"Halwa me kike yi anan? Me yafaru ne?"
Bata ɗago kai ba sai ma ƙara volume ɗin kukan ta da tayi, nan da nan jikinta yasoma rawa kamar an sakata a shocking, Nura zuwa yayi yariƙo ta yana faɗin
"Lafiya Halwa? Menene haka wa yabige ki?"
Still shima shiru tayi masa
Baba yace "Nura taho da ita mushiga gidan sai muji ba'asi wajen Maman taku".
Riƙo ta kuwa Nura yayi, babu musu tabi shi suka shiga ciki, ɗakin Mama suka nufa gaba ɗayan su, Mama na zaune tana faman hawaye suka shigo, abinda yaƙara ɗaure musu kai kenan suka hau tambayan ta "lafiya?" Hankalin su duk atashe, but Mama taƙi tayi magana sai Hawayen ta take yi, zama Baba yayi gefen ta yayinda Nura ma yasamu waje yazauna yajanyo hannun Halwa itama tazauna kusa dashi
Baba yace "wai Hauwa lafiya muka ganku a wannan yanayin? Meke faruwa ne kiyi mana bayani?"
Ɗago kan ta tayi cikin baƙin ciki tace
"Wani bayani kakeso kaji Baban Nura? Ace wai yau Halwa ce tayo mana ciki agida, cikin shege fa Halwa tayi a gidan nan". Sai tasake fashewa da kuka
Atare Baba da Nura suka maimaita cikin Shegen, Nura har da ja da baya yana matsawa kusa da ita, cikin kaɗuwa Baba yakalli Halwa da har yanzu takasa buɗe idanun ta yace
"Dagaske ne cikin Shege kikayo min agida?"
Shiru Halwa tayi
"To ya za'a yi tafaɗa maka? yanzu muka dawo daga asibiti likita yatabbatar mana tana ɗauke da cikin Shege acikin ta, to wlh tallahi ba dai nan gidan ba, bazai taɓa saɓuwa ki haifa mana ɗan Shege agidan nan ba, duk gatan da mukayi miki Halwa kikasa saka mana da abun kirki sai abun tsiya? ashe duk zaman da muke yi dake amanar mu kike ci mu duk bamu sani ba? To baza mu ga wannan abun kunyan ba dole ki koma can dangin mahaifin ki tunda bakisan halacci ba, na rabo ki da can ne don naga kina shan wahala amma kin nuna mana ke ba mutumiyar arziƙi bace".
Baba ya'amshe zancen cikin sauri yace
"Ni Malam Ayuba za'a zubar min da mutunci agida? da ƙima ta da daraja ta yau za'a haifa min shegen ciki?"
Halwa kuwa in banda kuka babu abunda take yi, sosai zuciyarta takaɗu da kalaman Maman nata, "wanna wace irin baƙar rana ce tazo mata?" Meyasa duniya take son juya mata baya?"
Baba yaci gaba da faɗin
"Kin bani mamaki Halwa kinci amanar yardan da mukayi miki, kina son ki zubar mana da mutunci duk yanda ake ganin mu a gari sai gashi ace za'a haifi ɗan Shege a gidana, to ba dai nan gidan ba dole kibar min gida, iya zaman da kikayi agidan ma ya isa haka, kitashi kiwuce kije kihaɗo kayan ki tun kafin wasu suji, in kin shirya kizo ki amshi kuɗin mota".
Ɗago kanta Halwa tayi da idanuwanta suka kaɗa sukayi jazur sukayi luhu-luhu, cikin tsananin kuka tace
Don girman Allah Mama kuyarda dani wlh Fyaɗe akayi min, Yaya Nura ma ya sani wlh ban taɓa sanin wani namiji ba.."
Dasauri Nura yace "keeee Halwa sharrin kuma kaina zai koma? Aina nasan anyi miki Fyaɗe? Ke dai kawai kina zuwa makaranta kina yawon banzan ki kin kwaso ciki zakice na sani, kinci amana ta Halwa, kinci amanar soyayya da yardan da nayi miki, Allah ya isa tsakani na dake".
A firgice takalle shi sai dai takasa furta komi sabida zallan mamaki da kuma rawan da bakin ta yake yi, shi kuma Baba cikin ɓacin rai yace
"Halwa wato so kike yi kidangana akan ɗana? Cikin ma sai ki iya cewa shine yayi miki ko?".
Girgiza kan ta kawai take yi tana hawaye, ita har yanzu takasa yarda da cewa Yayan ta Masoyinta shine yajuya mata baya yake faɗan kalman ɓatanci akan ta, takasa yarda Mama da Baba zasu ƙi yarda da ƙaddaran da yasaukar mata
"Ya Allah.. meke shirin faruwa da ni ne? Wayyo Allana ko dai mafarki nake yi?".
"Abinda kika aikata ne yake bibiyanki Halwa, kitashi kiwuce kibar mana gida, wlh nayi imani da Allah da Lubabatu tana raye kika kwaso wannan abun kunyan wlh da sai ta kashe ki". Mama tafaɗi hakan tana sake fashewa da kuka, cikin kukan take faɗin
"Allah mun gode maka da ɗana be auri mazinaciya ba, da yanzu anyi auren shikenan kin cuce shi".
Tsawa Baba yasake daka mata babu shiri tamiƙe tana dafe da kanta dake faman sara mata kamar zai rabe gida biyu tafice, bata iya tsayawa ko ina ba Direct waje tanufa, sabida gaba ɗaya hankalin ta da tunanin ta sun gushe, maganganun Nura kawai suke dawo mata cikin kunne
_"Ke dai kawai kina zuwa makaranta kina yawon banzan ki kin kwaso ciki zakice na sani, kinci amana ta Halwa, kinci amanar Soyayya da yardan da nayi miki, Allah ya isa tsakani na dake"_
Hannu biyu tasanya tatoshe kunnuwan ta tana wani irin kuka me tsuma ran me sauraro, kuka take yi sosai da har yasa bata iya ganin gaban ta, sabida yanda hawayen suke ambaliya kamar an kunna famfo, har yanzu takasa yarda da cewa abinda ke faruwa da ita a yau ɗin gaske ne, so take yi kawai tafarka daga wannan mummunan mafarkin, tasan dacewa Mama, Baba, Nura bazasu taɓa juya mata baya haka ba
Wani lungu tasamu tazauna nan tana ta rizgan kuka har muryan ta yadena fita, sai hawaye da suka ƙi ƙafewa a idanun ta, ta jima a wajen tana son ko wani ne yazo yatashe ta yace mata "Mafarki ne Halwa". Sai dai babu wanda yagibta tun zaman ta, haka tatashi takoma wajen gidan nasu tatsaya tana kallon gidan, idanun ta fal da hawaye, zuciyarta na wani irin bugawa kamar zai faso yafito
_"Kin bani mamaki Halwa kinci amanar yardan da mukayi miki, kina son ki zubar mana da mutunci, duk yanda ake ganin mu a gari sai gashi ace za'a haifi ɗan Shege a gidana, to ba dai nan gidan ba, iya zaman da kikayi agidan ma ya isa haka, kitashi kiwuce kije kihaɗo kayan ki tun kafin wasu suji"_
_Wlh nayi imani da Allah da Lubabatu tana raye kika kwaso wannan abun kunyan wlh da sai ta kashe kiiiiiii"_
_"Wato so kike yi ki dangana akan ɗana? Cikin ma sai ki iya cewa shine yayi miki ko?_
_Ki tashi kiwuce kibar mana gida, ki tashi ki wuce kibar mana gida, ki tashi ki wuce kibar mana gida"_
Maganganun su ne suke ta kai kawo cikin ƙwaƙwalwan ta, Wani abu ne yazo yatokare mata wuya batasan sanda taƙwallara ƙara ba tazube nan tana fashewa da sabon kuka, bata taɓa tunanin ita ɗin marainiya bace sai yau
"Wayyo Allana na shiga uku na lalace, meyasaka zakuyi min haka? Bakusan cewa wannan shine ƙaddara ta ba? Ya zan yi in kauce masa?" Meyasa? Meyasaka Yaya zaka juya min baya bayan kasan komi? Meyasaka ka aikata min haka duk da kasan abun da yafaru agaban ka akayi komi? Shin ko ka manta soyayyar dake tsakanin mu ne? Ka manta ni ce Halwa Halwan ka kuma ƙanwar ka? Dan Allah kafito kaban amsa Yaya, kazo kafaɗa min dalili".
Wasa-wasa Halwa tazama tamkar mahaukaciya a wajen, gaba ɗaya tagama fita hayyacin ta, kuka kawai take yi, kukan da babu hawaye a yanzu bare kuma murya, ta jima anan wajen kuma ikon Allah babu wanda yafito suna can suna jajanta abun da yafaru
Kamar an tsikare ta kuma tatashi dasauri tana saka bayan hannun ta tana share hawaye, nufan hanya tayi tana tafiya tana tangaɗi kamar wacce tasha wu, dai-dai lokacin da ta'iso ƙofar gidan su Zainab tanufi gidan, tana saka ƙafa a zauren sai taja tatsaya, maganganun Baba ne suka dawo mata cikin kunnin ta
_"Kina son ki zubar mana da mutunci duk yanda ake ganin mu a gari, sai gashi ace za'a haifi ɗan Shege a gidana_"
_"Ki tashi kije ki haɗo kayan ki tun kafin wasu suji"_
"Kenan sun gunmaci ni nabar su akan ƙimar su da mutuncin su yazube? Shin bakusan ƙaddara bace? Ashe dama zaku iya korata akan laifin da na aikata bada son raina ba?" Meyasa zakuyi haka?" Tafaɗa afili cikin dashashshiyar muryan ta tana runtse idanu wasu sabbin zafafan hawaye suna gangaro mata
Still hannu tasaka tashare hawayen, tajuya da sauri tatafi, tafiya take yi ahankali har ta'isa bakin titi, tadoshi hanya tasoma tafiya a gefen titin batare da tasan takamaiman inda zataje ba, don ko alokacin ba cikin hayyacinta take ba tafiyan kawai take yi, tana juya baya tawuce sai ga Zainab ta ɗaya side ɗin an wuce da ita a cikin keke Napep.
_Shin ina kuke tunanin Halwa zata je?_
_wani irin hali zata faɗa?_
_mene yasaka Nura yayi mata wannan abun?_
_Shin ko ya manta da ita wacece a gare shi yayi mata hakan?_
_amsan ku na wajena kubi ni asannu don jin Me zai faru hmmmm._
[9/23/2020, 10:00 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 27*
Tayi tafiyan da yakai kusan awanni biyu batare da ta gajiya ba, kuma bata da alaman tsayawa tafiyan kawai take yi but batasan inda take tsulmiya ƙafafuwan ta ba, har sai da taji ƙafafun nata sun soma nauyi suna takawa daƙyar kafin tasamu gefen wani shago tazauna tana sakin nishi, kallo ɗaya kayi mata zaka gane tana cikin wani mawuyacin hali da baza ka iya fassara shi ba, idanunta gaba ɗaya sun wani jeme sun yi luhu-luhu, har alokacin kuma basu gama washe wa daga canza kalan da suka yi ba, hannun ta tasanya tariƙe goshin ta tana runtse idanu, shiru tayi tana sauraron bugun zuciyarta da yanzu yaƙara hauhawa kamar zai faso ƙirjin ta sabida wani irin bugawa da yake yi
Takun takalmi taji da gudu-gudu, hakan yasaka tabuɗe idanun ta tasauke akan sa, shima ɗin itan yake kallo har ya'iso wajen ta, sai yashiga wani lungu da shaguna biyu suka rufe wajen, bata sauke idanun ta a wajen ba kuma bata motsa ba har sai da tajiyo takun wasu mutanen, hakan yasaka tajuya tana kallon su, mutane uku ne da baƙaƙen kaya sun sha Suit, hannun su na cikin rigan su da alamun dai akwai abinda suka ɓoye, har sun gibta ta sai ɗaya yadawo da baya yana kallon ta da fuskar shi a ɗaure yace
"Keee ƴan mata bakiga wani yawuce tanan ba? Ina kikaga yabi?"
Ɗauke idanun ta tayi akan sa tamayar inda taga mutumin nan ya ɓoye, sai taga yaleƙo kan sa suka sake haɗa idanu, kallon ta kawai yake yi da idanun sa masu bala'in kyawu ko ƙyaftawa baya yi batare da ko yayi mata alaman kar tatona shi ba
"Ke magana muke miki fa? Baki ga wani yawuce tanan ba?"
Gyaɗa kan ta kawai tayi tana sauke idanun ta ƙasa, wucewa sukayi batare da sun sake magana ba, sai da sukayi nisa da tafiya kafin yafito, ita kuma taɗago idanu tana kallon sa still shima kallon ta yake yi, sai da sukayi 2min suna kallon juna kafin yajuya dasauri yawuce, kau da kai tayi tana tunanin abinda yasaka mutanen suke neman sa? Sai kuma taruntse idanuwan ta tana jin damuwan ta na dawo mata, hawaye ne suka soma zuba cikin idanun suna gangarowa saman kuncin ta
"Ya zan yi?" Tafaɗa a fili tana wurwurga idanu a hanya
"Wayyo Allah Ni Halwa, Allah na roƙe ka Allah kakawo min agaji, Allah na roƙe ka ya Allah kataimake ni, kataimaki rayuwata, Allah ina buƙatan taimako". Sai tafashe da kuka me ban tausayi
Ɗaura kanta akan ƙafafunta tayi tasoma rerawa, kai daga jin kukan kasan na ƙunci da baƙin ciki ne, ta jima a wannan yanayin kafin tamiƙe tasoma tafiya, alokacin hankalin ta baya jikin ta tana can tana tunanin kalaman Nura tana yi tana sharan hawaye, sosai tadamu ƙwaƙwalwan ta da son sanin meyasaka ya'aikata mata hakan? sai jinta tayi a ƙasa batare da tasan abinda yasame ta ba
"Subhanallah.. don Allah baiwar Allah kiyi haƙuri, wlh bansan kin taho ba nabige ki da motata".
Sai alokacin Halwa taɗago kanta tasauke shanyayyun idanunta kan matashiyar budurwan da aƙalla zata bata shekara ɗaya zuwa da rabi
"Don Allah kiyi haƙuri, muje chemis ayi miki dress ɗin ƙafan kinji don Allah?".
Hakan yasaka halwa tamayar da idanunta kan ƙafanta dake zubo da jini sakamakon ƙurjewan da tayi, but ko kaɗan bataji zafi ba bare tasan taji ciwon, bcoz zafin da take ji cikin zuciyarta da jikinta ya hana taji zafin ciwon, yarinyan taɗago ta suka nufi Motan ta, tabuɗe mata gaba tashiga sannan itama tazagaya tashiga taja motan, Chemis ɗin takaita akayi mata dressing ƙafan sannan suka fito, kallonta yarinyan tayi tace
"Ina ne gidan ku sai in Kai ki ko?"
Shiru Halwa tayi batare da takalli yarinyan ba, kuma bata da alaman bata amsa, ita kuma yarinyan sai kallon ta take yi da alamun tagane tana cikin wata damuwa sakamakon yanda fuskarta yanuna, ga kuma yanayinta, dafa kafaɗanta tayi tace
"Ƴar uwa don Allah kifaɗa min ko wani abu na damunki ne zan iya taimaka miki? Haƙiƙa duk wanda yakalle ki yasan da cewa akwai wani babban al'amari dake damunki, don Allah kisanar dani kamar yanda natambaye ki?"
Sai alokacin Halwa tasake ɗago kai takalle ta a karo na biyu tun haɗuwan su, still dai batace komi ba tasake sad da kanta ƙasa tana jin hawaye na son zubo mata
"Ko baki yarda dani bane?"
Yarinyan tafaɗa tana ɗago haɓan ta, dai-dai da lokacin da hawayen da suka taru a cikin kwarmin idanun nata suka gangaro izuwa saman kuncin ta
"Subhanallah.. kuka kuma? Me yayi zafi ƴar uwa? Don Allah kifaɗa min damuwar ki?" Tafaɗi maganar itama tana son yin kukan
Hakan da Halwa tagani ne yasanya ta motsa baki kaɗan, sai dai yarinyan batasan me tafaɗa ba, don haka tariƙo hannun ta taja ta suka shiga mota, kana tayi wa motan keey tasoma tafiya, shiru babu wanda yayi magana ciki, ita kuma atunanin yarinyan Halwa zata faɗa mata inda zata kaita, saɓanin haka sai taji shiru, hakan yasaka kawai tayanke shawaran tafiya gidan su da ita, don sosai Halwa ɗin taba ta tausayi, haka kawai kuma taji ta kwanta mata arai, kuma nan take tagane tabbas akwai abinda yakorota daga gidan su, ba kuma ƙarami bane babban abu ne
A wani gida me ɗankaren kyau da yalwa yarinyan tatsaya tare da yin hon, babu jimawa aka buɗe mata Gate ɗin takutsa motan ciki, bayan tayi parcking ne tajuyo tana kallon Halwa da itama tabaza idanu tana kallon gidan, ita tun sanda tasaka ta cikin motan tarasa tunanin da zatayi, kawai tatsaya ne taga ikon Allah ina zata kaita, kuma ko kaɗan babu tsoro a fuskarta, domin ita yanzu duk abinda zai same ta idan har wanda zai rabata da duniyar ta ne to tana maraba dashi
"Muje ko?" Yarinyan tafaɗa tana buɗe motan tafita
Babu musu Halwa itama tabuɗe tafito, tabi yarinyan abaya kamar yanda taga ta doshi cikin gidan, bayan sun shiga parlour'n ne yarinyan takalle ta da murmushi a fuskarta tace
"Kizauna bari in Kira Ummina".
Daga haka tajuya tanufi wani ƙofa tana kwaɗa ma Ummin nata kira
Halwa kuwa ƙyam tayi anan tsaye bata da alamun zama, kuma kanta a ƙasa yake batare da taɗago shi ba, babu jimawa yarinyan suka fito tare da wata babban mata me kama da ita sak, sai kuma wani babban mutum da shima suke yanayi da yarinyan, don hasken shi ma tabiyo, atare suka iso cikin parlour'n suna kallon Halwa da itama taɗago idanunta tasauke akan su
"Baki zauna ba? Kizauna don Allah?" Yarinyan tace hakan lokacin da ta'iso wajen Halwa takama hannun ta suka zauna kan 2sitter, su ma iyayen nata zama sukayi duk fuskar su cike da mamaki duk da sun san halin ƴar tasu, Mahaifin nata ne yasoma magana da cewa
"Saleema ina kika samo wannan yarinyan kuma?"
"Abba wlh a hanya ne nabige ta da zan dawo daga school, shine nakaita akayi mata dress".
Sai tamarairaice fuska taci gaba da faɗin
"Kuma Abba naganta cikin damuwa ne shiyasa nace bari in taimaka mata".
Ummee tace "kuma banda abinki Saleema, kinganta cikin damuwa kina son taimaka mata ai gidan su zaki kaita ba nan ba".
Abba murmushi yayi yace
"Ina ruwan ƴar Baba, kinsan halinta da son taimako".
Saleema tace "to Abba ai na tambaye ta inane gidan su bata sanar min ba, shine nakawo ta nan".
Jinjina kansu gaba ɗayan su sukayi suna kallon Halwa da kanta ke ƙasa tana sauraron su
"To ke kuwa Baiwar Allah Aina kike? Ina ne gidan ku?" Cewar Ummi kenan
Shiru Halwa tayi tana wasa da hannun ta don batasan me zatace ba, Abba shima kallon ta yayi yace
"Yarinya ki sanar damu mana, zan saka amayar dake har gida insha Allahu".
Cikin dashashshiyar muryan ta da ba'a ji sosai tace
"Iyayena sun kore ni".
"Saleema me tace ne? Mu bamu ji ba". Ummi tafaɗi hakan
"Wai iyayen ta sun kore ta". Saleeman tafaɗa cike da tausayi
"Subhanallah.. kora kuma?" Abba da Ummi suka faɗa atare
"To me kikayi musu?" Ummi tasake tambayar ta
Sheshsheƙan kuka Halwa tasoma yi tare da rufe fuskarta da Hijab, cike da tausayin ta Ummi tace
"Baiwar Allah kisanar damu abinda ke damun ki, inda hali kibamu tarihin ki, muna Son musan meysaka iyayen ki suka kore ki sabida musan ta inda zamu taimaka miki kinji? Kidena kuka kifaɗa mana damuwar ki".
Riƙo ta Saleema tayi tasoma rarrashinta kamar zatayi kuka, duk fuskarta ya nuna tsananin damuwa, sai da tayi shiru tukun tasoma basu labari kamar haka, tanayi tana kuka.
Ni sunana Halwa, kuma Ni marainiya ce, tun ina ƙarama Mamana da Babana suka rasu, shine dangin Babana da suke garin Gombe suka ɗauke Ni, na taso a hannun su cikin baƙar azaba har izuwa sanda nasoma girma, shine lokacin da ƙanwar Mahaifiyata tazo ganina taga wahalan da nake sha a hannun su taɗauke ni tadawo dani hannun ta, daga nan naci gaba da zama a wajen ta har suka saka ni makaranta, sun ɗauke ni ita da mijinta tamkar ƴar su, sun bani gatan da ko iyayena ne iyakacin abinda zasu bani kenan".
Fashewa tayi da kuka me tsananin gaske, daga nan taci gaba da basu labarin zamanta a gidan da rayuwan da tayi har soyayyarta da Yaya Nura, zuwa iftila'in da yafaɗa mata da abinda yafaru da ita a yau ɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." atare Ummi da Abba suka faɗa cike da tsananin mamaki da al'ajabi
"Dama har yanzu akwai irin waɗannan iyayen da zasu kore yaran su akan ƙaddara ta faɗa musu? Ashe har yanzu akwai marasa imani irin su? Basu tunanin abinda zai faru da ita yarinyan idan har sun kore ta? Meyasa wasu iyayen jahilai ne? Me zai saka su kori yarinyan su don kawai wani iftila'i ta afka mata? Basu tunanin kuma taje tafaɗa hannun ɓata gari? Ko kuma abinda suke gudu na zubewar mutunci taje taci gaba da aikata wa? Sannan kuma daga ƙarshe tadawo musu da abun kunyan da suke gudu? Gaskiya su Mamanki sunyi ganganci sun yi wauta, sun maye ladan su da babban zunubi, Allah bazai bar su ba wlh sai sun yi dana sanin abinda suka aikata miki". Ummi ce take faɗan hakan cike da ɓacin rai
Saleema kuwa me saurin kuka tuni tasoma hawaye sabida tsananin tausayin Halwa
Abba dake ta faman girgiza kai sabida al'ajabi yace
"Tabbas sun yi ganganci sun aikata babban kuskure, amma Allah ai ba azzalumin bawan sa bane kuma shi ke kare duk wanda yaso, sun kore ki don kawai mutuncin su kar yazube, sun gunmaci ke ki wulaƙanta don kawai taki ƙaddaran kenan, amma insha Allahu bazamu taɓa bari ki wulaƙanta ba, mu zamu maye miki gurbin iyayen ki, zamu zame miki haske cikin rayuwan ki, a kuma shirye muke muɗau duk wani ƙaddaran da Allah yaɗaura miki, zamu tayaki yaƙi don kici jarabawan ki, haƙiƙa Allah shi yasan yanda yayi yahaɗa ki da ƴar mu don mutaimake ki, idan har muka bari kika bar gidan nan to tabbas sai Allah ya tambaye mu, ƴata zaki zauna tare damu zamuci gaba da kula dake kamar yanda muke ma ɗiyar mu, kuma insha Allahu duk abinda kike nema bazaki rasa shi agidan nan ba, kiɗauke mu tamkar iyayen ki waɗanda suka zuƙuna suka yahaife ki, mu nan munyi alƙawari zamu share miki hawayen ki".
Ahankali Halwa dake ta faman rusa kuka tazamo ƙasa, cikin kukan take faɗin
"Haƙiƙa kun cika iyaye na gari waɗanda basusan suga na wasu sun wulaƙanta, Nagode Allah da yahaɗa ni daku, wlh koda iya haka kuka bar ni da kalaman ku bazan taɓa manta ku cikin rayuwata ba, Nagode Allah yasaka da mafificin Alkhairin sa, Nagode Nagode.."
Kukan da yaci ƙarfin ta ne yasaka ta yin shiru, dasauri Saleema tasauko tarungume ta tana nata hawayen tana rarrashinta
Abba yace "Saleema kamata kuje ɗaki sai ki rarrashe ta acan".
"To Abba".
Miƙe wa tayi taruƙo ta suka nufi ɗakin ta, yayinda su kuma suka bi bayan su da kallo har suka shige, atare suka sauke ajiyan zuciya sannan suka dawo da fuskokin su izuwa junan su.
.
_Yanzu Labarin yasoma muje zuwa FAN'S._🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
[9/24/2020, 4:49 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 28*
Ringing tune ɗin wayan sa ne yadawo dashi cikin nutsuwar sa, ahankali yasaka hannun sa yaɗau wayan yana duba wanda ke kiran sa, sai kuma yayi peacking call ɗin yana karawa a kunne, shiru yayi don haka Brr. Tahir yace
"Ya man meke faruwa ne wai? Nafita nazo na tarar da missed calls ɗin ka, I'm so surprised da naga kiran ka har 5missed call, ina fata lafiya dai?"
Numfashi Khalil yasauke a hankali kana yace
"Brr. Tahir yau fa daƙyar nasha hannun wasu mutane".
"Subhanallah.. wasu mutane kenan? Me kayi musu?" Brr. Tahir ɗin yafaɗa cike da firgici
"Hmm wasu mutane kasani in banda mutanen da muke Shari'a dasu, kasan da cewa kwanaki nafaɗa maka suna bibiyana but duk da haka ban yi tunanin abun ya kai hakan ba, nafita zuwa wajen Mr. Abdullah, lokacin nafito daga gidan sa sai natsaya nan Resturent inci abinci, bayan nafito nagan su sun biyo ni, wlh naji tsoro sosai coz suna ɗauke da bindiga, daƙyar nasha ina faɗa maka, ƙarshe dai can nabaro motan sai dai na'aika drever yaɗauko min".
Brr. Tahir yace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Ib ina tsoron fa mutanen nan su cutar da kai, why not mu sanar da Police👮? sannan yakamata kabar gidan nan zuwa lokacin da za'a gama, hankalina be kwanta ba maybe su biyo ka har gida".
Shiru Khalil yayi naɗan wasu sakonni kafin yace
"Nima hakan ne araina, but nariga da nayi ma DPO magana, yace "zai turo yaran sa suyi gadina".
Ajiyan zuciya me ƙarfi Brr. Tahir yasauke kana yace
"But duk da haka dai hankalina be kwanta ba wlh".
Murmushi Khalil yayi yace "babu abinda zai faru sai alkhairi, insha Allahu gobe komi zai wuce".
"Hakane.. Allah yakaimu to".
"Ameen" Khalil ya'amsa masa
Daga nan sai da suka daɗe suna tattaunawa akan aikin nasu kafin suyi sallama, ya'ajiye wayan yana sakin ajiyan zuciya, kana yaɗan kwantar da kan sa saman pilow yana rufe idanun sa, fuskar ta ne yabayyana acikin ƙwayan idanun nasa, dasauri yabuɗe yana jin zuciyar sa na bugawa
"Meyasaka yarinyan taƙi ɓace masa?" Yatambayi kan sa yana dafe kan sa dake sara masa a hankali
Tun da yadawo gida yake tunanin ta, da zaran yarufe idanun sa kuma fuskar ta yake hangowa, kuma sosai yake ganin tsananin damuwa a fuskar nata, afili yafurta
"Wacece ita? Meyasaka tataimake ni? Meke damun ta?"
Sai yatallabo kumatun sa yana tsira wa waje ɗaya ido, ya jima ahaka yana tunanin da besan na menene ba kafin yamiƙe yashige toilet, alwala yayi yafito yashinfiɗa sallaya yagabatar da sallan magriba, yau be jin zai iya zuwa ko ina, don haka tun da yashigo ma yasanar da ma'aikatan sa kar wanda yafita, sannan yabada umarnin a kulle masa gida, yana nan zaune har aka kira isha'i yagabatar sannan yamiƙe yafita, kichen yawuce yahaɗa Coffee yazauna nan yashanye kana yakoma ɗaki, wanka yasoma yi yasauya kaya izuwa na barci, yakashe wuta yahaye gado, addu'a yayi yashafa tare da rufe idanun sa, ya jima kafin barci yaɗauke sa
Can cikin dare yatashi afirgice yana salati, gaba ɗaya yahaɗa gumi sakamakon mafarkin da yayi da ita, runtse idanun sa yayi yana tuna kukan da take masa cikin mafarkin kuma tana neman taimako a wajen sa, shiru yayi yana sauraron bugun zuciyar sa, sai yadafe kan sa da duk ka hannayen sa yana sake runtse idanun, ya jima ahaka kafin ahankali yazuro ƙafafun sa ƙasa yasauka saman gadon, sai da yayi kusan mintuna biyar a tsaye yana tunani kafin yataka yashige toilet, alwala yaɗauro yafito yasauya kayan sa zuwa jallabiya yasoma gabatar da nafila.
_*****_
Alhaji Mubarak mai Kuɗi wani babban attajiri ne da yayi ƙaurin suna a faɗin garin Katsina da kewaye, matar sa ɗaya da ƴaƴan sa biyu, Hassana ita ce Babba tana aure a ƙasan England, sai A'isha da take zaune a wajen ta tana karatun ta acan ɗin.
Mutum ne shi me taimako wajen mutanen gari, kuma kowa ya shaida hakan domin sosai ake girmama sa sabida ana ganin sa me ƙaunar talakawa, sai dai abinda basu sani ba na daga halin sa, shi mutum ne da ko kaɗan baya da imani baya da tausayi abaɗini, sana'ar sa shine kasuwan ci, sai dai babu wanda yasan da cewa yana safaran ƴan mata zuwa wani ƙasa, sannan yana harƙallan sai da Coken, yana kuma gudanar da sana'ar tasa ne batare da kowa ya sani ba.
Dr. Sabit shine wanda yake taimaka masa, kuma tare suke harƙallan tasu, babban Likita ne shi da yayi fice sosai kuma wanda ake ji dashi cikin garin Katsina, Shine Doctorn da yake ma duk wasu yara da suka samu operation yazuba musu Coken ɗin sabida afita dashi waje batare da an gano su ba.
Akwai wani Doctor Salis abokin aikin Doctor Sabit ne, shi yafara gano abinda suke aikatawa, har yayi yunƙurin kai su ƙara don yatona musu asiri, but daga ƙarshe sai dai aka nemi Doctor Salis aka rasa ya ɓace ɓat, kuma ba'a san me yafaru dashi ba.
Alhaji Mubarak ba iya mutanen gari kaɗai yake ma kirki ba, har ta da ƴan aikin gidan sa, don haka sosai suka saki jiki agidan, sai dai abinda basu sani ba yana amfani da hakan ne don cin ma burin sa, coz sau da dama yawancin masu aikin suna da yara, sannan kuma akwai ƴan mata acikin su, babu wanda yasan meyasaka masu aikin gidan sa mata basu daɗewa, sai dai lokaci kaɗan za'a neme su a rasa.
Hajjo tana ɗaya daga cikin masu aikin gidan, kuma tana ɗaya daga cikin waɗanda suka daɗe sosai suna aiki a gidan, asalin ta bafulatana ce mazauna ƙauye, sun zo tare da mijinta da yarinyan su ɗaya Nazeefa cikin birni, wata mata ce tayi ma Hajjo hanya har tasami aiki agidan, sosai take jin daɗin aiki a gidan Alhj. Mubarak me kuɗi kuma suna samun duk abinda suke so
Bayan wasu shekaru ne mijinta yarasu don haka taɗauki Nazeefa suka taho gidan Alhj. M. Me kuɗi don tanemi alfarma wajen sa don yaba su waje agidan nasa su zauna tunda ya saba yin haka, lokacin da tagabatar masa da alfarman ta gare sa babu musu ya amince, Hajjo tayi murna sosai sai dai batasan cewa Alhj. M. Me kuɗi ya amince ne don ganin Nazeefa da yayi, yasan da cewa idan suka zauna agidan sa hakan zai basa daman cikan burin sa akan ita Nazeefan.
Rayuwa taci gaba da gudana, lokaci ɗaya Allah yajarabbi Hajjo da ciwo, ashe ciwon ajali ne, don batayi sati ɗaya ba tarasu, Nazeefa tayi kuka sosai sabida tasan bata da wasu ƴan uwa kuma da suka rage mata, sannan batasan ma ina ne ƙauyen su ba bare takoma, ana haka Alhj. Mubarak yakira ta har parlourn sa bayan yayi mata ta'aziya yace
"Nazeefa sunan ki ko?"
Kanta a ƙasa ta'amsa mishi
"Ok zakici gaba da zama anan idan kinaso, sai ki maye gurbin Mahaifiyarki, sannan duk abinda kike nema ki sanar dani ko ki sanar da Hajiya, daga yau karki ɗauki kan ki marainiya tunda har kina damu".
Sosai Nazeefa tayi murna da jin maganar sa, don haka tayi masa godiya tafice, shi kuwa murmushi yayi yaɗau Jaridan sa yasoma karantawa, yasan da cewa nan da ɗan lokaci kaɗan zai cika burin sa akanta
Ana nan wata rana Hajiya ta aiki Nazeefa gidan ƙawar ta ta'amaso mata saƙo, kasancewar babu nisa da gidan su a ƙasa tatafi, bayan taje ta dawo ne a hanyan ta na dawowa gida sai ga Motan Alhj. Mubarak ya tsaya tare da zuge glass ɗin motan yana kallon ta da murmushi a face ɗin sa, ita kuwa tayi mamaki sosai ganin sa shi kaɗai babu drever, umarni yabata tashigo motan babu musu kuwa tashiga, don shi mutum ne me tsananin kwarjini da babu yanda za'ayi kayi masa musu a matsayin sa na babba, lokacin da suka iso gidan sai taga sun wuce but bata iya ce mishi komi ba, sai dai sosai tayi mamaki kuma tana son tatambaye shi sai dai babu dama, har suka isa wani babban gida yace da ita tajira sa bari yazo, fita yayi yashiga gidan, ita kuma gaban ta sai faɗuwa yake yi, tasan da cewa shi ɗin mutum ne me sauƙin kai, amma babu abinda yahaɗa ta dashi a matsayin ta na ƴar aikin gidan sa bare yaɗauko ta cikin motan sa, that's why gaba ɗaya hankalinta yaƙi kwanciya, duk tsoro ya cika ta, tana nan zaune wani mutum yazo yace mata tashigo inji shi, babu musu tafito tabiyo bayan mutumin suka shiga gidan, lokacin da suka shiga babu kowa, a lokacin ne taji kamar ana buga mata guduma a ƙirjinta, tsinkayan muryan mutumin tayi yana faɗin "tabiyo shi" wani ƙofa taga yabuɗe yashiga sai tabi bayan sa, suna shiga tatsaya tana kallon tsarin ɗakin da babu komi sai gado da sif taji ƙaran rufe ƙofa, kallon ƙofar tayi sannan kuma tawur-wurga ido cikin ɗakin taga babu mutumin da suke tare, a sukwane tanufi ƙofan da yake a kulle tasoma taɓawa tana son buɗewa, sai dai da alamun an rufeta ta baya ne, wani irin bugawa zuciyarta tayi batasan sanda tasoma jijjiga ƙofan ba tana ɓarkewa da kuka, cikin kukan take faɗin
"Don Allah kabuɗe, ina ne nan ina kakawo Ni? Na shiga uku Ni Nazeefa, wayyo Allana Wayyo Mamana".
Kuka take yi sosai tana jijjiga ƙofan da ko motsi baya yi, daga ƙarshe zubewa nan ƙasa tayi tasoma rusa kuka tana shushshura ƙafafu, ta jima ahaka tana kukan wanda har muryan ta yadena fita sai hawaye dake ta zirara.
[9/25/2020, 11:26 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 29*
Wasa wasa sai da Nazeefa tayi kwanaki bakwai a wannan gidan batare da tasan takamaiman inda take ba, tayi kukan duniya tayi ihun duniya babu wanda yazo wajen ta, sai dai da zaran tayi barci ta farka zata tashi taga an ajiye mata abinci, tun bata taɓawa da taga alamun kanta take cuta sai tasoma ci, sau da dama tayi yunƙurin kwana ido biyu don tasami nasaran guduwa idan akazo kawo mata abinci, but bata taba samun sa'a ba, abinda bata sani ba akwai Camera cikin ɗakin, idan har sukaga batayi barci ba to bazasu kawo mata abinci ba, haka zata ƙariki zamanta babu su babu alamun su, daga ƙarshe har tacire rai da samun daman fita, jira kawai take yi ranan da zasu kawo ƙarshen rayuwanta, domin a tunanin ta gidan cin kai take.
Wata rana tana zaune taga wannan mutumin da yashigo da ita yabuɗe ƙofan yashigo, zabura tayi tayi kansa da gudu tana ƙoƙarin guduwa yayi saurin cafko ta da hannu ɗaya, abinku da wacce bata da ƙarfi ko na sisin kwabo nan tadawo baya tafaɗa jikin sa, kuka tafashe dashi tana faɗin
"Don girman Allah kataimake ni kabar ni in tafi, wayyo Allana me kuke so dani ne..?"
Bata rufe baki ba Doctor Sabit da Alhj. Mubarak suka shigo, duk kan su face ɗin su a ɗaure ne babu alaman wasa, doctor Sabit ne yanufo ta riƙe da wani allura a hannun sa, ita bata kula da alluran ba sai kallon Alhj. Mubarak take yi tana kuka don takasa magana, so take yi taroƙe shi yafitar da ita amma ina, kafin ma tagama tunanin zucin ta har taji an sanƙama mata allura, batasan sanda takurma ihu ba tana riƙe hannun doctor ɗin, kallon shi take yi idanun ta cike da hawaye tana motsa baki, sai kuma tatafi luuuuuu tafaɗi nan ƙasa.
Alokacin da tafarka alluran be gama sakin jikin ta ba, ga wani zafi da yaziyarci ƙwaƙwalwanta, nan take taɗaura hannun ta saman maranta tana sakin kuka mara sauti, tayi tsawon mintuna 5 ahaka kafin tayi yunƙurin miƙewa, daƙyar talallaɓa tatashi zaune tana jin kanta na sara mata, ga wani irin jiri dake ɗiban ta tana ganin abubuwa bibbiyu, ɗakin take bi da kallo sai dai ba wanda aka ajiye ta bane, wannan cike yake da mata Sa'annin ta da waɗanda suka girme ta, su ma da alamun dai abinda akayi mata shi akayi musu, sai dai su basu farka ba saɓanin ita, Allura ne da akayi musu na tsawon awanni but abun mamaki ita be yi tasiri ajikin ta ba, mintuna 20 kenan da yin mata sannan tafarka, kuma anyi musu ne har sai an fita dasu zuwa ƙasashen da za'a kai su sannan su farka
Miƙewa tayi cikin yanayin rashin hankali tasoma tafiya aduƙe tana tangal-tangal kamar wacce zata kife ƙasa, tariƙe cikin ta dake mata bala'in zafi, ƙofa tabuɗe tafice sai gata cikin parlour, babu kowa ciki suna can suna shirin yanda zasu fitar da ƴan matan bayan sun dawo cikin hankalin su na mintuna ƙalilan, domin alokacin da suke zuwa Airport dasu a farke suke kai su har sanda zasu shiga jirgi, sai dai hankalin su da tunanin su sun riga sun gushe, duk yanda akayi dasu haka zasuyi
Direct wani ƙofa tanufa tabuɗe tafice, Allah yabata Sa'a ashe waje ne, haka tafita gidan batare da taga kowa ba, tafiya take tayi batasan inda take saka ƙafarta ba, tayi tafiyan da ita kanta batasan awanni nawa yaɗauke ta ba, sai faɗi tayi ƙasa a sume batare da tasan inda kanta yake ba.
Lokacin da tafarka garin yayi duhu sosai kuma babu wanda yaganta, kasancewar anguwan na masu kuɗi ne zai yi wuya kaga mutum a waje, zuwa lokacin tsananin azaba take ji a cikin ta, a lokacin kuma ta dawo hayyacin ta gaba ɗaya, sai tariƙe cikin ta tana ta kuka tana burgima awajen, tsawon lokaci kafin tayunƙura daƙyar tamiƙe taci gaba da tafiya tana kuka, a wannan lokacin ne Brr. Ibrahim Khalil yazo wucewa yabige ta batare da yasani ba, yana fitowa yaganta yashe a ƙasa da alamun ta sume ne, ɗaukan ta yayi yasaka ta a mota yanufi da ita asibiti, lokacin Dr. Sameer be riga ya tafi ba, shi ya'amshe ta yakira abokin sa Dr. Hashim, babu jimawa kuwa yazo yasoma dubata, duk Brr. Khalil yadamu yakasa zama waje ɗaya sai zagaye yake yi, sai da Dr. Sameer yabashi ƙwarin gwiwa tukun hankalin sa yakwanta
Sai da akayi 2 hours ana duba ta kafin Likitocin dake kan ta su fito, Dr. Hashim ne yayi musu bayanin da yaɗaga musu hankali, sosai suka shiga damuwa jin cewa Coken ne acikin ta, kuma ya kai tsawon lokacin da Yakamata acire mata but ba'a cire ba, don haka har yasoma narkewa yataɓa mata hanji dole sai anyi mata aiki an cire, sannan kuma sai anyi mata dashen hanji, Khalil ne yasaka hannu aka shiga da ita Theater, tsawon awa biyu kafin aka fito da ita, sai alokacin suka tafi gida bayan da suka tabbatar komi normal.
Watan ta biyu kafin tafarfaɗo, kuma duk alokacin tana ƙarƙashin kulawan Khalil ne tare da Doctor Hashim da Doc. Sameer, sosai take jin jiki duk da an samu nasaran aikin, ko magana bata iyayi bare tashi, komi sai dai ayi mata
Khalil sosai yadamu da halin da take ciki haka kawai yake jinta tamkar ƙanwar sa, kuma yayi imani cewa yarinyan zaluntar ta akayi, don haka alokacin ne yasoma bincike akan ta, kuma ya yi ƙudirin sai ya ƙwato mata haƙƙinta, tsawon wata yana bincike sannan yagano inda take zaune, wato gidan Alh. Mubarak, a ranan da yashirya yaje yayi hira da me gadi har yagano labarin ta a wajen sa, bayan ya dawo ne a ranan wasu suka zo kashe ta cikin asibitin, abinda be sani ba Khalil yana tafiya me gadin yasanar da Alh. Mubarak, tunda dama neman ta ake yi ana tunanin ɓata tayi, Dr. Sameer ne yashigo cikin ɗakin lokacin da mutumin da zai kashe ta yaso kashetan, shine yagudu batare da yayi abinda yazo yi ba, wannan dalilin ne yasaka suka yanke shawaran afitar da ita daga asibitin, don sun gano kasheta ake da ninyan yi, Shine Khalil yakaita gidan Baaba Talatu, anan akaci gaba da kula da ita sannan shi kuma yaci gaba da bincike kan lamarin, har sanda yagano komi akan Alhj. Mubarak tare da Doc. Sabit, babu ɓata lokaci yashigar dasu ƙara zuwa kotu
A lokacin hankalin su Ahj. Mubarak be wani tashi ba, domin acewar su babu yanda za'a yi akama su da laifi, sannan kuma su ɗin masu hannu da shuni ne waɗanda sukayi fice kuma kowa yasan halin su, babu yanda za'a yi yayi nasara, but zaman farko a kotu sai ido yaraina fata, yanda Brr. Khalil yayi takawo shaidu hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba, anan Alƙali yabada hutun wata ɗaya da sati biyu bayan da kowa yagama kawo shedun sa, kuma ya bada umarnin ranan da za'a dawo yakasance Nazeefa ta hallara, sakamakon hujjojin da Brr. Khalil yaba da ne aka tsare Ahj. Mubarak tunda an gano yana da laifi
Wannan shari'ar ya ja cece kuce sosai a wajen jama'a, sosai mutane suka ƙosa suga ranan da za'a dawo don yanke hukuncin, kuma duk alokacin mutane basu yarda cewa Alh. Mubarak yana da laifi ba, sai dai mujira ranan dawowan kamar yanda yakasance gobe da ƙarfe 02:00pm.
_Hmmm masu karatu ku ma sai kushirya don jin Me zai wakana a Court._ 😅
_ina gayyatar Masoya Brr. Ibrahim Khalil da Nazeefa, kuzo kugani da idanun ku._💃💃💃💃
[9/29/2020, 12:44 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️ ~What'sapp Number 07065334256~
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 30*
Washe gari ƙarfe 07:15am. Saleema tagama shirin ta na zuwa school, tana shirin ɗaukan jakan ta taji cikin ta yasoma murɗa mata, dasauri tariƙe tana runtse idanun ta, lokacin ne Halwa tafito daga Toilet tana kallon ta, ganin tana riƙe da ciki taƙi jirgawa yasa tamatso kusa da ita cikin sanyin murya take tambayan ta "ko wani abun na damun ta?" Murmushi Saleema taƙaƙalo tare da girgiza mata kai, sai dai har alokacin tana riƙe da cikin nata ne, hannu tasanya taɗau jakan kafin takalle ta tace
"Ni natafi school sai na daw.."
Bata ƙarisa maganar ba tadurƙushe nan ƙasa tana faɗin
"Wayyo cikina wayyo Allana".
A ruɗe Halwa tabi ta ƙasan tana kiran sunan ta tare da tambayan ta abinda ke damunta, ganin tasoma kuka sosai tana sake riƙe cikin ta yasaka tamiƙe dasauri tafita, ɗakin Ummi tashiga dasauri, tana tsaye kuwa itama tagama shirin ta nazuwa Hospital kasancewar ita ɗin Nurse ce, taburmo ɗakin tana kiran sunan ta, Ummi kallon ta tayi tace
"Lafiya Halwa meke faruwa?"
Cikin rawan murya kamar zatayi kuka tace "Saleema ce babu lafiya".
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Ummi tafaɗa cikin tashin hankali kafin tanufo wajen ta tana faɗin
"Tana ina? Ina take?"
"Tana ɗaki".
Atare suka isa ɗakin lokacin gaba ɗaya Saleema tafita hayyacin ta sai kuka take yi, ga duk kan alamu tana jin jiki sosai, riƙo ta Ummi tayi tana kiran sunan ta tare da tambayan ta "Ina ke mata ciwo?" Duk hankalin Ummi atashe yake tarasa ma me zatayi
Halwa tace "Ummi ko za'a kira Abba akaita asibiti?".
Sai alokacin tunanin hakan ma yazo ma Ummi, tayi saurin cicciɓan ta Halwa tatayata suka fito da ita, suna fita waje Drever yazo da gudu yabuɗe musu mota suka saka ta, Ummi tashiga baya kusa da Saleema, ita kuma Halwa tashiga gaba tare da drever suka tafi, sai acikin motan Ummi ta'ari wayan drevern takira Abba tasanar masa.
Lokacin da suka isa asibitin tuni an amshe ta kasancewar ba yau suka saba zuwa ba, kuma dama tana da Doctorn da yake duba ta na musamman acikin asibitin, ana shiga da ita Abba shima ya'iso duk hankalin sa atashe, Halwa yanda taga su Ummi sun tashi hankalin su sosai itama sai taji duk ta damu, haka tazauna waje ɗaya tatakure tana tuna ɗan zaman da sukayi daga jiya zuwa yau, sosai tafahimci ita ɗin yarinya ce me tausayi da son mutane, sannan kuma ta fahimci akwai ƙauna sosai a tsakanin ta da iyayenta, take taji hawaye ya zubo mata tayi saurin saka hannu tana sharewa.
Koda aka fito da ita Abba ne yanufi wajen doctor, Ummi da Halwa kuma suka shiga ɗakin da aka kwantar da Saleema, tana kwance ne asaman gado, abun tausayi kamar ba itace lafiyan ta lau yanzu ba, amma Allah da ikon sa numfashi ma bata iya yi sai da taimakon Oxygen, Ummi hawaye tasoma zubarwa da ganin tilon ƴarta a irin wannan yanayin, takawa tayi taƙarisa wajen gadon, itama Halwa ahankali ta'isa jikin gadon tana ƙure Saleeman da idanu, zama Ummi tayi tariƙo hannun ta ɗaya wanda ba'a saka mata drip ba tana ƙare mata kallo, cikin zub da hawaye tace
"Allah Sarki Saleema, Allah yabaki lafiya, haƙiƙa kinga jarabawa a rayuwan ki, ko yaushe ne zakiji daɗi kamar kowa?"
Cikin tsananin tausayi da jin kalaman Ummin Halwa tazame nan gefen gadon tazauna, share hawayen ta Ummi tayi taɗago kanta tana kallon Halwa tace
"Tun tana ƙarama Allah yajarabce ta da ciwon zuciya, dashi tataso har girman ta, duk iya maganin da muka nema akan ta Allah be sa an dace ba, tasha baƙar wahala kamar bazata rayu ba, acikin shekaru biyu da suka wuce akayi mata aiki a ƙasan OXFORD, Allah yasa an dace, duk da haka muna gudun ɓacin ranta domin da zaran ranta ya ɓaci ciwon ta yana ƙoƙarin tashi ne, sai dai ba'a rufa watanni biyu ba tasoma ciwon ciki me tsanani, koda muka kaita asibiti aka gano tana ɗauke da ciwon hanta ne".
Cikin sheshsheƙan kuka Ummi taci gaba da faɗin
"Bamu san ya zamuyi ba idan muka rasa Saleema, muna tsananin ƙaunar ta Ni da mahaifin ta, kuma ita kenan gare mu ita kaɗai ce mallakin mu, amma kuma Allah ya ɗaura mata ciwon da muke ganin koda yaushe zamu iya rasa ta, a kullum burin mu shine musaka ta farin ciki, duk abinda take so shi muke yi, sai dai fargaban mu wanene zai ci gaba da kula mana da ita idan har takoma ƙarƙashin sa, wani namiji ne zai iya zama da ƴar mu yasaka ta farin ciki kamar yanda Likitoci suka sanar mana? yah Allah gamu gare ka, ya Allah kasauƙaƙa ma wannan baiwa taka, Allah yabaki lafiya Saleema".
Halwa batasan tana zirarar da hawaye ba sai da taji danshin su akan hannun ta, cikin rawan murya ta'amsa ma Ummi da "Ameen". Tana saka hannu tashare hawayen, Abba ne yashigo cikin ɗakin, dasauri Ummi tamiƙe tana kallon sa tace
"Abban Saleema me likitan yace? Da fatan babu abinda yasami ƴar mu? Ya Allah..". Sai tafashe da kuka tana saka hannu tarufe idanun ta
Ahankali yasaka hannun sa yana bubbuga kafaɗan ta, cikin ƙarfin hali yace
"Kiyi shiru don Allah, babu abinda zai sami ƴar mu insha Allahu, Doctor yace ciwon ta ne kawai yatashi but zata sami sauƙi very soon".
Ummi tace "Ina jin tsoro sosai Abban Saleema, ina jin tsoro kar mu rasa ta".
"Baza mu rasa ta ba Asma'u, ki dena faɗan haka kinji?"
Rarrashinta yayi sosai, sai da yaga tayi shiru ta kwantar da hankalin ta kafin yamayar da kan sa zuwa ga Halwa da har yanzu take zuban hawaye, gaba ɗaya ta takure waje ɗaya ta duƙar da kanta ƙasa, kiran sunan ta Abba yayi kana yace
"Kema ya dace kiga likita coz ɗazu kafin nafita Saleema tafaɗa min da zazzafan zazzaɓi kika kwana, kuma dama Yakamata aduba lafiyan ki da abinda ke cikin ki, be kamata abarki haka da ciwo ba, bari nafita nayi ma Doctor ɗin magana".
Daga haka Abba fita yayi ita kuma Ummi takoma tazauna tare da riƙo hannun Saleema tana kallon ta.
***** ****** ******
Ƙarfe 01:10pm. Brr. Khalil yagama Shirin sa, ya saka riga da wando white colour, sannan yaɗau rigan aikin sa tare da hulan yariƙo briafcase ɗin sa yafito, Direct wajen farar motan sa yanufa yabuɗe yashiga yazauna, ya kai wajen five minutes kafin yatada motan yanufi bakin Gate, hon yadanna Gate man yazo yabuɗe masa yaja motan ahankali yafice, sai da yadaidaita motan saman kwalta kafin yaɗau wayan sa yakira Sameer
"Hello Bro".
Daga can Sameer ya'amsa mishi da faɗin
"Kana gida ne ko ka tafi?"
"No gani a hanya, zan wuce gidan Mom".
"Ok shikenan, dama tambayan ka zanyi don mu mun riga mun isa". Sameer ɗin yafaɗi hakan
"Ok nima bazan daɗe ba, yanzu insha Allahu zan ƙariso".
Daga haka sallama sukayi ya'ajiye wayan, sannan yamayar da hankalin sa ga tuƙin sa, be ɗau lokaci ba ya'isa gidan su Kasancewar yau ɗin ya ɗan taka motan da gudu, yana yin parcking yafito yanufi cikin gidan, a Parlour yatarar da Mom tana zaune tana shan Fuirt, ƙarisawa yayi yazauna gefen ta yana riƙo hannunta yayi mata peck a bayan hannu kana yace
"Sannu da hutawa Mom".
Murmushi tasakar masa tace
"Yauwa My Son, har ka iso?"
Gyaɗa mata kai yayi yana ɗaukan Apple yasoma gutsira yana taunawa a hankali
"Masha Allah.. yanzu itama Nazeefan tashiga ɗaki taje shiryawa, nima wannan karon dani za'a je, bari inje in shirya".
"Yakamata kam, but ina Dad yake?"
"Oh Dad ɗin ka yafita tun safe akwai meating ɗin da yake dashi, but yace "idan sun gama da wuri zai same mu acan".
Nazeefa ce tafito cikin shirin ta na riga da wando farare, sai taɗaura Coffee ɗin Hijab, sosai tayi kyau kasancewarta fara, tana hango Khalil shima da fararen kayan sai wani irin farin ciki Yakamata, ko ba komi sun yi anko yau, kuma hakan yayi mata daɗi
"Ƙariso mana kin tsaya, me kike tunani?" Muryan Mom yadawo da ita hayyacin ta
Sai alokacin Khalil yakalli inda take tahowa, idanun sa kawai yaƙura mata har ta'iso wajen kanta a ƙasa tagaishe sa, amsa mata yayi yana tauna Apple ɗin dake bakin sa har yanzu kuma yaƙi kau da idanun nasa kanta
Mom tace "bari inje in shirya".
Tashi tayi tawuce ɗakinta, shima kuma Khalil dake kallon Nazeefa yayi mata alama da ido alaman tazauna gefen sa, babu musu tazauna cike da kunya, sauran tufan dake hannun sa yamiƙa mata, hakan yasaka taɗago kanta tana kallon sa don bata fahimci abinda yake nufi ba
"Ki ci". Yabata umarni yana kawar da kansa
Ahankali tasanya hannu ta'amsa takai bakin ta idanun ta akan sa, gutsira tayi tana lumshe idanuwanta cike da wani irin daɗi da yaziyarci zuciyarta, shi kuma hakan yabashi daman sake maida idanun sa kanta yana ƙare mata kallo, har sanda tabuɗe idanun ta tasauke acikin nasa, sai tayi saurin Sad da kai ƙasa tana murmusawa
kiran sunan ta yayi, bata amsa ba sai ɗago kai da tayi tana kallon sa
"Kina jina ina son in sanar dake, kikasance me juriya ga duk tambayoyin da za'a yi miki a Court, bana son ki nuna tsoro ko firgita a wajen, ina son ki amsa duk wasu tambayoyi da za'a miki batare da fargaba ko tsoro ba, Nazeefa kina dani a wajen don haka kiɗaura wa kanki ƙwarin gwiwa kinji?" Yayi maganar cikin tausasa murya still yana kallon ta
Gyaɗa masa kai tayi, kana tace "insha Allahu Yaya zan amsa duk wata tambaya batare da na nuna tsorona a fili ba".
Murmusawa yayi kawai yana kau da kan sa, lokacin ne kuma Mom ta'iso wajen tana cewa
"Kutashi Muje to na shirya"
Gaba ɗaya suka tashi suka fice, motan Khalil ɗin suka shiga yaja yafice a gidan.
[9/29/2020, 12:58 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 31*
Lokacin da suka isa, gaba ɗaya haraban court ɗin cike yake da mutane, Khalil ce musu yayi "su shiga ciki". Don haka suka fice suka bar sa cikin motan yaɗau wayan sa yana neman layin Brr. Tahir.
*20 minutes*
Shigowan Alƙali yasaka kowa yayi shiru, duk kan su tashi sukayi har sai da Alƙali yazauna kafin kowa ma yazauna, daga nan Maga-takarda yamiƙe yasoma bayani kamar haka:
"Ayau 26 September 2020 zamu ci gaba da gabatar da shari'ar Alhaji Mubarak Mai kuɗi da Nazeefa Shehu".
Sannan yamiƙa takardun ga Alƙali, shi kuma ya'amsa yana gyara glass ɗin sa yasoma dubawa, sannan yaɗago kansa yana cewa
"Lauyoyi zaku iya farawa".
Khalil ne yatashi yasoma gabatar da kan sa
"Ni sunana ```BARRISTER IBRAHIM KHALIL ABDURRA'UF.``` lauya me kare wacce takawo ƙara, tare dani kuma akwai abokan aikina..".
"Brr. Tahir .A. Tahir". Cewar Brr. Tahir kenan da shima yatashi yagabatar da sunan shi
"Tare dani Brr. Bilkisu Ahmad Sofana".
Zama sukayi gaba ɗayan su.
"Ni kuma ni ne Brr. Mahmud Sudais, lauya me kare wanda ake ƙara, tare dani akwai..".
"Brr. Shamsudden Munir".
Su ma zama sukayi, Alƙali duƙar da kansa yayi yaɗan yi rubutu tukun yaɗago kai yana kallon su, hakan yasaka Brr. Khalil yamiƙe yasoma magana
"Ya me girma me Shari'a, ina son agabatar min da Nazeefa Shehu don in mata tambayoyi".
"Kotu ta baka dama". Alƙali yafaɗi hakan yana aje Bairo ɗin hannun sa
Maga-takarda yamiƙe yace "idan akwai Nazeefa Shehu anan tafito".
Nazeefa da jikin ta yayi mugun sanyi, gaba ɗaya sai taji cikin ta yasoma rugugu ƙafanta kuma sai faman rawa suke yi don bata taɓa tsayawa cikin taron mutane ba, Mom dake kusa da ita tace
"Tashi kije mana, ki cire tsoro aran ki kinji".
Gyaɗa kai kawai tayi taɗago tana kallon mutane nan idanun ta yafaɗa akan na Khalil, kafe ta da idanu yayi ko ƙiftawa baya yi hakan yasaka tamiƙe tafara nufo shi, tana isowa wani ɗan sanda yace tashiga nan". Babu musu kuwa tashiga tatsaya kanta a ƙasa, takowa Khalil yayi ya'iso gaban ta
"Kotu zataso taji cikakken sunan ki".
Bata ɗago kai ba tace "sunana Nazeefa Shehu".
"To Nazeefa Shehu zan so in san menene alaƙan ki da wanda kika kawo ƙara, ina nufin Alh. Mubarak me kuɗi".
Sai alokacin taɗago kanta tana kallon Khalil, yayi mata alama da ido, hakan yasaka tamayar da idanun ta kan jama'a sai kuma tasauke kanta tasoma bayani
"Muna aiki ne a ƙarƙashin sa".
"Kenan kina nufin ke ƴar aikin gidan sa ne?"
Gyaɗa kanta tayi sai kuma tace "Eh".
"Ok zan so ki bama kotu taƙaitaccen labarin ki, da yanda har kuka zauna a gidan Alh. Mubarak".
"Ni bansan sanda muka soma aiki a gidan sa ba, sabida alokacin bani da wayau sosai, sai dai a sanda mahaifina yarasu nasan sanda muka koma gidan sa da zama".
Daga nan tasoma bada labari tiryan-tiryan abun da yafaru da ita a gidan, har sanda yaɗauke ta yakaita wani gida, zuwa taimakon da Khalil yayi mata har kawo iyanzu, tanayi tana kuka, sai da tagama bada labarin surutun mutane yasoma tashi, sai da Alƙali yabuga guduma kafin sukayi shiru
"Ya me girma me Shari'a iya tambayoyin da zan iya mata kenan" Khalil yafaɗi hakan kana yaje yazauna
Brr. Mahmoud ne yatashi
"Ya me girma me Shari'a ina so nayi ma Nazeefa Shehu tambayoyi".
"Kotu ta baka dama".
Ƙarisawa wajen ta yayi yana ƙare mata kallo, ita kam har yanzu kanta a ƙasa yake tana share hawaye, don haka batasan ma yanayi ba
"Malama Nazeefa zaki iya faɗa min iya adadin mutanen da suke aiki a ƙarƙashin Alh. Mubarak?"
Ɗago kanta tayi takalle sa sai tace "Eh zan iya, zamu kai mu Goma ne".
Jinjina kansa yayi kana yace "A sanda Alhj. Mubarak yafita cikin motan yabaki umarnin kijira sa, meyasaka kika fito?"
"Wani ne yace min in zo yana kira na".
"Kina nufin wani ne yajagoran ce ki zuwa ciki? Meysaka to kika bishi? Alamu sun nuna kenan ta yiwu wasu ne suka aikata miki hakan?"
"Ya me Shari'a Brr. Mahmoud yana ƙoƙarin canza mata tunani sannan yatilasta ta tafaɗa abinda bashi ne ba".
Alƙali yace "kagyara tambayoyinka Barrister Mahmoud".
"Ok ya Me Sharia".
Sannan yamayar da kallon sa gare ta yaci gaba
"Ina jinki, kin tabbatar kinga Alh. Mubarak a wannan gidan koda kika shiga?"
"Eh na gansa alokacin da suka shigo shi da wani mutum har sukayi min allura".
Jinjina kansa yayi kafin yajuyo yana kallon Alƙali yace
"Iya abinda zan iya tambayan ta kenan". Sannan yaje yazauna
Miƙewa Khalil yayi yace "zan so a gabatar min da Alh. Mubarak Me kuɗi don amsa tambayoyina".
"Kotu ta baka dama".
Fito da Alh. Mubarak akayi, wasu ƴan sanda suka tsaya bayan sa
"Alh. Mubarak shin kasan wancan yarinyan?".
Kallon Nazeefa yayi sannan yace "Eh na santa".
"Menene alaƙan ka da ita?".
"Babu wata alaƙa da nake da ita, illa ita ɗin ƴar aikin gidana ne".
Jinjina kan sa Khalil yayi kana yace
"To yanzu ka yarda da abinda tafaɗa ko har yanzu kana tantama?"
"Ni ban yarda da abinda tafaɗa ba, coz ni ba mutumin banza bane da har zan yi wannan mummunan harƙallan".
Murmushi Khalil yayi yace "kenan duk kanaso kace mana abinda ake zargin ka ba Gaskiya bane?"
"Eh ba Gaskiya bane, don Ni taimakon ta kawai nayi shine take so ta saka min da sharri".
"Kamar ya taimakon ta kayi?"
"Eh lokacin da naganta a hanya shine naɗauke ta nakaita gida, shikenan iya abinda yahaɗa ni da ita".
Khalil yace "a matsayin ka na babban mutum ka taho ka ganta a hanya, sannan kuma babu nisa da gidan ka da inda take, meysaka kayi sha'awan kaɗauke ta a mota ka ƙariso da ita gidan ka?"
"Kasan taimako ajinina yake don haka don na ɗauke ta na kawo ta gida wannan bazai saka a zarge Ni ba, sannan kuma ina tausayin ta ne saboda Mahaifiyar ta a gidana ta rasu".
"Ya me girma me Shari'a iya tambayoyin da zan masa kenan,, sannan zan so abani dama nasake yin ma Nazeefa tambayoyi". Khalil yafaɗa hakan sannan yakoma wajen zaman sa
Alƙali da yagama rubutu yaɗago kansa yace "ko lauyan da yake kare wanda ake zargi yana da abin cewa?"
Miƙe wa Brr. Mahmud yayi yace "A'a ya me Shari'a, sannan yakoma yazauna
"Kotu ta baka dama".
Tashi Khalil yayi ya'isa gaban Nazeefa yace "zan so ki sanar dani tun sanda kika taso da wayon ki kika ganki agidan Alh. Mubarak masu aiki nawa ne aka sanja agidan? Ko waɗanda kika sani iya su ne agidan har tafiyan ki?"
Cikin sanyin murya Nazeefa tace "gaskiya tun zuwana gidan har sanda natafi masu aikin gidan waɗanda aka sauya bazan iya ƙirgawa ba, amma suna da yawa sosai".
"Kenan kina nufin a gidan Alh. Mubarak ansha sauya masu aiki batare da wasu dalili ba?.."
Miƙe wa Brr. Mahmoud yayi yace "Of jection my Lord Brr. Ibrahim Khalil yana neman yaɗaura wacce yake karewa akan hanya".
"Kakula Brr. Ibrahim". Cewar Alƙali
"Nagode ya me Shari'a, ok ina jin ki, ko zaki faɗa min akwai wani laifi da kikasan suna yi ake sauya su?"
"A'a Ni bansani ba, haka kawai muke neman su mu rasa sai akawo sabbi".
"Ok zaki iya komawa kizauna".
Sannan yajuya ga alƙali yace "ya me Shari'a ina son nayi ma Malam Umaru tambayoyi".
"Kotu ta baka dama".
Maga-takarda yatashi yayi kiran sa sannan yafito
"Malam Umaru abaya na tambaye ka wasu tambayoyi, sannan nace idan da buƙatar nasake kiran ka zan sake".
Gyaɗa kansa Malam Umaru yayi
"Yauwa a lokacin da Nazeefa tafita gidan Alh. Mubarak a matsayin ka na me gadi kana ina?"
"Ina bakin Gate ɗin tazo tafita".
Kaɗa kansa Khalil yayi kana yaƙure sa da idanu yace "to kaga dawowan su kamar yanda Alh. Mubarak yafaɗa shine yadawo da ita?"
Hannu Malam Umaru yasanya yagoge zufan da yake tsatstsafo mishi kana yace
"Eh na gani".
"Kana nufin sun dawo tare ɗin?"
"Eh tare suka dawo a motar sa bayan mituna ƙadan da fitan ta".
Murmushi Khalil yayi yana sake tsare sa da idanu yace
"Ok to idan har kaga dawowar ta cikin gidan, to da yaushe kenan takuma fita?"
Malam Umaru yace "gaskiya ban sani ba".
"A matsayin ka na me gadi ya akayi har mutum yafita cikin gidan baka sani ba?".
"Eh.. uhm naje zagayawa ne ai, don haka bansan ta fita ba".
"To a yaushe kafara jin ana cigiyar ta?".
"Bayan sa'o'i uku da dawowar ta, sai Hajiya tazo tasame Ni take tambayana "har yanzu Nazeefa bata shigo bane?" Shine nace mata ai tun ɗazu Tawuce".
Daga nan Brr. Kahlil zama yayi, sai Brr. Mahmoud yatashi shima yayi masa tambayoyi, Kana Brr. Kahlil yasake tashi yace
"Ina son inyi wa Hajiya Asiya Tambayoyi".
"Idan akwai Hajiya Asiya tafito".
"Zan so insan alaƙan ki da Alh. Mubarak".
"Mijina ne".
"Kun kai shekaru nawa dashi?"
"Mun kai shekaru 32yrs dashi".
"Ok kin taɓa fuskantar wata matsala dashi? Kamar kina zargin sa da yana aikata wani abu a ɓoye batare da sanin ki ba?"
Kallon inda Alh. Mubarak yake tayi, sai tayuyo da kanta tare da sad da kan ƙasa tace
"Ni ban taɓa zargin sa ba, kuma Mijina baya ɓoye min komi".
"Ok lokacin da kika ji shiru Nazeefa bata dawo miki aike ba, me kikayi akai?".
"Nazo na tambayi me gadi sai yace min "tariga da tawuce ai".
"Sannan kuma da kika koma nemanta kika yi ko me?" Khalil yafaɗa yana tsare ta da idanu
Yawu tahaɗiye kana tace "eh naje na neme ta ciki amma ban ganta ba".
Murmushi Khalil yayi yajuya yana kallon Alƙali yace
"Ya me girma me Shari'a ko da wannan jawaban da Malam Umaru da Hajiya Asiya sukayi zai tabbatar da ƙarya suke yi, coz inda Nazeefa ta dawo gida kamar yanda sukace ya akayi aka rasa ta lokaci guda? Taya har zata fice gidan batare da wani ya ganta ba idan akayi duba da gidan na mutane ne, sannan idan akayi la'akari da Labarin da Nazeefa ta bayar za'a gane gaskiya take faɗa, sannan kuma ansha neman masu aikin gidan Alh. Mubarak ana rasa su lokaci ɗaya batare da wasu dalili na laifi da suka aikata ba, sai dai aga an kawo sabbi, ko anan ya me Shari'a yakamata asan cewa Alh. Mubarak yana amfani da wannan daman ne wajen ɗaukan yaran mutane yana safaran su zuwa wani ƙasa, Nagode ya me Shari'a".
Komawa yayi yazauna, sai da Alƙali yayi rubutu kana yace
"Brr. Mahmoud ko kana da tambayan da zakayi?"
"A'a ya me Shari'a".
Rubutu yasake yi sannan yaɗago yana kallon Brr. Khalil yace
"Zaka iya ci gaba da bada shaidun ka".
Miƙewa Khalil yayi yana sakin wani kyakykyawar murmushi kana yace
"Ya me Shari'a abani dama Brr. Tahir zai je yazo da shedata ta gaba".
"An baka dama".
Miƙewa Brr. Tahir yayi yafita, bayan kamar mituna 3 sai gasu sun shigo da wani mutum, dasauri Alh. Mubarak dake tsaye tsakankanin ƴan sanda yaɗago idanun sa kamar wanda zasu fito waje yana kallon mutumin.
_To fa wanene wannan mutumin?_
[9/29/2020, 1:10 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 32*
Alh. Mubarak murmushi yasaki, coz yasan da cewa babu abinda Brr. Khalil zai samu a wajen mutumin, sabida sun riga da sun biya sa zunzurutun kuɗi kuma yayi musu alƙawarin bazai taɓa tona musu asiri ba
Ƙarisawa gaban sa Brr. Khalil yayi yace "kotu zata so tasan ainihin sunan ka da sana'ar ka?"
"Sunana Aliyu Gusau, amma amfi sanina da Gadanga, kuma sana'a ta shine gadi".
"Madalla.. to zan so kafaɗa min wa kake ma gadi?"
"Ina yiwa Alh. Mubarak da Dr. Sabit gadi ne".
"Ma'ana kana nufin kana aiki a gidan Alh. Mubarak sannan kuma kana aiki gidan Dr. Sabit?"
Girgiza kan sa yayi kana yace "ina musu gadi ne a wani gidan su dake Sabon layi G.R.A".
Brr. Khalil yace "to zan so kasanar da kotu abinda kasani a waɗannan mutanen biyu da ka lissafo".
"Da farko dai Ni me gadin gidan ne, kuma shekaruna 20 ina tare da waɗannan mutanen, abinda nasani shine suna kawo mata gidan suna ajiye su, kuma Ni ne jagoran da nake taimaka musu wajen tsare musu Matan da suke kawo wa, sannan Ni ke basu abinci a ko yaushe".
Murmushi Brr. Khalil yayi yace "ina jin ka, daga nan kuma ya ake yi dasu?"
"Dr. Sabit shi ke musu allura sannan yasaka musu Coken acikin su, bayan kamar mintuna 20-30 za'a zo da motoci a tafi dasu, suna safaran su zuwa wasu ƙasashe ne, Ni iyakan abinda nasani kenan".
Still Murmushi Brr. Khalil yayi kana yace "ita kuma Nazeefa ya akayi tabar gidan batare da sanin ku ba?"
"A lokacin Dr. Sabit ya aike Ni zuwa gidan sa don naɗauko wasu yara, to ina tunanin a lokacin ne tafita don basuyi zaton zata iya farkawa a time ɗin ba".
Gaba ɗaya kotun ne yahargitse da surutu sai hayaniya ake yi, shi kuwa Alh. Mubarak tun sanda yaji Gadanga yana zayyano bayani yarufe idanun sa yana jin wani baƙin ciki a ransa, saɓanin Dr. Sabit dake zaune cikin mutane, be taɓa tunanin asirin sa zai tonu ba da be zo wajen ba, sosai yashiga firgici don yasan yau kashin su ya bushe tasu ta ƙare
Brr. Khalil yace "ina son kotu tabani dama zan kira Dr sabit don amsa tambayoyi".
"Dr. Sabit zaka iya fitowa gaban kotu".
Jiki a sanyaye yafito yana gyara glass ɗin idanun sa duk zufa ya jiƙa masa fuska, matsowa kusa dashi Khalil yayi yace
"Dr. Sabit shin me zaka iya cewa game da bayanin Gadanga?"
Shiru yayi yana sad da kai ƙasa, gaba ɗaya hannayen sa rawa suke yi don be san kuma abinda zai iya cewa ba, "shin yaƙaryata abinda aka faɗa akansa ne ko ya?"
"Dr. Sabit kai muke sauraro, kana da abin cewa ko kuwa ka yarda da zargin da ake muku?"
"Eh.. eh na amince mun aikata duk abinda ake zargin mu dashi.."
"Ƙarya ne wlh ƙarya yake min ni dai, Ni ban amince da abinda yafaɗa ba". Cewar Alh. Mubarak gaba ɗaya yazama tamkar zararre, sai ƙara maimaita abinda yafaɗa yake yi
Buga guduma Alƙali yayi yace "ya isa Alh. Mubarak, nan kotu ne Yakamata kanutsu kasan me kake yi".
Sai alokacin yayi shiru yana share zufan dake keto masa, mutane kuwa sai faɗin albarkacin bakin su suke yi, sai da Alƙali yasake buga guduma sannan suka nutsu, takowa Brr. Khalil yayi zuwa tsakiyan kotun yana cewa
"Ya me girma me Shari'a sai kuma Shaidata ta ƙarshe, abani dama in gabatar da Fadila Muhammad".
"Idan da Fadila Muhammad tafito".
Baby Dil dake zaune can baya tamiƙe tataho, sai da idanun kowa yakoma kanta coz yanda take tafiya cike da yanga, wanda kallo ɗaya zakayi mata kagane ita ɗin ba ƙaramar gogaggiyar ƴar duniya bace, duk a yanzu ɗin tayi shigan mutunci, but hakan be hana bayyanuwan Tatue ɗin dake zane a jikin ta ba, ƙarisawa tayi tasaya kamar yanda kowa ke yi, sannan shi kuma yatako kusa da ita yana faɗin
"Fadila zan so kisanar da Kotu sunan ki da inda kike?"
Murmushi tasakar masa kana takalli dandazon mutanen wajen tace
"Sunana Fadila kuma Ni ɗin ƴar garin Kano ce, but ina zaune a EGYPT yanzu, kuma daga can nadawo nan".
"Ok shin ko kinsan Alh. Mubarak me kuɗi?"
"Ƙwarai kuwa nasan shi tun shekaru 7 da suka wuce, yana yawan zuwa EGYPT wajen uban gidan mu".
"Shin menene alaƙan shi da uban gidan naku? Kuma kinsan me yake zuwa yi?"
"Eh na sani, yana siyar wa da Mr. Jay pitter ƴan mata, shi kuma sai yazamar dasu karuwai".
Murmushi Brr. Khalil yayi yace "mun gode Fadila, zaki iya komawa kizauna".
Sannan yajuya ga wajen zaman sa, kallon Brr. Bilkisu yayi yai mata alama da ido, sai tamiƙo masa wasu Files, amsa yayi yadawo tsakiyar kotun yana cewa
"Waɗannan Files ɗi su ne duk wani shaidu da ke kan Alh. Mubarak me kuɗi na zuwan sa EGYPT da safaran ƴan mata da yake yi duk suna cikin nan".
Sannan yamiƙa ma Maga-takarda yaci gaba da faɗin
"Da wannan nake roƙon kotu da tayanke wa Alh. Mubarak da Dr. Sabit da duk wasu waɗanda suke da hannu aciki hukunci dai-dai da abinda suke aikatawa, Nagode ya Me Shari'a".
Zama yayi, Alƙali yakalli Brr. Mahmoud yace
"Kana da abin cewa Brr. Mahmoud?"
Miƙe wa yayi yace "a'a ya me Shari'a, sannan yakoma yazauna
Rubutu yasoma yi Alƙalin kafin yaɗago kansa yana kallon mutanen wajen yace
"Abisa zargin da ake ma Alh. Mubarak me kuɗi tare da abokan aikin sa bisa ga tarin hujjoji da aka gabatar, kotu ta gamsu kuma ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga Alh. Mubarak me kuɗi tare da Dr. Sabit, sakamon kama su da yin babban laifi na safaran mata tare da raba su da iyayen su amaishe su karuwai, sannan tare da laifin siyar da Coken, zasu ƙare rayuwan su cikin Jail tare da horo me tsanani, sannan kuma zasu biya taran Miliyan biyar ko wannen su, sannan kotu ta yanke ma Aliyu Gadanga ɗaurin gidan kaso na shekara 10 sakamakon da hannun sa cikin aikata laifin, wannan shine sakamakon hukuncin da suka aikata".
Daga nan Alƙali yabuga guduman sa yamiƙe tsaye, gaba ɗaya mutanen wajen suka miƙe suna me faɗin "Kooooooootuuuuuuu".
Hayaniya wajen yakaure dashi yayinda mutane ke ta turuwan ficewa, alokacin ne kuma ƴan sanda suka taso ƙeyan su Alh. Mubarak zasu tafi dasu, iyalan su in banda kuka babu abinda suke yi
Brr. Khalil kuwa tun aciki yasoma gaisawa da mutane ana masa murna sai zuba murmushi yake yi, koda suka fito waje nan ƴan jarida sukayi masa caaa, dasauri Kausar tature mutane tamatso kusa dashi tana cewa
"Brr. Zamu so kasanar mana wani irin farin ciki kake ji yayinda kayi nasara a wannan gagarumar shari'ar?"
Murmushi yasakar mata kana yace "Farin ciki mara misaltuwa, ko ba komi yau na kawo ƙarshen wasu daga cikin mugayen ƙasar mu, kuma ina roƙon Allah yatona asirin duk waɗanda suke da hannu a ɗaukan ƴaƴan mutane suna fita dasu wasu ƙasan don karuwanci".
"To wani jan hankali kake dashi a gare su?"
"Su tuna cewa su ma suna da ƴaƴa, idan hakan tafaru dasu bazasu ji daɗi ba, idan har basu tuba sun dena wannan banzan harƙallan ba to da sannu zasu girbe abinda suka yi sannan ƙarshen su bazai taɓa kyau ba".
Wasu tambayoyin suka soma mishi amma yayi gaba abin sa batare da ya amsa musu ba
"BARRISTER".
Yaji an kira sunan sa daga bayan sa, juyowa yayi yana kallon ta sai yasakar mata murmushi, ƙarisowa tayi wajen itama tana murmusawa tace
"Congratulations, na gode sosai da taimakon ka gare Ni, haƙiƙa bazan taɓa mantawa da kai ba, thank you so much BARRISTER".
Still yana murmusawa yace "Babu komi Fadila, yanzu yaushe zaki koma gida?"
Ɗan fari tayi da idanu tace "yanzu".
"Ok sai kin kawo mana ziyara kenan?".
Murmushi tayi tace "insha Allahu".
Daga nan sallama sukayi kafin yanufi wajen motan sa inda su Sameer da su Mom tare da su Brr. Tahir suke jiran sa, yana isowa Sameer yaja kumatun sa yace
"Ɗan ƙanina na tayaka murna".
Dariya gaba ɗayan su sukayi kafin sukayi sallama duk suka shiga motocin su ganin Ƴan Jarida na damun su, suka bar wajen.
[9/30/2020, 10:43 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️ ~Wattspp Number 07065334256~
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 33*
Halwa ce zaune saman gado kusa da na Saleema dake barci har yanzu bata farka ba, but yanzu babu Oxgyen da aka saka mata sabida Numfashin ta ya dai-daita
itama Halwan an sanya mata drip a hannun ta, Ummi dake zaune saman kujera tana yanka Lemo cikin plate, bayan ta gama sai taɓare ayaba shima duk tajera akan plate ɗin tamiƙa ma Halwa tace
"Riƙe kisha wannan nasan zai fi miki, bazaki zauna haka tun safe baki ci komi ba".
Babu musu Halwa ta'amsa tasoma ɗauka tana sha, Nurse ce tashigo da sallaman ta taƙariso wajen su tana cewa
"Ya jikin naki? Da fatan yanzu kina jin ƙarfi sosai ajikin ko?"
Gyaɗa kai Halwa tayi tana kallon ta
"Ok gashi wannan maganin ki ne zaki riƙa sha a rana sau biyu, Allah yasauwaƙe".
Ummi ne ta'amshi maganin tana cewa "Ameen mungode".
Matsowa tayi tagyara mata ruwan kafin tafito da allura cikin aljihun ta tasoma haɗawa tana faɗin
"Har yanzu ita bata farka bane?".
"Eh". Ummi ta'amsa mata tana kallon Saleema".
"Ok idan ta farka Sister Asma'u sai ki sanar da Doctor ɗin".
Ummi tace "ok ba matsala".
Alluran tatsira cikin Drip ɗin Halwa kana tayi musu sallama tafice, ruwa Ummi tamiƙo mata tare da ɓallo maganin shima tamiƙa mata tace
"Gashi kisha, amma kiyi sauri kishanye Fruits ɗin kinsan babu komi acikin ki".
Gyaɗa kanta tayi ta'amsa maganin tazuba a baki tana runtse idanu kafin takora da ruwa, daƙyar ta iya haɗiyewa tana sakin nishi, murmushi Ummi tayi tace
"Da alamu bakison magani ko?"
Itama Halwa murmushin tayi tana sauke kanta ƙasa
"To yi sauri kishanye mana".
Ci gaba tayi da shan Fuirts ɗin har tashanye, Ummi ta'amsa plate ɗin ta'ajiye, gyara zaman ta tayi tana kwanciya tare da rufe idanun ta, barci take ji sosai kasancewar Alluran da akayi mata cikin Drip ɗin na barci ne coz ana son tasamu hutu sosai, babu jimawa kuwa barci yayi awon gaba da ita, koda Ummi tayi magana taji shiru hakan yatabbatar mata da barci ya ɗauke ta, tashi tayi takoma saman kujerun dake ɗakin taɗau remote tana sauya tasha, a *ƳAN CI T.V* tabari tasoma kallon Labaran da ake nunawa na hukuncin da aka yanke akan su Alh. Mubarak, in banda girgiza kai babu abinda Ummi take yi.
Tsawon awa ɗaya kafin ruwan da aka saka ma Halwa yaƙare, har wannan lokacin kuma acikin su babu wacce tafarka, tashi Ummi tayi tacire mata Drip ɗin kana tashiga Toilet tayi alwala tafito, fita tayi babu jimawa tadawo riƙe da dadduma, sallan la'asar tayi, bayan ta idar tana zaune tana lazimi Abba yashigo, ƙarisowa yayi yazauna yana kallon ta, itama ɗago kanta tayi tai masa sannu da zuwa, amsawa yayi yace
"Yakamata ki koma gida sai in zauna dasu, tunda yau ba aiki zakiyi ba".
Ummi tace "a'a Abban Saleema babu abinda zan yi ko na koma gida, nasan tunda akwai Larai zata kula da komi, kuma zata kawo mana abinci nan tunda tasan muna nan ɗin".
Gyaɗa kansa yayi yace "ok shikenan, bari ni inje yanzu zan dawo insha Allah, idan ƴar Baba tatashi ki kira ni awaya idan ban dawo ba".
"Toh".
Daga nan tashi yayi yafice ita kuma taci gaba da lazimin ta.
***** ******* ***********
Shigowan sa kenan cikin gidan nasa, tun gama shari'an gaba ɗaya suka wuce gidan su sai yanzu yadawo, ahankali yabuɗe ɗakin nasa yashiga, aje komi yayi tare da cire kayan jikin sa yawuce cikin Toilet wanka yayi sannan yafito, ko mai be shafa ba yaɗauko kayan sa ƙaramar riga fara da dogon wando robber shima fari yasaka, fitowa Parlour yayi yazauna saman 3sitter, wayoyin sa da suke kashe duk ka biyun yaɗauka yakunna, saƙonni ne suka soma shigowa, sai da suka gama gaba ɗaya sannan yasoma buɗe wa yana gani, duk yawanci Abokan sa ne da waɗanda yasani suke tayasa murna, be fi guda goma yabuɗe ba yamayar da wayan ya'ajiye tare da kwanciya yana ɗaura hannun sa ɗaya saman fuskar sa yalumshe idanun sa, ya ɗau tsawon awanni yana ahaka, babu abinda yake yi sai tunani, sai da yaji kiraye-kirayen sallan Magriba kafin yamiƙe a kasalance yashiga Toilet ɗin dake parlour'n yaɗaura alwala yatafi masjid.
*** ***** **** ****
*BAYAN KWANA BIYU*
A kwana biyun nan sosai jikin Saleema yayi sauƙi, don haka aka sallame su suka koma gida, gaba ɗaya Ummi tahaɗa su tana basu kulawa kasancewar har alokacin itama Halwa sosai take fama da jikin ta, laulayi ya sako ta gaba ko abinci sai anyi dagaske take ci, gaba ɗaya ta rame sai haske da tayi, komawar su gida ma sai da Ummi tasake saka mata Drip sabida yawan aman da take yi.
Yanzun ma kwance take saman gado, duk ta ƙudundune jikinta cikin bargo tana ta rawan ɗari, Saleema kuma na zaune gefen ta tabuga uwar tagumi tana kallon ta, fuskarta ya nuna damuwa sosai kamar tayi mata kuka, cikin tsananin tausayawa tace
"Wai meyasaka baza'a cire cikin bane? Kina shan wahala da yawa.."
Ummi da shigowar ta ɗakin kenan taji maganar da Saleeman take yi tayi saurin katse ta
"Kull.. kar in sake jin kin bata wannan shawaran, bakisan haramun bane zub da ciki? Bana son in sake jin kin faɗa mata hakan kinji ni?"
Gyaɗa kanta Saleema tayi tace "Toh Ummi".
Zama Ummin tayi tana ajiye Coolarn da tashigo dashi tare da plate tace
"Tashi kici abinci Halwa, Faten wake ne nasanya akayi miki nasan zakiji daɗin sa kinji? Tashi maza kici".
Saleema tace "to Ummi kawo in zuba mata".
"Ai har dake zakici, in kun gama sai kusha maganin ku ni zan tafi asibiti, sannan nasaka Larai tayi muku Farfesun kayan ciki, shima sai kuhaɗa dashi kuci, ni natafi ku kula da kanku sosai kunji?".
Gyaɗa mata kai sukayi, daga nan ficewa tayi bayan Saleema tayi mata "adawo lafiya". Tana fita Saleema tabuɗe Coolar'n tazuba musu Faten waken da yaji nama sai tashin ƙamshi yake yi, kallon Halwa da har yanzu take kwance tayi tace
"Tashi muci".
Sai kuma ta'ajiye abincin a ƙasa tana matsowa kusa da ita tataimaka mata tasauko, zama sukayi a ƙasa suka soma ci, Halwa bata wani ci sosai ba tamatsa gefe tana ɗan sakin nishi, Saleema kallon ta tayi tana shirin yin mata magana sai taga tasoma kwarara amai, dasauri tamatsar da abincin tamiƙe tana riƙo ta ganin tana shirin faɗuwa, sai faman sannu take mata kamar zatayi mata kuka, sai da ta amayar da duk wani abinda ke cikin ta sannan tatsakaita tana numfarfashi cike da galabaita, taimaka mata Saleeman tayi suka shiga Toilet tawanke jikin ta kafin suka fito, zaunar da ita saman gadon tayi takoma Toilet ɗin taɗauko kayan Moping tawanke wajen tare da sharewa, sai tadawo tazauna tana kallon Halwan da itama tazuba mata idanu tana jingine jikin gadon, murmushi tasakar mata cikin sanyin murya tace
"Na.. go..de".
Waro idanu Saleema tayi tana mata alama da hannu "na mene?"
"Bansan da me zan saka miki ba, kin taimaki rayuwata sosai, kin zame min ƴar uwa alokacin da narasa kowa nawa, sannan kin kawo ni gidan ku kin maishe da ahalin ki ahalina, wlh bansan da bakin da zan miki godiya ba, haƙiƙa bazan taɓa manta ki cikin rayuwata ba, daga yau kece komi nawa kuma insha Allahu zan ɗauke ki ƴar uwa kuma wacce zata maye min gurbin ƙawata Zainab".
Runtse idanun ta tayi jin hawaye na son zubo mata, Sai kuma tabuɗe tana murmushi tace
"Daga yau bazan sake kewarta ba tunda har nasami madadin ta".
Riƙo hannun ta Saleema tayi itama tana murmusawa tace
"Ki dena faɗan haka, Ni nayi ne duk sabida Allah, sannan naji daɗi da kika ɗauke Ni ƴar uwa ƙawa, dama na daɗe ina jiran ranan da zan sami tawa ƴar uwan, sai gashi Allah yabani ita har gida".
Sai kuma tasaki dariya har haƙoran ta suna bayyana, tamiƙe tsaye tana faɗin
"Bari in amso mana ferfesun sai ki ƙara ci tunda kin amayar da wannan da kikaci, ina zuwa".
Daga haka fita tayi dasauri, bata jima ba tadawo ta'ajiye musu a saman gadon, sai taɗauko maganin Halwan dake ajiye a kan drower tadawo tazauna, nata tabuɗe taɓalla tasha tare da korawa da ruwa, sai takalli Halwa tana sakar mata murmushi tace
"To kema kici sai kisha maganin ko?"
Gyaɗa kanta tayi tana saka hannu tashare hawayen da suka sulmiyo kan kuncin ta batare da Saleeman tagani ba, bayan ta ɗan ci kaɗan sai tasha maganin sannan taci gaba taci, Saleema kuwa cire hannun ta tayi tana yin gyatsa tare da faɗin
"Alhmadulillah Ni dai na cika cikina, saura ke".
Kallon juna sukayi sai suka saki dariya gaba ɗayan su
"Kinsan me?" Cewar Saleema tana shafa cikin ta
Girgiza mata kai kawai tayi tana kallon ta
Cikin sakarci irin na yaran masu kuɗi tace "Idan kin haihu ko Ni zaki bama Baby, Ina son shi ni zan kular miki dashi, zamu riƙa wasa tare in koya masa karatu da komi da komi, kinji zaki bani ko?"
Saurin sauke kanta ƙasa Halwa tayi tana jin hawaye na zubowa daga idanun ta, sai tayi saurin tare hannun ta tasharce shi, hannu itama Saleeman takai tana sharo mata hawayen cikin sanyin murya tace
"Kuka kike yi? Ni ce ko? Kiyi haƙuri Don Allah".
Ɗago kanta tayi tana kallon ta tare da girgiza mata kai, still tana hawayen tace
"A'a ba don ke nake yin kukan ba, kawai na tuna da gida ne, ina matuƙar kewar su Mama, ina matuƙar kewar su sosai.."
Sai tafashe da kuka, nan da nan jikin Saleema yasoma yin rawa sai itama tafashe da kukan
_"Bamu san ya zamuyi ba idan muka rasa Saleema, muna tsananin ƙaunar ta ni da mahaifinta, kuma ita kenan gare mu ita kaɗai ce mallakin mu, amma kuma Allah ya ɗaura mata ciwon da muke ganin koda yaushe zamu iya rasa ta, a kullum burin mu shine mu saka ta farin ciki.."_
Tunawa da maganganun Ummi ne yasaka Halwa saurin katse kukan ta tana kallon Saleeman da ita har yanzu bata dena nata kukan ba, dafa kafaɗunta tayi cikin murmushi tace
"Menene na kuka ke kuma? Kinsan da cewa baki da lafiya don Allah ki dena kar wani abu yasame ki".
"Taya kike tunanin zan dena bayan na ganki cikin ƙunci? Ina matuƙar tausaya miki idan natuna labarin ki, bana jin daɗi ko kaɗan idan naganki cikin damuwa".
Dariya Halwa tayi tace "to na daina ai, kuma Ni ina kuka ne sabida farin ciki, farin cikin na sami ƴar uwa me ƙaunata, wacce take ƙaunar abinda zan haifa tun kafin yazo duniya, insha Allahu idan har nahaife shi na baki shi kyauta, daga lokacin kece mahaifiyar duk abinda zan haifa".
Itama dariya Saleema tayi tace "wayyo naji daɗi sosai, bari su Ummi su dawo zan sanar musu, amma kuma kinsan me Yakamata in saka masa a suna?"
Girgiza kanta Halwa tayi tana dariyan shirmen Saleema, wani lokacin in tana abu tamkar ƙaramar yarinya, kuma duk sangarta ne da yayi mata yawa, sai da ta ɗan yi tunani kana tawashe baki tace
"Idan mace ne zan saka mata sunan Ummi, idan kuma na miji ne sai in saka masa Abbana".
Murmushi Halwa tayi tace "hakan yayi".
Matsowa sosai Saleema tayi kusa da ita kana tace "yauwa yanzu ya jikin naki dasauƙi ko?"
Gyaɗa mata kai tayi, duk da tana jin ciwo amma bazata iya nuna mata ba coz yanda taga tana nuna damuwarta sosai
"Ok bari in baki labari, zan baki labarin school ɗin mu tare da ƙawaye na".
Labarin tasoma bata suna ta dariya kamar basu ba, kuma duk kan su idan kakalle su zaka gane ba ishashshen lafiya ne dasu ba, sai dai ƙarfin hali kawai da suka ara suka yafa, daga ƙarshe ma barci ne yaɗauke su sakamakon maganin da suka sha akwai na barci aciki.
_Allah Sarki wannan shi ake cewa gamon jini, Allah yahaɗa mu da masu son mu fisabilillahi._❤️🙏🏼
[10/1/2020, 1:46 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 34*
Kwance take saman gadon ta daga ita sai ƴar shimi fara ƙal, sai jan wando robber da yamatse ta sosai wanda da kaɗan yawuce gwiwarta, wayan ta dake ajiye saman gadon ne tasoma ringing sai tajawo tana kallon screan ɗin wayan, ganin sunan HONEY yafito ɓaro-ɓaro yasaka tayi peacking call ɗin tana kangawa a kunne, shiru tayi tana sauraron sa sai kuma ta'ajiye wayan tamiƙe tsaye tana ɗaukan Red colour Jaket ɗin dake ajiye saman gadon tasaka, Jaket ɗin irin me buɗaɗɗen gaba ne sai Belt da aka saka a iya tsakiya wajen cikin ta, iyakan cinyan ta yatsaya mata, sai taɗau Facing cap shima Red tasaka tafito, Ahmad ne kaɗai yake zaune Parlourn yana kallo takalle shi tace
"Idan Mami tafito kasanar mata nafita wajen Sharif".
Ahmad yace "ok".
Fita tayi tanufi inda yake tsaye jikin motan sa, tun fitowan ta yake kallon ta yana murmushi har ta'iso wajen
"My beautiful girl". Yace hakan yana sake faɗaɗa fara'ar sa
Ɗan cije laɓɓanta tayi tana kallon sa itama cikin murmushi tace "ya kake?"
"Lafiya, kefa?"
"Lafiya lau". Tayi maganar tana jingina da motar itama kamar yanda yayi, sai dai facing juna suke yi
"Kinsan me?".
Girgiza kanta tayi still tana kallon sa
"Kullum sai in riƙa jin ƙaunar ki na ƙara zauta Ni, har yanzu nakasa sabawa da yanayin da nake ji a kanki".
Sai ya ɗan yi murmushi yana shafa kwantaccen ƙasumban sa yaƙure ta da ido yace
"Na ƙosa Kausar kikasance mallakina, ina ji ajikina kamar in ban yi dagaske ba zan iya rasa ki".
Kallon da take masa ne yasauya zuwa mamaki, amma sai batace komi ba taɗauke kai tana jin zuciyar ta na bugawa, kiran sunan ta Sharif ɗin yayi, sai taɗago kai kawai tana kallon sa
Yace "har yanzu baki bani amsa ba akan maganar da mukayi dake".
"Wace magana kenan?" Tatambaye sa cike da rashin fahimta
Murmushi yayi yace "har kin manta maganar da mukayi lokacin da zamu dawo Nigeria? Haba Dear yakamata ki bama zance na muhimmanci, Ni nayi miki alƙawari wlh zan bar ki kici gaba da aikin ki koda munyi aure, be kamata mu zauna muna ɓata lokaci ba bayan kinsan da cewa mun fahimci juna, kuma iyayen mu sun san komi, to me muke jira?"
Shiru kawai tayi tana sauraron sa har sanda yadasa aya, sai kawai tasaukar da kanta ƙasa tana tunani, gaba ɗaya murmushin dake fuskarta ya ɓace, sai damuwa da yamaye gurbin
"Kausar".
Saurin ɗago kai tayi takalle sa
"Wai me ke damun ki ne? Na kula gaba ɗaya kin sauya yau meke faruwa?"
"Ban jin daɗi ne Honey".
"Eyya shine baki sanar min ba? Kinsan bana Son abun da zai dame ki, yanzu meke miki ciwo?"
Yaƙe tayi tana kallon sa tace "kar ka damu kawai gajiya ne yahaddasa min ciwon kai".
"Eyya sorry, kije gida to sai muyi maganar awaya, Allah yasawaƙe kinji?"
"Ameen".
Sake sallama sukayi sannan tajuya tatafi, shi kuma yabi bayan ta da kallo har sanda tashige, ajiyan zuciya yasauke yana buɗe motan sa yashiga yabar gidan
Ita kuma tana shiga parlour tawuce ɗakin ta dasauri, akan gadon ta tafaɗa tana sauke numfashi, shiru tayi na ɗan wani lokaci kafin tajawo wayan ta tana latsawa, Numban Khalil talalubo sai tatsaya kawai tana kallo, daga ƙarshe sai tadanna masa kira, har yatsinke be ɗauka ba, akaro na biyu ma da takira be ɗaga ba sai tayi jifa da wayan tana kifa kanta tare da rufe idanu, kamar an tsikare ta kuma sai tamiƙe tafito parlour, har yanzu Ahmad ne kaɗai zaune, ficewa kawai tayi shi kuma yabi ta da ido.
Tana fitowa gidan su ta'isa bakin Gate ɗin gidan Khalil tasoma nocking, Me gadi ne yaleƙo da kansa yana ganin ta yabuɗe mata, murmushi tayi masa tace
"Yana nan ko?"
"Eh yana nan, yanzun nan yadawo".
Shiga tayi tanufi cikin gidan, tana isa tasoma nocking sai dai shiru babu amsa, ta ɗan jima a wajen tana tunani sannan kuma sai tasaka hannun ta tamurɗa handle ɗin ƙofan yabuɗe, shiga tayi tana kallon parlour'n, babu kowa sai plasma dake aiki shi ƙadai, kan kujera tasamu tazauna sannan tasoma sallama
Khalil dake cikin ɗakin sa, fitowan sa kenan daga wanka yajiyo sallaman ta, ya gane ko wacece don haka kawai yaci gaba da shiryawan sa, bayan ya gama ne yafito parlour'n yasami wuri yazauna yana kallon ta, murmushi tayi masa tace
"Ashe kana lafiya? Na kira wayan ka naji shiru baka ɗauka ba shine nashigo in duba ka".
Shima murmushin yayi mata yace "sorry ban jiba ne, to ya aikin naki?"
Still tana murmusawa tace "alhmadulillah, kai fa?"
Sai ya ɗan kwaɓe fuska sannan yace "ba daɗi".
Dariya tayi sosai tana kallon sa yayinda shima ɗin ita yake kallo yana sakin murmushi, sosai take jinta cikin farin ciki ganin ta tare dashi
"Yunwa nake ji ko zaki dafa min abinci irin na ran nan?"
Tsayar da dariyan nata tayi tana kallon sa da murmushi a face ɗinta tace
"Me zai hana, ko me kake so zan yi maka ai".
Sai tatashi kuma tana faɗin "kabani mintuna 20 yanzu zan gama maka".
"Ok to muje nima in tayaki ko na koya nima".
Kausar taji daɗi sosai ganin yanda Khalil yasaki jiki da ita a yau ɗin, atare suka gama abincin suka zubo kuma sukaci tare, duk kan su in kakalle su zaka gane suna matuƙar farin cikin kasancewar su tare, duk abun da ɗaya yayi sosai yake burge ɗayan, Kausar ba ita tabar gidan ba sai bayan la'asar.
***** ***** ***** ****
"Zainab wai yaushe zaki dena wannan kukan ne? Tun sanda Halwa tatafi kullum cikin kuka kike yi, ko kukan naki ne zai dawo da ita?"
Shiru Zainab tayi sai dai har yanzu hawaye basu dena zuba cikin idanun ta ba
Umma tace "ki tashi kije ki ɗiba ruwa kiyi wanka tunda yanzu kin zama ƙazamiya wankan ma kin dena".
"Umma Ni har yanzu na kasa yarda da abinda Mama da Nura suka faɗa mana, ta ya Halwa zata tafi tabar su lokaci ɗaya? Ya za'a yi Halwa tatafi batare da ta sanar min ba? Tunda muke da ita ban taɓa jin Halwa tayi maganar dangin mahaifin ta ba, ta ya zasu ce don sun zo ganin ta zata bi su tabar su?"
Sai kuma tafashe da kuka, cikin kukan take cewa
"Wlh Umma ƙarya ne, ƙarya suke yi suce Halwa tazaɓi dangin Mahaifin ta akan su, zuciyata takasa yarda da abinda suka faɗa, suna nufin kenan fa tatafi bazata sake dawowa ba? Ni na tabbata sai dai in wani abu ne yafaru amma Halwa baza ta taɓa tafiya ba".
"To don ubanki tunda baki yarda dasu ba sai kiyi tayi, ko kuma kibi ta inda kikasan tatafi". Umma tafaɗi hakan a zafafe domin Zainab ɗin tasoma kai ta maƙura akan zancen Halwan
Tashi Zainab ɗin tayi tashige ɗakin ta batare da tasake furta komi ba.
October 2020.
[10/19/2020, 7:48 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 35*
Dad da Mom da Nazeefa ne zaune saman dainnig table suna yin luncing, baka jin ƙaran komi sai Spoons, ita Nazeefa kanta na ƙasa daƙyar take cakalan abincin, don har yau bata saba dasu ba, gwara-gwara Mom in suna tare su biyu.
Sameer ne yashigo cikin parlour'n yanufo su yana faɗin "wow nazo a sa'a domin yunwan nima nake ji".
Mom da taɗago kai tana kallon sa tace "ba daga gida kake bane?"
"Eh naje wajen Friend ɗina ne, kuma daga nan muka wuce Hospital shine nabiyo ta nan".
Gyaɗa kai kawai Mom tayi tamayar da hankalin ta ga abincin ta
"My Dad barka da rana". Sameer ɗin yafaɗa yana dafa glass table ɗin da hannayen sa
Dad kaɗa masa kansa kawai yayi sakamakon ya sanya abinci a baki
sai lokacin Nazeefa taɗago kanta tace "sannu da zuwa Yaya".
Sameer ɗaura hannun sa yayi akanta yana kallon ta yace "Yauwa ƙanwa ta, abinci kike ci ne haka babu tayi?"
Murmushi Nazeefa tayi tana Sad da kai ƙasa, zama yayi gefen ta kana yace
"To nima yi saving ɗina in tayaku".
Plate tajawo tasoma saving ɗin shi
Dad yace "Sameer yau wai ya naji wayan Ibrahim be shiga lafiya dai? Kuma ban gansa ba kwana biyu".
Ɗago kai yayi Sameer yana kallon sa yace "Dad wlh ban sani ba, nima dai tun yesterday rabona dashi kuma bamuyi waya ba".
"Ok ƙara try Numban sa kaji yanzu".
"Ok Dad".
Wayan sa yaɗauka yasoma kiran Khalil, ringing ɗaya tashiga but babu answer, sai da yayi two missed calls kafin Dad yace masa "yaƙyale sa haka". Abincin su sukaci gaba da ci, kamar 5mint kuma sai ga wayan tana ringing, Khalil ɗin ne yakira, ɗauka Sameer yayi zai miƙa ma Dad sai yace masa
"Ɗauka kawai kace masa ina kiran sa yanzu yazo yasame Ni".
"Ok Dad".
Peaking call ɗin yayi yace "Hello ɗan ƙanina".
Khalil dake zaune bakin gado daga shi sai gajeren wando yaɓata fuska yana cewa "Bro bana so fa nace maka".
Ɗan dariya Sameer yayi kana yace "ok na daina, kazo Dad na Kiran ka".
Ɗan jimm Khalil ɗin yayi kana yace "ok ga ninan".
Daga nan kashe wayan sukayi ya'ajiye tare da miƙewa tsaye yanufi wajen sif ɗin kayan sa yafito da wanda zai saka, bayan ya shirya as usual cikin ƙananan kaya farar riga da blue jeans, yasanya brown cover shoes yanufi gaban looking glass yabuɗe locker yafiddo car key yafice, a cikin ɗaya daga cikin motocin sa kalan ruwan zuma yashiga, be cika hawa motan ba sai yaga dama, yanzun ma yau yafiddo ta yasaka aka wanke masa, yana isa bakin Gate yadanna hon aka buɗe masa Gate ɗin yafice, ahankali yake tuƙin nasa har yakai gidan nasu yafito yashige cikin gidan, a lokacin su Mom sun dawo saman kujerun parlour'n suna zaune suna hira, in kaɗauke Nazeefa da bata wajen ta shiga ɗakinta
Lokacin da ya'isa cikin parlour'n bayan ya gaishe da iyayen nashi zama yayi kusa da Sameer dake zaune kan Two sitter
Dad yace "yauwa ina maganar mu da muka yi, shin ka samo matar da zaka aura?"
Shiru Khalil yayi yana kallon Dad ɗin batare da yace komi ba, haka zalika su ma kallon sa suke yi suna son suji me zai faɗa, ganin shirun nasa yayi yawa Mom tace
"Auta kayi shiru, ko har yanzu baka samu matar bane?"
"Ai kuwa idan be samu ba Ni sai in nema masa tunda naga abun nasa yana ɗaukan sa da wasa ne". Cewar Dad kenan
Khalil kuwa shafo gashin kansa yayi yajuya kai yana kallon Sameer Wanda shima ya kafe shi da nashi idanun yana kallon sa, alama yayi masa da ido sai yakau da kansa yana kallon Dad ɗin yace
"Dad na samu".
"Masha Allah haka ake so, yanzu yarinyan aina take kuma ƴar wacece?"
"Suna zaune a Jan Bulow, mahaifinta sunan sa Alh. Ahmad Sofana".
"To Alhmadulillah insha Allahu zamu je zuwa gobe ko jibi don gwara ayi a huta".
Mom washe baki tayi tace "My Son na tayaka murna, Allah yatabbatar da alkhairi".
Murmushi kawai yayi yana faman sosa kai, Sameer kuwa ɗan bugun kafaɗan sa yayi yace
"Congratulation My Lil Bro Allah yasanya alkhairi Allah yasa ayi damu, Burina dama kenan naga auren ka gashi komi yakusa zuwa".
Mom itama cikin farin ciki ta karɓe zancen da cewa "wlh kuwa ai nima nafi kowa son ganin wannan ranan, amma Auta mene sunan surukar tawa? ya kamata kasanar min tun yanzu in sani sannan kakawo min ita in ganta don in tabbatar da cewa ka dace da yarinyan ko kuwa".
Dariya Dad yayi yace "kai uwar yara wannan zumuɗi haka? Ai sai ki bari komi yakankama tukuna ko?"
Itama dariya tayi tace "Uhm baza ka gane bane amma Ni kaɗai nasan irin farin cikin da nake ji, Ni kaɗai nasan me na tanada a auren Autana".
...... ........ ........ .......
Da gudu ta'isa kan gadon ta tafaɗa tana sakin kuka me ƙarfi, sosai take kuka sai kazata yanka ta ake yi, kukan baƙin ciki na jin hiran nasu, bata taɓa tunanin ƙaunar Khalil take yi ba sai a ɗan kwanakin nan tagane, hakan yasaka wani baƙin kishi yaturnuƙe ta jin ya sami wacce zai aura "shikenan yanzu ita ta rasa shi?" Tambayan da tayi ma kanta kenan tana sake kecewa da kuka, duk da tasan yafi ƙarfin ta amma sosai take matuƙar ƙaunar sa fiye da tunanin me karatu, batasan wani hali zata shiga ba idan har tarasa shi, baza ta iya juran ganin sa da wata ba
Jin motsi kamar za'a shigo tayi saurin tsayar da kukan nata cak tana juyawa takalli ƙofan shigowa, dasauri takuma saka hannun ta tashare hawayen fuskarta dai-dai lokacin da Mom tabuɗo ƙofa tashigo, kallon ta tayi yayinda ita kuma tasad da kanta ƙasa tana murɗe yatsun hannunta
"Nazeefa lafiyan ki ƙalau kuwa naga kamar kin yi kuka? Meke damun ki?" Mom tatambaye ta cike da kulawa
Shiru Nazeefa tayi sai kuma tabuɗe baki ahankali cike da rawan murya tace "ba..bu ko..mi Momy, wani abu ne yafaɗa min a idanu".
"Subhanallah sannu, yanzun ya fita ko kuwa?" Still Mom ɗin tasake tambayar ta cike da nuna kulawan ta tana saka hannayen ta taɗago kan Nazeefan tana kallon idanun da suka sauya kala
"Eh ya fita".
Mom tace "ok sannu ko? Allah yakyauta gaba".
"Ameen".
"To tashi yanzu kije Yayan ki na kiran ki zakuyi maganar School ɗin ki da zai saka ki".
Nazeefa ta'amsa mata da "Toh". Kana tatashi tanufi ƙofa, itama Mom bayan ta tabi suka fice atare.
****** ****** *******
A cikin satin ne Alhaji Abdurra'uf tare da abokin sa Alh. Mustapha sai kuma Yayar Mom Alh. Maddibo suka je nema ma Khalil auren Bilkisu, koda suka isa gidan kyakykyawar tarba suka samu wajen ƙanin Mahaifin ta kasancewar a wajen sa take zaune, bayan da su Dad suka gabatar da abinda suka zo nema, Alh. Umar wato ƙanin Mahaifin nata nan yasoma magana cikin dattako
"Alhmadulillah gaskiya naji daɗi sosai da akace kamar ku kun zo neman auren ƴata hakan ya faranta min rai matuƙa, sai dai matsalan da akwai wanda nayi mamaki matuƙa cewa ita yarinyan bata sanar muku ba sannan kuma nayi mamaki kan cewa ta turo wani don yanemi auren ta".
Ɗan jan numfashi yayi yana kallon su yaci gaba da faɗin
"Zan baku haƙuri da cewa mun riga da munyi wa ƴar mu Miji tun tana ƙarama, wanda hakan shine abinda muka saba tun farkon dangin mu wato haɗa auren zumuncin, ina fata zaku fahimce Ni kuma hakan bazai ɓata muku rai ba?"
Alh. Maddibo ne yace "a'a wlh babu komi, ai kayi mana bayanin da zamu fahimta hakan ya gamsar damu, shikenan dama Allah yayi nufin ba matar sa bane Muna godiya sosai".
Alh. Umar yace "ai Ni ne da godiya bisa abinda ƴar mu tayi, tunda da tasanar dashi duk hakan bazai faru ba".
Daga nan dai tashi su Dad sukayi tare da yi masa sallama suka tafi, a hanya Alh. Maddibo yayi musu sallama suka rabu yayinda Dad da Alh. Mustapha suka wuce wajen aikin su.
Bilkisu asalin su Nufawa ne ƴan garin Minna, tana zaune wajen ƙanin Mahaifinta ne anan Katsina, babban Family ne dasu kuma sun saba yin auren zumunci ne, ita kanta Bilkisu akwai wanda aka haɗa ta dashi tun tana ƙarama, sai dai shi ɗin baya ƙasar ne yana zaune can Sudan yana aiki, daga zuwa karatu yazauna har yanzu yaƙi yadawo, Allah ne yasaka mata ƙaunar Khalil har takasa haƙuri dashi duk da tasan zai yi wuya ta aure shi, amma soyayya ya rufe mata idanu kwata-kwata ta manta da cewa akwai wanda iyayen ta zasu bata, kuma nan bada jimawa ba ake tunanin sanya ranan auren nasu.
[10/21/2020, 4:12 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
_wannan shafin naki ne ZEENAT, ina godiya da yanda kike ƙaunar Littafina, Allah yabar ƙauna_❤️
.
*CHAPTER 36*
Dad na zaune a parlour'n sa Khalil yashigo yazauna kan kujeran da ke Facing Dad ɗin, Dad ce masa yayi
"Ina fata kaji abinda ke faruwa ko?"
Gyaɗa kansa Khalil yayi
Dad yace "yanzu kana da wata ko kuwa?"
"Dad ni Banda wata, ni abar ma maganar sai zuwa nan gaba don ban shirya aure yanzu ba dama".
Kallon sa Dad ɗin yake yi be ce komi ba, sai kuma can yabuɗi baki yace "Ibrahim ba maganar wasa muke yi da kai ba, aure nake so kayi kuma a wannan lokacin na gaji da ganin ka haka, idan har maganar neman mata kake yi to Ni na samo maka, akwai yarinyan Abokina da zaka je kanema domin yanzu mun riga da mun gama maganar da Alh. Mustapha".
Ɓata fuska Khalil yayi yace "Dad meyasaka kake son kabani wacce bana so?"
Murmushi Dad ɗin yayi yace "har yanzu kai yaro ne Ibrahim, ba wai zan maka dole bane amma tunda naga matar ce kakasa nemowa shine Ni nayi maka gwanin ta nanemo maka, kaje wajen ta idan har kun dai-daita kanku shikenan".
Khalil yace "Dad don Allah meyasaka baza'a janye maganar ba? infact ma Ni yanzu bani da lokacin aure sabida zan tafi England yin wani course, kuma One year zanyi acan".
Dad yace "ok kana nufin Adena maganar auren ka har sai kaje kadawo?"
Gyaɗa kansa yayi yana kallon Dad ɗin tare da turo baki, daƙuwa Dad ɗin yayi masa yace
"Kaga naka Ibrahim babu inda zakaje sai kayi aure koda kuwa gobe ne zaka tafi".
Cikin shagwaɓa Khalil ɗin yace " Haba Dad please Mana kabari sai nadawo inyaso sai in auri ita yarinyan da kakeso".
Shiru Dad ɗin yayi yana kallon sa kana yace "ok shikenan, dama itama yarinyan tana karatu kuma dama Mahaifin ta yace min zuwa nan da shekara ɗaya da rabi zata kammala, kaga idan kadawo sai asaka ranan auren hakan yayi?"
Jinjina kansa yayi yace "eh Dad".
"Ok tashi kaje Allah yataimaka, yaushe ne zaka tafi?"
Khalil da yamiƙe tsaye yabashi amsa da cewa "nan da Three weeks".
Dad yace "kana da lokaci ai Yakamata kaje wajen yarinyan kaganta, kuma bana son inji cewa bakaje ba".
Gyaɗa masa kai yayi kafin yayi masa sallama yafice. Koda yafito babu kowa a palrour, kawai ficewa yayi batare da yashiga wajen Mom ba, motan sa yashiga yabar gidan, wayan sa yaɗauka yakira Brr. Tahir ringing biyu yaɗauka yace
"Ango ango".
Ɓata fuska Khalil yayi yace "wanene Angon?"
Dariya Brr. Tahir ɗin yayi yace "ai naji komi wajen Dr. Sameer, yace "min anje nema maka auren Billy".
Tsaki Khalil yaja cike da haushi da zaka gane cikin muryan sa yace "kabari dai kawai Tahir, yarinyan nan ashe yaudarana tayi".
Brr. Tahir yace "bangane ba kamar ya yaudaran ka tayi?"
Daga nan Khalil yasanar masa da abinda yafaru da su Dad da sukaje kana yaƙara da cewa
"Dama abinda nake gudu kenan Tahir tun farko shiyasaka bana son yin soyayya bcoz yawancin matan mayaudara ne, and duk da bana wani son ta but naji haushi sosai ɓata min lokacina da tayi, gashi yanzu taja min Dad ya samo min wata".
"To fa haka akayi? Gaskiya banji daɗi ba kuma Bilkisu bata kyauta ba, amma kayi mata uzuri mana don Ni banga laifin ta anan ba matsalan daga iyayen ta ne, meyasaka baza su bata wanda take so ba?"
Gajeren tsaki Khalil yayi yace "har kana da bakin kare ta anan? Ni Abokin wasan ta ne?"
Brr. Tahir yace "kayi haƙuri kabi abin a sannu, kuma don Allah karka ce zakayi mata wata magana da be dace ba".
Shiru Khalil ɗin yayi don shi yariga da ya rufe shafin ta
"Yanzu to aina yarinyan da Dad ɗin yasamo maka take?" Brr. Tahir ɗin yatambaye sa
Taɓe baki Khalil yayi yace "wai ƴar Abokin sa ne, sai kace suna neman kai dani".
Brr. Tahir dariya yayi yace "kai masha Allah Allah yasanya alkhairi, gaskiya naji daɗin wannan haɗin domin kuwa idan Dad yabiye taka baza kayi auren yanzu ba".
Yamutsa fuskar sa yayi yace "kaga ni zan aje waya ina tuƙi ne sai anjima".
Still dariya Brr. Tahir yayi yace "ok zuwa a anjiman zan kira ka bye".
Daga nan ajiye wayan yayi yaci gaba da tuƙin sa.
**** ***** ****** *******
Ummi ce zaune kan Three sitter Saleema tayi matashi akan cinyan ta, gefe ɗaya kuma Abba ne zaune kan Two sitter suna hira
Abba ne yace "ƴar Baba tashi akwai maganar da zamuyi dake me muhimmanci".
Amsa mishi Saleema tayi tana tashi zaune
"Shin kin tuna Abokina Alh. Abdurra'uf?".
Kallon Abban tayi kana tace "eh Abba nasan shi, ko ba wanda ada kake yawan kai ni gidan ba?"
Murmushi Abba yayi yace "yauwa shi ƴar Baba, kinsan yaran sa ko?"
Gyaɗa kai tayi tace "nasan su Abba".
"To ki saurare ni da kyau ƴar Baba, kinsan Burin mu shine mu aurar dake ga mutumin da zai kula dake kamar yanda muke kula dake, muna Son farin cikin ki Daughter wannan dalilin ne yasaka muka yanke shawara Ni da Mahaifiyar ki mu samo miki Miji wanda zai baki duk wani kulawa, ɗan gidan mutunci wanda zai iya riƙe mana ke bisa amana, akwai ɗan sa Ibrahim Khalil shine mahaifin sa yake nema masa auren ki, Ni kuma ganin haka yasa na'amince but duk da haka sai na tambayi ra'ayin ki, idan har kin amince zai zo wajen ki don ku dai-daita, kiyi tunani da kyau My Daughter don baza mu taɓa baki abinda baki so ba, zaɓin ki shine namu".
Saleema kallon Abban nata kawai take yi har yadire maganar kafin cikin zaƙuwa tace
"Abba wai kana Nufin Yaya Barrister?"
"Eh Shi ƴar Baba".
Rufe bakin ta tayi tana waro idanu cike da wani irin farin ciki tace "Kaiiiii.."
Ummi tace "lafiya Daughter me yafaru?"
Dariya tasaki tana yarfe hannayen ta sai kuma tasake rufe bakin ta tana kallon iyayen cike da tsananin farin ciki, su kuwa kallon ta kawai suke yi suna tunanin "meyasaka ta farin ciki haka lokaci ɗaya?" Muryan ta suka tsinkaya tana cewa
"Anya Abba Yaya Barrister shine Wanda mahaifin sa ke nema masa aure na? Ina mamaki Abba taya?"
Murmushi Abban yayi yace "Ƴar Baba kenan ki dena mamaki ai komi ba yanda Allah baya nuna ikon sa, yanzu menene ra'ayin ki akai? shin kin amince ne?"
Saurin gyaɗa kanta tayi tana me tsananin farin ciki, riƙo hannun ta Ummi tayi tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta tace
"Wai farin cikin na menene da alamun dai kina son sa kenan?"
Saleema har ta buɗe baki zatayi magana sai kuma tayi saurin rufewa don baza ta iya yin musu bayanin abinda ke ranta ba, illa tashi da tayi da gudu tanufi hanyan ɗakin su tana ci gaba da dariya, bin bayan ta sukayi da idanu cike da tsananin mamakin ta kana Abba yace
"Ikon Allah wai lafiyan ƴar Baba ƙalau?"
Ummi cike da farin ciki tace "ai inaga Abban Saleema da alamun ƴar mu ta daɗe tana ƙaunar sa ne, domin Ni sheda ne abaya sanda kake yawan ɗaukan ta kuje gidan kullum idan tadawo bata da magana sai na Yaya Barrister, Kai har dai na gaji daji don idan tazauna labarin kenan, to tun sanda tayi ciwon nan sosai aka kwantar da ita asibiti kadena kaita to ban sake jin tayi maganar ba, amma Ni ina da tabbaci son sa take yi kuma ina ganin tana cikin mamakin abun ne".
"Kai amma idan ko hakane zamuyi farin ciki sosai ai dama fatar mu kenan, burin mu shine tasami miji na gari kuma ina da yaƙini ta samu, domin Khalil be da wani matsala yaro ne me tsananin kirki da biyayya na tabbata bazai taɓa wulaƙanta mana ƴa ba, wannan dalilin ne yasaka nayi tunanin haɗa wannan auren".
Ummi jinjina kanta tayi cike da gamsuwar bayanin mijin ta kana tace "to Allah yatabbatar da alkhairi Allah yasa ayi damu".
"Ameen ameen". Cewar Abba still yana me nuna farin cikin sa
"Amma ina tunanin ba yanzu za'a yi auren ba sabida yaron zai yi tafiya, kin ga har sai ta gama school ma anan, sai kiyi mata bayani yanda zata fahimta".
"To babu matsala ai hakan yayi ma". Cewar Ummi kenan
Daga nan hira sukaci gaba dayi suna tattaunawa akan maganar.
0 comments:
Post a Comment