"Wayyo Allana yau ina farin ciki sosai kitashi ki tayani murna".
Ahankali Halwan tatashi zaune tana ci gaba da kallon ta tace "me yafaru ne Sister?"
Murmushin da yabayyana haƙoran ta tayi tace "kinsan me Abba yazo da maganar aure na Ni da ɗan Abokin sa".
Waro idanu Halwa tayi tana kallon ta, sai kuma tayi dariya tace "shine yasaka ki farin ciki?"
Gyaɗa kanta tayi tana sake washe bakin ta tace "eh mana abin ne ya matuƙar bani mamaki, ban taɓa tunanin wannan ranan ba, ban taɓa tunanin Ni Saleema ina da matsayin da zai sa ace yau zan zama matar Barrister ba, Mutumin da ko magana ban taɓa samu ya haɗani dashi ba, ada nayi burin ace Barrister ya zama nawa but ko kaɗan babu hanyan da naga yiwuwar hakan, amma yanzu kiji abin mamaki sai gashi lokaci ɗaya Allah ke ikon sa wai ni ce yau ake son haɗa ni dashi, abun sai kace amafarki wlh".
Yanda taƙarike maganar nata ne yaba Halwa dariya, sai da tadara kafin tace "to menene aciki? Ni a ganina banga Namijin da yafi ƙarfin ki ba, kar ki manta kema fa kina da kyau da haɗuwar da ko wani namiji zai yi fatar samun ki, ki dena zuzuta shi da yawa don nasan bazai fi ki da komi ba".
Saleema tace "uhmmm baza ki gane bane Sister, ko wace mace idan har tagan shi zata so yazama shine Mijin ta, ba wai don haɗuwan sa ko kyawun sa ba amma yana da nagartan da idan har kin ganshi kema wlh sai kin so shi, domin bakiga yanda mata suke rushing akan shi bane".
Taɓe baki Halwa tayi tana kallon ta tace "da alamu dai kina son sa da yawa, amma to kina ganin shima yana ciki?"
Zaro idanu Saleema tayi tace "hmm mutumin da ban taɓa magana dashi ba taya kike tunanin yana sona? I Think ko sanina be yi ba".
Shiru kawai Halwa tayi tare da tunanin Nura aran ta
"Burina a rayuwa shine in Sami Miji tamkar Barrister sai gashi shi ɗin na samu, nasan ko baya so na watarana zai ƙaunace ni domin kuwa zan yi duk abinda yake so". Saleema taƙarike maganar tana rufe fuskarta cike da farin ciki
Buɗe fuskar tayi tana kallon Halwa da tafaɗa tunani, sai tataɓo ta tana cewa "Sister lafiya tunanin me kike yi?"
Ajiyan zuciya Halwa tasauke kana tace "Babu".
Murmushi tayi tace "to faɗa min kema, menene burin ki a rayuwa?"
Shiru Halwa tayi tana kallon ta batare da tace komi ba
"Sister kisanar min mana kinji?"
Duƙar da kanta tayi tana murza ƴan yatsun hannayen ta masu tsawo da burgewa kana taɗago kanta tana kallon Saleema da murmushi a fuskarta tace "ada bani da wani buri a rayuwa sama da inyi aure in ganni gidan Yaya Nura amma.."
Shiru tayi tana kawar da kanta kana taci gaba da cewa "amma a yanzu Burina inyi karatu me zurfi in zama lauya ko dan naɗau fansar abinda Haris yayi min".
Ɗaura hannun ta Saleema tayi akan na Halwan tana cewa "meyasaka kike Son ɗaukan fansa? Meyasaka baza ki barshi da Allah ki manta dashi cikin rayuwan ki ba? Idan har kikace zaki ɗau fansa hakan na nufin kenan zaki riƙa tuna sa har zuwa wani lokaci?"
Halwa tace " Ni kaina nayi tunanin barin shi da Allah kamar yanda tun farko nabar shi, amma yanzu wani tunani yazo min arai saboda shigan ciki a gare ni, idan har nahaifi abinda ke cikina dole ne watarana yatambaye Ni "ina Mahaifin sa?" kina tunanin wani amsa zan bashi?"
Taƙarike maganar hawaye na cikowa cikin idanun ta, kana taci gaba da cewa
"Wannan dalilin ne yasaka nayi tunanin na zama lauya don nan gaba na kaisu ƙara kotu domin hakan ne kaɗai zai saka gidan su Haris su amshi abinda nahaifa, baza su taɓa amsan abinda zan haifa ta daɗin rai ba dole sai ta wannan hanyan".
Numfashi taja me ƙarfi still taci gaba da faɗin
"Burina na biyu shine in San meyasaka Yaya Nura yajuya min baya? Ina son in San dalili ina son insan meyasa?.."
Sai kuma tasaki kuka me ƙarfi, cikin rawan murya tace "na.. na kasa yarda cewa Ya..ya Nura zai juya min ba..ya, zuciyata takasa amince wa da hakan.."
Kasa ci gaba tayi da magana dole yasaka tayi shiru, rungume ta Saleema tayi cike da tsananin tausayin ta tace
"Kiyi shiru don Allah Sister ki dena kuka kinji? Ni nan zan taimake ki wajen cika burin ki, in Allah ya yarda zaki cika burin ki, zanyi wa Abbana magana zai saka ki aduk makarantar da kike so a faɗin duniya domin cikar burin ki, please ki dena kuka".
Shiru Halwa tayi tana sauke ajiyan zuciya, ɗago kanta Saleema tayi tasaka hannu tasoma share mata hawaye.
*****
*TWO WEEKS*
Khalil ne zaune ƙasar Roll ɗin parlour'n sa, daga shi sai gajeren wando fari da baƙin t.shirt, gaban sa takardu ne masu yawan gaske yake dubawa, gefe kuma Kausar ne kan kujeran da yajingina bayan sa tana ɓare maggi dake cikin Vowel
A ɗan wannan lokacin sosai suka shaƙu da juna kullum Kausar tana gidan, ita take mishi girki da gyaran gidan, su zauna suyi ta hira kamar wanda suka daɗe da sanin juna, yanzun ma hiran suke yi aciki yasako mata maganar auren sa da zai yi
Ɗan kallon ta yayi yana smile yace "kin kusa hutawa dai duk ranan da akace nayi aure, babu ke babu ɗawainiya dani".
Tsayar da abinda take yi tayi tana ɗago kanta takalle shi, kana cikin rashin fahimta tace "ban gane ba?"
Ɗan taɓe bakin sa yayi yana kawar da kai yace "nan ba da jimawa ba zanyi aure.."
Ɗif Kausar tayi gaba ɗaya tadena jin abinda yake cewa, maggin kawai take ɓarewa amma batasan ma takamaiman a halin da take ciki ba, sai da yagama maganar sa kana yajuyo yana kallon ta, ganin kamar tayi nisa a tunani sai yakau da kansa yaci gaba da abinda yake yi
Ita kuwa sosai tashiga ruɗu da jin abinda yafaɗa, ba don komi ba sai don ƙaunar da tatsinci kanta dumu-dumu aciki tana yi masa
Nocking ɗin da akeyi ne yadawo da ita hankalin ta
Khalil yace "Yes Come in".
Brr. Tahir ne yashigo ciki da sallama, sauke idanun sa yayi akan su yana bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo cike da tsananin mamaki da al'ajabi, Kausar itama shi take kallo sai dai kawai kallon nasa take yi but tunanin ta yana wani wajen daban, maganar Khalil ne kawai ke mata yawo a tsakar kai
"Lafiya katsaya nan? Kashigo mana". Cewar Khalil kenan yana kallon sa
Ahankali Brr. Tahir yasoma takowa yana shigowa, sai da ya'iso wajen yazauna saman sofa kana Kausar tamiƙe tsaye da hanzari tana ajiye Vowel ɗin hannun ta asaman Centre table, kallon Khalil tayi fuskarta babu walwala tace
"Zan je gida".
Shima ɗin kallon ta yake yi cike da mamaki, sai kuma bai iya cewa komi ba in banda gyaɗa mata kai da yayi, ita kuma tajuya tayi hanyan ƙofa dasauri yayinda Brr. Tahir yaraka ta da idanu, sai da tafice kana yamayar da kallon sa ga Khalil yace
"Kai Man ina kasamo wannan Babe ɗin? Shin anya ba idanuna bane ke min gizau?"
"Kamar ya?" Khalil ɗin yatambaye sa yana ɗago kansa yakalle sa
_plz Share🙏🏼_
[11/1/2020, 9:10 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 38*
Brr. Tahir yace "abin ne da mamaki mace nake gani agidan ka? Taya hakan zai faru? Meye alaƙan ka da ita?"
Gajeran tsaki Khalil yasaki yana kawar da kansa, domin shi a tunanin sa ko wani abun yagani don har ya tsorata shi
"Kayi min bayani mana meye alaƙan ka da ita? Kar dai ace.."
Wani kallo da Khalil yasakar masa ne yakasa ƙarisa abinda yayi ninya, sai yatsaya kawai yana kallon sa batare da ya ɗauke idanun sa akan sa ba, Khalil kuma juyar da kai yayi yaci gaba da abinda yake yi kana yace
"Ba abinda kake tunani bane, maƙociya ta ce".
"Maƙociyar ka?"
Brr. Tahir yamaimaita maganar kamar be fahimta ba, sai kuma yasaki murmushin gefen baki yana cewa
"Kayi min bayani yanda zan gane har yanzu ban fahimce ka ba?"
Tsaki Khalil yaja yana hararan sa, nan dai yabashi labari yanda suka haɗu da alaƙan sa da ita
dariya Brr. Tahir yakece dashi yana cewa "Cab ɗi.. wai dama ka iya sakewa da mata har haka?"
Kallon banza Khalil yayi masa yace "me kaɗauke ni to?"
Ɗage hannu Brr. Tahir yayi yace "No babu".
"Kafaɗa karta kashe ka, ai nasan duk abinda kake tunani".
Shi dai Brr. Tahir dariya kawai yake yi, sai da yagama dariyan sa son ransa Khalil be sake kula sa ba, sannan daga baya yace
"Kasan me? na samo maka shawara, me zai hana kawai kakai ma Dad ita a matsayin wacce kake so tunda naga taku tazo ɗaya".
Idanun Khalil kamar zai faɗo ƙasa sabida kallon da yake yi masa, Brr. Tahir da yabuɗe baki zai ci gaba da magana Khalil yayi saurin katse sa da cewa
"Banso don Allah kadena wannan maganar, ce maka akayi ina son ta? ko ce maka akayi ita tana so na? Babu wani abu da zai haɗa mace da namiji ne sai soyayya? Ni kawai burge Ni take yi ba wani abu ba".
"To ai hakan shi ke kawo ƙauna, don me zata burge ka idan har babu ƙauna aciki?"
Ɗaure fuska Khalil yayi yakawar da kai don bazai iya biye masa ba, kuma yasan halin Brr. Tahir idan yakama abu to baya jin bari
"Uhm Ni kawai shawara nake baka, idan kuma kafison wacce Dad zai baka ai shikenan , ta yiwu ma kaje kaganta batayi maka ba".
Shiru dai Khalil yayi be ce komi ba, amma tunanin maganar Brr. Tahir ɗin yake yi da yayi a ƙarshe
Brr. Tahir yakatse masa tunanin sa da cewa "katashi kashirya mana mutafi, in kuma ka fasa ne sai nayi tafiyana don ina da abin yi".
Miƙe wa Khalil yayi still be ce masa komi ba yanufi ɗakin sa, sai da yayi wanka yashirya cikin wani farin Gezna da yayi masa kyau ainun, yasaka baƙar hula me ƙube tare da baƙin Sandal shoes, babu abinda ke tashi ajikin sa sai sassanyan ƙamshi, car key yaɗauka tare da wayoyin sa yafito parlour, Brr. Tahir kallon sa kawai yake yi ganin yanda yayi masa mugun kyau
"Kai Abokina kaga yanda kayi kyau? Ni namiji kenan ina ga mace ta ganka? wannan wanka gaskiya Amarya dole tabiya mu".
Tsaki Khalil kawai yaja yanufi ƙofa batare da ya tanka sa ba, shi kuwa Brr. Tahir biyo sa yayi yana ta tsokanar sa yana faman dariya
A cikin motan Khalil ɗin suka fita, mintuna ashirin yakaisu gidan Alh. Mustapha, suna yin hon aka buɗe musu Gate don dama gateman ɗin yasan da zuwan su, lokacin da sukayi parcking duk kan su suka fito alokaci ɗaya, Brr. Tahir sai gyara wuyan rigan sa yake yi yana faman doka murmushi sai kace shine aka rako, Khalil kuwa in banda harara da yake aika masa babu abinda yake yi, ahaka akayi musu iso har zuwa Parlour'n Alh. Mustapha inda anan ne aka sauke su, me aiki aka saka takawo musu abin motsa baki, babu abinda suka taɓa sai hira da Brr. Tahir yake jan Khalil dashi, shi kuwa sai latsa wayan sa yake yi ko kula sa be yi ba
A ciki kuwa Saleema ce taci uban kwalliya cikin wani tsadadden less me ruwan toka, ɗinkin riga da sket ne da yayi mata kyau matuƙa, tayi ma fuskarta Light makeup Wanda yaƙara fito da tsantsan kyau ɗin ta, dama Saleema ba baya ba wajen kyawu, Halwa na zaune tana kallon ta har tagama shiryawa tayafa gyale fari ƙal me kwalliyan stone, haka ma flat shoes ɗin da tasaka a ƙafafun ta fari ne, murmushi kawai Halwa take zubawa kafin tace
"Gaskiya kinyi kyau My sister, anya baza ki zautar da Angon nan naki ba yakasa manta ki?"
Washe baki kawai Saleema take yi cike da farin ciki, kana tace "dagaske nayi kyau Sis?"
Halwa tace "wlh sosai kinyi kyau Sister, kuma ina da yaƙini dole ki shiga ran sa alokaci guda, don babu wanda zai ganki be yi fatan ki zamo matar sa ba".
Dariya Saleema tayi tace "Thank you My Sister, bari inje kar suji Ni shiru tunda nace kizo muje kinƙi".
Girgiza kanta Halwa tayi tana murmushi tace "O'o Ni bazan iya zuwa ba, ke dai kawai kije ke kaɗai, idan yasake dawowa watarana sai mu gaisa".
"To na tafi, sai na dawo Sis".
Daga nan fita tayi ita kuma Halwa kwanciya tayi tana sauke ajiyan zuciya cike da tunani a ranta, Saleema tana shiga Parlour'n da sallama Brr. Tahir da yatsare ƙofan da idanu ya'amsa mata yana sakin murmushi, a ransa kawai "masha Allah yake faɗa". Don ba ƙarya Abokin nasa ya dace da zaɓi, Saleema kanta a ƙasa ta'iso tazauna kan sofa me facing nasu, sai tagaishe su alokaci ɗaya tana ɗago kai tana kallon su, dai-dai da shima Khalil ya ɗago kai yasauke idanu kanta suka haɗa idanu, sauke kanta ƙasa tayi cike da tsananin kunya tare da zallan farin ciki, shi kuwa taɓe baki kawai yake yi amma yakasa ɗauke idanun sa akanta, Brr. Tahir kuwa cikin murmushi ya'amsa mata tare da tambayan ta "ya take da ƴan gidan?" Amsa mishi tayi, sai Brr. Tahir ɗin yakalli Khalil dake faman ƙare mata kallo, hakan yabashi dariya yayi saurin ƙumshe bakin sa yana cewa
"To Abokina ga fa Amarya ta iso, Ni bari in fice in baku space don kutattauna ko?"
Sai lokacin Khalil yaɗauke kansa yamayar ga Brr. Tahir, be ce masa komi ba hakan yasaka Brr. Tahir yatashi yafice
Shiru ne yabiyo bayan fitan Brr. Tahir, ita Saleema tunani kawai take yi yanda Khalil ɗin yasauya mata sosai fiye da yanda tasan shi, wani irin kyau da kwarjini yasake yi tare da wani irin gogewa yasake ƙiba, kai da gani kasan hutu da kwanciyan hankali tare da kuɗi sun zauna masa, so take yi tasake ɗago kai takalle sa amma ta kasa domin yanda take jin idanun sa masu matuƙar kaifi suna yawo ajikin ta, shi kuwa a nashi fannin zuba mata idanuwa yayi yana ta kallon ta, a haƙiƙanin gaskiya dogon tunani yafaɗa har be san iya adadin mintocin da suka wuce ba, Saleema dai har ta gaji taɗago kanta tana kallon kyakykyawar fuskar sa da yatsare ta da kallo, cikin sanyin murya tace
"Ko in Kira Abokin ka ku fara cin abincin ne?"
Sai alokacin yaɗan ƙifta idanun sa da alamun yadawo tunanin sa, kallon ta yayi yana ɗan jije leɓe, ba ƙarya ayanda yafahimta yarinyan zatayi sauƙin kai, duk da ba wai tayi masa yanda yake so bane kuma ba wai yaji ta a ransa bane, but ta kwanta masa arai kuma zai iya zama da ita a matsayin matar sa, ajiyan zuciya yasauke kafin yace
"Kina lafiya?"
Saleema da har tagaji da shirun nasa tasad da kai ƙasa tana wasa da yatsun ta, jin sassanyan muryan sa me daɗi yasaka ta ɗago kai tana kallon sa kana ta'amsa mishi cikin biyayya da son burge shi
"Nasan kinsan me yakawo ni nan ɗin don nasan an riga da an miki bayani? Any way ni sunana Brr. Ibrahim Khalil Abdurra'uf, ina fata.."
Shiru yayi don be san me zai faɗa ba, ita kuwa kallon sa kawai take yi tana jin yanda muryan sa me tsananin daɗi yake shiga kunnuwan ta, kamar an matse bakin sa sai yace mata
"Me kike karanta a School?"
Cike da farin ciki ta'amsa masa da "Pharmacy".
Gyaɗa kansa yayi sai kuma sai kuma yayi shiru yana ajiyan zuciya, wayan sa yaɗauka kana yaɗago kai yana kallon ta yace "kiyi haƙuri ni ba gwanin iya soyayya bane Thats why ban iya hiran ba".
Murmusawa tayi kawai tana sunkuyar da kai, sosai yaburge ta hakan na nufin kenan be taɓa budurwa ba kamar yanda itama bata taɓa yi ba? Duk kallon da take masa bata taɓa tunanin yana da sauƙin kai irin haka ba
Brr. Tahir yakira yace masa "yashigo". Babu jimawa kuwa yashigo yana kallon su yana murmushi yace
"Har an gama hiran?"
Khalil be basa amsa ba sai miƙewa da yayi yana saka wayan sa a aljihu hakan yasa Brr. Tahir cewa
"To Amarya mu zamu tafi, sai kuma gani na gaba".
"To bakuci komi ba".
"No karki damu next time idan muka zo zamuci yanzu muna sauri ne".
Gyaɗa kanta tayi tana tashi tsaye, daga nan raka su tayi har wajen motan su kafin suka sake sallama tataho gida.
.
_More Comments More post._🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
[11/1/2020, 9:23 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 39*
*AFTER SEVEN MONTH*
A wannan watannin da suka shuɗe abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da haihuwar da Halwa tayi, ta haifi yarinyan ta kyakykyawa me ban sha'awa, sosai yarinyan take kama da ita, sai dai kuma ta ɗakko abubuwa da dama na mahaifin ta wanda idan kakalle ta tabbas zakasan ƴar sa ce, sunan Ummi aka saka mata kamar yanda Saleema tabuƙaci asaka, wato Asma'u suna kiran ta da Husna, duk wani hidima kama daga kan kayan Baby zuwa na uwar Babyn babu abinda Abba be siya musu ba, komi ya wadata su dashi tamkar tana gaban iyayen ta, tun sanda tahaihu kuma Ummi tace "baza ta shayar da yarinyan ba". Don haka da madaran kanti ake shayar da ita, Halwa sosai taji daɗin hakan ko ba komi an ɗauke mata wani nauyi kuma an taimake ta, duk wani hidiman yarinyan Saleema ce me yi, kullum yarinyan tana hannun ta ita take kula da ita, ita take mata komi sai dai wanka da Larai ƴar aikin su take mata, ita kuwa Halwa sai dai taci tasha takwanta hakan yasaka gaba ɗaya tasauya tasake ƙiba tayi kyau gunun sha'awa, dama gashi tana tsaka da jego ne kuma ga hutu da yayi mata yawa
Yanzun ma zaune take agaban madubi tana shafa lipstick a ƙananun laɓɓan ta, fuskarta babu wani kwalliya illa powder da tashafa sannan tazizara kwalli cikin idanuwanta, miƙe wa tayi tana gyara zaman rigan ta, doguwar riga ce na atamfa tasaka Milk and Coffee colour, sosai rigan yayi mata matuƙar kyau duk da kasancewar ta bata da hasken skin, Halwa irin Chocolate Colour ɗin nan ce me ɗan haske, tana da kyau na ban sha'awa da burgewa, idan har zaka ganta to dole sai ka sake kallon ta coz yanayin ta da komi nata yana da kyan kallo, bata da wani tsayi amma tana da ɗan kauri kaɗan tare da sura me kyau da ɗaukan hankalin me kallon ta, duk da kuwa ita ɗin ba ma'abociyar son cin abinci bane, kallo ɗaya idan kayi mata zaka fassara ta da me sanyi don ko a maganarta ne cikin sanyi sosai zakaji muryan ta, sai dai kuma akwai ta da tsiwa sannan tana da surutu matuƙa sai dai idan bata sami wajen yi ba
Tana cikin ɗaura ɗankwali Saleema tashigo ɗakin, itama ɗin doguwar riga tasaka iri ɗaya da na Halwa har ɗinkin da komi, Ummi taba da aka ɗinka musu wajen kala bakwai lokacin da Halwan tahaihu, itama ɗin sosai yayi mata kyau kasancewar ta fara ce, murmushi tasakar wa Halwa kana tace
"Kinyi kyau Sister".
Murmushi Halwa tayi tana kallon ta tace "Thanks".
"Ok Ina kayan Husna? Larai ta gama mata wankan za'a shirya ta".
"Ban ciro mata ba". Halwa tabata amsa tana saka Room Slippers a ƙafafuwan ta da suka sha lalli ja da baƙi
Saleema wajen kayan Husna tanufa tana cewa "but sai da nace miki ki ciro kafin in dawo fa"
Ƙarisawa kusa da ita Halwa tayi tana taya ta cirowa tace "I'm sorry Sis, ban gama shiryawa bane shiyasa".
"Ok".
Fita sukayi gaba ɗayan su bayan sun gama ɗaukan abinda zasu ɗauka, suna fita parlour Halwa zama tayi akan sofa ita kuma Saleema tawuce da kayan ɗakin Larai, can kuma sai gata tafito ɗauke da Husnan a hannu, an shirya ta tsaf-tsaf cikin kayan ta masu kyau, zuwa tayi tazauna gefen Halwa tana cewa
"Kinga Babyna yau tayi kyau sosai, har carbing mukayi mata".
Halwa kallon yarinyan tayi sai kuma taɗauke kai tana yamutsa fuska kamar yanda tasaba
Kallonta Saleema tayi tace "Yauwa Sis idan nayi aure kema zaki dawo gidana ko? Sai mu zauna tare".
Murmushi Halwa tayi tace "to sai mu bar Ummi da wane? Kinga ke kin tafi dole zasuyi kewarki".
Gyaɗa kai Saleema tayi kana kuma tace "but duk da haka dai zaki riƙa zuwa kina min sati ko fiye da hakan, kinga kuma Ni ban ma iya girki ba idan naje wanene zai min?".
Halwa tace "zaki sami House girl ne sai tayi miki".
Kwaɓe fuska Saleema tayi tace "no bana son ƴar aiki sai dai muje muriƙa yi tare dake".
"To ai nima ban iyaba wlh". Halwa tafaɗa tana dariya
Dariya itama Saleema tayi tace "haba dai? Kice duk jirgi ɗaya taɗauko mu?"
"Eh mana, ko Mama tasaka Ni bana yi har ma ta saba ta dena cewa inyi, sabida Ni dai gani nake yi tunda bana cin abincin to bazan koya ba".
Still dariya Saleema tayi tace "tabb ai kuwa dole mu saka Larai gaba takoya mana".
Ummi ce tayi sallama tashigo
"Oyoyo Ummi". Cewar Saleema tana miƙe wa ta'isa wajen ta
Ummi kuma amsan Husna tayi tana dariya tace "iyeee ga takwarata ga takwara ta".
Sannu da zuwa sukayi mata sannan tazauna tana cewa "Abban ku be dawo ba?"
Saleema tace "ya dawo ya fita ne".
"Ok".
Yarinyan tamiƙa wa Saleema sannan taɗau jakan ta, ita kuma Halwa lokacin tadawo ɗauko ma Ummi ruwa tace
"Ummi ga ruwa kisha".
Murmushi Ummi tayi tace "Yauwa na gode".
Har ta juya Ummi tasake cewa "zo riƙe wannan ledan".
Halwa amsan ledan tayi tana kallo
"Magani ne idan Larai zatayi miki wanka sai ki riƙa Using dashi".
Gyaɗa kai Halwa tayi tana komawa tazauna, ita kuma Ummi miƙe wa tayi tanufi ɗakin ta, sai da tashige sannan Saleema tace
"Menene acikin ledan?"
Kallon ta tayi taɗage kafaɗa alamun bata sani ba, sai kuma tace "ki tambayi Ummi".
Ɗan waro idanu Saleema tayi sai kuma tasaki dariya tace "ai bazan iya bane wlh".
Harara Halwa tayi mata tace "ashe kin sani kenan kike tambaya?"
.
**** ***** ***** ******
Wani irin kallo take masa har sanda yadasa aya a maganar sa sannan tabuɗi baƙi cike da baƙin ciki tace
"Wlh Nura kabani mamaki domin ban taɓa tunanin haka halinka yake ba, har Ni zaka dubi idanuwana kace kana so na? Idan har baka bar mana ƙofar gida ba wlh zan maka rashin mutuncin da baka taɓa tunani ba..'
Bata rufe baki ba Nura yace "haba Zainab wai meye laifina anan? me namiki da baza ki so ni ba? Kar ki manta fa wacce kike tunani akanta bata nan don me baza ki bani dama in maye gurbin ta dake ba, wlh ina ƙaunar ki tsakani da Allah.."
Cikin wani irin tsawa Zainab takatse shi
"Dalla kayi mana shiru, duk wani mutunci da nake gani naka wlh ka ɓarar dashi, bari kaji wlh koda maza sun ƙare a duniya Nura bazan taɓa son ka ba bazan taɓa auren ka ba, har yanzu kallon ka nake yi a matsayin saurayin ƙawata kuma Ni bana cikin maciya amana, and nasan da cewa Halwa baza ta taɓa barin ka ba coz nasan irin ƙaunar da take maka, duk inda take a faɗin duniya tana nan tare da kai aranta, idan ma har wani abu kuka ƙulla domin tabar gidan nan to wlh kun ci amanarta".
Wani irin kallo tabuga masa kafin taci gaba da cewa "kasani duk inda Halwa tatafi zata dawo wannan alƙawari ne, anan ne zan tabbatar maka da cewa ita ɗin me ƙaunar ka tsakani da Allah ne ba irin ka ba".
Daga haka tajuya tashige gida batare da tabari yasake furta komi ba, shiru Nura yayi yana kallon hanyan da tabi, ya jima anan tsaye kafin yabuɗe kyakykyawar motar sa yashiga yabar wajen, gidan da yasiya wa iyayen sa yanufa, yana zuwa yadanna hon aka buɗe masa Gate yakutsa motan ciki, bayan yayi parcking yafito yashiga cikin gidan, Mama na zaune a parlour tana faman kallon da tasaba, don tunda suka dawo gidan da zama yazame mata jiki kallon, zama yayi akan kujeran da yake Facing ɗin nata, ita kuma kallon sa take yi ganin yanda duk yasauya face ɗin sa kamar wani abu na damun sa, hakan yasaka tatambaye shi da cewa
"Lafiya Nura meke damunka ka fita cikin walwala kadawo fuska a turɓune?"
Sai alokacin yakalle ta yace "Mama Zainab ce".
Numfashi Mama taja don tariga tasan da zancen, sai da taɗan ɗau lokaci tana ci gaba da kallon sa kafin tace "wai ni Nura meyasaka baza ka nemi wata bace sai ita? Taya zaka zauna yarinya tana wulaƙanta ka amma kaƙi kasauya ta? Ni fa dama hankalina be kwanta da ita ba tunda ita ɗin ƙawar Halwa ce ƙut da ƙut, kuma dama abokin ɓarawo ai ɓarawo ne ban ɗauke tsammanin itama halin su ɗaya ba".
Cike da rashin jin daɗin kalaman Maman nashi yace "Mama don Allah ki dena aibanta ta, Ni nasan Halin Zainab baza ta taɓa aikata abinda Halwa tayi ba duk da kuwa suna ƙawaye, kuma Ni ita kaɗai nake jin zan iya aura sabida ina matuƙar ƙaunar ta tun ba yanzu ba, kawai ki taya ni da addu'a shine nafi buƙata a wajen ki".
Yana ƙarisa maganar nasa yamiƙe yayi hanyan fita, ita kuma Mama tabi shi da kallo har yafice, sai kuma takaɗa kai cike da tausayin ɗan nata a ranta tana masa fatan alkhairi
...... ...... ...... ...... . ..
Tun tafiyan Halwa babu daɗewa Nura yazo ma iyayen sa da zancen zai tafi Legos wani kasuwanci acewar sa bazai dogara da aikin gwamnati ba, dama can yana siye da sayarwa ne na kayan gona, yanda yayi musu bayani akan kuɗin da zai iya samowa hakan yasaka basu wani ja maganar ba suka barsa yatafi, to be rufa watanni uku ba yadawo da zunzurutun kuɗi acewar sa sana'ar da yayi ne Allah ya albarkace sa, iyayen sa sunyi murna matuƙa da samuwan ɗan nasu, acikin lokaci ƙanƙani Nura yayi kuɗi ya buɗe shaguna da yawa ya saka masu kula dasu, kuma ya siyan ma iyayen sa gida me kyan gaske suka koma, sannan shima ɗin yasoma ginin sa inda zai yi aure
Tun dawowar sa yasoma neman Zainab a matsayin wacce zai aura, amma har yanzu ita Zainab taƙi amincewa dashi, shi kuma yaƙi haƙura da ita sabida mugun son da yake mata.
.
_To ya za'a kaya?_
_Plz Kar ku manta kuyi_
*Shere*
*Vote*
*Comments.*
[11/1/2020, 9:20 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
_*NANA FARUK* wannan shafin naki ne ke kaɗai, Allah yabar ƙauna🥰_
.
*CHAPTER 40*
Turo ƙofan Mom tayi tashigo cikin ɗakin, Nazeefa dake zaune tsakiyan gado ta tanƙwashe ƙafafun ta tana faman tunani taɗago kai tana kallon Mom ɗin, ita kuma ƙarisowa tayi tazauna gefen gadon tana kallon ta tace
"Meke damunki Nazeefa?"
Nazeefa kallon Mom tayi tace "babu komi Momy".
"Ban yarda ba ki faɗa min gaskiya idan da akwai abinda ke damun ki, gaba ɗaya na lura dake tun da daɗewa kina cikin damuwa, kullum cikin tunani kike kuma kinƙi kifaɗa min abinda ke damun ki, bana son in ganki cikin damuwa hakan na damuna coz Ina jinki tamkar ƴata ta cikina ne".
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana jin hawaye na son zubo mata, idan da tana da daman faɗa mata abunda ke damun ta da tuni tadaɗe da sanar mata, sai dai kashhh baza ta taɓa iya faɗa mata gaskiyan abinda ke cin zuciyarta ba
Dafa bayanta Mom ɗin tayi tace "ki sanar dani kinji Nazeefa zan miki duk abinda kike buƙata idan har ina da halin yi, bazan taɓa barin hawayen ki yazuba ba zan kasance me share miki hawayen ki".
Wani irin sanyi Nazeefa taji acikin ranta tare da wani irin ƙaunar Mom na sake shiga zuciyarta, sai dai baza ta taɓa iya faɗa mata ciwon son ɗanta ne yakamata ba, "to taya?" Hawayen da taji suna son zubo mata ne tayi saurin mayarwa tana ɗago kai takalli Mom cikin sanyin murya tace
"Momy babu abinda ke damuna, idan har akwai kece ta farko da zan faɗa miki sabida na ɗauke ki tamkar ke kika zuƙuna kika haife ni, ki yarda dani Momy babu abinda ke damuna".
Shiru Mom tayi tana kallon ta, sai dai ko kaɗan bata yarda babu abinda ke damun ta ba bcoz ko wanene yaga halin da take ciki dole yatabbatar wa kansa tana cikin tsananin damuwa, sosai take mamakin abinda ke damunta har takasa bayyana mata, amma kuma tayi wa kanta alƙawari sai ta gano ko me ke damun ta kuma sai ta share mata hawaye da iznin Allah, ajiyan zuciya tasauke kafin tace
"To shikenan na yarda dake, amma duk abinda ke damun ki kiyi gaggawar sanar dani ki dena ɓoyewa kinji?"
Gyaɗa kanta Nazeefa tayi sai kuma tace "insha Allahu Momy".
"Ok tashi ki cire kayan makarantan akwai inda zaki raka Ni".
Amsa mata tayi tana tashi tare da saukowa daga kan gadon, itama Mom tashi tayi tafice a ɗakin, sauya kayan ta tayi tasanya doguwar rigan abaya Blue Black, sannan sai tayi Rolling da ɗankwalin abayan, komai bata shafa a fuskarta ba illa flat shoes da tasanya a ƙafafuwan ta, sosai tayi kyau white skin ɗin ta sai sheƙi yake yi kasancewar ta samu hutu har wani ƙiba tayi tare da ƙara girma, fita tayi ta'iske Mom a parlour suka fice, motar Mom ɗin suka hau drever yatuƙa su suka bar gidan.
A wani ɗan madaidaicin gida Drever yasauke su suka fito suka shiga, matar gidan tana zaune a parlour tatarbe su cikin fara'a tare da kawo musu Drinks, sai da suka ɗan yi hira kafin Mom tace
"Yauwa Hajja Turai maganar da muka fara dake a waya ne akan kayayyakin da zaki ɗauko min a London, don haka shiyasa nataho muyi maganar sosai sai ki faɗa min da yaushe zaki tafi?"
Cikin fara'a Hajja Turai tace "ai ina da kaya a ƙasa gaskiya ba yanzu zan koma ba, inaga sai nan da One Month, yanzu abinda yakamata dai sai kiyi min list ɗin komi kibani hakan zai fi, bari in ɗauko miki Littafi".
Miƙe wa tayi tashige ɗaki babu jimawa tadawo riƙe da Littafin tamiƙa mata, Mom amsa tayi tana cewa
"Yauwa sannan kuma zan baki saƙon ƴata ga tanan, itama ɗin kizaɓo mata kayan fitan biki masu matuƙar kyau, acikin gwala-gwalan da zaki siyo min sai ki ɗaukar mata ɗaya, Ni dai ina son ki gwangwaje ta sosai komi yakasance Expensive ne nata".
Dariya Hajja Turai tayi tana kallon Nazeefa tace "ai babu matsala Hajiya Hajara duk abinda kikeso hakan za'a yi, amma ko itace Amaryan don naga kina ji da ita?"
Mom tace "a'a ƙanwar sa ce ai".
"Allah Sarki". Cewar Hajja Turai still tana kallon Nazeefa
Mom tace "don Allah Hajja kaya masu kyau nake so sabida kinsan bikin Autana ne that's why nazo wajen ki, and sai kuma Furnitures ɗina don Ina son nasauya komi na ɗakina".
"Baki da matsala insha Allahu duk abinda kikeso zan yi ƙoƙarin naga na samo miki dai-dai da zaɓinki".
Ita kuwa Nazeefa da tun sanda tazauna tasad da kai ƙasa tana sauraron su, wani irin ƙunci take ji a maƙogaron ta, ji take yi tamkar tabuɗe baki tayi ta zunduma ihu sabida tsaban baƙin ciki, har hawaye sai da tai ta sharewa batare da sun kula da ita ba suna ta tattaunawa, bayan Mom ta gama yin mata list ɗin gaba ɗaya sannan sukayi sallama suka fito, har wajen mota Hajja Turai tarako su sai da taga fitarsu kafin takoma cikin gida
Suna cikin motan Khalil yakira Mom, bayan tayi peacking call ɗin suka gaisa take cewa
"Ɗazu ka kira bana ji ne matsalan network ne, yanzu kuma muna kan hanya ne naje gidan Hajiya Turai".
Khalil da be san ma wacece Hajiya Turan ba sai tambayan ta da yayi "me taje yi?"
Nan take faɗa masa sannan taƙara da cewa "wai kuwa kana kiran surukar tawa don nasan Halin ka?"
Shiru yayi don be san amsan da zai bata ba, shi idan har basu suke masa maganar bikin ba sam mantawa yake yi zai yi aure, kuma ita yarinyan tun sanda yabar ƙasar yamanta irin ta, ko za'a tsare sa da bindiga yafaɗa yanda take bazai iya ba, abinda yasani kawai fara ce ita but kamannin ta ya daɗe da gushe masa, sunan ta ma kanshi be riƙe ba duk da su Mom wani lokacin suna faɗar sunan idan suna waya
"Kayi shiru ko dai dagaske ba ka kiran ta?'
"Ina kiran ta mana Mom". Yafaɗa cike da sanyin murya don shi sai yanzu yasan be kyauta ba tunda ko Phone numbern ta be amsa ba
Daga nan sallama suka yi Mom ta'ajiye wayan cikin jaka, kallon Nazeefa da tatakure a jikin motan tayi idanuwanta a rufe ruf, numfashi kawai Mom taja tana ɗauke kai.
.
*** *** *** *** *** ***
Da hannu biyu tazuba tagumi tana tunani har batasan sanda Mami tashigo tatsaya a kanta ba, sai da tagama ƙare mata kallo kafin takira sunan ta
Firgigit Kausar tayi tana ɗago kai takalli Mamin nata
"Wai ke lafiyan ki lau kike yawan tunani meke damun ki ne?"
Shafo fuskarta da hannun ta tayi cikin sanyin murya tace "babu komi".
"Baza ki faɗa min ba kenan?".
"Mami babu komi fa tunanin aiki ne kawai".
Gyaɗa kai kawai Mami tayi kafin tace "to ki tashi kije Sharif na parlour yana jiran ki".
Kausar kallon Mamin tayi fuska babu walwala tace "Mami kice masa bana nan Ni bazan iya fita ba".
"Wai ke kanki ɗaya kuwa? Wai meyasaka yanzu bakison fita ne idan yazo? Ko faɗa kukayi ne?"
Kausar tace "a'a kema Mami kinsan Da da yanzu ba ɗaya bane, bana son takura ne kawai".
Baki Mami tabuɗe tana kallon Kausar, ita kanta da take Mahaifiyar ta tasan Kausar ta sauya, gaba ɗaya ta dena walwala agidan, sai tashige ɗaki ita kaɗai tazauna su rasa me take yi cikin ɗakin, kuma duk uzurin da zata kawo be da wani kan gado, ajiyan zuciya tasauke kafin tace
"Ki fito ki same sa yana parlour yana jiran ki".
Daga haka tajuya tafice batare da tajira ta bakinta ba
Ita kuwa Kausar ba'a son ranta ba tamiƙe tafito, yana zaune a parlour'n shi kaɗai, gaban sa duk an cika masa da kayan motsa baki amma be taɓa komi ba, shi kansa idan kakalle sa baya cikin hayyacin sa duk ya rame yasaka damuwa a ransa sakamakon sauyawan da Kausar tayi masa, kuma hakan sosai ke barazanan tarwatsa rayuwan sa sabida ba ƙaramin so yake mata ba, kullum ji yake yi ƙaunar ta na sake hauhawa acikin ransa memakon raguwa, ya rigada ya saka ta acan cikin zuciyarsa wanda rabuwa da ita zai mishi matuƙar wahala kuma zai taɓa masa rayuwan sa
Tunda tafito yake kallon ta har taƙariso tazauna akan kujeran dake Facing nasa, cikin sanyin murya batare da ta kalle sa ba tace
"Barka da zuwa".
Murmushi yasaki yace "yauwa gimbiyata kina lafiya?"
"Lafiya lau".
"Kwana biyu ina ta kiran wayan ki akashe na kasa haƙura dole nayi tunanin zuwa yau, shin meke faruwa ne Baby?".
Sai alokacin taɗan kalle sa kana taɗauke kai tace "kashe wa nayi".
Shiru kawai yayi yana kallon ta, sai kuma daga baya yace "wai Kausar ko dai kin samu wani ne kikeson min wulaƙanci?"
Sosai taɗago kanta a wannan karon tana kallon sa, shima ɗin ita yake kallo cike da tuhuma, sun jima suna kallon juna batare da ta sami amsar da zata bashi ba kafin taɗauke kai tare da haɗiyan yamu
"Kinyi shiru ina son insan abun da yasaka kikeson juya min baya Kausar, don Allah ki sanar dani idan wani laifi nayi miki wlh nayi alƙawari zan nemi yafiyar ki".
Sai kuma yayi shiru yana saukowa kan kujeran yayi Neeldown agaban ta yana ci gaba da cewa
"Idan ma kina so in duƙa a gaban ki ne to gani na duƙa don Allah ki yafe min, wlh Kausar ina matuƙar ƙaunar ki bazan iya rabuwa dake ba, dan Allah ki taimaki rayuwata ki faɗa min laifin da nayi miki in nemi gafarar ki". Yaƙarike maganar nasa da rawan murya
Kausar kallon sa kawai take yi don batasan sanda yazuƙuna ba, take taji hawaye sun cika mata idanu sabida tausayin sa, tasan da cewa tana ƙaunar Sharif matuƙa amma yanzu shigowar Khalil rayuwan ta tarasa soyayyan sa a zuciyarta, tayi iya ƙoƙarin ta don taga tayi yaƙi da abinda ke damun ta amma ina ta kasa, ta kasa dawo da ƙaunar da take masa aranta, burin ta yanzu kawai tazama mallakin Khalil, amma tarasa ta wani hanya ne hakan zai faru, tasan da cewa yanzu Khalil yayi mata nisa nisan da baza ta iya samun sa ba tunda yana shirin aure
Wani irin kuka yataho mata batasan sanda tasake sa ba, jikin Sharif har yana rawa wajen matsowa kusa da ita yana tambayan abinda ke faruwa da ita, gaba ɗaya ya shiga damuwa ya rasa yanda zai yi, ita kuwa kukan take yi tana toshe bakinta da hannayen ta, sosai take tausayin kanta don batasan halin da zata shiga ba nan gaba
"Dan girman Allah kiyi shiru Kausar, kiyi shiru ki faɗa min abinda ke damun ki, wlh idan har Ni ne baki ƙauna yanzu zan barki, zanyi nesa da rauyuwan ki idan har hakan zai saka ki farin ciki, bana son kukan ki".
Still kallon sa take yi da idanuwanta da sukayi jazur tana ci gaba da kukan ta, daƙyar ta'iya buɗe baki tace
"Bakayi min komi ba Sharif kuma babu abinda ke damuna, idan har ka shirya aurena to katuro".
Tana faɗan haka tatashi da gudu tayi ɗakin ta, tana zuwa tafaɗa kan gado tana sakin wani kukan da ƙarfi
Ta san da cewa hakan shine kaɗai mafita agare ta, ta hakan ne kaɗai zata sami salama tamanta shi cikin rayuwanta, hakan zai sa tayi nesa dashi gaba ɗaya.
_ ****_
A cikin kwana biyu Sharif har ya turo magabatar sa, kuma komi ya kammala har an saka rana nan da wata biyar masu zuwa, SAI MUCE ALLAH YAKAIMU LAFIYA MUSHA BIKI😅
.
_Plz karku manta da comments da Vote_
[11/7/2020, 2:21 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 41*
*FIVE MONTHS AGO*
Yau ake saka ran dawowar Brr. Ibarahim Khalil, don haka Mom tashirya tarban Autan nata, Sameer da matar sa tare da ƙanwar ta Abida duk sun zo gidan su ma tarban sa, su suka taya Mom girki tare da gyare-gyaren gida, anyi soye-soye anyi duk abinda yadace sannan ne lokacin driver yatafi ɗauko sa a airport don ƙarfe 02:00pm. Jirgin su zai sauka, drever na tafiya shima Brr. Tahir yazo da nashi iyalin matar sa Suhaila da ɗan su ɗaya Adam.
Bakin Nazeefa har kunne sabida tsaban farin ciki zataga Yayan nata kuma mafi soyuwa a ranta, da ita ake aikin komi don ko kaɗan babu wanda yakula da yanda tasaki jiki take ta fara'a kamar bakin ta zai tsake becouse su ma ɗin cikin su kowa tashi murnan ya ishe sa.
Lokacin da jirgin yai landing *BRR. IBRAHIM KHALIL* yana ɗaya daga cikin waɗanda suke sauko wa ta matattaƙalan jirgin, Ni dai gaskiya bangane sa ba sai dai bansani ba Fans ɗinsa ko ku zaku gane sa, don dagaske ya sauya sosai fiye da yanda nasan shi, gold skin ɗin sa yayi wani irin haske sosai sai ɗaukan ido yake yi, hutu da kwanciyar hankali kawai nake hangowa a tattare dashi da alamun dai ƙasar tayi mugun amsar sa don ba ƙarya ya sauya ɗin, sai zuba murmushi yake yi abinda ba kasafai kake gani a face ɗin sa ba
Har sanda ya'amso trolly ɗin sa yafito haraban airport ɗin sannan ne drever yahange shi yataho dasauri yazo wajen sa yana miƙo masa gaisuwa, amsa masa yayi cike da fara'a sannan suka shiga mota sukayo gida, bazan iya fasalta muku yanda Familyn suka nuna farin cikin su ba, bayan an gaigaisa ya huta sosai sannan aka wuce dainning, anan kowa yaci abinda yakeso tukun suka dawo parlour, hira aka dasa ana ta dariya, wlh idan kukaga Khalil baza kuce shine ba domin har dashi ake ta wasa da dariya, kai sai ince har da ɗabi'u aka sauyo masa acan ɗin, Nazeefa da Abida kuwa babu abinda suke yi sai kallon sa ko wacce zuciyarta na mafarkin yakasance nata na har abada, don har alokacin Abida taƙi tacire sa aran ta duk da kuwa Hakima sai da tagargaɗe ta tamanta dashi baza ta taɓa samun sa ba coz yanzu aure zai yi, kuma itama taso ƴar uwan nata ta aure shi har mitan maganar tarinƙa ma Sameer but basu samu nasara ba.
Su Brr. Tahir suka soma tafiya sannan Khalil shima yayi musu sallama drever yanufi gida dashi, lokacin da suka isa layin su motoci yai ta gani duk sun cika layin, sai da suka matso gab gidan sa sannan ne yafahimci agidan su Kausar ake taron, ga jama'a nan burjik awaje maza da mata kowa na sha'anin gaban sa da alamu dai biki ake yi, mamaki sosai ne a fuskarsa sai dai be iya furta komi ba har Drever yayi hon agidan sa aka buɗe musu Gate motan tashige, bayan drever yayi parcking Khalil yafito lokacin duk ma'aikatan gidan sa sunyo wajen suna miƙa masa gaisuwa, haka yai ta amsa musu cikin sakin fuska sannan ne yanufi cikin gida Sale na biye dashi da trolly ɗin sa
Cikin gidan an gyara masa ko ina kuma yasan duk aikin Sale ne hakan ya faranta masa rai sosai, anan parlour yaba ma Sale umarnin ya'ajiye Jakan sannan yafice, shi kuma yaja trolly ɗin yanufi ɗakin sa, yana shiga yasaki hannun trolly ɗin yazauna gefen gadon sa, ya ɗan yi wajen mintuna 5 kafin yatashi yacire kayan sa yashiga wanka, yayi kusan mintuna talatin kafin yafito yashirya cikin farar t.shit da gajeren wando fari da ɗige-ɗigen ja, zuwa yayi yazauna kan kujera yasoma latsa wayan sa, kusan mintuna goma yaɗauka sannan yasoma laluban numban Kausar yadanna mata kira
Lokacin Kausar na zaune a ɗakin ta tare da ƙawayen ta an gama mata kwalliya, kasancewar yamma tayi har motocin ɗaukan amarya sun zo, becouse acan garin Daura zasu zauna tunda anan ne Sharif ɗin yake aikin sa, duk da dama nan ne tushen sa amma iyayen sa anan Katsina suke zaune
Tsananin firgita Kausar tayi da ganin wanda yake kiran ta har batasan sanda takusa sulmiyar da wayan ƙasa ba, sai wata ƙawarta dake kusa da ita ne tayi saurin taro wayan tana cewa
"Kee Kausar Ina hankalin ki yaje zaki saki waya ƙasa?"
Kausar da tayi mutuwar zaune sabida mamaki, ƙyafta idanun ta tayi da suka cicciko da hawaye tana bin wayan da kallo, ƙawarta me suna Rumaisa tamiƙo mata wayan da aka sake kira akaro na biyu tace
"Riƙe gashi an sake kira".
Ahankali tasaka hannu ta'amsa wayan sai dai takasa anwer call ɗin, ko kaɗan bata taɓa tunanin ganin kiran sa a wannan lokacin ba duk da tasan cewa lokacin dawowan sa yayi, tun sanda yatafi basu taɓa waya dashi ba wannan dalilin ne yasaka tashiga ruɗu da bugawar zuciya
Shi kuma a fannin Khalil tunda yatafi ya nemi layin ta sama da biyar duk sanda zai kira ta wayanta sweech off, daga ƙarshe shine yadena kiran ta gaba ɗaya don a tunanin sa ko akwai matsala ne, ita kuma kullum da tunanin kiran nasa take kwana dashi kuma take tashi, koda yaushe tana jiran taga kiran sa amma har tsawon wannan lokacin babu shi babu labarin sa kuma gashi ita bata da numaban sa na can
Batasan tana zub da hawaye ba sai da Rumaisa tadafa ta tana cewa
"Wai lafiyan ki ƙalau kuwa? Kuka fa kike yi Kausar?"
Sai alokacin tadawo hankalin ta tana kallon Rumaisa da tabi ta da kallo cike da tsananin mamakin ta, lokacin gaba ɗaya hankalin ƴan matan har ya dawo kan su, dasauri Kausar tatashi batare da ta furta komi ba tashige Toilet tana rufo ƙofa, hakan yasaka duk suka bi ƙofan da kallo suna tunanin abinda ke faruwa da ita
Tana shiga kiran yasake katsewa, sai ga wani kiran don shi Khalil ya kasa haƙura da kiran nata, sai da tajingina da bango kafin ta'amsa kiran tana sakawa a kunne, cikin ƙasa da murya tace
"Hello".
Daga can ɓangaren Khalil kuwa shima jingina bayansa yayi da kujera cikin cool voice ɗin sa me daɗi yace
"Hello Friend".
Kausar danne duk abinda ke cikin ranta tayi cikin ƙarfin hali tace "dama ashe zaka iya mantawa dani?"
Ɗan shafo sajen sa yayi yace "Kausar kiyi haƙuri nasan ban kyauta miki ba, amma kuma nayi ta neman Phone Numban ki bana samun ki".
Hannun ta taɗago tana kallon fingers ɗin ta da suka sha jan lalli, cikin son maida kukan da yataho mata tare da ɗaura jarumta a muryan ta tace
"Na gane Barrister, ya hanya to?"
"Alhmadulillah.. da fatan kema kina lafiya?"
Murmushi taƙirƙiro dai-dai lokacin da hawaye suka sauka kan kuncin ta tace "sai alheri friend".
Khalil shima cikin murmushin yace da ita "Allah ko?"
"Ƙwarai". Tataɗa tana dariya ahankali
"To bani nasha".
Sai da taja numfashi kafin tace "Allah yayi an ɗaura aurena yau".
Cikin tsananin mamaki da al'ajabi Khalil yace "haba dai serious fa?"
Kausar tace "I'm serious.."
Sai kuma taɗan saki murmushi me sauti tace "kaga na rigaka ko?"
"Sosai don ban yi tunanin hakan ba, sau da dama kina bani labari kuma ban taɓa jin kinyi min maganar samarin ki ba, ashe ashe.."
Sai kuma yai dariya yana cewa "to Allah yatabbatar da alheri gaskiya naji daɗin wannan maganan".
Shiru kawai Kausar tayi bata amsa ba, hakan ya tabbatar mata da cewa tabbas bata cikin zuciyarsa, ita kaɗai take kiɗan ta kuma take rawan ta
Murmusawa shi kuma yayi yace "Amarya kenan bari in barki haka ko? don nasan yanzu kina busy".
Share hawayen ta tayi cikin rawan murya tace "to".
Daga haka bata iya furta komi ba don idan tasake faɗan kalma ɗaya zata iya fashewa da kuka
Nocking ƙofan da akayi yasaka tayi saurin juyowa tana kallon ƙofan, sai kuma tamaida idanunta kan wayan lokacin ne Khalil yadatse kiran, lumshe idanuwan ta tayi tana jin wani ƙunci da baƙin ciki na mamaye ilahirin zuciyarta
"Kausar wai me kike yi aciki? ki buɗe mana".
Maganar Rumaisa yadawo da ita cikin hayyacin ta, dasauri tasanya hannu tashare sauran hawayen ta tanufi ƙofan tabuɗe, duk bin ta suka yi da kallo har da ƙanwar Mamanta da tashigo yanzu, ita kuma sai tasad da kai ƙasa don bata son su fahimci wani abun
Ƙanwar Maman nata ne tace "wai me kuke jira ne, ku fito motoci sun rigada sun iso".
Juyawa tayi tafita tana cewa "su hanzarta".
Kausar sai da tasha nasiha wajen ƴan uwa kafin aka fito da ita, a lokacin sai kuka take yi, Ni dai bansan ko na menene ba ni dai naga an saka ta a mota sun fice, to sai muce Allah yasanya alkhairi *KAUSAR.*
....... ....... . .. ....
Khalil kuwa tunda suka gama wayan ya'ajiye yalumshe idanun sa yana tunani, yaji babu daɗi yanda suka rabu sabida shaƙuwan da sukayi, be taɓa tunanin baza su sake haɗuwa ba idan yadawo, ya so ba yau bane auren ta ko shima yahalacci auren nata, amma gashi har anyi an gama batare da yaje mata ba, hakan yaƙara saka shi rashin jindaɗi
Allah Sarki haka shaƙuwa yake dama, a ranan kuwa haka yawuni shiru duk bashi da walwala, har yayi sallan magriba da isha'i yadawo gida komi be ci ba yakwanta, ya daɗe yana tunani kafin barci ɓarawo yaɗauke shi.
.
**** **** ***** *****
A cikin kwana biyu da dawowar Khalil sai gashi ya samu kira agidan gwamnati, koda yaje meeting akayi dashi, sun tattauna na wajen awanni kafin su gama, daga ƙarshe dai an ɗauke shi aiki a matsayin Lauyan gidan
Gwamnati, ga albashi me tsoka da zai riƙa samu, duk da dama can sosai Khalil yake samun kuɗi don zan iya cewa ko mahaifin sa be fi sa kuɗi ba, sai dai shi Lauya ne me zaman kansa haƙƙin talakawa kaɗai yake ƙwatowa, Duk wani mara galihu idan har yaje gare sa shi kuma zai share masa kuka, asannu-asannu sunan sa yayi shura sosai talakawa sun soma sanin sa, gaba ɗaya gidajen talabijin da rediyo, jaridu duk maganar sa yanzu ake yi, acikin lokaci ƙalilan Allah ya ɗaukaka shi fiye da Da, kuma duk saboda ƙarin girman da yasamu ne yanzu da kuma ɗaukan sa aiki da akayi agidan gwamnati, sanin da talakawa sukai mishi yanzu har sun soma kawo masa Cases kala-kala, shi kuma don yashare musu kuka haka yake faɗi-tashi wajen taimaka musu da ƙarfinsa da kuɗin sa.
_dama akace dare ɗaya Allah kan ɗaukaki bawa fiye da tunanin me tunani, yanzu sunan Brr. Khalil ya zagaye duk faɗin garin Katsina da kewaye sabida ƙwazon sa, sosai ake ji dashi.
October 2020.
[11/7/2020, 2:40 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 42*
An tsai da ranan auren Brr. Kahlil da Saleema nan da Four Month, zuwa lokacin tarigada ta rubuta Final Exams ɗin ta, asannu-asannu rayuwa taci gaba da tafiya cikin nasarori da akasin sa, wasu tazo musu da daɗi wasu kuma tazo musu a yanayin da babu daɗi, ga dai shi Saleema a wannan lokacin sosai ciwon ta yatashi kullum cikin nema mata magani ake yi, wani lokacin adace wani lokacin kuma rashin sa, ga kai ya ɗau zafi karatun su ya zo ƙarshe haka take lallaɓawa take zuwa School sai dai ba kullum ba, duk ta rame sosai take jin jiki.
A fannin Khalil kuwa yanzu yana da Numban ta kuma yana kiran ta akai-akai yatambayi jikin ta tunda yasan bata da lafiya, kusan sau biyu yana zuwa gidan, shima yanzu aiyuka sun yi masa yawa baya zama sosai kullum cikin aiki yake, ahaka Allah yasa biki yaƙarato ko wani fanni tuni sun soma shiri ana hidima kala da iri, amma ta fannin Amarya babu lafiya har yanzu sai dai ba kamar da ba don yanzu jikin da sauƙi
Ummi tare tahaɗa su da Halwa ake musu gyaran jiki, itama yanzu Halwa ta soma shirye-shiryen zana WAEC da zatayi.
Yau ta kasance saura sati ɗaya biki kuma a yau ne Halwa zata soma zana jarabawan ta, haka tatsallake tatafi bada son ranta ba don ko kaɗan bataji daɗin yanda za'ayi bikin Saleema ita kuma tana Exams ba, sai idan taje tadawo ne ake Hidiman biki da ita.
Fannin su Mom yanda suka ɗau bikin nan da girma zai baka mamaki, komi cikin wadata da nuna su ɗin masu kuɗi ne don tun ana saura sati biyu ake shagulgula agidan, idan kashiga cikin gidan ko matsuguni baza ka samu ba tun kafin ma bikin yazo kenan, ƴan uwa da abokan arziƙi duk sun cika gidan.
Nazeefa kuwa damuwan da tasaka aranta har bacci bata iya yi ishashshe hakan yahaifar mata da ciwon kai me tsanani tare da zazzaɓi, duk shagulgulan da ake yi tana ɗaki taƙule taƙi fita ayi da ita, sosai take jin jiki har sai da Sameer yakaita asibiti aka dubata, koda suka dawo Mom tayi ta kula da ita tana bata drugs duk ta tashi hankalin ta, gaba ɗaya ko lokacin kanta bata dashi ga jinyan Nazeefa ga hidiman mutane, wannan yasaka taba Nazeefa tausayi sosai hakan yasa tadaure taɓoye duk abinda ke damunta tayi kamar ta samu sauƙi tana fitowa ana biki da ita, hakan yasa Mom taji daɗi har hankalin ta yakwanta.
Fannin Ango kuwa baya zama yanzu sabida Case ɗin da yake gudanarwa a Court, shiyasa duk wani shagulgula bashi ciki, sai idan ya sami kansa ko zuwa dare ne yake zuwa gidan su.
..... ...... ...... ...... ....
Gidan su Amarya su ma ba laifi ana ta shagulgula duk da babu wani armashi Amarya tana kwance babu lafiya, wannan dalilin ne ma yasa basu shirya komi ba in banda taron bikin kawai da za'a gudanar
Duk abunda ake ma Amarya anyi wa Saleema, an mata lalli an mata gyaran jiki komi an mata, sosai tayi kyau tafito a Amaryan ta duk da kuwa zallan raman da tayi
Sai ana gobe biki ita Halwa akayi mata nata Lallin sabida ranan bata da Exams, kuma a ranan akayi musu gyaran kai ita da Saleema, komi har gida ake zuwa ayi musu basu zuwa ko ina.
*** **** **** **** ****
Washe gari ya kasance Saturday aka shaida ɗaurin auren *BARRISTER IBRAHIM KHALIL ABDURRA'UF* tare da Amaryan sa *SALEEMA MUSTAPHA*
Ana gama ɗaurin auren ango da abokanan sa suka tafi Hotel inda zasuyi ƙwarya-ƙwaryan liyafan da suka shirya.
*GIDAN SU AMARYA*
Amarya tasha kyau cikin shigan ta na Material Less me ruwan Hoda da ratsin ash colour, ɗinkin riga da sket da suka ɗauki jikinta sosai, ba'ayi mata kwalliya ba don taƙi yarda shiyasa ba'a matsa mata ba
tana zaune akan gado ta ɗaura Husna ajikin ta da take ta faman wasa da kayan Saleeman, sosai yarinyan tasake girma ga wayau sosai, idan kaganta baza kace watanni tara da haihuwar ta ba
Cikin ɗakin akwai friends ɗin ta na school su wajen biyar, sai hira suke yi suna shewa, wasu kuma suna mata tsiya "gwara tawarke don dole akaita yau ɗin"
Ita kuwa ɓata fuska tayi sai sake marairaice face ɗin ta take yi, kallo ɗaya idan kayi mata zakasan ta faɗa ainun hakan yasa tasake haske sosai, bata kula su ba sai dai bin su da ido da take yi
Ana haka Halwa taturo ƙofa tashigo, dawowarta kenan daga Exams da taje tarubuta, fuskarta yalwace da murmushi take kallon Saleema da itama tasanya mata idanu tana ƙara ƙwaɓe fuska kamar zatayi kuka, takowa tayi tashigo ciki tana gaisawa da ƙawayen Saleeman sannan tanemi wuri tazauna gefen Saleema tana sake yalwata fuskarta da murmushi, sosai take farin ciki a yau ɗin tana taya ƴar uwan nata murna
Hannu tasaka tadafa kafaɗun Saleema bakin ta yaƙi rufuwa, sai kuma tamaida hannun kan kumatun ta taja tana cewa
"Haba ƴar uwa ya haka kin ɓata fuska? Don Allah ki saki ranki kiyi farin ciki yau ranan ki ne, ko so kike Angon yayi tunanin bakya son sa ne? Kinga hakan zai jawo masa matsala akasa gane kansa".
Hakan yasa Saleema tasaki dariya babu shiri saboda maganar Halwa ɗin, ita kuwa Halwa kallon ta take yi tana murmusawa cike da jindaɗi, sai kuma tamaida kallon ta kan Husna tana haɗe rai tace
"Waye kuma yakawo wannan yarinyan nan?"
Itama Saleema kallon Husnan tayi da tatsare su da idanu ta saka hannu ɗaya cikin baki tana ɓashe bakin kamar tana jin su
"Kawo ta in kaita wajen Larai, yau fa ranan ki ne be kamata kizauna kina raino ba, banda abinki ma ke da baki da lafiya?"
Ture hannun ta Saleema tayi tana hararan ta tace "to Ni nace akawo ta ina ruwan ki?"
"Haba Sister don Allah yau rana ɗaya kibarta wajen Larai". Cewar Halwa tana sake kai hannu zata ɗauke ta
Sake ture hannun Halwan tayi tarungume ta da kyau tana cewa "Ni fa nace akawo min ita, wlh babu inda zata don tana nan wajena har mu tafi".
Waro idanu Halwa tayi tana cewa "wai da ita kike nufin zaki tafi?"
"Eh mana.. da dake zan tafi?"
Sai ƴan ɗakin dake kallon su suka kwashe dariya
Zaliha tace "kai wani lokacin Saleema bata da hankali al'ƙur'an tana jinta kamar sokuwa ne".
Sai suka sake ɓarke wa da dariya, ita kuma tabi su da harara tana cewa
"Ni ce bani da hankali ko?"
"Ai da gaskiyar Zaliha idan ba sokuwa bace ke taya ma zaki tafi da yarinyan nan? Ai mijin ma sai yakoro ki". Cewar Dija Babbar ƙawarta tana sake kecewa da dariya
Halwa murmushi tayi tace "Sister wlh kuwa maganar su gaskiya ne, kema kinsan Ummi baza ta barki ki tafi da ita ba gwara ki sauya shawara".
Shiru kawai Saleema tayi bata sake cewa komi ba
Cikin lallami Halwa tasake cewa "kinga koda nan da sati ɗaya ne sai in kawo miki ita idan ma wai tafiyar da ita zakiyi".
Saleema tace "sati ɗaya ai yayi yawa, sai dai idan zakiyi min alƙawari gobe".
Gyaɗa mata kai kawai Halwa tayi don ba wai ta yarda zata kai mata ɗin ba, daga nan hira sukaci gaba dayi, sai da Saleema tace ma Halwa taje tashirya sannan tamiƙe tashiga wanka.
*****
Da ƙarfe 08:00pm. Akazo ɗaukan Amarya, tasha kuka sosai haka taƙanƙame Ummi taƙi tafiya, daƙyar aka samu aka shiga da ita mota Halwa tazauna kusa da ita tana rarrashin ta
A gidan sa aka kaita, sosai gidan yaɗau hankalin duk wanda yashigo, kamar ba gidan da akayi amfani dashi ba komi an sauya sai ƙamshin sabunta yake yi
Ɗakin ta kusa dana Khalil aka shigar da ita, haka mutane sukai ta zagayawa suna ganin abun arziƙi har da Halwa a zuwa gani, anan sukayi sallan isha'i suna ta hayaniya kamar zasu tsaga gidan
Wajen ƙarfe 10:00pm. Abokan ango suka zo tafiya dasu, lokacin ne itama Halwa takira Drever'n gidan su A wayan da Abba yasiya mata don yazo yaɗauke ta, ko kaɗan bata son bin abokan Angon sabida yanda wani yamaƙale mata ɗazu da suka zo daga ta buge sa bata sani ba, ita ta ma rasa uban wa yace musu ita ɗin Sister ɗin Amarya ce, yanzu da suka shigo parlour'n sai faman kiran ta suke yi, komi akayi sai suce "ina Sister ɗin Amarya tazo tayi musu sheda" daga ƙarshe ma tashi tayi tashiga ciki tazauna kusa da Saleema dake zaune saman gado
Har Drever yazo basu tafi ba, sannan ne ma suka soma haraman tafiya, anan ne fa Saleema tariƙe Halwa tana kuka wai baza ta tafi ba, in banda dariya babu abinda su Dija suke mata sai faman tsokanarta suke yi, daƙyar dai tasaki Halwa suka tafi suka barta ita kaɗai kamar Mayya.
.
_Nace ko ina Mijin Oho?_🤔😅
[11/7/2020, 3:02 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 43*
Ƙarfe 10:30pm. Su Khalil da Brr. Tahir tare da Sameer suka shigo gidan, daƙyar ma Khalil yayarda suka biyo shi don da yace "baya son rakiyan". Shi da kan sa yashiga har ɗakin ta yace "tafito parlour" daga haka yajuya yafita, ita kuma tamiƙe jiki a sanyaye tagyara mayafinta tafito, ahankali taƙarisa tazauna aƙasa tana gaishe su, cike da fara'a suka amsa sannan ne Sameer yasoma musu wa'azi cikin raha, daga ƙarshe suka yi musu fatan alkhairi tare da sanya alkhairi a auren nasu
Har bakin Gate Khalil yaraka su da zasu tafi, yadawo yatarda Saleema tana nan zaune inda take, be ce komi ba yanufi ɗakin sa, yana shiga yasoma cire babban rigan dake jikin sa bayan ya cire Hulan kansa, agogon hannun sa yacire tare da cire links ɗin rigan sa yazube su yanufi parlour
Har yanzu tana nan zaune inda take, zama yayi kan kujera yana kallon ta, sai kuma yaɗauke kai yana kallon ledan da suka shigo dashi, miƙewa yayi yanufi kichen sai gashi ya dawo da plate a hannu tare da wuƙa, zama yayi a ƙasa kamar yanda itama take zaune a ƙasan, yajawo ledan yabuɗe yaciro Kazan ciki yasoma yanka wa cikin plate ɗin don yayi daɗin ci, bayan ya gama duk yajera mata a gabanta da su Holandia sannan yakalle ta yace
"buɗe fuskar ki kici".
Ahankali tayaye gyalen daga kanta taɗago tana kallon sa sai kuma takalli abinda ke gabanta, cike da tsananin kunya tanoƙe ko motsi ta kasa yi, ganin haka yaja baya yana ɗaukan wayan sa yasoma latsawa yana cewa
"Ki ɗauka kici nace".
Wannan karon batayi musu ba ganin ya matsa can baya kuma hankalin sa baya kanta, hakan yasa tasoma ɗauka tana ci duk da dama tana jin yunwa amma baza ta iya buɗe ciki taci ba, kaɗan taci tacire hannun ta cikin sanyin murya tace
"Na gama".
Ɗago kai yayi yakalli plate ɗin sannan yasake maida kansa kan waya yace "ki ƙara".
Hannu tasaka taci gaba taci, bata daɗe ba tasake tsame hannun ta, wannan karon da yaɗago kai miƙewa yayi yaɗau komi yanufi kichen dashi, yana dawowa yace tataso su je ɗaki, miƙewa tayi tabi bayan sa, suna shiga yanuna mata Toilet tashiga tawanke hannu da bakinta tafito, yasake nuna mata kan gadon.. ta ko haye can lungu taƙudundune da gyalen ta
Shi kuwa Toilet yashiga yayi wanka yafito yashirya cikin kaya sannan yahayo kan gadon yakwanta, shiru sukayi ko wanne yana jin numfashin juna, can kamar amafarki tatsinkayi muryan sa
"Ya jikin naki?"
Cike da jindaɗi ta'amsa masa ganin yanda yadamu da ita sosai, daga haka basu sake yin magana ba har sanda Khalil yaji numfashin ta na fita da ƙarfi hakan yagane tayi barci, juyowa yayi setting ta duk da baya kallon fuskarta hakan be hana yaƙure ta da idanuwansa ba, shiru yayi yana tunani yana bin ta da kallo, abinda be taɓa faruwa dashi ba yau sai gashi zai kwana da mace
Ya daɗe ahaka yana ta saƙe-saƙe kafin yasauke ajiyan zuciya yamiƙe yakashe fitila yadawo yakwanta, addu'a yayi yarufe idanun sa, lokaci ƙanƙani barci yaɗauke sa kasancewar baya samun hutu.
Washe gari shi yasoma tashi bayan da suka koma barcin asuba, wanka yayi yashirya yasaka Milk colour ɗin Gezna da yayi masa kyau matuƙa gaya, duk da bashi da aiki ya ɗauki hutu amma Shari'an da yake yi be rigada ya ƙarƙare ba, akwai sauran aiyukan da yake yi a Court, yana cikin saka Wrest watch yaji Nocking ƙofa, fita yayi yaje yaduba yaga drever'n gidan su ne Mom ta aiko sa da breakfast, amsa yayi kawai yaje ya'ajiye a dainning table yakoma ciki, sai da yayi rubutu a ɗan Pepper ya'ajiye mata saitin kanta sannan yaɗau abubuwan da zai ɗauka yafita.
Babu jimawa da fitan sa tafarka, ahankali tabuɗe idanuwan ta yayinda ƙamshin turaren sa suka cika ƙofofin hancin ta, sake lumshe idanun tayi tana murmushi cike da jin daɗi, sai da tajima ahaka bataji motsin sa ba sannan ne tayaye gyalen fuskarta, da takardan da ya'ajiye mata tasoma cin karo, take gaban ta yafaɗi babu shiri tayi saurin kai hannu taɗauka tana jujjuya shi, sai kuma tamiƙe zaune idanun ta har yanzu akan takardan, buɗewa tayi sai taci karo da
.
_"Aslm alaikum Ni na fita zuwa wani waje bazan jima ba zan dawo, and akwai breakfast a dainning Mom ta kawo..."_
_Mijin ki✍️_
Batasan sanda murmushi yasuɓuce mata ba, kalman Mijinki shi ke ta mata yawo a ƙwaƙwalwa, gaskiya Brr. Daban ne da sauran Mazaje, duk da kuwa ta tabbatar ba son ta yake yi ba amma kuma kulawan sa agare ta da tausayin ta ya wuce tunanin me tunani, yana da halin ƙwarai sosai, memakon yanuna mata tsangwama a'a sai yana sauke haƙƙinta akansa, wannan shi ake kira adalin namiji, tayi imani koda baya son ta zata zauna dashi ahaka domin tasan shine ɗorewar farin cikin ta na har abada
"Allah yabarmu tare".
Tafaɗa a maƙoshi tana sake faɗaɗa fara'an ta
Miƙewa tayi tasauko kan gadon tanufi ɗakin ta, Toilet tashige tawanke bakin ta tafito parlour tanufi dainning, tana jin yunwa sosai don haka baza ta iya jira har sai tagama abinda take yi ba gudun lafiyan ta, zama tayi tahaɗa tea me kauri tasha tare da ƙwai da Arish, bayan ta gama tatashi tashige ɗaki taɗauko Maganin ta cikin kayan ta taɗiba tafito tasami ruwa tasha dashi, sai kuma takoma ɗakin Khalil ɗin tasoma gyarawa musamman kan gadon da sukayi amfani dashi, duk da ita ba ma'abociya aiki bane komi yin musu ake yi, ba'a barin ta tayi komi amma aɗan kwanakin da zatayi aure sai da duk takoya abinda zai bata wahala, don bata son me aiki cikin gidan ta tana da kishi sosai
Bayan ta gama takoma ɗakin ta tayi wanka tashirya cikin farar shadda wanda tare akayi musu da Khalil ɗin, shi kuma yarigada ya saka nashi jiya, ta fito ɗas Amaryan ta sai zabga ƙamshi take yi, kallo ɗaya idan kayi mata zakaga ƙyallin amarci atattare da ita (aure ba wasa ba🤫)
Parlour takoma tazauna a lumsassun kujerun ta masu tsantsan kyau da burgewa, wayanta dake hannun ta talatsa takira Ummi, ringing biyu taɗauka
"Ummina I miss You so much". Tafaɗa cike da zumuɗi
Daga can Ummi murmushi tayi na jindaɗi tace "me too My dear, har kin tashi?"
"Eh Ummi kuna lafiya? Ya Daddy da Halwa?"
Cikin dariya Ummi ta'amsa mata tana cewa "ai ga Halwan ma anan".
"To Ummi bata mu gaisa".
Miƙa mata wayan tayi suka gaisa cike da kewan juna sannan tamaida ma Ummi nan ma sukaci gaba da hira, daga baya kuma tabuƙaci akawo mata Husna, Ummi tayi ta rarrashinta akan tabari zuwa nan da sati biyu amma sam Saleema taƙi yarda ita lallai sai an kawo mata Husna yau
"Haba ɗiyata ki kwantar da hankalin ki, ki bari zuwa gobe insha Allahu zan sa akawo miki ita, kinga yau su Gwaggon ki zasu zo zasu kai ki gidan iyayen mijin naki to wa zaki bar ma wa? Ki bari gobe sai akawo miki ita kinji".
"To Ummi amma kar yawuce gobe". Tafaɗa a shagwaɓe".
Daga nan sallama sukayi, tana nan zaune tana tunanin mijin nata sai murmushi take yi, sai da tagaji don kanta ga barci da tasoma ji hakan yasaka takwanta a 3sitter tana rufe idanun ta, babu jimawa barci yaɗauke ta
Can tasoma jin hayaniyan baƙinta tare da bugun ƙofa, babu shiri tatashi tana riƙe kanta dake faman sara mata, daƙyar take tafiya sabida yanda take jin wani zazzaɓi-zazzaɓi na son kawo mata cafka, tana buɗe ƙofan suka shigo nan tatare su da fara'a, duk ƴan uwan Abbanta ne dana Ummin ta su wajen biyar
Su suka sakata tashirya cikin wata Farar atamfa anyi mata Flower da kalan ja da baƙi, sosai atamfan tayi mata mugun kyau kasancewar ta fara, ga ɗinkin da yaɗauki jikin ta sosai na riga da zani, Hijab tasaka fari da takalmi ,sannan suka fito sukayo waje, a motoci biyu suka bar gidan.
*****
Tarba me kyau Mom tayi musu cike da farin ciki sai nan nan take da Saleema, hakan sosai yafaranta ran Ƴan uwanta har basuyi fargaban danƙa mata amanar ƴar su ba, ita kuma Mom ta'amshe ta hannu bibbiyu
Basu jima ba sukace zasu tafi duk da Mom tayi musu tayin abinci amma sukaƙi ci illa ruwa da suka sha, haka suka tafi suka bar Saleema anan, sauran dangin Mom da basu rigada sun tafi ba sai shigowa ɗakin Mom suke yi suna ganin amarya, bayan sun tafi yarage daga Mom sai Saleeman, duk da Saleema tasaba da Mom abaya hakan be sa taƙi nuna kunyan ta ba, Mom kuwa sai janta da hira take yi cike da ƙaunar ta, daga ƙarshe dai da taga taƙi sakin jiki da ita sai tatashi tana cewa
"Tunda kinƙi sakin jiki dani bari in Kira miki Nazeefa tataya ki hira tunda Ni fita zanyi".
Saleema dai batace komi ba har Mom ɗin tafice.
Nazeefa tana kwance akan gadon ta duk abin duniya yabi ya ishe ta, tun sanda aka soma hayaniyan zuwan Amarya tana jin su amma takasa fita, sosai take jin baƙin ciki da kishi aranta sai dai tadage tana ta ƙoƙarin hana kanta kuka, shigowar Mom cikin ɗakin yasa tatashi tana ma Mom ɗin sannu
"Yauwa Nazeefa bakije kinga Amarya ba ga ta can an kawo ta?".
Murmushi Nazeefa tayi tasauke kai ƙasa tace "Mom banji bane barci ya soma ɗauka na".
"To tashi kije wajen ta tana nan aɗaki sai ki tayata zama ko".
Batayi musu ba tatashi sai dai bada son ranta ba tafito tanufi ɗakin Mom ɗin, ita kuma Mom tanufi wajen Dangin ta
Sallama tayi tatura ƙofan tashiga, Saleema dake zaune saman gado ta'amsa mata tana ɗan jan Hijabin ta baya da tarufe idanun ta dashi, kallon kallo sukai ma juna ko wacce da tunanin dake ranta
Ita Nazeefa tana kallon Amaryan Yayan nata ne cike da jin haushi duk da kuwa ta burge ta don kyakkyawa ce sosai wacce kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa ba ƙaramar ƴar jindaɗi da hutu bane, coz ko kaɗan ma batayi yanayi da ƴar talakawa ba
Ita kuma Saleema tana mata kallon rashin sani ne don tasan dai ba ƴar gidan bace, sai dai ko ƴar uwan shi ne duk da babu wani kama da sukayi
Zama tayi akan kujeran dake ɗakin tana ci gaba da kallon Saleeman sannan taƙaƙalo murmushi tace "sannu Amaryan mu, kinzo lafiya?"
Murmushi itama Saleema tayi ta'amsa mata cike da sakin fuska kasancewar ta me yawan fara'a ga kowa
Daga haka shiru ne yabiyo baya dan Nazeefa batasan me zatace mata ba saboda ita ba me yawan surutu bane, itama kuma Saleeman bata sake furta komi ba tayi shiru tana sad da kanta ƙasa, ahaka har Mom tashigo da wasu baƙi tatarar dasu haka, baƙin sun zo ganin Amarya ne, haka Saleema tagaishe su cike da kunya su kuma suna ta yaba mata suna sanya alkhairi, hakan ba ƙaramin sake ƙular da Nazeefa yayi ba har takasa jurewa tatashi tasulale ɗaki batare da sanin Mom ba
koda Mom suka tashi fita bata kula ba haka suka fita ɗakin aka bar Saleema ita kaɗai tana ta zaune, daga ƙarshe kwanciya tayi sabida yanda take jin zazzaɓin jikin ta yana ƙara yawa, lokaci ƙanƙani ciwo yarufe ta ga sanyi da take ji sosai, haka ta ƙudundune jikinta sai faman maƙyarƙyata take yi
Ahaka Mom tashigo taganta, hankalin ta idan yayi dubu ya tashi nan tasoma neman wayan ta, sai tatuna tabar wayan a palrour, fita tayi dasauri babu jimawa sai gata ta dawo tare da wasu mata su biyu, su ma duk hankalin su ya tashi ganin yanda jikin Saleeman yai zafi zauuu
Mom Kiran Khalil tayi tabashi umarnin yai maza-maza yazo matar sa tana gidan ta babu lafiya.
[11/7/2020, 3:33 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 44*
Lokacin da Khalil yazo har su Mom sun fito da ita parlour, babu ɓata lokaci yariƙe ta suka fito waje inda motan sa yake, Mom tace mishi "yakai ta asibiti" amma ita Saleeman tace "tana da maganin ta a agida" don haka gida kawai yanufa
Suna zuwa yayi parcking yafito yabuɗe mata motan yariƙo ta tafito, duk da a halin ciwo take amma sosai taji daɗin kusancin sa gare ta, har wani sanyi take ji aranta tana jin kamar ciwon na son tafiya
Tana jingine da jikin sa har suka isa parlour yataimaka mata tazauna sannan yakalle ta cike da tausayi yace
"Ina kika ajiye maganin in ɗauko miki?"
Cikin muryan marasa lafiya tace "yana cikin trolly na Wanda nazo dashi daga gida".
Gyaɗa kai kawai yayi yanufi ɗakin nata, yana shiga yasoma wurwurga idanu, can yahangi akwatunan da yayi mata guda shida, sai yamaida idanun sa kan wani babba kalan sa daban, yana da tabbacin shine wanda take nufi
Wajen yanufa yabuɗe, duk abubuwan amfanin ta ne da tazo dashi daga gida, yana soma bincika wa yaga ledan maganin, ɗauka yayi yanufi parlour'n
Zama yayi gefen ta yabuɗe tare da nuna mata alamun tayi masa bayani, nuna masa waɗanda zata sha ɗin tayi yaciro yamiƙa mata sannan yatashi yaje yaɗauko ruwa a Fridge yabata
Har tagama sha yana ta kallon ta kamar wanda zai haɗiye ta, hakan yasa taji kunya tana sad da kanta ƙasa, be san sanda yasaki guntun murmushi ba yamiƙe tsaye yanufi kichen ita kuma tabi bayan sa da kallo cike da tsananin ƙaunarsa a ranta
Be wani jima ba yadawo riƙe da Cup a hannun sa, miƙa mata yayi yana tsaye a kanta, ita kuma tasaka hannu ta'amsa tana kallon abinda ke ciki, Tea ne yahaɗo mata, be ce mata komi ba sai dai kallon ta da yake yi har tashanye tatashi da ninyan kai Cup ɗin
"No kawo cup ɗin, je ki kwanta idan an kira sallah zan tashe ki".
Babu musu tanufi ɗakin ta tashige, shi kuma bayan ya kai Cup ɗin kichen yadawo yanufi ɗakin sa, ɗakin karatun sa yashige (Library) yasoma binciken abinda yakawo sa, har aka kira sallan azahar yatashi yagabatar yakoma yaci gaba da aikin sa, yana tune da Saleema sai dai yaƙi tashin ta ne saboda bata daɗe ba aka kira sallan, don haka yabari zuwa sallan Asar yatashe ta
Sai da aka kira sallah yafito yashiga Toilet yaɗauro alwala, fitowa yayi yana warware hannun rigan sa da yanannaɗe wajen yin alwalan, yafito daga ɗakin nasa yashiga ɗakin Saleema, yana shiga ya'isa bakin gadon yatsaya yana kallon ta, barcin ta take yi cikin kwanciyan hankali, sai dai yanda take fitar da numfashi da ƙarfi hakan zai sa kagane ba lafiya ba
Ya daɗe atsaye a wajen yana kallon ta cike da tsananin tausayin ta, yasan da cewa tana fama da ciwo tunda lokacin gab da za'ayi auren su Abbanta yakira sa musamman don su tattauna matsalan Saleeman, anan yake faɗa masa komi kuma yaɗaura da roƙon sa akan don Allah yariƙe masa ƴa bisa amana
Ajiyan zuciya yasauke kana yasaka zara-zaran hannun sa me yalwataccen gashi a kwance yasoma tadata, pilon yake ɗan ja ahankali yanda zata iya tashi, kasancewar bata da nauyin barci hakan yasa yana soma taɓa wa tabuɗe idanunta da sukayi ja alamun barcin yayi nisa sosai, suna haɗa idanu tayi saurin yunƙurin tashi amma yanda jikinta be da ƙarfi dole takoma takwanta tana sake rufe idanunta
"Ya jikin naki?" Yafaɗa ahankali cike da kulawa kuma har alokacin idanun sa na yawo a jikinta
Bata buɗe idanun ta ba tace "da sauƙi".
Gyaɗa kansa yayi kafin yace "ki tashi kiyi sallah".
Daga haka yajuya yafita batare da yajira me zatace ba
Sai da tatabbatar ya fita kafin tabuɗe idanun nata cike da kasala tatashi zaune tana riƙe kanta, babu ƙarfi ko kaɗan ajikin ta ga kuma kanta dake faman ciwo baya ga haka babu komi yanzu dake damun ta, waigawa tayi taɗauki wayan ta dake kan drowan Gadon taduba lokaci, zaro ido tayi tana kallon wayan cike da mamaki, batayi tunanin har tayi barci me nisa haka ba tunda har gashi ƙarfe 04:07pm.
Ajiye wayan tayi tazuro ƙafafuwan ta ƙasa tasauko, Toilet tanufa taɗauro alwala tafito tasanya Hijab ta tada sallah, azahar da la'asar tayi sannan tacire Hijabin ta'ajiye, wanka tashiga tayi don tasami ƙarfin jikin ta, tana fitowa tashirya cikin jan atamfa me ratsin baƙi da fari, ɗinkin riga da skert ne wanda yayi mata kyau sosai sai zuba ƙamshi take yi, ɗankwali kawai taɗaura tafito Parlour
Yana zaune saman kujera yana latsa wayan sa, ƙamshin turaren ta yasa shi ɗago kai yana kallon ta, sosai yake bin ta da idanu sabida tayi masa kyau ainun
Ita kuwa bata kula dashi ba sai faman gyara zaman ɗankwalin ta take yi da be gama zama da kyau ba, sai da ta'iso cikin parlour'n kafin taɗago kanta su haɗa idanu, yanda yake kallon ta ne yasa ta jin kamar tajuya takoma amma babu hali dole ta'iso tazauna can kujeran da ke gefen sa, hakan yasa babu yanda za'ayi yaganta dole sai idan ya juya kansa
Ɗan lumshe idanun sa yayi yabuɗe yaci gaba da latsa wayan sa, amma yanda turaren ta ke shiga masa ƙofofin hanci hakan yasa duk yarasa tunanin sa, sosai turaren yayi masa daɗi, sai lumshe idanu yake yi yana buɗewa, daga ƙarshe yaɗago kai yana kallonta yace
"Kin sha maganin ki?"
Ita da taɗan buga tagumi tana tunani nan taji saukar muryan sa a kunnen ta, tayi saurin ɗagowa tana kallon sa kafin tace "a'a sai anjima ne lokacin sha".
Be ce komi ba yakau da kansa yaci gaba da latsa wayan, dama chatting yake yi da Brr. Tahir, ganin dai turaren duk ya ishe sa da ƙamshi hakan yasa yatashi yanufi ƙofa yafice
Tabi bayan sa da kallo tana tunanin inda zai je
Yana fita Garden ɗin gidan yanufa yazauna kan fararen kujerun dake wajen, lumshe kyawawan idanun sa yayi yana sauraron bugun zuciyar sa, hannu yasaka yana dafe setting zuciyar sa tare da faɗa wa duniyar tunani
Har yau ya gaza gane meke damun sa, meyasa yake shiga damuwa akan abinda baya tunanin zai sake gani, kullum zuciyar sa ƙulafucin ranan da yakasa mantawa yake yi tare da fatan sake ganin makamancin ta
Numfashi yaja tare da fesarwa yana ci gaba da latsa wayan sa, be tashi a wajen ba sai da yaji kiran sallah, miƙe wa yayi yasaka wayan sa a aljihu yanufi wajen Me gadi, anan yayi alwala yafita masjid, sai da akayi isha'i kafin yadawo gida
Tana nan zaune a parlour'n, sallah kawai taje tayi tadawo tasake zama, sai dai yanzu kallo take yi, yana shigowa ta'amsa masa sallaman sa tare da yin masa "sannu da zuwa"
Amsa mata yayi yana kallon ta kafin yanufi ɗakin sa yaɗauko car keey yafito yafice
Mintuna goma da fitan sa yadawo riƙe da Ledoji, miƙa mata yayi yace "tasake abincin dake cikin Take-away ɗin a plate" ta'amsa tayi yanda yace sannan tadawo takawo masa, umartan ta yayi tazauna su ci, babu musu tazauna suka ci abincin suka gama sannan tatashi takwashe komi takai kichen, dawowa tayi tazauna taci gaba da kallon ta yayinda shi kuma yana ƙasa har yanzu yana danna waya, babu jimawa kuma yamiƙe yashiga ɗakin sa yaɗauko computer'n sa yadawo yazauna kan kujera yasoma aiki aciki
Har barci yakwashe Saleema a wajen yana nan yana aikin sa, sai wajen ƙarfe 11:00pm. Sannan yadakata yana kallon ta, hakan yasaka yamiƙe ba don ya gama aikin ba yatattara kayan sa yamayar ɗaki yadawo yatashe ta yace "su je su kwanta". Bayan shi tabi suka shige ɗakin sa yarufo ƙofa.
.
***** ****** ****** ****
Yau a makare suka tashi sai ƙarfe 11:30am. Sannan Khalil yasoma farkawa, wanka yayi yafito yana tsane jikinsa, alokacin ne Saleema tafarka itama sai dai taƙi tashi bare tanuna alamun ta farka, har yagama shiryawa yafita parlour yazauna, Kallo yakunna yasaka tashan CCT.V NEWS yana kallon labarai, jefi-jefi kuma yana latsa wayan sa
Ƙaramar wayan sa dake ajiye ne tayi ƙara yaɗauka yana karawa a kunne tare da yin sallama
Brr. Tahir amsa mishi sallaman yayi yana faɗin "Ango Ango kasha ƙamshi".
Murmushi Khalil yayi yana shafo kwantaccen gashin kansa yace "zaka fara ko?"
Dariya Brr. Tahir yaƙyalƙyale dashi yana cewa "iyeee Ango uhmm Ango Mijin Amarya.."
Katse shi Khalil yayi yana ɗaure fuska
"Wai kai meye haka ne kanka ɗaya kuwa?"
"Uhmm ai baza ka gane kaina ɗaya ba sai idan nazo ganin Amarya". Cewar Brr. Tahir Yana sake sakin dariya me sauti
Shiru Khalil yayi be sake ce masa komi ba sai yamayar da hankalin sa kan kallon sa
"Hello kana jina kuwa?"
Guntun tsaki Khalil yaja yana faɗin "ina jinka mana idan ka gama zan kashe wayana".
Brr. Tahir murmushi yayi yace "sorry Man akwai magana fa, kasan narigada naga gidan da mutumin nan yake zaune sai dai be bani dama har yanzu mun tattauna ba".
Khalil ɗan tattaro naman goshin sa yayi cike da takaici yace "yana son Raina mana wayau ne fa, but bari dai in taho sai mu tattauna don nima na samu ƙwaƙwƙwaran hujjan da dole sai ya saurare mu".
"Ok sai ka zo".
Daga haka sukayi sallama yaciro wayan daga kunnen sa yana miƙe wa tsaye yakoma ɗakin sa, abubuwan da zai buƙata yaɗauka sannan yanufi wajen gadon sa yana kallon Saleema da har yanzu tana nannaɗe acikin bargo taƙi tashi, yasan da cewa tun ɗazu ba barci take yi ba don haka yamatso gab da ita yaraɗa mata
"Ni na fita bazan daɗe ba zan dawo, ki kula da kanki uhmm?"
Tun sanda yasoma mata magana tabuɗe idanu tana kallon sa, sai tasaki murmushin da yakufce mata batare da ta shirya yin sa ba tayi saurin gyaɗa masa kai
Shima murmushin yayi bece komi ba yajuya yafice tabi bayan sa da kallo.
[11/7/2020, 4:01 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 45*
Minti goma da fitan shi kafin tamiƙe tasauko daga gadon, Toilet ɗin sa tashiga tayi wanka tasaka towel ɗin sa tafito tanufi ɗakinta, akan stool tazauna gaban dressing mirror tasoma shafa Lotions a tattausar farar skin ɗinta, shafa Lotions ɗin take yi but hankalin ta baya wajen, sai faman zuba murmushi take yi cike da tsananin nishaɗi da kallo ɗaya kayi mata zaka fahimta, har tagama batasan a wani duniyar take ba, hakan yasa tashafe fiye da awa ɗaya tana abu ɗaya, daga ƙarshe tamiƙe tanufi wajen kayan ta tazaɓo wanda zata saka
Jan Material Less me stone ajikin sa, ɗinkin doguwar riga pitted, yayi mata kyau sosai ya kamata cif-cif cike da sha'awa, tayi wannan ɗaurin na ture gaka tsiya sai ƙamshin amarci take zabgawa
Fitowa tayi takoma ɗakinsa tagyara tasaka air freshener, har toilet sai da tawanke kafin tafito tazauna aparlour takunna t.v
Zaman ta babu daɗewa tajiyo Nocking, miƙewa tayi tanufi ƙofan don tasan ba Khalil bane, tana buɗe ƙofan idanuwan ta suka faɗa cikin na Halwa dake tsaye tana zabga mata murmushi, tana riƙe da Husna da hannu ɗaya rungume ajikinta, ɗayan hannun kuma tana riƙe da ɗan ƙaramin trolly
Cike da tsananin murna Saleema tatarbe ta tana rungume ta daga ita har Husnan dake barci
Daga ƙarshe shigowa sukayi suka yada zango a parlour'n bayan Saleema ta amshi Husna ta shimfiɗe ta akan kujera
"Sister kinga yanda kika sauya kuwa? Sai ƙyallin amarci kike yi sai dai fa kin rame". Cewar Halwa da tazuba mata idanu tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta
Itama Saleema dake faman zabga murmushin tace "Hmm Ni dai bana son sharri, duka yaushe nayi auren da zakice ina ƙyallin amarci".
"Allah kuwa dagaske my Sister kin sauya sosai, gani nake kamar na shekara ban ganki ba saboda tsaban kyau da kikai min, gaskiya aure rahma ce".
Dariya Saleema tayi wannan karon tace "Allah ko ƴar uwa?"
Ɗage gira ɗaya Halwa tayi tace "dagaske My Sister".
"To kice kema kin kusa motsawa musha biki?"
Ɓata fuska Halwa tayi tana sauya zancen da faɗin "ƴar uwa nifa ba zama zanyi ba don tare da drever nake zai kai ni School, ƙarfe 02:30pm nake da Exams, Ina Mijin naki mu gaisa kafin in tafi?"
Saleema tace "ya fita yanzu".
Murmushi Halwa tayi tana kama haɓa tace "har ya gama cin amarcin ne ya soma fita?"
Hararan ta kaɗai Saleema tayi tana wani irin murmushi da bakinta yaƙi rufuwa
"To sister zan tafi kinga lokaci ya ja da yawa, akwai saƙon Ummi cikin jakan nan tabani in kawo miki, tace tana gaishe ki tare da Abba ma".
Saleema kamar zatayi kuka tace "Allah Sarki ina amsawa nayi kewar su sosai".
Dariya Halwa tayi tamiƙe tana faɗin "ko dai zakiyi kuka ne?"
Hararan ta tayi itama tatashi tana cewa "Sister ko ruwa baki sha ba fa? Bari in ɗauko miki".
Taƙarike maganar tana nufan wajen Fridge batare da tajira cewar Halwan ba, ɗauko ruwan tayi tadawo tana cewa
"Sai yaushe kuma sister?"
Wulla idanuwan ta tayi alamun tunani tace "uhmm sai dai idan nagama Exams ɗin nan sai in zo inyi miki wuni ko?"
Turo baki Saleema tayi kamar zatayi kuka tace "kai sister kenan har sai na jira kin gama Exams zaki sake zuwa?"
Murmusawa Halwa tayi tace "ke dai karki damu zuwa gidan ki ai sai kin gaji da ganina, yaushe ma akayi auren ne? Ki kwantar da hankalin ki".
Dariya Saleema tayi tace "to shikenan muje in raka ki".
Har wajen mota Saleema taraka ta, anan suka gaisa da Drever, Halwan tashiga mota yaja suka bar gidan
Sai ɗaga musu hannu take yi har Me gadi yarufe Gate ɗin kafin tasauke hannun ta tajuya cikin gidan cike da kewar ƴar uwan nata
Tana shiga parlour'n ta'iske Husna ta farka sai wutsil-wutsil take yi tana son sauko wa, dasauri taƙarisa wajen ta taɗauke ta tana dariya cike da ƙaunar ta tasoma yin mata rawa tana mata wasa
"Iyeee Mamana kin tashi? Yau kin dawo wajena ko? Oh i miss You so much".
Tamanna mata peck a baki, ita kuma sai faman ɓangale mata bakin take yi tana yarfe hannayen ta tare da tsalle jikin ta
Dariya Saleema tayi tana sake riƙe ta dakyau ganin yanda take ta zillewa wai adole tana wasa
"My dear ki dena karki suɓuce min kinsan girma ne dake".
Ita kuma kamar tana jinta taci gaba da zillewa tana tsallen murna sai ɓangale baki take yi, Allah ya zuba mata wayau gata kuma bata da ƙyuya ko kaɗan, duk wanda yaɗauke ta haka zatai ta ɓangale masa baki kamar tasan shi
Tana nan zaune tana ta jijjiga yarinyan tana mata wasa kamar ta sami sa'ar ta sai faman yin mata hira take yi da surutu
Khalil yaturo ƙofan yashigo da sallama a bakin sa
Ɗago kai tayi tana kallon sa kamar yanda shima ɗin yaƙure su da nashi idanun me tsananin kyawu da kaifi
Gaban Saleema ne yafaɗi, sai Lokacin tatuna bata sanar masa da maganar dawowar Husnan ba, daƙyar takawar da fargaban nata tana amsa mishi sallaman
Takowa yayi yashigo ciki still idanun sa na kansu, yarinyan kawai yake kallo cike da sha'awa, shi me son yara ne sosai suna matuƙar burge sa
Matsowa kusa da ita yayi yana faɗin "wannan yarinyan wacece?"
Yaƙarike maganar yana duƙowa gaban ta ya'amshi yarinyan yana sake ƙure ta da idanu, sosai yarinyan tayi masa kama da wacce yasani, lokaci ɗaya kuma yaji ta shiga ran sa har be san sanda yasakar mata kyakkyawar murmushin sa yana wasa da hannun ta ba, itama ɗin sai ɓangale masa baki take yi kamar yanda tasaba tana kallon sa
Mai da idanun sa kan Saleema da taduƙar da kanta ƙasa yayi
Har alokacin bata iya basa amsar tambayan da yayi mata ba
cikin murmushin sa yace "Ya sunan ta?"
Cike da sanyin murya tace "Husna".
Kallon yarinyan yasake yi sai kuma yamiƙe tsaye yana zama kan kujera ya'ajiye ta a cinyan sa yaci gaba da mata wasa
Ita dai Saleema na zaune tana jin su tare da satan kallon su, sosai taji daɗin yanda yanuna son yarinyan duk da kuwa be san ita wacece ba
"Ina Maman ta ne?" Yajeho mata tambayar yana kallon ta
Cike da fargaba Saleema tace "tana gida".
Ɗan waro idanun sa yayi cike da mamaki yace "kenan kawo miki ita akayi?"
"Eh zata zauna a wajena ne".
Kallon ta kawai yake yi cike da tsantsan mamaki, be kai ga magana ba yahangi ɗan kyakykyawar Trolly ɗin dake ajiye gefe
"Kayi haƙuri don Allah nasa an kawo min ita ban tambaye ka ba, wlh na manta ne". Tayi maganar cikin ladabi da sanyin murya
Still kallon ta yasake yi sai kuma yamaida idanun sa kan yarinyan
Shiru kamar bazai yi magana ba sai kuma yace "yanzu har kin warke da zaki iya raino?"
Murmusawa tayi bata iya cewa komi ba sai ɗauke ganin ta da tayi daga kansa
Ajiyan zuciya kawai yasauke be sake cewa komi ba kuma be bata yarinyan ba, aransa kuma tunani yake yi yanda ita Saleeman take son yara har da zata ɗauko yaran mutane da sunan riƙe wa, sai kuma tsananin mamakin uwar yarinyan da ta'iya rabuwa da ƙaramar yarinya kamar wannan, yana son yayi mata tambayan ya zatayi idan zata shayar da ita amma kunya ya hana sa tambayan ta, baya ga haka akwai tarin tambayoyi da yake son yin mata
Saleema ganin shirun dai yayi yawa sai tamiƙe taja Trolly ɗin tanufi ɗakin ta.
.
***** ***** ******* ****
*BAYAN SATI BIYU*
A cikin wannan kwanakin shaƙuwa ne sosai yashiga tsakanin Khalil da Saleema, sun yi kwanakin ne cikin nuna kulawan junan su tare da girmama juna
Duk wani kulawa Khalil yana nuna mata tare da tausayin ta me tsanani da yake yi cikin ransa, baza ka taɓa tunanin su ɗin ba masoya bane domin yanda suke gudanar da zamantakewar su ko masoyan asali albarka
A yanzu soyayyar Khalil sosai yaginu a zuciyar Saleema, tasan da cewa tayi dace ga miji na gari don Khalil ɗan halak ne kuma ya haifu
Shi kuma har alokacin ya kasa jin soyayyar ta cikin ransa, sai dai yasan yayi dace da mata na gari kuma yana ji aransa zai iya zama da ita har ƙarshen rayuwan sa batare da yayi dana sani ba
Zan iya cewa tare suke rainon Husna sabida yanda Khalil ke nuna kulawan sa agare ta, idan har yana gida ko baya aikin komi yarinyan ko yaushe tana hannun sa, sosai yarinyan tashiga cikin ransa.
Jikin Saleema alhmadulillah yanzu ta warke sumul babu abinda ke damunta, tattalin mijinta kawai tasaka agaba sai kuma rainon Husna.
*******
Yau ce ranan da Halwa tace zata zo don haka da sassafe Saleema tatashi cikin ɗoki tasoma aiyukan ta, babu laifi yanzu ta saba da duk wani hidiman gidan duk da ba wani aiki me yawa take yi ba
Shi kansa Khalil yasan da zuwan Maman Husna don tun jiya da sukai ta waya da Halwa yaga tana ɗoki yatambaye ta take faɗa masa Mamar Husna ce zatazo
Shirin Office yayi cikin Ash colour ɗin Suit da yayi masa kyau matuƙa yawuce wajen aiki bayan yayi musu solfie su ukun cike da nishaɗi.
Har tagama abinci da duk abinda yakamata kafin Halwa ta'iso.
_Alhamdulillah anan nakawo ƙarshen BOOK ONE sai ku tara a BOOK TWO don jin me zai faru._
.
_ya zaman Khalil da Saleema sai kaya, kuna ganin tausayin da yake mata zai iya juye wa yazama ƙauna?_
_Shin kuna ganin Halwa zata cika burin ta?_
_me zai faru idan ta mayar da Husna ga Mahaifin ta?_
_ya Maganar Haris da be san yana da ƴa ba?_
_kuna ganin Zainab zata amince da soyayyar Nura?_
_Ya maganar Nazeefa da takamu da soyayyan wanda be san ma tana yi ba?_
_kuna ganin idan har Mom tagane zata aura mata shi kamar yanda tayi alƙawarin gano meke damunta kuma tashare mata hawaye?_
_Shin kuna ganin Halwa zata koma ga Iyayen ta?_
_Shin ya za su karɓe ta?_
_duk a Two ne zaku samu amsar tambayan ku da dalilin da Nura yajuya wa Halwa baya?._
_sai ku biyo NI don ji amsoshin ku_
_Nafisat Jikar Lawal ce_✍️
Ba_byeee 👋👋👋👋👋👋👋👋😉🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
[11/9/2020, 9:13 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈 _WhatsApp Number 07065334256_
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
````Allah ya dawo dani mu tsunduma cikin labarin
Na gode masoyana.```
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER One*
________🎓Suna zaune su Biyu akan dainning table suna cin abinci
Halwa kai abincin bakin ta tayi tana lumshe idanun ta cike da jindaɗi, sai kuma tabuɗe idanun taɗaura akan Saleema da itama tamayar da hankali wajen cin abincin ta, murmushi me sauti Halwa tasaki still tana kallon ta tace
"Sister gaskiya abincin nan kamar zai tsinke min kunnuwa, kina gani fa har rawa suke yi sabida tsaban daɗin abincin nan".
Dariya Saleema tasaki tana kallon Halwa da taƙara ɗibo wani abincin takai bakin ta tana faman lumshe idanu
"Bari dai in tashi in ɗauko pilow in tare ki dashi, idan ba haka ba babu me iya tare ki nan gaba in kikaci gaba da wannan santin".
"Allah Sister ba santi bane, kinji yanda abincin yake da matuƙar daɗi ne sai kace wacce tadaɗe da ƙwarewa, wlh ko Ni bazan iya rin wannan ba".
Murmushi Saleema tayi cike da jindaɗi sai dai bata iya cewa komi ba
"Ƙara min miyan". Halwa tace hakan tana miƙo mata plate ɗin shinkafan
Zuba mata miyan tayi tana faɗin "Kinsan jiya da Zazzaɓi Husna ta kwana, wlh duk na ruɗe sabida yanda naga tana yi, da ba don Yaya Barrister ba bansan yanda zan yi ba, shi yatashi yayi ta rarrashin ta har yana cewa in koma in kwanta". Taƙarishe maganar nata tana wani irin murmushi me ma'anoni da yawa wanda Ni kaina bangane mata ba
Shiru Halwa tayi bata ce komi ba illa kai abinci bakin ta da take yi
Ɗago kanta Saleema tayi takalli Halwan sai kuma tamayar da kanta kan abincin tana sake yin murmushi
Tasan da cewa baza ta taɓa tankawa ba, halin ko in kula shi Halwa ke nuna wa Husna, tunda tahaife ta ko ɗaukan ta idan ba ya zama dole bane to ko kallo bata ishe ta ba, baza ka taɓa tunanin itace uwarta ba
Basu sake magana ba har sanda suka gama cin abincin suka koma parlour, Hira suka ɓarke dashi cike da nishaɗi, sai da aka kira sallah kafin Saleema tashige ɗaki don yin Sallah, ita kuma Halwa tadasa Kallo kasancewar bata sallah
Khalil ne yaturo ƙofan da sallama a bakin sa hakan yasa Halwa ɗago idanuwan ta tasauke acikin nashi idanun wanda yayi dai-dai da yankewar gaban su a lokaci ɗaya
Kallon kallo suke ma juna cike da wani irin yanayi me wuyan fassara
Khalil sandarewa yayi a tsaye a wajen kakkaifan idanun sa akanta, ganin abun yake yi tamkar a mafarki yau yarinyan da tahana zuciyarsa sukuni tsawon lokaci itace agaban sa a kuma cikin gidan sa, kullum cikin tunanin ta a barci kuma mafarkin ta
Janye idanunta Halwa tayi daga kallon sa, ko kaɗan kuma bata gane sa ba sai dai idanun sa sun mata kama da wanda tataɓa gani
Be jirga daga wajen da yake ba illa zuba mata idanuwa kawai yayi kuma ya kasa ɗauke wa
Fitowar Saleema daga ɗakin ta tahange sa tsaye ya kafe Halwa da kanta ke ƙasa da kallo, irin kallon da yake mata shi yasaka gabanta yayanke yafaɗi, take taji wani abu ya soke ta a ƙahon zuciya da yasaka tayi saurin ɗaura hannunta a ƙirjin ta tana runtse idanu
Halwa da har yanzu take jin idanuwan sa masu tsananin kaifi suna yawo ajikin ta, dai-dai tana ɗago kanta tahangi Saleema tsaye dafe da ƙirji, dasauri tamiƙe tana faɗin "Sis lafiya kuwa?"
Buɗe idanuwan ta tayi tana kallon ta sai kuma tamaida ga Khalil da maganar Halwan shima yadawo dashi hayyacin sa, haɗa idanuwan da sukayi yasaka shi sakar mata kyakkyawar murmushin sa yana takowa cikin parlour'n
Wannan murmushin da yayi mata shi yasaka taji sanyi aranta, takalli Halwa dake nufo ta a yanzu ɗin taƙirƙiro murmushi tace
"Babu komi".
"Anya kuwa? Ko dai wani abun ke damun ki?" Halwa tasake tambayar ta cikin damuwa don bata yarda babu komi ɗin ba
Still Saleema tana murmushi tariƙo hannun Halwan suka nufi kan kujera tana faɗin
"Yaya sannu da zuwa".
Idanun sa akan su ya'amsa mata cike da kulawa
Zuciyar Halwa har alokacin bugawa yake yi kuma ta rasa dalili, har a time ɗin kuma bata iya ɗago kai ta sake kallon sa ba, zama kawai tayi tana sake mayar da idanun ta kan t.v
Cike da son kawar da abinda ke cikin zuciyarsa yayi hanyan ɗakin sa cikin takunsa me burgewa da cikan mazan taka
"Yaya baku gaisa da Maman Husna ba". Saleema tafaɗi hakan tana kallon bayan sa
Cakk yatsaya zuciyar sa na wani irin bugawa dasauri-dasauri
"Ina yini". Cewar Halwa itama da taɗago kanta tana kallon bayan nasa
Runtse idanun sa yayi da ƙarfi yana sake danne abun da yake ji, cikin wani irin murya da dole kagane akwai wata matsala ya'amsa mata da "lafiya". Sannan yawuce ciki da sassarfa
Basu kawo komi akai ba illa mayar da hankalin su ga juna da sukayi
Cikin murmushi Halwa tace "baza ki bi bayan sa bane?"
Hararan wasa Saleema tasakar mata tana murmushi da son kawar da abinda take ji cikin zuciyarta, domin kallon da Khalil yayi wa Halwa sosai yatsaya mata arai har tana son dasa zargi cikin zuciyarta, bata iya cewa komi ba sai murmushin da take faman yi
Matsowa Halwa tayi taraɗa mata magana a kunne, dariya suka fashe dashi suna tafawa.
____________________
Cike da sanyin jiki yaƙarisa kan gadon sa yazube yana ɗaura kansa akan pilow, sosai zuciyarsa yake faman bugawa kamar zai faso ƙirjin sa ba don komi ba sai maganar da Saleema tafaɗa masa Halwa itace Mamar Husna, numfashi yasoma fesarwa yana son dai-dai ta nutsuwar sa dake son gushe wa, hannun sa yaɗaura akansa yariƙe yana lumshe idanuwan sa sabida jin yana faman sara masa, baya son ko kaɗan zargin sa yazama gaskiya
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.."
Abinda yake ta faman maimaita wa kenan har yasoma jin nutsuwarsa na dawo masa tare da sassaucin bugun zuciyar sa
Dantsen hannun sa yaɗaura akan kyakykyawar face ɗin sa yayi shiru kamar ruwa ya cinye sa
Har Saleema tashigo be motsa ba
Maganar abinci tayi masa amma sai yagirgiza mata kai alaman bazai ci ba
Shiru tayi kamar zata yi masa magana sai kuma takasa tajuya tafita
Parlour takoma sukaci gaba da hiran su da Halwa, har sanda tajiyo kukan Husna dake barci a ɗakin ta, zuwa tayi taɗauko ta tadawo parlour'n tahaɗa mata abincin ta tasoma bata
Khalil har akayi sallan la'asar be tashi daga inda yake shingiɗe ba, abun duniya duk yayi masa yawa, sai daga baya daƙyar yamiƙe yasoma cire kayan jikin sa, zuwa yanzu kuma kansa sosai yake mishi ciwo kamar zai fashe
Toilet yashiga yayi wanka yaɗauro alwala yafito, jallabiya yazura yafito parlour'n fuskarsa duk babu walwala, kallo ɗaya yayi musu yaɗauke kansa saboda haɗa idanun da sukayi da Halwa
Itama dai sauke kanta ƙasa tayi tana me mamakin kanta da wannan mutumin, shiru tayi tana sauraron bugun zuciyarta wanda haɗa idanun da sukayi yahaddasa mata hakan
Miƙewa Saleeema tayi da Husna a hannun ta tace "bari inyi sallah sister".
"Ok muje nima in shirya tafiya zanyi". Halwan tafaɗa tana tashi tsaye
Hararan ta Saleema tayi tace "tun yanzu? Ai ba haka mukayi dake ba".
Dariya kawai Halwa tayi tazo tawuce ta tayi gaba
Itama tabi bayan ta tana ƙorafi
Suna shiga ɗakin Saleema tashimfiɗe Husna da takoma barcin ta, ita tasoma shiga Toilet ɗin taɗauro alwala kafin tafito Halwa tashiga
Bata jima ba tafito tazauna akan drowan Gadon taɗau wayan ta tana neman layin Drever, sai dai wayan tasa akashe ne, tsaki taja tamiƙe tanufi kan stool dake gaban mirror tazauna tasoma shafa Powder tana gyara fuskarta
Tana nan zaune har Saleema ta'idar da sallan ta tajuyo tana kallon ta tace
"Wai don Allah dagaske yanzu zaki tafi? Please ki bari sai dare mana".
Murmushi Halwa tayi tana kallonta ta cikin mirror tace "kina son gobe in ƙi zuwa miki kenan?"
Girgiza kanta Saleema tayi itama idanun ta akanta, sai kuma tace "amma dagaske zaki zo ɗin gobe?"
Cike da son riƙe dariyan ta dake son kufce wa tace "sosai ma sister gobe zan dawo shiyasa zan tafi yau da wuri".
Gyaɗa kanta tayi sannan tamiƙe tana cire Hijabin ta tace "to shikenan na yarda ki tafi amma goben ki zo da wuri".
Halwa bata iya bata amsa ba saboda dariya da yacika cikin ta sosai ƙiris yarage tasaki dariyan, ɗaga mata kai tayi tana sauke kanta ƙasa tasoma dariyan ta yanda baza ta ganta ba
Saleema kuwa kan gado tanufa batare da ta kula da ita ba, sai zayyano mata saƙon gaisuwa da zata kai ma su Ummi da Abba take yi
Ɗago da kanta Halwa tayi tajuyo gaba ɗaya tana kallon Saleema cike da murmushin da yabayyana haƙoran ta tace "amma fa na kira drever wayan sa be shiga ba kuma gashi ban fito da kuɗi ba".
Saleema tace "to nima ai bani da kuɗi gaskiya, amma bari in duba ko Yaya Barrister ya dawo sai ince yayi ma Drever magana yakai ki".
Gyaɗa kanta kawai Halwa tayi
Ita kuma tatashi tafita tashiga ɗakin Khalil
Yana tsaye ne agaban mirror ya sauya kayan jikin sa zuwa ƙananan kaya, yana fece suman sa da Cumb tashigo
Takowa tayi tazo inda yake tana kallon sa cike da ƙauna, sosai yayi mata mugun kyau har ta manta abinda yashigo da ita ta shagala wajen kallon sa
Ajiye cumb ɗin yayi yajuyo yana kallon ta, tayi saurin duƙar da kanta cike da kunyan kamata da yayi tana kallon sa
Be ce komi ba yamatsa gaban gadon sa yaɗau Wrest watch ɗin sa yana ɗaurawa a tsintsiyan hannun sa
"Uhm dama Halwa ce zata tafi gida shine nace ko zakayi ma drever magana yakai ta?". Tayi maganar a hankali tana kallon sa
Tsayar da abinda yake yi yayi yana juyowa yakalle ta, ganin sun haɗa idanu sai yagyaɗa mata kansa tare da ci gaba da ɗaure Wrest watch ɗin
Murmushi tayi tajuya zata fice, har ta kai bakin ƙofa tajiyo muryan sa
"Tafito sai in sauke ta".
Kallon sa tayi shi kuma yaɗauke kai yana takawa yanufi wajen takalman sa
Cikin sanyin murya ta'amsa mishi sannan tafice.
0 comments:
Post a Comment