_______📖Washe gari sai kusan ƙarfe 11:30am. Ramcy tasoma farkawa, sai da tashiga Toilet tayi alwala tafito sannan tasoma tashin RAUDHA but ko motsin kirki taƙi yi, haka ta haƙura taƙyale ta tayi sauri tagabatar da sallan asuba da basu yi ba, sannan taje tayi wanka, tana fitowa sannan ne RAUDHA tabuɗe idanun ta
Tana nan kwance har sanda Ramcy tasaka kayan ta sannan ne tatashi ahankali tashiga Toilet ɗin, wajen mintuna goma taɗauka tafito tana zama kan sofa, kwantar da kanta tayi tana lumshe idanun ta
Kamar jiya Ramcy ce tayi musu odan breakfast da zasu ci, bayan sun gama ne sannan ne RAUDHA tayi wanka tafito
Time ɗin ita kuma Ramcy ta sauya kayan ta zuwa wani jan yadi dack da ɗige-ɗigen fari ajiki, sai akayi zanen Flower da blue colour, ɗinkin doguwar riga ne fitet gown da yamatse ta sosai
Itama RAUDHA kayan ta taciro tasaka bayan ta shafa Lotions ajikin ta, batayi kwalliya ba sai Powder da tasaka a baby face ɗin ta
Tunda tagama shiryawa Ramcy take kallon ta, tana son tayi mata magana akan kayan amma tana tsoro don bata son yau ma mutane suriƙa mata kallon arniya
Riga ce tasaka irin na jiya, sai dai shi wannan maroon colour ne saɓanin na jiya baƙi ne, kuma wannan yafi Robber sosai gashi shara-shara ne, gaban rigan ma sosai yabuɗe har yafi na jiya, sannan ma be kai mata iya gwiwa ba, kai gwara ma na jiya sau dubu akan wannan
Har ta zauna tasoma saka Socks a ƙafan ta sai kuma taja tsaki tana miƙe wa tasoma cire kayan, sauyawa tayi da pencil ɗin wando ja da ƙaramar riga me ruwan zuma, sai tasaka top shima ja me kwalliyan Flower da stone, gashin ta ta tattare tasaka Ribom sannan tasaka Socks da Hill shoes me tudu white, sai tasanya Facing Cap white colour sai dai Robber ne wanda yakama mata kanta sosai
Ita RAUDHA tayi kwalliyan nan ne don fita yawo don ko kaɗan bata son komawa gidan bikin nan
Koda suka fita suna cikin mota anan Ramcy tace mata
"Besty mu leƙa gidan biki".
Turo baki gaba RAUDHA tayi tace "Ni babu inda zani yau".
"Please mana Besty don Allah muje yau babu abinda zai faru, kinga yau ne bikin dole zanje kuma bazan barki natafi Ni kaɗai ba".
Daƙyar dai da suɗin goshi RAUDHA tayarda zataje, daga yawon su suka nufi gidan su Shatu, amma firr RAUDHA tace "baza ta fita daga motan ba" dole Ramcy taƙyale ta ita tashiga cikin gidan su Shatu ɗin
Wajen mintuna 20 taɗauka kafin tafito tanufi maƙotan su inda Shatu take taron ta
RAUDHA da tagaji da kallon mutane ta cikin Glasses gyara kujeran tayi takwanta tana lumshe idanun ta
Koda Ramcy tadawo batace mata komi ba taja motan suka tafi, wani restaurant suka je anan suka ci abinci suka koma Hotel ɗin da suka sauka
Tun da suka shiga RAUDHA tahaye gadon tasoma barci, ba ita tatashi ba sai magriba, har Ramcy ta fita ta dawo
Anan tayi wanka tasoma ramuwar sallan da ake bin ta, bayan ta idar suka ci abinci suka yi kallo sannan suka koma barci lokacin har 12:00pm na dare tayi.
The following day Ramcy ita kaɗai tafice tanufi gidan su Shatu, so take yi tayi musu sallama daga nan idan tadawo sai su wuce gida.
Koda tadawo RAUDHA cewa tayi ba yau zasu tafi ba, itama Ramcy bata wani damu ba tunda tasan Baban ta yayi tafiya kuma ba lokacin dawowar sa bane yanzu, idan ƴan gidan su ne zata kira su tasanar musu tana gidan su Umma.
Tun daga ranan kuwa basu da aiki sai yawo cikin gari, su je nan wajen shaƙatawan su je nan, kullum cikin siyan kayan daɗi da maƙulashe suke yi, su ci wannan su sha wannan, har Club suke zuwa
Satin su ɗaya cif kafin su nufo hanyan Zaria, ko a hanya wannan karon basu haɗu da Sojoji ba, iyakan motar su da suka gani guda ɗaya a wajen.
🌐🌐 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*FEW WEEKS*
Gobe ko jibi Daddyn RAUDHA yafaɗa mata zai dawo, shiyasa take ta farin ciki, taso yafaɗa mata Real time ɗin ne sabida taje tarbo shi amma yaƙi, shima yace be da tabbas ko zai dawo a ranan da yaɗiba mata.
Washe gari tana cikin barci Saude tashigo cikin ɗakin, ita tatashe ta tafaɗa mata Samuel yazo
Kamar an tsikare ta tamiƙe tafita da gudu
Samuel shine drevern Daddyn ta, tunda taganshi tasan Dad yau zai dawo
Lokacin da taƙarisa wajen sa yana kusa da motan da yazo, cikin fara'a take tambayan sa
"Samuel Daddy ya dawo ne?".
"No Ma'am ya bani umarni ne in ɗauke ki zuwa can gidan".
Bata ce komi ba tajuya dasauri, a Parlour tatarar da Saude tace mata su haɗa kayan su su koma can gidan, sannan ita tawuce ɗakin ta da gudu
Dama duk idan Daddy zai dawo gaba ɗaya ma'aikatan gidan suke komawa can tunda dama daga can ɗin ne suka zo, sai masu kula da gidan kawai ake bari.
Babu abinda taɗauka sai jakarta, takwashe duk ƙwayoyin ta tazuba a ciki, baza ta iya tsayawa tayi wanka anan ba idan taje can zatayi, daga ita sai riga da gajeren wando na barci tafito tana riƙe da waya a hannun ta, Numban Dad ɗinta take Kira Amma baya shiga, ahaka tafita tafaɗa cikin motan Samuel suka bar gidan
Babban katafaren gidan su suka nufa, suna zuwa gateman yabuɗe musu suka shige ciki
Wani katafaren mahaukacin mansion suka nufa wanda tsananin girman sa ya zarce na mai karatu, tun daga bakin Gate kusan tafiyar minti goma ne a mota kafin ka'isa inda aka shata wani ƙaton round about me matuƙar kyau da ƙawatuwa, da wasu irin manyan lanters masu Flower a jiki wanda ruwa ke ɓulɓulowa zuwa sama yana wani irin buɗe wa kamar zai zubo ƙasa sai yakoma ciki.
Haka suka zagaye round about ɗin suka wuce wani ƙaton gini dayake na securities ne da masu gadi haɗe da masu gyaran haraban wurin
Nan ɗin ma kusan tafiyan minti goma sukayi kafin suka isa ga ainihin gidan wanda tun daga nesa ƙayatuwar sa da tsantsan kyawun sa zai iya zautar da kai da baka taɓa gani ba
3 upstairs ne ginin kuma akwai lifter da zai kai ka duk inda kake so
A hawa na uku ɗakin RAUDHA yake, gaba ɗaya saman Glasses ne wanda idan kana wannan ɗakin zaka iya hango wancan ɗakin, but an saka cootens ako ina ta yanda baza ka iya ganin waje ba sai ka yaye labulen
Ɗakin RAUDHA babban Parlour ne da ɗakuna biyu da Toilet har da kichen aciki, akwai ɗakin games komi na more rayuwa akwai aciki, gefe ɗaya kuma ga kayan wasa irin su teddy's da sauran su, duk Daddy yazuba Mata don ya mayar da ita ne tamkar yarinya ƙarama, babu abinda zata nema be mata ba
Tana shiga ɗakin ta inda babu komi aciki sai babban katafaren Royal bed tare da dogayen sif wanda yamamaye kafataren bangon gaba ɗaya, komi na ciki Sky Green
Ɗayan kuma ɗakin kujeru ne kawai da kayan kallo aciki, sai speaku 🔊 manya-manya da sauran abubuwa na ƙyale-ƙyale, duk abinda ke ciki pink and white colour
Kayan ta tacire tashiga cikin Toilet, cikin Jacuzzi tafaɗa bayan ta haɗa ruwa da kumfa, tayi mintuna goma aciki tana kwance kafin tasoma wanka, bata son ko kaɗan Daddyn ta yadawo bata gama shiryawa ba
Bayan ta fito ta gama shafa Lotions tazira kayan ta, riga ce off Shoulder me ruwan madara, sai guntun wandon shi iya cinya shima Milk ɗin, ɗaure gashin ta tayi tasaka Room Slippers pink colour me tuntu a sama
Fitowa ɗakin tayi sai dai bata hau lifter ba sai tabiyo takan bene, da gudu take taka kan Steps ɗin har tasauka ƙasa, a cikin kujera talume tana kallon katafaren t.v plasma dake aiki shi kaɗai
Babu kowa cikin tanƙamemen parlour'n sai ita kaɗai, girman parlour'n sai da yaɗauke set uku na kujeru daban-daban
Bata jima da zama ba tajiyo horn ɗin motoci, da gudu tatashi tafita, tun daga nesa tahango motoci kusan goma suna tahowa amma haka tanufi wajen da gudun ta tana farin ciki
Kafin ta'iso har motocin sunyi parcking mutane sun soma fitowa
Motoci biyar na bodyguard ɗin Daddy ne, sauran kuma na mutanen sa ne tare da abokan sa da sukai mishi rakiya
Farin dattijon mutum ne yafito a motan tsakiyan wanda shi kaɗai ne fari tar kuma babba sosai, mutumin yana da tsananin kwarjini da cikan haiba, kallo ɗaya idan kayi masa zakaga tsantsan kamar da suke yi da RAUDHA, sai dai kuma bashi da maraba da Suhaib don shi yafi ɗauko sa sak kamar kaki yayi ya'ajiye
Da wani irin gudu tanufo mahaifin nata, duk yawan mutanen wajen tunda taƙilla idanu kansa bata ƙara waiwayan su ba
Tana isowa yamiƙa hannu yacafe ta a jikin sa, juyata kawai yake yi yana dariya cike da tsantsan ƙaunar ta, itama ɗin dariya take yi tana kiran
"Daddy.. Daddy.."
Duk wanda yagansu yasan akwai soyayya me ƙarfi a tsakanin su
Duk mutanen wajen kallon su kawai suke yi suna murmushi cike da sha'awan su
Sosai Daddy yaga Babyn nasa ta sauya masa, tayi rama sosai duk da yasan ita ɗin ba ma'abociyar cin abinci bane
Inda RAUDHA me tarbiyya ce be kamata tafito da wannan kayan agaban mutane ba, shima kuma Daddy ko kaɗan be damu da ganin ta ahaka ba bare har yaga tayi laifi
Tana jikin sa be sauke ta ba yakalli mutanen da murmushi a face ɗin sa yace
"Mu shiga ciki".
Babu musu suka nufi cikin gidan gaba ɗayan su
A Parlour suka yada zango gaba ɗayan su
Daddy ajikin sa yaɗaura RAUDHA ko kunyan mutane baya ji, dayake yana rayuwan sa irin na turawa ne shiyasa be ji kunya ba, kuma ko kaɗan baya jin shakkar nuna tsantsan soyayyar da yake mata ako ina, bare kuma ya ɗauke ta ne tamkar yarinya ƴar shekara biyar, sosai yake tsananin tausayin ta kasancewar ta tashi cikin maraicin uwa, shiyasa duk wani abun da yakamata uwa tayi ma ƴarta shi ke yi ma RAUDHA
RAUDHA lafewa tayi ajikin sa tana kallon mutanen dake zaune ana gaggaisa wa, wasu daga cikin abokan shi sai tonan ta suke yi tana murmusawa amma batace komi ba
Ahaka dai sukai ta yin ma Daddy barka tare da nuna murnan su na samun nasara da yayi a kasuwancin sa
Masu aiki duk sun jibge musu Drinks a gaban su
Sun ɗan ɗauki kusan mintuna 20 kafin suyi masa sallama su tafi
Anan RAUDHA tasake matse shi tana faɗin "I miss You Daddyyyy?"
Har da ƙwallan ta
Shima sake Hugging ɗin ta yayi yana murmushi me bayyana haƙora yace "I miss You more than you Babyna".
Ɗago kanta tayi tana kallon sa da dariya a fuskarta, sosai za'a gane farin ciki tsantsa da take ciki
"Daddy na.." Tafaɗa tana sake yin dariya bayan ta sake shigewa jikin sa
Daddy dariya yayi yace "Baby murna yayi miki yawa kin kasa magana ko".
Still ɗago kanta tayi tana kallon sa, baki awashe tagyaɗa masa kai
A lokacin ne sauran ma'aikatan gidan suka soma shigowa suna kawo mishi gaisuwa har dasu Saude aciki
Amsa musu yake yi cikin fara'a wanda zaka gane ɗab'ian sa ne hakan
Sai da kowa yafita kafin yasake kallon RAUDHA, wannan karon ma da murmushi a face ɗin sa yace "to ya kike Babyna na same ki lafiya?"
"Eh Daddyna".
Shafa kanta yayi yace "duk kin rame Sweetheart, kin yi ciwo ne baki faɗa min ba?"
Girgiza kanta tayi tana sake cusa hannun ta cikin nashi tace "Daddy ban yi ciwo ba kewar ka ne ya ramar dani".
Dariya yayi sabida yanda tayi maganar
Itama sai tatayashi tana yi tana cino baki alamun zatayi fushi
Cikin dariyan yace "sorry Baby Kar ki ɓata rai, tashi muje ɗakina sai inyi wanka mu sake gaisawa ko?".
Ɗaga ta yayi tana jikin sa wannan karon ma be sauke ta ba yanufi lifter yabuɗe yashiga.
[11/23/2020, 10:01 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON FOURTEEN*
_______📖Bayan Daddy yayi wanka parlour'n sa suka zauna, anan an rigada an jera masa abinci a dainning, don haka tare suka soma ci da RAUDHA, suna yi suna hira yana tambayan ta matsalolin ta
Sai da aka kira sallan Asar kafin yamiƙe yafita bayan yayi alwala
Itama RAUDHA dasauri tashiga ɗakin ta na Part ɗin Daddy ɗin taɗauro alwala
Ko wani upstairs akwai ɗakin ta aciki, Dad ɗin ta yana hawa na biyu ne
Bayan an idar da Sallah koda yadawo mutanen anguwa yagani sun yi masa dafifi a ƙofar gida, a zummar sun zo tayasa murna but a baɗini maula suka zo yi, sun san Alhaji me kyauta ne bazai taɓa barin su haka ba
Ai kuwa bayan ya gaisa dasu faram-faram sai yashiga cikin gidan yakira bodyguard ɗin sa ɗaya yace " yabiyo sa ya'amso musu saƙo".
Kuɗi yabashi yace yaraba musu sai wasu daga cikin kayayyaki na masarufi da yasa a ɗibo daga store duk a rabar musu kar yalalace
Zama yayi a parlour'n sa RAUDHA na jikin sa sai zuba masa surutu take yi
Sosai RAUDHA take da miskilanci amma idan tazauna gaban mahaifin ta zakai tunanin ta haɗiye rediyo ne saboda yanda take zuba kamar ana ƙara mata sabbin batir
Koda aka kira wayan Daddy dake can cikin bedroom ɗin sa da gudu taje taɗauko masa, zama tayi gefen sa tana faɗin
"Daddy Yaya ne yakira ka".
Amsan wayan yayi yana murmushi yakara a kunne da sallama a bakin sa
Daga can Suhaib amsawa yayi cikin jindaɗi sannan yagaishe shi
Ga duk kan alamu yanda suke wayan zaka san akwai shaƙuwa da junan su, anan Suhaib yake faɗa masa bazai samu zuwa ba sai jibi sabida aiki da sukai masa yawa
Daddy be wani damu ba yace masa yakula da kansa sosai Allah yakawo sa lafiya
RAUDHA ce ta'amsa wayan tana ta zuba masa shagwaɓa akan ita dai sai yazo, daƙyar ya rarrashe ta tahaƙura
Haka suka kasance a ranan cikin farin ciki, duk inda Daddy yake tana maƙale dashi, ƙarshe ma a part ɗin sa takwana.
Washe gari da wuri tatashi tayi wanka tashirya cikin biri da wando me hannun vest, sai dai bata saka wani riga aciki ba kamar yanda ake saka wa, blue colour ne na jeans, sai ta tufke gashin ta a tsakiyar kai da jelan
Tana fitowa ta tarar da Daddy zaune yana amsa call, shi lokacin ya daɗe da tashi ma har ya fita waje ya gaisa da baƙi, shigowan sa kenan yasoma waya da wani abokin kasuwancin sa
Zama tayi gefen sa har yagama sannan yakalle ta cikin so da ƙauna yace "My Baby kin tashi?".
Gyaɗa masa kai tayi tana turo baki gaba
Murmushi yayi yashafa mata kai kana yace "oya tashi muje muyi breakfast tukuna sai ki faɗa min meke damun ki".
Dasauri tatashi tariƙo hannun sa suka nufi kan dainning inda aka jera musu breakfast kala-kala
Akan cinyan sa ya'ajiye ta yahaɗa musu duk abinda suke buƙata, shi yadunga ciyar da ita har suka kammala sannan suka dawo parlour
Jan hannun ta yayi suka koma bedroom ɗin sa inda yanuna mata wasu manyan Trollys guda uku yace mata duk tsaraban ta ne, sannan yaƙara mata da sabuwar waya iPhone 11pro har da Lapton tare da keey ɗin mota, sai yanuna mata wani ƙaton computer me kamar t.v yace mata sai ta'ajiye a ɗakin games ɗin ta
Ihu kawai RAUDHA take yi tana murna, ɗarewa jikin sa tayi tai ta zuba msa peck a fuska kamar zata cinye sa
Shi kuwa sai dariya yake yi yana jindaɗin yanda take murna da annashuwa
Waya yakira, babu jimawa ɗaya daga cikin bodyguard ɗin sa yashigo yanuna masa computern yace masa yakai ɗakin games ɗin RAUDHA, dayike yasan komi na gidan tunda shine Amintaccen sa, haka yaɗauka yafice su kuma suka dawo Parlour
A ranan tare suka wuni ko fita be sake yi ba
Wajen 02:00pm. Ramcy tazo gidan taya Daddy murnan dawowa, har Part ɗin shi RAUDHA tajanyo ta tunda dama sun saba dashi, kuma shima ya ɗauke ta tamkar ƴar sa ne tunda RAUDHA tana son ta, duk abinda zai iya ma ƴarsa to itama zai mata
Har ƙasa tazuƙuna tagaishe shi, ya'amsa mata cikin fara'a yana ta tambayan ta mutanen gida, daga ƙarshe yace mata tatashi tazauna itama kan kujera, babu musu kuwa tatashi tazauna ɗin kamar yanda yabuƙata, sai suka soma hira gaba ɗaya su ukun cikin nishaɗi
Sai kusan magriba Ramcy tace zata tafi, Trolly ɗaya na tsaraba Daddy yabata, dama yayi ne don ita, itama RAUDHA sai da taƙara mata da wasu abubuwan, Ramcy tayi murna sosai kuma tayi ma Daddy godiya har sai da yace ya isa
Duk da yasaba bata kyauta amma na yau yafi na ko yaushe tunda wannan tafiyan wajen watanni uku yashafe kafin yadawo, kuma be saba yin hakan ba iyakan wata ɗaya ko zuwa kusan biyu yake yi
Drever yamayar da Ramcy har gida tare da tsaraban ta
Su ma sauran ma'aikatan gidan duk sun samu nasu tsaraban, duk wanda yake gidan kuwa ya shaida tunda an ba kowa, sun yi murna sosai tunda tsaraban ba kaɗan bane.
Da dare suna zaune aka kira Daddy a waya, abokin kasuwancin sa ne yake shaida masa akwai matsala yayi gaggawan zuwa yanzu
Kayansu da sukayi oda a UK sun samu matsala, kuma ana buƙatar su nan da 24hours
Dole hankalin Daddy yatashi, anan yake faɗa ma RAUDHA zai koma China akwai matsala
Ai nan RAUDHA tasa mishi fitina, daƙyar ya rarrashe ta tahaƙura
Wanka yayi yasauya kayan sa zuwa farar tissue yai shigan sa na hausawa, dama Daddy be cika saka kayan turawa ba anan ɗin in ba can yaje ba, amma idan yana nan shigan hausawa yake yi na manyan kaya
Motoci biyar na bodyguard suka raka sa zuwa airport, har da RAUDHA sai da tabi shi sai kukan taɓara take mishi yana rarrashin ta
Sai da Flight ɗin su yaɗaga kafin suka dawo gida.
Wajen ƙarfe 11:37pm. RAUDHA tana cikin tsaka da barci tatashi a firgice sakamakon harbin Bindiga da taji
Sosai ake harbi kamar za'a tarwatsa gidan
Nan da nan tafirgice tasaki kuka cike da tsananin tsoro, wani irin kifo wa tayi takai tabuga kanta da tyles, but bata damu ba tanufi ƙofar ɗakin tasaka keey jikin ta na wani irin kyarma kamar an saka ta a shock, zame wa ƙasa tayi tana ci gaba da sharɓan kuka, wani harbin da tasake ji kurkusa sai da tasaki fitsari tarufe bakin ta dasauri tana ƙwalalo idanu, tsaban tsoro ƙirjin ta kamar zai faso yafito, daƙyar tararrafa tanufi bakin gadon taɗau wayan ta tasoma kiran Numban Daddyn ta, sai dai baya shiga hakan yasa tasake ɓarke wa da kuka kamar ana tsuma ta, izuwa lokacin majina da hawaye ne suka haɗe sukai dame-dame a fuskar nata, yau dai ta sadakar mutuwa zatayi
Hannun ta na rawa tanemo Numban DPO ta danna masa kira, yana ɗauka tasoma faɗa masa abinda ke faruwa tana yi tana kuka
Ai kuwa nan da nan DPO da yaran sa suka nufo gidan
A can kuwa tsakar gidan sai karan batta ake yi tsakanin ɓarayin da suka shigo su wajen ashirin da bodyguard ɗin gidan, in banda musayar wuta babu abinda suke yi duk an ji ma wasu ciwo
Gaba ɗaya gidan ya hargitse kamar filin dambe, masu aiki duk sun nemi maɓuya, haka ma maƙota duk da basu san takamaiman inda ake harbin ba.
RAUDHA tana gama waya da DPO Yayan ta takira tana kuka tana faɗin "Yaya don Allah kazo kaɗauke Ni zasu kashe Ni, wayyo Allah yaya na shiga uku shikenan zasu kashe Ni mutuwa zan yi..."
Sai tasaki kuka tana sharɓan majina
Hankalin Suhaib a matuƙar tashin hankali yake tambayan ta su wanene? Amma ina ta kasa ma magana sabida tsaban kuka
Sai da yayi ta faman rarrashin ta kafin daƙyar ta'iya mishi bayani
"Don Allah kiyi shiru kinji? Kiyi shiru my dear please, I promise you babu abunda zai same ki baza su kashe ki ba kinji... Sorry.. sorry My dear zuwa gobe insha Allahu zan zo.."
"A'a yaya kazo yau katafi dani don Allah zasu kashe ni".
Suhaib kamar zai yi kuka yace "Dear baza su kashe ki ba yanzu bari in Kira Asp. Aryan yanzu zai zo kin ji ki kwantar da hankalin ki, ina zuwa zan sake kiran ki".
Ɗif yakashe wayan
Sake maƙurewa tayi ajikin bango tana ci gaba da kukan ta cike da tsananin tsoro.
A waje kuwa har ƴan sanda 👮 sun zo kuma anyi nasaran kama wasu, wasu kuma sun gudu, a cikin bodyguard ɗin wasu duk sun samu harbi sannan an kashe mutane uku har lahira.
RAUDHA bata buɗe ƙofar ɗakin ta ba sai da taji muryan DPO, nan tasake haukace musu akan sai sun kira mata Daddyn ta, shi da kanshi DPO ɗin yakira sa amma wayan sa akashe, shaf sun manta a yanzu ɗin yana jirgi wayan sa baza ta shiga ba
A taƙaice dai aranan daƙyar suka rarrashe ta suka haɗa ta da ƴan sandan da zasu yi gadin ɗakin ta, kuma bata yarda ta kwana ita kaɗai ba sai da aka kira mata su Saude da sauran masu aiki, a waje kuma duk aka ƙara matakan tsaro
RAUDHA ƙiri-ƙiri ta kasa barci in banda firgita babu abinda take yi duk da kuwa ba ita kaɗai bace a ɗakin, kuma ta hana kowa barci dole su zauna gadin ta, aranan dai haka suka kwana gaba ɗayan su ido buɗe har Suhaib da ba ma agidan yake ba, koda yakira ta saka mishi rigima yayi kar yafara yakashe wayan, a haka takwana da waya a kunne tana jin motsin sa, shi kuma sai faman kwantar mata da hankali yake yi tunda tuni barci ya ƙaurace ma idanun sa, ko kaɗan bazai iya barci ƙanwar sa na can cikin firgici ba.
Ta tsorata sosai ita duk a ganin ta ɗauke ta suka zo yi tunda tasha jin ana ɗauke mutane akashe su, sosai take matuƙar tsoron ƴan kidnappers, bata so ko kaɗan taje hannun su.
[11/26/2020, 11:51 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON FIFTEEN*
_______📖Ƙarfe 07:30am. Yayi ma Suhaib a garin Zaria, lokacin da yashiga gidan RAUDHA maƙalƙale shi tayi tana ta kuka, daƙyar yararrashe ta tayi shiru sannan yace "taje tahaɗo kayan ta su tafi" babu musu kuwa tasaka Masu aiki suka haɗa mata kayan ta
Duk ka gaba ɗaya duk wani abun buƙatun ta sai da Suhaib yasaka aka kwashe mata aka zuba a mota, mota biyu aka cika drevers sukai gaba dashi, su kuma sai suka biyo Flight suka nufi Abuja
Drevern sa yazo yaɗauke su a airport suka nufi gidan Suhaib ɗin dake Asokoro, babban gida ne me hawa biyu, sosai gidan yahaɗu matuƙa gashi an kashe kuɗi kamar baza'a mutu ba
Drever na yin parcking suka fito, Suhaib yariƙe mata hannu suka nufi cikin gidan, suna shiga parlour'n gidan
Matar sa Farida tafito daga ɗaki tana kallon su da murmushi a face ɗin ta, tana da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe
"Sannun ku da zuwa, maraba da ƙanwata".
Suhaib ne kaɗai ya'amsa gaisuwar matar tasa yayinda RAUDHA kuma in banda kallon ta babu abinda take yi, har yanzu tana cike da tsoro sosai duk da kuwa sun bar garin
Zama Suhaib yayi yazaunar da ita kusa dashi
Ita kuma Farida sai tanufi Fridge taɗauko musu drinks tahaɗo da Cups ta'ajiye musu a gaban su kana tazauna tana cewa "My Husband kayi sauri da yawa".
Suhaib dake kallon ta yace "to me zan zauna yi tunda na ɗauko ta? An gama gyara mata ɗakin saman?"
"Eh an gama, Allah yakyauta gaba to, mun gode Allah da babu abinda yafaru".
Sai kuma tamayar da idanun ta kan RAUDHA tace "Baby babu magana?"
Sai lokacin RAUDHA tabuɗi baki tace "Sannu to".
Gaba ɗaya sai da suka dara ganin yanda tayi maganar tana turo baki
Suhaib yace "tashi Baby in Kai ki ɗakin ki sai ki huta ko kafin akawo miki kayan ki?".
Babu musu tamiƙe yariƙe mata hannu suka haura sama
Farida tabi su da kallon aranta tana mamakin irin ƙaunar da Mijin nata yake nuna ma ƙanwar sa
Ko kaɗan bata kishi da RAUDHA, hasali ma itama tana ƙaunar ta sosai tunda ta silan ta ne tasamu Suhaib ɗin, da fari ita take mahaukacin ƙaunar sa tun lokacin da yasoma aiki a Companin Daddyn sa, itama a lokacin tasamu aiki a Companin, sai tasoma shige masa suna mutunci batare dashi yasan son sa take yi ba
Duk wanda yake mu'amala da Suhaib dole ne yasan ƙaunar da yake ma ƙanwar sa, koda kuwa baka taɓa ganin ta bane labarin ta sai ya ishe ka, be da wani magana sai ta RAUDHA, hakan ne yasaka itama Farida tasoma nuna ƙaunar ta gare ta, duk da batasan RAUDHA ba amma sai tasoma tayasa ƙaunar ta, wannan dalilin ne Suhaib yasake sakin jiki da ita, domin sosai yake jin daɗin yanda take nuna ƙaunar ta ga ƙanwar sa, komi tasamu tace yakai ma RAUDHA, komi maganar ta RAUDHA, hakan yasaka soyayyar Farida tashiga ransa ainun tunda tana son ƙanwar sa, ita kanta Faridan tasan sabida RAUDHA yake son ta
Har Allah yasa daga ƙarshe suka yi aure, wajen shekara ɗaya da rabi kenan yanzu
RAUDHA sau biyu tataɓa zuwa gidan, sai dai har yanzu ta kasa sake jikin ta da Faridan duk da kuwa tana nuna mata kulawa da soyayya, sai dai ita akwai ta da rashin sabo idan har bada Daddy ko Suhaib ba bata son wani yashiga jikin ta, that's why bata cika zuwa ba tunda shi Suhaib ɗin yana zuwa can.
A halin yanzu Farida ta ajiye aikin ta, tun sanda tasamu ciki Suhaib yace mata sai dai ta'ajiye aikin ta rainan masa Yaron sa, dama can shi baya son Matar sa tariƙa aiki tunda suna da kuɗin da komi zai iya wadata ta dashi
Itama kuma bata yi musu ba ta'ajiye kamar yanda yake so ɗin, but duk wata yana bata albashi hakan yaƙara faranta mata sosai, kuma taji daɗin abun da yayi mata shiyasa bata damu yanzu tayi aiki ko kar tayi ba, tunda mijin ta na mata duk abinda take so..
Dafa kafaɗan ta yayi hakan yasa tadawo duniyar tunanin da talula tabi sa da ido
Murmushi yasakar mata yace "tunanin me kike yi haka har na dawo baki ji ni ba?"
Numfashi taja tace "babu komi Husband".
"Ok to ki kula min da ƙanwata don Allah, idan tatashi kiyi mata duk abinda take so ki kula da ita plz sweetheart?"
Murmushi tayi tace kar ka damu insha Allahu bazan baka kunya ba Mijina".
Kyakykyawar murmushin sa yayi mata yana shafa gefen kumatun ta yace "Thanks Sweetheart, yanzu ta kwanta ne kayan ta na kan hanya idan sun iso sai ki saka a shigar mata dashi ɗakin ta, Ni zan tafi office insha Allahu Nima bazan daɗe ba zan dawo".
"To amma bakayi breakfast ba katafi yanzu kuma haka zaka tafi kenan baka yi ba?" Tayi maganar idanun ta cikin nasa
Suhaib yace "nayi late yanzu Sweetheart idan na je office zan yi kinji?"
Gyaɗa masa kai tayi
Shi kuma yayi mata kiss a lips ɗin ta sannan yasake shafa kumatun ta yace "sai na dawo Byeee ki kula da kanki".
Murmushi tayi masa tare da addu'ar dawowa lafiya.
Sai da yabar parlour'n kafin tamiƙe daƙyar takoma ɗakin ta dake ƙasa.
🌐🌐🌐
Kwana biyu da zuwan RAUDHA gidan sannan Suhaib yasamu Numban Daddy ya shiga, lokacin suna zaune a parlour sai yatashi tsam yafice, sai da suka tattauna da Daddy ɗin kafin yadawo yamiƙa wa RAUDHA wayan
"My sweetheart ga Daddy zai yi magana dake?"
Wani irin tsalle tayi tararumi wayan tana ihu tasaka a kunne
"Daddyyyy". Tafaɗa da ƙarfin da yasa Suhaib da Farida suka rufe kunnen su suna dariya
Dama koda yafita yin wayan batasan da Daddy yake yi ba
Daga can Daddy murmushi yayi cike da farin ciki yace "my Baby Kar ki fasa min dodon kunne mana".
Kawai sai tasaki kukan shagwaɓa tana faɗin "Daddy nayi missing ɗin ka.. yaushe zaka zo kaɗauke Ni?"
"Sorry My Baby.. bazan dawo nan kusa ba coz akwai matsala da kayana suka samu dole zan zauna zuwa ɗan wani lokaci".
Kuka tasoma mishi sosai tana bubbuga ƙafa tace "Daddy Allah Ni bazan koma can ba sai dai kazo kaɗauke Ni bazan iya zama Ni kaɗai ba".
Daddy yace "my dear ai dama bance ki koma can ɗin ba, tunda kina gidan yayan ki zaki zauna har nadawo sai in zo in ɗauke ki ko?"
Ɗaga kai tayi takalli Suhaib dake kusa da ita, fuskarta sharkaf da hawaye tace "Daddy bana son nan.."
Riƙo hannun ta Suhaib yayi kafin yace "baki son wajena ko my sister? Kin fi son ki zauna acan kidnappers su kama ki su kashe ki.."
Tun kafin ma yaƙarisa maganar tasoma girgiza mishi kai
Daddy yace "my dear ki zauna a wajen yayanki zaki fi samun kulawa, kinga waɗannan mutanen da suka shiga gida na anyi bincike an gane ke suka zo ɗauka sabida suyi garkuwa dake, idan kika koma yanzu akwai matsala".
Cikin zubar hawaye tace "to Daddy zan zauna bana so su kama Ni".
"Yauwa my dear, kinga sai ki soma karatun ki anan tunda Yayan ki yace min an soma siyar da Admission uhmm?"
Shiru kawai tayi bata ce komi ba
Suhaib da har yanzu yana riƙe da hannun ta yasoma murza mata yatsu yana faɗin
"Daddy zata zauna anan ɗin insha Allahu zanna kula da ita babu abinda zai faru da ita".
"Yauwa Suhaib ka kula min da ita sosai duk abinda take so kayi mata, idan nadawo zan zo har nan in ganki, and mutanen da suke neman ki acan ma baza su ƙara ganin ki ba bare su kama ki ko my dear?".
"Eh Daddy". Tafaɗa tana turo baki
Farida ita dai nata ido ne, kallon su kawai take yi cike da burgewa, tabbas duk wanda yazauna dasu zai san suna matuƙar ƙaunar ta, tana jinjina irin girman soyayyar da suke nuna mata, tana ta kallon su har sanda suka gama wayan ita kuma RAUDHA tamiƙe dasauri tanufi upstairs inda ɗakin ta yake
Tana shiga tafaɗa kan gado tana rufe idanunta, ko kaɗan bata jin daɗin zaman gidan, ta saba da can ta saba da rayuwanta ita kaɗai, a kwana biyun nan sosai take jin kewar can, ga matsanancin kewar Ramcy da take ji, ko babu komi baza ta so tarabu da ƙawarta ba shiyasa duk bata jindaɗi a zamanta na nan
Tashi zaune tayi taɗau wayan ta dake ajiye a bed side drower, tun sanda tazo takashe ta'ajiye bata sake ɗauka ba sai yanzu, kunnawa tayi tay dialling Numban Ramcy, sai da taɗauka sannan takoma takwanta
"My Besty Ina kika shiga nayi neman ki har na gaji?" Cewar Ramcy kamar zata yi kuka
Lumshe idanu RAUDHA tayi kafin tabuɗe tace "I miss You my Besty.. Ina Abuja?"
"Shine baki kira ni kin sanar min ba? Sannan kika kashe wayan ki, naje gidan ku but ba'a buɗe min ƙofa ba, kullum sai naje ko yau ma sai da naje amma banga kowa ba, meke faruwa ne?"
Abinda yafaru RAUDHA tasanar mata
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Amma basu yi miki komi ba ko Besty?"
"Babu abinda sukai min ki kwantar da hankalin ki".
Ajiyan zuciya Ramcy tasaki da ƙarfi wanda sai da yasa RAUDHA darawa tace
"Wannan ajiyan zuciya haka my Ramcy?"
"Hmm ai dole ne my Besty wlh bazan taɓa jindaɗi ba idan wani abu yasame ki, dole zan shiga tashin hankali sosai".
Murmushi RAUDHA tayi cike da jindaɗi batare da tafurta komi ba
"To yanzu yaushe zaki dawo ko sai Daddy ya dawo garin?"
Girgiza kanta RAUDHA tayi fuskarta na nuna damuwa tace "Besty bazan dawo nan kusa ba sabida waɗanda suke son yin garkuwa dani suna nan ba'a kama su ba, dole zan zauna anan har sanda za'a yi solving matsalan".
Shiru Ramcy tayi batace komi ba
Sai da RAUDHAN tasake mata magana kafin tace
"Shikenan Besty mun yi nisa?"
"Nima banji daɗi ba wlh, amma komi zai wuce ai zamu sake haɗu wa ba da jimawa ba, zan saka Ya Suhaib yakawo ni".
Ramcy tace "nima idan nasami lokaci insha Allahu zan riƙa zuwa har nan Besty, muna nan tare ako ina ne, nisan gari bazai hana Ni zuwa gare ki ba".
Murmushin jindaɗi RAUDHA tayi kafin tace "Thanks friend Allah yabar mu tare".
"Ameen ameen My Besty, kinga aunty Nafeesa ta haihu ɗan babu rai?"
Cikin damuwa RAUDHA tace "oh yaushe kenan?"
"Jiya ne, dama cikin be isa haihuwa ba".
"Eyya.. ki miƙa min gaisuwa ta gare ta kinji?"
"Insha Allahu zata ji Besty".
Daga nan hira suka ɗan taɓa kaɗan kafin takashe wayan ta'ajiye
Tana nan kwance shiru kamar ruwa ya ci ta, sai kuma daga baya tamiƙe taɗauko HangBag ɗin ta wanda tazuba ƙwayoyin ta
Tunda tazo gidan komi bata sha ba, shiyasa take jin ta daban
Kallon cikin jakar tayi, babu yawa duk ya kusa ƙare wa
Tsaki taja tana ajiye jakan, sai kuma taɗauka taciro tasoma afa ƙwayoyin, sannan kuma takoma takwanta tana lumshe idanun ta, ajiyan zuciya kawai take sauke wa har zuwa lokacin da ƙwayoyin suka soma mata aiki, gyara kwanciyarta tayi babu jimawa barci yayi awon gaba da ita, a lokacin ƙarfe 05:30pm.
Har bayan isha'i bata farka ba, don haka Farida tashigo ɗakin domin tatashe ta tunda ta shigo har sau biyu tana duba ta
A bakin gadon tatsaya tasaka hannu tana shafa baby face ɗin ta, ta jima tana ƙoƙarin tashin ta kafin tabuɗe idanun ta da suke a rine sosai, sake lumshe idanun tayi tana buɗe wa ahankali
Murmushi Farida tayi mata tace "ƙanwata wai barcin nan baya isan ki ne? Tunda kika zo babu abinda kike yi koda yaushe sai barci, ko kasa sai ya shafa miki lafiya ai".
Kallon ta kawai RAUDHA take yi bata ce komi ba, sai dai a yanzu ɗin ta ɓata fuska
Still Farida murmushi tayi tasaka hannu tana janye jakar dake ajiye akan gadon tana faɗin "kiyi haƙuri kinji, naga Yakamata ki tashi kiyi sallah ne kici abinci tunda lokaci na ƙure wa".
Kamar ance taleƙa cikin jakan sai taga ƙwayoyin ciki, duk da Farida ba wai tasan kayan maye bane amma taga an rubuta sunan shi ajiki, sai kawai tasaki baki tana kallon RAUDHA dake ƙoƙarin miƙewa zaune
Bata ce komi ba kuma taɗau jakan tamayar mata inda sauran suke sannan tafice
Ɗakin su takoma inda Suhaib ke zaune yana faman aiki a Lapton, zama tayi kusa dashi kan Two sitter tana kallon sa, cikin sanyin murya tace
"Dama RAUDHA tana shan kayan maye?"
Cakk yatsai da abinda yake yi yana ɗago wa yakafe ta da idanun sa masu matuƙar kyau.
[12/20/2020, 4:01 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON SIXTEEN*
_______📖Iska yafesar ta cikin bakin sa kafin yace "Nasan tana sha ai".
Baki sake Farida take kallon sa, cike da tsantsan mamakin sa tace "kana nufin kana sane tana wannan rayuwan but bakayi komi akai ba?"
Zuwa yanzu damuwa ne sosai yanuna a face ɗin nasa, cikin rashin jin daɗin halin da ƙanwar nasa take ciki yace "Ni kaina bana jindaɗin halin da Baby take ciki amma bansan ya zan yi ba, na rarrashe ta na faɗa mata illan hakan but taƙi ji".
Ido Farida tazuba masa ta kasa cewa komi, mamaki al'ajabi duk ya cika mata zuciya, bata taɓa tunanin soyayyan da suke mata zai saka su bar ta tana irin wannan rayuwan ba, a matsayin ta na ɗiya mace ma ba na miji ba
"Lallai kam akwai aiki". Tafaɗa a ranta kafin a fili tace
"Wannan wani irin so kake mata da har zaka kai ta ga halaka?"
Tsare ta da idanu yayi cikin rashin fahimta yace "me kike nufi Wifey?"
"Ina nufin taya zaka bar RAUDHA tana shaye-shaye but ka kasa hana ta? Kana tunanin halin da zata shiga nan gaba? Meyasa soyayyar ta zai rinjaye ka kakasa ɗaukan mataki akanta? Idan baka sani ba wannan ba soyayya bane Husband, idan har baza ka hana ta wannan ɗabi'an ba tabbas nan gaba zaka yi nadama".
Suhaib yace "ya kike so in yi My Wife? Kar ki manta bazan iya ko ɗaga yatsa bane akan ta, Ni na rasa ta yanda zanyi in hana Baby Shan kayan maye, ko kaɗan bana son ɓacin ranta.."
"Wannan ba hujja bane Sweetheart, tabbas idan har zaka ga tana aikata saɓon Allah kabar ta to wlh baka son ta sannan baka ƙaunar ta, kuma wlh sai Allah ya tambaye ka idan har baka taimaki rayuwan ta ba tunda har da kwamashon ka cikin gurɓacewar tarbiyyar ta". Taƙarike maganar ta tana ƙoƙarin miƙe wa
Ruƙo hannun ta yayi yana mayar da ita yace "ina zaki je kuma? Don Allah ki zauna ki bani shawara bansan ya zanyi ba, Ni kaina nasan ina da laifi, but ke kanki kinsan halin Baby, hakan zai iya kawo babban matsala a tsakanin mu, sannan bansan ma taya zan iya ɗaukan mataki akanta ba".
Izuwa yanzu haushi sosai yake bata, duk da tasan girman soyayyan da suke mata shi da Daddy amma hakan ba yana nufin baza su iya mata faɗa ba don kawai kar ranta yaɓa ci..
"Kinyi shiru my Wife? Taya kike ganin zan ɓullo ma al'amarin?"
Ajiyan zuciya tasauke kafin tace "dole ka ajiye soyayyan ta agefe kafaɗa mata gaskiya, idan takama ma har hukunta ta kayi idan har hakan zai saka tadena.."
Dariya Suhaib yasaki hakan yasa Farida tatsayar da maganar ta tana bin sa da idanu
"Wai kina tunanin Baby zan hukunta? Ni ɗin?"
Sai kuma yasake kecewa da dariya
Ita kuwa wannan karon kallon sa take yi cike da tsantsan tausayin sa, tabbas soyayyar RAUDHA ya rigada yayi tasirin da baza su taɓa koda ɗaga yatsa akanta ba, koda kuwa hakan na nufin rabuwa da farin cikin su ne
Kanta tajinjina kafin tace "to Allah yakyauta tunda baza ka iya ba".
Sai tajanye hannun ta kawai tamiƙe tafice a ɗakin
Shima be sake dakatar da ita ba yaci gaba da aikin sa, be jima ba yajanye Lapton ɗin yana miƙe wa tsaye, miƙa yayi yana yarfe hannayen sa, sai da yaɗan jujjuya jikin sa yanda zai saki kafin yanufi ƙofa yafice
Akan kujera yatarda ita zaune
"My wife taso muje muyi dinner yunwa nake ji, Ina Baby bata fito bane?"
Yaƙarike maganar yana kallon saman, kafin kuma yamayar da idanun sa kan Faridan da a yanzu take ƙoƙarin tashi, zuwa wajen ta yayi yataimaka mata tatashi
"Bata fito ba". Taba shi amsa tana yin gaba abin ta
Juyawa yayi yanufi upstairs ɗin don kiran ta
Ita kuma Farida kan dainning tanufa taja kujera tazauna, sannan tabuɗe abincin tana zuba wa a plate iya wanda zata ci
Kamar minti 5 da hawan sa sai ga su sun sauko, tana manne da jikin sa sai mishi shagwaɓa take yi shi kuma yana mata dariya
Idanun Farida na kansu har suka ƙariso, zama suka yi Suhaib ɗin yasoma saving ɗin su shi da ita
Tun da suka soma cin abincin babu wanda yayi magana
RAUDHA tasoma tashi bayan ta ture Plate ɗin
"Aaah Baby har kin gama?" Suhaib yafaɗa idanun sa akanta yana taunan abinci
Gyaɗa masa kai tayi tana langaɓe kai
"Ok Nima na ƙoshi jira Ni muje".
Tashi yayi yariƙe mata hannu suka nufi cikin parlour'n
Ido kawai Farida tasanya musu ta ma rasa tunanin da zata yi, janye idanun ta tayi taci gaba da cin abincin ta har sanda tagama sannan takoma cikin parlour'n
Hira suke yi don haka itama tadunga saka musu baki.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
A cikin sati biyu da zuwan RAUDHA gidan har Suhaib ya gama mata komi na school ɗin ta, yau ce ranan da zata fara zuwa don haka tatashi da wuri cike da ɗoki, dama ita akwai ta da son karatu sosai
Ta gama shirin ta cikin farar riga me taushi sosai, rigan dogon hannu yake dashi kuma irin me wuyan nan ne dogo, sai tayi stocking ɗin rigan cikin blue pencil Jeans ɗin ta, tasaka Belt baƙi me ƙyalƙyali, Combat tasaka a ƙafafun ta baƙi sannan ta tsaga gashin kanta tasanya Ribom biyu kalan blue, yau har da saka Wrest watch a hannun ta fari, sosai tayi kyau kamar wata baby doll sai tashin ƙamshi take yi, haka taɗau HangBag ɗin ta tafito tana zuba murmushi
Tunda Suhaib yahango ta yake faman zuba murmushi, abinci yake ci but sai ya'ajiye spoon ɗin yana faɗin
"Wow my dear Baby kinyi kyau".
"Thanks Yayana". Tafaɗa tana murmusawa har haƙoran ta suna bayyana
Farida dake zaune gefen Suhaib ɗin akan dainning ita dai kallon RAUDHAN take yi cike da mamaki, sai dai bata iya cewa komi ba tana jiran taji me Suhaib ɗin zai ce game da shigan ta
Zuwa tayi taja kujera tana kallon Farida
Hakan yasa Faridan sakin murmushi tana cewa "baby kinyi kyau".
Cike da jindaɗi RAUDHA tace mata "tnz Aunty".
Suhaib yace "Baby gan ɗoki baza ki yafa ko mayafi bane a kan ki?"
Ɓata fuska tayi tana kallon sa tace "Ni bazan saka ba".
Miƙe wa yayi be sake bi ta maganan ba, sai peck da yayi mata a goshin ta sannan yayi ma Farida yay musu sallama yafice
Farida tana so tayi mata magana amma kuma tana jin tsoro, daga ƙarshe dai tayanke shawaran yin mata maganan, ɗago kai tayi tana kallon RAUDHAN dake sipping coffee tace
"Ƙanwata meyasaka zaki yi wannan shigan bayan fita zaki yi?"
Cakk RAUDHA tatsai da shan Coffee ɗin tana kallon Farida, sannan takuma maida idanun ta jikin ta tana kallon abinda Faridan tagani har ta'iya mata magana, bata ga komi ba hakan yasa taɗago kai tana kallon ta, sai dai bata iya cewa komi ba illa zuba mata shanyayyun idanunta da tayi
Murmushin yaƙe Farida tayi tace "naga baki rufe gashin ki bane kamar yanda Yayanki yafaɗa".
Taɓe baki RAUDHA tayi tana miƙe wa
"Ban buƙata ne". Tafaɗa tana yin gaba
Kallon ta kawai take yi har tafice, sai tasaki ajiyan zuciya tana faɗin "Allah ya kyauta to".
Fitan RAUDHA parcking lot tanufa tashiga motan ta da Daddy yasake mata, tunda har dashi duk aka ɗauko mata, jan motan tayi tay bakin Gate tana buga horn
Jiki na rawa Gate man yabuɗe mata tafice da gudun gangancin ta
Bata zarce ko ina ba sai makarantan su, bayan tayi parcking sai da taɗau lokaci kafin tafito cikin motan sannan tarufe, tasoma tafiya cikin tafiyan ta me nutsuwa tamkar baza ta taka ƙasa ba
Dayike school ɗin haɗuwan mutane daban-daban ne kuma ƙabila iri-iri don haka shigan RAUDHA be zama baƙo agare su ba, sai dai hakan be hana idanun mutane sauka kanta ba sabida haɗuwan ta, duk inda tabi ana kallon ta
Ta rigada tasan department ɗin su tunda ranan ƙarshe da Suhaib zai zo ya kammala mata duk registration ɗin ta da ita suka taho, kuma duk ya nuna mata wajaje da dama a school ɗin
English double major zata karanta don haka can department ɗin tanufa.
.
_to ga fa RAUDHA a school bari mu ga me zai faru?_
[12/26/2020, 3:28 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON SEVENTEEN*
_______📖Holl ɗin da zasu yi karatu ta dosa tashige
Babu wasu ɗalibai sosai aciki kasancewar safiya ne kuma sabbin zuwa ne, gashi time be yi ba
Can ƙarshen kujeru tanufa tazauna batare da ta kalli kowa cikin holl ɗin ba, tana nan zaune tana latsa wayan ta ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, mutane sukai tashigo wa da ɗai-ɗai har suka yi rabin ajin wanda ga duk kan alamu yawan nasu bazai fi hakan ba
Can kuma Malamin da zai ɗauke su lecture yashigo, suka gaishe shi ya'amsa da fara'a
Da fari Barka da zuwa yasoma yin musu a matsayin su na sabbin ɗalibai, sannan yaɗaura da ɗan guntun nasihan sa kafin yasoma gabatar musu da sunansa da kuma lecturen da zai musu
RAUDHA na zaune har a lokacin kamar yanda take, sai dai yanzu ta ɗauko Tap ɗin ta wanda Suhaib yasiya mata tana yin jotting a ciki, bata kallon malamin amma duk abinda yake faɗa tana ji kuma tana rubuta abinda zata ƙaru aciki.
Bayan ya gama sai yatambaye su idan da me tambaya yayi masa, kun san sabbin ɗalibai akwai su da tsoro sai idan sun saba, don haka kowa yanoƙe yaƙi ɗaga hannu duk da kuwa wasun su suna da tambaya
RAUDHA da sai yanzu taɗago kanta takalli Malamin da mutanen ciki taɗaga hannun ta batare da ta furta komi ba
Malamin da idanun sa yasauka kanta yabata daman tambayan
Don haka kowa yajuyo yazuba mata idanu ana kallon ta, wasu ma sai lokacin suka ganta, wasu kuma basu yi zaton ƴar ajin bane duba da yanda taje can baya nesa dasu ta keɓe kanta
Tambaya tasoma jero masa yana bata amsa
Abun har sai da yaba ɗalibai mamaki, ganin yanda take ta zubo tambayoyi cikin daddaɗan muryan ta me sanyi
Shi kuwa Malamin sai amsa mata yake yi, don har shi ta burge shi, shi a rayuwa yana son ɗalibi me yawan tambaya akan karatu, hakan na saka wa ɗalibi yay saurin fahimta tunda bashi da tsoron tambayan Malami
Ita kuma RAUDHA dama halin ta ne tambaya a aji, ka mun kaga ta ɗaga hannu da sunan ba ma malami amsa to sai dai shi yatashe ta, amma duk tambayan da malami zai yi a aji koda ta sani baza ta tashi ta faɗa ba, but da zaran ya ba da daman tambayar sa to anan ne zatai ta jero mishi tambayoyi kaf abinda take so tasani, kuma baza ta taɓa ko jin kunya ko tayi tunanin shi malamin zai yi tunanin tana son ƙure sa ne ba, ko ya kai ashirin ne tambayoyin ta sai tayi maka, sai dai kai kace ya isa haka nan
Shiyasa sanda tayi secondary school babu malamin da be san ta ba har CE mata suke yi sarkin tambaya.
Questions biyar tatambaye sa kuma duk ya amsa mata
Shirun da tayi yatabbatar ma Malamin ta gama don haka sai yatambaye ta sunan ta
Taba shi amsa da *"RAUDHA ElMUSTAPHA MAKAMASHI".*
Jinjina kansa yayi kafin yace "That's good RAUDHA, da fatan dai kin fahimci duk tambayoyin naki ko?"
Tagyaɗa masa kai
Murmushi kaɗai yayi mata yakalli ƴan ajin da suke mamakin ta jin sunan musulmai ke gare ta, yayi musu sallama yafita
Kasancewar Lecture ɗaya suke dashi a yanzu ɗin, sai zuwa goma zasu shiga wani don haka ɗalibai suke ta fita, waɗanda kuma zasu zauna suka gyara zama suka dasa hiran su a tsakanin su
RAUDHA ma tana zaune bata tashi ba tana bitan karatun, sosai RAUDHA take son karatu shiyasa idan har ba komi take yi ba to karatu shine abokin hiran ta, bata wasa da karatu ko kaɗan that's why take da ƙwaƙwalwa
Har time ɗin lecture yayi Malamin yashigo yasoma gabatar musu da karatun sa, One hour yaɗauka kafin yafice
A lokacin ne RAUDHA tamiƙe tasaka Tap ɗin ta cikin jaka sannan ta rataya tayi hanyan fita, bata lura ba tayar da keey ɗin motan ta
Wata dake zaune su biyu da wani saurayi manne da juna a tsakankanin kujerun bayan, ita talura takalli Saurayin nan tace
"Kaga wancan Babe ɗin ta yarda keey ɗin ta".
Kallon wajen da tatashi yayi yahangi mukullin yashe a ƙasa, kafin yace "to yanzu ya za'a yi zaki kai mata ne ko kuwa?"
"Bari in Kai mata dai, kasan Babe ɗin ta min kaga sai mu ma ƙulla ƙawance".
Dariya yayi yace "baki da dama ke dai, daga shigowar ki har zaki soma jaye-jaye".
Fari tayi da ido tana miƙe wa tsaye tace "ya son ranka? na san ko kai ta burge ka ba dai zaka faɗa bane kawai".
Still dariyan yasake yi
"To je ki dawo dai sai mu tattauna maganar mu, kar kuma ki shanya Ni fa".
"Baka da damuwa". Tayi maganar tana ɗaukan keey ɗin lokacin da taƙarisa wajen
Tana fita hole ɗin tahangi RAUDHA batai wani nisa sosai ba, kasancewar tana tafiyan ne tana latsa wayan ta
Cikin sauri taƙarisa wajen ta tayi mata sallama
RAUDHA bata san da ita ake yi ba duk da kuwa taji sallaman kusa da ita
"Aslm alaikum RAUDHA". Tasake sallaman tare da kiran sunan ta
Hakan yasa RAUDHAN taɗago kai tana kallon matashiya ƴar gayun dake tsaye a gaban ta, wanda a girme dai baza ta fi ta da shekaru biyu ba
Ganin kallon da RAUDHA ke mata batare da ta amsa mata sallaman ba, sai tayi mata murmushi tasake cewa
"Sannu ko?"
Gyaɗa mata kai tayi tana sake kafe ta da idanu
"Keey ɗin ki kika yar a class shine na ɗauko miki".
Tayi maganar tana miƙa mata keey ɗin
Kallon keey ɗin tayi kafin tasaka hannu ta'amsa tana maida idanun ta kanta
"Thanks". Tafaɗa cikin dashashshiyar muryan ta
"Babu damuwa.. Ni sunana Rash ko zamu iya zama friend sabida gaskiya kin burge Ni? Zan so mu kasance ƙawaye". Rash ɗin tayi maganar tana faɗaɗa murmushin ta
Ɗan jimm RAUDHA tayi tana kallon ta batare da tace komi ba
"Yanzu ina zaki je sai muje in raka ki kafin mu shiga Lecture".
Waro idanuwa RAUDHA tayi cike da mamakin ta, sai kuma tayi gaba batare da ta furta uffan ba
Duk da Rash taji haushin shirun da tayi mata, amma ita a ganin ta ci gaba ne a ganta tare da RAUDHA, duk da bata san ƴar gidan wanene ba but kallo ɗaya kayi mata zaka san a gidan manyan mutane tafito, barin ma yanzu da mutane suke ta kallon su, tasan idan tayi tarayya da ita zata sake zama Big gril ne
RAUDHA da har ta kai jikin motan ta tana ƙoƙarin buɗe wa, sai tatsinkayi muryan Rash kusa da ita
"Plz sister ko dai ba kya son tarayya Dani ne shiyasa kika ƙi kula Ni?"
Juyowa RAUDHA tayi takalle ta, sai kuma ta ɓata fuska tace "bana son friend.. ba shi.. yakawo ni.. ba".
Yanda tayi maganar a ɗai-ɗai yasaka Rash tasaki baki tana kallon ta, har tashige motan ta bata motsa a wajen ba, sai da taji an dafa ta sannan tajuya dasauri tana kallon wanda ke kusa da ita
Murmushi yayi mata yace "maganin ki kenan ai, taƙi kula ki ko?"
Huro hancin ta tayi batace komi ba illa maida idanun ta kan motan RAUDHA da tay nisa tayi
"Ke da ganin yarinyan nan kin san ba kalan ki bace, kallo ɗaya wlh nayi mata nasan zatay girman kai ne, muje da Allah kin tsaya anan rana na gasa mu".
Kallon sa tayi tana hararan sa kafin tace "mtsww dalla kar ka ishe Ni, ina zamu je ne?"
Baki yabuɗe
"Ke fa kika ce yunwa kike ji zamu je capteria amma kuma kike tambayana? Ko dan wannan yarinyan ta ɓata miki rai zaki fanshe a kaina, ke fa baki da mutunci wlh, baki sanin wanda zaki sauke tijaran ki a kanshi sai Ni".
Murguɗa masa baki tayi tay gaba abinta
Shi kuma yabi bayan ta yana sauya zancen dan dai ta sauko
"Rashh muje mana mu kora wlh yau gaba ɗaya bana jindaɗin yanayin sabida ban jini a sama ba, gashi kuma wancan shegen be zo ba shiyasa yau ko son shiga Lecture bana yi na zo na tare a wajen ki".
Bata tanka sa ba illa tafiyan ta da taci gaba da yi
Sai shima yayi shiru be sake cewa komi ba.
🌐🌐🌐
Fitan RAUDHA cikin school ɗin sai tasoma zagaye akan titi ta rasa inda zata je, so take yi tasami wajen da zata sayi kayan mayen ta tunda nata duk sun ƙare
Haka tay ta kewaye gari, sai a wani Club tatsaya tashiga tatambaya, bata samu abinda take so ba illa su Wine 🍷 kala-kala da suke dashi, fito wa tayi batare da ta siya ba don ita tafi son na afawa ba kasafai take ƙaunar Giya ba
Motan ta tahau tay gaba, a wani babban kanti ta tsaya tayi siyayya cikin baƙin leda takoma mota, kayan ciye-ciye ne fal a cikin ledan
Tana tuƙi tana cin Cake 🍰 har takoma school, bayan tayi parcking sai tazauna cikin motan taci gaba da ciye-ciyen ta, youghot taɗauka tana korawa da Cake ɗin
Bayan ta gama tazuge glass ɗin ta jefar da goran tamayar tarufe, share bakin ta tayi da tissue sannan takalli Wrest watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyan hannun ta, ƙarfe 12:40pm. Don haka tabuɗe motan tafita tarufe tanufi Hole ɗin da zasu ɗau darasi
Tana shiga tazauna a inda tazauna ɗazu
Sai ga Rash itama ta ƙariso wajen tazauna kusa da ita tana mata murmushi
Kallon ta kawai RAUDHA take yi batare da tace komi ba ganin Malam ya shigo, sai taɗauko Tap ɗin ta taɗaura a cinya tasoma sauraron karatun sa
Rash kuma ko a jikin ta sai ma buɗe jakan ta da tayi taciro wani ƙaramin kwalba, ta ɗan duƙar da kai tana kurɓan abinda ke ciki
Hakan yasa RAUDHA taɗago kai tana kallon ta, kwalban tabi da kallo na tsawon lokaci kafin takau da kanta, bata sake kallon ta ba har sai da Malamin yafita sannan tajuyo tace
"Aina zan samu wannan?" Tayi maganar tana nuna kwalban hannun ta
Washe baki Rash tayi tace "kema kice ƴar hannu ce kenan?"
RAUDHA bata fahimci abinda take nufi ba sai tagyaɗa mata kai tasake cewa "ina so ne idan zan samu".
"Ai kuwa kin zo inda zaki samu duk kalan da kike so, Ina zuwa bari in Kira Maan".
Wayan ta taɗauka talatsa tanemo wani Numba da akayi serving da Sweety, sai ta danna kira, yana ɗagawa tace
"Maan shigo class ɗin mu yanzu ina jiran ka".
Wayan takashe tamaida kallon ta kan RAUDHA tace "baki da damuwa domin Zen ke samo mana duk abinda muke buƙata, kema zaki samu".
Murmushi RAUDHA tayi bata ce komi ba
Dai-dai nan Maan yashigo yazauna saman Deks yana faɗin "ya dai menene?"
Rash tace "ƙawata ce take buƙatan kayan maye ina Zen yake?"
Kallon RAUDHA yayi sannan yamaida idanun sa kan Rash yace "ke dai sai da kika shige mata kamar wata mayya, to yanzu Ni zaki tambaya bayan kinsan be shigo school ba yau?"
Hararan sa Rash tayi tace "wai to ina ruwan ka idan na shige mata, bana son fa saka ido".
Sai taja tsaki tana kallon RAUDHA da tamayar da hankalin ta kan Tap tana shafawa batare da ta maida hankali kan abinda suke cewa ba
"Ƙawata ki bari gobe wanda zaki samu a wajen sa zai zo, idan ya zo sai in haɗa ki dashi kuyi maganar wanda kike so yakawo miki".
Ɗago kai RAUDHA tayi takalle ta, sai ta ɗan yi murmushi kafin taɗau jakar ta tabuɗe taciro kuɗi, miƙa ma Rash tayi sannan tayi mata bayanin wanda take so idan ya zo sai ta amsar mata ta'ajiye mata
Rash kuwa sai washe baki take yi ganin kuɗin da RAUDHA ta bayar me yawan gaske
Ita kuma RAUDHAN sai tatashi tafice tabar su nan
"Kutt.. wlh yarinyan nan ba ƙaramar yarinya bace, kai daga gani zan ji daɗin ƙawance da ita".
Dariya Maan yasaki yace "ke dai kin bani wlh".
"Eh ɗin naji, kasan yanzu abinda za'a yi? Bari in ɗibi rabo na domin kuɗin nan yayi yawa wlh, wannan kuma kariƙe nasan zaku fi haɗuwa dashi sai kaba shi".
Amsar kuɗin Maan yayi yatura cikin aljihu yana miƙe wa
"Da Allah tashi muje in sauke ki, yau akwai inda zani wlh, gashi ma ina so in gangara wajen Asha be da lafiya".
Miƙe wa tayi tana rataya jakanta kafin tace "shine baka faɗa min ba? Ai kawai mu wuce tare don babu inda zan fita yau, wahalan makarantan nan ma ta ishe Ni".
Dariya yayi yana faɗin "ke dai wlh raguwa ce daga soma zuwa har kin fara ƙorafi, amma idan yawo ne babu inda ƙafanki be takawa".
"To ya son ranka? Wancan fa neman kuɗi nake yi ka ga kuwa bazan gaji ba, Ni dai muje da Allah na ƙosa in jini a kan gado na".
Hannu yasaka yatallabe mata ƙeya
"Mayya kawai, to zo ki hau bayana mana".
Rash da har ta saka ƙafa a waje tajuyo tana buga masa harara tace "wlh Sweety na fi ka iskanci kasan halina yanzu zan ɗare ka, kuma wlh bazan sauka ba duk uban da zai gan mu sai dai yagan mu".
Taɓe baki kawai yayi yabangaje ta yay gaba
Tabi bayan sa kuwa dasauri tana ɗurma masa duka a baya, ahaka har suka kai wajen Motan Maan ɗin suka shige, lokacin sun sauya hiran su har da tafa wa cike da nishaɗi.
[12/26/2020, 3:48 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON EIGHTEEN*
_______📖 lokacin da RAUDHA ta isa gida Packing tayi tafito rataye da jakar ta a kafaɗa sannan tarufe motan tay cikin gidan
Tana shiga cikin parlour'n Farida na fito wa daga kichen riƙe da Plate a hannun ta shaƙare da kayan marmari
"A'ahh ƴan makaranta har an dawo?". Farida tafaɗa fuskarta yalwace da fara'a
RAUDHA murmushi tayi tana kallon ta sannan tagyaɗa mata kai, sai tace
"Ina Yayana be dawo ba?"
"Eh Yayan ki be dawo ba sai zuwa anjima".
Bata sake magana ba tayi hanyar upstairs
Ita kuma Farida sai tanufi saman kujera tazauna tana ɗaukan Apple ɗaya tana kai wa baki.
Koda tashiga ɗaki jakan tayar saman gado sannan tazauna gefen gadon tana saka hannu tazare combat ɗin ƙafafun ta, sai tacire agogon hannun ta ta'ajiye sannan tamiƙe tasoma cire kayan jikin ta, anan tazubar tatsallake su nan ƙasa tanufi Toilet bayan ta ɗaura towel a jikin ta, wanka tayi tafito tasanya farar shimi iya cinyan ta, sannan tabarbaza gashin kanta yasauka zuwa kafaɗa kafin taɗau wayan ta tafito Parlour
Har a lokacin Farida na zaune tana shan Fruits ɗin ta tana kallo
Kai tsaye dainning tanufa taja kujera tazauna, sai da tazuba farar shinkafa a cikin Plate sannan takalli Farida taɗauke kai tace
"Aunty Wai baki da masu aiki ne anan?"
Da fara'a Farida tace "eyya ina dasu mana, wani abun zasu yi miki?"
Yamutsa fuska tayi kafin tace "naga yanda nafita nabar ɗakina haka nazo na tarar, na kula ma gaba ɗaya ba'a gyara min ɗaki".
Farida tace "Ni nace mata kar tashiga ɗakin ki wataƙil baki son me aiki tayi miki gyara idan bakya nan, but zuwa anjima zata shigo sai ta gyara miki, ina sallaman ta ne idan ta gama aikin nata".
Abinci tazuba cikin bakin ta tana tauna wa idanun ta akan Faridan kasancewar Facing ɗin ta takey, sai da tacinye na bakin ta kafin tace
"Ya za'a yi ki riƙa barin ta tana tafiya ba aiki take yi bane? Idan kuma ana buƙatar ta fa?"
"Eh ai nan kusa take bata da nisa duk da tayi tafiya ne but jiya ta dawo, tana zuwa sau biyu ne a rana, idan tazo da safe tagama aikin ta sai tatafi sai yamma, tunda dama Kuku ne me mana abinci, shine kaɗai yake zama a gidan nan idan yagama abincin sa sai yakoma BQ yazauna sai an buƙace shi, kuma Yayan ki ne ma be son zirga-zirgan ƴan aiki sannan nima ina yin abinda yasauwaƙa da kaina don nima bana so komi ai min". Farida tayi maganar idanun ta duk akan RAUDHA dake ta zuba abinci a cikin ta
Kaɗa kanta RAUDHA tayi sannan ta'ajiye spoon ɗin hannun ta tana tsiyaya Lemu cikin glass Cup tace "to Ni dai ina buƙatar ƴar aiki kusa dani sabida bana yin abu da kaina, ban saba ba kuma bazan yi ba, and yanzu da kike barin ta tana tafiya gida gashi na cire kayana babu wanda zai matsar min dasu sai Ni kenan?"
Murmushi Farida tayi tace "kai ƙanwata yanzu har kayan naki baza ki iya kai su inda yadace ba dole me aiki zata kawar miki? Ke fa macece yakamata kisan abinda yakamace ki tunda yanzu kin girma a koda yaushe za'a iya kai ki gidan miji, to wa zai miki acan ɗin?"
Waro manyan idanuwan ta da suke farare fat tayi kafin talumshe su tasake buɗe wa tana ci gaba da kora Juice ɗin ta
"Kina tunanin Ni ƴar gata har akwai auren da zan yi nan gaba in koma ina yin aiki da kaina? Ko kin manta wanene ubana?"
Sai kuma tayi murmushi tana ajiye cup ɗin hannun ta taɗau spoon tasoma tsakalan abincin kafin kuma taci gaba da faɗin
"Idan har ina da Daddy da Yayana a doron ƙasa to ba zan taɓa yin bauta ba, ki dena ma wannan shashancin".
Numfashi Farida taja tana jin babu daɗi ta yanda RAUDHA take gaya mata magana a haka tamkar bata san da wa take yi ba, sai dai tasan bata da ishashshen tarbiyya bare ta san ba dai-dai tayi ba, don haka tamatse ɓacin ranta tare da saka murmushi a face ɗin ta tace
"RAUDHA duk abinda ɗiya mace zata yi a gidan Mijinta to ba bauta bane kamar yanda kike tunani, Bauta ne a wajen Allah sannan neman lahiran ta ne, kuma ta wannan bautan zata samu lada har a gobe ƙiyama ta samu wuce wa ni'imar Allah, wato Aljanna kamar yanda Allah yayi mana bushara, RAUDHA babu yanda za'a yi ace kamar ki har yanzu baki san abinda yadace dake b.."
"Enough Aunty". RAUDHA tafaɗa da ɗan ƙarfin muryan ta
Miƙe wa tayi tana kallon ta tace "baki da hurumin da zaki shiga rayuwata da har zaki koya min dai-dai da wanda ba dai-dai ba, please and please bana son ganin ɗakina da datti, idan zaki nemo min me aiki tariƙa gyara min ɗaki a duk sanda nake buƙata ki kawo, idan kuma baza ki nemo ba.."
Sai tayi hanyar Steps batare da ta ƙarisa ba, tahaye da gudu ta wuce ɗakin ta
Ajiyan zuciya me ƙarfi Farida tasaki jikin ta duk a sanyaye, tabbas RAUDHA tana buƙatar sabuwar tarbiyya idan ba haka ba tana cikin halaka, tana son yarinyan har cikin ranta shiyasa take son taba da gudunmuwar ta wajen sauyawan ta, amma taya? Bata da ikon da zata iya sauya RAUDHA sabida bata kai matsayin ba, amma kuma idan har Daddy da Suhaib sun so ta sauya to tabbas zata sauya, gatan su a gare ta shine ya gurɓatar da ita sannan kuma su ne a yanzu zasu iya tanƙwara ta wajen sake bata tarbiyya tun kafin tafi ƙarfin su, duk da a yanzu ɗin tafi ƙarfin nasu amma su ne kaɗai zasu iya hukunta ta, idan har bada amincewar su ba to babu wanda ya'isa ya gaya ma RAUDHA gaskiya
Insha Allahu ta ɗau alƙawari daga yau zata soma nuna ma Suhaib kuskuren sa ko zai dawo hankalin sa yakula da ƙanwar sa ta hanyar da yadace, da sannu idan har suna zaune a gidan nan tabbas sai tayi nasaran sauyawan RAUDHA da iznin Allah kuma tare da yardan mahaifin ta da yayan ta, dole abu na farko ta fara nuna musu kuskuren su ta yanda zasu dawo hayyacin su akan wannan mummunan makauniyan soyayyan da suke mata
A karo na babu adadi tasake jan numfashi kafin tayunƙura daƙyar tatashi tanufi kichen ta ajiye Plate ɗin sannan kuma tafito tanufi ɗakin su.
🌐🌐🌐
Tunda RAUDHA tashiga ɗaki wayan ta taɗauka takira Ramcy suka sha hira kafin takira Daddy, but har a lokacin baya shiga, jefar da wayan tayi tana turo baki, ƙunƙunai tasoma yi ita kaɗai tana janyo HangBag ɗin ta taciro Tap ɗin ta tasoma revision ɗin karatun da suka yi yau
Bata sake fita ba sai da tasan cewa lokacin yayan ta ya dawo gida sannan tafita, Can tazauna sukai ta hira har dare kafin tadawo ɗaki
Alwala taɗauro tazo tazauna bakin gado tasoma ƙirgan sallan da ake bin ta na kusan kwana biyar, sai da tagama lissafi kafin tatashi tazurma Hijab tasoma gabatar da sallan
Wajen awa biyu tayi tana gabatar wa kafin tagama, duk da kuwa ƴar faki take yi but sai da yaɗauke ta tsawon wannan lokacin
Miƙe wa tayi tacire Hijab ɗin sannan tasaka kayan barci riga da wando farare masu taushi da zanen Flower kalan Coffee a jikin sa, gado tahaye taja pilow taɗaura kanta tana sakin hamma, dayike barcin ne a idanun ta babu jima wa yaɗauke ta.
Can cikin dare tasoma mutsu-mutsu duk ta haɗa zufa kashirɓan, duk da kuwa akwai a.c ga fan da yake aiki amma haka RAUDHA tajiƙe da zufa yana ta kwaranya daga fuskarta zuwa cikin rigan ta
Mummunan mafarki take yi na baƙaƙen halittu, gashi wani narkeken maciji da yaninka ta a tsawo da girma ya kanannaɗe mata jiki ya cure ta, wannan dalilin ne yasaka take fitar da huci tare da gumi tana son ƙwace wa amma ina ko motsi ta gaza, kuka sosai take yi tana neman taimako babu me jin ta, wani irin baƙin daji ne da babu komi sai ƙoramu da namun daji masu ban tsoro, kukan su kawai ya cika jejin yana wani amsa kuwa a kunnen ta
Macijin buɗe bakin sa yayi tare da saita kanta yanufo da bakin sa zai haɗiye mata kai
Wani irin ihu tasaki wanda lokaci ɗaya tafarka a matuƙar gigita tana ci gaba da ihun a gaske, jikin ta wani irin mazari yake yi gaba ɗaya idanuwan ta sun fito waje tamkar zasu faɗo, izuwa yanzu kamar an ɗibi bokitin ruwa ne an kwara mata sabida yanda tayi tsamo-tsamo cikin zufa
Zumbur tamiƙe saboda yanda idanun ta suka hango mata ƙaton macijin a jikin bango Ya biyo ta baki a buɗe yana wani irin fitar da sauti me ƙara wanda gaba ɗaya ɗakin sai da yagirgiza yasoma juyawa
Ƙofa tanufa a guje tana sakin wani ƙara me firgitar wa, tana riƙe handle ɗin ƙofan sai wani irin juwa yaɗibe ta tazame ƙasa tafaɗi a ƙasa sumammiya.
Kuma duk wannan halin da tashiga da kuma ƙaran da tasaki babu inda be amsa ba a gidan, amma kuma babu wanda yaji ta, har ta su Suhaib da suke cikin gidan basu san meke faruwa ba.
.
_plz ku riƙa yin comments da yawa wlh shi ke ƙara min ƙwarin gwiwa._
_yanzu wasan zai so ma, ku dai kuji gaba da bi na a sannu alƙalami na ✍️ zai warware muku duk abinda kuke son sani._
*Jikar Lawali ce* ❤️
[12/31/2020, 10:35 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
_wannan shafin naku ne masoyana na Wattapad, ina jindaɗin yanda kuke suburbuɗo min comments, ku ci gaba da gashi Ni kuma zan ci gaba da sambaɗo muku me daɗi, ku sha sha'anin ku da wannan ɗin👈_
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON NINETEEN*
_______📖 Bata farka ba sai da hasken rana yabugi fuskar ta sannan ne tafara buɗe idanuwan ta tana lumshe su, juya mata wajen yake yi duk da kuwa bata san takamaiman inda take kwance ba, ta ɗau tsawon mintuna goma kafin tatashi zaune tana riƙe kanta da yayi mata nauyi sosai yake mata ciwo
Mamaki sosai tayi ganin ta bakin ƙofa a kwance sabida ko kaɗan bata tuna abinda yafaru jiya ba, komi ya shafe mata kamar babu shi a ƙwaƙwalwan ta
Daƙyar taɗaga kanta tasauke a agogon dake manne a ƙusurwan bangon ɗakin, idanuwanta ta fid do waje ganin ƙarfe 11:10am. yanzu, Kuma ƙarfe goma yau take da lectures tunda kafin takwanta sai da taduba tantable
Tun sassafe da Suhaib zai fita yazo yabuga ƙofan nata don yatashe ta, har yagaji da bugawa yatafi sabida a tunanin sa bata da Lecture ɗin safe ne
Shiru-shiru Farida zata ji ta sauko amma kuma babu RAUDHA babu alamun ta, itama sai tahayo tay bugun duniya but RAUDHA ko kaɗan ba ta jin su, wani irin barci take yi wanda tayi nisa da duniyar mu, dole Farida tasauka tatafi tunda taƙi buɗe ƙofan.
Wani gauran numfashi RAUDHA tasaki kafin tajanye hannun ta a kanta tamiƙe a hankali jikin ta kamar anyi mata duka, ko kaɗan bata jin ƙarfi a jikin ta amma haka nan talallaɓa tashiga Toilet tayi wanka tafito, cikin sauri take yin komin ta duk da kasalan dake jikin ta
Shiryawa tayi cikin dogon wando fari ƙal me guntun skert a saman sa kalan orange, sai tasanya rigan shi me gajeren hannu da igiyoyi a gaban anyi ado dashi, itama rigan orange ne amma kuma akwai ɗige-ɗigen fari a ƙasan rigan da kuma saman rigan, me hula ne don haka ta ɗauka tasaka akanta yayinda ta cure gashin ta a ƙeya, wannan dalilin ne yasaka tuntun gashin be shiga cikin hulan ba yafito waje, Sandal shoes tasaka fari tare da Socks, haka ma Wrest watch ɗin ta da HangBag ɗin ta duk fari ne, sannan sai takanga faskeken eyeglasess na Robber a baby face ɗin ta fari tarr ana ganin idanun ta tamkar ba Glasses tasaka ba
Ƙofa tanufa tabuɗe tafice, ahankali take taka Steps ɗin tana riƙe da ƙarfen benen, tana sauka tayi hanyan ƙofa da ninyan fice wa
Farida dake zaune tana hangen ta takira ta
"RAUDHA ina zaki baki karya ba?"
Ɗan juyo wa tayi takalle ta, sai yanzu ita takula ma da ita tunda tana ɗaya side ɗin ne na cikin parlour'n, wanda babu yanda za'a yi tahangi me sauko wa daga sama sai idan mutum na cikin parlour'n
"Bana jin yunwa". Tafaɗa ahankali tana yin gaba batare da ta jira amsar ta ba
Kafaɗa Farida taɗage kafin tasoma kwaɗa ma House girl ɗin ta kira
Nan da nan tagurfana a gaban ta
"Yauwa Ester hau sama ki gyara ma RAUDHA ɗakin ta tunda ta fito".
"Ok Ma'am". Cewar Ester tare da rusunar da kanta alamun girmamawa sannan tawuce saman.
🌐🌐🌐
A cikin mintuna ƙalilan RAUDHA ta'isa school ɗin sabida gudun da ta sharara, tana yin parcking tafito tarufe motan tanufi department ɗin su
Koda ta'isa ta tarar akwai Malam acikin class ɗin, shiga tayi ta ƙofan baya tazauna taciro Tap ɗin ta tasoma sauraron karatun nasa
12:00pm. Na cika yafice wani yashigo
Duk karatun yau RAUDHA bata wani fahimta sosai, sabida sosai take jin babu daɗi a jikin ta, ƙarfin jikin ta yaƙi dawowa Sai kuma tana jin kamar ana buga mata guduma akai lokaci-lokaci, sannan sai tariƙa jin kamar da mutum kusa da ita ana yawan motsi, idan ta juya sai taga babu kowa tunda dama acan bayan tazauna, that's why bata maida hankalin ta sosai kan karatun ba
Bayan malamin ya fita sai takifa kanta saman Deks tana fid da numfashi.
Rash ce taƙariso wajen tare da yin sallama tazauna
Hakan yasa RAUDHAN tatashi zaune tana kallon ta batare da ta amsa mata sallaman ba
Murmushi Rash tayi tace "yau kin yi late baki samu Lecture ɗaya ba".
Gyaɗa mata kai tayi sai dai bata yi magana ba
Izuwa yanzu Rash ta gane halin RAUDHAN ba wai ta cika son magana bane, don kafin tayi magana sau ɗaya ta baka amsa sau ba adadi da kanta
Jakan ta tabuɗe taciro mata wani leda me ruwan zuma babba, tamiƙa mata tana faɗin
"To ga saƙon ki an siyo".
Hannu RAUDHA tasaka ta'amsa tana jin farin ciki sosai aranta, ba ƙaramin wahaltuwa tayi ba a kwanakin nan da bata ji ta a sama ba, ta rigada ta saba shiyasa ko kaɗan bata jindaɗi in bata sha ba
"Thank you". Tafaɗa tana murmushin ta me kyau
Itama Rash murmushin tayi tace "to yanzu ki tashi mu je capteria mu ci abinci yunwa nake ji".
Bata ce mata komi ba tamiƙe suka fito, duk a cikin su babu wanda yay tunanin zuwa sallah tunda babu me damuwa dashi
Capterian suka wuce suka yi odaring abinci, bayan sun gama RAUDHA tabiya suka fito.
"Kai mutumina ga fa yarinyan can da nake baka labari ita da Rash". Maan yafaɗa yana kallon su Rash ɗin dake doso wajen su
Kyakykyawar saurayin dake zaune saman mota yakai duban sa inda Maan ke kallo, nan yazuba idanun sa kan RAUDHA ko ƙyafta wa baya yi
"Maan wannan yarinyan kuma fa?" Yatambayi Maan batare da ya ɗauke idanun sa kan ta ba
"Nima dai bansani ba yanda kaganta haka na ganta, ai na faɗa maka ƴar Class ɗin su Rash ne kasan ta da jaye-jaye, itace wacce kakawo mata kaya".
"Haba dai amma fa ta haɗu, kace irin mu ce?" Yayi maganar yana shafa gemun sa still idanun sa akan ta
Dariya Maan yayi yace "kai dai maye ne Zen.."
Shiru yayi be ƙarisa maganar ba ganin har sun kawo setting su, hakan yasa yasauya maganar da kiran Rash
Sai a lokacin Rash tahange su, don haka takalli RAUDHA tace "ƙawata muje wajen su mana, kinga wancan shine wanda yake kawo mana wannan kayan, muje mu gaisa sai mu wuce Class".
RAUDHA bata ce mata komi ba illa bin ta da tayi suka isa wajen su
Dasauri Zen yasauko daga kan motan yana faɗin "Rash wannan Babe ɗin fa?"
Kallon sa Rash tayi
Yakashe mata idanu
Sai tayi dariya tace "friend ɗina ce Her name is RAUDHA".
Sai takalli RAUDHAN kafin tace "Ƙawata wannan shine Zen Abokin Maan ne".
Idanu RAUDHA tasanya masa kamar yanda shima yazuba mata yana murmushi, ƙare masa kallo kawai take yi da shigan da yayi
Yana sanye da farar riga me yankakken hannu, sai wando jeans blue colour duk an yayyanka shi as kwalliya, yasha askin zamani me tugaggen gashi, wuyan sa kuma sarƙoƙi ne wajen biyar da me Cross a ciki, hakan yatabbatar mata shi ɗin Christian ne
Bata ce komi ba illa ɗauke kanta da tayi
"Hi". Yafaɗa yana miƙa mata hannu alamun su gaisa
Idanun ta tamaida kansa kafin tabi hannun da kallo, sai kuma tace "Hi". Batare da ta bashi hannun ba
Murmushi yayi yakalli Rash yace "ƙawar ki fa tayi min tana da kyau sosai, zan zo tazama friend ɗina".
Dariya Rash tayi tace "kaga ga ita nan sai kafaɗa mata".
Kallon ta yayi yace "ko zamu iya zama friend RAUDHA? I Like you".
Fuska ta yamutsa kafin takalli Rash sai kuma tajuya tawuce batare da tabashi amsa ba
Hakan yasa Rash tayi saurin ce musu "byee na tafi sai mun haɗu anjima". Tay gaba itama
Zen be ɗauke kai akanta ba har sanda suka ɓace ma ganin sa, sai yasauke ajiyan zuciya yana kallon Maan dake mishi magana amma be ji ba
"Guy wlh yarinyan tayi sai ta zama nawa, dole ne duk yanda za'a yi nahaɗa alaƙa da ita".
Maan yay dariya yace "cabb wlh kana da aiki Zen, Nima Tunda naganta taburge Ni but bana tunanin fa ƴar hannu ce that's why ban ƙwallafa raina ba".
Kallon sa Zen yayi yace "kai kasan halina duk yarinyan da tayi min dole ne sai ta shiga hannu na, bare kuma wannan Babe ɗin da tahaɗu sosai, wlh dole ne sai ta shiga cikin mu, kai dai kabari zamu san abun yi".
"Allah ko mutumina?"
Jinjina masa kai Zen yayi alamun tabbaci kafin yace "kazuba idanu kagani".
Ihu Maan yasaki yana bashi hannu suka kashe
"Yanzu mu je gida, anjima idan mun haɗu da Rash sai mu tattauna". Zen yay maganan yana nufan ƙofan me zaman banza yabuɗe yashige
Shima Maan motan yashiga yaja suka bar wajen.
Kasancewar Lecture ɗaya yarage musu biyu zuwa uku, suna gama wa RAUDHA tayi gida.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐
Rash asalin sunan ta Rashida ne, a Kano suke ita da Mahaifiyar ta da ƙannin ta biyu, kasancewar mahaifin su ya daɗe da rasuwa sai yazamana Maman su ke ci dasu tunda basu da me taimaka musu ƴan uwa duk sun guje su
Tun tasowar Rash idanuwan ta suka buɗe da son kuɗi, kasancewar ta yarinya me son ƙarya shiyasa take bin gidajen yaran masu kuɗi tana ƙulla alaƙa dasu, a haka har tasoma haɗuwa da maza ɓata gari tana ba da kanta gare su suna biyan ta
Wannan abun duk da take yi Maman ta bata taɓa hana ta ba, a ganin ta yarinyan ta tayi farin jinin da tun kafin tagama girma samari na mata rubibi, hakan baya damun ta tunda tana kawo mata kuɗi duk abinda tasamu tare suke ci
Abu yayi gaba har takai ta kawo ma Rash ita ke ci da ƴan gidan su, ta zama tantiriyar karuwa wanda duk wani namiji me ji da kansa ya san Rash saboda shaharan ta
Maman ta da tagano ainihin abinda take yi take samun kuɗi hakan be wani ɗaga mata hankali ba, tunda dai tasan wannan shine zamanin, babu me baka sai idan ka ba shi wani abun da zai ƙaru da kai, sai dai ko kaɗan bata yarda ƙannin Rash sun faɗa wannan mummunan rayuwan ba, a ganin ta Rash ita kaɗai ta isa tawanke musu matsalan rayuwan su, ta yarda ta sadaukar da rayuwan Rash don su samu kuɗin da zasu ci gaba da rayuwa gaba ɗayan su, a cewar ta idan sun gama samun abinda suke so sai taja ƴar ta ajiki ta tuba takoma ga Allah sannan tayi mata aure shikenan komi ya wuce hmmm.
Rash babu inda bata bin namiji in dai zai biya ta kuɗi, ana haka suka haɗu da Sulaiman wanda a yanzu suke kiran sa da Maan, a salin haɗuwar su a social media suka haɗu wanda har yakai ga sun haɗu a fili
Maan ɗan Jigawa ne, babu laifi iyayen sa suna da kuɗi sosai, duk abinda yake so suna masa sabida shi kaɗai ne suka haifa
Tun fara abotan su soyayya tashiga tsakanin su, Rash tunda taga hoton Maan takamu da tsananin ƙaunar sa sabida babu ƙarya Maan yana da matuƙar kyau, irin kyakykyawar bafulatanin nan ne tamkar su sukai kansu
Dayake shima ɗan hannu ne shiyasa tunda suka haɗu Rash take bashi kanta suke rayuwan ƙasƙanci, shaƙuwar da suka yi da soyayyan da suke ma juna ko yaushe suna tare tamkar Chwingum
A lokacin da Maan zai tafi karatun sa a Abuja inda anan ne yazaɓan ma kansa don ci gaba da karatun sa, sai Rash itama tace zata bi sa, hakan ya saka sa farin ciki sosai don haka yace tahaɗo kayan ta su tafi
Batare da sanin Mahaifiyar ta ba Rash tahaɗa kayan ta tabi Maan Abuja, ya kama musu hayan gida Plet anan suke zaune, sun ci gaba da zama tamkar mata da miji
Kasancewar Rash tayi karatun ta zuwa matakin primary sai Maan yanema mata school taci gaba, sai dai tana yi tana tsallake sabida tafi son rayuwan jami'a ne, ita babu abinda take ƙauna in banda taganta cikin jami'a tana rayuwan wayewa irin ta ƴan mata masu ji da kansu
Wannan yasa koda tagama Scondary school sai tashiga school ɗin su Maan inda a lokacin yana Degree ɗin sa ne
A yanzu ita take biyan ma kanta kuɗin makaranta sabida Maan be hana ta bin maza ba, shima kuma duk yarinyar da yagani zai bi batare da ta damu ba duk da kuwa cewa har yanzu soyyayyar su tana nan
Zen Abokin Maan ne tun zuwan sa school ɗin, shima Baban sa me kuɗi ne sosai kuma fasto a babban Church ɗin dake garin Abuja
Har shi Zen ɗin yana tarayya da Rash babu ruwan su, iyakan dai yaba ta kuɗi takashe matsalan gaban ta tunda ta ɗau abun yanzu tamkar sana'a ne
A kayan maye babu abinda basu sha gaba ɗayan su, babu Club ɗin da ba sa zuwa duk inda akwai sheɗanan ta to suna nan wajen
Haɗuwar su da Zen shi yaƙara dulmiyar dasu sabida shi yafi su sanin kan duniya, yana da abokai tantirai sosai wanda suke cin karan su babu babbaka tare.
0 comments:
Post a Comment