"Sis ki shirya Yaya Barrister zai kai ki".
Halwa wani kallo tayi mata sai dai batace komi ba tamiƙe taɗauki Veil ɗin ta tayi Rolling ɗin sa akanta, sai taɗau HangBag ɗinta tarataya, wayan ta a hannun ta suka fito tare da Saleeman, waje suka fice a tunanin su zasu ganshi sai dai babu shi be fito ba, a compound ɗin gidan suka tsaya suna taɓa hira har sanda sassanyan turaren sa yakawo ma hancin su cafka
Saleema kallon kyakykyawar Mijin nata tayi cike da tsananin ƙaunar sa
Ita kuwa Halwa tunda tayi masa kallo ɗaya taɗauke kanta
Zuwa yayi yawuce su yanufi wajen Farar motan sa yabuɗe yashiga
Su ma takowa sukayi har wajen motan, Saleema tabuɗe mata ƙofan tashiga tarufe mata
Tana nan tsaye har suka fice a gidan kafin taja numfashi ahankali takoma cikin gidan
Shiru cikin motan babu me motsin kirki ahaka sukai ta tafiya
Halwa ma duƙar da kanta tayi ƙasa tana faman juya wayan ta
Yayinda Khalil yake tuƙi amma hankalin sa gaba ɗaya yana kanta, so yake yi yacire duk wani abu dake cikin ransa a game da ita tunda yasan ita ɗin mallakin wani ne
Tafiya suke yi sosai babu me magana cikin su
"Ina ne gidan naki?"
Tatsinkayi sassanyan muryan sa me tsananin daɗi a kunnen me sauraro, ɗago kai tayi takalle sa kamar me tunani sai kuma taɗauke kanta tana faman maimaita maganar nasa aranta har sanda tafahimta sannan tabashi amsa
"Sabon layi".
Kallon ta yayi kamar zai yi magana sai kuma yafasa, ya san cewa Sabon Layi ne gidan su Saleema, to amma taya ita zatace masa anan take? Sai kuma yayi tunanin maybe itama a anguwan take aure
Be sake magana ba har sanda yashigo cikin anguwan, yana jiran yaji ta nuna masa hanya ko wani gidan but shiru hakan yasaka yaci gaba da tafiya batare da ya sake tambayan ta ba
Sai da aka kawo dai-dai gidan su Saleema taga yana shirin wuce wa, takalle sa tace "Nan ne fa".
Tsai da motan yayi kafin yayi Rivers yakoma baya yadanna horn me gadi yaleƙo sannan yabuɗe musu, tura hancin motan yayi cikin gidan sannan yayi parcking
Tana ganin ya tsaya tabuɗe motan sannan taɗan juyo takalle sa suka haɗa idanu tayi saurin janye nata cike da tsananin faɗuwar gaba
"Na gode". Tafaɗa ahankali kafin tafice dasauri tarufe masa ƙofan tatafi
Har tashige yana kallon ta cike da mamaki aransa, yana da tarin tambayayo aran sa sai dai be san wanene zai amsa masa ba
Yasan da cewa Saleema ita kaɗai iyayen ta suka haifa bare yayi tunanin ƴar uwanta ce, sannan ma basu kama ko kaɗan, sai dai yana tunanin ko dangin ta ne
Motan sa yaja yabar gidan yanufi inda zai je.
*____________________*
Sallama tayi tashigo gidan agajiye
Umma ta'amsa mata tana kallon ta
Zuwa tayi tazauna akan tabarman da Umman take zaune
"Kin dawo?"
Gyaɗa mata kanta tayi tana me zame jakan ta kafin tace "sannu da gida Umma".
"Yauwa Zainab da alamun dai yau kinsha wahala tunda naga kina langaɓewar nan?"
Zainab tace "uhm umma ai ba'a magana, wahala kam akwai ta, ko abinci yau ban iya ci ba tun safen nan wlh lectures yayi zafi".
Sake kallon ta dakyau Umma tayi tace "sai kika zauna haka babu abinda kika ci? To ai dama Dole kisha wahala, ki tashi kije ɗakina ki ɗauko abincin ki".
Miƙewa Zainab tayi don dama sosai cikin nata yake ƙwaƙulan ta, shiga ɗakin tayi taɗauko abincin tafito tazauna inda tatashi
Tana ci suna hira kuma duk na hiran makarantan ne
"Ni wlh dama zaki haƙura da karatun nan haka nan abu yaƙi ci yaƙi cinye wa, memakon ki samu miji kiyi aure sai ƙara karatun ma kike yi shi kuma ba me ƙare wa ba".
Kumburo fuska Zainab tayi tace "Umma kema kinsan karatu nake so a yanzu, ban tashi yin aure ba shiyasa ma bana kula kowa a yanzu ɗin".
"To wa yace miki karatu na hana aure ne? Tunda gashi kin soma ai abu me sauƙi ne Mijin naki yabar ki kici gaba, shiyasa wlh nake miki sha'awar auren Nura tunda shi yayi karatun kuma bana da haufi akan zai barki kiyi karatun ki".
Tashi Zainab tayi tsam bayan da Umman nata tagama zayyano maganan, batace komi ba tashige ɗakin ta tafaɗa kan gado
Umma kuwa da tabi ta da kallo baki sake tayi ƙwafa tana faɗin "wawiya kawai wacce batasan me yake mata ciwo ba".
Lumshe idanun ta Zainab tayi wasu hawaye masu zafi suka sauko mata a kunci
Ta rasa meyasaka Umman ta take magana akan Nura, meyasa Ummanta take son auren ta da Nura, taƙi tagane cewa ita baza ta iya auren sa ba, baza ta taɓa auren saurayin da Halwa take mutuwar son sa ba koda kuwa ita tana son shi".
Hannu tasaka tana share hawayen ta tare da yin matashi da duk ka hannayen ta
Tana jin sanda Abban ta yashigo Umma take ta rattabo masa bayani, har da faɗin "wlh Malam tun wuri ayi wa tufkan hanci idan har ba so kake yi Zainab ta tsofe agida babu mashinshini ba, ga yaro son kowa ya fito yana son ta amma ita ƙiri-ƙiri ta shafe wa idanun ta toka taƙi shi akan dalilin ta na banza dana hofi, to Ni gaskiya bazan iya zuba idanu har sai sanda tagama wannan ƙaddararren makarantan ba, kawai kace ma Nura yaturo idan yaso sai taƙarisa can agidan sa yafi".
Murmushi Abba yayi yace "Jummai Ni wannan cece kucen da kike yi banga amfanin sa ba, tunda yarinyan nan ta nuna bata son yaron nan menene na son sai ta aure shi? Duk a ƴaƴana babu wacce nayi mata auren dole bare kuma kan Autana, kibari idan har sun dai-dai ta kansu falillahil hamdu amma Ni bazan mata auren dole ba".
Shiru Umma tayi tana gyaɗa kanta cike da takaici, ba wai don tarasa abun faɗa bane sai dai don haushin Abban da yake goya wa Zainab baya, idan da ya amince ita ana ta da tuni anyi an gama, in taje can sai su daidai ta.
Miƙe wa Abba yayi be sake cewa komi ba yaɗau buta yashiga bayi don taɗauro alwalan magariba da har an soma kira
Ita kuwa Zainab sanyi taji cikin ranta ko banza tasan Abba bazai bari ayi mata aure ba sai da yardan ta, kuma idan har itace zata amince da Nura kafin ayi musu aure to baza ta taɓa amincewa ba har abada..
*______________________*
Turo ƙofan tayi tashigo da sallama a bakin ta
Khalil dake zaune gefen gadon sa yana faman aiki acikin Lapton yaɗago yayi mata kallo ɗaya sannan yamayar da kansa yana amsa mata sallaman
Takowa tayi zuwa wajen gadon tashimfiɗa Husna akai sannan itama tazauna tana kallon sa
Shima alokacin yasake ɗago kansa yakalle ta sannan yamaida idanun sa kan Husna, tsawon sokonni biyar yana faman kallon ta kafin yace
"Wai ina Mahaifin yarinyan nan?". Yaƙarike maganar yana aza idanun sa kan Saleema
Shiru tayi tana sad da kanta ƙasa, ba ta jin zata iya sanar masa haƙiƙanin gaskiya kuma bata san me zata ce masa ba a yanzu
Ci gaba da danna Lapton ɗin sa yayi be sake ce mata komi ba, sai can kamar mintuna biyar yasake jeho mata tambayan
"Ina Mahaifin yarinyan nan nace?"
Yanda yayi maganar ne a kausashe yasa hantan cikin ta ya yamutse, batasan sanda bakin ta yafurta "sun rabu ba".
Cakk yatsaya da abinda yake yi yajuyo yana kallon ta
Itama ɗin shi take kallo cike da tunanin meyasaka yake son sanin Mahaifin Husnan bayan ada be taɓa tambayan ta ba?
Kau da kansa yayi yaci gaba da aikin sa
Ita kuma ajiyan zuciya tasauke sannan tagyara takwanta tana tunani aranta
"Shin meyasa nake son kawo zargi ne acikin auren mu? Meyasa zuciyata take son kawo min abinda zai hargitsa min rayuwa? Shin menene abun zargi anan?"
Kwanciyar ta tagyara tana kallon sa, ahankali kuma tafurta "Allah na tuba Allah ka cire min zargi araina".
Aikin yake yi amma maganar Saleema ke kai kawo cikin ransa, duk da yaji sanyi ta wani gefe nasa amma kuma yasan cewa mafarkin sa bazai taɓa zama gaske ba
A haƙiƙanin gaskiya zuciyar sa ta kamu da ƙaunar Halwa tun ranan farko da yaganta, amma taya zai iya mallakan ta bayan ita ɗin ƴar uwa ce ga matar sa?
Har Saleema tayi barci yana nan zaune yana latsa Lapton ɗin sa duk da kuwa tunani ne cinkushe aran sa wanda yahana sa jindaɗin aikin
Daga ƙarshe ma tashi yayi yashige toilet yaɗauro alwala, fitowa yayi yazauna a bakin gadon yana kallon Saleema dake maƙale da Husna, sosai yake mamakin yanda take ƙaunar yarinyan
Ya jima a zaune awajen yana kallon su, amma azahiri tunani ne aransa wanda har yasoma haddasa masa ciwon kai
Kwanciya yayi yaci gaba da tunanin, yafi mintuna 20 kafin yamiƙe yatashi yasoma jero nafilfilu ganin hakan shine kaɗai mafita a gare shi, domin ko kaɗan ayau ɗin baya jin barci zai iya ɗaukar sa.
.
*Plz Share and Vote*
_More Comments more typing._
[11/13/2020, 11:10 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Three*
________🎓Washe gari ƙarfe 07:30am. *BRR. IBRAHIM KHALIL* yagama Shirin sa na zuwa office
Yau yayi shiga na Red colour suit, sai na cikin kuma whiter ne, necktie ɗin sa da Belt ɗin wandon sa baƙi ne, yayi kyau sosai sai tashin ƙamshi yake yi, sosai kwarjinin sa da cikan halittansa suka sake fitowa ainun
Be tsaya yayi breakfast ba duk da kuwa Saleema tuni tatashi tayi masa, haka yafice sabida yana sauri
Aiki sosai yake dashi a office, gashi kuma zasu je wani waje shi da Brr. Tahir
Sai wajen 12:00pm. Yagama sannan suka tafi.
Ƙarfe :2:30pm. Suka gama yanufi gidan su
Yana yin horn me gadi yazo yabuɗe masa, shiga yayi da motar ciki yayi parcking yafito yarufe murfin motan yashiga gidan
Mom na zaune a parlour tana cin Fruits tana kallon tashan African t.v ana wa'azi tajiyo sallaman sa
Fara'a tasaki tana amsa masa sallaman kafin taɗau Remote tarage t.v n
Ahankali yatako cike da gajiya yazauna gefen ta sannan yagaishe ta
Murmushi tayi tana shafa kansa ta'amsa masa tana tambayan Saleema
Sai da yayi releasing akan kujeran kafin yabata amsa da "lafiyan ta ƙalau Mom".
"Masha Allah haka ake so".
Sai da tagutsira 🍌 Bananan hannun ta kafin takalle sa tace "ko asawo maka abinci?".
Gyaɗa kansa kawai yayi yana jan numfashi
Mom har ta buɗe baki da ninyan kiran ƴar aikin ta sai ga Nazeefa ta fito daga ɗakin ta riƙe da plate a hannun ta
"Yauwa Nazeefa sawo ma Yayan ki abinci".
Nazeefa da idanun ta ke kan Khalil ta'amsa mata da "Toh". Sannan tagaishe da Khalil ɗin
Idanun sa shima akanta ya'amsa mata
Kichen ɗin tanufa zuciyarta cike da ƙaunar sa, sosai yau ɗin yasake mata kyau fiye da ko yaushe, domin ta ɗan jima rabon da tagan shi, ko da yazo gidan ita tana makaranta a lokacin
Fitowa tayi riƙe da plate da spoon aciki, taƙariso ta'ajiye masa kan Centre table bayan ta ɗan matso masa dashi, zuwa tayi tazauna can kujeran dake Facing nashi taduƙar da kanta tana satar kallon sa
Shi kuwa abincin sa yaɗauka yana ci yana sauraron hiran Mom da take yi masa akan Yayan nasa Sameer
Ko kaɗan bata gajiya da kallon sa, da ace zata kwana tana kallon sa to baza ta taɓa gajiya ba, a kullum ƙaunar sa sake wanzuwa yake yi a zuciyar ta, ta rasa yanda zatayi tacire sa aranta, bata da damuwa a ko yaushe sai nasa, burin ta kullum tasami hanyar da zata mallake sa duk da tana ganin abu ne me wahala ta same sa, amma baza ta cire rai ba da ikon Allah sai Allah ya mallaka mata shi, koda kuwa zata kasance matar sa ta huɗu ne to zata zauna dashi in dai zai aure ta..
"Nazeefa lafiyan ki ƙalau kuwa tunanin me kike yi?"
Maganar Mom yadawo da ita hayyacin ta, dasauri taɗago kanta tana kallon su
Mom ce kaɗai idanun ta ke kanta, yayinda shi kuma yake cin abincin sa hankalin sa kwance
Cikin daburce wa tace "Mom ban ji bane".
"Yayan ki ne ke magana".
Nazeefa sauke idanun ta kansa tayi tace "Yaya me kace?"
Sai alokacin yaɗago fararen idanun sa yana kallon ta, hararan ta yayi yace "ban sani ba".
Bata san sanda tayi murmushi ba sabida yanda yayi maganar har hararan sai kace wani mace
Mom ma sai da tamurmusa don itama taga sanda yayi hararan, cikin murmushin tace "ayi mata afuwa mana Auta wannan harara haka?".
Ajiye abincin yayi yana kallon Nazeefan da tasauke nata idanun ƙasa yace "meyasa baki taɓa zuwa gidana ba?"
Hannun ta tamatse waje ɗaya cike da fargaba taɗago kanta tana kallon sa tace "Yaya makaranta ne yahana Ni zuwa".
Hararan yasake aika mata dashi cikin ɗaure fuska yace "makarantan ne zai hana ki zuwa gidana?"
Mom tace "ai nima nayi godo da ita taje amma taƙi zuwa wlh, Ni bansan meke damun Nazeefa ba yanzu, ko ranan Saturday ɗin nan sai da nasake yin mata magana".
Nazeefa sad da kanta ƙasa tayi kamar zatayi kuka, ko kaɗan bata son zuwa gidan Yayan nata ba don komi ba sai don kishi, baza ta iya juran ganin sa da wata ba idan har ba ita ba
"Je ki shirya kizo mu tafi, ki haɗo da kayan makarantan ki don kwana zakiyi, idan kin wuce makaranta kya dawo nan".
Tashi tayi batare da tace uffan ba tanufi ɗakin ta, tana shiga tacire riga da skert ɗin jikin ta tasaka dogowar riga baƙi da yasha stone masu ƙyalƙyali, sosai take son dogoyen riguna shiyasa ma Mom Ko da ɗinki zata bada ayi mata, dogayen riguna take saka wa ayi mata, tunda ko anyi mata sauran ɗinkunan bata saka wa sai taga dama
Ɗan ƙaramin jaka taɗauka tasaka kayan makarantan ta sannan taɗau school bag ɗin ta tafito
Ko kaɗan bata murna da zuwa gidan Yayan nata, sai dai sauƙin ta ɗaya zata riƙa ganin sa yanzu
Tana fitowa Khalil miƙe wa yayi sukai sallama da Mom sannan yayi gaba Nazeefa tabiyo bayan sa bayan itama tayi ma Mom ɗin sallaman.
*_____________________*
A mota babu me magana cikin su, tun sanda yatambaye ta karatun ta be sake magana ba, hankalin sa na ga titi har suka iso gidan
Bayan yayi horn me gadi yabuɗe masa yasaka motan ciki, yana parcking suka fito atare, yana gaba tana bin sa a baya sai bin gidan take yi da kallo, komi an sauya ba kamar sanda tataɓa zuwa ba
Suna shiga babu kowa sai Husna dake wasa a ƙasa
Wajen ta Khalil yawuce yaɗauke ta yana saɓa ta sama yana mata wasa
Sai Nazeefa tasaki baki kawai tana kallon su
Sai shine da yajuyo yaganta har yanzu a tsaye yace "tsayuwar me kike yi kuma?"
Sai alokacin tadawo duniyar tunanin ta tasamu wuri tazauna
Shi kuma yawuce ɗakin Saleema da Husna a saɓe a wuyan sa
Yana tura ƙofan da sallama yahange ta zaune kan stool tana shafa Lipstick a bakin ta, tayi shiga cikin riga da skert na ɗan kanti, farar riga me gajeren hannu sai jan skert me ɗan faɗi tare da tsagi ta baya, kayan sun yi mata kyau gashi kuma sun ɗauki white skin ɗin ta, kanta da ɗan siririn ɗan kwali da taɗaura be gama rufe mata tsakiyar kai ba
Amsa sallaman tayi tana juyowa takalle su
Sosai tayi masa kyau yatako wajen yana kallon ta batare da yace komi ba
Sannu da zuwa tayi masa tana murmusawa
Ya'amsa mata still yana kallon ta kafin yace "kin yi kyau matata".
Rufe fuskarta da tafin hannayen ta tayi tana ɗan sakin dariya me sauti kafin tace "Nagode Mijina".
Shima sai yayi dariyan yana sauko Husna yariƙe ta sosai a hannun sa sannan yace "ga ƙanwata nan nazo da ita zata kwana gobe zata tafi".
Miƙe wa tayi ta'amsa mishi da "Toh". Tanufi ƙofa, shima yabi bayan ta
Suna fitowa idanun ta yahaɗe dana Nazeefa, har yanzu dai bata san wacece ita agare su ba duk da kuwa tasan ba ƙanwar Khalil ɗin bane, amma ta danganta hakan da ƙila ƴar uwansa ce
Zuwa tayi da fara'an ta tazauna
Ita kuma Nazeefa ganin Khalil shima yazo ya zauna ne tasaki fuskarta itama sannan tagaishe ta
Saleema ta'amsa mata tana murmusawa sannan tatambaye ta Mom? Ita kuma tabata amsa "tana nan lafiya tace agaishe ki".
"Yaya ko in kawo maka abincin nan ne?" Saleema tayi maganar tana kallon Khalil da yatasa Husna gaba yana faman mata wasa
Girgiza mata kai yayi batare da ya kalle ta ba yace "no sai nayi wanka zuwa anjima zanci".
Sannan yamiƙe tare da Husnan yanufi ɗakin sa
"Ƙanwata taso muje kici abinci". Saleema tafaɗa tana kallon Nazeefa da tabi bayan Khalil da kallo
Murmushi taƙirƙiro tana kallon Saleeman tace "a'a Aunty Alhmadulillah sai da naci abinci kafin na taho".
"Haba dai ko ɗan ruwa ne ai kya sha, bari in kawo miki".
Tashi tayi tanufi wajen Fridge
Nazeefa taraka ta da kallo, sosai take mamakin yarinyan da tagani don bata da masaniyar zaman ta agidan, har Mom ma itama sai daga baya tasani, sai kuma tataɓe baki aranta tace "to Ni ina ruwana".
Saleeman tadawo riƙe da
Drinks da taɗauro saman plate ta'ajiye Mata a gaban ta kan Centre table sannan takoma tazauna tana faɗin "bismillah".
Babu musu Nazeefa taɗauka Robbern Fanta tabuɗe tazuba cikin glass cup ɗin da tahaɗo mata dashi, tana sha suna kallo batare da ɗayan su ya sake magana ba tunda babu sabo ko kaɗan a tsakanin su
Suna nan zaune har Khalil yafito, da alamun yayi wanka ne don ya sauya kayan sa cikin shiga na ƙananan kaya wanda sukai ma jikin sa kyau sosai
Duk kansu kallon sa suke yi cike da tsantsan ƙauna
Shima dai kallon su yayi sai ya'aza idanun sa kan Saleema yaɗan ɗage mata gira ɗaya yace "My dear na wuce masallaci, ga ƴar ki can tana barci".
Murmushi Saleema tayi tace "to adawo lafiya".
Gyaɗa kansa yayi yanufi ƙofa yafice
"Ƙanwata muje in Kai ki ɗaki".
Maganar Saleema yakatse mata tunani, cikin son kawar da abunda yatokare mata maƙoshi tamiƙe da jakanta tabi bayan ta
Ɗakin ta takai ta sannan tafito tanufi ɗakin Khalil, anan ita tayi sallan ta kafin tadawo parlour
Alokacin shima Khalil ya dawo har ya zauna saman dainnig yana latsa wayan sa
Wajen tanufa tasoma saving ɗin sa sannan tajuya zata tafi
"Ke kinci abincin ne?"
Juyowa tayi tana kallon sa sannan tagyaɗa masa kanta tana murmusawa
Be ce komi ba yaɗau spoon ɗin yasoma cin abincin sa
Nazeefa tunda tagama Sallah tazauna nan kan sallayan taƙi tashi, sai ma zuba tagumi da tayi ta'af ka tunani
Bata sake fitowa ba har dare
Koda Saleema tashigo tayi mata maganar tafito Parlour ko zata fi jindaɗi, sai tace "a'a nan yayi mata".
Juyawa tayi kawai tabarta takoma parlour taci gaba da kallon ta don shi tuni Khalil ya shige ɗakin sa yana faman aiki a Library ɗin sa
Daga karshe da tagaji da zaman sai tanufi kichen tayi musu girki me sauƙi, taliya tadafa da raguwar miyan ta na jiya
Sai da tagama komi taje tajera a dainning table, lokacin har an kira sallan magriba
Ɗakin Khalil ɗin tanufa tashiga ciki, alokacin ya fito daga Toilet bayan ya ɗauro alwala, kallon ta kawai yayi yafice dasauri
Ita kuma tanufi kan gadon inda Husna ke kwance tarigada ta farka tana ƙananun kukan ta, ɗaukan ta tayi tanufi ɗakin ta da ita
Shiga tayi da sallama a bakin ta, kallon Nazeefa dake sallah tayi tawuce cikin Toilet
Kayan Husna tacire tawanke mata kashin da tayi sannan tayi mata wanka tafito taɗaura ta kan gado, sai takoma taɗauro alwala tadawo tagabatar da Sallah
Nazeefa na zaune akan kujera tana faman kallon Husna dake ta mutsil-mutsil cikin towel da aka nannaɗe ta dashi tana son cire wa tasauko
Har Saleema ta'idar da sallan ta tamiƙe tasoma shirya Husnan, ta kula Nazeefa ba me son yin magana bane shiyasa itama taƙyale ta batare da ta kula ta ba, amma abinda yadace tana tambayan ta
Har tagama abinda zatayi tafito Parlour tazauna tana ma Husna wasa tana kallo
Sai bayan isha'i sannan Khalil yadawo gidan
Suna zaune kan dainning shi ya ɗaura Husna ajikin sa yana cin abinci yakalli Saleema da itama take saving nata yace
"Ina Nazeefa ne?"
"Tana ɗaki tana sallah nayi mata magana yanzu zata fito.."
Bata rufe baki ba nazeefan tafito taƙariso wajen tana gaishe da Yayan nata
Amsa wa kawai yayi yaci gaba da cin abincin sa
Itama zama tayi tayi saving kanta tasoma ci, can kuma taɗago kanta tana kallon sa yanda duk yabada hankalin sa kan Husna ko abincin ma baya ci sosai
"Yaya wai wannan yarinyan wacece?" Tayi tambayar tana ci gaba da kallon sa
Daga shi har Saleema suka ɗago kansu suna kallon ta
Sai da yakau da kansa gare ta kafin yace "Ƴata ce".
Bata sake cewa komi ba taci gaba da cin abincin ta sai dai zuciyarta haushin amsar da yabata take ji
Ita kuwa Saleema murmushi kawai tayi tana kallon Khalil ɗin cike da ƙaunar sa, sannan taci gaba da cin abincin ta
Shi yasoma tashi yanufi ɗaki
Kamar ana tsikarar Nazeefa tana ganin ya shige itama tamiƙe tanufi parlour
Saleema dai bata ce mata komai ba illa kallo ɗaya da tayi mata taɗauke kanta, sai da tagama tattara komi takai kichen sannan tanufi ɗakin ta
Wanka tayi tasanya kayan barci sannan taɗau abubuwan da zata buƙata tare dana Husna tafito tana kallon Nazeefa dake zaune tana kallo
"Ƙanwata koda akwai abinda kike buƙata ne?"
Sai alokacin Nazeefa taganta ma, kallon ta kawai take yi cike da tsananin kishi, tasan tunda tagan ta da shiri ɗakin Khalil zata tafi
"Kenan ko hiran daren ma basuyi sai su shige ɗaki?" Tatambayi kanta tana ci gaba da kallon Saleeman cike da tsantsan haushin ta
Ita kuma Saleema ganin tayi shiru sai tabuɗe ɗakin Khalil kawai tashige abunta aranta tana jinjina wulaƙacin yarinyan, ko ba komi ai ita Matar YaYanta ne bare ma ta girme mata sosai don aƙalla zata bata shekaru uku ƙwarara
Tana ganin ta shige itama tatashi tanufi ɗakin Saleeman zuciyarta kamar zata tarwatse, har wani ɗaci-ɗaci take ji a maƙoshin ta.
Sai Khalil ne daga baya yafito yakashe t.v n yakulle ƙofan Parlourn yakoma ɗaki.
Washe gari ƙarfe 07:20am. Ya riga ya gama shirin sa har breakfast yayi sannan yafita
Lokacin itama Nazeefa tafito da shirin ta na makaranta tana rataye da school Bag ɗin ta tare da jakan da tasaka kayan da tacire, fuskarta duk babu walwala idanunta sunyi luhu-luhu kamar wacce bata samu ishashshen barci ba
Saleema dake kakkaɓe parlour'n taɗago tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta tace "Ƙanwata har kin fito?"
Itama Nazeefan murmushin tayafa ma fuskarta sannan tace "eh Aunty Ina kwana?"
"Lafiya lau kin tashi lafiya? Ya baƙunta?" Saleema tasake yin maganar da fara'a
"Alhmadulillah".
"Ok ga breakfast ɗin ki kizo kici".
Nazeefa tace "a'a bazan iya cin komi ba, zan tafi Aunty sai kuma wataran in na sake dawowa ki gaida yaya".
Saleema kallon ta kawai take yi cike da mamakin ta, sai kuma dai batace komi ba ta'amsa mata sannan tabata saƙon gaisuwa wajen Mom
Tana kallo Nazeefan har tafice sannan taci gaba da aikin ta
Drever yaɗauki Nazeefa yanufi da ita school ɗin su.
[11/16/2020, 6:56 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Four*
________🎓 *TWO MONTHS AGO*
A cikin wannan watannin abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da soma zuwan Halwa makaranta, tayi farin ciki matuƙa
Da farko Saleema ce ma Abba tayi yakaita Abroad tayi karatun, har Abba ya amince amma Halwa ita tace sam bata son tayi nesa dasu dole aka barta anan Katsinan
Tunda tasoma zuwa school ɗin babu ruwan ta da kowa harkan gaban ta kawai take yi, kuma sosai take gane karatun tunda shi tasaka a gaba
Duk da kuwa mutane da dama suna sonn ƙulla alaƙa da ita amma taƙi yarda musamman ma maza da yawancin su suke nuna suna son ta, wannan dalilin ne ma yasa take saka niƙap, da zaran drever ya kawo ta zata ɗau niƙap ɗin ta tasaka, idan kuma yazo ɗaukar ta sai ta shiga motan sai tacire
Har yanzu ta kasa manta tabon ɗa namiji cikin rayuwan ta, ta kasa manta abinda Haris yayi mata, sannan takasa manta abinda Nura yayi mata duk da kuwa har yanzu zuciyarta na mishi uzuri
Ko kaɗan ta tsani namiji yanuna yana son ta sabida tarigada ta cire soyayya cikin ranta
Zuwan ta gidan Saleema sau biyu shima daƙyar taje don aranta ko kaɗan bata son sake haɗuwa da Mijin nata da yatsaya mata arai yaƙi gushe wa, sau tari tana tunanin sa sai taji gabanta ya faɗi kuma tarasa me yasa, sai dai tana ƙoƙarin yakice sa aranta musamman ganin ta dena tuna sa gaba ɗaya, sosai take mamakin haɗuwa da cikan halitta irin Mijin Saleema, sai yanzu tagane abinda Saleeman tahango atare dashi har tamutu a ƙaunar sa haka, domin samun irin sa sai wanda yake da babban daraja wanda kuma yakai
Zuwan da tayi gidan duk sun haɗu amma gaisuwa kaɗai ke haɗa su, shima daga nan ko kallo baya sake yin mata har kuwa tatafi
Don shima a nashi fannin sosai yake son cire ta aran sa musamman yanzu da yasan matsayin ta a wurin shi, yana auren ƴar uwan ta, ko kaɗai baya son abunda zai kawo saɓani a tsakanin zaman sa da matar sa tunda yana jindaɗin zama da ita ainun
Amma abinda akace zuciya na so babu me iya raba ta da shi, bare shi da ya jima a ƙaunarta tun lokacin da be san ita ɗin wacece ba, a kuma kallo ɗaya da yayi mata, sau da dama yana mamakin irin Wannan soyayyan, har zama yake yi yayi ta tambayan kansa "wai dama ana soyayya irin haka daga kallon farko da akayi wa mutum koda kuwa baka san ko shi waye ba? Koda kuwa bakasan zaku sake haɗuwa ba?" A yanda take zuwa masa a mafarkin sa ne yake basa mamaki, kullum idan har be yi mafarkin ta ba to zai yi tunanin ta, idan har zata zo mishi kuma a mafarkin tana me kuka ne tana neman taimakon sa, ya kasa gane irin wannan mafarkin musamman yanzu da yaganta cikin gatan ta.
*______________________*
A fannin Nazeefa ma tana nan tana ta fama da son maso wani, ta ari damuwa duk ta yafa ma kanta, yanzu abun har yakai ko karatun ta bata maida hankali a kanshi
Mom tayi mitan sauyawan ta har ta gaji amma taƙi faɗa mata abinda yake damun ta
Wannan halin da take ciki kullum idan taje makaranta bata kula kowa ko ajin ma sai taga daman shiga, da zaran taje zata wuce bayan makarantan inda ɗalibai ƴan Pramary suke wasa taɓoye anan tazauna tayi ta tunanin ta
Ƙawarta Haneefa ita take damun ta kullum tafaɗa mata damuwarta, ta kai ta kawo ma har faɗa sukayi akan ƙin faɗa mata da tayi, daga ƙarshe dai Haneefa da taga fushin bazai kai ta ko ina ba sai tadawo tana rarrashin ta don tasanar mata damuwarta, daƙyar dai Nazeefa tabuɗe baki aranan tasanar mata tana yi tana kuka kamar ana yankan naman jikin ta, har wani rawa jikin nata yake yi sabida tsaban yau komi ya kai mata maƙura
Haneefa na zaune gefen ta tana bin ta da idanu cike da tsananin mamakin ta, bata hana ta yin kukan ba har sanda tayi ma'ishi tafitar da duk ƙuncin dake cikin ranta, sannan ne tadafa kafaɗan ta da hannu ɗaya tace
"Ban taɓa tunanin akan ɗa namiji bane kika shiga duk wannan damuwar Nazeefa, sabida ɗa namiji kika dena shiga aji kika dena mayar da hankalin ki kan karatun ki duk a sabida ɗa namiji? nayi mamaki wlh ƙawata duk kyawun ki kizauna kina ma ɗa namiji kuka".
Shiru Haneefa tayi tana jan numfashi tare da tsare Nazeefan da idanu
Ita kuma Nazeefa alokacin ne taɗago kanta tana kallon ta da rinannun idanuwan ta tace "baza ki gane a halin da nake ciki bane Haneefa, zuciyata tariga da ta mutu a ƙaunar sa, nayi duk iya abinda zanyi don in cire sa araina amma na kasa, wlh ji nake yi kamar in mutu saboda yanda nake ji a kansa, bana jin zan iya auren wanin sa idan bashi ba, bazan taɓa zama da kowa ba sai shi, tun bansan meye so ba zuciya ta takamu da mahaukacin ƙaunar sa har sanda nagane, gashi yanzu yayi min ratan da samun sa babban wani aiki ne agare Ni".
Dariya ma abun yaba ma Haneefa, sai tasaki baki tana yi
Hararan ta kawai Nazeefa tayi tana ɗauke kai cike da haushi
Tsai da dariyan Haneefa tayi tace "ƙawata kenan kin faɗa da yawa, Ni kuwa zan so ganin wannan Jarumin me babban matsayi a wurin ki, amma fa idan har kina son samun sa to ba wani babban aiki bane a wurin ki ƙawata sai dai idan kece baza ki bi hanyan da yadace ba, Allah na tuba don yana da mata sai kice yayi miki nisa?"
Kallon ta kawai Nazeefa take yi kamar idanun ta zasu faɗo ƙasa har sanda tadire aya kafin taɗaura da nata
"Wace hanya ce tadace da zanbi don samun sa? Kina ganin har akwai sauran hanyan da zanbi Ya Khalil yakalle Ni a matsayin Masoyiya?"
"Ƙwarai kuwa, me zai hana ki faɗa ma Mahaifiyarsa tunda ita tabuƙaci haka, na tabbata wlh zata share miki hawayen ki tunda tana ƙaunar ki".
Shiru kawai Nazeefa tayi don tasan baza ta taɓa iya faɗa mata ba, to taya shi Khalil ɗin zai kalli maganar? Abinda take tunawa kenan, ba wai faɗan bane.. matsalan ta na ga Uban gayyar".
Maganar Haneefan ne takatse mata tunanin ta, taɗago tana kallon ta cike da wani irin kallo me wuyan fassara, bakin ta har rawa yake yi wajen cewa
"Baki da hankali ne wannan wani irin shawaran banza ce? No bazan taɓa iya aikata hakan ba, idan kuwa nayi masa haka tabbas na zama butulu, tabbas idan na aikata hakan mutane zasu zage Ni sannan zasu la'ance ni tunda ban riƙe maraicina ba.."
Sai kuma tagirgiza kanta cikin kuka tace "bazan taɓa iya aikata masa haka ba, wlh gwara in mutu da in je wajen boka in cutar da wanda yataimaka min".
Haneefa cikin son nuna mata abunda take nufi tace "ƙawata ki gane mana hakan shine kaɗai mafita kuma hanyan da zaki samu zuciyar sa..."
Ɗaga mata hannu Nazeefa tayi tace "ya isa bana son ji, Kar ki sake min irin wannan maganan".
Tana faɗan haka tamiƙe tawuce tabar Haneefa nan zaune baki sake tana bin bayan ta da kallo.
Tun daga ranan kuma sai Nazeefa tadena sake ma Haneefa fuska, ko tazo school ɗin babu ruwan ta da ita, ita a ganin ta Haneefa ba ƙawar kirki bace da har zata bata wannan shawaran, duka-duka ma nawa suke da har zata bata shawaran zuwa wajen Boka?
Ita ma dai Haneefan tasha jinin jikin ta, tun daga ranan itama taja baya da ita, idan ba gaisuwa ba babu abinda ke haɗa su, a ganin ta taimakon Nazeefa zata yi, amma tunda ta nuna bata so to itama ta bar maganan, duk ranan da komi yarincaɓe mata tazo taneme ta ita kuma anan ne zata taimaka mata.
.
*Facebook: Muh'd Lawal Nafisat*
*Wattpad: UmmuDahirah*
*WhatsApp number:07065334256*
_plz karku manta da share, Vote, Comments. Nagode._
[11/22/2020, 1:20 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Five*
________🎓Rayuwan Khalil da Saleema rayuwa ce da suke yin ta cikin jindaɗin juna da nuna ƙauna da kulawa, zuwa yanzu komi yana tafiyan musu dai-dai
Gefe ɗaya kuma ciwon Saleema na zuwa mata jefi-jefi, duk da tana shan magani amma wataran haka zata tashi da tsananin ciwo har asibiti Khalil yake kai ta, sai kuma daga baya ciwon nata yalafa
Yanzun ma kwana biyu kenan bata jindaɗi sai dai ba sosai ba tana yin duk aiyukan ta tare da taimakon Khalil, idan yana gida shi yake taimaka mata da rainon Husna, girki kuma hanata yayi sai dai yayi musu Take-away, idan tatashi kuma da ƙwarin jiki sai tayi musu girkin
........ ........ ....... ........
Yau tun safe da Khalil yatafi aiki bayan ta gama gyaran gidan tayi ma Husna wanka itama tayi, sun shirya cikin farar atamfa me zanen ja da ruwan goro, ɗinkin riga da skert akayi mata sai akayi ma Husna doguwar riga dai-dai ita, duk kwalliyan da akayi iri ɗaya akai musu a rigan
Fitowa Parlour tayi da Husna a hannun ta ta'ajiye ta saman carpet, ita kuma tahaye kan 3sitter takwanta, yau sosai jikin ta yamatsa mata ga sanyi da take ji sosai duk da kuwa ta kashe AC da Fan ɗin parlour'n
A hankali ciwon yaci gaba da cin ta, hakan yasa tamiƙe takoma ɗaki tahaye kan gado taƙudundune da bargo, nan da nan tasoma rawan ɗari.
Wajen awanni biyu da shigan ta Khalil yadawo gidan, da sallama yashigo cikin parlour'n, da Husna yasoma cin karo tayi wasan ta har ta gaji tasoma ƙananun kukan ta daga ƙarshe barci yaɗauke ta a dungure a wajen ta kofa kanta kamar wacce take sujjada
Dasauri yaƙariso yana ajiye briafcase ɗin sa yasaka zara-zaran hannayen sa yaɗauke ta, sannan ne yaga ashe barci take yi, murmushi yayi yana kallon fuskarta da tataɓe baki duk hawaye ya gama bushe mata a fuskar
Gaban sa ne yafaɗi sakamakon ganin yanda kamannin ta da Halwa yasake fitowa ainun, basu da maraba a yanzu ɗin
Shiru yayi yana ƙure ta da kyawawan idanun sa, ya ɗau tsawon mintuna 3 kafin yamiƙe yanufi ɗakin Saleema da ita a hannun sa, yana shiga yahangi Saleeman kan gado nannaɗe cikin bargo
Dasauri yanufi bakin gadon dan yasan babu lafiya, ajiye Husna yayi can ƙarshen gadon kafin yamatso kusa da Saleeman yana zama ya yaye bargon yana kiran sunan ta
Zafin da yabuge sa ne yayi saurin sake yaye bargon yana tallabo kanta, nan yaga fuskarta sharkaf da hawaye idanun ta kuma sun kaɗa sunyi jawur gunun tausayi, gaba ɗaya jikin ta rawa yake yi ga shegen zafi kamar tafashashshen ruwa, shi kanshi dauriya yayi wajen riƙe ta
Cikin tsananin firgici yace "subhanallah.. Saleema meke damun ki? Tun yaushe kika fara ciwon?"
Bakin ta rawa yake yi ta ma kasa magana in banda hawaye da ke zuba kan kuncin ta yana gangara ta gefe yasauka hannun sa
Dasauri yakwantar da ita yana miƙe wa cikin sauri, wayan sa yaɗauka yakira doctorn ta, sai dai baya shiga hakan yasaka ya'ajiye wayan yafita da sauri
Sai kuma yasake dawowa yaɗauki Husna yakaima drever akan yakaita gida sannan yadawo yatallabi Saleema yasaka mata Hijab suka fito
A back seat yakwantar da ita yashiga yaja motan yafice cikin gidan da mugun gudu.
*___________________________*
Drever na zuwa gidan su Saleema Gateman yamiƙa ma Husna sannan yatafi
Nocking gate man yayi a bakin Parlour
Halwa na tsaye gaban Fridge tana shan ruwa, dawowar ta kenan dama daga makaranta tasoma nufan Fridge ɗin, ajiye ruwan tayi tanufi ƙofan tabuɗe, kallon Gate man tayi tare da Husna dake hannun sa
"Dama drever ne yakawo ta inji Mijin Hajiya Saleema". Cewar Gate man ɗin yana kallon Halwa
Mamaki ne Yakamata amma sai batace komi ba ta'amshe ta tarufe ƙofan takoma cikin parlour'n, ajiye ta anan ƙasan carpet tayi tanufi kan kujera inda jakar ta yake tazaro wayan ta tasoma kiran numban Saleema, sosai hankalin ta yaba ta babu lafiya ne don tasan babu ta yanda za'a yi Saleema tayarda adawo da Husna, ƙirjin ta sai fat fat fat yake yi gashi Ummi tana Hospital kuma tace mata zata biya anguwa, so dawowarta ma ba yanzu ba
Ringing wayan take yi but not answer, zuwa lokacin Halwa ta kasa zama sai Safa da marwa take yi tana sake danƙara mata kira, tsaki taja tana ɗaukan jakan ta tanufi ɗakin Saleema wanda yazama nata a yanzu
Ta dawo makarantan yau agajiye Allah-Allah take yi tadawo tayi wanka ko zata rage gajiyan, ga mugun yunwa dake addabar ta, amma a yanzu bata jin zata iya cin wani abu idan har batasan halin da take ciki ba, kayanta tacire tashiga wanka.
Larai ce tafito daga ɗakin ta tahangi Husna tana kuka, dasauri taƙarisa wajen ta taɗauke ta tasoma jijjiga ta tana tambayan ta "ina Mamarta? Wa yakawo ta?" Sai kace tana jin ta
Ɗakin Halwan tanufa tunda a tunanin ta Saleeman ce tazo gidan, amma koda tashiga babu kowa sai ƙarar ruwa da taji, hakan yasa tafita takoma ɗakin ta da Husnan.
*________________________________*
Lokacin da Khalil yakai Saleema asibiti Ummi tabar asibitin
Emargancy ward aka nufa da ita, hankalin Khalil duk ya tashi haka yake ta Safa da marwa, gashi be zo da wayan sa ba bare yakira gidan su yasanar musu
Wajen 1hour aka ɗauka ana duba ta kafin likitan yafito yabuƙaci ganin Khalil, kan dai matsalan ciwon ta ne sai kuma shigan ciki na sati Uku, gashi kuma sun gano da matsala sosai a mahaifar ta zai yi wuya ta'iya ɗaukan ciki har yagirma a jikin ta, sai dai sun ɗaura ta akan magani don aga yanda hali zai yi
Hankalin Khalil sosai yasake tashi da jin bayanin doctor, sai dai komi ya fawwala ma Allah hakan shine cikan imani
Motar sa yashiga yanufo gida tunda dama a kulawan likitoci take, yanke shawara yayi yasoma wucewa gidan su Saleeman yafaɗa ma iyayen ta don haka yakarya kan mota yanufi gidan.
_...... ........ ....... ....... ......_
Fitowar Halwa a wanka doguwar riga kawai tazira taɗaura ɗankwalin rigan tafito parlour
Tana zama Larai tafito cikin ɗakin ta goye da Husna abaya zataje kichen
"Au Ashe kin fito? Na shigo ɗakin ai duba ko Saleema ce tazo amma bangan ta ba".
Halwa kallon ta tayi da yanayin damuwa a face ɗin ta tace "eh na fito amma ba Saleeman bace tazo drever ne yakawo ta".
"Allah yasa dai lafiya ko?" Larai tafaɗa itama a yanayin wasi-wasi
Domin sun san babu yanda za'a yi akawo ta gidan idan har ba Saleeman bace tazo
"Wlh nima bansani ba, na kira dai wayan ta amma shiru ba'a ɗaga ba hankalina duk ya tashi, nayi tunanin kiran Ummi kuma kar yazo fahimtar mu ce hakan".
Larai tace "eh gwara kam kar ki kirata saboda bamu da tabbacin ko matsala ne, amma dai kici gaba da gwada kiran wataƙil adace".
Gyaɗa kanta kawai Halwa tayi taci gaba da kiran wayan kamar yanda Larai ɗin tace
Ita kuma Larai kichen tanufa don ɗaura girkin dare
Tashi Halwa tayi tanufi kan dainning tazauna, sosai take jin yunwa kamar hanjin ta zai tsinke, yau bata ci komi a school ba haka taje tadawo
Zama tayi tazuba abincin da yakasance Macoroni ne me manja, tana cin abincin tana sake kiran layin Saleema, ko kaɗan ta gaza haƙura, zuwa yanzu hankalin ta yayi ƙololuwar tashi, tabbas tasan akwai matsala
Abincin ma sai yakoma baya mata daɗi, turewa tayi dai-dai da lokacin da taji ana buɗe Gate ɗin gidan
Dasauri tamiƙe tanufi hanyan fita don tasan bazai wuce Ummi bane ko Abba, hankalin ta ne ya gaza kwanciya shiyasa tanufi wajen don tarban su duk da kuwa bata san me zatace musu ba
Tana fita tahangi motan da bana gidan ba, bata san cewa Khalil bane aciki tunda bata ganin shi, kuma ba wai tasan motan gidan shi bane bata tsayawa kallo bare ta tantance, tasan dai yana da motoci aƙalla sun kai biyar agidan
Shi kuwa tun sanda tafito idanun sa yasauka akan ta, har yayi parcking yafito yarufe motan
Zuciyar ta ne tabuga sakamakon ganin sa, duk da dama idan har zata ganshi hakan ke faruwa da ita amma kuma da fargaban ko wani abu ne yasamu Saleema, tana nan tsaye tana kallon sa yayinda zuciyarta ke ci gaba da dukan uku-uku, gaba ɗaya ta dunƙule hannun ta waje ɗaya saboda rawan da suke yi, daƙyar ta'aro jarumta da ya'iso wajen tagaishe sa
Amsa mata yayi yana ci gaba da kallon ta kamar zai cinye ta, tsananin ƙaunar ta ne ke ɗawainiya dashi, ya jima rabon da yaganta sai yaji wani sanyi aransa tare da wucewar wani abu da yatsaya masa a maƙoshi kwana da kwanaki
Matsa masa a hanya tayi batace komi ba
Shi kuma sai yashiga kafin tabiyo bayan sa
A kan ɗaya daga cikin kujerun yasamu wuri yazauna
Ita kuma taje taɗauko masa ruwa duk da kuwa batasan ko yana buƙata ba
Ajiyewa tayi a gaban sa saman Centre table tajuya da ninyan wuce wa duk da kuwa tana son tambayar sa Saleema, gashi kuma yanda idanun sa yake faman yawo ajikin ta yayi bala'in takura ta
Har ta soma tafiya taji sassanyan muryan sa yayi mata magana
"Ina Ummi?"
Juyowa tayi sai dai wannan karon baza ta iya kallon sa ba tasad da kanta ƙasa tace "bata dawo ba".
Shiru yayi kamar bazai yi magana ba
Ita kuma hankalin ta yagaza kwanciya, bata san sanda tajeho masa tambayan
"Meke damun ƴar uwata?" Tayi maganar idanun ta na kansa
Kai tsaye Khalil yasanar mata inda take
Hankalin Halwa atashe kamar zatayi kuka tace "don Allah zan bika mu tafi".
Gyaɗa mata kai kawai yayi yamiƙe yanufi hanyan fita
Dasauri taɗau wayan ta tacire ɗankwalin ta tayafa tabi bayan sa, lokacin har ya shige motan ya tayar yana jiran ta
Cikin sassarfa taƙarisa tabuɗe gaban tashiga yaja motan yafice bayan da me gadi yabuɗe masa Gate ɗin
Duk da Khalil yana son zuwa gida amma bazai ƙi biya mata buƙatar ta ba, wannan dalilin ne yasaka yayi tunanin kai ta kafin yakoma gidan
Koda yakaita be daɗe ba yace mata zai tafi
Bata tanka shi ba har yafice, sannan ne tasoma kiran layin Ummi, bugu biyu taɗauka anan Halwa tasoma sanar mata Saleema ce babu lafiya tana Hospital
Hankalin Ummi ya tashi nan da nan takaryo motan ta don har takusa isa gida, tana zuwa tatarar da Saleeman barci take yi Halwa ta tasa ta gaba sai kallon ta take yi
Fita tayi tanufi Office ɗin Doctor ɗin ta, anan take jin bayanin matsalan Saleeman, idan hankalin Ummi yayi dubu to ya gama tashi, sosai taruɗe da jin abinda ke faruwa
Koda tafito lungu tasamu tafashe da kuka na tsananin tausayin ƴar nata, babu abinda bakin ta ke furtawa sai salati, tabbas Saleema tana cikin jarabawa
Da fari ciwon zuciya sannan kuma ciwon hanta, yanzu kuma ga ciwo a mahaifar ta wanda ke barazanar da zata rasa haihuwa har abada
Tasha kuka sosai kafin tashare hawaye tagyara fuskarta, sannan taciro wayan ta a jaka takira Abba tasanar masa
Shima babu jimawa yataho
Gaba ɗaya sun yi zugun a ɗakin sun saka ta gaba sai kallon ta suke yi
Sai gab da magriba tafarka lokacin shima Khalil ya dawo, sosai take jin jiki don ko magana bata yi
A lokacin ne Abba ya lallaɓa Ummi suka tafi gida da Halwa tunda an sake mata alluran barci ta koma
Babu jimawa itama Mom tazo tare da Nazeefa, sun jima har wajen ƙarfe 11:00pm kafin suka tafi
Khalil shi yace zai kwana da ita don haka babu musu Abba yataho yabarta.
[11/24/2020, 2:36 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Six*
________🎓 Wasa-wasa sai da Saleema tayi kwana biyar cur kafin tasoma samun sauƙi, sai kuma daga baya ciwo yazo mata rigigim, blending take tayi nan likitoci suka rufu akan ta
Halwa kuka Ummi kuka sun rigada sun cire rai ma Saleema zata iya rayuwa
Khalil shi kansa ya rasa inda zai saka kansa, tsananin tausayin matar sa gaba ɗaya ya cika sa, sosai yadamu da halin da take ciki
A ranan duk wani me tausayi dole yatausaya mata, ashe wai duk ɓari zatayi shine yaja mata hakan, sai da aka ƙara mata jini leda biyu sabida yanda tazubar da jinin ta wajen ɓari
Kwanan ta biyu kafin tafarfaɗo, sosai Saleema tayi jinya gaba ɗaya ta rame tayi baƙi sabida jinin da ake ƙara mata, kullum zuwa gaishe ta ake yi
Ita Halwa ma gaba ɗaya dena zuwa school tayi sai da tasoma samun sauƙi sannan ne Ummi tatakura mata tafara zuwa
Idan kuma tadawo nan take fara wuto wa sai dare takoma gida
Haka shima Khalil yake yi, duk da aiki yayi masa yawa amma kullum yana kan zuwa
Satin ta ɗaya aka sallame ta duk da ba wani warkewa tayi ba amma haka takoma gida tana jinya, Khalil shi ke kula da ita ko kaɗan baya gajiya, tausayin ta tsantsa ne a ransa
Haka rayuwa taci gaba da shuɗewa gashi yanzu har an shafe watanni uku da ciwon da Saleema tayi, yanzu komi ya koma normal sai dai ciwon da ba'a rasa ba wanda take fama dashi koda yaushe.
*________________________________*
Ƙarfe 03:20pm. Su Zainab da friends ɗin ta suka fito lectures
Tafiya suke yi suna hira ɗaya daga cikin su tana basu labarin gwaraman da akayi a anguwan su, sai dariya suke yi sabida yanda me basu labarin ta dage tana nuna yanda matar take ɗaukan mijin ta tana tiƙa sa da ƙasa
Daga bayan su can ɗan nesa kaɗan Halwa ce ke tafiya tana latsa wayan ta, tun daga inda take tana jiyo dariyan su sai dai hankalin ta baya kansu sai faman neman layin Drever take yi
Yau yayi late be zo ya ɗauke ta ba shiyasa take sake kiran sa taji inda yake, yana ɗagawa yace mata "gashi nan yanzu zai shigo school ɗin"
Tsayawa tayi a wajen har sanda tahango shi ya shigo cikin makarantan, sai tanufi wajen shi tana ɗaga masa hannu, shima ɗin ya ganta don haka yatsaya tahau yaja yayi reverse suka nufi bakin Gate
Lokacin su Zainab har sun kusa fita motan tazo tawuce su, har alokacin sai faman dariya suke yi, ahaka suka fita cikin school ɗin cike da nishaɗi
Suna fita sauran friends ɗin ta duk suka dare biyu daga ciki sukai musu sallama suka ci gaba da tafiya sabida babu nisa da gidajen su, ɗaya ce tahau keke napep tatafi aka bar Zainab ita kaɗai tunda ba hanya ɗaya zasu bi ba
Tana nan tsaye wajen sai ga wata dalleliyan mota ta faka a gaban ta, tunda takalli motan sau ɗaya takau da kanta tana kicin-kicin da fuska
Fitowa yayi daga cikin motan yana kallon fuskarta, ɗan taku uku yayi ya'iso gaban ta, murmushi yasaki yace
"Plz Zainab don Allah kihau in Kai ki gida, yau rana ɗaya dai kiyi min wannan alfarman".
Tsaki Zainab taja batare da ta kalle sa ba, ji take yi idan har tatanka masa zuciyarta zata iya bugawa sabida tsaban jin haushin sa, don haka batace komi ba tajuya taci gaba da tafiyan ta
Nura kallon ta kawai yake yi har sanda taɗan yi nisa sannan yanufi motan sa yashiga yabi bayan ta
Kullum ranan duniya sai yazo domin ta amma bata taɓa masa kallon arziƙi ba, kuma shi be taɓa gajiya ba sabida yanda yake jin ta cikin ransa, duk wulaƙancin da zata yi mishi zai iya jurewa idan har zai same ta, yana matuƙar ƙaunar ta fiye da tunanin mutum
Yana biye da ita abaya har sukai nisa, gashi ta kasa samun keke napep duk rana sai faman gasa ta yake yi
Shi kuwa gab da ita yazo suka jera yana mata magiya ta cikin motan amma firr Zainab taƙi kallon sa bare tatanka masa
Gajiya tayi kawai tasamu acaɓa tahaye tunda babu napep ɗin
Nura yana kallon ta har tahau suka tafi yabi bayan su, duk inda me machine ɗin yabi nan shima yake bi har suka kawo ƙofar gidan su Zainab ɗin tasauka tamiƙa ma me machine ɗin kuɗin sa tajuya tashige gida batare da ta amshi canjin ta ba, don baƙin cikin ganin Nura ƙofar gidan su ya hana ta ma tsayawa
Ajiyan zuciya Nura yasauke yana bin ƙofar gidan da kallo, ya jima acikin motan.. shi be tafi ba shi kuma be fito ba, sai da yashafe mintuna 20 zaune anan kafin yafito yana rufe motan
Kalle-kalle yai tayi sai daga baya yahangi yaro yakira sa yace masa yashiga ciki yakira masa Zainab
Da gudu yaron yashige gidan
...... ....... ....... .....
Zainab tun shigan ta da tayi sallama taji babu umma sai tashiga ɗaki kawai ta'ajiye jakar ta tare da gyalen ta tafito tashiga kichen taɗauko abincin ta
Zama tayi anan farandan ɗakin su taci abincin tagama, miƙe wa tayi takai coolarn wajen wanke-wanke taɗibi ruwa a buta tashiga Toilet.
Tana cikin Toilet ɗin tajiyo sallaman yaro, bata amsa ba har sanda tafito tabi yaron da kallo, bata raba ɗayan biyu Nura ne ya'aiko shi
Ai kuwa bata gama tunanin zucin ta ba yaron yace
"Wai ana kiran Zainab a waje".
Ajiye Butan hannun ta tayi tazauna kan dutse a bakin Toilet ɗin, sannan takalli yaron tace
"Je kace masa baza ta zo ba".
Babu musu kuwa yaron yajuya yatafi don isar da saƙon ta
Sosai baƙin ciki ke ɗawainiya da Zainab, ta rasa wani irin maye ne wannan mutumin, ko kaɗan ita bata ƙaunar sa a ranta bata jin kuma zata iya son sa ko anan gaba, sa'ar ta ɗaya Umma bata nan amma da dole sai ta saka ta fita
Shiyasa take roƙon Allah aranta Allah yasa yatafi kafin Umma tadawo
Ta soma alwala kenan yaron yasake dawowa yace
"Wai yace don Allah tazo zai bata saƙo ne".
"Dan ubanka wuce anan gidan". Zainab tafaɗa cikin tsawa tana zazzare ma yaron idanu
Da gudu kuwa yasheƙa yafice har da waigen ta
Baƙin ciki da ƙunci ne suka taru mata iya wuya, ta rasa me za tayi ma Nura don huce takaici
Ƙyalla idon ta tayi tahangi taɓarya, dasauri tatashi tanufi wajen taɓaryan taɗauka tayi hanyan fita a fusace
Yau dole ne sai ta kawo ƙarshen zuwa wajen ta da yake yi.
.
_hahaha Fans kar ku damu ba daku zata rotsa ma kai ba, Nura kawai tanufa banda ku._
_Kuyi haƙuri da wannan babu yawa, aiyuka sun yi min yawa shiyasa nayi muku ɗan kaɗan._
_kar ku manta da Comments ɗin ku shi ke ƙara min ƙwarin gwiwa._
_Ina jiran Comments ɗin ku shin ayi maganin Nura ko ya? Nasan da yawa haushin sa kuke ji bayan kuma be muku komi ba bawan Allah._😅
[11/24/2020, 2:50 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Seven*
________🎓Tana shiga zaure sukaci karo da Umma dole taja tatsaya tana ƙifƙifta ido
Umma da tafiddo ido waje tana kallon Zainab ɗin da taɓaryan dake hannun ta tace "na shiga uku ni Jummai me zan gani haka Zainab? Ashe dama baki da mutunci dan ubanki? Yanzu abun naki har ya kai kifita da taɓarya kije wajen Nura? To me kike shirin aikatawa kenan?"
Turo baki Zainab tayi tana sosa kai, sai kuma tajuya dasauri tayi ciki tana jefar da taɓaryan
"To dan ƙwal uwar ki zo ki wuce kije wajen shi". Cewar Umma tana bin bayan ta itama tashiga cikin gidan
"Wlh Umma babu inda zani, nifa nace miki bana ƙaunar sa bana son sa bana son sa, Ni bazan iya son sa ba wlh".
Umma kama haɓa tayi tana kallon Zainab ɗin dake masifa kamar batasan da wa take yi ba
"Zainab Ni Sa'an wasan ki ne ina faɗa kina faɗa? Wlh sai kin fita ko in saɓa miki kamanni, shashashan yarinya mara hankali.."
Kuka Zainab tafashe dashi
Sai umma kawai takama haɓa tana kallon ta
Cikin kukan take cewa "wlh Umma bana ƙaunar sa, koda kuwa be so Halwa ba Ni bana son sa, har cikin raina nake faɗa miki bazan iya auren sa ba wlh".
Sai taja majina tanufi wajen butan ta tazuƙuna tasoma alwala
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yanzu Zainab har kin isa in saka ki abu kice baza kiyi ba? Baza ki tashi ki wuce ba yana jiran ki?"
Cikin tsananin ɓacin rai Zainab tace "Umma zan yi sallah ne lokaci na ƙurewa, kuma kinsan illan rashin yin sallan Asar da wuri, yana ɗaya daga cikin sallolin da ake so mutum yakula..."
"Dalla rufe min baki, kiyi sauri ki idar kizo ki wuce".
Zainab bata sake cewa komi ba taci gaba da alwalan ta, sosai take mamakin Mahaifiyar ta akan yanda tasauya lokaci ɗaya akan Nura, duk da tasan Nura yana banka mata kuɗi da kaya amma kuma bata taɓa tunanin zata sauya har haka ba
Tana idar wa tashiga ɗaki tasaka Hijab tasoma sallah, ta ɗau lokaci tana yin Sallah taƙi tasallame sai da Umma tazo tasake mata magana sai faman masifa take mata
Dole Zainab ba don taso ba tamiƙe tafito tafice
Tana fita kuwa taganshi tsaye gaban motar sa, ta rasa wani irin mayen mutum ne wannan
Nura tunda tafito kallon ta kawai yake yi yana murmushi, ko kaɗan be ji haushin daɗewan da yayi a wajen ba tunda Umma tace mishi yajira zata fito, kuma yasan dole zata fito ɗin
Wani mugun kallo Zainab tabuga masa tana jan tsaki taɗau hanya taci gaba da tafiyan ta batare da taƙarisa inda yake ba
Yana kallon ta har taƙule ma ganin shi
Ita kuwa tana shan kwana tasheƙa aguje bata tsaya ko ina ba sai gidan Yayarta Zaituna
Suna zaune ita da kishiyarta suna ƙullin Gishiri sai ganin ta sukayi ta faɗo gidan
"Subhanallah..lafiya Zainab?" Atare suka tambaye ta yayinda Zaituna taƙara da faɗin
"Wa yabiyo ki ne kika shigo haka kamar an jeho ki?"
Zainab da tariƙe gwiwowin ta tayi ruku'u tana numfarfashi ta ma kasa magana
Kishiyar me suna Murjana tace "ikon Allah wai lafiya ko dai gudun fanfalaƙi kika yi ne?"
Bata ce komi ba tanufi wajen randan ruwan su tana sake jan numfashi, ɗiban ruwan tayi tasha kafin tadawo taja kujera ɗan tsuƙuno tazauna agaban su, duk sun tsare ta da idanu suna ganin ikon Allah kuma suna jiran suji abinda yakoro ta gidan da gudu
Sai da taƙara gyara zaman ta tana kallon su tace "wlh daga gida nake.."
Tsaki Zaituna taja tana hararan ta tace "amma kinji kunya wlh, ƙatuwa dake shine kika sheƙo hanya da gudu ga mutane ko kunya ko?"
"To Aunty ki tsaya mana kiji me yakoro Ni, wlh Umma ce tatakura min akan maganar Nuran nan shiyasa na'ari na kare nayo nan".
Dariya Murjana tayi tace "kai wlh Zainab baki da dama, to Ni wai meye laifin Nuran nan kullum kina wahalar dashi? Magana dai taƙi ci taƙi cinye wa".
Taɓe baki Zaituna tayi tace "kema dai kya faɗa, bata da hankali Zainab ko kaɗan, wai inace duk kina wannan abun ne don Halwa?"
"Aunty baza ki gane ba wlh, nifa gaba ɗaya tun sanda yasoma nema na natsane shi, wlh koda ba batun Halwa aciki Ni bazan iya auren sa ba, kullum idan yazo min da nacin nan nasa kullum sake jin tsanar sa nake yi araina". Zainab tayi maganar cike da baƙin ciki
"Aiki ya ganki". Zaituna tafaɗa tana ci gaba da ƙullin ta
Murjana tace "kiyi ma kanki faɗa don Allah, ko wace mace tana burin tasamu masoyi me ƙaunarta amma ke kin samu kina wasa da damar ki, wlh Nura yana son ki tunda kikaga yana jure wulaƙancin nan naki, Zainab babu batun yaudara anan ki karɓe shi hannu bibbiyu tun kafin lokaci yaƙure miki, dama ce tazo miki har gida, idan kuma kikace zaki tsaya tunanin wata to zaki rasa wannan damar taki, ki duba magana ta".
Numfashi Zainab taja, baza su taɓa gane abinda take nufi ba, ita tayi alƙawarin wlh sai dai gawan ta za'a kai gidan Nura amma baza ta taɓa auren sa ba, koda kuwa Halwa ce tazo da kanta tace ta'aure shi, amma a yanzu tarigada ta ƙudurta ma kanta dole ne tasamu saurayi tayi aure ko Allah zai sa yabarta, ada dai bata da burin aure yanzu amma tunda taga abun yazo da haka tasan komi zai iya faruwa
Yanzu ma baza ta koma gidan ba sai dare, sai dai idan ta koma Umma tahaɗiye ta
Hannu tasaka tasoma tayasu ƙulla gishirin batare da tasake cewa komi ba
Su kuma tuni sun sauya zancen ma sun ci gaba da hiran su da suke yi.
.
*__________________________*
*BAYAN WASU WATANNI*
A halin yanzu Saleema tasake samun ciki a karo na biyu, kamar dai wancan haka tasha baƙar wahala watan shi ɗaya yafice bayan da tazubar da jini sosai kamar baza ta rayu ba
A wannan lokacin ne kuma tasan matsalan ta, tayi kuka kamar baza ta dena ba, har sai da iyayen nata sukai dana sanin faɗa mata sabida gudun tashin ciwon zuciyarta
Ita kanta Halwa ta taya ta kukan kuma ta tausaya mata sosai
Sai da tayi jinya na tsawon sati biyu a asibiti kafin a sallame ta
Tun daga ranan kuma Khalil yasoma bata maganin hana ɗaukan ciki batare da sanin ta ba, ita a ganin ta duk cikin drugs ɗin da aka bata ne a asibiti tunda wani lokacin shi ke bata magungunan, kuma bata taɓa saka wa aranta zai iya cutar da ita ba bare tayi tunanin wani abu, sosai yake matuƙar tausaya mata baya son tasake shan wahala kamar yanda tasha a baya, duk da yana son yara amma hakan shine mafitan da zai iya taimaka mata idan har yana tausayin ta
A sannu a sannu rayuwa taci gaba da tafiya, tun Saleema na damuwa da matsalan da take fama dashi tunda itama tana ƙaunar yara har dai tacire komi a ran ta, ta buƙaci a dawo mata da Husna taci gaba da riƙe ta amma firr Ummi taƙi tunda har yanzu jiya iyau take, yau lafiya gobe ciwo, kuma Ummi tayi tayi takawo mata ƴar aiki but Saleema ta baɗe ma idanun ta toka akan baza'a kawo mata ƴar aiki ba, ita ta saka a ranta duk ƴar aiki tana ƙwace Mijin matar gida ne, shiyasa take jin tsoron a kawo mata ƴar aiki watarana taƙwace mata miji, anan Ummi tace "to tunda baza ta yarda akawo mata me taimaka mata ba dole tahaƙura da rainon Husna har sai taji sauƙi", ba da son ranta ba haka tahaƙura
Khalil na iya ƙoƙarin sa wajen ganin ya taimaka mata ainun, a haka zaman su yaci gaba har zuwa wani lokaci, kuma har a lokacin soyayyar Halwa na nan cikin zuciyar sa sai dai ya binne abun aransa tunda babu yanda zai yi
Ita kanta Halwan abun da take ji akan sa ne har yanzu takasa sakin jiki dashi bare su saba, ko magana zata iya ƙirga iya adadin da yataɓa shiga tsakanin su, sau tari idan tayi tunanin komawa gidan Saleema don ta tayata zama sai ta fasa, bata son ko kaɗan abinda zai sa su haɗa hanya, duk da har yanzu batasan menene musabbabin abinda yasa take jin haka daga gare shi ba, amma ita a ganin ta nesa dashi shine kwanciyar hankalin ta
Har yanzu kuma bata taɓa tunanin yin saurayi ba duk da kuwa ansha biyo ta, amma a ranan farko take taka ma mutum burki
Ummi kanta sai da tazaunar da ita akan tadena koran samari auren nata shine abunda yadace da ita, amma ita Halwa abinda take hangowa tabon da ɗa namiji yayi mata a rayuwa, ta tabbata ko wanene zai so ta idan har yasan da Husna wacce tahaife ta bata hanyar aure ba to zai tafi yabarta, bata son taba ma namiji yardan ta a karo na biyu, tunda wanda yafi kowa sanin ta a duniya kuma yafi kowa sanin me zata iya aikata wa ya juya mata baya akan hakan, tayi imani ko waye ma hakan zai mata, shiyasa maganin kar ayi kar a fara, ta yarda zata ci gaba da rayuwan ta ahaka har ƙarshen numfashin ta, idan har ba Nura bane yadawo gare ta to bata jin zata iya auruwa
A yanzu haka ta shiga aji na biyu, babu abinda tasaka a gaba sai karatu, ko ƙawaye taƙi yarda tayi har yanzu, sai dai mutunci kawai da take yi da wasu daga cikin ƴan ajin su
Har yanzu har gobe tana tunawa da ƙawarta Zainab, sau tari tana tunanin zuwa koda gidan su ne, amma kuma hakan na nufin kamar ta tona ma kanta asiri ne duk ranan da takoma wajen waɗanda suka santa, kuma hakan na nufin zubar da mutuncin su Baba kamar yanda suka guda tun farko, wannan dalilin yake saka wa tafasa zuwa.
.
*____________________________*
Baku tambaye Ni labarin Haris ba?
Tunda baku tambaya ba nima bari in ƙyale KU, byeeee👋👋👋 sai ajiman ku ko in CE sai gobe.😅🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
_kar ku manta don Allah 🙏🏼ku danna Vote sannan kuyi comments don jin ra'ayoyin ku, na gode._
[11/24/2020, 3:14 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Eight*
________🎓Haris ɗan wani babban attajiri ne ɗan siyasa, yanzu haka yana riƙe da kujeran Minister, shi ɗaya ne ɗa wajen iyayen sa duk da iyayen Familyn su ɗaya ne kuma babban Family ne dasu
Ya taso cikin gata sosai, babu abinda yarasa a rayuwan sa, wannan dalilin ne yasa yake taka duk wanda yaso yakuma hukunta duk wanda yake ƙi, sabida yana da ɗaurin gindin mahaifin sa don ko kaɗan baya ganin laifin sa
Haris yana da son mata da yawa sannan kuma yana da farin jinin ƴan matan, su da kansu ƴan matan suke kawo kansu wajen sa don yayi amfani dasu yabiya su kuɗi, duk da sau da dama suna kawo kukan su akan ya taimaka ya aure su amma shi a ganin sa babu macen da ta'isa yaso ta, shi dai kawai ya san mata a wajen sa su biya masa buƙata ne yajefar dasu don basu da wani Amfani
Ana cikin haka kwatsam yazo giftawa ta hanyar makarantar su Halwa yakusa bige ta, tun a lokacin da yaganta yakamu da tsananin kaunar ta har yana jin koda zai yi aure to babu shakka ita zai aura, duk da alokacin mafi rinjaye na zuciyarsa sha'awar ta ce, amma kuma ita kaɗai ce yake iya mata kallon wacce zata iya kasancewa matar sa anan gaba
Sai dai abinda be sani ba Halwa ta mutu a ƙaunar Nura a lokacin, duk da alokacin yaso yanuna mata kuɗi da gadara, amma da yaga yarinyan tana da taurin kai babu yanda zai yi yasame ta sai yakoma yana bin ta talalama
Sai kuma tsautsayi yagifta a ranan da Halwa tamare shi, wannan dalilin ne yaɗau alwashin sai yayi mata abinda baza ta taɓa mantawa dashi ba, domin kuwa tunda yake babu wanda yataɓa taɓa masa lafiyan jiki
A lokacin babu abinda be sani akanta ba, har soyayyar da suke yi da Nura ya san komi sabida yana da yaran da suke bibiyan masa ita
Abu na farko da yasoma yi shine neman Nura, har gida aka kawo masa Nura kuma yafaɗa masa buƙatarsa, a lokacin Nura be amince ba sai da yaji kuɗi Miliyan uku da yayi masa alkawarin zai basa in dai zai sadaukar masa da budurcin Halwa, shi a ganin sa idan har yakawar da sha'awar Halwa aransa to tabbas duk wani soyayya da yake mata zai gushe, wannan dalilin ne yasaka yanemi aikata mata fyaɗe bayan ya nemi taimako wajen Nura
Shi kuma Nura babu musu ya amince, a ganin sa idan har yasadaukar da budurcin Halwa akan wannan zunzurutun kuɗin be faɗi ba, kuma hakan yana ganin dama ce tazo mishi da zai yi kuɗi batare da yasha wahala ba, sannan yarigada ya saka ma ransa shi zai auri Halwa ɗin yarufa mata asiri tunda SHINE SILA, kuma shine zai ɗau alhakin duk abinda zai same ta don yarage girman laifin sa
Take nan ya amince sannan suka shirya yanda za'a yi har Halwa tazo hannun Haris, kamar yanda kuka gani abaya
Duk wannan abinda yafaru da Halwa da haɗin bakin Nura, sannan kuma lokacin da yaji maganar ciki hankalin sa yayi mugun tashi duk da alokacin yana tunanin bazai iya auren macen da yasan ba ta tare da mutuncin ta ba, anan ne dabara yazo masa har yanuna shi be san da maganar Fyaɗen da akayi mata ba don kawai ya yakice ta ajikin sa
Haris kuma tun sanda yayi mummunan aika-aikan nan yakoma Abuja kasancewar acan yake aiki, yana kula ma mahaifin sa da ƙaramar Companin sa da yabuɗe na Shinkafa, amma me tunda yakoma sai yazamana bashi da sukunin zuciya, ƙaunar Halwa tayi masa bakeke a rai ta hana sa saƙat, be taɓa tunanin sonta ya kai haka ba sai da yayi nisa da ita, ya so yadanne yajure ko zai manta da ita amma hakan ba me yiwuwa bane
Dole yadawo gida don ganin ta ko yaji sanyi a ransa, lokacin watan sa biyu acan kuma a lokacin tuni Halwa tayi wajen two weeks da barin gida
Dawowar sa da jin abinda yafaru wajen Nura hankalin sa yayi ƙololuwar tashi, yayi baƙin cikin koran ta da sukayi da cikin sa ajikin ta, ya sake shiga damuwa matuƙa, haka ya bazama neman ta ko Allah zai sa adace, domin ya rigada ya ɗau alwashin muddin yaganta zai aure ta kuma su raine abunda zata haifa, yana matuƙar son ta bazai iya rabuwa da ita ba, har Gombe can dangin mahaifin ta sai da yaje amma akace bata zo ba, su ma alokacin suka ji abinda yafaru, sai dai basu wani damu ba tunda Mama ta faɗa musu cikin Shege tayi suka koro ta nan ashe bata zo ba, su aganin su hakan ma da tayi yadace tunda ko tazo su ma ɗin korata zasu yi don baza su iya riƙe ta da abun kunya ba
Rayuwa ta sauya ma Haris matuƙa ya shiga damuwa sosai akan rasa Halwa wanda har sai da yakwanta ciwo, kullum bashi da buri idan ba yahaɗu da ita ba, a haka iyayen sa suka tilasta masa auren ɗaya daga cikin dangin su, domin su a ganin su idan har yasamu mata hakan zai dawo masa da nutsuwar sa, duk da dai basu san musabbabin abinda yafaru ba amma sun san cewa akan mace yashiga wannan halin, tunda be da abin faɗa sai sunan ta
Be musa musu da auren ba tunda shima hankalin sa baya jikin sa, ahaka akayi auren Amarya Zubaida tatare a gidan auren ta, da daɗi babu daɗi haka tazauna dashi tunda dama ita tana matuƙar ƙaunar sa, haka rayuwa taci gaba da tafiya har komi yalafa ma Haris duk da har yanzu ƙaunar Halwa na ransa sai dai yanzu ya cire duk wani damuwa aran sa ya dawo daidai yaci gaba da aikin sa, sai dai yaƙi komawa Abuja acewar sa anan Katsina Yakamata yazauna yayi aikin sa koda Allah zai haɗa sa da Halwa, baya son ko kaɗan yayi nisa da garin duk da be san cewa tana nan ko bata nan ba
Haka shekara ɗaya da watanni yashuɗe Zubaida bata taɓa koda ɓari ba, gashi burin iyayen sa su samu jikoki masu yawa tunda shi kaɗai Allah yabasu, hakan sosai yaɗaga musu hankali har shi Haris ɗin don shima yana son ganin yaran sa, don haka suka soma ziyartan asibiti amma sakamako ya nuna lafiyan su ƙalau lokaci ne be yi ba
Ana cikin haka Mahaifiyar Haris tasake ce masa yayi aure domin ita bata yarda matsalan ba daga wajen Zubaida yake ba, shi kuma Haris ko kaɗan baya ƙaunar tara mata da yawa don haka yabijire mata duk da kuwa ba wai yana son Zubaida bane amma suna zaune lafiya sosai sabida kyautata masa da take yi
An kai ruwa rana kafin Haris yayarda aka yi masa aure, don iyayen nasa duk sun goyi bayan ƙara auren nasa tunda suna son suga jikokin su nan kusa, duk da kuwa shekara biyu kenan da auren
Haris ya rigada ya sa aransa duk sanda yahaɗu da Halwa idan har zata aure sa to tabbas sai ya rabu da duk matan nasa tunda shi a tsarin sa mace daya yake so, sosai yaji daɗin cikin da tatafi dashi, kuma hakan yasa ya gane cewa shi ɗin yana haihuwa Allah ne be kawo ba, bashi da buri a yanzu illa yaga abinda tahaifa masa, ƙaunar ɗan nasa da be taɓa gani ba tuni ya shiga ransa sosai
Da maganar ƙara auren nasa da auren be fi wata biyu ba akayi komi aka gama, Amaryan sa Fahima ta tare a sabon gidan da mahaifin shi yagina masa tare da Uwar gida Zubaida
Itama dai tunda tazo ɗin bata taɓa koda ɓatan wata bane, har sanda itama tashafe shekara ɗaya curr kafin Allah yabata Ciki, zo kuga murna wajen Familyn baki ɗaya don kowa ya ƙosa yaga yaran Haris, iyayen sa babu wanda yakai su murna, haka akai ta tattalin Fahima da ɗan tayin cikin ta
Sai dai tunda tasamu cikin babu lafiya, yau suna asibiti gobe suna gida, yana watanni uku tayi ɓarin sa wanda har sai da aka dangana ga asibiti saboda yanda take zuban jini ta fita hayyacin ta gaba ɗaya, haka aka ɗauke ta ranga-ranga aka nufa Hospital da ita duk hankalin su a tashe.
______________________
A wannan lokacin itama Saleema ashe ciki ya shiga jikin ta, duk yanda kaso da dabara Allah idan yariga yaƙaddara abunsa to babu yanda zakayi, duk maganin hana ɗaukan cikin da Khalil yay ta bata amma a banza gashi ta samu shigan ciki har na wata ɗaya kamar yanda idan yakai hakan take ɓarin sa wannan ma karon hakan tayi, sai dai na wannan karon yafi na kowanne baƙin wahala
Tunda aka kai ta asibiti suke sintiri su ji me zai biyo baya amma babu likitoci babu alamun su, sai da akayi kamar mintuna 30 kafin suka fito suka nemi jini, tana buƙatar jini leda huɗu saboda ta bala'in zub da jinin ta
Haka aka ɗibi na Khalil dana Abba, sai aka siya ɗaya duk aka saka mata, su kansu Likitocin basa tunanin ma ko zata iya rayuwa a yanda take, ko numfashi bata yi sai da taimakon Oxgyen
Likitan ta yarigada yayi ma su Abba bayani dole sai an juya mata mahaifa sabida idan taci gaba da samun ciki to ƙarshe rasa ta zasu yi har abada, yanzu ma basu da tabbacin ko zata iya rayuwa.
Can ɗakin da aka kwantar da Saleema, su Ummi ne suka shiga tare da Halwa, gaba ɗayan su hawaye suke yi, yanda suka ganta tamkar matacciya hankalin su ya daɗa tashi ainun, Halwa kasa jurewa tayi tarufe bakin ta tafita dasauri cikin ɗakin, wani lungu tasamu tasoma gurzan kuka kamar zata shiɗe, kuka sosai take yi na tausayin Saleema
Haris lokacin yashigo asibitin kawo ma Matar sa abubuwan buƙata tare da abinda zasu ci, tunda a ranan kwanan ta biyu a asibitin kuma har tasamu sauƙi ana saka ran sallaman su yau ko gobe
Tunda yashigo idanun sa yasauka kan Halwa da tahaɗa kai da gwiwa tana ta sharɓan kuka, sosai yaji babu daɗi aran sa, haka kawai kuma yaji yana son ganin ko wacece yasan damuwar ta, sai kallon ta yake yi kamar yaje sai kuma yashige cikin asibitin yanufi ɗakin da aka kwantar da matar sa
Ƙanwar Maman Fahiman ce take jinyan ta, su biyu ne a ɗakin
Yana shiga suka gaisa ya'ajiye kayan da yazo dashi, tunda yazauna yarinyan da yawuce tana kuka ita ce tahana zuciyarsa sukuni, daga ƙarshe sai yamiƙe yafito don zuwa wajen ta yatambayi abinda ke damunta.
[11/24/2020, 9:03 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
_Wannan shafin naku ne masoyana na cikin group ɗin Khaleesat Haydar, na gode da nuna soyayyar ku gare Ni, Allah yabiya._❤️
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Nine*
________🎓Yana zuwa wajen sai dai babu ita, ya dudduba amma be ganta ba don haka yakoma cikin ɗakin da aka kwantar da Fahima, dama kawai don ta tsaya masa a rai ne but tunda yaduba be ganta ba sai be sake tuna ta ba har yabar asibitin.
____________________
Halwa tana tashi a wajen komawa ɗakin tayi, sai dai tana zuwa bakin ƙofa kunnuwan ta suka jiye mata maganganun Abba dake faɗa ma Ummi matsalan Saleema ɗin, sai kawai tazame nan ƙasa tasaki kuka me sauti, daga inda take zaune tana jin kukan Ummi itama don takasa jurewa, sai da Abba yayi ta rarrashin ta yanuna mata zata iya damun Saleema idan bata dena kukan ba tunda an ce kar suyi hayaniya da zai dame ta, hakan yasa Ummi tarage kukan ta takoma kukan zuci da hawaye
Abba ne yafito yatarda Halwan anan ƙasa tana nata sharɓan kukan, gaba ɗaya idanunta sun rine sun kumbura suntum wanda kallo ɗaya zaka yi mata katabbatar ta jima tana kuka yanda har fuskarta sai da yakumbura
"Subhanallah.. Daughter me kike yi anan? Kukan me kike yi?" Yatambaye ta yana saka hannu yaɗago ta
Halwa bata iya bashi amsa ba sai ƙara sautin kukan ta da take yi, duk da kuwa ta toshe bakin ta da Hijabin ta hakan be hana an ji fitan sautin kukan ta ba
Dafa kanta Abba yayi cike da ƙarfin halin sa yace "kiyi shiru kinji? insha Allahu ƴar uwanki zata samu sauƙi ki dena kuka haka nan".
Ya daɗe yana rarrashinta kafin yabuɗe mata ƙofar ɗakin yabata umarnin tashiga, shi kuma yajuya yatafi.
Tana shiga taƙarisa gaban gadon inda Ummi ke zaune ta tasa Saleema agaba tana zirarar da hawaye
Gefen gadon taɗan ɗofana mazaunan ta tana kallon Saleeman itama, wasu sabbin hawayen ne suka soma sintiri a face ɗin ta sabida tausayin ta, lumshe idanuwan ta tayi tabuɗe su akan Ummi da har yanzu ko ƙifta idanu bata yi, cikin rawan murya tace
"Yanzu shikenan Ummi.. baza ta haihu ba? Meyasa za'a juya mata mahaifa? Meyasa baza'a nema mata magani ba? Don Allah.. kar ayi.. gaggawan wannan..aikin". Taƙarike maganar nata cikin tsananin rawan baki da jan numfashi
Itama Ummi numfashin taja cike da sanyin murya da idan kaji zaka san tana cikin matuƙar damuwa tace "Ni kaina bansan wani irin ciwo ne wannan dake damun ta ba, sai dai sun tabbatar mana akwai wasu tsirrai a cikin mahaifan ta da baza su taɓa bari ta raini ciki ba, sannan kuma mahaifan ta babu ƙarfi ko anyi mata aiki ba lallai ne asamu nasara ba".
Halwa tace "Ummi idan har za'a iya dashen cikin ajikina Ni zan iya rainon mata, zan haifa mata idan har zata ga ɗan ta a duniya, a shirye nake in sadaukar da komi nawa don samun farin cikin ta".
Ummi kallon Halwa take yi kamar bata gane me take nufi ba
Sai Halwan tasake cewa "Ummi ki duba magana ta, idan har Saleema tasan da cewa an juya mata mahaifa hakan na nufin baza ta ƙara haihuwa ba to zata shiga matsanancin damuwa, kuma kinsan tana da ciwon zuciya idan hakan yayi tasiri zamu iya rasa ta, tunda ina da hanyan taimakon ta zan rainan mata cikin in haifa mata sai in bata yaron ta".
"Halwa idan har na amince za'a yi hakan Mahaifin ta da Mijin ta ba lallai su yarda ba, bansan me zan faɗa musu ba".
Daga maganar Ummin sai suka yi shiru gaba ɗayan su suna tunani
A lokacin ne Mom suka zo ita dasu Dad har da Khalil dasu Sameer, gaigaisa wa akayi tare da tambayan me jiki?
itama Halwa tagaishe su suka amsa cikin farin ciki, daga haka bata ƙara cewa komi ba tana jin su suna maganan su, daga baya su Dad suka fita ɗakin yarage daga Mom sai Ummi sai ita Halwan, har sai da likita yazo kafin suka fito waje
Sai dare ita Mom tatafi gida lokacin Khalil ya dawo sai yatafi da ita
Ita kuma Halwa sai da Larai takawo musu abinci sannan suka koma tare
A ranan Ummi ta kwana ne da maganganun Halwa a ranta, sosai tahau tunanin neman mafita, daga ƙarshe kuma tayanke shawaran zata soma tuntuɓan mijin Saleema da maganar idan ya amince tasan sauran babu matsala
Da sassafe Khalil ɗin shi yasoma zuwa, Ummi batayi ƙauron baki ba tafaɗa masa komi da kuma taimakon da Halwa tace zata yi ma ƴar su
Khalil shiru yayi kawai yana sauraron Ummi har sanda tagama maganar ta, lokacin hawaye kawai take yi
Sai tausayin ta duk yakama sa, shi kansa zai so hakan sabida tsananin tausayin Saleema dake ransa, yasan da cewa idan har taji komi zata shiga wani hali sosai, ba abu ne me sauƙi ba ace baza ka taɓa haihuwa ba bare kuma fa waɗanda suke son ƴaƴan, yana matuƙar tausayinta ta yanda Allah yajarabce ta da cututtuka kala-kala, gwara shi namiji ne yana da damar da zai iya ƙara aure yahaihu da wata matar, idan har hakan shine maslaha to ya yarda zai taimaka mata, idan tasamu ɗanta ko guda ɗaya ne hakan zai sanyaya mata ranta, sannan ma ba wai wata daban ce zata rainan masa cikin ba Masoyiyarsa wacce yake matuƙar ƙauna aransa ne zata raini cikin, ko babu komi zai yi farin ciki da hakan
Don haka koda yanuna ma Ummi ya amince tayi farin ciki sosai, su biyun suka nufi office ɗin Doctor sai suka bar Halwa don alokacin tarigada tazo
Sun jima suna tattaunawa, duk da shi doctor ɗin ya nuna musu kuskuren yin hakan tunda musulunci Bata yarda da hakan ba, amma kuma duk kansu sun rigada da sun san hakan mafita kawai suke nema, ba don komi ba sai dan taimakon Saleema, sun manta da cewa haka ƙaddaran ta yake, sai dai sun san idan da lafiyan ta lau ba ta ɗauke da ciwon zuciya tabbas haka nan zata ɗau ƙaddaran ta
Kasancewar akwai kayan aikin a asibitin don haka anan suka shirya yin aikin
Doctor shi da kansa yayi ma Abba bayani kamar yanda suka shirya, kuma Ummi bata son Abba yasan da zancen, don haka Doctor yayi masa bayani akan baza su juyar mata da mahaifa ba zasu soma ɗaura ta a magani da suke sa ran za'a iya dacewa
A zahiri kuma sun shirya za'a juya ma Saleeman mahaifa batare da kowa ya sani ba sai su kaɗai ɗin, ko da nan gaba Halwa ta haifa mata yaron kowa zai ɗauka Saleeman ce tahaifa tunda sun san dama ba'a juya mata mahaifa ba, ita kuma Halwa zata koma gidan Khalil da zama ta raini cikin a sirri har tahaifa.
___________________________
Kwanan Saleema biyar kafin tafarfaɗo, tunda tafarka take kuka Ummi tayi rarrashin duniya taƙi yin shiru, duk hankalin Ummi ɗin ya tashi kar yazo wani abun yafaru da ita
A lokacin Ummi ita kaɗai ce a ɗakin
Sai doctor da yashigo yanzu yaganta tana kuka, yasoma tambayan Ummi abinda yafaru
Cikin tsananin tashin hankali Ummu tace "wlh doctor bansan meke faruwa da ita ba, yanzu tatashi kuma tunda tatashi take kuka, nayi-nayi tayi shiru taƙi yi, yanzu nake shirin kiran ka sai ga ka ka iso".
Kallon Saleema dake kwance tana sharɓan kuka yayi, cikin tausayawa yace "Saleema meke faruwa ne me yasaka ki kuka? Ko wani wajen na miki ciwo ne?"
Girgiza kanta tayi tana kallon su da rinannun idanuwan ta wanda suka faɗa suka yi baƙi, ita kanta gaba ɗaya ta zurma ta faɗa sosai gunun tausayi
"To menene faɗa min?" Likitan yasake tambayar ta
Cikin kukan take cewa "Doctor.. cikinaa.."
Sai tasoma numfarfashi kamar ranta zai fita
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Ummi tafaɗa cikin ruɗewa tana ruƙo ta tare da fashewa da kuka
Shima Doctor ɗin ya ruɗe Nan da nan yamatso da zumman taimaka mata
Sai tasake cewa "doctor.. cikina.. ya zube ko?"
Duk kan su shiru suka yi don basu san amsar da zasu bata ba, ita Ummi kuka ya hana ta magana
Sai Doctor ne yayi ƙarfin halin kwantar mata da hankali
"Don Allah Saleema ki kwantar da hankalin ki, yanzu insha Allahu mun samo matsalar ki komi zai wuce kinji? Kiyi haƙuri kar ki saka ma ranki damuwa tunda yanzu lafiyan ki muke so, Ummin ki zata yi miki bayani kinji kiyi shiru".
Ummi ma cikin son ƙara kwantar mata da hankali tace "my Dear ki dena kukan yanzu komi yazo ƙarshe kinji?".
Sai tasaka hannu tana share mata hawayen
Doctor yace "Sister yanzu abata ko ruwan tea ne tunda jikin ta babu ƙarfi, idan nadawo zan yi mata allura sai in saka mata Drip, ki kula da ita sosai Please".
Gyaɗa kanta Ummi tayi sannan tace "to doctor".
Sai da yasake duba ta tare da yin mata tambayoyi kafin yafice.
Ummi taimaka mata tayi tatashi zaune, tagyara mata pilow abayan ta yanda zata ji daɗi sannan takoma tazauna tana kallon ta, cikin tausayin ta tace "Daughter don Allah ki dena kukan haka nan, kinsan bazan ji daɗi ba idan naga hankalin ki ba'a kwance ba".
Share hawayen ta Saleema tayi wasu na sake fitowa, cikin muryan mara lafiya sosai tace "Ummi shikenan idan nasami ciki zai dinga zube wa bazan haihu ba? Kullum haka zan riƙa shan wahala idan na samu ciki?"
Hannun ta Ummi taruƙo cikin lallami tace "kar ki damu komi ya wuce zaki haifi yaron ki kema?.."
"Taya Ummi bayan ina da matsala?" Takatse Ummin da faɗin hakan idanun ta na zirarar da hawaye
Ummi har ta buɗe baki zata yi magana Halwa taturo ƙofan tashigo, daga school tabiyo ta nan tunda dama haka take yi
Ganin Saleema zaune ya matuƙar faranta ranta, nan da nan tawashe bakin ta tanufo bakin gadon tana faɗin
"Sister kin tashi?"
Sai kuma tasauya fuska tana kallon Ummi tace "Ummi me yafaru ne meyasaka take yin kuka?"
Numfashi Ummi taja kafin tace "tunda tatashi take yin kuka sabida cikin ta ya zube".
Kallon ta Halwa tayi kafin tariƙe ɗaya hannun ta da Ummi bata riƙe ba tace "Sister meyasa zaki riƙa saka ma kanki damuwa bayan kinsan kina fama da ciwo? Don Allah ki dena in ba so kike mu ma mushiga wani hali ba".
Cikin rawan baki Saleeman tabuɗe baki zata yi magana sai kuma takasa sabida kukan da yataho mata, saurin duƙar da kanta tayi tana sakin kukan ahankali
Itama Halwa sai tasoma kuka tana sake riƙe hannun ta sosai
Ummi tace "kiyi shiru don Allah Saleema Allah ne yabaki cikin nan kuma shine ya'amsa ko baki yarda da ƙaddara bane?"
Shiru Saleeman tayi sai dai bata yi magana ba tana sauraron Ummi ɗin da taci gaba da maganar ta, cakk tahaɗiye sauran kukan nata tana ɗago kanta tana kallon Ummin, sai kuma takalli Halwa da tasakar mata murmushi tana gyaɗa mata kai alaman tabbaci da abinda Ummi ke faɗi
Shafa fuskar ta Ummi tayi tana murmushi tace "Halwa ta amince zata rainan miki cikin ki har tahaifa miki, sai dai ban sanar ma Abban ki ba don kar yahana, amma kuma da yardan Khalil muka yanke hukunci, yanzu kar ki bari Abban ki yaji ko kuma wani kinji? Mun yanke hukunci Halwa zata yi rainon cikin a sirri ne".
Saleema kallon Halwa kawai take yi cike da farin ciki, tabbas bata san da bakin da zata yi ma Halwa godiya ba, kawai sai tafashe da kukan farin ciki tana faɗin
"Wlh bansan da bakin da zan miki godiya ba ƴar uwata, amma na san cewa..."
"Shiiiiiiii... Yi shiru my Sister".
Halwa tafaɗa tana rufe mata baki, sannan taci gaba da faɗin
"Duk abinda zan miki Sister babu godiya a tsakanin mu, ke ce kika taimaki rayuwata a lokacin da narasa tudun dafawa, inda baki shigo rayuwata ba a yanzu bansan wani hali zan shiga ba, duk abinda zan yi wlh sister bazan taɓa biyan ki ba don haka kar ki soma kiyi min godiya kinji?"
Taƙarike maganar tana cire hannun ta kan bakin Saleeman, idanun ta cike da hawaye
Murmushi Saleema tasaki hawaye na zirara a kuncin ta
Hannu tasaka tashare mata lokacin itama nata sun zubo
Ummi kuwa kallon su take yi cike da farin ciki, ta gode Allah da yahaɗa su da Halwa, idan ba ita ba babu wanda zai iya taimaka ma ƴar su, tabbas ta cancanci Godiya me yawa
Murmushi tayi tace "yanzu to bari in haɗa miki tea ɗin kisha kar doctor yadawo tunda hankalin ki ya kwanta".
Kallon Ummin suka yi gaba ɗaya suna murmushi
Vowel tasoma ɗauko wa tare da ruwa tace "ki wanke bakin ki don kiji daɗin bakin, bari in taimaka miki".
Amsar Vowel ɗin Halwa tayi tace "kawo Ummi bari in taimaka mata".
Da taimakon Halwa Saleema tawanke bakin ta don ko kaɗan bata da ƙarfi ajikin ta, bayan ta gama tasha tea ɗin kaɗan
Doctor da yadawo yaɗaura mata Drip sannan yabata magani, babu jimawa tasoma barci tunda har da maganin barci aka bata don samun hutun ta
Sanda su Abba suka zo suka ji ta farka jikin kuma alhmadulillah sun ji daɗi sosai, tunda basu yi zaton hakan ba, amma Alhmadulillah kowa yake faɗi.
[11/26/2020, 6:00 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Ten*
________🎓 Satin Saleema biyu acikin asibitin kafin abata sallama tunda ta samu sauƙi sosai
A ranan da aka sallame ta Ummi tasamu Abba da maganar komawar Halwa gidan Saleema ɗin a matsayin zata zauna da ita
Abba be kawo komi akai ba ya'amince tunda shi da kansa Khalil ɗin yabuƙaci hakan kamar yanda Ummi tafaɗa masa
A ranan Halwa tahaɗa kayan ta da komi drever yakai ta gidan, ɗakin da Lubna tazauna ada nan aka gyara mata komi sai da Khalil yasauya mata na ciki
Wannan ranan kuma tazo ma Khalil cikin wani irin farin ciki, sosai yatsinci kansa a matuƙar murna kasancewar sa gida ɗaya da abar kaunar sa.
Tun daga ranan Halwa take musu komi girki, gyaran gida da duk abinda yadace, har alokacin kuma gaisuwa kaɗai ke haɗa su
Ahaka har kwanaki suka shuɗe inda Saleema tasake samun sauƙi sosai, a lokacin ne kuma suka shirya gaba ɗaya suka tafi asibiti inda za'a yi aikin saka ma Halwa ƙwayoyin haihuwar su don tahaifa musu ɗa, Ma'ana Invibrosfertilization a turance
A can suka haɗu da Ummi tana jiran su, babu ɓata lokaci Likita yahaɗa duk abinda Yakamata sannan aka shigar dasu ɗakin Theater aka yi, a lokacin ne kuma aka juyar ma Saleema da mahaifa batare da ta sani ba, tunda ita a tunanin ta duk aikin da za'a yi ne wajen saka ma Halwa ƙwan haihuwar ta
Har yanzu basu faɗa mata za'a juyar mata da mahaifa ba sai zuwa nan gaba idan hankalin ta ya kwanta sanda Halwa tahaifa mata yaron ta, hakan zai sa baza ta wani tada hankalin ta ba.
****** ****** ******* ***** *******
*TWO MONTHS AGO*
A cikin wannan watannin sai ga Halwa ta soma Laulayin ciki, koda suka je asibiti an tabbatar musu tana ɗauke da cikin dagaske har na tsawon watanni biyu
Zo kuga murna wajen Saleema da Khalil, sosai suke tsananin murna, ita dai Halwa sai dai tataya su da murmushi
Tun daga ranan kuma sai yazamana babu abinda Halwa take yi sai zaman hutu idan taje makaranta ta dawo, Khalil da kanshi wani lokacin yake kai ta school idan tana da lectures ɗin safe, sai drever kuma yaɗauko ta
Sun saba sosai dashi tunda yanzu suna zaune gida ɗaya, har hira suna yi tare
Saleema bata barin ta tayi komi duk ita take yi yanzu duk da Halwan tana taimaka mata tunda cikin ba me laulayi sosai bane kamar yanda tayi na Husna me wahala
Ummi ita da kanta tasanar da Abba Saleema na da ciki, sosai yayi farin ciki musamman jin cikin ya wuce wata ɗaya hakan na nufin an samu nasara kenan.
*****
Yau ma tana da lectures ƙarfe 11:00am.
Bayan ta shirya cikin blue and white colour ɗin atamfa ɗinkin riga da skert, tayi Rolling Farin gyale akanta, sai tasaka flet shoes shima fari da kalan baƙi a ƙasan, ta ɗau jakar ta kenan tana ƙoƙarin ratayawa
Saleema tashigo ɗakin riƙe da Plate a hannun ta, tana sanye cikin atamfa ja da kalan ruwan Powder ajiki, ɗinkin riga da zani sai taɗaura zanin ta gefe, ɗankwalin kuma taɗaura sa normal
Zuwa tayi kusa da ita tajanye jakan tana faɗin "ina zaki je baki ci abinci ba?"
Murmushi Halwa tayi tana kallon ta tace "wlh sister bana jin yunwa ne".
Hannun ta tajanyo suka zauna gefen gado tace "ai baki isa ba babu inda zaki je sai kinci wannan, shiyasa ma nashiga na dafa miki taliyan nan me ɗan romo-romo sabida yayi miki daɗi, kin gani ma har da yaji nazuba miki da yawa zai miki daɗi ai".
Sai kawai Halwa tasoma dariya
Itama kuma Saleeman dariyan tasoma duk da batasan me take ma dariyan ba, kafin taɗibo taliyan a cokali takai bakin ta tana faɗin
"Haaa bakin ki".
Hakan yaƙara saka Halwa tsananin dariya har tana tuntsura wa kan gadon
Wannan karon baki Saleema tasaki tana kallon ta
Kusan shuɗewar one minute kafin tace "wai menene kike ma dariya haka?"
Tashi zaune Halwa tayi tana ci gaba da dariyan nata kafin tace "Allah dariya kike bani Sister kin maishe Ni tamkar yarinya".
Murmusawa Saleema tayi tace "to ba dole ba kina ɗauke da cikin babynmu, nifa wlh ma kewar Husna nake yi dole zan saka Yaya Barrister yaje yaroƙi Ummi tabani ita".
"Me kike ci na baka na zuba tunda ga sabon baby zai fito? kibar wancan me ƙwallon kan".
Hararan ta Saleema tayi tace "Ummina ce me ƙwallon kai ko?"
Sai Halwa tayi saurin girgiza kanta tana fiddo ido waje tace "wlh suɓutar baki ne".
Sai da Saleema ta dara sabida yanda tayi maganar a tsorace
"To shikenan naji amma kar ki sake, yanzu kici abincin kar kiyi latti".
Amsan Plate ɗin tayi tana faɗin "wlh bana jin yunwa my sister don ke kawai zan ci".
"To na gode yi maza kici sai kisha ruwa". Saleeman tafaɗa tana tsare ta da idanu
Murmushi Halwa tayi lokacin da takai spoon ɗin bakin ta, ahankali tay taci ba don ranta na so ba don dai kawai ta faranta ran Saleeman, suna yi suna hira har tagama sannan Saleema taɗauko mata ruwa taba ta tasha suka fito
Har wajen mota sai da taraka ta taga fitan su kafin tadawo cikin gidan.
****** ****** ****** *****
Ƙarfe 01:45pm. Khalil yabar office yanufi gidan su, yau a waje yayi parcking ɗin motan nasa tunda baya son yadaɗe, kwana biyu rabon sa da zuwa gidan shiyasa yau yayanke shawaran zuwa daga nan kuma yasanar ma Mom ƙaruwar da suka samu Saleema na da juna biyu
Koda yayi sallama cikin parlour'n Mom ɗin ce kaɗai zaune, ta ɗan kishingiɗa kanta saman kujera tana ta faman kallo
Sallaman sa shi yatada ita tana amsa mishi kafin tace "my son idanun ka kenan ko?"
Shafa kansa yayi yana nufo ta
Shi kansa yasan be kyauta ba, musamman yanzu da ba samun lokaci yake yi ba ko waya ba suyi a kwanakin
Zama yayi yana kallon ta da tsadadden murmushin sa yace "I'm very sorry Mom kinsan aiki yayi min yawa shiyasa bana samun zuwa wlh, ina yini?"
"Lafiya lau my son ya matar taka?" Mom ɗin ta'amsa masa cikin fara'a
"Lafiya lau Mom tana gaishe ki ma".
"Ina amsa wa, yanzu Sameer yafita baku haɗu ba?"
Girgiza kansa yayi yana kallon ta, kafin yace "Mom babu lafiya ne?"
"To lafiyan dai za'a ce, Aamir ne yake fama da zazzaɓi, duk da dai Baban nasa ma yace min ya samu sauƙi".
Cike da damuwa Khalil yace "ayya bansani ba insha Allahu zan je gaishe shi yau ɗin nan".
"To Allah yabaka iko".
Sallaman Nazeefa yasaka suka kalli ƙofan suna amsa mata
"Nazeefa an dawo?" Cewar Mom tana kallon ta da murmushi
Itama Nazeefan murmushin take yi cike da farin cikin ganin Khalil tana tahowa ta'amsa mata da "Eh Mom Barka da gida".
Sannan takalli Khalil ɗin da a yanzu yafito da waya cikin aljihu tace "Yaya ina wuni".
Sai da yaɗago yakalle ta kafin yace "lafiya ya school?"
"Alhmadulillah Yaya".
Je ki cire kayan makarantan sai ki zo ki zuba ma Yayan naki abinci, yau babu Atine agidan".
Kafin takai ga amsawa Khalil yayi saurin faɗin "a'a Mom bana jin zan iya cin komi yanzu".
Mom ɗin bata tsawaita bincike ba tace "to shikenan".
Ita kuma Nazeefa sai tayi hanyan ɗakin ta Mom tabi ta da kallo, kafin tajuyo ga Khalil dake latsa waya tace
"Wai ni kam Auta dama akwai maganar da nake so muyi da kai".
Be amsa mata ba illa ɗago kai da yayi yana bata attention ɗin sa
Nazeefa da har ta shiga ɗaki tana ƙoƙarin rufe ƙofa tajiyo muryan Mom tana faɗin sunan ta, hakan yasa tadakata don jin me zata ce
"Ni kuwa ina maka sha'awar Nazeefa".
Kallon rashin fahimta Khalil ɗin yayi mata, kafin kuma yace "Mom sha'awa kuma? Kamar ya?"
Murmusawa tayi tace "Ni naga tunda matar ka bata da lafiya kuma kaima kana buƙatan ƴaƴa, ba'a son ranan dacewa ba bare ta haifa maka, me zai hana kaƙara aure? Ga ƙanwar ka Nazeefa tunda ba wani matsala ce da ita ba sai ka aure ta, in yaso sai wani hidindimun dake kan Saleeman su ragu, kaima zaka fi samun nutsuwa ko?"
Tunda tafara maganar yake yamutsa fuska, maganar tazo masa a bazata sosai, cikin rashin jindadin abinda tafaɗa yace
"Momyyy why zaki yi irin wannan tunanin? Ni fa na ɗauki Nazeefa tamkar ƙanwata ce wacce muka fito ciki ɗaya da ita, ban taɓa kallon ta a matsayin da kike magana ba, don Allah ki dena wannan maganar ma kar wani yaji".
Mom dariya tayi tace "sai kace wani abun kunya? Tunda baka so shikenan, dama sai da nayi ma Daddyn ku magana yace "shima babu ruwan sa idan ka amince to" tunda yanzu ka nuna baka so ai shikenan babu dole a zancen".
"Kuma Mom komi yanzu ya zama normal tunda yanzu tana ɗauke da ciki har na tsawon Two month". Yayi maganar yana turo baki
Da fara'an ta tace "haba dai? An dace kenan?"
"Insha Allahu Mom haka muke saka rai tun da gashi ya wuce wata ɗaya".
"Masha Allah, Allah Sarki wlh yarinyan nan tana bani tausayi matuƙa Allah yaraba lafiya, yanzu tana gidan su ne ko kuwa don kasan dai baza ta zauna ita kaɗai ba?"
Khalil yace "A'a bata koma gida ba, sai dai Halwa tana zaune da ita".
"To masha Allah haka ake so, har yanzu ita babu labarin komawar ta gidan mijinta ne?"
Khalil ɗan waro ido yayi don be fahimci maganar da take yi ba
Hakan yasa Mom ɗin tasake cewa "ina nufin ita Halwan tunda naji ance sun rabu da mijin ne".
Ɓata fuska Khalil yayi yana shafa sajen sa yace "Ni bansani ba".
Yanda yayi maganar ne sai da Mom tasake duban sa, sosai taga ɓacin rai a fuskarsa har a maganan da yayi sai da yanuna
"Mom zan tafi". Yafaɗa yana miƙewa tsaye
Itama miƙewar tayi tana faɗin "yauwa bari in baka saƙo sai kabata, ina zuwa".
Wuce wa ɗaki tayi taɗauko tabashi sannan suka sake sallama yafice.
****
Kuka Nazeefa tafashe dashi tana zame wa ƙasa, da rarrafe tanufi cikin ɗakin har zuwa bakin gado tahaɗa kai da gwiwa tasoma rera kuka ahankali, kukan rashin madafa a wannan halin da take ciki, shikenan tasan babu ita babu auren KHALIL tunda be taɓa mata kallon yanda take masa ba, infact ma ya ɗauke ta tamkar wacce suka fito ciki ɗaya ne, hakan yasa tasake fashe wa da kuka tuna abinda yace, sai dai yanzu tasan dole tararrashi zuciyarta tunda baza ta taɓa samun sa ba.
0 comments:
Post a Comment