💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
1to5
Sorry my fans najin banci gaba dayi muku posting ba hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiya da nayi gashi yanzu na fara daka farko thx
Bismillahir rahmanir rahiim, godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sake bani dama na rubuta wani littafi, Allah ya bani ikon gamawa lafiya,
KIRA GA MASU CANZA MIN NOVEL
Duk wanda ya kara canza min novel koya cire suna na ban yafe ba, Allah ya isa,
Tana zaune a cikin daya daka cikin jerun manya manyan kujerun falon wanda ya sha ado da kayan more rayuwa, idonta na kan tv, tana kallon tashar channel, amma gaba daya tunaninta baya wajan, inka ganta zaka rantse hankalinta na kan Jin sauraran news din da akeyi ne, gaba daya Kiran da kanwarta ta Mata a waya taji tana kuka shine ya d'aga Mata hankali, toh maiya sameta data ki fada Mata, tace sai tazo, ta danyi ajiyan zuciya tare da fadin nasan dai tatsuniyar gizo bata wuce koki, bari tazo inji koma miye.
Hauwa ta shigo cikin falon gidan tana kuka, ganin haka yasa hajiya salma ta tashi tana fadin Hauwa maiya faru haka? Tun dazu kinsa na kasa sukuni, Hauwa bata kulata ba sai kukan ta da taci gaba dayi, ganin haka hajiya salma yasa ta zauna ta gefenta tare da fadin Hauwa miye amfanin wannan kukan, kina ganin shine zaiyi miki maganin matsalanki?
Lokaci daya ta kurama hajiya salma ido, kaman mai son gano wani abu, tace salma anya ni dake uwarmu daya kuwa? Hajiya salma da mamaki tace Hauwa mai kike fada haka, anya kina cikin hayyacinki kuwa, karfa ki manta uwarmu daya uban mu daya, dan mai yasa zaki dinga tantama, bayan kin san mu biyu ma suka mallaka iyayenmu,
Hauwa dai kallonta kawai take, lokaci daya tace salma mai yasa bakya son nima inji dadi irin yanda kike ji, mai yasa bakya son ganin farin ciki na, mai yasa ba zaki sa nima na zama tauraruwa wajan mijina ba, kaman yanda kike a wajan mijinki, indai ko ciki daya muka fito zaki soni da wannan abubuwan, salma tace Hauwa bani da wani buri a kullum shine inga farin cikin ki, wlh Hauwa ina shiga damuwa fiye da yanda kike zato duk ranan da naji kin samu matsala da mijinki ko kuma na tuna irin rayuwar da kuke yi, bakin ciki na daya shine babu abun da zan iyayi a kai, sai dai in tayaki da Addu'a duk da kema kina da naki laifin..... Dan Allah niba wannan nake son jiba salma, nidai kawai ki hadani da malaminki yamin aiki ko zan dace, "Salma tace Hauwa wani irin malami kuma, Hauwa ta Mata kallon rainin wayau tare da furta in baki gane ba ina nufin bokan ki wanda ya mallake miki mahmud baya ganin kowa sai ke," Salma tace amma Hauwa kin ban mamaki wlh ke har zaki iya furta min wannan maganan, bayan kinfi kowa sanin koni wacece, wlh Hauwa ban taba zuwa wajan boka ba ko wani malami ba... Dan Allah ya isa haka nifa ba yarinya bace yanzu nasan komai, kuma wannan maganan da kike fada kin San ko mahaukaci bazai kama ba balle ni da hankali na, duk matar da mahmud ya aura saita bar miki gidan nan, sannan duk abunda kika cemai shi zai miki, sannan kice wai bakya bin malami, kima daina wani boye2 domin nasan komai, tana fadin haka ta tashi tare dayin tsaki ni zan wuce in kinki hadani da malamin zan nemo wani, tayi fuuuuu ta fita cikin fushi, salma ta girgiza kai cikin takaici yanzu itama Hauwa ta yarda ina bin boka, tace wai mai yasa ake samun irin wannan matsalan ne musamman a kasar hausa, indai miji zai nuna miki so toh za'a ce kin mallake shi, amma idan yau za'aga Kuna fada zaki ji bamai cewa komai sai dai ma a sami masu muku dariya, na rasa mai yasa Mata da yawa suka yarda da bin boka ba, wanda a dan nazarin da nayi, duk mace mai bin boka bata cikin kwanciyan hankali domin kullum tana cikin fargaba kar abun data kulla ya warware, na rasa mai yasa mutane ke zargina akan ina bin malamai ba, shin laifi ne dan mahmud yaso ni a matsayina na matarshi? Tayi dan shuru domin bata da amsa kuma bata damai bata, ganin tunanin bashi da amfani yasa tayi kitchen dan daura dinner,
Ya fito daka office, yana irin tafiyar nan tashi na kasaita, gefe kuma masu bashi tsaro ne suke biye dashi, yazo zai shiga mota sukai ido biyu dashi wanda wajan kwana biyu kenan yana ganinta, kaman zai Mata magana saiya share kuma, ya shige motar security ya rufe, sannan suka wuce tunanin yarinyar daya gani yake tayi wanda yau shine rana na biyu daya taba ganinta, tabbas yarinyar nan akwai abun da take nema, daka gani tana neman taimako, har suka shiga gida ya fito yayi ciki, wani kamshin turare ya bigi hancin shi, ta fito da sauri cikin English wear tayi hugging dinshi lokaci daya duk yaji ya manta da damuwar shi, salma tana da kyau wanda duk wani namiji zaiso ya mallake ta, uwa uba ga biyayya sai yasa mahmud baya ganin ko wace mace sai ita, duk da irin miskilanci irin nashi inka ganshi wajan salma da yanda yake mata sai kayi mamaki, ya kuma janyo ta tare da kara rungumeta yana Jin kamshin jikinta wanda ako da yaushe yake son ji, salati sukaji tare da tafi duka suka waiga dan Jin muryan hajiya binta maman mahmud, fuskanta babu alaman wasa ta kalli Salma wanda tayi kasa dakai gabanta na fadi dan tasan yau akwai rigima domin zuwan hajiya binta gidan ba alkairi bane, cikin sanyin murya ta gaidata amma bata amsa ba, ta kalli mahmud tace dole ka like mata bayan sihirin data maka harda karuwanci, toh wlh bari kaji indai nice uwarka kuma nono na kasha inaso ka kara aure koh naga jikana domin na gaji da jira,wannan karan ma sai nasa anyi min Addu'a sosai domin a barka da wacce zaka aura karta kuma koranta, kuma wlh wata uku na baka indai ya wuce haka zaka ga fushi na, tana gama fadin haka tayi waje, gaba daya jikin mahmud yayi sanyi tare da tausaya ma Salma ya rasa mai yasa zuri'anshi suka tsaneta sunbi sun damu akan bata haiyuwa wanda ni nasan na Allah ne kuma komai lokaci ne, Salma duk da irin tashin hankalin data shiga, ganin mijin nata yayi shuru yasa ta matsa gareshi tare da hura mishi kunne, yayi firgit ya kalleta ta sakar mai murmushi tare da fadin baby ba tunani zaka tsaya yiba yanzu kazo mu zauna musan miye mafuta kafin nan da wata daya ka nemo min kanwata nasan hajiya za tayi farin ciki, nima hakan zaisa inji dadi, yace salma bani da wacce nake so Sai ke wlh salma bazan iya auren wata mace ba, domin nasan bazan iyayin adalci ba, domin ke daban ce a cikin rayuwa na, tabbas tasan mahmud na santa itama tana sonshi tana bala'in kishin shi, amma dole ta daure tayi hakuri a wannan karon ma ya kara aure, duk da tasan abune mai wuya ya dade da matar, lokaci daya taji wani azababban kishi.
Hajiya binta rai bace ta shiga gida, taga zaliha a falo zaune da alama ta dade da zuwa,kanwar hajiya binta ce, tace a'ah zaliha yaushe kika zo tace tun dazu, ina kika je da wannan yamman haka, tace gidan mahmud mana, yaro matarshi duk ta shanye shi baya ganin kowa sai ita, zaliha tayi murmushi domin an tabo Mata inda yake Mata kaikayi, tace aini hajiya wlh da zaki dauki shawara na da anyi yar gida shida fauziya hala ma itace keda rabo dashi, nan hajiya binta ta washe baki tace aiko kin kawo shawara amma fah kin San wannan matar tashi a tsaye take dan muma sai mun tashi tsaye, zaliha tace kar ki damu ni zanyi maganinta yanzu dai saiki fada mishi dan nasan bazai miki musu ba tace babu damuwa, zaliha tayi wani murmushi wanda ita kadai tasan na miye.......
Maryam obam😘
💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
6to10
Washe gari da safe salma tana kitchen tana hada breakfast mahmud ya shigo daka shi sai gajeran wando da singlet a jikin shi, kasan cewan yau sati babu office duk ranan da yake gida tare suke girki suna yi suna fira cikin so da kauna har suka kammala suna cikin yin breakfast wayan shi yayi kara ya duba yaga Hajiya a screen din wayar cikin ladabi ya dauka tare da gaida ta, ta gefenta ta amsa cikin fara'a, tace anjima kazo ina son ganin ka, ya amsa da toh insha Allah zanzo bada dadewa ba, ta kashe wayan, salma wacce tayi shuru ko ba'a fada ba tasan mamnshi ce, suka hada ido ta sakar mishi murmushi yace Mata Hajiya nason gani na bari inzo inje tace gaskiya ya kamata kaje kaji ko miye, mahmud yana matukar son salma yanda take nuna ma yan uwanshi kulawa duk dasu basa ganin hakan komai tayi a wajansu bata iya ba, amma bata taba nuna gazawa wajan yi musu hidima duk da Halin da suke nuna Mata, mahmud yayi daki baiyi 30 minutes ba ya fito cikin kananan kaya wanda ya kara fito mishi da kyawunshi, salma tace anya ba zance zaka ba kuwa yayi dariya tare da fadin haba dai ina da kamarki a gida ai babu ni babu zuwa zance ke kadai kin isheni tayi dan murmushi tare da fadin Hajiya na jiranka gwara ka tafi yace hakane bari inje in dawo ya fita.....
Mahmud yana bayan motar driver yana janshi sunzo wajan traffic suka tsaya tazo ta wajan motarshi tana fadin sadaka fisabillillahi, ganin fuskanta yasa yayi saurin saukar da glass din motar amma lokacin traffic ya basu alaman su wuce driver yaja motar sukai gaba, har suka karasa gidan Hajiya yana tunanin yarinyar wanda baiga dacewan ace tana bara ba, tsayuwan motar da yaji yasan sun karaso ya fito cikin tafiya irin ta wanda yaji naira, masu aikin gidan suna ta gaidashi cikin girmamawa suna Jin dadin ganin shi domin indai yazo gidan to ranan suna shan kyauta, kai tsaye falo ya nufa yako ci Sa'a hajiyan na falo nan ya zauna yana gaidata ta amsa cikin fara'a, suka dan taba fira na tsakanin d'a da uwa, tayi gyaran murya tace abun da yasa na kiraka na yanke wani hukunci duk da ba yardan ka nake nema ba, yace Hajiya ai duk abun da kika yanke nasan bazai cutar dani ba, tayi dan murmushi tare da fadin na maka Mata lokaci daya yaji zufa ta keto mai kuma wannan karon na gida ne, fauziya na zaba ma, nan yaji gabanshi ya fad'i yace Hajiya Wace fauziya? Tace wacce ka sani mana yar uwarka, ji yayi komai nashi ya tsaya, yace Hajiya da an zabo min wata amm....... Dakata malam wato a zabo maka wata bare wacce matar ka zata koreta koh toh wlh baka isa ba, koh kaki koh kaso saika auri fauziya, yai kasa dakai tare da fadin Hajiya kiyi hakuri Allah yasa hakan shine alkairi tace amin cikin fushi, tabbas an cuceshi domin fauziya ba irin tsarinshi bace bata da tarbiya uwa uba bata da kamun kai ga shegen sangarta da rashin kunya babu mai fada Mata taji, shi baima cika shiri da ita ba, ganin tunanin bashi da amfani yasa yama Hajiya sallama ya wuce......
Tunda mahmud ya koma gida salma taga yana yinshi tasan akwai abun daya faru, tamai Sannu da zuwa ta koma kitchen ta kammala hada lunch, kai tsaye bedroom dinsu tayi ta ganshi a kwance yayi shuru yana tunani, tace dear lafiya kuwa naga kayi shuru haka, yayi dan gajeran tsaki tare da fadin lafiya babyna, ta kafeshi da ido tace kar muyi haka dear nafi kowa sanin ka, in kana farin ciki na sani haka in kana da damuwa na sani, yayi shuru can yace salma dazu da naje gidan Hajiya tayi min maganan aure, nan taji wani iri amma saita dake, tace kai dear shine kake damuwa, yace babyna Kin San ko wacece kuwa? Ta girgiza kai alaman a'a yace fauziya ce fah wacce Hajiya tace zan aura, nan taji dus domin tafi kowa sanin waye fauziya, wani kishi ya taso Mata amma saita dake, tace dear aiko abu yayi kyau kaga tuwo na mai na, kaga da auran wanda baka sani ba gwara wanda ka sani, kallon salma kawai yake domin yasan dama hakan zai faru, sai yasa a kullum yake son salma tare da tausaya Mata, duk abun daya kawo za tayi na'am dashi duk munin abun indai bai saba ma addini ba, ya dan janyo ta jikin shi tare da fadin Allah yayi miki Albarka, tayi murmushi tare da fadin muje kaci abinci, yace no ki kawo min nan tace ok sir, tayi waje, tana shiga kitchen ta saki kuka mai zafi tare da wani zafin kishi daya taso Mata, yanzu mahmud fauziya xai aura wani abu ya taso mata a wuya........ Hmmm anya salma zata iya jurewa kuwa?????
Maryam obam😘
💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
10to15
MASOYA KUYI HAKURI NAJI NA SHURU YANZU INSHA ALLAH NA DAWO ZANCI GABA NA DAN DAKATA NE SABODA RASUWAN MAHAIFINA ALLAH YAJI QANSHI YASA YA HUTA, WA INDA SUKA KIRANI SUKAI MIN TA'AZIYA DA WANDA SUKA ZO DA WA INDA SUKAI MIN MESSAGES INA MIKA GODIYA TA A GAREKU ALLAH YABAR ZUMUNCI👏👏
Wannan page din naki ne kawata ta rai da rai habiba s Ali👌👌
Salma taci kukanta lokaci daya ta share hawayen tare da wanke fuskanta dan kar mahmud ya gane tayi kuka, ta gama hada mai kayan abincin ta dauka ta nufi dakin dashi kallo daya yayi mata ya gane tayi kuka dan idanta ya dan sauya kala duk sai yaji babu dadi ta kuma bashi tausayi inda badan karya saba ma mahaifiyarshi ba toh wlh daya fasa auren fauziya dan baya kaunar ganin bacin ran salma ko abun da zai daga mata hankali, bayan ta ajiye abincin ta koma gefe ta zauna tashi yayi yaje kusa da ita yayi hugging nata tare da mata magana cikin kunne salma mai yasa kikayi kuka kin san bana San ranki na baci dan Allah ki daina sama kanki damuwa please my dear kinji tayi dan murmushi tare da fadin waya cema nasa ma kaina damuwa ka daina tunanin haka babyna ina farin ciki yanda baka misali yayi dan murmushi tare da kara janyota jikin shi.....
Hajiya zaliha na zaune a tsakar gida tana gyara shinkafar tuwo fauziya ta shigo tana sanye da riga da wando na yan kanti duk sun matse ta, ga wani kitso da tasha na attachment ta yafa wani siririn gyale waita rufe gashin amma gaba daya rabin gashin a waje yake,tace Amma yau tuwo kuma za kiyi daka shugowa na nayi Karo da tuwo, hajiya zaliha tace wai ina kikaje baki dawo gida ba tun jiya sai yanzu nayi ta kiranki baya shiga, fauziya ta dan tabe baki tare da fadin daka dawo wana har kin fara jeromin tambayoyi ko zama banyi ba ta daure fuska ganin haka hajiya zaliha tace kiyi hakuri y'ata hankalina ne ya tashi da ban ganki ba wlh, ta dan ya matse fuska tare da fadin gidan kawata na kwana sai yasa ban dawo ba, hjy zaliha ta washe baki tare da fadin yar albarka mai kashin Arziki albishirinki tace goro, ta mika mata hannu fauziya ta xaro dari biyar ta bata, tace wlh yayi kadan ai dubu goma zaki ban sai kiji albishir mai dadi, fauziya tace ni banda kudi in zaki fada ki fadamin in kuma ba zaki fada ba kinga bani kudina, hjy zaliha tayi dariya tace shikenan bari in fada miki na shawo miki matsalanki binta ta yarda mahmud ya aureki tsalle fauziya tayi tare da fadin Amma ban San wasa fah, tace wlh y'ata dagaske nake nan fauziya ta tashi tana rangada bud'a tare da rawa ta zaro dubu ishirin taba maman tace ga kyautar albishir Amma ya akai ta yarda haka cikin sauki, hjy zaliha tace ni wasa ce wajan wani boka naje yaban wani turare yace indai zani gidan insa komai nace mata zata yarda, fauziya tace amma ina tsoran ta canza ra'ayi kin san yar uwarki din nan sai a hankula, hjy zaliha tace wane ita indai akwai bokaye kuma ina da rai ai Sai kin auri mahmud wlh munci daula mun barta suka saki shewa cikin jin dadi duniya tasu,
Hajiya zaliha tana sa kaya fauziya tace ina zaki kuma kike ta sauri tace wajan malam mana inje inji yanzu miye abun yi dan kin San dole sai mun san yanda mukayi muka rabashi da wannan matar tashi dan yana bala'in tsoran ta, itama kin San a tsaye take sai munyi dagaske karta bata mata shirin mu sai yasa gwara ma ayi abun da wuri fauziya tace nima ai banga ta zama ba, tare zamu hjy zaliha ta saki dariya tace yauwa yar gari gwara muje in kina da wata matsalan saiki fada mai ma ya miki magani, suka fita.
Sun isa gidan boka yau sunyi sa' a babu kowa a wajan, nan suka zauna a kasan carpet din dake falon, hjy zaliha tace kaga likita mai bada maganin ko wani ciwo, mai yaye ma mutum damuwa wanda ya bika ya more wanda ya bijire maka yana cikin wahala, wa'iyazubillah Allah yasa mu dace, ya saki dariya wanda tun shigowansu idonshi nakan fauziya yace wannan fah, zaliha tace y'ata ce, wanda na baka labari ya lashe baki tare da fadin toh toh barka yan mata naji duk matsalanki, yanzu mai kikeso ai miki, tace ina so a mallake min mahmud sai abun dana ce ya soni kaman zaiyi hauka, yaji ya tsani matarshi, sai kuma mahaifiyarshi ita inaso a mallake min ita, boka ya fara dariya ya fara duba kasa lokaci daya ya daure fuska gaba daya muninshi ya fito, ya kalli fauziya yace kina da aiki a gabanki domin mallakan mahmud abune mai wuya dan matarshi tana yawan tsayuwan dare shima yana yi, tace toh yanzu miye abunyi yace abu daya ne shine Zan sa ayi auran da wuri in kin shiga gidan sai muga ko zamu iya mallake shi, ga wannan ki dinga amfani dashi kullum ta amsa turare ne sannan ya bata wani laya yace tasa a jikinta ta daure ta amsa tare da fadin to, yace karta taba kwance layan sai anyi bikin yace suje gida zasu ga abun mamaki suka bashi kudi suka wuce......
Fauziya tace anya wannan bokan ya iya aiki kuwa? Hjy zaliha tace tabdi ai bana tantama akan aikin sa wlh, suna firan har suka je gida suna isa kofar gida suka ga mota ko ba'a fada ba sun San hjy binta ce, cikin sauri suka shiga gidan, suka ganta zaune kan kujera a tsakar gida, hjy zaliha tace a'ah yaushe kika zo badai kin dade ba tace a'a ban dade da zuwa ba, fauziya ta gaidata ta amsa cikin fara'a tace nazo miyi maganan bikin nan ne tun da kika zo na jiki shuru hjy zaliha cikin jin dadi tace aida kirana ma kikayi, fauziya cikin murna tace gskiya wannan bokan ya iya aiki......... Hmmmm
0 comments:
Post a Comment