"Wai Babe kina Ina ne naji ki shiru har yanzu?".
Cikin siririyan muryan ta me sanyi tace "ga ninan zuwa".
"Ok sai kin zo". Cewar Ramcy tana katse kiran
Ajiye wayan kawai tayi taƙara speed, tana tuƙin ne cike da gwaninta har Allah yasa takawo ƙofar gidan su Ramcy ƙawarta, Ramcy dake bakin ƙofar gidan su a tsaye tanufo motan tabuɗe tashige, ita kuma taja sukaci gaba da tafiya, kallon ta Ramcy tayi tana murmushi tace
"Kinyi kyau Babe".
"Thanks". Ta'amsa mata ataƙaice
Daga haka basu sake magana ba har suka iso gaban wani kyakkyawan Club, fitowa sukayi cikin motan bayan tayi parcking motan aciki, atare suka jera sukayi cikin Club ɗin
Sosai ciki yacika da mutane maza da mata kowa na harkan gaban shi, an saka music wasu na ta faman cashewa, suna shiga Direct RAUDHA wajen masu rawa tanufa tashige cikin su tasoma kaɗa jiki tana rawa me ban sha'awa, dama abinda ke kawo ta Club kenan RAWA, tana ƙaunar rawa a rayuwan ta, koda tana cikin damuwa ne idan har zataji kiɗa na tashi to fa sai zuciyarta tayi mata sanyi, haka tayi ta cashewa tana rausaya jiki kamar zata karye, dama ba wani auki ne da ita ba, ita kuwa Ramcy ba gwanar rawan bace, zuwa tayi tazauna cikin wasu maza tasoma kora sheesha tana yi tana kaɗa kai
RAUDHA rawa yayi rawa sai zuba ihu take yi tana dariya tana tiƙan rawa, sai da tagaji sosai kafin tayo wajen Ramcy tazauna tana waftan Sheeshan hannun ta tasoma sha tana fesarwa ta hanci ta baki cike da ƙwarewa, mazan wajen duk kallon ta suke yi suna dariya, yayinda ɗaya daga ciki yasoma mata kirari yana faman koɗa mata kai, ita kuwa sai faman bankan sheesha take yi tanayi tana shaƙan Coken, Ramcy tashi tayi tanufi wajen wani saurayi dake can zaune tare da ƴan mata, magana sukayi sannan yamiƙo mata wasu ƙwayoyi da bansan ko menene ba, amsa tayi tanufi wajen Receptionist tayi odan Juice tadawo, kallon ta kawai RAUDHA take yi har tazauna kana tamiƙa mata hannu, ita kuma tabata Cup ɗaya bayan da tasaka mata ƙwayoyin ciki, amsa kawai tayi tasoma korawa tana jin ta asama, zuwa lokacin tasoma kai ƙololuwan bugawa, don daƙyar take iya buɗe kyawawan idanuwanta tana kallon mutane, sai da tashanye gaba ɗaya tasaki Cup ɗin Ramcy tayi saurin tarewa
Lumshe idanu tasoma yi tana buɗewa daƙyar, cikin tsananin maye take cewa "ahh.. ahhm Rammmm.. Rammcyyyy ƙaro min.."
Bata iya ƙarisa maganar ba ma sai shiru tayi tana ci gaba da zuƙan Sheeshan tana fesarwa ta cikin hancin ta, Ramcy itama da tagama buguwa tashi tayi takoma tasake yin musu odan wani Juice ɗin tadawo, zuba musu ƙwayan tayi suka ci gaba da sha, yayinda su kuma mazan nan sai harkan gaban su suke yi, daga ƙarshe ma tashi sukayi ɗaya bayan ɗaya suna barin wajen, yayinda wasu suka wuce wajen ƴan matan su, wasu kuma sukayi gida don alokacin dare yayi sosai
RAUDHA buɗe manyan idanuwan ta da suka kaɗa sukayi jazur tayi tana kallon Ramcy tace "amm... Babe muje.. giii..gida, yauuu banjin zannn iya kaaaiiiii asuba".
Gyaɗa kai kawai Ramcy tayi tana miƙe wa tsaye, taɗau jakan ta tana ƙoƙarin rataya wa, ita kuwa RAUDHA kasa miƙe wa tayi sai da tafi minti 3 azaune kafin tayunƙura tamiƙe, sai kuma takoma yarabb kamar wacce aka jefar
"Oshhhhhhh". Tafaɗa tana riƙe kanta da yabugi kujera
Still sake miƙe wa tayi, har ta soma tafiya kuma sai tasake faɗi, dole Ramcy ne tariƙo ta suna tafiya suna layi har suka fice daga Club ɗin
"Babe anyaaa zzzaki iya tuƙi? Kar fa kije ki zubarrr damu?"
RAUDHA dake faman layi takai tadawo tana son buɗe mota but takasa, taɗago kanta tana kallon Ramcy daƙyar, lumshe idanu tayi tasake ware idanun sosai kan Ramcy kana tace
"Kin fini.. sanin.. abinda nake yi ne? Common shiiiiiga... Muje ma..na.."
Bata rufe baki ba tayi taga-taga zata faɗi, har takusa kai ƙasa tayi saurin riƙo motan tana gyara tsayuwar ta, buɗe motan tayi tafaɗa ciki tana mata key, itama Ramcy shiga tayi sannan taja motan da gudun tsiya tafice haraban wajen, izuwa lokacin tsit kake ji a titi domin kuwa wajen ƙarfe 0300pm. Ne na dare, ahankali take jan motan sai dai yanda motan take yawo akan titin zakasan ba cikin hankali mamallakin motan take ba, idan tayi nan sai tayi nan, daƙyar take buɗe idanun ta tana kallon titin, har ƙofar gida tasauke Ramcy kafin sukayi sallama taja motan tayi gaba, tana isa tanƙamemen gidan su tadanna hon ɗin da gaba ɗaya layin gidajen sai anji, Me gadi da yake zaune yana jiran dawowarta yamiƙe dasauri yabuɗe mata, tashigo aguje kamar zatayi ciki dashi tanufi parcking space, parcking tayi tajanyo jakan ta tana ratayawa tabuɗe motan tafito, tafiya take yi tana tangaɗi har taƙarisa bakin ƙofar Main parlour tabuɗe tashiga, ahankali take takawa tana faman layi taje gaba tadawo baya har dai ta'isa steps tasoma takawa tana haurawa sama, tana hawa tashige ɗakin ta tanufi kan gado tafaɗa kai, ahaka barci yakwashe ta batare da tacire ko takalmin ƙafafun ta ba.
Ba ita tatashi ba sai washe gari ƙarfe 01:30pm. Ahankali take buɗe kyawawan idanunta da suke ashanye koda yaushe, hannun ta duk ka biyun tasaka tariƙe kanta tana sake lumshe idanuwanta, ta ɗan jima ahaka kafin tacire hannun tana sake gyara kwanciyarta cike da tsananin gajiya, ko kaɗan barcin be ishe ta ba so take yi tasake komawa, sai dai ƙarar wayan ta shi yawartsakar da ita, hannu tasaka taciro cikin jakan ta tana kallon screan ɗin, MY DEAR DAD aka rubuta, peacking tayi tasaka a kunne still tana gyara kwanciyarta, daga ɗaya side ɗin Dad ɗin ta ne yasoma magana
"My Baby good morning".
Lumshe idanu tayi tana buɗe wa kana ta'amsa mishi "morning Daddy".
"Baby har yanzu baki tashi barcin bane?"
"Eh". Tabashi amsa ataƙaice
"Ok Allah yasa bani natashe ki ba don bana son takura miki?"
Memakon ta'amsa mishi tambayan sai canza maganar tayi dacewa "Daddy yaushe zaka dawo ne I miss You More?"
"Sorry My Baby umm? very soon Zaki ganni".
Cikin dashashshiyar muryan ta cike da shagwaɓa tace "Daddy kasaka mana azo a ɗauke ni nagaji da zama Ni kaɗai, komi babu daɗi".
Daddy cikin lallami tare da ƙaunar ƴar tasa yace "sorry Babyna ai nace miki nakusa dawowa very soon zaki ganni, and kuma kinga kin kusa fara school bazai yiwu ki biyo ni ba".
"Daddy to ba sai kasaka Ni school ɗin nan ba, dama bana son anan".
Murmushi yayi yace "Sweetheart kinsan ba zama nake yi ba, bana son kiyi nesa Dani that's why nafison kiyi karatun ki anan Nageria".
Turo baki kawai tayi bata sake cewa komi ba, Daddy lallaɓa ta yai tayi don yasan fushi tayi, shi kuma baya son ne taje Abroad tasake lalacewa coz yasan ta ba tarbiyya ne ya'ishe ta ba, yanzu haka ma nema mata shiriya yake yi Allah yashirye ta don duk abinda take yi yana sane dashi, sai dai tsananin ƙaunar da yake mata bazai saka yayi mata faɗa ba
Muryan ta shi yadawo dashi gajeren tunanin sa
"Daddy I will call you back idan nayi Lunch".
"Ok My Baby Baki buƙatar komi ko?"
Cikin nuna sangarta tace "Daddy katura min kuɗi zan fita Shopping yau".
"Ok byee take Care".
"Byeeee Daddy".
Ajiye wayan tayi sannan tatashi tazauna tasoma cire Hill shoes ɗin ƙafanta, Ribom ɗin kanta dake yashe a ƙasa taɗauka taɗaure gashin ta sannan tamiƙe tanufi gaban plasma t.v dake ɗakin takunna, Remote taɗauka tasoma sauya Channels, a BOM t.v tabar shi sannan tasaka Volume gaba ɗaya, nan da nan ko'ina yaƙaraɗe da Music ɗin da akeyi kasancewar akwai irin manya-mayan speakers🔊 masu matuƙar ƙara da ɗaukan duma, Toilet tashige tana bin waƙar kamar ita take rerawa, Brosh kawai tayi tafito tanufi ƙofan fita tafice ƙafarta ko takalmi, Steps tasoma takawa da gudu-gudu don ita akwai son gudu, tana jinta kamar ƴar chali-cahli ce
lokacin da ta'isa tanƙamemen parlour'n tabuɗe muryan ta da yake adishe koda yaushe tamkar tana mura tasoma kiran masu aikin ta, kafin tarufe baki suka fito suka gurfana gaban ta
"Where is my lunch?". Tatambaye su tana bin su da kallo da shanyayyun idanun ta
Saude wacce take kula da abincin ta tace "yanzu zan zuba a warmers in kawo dainning".
"Ok ki kawo min ɗakina ne".
"An gama ranki yadaɗe". Saude tafaɗa sannan tajuya takoma kichen
Kallon Larai tayi tace "ke kuma je ki sanar da Idi yawanke min Motan Daddy yanzu".
Cike da girmamawa Larai ta'amsa mata sannan tafice dasauri don isar da saƙon uwargijiyarta, ita kuma juyawa tayi tasoma taka steps ɗin da gudu takoma ɗakinta, tana shiga tanufi Drower tabuɗe taciro wasu Tables taciri ɗaya tasaka a bakin ta, Fridge tanufa tabuɗe taɗau Faro water takora dashi, kan sofa tanufa tana riƙe kanta tazauna dai-dai lokacin da Saude tashigo riƙe da farantin Silver ta'iso gabanta ta'ajiye kan Centre table dake gaban kujeran da yake guda ɗaya cikin ɗakin
"Ranki yadaɗe gashi".
RAUDHA da tasoma hawa kan network ɗago shanyayyun idanunta tayi takalle ta kafin tayi mata alama da hannu tatafi, juyawa Saude tayi tanufi ƙofa, sai da tabuɗe ƙofar kafin tajuyo tana kallon RAUDHAN da har yanzu take riƙe da kanta, cikin ranta sosai take tausayin yarinyan kuma take mata fatan shiriya, duk da wani lokacin bata da kirki idan har sukayi mata ba dai-dai ba haka zata zazzage musu tijara son ranta, but idan har zasu kiyaye ƙa'idan ta to babu abinda ke shiga tsakanin su don ita ɗin ba me son shiga rayuwan wasu bane idan be shafe ta ba
Saude ganin RAUDHA zata ɗago kai yasaka tayi saurin fita tana rufo ƙofan.
Ahankali tasaka zara-zaran hannunta tabuɗe abincin, Jolof Raice ne da yaji meat and veggies a sama, ɗayan Coolar'n kuma da tabuɗe ferfesun kayan ciki ne, a plate tazuba tasoma ci, sosai taci abincin kasancewar batayi breakfast ba, bayan ta gama miƙe wa tayi tacire kayan jikin ta tashige toilet, ita kuma Saude lokacin tadawo takwashe kayan abincin tafitar dasu
Minti 15 yaɗauke ta kafin tafito, doguwar riga tazira sannan tasaka Hijab tasoma gabatar da sallan asuba kafin tayi azahar, dama haka take yi koda yaushe, wani lokacin ma gaba ɗaya haɗe su take yi da dare tayi su, akwai ta da son wasa da ibada duk da ba wani addini tasani ba, but ko ta tara su idan tatashi sai tahaɗe tayi, tana idarwa ko tsayawa addu'a batayi ba tamiƙe tasoma tuɓe rigan, towel taɗaura tanufi gaban mirror tazauna tasoma shafa Lotions tana bin music ɗin dake tashi cikin t.v at the same tana kaɗa jikinta tana rawa, Light makeup tayi tamiƙe tanufi gaban sif ɗin kayan ta tazaɓo kayan da zata saka tazube kan gado, komawa tayi tazauna a bakin gadon taɗau wayan ta tana latsawa, ta ɗan jima kafin tamiƙe tasanya kayan, ƙaramar riga ce White wanda tatsaya mata iya cibiya, don idan har zata ɗaga hannun ta ko tayi motsi me ƙarfi ana hango cibiyanta, sai tasaka wandon rigan Robber iya gwiwarta shima fari, gaba ɗaya santalelen ƙaurin ƙafanta a waje yake, zama tayi tasoma zira socks white da yakawo mata har kusa da wandon ta sannan tasaka Hill shoes Black me igiya, miƙewa tayi takoma gaban mirror tasake gyara gashinta da yake baƙi siɗik taɗaure da Black Ribom sannan tafeshe jikinta da Parfomers masu shegen ƙamshi, miƙewa tayi tana wani jujjuya wa tana sake kallon kanta a mirror, sosai tayi matuƙar kyau kamar wata baturiya, dama ita irin shigan Turawa ke burge ta kuma shi ɗin take yi, ko kaɗan bata ta'ammali da kayan Hausa don haka farat ɗaya idan kaganta baza ka taɓa tunanin ta haɗa hanya da Hausawa ba coz babu ta inda take kama dasu, sai da tagama jujjuya jikin ta kafin taje tazaro Wizy Bag ɗin ta tare da ɗaukan wayan ta tafice batare da tayafa komi ba, haka tabar ɗakin ko T.v bata kashe ba, sai dai idan Larai me aikin ta tazo gyara ɗakin itace zata kashe mata.
[11/13/2020, 2:32 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️ ~What'sapp Number 07065334256~
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON TWO*
_______📖Packing space tanufa tabuɗe motan tashiga but sai dai bata shigar da ƙafafunta ciki ba, Lockern cikin motan tabuɗe taciro wani farin Robber tabuɗe, Coken ne aciki sai tazuba a tafin hannun ta tana shaƙa, sosai tashaƙa don sai da taji ta kan network kafin tajinginar da kanta tana lumshe idanu, as usual tana son taji ta kan network that's why bata rabo da shan kayan maye, abin ma har yabi jininta, kana kallon idanunta da kuma yanda take yawan lumshe su zakasan ita ɗin ƴar ƙwaya ce, sai da taɗau kamar minti 5 kafin tashigar da ƙafafuwan ta tarufe murfin, key tayi wa motan tafige ta tayi bakin Gate, oready dama Gateman yarigada ya buɗe mata Gate don yasan halin ta bata da jimirin jira, tana fita tahau kan titi kasancewar gidan nasu a bakin titi yake, da wani irin speed take Jan motan Wanda idan kagani kasan Drever'n ciki ba ƙalau take ba, duk inda tawuce sai an kalle ta, haka take over taking Cars tana wuce wa babu ruwan ta
A cikin minti 15 ta iso wani supper market, cikin haraban tayi packing sai da tayi kusan mintuna goma tana zaune abunta kafin tabuɗe tafito, cikin wani irin tafiya tare da ficchi take takawa tadoshi cikin supper market ɗin, duk wanda ke haraban wajen sai da yaɗaga kai yana kallon ta, ita kuwa batasan ma suna yi ba, tafiya kawai take yi tana wani irin karairaya tare da lumshe idanu tamkar bata ganin gaban ta
Just 10minute taɗauka aciki before tafito riƙe da Ledoji a hannun ta tatunkari motan ta
"Woww wow Nazee ji wata zazzafan Babe sai kace ita tatsara kanta".
Nazee da yake ƙoƙarin rufe ƙofar mota yajuyo yana kallon RAUDHA, sai kuma yaɗauke kai yana kallon Abokin nasa da ninyan yayi magana but sai shi yariga sa dacewa
"Kai wlh sai naje wajen ta don bazan bari tasuɓuce min ba, kutttt wannan irin su ai muke so Young Killer Babe".
Har ya soma tafiya Nazee yajawo shi baya
"Kai rufawa kanka asiri wlh, kai baka san ko ƴar wanene ba ko?"
Saddeq dake kallon sa yace "ƴar wanene to? Kaga da Allah sake Ni kar tatafi". Yaƙarike maganar yana fizge rigan sa tare da kallon motan RAUDHA da har tasoma tafiya
Nazee saurin cewa yayi "wlh yarinyan M. makamashi ne, gwara ma kadawo kafin ka kwashi wulaƙanci a wajen ta".
Cak Sadeeq yatsaya yana kallon Nazee yace "Haba dai kana nufin Alh. Mustapha Makamashi?"
"Wlh kuwa itace". Nazee yasake tabbatar masa
Rufe baki Sadeeq yayi yace "kai wlh nayi tunanin ko irin Babes ɗina ne, wai kana nufin yanzu wannan musulma ce? Ikon Allah lallai kam huuuuu.."
Kasa ma ƙarisa maganar yayi yana sake bin hanyan da kallo da tuni RAUDHA taɓace a wajen, sai kuma yajuyo yana kallon Nazee yace "wlh nayi tunanin ko Christian CE kasan Ni dasu nafi harka coz waɗannan ƴaƴan musulman babu abinda suka iya sai girman kan tsiya".
Dariya Nazee yafashe dashi kafin yasoma tafiya yana cewa "kai dalla muyi abinda yakawo mu Ni kaga tafiyana".
Bayan sa Sadeeq yabi yana cewa "Guy Amma fa ta haɗu, duk sanda nasake ganin ta sai nayi mata magana Yasin".
🌐🌐🌐
WUTA kawai take ba ma Motan har ta'isa gida, wani irin hon take dannawa kamar zata tashi sama, dasauri Gateman yabuɗe mata tashigo aguje tanufi Compound ɗin gidan, anan tayi packing tafito takwashi kayan ta tanufi cikin gida, tana buɗe ƙofan parlour'n suka haɗa idanu dashi, tsaye yake ya sanya hannayen sa cikin aljihun wandon sa yana kallon ta, wani irin ƙara tasaki tazubar da ledojin dake hannun ta tanufe shi aguje, tana isowa wajen sa yacafe ta yasoma juyata tana dariya, shima ɗin dariyan yake yi yana faman wulwula ta sai kace ya ɗauki ƙaramar yarinya, sai da yadaɗe yana faman jujjuya ta acikin parlour'n sannan ya'ajiye ta a ƙasa tabiyo jikin sa suka faɗa saman sofa suna ɓaɓɓaka dariya tare da sakin nishi, sake maƙalƙale shi tayi cike da tsananin murna tace
"I'm so surprise Yaya yaushe kadawo?"
Hannun sa yasaka yana shafa fuskarta cikin murmushi yace "Yesterday Baby, mun dawo gaba ɗaya kenan fa".
Wani irin tsalle tadaka ajikin sa cikin ihun murna tace "dagaske Yaya?"
Still Murmushi yasaki yace "Yes my dear".
"But anan gidan zaku zauna ko?" Tasake tambayan sa cike da zumuɗi
Girgiza mata kai yayi yana taɓe baki yace "No muna Abuja fa".
Hannun sa still dake yawo saman fuskarta tayi saurin cafke yatsan sa da baki tana gantsara masa cizo cike da mugunta, ihu yasaki yana janye hannun yace
"Oshhhhhhh Babe Zaki kashe Ni ne da zafi fa?"
Turo bakin ta tayi tana tashi ajikin sa tace "Yaya meyasaka sai acan zaku zauna?"
"Sorry Baby kinsan can nake aiki dole acan ɗin zan zauna, kinga shiyasaka ma nazo naɗauke ki mu koma can tunda nasan zakiyi fushi dani".
Cikin dashashshiyar muryan ta tace "No Yaya bazan je ba".
"Why dear?' yatambaye ta yana kallon ta
"Ni bana son can nafison Nan".
Riƙo hannun ta yayi still yana kallon ta yace "yanzu Baby kinfi son kizauna anan ke kaɗai? Why baza ki bini mu tafi tare ba? Idan Daddy yadawo I promise you zan dawo dake kinji?"
Juya kanta tasoma yi cike da shagwaɓa tace "Nooo Yaya bazan je ba".
Kallon ta kawai yake yi cike da tsananin ƙaunar ta da tausayin ta, yasan halin ta idan takafe a abu to dole sai dai kaƙyale ta, be ce komi ba illa sake mata hannu da yayi yasoma tunani, miƙewa ita kuma tayi tana cewa
"Yaya kaci wani abu?"
Bata jira amsar sa ba kuma tasoma kwaɗa ma ƴan aikin ta jira, kankace me sun fito sun gurfana gabanta
"Uban me kuke yi aciki da bazaku Bama Yayana abinci ba?" Tafaɗa cikin ɗaga murya da baya fita, at the same time kuma tana riƙe da ƙugu tana kallon su
Kafin su buɗe baki suyi mata magana Suhaib ya riga su dacewa "come down Baby sun tarbe Ni mana har naci abinci".
Hakan yasaka tasauke hannun ta a ƙugu tajuyo tana kallon sa yasakar mata murmushi, takowa tayi tazauna kusa dashi, sai Suhaib ne yabasu umarnin tafiya don ita bata sake bi takan su ba, daga nan hira suka soma yi har lokacin sallan asar yayi sannan yatashi yayi alwala a Toilet ɗin dake parlour yafice masjid
Ita kuma wajen kayan ta da tazubar tanufa takwashe tanufi ɗakin ta, tana shiga ta'ajiye kayan tafaɗa Toilet tasoma wanka, har Suhaib yadawo yashigo ɗakin nata but tana cikin Toilet bata fito ba, don haka yajuya yakoma parlour.
.
Please🙏🏼
*Share*
*Vote*
*Comments*
[11/13/2020, 2:47 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️ ~What'sapp Number 07065334256~
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON THREE*
_______📖Tana fitowa tashirya cikin ƙananan kaya farar Vest da farar wando Three qweater, komi bata shafa a fuskarta ba tafice dasauri, da gudu take taka matattaƙalan benen har ta'isa cikin parlour'n taƙarisa wajen Suhaib dake zaune yana kallo, Bin ta da kallo yayi har tazauna kusa dashi kana yace
"Kinyi sallah dai ko don nasan halin ki?"
Ɗan ware manyan idanuwanta tayi tana ɗauke kai tace "eh yaya".
Be ce komi ba yamayar da kansa kan kallon sa, ita kuma jingina tayi da jikin sa tana kallon, MBC Action yake kallo ana wrestling🤼, miƙe wa kuma tayi tanufi wajen Fridge taɗauko Apple guda ɗaya tadawo tazauna tana ci idanunta na kan t.v, Suhaib kallon ta yayi sannan yamiƙa hannu ya'amsa Apple ɗin yakai baki yagutsira yamiƙa mata, can wrestling yayi nisa RAUDHA tasoma ihu tana kiran sunan Jonecena ganin yana shirin cin Kevin Owne (KO), shi kuwa Suhaib kallon kawai yake yi abinsa, can da tadame sa yajuyo yana kallon ta yaga tsaban ihu bata ma san tayar da raguwan Apple ɗin ba, ɗauka yayi yasoma ci kafin yace
"Baby kiyi ahankali Mana karki kashe min dodon kunne".
Bata ma san yana yi ba, daga ƙarshe ma gaban t.v ɗin takoma kamar zata shige cikin plasma ɗin, Suhaib sai faman ƙorafin tana kare masa yake yi but taƙi tashi, lokacin da Jonesina yaci kuwa wani irin ihu tasaki tamiƙe tsaye tana tsalle cike da murna, sai kuma tasheƙo wajen Suhaib tana cewa
"Kagani Yaya yaci dama nasan shi zai ci, ina son mutumin nan wlh, kai kuma kafison KO yaci ko?".
Suhaib yace "no nima ai Jonesina ne masoyina".
"A'a Yaya kai dai kafaɗa gaskiya".
Dariya Suhaib yayi yana jan hancin ta yace "wato ƙarya nake miki ko? Kin fiye son kanki da yawa Baby".
Dariya itama tayi tana shigewa jikin sa tace "sorry yaya bazan sake ba".
"Ok".
Daga haka hira suka ci gaba dayi suna ci gaba da kallon su, har sanda aka kira Magriba kafin Suhaib yatashi yatafi masjid, ita kuwa RAUDHA tana nan zaune taci gaba da kallon ta batare da ta damu taje tayi sallan ba ita
Sai da akayi isha'i kafin Suhaib yadawo, lokacin tuni Saude ta gama deener ta jera saman dainnig, don haka yana dawowa kan dainning ɗin suka hau suka ci abinci sannan suka dawo parlour suka dasa hira, sai wajen ƙarfe 10:00pm. Sannan Suhaib yace "su je su kwanta".
Tana shiga ɗakin ta taji ringing ɗin wayan ta, ƙarisawa tayi tazauna a bakin gado tana ɗaukan wayan, ganin sunan Ramcy yasaka tayi peacking call ɗin, daga can side ɗin Ramcy tace
"Hello Babe yakike?".
"Lafiya".
"Nayi ta kiran wayan ki bakiyi peacking ba, lafiya dai ko?"
Sai da takwanta kan gadon kafin tabata amsa da cewa "ƙalau bana kusa ne?"
Ramcy tace "ok yau zamuje Club?"
"No bcoz Yayana yazo sai dai idan ya tafi kuma".
"Ok na gane, sai munyi waya kenan?"
RAUDHA tace "ok byeee".
Daga haka aje wayan tayi tatashi tashige toilet, bata jima ba tafito tanufi ƙofan ɗakinta tasaka keey, wajen Fridge taje tabuɗe da makulli tana duba Wine🍷 ɗin da zata sha, ga sunan kala-kala aciki irin su Champagne, Whiskey, Vodka, Beer 🍺, but bakasafai tafi amfani dasu ba don tafi son ƙwayoyi, ko kuma irin su Cocaine da Codeine su tafi amfani dasu, ɗaukan Champagne tayi kwalba biyu ta'isa kan sofa tazauna, sai kuma tatashi takunna t.v tasanya music tare da ƙure ƙara taɗauko Cup takoma tazauna, waƙar take bi tana zuba Champagne ɗin acikin Cup, sai da tacika Cup ɗin damm sannan tasoma sha tana yi tana sake zubawa idan yaƙare
Acan kuwa ɗakin Suhaib yana kwance yana jin kiɗan da RAUDHA tasaka, shiru kawai yayi yana sauraron Music ɗin yana tunanin halin ƙanwar tasa, kuma yasan halin ta duk abinda tace zatayi babu wanda ya'isa yahana ta koda Daddy ne kuwa, idan har ba itace tabar abun don kanta ba, Allah ya ɗaura mata taurin kan tsiya babu wanda ya'isa yasauya mata ra'ayi, tun farko haka tatashi duk abinda take so shi take yi that's why yanzu ta fi ƙarfin su sai dai su zuba mata idanu tare da nema mata shiriya, and kuma basa ƙaunar laifin ta bare suga fushin ta, suna matuƙar son ta fiye da tunanin me karatu, kar ma ace Daddy yaji, wannan dalilin ne yasaka RAUDHA tasangarce take yin duk abinda ranta ke so
Sai da tashanye gaba ɗaya kwalba biyun da taɗauko, alokacin tuni hankalin ta baya jikinta ta gama buguwa, a wajen barci yaɗauke ta batare da tasani ba, sai ƙarfe 11:30am. Sannan tafarka, shima ɗin Saude ne tazo take ta mata nocking bisa umarnin Suhaib, daƙyar ta'iya buɗe idanuwan ta tana buɗe wa suna rufewa sabida har alokacin giyar da tasha be sake taba, hannu biyu tasanya tariƙe kanta, ta daɗe ahaka kafin tatashi zaune idanuwanta a rufe, ɗaura kanta tayi saman gwiwowin ta still idanun ta arufe tana son komawa barcin, wajen mintuna 30 Saude tasake dawowa tabuga mata ƙofa tana cewa
"Ranki Yadaɗe yallaɓoi na jiran ki ne?"
Buɗe idanuwan ta da sukayi ja tayi tana ɗago kanta, bata amsa ma Saude ba illa miƙe wa da tayi tafaɗa Toilet, tana shiga tasakarwa kanta Shower ko cire kayan batayi ba, ta jima ahaka tana jiƙa kanta da jikin ta kafin tayi wanka tafito, Lotions kawai tashafa sannan tasaka ƴar yaloluwar baƙar riga me dogon hannu da iyakacin ta ƙwaurin ƙafafuwan ta, sai da takwashe kwalban champagne ɗin tasaka a Fridge sannan tarufe da keey kana tasaka Room Slippers tafice
ahankali take taka Steps ɗin benen don har alokacin ba wai giyar ya sake ta bane, idanuwanta da suka kumbure sai faman lumshe su take yi kamar wacce bata iya ganin gaban ta, ahaka taƙarisa kan dainning table inda Suhaib yake zaune har ya gaji da jiran ta ya soma breakfast ɗin sa, zama tayi kan kujeran dake Facing ɗin nasa sannan cikin siririyan muryan ta da kamar tana yin Mura koda yaushe tace
"Good Morning Yaya".
Suhaib da yaɗago kai yana kallon ta yana taunan arish, ƙare mata kallo kawai yake yi har yacinye sannan ya'amsa mata
"Morning dear, how's your night?"
"Fine". Tafaɗa tana gyara gashinta dake rufe mata idanu don bata saka Ribom ba
Shi da kansa yazuba mata breakfast ɗin yatura mata gabanta tasoma ci, ɗaukan tissue yayi yashare bakinsa yana miƙe wa yanufi cikin parlour'n, zama yayi yaɗau wayan sa yana neman layin matar sa
RAUDHA tunda taduƙar da kanta tana tsakalan abincin bata sake ɗago kai ba har sanda tagama tatashi tadawo kusa da Suhaib tazauna, a time ɗin kallo yake yi itama sai tayi joining ɗin sa bayan ta kwantar da kanta a jikin sa
"Yaya How many days before you go?" Tatambaye sa tana ɗago kai takalle sa
Idanunsa akan t.v yabata amsa
"Yau".
"Yau kuma Yaya? Why baza ka bari sai kayi one week ba? Gaskiya bana son katafi". Tafaɗa tana ɗauke kai akansa tare da turo baki
Lokacin ne yajuyo yana kallon ta yace "kema kinsan ina da iyali bazan zauna anan in tare ba, kuma nace ki bini kinƙi ya kikeso in miki?"
Kallon sa tayi sai kawai hawaye suka soma zubo mata, hakan ba ƙaramin ɗaga wa Suhaib hankali yayi ba ganin hawaye a idanun tilon ƙanwar sa, cikin sauri yajawo ta jikin sa yasoma rarrashinta
"Why are you crying my dear? Please stop it".
Ita kuma har sake matso wasu hawayen take yi da hannu, cikin sangarta tasoma cewa "um um ni bazan Dena ba sai idan kace baza ka tafi ba".
Suhaib yace "haba Baby kinsan fa tomorrow Monday Ina da office kinga bazai yiwu in zauna anan ba, but i promise sai dare zan tafi kuma zan fita dake muje yawo tare kinji?"
Daƙyar dai da daɗin baki sannan yasamu tahaƙura
"To tashi kije ki shirya mu tafi".
"To Yaya".
Tatashi dasauri tahaura sama da gudun ta, Suhaib da yabi ta da kallo girgiza kai kawai yayi cikin zuciyarsa yana jinjina hali irin na RAUDHA, sai kuma yasaki murmushi yatashi shima yanufi upstairs zuwa ɗakin sa
Wando pencil tasaka robber fari ƙal, sai tasaka jan riga wanda yatsaya mata iya cinyan ta, gashinta kawai takama da Ribom sannan tasanya hill shoes fari me igiya, tayi kyau sosai duk da batayi makeup ba, fitowa parlour tayi nan ta tarar da Suhaib shima yayi shiga na ƙananan kaya sun matuƙar fito da kyawun sa, tana isowa kusa dashi yakalle ta cikin cool voice yace
"Baby meyasaka kikeson fita kanki abuɗe ne?"
Ɓata fuska tayi batace komi ba, don ita ko acikin kayan ta idan ba Hijabin Sallah ba to ko gyale bata dashi, kuma haka tatashi tun farko take yawon ta ko ina
"Please je ki saka Veil kinji?" Yayi maganar cike da rarrashi
Sai da tatura baki kafin tajuya takoma ɗakinta taɗauko Facing Cap Red colour, a hannu tataho dashi ta ƙi tasaka, sai da tadawo sannan ya'amsa shi da kansa yasaka mata, har da juya mata shi gefe in style sannan suka fice, motar sa suka hau suka bar gidan.
Yawo sosai sukayi har yamma suna can kafin daga ƙarshe suka wuce Shopping yayi mata siyayyan duk abinda zata buƙata da wanda take so, ka ma daga kan suturu kayan makeup dasu Chaculates, buskit e.t.c sannan suka dawo gida
Ƙarfe 80:30pm. Drever yakai Suhaib Airport yahau girgi yakoma Abuja.
.
_More Comments more post._
[11/13/2020, 3:00 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️ ~What'sapp Number 07065334256~
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON FOUR*
_______📖Ƙarfe 90:30pm. Na dare RAUDHA tagama shirin ta cikin ƙananan kaya kamar yanda tasaba, Black Jeans da yellow ɗin riga me hannun vest tasaka, gaban rigan anyi zanen heart❤️ da stune masu ƙyalƙyali, sai tagyara gashinta tasaka Ribom baƙi tafeshe jikin ta da turare masu ƙamshi da ɗaukan hankali, Hill shoes tasaka me igiya shima baƙi sannan taɗau Wizy back ɗin ta da car keeys tafice, tana shiga motan tabata wuta tayi bakin Gate, nan da nan Gate man yawangale mata ƙofa tafice
Cikin tuƙin ta na ganganci ta'isa ƙofar gidan su Ramcy acikin ɗan mintunan da basu gaza 8 ba, tana tsai da motan tasoma danna hon kamar zata tashi garin sabida ƙara, da gudu Ramcy tafito tashige motan taja sukayi gaba, yau kam sun ɗan taɓa hira ba kamar ko yaushe ba, don ita RAUDHA ba kasafai tafiye son surutu ba
Suna isa Club ɗin da suka saba zuwa suka fito sukayi ciki, dama ɗabi'ar RAUDHA kenan duk idan tazo club sai ta tiƙa rawa son ranta sannan ne zata nemi wajen zama, haka ma takasance yau tana shiga tafaɗa cikin masu rawa tasoma girgiza jiki, rawa take yi na ban sha'awa da burgewa, sosai taƙware a rawa wanda ko gasan rawan akaje ita zata cinye, ko wani irin waƙa irin rawan sa take yi
Acan gefe kuwa wani matashin saurayi ne zaune yana faman kurɓan Whiskey Yana kallon ta, murmushi kawai yake zubawa sabida tsananin burgeshin da tayi, har yana tunanin yanda zai je wajen yarinyan tashigo hannun sa, yana nan zaune yana faman kallon ta har yagama kurɓe na cikin Cup ɗin hannun sa kafin yatashi yadoshi wajen, babu zato babu tsammani RAUDHA tana cikin tiƙan rawan ta tana ihun murna taji hannu a kwankwason ta abinda be taɓa faruwa da ita ba, dasauri tajuyo tana kallon saurayin dake gabanta yana faman doka mata murmushi, kafin tasake wani motsi ya riƙo mata hannaye yana faɗin
"Wow Babe you look so cute, kin matuƙar burge Ni fa".
Saurin janye hannun ta tayi tana me buga masa wani banzan kallo batare da tace uffan ba taci gaba da rawan ta, shi kuma memakon yaƙyale ta sai zuwa yayi yasake riƙo ta tare da janyo ta jikin sa gaba ɗaya yana cewa
"Common Baby muyi tare mana".
Wannan karon ma ƙwace jikin ta tayi but batayi wata-wata ba tatsinka masa mari, dasauri yariƙe kuncin sa yana kallon ta da tsananin mamaki, ita ma ɗin kallon sa take yi da kyawawan idanuwan ta fuskarta aɗaure, kaɗa masa hannu kawai tayi alaman gargaɗi sannan taci gaba da rawan ta batare da tasake bi takan sa ba, shi kuwa cikin haushi yake kallon mutanen wajen duk da basu lura da abinda ke faruwa ba, azuciye yanufe ta yadanƙo gashin ta zai wanka mata mari Abokin sa da yake ganin komi yayi saurin damƙe hannun, kallon abokin nasa yayi shi kuma yagirgiza masa kai alamun kar ya'aikata, ita kuwa RAUDHA zafin riƙe mata kan da yayi ne yasanya ta sake taska masa mari cike da tsananin jin haushi
"Whattt.." yafaɗa da ƙarfi idanuwan sa kamar zasu faɗo ƙasa yana ƙoƙarin fizge hannun sa cikin tsawa yace
"Please Deeni kasake Ni in kakkarya yarinyan nan kana ganin abinda tayi min".
Wanda aka kira da Deeni sake riƙe sa ƙam yayi yana basa haƙuri har alokacin kuma ya ƙi sakar mata gashi, RAUDHA kuwa azaba ya ishe ta sabida yanda yake ƙara jan mata, tayi saurin saka hannu tana son fizge gashin ta but ta kasa
sai alokacin su Ramcy dake zaune can nesa suka soma lura da abinda ke faruwa, dasauri tataho ganin da RAUDHA ake yi, itama tana zuwa tasoma janye gashin RAUDHAN amma duk sun kasa ƙwacewa, da yawa mutanen wajen duk sun taru a wajen ana basa haƙuri bcoz yawancin su sun san ita ƴar wanene, wannan dalilin ne yasaka ma babu wanda ke kula su idan sun zo suke cin karen su babu babbaka
Jawad fa yaƙi sakin gashin RAUDHA adole sai ya rama marin da tayi masa, sai fitina yake yi yana son ƙwace ɗayan hannun sa da Deeni yariƙe
Cikin tsananin ƙulewa RAUDHA tace "dan ubanka kasakar min gashina idan ba uwarka tashuka min ba".
Har wani rawa jikin Jawad yake yi sabida tsananin ɓacin rai da irin zagin da tayi masa, wani irin ƙarfi da yazo masa take yahankaɗe Deeni yafuzgo ta yasoma naushin ta, nan da nan matasan wurin suka rufar masa suka riƙe sa ana son ƙwace RAUDHA, a time ɗin har ya farfasa mata hanci da baki sai zuban jini suke yi, hakan ya ɗaga ma RAUDHA hankali sosai tafashe da kuka tana jin wani baƙin ciki na turnuƙe ta, daƙyar aka ƙwace ta a hannun sa Ramcy tayi saurin riƙe ta tana duba inda yafasa mata duk hankalin ta atashe, furzo da jinin bakin ta RAUDHA tayi tana ɗago shanyayyun idanuwan ta da suka gama rinewa sabida tsaban wahala tana kallon Jawad wanda ake ta faman riƙe wa har yanzu be huce ba, bata iya cewa komi ba illa fizge jikin ta da tayi daga riƙon da Ramcy tayi mata tabi hanyan fita da mugun gudu tafice, motan ta tashige ko jiran Ramcy batayi ba tabata wuta tabar haraban Club ɗin, sosai take gudu akan kwalta kamar zata tashi sama sabida tsaban baƙin ciki, tana yi tana share jinin dake zuban mata da bayan hannu, Allah ne kawai yakaita gida da babu abinda zai saka batayi hatsari ba, tana zuwa bakin Gate ɗin tabugi Gate ɗin da motan kamar mara hankali, hon take dannawa akai-akai ɗaya kan ɗaya
shi kuwa Gateman sosai yatsorata da yanda aka bugi Gate ɗin, Bama shi kaɗai ba har ta sauran masu aikin gidan sai da sukayo wajen da gudu don suga meke faruwa, dasauri me gadin yabuɗe ƙaramin ƙofa yana leƙawa don be yi tunanin RAUDHA bace tunda bata taɓa yin hakan ba, ganin motan ta yayi saurin komawa yaja mata gate ɗin, ba don Allah ya tsare sa ba da tuni tataka kansa ta wuce sai yayi wuf yakauce, haka sauran masu aikin ma suka dare da mugun gudu ganin yanda tayi kansu suka bata hanya, ko kashe motan batayi ba bare tayi parcking me kyau tafito tanufi cikin gidan da gudu, Direct ɗakinta tashige tafaɗa kan gado tana kuka, sosai ranta yaɓaci har wani ɗaci-ɗaci take ji a maƙoshinta sabida mugun ɓacin rai, wani irin ƙara tasaki tana miƙewa tasoma wargaza duk abinda ke ɗakin tana yi tana ihu, abunka da taɓararriya abun kuka baya mata kaɗan
Saude da Larai da suka fito daga ɗakin su sukayi cirko-cirko a parlour suna kallon saman suna me jiyo ihun da RAUDHA take yi
Saude tace "yau fa an taɓo Hajiyan mu Allah yasa dai lafiya?"
"Hmm bana tunanin lafiya gaskiya, Yakamata muje mu dubo ta". Cewar Larai tana kallon Saude
Ita kuma zaro idanu waje tayi tace "ke ki rufa mana asiri, muje tahuce akan mu kenan ko? Kinga gwara mu lallaɓa mukoma ciki muyi gumm hakan shi zai fi mana alkhairi don wlh yau ba ƙalau take ba yarinyan nan".
Larai tace "maganar ki dutse fa, Ni fa har na soma barci ƙarar buga gate ɗin da tayi yatashe Ni, wlh na tsorata nayi tunanin ɓarayi ne".
Dariya Saude tasheƙe dashi tana cewa "kai Larai kin cika tsoro wlh".
"To ai tsoro halas ne, wanga buga ƙofa aradun Allah kiris yarage natsure".
Saude in banda dariya babu abunda take mata, itama ɗin dariyan take yi suka nufi ɗakin su suna maida maganar
Gaba ɗaya sai da tagama hargitsa ɗakin kafin tanufi Fridge tajido Wine🍷 tazauna nan ƙasa tasoma kwankwaɗa, sha take yi amma hawaye na kwaranya a idanuwan ta, kawai hango yanda Jawad Yakamata yadunga naushin ta a fuska take yi, abinda ba'a taɓa mata ba koda a mafarki, don ita tunda tataso babu wanda yataɓa ɗaukan hannu yabuge ta a iya tsawon rayuwan ta sai shi, sosai take zub da hawaye duk jinin hancin ta da bakinta da suka fashe ya haɗe da ruwan hawayen ta sun yi mata caɓe-caɓe a face, kuma bata damu ba illa kwankwaɗan giyar da take yi, batasan sanda tashanye kwalba biyar ba don bata cikin hankalin ta, kuma hakan be taɓa faruwa ba don iyakacin ta kwalba biyu-uku bata wuce haka, anan tazube takwanta tana kwarara amai kamar zata zubo da hanjin cikin ta, daga ƙarshe barci ne yakwashe ta bayan ta gama surutan ta.
[11/13/2020, 3:14 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️ ~What'sapp Number 07065334256~
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON FIVE*
_______📖Hasken ranan da yashigo ta windon ɗakinta ne yabugi kyakykyawar fuskarta da yakumbura yayi jazur, hakan yasaka tasoma motsa lumsassun idanuwan ta tana son buɗe wa, daƙyar ta'iya buɗe su sai kuma tamayar tarufe tana me saka hannaye biyu takama kanta sakamakon mugun sara mata da yake yi, ta ɗau tsawon mintuna 10 kafin tasake yunƙurin buɗe idanun, sosai suka sauya kala sukayi ja har wani yalo-yalo suke yi sabida tsaban rinewa, ahankali tasoma motsa jikin ta tana bin ɗakin da kallo, nan taganta cikin aman da tayi tai dame-dame aciki, fuskarta kuma gaba ɗaya ya bushe da jini, abun da yafaru da ita jiya ne yadawo mata ƙwaƙwalwa tayi saurin runtse idanu tana jin zuciyar ta na tafarfasa, batasan iya lokacin da taɗauka ahaka ba kafin tasoma yunƙurin tashi, daƙyar take iya motsawa sakamakon tsamin da jikinta yayi mata sabida kwanciyar da tayi a ƙasa wanda bata saba hakan ba, miƙewa tayi tashige Toilet takunna shower tatsaya ruwan na dukan ta batare da ta cire kayan jikinta ba, lumshe idanuwan ta tayi tana ɗago kanta ruwan na dukan innocent face ɗin ta, sai da tayi kusan mintuna 15 kafin tacire kayan jikinta tayi wanka tafito ɗaure da towel, gaban gadon ta tanufa tazauna tare da ɗaukan jakanta tazaro wayanta tasoma dubawa, 20missed Call taga an mata, duk na Dad ɗinta ne sai kuma na Ramcy tare da Suhaib, miƙewa tayi riƙe da wayan a hannu tafito cikin ɗakin, ahankali take taka Steps ɗin benen tana saukowa, gab da zata isa ƙasa Larai tafito daga ɗakin su, tana ganin ta dasauri taduƙa tana gaishe ta, fuskar RAUDHA babu walwala tabi ta da kallo kana tace
"Kishiga ɗakina ki gyara min".
"To Hajiya". Cewar Larai tana sake rissina mata
Direct ita kuma RAUDHA cikin parlour'n tanufa tashige cikin luntsuma-luntsuman kujeran tazauna, wayanta tasoma latsawa takira Dad ɗin ta, ringing ɗaya yaɗauka cike da matuƙar damuwa a muryan sa yace
"Sweetheart Ina kika shige ne nayi ta kiran ki baki anwer ba? Lafiya dai ko?"
Cikin muryan ta da yasake dishewa sabida kwanan tyles da tayi tace "Daddy lafiya lau ban tashi daga barci bane".
Ajiyan zuciya me ƙarfi Daddy yasaki kana yace "har naji daɗi nayi tunanin ko babu lafiya ne gaba ɗaya hankalina ya tashi".
Shafa kanta kawai tayi bata iya cewa komi ba
"But me yasami muryan ki naji baya fita sosai?"
Shanyayyun idanun ta tasake warewa tana jan hanci cike da jin zafi tace "Daddy a ƙasa na kwana".
"Subhanallah.. Why dear? Kinsan bana Son wani ciwo yakamaki fa".
Nan ma shiru tayi don bata son yawan magana sabida zafin da laɓɓan ta ke mata, ga kuma hancin ta dake zugi
Daddy yasake cewa "Sweetheart bari zan kira doctor Sadeeq sai yaduba ki don nasan mura ne yakama ki".
"A'a Daddy bana so".
Daddy be sake matsa mata ba don yasan halinta sai ce mata yayi "zai sake kiran ta yanzu yana aiki a office ne" daga haka sukayi sallama ta'ajiye wayan takwanta
Tana nan kwance idanuwan ta a lumshe Larai tadawo tasanar mata "ta gama" hakan yasaka tatashi tanufi ɗakin nata tashirya cikin gajeren wando yellow da yatsaya mata iya cinya, wata ƴar yaloluwar farar Vest tasaka tafaɗa kan gado batare da ta shafa koda Lotions bane a jikin ta sabida ko kaɗan bata jin ƙarfin jikin nata, har alokacin giyar da tasha be gama sakin ta gaba ɗaya ba don daƙyar take iya buɗe lumsassun manyan idanuwan ta, hannu tasanya tana shafa laɓɓan ta zuwa wajen hancin ta tana runtse idanu, ba wani ciwo taji ba kawai haɓo ne amma yanda take nuna rakin ta zakayi tunanin dagaske ɗin ciwo yaji mata, tana nan kwance Saude tashigo tasanar mata "Ramcy tana jiran ta a parlour" bata ɗago kai ba tace da ita
"Kice tashigo".
Juyawa Saude tayi tafice taje tasanar wa Ramcy saƙon ta, sai gata taturo ƙofan tashigo idanunta akan RAUDHA da har yanzu take kwance idanunta a rufe, wajen gadon tanufa tazauna agefe tana ci gaba da kallonta tace
"Besty lafiya meke damun ki?" Tayi maganar ne cike da kulawa
Shiru RAUDHA tayi kuma bata buɗe idanu ba bare takalle ta, Ramcy bata damu ba don tasan halin ƙawar tata sai sake cewa tayi
"Nayi ta kiran wayanki baki ɗauka ba shine nataho in duba ki, duk abinda yafaru adaren jiya ya ɗaga min hankali sosai".
Tana ajiye maganar ta RAUDHA tabuɗe kumburarrun idanunta da har yanzu suke a rine takalli Ramcy, fuskarta babu ko ɗigon fara'a hakan yasaka hankalin Ramcy yasake tashi, cike da son rarrashin ta tace
"Don Allah kiyi haƙuri da abinda yafaru karki saka damuwa acikin ranki, duk abinda yafaru yarigada ya wuce bana Son Inga.."
"Wanene shi?" Cewar RAUDHA tana katse mata maganarta da faɗan hakan
Shiru Ramcy tayi tana kallon ta, itama ɗin idanun ta akanta suke tana jiran amsar ta
"Bansan shi ba Gaskiya don baƙo ne awajen".
Shiru ne yagibta a tsakanin su naɗan wani lokaci kafin RAUDHA tatashi zaune tana kawar da kanta daga kallon Ramcy ɗin tace
"Ina son ki binciko min ko shi wanene, ina son insan komi daga gare shi".
Sai tajuyo da kallon ta ga Ramcy taci gaba da faɗin
"Dole zan ɗau fansar abinda yayi min bazan taɓa yafe masa ba, zan nuna masa nafi ƙarfin sa, ki tabbatar kin binciko shi ɗin waye na baki nan da kwana biyu".
Daga haka tamiƙe tashige Toilet tabar Ramcy anan tana Bin ta da kallo.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
Alh. El.Mustapha Makamashi wani hamshaƙin me kuɗin gaske ne wanda duk faɗin garin Kaduna da kewaye babu wanda be san shi ba, babban ɗan Siyasa ne da yayi ƙaurin suna ako ina, ya riƙe muƙamai iri da kala har zuwa matakin gwamna, alokacin da yanemi takarar gwamnan Kaduna Allah be sa yaci ba sakamakon juyin mulki da akayi masa, wannan yasaka yafita siyasa gaba ɗaya yakoma harkan kasuwanci tsundum, Asalinsa Bazazzage ne kuma anan Zaria yake zaune, iyayen sa sun daɗe da rasuwa a hannun kawun sa yataso, shima Kawun nasa yanzu haka ya daɗe da rasuwa, yana da gidajen man fetur sun fi biyar agari mabanbanta acikin Nigeria, kuma yana da Companin haɗa auduga agarin Abuja wanda Suhaib ne ke kula dashi, Allah ya albarkace sa da yara biyu rak Suhaib da RAUDHA, tun RAUDHA na ƴar shekara biyar a duniya Allah ya'amshi ran mahaifiyar su, kuma har alokacin Daddy yaƙi aure sabida ƙaunar da yake ma Matarsa.
Babban Katafaren gidan Alh. M. Makamashi yana cikin K.R.G. ne, gidan da RAUDHA kuma ke zaune mallakin ta ne da Daddyn ta yamallaka mata, dawowarta gidan kuma ya samo asali ne saboda tafiye-tafiyen da Dad ɗin ta yake yi don mutum ne da ba mazauni ba, idan yadawo shine take komawa babban katafaren gidan su acewarta tana jin tsoron gidan.
```RAUDHA```
Duk yanda zan fasalta muku yanda take ta wuce nan, yarinya ce sangartacciya da iyayenta suka ɓata ta da gata tun tana tsunman goyo, sun ɗau son duniya sun ɗaura mata, basa son kukan ta bare fushin ta, hakan yasaka tataso babu ƙwaɓa take yin duk abinda taso, tun tana ƴar shekara 15 tasoma harkan shaye-shaye kuma hakan ya faro asali ne daga ƙawayen ta na school, ita ɗin yarinya ce me son rayuwan ƴanci don haka take yin duk abinda taso akuma lokacin da taso babu me hana ta, daga mahaifin ta har Yayanta suna matuƙar ƙaunar ta fiye da kansu, haɗuwar su da Ramcy tun fara zuwan ta Club ne, ita yarinya ce me son rawa don haka take zuwa sabida nishaɗin ta, anan suka haɗu da Ramcy har tasu tazo ɗaya
Ramcy ƴar talakawa ne amma suna da rufin asiri sosai, itama gangararriya ce sosai agidan su, haɗuwan su da RAUDHA kuma sai abun yaƙara yin yawa, a kayan maye babu abinda basu sha
Dad da Suhaib sun daɗe da sanin halin da RAUDHA take ciki sai dai har yanzu sun kasa hana ta abinda take yi sai fatan shiriya da suke mata, kuma hakan yana faruwa ne saboda basa ƙaunar su ɓata mata.
RAUDHA irin yarinyan nan ne masu bala'in taurin kan tsiya, idan har tace zatayi abu to babu wanda ya'isa yahana ta, idan kuma tace bazata yi ba babu wanda ya'isa yasata tayi, ko kaɗan bata damu da rayuwan kowa ba rayuwanta kawai tasani duk wanda yataka ta to tana ƙoƙarin ɗaukan mataki, bata da sabo ko kaɗan idan har bada mahaifinta ko Ƴayanta ba, har ta da saurayi taƙi yarda tayi sabida a rayuwanta ko kaɗan babu tsarin soyayya, babu namijin da yataɓa burge ta bare har tashiga sabgan sa, ita dai ƙyale ta da harkan shaye-shaye anan tafi auki
Yanzu shekaran ta 19years ne, kyakkyawa ce na gaban kwatance, bata da ƙiban jiki sai dai kuma bata da rama ko kaɗan, kai da ka ganta kasan ita ɗin ƴar hutu ce da jindaɗi, skin ɗin ta fari ne me haɗe da sirkin ja, idanuwanta manya masu gazar-gazar ɗin gashi, haka ma gashin giranta me yawan gaske ne har yana haɗewa, sosai take da kufan gashi ajikinta ko ta ina, kallo ɗaya idan kayi mata baza ka so kaɗauke idanunka akanta ba coz haɗuwarta da tsananin kyawun ta, abu mafi burgewa atattare da ita shine muryan ta, idan tana magana har baza ka so tadena ba yanda muryan ta yake fita ɗan siriri kuma kamar tana mura, hakan na ɗaukan hankalin mutune sosai
Yanzu haka ta gama scondary school🏫 ɗinta tana jiran Admission taci gaba da karatun ta, sosai take da ƙoƙari a makaranta don bata wasa da karatun ta, wannan yasa duk rashin jinta Malamai suna ƙaunarta sosai, kuma ƙoƙarin nata yajawo mata farin jini har take yin duk abinda taso a school ɗin batare da ko harara ta samu ba, sannan kuma ansan matsayin mahaifin ta hakan yasaka da wanda ke sonta don Allah da wanda ke sonta ba don Allah ba duk suna tare da ita.
.
_hmm yanzu me zai faru? Me kuke tunanin RAUDHA zatayi wa Jawad?_
*Vote and comments plz*
[11/13/2020, 3:28 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON SIX*
_______📖 *THE FOLLOWING DAY*
Tashinta kenan daga barcin da tasha tun daren jiya har ƙarfe 02:00pm. Na yau tana sheƙa barci, wanda hakan ko kaɗan baya damunta daɗewan ta tana barci, kuma hakan na faruwa ne idan tabugu takwanta bata iya tashi sai tai ta sheƙa barci kamar za'a sake mata wani daren, ahankali tamiƙe daga kan gadon ta tanufi Toilet tana murza idanun ta, wanka tayi tafito ɗaure da towel ajikin ta, direct gaban dressing mirror tanufa tazauna kan stool tasoma shafa Lotions ɗin ta masu tsananin ƙamshi da tsada, bayan ta gama tamiƙe batare da tasake shafa komi ba tanufi Sif ɗin kayan ta taciro, ƴar shimi tasaka Milk colour da ɗan ƙaramin wandon sa shima Milk taɗau wayan ta tafito, ƙafafun ta babu takalmi haka take taka Steps ɗin benen tana saukowa at the same time tana latsa wayan ta, kan kujerun parlour'n tanufa tashige cikin one sitter tana ɗaura ƙafafuwan ta kan Centre table, latsa wayanta take yi tana girgiza ƙafafu, can taɗago kai tana kwaɗa wa Saude kira, kamar tana jira sai gata tafito ta gurfana gabanta
"Miƙo min Malt".
Tashi tayi tanufi wajen Fridge tabuɗe taɗauko Mata Maltina takawo mata, bata amsa ba kuma bata ɗago kai daga latsa wayan da take yi ba
"Ranki yadaɗe gashi".
"Buɗe". Tafaɗa ataƙaice
Buɗewa tayi tamiƙo mata tasanya hannu ta'amsa, ita kuma tatashi tawuce
Tana nan zaune tana kurɓan Maltinan ahankali tana Chatting wayan ta yasoma ringing, kallon screan ɗin wayan take yi tana ci gaba da kurɓan Maltinan, peacking call ɗin tayi takanga a kunne, daga can Ramcy tace
"Besty komi ya kammala, yanzu haka ina da labarin Saurayin nan".
"Ok ki taho ina jiran ki".
Bata jira cewarta ba takatse wayan tana ci gaba da Chatting ɗin ta
Mintuna 20 sai ga Ramcy ta shigo, zama tayi tana kallon RAUDHA da taɗago kai tasauke shanyayyun idanuwan ta akanta, tasan tana jiran tabata bayanan ne hakan yasaka tasoma sanar mata
"Sunan sa
Jawad Abdullahi yana zaune a Tudun wada, sana'ar sa shine harkan zane kuma shagon sa yana bakin titin gidan su ne, anan koda yaushe za'a iya samun shi, sannan shi ɗaya ne ɗa agidan su kuma shi ke ɗaukan nauyin.."
Tsai da ita tayi da faɗin "wannan bayanin be shafe Ni ba tunda kin gano inda yake".
Sauke ƙafafuwan ta tayi daga kan Centre table ɗin tamiƙe tsaye tana kai komo a tsakankanin wajen, Ramcy kuma sai kallon ta take yi kamar wata baƙuwa agare ta, tasan halin RAUDHA sosai yanzu haka mugun abu take shiryawa aranta, tasan tunda tayi ninyan ɗaukan fansa babu wanda zai iya hanata That's why tayi shiru da bakin ta tana jiran taga abinda zata aiwatar
Riƙe ƙugunta tayi da hannayen ta tana sauke manyan idanuwanta da suka sake ƙanƙancewa akan Ramcy ɗin, cije laɓɓanta tayi cike da tsananin ɓacin rai tace "Ramcy ina zan samu Ƴan daba?"
Ramcy zaro idanuwanta waje tayi tana kallon RAUDHA da lokaci ɗaya tarikiɗe babu ko ɗigon rahma a fuskarta, idanun ta sunyi jazur haka ma fuskarta yayi ja tamkar tattasai, haɗiye yawu Ramcy tayi don ita akwai ta da tsoro, cikin tashin hankali tace
"Me kike shirin aikatawa ne Besty? Kar kuma daga baya asamu.."
"Ban tambaye ki wannan ba, ki sanar dani inda zan samu ƴan daba".
Cike da sanyin murya Ramcy tace "sai dai anemo su tunda kina buƙata".
Murmushi me kyau RAUDHA tasaki tana wani lumshe idanuwa tana buɗewa, kana kuma takoma tazauna tana harɗe ƙafafu tace "good My Besty".
Daga haka tayi shiru tana jingina kanta da kujera talumshe lumsassun idanun ta tana jan numfashi, shiru ne yagibta a tsakanin su ita dai Ramcy idanuwanta na kan ta sai dai tunanin abinda take shirin aikatawa take yi da abinda zai biyo baya
"Bana Son in ganki cikin damuwa ƙawata ki saki ranki". Cewar RAUDHA da tabuɗe idanu tana kallon Ramcy tana me yalwata Innocent face ɗin ta da murmushi
Tasan da cewa tana son Ramcy sosai aranta, haka kawai jinin su yahaɗu shiyasa taɗauke ta tamkar wata ƴar uwanta batare da taji ƙyamarta a matsayin ita ɗin ƴar talaka bace, tayi friends daban-daban ƴaƴan masu kuɗi irin ta amma duk ta watsar dasu duk a dalilin rashin son takura wa kanta, a cewar ta yawan tara friends trouble ne agare ta, tafi son rayuwa ita kaɗai hakan yafi mata daɗi tunda a haka tatashi
Ramcy dai bata iya cewa komi ba sai miƙewa da tayi tana shirin tafiya tace "Besty Ni zan tafi".
Miƙewa itama RAUDHA tayi tana nufan hanyan dainning tace "kizo muci abinci sai ki tafi".
Babu musu Ramcy tabi bayan ta suka zauna a dainning table ɗin, tun ɗazu Saude tagama abincin tajera kuma RAUDHAN na kallo taƙi zuwa taci sai yanzu da taga dama, ita dama cin abincin ta sai taga dama ne, don watarana ma bata ci gaba ɗaya sai dai Saude tazo taɗauke shi yanda ta'ajiye, in kuwa zataci baya wuce sau ɗaya a rana ko biyu, kayan ƙwalan da maƙulashe shine abinda take so, shiyasa bata rabo dasu Chaculates, buskit e.t.c
Ramcy tayi saving ɗin su suka soma cin abincin, babu wanda ke magana cikin su har sanda suka gama, RAUDHA tasoma tashi tana share bakinta da tissue tawuce cikin parlour, ita kuwa Ramcy sai da tacika cikin ta tayi nak kafin tamiƙe tataho wajen ta tana cewa
"To zan tafi Besty".
"Ok". Ta'amsa mata ataƙaice tana latsa wayanta
Hanyan ƙofa tanufa tafice cikin parlour'n
Tana fita itama tatashi tanufi ɗakin ta, Direct gaban drower tanufa tabuɗe taciri tables tawatsa abaki takoma kan gado takwanta tana tsotso, wayanta ta'ajiye tana lumshe idanuwan ta, shiru tayi tana tunani aranta, ta ɗau tsawon lokaci ahaka kafin tabuɗe idanunta da ayanzu suka juye zuwa Red, Remote taɗauka dake kan drower daga kwancen takunna t.v, Bom t.v tasaka da ake waƙa tana me ƙure Volume, tuni ko ina ya game da ƙarar music ɗin, kwanciyar ta tagyara tana me rufe idanuwanta cike da kasala, ahaka har barci yasure ta.
Sai bayan magriba tafarka, daƙyar tatashi tana sakin hamma tanufi Toilet, wanke fuskarta tayi tafito tafaɗa kan kujera, lumsassun idon ta take ta sake lumshewa tana yamutsa fuska, gaba ɗaya jikin ta ciwo yake mata musamman ma kanta, riƙe kan tayi da hannu tana jan siririn tsaki tamiƙe taɗau Remote takashe plasman, wayan ta dake ringing taɗauka ganin sunan Ramcy, nan Ramcy take tambayan ta "yau zasuje Club ne?" RAUDHA tace "baza su je ba". Daga haka takashe wayan ta'ajiye, ita dama tana da zuciya idan har tayi fushi da abu to ta barsa kenan har abada, tuni ta cire ran komawa Club ɗin sai dai su nemi wani kuma
Miƙewa tayi tashige Toilet taɗauro alwala tafito, zama tayi tasoma lissafin sallan da ake bin ta na wajen kwana biyu kenan, sai da tagama lissafin ta sannan tamiƙe taɗau Hijabin sallanta tazumbula har ƙasa tasoma gabatarwa, gaba ɗaya sai da talissafo sallan nan kafin tasallame, bata tsaya wani yin addu'a ba tamiƙe tasauya kaya zuwa na barci tahaye kan gado tarufe jikinta da bargo taɗau wayan ta tasoma chatting, sai da taraba dare kafin takwanta.
Washe gari ƙarfe 11:30am. Tatashi, wanka tayi tasaka ɗan guntun wando iya cinyan ta baƙi me baza a ƙasan, sannan tasaka have-Vest ɗin wandon shima baƙi, Ash colour ɗin Jarket mara nauyi taɗaura asaman have-Vest ɗin wanda yatsaya mata iya setting wandon, tafeshe jikinta da turare tare da ɗaure gashinta da jelan a tsakiyar kai, tasaka Room Slippers taɗau wayan ta tafito parlour, directly kan dainning table tanufa taja kujera tazauna, Tea cup tahaɗa me zafi tasoma sipping tana faman latsa waya
Wajen mintuna 30 tana nan zaune kafin taɗago kanta tana ƙwala kiran masu aiki cikin dashashshiyar muryan ta, shiru babu wanda yafito don haka tamaida kanta taci gaba da danna wayan ta, sai da tagama abinda take yi sannan tamiƙe tadoshi hanyan ɗakin su Saude, tana zuwa tahankaɗa ƙofan tashige.
.
_Yanzu cakwakiyan yasoma_
_plz ku ƙara yawan comment don Allah, karku manta da danna *Vote, share.*
[11/14/2020, 7:42 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON SEVEN*
_______📖Su Saude dake zaune suna kallo a wayan Larai suka ɗago kai dasauri suna kallon RAUDHA, ko waccen su nan da nan tashiga hankalin ta coz sun san bata shigowa cikin ɗakin su idan har ba wani laifi sukayi mata ba, shanyayyun manyan idanuwan ta tasauke akan su tana bin su da kallo, sai da tagama ƙare musu kallo cike da isa tace
"Uban me kuke yi da har zan kira ku ku kasa amsa min?"
Zuru-zuru sukayi da ido suna kallon ta, sai Larai ne tayi ƙarfin cewa
"Kiyi haƙuri Hajiya wlh bamu ji bane".
Dogon tsaki taja tace "ki shirya kizo in aike ki supper market".
Idanunta dake kan Saude shiyasa tagane da ita take yi
"To ranki yadaɗe". Cewar Saude tana miƙewa dasauri
Ita kuwa juyawa tayi tafice tanufi ɗakin ta, bata daɗe da zama ba Saude tashigo, kuɗi tamiƙa mata tafaɗa mata abinda zata siyo mata tafice, wayan ta taɗauka takira Ramcy, ringing ɗaya taɗauka
"Ramcy kibar aikin nan kawai".
Cike da mamaki Ramcy tace "meyasa?"
RAUDHA tace "na sauya shawara ne, zan kira ki anjima yanzu zan fita bye".
Ƙitt takashe wayan ta'ajiye, tashi tayi taɗauko Socks baƙi tasaka, dogo ne da yatsaya mata har gwiwa tasanya Hill shoes black me igiya, wayan ta tasake ɗauka takira Mahaifin ta yana ɗauka tace
"Daddy Ina buƙatar kuɗi".
"My dear me zakiyi da kuɗi haka?"
"Dad Kai dai kabani akwai abinda zan yi dashi ne". Tafaɗa a shagwaɓe
"Ok to bari in tura miki".
Tana katse kiran babu daɗewa taji Alarm ya shigo, HangBag ɗin ta taɗauka tafice, dasauri-sauri take taka Steps har tasauka tabar Parlour'n, a compound tatsaya tana gyara ɗan silin gashin ta da yasauko mata wajen ido, jakan ta tabuɗe taciro wani faskeken Eyeglasess baƙi tasaka, ko kaɗan bataji ɗar ɗin fita da kayan jikin ta ba don tarigada tasaba, sai dai ta zuge zeey ɗin Jarket ɗin ta rufe iya cikin ta dake waje, mota tashiga tabar gidan.
Bank 🏦 tafara zuwa taciri kuɗi sannan tanufi police station👮, tana yin parcking tafito takulle motan, gaba ɗaya duk mutanen dake haraban Station ɗin babu wanda idon sa be kai kanta ba kuma duk kallon da ake mata ba wanda yake mata kallon musulma sai dai waɗanda suka san ita ɗin wacece, kallon ta kawai ake yi ita kuwa ko ajikin ta tanufi ciki cike da tafiyan ta me burgewa
Tana shiga duk ma'aikatan dake zaune wajen suka yi mata caa da idanu, daga masu haɗiyan yamu sai masu sakin baki kamar zasu cinye ta, bata kalli kowa ba tanufi Office ɗin DPO kanta tsaye kuma duk acikin su babu wanda yayi yunƙurin yahana ta
Nocking tayi aka bata damar shiga tatura ƙofan tashige, DPO dake duba wasu files a gaban sa yaɗago kai, dasauri kuma yatashi tsaye yana faɗaɗa fuskarsa da fara'a yace
"A ah Ranki yadaɗe kece yau a office ɗin mu? Barka da zuwa zauna mana".
Babu musu tazauna tana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya taɗaura HangBag ɗin ta a jikinta, shima komawa yayi yazauna yana sake mata Barka da zuwa, sannan yaƙara dacewa
"Ranki yadaɗe da kanki yau Alhaji ya aiko?"
Yana nufin mahaifin ta sabida mutumin sa ne kuma shine yasama masa aiki lokacin da yake ganiyan Siyasan shi, shiyasa duk abinda Daddy yanema awajen sa yana masa da gaggawa sabida albarkacin muƙamin da yaɗaura sa akai
Zare Eyeglasess ɗin ta tayi sai ga kyawawan lumsassun idanuwan ta sun bayyana, cikin muryan ta me daɗi ga kowa tace "No DPO wannan aikina ne".
DPO dake haɗiyar yawu kamar wanda zai cinye ta sabida kafe ta da idanu da yayi, yasake washe baki yace "to ranki yadaɗe wani aiki kenan za'a yi miki?"
Murmushi tayi me zautar da mutum kafin tace "Wani yaro nake so ku kama min shi, ina son ku hukunta shi bisa laifin Fyaɗe da yai ninyan min, sannan bana son ku bada belin shi har sai anzo an bani haƙuri".
"Ai baki da damuwa ranki yadaɗe duk abinda kikace shi za'ayi, aina yaron yake?"
Kamar yanda Ramcy tasanar da ita bayani akan sa haka itama tafaɗa masa, sannan taƙara dacewa "wannan maganan Ni da kai ne DPO, ko Daddyna bana son kasanar masa".
Sai kuma tabuɗe Jakan ta taciro maƙudan kuɗi ta'ajiye masa batare da ta furta komi ba, shi kuwa cikin tsananin murna yaɗau kuɗin yana kallo, sai kuma yamaida idanun sa kan ta yana lanɗe baki, Allah ya sani yafi buƙatar ta akan kuɗin nan, duk da yawan kuɗin da ace zata riƙe tabashi kanta da yaji daɗi fiye da bashi kuɗin da tayi, sai dai bazai taɓa iya nuna mata maitan sa ba gudun samun matsala, don yasan aikin sa ma da yake taƙama dashi zai iya rasa shi, yasan cewa rijiya ba wajen wasan makaho bane, yanzu sai yajawo ma kansa gobarar da bazai taɓa iya kashe sa ba
Muryan RAUDHA yakatse masa tunanin sa, yayi firgigit yana kallon ta da har ta rigada ta tashi, shima dasauri yatashi yana cewa
"Ai ranki yadaɗe yanzu ma zamuje har dani don mu soma miki aikin ki da wuri".
Murmushi tayi tace "nima ina son in bi ku".
"Ok babu matsala muje". Cewar DPO yana yin gaba dasauri kamar ana hankaɗa shi yabuɗe mata ƙofa
Sai da tafice sannan yabi bayan ta, tare da wasu ma'aikatan su biyar suka tafi, motan su ne agaba nata abaya suka nufi anguwan su Jawad
Suna zuwa da tambaya aka nuna musu shagon sa, huɗu daga cikin ƴan sandan ne suka shiga shagon, babu zato babu tsammani Jawad dake aikin zanen sa yaji anyi ram dashi, dasauri yajuyo yana kallon kwalawan dake tsaye kan sa biyu sun riƙe sa, miƙewa yayi jiki na rawa yasoma tambayan su abinda yayi
Ɗaya daga ciki yabuge masa baki yace "idan mukaje zakaji wuce muje".
Turjiya yasoma nuna musu suka hangaɗa shi sukayo waje dashi, lokacin ne Deeni abokin sa yaƙariso wajen don har an kai masa rahoton ga ƴan sanda can a shagon Jawad, dayake shima Shagon sa yana layin anguwan ne, ganin za'ayi wajen mota dashi Deeni yayi saurin zuwa yana cewa
"Dan Allah ranku yadaɗe me yayi zaku tafi dashi?"
Wani kallo ɗan sandan cikin su yayi masa yace "idan kuka biyo mu Office zakuji".
Jama'a sun taru ana ta tambayan ba'asi amma firr ƴan sandan nan sun ƙi magana sai son tura Jawad suke acikin mota, shi kuma ya dage akan lallai bazai shiga ba tunda yasan be yi komi ba duk da akwai tsoro a tattare dashi
Lokacin DPO yafito a mota yana cewa "wai ya gagare ku ne?"
RAUDHA dake cikin mota zaune tana kallon duk abinda ake yi sai faman cije laɓɓa take yi tana sakin murmushi, sai da taga an saka sa cikin mota sannan tafito tana gyara zaman Eyeglasess ɗin ta, nufan wajen tayi cikin tafiyan ta me ɗaukan hankali, nan kuwa sauran mutane suka maida kallon su gare ta har sun manta me ma ake yi
Deeni tunda yahango ta yasha jinin jikin sa, dama ya rina aransa dole ne abokin sa yafuskanci hukunci duk ranan da tajuyo kansa, shi yarigada yasanta yasan waye ita sabida ya daɗe yana zuwa Club ɗin
Tana zuwa wajen ƴan sandan suka matsa mata hanya ta'isa jikin motan tana kallon Jawad da shima yake kallon ta, sai dai nashi kallon na rashin sani ne don ba wani sanin ta yayi ba, bare cikin club ɗin akwai duhu sosai, cire Eyeglasess ɗin ta tayi tana sake ƙare masa kallo tana murmusawa, batace komi ba kuma takalli DPO tace
"Daga nan zan wuce gida DPO, ku gana masa azaba sosai bana son ko kaɗan ku raga masa".
Daga haka tajuya batare da tasake bi takan su ba tanufi motan ta tashige taja tabar musu ƙura nan, ƴan sandan har suka shige su ma suka ja tasu motan Jawad kallon motan ta yake yi, har alokacin ƙwaƙwalwan sa be kawo masa inda yasanta ba duk da kuwa yaso yagane muryan, shi dai mamaki da yarufe sa ne yasa yamanta ahalin da yake ciki har suka tafi dashi
Jama'an wajen kuwa sai mayar da zance suke yi sun kasa sanin meke faruwa, wasu kuwa har sun rigada sun bata laifi sai zagin ta suke yi suna cewa "dama haka ƴaƴan masu kuɗi suke, don sunga sunfi ƙarfin mutum sai su nemi su takasa koda laifi kayi musu a rashin sani" wasu kuma wajen Deeni suka nufa suna tambayan ba'asi, amma shi hankalin sa duk atashe yake be saurare su ba yayi hanyan gidan su Jawad ɗin, wasu daga ciki suka rufa masa baya don jin ƙwaƙwaf.
Har ta kai anguwan su sai kuma tajuya kan Motan tanufi gidan su Ramcy, a bakin ƙofar gidan tayi parcking tafito tarufe motan tashige cikin gidan kanta tsaye
Gidan madaidaici ne me ɗakuna biyar dasu Toilet da kichen, gidan yana da kyau irin dai na masu rufin asiri, Mahaifiyar Ramcy ta daɗe da rasuwa sai Amaryan Baban su take riƙe ta, su huɗu ne wajen mahaifiyar tasu, biyu maza sai ɗaya mace da tayi aure sannan ita Auta, Mahaifin su Dattijo ne sosai kuma itama Amaryan da ya'auro dattijuwa ne don bata taɓa haihuwa ba
Kasancewar Baban su na tafiye tafiye yana sana'ar Gwari wannan yasaka Ramcy take yin duk abinda taga dama, don bata jin tsoron yayyin nata bare Amaryan Baban su
RAUDHA na shiga tanufi ɗakin Ramcy ɗin tabuɗe labule tashige, ɗakin yayi kyau sosai dai-dai na budurwa me ji da kanta, kuma duk RAUDHA ce tasiyan mata duk abinda ke cikin ɗakin, har ta dana Amaryan Baban nasu sai da tasauya mata kayan ɗaki, shiyasa babu wanda be san ta ba agidan, kuma hakan yasaka wani lokacin basa matsa ma Ramcy idan sukaga ta fita don sun san can wajen RAUDHA take zuwa
Babu kowa cikin ɗakin sai tatsaya tana ƙare wa ɗakin kallo na tsawon daƙiƙu sannan tanufi kan katifa tafaɗa har da takalmin ta da bata cire ba, numfashi taja me ƙarfi tana lumshe kyawawan idanuwan ta.
Ramcy ce tashigo cikin ɗakin, ganin RAUDHA abun ya bata mamaki, dasauri taƙarisa kusa da ita cike da farin ciki tace
"Besty yaushe kikazo?"
Lokacin ne RAUDHA tabuɗe shanyayyun idanuwan ta tasauke kan Ramcy ɗin, memakon ta'amsa mata tambayan ta sai cewa tayi "ina kika shiga nashigo bakya nan?"
Ramcy tace "na shiga bayi ne wlh".
"Ok". Tafaɗa tana ɗauke kanta daga kallon Ramcy ɗin
"Besty me zakici in kawo miki?"
"Babu". Tafaɗa ataƙaice tana tashi zaune
Ramcy tace "yanzu dama nake tunanin kiran ki ashe zakizo, zan kira ki in sanar miki bikin da nace miki zani a Kaduna ya matso".
Kallon ta RAUDHA tayi kamar baza tace komi ba sai kuma tace "yaushe ne kenan?"
"Wannan satin amma sai ana gobe zan tafi".
Gyaɗa kai kawai RAUDHA tayi tana ɗaukan wayan ta tana latsawa, hira Ramcy tafara mata tana jinta bata amsa ba har sanda tagama abinda take yi a wayan taɗago kai tana kallon ta, cikin yatsina tace "zan biki mu tafi tare".
"Dagaske kike yi don Allah?" Ramcy tafaɗa cike da zumuɗi".
Murmushi RAUDHA tayi tana gyaɗa mata kai
"Wow besty naji daɗi wlh, dama Ni kaɗai ne zani don Aunty Nafeesa tace min bata jindaɗi baza ta je ba tunda tare zamuje da ita".
"Me yasame ta?" RAUDHA tafaɗa cike da kulawa tana kallon ta
"Wlh tunda tasami cikin nan abun dai babu daɗi, gashi har ya shiga wata shida bata dena ciwo ba".
"Ok Muje ki rakani in gaishe ta". RAUDHA tafaɗa tana miƙewa tsaye
Tashi itama Ramcy tayi taɗau gyalen ta suka fito waje
Da Amaryan Baban Ramcy sukaci karo tana fitowa daga ɗaki
"A'a babbar baƙuwa mukayi ne?" Cewar Amaryan Baba tana faɗaɗa fuskarta da fara'a
Murmushi RAUDHA tayi cike da rashin tarbiyyar da be ishe ta ba tace "Yakike?"
Murmushi Amarya tayi tace "lafiya lau RAUDHA, ya gidan naku?".
"Lafiya". Ta'amsa ataƙaice
Ramcy tace "Zamuje gidan Aunty Nafeesa ne?"
"To adawo lafiya".
Daga haka suka fice tabi bayan su da kallo tana murmushi, aranta tana tunanin yanda yarinyan take shigan banza babu me kwaɓa mata, tana da kirki sai dai babu tarbiyya ko a ido aka ganta an san haka, wuce wa kichen tayi aranta tana nema musu shiriya gaba ɗayan su
Duk da gidan babu nisa amma a mota suka je, bayan sun kai lungun gidan su Aunty Nafeesa inda mota bata shiga sai suka fito suka soma takawa a ƙasa, wani babban kwata suka zo tsallaka wa RAUDHA sai toshe hanci take yi tana yatsina fuska, abinda yake sawa bata zuwa anguwan kenan saboda wannan mummunan kwatan dake bata tsoro
Daƙyar tatsallaka shima sai da taimakon Ramcy, mutanen dake wajen kuwa sun kafo musu idanu sun saki baki suna kallon abun mamaki
Sun ɗan yi tafiya da suka shiga lungun sannan suka isa gidan Aunty Nafeesa, ita kaɗai ce agidan kuma ba wani babban gida bane, gida ne me ɗakuna biyu da Ban-ɗaki da kichen.
[11/14/2020, 8:02 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
_wannan shafin naku ne masoyan Littafin RAUDHA, ban taɓa tunanin laittafina yana da ɗumbin masoya haka ba sai yau, gaskiya naji daɗi, kuci gaba da sporting ɗina Ni kuma zan ci gaba da suburbuɗo muku me daɗi wanda zai saka ku farin ciki, nagode 🤙🏾 😉_
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON EIGHT*
_______📖Suna shiga ciki Ramcy tarangaɗa sallama
Aunty Nafeesa dake kwance saman kujera ta'amsa musu tana tashi zaune daƙyar
Su kuma lokacin ne suka shigo cikin ɗakin
Aunty Nafeesa tana ƙyalla idanu taga RAUDHA dake bayan Ramcy tafaɗaɗa fuskarta da fara'a tana cewa "kai kai kai yau RAUDHA ce a gidana?"
RAUDHA kuwa murmushi tayi tasami kujera taɗan ɗofana akai kamar wacce take jin tsoro
Ramcy itama zama tayi tana cewa "Aunty cewa tayi in kawo ta tagaishe ki".
"Allah Sarki ai kuwa na gode sosai".
Sai lokacin ne RAUDHA tabuɗi baki ahankali da muryan ta adishe tace "ya jiki?"
Cike da fara'a Aunty Nafeesa tace "Alhmadulillah RAUDHA, kina lafiya?"
Gyaɗa kanta tayi tana wasa da igiyoyin wandon ta (bazar)
"Rahma ɗauko mata ruwa mana".
Miƙewa Ramcy tayi tabuɗe ɗan ƙaramin Fridge ɗin dake ɗakin taciro fure water guda biyu taɗaura akan Fridge ɗin, sai da tarufe sannan taje taɗauko plate tajera ruwan takawo gaban RAUDHA ta'ajiye, ita dai kallon ruwan kawai take yi batare da ta motsa ba
"Besty kisha ruwa". Cewar Ramcy tana kallon ta da murmushi
Ɗan kwaɓe fuskarta tayi kawai tana girgiza mata kai alamun baza ta sha ba
Ƴarinyan Aunty Nafeesan ce tashigo ɗakin aguje, sai tatsaya kawai tana kallon su Ramcy, sai kuma tamaida idanun ta kan RAUDHA da itama takafe ta da idanu, ga duk kan alamu yarinyan bata gane ta ba don tasan Ramcy sosai, sai tanufi wajen ta tana ɗaura ƴan ƙananun hannayen ta saman cinyan RAUDHA, dai-dai wajen tsakankanin inda wandon ta da Socks ɗin da tasa basu rufe ba, sai kuma takoma tana wasa da bazar ɗin wandon
Ramcy tace "ke uwar ki tashi awajen nan".
Yarinyan kamar bataji ba sai tasake matsawa sosai wajen RAUDHA tana tattaɓa ta, ita kuma RAUDHA sai janye jikin ta take yi kamar taga abun tsoro, duk da yara suna burge ta amma bata son ko kaɗan su zo kusa da ita sabida suna bata tsoro wani lokacin idan suka cika ƙanƙanta, bare kuma wannan itama ƴar ƙanƙanuwa ce don baza tafi 2yrs ba
Ganin dai baza ta dena taɓa ta ba sai tazare mata manyan idanuwan ta tana hararan ta tare da matse jikin ta waje ɗaya, ko kunyan akwai Maman ta awajen bata ji ba
Aunty Nafeesa kuwa murmushi kawai tayi tamiƙe tana janyo hannun yarinyan tace "zo nan Khadeeja, bakiga baƙuwa bace?"
Ɓata fuska Khadeejan tayi tasoma gwarancin ta, sai kuma taƙwace hannun ta tana ficewa da gudu
Ajiyan zuciya RAUDHA tasaki wanda hakan yasaka duk suka kalle ta, ita kuma bata ma san suna yi ba
"Kin ƙi shan ruwan RAUDHA, gashi kuma babu abinci"
Yaƙe tayi tana sake girgiza kanta, sai kuma tace "a'a anty na ƙoshi ne".
Ramcy tace "Aunty tare da besty zamuje bikin Shatu fa"
"Haba dai don Allah dagaske?"
"Wlh kuwa tace zataje".
Murmushi Aunty Nafeesa tayi tace "Allah Sarki mun gode kuwa, idan kinje sai kigaishe ta dakyau ki faɗama Mama bani da lafiya ne, nima dai zan kira ta awaya in sanar musu".
RAUDHA miƙe wa tayi tana kallon su, hakan yasa itama Ramcy tamiƙe tana cewa
"Aunty mu zamu tafi, zan faɗa mata insha Allah".
Itama tashi tayi daƙyar tana cewa "to muje in taka muku".
RAUDHA da taciro kuɗi cikin jaka tamiƙa wa Aunty Nafeesa tana cewa "gashi anty".
Kallon kuɗin me uban yawa tayi tana cewa "ah RAUDHA har da ɗawainiya?".
Murmushi RAUDHA tayi
Kuɗin ta'amsa tana ta mata godiya cike da farin ciki, fitowa sukayi gaba ɗayan su Aunty Nafeesa sai sake mata godiya take yi aranta tana yaba halin kyauta irin na RAUDHA
Wani matashin saurayi ne yashigo gidan yana taje kansa da kumb, tsayawa yayi akan hanya yana kallon su gaba ɗaya kamar yanda suka tsaya su ma suna kallon sa, sai yarausayar da kai yana sauke idanun sa kan RAUDHA
"Aunty Nafeesa wannan kuma fa? aina kuka samo mana inyamura har cikin gida?"
Sai kawai tasaki baki ita da Ramcy suna kallon sa a yanayin tsoro
Ita kuwa RAUDHA naɗe hannayen ta a ƙirji tayi tana zuba masa lumsassun idanun ta da bata iya buɗe su sosai
Zai sake magana Ramcy tayi saurin katse sa da faɗin "haba don Allah Yaya Abba, tare fa mukazo da ita ina ruwan ka da ita?" Taƙarike maganar ta tana hararan sa
Washe baki yayi yace "eyya ai bansani ba my dear, shiyasa wlh nake ƙara son ki sabida wannan farin da kike min da ido🤒😅, wai yaushe ne zaki bani dama ne nariƙa zuwa gidan ku? kinsan son da nake miki Rahma bazan iya rabuwa dake ba, ki daure kiduba maganata"
Ramcy turo ɗankwali gaba tayi cike da jin haushin sa, tasan halin sa sarai zai iya tsokano RAUDHA yanzu abu yacaɓe musu idan har basu rabu lafiya ba, don haka tace "kabar wannan maganan idan muka sake haɗuwa zamuyi magana yanzu ina da baƙuwa".
Cike da jindaɗi Abba yamatsa musu a hanya yace "yauwa masoyiya to shikenan sai mun haɗu ɗin, zan Bama Aunty Nafeesa saƙo sai ki amsa a wajen ta".
Yatsina fuska tayi kawai tawuce don tuni RAUDHA tafice abinta tunda yamatsa musu a hanya
Sai da Aunty Nafeesa tabi su har ƙofar gida tasake ɗaga musu hannu kafin tashige gida
Suna zuwa wajen motan suka shige RAUDHA taja suka tafi, a ƙofar gidan su Ramcy tatsaya taɗau jakan ta tabuɗe taciro kuɗi tamiƙa mata
Gashi ki Bama Amarya Ni zan tafi bazan shiga ba, gobe sai kizo ke ki amsa naki sai ki siya duk abinda kike buƙata a bikin, ban da ishashshen kuɗi anan".
Murmushi Ramcy tayi ta'amsa tace "thanks Babe Allah yabar mana ke".
RAUDHA riƙe sitiyarin motan tayi tana kaɗa yatsunta akai batare da tace uffan ba, ita kuma Ramcy ganin haka yasa tabuɗe motan tayi mata sallama tafice sannan taja motar tatafi.
Itama Ramcy halayyan su ɗaya da RAUDHA na rashin kula maza ko kaɗan babu ruwan su da shiga shirgin namiji, wannan dalilin ne yasaka RAUDHA tasake yarda da Ramcy tazama ƙawarta tunda halin su ɗaya, kuma shiyasa take mata duk wani abu ba sai ta buƙata wajen samari ba, duk da iya ƙoƙari dai mahaifin ta yana mata duk abinda tatambaye shi in dai yana da halin yi zai yi mata.
Cikin ƙanƙanin lokaci RAUDHA ta'isa gida, tana yin parcking tafito tarufe ƙofan tanufi cikin gidan, Direct ɗakinta tanufa, tana shiga taci karo da Babban baƙin leda ajiye saman Centre table dake kusa da kujera, siyayyar da Saude tayi mata ne
Kan gado tafaɗa tana sauke ajiyan zuciya, gaba ɗaya duk ta tara ma kanta gajiya a ɗan wannan fitan da tayi, sai faman yamutsa fuska take yi duk tana jinta babu daɗi sakamakon mummunan ƙaton kwatan nan na anguwan su Aunty Nafeesa da tagani, miƙe wa tayi a yanayin gajiya tafara cire kayanta tashige Toilet, wanka tayi sosai wanda yaɗauke ta tsawon lokaci kafin tafito, shiryawa tayi cikin Shuɗin Vest da baƙin Leggings takoma Kan kujera tazauna, buɗe ledan tayi tana duba duk abinda ke ciki, kayan zaƙi ne kala da iri su Chaculates, Biscuits, sweets da sauran su, ɗaukan Sweet tayi tabuɗe tasoma sha tatashi tanufi wajen gadonta taciro wayan ta cikin jaka, komawa kan kujeran tayi tasoma latsa wayan takira Daddyn ta, yana peacking tace
"Daddy Good Evening".
"My daughter kina lafiya?"
"Lafiya Daddy ya aikin ka?" Tace hakan tana lanɗe baki
"Me kike ci haka ki tsanmin my dear?" Daddy yafaɗa cike da ƙaunar yarinyan tasa
RAUDHA dariya tayi har fararen haƙoran ta suna bayyana tace "Daddy sweet ne".
"Oh Daughter ba na hanaki Shan kayan zaƙi ba?"
Cikin shagwaɓa tace "Daddy ai bana sha, wannan yanzu ne nasiya nasha".
"Ok to ki kula bana so, kinsan nafison lafiyan ki".
RAUDHA tace "ok.. Daddy zan bi Ramcy Kaduna ana bikin Cousin ɗin ta".
"Kaduna kuma Daughter?"
"Eh Daddy". Tafaɗa tana marairaice murya
Daddy yace "ok to shikenan but Sweetheart ki kula da kanki uhmm?"
"To Daddy Kai fa yaushe zaka dawo?"
"Zuwa nan da One Month insha Allahu ina tare dake my sweetheart".
Kuka tasaki cikin taɓara, nan da nan hankalin Daddy yatashi yasoma tambayan ta
"My daughter lafiya menene faɗa min mana kiyi shiru kinji?"
Cikin kukan take cewa "Daddy har sai One Month zaka dawo? Gaskiya Ni bazan yarda ba sai na biyo ka".
Cikin rarrashi Daddy yace "sorry My Baby umm? Kinga inada aiki sosai ne kuma zan wuce Chaina wani Business Ni da abokan aikina, zan yi two weeks acan kinga zan iya kai wata ɗaya kafin in dawo".
Tsalle tabuga akan kujeran tana cewa "Daddy Chaina?"
"Yes my dear".
Cike da tsananin murna tace "Daddy please kaje dani ina son zuwa".
Murmushi yayi don yasan babu ƙasar da tafi so sama da Chaina, Allah ya ɗaura mata son ƙasar kamar ranta, tana son duk wani abu da yadanganci can ɗin kuma sau ɗaya tataɓa zuwa, sai da tayi wata ɗaya acan ita da Daddyn ta har yaren sai da tasoma koya a lokacin, daga wancan zuwan bata sake komawa ba
"Kar ki damu Babyna kibari idan kin soma zuwa school kuna samun hutu acan zakiyi Holiday ɗin ki".
"Yeeeee Daddy I Love you so much".
Tabuga masa Kiss 😘 ta wayan cike da tsananin murna
Dariya Daddy yayi yace "I love you too my dear Daughter, ki huta kinji sai anjima zamuyi waya".
"To Daddy Byeee".
Daga nan katse wayan tayi tana ajiyewa cike da farin ciki.
.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
Yau kwana uku kenan da kama Jawad, idan kuka ganshi baza ku iya shaida shi ba sabida dukan da yake sha duk sun sauya masa kamanni, kuma an ƙi barin kowa yaganshi
A ranan na huɗun ne daƙyar DPO yayarda yagansu, Mahaifiyar Jawad ɗin ne tare da Deeni suka zo, duk iya magiyan da sukai masa sam ya hanasu ganin Jawad kuma yaƙi bada belin sa, daga ƙarshe sai ce musu yayi su je can su nemi RAUDHA su bata haƙuri sannan idan ta yafe sai asake shi
Babu yanda suka iya suka fito suka nufi gidan su RAUDHA, babban katafaren gidan mahaifin ta sukaje don nan Deeni yasani, sunyi bugun duniya amma an ƙi buɗe musu ƙofa, sun fi awa ɗaya a wajen ko zasuga wani yafito amma babu kowa dole suka tafi gida da niyyar gobe su bugo sammako su dawo.
[11/14/2020, 8:15 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON NINE*
_______📖Ƙarfe 11:30am. Suka bugo sammakon komawa ƙofar gidan, yau ma sunyi bugun duniya amma shiru anƙi buɗe musu ƙofa, wasa-wasa sai da suka share fiye da awanni biyu a wajen suna jiran tsammanin marabbuka
Can daga ƙarshe da sukayi ta bugun ƙofan sai gashi an buɗo ƙaramin Door ɗin wani shirgegen mutum ya fito fuska a ɗaure, Me gadi ne kuma tun sanda suka soma buga ƙofan duk yana ji amma yaƙi fitowa a tunanin sa masu maula ne tunda sun saba zuwa, koron duniya idan yayi musu sai gobe ma sun sake dawowa kasancewar Alh. Mustapha mutum ne me kyauta sosai, abun hannun sa baya rufe masa idanu kuma a wajen shi RAUDHA takoya, don tacire maƙudan kuɗi ta kyautar hakan ba komi bane
"Wai uwar me za'ayi muku kuke ta bugun ƙofa? An ce muku Alhajin baya nan amma tunda ku mahaukata ne baza ku dena zuwa ba". Me gadi yafaɗa hakan yana bin su da uwar harara kamar yamaƙure su yake ji sabida tsaban takaici
"Bawan Allah ba abinda kake tunani bane yakawo mu, mun zo ganin Hajiya ne". Cewar Mahaifiyar Jawad cike da muryan tausayi
Me gadi sake bin su da kallon ƙasƙanci yake yi kamar ma be ji me suka ce ba yace "Hajiya..? Kuke neman Hajiya wata Hajiyar kenan?"
Tace "Yarinyan Alhaji".
Dogon tsaki yaja don takaici be tsaya sake jin me zasu ce ba bare yabasu amsa yajuya da ninyan komawa
Deeni yayi saurin matsawa kusa dashi yace "don Allah kataimaka mana kayi mana magana da ita, itace tace har sai munzo mun bata haƙuri kafin tasaka asaki Abokina da ƴan sanda suka kama".
Sai alokacin me gadi yaɗan dakata daga rufe ƙofan da yasoma yi, fuska babu walwala yace "to babu ita anan, ku neme ta acan gidan ta".
Sai da suka sake roƙon sa gaba ɗayan su don yafaɗa musu inda gidan ta yake, daƙyar yasanar dasu shima ɗin sai da yagama musu wulaƙanci da faɗa musu baƙaƙen maganganu
Daga haka dai basu iya cewa komi ba suka juya suka tafi, Napep suka hau yakai su har Zaria Locost inda gidan RAUDHA yake
Bayan sun sauka suka nufi bakin Gate ɗin gidan suka ƙwanƙwasa, babu jimawa Gate Man yabuɗe musu
"Bayin Allah lafiya?' cewar Gate man yana bin su da kallo
Deeni ne yayi masa bayanin RAUDHA suka zo nema, don haka yace "su jira sa anan yaje ya'isar mata da saƙon zuwan su"
Yanda yafaɗa musu haka sukayi suka jingina a garun gidan suna jiran dawowarsa
Shi kuma yanufi cikin gidan yayi Nocking a bakin ƙofan parlour'n
RAUDHA na kwance cikin one Sitter, sai lilo take yi da ƙafafuwan ta da basu samu zama kan kujeran ba, wayan ta take latsawa kuma tana bin music ɗin da yakaraɗe parlour'n da ƙara wanda tasaka shi a t.v
Har Larai dake Moping wajen Fridge sai da tajuyo Nocking ɗin ƙofa amma RAUDHA bataji ba, hakan yasa ta'ajiye sandan Moping ɗin tanufi ƙofan tabuɗe
Ganin Me gadi yasaka ta faɗaɗa fara'arta tana faɗin "Baba Ashe Kai ne?"
"Eh wlh tun ɗazu ina ta buga ƙofa shiru, dama Hajiya ce tayi baƙi awaje nazo in sanar mata".
"To Baba bari in faɗa mata". Larai tafaɗa maganar tana juyawa ciki dasauri
Gaban RAUDHA taje tarisina tasanar mata saƙon me gadi
Yamutsa fuska tayi tana kallon ta kamar baza tayi magana ba, can kuma tace "aje a tambayi su waye?"
"To ranki yadaɗe". Larai tafaɗa tana miƙewa tsaye takoma tasanar da Me gadi
Sai da yasake komawa yatambaye su kafin yadawo yafaɗa mata
Larai takoma wajen RAUDHA tace "Hajiya wai Mahaifiyar Jawad ne".
Shiru RAUDHA tayi tana tunanin me irin sunan, sake maimaita sunan tayi cikin ranta amma takasa tuno inda tasan me sunan, kuma bata tunanin tasan me sunan don haka takalli Larai tana jan gajeren tsaki tace
"Ke koma kice idan baza suyi bayani yanda zan gane ba su koma inda suka fito".
Babu musu kuwa Larai tasake komawa tashaida wa me gadi, shima yasake komawa yafaɗa musu yanda tace
Deeni ne yayi musu bayani yanda zata fahimta sannan akazo aka sanar mata
Umarni taba da a shigo dasu.
Lokacin da suka shigo cikin parlour'n sanyi da ƙamshin daɗi ne kawai ke ratsa ƙofofin hancin su, haka suka koma ƴan ƙauye suna kallon haɗaɗɗen tsararren parlour'n da aka kashe masa maƙudan kuɗi kamar baza'a mutu ba
"Gaskiya kuɗi na inda suke waii". Cewar Deeni da yayi maganar a maƙoshi yana sake ƙare ma parlour'n kallo alokacin da suka gurfana gaban RAUDHA
Bata yi musu magana ba don kallo ɗaya tayi musu tunda suka shigo
Mahaifiyar Jawad ɗin ne cikin girmamawa tace "dama munzo ne maganar yarona da kika sa aka kama, kuma ance sai munzo mun baki haƙuri kafin asake sa, don Allah kiyi haƙuri da duk abinda yafaru munsan yayi laifi hakan bazai sake faruwa ba, ki taimaka ki saka baki a sakar min ɗa shi kaɗai Allah yabani". Taƙarike maganar nata tana sharan hawaye da gefen Hijabin ta
RAUDHA kuwa sai faman yamutsa fuska take yi maganar matan duk ya cika mata kunne, sai da tadire aya kafin taɗago lumsassun idanuwanta taƙare musu kallo daga matar har Deeni dashi yakasa furta komi sai kallon RAUDHA yake yi, a ransa yana tunanin rashin mutunci da rashin imani na masu kuɗi
"zan saka a sakar miki yaro amma ki ja masa kunne, duk ranan da yasake muka sake haɗa hanya dashi wlh billahi sai na wulaƙanta rayuwansa, sai nayi masa abinda har ke uwarsa sai kinyi dana sanin zuwan ki duniya". RAUDHA tafaɗa maganar cike da wani irin fushi da rashin tarbiyya
Sosai ranta yasake ɓaci akan abinda yayi mata kamar yanzu ne abun yafaru, duk idan tatuna cewa shi kaɗai ne mutumin da yataɓa ɗaukan hannu yasaka ajikin ta da sunan duka sai ranta yayi mata ɗaci tare da tsananin tsanar sa me girma, har tana jin kamar hukuncin da taɗauka akan sa yayi kaɗan akan abinda yayi mata
Su kuwa tsananin mamakin maganar ta ne yake ɗawainiya dasu, sai dai sun kasa furta komi sai sake bata haƙuri da Maman Jawad tasake yi
Hannu kawai tanuna musu alamun su bar mata gida, haka suka tashi suka fice suna me sake mamakin yarinyan da babu ko ɗigon tarbiyya atare da ita
Larai dake tsaye tana ganin abinda ke faruwa taɓe baki kawai tayi taci gaba da aikin ta, aranta tana mamakin abinda waɗannan mutanen sukayi da har suka fusata Hajiyar tasu haka don tasan ba abu bane ƙanƙani
Ƙaran gudun RAUDHAN ne yasa tasake ɗaga kanta tana bin RAUDHA da kallo da har ta haye sama, gashi dama takalmi ne me tsini a ƙafafun ta da tafita dashi bata cire ba kasancewar a parlour tayaɗa zango dawowarta inda taje
Jinjina kanta Larai tayi tana al'ajabin wannan kasada na RAUDHA, ko tsoron tagurɗe tafaɗo bata yi
Ita kuwa tana shiga ɗakin Fridge tanufa tasaka keey tabuɗe taciro Wine 🍷 takoma Kan kujera tazube tana sha, yanda fuskarta yayi jazur zaka gane ba cikin Mood ɗinta take ba, sai faman kurɓan wine ɗin take yi babu ko sassautawa
Ringing ɗin wayan ta yadawo da ita cikin hayyacin ta, taɗau wayan taduba screan ɗin, DPO ne yakira ta sai tayi peacking batare da tajira yayi magana ba cikin muryan maye tace
"D..P..O kasakeee shiii kawai".
Tsinke wayan tayi batare da taji me zai faɗa ba, ta'ajiye taci gaba da kwankwaɗan Wine ɗin ta, sai da tasha tayi tatul sannan tahaƙura, daga nan barci ne yaɗauke ta a zaune akan kujeran kan ta na jingine jikin sofan.
🌐🌐🌐
Sai bayan magriba tafarka, idanunta tasoma buɗe wa tana rufewa, daƙyar ta'iya buɗe su gaba ɗaya tana faman yamutsa fuska, hannunta ɗaya taɗago taɗaura kan wuyan ta da yasanƙare sakamakon yanda takwanta ɗin, sake yamutsa fuskarta tayi jin azaban zafi ya ziyarce ta kasancewar wuyan yayi tsami sosai, daƙyar ta'iya ɗago kanta tana faman runtse idanu, a wannan karon duka hannunta taɗaura saman wuyan ta tana faman matsawa tare da juya kanta, ta jima ahaka kafin tasoma jin dai-dai
Wayan ta da tasoma tsiwa tana neman agaji takai dubanta ga wayan, sai kuma tasauke hannayen nata tana sake jujjuya kanta kafin taɗau wayan tana kallon screan ɗin
MY BLOOD yafito ɓaro-ɓaro a gaban wayan, peacking tayi takara a kunne cike da muryan maye da yahaɗe dana barci tace
"Ya..yah.."
Suhaib da yaji muryan ƙanwar tasa ta ratsa masa kunne sai yalumshe idanun sa cike da ƙaunar ta yace. "my Sweetheart Ina kika shiga ne na kira wayan ki but baki ɗauka ba?"
"Uhmm.. uhm ina.. barci ne Ya..yaah.."
Shiru yayi Suhaib yana sauraron yanda take masa magana, babu shakka yasan da cewa har yanzu ƙanwar sa bata bar halin ta na shaye-shaye ba, a duniya babu abinda yatsana sama da wannan ɗibi'an da ƙanwar tasa ta koya, but ƙaunar da yake mata yafi rinjayar komi hakan yasaka baya iya ɗaukan mataki wajen ganin ya hanata banzan ɗabi'an nan..
"Ya..ya kana jiiinaaa kuwa..?" Takatse masa ɗan guntun tunanin sa
Ajiyan zuciya yasauke cikin taushin murya yace "Baby Wai yaushe ne zaki dena shaye-shayen nan da kike yi? Babu shakka naji ajikina sai da kika sha kafin kiyi barci, ina ƙaunar ki My sister bazan taɓa iya juran abinda zai same ki ba nan gaba, kinsan da cewa duk wanda yake shaye-shaye ƙarshen sa baya kyau? Bana son kina cutar da kanki ƙanwata don Allah ki dena kinji?"
Shiru kawai tayi tana sauraron sa ba wai don taji maganar nasa ba, sai tamatse baki kawai tana cije leɓen ta batare da ta kula sa ba
Shi kuma shirun ta ya san cewa baza ta amsa bane, kuma yasan idan yaci gaba da mata magana zata iya yin fushi yanzu takashe wayan wanda baya fatan hakan tafaru
Murmushi kawai yayi yace "Baby ki kula da kanki kinji I Love You".
Kamar baza ta amsa mishi ba sai kuma tace "me too".
Still Murmushi yayi kawai yatsinke wayan yana sauke ajiyan zuciya, fatan sa ɗaya kawai kar ƙanwar tasa tayi fushi dashi don yasan fushin ta babu kyau, tana da matuƙar kafiya da taurin kan tsiya, wanda hakan yake sa duk abinda tabar shi ta barshi kenan har abada, idan kuwa tayi fushi dasu tana ɗaukan lokaci kafin takula su, sai tayanke duk wani alaƙa dasu gaba ɗaya.
[11/14/2020, 8:35 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON TEN*
_______📖 *WASHE GARI*
Ranan da zasu tafi Kaduna bikin ƴar ƙanwar Maman Ramcy
12:30pm. Me keke napep yasauke Ramcy a ƙofar gidan RAUDHA
Tayi shiga cikin wata koriyar atamfa me ratsin ruwan hanta ajiki, ɗinkin babu ƙarya yayi kyau sai dai anci ma atamfan mutunci sosai, riga da skert ne akayi mata kuma yayi mata kyau duk da kasancewar ta baƙa amma kyakykyawa ce Ramcy sosai, ta yafa gyale a kafaɗun ta sai jakan da tazuba kayan ta ciki
A haka tashige gidan tana taku ɗai-ɗai
Koda tashiga cikin parlour'n da Saude suka ci karo ta fito daga kichen, gaisawa sukayi tatambaye ta RAUDHA
Saude tafaɗa mata tana ɗakin ta har yanzu bata sauko ba
Bata sake cewa komi ba tanufi upstairs ɗin, tana zuwa tatura ƙofan tashiga tana kallon RAUDHA dake kwance tayi baja-baja saman tafkeken gadon ta dake iya cin mutum biyar, sai sharan barcin ta take yi hankali kwance bata da alaman farkawa
Shigowa ciki Ramcy tayi tanufi bakin gadon tazauna, shiru tayi naɗan wani lokaci tana tunanin yanda za'a yi tatashe ta, daga ƙarshe dai tayanke shawara takai hannun ta tana taɓa ta tare da kiran sunan ta a hankali
Ta jima tana faman tashin ta kafin tabuɗe shanyayyun kumburarrun idanuwan ta da suka sauya kala sosai sabida tsaban barci, sake lumshe idanun tayi tana sake buɗe su akan Ramcy dake faman kallon ta
Cikin tausasa murya tace "Besty har yanzu baki tashi ba? gashi har 12:00pm. Ɗin ta wuce".
Shiru RAUDHA tayi bata iya ce mata komi ba, sai faman kokuwa take yi da lumsassun idanun ta da suka ƙi buɗe wa
Sai da tayi wajen mintuna 5 kafin tasoma yunƙurin tashi zaune tana faman riƙe kanta
Ramcy kuma tashi tayi takoma kan kujera tana faman kallon ta sai dai bata furta komi ba, don tasan ko ta sake magana ba kula ta zatayi ba
Sai da tagama nawan ta kafin tatashi tasoma cire kayan ta batare da taji kunyan Ramcy ɗin ba tunda ta saba
Ita ma kuma Ramcy ko ajikin ta sai kawar da kai tayi tana latsa wayan ta
Mintuna 20 RAUDHA taɗauka kafin tafito cikin Toilet ɗin, lokacin duk abinda tasha a daren jiya ya sake ta ta koma normal, idanun ta ma sun washe sosai sun koma fari tarrr ɗin su sai dai kumburan da sukayi ne be washe ba, wanda hakan yasaka suka sake lumshewa
A gaban dressing mirror tazauna tasoma busar da yalwataccen gashin kanta da yakasance baƙi siɗik me yawan gaske, bayan ta gama tashafa Expensive Lotions ɗin ta masu tsananin ƙamshi, batayi kwalliya ba illa powder da tashafa tasaka gazal a fararen idanuwanta, hakan yasaka suka ƙara kyau tare da ɗaukan hankali ga duk wanda yakalla, Lipstick tashafa a ƙananun laɓɓan ta tamiƙe tanufi Sif ɗin kayan ta
Kaya tasoma zaƙulowa tana ajiye wa asaman gado
Lokacin ne Ramcy tataso tazo bakin gadon tazauna tana kallon ta tace "dasu zaki tafi?"
Gyaɗa mata kanta kawai tayi taci gaba da ciro kayan
Ramcy tace "ok Aina zan shirya miki?".
Tsayar da abinda take yi tayi tanuna mata jerin Trolly ɗin ta tace "ki ɗau na saman".
Tashi Ramcy tayi taɗauko ɗan ƙaramin Trollyn kamar yanda tace mata tasoma shirya mata kayan ta ciki
Ita kuma alokacin taciro waɗanda zata saka tamatsa wajen kujera tasoma saka wa
Riga ce Robber me gajeren hannu baƙa da tatsaya mata iya ƙasan gwiwan ta, gaban rigan me tattara ne kuma anyi masa ado da stone masu tsananin ƙyalƙyali, sannan yana da igiya da taɗaure ta bayan ta, sai tasaka gajeren Socks red colour da Hill shoes ɗin ta me igiya shima Red colour, sai yazamana Ƙwaurin ƙafafun ta a waje suke
Gaban Looking mirror tanufa tasoma gyaran gashin ta sannan taɗaure da jan Ribom a tsakiyar kanta, shi kuma jelan taninke shi tayi kamar Dhounot, sai taɗaura Facing Cap baƙi da akayi harafin *R* agaban da jan zare, Parfomers ɗin ta taɗauka tafeshe jikin ta dashi sai faman zuba ƙamshi take yi, sosai tayi kyau kamar wata baby doll
Duk abubuwan da zata ɗauka sai da tazuba su cikin HangBag ɗin ta sannan suka fito Ramcy na jaye da Trolly ɗin
Su Saude da suke parlour nan sukayi musu adawo lafiya duk da kuwa basusan inda zasu je ba, amma ganin su da Trolly sun san tafiya ne yakama su
Ramcy ce kawai ta'amsa musu har suka fice
Suna fita compound ɗin gidan suka shige cikin farar motan da RAUDHA tace a wanke mata, horn tadanna tanufi bakin Gate a guje
Kafin ta'iso tuni me gadi ya hangame mata Gate ɗin tacilla motan waje sai saman kwalta
Kallon Ramcy tayi kafin takau da kanta zuwa titi tace "Besty ciro min tables ɗin nan cikin HangBag".
"Ok". Cewar Ramcy tana ɗaukan HangBag ɗin tabuɗe taciro mata
Nuni tayi mata da yatsu biyu hakan yasa taɓallo mata guda biyu tamiƙa mata, ta'amsa tasaka abaki tasoma tsotsa
Itama Ramcy ɗin cire ɗaya tayi tasaka a bakin ta sannan tamayar da sauran cikin jaka
Gudun da RAUDHA take tsulawa a saman kwalta ɗin baza ka taɓa tunanin zasu iya kai wa lafiya ba, over taking kawai take yi cike da ƙwarewa batare da ko tsoro ba
Sun ɗau hanyan Kaduna ɗoɗar lokacin ƙwayoyin da ta'afa sun soma aiki, gudun yanzu da take yi ma yafi na da
Gab da sun kusa shiga Kaduna tun daga nesa suka hango Sojoji sun tare hanya, but hakan be sa ta rage Speed ɗin motan ba
Wannan dalilin ne yasaka wasu daga cikin sojojin suka tsaya a tsakiyar hanyan riƙe da bindigogi suna jiran isowar motan
Sai da ta'iso gab dasu kamar zatayi ciki dasu kafin taja wani wawan burki da har yatsorata su tatsayar da motan cakk
Tashin hankali, gaba ɗaya Ramcy ta tsure don batasan me zai biyo baya ba da ganin yanda sojojin suka fusata sosai sukayo wajen motan
Ita kuwa RAUDHA ko a jikin ta sai faman ware lumsassun idanun ta dake faman rufewa take yi
Suna isowa biyu daga ciki suka bugi motan da ƙaton takalmin su cikin tsawa suka basu umarnin fitowa
Waɗanda suka hangi su Ramcy cikin motan sai abun yayi matuƙar basu mamaki ganin macece me wannan aika-aikan batare da taji tsoron abinda zai biyo baya ba, sakin baki kawai sukayi suna kallon RAUDHA da tasauke hulan ta ta'ajiye saman cinyan ta tazuba musu narkakkun manyan idanuwanta bata da alamun fitowa
Biyun da suka bugi motan waɗanda suka fi kowa fusata su ma leƙa motan sukayi da ninyan su ci mutuncin na ciki sai suka hangi mata , haɗiyar yawu duk kansu suke yi suna kallon su cike da sha'awa, kun san yawancin sojoji mayun mata ne 😅🤫, bare waɗannan masu ido a tsakar ka kallo ɗaya kayi musu zaka hango zalaman su, yawancin su ma duk Christian ne
Ɗaya daga ciki ne yabuɗe baki cike da murmushi a face ɗin sa yace "ah Madam Ina zuwa haka?"
Ramcy da har yanzu jikin ta ke faman rawa takalle sa kamar zatayi magana sai kuma taga RAUDHA yake kallo tayi gum da bakin ta
Cikin dashashshiyar muryan ta tabashi amsa a taƙaice tana kawar da kanta
Washe baki yasake yi yana kallon sauran ƴan uwan nasa da suka tsira wa RAUDHA idanu kamar sun sami t.v yace "ku wuce kawai zan ji dasu".
"Ok". Suka faɗa atare suka juya suka tafi batare da sun so ba, sai dan shi ɗin shine babban su dole subi umarnin sa
"Baby bakya jin tsoro kike yin irin wannan tuƙin?"
Shiru tayi bata tanka sa ba
Sai yasake sakin murmushi yakalli Ramcy yana kashe mata ido ɗaya sannan yanuna mata RAUDHA da hannu
*_________________________*
Daga can nesa wani matashin saurayi ne da yake tsaye yana waya amma idanun sa na kan motan su RAUDHA, tun sanda suka taho yake kallon motan yana mamakin ƙarfin hali da rashin hankalin matuƙin
Sanye yake cikin kakinsa da sukayi masa bala'in kyau tare da fito da ƙaƙƙarfan ƙirar jikin sa, wanda kallo ɗaya idan kayi masa zaka san Jarumin Namiji ne na bugawa a jarida, sannan a kallo ɗaya idan kayi masa baza ka iya tantance shi ɗin wani irin yare bane coz ko kusa be yi kama da ɗan Nigeria ba
Wayan yakashe sannan yatura cikin aljihu yanufi wajen motan cikin takunsa na mazantaka da nuna shi ɗin Jarumi ne
Isowar sa wajen maganar Sojan da yake wajen su Ramcy yasauka a kunnen sa, yana tambayan su Numban waya
Ɗaure kyakykyawar fuskar sa tamau yayi don yarigada ya gane mata ne aciki
Jikin motan yaƙarisa yanda zai hangi mutanen ciki, nan kuwa yasauke idanun sa kan Ramcy da itama tazuba masa idanun cike da tsananin firgita da ganin murɗaɗɗen mutumin dake tsaye a gaban ta babu ɗigon annuri
Saurin Solute ɗin sa Sojan yayi
Be kalle sa ba sai sake tamke fuska yayi yakai duban sa side ɗin RAUDHA da takawar da kanta har alokacin kuma bata sauke hannayen ta kan sitiyarin motan ba, sai faman karkaɗa yatsunta take yi
Tsira mata idanu kawai yayi yana kallon kyakykyawar fuskarta
Lokacin ita kuma tajuyo da face ɗin ta sosai yanda zai iya ganin ta sai dai idanun ta suna lumshe ne batare da ta kalle sa ba takwantar da kanta jikin kujeran
Gashin giranta dake haɗe masu yawan gaske yabi da kallo kafin yasoma bin jikin ta da idanunsa kamar wanda ke neman wani abu, sosai yarinyan tatafi da imanin sa sai dai shigan da tayi ya san cewa ita ɗin ba kalan su bane don batayi masa kama da me kallon gabas ba
Ajiyan zuciya yasaki a ɓoye, sannan yakalli sojan dake tsaye yana kallon sa tare da Ramcy sai yaji kunya, amma sai yawayance yakau da kansa yana sake haɗe rai yace
"Jone Aikin da kazo yi kenan tambayan numban su?"
Jin muryan sa cikin kunnen ta yasaka ta buɗe idanun ta tana kallon sa
Shi kuma alokacin kallon Jone ɗin yake yi
"No Sir". Cewar Jone ɗin yana sake Solute ɗin sa
Gajeren tsaki yaja yana maida idanun sa cikin motan, nan kuwa idanun sa yafaɗa cikin nata da tazuba mishi tana kallon sa batare da kunyan sa ba
Gaban sa ne yafaɗi sai yayi saurin ɗauke nashi idanun murya a kausashe yace "kuna mata kuke irin wannan tuƙin gangancin kuna da hankali kuwa?"
Duƙar da kanta Ramcy tayi duk jikin ta sai mazari yake yi, sosai muryan sa yatsorata ta, tasan da cewa wannan mutumin ba barin su zai yi ba, shikenan yau RAUDHA taja musu ta kawo su inda za'a kashe su
Ita kuwa RAUDHA har yanzu kallon sa take yi batare da tsoro ba, sai ma lumshe idanun ta tayi bata da ninyan bashi amsa, ko kaɗan a yanzu bata son yin magana sabida ƙwayoyin da tasha
Sosai yaji haushin shirun da tayi, cikin fusata yace "ba da ku nake magana ba?"
A karo na biyu tasake kallon sa shima ɗin tsatstsare ta da idanun sa yayi batare da ya kawar ba
Cikin rawan murya Ramcy tace "yallaɓai kayi haƙuri don Allah".
Shima Jone cikin girmamawa yace "Oga sorry sun faɗa min abinda yasa..."
Ɗaga masa hannu yayi dole yayi shiru yahaɗiye ƙaryan da yake son shirgawa.
.
_To fa yau RAUDHA da alamun ta taɓo dai-dai ita, bari mu jira me zai faru._
_Kar ku manta da yawan Comment shi zai sa naƙara yawan typing._
[11/14/2020, 8:51 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON ELEVEN*
_______📖"Katabbatar sun nuna maka takardun motan su kafin su wuce". Yafaɗa maganar yana kallon Jone fuska a ɗaure
"Ok sir". Jone yafaɗa yana me sara masa
Juyawa yayi kawai yatafi cikin tafiyan sa na zaratan maza yabar wajen
Lumshe idanun ta tayi tana sake kwantar da kanta jikin kujeran, tana jin sanda Jone yake sake tambayan Ramcy numban wayan ta, kuma tana jin sanda yayi musu sallama har yana ce mata
"Baby baza ki buɗe idanun ki muyi ban kwana ba?"
Buɗe idanun kuwa tayi sai dai bata kalle sa ba tayi wa motan keey taja da wani irin Speed tabar wajen
Gaba ɗaya sojojin sake kallon motan sukayi suna jinjina ƙarfin hali irin na RAUDHA, tabbas ko basu faɗa ba akwai abinda tataka har take iya yin hakan agaban su
Shima ɗin idanun sa kawai yazuba ma motan cike da mamakin tantiranci irin na yarinyan da har take musu tsaurin ido, har motan taɓace ma ganin sa kafin yadena kallon hanyan. Ahankali yasauke ɓoyayyen ajiyan zuciya yana me lumshe idanun sa cike da tuno suffarta, murmushin sa me kyau yasaki yana ɗaukan wayan sa dake faman ƙara yakanga a kunne bayan yayi peacking call ɗin.
🌐🌐🌐
Har suka shiga cikin Kaduna babu wanda ke magana cikin su
Akaro na biyu RAUDHA tasake kallon Ramcy da har yanzu bata dawo dai-dai ba, juya kanta tayi kafin tasake maimaita tambayan da tayi mata
"Ramcy tunanin me kike yi ne ina tambayan ki ina muka dosa?"
Sai alokacin Ramcy tadawo hayyacin ta sosai, cikin jan numfashi tace "uhmm Besty wlh ban ji ba duk hankalina ya tashi da ganin wannan dogon mutumin me murɗaɗɗen jiki, nayi tunanin yau kashin mu ya bushe wlh, don nasan halin sojoji basu da mutunci ko kaɗan".
Siririn tsaki RAUDHA taja batare da tace uffan ba taci gaba da sharara gudu
Ganin haka yasa Ramcy tasoma nuna mata inda zasu yi
A ƙofar wani madaidaicin gida suka tsaya, gidan me dakali ne da yasha suminti tare da sabon penti, koda gani ansan cewa gidan ana sha'ani sabida yanda mutane maza da mata suka cika ƙofar gidan, da alamun dai wani wajen Za'a tafi don gefe ɗaya motoci ne sun fi biyar afake
Tunda motan tatsaya yawancin mutanen wajen sai idanuwan su yadawo wajajen
Sun ɗau lokaci kafin Ramcy tasoma fitowa, sai da tafito taleƙa da kanta tana kallon RAUDHA da bata da alamun fitowa tace
"My Besty don Allah fito mushiga kiyi haƙuri".
Yamutsa fuska RAUDHA tayi tana sake kallon mutanen wajen ta cikin motan, cikin ƙare musu kallo da taɓara tace "kinsan bana Son mutane idan nafita kallona zasu riƙa yi".
Dawowa ciki Ramcy tayi tace "Plz Mana Besty Ina ruwan ki dasu? Kar ma ki kalli kowa kinji?".
Gyaɗa kanta tayi tana sake ware idanun ta tana kallon su, sai da ta ɗan ja lokaci kafin tabuɗe motan tafito bayan ta mayar da hulanta akai
Sai kawai gaba ɗaya mutanen wajen suka sanyo mata idanu suna kallon haɗaɗɗen yarinyan me cike da ban sha'awa a idanun duk me kallo, yarinya ƴar hutu da ji da kai
RAUDHA sai faman ɓata fuska take yi tatako zuwa wajen Ramcy tana ɗan lumshe idanun ta
Sai da Ramcy tariƙe hannun ta kafin suka nufo gidan
Ba maza ba har matan sakin baki da hanci kawai suka yi suna kallon ikon Allah, kuma akasarin su kallon arniya kawai suke mata sabida shigan dake jikin ta
Sai da suka zo gab shiga gidan ne, Amarya da har da ita ake kallon sannan ne tagane Ramcy ce ƴar uwanta, sai tadaka tsalle tanufo ta tana faɗin
"Rahma ke ce ashe?"
Ramcy da itama sai yanzu idanun ta suka kai kan Amarya Shatu sai tawashe baki tana sakin hannun RAUDHA suka rungume juna cike da farin ciki
"Wlh ban gane ki ba sai yanzu ashe kece?" Cewar Shatu bayan ta ɗago kanta tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta
Duk ƴan matan sai suka nufo wajen su don ba ma idanun su abinci wajen kyakkyawar matashiyar nan me kama da ƴan ƙetare
"Ni ce wlh kin gammu sai yanzu".
Murmushi Shatu tayi tana kallon RAUDHA dake tsaye tana bin mutanen wajen da kallo sai kace taga abun ƙyama, sai faman yamutsa fuska take yi
"Wannan kuma daga ina sarkin jajibe-jajibe?"
Sai da Ramcy takalli RAUDHA kafin tamayar da idanun ta kan Shatu da tayi maganar tace "mu shiga ciki mana ko anan ne zaki tarbe mu?".
Dariya Shatu tayi tana kallon sauran ƴan matan wajen tace "ku jira Ni yanzu zan dawo".
Gyaɗa mata kai kawai sukayi domin har yanzu sun kasa magana tunda sun samu abincin kallo
Riƙo hannun RAUDHA Ramcy tasake yi suka bi bayan Shatu da tayi gaba abinta
Dama tuni mutanen wajen sun soma gulma suna raɗe-raɗin ita kuma wancan wacece? Sai dai babu me basu amsa haka suka ci gaba da gulman su, yayinda ƙawayen amarya kuma suke jiran tadawo tabasu amsa
Suna shiga cikin gidan matan dake faman aiki suka sanyo musu idanu
Ramcy bata kalli kowa ba bare tagaishe su don tasan basu gane ta ba, haka tabi bayan Shatu har ɗakin Maman su, suna shiga babu kowa sai Maman Shatu ɗin tare da wata dattijuwa
Idanu suka sanyo musu cike da mamaki
Maman Shatu tace "ke Shatu wannan kuma daga ina?" Tayi maganar tana nuna RAUDHA da tatsaya ƙeƙam abakin ƙofa
"Mama baki gane ta bane? Rahma ce da baƙuwar ta".
Sai Maman da Dattijuwar suka mayar da idanun su kan Ramcy da har ta zauna ma
"Ƴar ƙwal uba kece da wannan shigan banzan Ramatu?" Cewar Dattijuwar tana kai hannun ta jikin Ramcy taɗaga mata duka
Matsawa gefe Ramcy tayi tana dariya tace "ƴar tsohuwa me ran ƙarfe har dake a bikin nan?"
Mama tace "Rahma wacece wannan wai da kika zo mana da ita me kama da ingozi?"
Ɓata fuska Ramcy tayi tace "wai menene haka don Allah ƙawata ce fa muka zo da ita biki".
Gaba ɗaya sai suka kama baki har Shatu suna sake maida idanun su kan RAUDHA dake tsaye har yanzu, sai dai yanzu sosai ta ɓata fuskarta tana sake sakar musu lumsassun idanun ta, kafin kuma tajuya tafice abinta
"Kun gani ko don Allah menene ruwan ku da ita? haka ake amsan baƙuwa?" Cewar Ramcy tana miƙe wa tsaye dasauri tafita
Sai suka juyo da kallon ga junan su
Shatu tace "cabb ɗi wai har yanzu Rahma bata dena halin ta ba? Ni nasan wlh daga shige-shigen ta ne ta samo wannan arniyan, wai ƙawancen ma har da arniya".
Sai taja tsaki tana nufan ƙofa batare da tabi takan Mama da tsohuwa dake surutu ba
A zaure Ramcy ta cinma RAUDHA tayi saurin riƙo ta
A fusace RAUDHA tajiyo tana kallon Ramcy da shanyayyun idanun ta tace "meye kika riƙe Ni?"
Cikin lallami Ramcy tace "don Allah kiyi haƙuri Besty basu san ko ke wacece bane, amma zanyi musu bayani yanzu kin ji?"
Gajeren tsaki RAUDHA taja batare da tace uffan ba
Roƙon ta Ramcy taci gaba da yi daƙyar tasauka, amma da sharaɗin baza ta kwana anan ba sai dai su tafi Hotel
Gyaɗa mata kai kawai Ramcy tayi cike da son kwantar mata da hankali
Shatu ce tafito itama tagan su anan tsaye, sai kawai tasaki murmushi tace
"Yanzu party zamu je Rahma, ki taho muje tunda ga motoci sun zo".
Murmushi Ramcy tayi tace "to zamu zo daga baya, aina ake yi?".
Faɗa mata address ɗin wajen tayi kafin tafice abinta
Riƙo hannun ta tayi zasu koma ciki amma RAUDHA tatirje alamun baza ta je ba, sai ita Ramcy ɗin ne takoma ciki don sanar musu da tafiyan ta
Tana shiga ɗakin taga mutanen wajen duk sun shiga ciki suna tambayan yarinyan da tafita
Anan ne ma suke sanin ashe Ramcy ce ɗayar
Tana shigowa duk suka yi mata caa aka suna faɗin "shine zata wuce su bata gaishe su ba?" Ita dai haƙuri tabasu kafin tayi ma Mama ƙarya akan zasu wuce wajen party amma ba lallai tadawo nan ba sai gobe, zasu sauka gidan yarinyan da suke tare da ita (tana nufin RAUDHA)
Bata jira ma abinda zasu ce ba tafito tasami RAUDHA tariƙe mata hannu suka fito cikin gidan
Yawancin mutanen wajen duk sun shige cikin mota, ko kallon sauran mutanen da suka banko musu ido basu yi ba suka shiga cikin motan RAUDHA taja suka bar wajen.
🌐🌐🌐
Suna isa ɗan ƙaramin Hotel ɗin me ban sha'awa suka fito suka shiga ciki
Ramcy ce tayi musu booking ɗakin da zasu zauna, sai da tagama komi sannan suka nufi inda jerin ɗakunan suke, a upstairs ɗakin nasu yake
Bayan tabuɗe suka shiga
Direct Kan gadon RAUDHA tanufa tafaɗa tana ajiyan zuciya, lumshe idanun ta tayi tana jin zuciyarta babu daɗi, sosai ranta yasosu da yanda mutanen suke kiran ta da arniya
Zuwa Ramcy tayi tazauna gefen ta, shiru tayi naɗan wani lokaci kafin tace "Besty ko zamu je wajen partyn ne?"
Shiru babu amsa
Sai da tasake maimaita mata sannan ne RAUDHA tabuɗe idanun ta cike da ɓacin rai tace "Ni baza Ni ba".
"Plz Besty kin San bazan iya tafiya in barki anan ba, sannan idan banje ba Shatu zata ji haushi tunda nazo mata biki ne kiyi haƙuri da abinda akayi miki, hakan bazai sake faruwa ba".
Gajeren tsaki RAUDHA taja tana miƙe wa zaune taja jakan ta dake hannun Ramcy ɗin, taciro ƙwayoyin ta ta'afa a bakin ta don jin kanta ya soma ciwo sakamakon hayaniyan mutane
Can kamar baza ta sake cewa komi ba sai kuma tatashi tana ajiye Facing Cap ɗin ta saman gadon takalli Ramcy tace "tashi muje".
Dasauri Ramcy tatashi tana murmusawa suka nufi ƙofa suka fice, Ramcy ɗin tarufe ƙofan suka sauka ƙasa, inda suka ajiye motan su suka nufa suka shiga RAUDHA tafiga motan suka bar haraban wajen.
[11/16/2020, 10:49 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON TWELVE*
_______📖A Hotel 🏨 ɗin da su Shatu suke yin party RAUDHA tatsaya, ɗan ƙaramin hotel ne me kyau da tsada, gaba ɗaya haraban wajen motoci ne manya-manya jibge, da gani kasan harkan da manyan mutane ake yi
Dama shi Mijin Shatu ɗin me kuɗi ne, don haka abokan sa duk yaran masu hannu da shuni ne kuma duk sun hallara wajen, partyn dama daga Ƴan mata sai samari ne
Fitowa suka yi cikin motan suka nufi ciki
Tunda suka doso bakin wajen Cool music ɗin da aka saka yaratsa kunnuwan RAUDHA, sosai taji wani sanyi da nishaɗi ya ziyarce ta duk da kuwa bata cikin Mood ɗin ta
Suna shiga sai idanun mutane da yawa yadawo kan su sai kallon RAUDHA ake yi wacce ita kuma ta kafe inda MC ke tsaye yana surutun sa da idanu
Sai da Ramcy tariƙo hannun ta suka shige wajen kujerun sannan ne tadawo da hankalin ta gare ta
Zama sukayi akan kujeran da babu kowa
Hankalin fa abokan ango gaba ɗaya ya koma kan RAUDHA tun sanda tashigo tatafi da duk wani nutsuwar su
Har wani daga cikin su dai sai da yaciri baki yayi ma ango magana "ko ya santa ne?" Shi kuwa yakaɗa kansa kamar ƙadangare yana murza baki yace
"A'a Niii..? wlh bansan taba, sai dai ko Babyna?".
Shatu dake gefen sa tana jin duk abinda suke faɗa tace "nima haka yanda kuka ganta haka naganta.."
Maganar da MC yayi ne yadawo dasu daga surutun da suke yi
Sai suka tashi suka fita filin rawa inda MC yakira ango da amarya akan su zo su taka
Duk abokan tashi sukayi suka nufi yin musu manne, amma banda wanda yake tambayar Ango ɗin ko sun san RAUDHA ne
Hankalin sa gaba ɗaya yana ga su RAUDHA, sai daga baya ne shima yatashi yanufi fili yana sakar musu maƙudan kuɗi kamar wanda be san zafin sa ba
Yana gamawa kuwa yaratsa yafito cikin cunkuson ƴanmata da samarin da suka cuɗe waje ɗaya duk wai akan sun zo ma Ango da Amarya manne
Wajen su Ramcy yanufa dake zaune su basu tashi ba, sai ma RAUDHA da takifa kanta saman table sakamakon Ciwo da kanta ke mata, duk da sosai take son daurewa amma abin ya gagara dole takwantar da kanta don taji daɗi
Yana isowa yayi musu sallama idanun sa akan RAUDHA wacce ma batasan yana yi ba
Amsa masa sallaman Ramcy tayi tana kallon sa, ganin dai ba ita yake kallo ba sai itama taɗauke kai taci gaba da latsa wayan ta
Zama yayi sannan ne alokacin yadawo da idanun sa kan Ramcy ɗin yana murmusawa yace "ƴan mata sannun ku dai".
"Yauwa sannu". Ramcy tabashi amsa batare da tasake kallon sa ba
Numfashi yasaki yana ƙara mayar da idanun sa kan RAUDHA ɗin yace "amma wannan lafiyan ta ƙalau ana shagali tana kwance?"
Sai alakocin Ramcy tasake dawo da idanun ta kansa, kuma a lokacin ne tayi masa kallon ƙurilla
Kyakkyawar saurayi ne me ji da kyau da kuɗi, ko kaɗan baya da makusa, yana sanye cikin farar Gezna wanda akasarin abokan dama shi suka saka, sai ɗai-ɗai ku da suka sanya farar Shadda
"Lafiya lau".
"Ok Allah yasa hakane, but don Allah ko zaki iya min magana da ita coz wurin ta nazo".
Ramcy tace "ai tana jinka duk abinda zaka faɗa".
Dafa table ɗin yayi yana ɗan bugawa yace "ƴan mata Plz ki tashi muyi magana".
Ramcy da taɗau Juice tana sha ta'ajiye tana faɗin "me zai sa sai tatashi? Kawai kayi maganar ka mana ai kunne🦻 ke ji".
"Kuma hakane fa". Yafaɗa yana dariya
Sai kuma yasake mayar da idanun sa kan tulin gashin ta cike da sha'awa yace "Baby Ni dai har ga Allah kinyi min ne shiyasa nataho don na yaɗa manufa na akan ki, sunana Saifullah zan zo insan naki sunan?"
Shiru RAUDHA tayi bata da alamun tashi duk da tana jin sa
Ramcy kuwa ganin ya hau mata magiya sai takatse shi da faɗin "Besty bata da lafiya kayi haƙuri ka ƙyale ta haka nan".
Bada son ransa ba yayi shiru but ya so yasake ganin baby face ɗin ta, amma babu yanda ya'iya sai yanemi Numban wayan ta wajen Ramcy
Ita kuma Ramcy tabashi nata kamar yanda tayi ma Sojan can
Miƙe wa yayi yayi musu sallama yakoma wajen abokan ango wanda tuni sun ƙosa yazo yabasu labarin RAUDHA don sun san wajen ta yatafi, duk da kuwa su ma suna son ace su ne suka samu gurbi a wajen ta
Ramcy magana tayi ma RAUDHA akan zata je wajen Shatu kafin tatashi tatafi, bata jima ba tadawo tace
"Besty tashi muje naga alamun wajen baya miki daɗi".
Kamar jira take yi kuwa tamiƙe dafe da kanta tayi gaba Ramcy tabi bayan ta
Wani daga cikin abokan Angon da tun sanda yaƙyalla idanu akan RAUDHA yasusuce, yana ganin sun fita yamiƙe kamar yana waya shima yafice
Yana fita yasoma waige-waige ko zai hango su amma ko me kama da ƙeyan su be gani ba, sai motar da yagani tafice da gudun tsiya, sai da yaɗan ƙara duddubawa ko zai gansu kafin yayi tunanin ko su ne suka fita, sai yayi saurin shiga motar sa yatake musu baya, but ko me kalan motan su ma be gani ba a hanya amma haka yaci gaba da tafiya ko Allah zai sa yadace
Abinda be sani ba bata hanyan ma da suka bi yabi ba, domin suna soma tafiya RAUDHA tatsayar da motan, sosai kanta ke sara mata kamar zai rabe gida biyu, riƙe kan tayi da hannu ɗaya tana yarfe ɗaya hannun
"Lafiya Besty menene?" Ramcy tafaɗa cike da tashin hankali
Jujjuya kanta take yi kafin tace "kaina ke ciwo zafiii".
Duk hankalin Ramcy ya tashi haka take ta mata sannu, daga baya tace "su je asibiti"
But ita RAUDHAN tagirgiza mata kai alamun a'a, sai tabuɗe Lockern cikin motan taciro Cocaine ɗin ta tasoma shaƙa wai ko zai sa taɗan ji dama-dama idan hankalin ta yagushe
Ramcy dai sai kallon ta take yi tana mata sannu
Tsawon mintuna 5 taɗauka idanun ta a lumshe kafin tayi ƙarfin halin kunna motan taci gaba da tafiya, but sai dai yanzu ɗin a hankali take tuƙa motar har sanda suka ƙarisa cikin hotel ɗin tayi parcking, fita tayi batare da takashe motan ba
Sai Ramcy ce tazagayo ta'amsa keey ɗin takashe kafin takulle motan suka nufi ciki, har sun shiga reception Ramcy tatuna basu ɗauko Jakan kayan su ba, sai tadubi RAUDHA dake riƙe da kanta tana faman haɗa hanya tace
"Besty jira Ni anan bari in ɗauko Mana Jakan mu".
Gyaɗa mata kanta tayi, ita kuma tafice dasauri
Ci gaba da tafiya tayi tahaye benen, daƙyar take tafiyan saboda yanda Cocaine ɗin yasoma gusar mata da hankali, ahaka tahaura saman tadoshi ɗakin su, tana shan kwana taji tayi karo da mutum sai dai takasa ɗago kanta bare taga wanda tabuge, illa lafewa da tasake yi ajikin sa tana shaƙar daddaɗan ƙamshin sa
Hannun sa biyu yasa yaɗago kanta yana kallon Beauty face ɗin ta da talumshe idanuwan ta, wani irin ƙunci da baƙin ciki ne yaji ya ziyarce shi lokaci ɗaya
Sosai yagane ta tunda kayan ɗazu ne ajikin ta
Tabbas tun kallon farko da yayi mata yatabbatar da ita ɗin mara tarbiyya ce duk da har yanzu be tabbatar wa kansa ita musulma ce ko Christian ba, yanzu kuma gashi ya ganta cikin hotel kuma a buge hakan ya tabbatar masa da zargin sa, hakan yasaka kuma yaji mugun tsanar ta da haushin ta cikin ransa wanda be san dalili ba
RAUDHA buɗe kyawawan idanunta da a yanzu suka sauya kala tayi, tasauke cikin nasa idanun da yakafe ta dasu
Duk da gaban sa yayi mugun faɗuwa amma hakan be sa ya tattakura ya tunkuɗe ta ajikin sa ba
Da bango tabugu kafin tafaɗi yarab a ƙasa, tsananin azaban da yaziyarce ta batasan sanda taware idanun ta duk ka waje ba tana fashewa da kuka, ban yi zaton idanun ta sun kai girman hakan ba sai yau da tafiddo su waje tsaban taji azaba 😄
Kallon kallo kawai suke yi yayinda take gunjin kuka
Cike da takaicin ta yatamke fuska yana aika mata da banzan kallo yace "kin zata kowa irin ki ne mara tarbiyya ƴar ƙwaya Da zaki haɗa jikin ki da nawa? Wawiya kawai". Yaja dogon tsaki yana tsallake ƙafafun ta yawuce dasauri-sauri cikin tafiyan sa na zaratan maza
Lumshe idanuwan ta tayi hawaye na kwaranya saman kuncin ta
Yau da tana da ƙarfi a jikin ta wlh da babu abinda zai hana ta cin collarn rigansa sai taga wanda yaɗaura wa Uwar sa aure
Tana nan zaune har sanda Ramcy tadawo, ganin RAUDHA a ƙasa ya ɗaga mata hankali, cikin sauri tace "Besty ya haka faɗi kika yi?"
Tatambaye ta tana ɗago ta a lokaci ɗaya
RAUDHA bata iya ce mata komi ba sabida tsananin tuƙuƙin da zuciyarta take mata da maganar da wannan mutumin yafaɗa mata da kuma abinda yayi mata, sabida tsaban baƙin ciki ma gaba ɗaya ta dena jin ciwon
Har sanda taɗaga ta sannan tariƙo ta suka ci gaba da tafiya
Suna shiga ɗakin RAUDHA taƙwace jikin ta tanufi kan gado tafaɗa kai tana lumshe idanuwan ta da har yanzu sun kasa dena fid da hawaye
Ramcy duk bata kula da hawayen da take yi ba, sai zama da tayi tana tambayan ta abinda zasu ci
Sai alokacin ne ma ita RAUDHAN tatuna rabon ta da abinci tun daren jiya, tunda koda Ramcy tazo gidan ta ita tatashe ta a barci, kuma bata ci komi ba suka taho, gashi yanzu har duhun magriba ya shiga bata sanya komi a bakin ta ba
Bata kula Ramcy ba itama kuma sai bata sake cewa komi ba, tasan halin ƙawarta ba ko yaushe take son magana ba sai idan taga dama koda zaka shekara kana mata maganan ne, ita ɗin ƴar ganin dama ce
Har aka kira isha'i RAUDHA bata motsa daga inda take ba
Ita kuma Ramcy tuni har tayi wanka ta sauya kaya ta gabatar da sallan da ake bin ta yau ɗin, sai da tagama ne tasake dawowa tatambayi RAUDHA abinda zasu ci
Sosai a yanzu take buƙatar abinda zata sanya a bakin ta koda kuwa bazai mata daɗi bane, sabida tsaban yunwan da a yanzu take ji, daƙyar ta'iya buɗe baki tace ma Ramcy ɗin "duk abinda taga yayi mata tace akawo"
Nan kuwa Ramcy taɗau wayan ɗakin tayi musu odan abinci sannan tazauna zaman jiran kawowa, babu jimawa taji ana Nocking taje tabuɗe ta'amso tadawo ta'ajiye akan table ɗin dake tsakiyar ɗakin
"Besty taso muci ga abincin an kawo".
Shiru RAUDHA tayi, sai kuma daga baya tayunƙura tatashi duk jikin ta babu ƙwari, ga fuskarta a a ɗaure kamar bata taɓa yin walwala ba
Sai a lokacin ne Ramcy takula tatambaye ta
"Besty lafiya wai meke damun ki ko kan ne?"
Girgiza mata kai kawai tayi tamiƙe tadawo kusa da ita da take zaune saman sofa, bata yi magana ba har suka soma cin abincin
Bayan sun gama ne tamiƙe tanufi Toilet tayi wanka, tana fitowa wayan Ramcy yasoma ringing
Ɗaukan wayan tayi taduba sannan taɗago tana kallon RAUDHA tace "Sojan nan ne da nabashi Number yake kira'.
RAUDHA batace uffan ba sai buɗe Trollyn ta da tayi tana ciro kayan da zata saka
Har wayan tatsinke aka sake kira amma batace komi ba, ita kuma Ramcy bata amsa ba, sai da yayi 3missed call kafin yadena kira
A lokacin har RAUDHA tagama saka kayan ta na barci riga da wando Three qweater farare masu taushi sosai, sai time ɗin takalli Ramcy tace "ki cire layin ki sanja wani".
Ramcy tasan me take nufi don haka tabuɗe wayan tacire layin tabar ɗaya simcard ɗin ciki, karyawa tayi tazubar sannan taci gaba da latsa wayan ta
Dama Numban ne kuma taba ma wanda suka haɗu a partyn Shatu
Kwanciya RAUDHA tayi tajuya bayan ta tana lumshe idanuwan ta
Itama Ramcy bata wani daɗe ba tazo takwanta nan da nan barci yafige ta
RAUDHA tana nan kwance amma barcin yakasa ɗaukan ta, takaicin Sojan da sukayi karo duk ya addabi zuciyarta, daƙyar tayi barci bayan ta haɗiye ƙwayoyin ta.
0 comments:
Post a Comment