ai, bata jindaɗi ne".
"Eyya Allah yasawaƙe, ai bani da labari".
Mama tace "ameen, ai zazzaɓi ne kuma jiya da dare ne ma jikin yamatsanta mata".
Cike da tausayin ƙawartan tasake cewa
"Mama Allah yasawaƙe bari in shiga wajen ta".
"Ameen Zainab".
Zainab na shiga taga Halwa saman gado ta kwanta tajuya ma ƙofa baya, ƙarisawa tayi kusa da ita tazauna a gefen katifan tana faɗin
"Halwa ya jikin naki?"
Halwa da tarufe idanunta batare da tamotsa ba tace
"Dasauƙi".
"Allah yabaki lafiya, shine kuma baki kiran awaya kin sanar dani ba? Yanzu da ba don naji Umma tana maganan saka ranan ki jiya ba shikenan bazaki faɗa min ba? Abin yaban mamaki ai ince kina cikin wannan farin ciki nasan da tuni kin garzayo kin fesa min".
Duk wannan surutun da Zainab take yi Halwa taƙi cewa komi illa jinta da take yi, hannu Zainab ɗin tasaka tataɓa wuyan Halwan tana cewa
"Wai jikin yayi tsanani ne haka da bazaki tashi muyi magana ba?"
Ahankali Halwa tabuɗe idanunta tatashi zaune tana kallon Zainab ɗin, cikin kasala tace
"Wani magana zamuyi?"
Zainab kallon yanda duk tayi wani yaushi idanuwanta sukayi luhu-luhu suka yi ja tayi tace
"Ƙawata me ke damunki ne? Kinga yanda kika koma? Ke da ciwo baya hana ki walwalan ki amma yanzu duk kin wani iri kamar kin daɗe kina ciwo?"
Ɗan dafa kan ta Halwa tayi tace
"Zazzaɓi ne kawai".
"To Allah yasawaƙe".
"Amin" Halwa tafaɗa tana komawa takwanta
"Banji daɗi ba ƙawata da baki da lafiya, sai da lokacin farin cikin ki yazo sai kuma gashi ciwo na son hanaki walwalan ki".
"Inji wa yace miki bana farin ciki?" Cewar Halwan tana ƙirkiro murmushi
"Hmm kowa yagan ki yasan da cewa sosai kina jin jiki Halwa, ciwon kwana ɗaya ya maidake haka, nasan da cewa da bakya jin jiki tabbas bazaki kwanta haka ba, ƙafan ki babu inda bazai zagaya wajen sanar da cewa an sanya miki ranan aure ba".
Halwa hararanta tayi tace
"Tunda an ce miki bani da kunya ko?"
Dariya Zainab tayi tace
"Anan kam ai nasan baki da kunya, zakiyi abinda yafi hakan ma".
"Ke dai kika sani". Halwa tace hakan tana ɗaura hannu asaman goshinta
"Yauwa ya maganar Assignment ɗin nan na Malam Isma'il? Kinsan yace "shine Test ɗin mu, kuma wlh na duba nawa bangani ba, ara min naki in kwafe Questions ɗin"
"Kiduba jaka na kiɗauka nima banyi ba, kije dashi kiyimin don Allah".
Miƙewa Zainab tayi tana faɗin
"Ok ba damuwa".
Inda take rataye School bag ɗin tanufa taciro, taduba littafin taɗauko tadawo tazauna tace
"Ni zan tafi gida Umma na can tana jirana zataje anguwa, amma goben zakije school ɗin? Don naga jikinki ya matsanta miki"
"Zani".
"Tom sai muhaɗe acan kenan, ina Yaya Nura? gashi zan tafi ban mishi Allah yasanya alkhairi ba".
Halwa tace "ki neme sa a waya mana, ko kin ban ajiyar sa?".
"To ai naga kece Gimbiyar tasa wataƙil kinsan inda yake, kinga ni ba jan magana zan yi ba na tafi".
Fita Zainab tayi tayima Mama sallama tatafi.
***** ***** ******
Kwance take saman gadonta ta ɗaura hannayen ta saman fuskarta, babu abinda take tunani sai Khalil, tun sanda yakawo ta gidan nan har tafiyan shi takasa samun sukuni, kullum dashi take kwana kuma dashi take tashi, tarasa meyasaka tunanin sa yake damunta kullum, kuma ta kasa gane takamaiman abinda take ji acikin ranta game dashi, tsananin kewar sa ne yake damunta ako da yaushe, burin ta kawai yanzu tasanya shi a idanunta ko ta sami sauƙin zuciyarta, ahankali tamiƙe zaune tana ƙura ma waje ɗaya idanu, can tasaki ajiyan zuciya tatashi tsaye tasanya room slippers tanufi ƙofa, tafiya take yi ahankali tana saukowa daga upstairs, tun sanda takusa saukowa tahango Mom zaune a parlour tana waya, har takusa isa kuma sai tajuya da ninyan komawa Mom takira ta
"Ina zakije kuma Nazeefa? Zo ga yayan ki kugaisa".
Jiki a sanyaye tajuyo tazo wajen Mom tana jin zuciyarta cike da farin ciki, amsan wayan tayi bayan da tazauna takara a kunne tana faɗin
"Hello Yaya".
"Nazeefa". Yakira sunan ahankali cike da salo
Hakan yasaka Nazeefa lumshe idanuwanta cikin jindaɗin muryan sa da yaratsa mata har cikin kwanya tace
"Ina wuni Yaya".
"Lafiya lau, ya jikin ki? Dafatan kina shan maganin ki akan ƙa'ida?".
Gyaɗa masa kai tayi kamar yana kallon ta, sai kuma tace
"Eh ina sha".
"Ok kici gaba da kulawa".
Shiru ne yagibta, hakan yasaka Nazeefa taɗan saci kallon Mom taga hankalinta na kan t.v, sai tace
"Yaya yaushe zaka dawo?"
Shi da har yai tunanin ko ta ba Mom ne still yaji muryan ta tana tambayan shi
"Kina so in dawo ne? Yatambaye ta cike da kulawa
"Eh Yaya nayi kewarka ne sosai".
Tafaɗi maganar ahankali, don ita kanta batasan sanda tafaɗa ba, umarnin zuciyarta kawai tabi
Shi kam Khalil jin maganar yayi wani iri a zuciyar sa, sai kuma yashare tunanin da yakawo mishi rai yace
"Very soon zaki ganni, miƙa ma Mom wayan".
Ba musu tacire wayan a kunni tamiƙa ma Mom, waya suka ci gaba da yi ita kuma Nazeefa tana zaune tana sauraron su, duk da bata jin muryan Khalil ɗin but sai sakin murmushi take yi kamar an mata bushara, tunanin ta kawai yatafi wajen tuno kyakykyawar fuskar sa ne, tana jin wani iri sosai a game dashi musamman ma duk sanda zasu haɗa idanu sai taji gaban ta ya faɗi, ko kuma da zaran ta gan shi hakan ke faruwa da ita, sai dai ita batasan menene ba bare tace ga matsayin abinda take ji, sai dai tasan shi ɗin wani haske ne a rayuwanta, me haskaka mata duk wani baƙin duhun dake cikin rayuwanta, kuma Mai Taimakon rayuwanta.
_Shin zaku iya faɗamata abinda ke damunta Fan's? Don nasan kun sani ai._
~Khalil-Billy~
~Khalil-Lubna~
~Khalil-Nazeefa~
_Muje zuwa Fan's_
_karku manta ku suburɓuro comments fa._
[9/15/2020, 11:32 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
~Khalil-Billy~
~Khalil-Lubna~
~Khalil-Nazeefa~
.
*CHAPTER 18*
*TOMORROW*
*MONDAY MORNING*
Halwa ce tsaye cikin ɗakin ta tana riƙe da Hijab ahannu, kayan makaranta ne ajikin ta da tagama sakawa, tanufi wajen jakan ta dake rataye taciro tasaƙala shi a kafaɗa sannan tasanya Hijab ɗin tafito waje, leƙa ɗakin Mama tayi dake zaune tana cin tuwo tace
"Mama ni na tafi sai na dawo".
"To uban wa kika bar ma abin karyawan naki?"
Yamutsa fuska tayi da yazame mata jiki tace
"Mama ni nayi latti banda lokacin cin abinci".
Harara Mama tawurgo mata tace
"Tunda an faɗi maƙiyin ki ai dole kice kinyi latti, kizo kizauna kici tun kafin in saɓa miki, ayi mutum sam baya son cin abinci? Rayuwan zata yiwun miki ahaka ne? Nura dai zai yi aiki wlh".
Buga ƙafa Halwa tayi cike da shagwaɓa tace
"Ni wlh Mama bazan iya cin tuwon nan ba, ki ƙyale ni kawai natafi".
"Wlh kuwa in bakizo kinci ba sai dai kifasa zuwa makarantan nan, shegiyar yarinya me taurin kai".
Fuska a kumbure Halwa tashiga cikin ɗakin tawafci kwanon tuwon dake ajiye agefe zata fita
"Dan ubanki dawo nan, zauna kici anan don nasan in dai kika fita sai dai kizubar".
Babu musu takoma tazauna, sai dai gaba ɗaya in kakalli fuskarta zaka gane ranta aɓace yake, haka tatsulma hannu tasoma kai abincin baki tana yamutsa fuska kamar tana cin kashi, Mama kam bata ƙara bi takanta ba taci gaba da cin tuwon ta duk tana ankare da ita, ganin tana yunƙurin yin mata amai a ɗaki ne tace
"Wlh Halwa idan har kikai min amai a ɗaki sai na mugun saɓa miki".
Gyaran murya Baba dake bakin ƙofa yayi yace
"Wai menene haka kika tasa yarinya gaba kina ta mata faɗa?"
"Kaima kasan halinta tunda an haɗa ta da abokin gaban ta, makaranta zata tafi bataci komi ba".
Murmushi Baba yayi yace
"Kiriƙa lallaɓa ta mana Hauwa, kinji tashi kije ɗakina akwai raguwan ƙosai da narage kiɗauka kitafi dashi".
Miƙewa tayi kamar zatayi kuka ta cika bakinta da tuwo amma takasa haɗiye wa
"Ungo nan riƙe wannan kiƙara ki sayi wani abun kici".
Amsan kuɗin tayi tafice dasauri, ɗakin Baban tashiga taɗauko ƙosan tafito, sai da tazubar da tuwon dake bakin ta tukunna takuskure bakin tafice dasauri, akan hanya suka haɗu da Zainab
"Ai da naji shiru baki biyo min ba nace bari in zo in duba Madam ɗin nan lafiya?" Cewar Zainab kenan
Yamutsa fuska Halwa tayi tace
"Ƙalau, Mama tatare ni dole sai na karya sannan zan fita".
Dariya Zainab tayi tace
"Ke dai har yanzu bazaki dena wannan halin naki ba sai kace ƙaramar yarinya, kullum sai kin saka Mama ta ɗaga murya akan cin abinci, Allah yakyauta miki, Yaya Nura dai zai yi aiki wlh".
"Uhm itama haka tagama cewa, ko wani aiki zai yi oho?"
Zainab tace "ai da gaskiyar Mama, kullum wajen cin abinci zai yi fama dake".
Taɓe baki kawai Halwa tayi bata sake cewa komi ba, ita kuma Zainab sai mata hira take har suka kai bakin titi suka tari abin hawa
Bayan sun kai suka sauka Halwa taciro Hamsin tamiƙa, ita kuma Zainab tajuya da ninyan tafiya Halwa tariƙo ta tana faɗin
"To uwar son banza ai ban bada da naki ba, sai ki biya sa".
Kuɗin taciro cikin jaka tamiƙa mishi suka juya suka tafi
Zainab tace "wlh ke ƴar wulaƙanci ne Halwa, nima zan rama".
Dariya Halwa tayi tana waro idanu tace
"me nayi miki kuma? Don kawai nace kibada kuɗi?".
"Oho ke kika sani". Cewar Zainab
Still dariya Halwa tayi tace
"Kiyi haƙuri to, wlh banda kuɗi ne yau, nasan kuɗin da nake dashi bazai ishe ni har nabiya miki ba, coz akwai abinda nake so nasiya dashi".
Zainab tace "uhmm naji, but kinsan da muka zo nan sai natuna da Haris? Wlh sai naji gabana na faɗi sabida abinda kikai mishi ranan Wednesday kullum mukazo nan sai na tuna, I know zai zo yarama".
Jin sunan Haris da Halwa tayi ba ƙaramin bugawa zuciyar ta tayi ba, tsoro da fargaba suka zo suka dirar mata alokaci ɗaya, nan da nan annurin fuskarta yaɓace ɓat, ɗan sauran kuzarin da take ji shima yaɓace ɓat, take tasoma jin kamar wani sabon zazzaɓi ne zai rufe ta, Zainab sai magana take mata but ko kaɗan takasa furta komi har suka shige makarantan, koda suka shiga cikin class ɗin su tunda Halwa tazauna bata sake magana ba, Zainab da tatambaye ta ce mata tayi "kanta ke mata ciwo, da alamu zazzaɓin ne ke son dawo mata", don haka Zainab ɗin bata wani matsa mata ba taƙyale ta, a ranan haka ta wuni duk bata da walwala, sai gab da za'a tashi ne wani Malami yayi musu Test sannan aka tashe su.
Lokacin da suka dawo gida, suna zuwa ƙofar gidan su Zainab, Zainab ɗin tace mata
"To ƙawata sai gobe kenan".
Gyaɗa mata kai kawai Halwa tayi tawuce gida, akan dakalin ƙofar gidan su tahangi Nura zaune shi kaɗai, ƙarisawa tayi tasami waje kusa dashi tazauna tana kallon shi tace
"Yaya har kadawo aikin yau?"
Ɗago kan sa yayi dasauri don da alamun be san da zuwan ta wajen ba sai maganarta da yaji, yace
"Uhm kin dawo? ai banji zuwan ki ba".
Murmushi tayi masa tace
"Tunanin me kake yi to?"
Ɗage kafaɗa yayi yace
"Tunanin wajen aiki mana".
Still murmushi tayi tace
"Menene abin tunani to? Ada da baka samu ba kana tunani, yanzu kuma kasamun ma baza kabar zuciyarka tahuta ba?"
Murmusawa yayi yace
"Bazaki gane bane Dear, amma dai yanzu share wannan batun, kinga kin dawo kinsha hanya kishiga gida".
"To kai kuma fa?" Tatambaye sa tana ƙure sa da ido
Ɗan kawar da kan sa yayi yabata amsa
"Ba yanzu ba, ni yanzu ma wajen Ali zani".
"Ok.. sai kadawo". Tafaɗa tana wuce wa tashige gida batare da tajira amsan shi ba
Shi kuma kallon bayan ta yayi har tashige kana yakau da kan sa yana sakin ɓoyayyen ajiyan zuciya, hannayen sa yasaka yatallabo cheeks ɗin sa yana ci gaba da tunanin sa.
**** **** **** *****
Da gudu tashigo cikin parlour'n tana kiran sunan Mami, matashiyar budurwa ce da shekarunta bazai gaza 24yrs ba, bayan ta kuma matashin saurayi ne me kimanin 20yrs, da alamun ƙanin ta ne don sosai suke kama da juna, Mami da fitowar ta kenan cikin ɗakin ta taji muryan ɗiyar nata tana kwaɗa mata kira, sai tawashe baki tana faɗin
"Oyoyo daughter".
Da gudu tazo tayi Hugging ɗin ta tana me cike da farin ciki
"Mamina I'm back". Tafaɗa tana sakin Mamin
Murmushi Mamin tayi tace
"Welcome My daughter, fatan kin dawo lafiya?"
Tana murmusawa tace
"Lafiya ƙalau Mamina" ina Dady?"
"Ai yanzu yafita". Mami tabata amsa
Ɓata fuska tayi kana tace
"Shine yafita bayan yasan da zan dawo?"
Mami tace "Ayya Daughter be yi ninyan fita ba, kiran sa akayi daga office yayi baƙi shine yafita but bazai daɗe ba zaki ganshi ai".
Matashin saurayin me suna Ahmad yace
"Aunty ga jakan ki nan tunda kin manta dani".
Juyowa tayi tana kallon shi, dariya tayi tace
"Sorry my bro, murnan ganin Mami ne".
Hugging ɗin sa tayi tasakar masa peck a cheeks ɗin sa
Mami tace "kashigar mata da kayan mana, muje ke kuma kizauna kihuta sai kici abinci ko?"
Langwaɓar da kanta tayi tace
"O'o Mami bari dai in soma wanka, na gaji wlh da yawa".
"Ok tom je kidawo" cewar Mami sannan tajuya taƙarisa cikin parlour'n, su kuma suka wuce suka shiga ɗaya daga cikin ɗakunan da suke parlour'n, Ahmad yana aje mata trolly ɗin ta yafito yadawo wajen Mami dake zaune cikin parlour'n suka soma hira
Ita kuma bayan tayi wanka tasauya kaya cikin wata ƙaramar riga ja me kwalliyan heart 💓 agaban, tasanya blue pencil jeans sannan taɗaura hula akan ta tafito parlour'n, a kusa da Mami tazauna tana faɗin
"Washhh Mamina".
Mami tace "har yanzu gajiyar ne?"
"Wlh kuwa Mami, kinsan zaman jirgi".
"To ya Maleysian? Yau dai kin dawo gida komi ya ƙare".
"Wlh kuwa Mami, kullum fatana naganni na gama karatun nan na dawo gare ku".
Mami tace "alhmadulillah gashi ai komi ya ƙare, yanzu kije kici abinci kar kuma kin dawo da yunwa".
Kallon Ahmad tayi tace
"Bro ɗauko min inci anan, bana jin zan iya tashi".
Dariya Ahmad yayi yace
"Aunty Kausar uwar son jiki, kin dawo kenan".
Itama dariya tayi tace
"Kai dai bari Baro, but yanzu fa na sauya kar kayi tunanin ko da ne".
Dawowa yayi riƙe da coolar a hannu haɗe da plate yace
"Ai bazan yarda ba sai naga kin soma aiki".
Shafa fuskarta tayi kana tace
"Wa ke maganar aiki yanzu?" Tabb ai sai na huta".
"You see? Dama na faɗa ai, kina jinta ai Mami".
Mami tace "ai kibar ma wannan maganan, don tuni Dadynku ya samo miki aiki a gidan t.v dake nan garin".
Waro idanu tayi tana tsayar da hannun ta daga zuba abincin da tasoma tace
"Mami da wuri haka? Ya Dady zai min haka bayan ni ba haka mukayi dashi ba?".
"Ai sai kibari in yazo kitambaye sa kun fi kusa".
Kaɗa kai kawai Kausar tayi taci gaba da zuba abincin, yayinda Ahmad yasaki dariya yamiƙo mata spoon yana cewa
"Aunty to meye amfanin zaman naki? Tunda kin riga kin gama karatun ki ai aiki yadace dake, ko kuma kin fi so kiyi aure ne?"
Harara tawurgo masa tana kai abincin bakin ta, sai da tagama taunawa kana takalli Mami tace
"Mami naga anguwar tamu duk tacika da sabbin gini, duk yanzu mun sami maƙota".
Mami tace "ai kam, ai gine-ginen ma sun jima, don waɗanda ma suke maƙotaka damu sunyi shekaru kusan biyu da tarewa".
Girgiza kai kawai Kausar tayi, daga nan sukaci gaba da ɗan taɓa hira tana cin abincin ta.
[9/15/2020, 11:32 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 19*
*4DAYS*
Ƙarfe 10:00pm. Na dare jirgin da yakwaso su Brr. Ibrahim Khalil daga Egypt yasauke su a airport ɗin Katsina, driver'n shi yaje yaɗauko shi, lokacin da suka isa gidan kowa yana barci don ba kowa yasan da dawowan sa ba illa me gadi, bayan sun shiga yafito daga motan yanufi cikin gidan jaye da trolly ɗin sa, ƙofan parlon a kulle yake don haka sai yasaka keey yabuɗe yashiga, duhu ne dumɗun cikin parlour'n, Direct ɗakin sa yanufa yabuɗe yashige tare da rufowa, akan gadon sa yayi ma kan sa mazauni, sai da yaɗau 10mins yana hutawa kafin yamiƙe yasoma rage kayan dake jikin sa yashige toilet, wanka yayi yaɗauro alwala yafito, baƙar jallabiya me hula yasanya sannan yatayar da Sallah, magrib da isha'i yayi, bayan ya idar yayi shafa'i da wutri kafin yamiƙe yahaye saman gado cike da gajiya, babu daɗewa kuwa barci me nauyi yaɗauke sa, wanda be tashi farkawa ba sai da gari yayi haske sosai wajajen ƙarfe 11:03am.
Hasken ranan da yashigo ta cikin windon sa ne yabugi fuskar sa, ahankali yasoma buɗe idanun yana rufewa har yaware su gaba ɗaya, take hasken yaƙyalle masa idanu don haka yayi saurin juyawa yaba ma windon baya, 5mins yaɗauka ahaka kafin yamiƙe zaune yana miƙa tare da hamma, ahankali yasanyo ƙafafunsa saman shimfiɗaɗɗen carfet ɗin dake malale cikin ɗakin, bedroom slippers yasaka a ƙafan nasa yamiƙe yanufi toilet, a bakin Toilet ɗin yacire slippers ɗin yashiga bayan yasanya Toilet slippers.
Koda yafito yana ɗaure da towel ajikin sa, ya riƙe ɗaya yana goge suman kan sa, Direct wajen mirror yanufa yasoma shafa Expensive Lotions ɗin sa, bayan ya gama kintsawa yanufi sif ɗin sa yaciro kayan sa, brown t.shirt ne me gajeren hannu sai blue jeans yasaka, feshe jikin sa yayi da Parfumer's ɗin sa masu ƙamshin daɗi sannan yafito parlour hannun sa zube cikin aljihu, dainning yakalla yaga babu komi sai yajuya da ninyan komawa ɗakinsa ɗauko waya, har yariƙe handle ɗin kuma sai yaja siririn tsaki yana juyawa yanufi ɗakin Lubna, ahankali yatura ƙofan yana motsa bakin sa, shashsheƙan kukan ta ne yasoma shiga kunnin sa kafin yasauke idanun sa akan ta, tana zaune a ƙasa ta manne a jikin gado sai takifa kan ta saman gadon, shiru yayi yana kallon ta na tsawon daƙiƙu kafin yakira sunan ta in a cool voice
Dasauri taɗago da kanta face ɗin ta jage-jage da hawaye tasauke idanunta kan shi, sosai tayi mamakin ganin shi don batasan ya dawo ba, shi kam takowa yayi yashigo ciki sosai yana kallon ta yace
"Meke damun ki?"
Ahankali tasunkuyar da kanta ƙasa cikin sanyin muryan ta da be fita sosai tace
"Babu komi".
"Ke banson ƙarya ki faɗa min abinda ke damun ki nace?" Yafaɗa da ɗan ƙarfi murya a kausashe
Jikin ta har rawa yake yi tace
"Dama wasu ne suka sace min Mamana da ƙannina".
"Whatt.." yafaɗa da ɗan ƙarfi yana tsare ta da idanu
"Meyasa to?" Yasake jeho mata tambayan
Cikin rawan murya tace
"Dama.. dama sabida sun saka ni aiki ne ban musu ba shine suka kama su".
Wani kallo yasakar mata kana yace
"Wani aiki kenan?"
"Uhmm hm sun ce ne naɗauko musu duk wani abu da nagani cikin ɗakin ka kamar takardu ko Lapton ɗin ka.."
Sai kuma tayi shiru tana zub da hawaye, Khalil ajiyan zuciya yasauke har yanzu idanun sa akan ta, dama yadaɗe da zargin ta, tun sanda yashigo ɗakin sa yaga ta tsorata hakan yasaka yaɗaura ayar tambaya akan ta, daga lokacin ne yasaka Camera 📷 cikin ɗakin sa yana ɗaukan masa duk abinda take yi, wannan dalilin ne yasaka ko kaɗan baya barin ɗakin da yake aje muhimman abubuwan sa aciki abuɗe, but besan da cewa mutanen da suka saka ta aikin sun yi garkuwa da mahaifiyar ta da ƙannin ta bane, sai yaji tsananin tausayin ta ya kama shi, ahankali cikin sanyin murya yace
"Ki dena kuka Lubna, insha Allahu Mahaifiyarki da ƙannin ki zasu dawo gare ki karki damu, ki kwantar da hankalin ki kinji?"
Ɗago kanta tayi tana kallon sa kafin tagyaɗa masa kai tana jin zuciyarta na mata sanyi sosai, bata yi tunanin zai ɗau abin da sauƙi haka ba idan har yagane cin amanar sa take yi, take tasake jin ƙaunar sa na sake shiga cikin zuciyarta
"Bani wayan ki". Yace hakan yana ciro hannun sa cikin aljihu
Dasauri tamiƙe taɗauko mishi tabashi, amsa yayi kawai yafice, ita kuma tabi bayan sa da kallo tana sauke ajiyan zuciya, zamewa nan ƙasa tayi tazauna tana share hawayen fuskarta
Shi kuma Direct waje yafita yanufi motan sa yashige yafita gidan, kamar ko yaushe yana jan motan ne ahankali yana riƙe da wayan sa ahannu yana neman layin Brr. Tahir, dai-dai zai karya kwana yafita titi yaɗago kan sa don duba hanya, nan yaga wata farar Mota itama ta shanyo kwana kamar zasu yi karo da juna, dasauri yaja burki yana son kaucewa but duk da haka sai da suka gwarawa juna, aje wayan nasa yayi kafin yabuɗe motan yafito dai-dai itama tafito cikin motan ta suka kalli juna, atare kuma suka faɗi
"I'm sorry".
Hakan yasaka sukayi murmushi kafin ita tace
"Kayi haƙuri bansan da zuwan ka ba ne".
"No laifina ne ai, nima ban kula ba, but kiyi haƙuri ko".
Murmushi tayi masa tagyaɗa kan ta
"Babu damuwa". Tace dashi kana tajuya tashiga motan ta
"Shima ɗin motan nasa yashiga, sai da taja nata motan yawuce kafin itama tawuce, Direct police station yawuce yayi reports ɗin ɓatan mahaifiyar Lubna da ƙannin ta biyu sannan yawuce gidan su.
[9/16/2020, 8:26 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 20*
Tana kwance saman katifan ta daga ita sai farar doguwar riga irin me taushin nan da zanen flowers ajikin rigan, kanta babu ɗankwali sai gashinta da yawargaje yazubo mata har kafaɗunta, littafi ne a hannunta tana karanta wa tajiyo sallaman ƙawarta daga waje, amsa mata tayi sannan tashigo takalle ta tana faɗin
"Ƙawata hutawa kike yi ne?"
Tashi zaune Halwa tayi tana yatsina fuska tace
"Uhm hutu kuma? Karatu dai nake yi".
"Yayi makaranciya, kinga ni wlh ban ma bi ta karatun ba don bani da lokaci yanzu, ina Mama naji kamar ke kaɗai ce gidan?"
"Eh Yaya Nura ya kai ta kasuwa".
"Kai ƙawata wlh baki ga yanda kika sauya ba, wai meye sirrin ne ni naga kamar kina ƙara wani haske ne da kyawu kamar bakijin dawan garin? Ko dai yaya Nura ne?" Zainab tafaɗi hakan tana ƙare mata kallo tare da dariya
Murmushi Halwa tayi, sosai itama take ganin sauyi daga gare ta, tayi wani haske fayau duk da ita ɗin ba fara bace, gashi kuma ko ina nata yaciko gunun sha'awa
"Hmm ke dai ban son tsegumi me kikeson cewa akan Yaya Nura?"
Dariya Zainab tayi tace
"A'a babu komi, kawai dai ina tunanin ko har yafara sauya kulawan sa ne daga gare ki tunda yaga kin kusa zama mallakin sa, kin gane dai irin uhm uhmmm.."
Dukan ta Halwa tayi a cinya tana cewa
"Banson sharri shegiya ke babu abinda kika iya sai saka idanu, yanzu me kikazo yi ne don nasan ba banza takawo ki ba?".
Waro ido Zainab tayi tace
"To me kike nufi? Ko nace miki wani abu nazo amsa wajen ki? Kinga ni tare da Safna muke zamuje gidan aunty Zaituna, shine nace bari in shigo ko zamuje tare sai gashi Mama ma bata nan".
Halwa tace "wato da Safna ma kuke taƙi shigowa? Lallai kam zataci uban ta wlh dani take zancen".
Zainab tace "ni fa bana faɗa miki bane kije kuyi halin naku".
"Ai kibar ni da ita zamu haɗu ne wlh, kuma kisanar da ita hakan".
"Baki da ƙafa ne? Kifito kije kisame ta mana". Zainab tafaɗi hakan tana nufan ƙofa zata fice
Gyara zaman ta Halwa tayi taɗau littafinta tana faɗin
"Banda lokacin ku yanzu, sai mun haɗe a school".
Zainab tace "Allah yakai mu to" sannan tafice da gudun ta
Kifa littafin Halwa tayi saman katifan tabi kai takwanta tana sakin numfashi, shiru tayi tana tunani aran ta, abun da yafaru da ita kwanaki 8 da suka wuce ne yadawo mata cikin ranta, take hawaye masu zafi suka soma sulmiyo mata a fuska
"Har yaushe ne zata dena tuna wannan abinda yafaru da ita? Yaushe ne zata manta da wannan baƙin ranan acikin sauran ranakun da tayi a doron ƙasa? Har yaushe ne zuciyarta zata dena shiga cikin wannan ƙunci da baƙin cikin?"
"Ya Allah gani gare ka, ya Allah kabi min haƙƙina akan wannan azzalumin, haƙiƙa yazalunce ni yasaka min tabon da bazan taɓa iya cire wa ba, Allah ya isa tsakanina dashi bazan taɓa yafe masa ba har duniya tanaɗe".
Tafaɗi hakan afili tana saka bayan hannunta tashare hawayen fuskarta.
***** ***** ********
*AFTER THREE DAYS*
Fitowa yayi daga ɗakin sa hannun sa riƙe da waya, yasami waje saman kujera yazauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, wayan sa yasoma latsawa yana yi yana ɗan ɗago kan sa yana kallon t.v, Lubna ce tafito daga kichen riƙe da coololi a hannun ta, dainning tanufa tajera kana tasake komawa taɗauko wasu su ma tajera su, bayan ta gama tanufi inda yake zaune ahankali tace mishi
"Na gama girkin, ko akwai wani abu?".
Girgiza mata kai kawai yayi idanun sa a kan wayan sa, juyawa tayi tanufi ɗakin ta, shi kam sai da yafi 10mins kafin yamiƙe yanufi dainning ɗin yazauna, aje wayan nasa yayi yasoma buɗe coololin abincin yana taɓe baki, gaba ɗaya babu abinda yayi masa aciki don baya tunanin zai iya sanya wani abu me nauyi acikin sa, rufewa yayi yatashi yanufi kichen, babu daɗewa yadawo hannun sa riƙe da glass cup ya haɗa Black tea, direct dainning table ɗin yakoma yaɗau wayan sa yadawo cikin parlour'n yazauna yasoma sipping tea ɗin yana kallon t.v, ahaka har yagama kafin ya'ajiye cup ɗin saman Centre table yaɗau remote yasoma sanja Channels, har yasaka wani tasha me suna *ƳAN CI T.V* yana shirin sauyawa aka nuno fuskar ta, hakan yasa yatsayar da tashan yana ƙure ta da idanu, duk da ba sosai yakalli yarinyan ba but zai iya shaida itace wacce sukayi karo a kwanakin baya, tana sanye ne cikin wata baƙar abaya me ɗan karen kyau da tsada, ta yane kan ta da Black veil, kasancewar ita fara ce sosai tayi kyau cikin kayan, tana gabatar da shirin ta kamar haka:
"Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa acikin sabon shirin mu na *RAYUWAR DUNIYA,* wacce ni Kausar Ali Aliyu zan riƙa kawo muku aduk ranan Litinin da Alhamis, shiri ne dake kawo muku abubuwan dake faruwa acikin duniyar mu, tare da bankaɗo muku duk wani abinda ke ɓoye don kusani..."
Ahankali yalumshe idanuwan sa yana jingina kan sa saman kujeran, yana jin muryan ta na ratsa cikin kunnen sa, sai kuma yabuɗe idanun sa yasake saukewa akan fuskarta, sosai yarinyan yaji ta burge shi, rana ta farko kenan da yaji mace tabashi sha'awa har be san sanda yadunga murmusawa ba, yanda take gabatar da shirin ta da komi nata a natse ne
Wayan sa da yasoma ringing ne yasaka shi ɗan ɗago kai yana kallon wayan, ganin sunan DPO na yawo a screan ɗin wayan, hakan yasaka shi miƙa hannu yaɗau wayan tare da rage volume ɗin t.v'n yana karawa a kunne, basu fi 5min suna wayan ba yacire Phone ɗin a kunnin sa yamiƙe yanufi ɗakin sa, Direct sif ɗin sa yawuce yasauya kaya zuwa milk colour ɗin riga me dogon hannu, rigan kamar Jaket ne da coller a wuyan, but sai dai bata da nauyi ƴar shugula ce, wandon sa pencil ne kalan blue Black, sai yasaka Combat shi ma kalan wandon da igiyar shi milk, sosai yayi kyau cikin shigan yafeshe jikin sa da Expensive Parfumer's ɗin sa me shegen ƙamshi, yaɗau wayoyin sa da car keey's yafice, yana fita Compound ɗin gidan yashiga cikin motan sa ash colouer yabar gidan.
...... ....... .........
Yana zaune a office ɗin DPO yana mishi bayani kamar haka:
"Ah BARRISTER a binciken da mukayi na daga ɓatan Matar da kakawo mana, ahm lokacin da kabamu report mun je wajen gidan ka don gudanar da binkice anan muka haɗu da wani mutum yana leƙa gidan ka, dama numban da kabamu mun riga da mun duba sai dai akashe yake kuma an datse hanyar sadarwan shi, to wannan dai mutumin mun kamashi don bamu yarda dashi ba, don haka koda muka kawo shi nan muka saka shi yayi bayani sai yayi mana taurin kai, sai da muka bashi wahala tukun yafaɗa mana abinda yasani, yace "shine wanda yake gadin Matar da ƴaƴan ta, sannan yazo gidan ka ne saboda aiko shi da akayi wajen ƴarinyan Matar da take gidan ka, munyi-munyi yayi mana bayani akan mutanen da suka saka shi aikin but yace "shi be san su ba, shi dai kawai an saka shi yatsare su ne", kaji abinda yafaru, but duk da haka dai muna tsare dashi ko zamu sami wani inpermation akan su".
Gyara zaman sa da kyau Khalil yayi yana kallon DPO ɗin yace
"Yanzu ina suke?"
"Suna nan mun aje su a wani ɗaki, zaka iya tafiya dasu yanzu haka but ko wani lokaci zamu iya neman su".
"Ok babu matsala ai".
Miƙa mishi hannu yayi sukayi musabaha kafin suka miƙe atare suka fice.
Bayan kamar minti goma Khalil yafito cikin station ɗin, bayan sa wata dattijuwar mata ce da matasan yara maza su biyu, buɗe musu mota yayi suka shiga sannan yakulle shima yashiga yaja yatafi, Direct gidan sa ya'isa, bayan yayi parcking yasake buɗe musu suka fito yace "su biyo bayan shi" babu musu suka bi shi a baya har cikin parlour'n, zama yayi bayan da yace
"Umma kuzauna mana".
"Toh". Cewar matar sannan suka zauna
Wayan sa yasaka yakira Lubna sai gata tafito, ai tana cin karo dasu tasheƙo da gudu tana kiran "Ummana", rungume Umman tayi tasaki kuka, su ma ƙannin ta suka rungume ta duk suka fashe da kuka, Khalil kallon su kawai yake yi yana murmushi cike da tausayin su, sai da suka gama rungume-rungumen junan da koke-koken kafin Lubna taɗago kanta fuska a jiƙe takalle shi tace
"Nagode Sir, ban san da bakin da zan maka godiya ba, na gode sos.."
"Shiiiiihh ya isa haka, kibasu abinci suci su huta sai ki kira ni bayan sun gama ok?"
Gyaɗa masa kai tayi tana share hawayen ta, shi kuma tashi yayi yashige ɗaki yarufo ƙofan, ahankali ya'isa gaban gadon sa yazauna tare da jinginar da kan sa a jikin gadon, rufe idanuwan sa yayi yana jan iska da ƙarfi yana fesar wa, tunanin abinda yakamata yayi kawai yake yi, tsawon lokaci kafin yaji wayan sa tana ringing, Koda yaduba yaga Lubna ce sai yamiƙe kawai yafice
Kallon Umman yayi bayan da yazauna yace
"Umma kuna da wasu ƴan uwa ne a wani wajen, ko dama anan kuke zaune?"
Umma tace "a'a muna dasu a ƙauye, dama mu ma can muke zaune sanadiyan aiki ne muka dawo nan muka kama haya".
Gyaɗa kan sa yayi kana yace
"To Yakamata ki ɗauki ƴaƴan ki gaba ɗaya kubar nan, ko ki koma ƙauyen ko kuma ku sauya wani waje me nisa, sabida mutanen da sukayi garkuwa daku ko wani lokaci zasu iya dawowa gare ku".
Sannan yamayar da idanun sa kan Lubna wacce itama kallon shi take yi yace
"Kije kihaɗa kayan ki".
Daga haka yamiƙe yakoma ɗakin sa, ita kam Lubna kasa riƙe kukan da yazo mata tayi tasake shi ahankali, Umman nata tace
"Ai hakan yadace muyi Lubna, wlh ko be ce mubar nan ba baza mu sake kwana ba, ai Allah mun gode maka da yataimake mu da bamusan me mutanen nan zasu yi mana ba, kitashi kije kihaɗa kayan ki mutafi".
Babu musu tamiƙe tashiga ɗaki, lokacin da tafito riƙe da trolly ɗin kayan ta shima Khalil yafito yana kallon ta, sauke kanta ƙasa tayi hawaye na zubo mata, bazai iya juran ganin hawayen ta ba don haka yaɗauke kan sa yanufi wajen Umma yace
"Ga wannan Umma, da fatan zai ishe ku ko da sana'a ne sai ku kama".
Jiki na rawa Umma tasaka hannu ta'amshi maƙudan kuɗin da yamiƙo mata
"Har da ɗawaniya ɗan nan? To mun gode Allah yasaka da alheri, Ubangiji yabiya maka duk kan buƙatun ka, mun gode ƙwarai da gaske".
Murmushi kawai Khalil yayi yana motsa laɓɓan sa, yana nan tsaye har suka fice kana yasami waje saman kujeran yazauna, lumshe idanuwan sa yayi yana tuna ranan da Mom ɗin shi takawo mishi Lubna a matsayin ƴar aiki, wacce zata riƙa taimakon shi da gyaran gida
Asali ita Umman Lubnan itace ƴar aikin Mom, daga baya ne tayi wani ciwo da yakwantar da ita tsawon lokaci har ta'ajiye aiki Mom kuma tasamo wata, lokacin bayan Umma ta sami sauƙi sai tazo wajen Mom tane mi alfarma ta samar ma Lubna aiki, shine ita kuma Mom tace "Khalil yaɗauke ta yatafi da ita, tunda dole yana buƙatar wacce zata riƙa dafa mishi abinci da sauran abubuwa na gyaran gida" babu musu Khalil yatafi da ita, wannan shine dalilin da yasaka LUBNA take aiki a gidan sa, kuma a gidan nasa take kwana but wani lokacin kuma tana komawa gidan su, musamman kamar ranan Weekends haka.
Ajiyan zuciya yasauke yana buɗe idanun sa, gyarawa yayi yakwanta a kan kujeran yasake lumshe idanun sa.
[9/16/2020, 8:26 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 21*
Kiran sallan magriba ne yasanya shi buɗe idanun sa da suka yi ja sakamakon barcin da yaɗauke shi, ahankali yamiƙe yanufi ɗakin sa, alwala yaɗauro yafito yanufi masjid, as usual sai da akayi sallan isha'i yadawo gida, Direct ɗakin sa yawuce yacire rigan sa yabar singlate ɗin dake jikin sa, drower yabuɗe yaɗauko keeys sannan yarufe, yaɗau briefcase ɗin sa yafito parlour, akan 2sitter yazauna yana ajiye briafcase ɗin saman Centre table, wayan sa yaɗauka sai da yalatsa kafin yakara a kunne, yana jin an ɗauka yace
"Kazo ina neman ka".
Daga haka yacire wayan ya'ajiye, buɗe jakan yayi yaciro Computern sa yasoma aiki
Da sallama wani matashin saurayi yashigo ciki, amsa masa sallaman yayi batare da yaɗago daga abinda yake yi ba
"Gani Sir". Cewar saurayin bayan da yaduƙa gaban sa
Ɗago kai yayi yana kallon sa yace
"Sale daga yau aikin ka zasu ƙaru agidan nan, zaka riƙa zuwa kana gyara min cikin gidan nan, don haka zan ƙara maka albashi in babu matsala".
Washe baki Sale yayi yace
"Ai babu komi Sir duk zan iya, har da ma abun da bakace ba".
"Ok.. ga keeys ɗin gidan sai kariƙe a hannun ka ko".
Hannu biyu yasa ya'amsa
Yace "katashi kaje".
Miƙewa Sale yayi yana godiya kafin yatafi, shi kuma yaci gaba da aikin sa, wajen ƙarfe 09:00pm. Yadakata kasancewar yunwan da yaji yana ƙwaƙulan cikin sa, miƙewa yayi yanufi kichen, tsayawa yayi yana nazarin abinda zai ci domin sosai yaji cikin sa na kukan yunwa, don haka kawai yayanke shawaran dafa indome, cikin abinda be gaza minti 12 ba yagama, indome ne haɗe da ƙwai yasoya yaɗauka yafito, zama yayi yasoma ci ahankali yana tunani har yagama, yatashi yamayar da plate ɗin da spoon cikin kichen sannan yadawo yaci gaba da aikin sa, sai wajen ƙarfe 12:04pm. Sannan yanufi ɗakin sa, sai da yaɗauro alwala yagabatar da sallan nafila tukunna yasauya kayan sa zuwa kayan barci yakwanta.
Washe gari ƙarfe 06:45am. Tuni yagama shirin sa na zuwa office, suit yasanya sky blue da ƴar cikin milik colour, sosai yayi kyau babu abinda yake yi sai tashin ƙamshi, yaɗau briafcase ɗin sa yafice, a farar motan sa yashiga yabar gidan.
Ƙarfe 02:30pm. Yadawo gida, yana shiga cikin ɗakin sa ya'ajiye briafcase ɗin sa sannan yazauna yasoma zare Combat ɗin ƙafan sa da socks, bayan ya gama yacire suit ɗin tare da necktie ɗin wuyan sa duk yazube saman gado, miƙewa yayi yashiga Toilet, be daɗe ba yafito yanufi parlour, kichen yawuce yahaɗa tea me kauri yazauna nan yasoma sha, bayan ya gama yafito yakoma ɗaki yacire kayan sa yashiga wanka
Lokacin da yafito yashirya cikin wani ɗanyen Boyel maroon colour, ba ƙaramin kyau suka yi masa ba kamar wani sabon ango, yafeshe jikin sa da farpume's yakwashi wayoyin sa da keeys ɗin mota yafice, mota yashiga yabar gidan, Direct super makert yawuce yayi shopping masu yawan gaske, yahau motan sa yanufi gidan ɗan uwan sa
Lokacin da ya'isa yana yin hon aka buɗe masa motan yakutsa ciki yayi parcking, yanayin gidan da komi irin nasa ne, sai dai ɗan abinda ba'a rasa ba, yana fitowa me gadi yanufo sa da gudu yana kai gaisuwa tare da taimaka masa yashigar da kayan, a parlour ya ajiye masa, shi kuma yaciro kuɗi yabashi yana ta godiya sannan yafita, zama yayi saman sofa yana sauke idanun sa akan plasma dake aiki shi kaɗai babu kowa, yafi minti 5 da shigowan sa be ji wani zai fito ba, hakan yasaka yaɗau wayan sa yasoma latsawa yana neman layin Sameer, sai ga Abida tafito, ƙanwa ce ga matar Sameer ɗin, tana hango shi tanufo wajen shi cike da fara'a tana faɗin
"Laa Ya Khalil yaushe kashigo?"
Ɗago kan sa yayi yakalle ta kana yace
"Yanzu".
"Sannu da zuwa to".
"Yauwa, ina masu gidan?" Yatambaye ta yana mayar da idanun sa kan wayan sa
Murmushi tayi tana zama akan hannun kujeran da yake kai, kana tace
"Suna ciki, ko in Kira su?"
Gajeren tsaki yaja batare da yace mata komi ba, yana ganin rainin hankali ne, har sai yace ma takira su zata kira mishi su? wayan sa yakara a kunne yana faɗin
"Bro gani a gidan ka fa".
Abinda yafaɗa kenan yakatse kiran, ita kam Abida kallon sa kawai take yi tana murmushi, sosai take ƙaunar Khalil sai dai ko kaɗan shi baya sakar mata fuska, ko tayi yunƙurin shiga jikin sa to baya bata dama
Sameer ne da Hakima suka fito daga ɗakin su, sun ci ado cikin wani farar kamfala iri ɗaya har aikin
"Uhmm ai wlh nayi fushi ba kaɗan ba, wai ace tun yaushe kadawo ƙasan nan har akayi suna bakazo ba sai yanzu?"
Cewar Hakima tana zama a ɗaya daga cikin kujerun parlour'n, yayinda shima Sameer yasami gefen ta yazauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kyakykyawar murmushin sa yayi kana yace
"Afwan Matar Bro, I know nayi laifi, amma sai da nace ma Bro yafaɗa miki uzurina, ko ba haka muka yi ba Bro?".
"O'o niii? Kar kahaɗa ni da matata, a yaushe mukayi haka da kai?" Cewar Sameer ɗin yana ɗaga hannaye sama tare da fito da idanuwan sa
"You see ka gani ko? Ai nasan Mijina bazai maka ƙarya ba, kai dai kawai bakayi ninyan zuwa ba sai sanda kaga dama". Hakima tafaɗi hakan tana murmusawa
"To yanzu dai first kifara ɗauko min My son nagan shi sai aci gaba daga baya".
"Hmm ai yayi fushi shima bazai gan ka ba".
"Haba Matar Bro Ni ne fa ko kin manta ni? Bro kasaka baki mana". Khalil yafaɗi hakan yana langwaɓar da kan sa kamar ƙaramin yaro
"To sweetheart ki yafe masa tunda naga kamar yayi nadama, but nest in yasake ki hukunta shi".
Gaba ɗaya sukayi dariya, yayinda shi Khalil ɗin murmushi kawai yayi yana shafa kan sa
Hakima tace "Abida ɗauko mishi Aamir".
"Tom Aunty".
Miƙewa tayi tawuce ciki, ita ma Hakima tashi tsaye tayi tana faɗin
"Bari nakawo maka abin motsa baki Mijin".
Khalil yace "No kibar sa kawai na hutar she ki".
Sameer yace "waɗannan ledojin fa? Menene aciki kakawo mana?".
"Shopping ɗin My Son ne".
Hakima tace "to mun gode".
Lokacin Abida tafito riƙe da Aamir a hannu takawo mishi, hannu yasaka ya amsa wanda har hannun su yana gogan juna, shi be ma lura ba yaron kawai ya'amsa, yayinda ita kuma Abida taji wani iri ajikin ta hakan yasaka tasaki murmushi tana jin farin ciki, yau rana ta farko jikin mafi soyuwa a cikin zuciyarta ya haɗu da nata
Bayan yagama ganin yaron ma sai tamiƙo hannu don yaba ta, but sai yamiƙe yaje yamiƙa ma Hakima yana faɗin
"To ni tafiya zan yi, sai kuma na sake kewayo wa".
"Da wuri haka?" Cewar Hakima bayan ta amsa yaron
Amsa mata kawai yayi ataƙaice, daga nan suka yi sallama suka fito tare da Sameer, sun kai wajen mintuna 30 atsaye wajen motan Khalil suna tattaunawa kana yashiga motan sa yatafi.
Yana tafiya a cikin motan sa ya kawo anguwan su, zai sauka kan titi yaji Motan tayi faci sakamakon taka ƙusa da tayi, tsaki yaja yana ɗan murza hannun sa a sitiyarin motan, yajingina kan sa jikin kujeran yana kallon saman motan, tsawon mintuna yana nan ahaka kafin yaji hon a bayan sa, hakan yasaka yaɗago kan sa yana kallon motan dake bayan sa ta mirror, siririn tsaki yaja yana mayar da kan sa yalumshe ido, motan ce tazo dai-dai setting shi kana tazuge glass ɗin motan tana kallon shi
"Kana neman taimako ne?" Tafaɗi hakan cike da sanyin murya
Ɗago kan sa yayi yakalle ta, ita ce dai budurwan da sukayi karo kwanaki kuma yaganta cikin t.v, sai yagyaɗa mata kai a hankali still yana kallon ta, murmushi tayi masa don ita tariga da tagane sa hakan yasaka tatsaya
"Ok why not kazo narage maka hanya in babu damuwa fa".
Murmushi yayi mata kana yafito daga motan yarufe, sai da yaciro wayan sa yayi ɗan gajeren text yatura kafin yanufi motan nata yashiga, taja suka tafi.
_Ku ƙara yawan Comments plzzzzzzz_ 🥰🥰🥰
[9/17/2020, 11:04 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
_Wannan shafin naku ne duk wani masoya littafin Brr. Ibarhim Khalil, ku ji daɗin ku_🥰🥰💃💃💃💃
.
*CHAPTER 22*
"Anan zaki sauke ni". Yafaɗi hakan yana nuna mata setting gidan sa
"Laa kace kusa da juna muke ma". Tace hakan lokacin da tatsayar da motan
Kallon ta yayi yace
"Really?"
Murmushi tayi itama tana kallon shi tagyaɗa masa kai
"But ban taɓa ganin ki ba ai? Kuma ina yawan ganin wani matashin saurayi yana fitowa gidan".
"Eh ai ni bana ƙasan ne, ina can Maleysia ina karatu, sai kwanan nan nadawo".
Gyaɗa kan sa yayi kana yace
"Ok thanks for your help me".
"Babu damuwa, yiwa kai ne ai".
Sai kuma tamiƙo mishi hannu still da murmushi a face ɗin ta tace
"Zamu iya zama friends?"
Kallon hannun nata yayi sai kuma yakalle ta, sannan yagyaɗa mata kai batare da yamiƙa mata hannun ba, janye hannun nata tayi tana yarfe shi tace
"Oh sorry" nayi tunanin ko maleysia muke". Tafaɗi maganar tana waro idanu
Hakan yasaka shi murmushi batare da yace komi ba, yabuɗe motan zai fita
"Aff baka sanar dani sunan ka ba?" But ni sunana Kausar Ali Aliyu, and You?"
Tafaɗi maganar tana ƙure shi da idanu
"BRR. IBRAHIM KHALIL". Yayi maganar ataƙaice shima yana kallon ta
"Wowwww! Nice Name, zan ji daɗin abota da kai kenan coz ni ƴar Jarida ce".
Cike da ƙosawa da surutun ta yasaka ƙafarsa awaje zai fice still tasake faɗin
"Am baka ji ba?"
Yajuyo yana kallon ta fuska a haɗe tare da nuna gajiyawar sa, ita kuma sai tayi murmushi tace
"Sorry na takura ka, dama zance ne kagaishe min da Madam kafin nashigo".
"Wa yace miki ina da mata?"
Yafaɗi maganar yana ficewa gaba ɗaya yataka yatafi batare da yajira amsar ta ba, ita kam babu abinda take yi sai murmushi, sosai Guy ɗin yaburge ta, ko kaɗan bashi da rawan kai irin samarin zamanin nan, sai da taga shigewan sa sannan ta tada motan tanufi bakin Gate ɗin gidan su tadanna hon da ƙarfi.
Shi kuma daga shigan sa gidan yamiƙa ma Gate Man keeys ɗin motan sa in Drever yazo yabashi, sannan yashige cikin gida, bayan yayi wanka ya kintsa cikin ƙananan kaya yasake fitowa yanufi masallaci, sallan asar yayi yadawo yazauna nan parlour yana danne-dannen waya, tsawon 1 hour yana wajen kafin yamiƙe yanufi kichen, Coffee yahaɗa yafito yazauna yakunna t.v yasanja channel zuwa MBC Action, abinda yake so kuwa ake yi wato wrestling, haka yakafa idanun sa akan kallon yana yi yana spping Coffee ɗin, sai da aka gama yamiƙe yanufi kichen ya ajiye cup ɗin yashiga ɗaki, ahankali yabuɗe ɗakin da yake aikin sa yazauna kan kujera, yajanyo Lapton ɗin sa yasoma aiki.
......... ........ ........ .....
Asalin Alhaji Abdurra'uf Abdullahi da Hajiya Hajara fulani ne kuma mazauna garin Katsina, Alhaji Abdurra'uf wato Dad shi irin baƙaƙen Fulanin nan ne na daji masu yawo wannan garin zuwa wancan garin, yayinda Hajiya Hajara wato Mom ita kuma irin fararen nan ne waɗanda kallo ɗaya kayi musu zaka gane su ɗin Fulani ne, Babban Family ne dasu, lokacin da su Dad suka zo Garin Katsina dashi da iyayen shi Mahaifin Mom ne yabasu mazauni a nan gidan su, zuwan sa gidan ne kuma yasoma karatu har matakin degree, da sannu da sannu suka saba da ƴan gidan har suka zama tamkar Family ɗaya, kuma alokacin ne Soyayya me ƙarfin gaske yashiga tsakanin Dad da Mom har suka yi aure, Allah ya albarkace su da yara biyu duk ka Maza Sameer da Ibrahim Khalil, kuma daga kan su basu sake haihuwa ba.
Rayuwan Sameer da Ibrahim Khalil sun yi shi ne cikin gata da ƙaunar iyayen su har zuwa matakin da suka girma, kuma sun yi karatun su ne a ƙasan Gamerny har zuwa sanda suka gama suka dawo, shi Sameer ya karanci Doctoring ne fannin ƙashi, shi kuma Ibrahim Khalil ya karanci BARRISTER
A tare Sameer da Khalil suka ƙera gidan su, sai dai ba anguwa ɗaya bane, Lokacin da Sameer ɗin yayi aure shima Khalil yace "bazai zauna a gidan su ba" shine yakoma sabon gidan shi, shekaru kusan biyu kenan da faruwan hakan.
Wannan shine taƙaitaccen tarihin su.
***** ****** ******
*TWO WEEKS AGO*
Da dare wajen ƙarfe 09:00pm. Khalil ne zaune a cikin Garden ɗin gidan sa, gaba ɗaya wajen haske ne yamamaye wajen tamkar rana don baza kace dare ne ba, yana sanye cikin wasu kaya riga da wando three qweater tamkar na sanyi, red colour ne irin dack ɗin nan, sun bala'in yin masa kyau sosai, kan sa babu hula sai gashin sa da iska ke ta kaɗawa, gaban sa kuma ɗan ƙaramin table ne ya ɗaura Lapton ɗin sa akai, gefe ɗaya kuma glass cup ne da Fruits a cikin plate, aiki yake yi time to time kuma yana ɗan kurɓan Black tea ɗin, wayan sa dake ajiye ne tasoma ringing yaɗan tsayar da aikin yakalli wayan, ganin sunan Dad ya fito raɗo-raɗo a screan ɗin yasanya shi saurin ɗauka yana peacking call ɗin tare da karawa a kunne
"Hello Dad.. au assalamu alaikum".
Murmushin Dad ɗin ne yabayyana cikin wayan kafin yace
"Kai dai baza ka dena halin nan naka ba ko?"
"Sorry Dad na manta ne, but ai na gyara ko?" Yayi maganar a shagwaɓe
Still Dad murmusawa yayi yace
"Auta kenan, Mom ɗin ka tariga ta gama ɓata ka, kana yin abu sai kace ƙaramin yaro".
Murmushi Khalil yayi yana shafa kan sa yace
"Dad ai ku kaɗai nake ma wa, coz a wajen ku ni har yanzu yaro ne".
Dad yace "to gobe da safe kafin kawuce office kabiyo gida ina neman ka".
"Dad lafiya kuwa?"
"Lafiya lau My Son, sai dai in ka zo zaka ji, kar kuma kace min ka manta kashanya ni jiran ka".
"Tom Dad, insha Allahu zan zo". Khalil ɗin yafaɗa cike da girmama wa
Daga nan sallama suka yi Khalil ya'ajiye wayan sa yaci gaba da aikin sa.
[9/17/2020, 7:20 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 23*
*TOMORROW MORNING*
Khalil ne zaune a parlour'n mahaifin nashi yana sauraron abinda yake faɗa mishi
"Ibrahim har yanzu dai bakasan zurun ba ko? Tun yaushe nayi maka maganar aure but har yanzu shiru babu wani motsi da kake yi".
Ɗago kan sa yayi yana kallon Mahaifin nashi, be yi tunanin wannan maganar ce tasaka yakira shi ba, kuma ko kaɗan be shirya ma hakan ba
"Ina jin ka tunda ka bari sai na tambaye ka, yanzu kasanar dani wacce yarinya ce kake so don mugaggauta nema maka auren ta?"
Shiru Khalil yayi yana sad da kai ƙasa
"Kayi shiru kuma?" Dad yatambaye sa yana kallon sa
"Uhm Dad ni har yanzu ban sami wacce nake ƙauna ba".
"Ohho nagane me kake nufi Ibrahim".
Cewar Dad yana kaɗa kan sa, sannan yaci gaba da cewa
"But nasan maganin ka tunda naga kamar har yanzu baka yi hankali ba, tun yaushe muke wannan maganar da kai amma dayake baka ɗau maganar ta wa da wata muhimmanci ba shine ka shashantar dashi, yanzu gashi har Sameer yana da yaro kai kazauna kana son kazama tuzuru, to na baka nan da lokacin da zaku gama wannan shari'an, katabbatar ka sami matar aure idan ba haka ba ni da kai ne, kana ji na?"
Dad ɗin yaƙarike maganar yana riƙe kunnen sa tare da kallon sa
Ɗan turo baki gaba yayi kana yagyaɗa masa kai
"To tashi katafi, Allah yamaka albarka".
Ciki-ciki ya'amsa yamiƙe yafita daga parlour'n, girgiza kan sa Dad yayi yana ɗaukan Jaridan da yake karantawa yace
"Wannan yaron in ba haka nayi maka ba, to naga alaman ba auren ne a gaban ka ba, in ba ma rashin wayau ba ya zauna har War haka be yi aure ba".
Shi kam Khalil daga fitan shi ɗakin Mom yashige, tana zaune a gefen gado tana gyara drowan ta data hargitsa tana neman sarƙan da zata saka, yashigo fuska a turɓune hannun sa cikin aljihu, ɗago kai tayi tana kallon sa, sai da takaranci yanayin sa kafin tace
"Yah ya Me yafaru ne? Me Dad ɗin naka yafaɗamaka naga fuskar ka ta sauya?"
Ahankali yatako yazo kusa da ita yazauna kafin yasoma magana ciki-ciki
"Wai Dad ya bani nan da bayan gama Shari'a na da Alhaji Mubarak in fito da mata, sai kace neman matan sauƙi ne dashi".
Murmushi Mom tayi tana riƙo hannun sa ɗaya da yaciro su daga aljihu yaɗaura saman cinyoyin sa yadunƙule su
"Haba My Son ya zaka ga laifin Dad ɗin ku? Ai ni inaga ya baka lokaci sosai tunda ba yau yasaba maka maganar ba?"
Kallon ta yayi yace
"Mom kwanaki ne fa suka rage? Meyasa bazai ƙara min zuwa nest year ba?"
Hannu taɗaura a saman kan shi tana shafa baƙin gashin sa da yasha gyara yakwanta luf gunun sha'awa tace
"Wai to menene na tada hankalin ka ne Son? inace Kai ɗin me farin jinin ƴan mata ne, duk wacce kazaɓo acikin matan da suke son ka da gudu zata aure ka, ko acikin Family ne sai kazaɓa ɗaya kaga hakan ma sai yaƙara mana ƙarfin Zumunci, don ban faɗa maka bane kwanaki ma Hajja Mero tazo har nan, takawo min maganar ƴar ta Shukra, me zai hana a haɗa auren ku tare, kaga in ka amince kawai sai in Kira ta in sanar da ita, cikin lokaci ƙanƙani sai ayi komi a gama ko ba haka ba?"
Kwaɓe fuska Khalil yayi yace
"Wai menene haka Mom, ya na kawo miki magana don ki rarrashi Dad yaƙara min time kuma kike mayar da hannun agogo baya? Ni in rasa ma waɗanda zan aura sai yaran nan da basu da kunya, kullum idanun su a tsatstsaye kamar zasu cinye mutum, ina Allah yakyau wlh". Yaƙarike maganar kamar yaga abin ƙyama
Dariya Mom tayi tace
"Ban da abin Auta to menene laifin su? Kuma menene laifin wanda ke son ka, in ma kana tunanin sun yi maka yara ne ai naga hakan kuka fi so yaran zamani, kuma sun fi daɗin zama ai, zaka ji daɗin zama dasu wlh".
"To ni Mom bance miki Ina son yara ko manya ba, Ni kawai har yanzu ban ga wacce nake ƙauna bane, and Mom kuma ki dena maganar yaran nan ma kar suji su ce zasu raina ni".
Mom tace "to shikenan na daina Autana, yanzu dai katabbatar ka samo matar da zaka iya zama da ita tun kafin Dad yazaɓo maka".
Marairaice fuska yayi yana faɗin
"Yanzu Mom baza ki roƙe sa ba?"
"Kasan halin Dad ɗin ka, in yariga yaba ma mutum dama kasan bazai saurare shi ba, don haka kawai kayi abinda yace maka, but insha Allahu dai zan yi masa magana yaƙara maka lokacin yanda zaka samo min suruka me kyau da hankali kamar kai, wanda take ƙaunar ɗana kuma takula min dashi sosai".
Murmushi Khalil yayi yace
"Mom kenan, to amma dai bari ince ameen".
mom dariya tayi tana jan kumatun sa tace
"Ja'iri kawai, kana so kana kai wa kasuwa ko?".
Shima dariya yayi kawai yana sosa kan shi
"To tashi kaje kar kayi late da yawa, kaga har 08:00am. Ta kusa".
"Ok Mom".
Sai da yayi mata peck a cheeks ɗin ta kafin yamiƙe yayi mata sallama yafice, har yakusa isa ƙofar da zai fita daga Parlour Nazeefa tafito daga kichen riƙe da plate a hannun ta, tana hango shi takira sunan shi
"Yaya".
Har yariƙe handle ɗin ƙofan yajuyo yana kallon ta, saurin ɗauke kan ta tayi daga kan shi ganin kallon da yake mata, ita kan ta batasan me zatace mishi ba takira shi, sai dai kuma bataso yatafi batare da ya ganta ba, ko da magana ce yahaɗa su
"Ina kwana Yaya". Tace dashi tana ɗago kan ta takalle shi
"Lafiya, ya jiki?"
"Alhamdulillah Yaya".
Fita kawai yayi batare da yasake furta ko kalma ɗaya ba, ita kam murmushi tasaki tana jin daɗi a ranta, juyawa tayi tanufi ɗakin ta.
Lokacin da ya'isa yayi parcking yafito, ahankali yake tafiya har ya'isa office ɗin sa, har yakama handle ɗin ƙofan zai murɗa sai yakalli setting office ɗin Billy dake rufe, taɓe bakin shi yayi kawai yashige office ɗin sa yamayar da ƙofa yarufe, ahankali ya'isa jikin window yana saka hannu ya yaye cooten ɗin, gyara tsayuwan sa yayi yasanya hannayen sa cikin aljihu yana ƙure waje da idanu, a zahiri titi yake kallo but a baɗini tunanin mafita yake yi, tsawon mintuna yana wajen kafin yataka yanufi kujera yazauna, buɗe computer'n sa yayi, sai kuma yadunƙule hannun sa biyu yaɗaura a haɓar sa yaci gaba da tunanin sa
Nocking Brr. Tahir yayi yashigo, har yazauna Brr. Khalil be san ya zauna ba, sai da yakaɗa masa hannun sa a setting face ɗin sa tukun yaƙyafta idanu yana kallon shi
"Wai tunanin me kake yi ne har nashigo baka sani ba?"
Ajiyan zuciya Brr. Khalil yayi yana gyara zaman sa yace
"Wlh Dad ne yake son tada min da hankali".
"Me yafaru?" Brr. Tahir yatambaye sa
"Wai cewa yayi nan da lokacin da zamu ƙarƙare Shari'a nafito da matar da zan aura, ko wa yace mishi na damu da auren yanzu, kawai zai jagula min lissafi wlh".
Dariya Brr. Tahir yayi kana yace
"Wlh kana bani mamaki Ib, wani lokacin har tunani nake yi ko dai ba lafiyanka ƙalau ba, ni a ganina kai kakeso katakura kan ka but ban ga aibun Dad anan ba".
"To me kake nufi kenan?" Khalil ɗin yatambaye sa yana ɗaure fuska
"No babu komi, but ni dai shawaran da zan baka kafitar da wata cikin matan da suke ƙaunar ka, ko da kai ba ka ƙaunar ta".
Khalil yace "kana nufin kenan in yi auren rashin ƙauna?"
"Eh mana tunda har yanzu baka sami wacce tayi maka ba duk acikin matan da suke son ka, ba mamaki kai irin mazan nan ne da basu gane meye so sai lokacin da suka auri matar, sannan alokacin zasu gane sun faɗa tafkin ƙauna".
Shiru Khalil yayi yana tunani
Brr. Tahir yace "kar ka matsa ma kanka Ib, me zai hana ka amince wa Billy, tunda ita kaɗai naga alaman zatafi dacewa da kai, kuma kai kan ka sheda ne yanda take matuƙar ƙaunar ka, zata iya yin komi sabida kai, don haka kawai kaba ma zuciyar ka dama takoyi son ta kafin zuwan lokacin, idan har kaji zuciyar ka bata kwanta da ita ba zaka iya sauya wa".
Still dai shiru Khalil yayi yana nazarin maganganun Brr. Tahir ɗin, kuma daga baya sai yace
"Shikenan zan yi tunani akai".
"Ok".
Daga nan tattauna wa sukaci gaba da yi kafin Brr. Tahir yatafi yabar shi, shi kuma yaci gaba da aiki har zuwa lokacin tashin shi, ahankali yamiƙe cike da gajiya yatattara kayan sa yafice, a hanya suka haɗu da Brr. Tahir har suka ƙarisa wajen motan su
Brr. Tahir yace "yau baka tambayi mutumiyar ka ba? Kuma kana gani yau ɗin baka ganta ba".
Ɗan taɓe fuska kawai Khalil yayi yabuɗe motan sa yana shirin shiga, riƙo murfin motan Brr. Tahir yayi yace
"Kenan baza ka tambaya ba ko?"
"To tunda kayi ninyan faɗa min menene kuma sai na tambaya?" Khalil ɗin yafaɗa yana tsare shi da idanu
Murmushi Brr. Tahir ɗin yayi yace
"Gaskiya baka da dama Abokina, in ba ni ba babu wanda zai iya da halinka".
Harara Khalil yayi masa kamar wani mace yace
"Tunda gani me baƙin hali ko? Dole kace babu wanda zai iya dani".
Dariya yayi yana rufe bakin sa yace
"Rufa min asiri don Allah wasa nake maka, but seriously Billy ɗin ka bata da lafiya fa, yanzu nima nake ji wajen Brr. Kuma".
Wani irin kallo Khalil yayi masa, be ce komi ba yajanye murfin motan sa yarufe, leƙo da kai Brr. Tahir yayi yace
"Bakace komi ba zaka tafi?"
"Me kake so nace maka Umhm?" Khalil ɗin yafaɗa yana ma Motan keey
"Muje mu gaishe ta mana, kaga daga nan sai kashigar da kanka ka gane ai". Brr. Tahir yace hakan yana dariya ƙasa-ƙasa
Gajeran tsaki yayi tare da jan motan sa yayi gaba, shima dai Brr. Tahir ɗin motan sa yanufa yashiga yana ci gaba da dariya tare da girgiza kan sa.
[9/18/2020, 9:47 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 24*
Lokacin da ya'isa gida yayi parcking motan sa, sai da yayi kusan mintuna 5 kafin yabuɗe motan yafito, ahankali yake takawa har yashiga cikin gidan, akan sofa yazube yana kwantar da kan sa cike da gajiya, dafe goshin sa dake ɗan sara masa yayi yana lumshe kyawawan idanun sa, few minutes ago yacire hannun yana tashi tsaye yanufi ɗaki, koda yashiga wanka yasoma yi sabida yaji ƙarfin jikin sa, don sosai yake jin sa kamar an mishi dukan tsiya, bayan ya shirya cikin brown ɗin jallabiya da Three qweater sai yafito parlour yanufi kichen kai tsaye, shiru yayi yana tunanin abinda zai dafa, don sosai yagaji da cin indome, kuma so yake yaci abu me ɗan nauyi coz yunwan dake ƙwaƙulan sa, tea yafara haɗawa yazauna nan kichen ɗin yashanye cikin ƙanƙanin lokaci, kana yasoma girka makaroni, shi ba wani ma'abocin iya girki bane don be taɓa yi ba in banda indome da yake dafa wa, but haka dai yayi karanbanin sa yasoma ƙoƙarin girka wa, sai da yaɗaura tukunya a wuta sannan yakurma ruwa rabin tukunyan, yana soma zafi yaɗauko makoroni biyu yasake, don yana son yagirka ne har dare yahuta da ɗame-ɗame, bayan ya sake ne sai yaɗauko Maggi yazuba sannan yaɗauko kayan miya, blanda yaɗauko yasoma yunƙurin blanding ɗin sa, lokacin duk zufa ya ishe shi hakan yasaka yatashi yafice, rigan jikin sa yacire yajefa saman sofa, yadawo daga shi sai singlate ajikin sa yasoma blanding kayan miyan, bayan ya gama duk yasake cikin tukunyan, yazauna nan yana jiran yanuna, gaba ɗaya ya manta da cewa ko mai be zuba ba, sai da yabuɗe yaga yana ta zaɓarɓaka yatuna ai be zuba mai ba, ɗauko wa yayi yadiddila yamayar yaci gaba da zama, sai da yabashi good 30min kafin yabuɗe, lokacin tuni ya nuna sai dai ruwa da yayi yawa hakan yasaka yacaɓe, but be damu ba yaɗauko plate yaɗiba yarufe sauran, ɗauka yayi yafito yanufi saman dainnig ya'ajiye, sai yaje yaɗauko Faro water da kwalin Juice yadawo yazauna, spoon yaɗauka yana kallon abincin, kamar baya son ci sai kuma yasaka spoon ɗin yaɗiba yakai bakin sa, taunan farko yadakata yana taɓe baki, ahankali kuma yaci gaba da taunawa har yahaɗiye, kana yasoma tsakalan abincin kaɗan-kaɗan yana ci, ko kaɗan babu daɗi but yakasa dena ci sabida yunwan da yake ji, yayi dana sanin dafa wa, da tun farko yayi indome'n sa da tuni yacinye lafiya lau duk da ba wani iyawa yayi ba, but yafi wannan jagwalgwalon, sai da yaji cikin sa yasoma murɗa masa yana mishi ciwo kafin yamiƙe yaɗau plate ɗin yakai kichen tare da sake sauran cikin tukunya
Parlour yadawo yazauna yana ɗaukan wayan sa dake ajiye yasoma latsawa, ahankali yatsai da abinda yake yi yana nazarin abinda yake son aikata wa, tsawon minti 3 kafin yaci gaba da latsawa sannan yakara a kunne
"Assalamu alaikum".
Jin muryan ta a cikin kunnen sa yasaka shi lumshe idanun sa yana gyara zaman sa tare da ɗaura kan sa saman kujeran
"Wa'asalaikis Salam". Ya'amsa mata cikin cool voice ɗin sa me daɗin sauraro
Shiru ne yabiyo bayan amsa sallaman nasa, domin ita a fannin ta mamaki ne yakusa kashe ta, abinda bata taɓa gani ba ko da a mafarki ne wai Brr. Khalil zai kira ta.. katse mata tunanin ta yayi da faɗin
"Baki iya gaisuwa ba?"
Bilkisu da rawan baki tace
"Ina yini?"
"Lafiya, ke fa yakike?"
Tace "lafiya lau".
"Ke da akace min baki da lafiya kuma shine kike Son yin min ƙarya?"
Batasan sanda tasaki murmushi ba cike da tsananin farin cikin da yakusa kashe ta tace
"Ai naji sauƙi, dama zazzaɓi ne".
Taɓe baki yayi sai kuma yagyaɗa kan sa, still kuma yace
"Ai naga alama tunda gashi kina min dariya".
Kamar yana ganin ta tayi saurin rufe bakin ta tana faɗin
"Wlh ba da kai nake yi ba".
"To da wa kike?" Yatambaye ta yana wani rage murya
Bilkisu ta kasa magana fa, sai kace ba abinda take nema bane yasamu amma kun ji tayi gumm kamar munafuka
"Kin yi shiru kuma? Ko bazaki faɗa min ba?"
"Uhm babu kowa".
"Ok dama nakira naji jikin ki ne, tunda kin sami sauƙi naji daɗi, bye".
Be jira cewar ta ba yakatse wayan.
Ita kam Bilkisu tana jin yakashe kiran sai tawani kurma ihu tana burgima saman gadon ta, Allah yasa ita kaɗai ce a gidan da har waje sai an ji
"Wayyo Allana yau daɗi zai kashe Ni, wai Ib ne yakira ni? Wayyo ko dai mafarki nake yi?"
Sai tamiƙe daga kwancen da take tana rarumar wayar ta taduba, washe baki tayi ganin dai ba mafarki bane, kwanciya takuma yi tana rarumo pilow tamatse tana cewa
"Wayyo daɗi kashe ni, wayyo ni Billy yau duniyar ta kai min inda nake so, gaskiya yau na kasance me Sa'a, wayyo Allana Wayyo Allana wa zai taya ni farin ciki?"
_(Ni kam nace *NAFEESA GROUP FAN'S* su taya ki, ko kuma *BRR. IBRAHIM KHALIL FAN'S* don Ni dai ban da lokacin ki lol😅 💃💃)_
Shi kuma da gama wayan miƙe wa yayi yaɗau rigan sa yasaka kafin yashige ɗaki, alwala yaɗauro yafito yanufi masjid, bayan ya idar da sallah yafito yakamo hanya, gab da yakusa isa gidan sa yahango Kausar tafito daga gida, tana sanye ne cikin wata Farar riga me dogon hannu zuwa cinyan ta, sai wani burgujejen wando Three qweater me manyan aljihu kalan Orange 🍊, sai tasanya hula facing cap shima kalan wandon, kitson da tayi guda biyu jelan tazubo shi gefe da gefen kafaɗan ta, tunda itama tahango shi tanufo shi da murmushi a fuskar ta, tana iso wa wajen sa tace
"Yanzu nake tunanin ka a raina sai ga ka".
Yanda tayi maganar ne yasaka shi ɗan murmusawa yace
"Zaki bani wani abu ne?"
Sai ta langaɓar da kan ta tace
"Eh in dai kana so".
"Why not?" Yafaɗa yana waro idanun sa
Sai tayi murmushi kana tace
"Dama ina so muhaɗu ne kawai, coz akwai tambayan da zan maka".
Be ce mata komi ba sai dai ƙure ta da idanu da yayi, yana jiran abinda zatace
"An bani labarin kuna Shari'a da wani Alhaji Mubarak mai kuɗi, and nan da five days zaku koma Court, shine zan iya zuwa muyi hira akai, ina nufin ina son nasan komai". Taƙarike maganar tana ɗan kwantar da murya tare da ƙifƙifta idanu
Shiru yayi still har yanzu idanun sa akan ta, sai tasake cewa
"Please kaji?"
"Ok". Yafaɗa ataƙaice yana ɗage kafaɗa
"Tom gidan ka zamu je yanzu ko?" tayi maganar cike da zumuɗi
"No kibari zuwa gobe sai kizo".
Daga haka yayi gaba, ita kuma tatsaya nan tana kallon shi har yashige, sai tasaki murmushi tanufi wajen gidan su tatsaya, dama abinda yafito da ita kenan shan iska, a cewar ta gidan yayi mata zafi, tana nan tsaye tana kallon tsare-tsaren gidajen mutane tana tunane-tunanen ta, wayan ta yasoma ringing, cirowa tayi cikin aljuhu takalli fuskar wayan, sunan HONEY ne yafito ɓaro-ɓaro hakan yasaka tasaki murmushi tana amsa call ɗin, tajuya tashige gida.
........ ........... ..........
Washe gari wajen ƙarfe 03:30pm. Kausar tashigo gidan Khalil, yau tana sanye cikin wata doguwar riga ce mare nauyi red colour, sai ɗankwalin shi da tayafa akan ta kawai, tansaya Hill shoes a ƙafafun ta, tana riƙe da wayan ta iPad fara, nocking tasoma yi amma shiru, hakan yasaka taci gaba da yi babu ƙauƙautawa, tafi minti goma a wajen tana nocking, sosai tagaji but kuma taƙi tafiya
A ciki kuwa tun da yadawo aiki yakwanta barci, sama-sama yake jiyo nocking ɗin daga ɗakin sa, ahankali yabuɗe idanun sa yana sake jiyo nocking ɗin, tsaki yaja yatashi zaune yana miƙa, sai da yafi 3min a zaune kafin yamiƙe yafito daga shi sai baƙar singlate ajikin sa, da gajeren wando yellow, ƙofan yabuɗe suka haɗa ido da ita, dasauri tasad da kai ƙasa tana jin matsananciyar kunya, cikin sanyin murya tace
"Sorry ban san kana barci bane, bari in koma zan dawo".
"Kishigo". Abinda yafaɗa kenan yajuya yashige ɗakin sa
Sai da taji ƙaran rufe ƙofa tukun taɗago kan ta, leƙawa tasoma yi kafin tashiga, saɗaf-sadaf haka take tafiya kamar wata munafuka, har ta'isa kan kujera tazauna tana kallon parlour'n, sosai tsarin gidan yayi mata kyau, har yaso yafi nasu duk da su ma nasu yana da kyau, but wannan komi kakalla kasan ba ƙaramin abu me tsada bane, sosai aka kashe kuɗi cikin parlour'n duk da ba wani kaya ne a ciki ba, tana nan tana kalle-kallen ta kamar wacce bata taɓa ganin irin sa ba, yafito sanye da riga me ruwan zuma da zane-zanen fari ajiki, sai wando Three qweater fari, ƙariso wa yayi yazauna a kujeran dake facing ɗin ta yana kallon ta, ɗago kai tayi itama tana kallon shi tace
"Ina yini?"
"Lafiya". Ya'amsa ataƙaice yana jingina bayan sa da kujera yalumshe idanu
Ita kuma sai tatsaya tana kallon shi cike da burgewa, komi nasa me kyau ne, yana da matuƙar kyau da kwarjini, babu macen da zata gan shi batayi fatan samun shi ba, buɗe idanun sa yayi yasauke a kan ta, sai tawayan ce takau da kai
Yace "me zaki sha?"
Sai tamaida idanun ta kan sa, kamar bashi yayi maganan ba
"I'm ok". Tace dashi tana mayar da idanun ta kan wayan ta da taɗaura saman jikinta, tasoma latsawa kana tace
"Ko zamu iya farawa?"
"Ok".
Daga nan yasoma bata bayani akan komi, har zuwa sanda suka gama yamiƙe yanufi hanyan kichen, wata iriyan yunwa yake ji, komi be saka a cikin sa ba tun tea ɗin safe, kuma da yadawo barci sosai yarufe masa idanu sakamakon jiya be yi ishashshe ba
Yana tsaye cikin kichen ɗin yana ƙoƙarin ɗaura tukunya, yaji muryan ta a bayan sa
"Me zaka dafa?"
Juyowa yayi yana kallon ta, don be tsammaci zuwan ta ba, murmushi tayi masa tatako ta'iso wajen sa tana faɗin
"Kaje sai in yi maka girkin".
Tayi maganar tana ɗaura hannun ta saman tukunyan tana gyara mishi zama
Babu musu kuwa yajuya yatafi, be san meyasaka yarinyan take son shige masa ba, but ko kaɗan ba ta bashi haushi sai burge shi da take yi, yana nan zaune a Parlour yana kallo har tagama tazubo mishi, a gaban shi ta ajiye saman Centre table tace
"Bismillah ko". Tayi maganar tana kallon sa da murmushi a face ɗin ta
Shima kallon ta yayi sai yakalli abincin, taliya ne me manygaɗa da yaji cUrry da yankakken ƙwai a sama, murmushi yasaki yace
"Thank you, kema ki zubo naki kici".
Yarfe hannun ta tayi tace
"No ni na ƙoshi, ina sauri akwai inda zan je".
Gyaɗa mata kai kawai yayi, sai tajuya tatafi shi kuma yabi ta da kallo, sai da takai bakin ƙofa tajuyo tana kallon sa taɗaga masa hannu sannan tafice.
[9/23/2020, 7:28 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 25*
*FEW DAYS*
"My dear kiyi sauri Kar kiyi late kuma?"
Halwa dake cikin ɗaki cikin sanyin murya tace "to Yaya ga ninan".
Fitowa tayi riƙe da Bairo a hannun ta tana kallon yayan nata, shima kallon ta yake yi cike da tausayin ta, gaba ɗaya duk ta rame sabida zazzaɓin da yasako ta agaba kwana biyu, tayi haske kallo ɗaya zakayi mata kagane sosai take cikin ciwo, itama Mama dake zaune kallon ta tayi tace
"Ni kuwa idan ba yazama dole bane Halwa a fasa zuwa makarantan nan mana, kinga yanda kika yi kuwa? Ba fa sauƙi kika ji ba?"
Kallon Maman tayi kawai tana marairaice fuska kamar zatayi kuka
Nura yace "Mama wannan jarabawan fa tana da muhimmanci tunda na fita ne, haka nan zata lallaɓa tayi har su kammala, kinga jiya ma taje tayi tadawo lafiya, zaki ga sauran ma kamar yanzu ne har an gama".
"Um um Nura, yau kaduba kagani sosai take jin jiki ko abinci ta kasa ci, ga wahalan da zataje tasha, me zai hana abari wani shekarar sai tarubuta".
Nura yace "kai Mama har shekara sai tayi ta zama agida? Kema kinsan halinta ba yarda zatayi ba".
Halwa tace "Mama ki dena maganar nan ma, kuma Ni haka nan zan je in zana jarabawa ta, sai dai in ciwon ya kwantar dani ne amma banga abinda zai hana ni zuwa ba".
Murmushi Nura yace "to kin ji dai".
Kaɗa kai Mama kawai tayi tace "ai shikenan Ni dama tausayin ki nake ji, yanzu ku hanzarta kutafi kar lokaci yaƙure".
Fita suka yi, A mashine ɗin Abokin Nuran yakai ta har cikin makaranta, yasauke ta a bakin ajin su.
Bayan kamar mintuna 20 aka zo raba musu pepper, lokacin ne kuma sosai jikin Halwa yayi tsanani, jikin ta sai kakkarwa yake yi zazzafan zazzaɓi yarufe ta, kasancewar mutum ɗaya-ɗaya ake zama a sit shiyasaka babu wanda ya lura da ita, tana can kusa da baya ajikin bango ta takure waje ɗaya, sai takifa kan ta a table tana hawaye, ita kan ta takasa jure yanayin da take ji, sai da Wani Malami yazo miƙa mata Pepper yakira sunan ta
"Halwa lafiyan ki lau kuwa? Za'a yi jarabawa kina kwance".
Ahankali taɗago kan ta tana ƙanƙame jikinta, face ɗin ta duk hawaye, kuma sai rawan ɗari take yi
"Subhanallah.. baki da lafiya ne?" Malam ɗin yafaɗa yana kallon ta
Gyaɗa masa kai tayi don takasa magana ma
"To yanzu ya za'a yi kenan? Zaki iya yin jarabawan?"
Shiru tayi bata iya cewa komai ba, su kuma ƴan ajin yawancin su hankalin su na wajen, har da Zainab aciki, duk tausayin Ƙawartan ya kamata, ɗaya daga cikin Malaman dake tsaron su yace
"Ku me kuke kallo ne baza kuyi abinda ke gaban ku ba?"
Sai kowa yamayar da kan sa ƙasa suka soma duba peppern, Malam Isma'il dake can bakin ƙofan yace
"Ai kabar su Malam Kamal, time na cika amsa zamuyi mu wuce".
Malam Jamilu dake tsaye har yanzu kan Halwa still yace da ita
"Halwa ko dai bazaki iya bane? In ciwon yayi tsanani kije ki amso magani kisha kinji?".
Cike da ƙarfin hali tace "zan iya Malam".
"Ok to gashi".
Aje mata yayi a gaban ta, yaja gefe nan yana kallon ta tare da kula da waɗanda suke wajen, ita kam ahankali tajanyo pepern ta'aza Bairo akai, tayi shiru ta kasa rubuta komi, sai da tayi kusan mintuna 5 kafin tasoma rubuta sunan ta daƙyar, bayan ta gama tasoma amsa Questions ɗin, Number One taɗauka tafara dashi, ahankali tatsayar da hannun ta daga rubutun da take yi tana runtse idanu, wannan karon jikinta sosai yake rawa har da hannun ta, Malam Jamilu dake tsaye yana kallon ta yace
"Gaskiya bazaki iya wannan jarabawan ba, tashi kije kisha magani, inyaso sai asamo wani yarubuta miki".
"Halwa". Malam Isma'il da yaƙaraso wajen yakira sunan ta
Zuwa lokacin kuka take yi kan ta a ƙasa ta kasa amsawa
Yace "wai meke damunki ne? Ciwon me kike yi sai a amso miki maganin?"
Still shiru babu amsa sai kukan ta dake daɗa ƙaruwa
Malam Jamilu yace "Zainab taso kije da ita tasha magani".
Dasauri Zainab tataso tataho wajen tariƙo Halwa dake langaɓe wa, ta rufe fuskarta still tana kuka, suna fita tasoma sheƙa amai kamar zata amayo hanjin cikin ta, sabida babu komi a aman kasancewar bataci abinci ba, nan da nan hankalin Malaman yatashi suka fito waje suna mata sannu
Malam Kamal yace "gaskiya wannan ciwon be kamata abarta anan ba, yakamata amaida ita gida".
Malam Isma'il yace "Eh haka za'a yi kuwa, tunda nasan gidan su bari inje in kai ta".
Daga haka yajuya dasauri yanufi inda suke parcking yaburgo mashine ɗin sa yataho wajen, da taimakon Zainab aka ɗaura Halwa akan mashine ɗin, zuwa lokacin duk ta galabaita bata ma iya tsayuwa
Malam Jamilu yace "Zainab kihau bayan ta kuje tare, sai ku dawo tare da Malam Isma'il".
"To Malam". Cewar Zainab kenan, kana tahau bayan mashine ɗin
Sai da sukaga tafiyar su kafin Malaman suka koma ciki.
Koda suka isa gida bayan sun sauka, Zainab tariƙo ta suka shiga cikin gidan, Mama na ɗaki tana kwance tajiyo sallaman Zainab, amsa mata tayi tana tashi zaune, ahankali suke tafiya har suka isa bakin ƙofar Maman, Zainab taɗaga musu labule suka shige
"Subhanallah.. lafiya Zainab me yafaru da ita?" Mama tafaɗa tana tashi tsaye cike da ruɗewa
"Mama wlh jikin ta ne yayi tsanani, shine Malaman sukace adawo da ita gida".
Mama tariƙo ta tana zaunar da ita saman gadon ta, kana tace
"Dama tunda naga jikin nata da tsanani na san bazata iya taɓuwa komi ba, sai dai taurin kanta ya saka taƙi haƙura, gashi an dawo dake ai".
Zainab tace "Mama bari inje, Allah yaƙara lafiya".
"Ameen ameen Zainab, mungode kinji?"
Zainab na fita, Mama tazauna gefen gadon tana kallon Halwa da har yanzu take rawan sanyi tana kuka tace
"Yanzu kuma da ina da ina yake miki ciwo inje nasiyo miki magani? Kamar ma amai kika yi ko? Don gashi duk kin ɓata Hijabin ki".
Tana sauke maganar ta Halwan tasoma kwarara wani aman daga kwance, dasauri Mama tariƙe ta ganin zata faɗo daga kan gadon, sai da tagama aman kafin tasake ta tana faɗin
"Oh Ni Hauwa, gaskiya ban ga tazama ba dole muje asibiti, tashi tashi muje kiwanke jikin ki mutafi asibiti, Allah dai yabaki lafiya ƴar nan, wannan ciwo haka".
Da taimakon Maman suka fito waje, taje taɗibo ruwa a botiki ta'ajiye a gaban ta, ita da kan ta Maman taɗauraye mata jikin takaita har ɗaki, kana tazaɓo mata wasu riga da wando na Pakistan, rigan Light and Dack Orange 🍊 colour ne, sai wandon kuma dack orange ne da ɗankwalin
"Gashinan ki saka, bari inzo". Mama tafaɗa tana ficewa
Ahankali Halwan tatashi tasaka kayan, sannan tasanya ƙaramin Hijab Baƙi tafito, itama Mama lokacin ta sanyo Hijabin ta suka fice.
Lokacin da suka isa asibiti minti goma suka ɗauka kafin sukaga likita, bayan sun shiga office ɗin sun zauna ne Doctor ɗin yasoma mata tambayoyi tana amsa mishi, har sanda yagama sannan yakira Wata Nurse yace "taje da ita tayi mata gwaje-gwaje". Bayan kamar mintuna 20 sai gashi sun dawo tare da Nurse ɗin, sakamakon Nurse tabashi sannan tafice, bayan ya amsa ya gani yayi rubuce-rubuce sannan yaɗago yana kallon su
"Am Mama.. a binciken da mukayi mata, sakamakon ya ba mu tana ɗauke da ciki har na wata ɗaya da sati, kuma sannan.."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Ci..Cikiii?".
Mama tafaɗa da ƙarfi tana kallon Likitan da shima yadakata yana zuba mata nashi idanun
"Haba dai Likita kasake dubawa kagani sam ban yarda ba, ciki fa kace? Ciki Halwa take dashi? Ina sam ƙarya ne wlh".
Halwa kuwa tun sanda kalman cikin yadaki kunnen ta, atare zuciyarta da ƙwaƙwalwan ta suka amsa, tsananin tsoro da firgici yabayyana a fuskarta har sai da komi dake motsi a jikin ta yadena aiki na tsawon wasu sakonni kafin tadawo dai-dai, sai kuma tazamo saman kujeran da take kai tazube ƙasa jikinta na wani irin kyarma tana shatatar da hawaye.
.
_To ya kukaji FAN'S?_
_Ya za'a kaya?._
_Me zai faru?._
_Hmm yanzu aka fara muje zuwa._
0 comments:
Post a Comment