Hankalin Suhaib ya tashi musamman yanda yaga RAUDHA tana fitan dare, bata tashi dawowa Sai idan dare ya tsala ko kuma asuba tayi, a wannan lokacin zata dawo musu abuge, ya rasa ya zai yi ya shiga tashin hankali matuƙa
Farida ita ke tausar sa akan yaci gaba da hakuri sannan yakula da ƙanwar sa wajen ceto rayuwan ta, tana nuna masa hanyan da zai bi don nuna ma RAUDHA kuskuren ta, amma duk hanyar da tanuna masa baya jin zai iya bi, abu ɗaya yaɗauka shine yin mata nasiha, yakan zaunar da ita yay ta mata nasiha wani lokacin har da hawayen sa, amma RAUDHA ko kaɗan bata taɓa jin sa ba, a ganin ta rayuwan ta ne kuma hakan tazaɓar ma kanta, babu wanda ya'isa yahana ta yanda take so tatafiyar da rayuwan ta, wani lokacin ma idan yamatsa mata wani irin fushi take yi dashi wanda ada ko kaɗan idan zata yi fushi dashi bata yin hakan, kamar wata mara hankali haka take koma wa, idan tasoma musu hauka sai abun yabasu mamaki matuƙa, har zagin Suhaib ɗin take yi idan fushin ta yayi ƙololuwar tashi, sai takoma tamkar ba ita ba, abun fa yay mugun ɗaga musu hankali ganin yanda RAUDHA tasauya lokaci ɗaya, baza ka taɓa gane bata da hankali ba sai idan ka shiga rayuwan ta, wannan dalilin ne yasaka daga shi har Farida suka shafa ma kansu lafiya tunda RAUDHA bata sauraron su.
Yanzu RAUDHA da Rash tare dasu Zen sun jone matuƙa, duk inda zaka gansu tare suke, RAUDHA ta saki jikin ta sosai dasu, yawon su da ko ina ma tare suke zuwa
Karatun ta yanzu bata cika maida hankali ba tunda bata da lokacin yi, sai dai abu ɗaya tamaida hankali yanzu idan har suna da Lecture bata zuwa ko ina sai ta gama, duk nacin da zasu yi tazo su tafi bata bin su sai ta saurari Lecture ɗin ta, idan kuma suka tafi yawon su time ɗin Lecture na cika duk inda suke sai ta matsa musu sun dawo
Wani lokacin Rash tana biye mata su shiga Lectures tare, wani lokacin kuma taƙi bin ta tazauna wajen su Maan har sai idan ta fito sannan su shiga motan Zen subar makarantar, basa kuma dawowa sai idan time ɗin Lecture yayi, idan kuma aka tashi RAUDHA bin su take yi wani lokacin su tafi gantali
A zaman da tayi dasu RAUDHA ta fahimci halin su gaba ɗaya, yanda Rash take bin mazaje da yanda su Zen suke bin mata hakan baya mata daɗi sosai, tunda suka nuna mata rayuwan tanuna musu ita kuma sam bata so ko kaɗan, ko idan Zen yana riƙe ta tare da rungume ta ta rinƙa faɗa kenan har fushi take yi dasu, sai idan sun lallaɓa ta gaba ɗayan su sannan take dawowa su haɗe tare.
Sai dai abinda bata sani na su Zen ba sun bata lokaci ne yanda zata ƙara sakin jiki dasu ta yanda zasu ƙara nuna mata abunda suke so a wajen ta, idan kuma taƙi suna da hanyoyin da zasu bi don cin ma burin su akan ta, ahankali-ahankali zasu ci gaba da jan ta, musamman ma Zen shine yake shige mata kuma sosai tasaki jiki dashi, shi kaɗai ne take iya bari yana riƙe ta, shima ɗin don taga ba addinin su ɗaya bane, sannan ma ita ko kaɗan hakan ba wai burge ta yake yi ba shiyasa tun farko bata yi kuma bata soyayya tunda ba wai tasan addini bane bare tasan an hana, sha'awar hakan ne bata dashi ko kaɗan, duk idan namiji yaraɓe ta tana jin tamkar zata haukace ne sabida tsananin baƙin ciki da ƙuncin dake ziyartan ta.
🌐🌐🌐
Yau ma kamar ko yaushe daga school suka fito yawon shaƙatawa, suna zaune a haɗaɗɗen wajen huta wa inda akwai ƙoramu a wajen wanda aka ƙawata su sosai, da irin su soomun pool da abubuwan more rayuwa
Daga can gefe Rash ne da Maan zaune akan fararen kujeru tsakiyan an saka musu glassess table, sai abubuwan sha da aka ajiye musu, hira suke yi suna dariya cike da nishaɗi
RAUDHA da Zen kuma suna zaune bakin ruwa, ita RAUDHA ta saka ƙafafun ta ciki tana wasa da ruwan sai jan wandon ta take yi don kar yajiƙe tana murmusawa cike da nishaɗi, sosai irin wajen nan yake mata daɗi tare da faran ta ranta
Ɗago hannun ta tayi takalli agogo kafin tajuya tana kallon Zen dake zaune kusa da ita yana latsa waya tace
"Zen I want to go time ɗin Lectures yayi".
Ɗago kai yayi yatsira mata idanu, ji yake yi tamkar yarungume ta yay ta tsotson bakin nan nata da yafi komi burge sa a jikin ta, shi dai yarinyan tayi masa ya gaji da jiran ranan da zai mallake ta akan gadon shi
Ganin kallon da yake mata ko ƙyafta idanu baya yi duk da kuwa ba yau yasa ba yin mata irin kallon ƙurilla ba, ita har mamakin sa take yi ko me yake kallo? Murmushi tayi tasaka hannu taɗana masa yatsan ta a saman fuska
Dasauri yayi firgigit yana sosa wajen
Hakan yasaka RAUDHA tasaki dariya tana kallon sa
Tunda yake be taɓa ganin dariyan RAUDHA ba, komin abu bata iya dariya sai murmushi, shiyasa sai yaga ta ƙara masa mugun kyawu musamman da yaga fararen haƙoran ta jere a waje
Sai da tayi dariyan ta son ranta kafin taturɓune fuska ganin dai kallon nasa yaƙi ƙare wa, miƙe wa tayi tana yamutsa fuska
Hakan yasa hankalin Zen yadawo jikin sa shima yamiƙe yana cewa "haba Babe muna tsaka da jindaɗin mu kike son tafiya? Please ki bar Lecture ɗin nan na yau ki zauna mu huta sosai".
Kallon sa tayi sai tataɓe baki tana yin gaba batare da tayi masa magana ba, mota tashige wajen me zaman banza
Tunda tatashi su ma su Rash suka tashi suka nofo wajen Zen
Maan yace "har time yayi ne?"
Ɗage kafaɗa yayi batare da yayi magana ba
Maan hannu yaɗaura saman kafaɗan sa yace "ka dena damuwa yau komi zai wuce, mu je dai mu mayar da ita school ɗin".
Dariya Rash tayi tace "babu ruwana Ni dai duk abinda yabiyo baya".
"Dama wa yace da ruwan ki?". Zen yafaɗa yana hararan ta kafin yayi gaba yanufi wajen motan
Taɓe baki tayi alamun ko ajikin ta, tashige jikin Maan tana faɗin "mu bar su don Allah su tafi Ni bana son mu bar nan".
"Ko Babyna?" Maan yayi maganar yana shafa fuskar ta bayan ya ƙara matse ta a jikin sa
Zata yi magana suka ji ƙaran horn
"Mu je Babe kinsan halin Zen, kuma kinsan yau muna da shiri akan RAUDHA so dole mu zauna musan abun yi".
Gyaɗa kanta tayi batare da tayi magana ba suka nufi wajen motan, baya suka shiga Zen yaja motan suka bar wajen
A cikin motan Rash da Maan suna manne da juna abun su yayinda suke ta romancing junan su ko gajiya basa yi
RAUDHA kuwa titi ta kafa ma idanu tana ta kallon gari
Kallon ta Zen yayi cikin ƙasa da murya yace "My dear Ina alƙawarin da kikai min?"
Kallon sa tayi tana waro manyan idanuwan ta akan sa batare da tace uffan ba
Murmusawa yayi yace "ko kin manta jiya kin ce min yau a gidana zaki kwana?".
Sai kawai RAUDHA tasaki dariya tana kwantar da kanta jikin kujeran, cikin dishewar muryan ta me sanyi tace "uhmm bazan iya zuwa gidan ka in kwana ba, dama wasa nake maka don ka matsa min nafaɗa haka".
Marairaice murya yayi yace "haba Babe meyasa Zaki yi min haka bayan kinsan Ni dagaske nake yi?"
Shiru ne yabiyo bayan maganar sa, don haka yasake cewa "shikenan to i know har yanzu baki yarda dani bane, kina ganin kamar zamu cuce ki tunda kinsan halin mu, but kinsan mu friend ne babu abinda zamu iya miki tunda yanzu mun zama ɗaya".
Sai yayi shiru idanun sa kan titi yana ci gaba da tuƙin sa, kafin kuma yaci gaba da faɗin "any way yau zamu je birthday ɗin Abokina ina gayyatar ki".
Ɗan kallon sa tayi taɗauke kai tana sake lafe wa akan kujeran tace "bana jin zan je yau bana jindaɗin jikina".
"No Babe yakamata ki je, nasan ke mayyan rawa ne I have surprise for you".
Murmushi tayi tana kallon sa kafin kuma tagyaɗa kanta tace "ok zan zo".
"Yeees ko ke fa Babe". Yafaɗa cike da murna
Daga nan hira suka ci gaba dayi, inda Zen ɗin ne ke bata labarin birthday ɗin yana ƙara ƙawata mata abun don yashiga ranta sosai.
Suna shiga school ɗin RAUDHA tafito daga motan tawuce class, yayinda su kuma suka fice a school ɗin har da Rash da tace baza ta shiga Lecture ɗin ba.
🌐🌐🌐🌐🌐
Direct gida RAUDHA ta wuce da suka gama Lecture, babu kowa a Parlour lokacin da tashiga sai tawuce ɗakin ta, tana shiga tafaɗa kan gado sai barci don shine a idanun ta ga kuma gajiya da take ji sosai a jikin ta
Sai 06:30pm. Tatashi daga barcin, wanka tayi tasaka ƙaramar riga shimi kalan sararin samaniya sannan tafito Parlour
Suhaib na zaune yana aiki da computer'n sa taƙariso wajen sa tazauna tana ɗaura kanta saman kafaɗan sa
Kallon ta yayi yana shafa fuskar ta da hannu ɗaya yace "Baby kin tashi? Na shigo naga kina barci".
Gyaɗa masa kai tayi tana lumshe idanun ta
Shima be sake cewa komi ba sai yamaida hankalin sa kan aikin sa yaci gaba dayi
Can kamar shuɗewar mintuna biyar tace "Yaya har yanzu Daddy shiru yaƙi kiran mu".
"Ki kwantar da hankalin ki insha Allahu nasan babu wata matsala sai kira mu da yardan Allah, idan kuma hakan be faru ba zan je har can ɗin in dubo sa".
Kallon sa tayi tana riƙo damtsen hannun sa da duk ka hannayen ta, cikin marairaice fuska tace "yaya nima kaje dani?"
"Baby school ɗin ki fa?"
Turo baki gaba tayi tace "a'a Ni dai kaje dani".
Shafa kanta yayi alamun rarrashi yace "to shikenan zamu tafi tare duk sanda na tashi tafiya, akwai aiki a Office sosai ga kuma Wifey bata jin daɗin jikin ta that's why bazan je yanzu ba".
Lumshe idanuwan ta kawai tayi tana jin kewar Daddyn nata na ƙara shiga zuciyarta, sosai take buƙatan sa a kusa da ita but yayi mata nisa, tana ji a ranta tamkar wani abun ne yasame sa tunda gashi an shafe tsawon lokaci babu labarin sa bare wayan sa tashiga
Maganar Suhaib ɗin ne yadawo da ita hayyacin ta
"Baby ɗaga Ni zan je sallah gashi can an soma kira, kema kije kiyi kinji?"
Bata ce masa komi ba illa miƙewa da tayi tanufi sama, tana shiga takwanta abunta bata ƙara motsi ba, sai da wayan ta tasoma ringing kafin tatashi ta ɗauka tayi peacking, lumshe idanun ta tayi tana saka hannu saman goshin ta tare da matse gashin kanta ta tattare shi zuwa baya, da alamun dai tana sauraron me maganar ne ta cikin wayan, sai kuma ta yamutsa fuska cike da sanyin murya sosai tace
"Ok I will".
Daga haka bata sake magana ba har sanda tagama wayan tacire a kunne tana ajiye wa, miƙe wa tayi tashige Toilet tasillo wanka tafito sanye da towel iya cinyan ta, kan stool tazauna tasoma shafe-shafen ta, duk abinda take yi a hankali take yin sa kamar baza ta yi ba, sosai idan kakalle ta zaka ga damuwa aranta, ko kaɗan bata jindaɗin jikin ta, ta rasa kuma meke mata daɗi ga dai tanan ne
Bayan ta gama tashirya cikin guntun wando Light blue, sai tasaka riga da yatsaya mata iya setting wandon me dogon hannu tamkar na sanyi sai dai be da wani nauyi sosai, kalan ruwan ƙasa ne sai siraran zane da aka zana guda uku daga ƙirjinta da Red colour, hill shoes tasaka red sannan ta tufke gashin ta a ƙasan ƙeyan ta da jelan gashin, turare tafesa taɗau HangBag ɗin ta tafito Parlour
Yanzun ma Suhaib ne zaune shi kaɗai saman dainning yana cin abinci
"Baby Ina zaki je kuma baki yi dinner ba?"
Wajen sa taƙarisa takwanto da jikin ta saman bayan sa tare da zagayo da hannayen ta a wuyan sa, batace komi ba illa tusa kanta da tayi a wuyan sa tana shaƙar ƙamshin jikin sa idanunta a rufe
Hannu yasaka Suhaib ɗin yazagayo da ita ta gaban sa yaɗaura ta saman cinyan sa, sai tasake shigewa jikin nasa still idanun ta a rufe
Numfashi ya ɗan ja yana shafa tattausan gashin kanta, sosai yake tausayin ƙanwar tasa tare da wani irin mahaukacin ƙaunar ta a ransa
Tsawon lokaci suna a haka, sai da wayan ta yayi ƙara sannan Suhaib ɗin yaɗago ta don ita taƙi motsawa ko kaɗan
"Sweetheart ana kiran wayan ki".
Bakin ta takai kan nashi tasakar masa kiss 😘 kafin tamiƙe tana kallon sa da shanyayyun idanuwan ta tace "Yaya sai na dawo".
Be iya ce mata komi ba illa bin ta da kallo da yake yi har takai bakin ƙofa tafice
Numfashi yasauke cike da tausayin ta, sosai yaga damuwa a fuskarta kuma yasan RAUDHA ko kaɗan ba ta faɗa ma kowa damuwar ta, koda kuwa ya tambaye ta ne kafin tafaɗa masa aiki ne, tana da zurfin ciki ga duk abinda ke damunta, ko kaɗan baya jindaɗin fitan daren nan da take yi duk da kuwa yasan inda take zuwa, sai dai babu yanda zai yi sabida idan yace zai hana ta ba sauraron sa take yi ba, yanzu sai abun ma yajuye yakasa gane mata, tabbas yasan ƙanwar tasa tayi mugun sauya wa fiye da tunanin mutum
"Amma meke damun ta me yasauya ta?" Shine amsar da yakasa samowa har yanzu.
🌐🌐🌐🌐
RAUDHA na fita kanta tsaye tayi bakin Gate
Me gadi na hango ta yatashi yabuɗe mata small Door tafice
Motan Zen na waje suna jiran fitowar ta, shi yafito yabuɗe mata murfin motan tashiga
Tunda suka kama hanya ko magana ta kasa musu har suka dan gana ga kyakykyawar club ɗin, tunda tashiga tasamu wuri tazauna bata sake motsa wa ba, tambayan duniya sun yi mata ko akwai abinda ke damun ta amma taƙi yin musu magana illa idanu kawai da tazuba musu
Lokacin da aka sake cika maƙil a wajen sai tamiƙe tafito waje sabida hayaniyan mutanen sosai yake damun ta, hakan har ya soma haddasa mata ciwon kai me tsanani
Haraban wajen haske ne tamkar rana, ba ka sanin ma dare ne sai idan kayi nesa da wajen
Tunda tafito tajingina da wani ƙarfe taharɗe hannayen ta a ƙirji tare da kwantar da kanta jikin ƙarfen tana lumshe idanuwan ta, shiru tayi tana sauraron sarawan da kanta ke mata, gaba ɗaya jikin ta kamar ana ƙara zare mata kuzari ne a duk sokonni, izuwa yanzu har rawa jikin nata yake yi, leɓen bakin ta kawai take cije wa sabida yanayin dake baƙuntan ta, har ga Allah baza ta iya fahimtar halin da take ciki ba izuwa yanzu, kawai tasan zuciyarta ta bata umarni kuma tabi
Buɗe idanuwan ta tayi tasoma takawa a hankali zuwa waje, ahaka har tafice Gate ɗin, tafiya take yi batare da tasan inda tanufa ba, a lokacin wajen ƙarfe 10:00pm. Hasken motoci ne kawai ke gilma wa da fitilu
Bata yi nisa sosai ba tasami wasu motoci guda biyu an faka su, jingina tayi ajikin ɗaya tare da zame wa ƙasa tana riƙe kanta sosai, izuwa yanzu duniyar ce take juya mata hakan yasa takasa tafiya tazauna nan, tana nan zaune tajiyo motsi sai dai ta kasa motsawa bare ta ɗago kanta da ta ɗaura saman gwiwar ta, bata san meke faruwa ba amma taji an haske ta da fitila me tsananin haske sai kuma tajiyo surutun mutane inda ɗaya ke cewa
"Baaba mun yi kamu fa, ka ga wata cikas anan kuwa..."
Daga nan bata sake fahimtar maganar da suke yi ba illa ji da tayi an ɗago ta an sanya mata wani ƙyalle an rufe mata hanci da baki, daga nan ne talumshe idanuwan ta numfashin ta yaɗauke gaba ɗaya.
Saka ta suka yi a cikin mota suka ja da gudu suka bar wajen.
[2/22, 3:35 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON TWENTY ONE*
_______📖 Direct wani gida suka nufa me kamar kango amma da akwai Gate a gidan, suna shigar da motan suka fito da ita, su uku ne mazan yayinda ɗaya ne yaɗauke ta yasaɓa ta a kafaɗa suka nufi cikin gidan da ko ƙofofi babu sai window
Kamar mintuna biyar da shigan su sai gidan yasoma amsawa da wani irin kuka me ban tsoro haɗe da wani irin gurnani tamkar za'a fasa gidan, kukan sosai yake ƙaruwa sai kuma yahaɗe na mutane da yawa wanda baza ka iya gane na aljanu bane ko na mutane, zuwa can kuma sai kukan yalafa sai ga RAUDHA ta fito tana layi gashin kanta duk ya barbaje ya rufe mata fuska, duk da dare ne but bazai hana ka hango yanda idanuwan ta ke wani irin walƙiya ba tamkar yanda na mage yake yi idan tafito da dare, tafiya kawai take yi har tafice cikin gidan tadoshi cikin daji, duk da dama gidan a wajen gari yake
Sai da tayi tafiya me nisa kafin tafaɗi ƙasa yashe babu alamun numfashi a tattare da ita.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
Washe gari har Suhaib yashirya zuwa Office yana jiran dawowar RAUDHA amma babu ita, duk da yasan bata kai wa har safiya idan tafita but yayi tunanin ko tana can ɗin ne inda tasaba zuwa, jin shiru bata dawo ba sai yatafi Office
Koda yadawo Farida ta tabbatar masa bata dawo gidan ba sai hankalin sa yayi mugun tashi, wayanta yasoma kira duk da kiran ya shiga but babu answer, sai da yayi Three missed calls kafin Rash taɗaga Kiran, tunda dama a motan Zen RAUDHA tabar jakan ta, su ma sun shiga tashin hankali musamman da suka neme ta suka rasa, daga baya kuma sai suka yi tunanin ta wuce gida ne duk da sun ji haushi sosai Zen da Maan tunda sun yi tanadin ranan sosai akanta, amma tatafi tabar su
Abinda yasoma fita a bakin Suhaib sanda Rash taɗau wayan shine "Baby Ina kika je har yanzu baki dawo gida ba kin ɗaga min hankali sosai?".
Jin hakan sai Rash ta tabbatar akwai matsala, itama cikin tashin hankali da yanuna a muryan ta tace, "Ba RAUDHA bace ƙawarta ce, ta bar jakarta ne a wajena kuma naga kana kira".
Suhaib dake zaune be san sanda yayi zumbur yamiƙe ba
"Whattt... Ki kace mene? Ita ina taje ne da tabar wayan a hannun ki?".
Cikin tsoro Rash tabashi amsa da yanda aka yi su ma suka neme ta suka rasa
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Abinda Suhaib yafaɗa kenan yana me sakin wayan a ƙasa
Lokaci ɗaya zufa ya tsatstsafo masa a saman goshi, ga wani irin jiri da yamamaye sa nan take sabida tsananin tashin hankalin da yaziyarce sa
Farida dake zaune da ciki a gaba tana tambayan sa "meke faruwa?" Be ma san tana yi ba
Sai da yayi good 5 minutes a gushewar tunani kafin yadawo dai-dai, lokacin kuwa tuni hawaye sun ciko masa idanu yakalli Farida da tamiƙe tsaye itama hankalin nata a tashe, cikin raunin murya yace
"RAUDHA .. RAUDHA.."
Abinda yake ta faɗi kenan ya kasa ma yin maganan, sai kuma kamar an tsikare sa yaɗau wayan nasa yasake kiran Numban RAUDHAN, wannan karon akashe wayan yake, ai be jira komi ba yayi waje asukwane yana sake neman layin duk da kuwa ance masa akashe ne
Farida biyo bayan sa tayi duk ta ruɗe yanda taganshi shima aruɗe, lokaci ɗaya ya fita hayyacin sa tamkar zararre, but kafin takai wajen ma tuni yaja motar sa yayi bakin Gate, dole takoma ciki tazauna jiran abinda zai biyo baya, duk da kuwa a matuƙar tashe hankalin ta yake abun ku da me ciki gashi ba lafiya tacika ba a kwanakin.
Babu inda yazarce sai police station, report yaba da akan ɓatan RAUDHA, abun ku da me shi suna ganin kuɗi nan da nan aka haɗa sa da Police zuwa school ɗin su RAUDHA, wasu kuma suka bazama neman ta
Duk wani bincike sai da aka yi but an tabbatar musu RAUDHA bata zo yau ba, daga ƙarshe aka sanƙamo su Rash zuwa station don amsa tambayoyi, koda aka tambaye su abinda suka sani sun faɗi komi basu ɓoye ba, sai dai anƙi sakin su sabida su ake zargi kasancewar su ne mutanen da RAUDHA tayi rabuwar ƙarshe dasu
Haka ƴan sanda suka dage wajen bincike, har a talabijin an saka hotunan ta ko za'a dace amma babu labarin ta har zuwa dare
Zuwa lokacin Suhaib ya gama fita hayyacin sa, kuka sosai yake yi tamkar mace, ƙiri-ƙiri yaƙi tafiya gida babu inda be yawata ba don neman ta but Allah be sa ya dace ba, sai bayan isha'i sannan yakoma gida
A yanda yadawo ne hankalin Farida yasake tashi fiye da yanda take tun safe, musamman yanda yasaka ta gaba sai rizgan kuka yake yi yana sambatu
Be san ya zai yi da rayuwan sa ba idan ba'a ga RAUDHA ba domin bazai taɓa yafe wa kansa ba, kuma yana ji ajikin sa RAUDHA itace bugun numfashin sa idan babu ita to tabbas babu shine, soyayyar da yake mata ba zai iya juran rasa ta a irin wannan yanayin ba
Sai da Farida tayi dagasken gaske wajen rarrashin sa, nasiha tayi ta masa tana nuna masa girman ƙaddara da tawakkali dashi, tabbas ɓatan RAUDHA ƙaddaran sa ne, idan kuma yajure yamiƙa al'amuran sa zuwa ga Allah to Allah me rangwame ne zai sauƙaƙa masa duk kan lamuran sa
Wannan nasihan da tayi masa ne yasanya Suhaib ya raya daren da roƙon Allah wajen bayyana masa ƙanwar sa, yana yi yana kuka cikin ficewar hayyaci, gaba ɗaya aranan be ko runtsa ba saboda tashin hankalin da yariske sa
Sosai Farida ta tausaya wa mijin ta, tabbas tasan yana cikin wani mawuyacin hali wanda samun kansa sai idan RAUDHA ce tadawo.
Washe gari da mugun zazzaɓi Suhaib yatashi har baya iya tsayuwa sabida tsananin ciwo, gashi ƙiri-ƙiri yaƙi cin abinci in banda waya da yatasa agaba yana faman kira da kuma jirayen kiran babu abinda yake yi
Daga ƙarshe ma fita yaso yi but ya gaza sai kwasan sa akayi aƙasa domin tuni ya sume
Kuka sosai Farida take yi sabida tsananin tashin hankali, duk yanda take jin ciwon ta be kai yanda take jin tashin hankalin halin da mijin ta yake ciki ba
Waje tafita takira ma'aikatan gidan su biyu da me gadi suka haɗu suka ɗauke sa zuwa mota, drever yaja aka nufi asibiti dashi
Direct emargency aka nufa dashi
Kuka kawai Farida take yi ta kasa zaune ta kasa tsaye ko jin nauyin cikin nata bata yi, wayan Yayan ta takira tafaɗa masa halin da ake ciki, ai kuwa babu jimawa yazo, shine yayi duk wani abinda ake buƙata na jigilan asibitin, daga ƙarshe ma yasaka aduba Farida saboda yanda jikin nata yatashi sai numfarfashi take yi
An bata gado akayi mata alluran barci sabida tasamu hutu don shi take buƙata a halin yanzu.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
A can Station kuwa ba'a saki su Rash ba sai da mahaifin Zen yazo, shine yayi belin su duk da daƙyar aka bashi don shima sai da yasaki bakin aljihu.
Wajen awanni biyu kafin Farida tafarka, lokacin har mahaifiyar ta da ƙanwarta Maryam wacce akayi musu aure tare sun zo, ita Maryam ɗin ne tazo musu da abinci, don haka Mahaifiyar su wato Umma tace ma Maryam ɗin tazuba ma Farida abinci taci
Daƙyar taci sabida hankalin ta na ga Mijin ta, don Umman taƙi barin ta zuwa wajen sa ne saboda gargaɗin da Doctor yayi musu adena barin ta tana zirga-zirga da yawa Cuz tana buƙatar hutu sosai.
Sai yamma kafin Umma tasoma tafiya, daga baya itama Maryam tawuce da zummar idan ba'a sallame su ba zata aiko musu da abinci.
Lokacin da Suhaib ya farka Farida na wajen sa, tunda yatashi yagansa a asibiti yatashi hankalin sa akan sai an sallame sa, acewar sa bazai zauna anan ƙanwar sa kuma na can cikin wani hali ba be je ya neme ta ba
Daƙyar doctor yashawo kansa har ma yayarda yazauna zuwa safe, gashi dama ko kaɗan bashi da ƙwarin jiki don tun jiya rabon sa da abinci, yaƙi saka komi acikin sa sai ruwa
Yanzu ma daƙyar Farida tashawo kansa yaci abinci doctor yazo yaba sa drugs yasha, baya buƙatar raunin sa a yanzu yafi son kuzarin sa yadawo ta yanda zai fita neman Ƙanwar sa
Kwana yayi a ranan yana waya da Police don jin me ake ciki, har yanzu dai babu labarin ta.
.
_To sai muce Allah yabayyana maka ƙanwar ka Suhaib._
[2/22, 3:59 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON TWENTY TWO*
_______📖 RAUDHA bata farka ba har washe gari
Wajen ƙarfe 07:00am. Wani magidanci yazo wuce wa yahange ta, da farko ya ji tsoro sai dai kuma yayi shahada wajen ƙarisawa wajen ta, hannu yakai yana taɓa ta sai dai ko kaɗan babu alamun numfashi a tattare da ita, sai da yasake kai hannun sa setting hancin ta nan ma be ji komi ba, sai yariƙe tsintsiyan hannun ta anan ne yatabbatar tana da sauran rai, ajiye fatanyan sa yayi yaɗago ta yasaɓa a kafaɗa sannan yayi hanyan gida
Kasancewar safiya ne mutane duk suna gida basu kai ga fitowa ba, don haka har yakai gida be haɗu da kowa ba duk da babu nisa sosai da rugan da suke
Yana shiga yasoma ƙwala wa matar sa kira
Da gudu Lantana tafito tana aza ɗankwalin ta kanta at the same time tana amsa mishi da faɗin "Malam lafiya..?"
Sai dai bata iya ƙarisa maganar ba ganin sa saɓe da RAUDHA a kafaɗa
"Tukunna dai ɗauko min Tabarma sai in miki bayani ko?"
Lantana ta'amsa mishi dasauri tana shigewa ɗaki taɗauko tabarman kamar yanda ya umarce ta, shimfiɗa wa tayi sannan yasauke RAUDHAN akan tabarman
"Malam wannan yarinyan daga ina, aina kasamo ta?" Lantana tayi masa tambayan lokacin da tasami waje tazauna tana kallon sa
"To nima dai ga tanan tsintan ta nayi cikin jeji, ganin tana numfashi shine nataimaka nakawo ta nan".
"To Malam me zai saka kakawo mana ita nan bayan gidan me Gari zaka kai ta? Mu kuma me zamu yi mata?"
Ɗan sauke numfashi Malam Umaru yayi kafin yace, "to nayi tunanin hakan nima ai, sai kuma na tuna ɗazu da asuba da muka yi sallah me Gari ya sanar mana zai yi tafiya a lokacin, har yake neman addu'ar mu shiyasa nayi tunanin kawo ta nan ɗin tunda ko an kaita can babu me kula da ita".
Lantana da idanun ta suka ƙi ɗauke wa akan RAUDHA tasake cewa, "Malam nifa wlh ina jin tsoro, yarinyan fa ko motsi bata yi yanzu mu wani taimako zamu bata? Kai da ganin yarinyan nan kasan ƴar cikin birni ce, asibiti Ya kamata a kai ta, kar mu zo Garin taimako mu afka cikin matsala, idan ka kaita can sai kayi musu bayanin tsintan ta kayi kaga sai su nemi ƴan uwanta tunda su ƴan birnin sun san yanda zasu yi su same su".
Kallon Lantanan yayi yace, "ke kina ganin haka kawai zan kai ta asibiti baza su caje Ni kuɗi ba? Dole sai mun biya kuɗi kuma kinsan ban da komi a yanzu, sannan wannan yaron ban san ranan dawowar sa ba da sai yataimaka mana, amma Ni abinda naga ya dace ki je gidan Jummai me magani tazo taduba ta sai aga abunda hali zai yi, kinga idan muka samu tafarfaɗo sai tafaɗa mana inda take mu maida ita, kinsan be kamata mu bar ta bamu taimaka mata ba domin tana buƙatar taimakon, Allah yaga zuciyar mu zai bamu nasara, ko sada ta muka yi da ƴan uwan ta zamu samu lada".
Ajiyan zuciya Lantana taja cike da sanyin jiki tace, "to shikenan Malam Allah ya bamu ikon taimakon nata, bari inje sai mu taho da Jumman".
"Amin Amin". Malam Umaru ya'amsa mata
Sai da tashiga ɗaki tayafo mayafi kafin tafice zuwa gidan Jummai me maganin gargajiya
Har suka dawo ita da Jummai Malam Umaru yana nan zaune a wajen, nan dai yawuce gona yabar Jummai na duba RAUDHA akan bazai daɗe ba zai dawo, in yaso idan yadawo sai yaji meke faruwa.
Buga tagumi Lantana tayi tana kallon Jummai da tazuba kayan magungunan ta tana ta faman duba RAUDHA
Bayan wasu lokuta taɗago tana kallon Lantanan kafin tace, "Iy to matsalan yarinyan nan babba ne domin dai gaskiya yafi ƙarfi na, na kasa gano komi a tattare da ita, amma kuma albishir ɗin da zan iya muku shine zata farka a ɗan ƙanƙanin lokaci, wannan turaren kin ganshi ko?"
Jummai taƙare maganan da ɗago mata turare a ɗan kwalba, sannan ta haɗa mata da wasu saiwan icce taci gaba da faɗin
"Zaki samu garwashin wuta ki murmusa wannan iccen akai, sannan sai ki ɗiga turaren nan a wutan da zaran iccen ya gama ruruwa, zaki kawo garwashin kusa da kanta ki riƙa turare ta a ƙalla sau uku a rana, zata iya farkawa zuwa gobe ko kuma nan da kwana biyu, yanzu zaki fara daga yau ne, sau uku zaki yi mata a yau ɗin kina ji?".
Gyaɗa kanta Lantana tayi dasauri, sannan tamiƙa hannu ta'amsa tana faɗin, "to iya abinda za'a yi kenan?"
"Eh iya abinda za'a yi mata kenan, idan kuma kwana biyu ya shuɗe bata farka ba sai ki taso ki faɗa min Ni kuma Nasan me zan yi".
"To mun gode Allah yasaka da alheri, Allah dai yataimake mu ta tashi ɗin". Cewar Lantana cikin jimami
"Zan wuce idan Mijin naki ya dawo sai ki faɗa masa".
Lantana tace, "to shikenan Jummai idan yazo ɗin zan kawo miki kuɗin har gida".
Miƙewa Jummai tayi bayan ta harhaɗa kayan ta, suka sake yin sallama sannan tafice a gidan.
Kamar yanda Jummai ɗin tace mata tayi, hakan kuwa tayi wa RAUDHA
Babu jimawa Malam Umaru yadawo Lantana tafaɗa masa yanda suka yi, kuɗi ya ba ta sadaka kamar yanda ake bata idan har ba faɗan yawan kuɗin tayi ba, Lantana ta'amsa tanufi gidan Jummai me magani takai mata kuɗin ta dawo
Tana dawowa Malam Umaru yace, "Ya kamata ki gyara mata ɗakin Basiru amayar da ita can don be kamata abarta anan ba".
"To Malam bari inyi".
Ɗakin Basirun Lantana tashiga da tsintsiya a hannun ta, cikin ƙanƙanin lokaci tashare ta kakkaɓe katifar ɗakin tasauya da wani zanin gadon, sannan tafito ta sanar wa Malam ta gama
Shi ya ɗauki RAUDHA zuwa ɗakin yashigar da ita
Ita kuma Lantana sai tanufi ɗakin ta taɗauko Zani talulluɓe wa RAUDHA jikin ta kasancewar ba wani kayan kirki ne da ita ba, gaba ɗaya santala-santalan ƙafafuwan ta a waje suke, ga gashin kanta shima a buɗe ya wargaje, sai da takama mata gashin taƙulle mata ta yanda bazai dame ta ba sannan tafito daga ɗakin
Anan Malam Umaru yayi mata sallama cewar ya fita zuwa majalisa, tayi masa adawo lafiya sannan tanufi bakin murhu tasoma kaye-kayen ɗaura girkin dare.
Da dare suna zaune a tsakar gida suna cin abinci, Malam Umaru yakalle Lantana bayan ya kai loman tuwon bakin sa, sai da ya haɗiye sannan yace, "Kin kuwa yiwa yarinyan nan turaren?"
"Eh nayi mata Malam, saura ɗaya ne yanzu idan mun kammala sai inyi mata".
Gyaɗa kansa yayi be sake cewa komi ba, sai da yagama cin abincin yasha ruwa tare da sakin gyatsa yafurta "alhmadulillah Allah mun gode maka, Allah kakawo mana na kullum".
Lantana ta'amsa masa da "ameen Ameen Malam".
"Yanzu haka zamu zuba ido mu bar Basiru yana tafiya gantali sai yayi kwana da kwanaki kafin mu saka sa a idanun mu?"
Tsame hannun ta daga kwanon tuwon Lantana tayi, fuskarta akwai damuwa sosai izuwa yanzu, sai dai kuma ya zasu yi dole sai haƙuri, Kallon sa tayi cike da sanyin murya tace, "to ya zamuyi Malam? Abinda Basiru yazaɓar wa kansa kenan, sai mu bi sa da addu'a Allah shi zai shiryar mana dashi".
"Hakane to Allah yashirye sa, amma abun na matuƙar damu na, ace ɗa ɗaya ya gagare mu?".
"Amin, wata rana zai shiryu insha Allahu, rayuwan ne yanzu sai ahankali, domin ba kaɗan ba Abokan banza suna taka muhimmiyar rawa wajen gurɓacewar Yara, Allah yasa mu dace".
Malam Umaru ya'amsa da "Ameen". Sannan yaƙara da faɗin, "ya kamata kije kiyi mata siracen nan dare na yi".
"To Malam". Lantana tace hakan tana miƙewa bayan ta harhaɗa kwanonin tuwon da suka ci
Kichen takai sannan ta wanke hannun ta tanufi cikin ɗakin ta don ɗauko turaren
Shi kuwa Malam Umaru gyara zaman sa yayi bayan ya gama wanke hannun sa da baki da butan dake ajiye a gaban sa, rediyon sa yajawo yakunna yana karawa a kunne bayan ya jingina da bango ta yanda zai ji daɗi.
Sai da tagama yin mata siracen sannan tarufo ƙofan tadawo wajen Malam tazauna suna ɗan taɓa hira jefi-jefi yana kuma sauraron rediyon sa, ahaka har dare ya tsala kafin su je su kwanta.
Washe gari RAUDHA bata farka ba har dare, wuni Lantana take yi a ɗakin tazauna tasaka ta gaba tana ta kallo, ko kaɗan bata rabo da mamaki aranta, komi zuwan mata arai yake yi game da RAUDHAN, duk da kuwa ɗari bisa ɗari ta yarda da mutum ce ita, amma kuma wani lokacin sai tayi tunanin ko dai ba ƴar nan bace? to daga ina take me yakawo ta nan da har Mijin ta zai tsince ta? Abubuwa dai kala-kala.
The following day bayan Malam Umaru ya tafi aikin gonan shi itama Lantana tashirya don tafiya bikin ƴar ƙanwar baban ta da ake yi a cikin anguwan, rufe ɗakin da RAUDHA take kwance tayi tasaka igiya ta ɗaure sannan tafice agidan bayan ta jawo ƙyauren gidan
Babu me shigo musu gida don haka bata ji ɗar ɗin barin RAUDHA ɗin ita kaɗai ba, duk da bata da tabbacin zata iya farkawa ko kuwa baza ta farka ba.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
"Kai Baaba sanƙamo min wayar ka in saka layina ciki don nawan nan ba kanta ƙalau ba, kuma ina tunanin zuwa anjima Master zai kira ni".
Miƙo masa wayan yayi yana cewa, "to yanzu da ƙarfe nawa zan zo ɗaukar ka?"
Wulla idanun sa Basiru yayi cike da duniyan ci yace, "zuwa dare kazo ka sanƙame Ni sai mu fantsama".
"Ok ba damuwa".
Wayan yamiƙa masa yana buɗe motan yafito yana faman gyara wandon sa, sai da yayi dogon hamma yagama miƙar sa kafin yabugo ƙofan motan yarufe, sannan yasaƙalo da kansa cikin motan yana kallon Ƙwaro yace, "Kai Baaba ka biya ku taho tare da Garzali don yau akwai fa zaman meating, kar kace kuma ban faɗa maka ba".
"Baka da damuwa ai Oga, zan biya mu taho tare".
Janye kansa Basiru yayi kafin yajuya yanufi gidan su bayan ya ɗaga masa yatsu biyu yana masa umarnin tafiya.
Da fito yashiga gidan yana jan ƙafafu tamkar me koyan tafiya, nan kuwa duk cikin iskancin sa ne, wur-wurga idanu yasoma yi cikin gidan still yana ci gaba da fiton sa, shi dama ba wai damuwar sa bane da ganin iyayen nasa don haka ya hura hanci yanufi ɗakin sa, ganin an ɗaure ɗakin da igiya sai yaja tsaki yana faɗin, "kai wlh Lantana wata iriyan baƙauyiya ce, har yanzu taƙi tafaso gari ta waye, don wulaƙanci da igiya ne zata ɗaure min ɗaki duk da tasan akwai eya ne a ɗakin, wa billahil lazi nashiga naga anyi min wuff da kaya sai na nuna mata asalin kalo na agidan nan".
Da ƙarfi ya buga ƙofan ɗakin da ƙafan sa yaburma ciki
Ganin mutum kwance a akan katifar sa yayi saurin ja da baya yana ƙara ware idanun sa, sai yanzu ya tabbatar da eh mutum ce a kwance cikin ɗakin sa
"Kutt.. mar uba.." yafaɗa da ƙarfi idanun sa akan RAUDHA
Dasauri yamatsa jikin katifan don yasake tabbatar da zargin sa yasaka hannu ya yaye zanin da aka rufe mata jiki, nan santala-santalan fararen dogayen ƙafafun ta suka bayyana, baki sake yatsaya yana kallon ta batare da ya nuna tsorata ba da ganin ta ɗin, sai kuma yakece da dariya yana faɗin
"Wlh tsuntsu daga sama gashashshe kuttt.."
Yariƙe bakin sa dake buɗe still idanun sa na yawo jikin ta
"Kaii Old man ya iya zaɓi alƙur'an, hhhh wlh na yarda suna son in dawo gida in kintsu tunda suka ajiye min zuƙeƙiyar budurwa haka, yo to aina suka samo ta ne?" Yaƙariƙe maganar nasa yana ɗaga kai alamun tunani🤔
"Kai anya Old man baya satan yaran Mutane? Daga nace yayi min aure da ƴar birni sai yaje ya sanƙamo ma mutane ƴar su? Yasin wannan babu me yarda yabashi ita, wannan ai ko a yawon duniya na ban taɓa haɗuwa da kyakykyawar yarinya kamar ta ba, anya ma?.."
Sai kuma yayi shiru yana duƙawa gaban ta yasoma shafa ta, jin wani irin taushi da skin ɗin ta ke dashi ai tuni ya soma lanɗe baki
"Na rantse da Allah ko aljana ce yarinyan nan sai na kusance ta, wayyo daɗi".
Dasauri ya miƙe ya soma cire kayan sa cikin zumuɗi da tsananin sha'awan da yataso masa sakamakon taɓa ta da yayi, har wani rawa-rawa jikin sa ke yi.😅
🤦🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
[2/22, 4:14 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON TWENTY THREE*
_______📖 "Subhanallah.. me kake yi haka Basiru?" Cewar Lantana da tashigo cikin ɗakin tahangi Basiru na ƙoƙarin zuge zip ɗin wandon sa
Cak yatsaya yana juyowa yakalle ta a kaikaice, sai kuma yakwashe da dariya yana nuna ta da yatsa yace "Kinji ki Lantana da wani zance, yo me zan yi kuwa in ba eya ne ba kin gane ai?" Yaƙarike maganar yana ɗage mata gira
Lantana da tagane abinda yake nufi tace "shin Basiru kanka ɗaya kuwa? agidan iyayen ka ko kunyan mu baka ji shine kazo zaka hayayyaƙe wa yarinya haka kawai baka san komi akanta ba".
"To Lantana Ina ce matar da kuka yi min ne tunda nace muku kuyo min aure?"
Girgiza kanta tayi tace "A'a wannan yarinyan mahaifin ka yatsinto ta acikin jeji, ina mu ina aura maka wannan yarinyan?"
Tsaki yaja yace "to wlh ko ma ƴar uban wacece ta zama nawa, wlh ita zaku aura min don tayi min, ki ware kawai ki bar Ni nashaƙata da ita.."
Be rufe baki ba ƙaran da RAUDHA tasaki yakaraɗe ilahirin gidan baki ɗaya, idanun ta a rufe suke har a time ɗin batare da ta buɗe su ba
Dasauri Basiru yazuƙuna agaban ta yariƙo hannun ta yana cewa "ke ke ke buɗe idon ki mana, mafarki kike yi ne? Halan Ni kika gani ƴar kyakykyawa?"
Ahankali RAUDHAN tabuɗe idanun ta tana tsai dasu kan Basiru dake gaban ta riƙe da hannun ta yana washe mata baki, lumshe idanunta tayi tasake buɗe wa akansa, kamar an tsikare ta kuma tayi zumbur tatashi zaune tana wurwurga idanu cikin ɗakin cike da tsananin tsoro
Bata kai ga tantance inda take ba Basiru yajawo ta jikin sa yana faɗin "sannu kyakykyawa kin tashi daga barcin ko?"
Sai kuma yakalli Lantana dake tsaye tana kallon ikon Allah bata sake cewa komi ba
"Da Allah ki fita kin tsaya min akai, ko so kike yi kiga abinda zan mata?"
"Basiru". Takira sunan sa cike da rawan baki, domin hankalin ta a yanzu ya tashi sosai musamman da taga Basirun dagaske yake yi don tasan halin sa
RAUDHA dake faman ƙwace jikin ta da yatattakura ya ƙwaƙume ta ƙam yana son kai hannu jikin ta, wani irin ihu taƙwalla tana ture sa, ihu kawai take yi babu ji babu gani tana faman kai masa duka, tsoro ne fal aranta sabida ganin ta a inda bata taɓa tsintan kanta ba
"Ke wlh zan ci uwar ki idan baki tsaya ba, uwar me zan miki? Ina ce zan cire miki rigan ne kisha iska naga kina zufa".
Ganin ya ɗaga mata riga zai cire mata tariƙe da ƙarfi tana kwantsama ihu me matuƙar firgitar wa
Ita kanta Lantana roƙon sa take yi yasakar musu ƴa amma be ma san tana yi ba
Babu zato babu tsammani sai ga Basiru yayi sama an buga sa da bango, sai gashi can gefe yashe yana ƙwalla ƙaran azaba dafe da ƙeyan sa, wani irin ashar yasaki yana kallon Lantana dake tsaye itama tana kallon sa cike da tsananin mamaki, ko kaɗan bata ga sanda yaje wajen ba sai ganin sa da tayi
RAUDHA tuni ta sume babu ko numfashi a tattare da ita
Cikin azaban zafin da yaziyarce sa yace, "kuttt.. sabida wannan shegiyar yarinyan ce zaki jefo Ni nan Lantana?"
Waro idanu Lantana tayi tace, "da wani ƙarfin zan iya jefa ka nan Basiru? Wlh Ni ban ma san sanda kazo wajen ba sai ganin ka da nayi".
Shiru yayi yana maida idanun sa kan RAUDHA, mamaki ne fal aransa don shima yasan Lantana bata da ƙarfin da zata iya mishi irin wannan jifan, ko mahaifin sa da yake da ƙarfi bazai iya masa wannan ba bare ita
"To wanene ya jefo Ni nan ɗin?" Yafaɗa afili
Kiran da Malam Umaru yake kwaɗa wa Lantana yasaka tafita dasauri tana amsa wa
A bakin ƙofa suka yi kicibir
"Yauwa Malam gwara da Allah yakawo ka, wlh Basiru ne zai yi wa ƴar mutane ta'asa, mun shiga uku Malam idan asirin mu ya tonu". Sai tafashe da kuka
Cikin tashin hankali Malam Umaru yatambaye ta "ina Basirun?"
"Yana ciki".
Wuce ta yayi ya shiga ɗakin tana take masa baya
Basirun na nan a inda yake, sai muzurai yake yi jin muryan Baban sa
Kallo ɗaya Malam Umaru yayi masa yanufi wajen RAUDHA, dasauri yasaka hannu yaɗauke ta yafito da ita zuwa ɗakin su, ajiye ta yayi ya saka Lantana ta ɗibo masa ruwa, amsa yayi bayan ta kawo ya shafa mata a fuska, bata farfaɗo ba sai da ya sake shafa mata wajen sau uku kafin taja numfashi tabuɗe idanun ta da suka shige ciki sukai matuƙar ja, abun zai baka mamaki idan ka kalli idanun RAUDHA
Su kansu Malam da Lantana sai da suka tsorata ganin yanda idanun nata suka sauya kala, har wani kore-kore suke yi sabida tsaban ja
Hankalin su be tashi ba sai da tasaka musu kuka me ban tausayi, wani irin kuka take yi tamkar ta haukace, gaba ɗaya ta firgice musu da kukan nata sun rasa yanda zasu yi da ita, gashi taƙi yin magana duk da kuwa tana son yin maganan, sai dai da zaran ta buɗe baki sai ta kasa sarrafa abinda zata ce illa kuka kaɗai da take iya yi
Daƙyar Malam Umaru ya dage da yin mata addu'a har kukan nata ya lafa, sai kuma ta firgice musu akan dole sai sun kai ta gida
Malam Umaru yace, "baiwar Allah ki nutsu ki kwantar da hankalin ki sai ki faɗa mana inda kike mu maida ke kinji?"
Gyaɗa masa kai tayi tana jan majina, cikin dashashshiyar muryan ta da yaƙara shigewa sosai don daƙyar ake iya jin me take cewa, tafaɗa masa inda take a Asokoro
Dayake Malam Umaru yana shiga birni sosai, kuma yana jin sunan anguwan duk da be taɓa zuwa ba, but idan ya tambaya ai za'a iya kai sa tunda ba ɓoyayyen wuri bane, don haka yasaka RAUDHA tatashi ya kai ta
Abin mamaki ta kasa tafiya domin ƙafar ta ɗaya ya markwaɗe tamkar na kuturwa sai zafi yake mata, kuka tasaka tana komawa tazauna
Cike da tausayi Lantana tace, "Malam yarinyan nan fa baza ta iya tafiya ba, kar dai wani abun ne yasame ta? aje a ɗauko me gyara ya duba ta".
RAUDHA dake kuka tasake ɓarke musu da kuka "wai sai dai su kai ta gidan su".
Abun har mamaki yake basu, yarinya sai kace ba mutum ba, ta ishe su da kuka sai kace sun sato ta, su kansu sun san ba ƙaramar taɓararriya bace ita ɗin, tunda gashi duk ta hana su kwanciyar hankali
Sai da Malam Umaru yasake rarrashin ta akan tazauna zai je yasamo me mota sai su tafi, hakan kuwa yafaru be jima ba yadawo da me keke napep, shi ya ɗauke ta ya kai ta har waje cikin keke napep ɗin tunda baza ta iya tafiya ba, sannan suka tafi.
🌐🌐🌐
Sanda suka isa ƙofar gidan Suhaib, wani daɗi ne sosai ya kama RAUDHA, sai dai rashin tafiyar ta ya saka dole sai da tajira Malam Umaru ya sake ɗaukar ta, dayake RAUDHA bata da nauyin jiki ko kaɗan kasancewar ta ba me yawan cin abinci ba, that's why Malam Umaru idan ya ɗauke ta tamkar ya ɗauko ƴar baby
Itace me buga Gate ɗin gidan, sai dai shiru ba'a zo an buɗe ba
Hakan yasa Malam Umaru yaduƙa yaɗauko dutse yayi amfani dashi wajen buga Gate ɗin
Babu jimawa kuwa me gadin yafito a fusace don ganin me buga musu ƙofa haka, tozali da RAUDHA da yayi a hannun Malam Umaru sai yayi saurin wangale musu ƙaramin Door ɗin da yafito ta ciki yana ma RAUDHA sannu, duk da kuwa mamaki ne fal aransa da al'ajabin ganin ta hannun wannan dattijon
Me gadin biyo su yayi yana nuna wa Malam Umaru inda zai bi, sai kace an saka sa
RAUDHA na jin sa don haka bata yi magana ba ma.
Suhaib na zaune shi kaɗai a parlour'n lokacin da suka shigo, dasauri ya ɗago kansa idanun sa da suka gama faɗa wa suka sauka kan RAUDHA
Kafin ma yayi magana ta kwaɗa masa kira
Ai tuni yayi zumbur ɗin tashi ya nufo su da mahaukacin sauri, jikin sa na rawa yasaka hannu ya amshe ta yana kiran sunan ta
Ita kuwa kuka ta saka masa tana ƙamƙame sa sosai.
Hayaniyan su ne yafito da Farida, ganin RAUDHA ba ƙaramin saka ta farin ciki yayi ba, ai tuni itama ta nufo su tana nuna murnan ta
Tsawon mintuna goma Suhaib na rungume da RAUDHA a jikin sa yaƙi sauke ta, faɗan tsantsan farin cikin ma da yake ciki ɓata lokaci ne, domin har da hawayen sa sabida tsaban murna.
Malam Umaru dai na gefe ya saki baki yana kallon abun mamaki
Sai Farida ne ma da takula dashi tayi masa maganar ya shigo ya zauna
Sai da yazauna kafin shima Suhaib yataho RAUDHA na jikin sa ya zauna
Ganin RAUDHAN ta ƙi dena kuka sai ya soma rarrashin ta, yana share mata hawaye da hannayen sa
"Kinga yi shiru my dear, ai gashi kin dawo ko? Babu abinda zai sake raba mu insha Allahu, yi shiru ki nutsu ki faɗa min waɗanda suke da hannu wajen ɗauke ki, nayi miki alƙawari sai na ɗau babban mataki akan su".
Sake sakin kuka RAUDHA tayi tana ƙwaƙume shi tamkar zata koma Cikin sa
Idanun Suhaib jazur ya ɗago kansa yana kallon Malam Umaru ya ce, "Malam menene haɗin ka da ƙanwata? Ya akayi tazo hannun ka?".
Malam Umaru duk jikin sa ya yi sanyi, daƙyar ya iya cewa, "wlh nima yallaɓai tsintan ta nayi a wani jeji, shine na taimake ta".
Daga nan ya soma faɗa musu komai tiryan-tiryan
Sosai hankalin Suhaib ya sake tashi da jin ƙanwar sa a jeji aka tsince ta, kuma cikin mawuyacin hali, Allah kaɗai yasa da rabon zata sake rayuwa har su gana, da tuni Dabbobin daji sun cinye masa ƙanwa
Ɗago kanta yayi yana kallon ta cike da tsantsan tausayawa, kana ya kalli ƙafan nata, ai kuwa sai da hawaye suka cika masa idanu sabida ganin ƙafan a nanƙwaye, saurin saka hannu yayi ya taɓa
Sai ta callara ƙara sabida azaban da ya ziyarce ta
Nan da nan Suhaib ya sake ruɗe wa, miƙe wa yayi dasauri ya saɓa ta a kafaɗa yana kallon Farida ya ce, "Wifey sallami bawan Allan nan, zan kai ta asibiti aduba mata lafiyan ƙafan ta".
Be jira cewar ta ba yajuya yafice dasauri, a back seat ya kwantar da ita yashiga mazaunin drever, da wani irin Speed yaja motan yanufi gate yana danna Horn da ƙarfi
Tuni me gadi ya buɗe masa ya fice.
[2/22, 4:27 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma'il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON TWENTY FOUR*
_______📖 Suna zuwa asibiti aka amshe ta sabida ya saki kuɗi, Doctors sun yi iya yin su don ganin ƙafar RAUDHA ya dawo dai-dai, duk da duk wani bincike da suka yi basu gano matsalan ba, kuma shi ƙafan ba targaɗe ba; ba karaya ba ba komi ba, lokacin da zasu jajja mata ƙafan sai da suka yi mata alluran barci, shiyasa har suka gama duk abun da zasu yi bata san ma suna yi ba
Doctor ɗin da ya jagoranci duba ta, yayi wa Suhaib bayani basu gano komi ba, amma dai sun saka mata magani da yardan Allah ƙafan zai dawo dai-dai, a hasashen da suka yi.
Wajen ƙarfe 03:20pm. Drever yakawo Farida, har da abinci ta taho musu dashi, kuma bata tafi ba sai da ta ga farkawan RAUDHAN
Suhaib ne yayi ruwa yayi tsaki akan shi zai kwana, duk da Faridan tace masa "ya bari zata kwana da ita". But yaƙi, dole tatafi ta bar shi.
Washe gari alhmadulillah ƙafan nata ya dawo dai-dai, sai dai ba duka ba, kuma tana jin zafi sosai idan ta taka
Anan Suhaib ya tambaye ta abinda ya faru a ranan, domin shi so yake yi ya hukunta waɗanda sukai sanadin shigar ta haka
Sai dai ta kasa tuna komi, abinda zata iya tuna wa kawai zuwan ta club da fitowar ta haraban wajen, sai kuma farkawan da tayi ta ganta gidan Malam Umaru
Da damuwa Suhaib ya kalle ta yace, "Dear ki dai sake tunani ko zaki tuna wani abun?"
Ɓata fuska RAUDHA dake shan ferfesun zabo tayi, tana zaune saman gadon mara sa lafiya tayi ɗai-ɗai abun ta, tana shirin magana ne wayan Suhaib ɗin tayi ƙara
Ciro ta daga aljihu yayi yana kallon screan ɗin wayan da mamaki, domin dai ba kowa ya kira sa ba illa drevern gidan sa
Ɗauka yayi yakara a kunne yana tambayan sa "Lafiya?" Batare da ya jira cewar sa ba, bare kuma su gaisa
Drever'n faɗa masa yayi gasu a asibiti ya kawo Farida babu lafiya
Tashin hankali ne yasake riskan Suhaib, nan da nan ya tashi ya fice batare da ya bi takan RAUDHA dake masa magana ba
Sai ta kwaɓe fuska tana turo baki, ajiye Plate ɗin tayi akan drowan kusa da gadon, ta ziro ƙafafuwan ta da babu takalmi ta sauko, ahankali take taka ƙafan ta tana cije leɓe, da haka ta ƙarisa bakin ƙofa tafice
Ahanya ta haɗu da Suhaib suna tsaye shi da drever sun yi cirko-cirko
Yana ganin ta yataho da sauri yana tambayan ta "meyasa ta fito?"
Kamar zata yi kuka tace masa, "ba kai ne kafito ka bar Ni ba, kuma ina maka magana ka tafi ka bar Ni".
Riƙe kansa yayi yace, "Oh I'm sorry Baby hankali na ne ya tashi, Wifey aka kawo ba ta da lafiya, yanzu mu je ki koma kar wani abun ya same ki".
Girgiza masa kai tayi tace, "a'a, Ni gida zan je, a sallame Ni ni dai".
"To Baby me zaki je kiyi agida bayan duk gamu anan? Kuma kin ga ai Doctor be sallame ki ba". Yayi maganar yana riƙo kafaɗun ta ganin kamar ta gaji tana shirin faɗuwa
Cikin yamutsa fuska tace, "yaya Ina son in je in Yi wanka ne, Please ka saka a sallame Ni, bana son zama nan".
Be musa mata ba, yace mata su koma ɗakin, sai yaje ya nemo likitan ya basu sallaman
Shi ya taimaka mata suka koma, sannan ya zaunar da ita ya fito
Ita RAUDHA ta ƙosa taje tayi wanka ne, shiyasaka ta matsa masa sai an sallame ta, gaba ɗaya bata jin daɗin jikin ta sabida tun ranan da tabar gida rabon ta da wanka, ita da take yin wanka sama da sau uku; huɗu a rana, amma gashi kwana uku rabon ta da tayi, ita kanta ƙyanƙyamin jikin ta take yi, musamman ma idan ta tuna gidan da tatashi ta tsinci kanta, da ɗaukan da Malam Umaru yayi mata, sai dai babu yanda zata yi tunda ahalin lalura take a lokacin.
Drever ya kai ta gida, tana zuwa wanka tayi tasaka ƴar shimi tahaye gado sai barci, ko tunanin ma ta koma asibiti taga halin da Farida take ciki bata yi ba.
Can kuwa a asibitin har wajen awanni huɗu babu haihuwar Farida, duk ta galabaita
Lokacin tuni Umman ta da Ƙanwar ta Maryam sun zo, har babban Yayan su da matar sa duk sun zo, gaba ɗaya sun yi jigun-jigun a reception ɗin suna jiran Likitoci
Sai Suhaib ne da Babban Yayan su suke zirga-zirga wajen samo abin da ake nema
Gab da magriba ta haifo ɗan ta na Miji kyakykyawa irin Suhaib sak, kowa yayi murna sosai, barin ma da aka ce musu babu abunda ke damun Farida, sai dai yaron ne tamkar bashi da lafiya don yaƙi yin kuka
Likitoci sun yi duk binciken da zasu yi akai, sannan suka sanar da Suhaib ɗin abinda ke damun yaron
Be da wani ƙoshin lafiya, irin cutan nan da yake mayar da mutum tamkar soko, yayi ta zulalan miyau, kansa yaƙi tsayuwa waje ɗaya, haka yaron yanzu yake yi, sai dai kasancewar sa jariri baza ka ga alamun zub da miyau ɗin nasa ba, sai idan ya girma
Suhaib ya shiga damuwa sosai, amma likitan ya kwantar masa da hankali, zasu ɗaura sa akan magani idan an dace komi zai wuce, da haka Suhaib ya fito Office ɗin likitan da ƙwarin gwiwa, tunda yaji akwai maganin ciwon yaron nasa, wataran kenan yana iya warke wa.
Koda yashiga ɗakin da aka kwantar da Farida duk ƴan uwan ta ne aciki, tana zaune itama tana shan tea da aka haɗa mata, yaron na kwance gefen ta baza ka ce akwai wani abinda ke damun sa ba
Ɗaukan yaron yayi yana kallon sa cike da farin ciki, ya jima yana riƙe da yaron a hannun sa kafin ya ajiye sa, yayi musu sallama akan zai je ya dawo yafice.
Gida ya wuce kai tsaye, koda yashiga parlour'n be tarar da RAUDHA ba, don haka ɗakin ta yawuce yashiga
Tana kwance har yanzu tana barci
Numfashi yasauke ya ƙarisa bakin gadon, ɗaga kanta yayi yacire pilon yazauna sannan ya ɗaura kanta saman cinyan sa, kallon ta kawai yake yi cike da tausayi, Allah ya gani yana ƙaunar ƙanwar tasa fiye da komi na duniya, soyayyar da yake mata baki ma bazai iya faɗan sa ba
Shafa gashin kanta yake yi idanun sa akanta, sai dai tunani yalula me zurfi, sai da yaji kiran sallan isha'i kafin yatashi ya gyara mata kwanciyar ta yafice
Ɗakin sa ya wuce yashiga Toilet, wanka yasoma yi, don rabon sa da wanka shima ɗin tun washe garin ɓatan RAUDHA, sai da ya ɗauro alwala kafin yafito, shirin sa yayi cikin sauri ya ɗau keey ɗin mota ya fice, sai da yatsaya a masallacin layin nasu yayi Sallah tukun ya wuce asibiti.
A lokacin su Umma duk sun tafi gida, sai Maryam da aka bari wajen ta
Shima ɗin koda ya isa ba wai zama yayi sosai ba, zuwa ƙarfe goma yayi musu sallama yadawo gida tunda Maryam ɗin zata kwana da ita.
Koda yadawo ya tarar da RAUDHA zaune a Parlour, tana ganin shi tanufe sa tarungume shi tana masa shagwaɓa, shi kuma sai biye mata yake yi
Koda taji Farida ta haihu bata wani nuna murnan ta ba, ba wai don bata yi farin ciki ba
Shima kuma be damu ba, sai yaja hannun ta suka tafi kan dainning suka soma cin abinci, ita kaɗan taci tunda tarigada taci kafin yazo, daga nan Parlour suka koma, ita kwanciya tayi shi kuma aiki yasoma yi cikin Lapton ɗin sa, kasancewar kwana biyu be je Office ba shiyasaka yake ragewa kar su taru mishi
Sai wajen 12:30am. Ya tashi, lokacin tuni RAUDHA tayi barci, sai ɗaukan ta yayi yamaida ita ɗakin ta, yarufe ta da bargo tare da ƙara mata A.C yafice.
Kamar shuɗewar awa ɗaya RAUDHA tasoma mummunan mafarki irin na ranan nan, gaba ɗaya ta haɗa gumi da zufa sai makyarkyata take yi, kuma har alokacin bata farka ba
Ƙaton maciji ne yake bin ta acikin baƙin dajin me tsananin duhu da sunkuru, kuka take tayi tana gudu tana waigen bayan ta, duk da kuwa bata ma ganin komi acikin dajin sai macijin nan me kamar wuta jikin sa
Sai da ya cafko ta yana ƙoƙarin haɗiye ta tafarka da ihu me tsananin ƙara, babu inda jikin ta baya rawa, ga kanta da yake faman sara mata kamar zai rabu gida biyu sabida dariyan da ya cika ɗakin, lokaci ɗaya numfashin ta yarabu da gangan jikin ta takoma yaraf kan gadon
Kamar wancan lokacin ihun ta babu wanda yaji agidan, har garin Allah ya waye
Zuwa tara Suhaib ya gama shirin sa zai koma Hospital ɗin, ya saka kuku ya haɗa masa Breakfast Wanda zai kai musu can
Ɗakin RAUDHA yashiga, sai dai ganin ta har yanzu tana barci be tashe ta ba yafice.
Sai ƙarfe 12:40pm. Kafin RAUDHA ta tashi, babu abinda ta tuna na game da mafarkin ta, sai dai yanda gaba ɗaya jikin ta ke mata ciwo ga tsananin zazzaɓi da yarufe ta, yunwa da ishin ruwa duk ya addabe ta, ita kanta mamakin yanda take jin wani irin bahagon yunwa take yi, ga bakin ta gaba ɗaya ya ƙafe daƙyar take iya samun miyau ɗin da take haɗiya
Rarrafa wa tayi tamiƙe tasauko daga kan gadon, sai dai kuma ƙafan ta ya riƙe sosai daƙyar take iya taka wa, zafi sosai yake mata ba kamar yanda ta kwanta jiya dashi ba, lumshe idanun ta tayi sai ga hawaye sun soma sulmiyo mata, hannu ta saka tashare kafin ta ɗingiza ahankali tanufi gaban Fridge, domin ji take yi tamkar zata mutu idan ba tayi gaggawar shan ruwan ba, ga jikin ta dake mata ciwo ko ina, kamar an hau jikin ta an kwana sukuwa a kanta haka take ji
Buɗe Fridge ɗin tayi taciro goran ruwa, tunda ta kafa a baki bata dakata ba sai da tayi rabin ruwan, kana ta zube nan ƙasa da rawan jiki, nan da nan zazzaɓin ya sake rufe ta, ta kwanta tana kuka sai juye-juye take yi.
Allah ne yakawo mata Ester, ta shigo gyara mata ɗakin, ai kuwa nan hankalin ta yatashi ta nufe ta tana kiran sunan ta, sai dai gani tayi tamkar ba ta numfashi, nan da nan ta sake rikice wa tatashi da gudu ta fice.
.
_plz share and Voting_
_kar ku manta da Comment plz._
[2/22, 10:38 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
𝐑𝐀𝐔𝐃𝐇𝐀
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
𝐌𝐀𝐋𝐋𝐀𝐊𝐀𝐑: ✍️
𝑁𝑎𝑓𝑖𝑠𝑎𝑡 𝐼𝑠𝑚𝑎'𝑖𝑙 𝐿𝑎𝑤𝑎𝑙 𝐺𝑜𝑚𝑎.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
\𝗙.𝗪.𝗔📚/
.
𝗡𝗢𝗧 𝗘𝗗𝗜𝗧𝗘𝗗 ___________________________📗
𝗦𝗘𝗔𝗦𝗢𝗡 𝗧𝗪𝗘𝗡𝗧𝗬 𝗙𝗜𝗩𝗘
_______📖 Wajen da aka ajiye Telephone a parlour, nan Ester ta ƙarisa tasaka number ta kira Suhaib
Lokacin yana Hospital ne, don haka koda ta sanar masa sai hankalin sa ya ɗugunzuma ya tashi, tare da Doctor suka taho don bazai iya jiran har yaje ya kawo ta asibiti ba, lokacin tuni ta galabaita kenan.
Suna zuwa kai tsaye ɗakin RAUDHA suka nufa
Ester na tare da ita, har ta shafa mata ruwa a fuska tunda a tunanin ta ta suma ne, sai dai bata sani ba tsaban ciwo ne yasaka ta dena numfashi, idanun ta a rufe sai hawayen dake gangarowa ta gefen idanun ta, gaba ɗaya jikin ta ya saki sai wani irin ciwon da baza ta iya misalta shi ba take ji.
Kanta Suhaib yayi yana kiran sunan ta, gaba ɗaya ya kiɗime ya rasa ma me zai yi
Daƙyar Doctor ɗin ya kwantar masa hankali, yace masa "ya ɗauke ta ya ɗaura saman gado sai ya duba ta".
Kamar yanda yace masa ahakan yayi
Ita tuni Ester ta fice a ɗakin ma
Duba ta doctor ɗin ya soma yi, Suhaib na zaune gefen gadon ya gaza motsa wa, zufa duk ya jiƙa masa jiki sabida tashin hankali, duk da kuwa akwai A.c da fan a ɗakin
Sai da Doctor ɗin ya gama duk abinda zai iya yi, kafin ya kalli Suhaib yayi mishi bayani akan "zazzaɓi ne kaɗai ajikin ta". Sannan yace masa "a bata abinci taci sai a nemo maganin da za'a bata".
Rubuta magungunan yayi ya miƙa wa Suhaib
Amsa yayi yana kallon Doctorn kamar zai yi kuka yace, "Doctor yanzu babu abinda ka gano sai zazzaɓi? Ni fa hankali na ya tashi, anya babu wani abinda ya same ta? Ba ka ganin yanda take yi ne?"
Murmushi Doctor yayi yana dafa kafaɗan Suhaib ɗin yace, "kwantar da hankalin ka Man, Ni abinda na gani kenan, ba na tunanin akwai abinda ke damun ƙanwar ka, Just zazzaɓin ne yayi mata kamu sosai that's why tashiga wani hali irin haka, but insha Allahu komi zai zama normal idan aka bata maganin nan, in kuma be sauka ba to sai a dangana ga asibitin".
Gyaɗa kansa Suhaib yayi cike da gamsuwa, kana yamiƙe tare da yi wa Doctor ɗin godiya
Tare suka fita cikin ɗakin, ɗaya daga cikin ma''aikatan gidan ya aika ya siyo masa maganin a Chamis, sannan ya koma ciki, shi da kansa ya haɗo mata Lunch ɗin da Kuku ya gama akan faffaɗan tiray, ya nufi saman dashi
Yana shiga ɗakin yanufi wajen ta, sai da ya'ajiye tiray ɗin a saman drowan gadon kafin ya zauna, yasaka hannu yaɗago ta yana faɗin "Baby tashi kici abinci kisha magani".
Langaɓe kanta tayi tana son komawa, nan da nan hawaye suka cika idanun ta, cikin dashashshiyar muryan ta da baya fita sosai tace, "Yaya Sanyi".
Suhaib duk ya ruɗe ya rasa yanda zai yi da ita, don tuni ta soma masa kuka, aza ta yayi ajikin sa yasoma rarrashin ta cike da tausayin ta, sai da yaga ta nutsu ta dena kukan sannan yamiƙe yashiga Toilet ya ɗauko mata Brush, shi ya taimaka mata ta wanke bakin ta yaje yazubar da ruwan a Toilet, sannan yadawo yamaida ita jikin sa, a haka yayi ta bata abincin tana ci, sai da ta ture hannun sa kafin yabar ta, sannan ya bata drugs ɗin ta tasha, be barta ta kwanta ba duk da kuwa tana ta mishi ƙorafi da shagwaɓan da tasaba yi, sai da ya tabbatar abincin ya narke ajikin ta kafin ya kwantar da ita yana faɗin
"Baby ko in haɗa miki ruwa kiyi wanka ne, zaki fi jindaɗin jikin ki ko?"
Girgiza masa kai tayi tana lumshe idanuwan ta, ita kaɗai tasan abinda take ji ajikin ta, tunda take bata taɓa jin irin wannan ciwon dake yawo can cikin jinin jikin ta ba, takamaime ma bata san ina ne ke mata ciwon ba, ko ina na jikin ta zafi take ji da radaɗi, ga kanta dake uban sara mata kamar zai rabe gida biyu, wasu zafafan hawaye ne suka soma sintiri a face ɗin ta, don ba ta da ƙarfin da zata iya yin kuka ma
Suhaib bawan Allah ya rasa inda zai saka kansa sabida tsantsan tausayin ƙanwar na sa, ya kai ya kawo haka yayi ta yi, sai daga baya ne dabara yafaɗo masa, ya ɗau bargo har guda biyu ya lulluɓe ta ganin yanda take rawan sanyi, heatern ɗakin ya ƙure mata ta yanda ko ina zai ɗau ɗumi, sannan ya dawo kusa da ita ya zauna yana shafa mata gashin kai, hannun sa ɗaya na cikin nata biyu ya ƙanƙame su, ahaka yayi ta lallaɓa ta har sai da yaga tayi barci tukun yasamu nutsuwar zuciya, numfashi ya sauke me ƙarfi kafin ya yatashi yafito tare da jawo mata ƙofa
Ester ya kira yace, "takula da ita zai je yadawo" sannan yafice agidan.
Barcin awa biyu tayi ta farka
Ester na gefen ta, ita ta taimaka mata da taga tana ƙoƙarin tashi
Ƙafafuwan ta kaɗai ta zuro ƙasa tana riƙe da kanta, bata tashi ba sai da tayi kamar mintuna biyar kafin taɗago kanta tana kallon Ester dake gaban ta a tsaye, ahankali cikin dishewar murya tace, "zan yi wanka".
Ester bata ji me tace ba, sai da tamatso sosai kusa da ita tasake tambayan ta, sake maimaita mata tayi sannan ne taji ta, hannu tasaka tariƙo ta; ta taimaka mata zuwa Toilet ɗin sannan tafito.
Mintuna 20 ta ɗauka aciki kafin tafito ɗaure da towel ajikin ta, gashin kanta da suka manne ajikin ta sai zirarar da ruwa suke yi, ahankali take takawa har zuwa gaban dressing mirror tazauna
Dasauri Ester taƙariso wajen ta tana faɗin "let me help you Ma'am".
Handrayer ta ɗauka bayan ta soka socket ɗin, tasoma busar mata da gashin kanta, bayan ta gama tasoma shafa mata Lotion a kyakykyawar white skin ɗin ta
RAUDHA bata hana ta ba, har sanda tagama shafe mata hannu da ƙafafu kafin tatsaida ita, miƙe wa tayi tanufi gaban Sip ɗin kayan ta
Ester na biye da ita, ita tabuɗe mata Sip ɗin
Ita kuma RAUDHA tanuna mata kayan da zata ciro mata
Akan gado tazube mata kayan sannan tafice.
Matsa wa gaban gadon RAUDHA tayi ta ɗauki kayan tasoma saka wa, riga da wando ne na sanyi masu tsananin taushi da kauri, kalan ruwan ƙasa, da Zip agaban rigan, Sannan ƙafan wandon da na hannayen Robber ne da ya kamata sosai, hula tasaka na kayan me tuntu a tsakiyan, gashin ta gaba ɗaya ta tusa acikin hulan tarufe har kunnen ta, sai da tasaka Socks kafin takwanta tana rufe jikinta da bargo, ba barci take ji ba but ta rufe idanun ta tayi luf akan gadon, har yanzu da sauran zazzaɓi ajikin ta, ga kuma sanyi da take ji can cikin ƙashin ta wanda gaba ɗaya ya hana ta jin daɗin rayuwan ta.
Ester CE tashigo tayi mata maganar "ko akawo mata abinci ne?"
Sai ta girgiza mata kai alamun "a'a"
Hakan yasa tafice tajawo mata ƙofan.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
Sai gab da magriba aka sallamo su Farida, sai dai likitocin sun haɗa su da magungunan da zasu riƙa ba ma jaririn, sannan zasu riƙa kawo shi ana duba sa sau biyu a sati, har aga abun da hali zai yi kafin yasoma girma.
Maryam da wata Dattijuwar mata me suna Inna Haule, ƙanwa CE wajen mahaifin Farida, tare suka dawo gidan, tunda ita INNA Haule ita ce zata zauna da Faridan har tayi arba'in, ita kuma Maryam zuwa bayan isha'i Mijinta zai zo ya ɗauke ta.
Har a time ɗin RAUDHA na nan a kwance, duk tana jin ɗan hayaniyan su daga ɗakin ta, amma bata tashi ba bare tafito
Suhaib ne yashigo ɗakin, idanun sa akan ƙanwar nasa yaƙarisa wajen gadon yana zama, a tunanin sa barci take yi, don haka sai yaɗaura hannun sa saman goshin ta don yaji jikin nata
Buɗe idanuwan ta tayi tana kallon sa, ahankali tafurta "Ya..ya".
"Baby kin tashi?"
"Uhmm". Tace dashi tana ƙoƙarin tashi zaune
Dasauri yasaka hannayen sa ya taimaka mata tatashi zaune, jingina tayi da jikin sa taɗaura kanta saman kafaɗan sa, hannayen ta saƙale a ƙugun sa tasake lumshe idanun ta
Yayinda shi kuma yake shafa mata gashin kanta, yana jin yanda zafin jikin ta ke shiga jikin sa, hakan yasa zuciyan sa sake jin tausayin ta fiye da ko yaushe
"Baby".
"Umm.."
"Ko mu koma Hospital ɗin ne?"
Girgiza masa kai tayi tana ƙara lafewa ajikin sa
Numfashi kawai yaja yana ranƙwafo da fuskar sa, ya sumbaci gashin kanta kafin ya zame jikin sa yana faɗa mata yana zuwa
Fita yayi, babu jimawa yadawo tare da tiren abinci, shi da kansa yaciyar da ita, sannan ya faɗa mata "Farida ta dawo, ko zasu je taga Baby?"
Gyaɗa masa kai tayi alamun zata je
Shi da kansa ya ɗaga ta, hannun sa na riƙe da nata ta jingina da jikin sa suka fito.
Ɗakin Faridan suka shiga, Suhaib ne kaɗai yayi sallama
Maryam dake zaune riƙe da Babyn ta'amsa mishi idanun ta akan RAUDHA
Zama akan stool ɗin mirror yayi, yayinda RAUDHA ke manne dashi taƙi ta sake shi
Cikin fara'a Maryam tace, "Ƙanwata ya jikin naki?"
Ɗan kallon ta RAUDHA tayi tana son tabbatar wa da itan take yi, ganin tana kallon ta sai ta'amsa mata a hankali
"To Allah ya sawaƙe, Allah kuma ya kiyaye gaba".
Wannan karon Suhaib ya amsa mata yana tambayan ta "ina INNA Haule?"
Maryam ta sanar masa ta fita zuwa kichen ɗaura ruwan wankan me gejo, kafin ta ƙara da faɗin "to Nima dai yanzu zan tafi tunda Baban Aliyu ya zo, gashi har yanzu Aunty Farida bata tashi ba, idan ta tashi Yaya sai ka sanar mata Ni na tafi".
Zuwa tayi ta miƙa masa jaririn, kafin ta ɗau jakan ta suka sake sallama tafice
Kichen ta nufa tayi wa INNA Haule itama sallama, sannan ta tafi.
[2/22, 10:55 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
𝐑𝐀𝐔𝐃𝐇𝐀
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
𝐌𝐀𝐋𝐋𝐀𝐊𝐀𝐑: ✍️
𝑁𝑎𝑓𝑖𝑠𝑎𝑡 𝐼𝑠𝑚𝑎'𝑖𝑙 𝐿𝑎𝑤𝑎𝑙 𝐺𝑜𝑚𝑎.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
\𝗙.𝗪.𝗔📚/
.
𝗡𝗢𝗧 𝗘𝗗𝗜𝗧𝗘𝗗 ___________________________📗
𝗦𝗘𝗔𝗦𝗢𝗡 𝗧𝗪𝗘𝗡𝗧𝗬 𝗦𝗜𝗫
_______📖 "Baby kin ga me sunan Daddy? Yana kama dake ko?"
RAUDHA da ta ƙura wa jaririn idanu ko ƙifta wa ba ta yi, ko taɓa sa ta kasa yi illa gyaɗa wa Yayan nata kai da tayi
Murmushi yayi don ya san halin ta akwai tsoron ƙananan yara, don ya tsokane ta yace, "ki ɗauke sa mana kar yayi fushi dake".
Maƙe kafaɗa tayi
"Baby Daddy ne fa, ko ba kya son sa?"
Har yanzu idanun nata akan jaririn yake taƙi dena kallon sa, cikin muryan ta da baya fita ko kaɗan tace, "yaya ka bari sai ya sake girma zan na riƙa ɗaukan sa".
Dariya kawai Suhaib yayi, yana sake rungume yaron nasa tare da sumbatar sa.
Lokacin ne Inna Haule tashigo ɗakin tana faɗin "a'ahh Mijina ashe kana nan ne?"
"Eh Inna, na rako RAUDHA ganin Baby ne".
"To madalla, ai ga ta nan kuwa ta kafa masa idanu amma taƙi ta ɗauke sa". cewar Inna cike da fara'an ta
Suhaib dariya yayi yana kallon RAUDHAN, kafin yace, "Baby baki gaishe da Inna ba".
Sai alokacin ma RAUDHA ta kalle ta tun shigowar ta, gaishe ta tayi kamar yanda Suhaib yace mata
Inna Haule kuma ta amsa mata cikin fara'a, itama tana tambayan ta "Ya jikin ta?"
Wannan karon ma Suhaib ne ya amsa mata, don yasan RAUDHA ba sake magana zata yi ba
Inna Haule zama tayi suka hau hira da Suhaib ɗin, don dama sun saba sosai, har aka kira sallan isha'i suna tare kafin ya tashi yafice, itama RAUDHA bin bayan sa tayi takoma ɗakin ta.
Inna Haule miƙe wa tayi taje ta sako ruwan wankan, kafin tazo ta tashi Farida don tayi mata wankan.
Bayan tayi mata wankan jegon sannan tayi wa jaririn, sai ta ɗauro alwala tafito, lokacin har Suhaib ya sake shigowa ɗakin ya fice
Babu jimawa Kuku yashigo musu da abinci da kunun me jego.
RAUDHA kuwa tunda tashige ɗaki kwanciyar ta tayi bayan ta saka ƙwayoyin ta cikin baki tana tsotso, bata jima ba barci ya ɗauke ta
Koda Suhaib yashigo duba ta yaga tayi barci, be tashe ta ba ya gyara mata Bargon da tarufa tare da kashe mata fitilan ɗakin yafice.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
Ranan suna jaririn ya ci sunan Daddy Mustapha, zasu riƙa kiran sa da Haneep kamar yanda RAUDHA ta saka masa
Ƴan uwa na nesa da na kusa duk sun hallara bikin sunan, gidan Suhaib ya cika maƙil don shi kansa yayi mamaki da mutanen da suka zo taya sa murnan sunan, har da wasu daga cikin dangin mahaifiyar su da ke Bayelsa sai da suka zo, dayake ita ɗin ƴar can ce, su ma wasu daga cikin dangin Daddy dake aure a gari maban-banta duk sun samu zuwa, duk da su ɗin ba dangin sa na kusa bane, but Daddy mutum ne me kyautatawa ko kaɗan ba ya manta wa dasu wajen taimako shiyasa har yanzu suke zumunci, duk da ƴaƴan sa ba zuwa suke yi ba, amma shi yana zuwa wajen su sosai don jin matsalolin su. Itama Farida ƴar dangi ce, don haka dangin ta masu yawa sun hallara ranan sunan, ga matan abokan Suhaib ɗin duk sun zo, hakan yasa jama'a suka yi yawa, an yi taron girma da arziƙi kowa ya tafi yana yaba wa.
Ita kanta RAUDHA da ba son mutane tacika yi ba, sai da tashiga cikin su aka yi suna da ita, daga ƙarshe ne ma da kanta ya soma mata ciwo tashige ɗaki ta'afa ƙwayoyin ta sai barci, bata sake sanin me ake yi ba sai dare da ta tashi, lokacin duk an gama watse wa, sai wasu tsirarun mutane ƴan uwan Farida da ƴan Bayelsa suka rage.
Washe gari su ma duk suka watse aka bar Inna Haule kaɗai dake mata wankan jego. Ita taci gaba da kula da ita har sanda suka yi arba'in, kafin ta tattara ta tafi cike da alhrerai kala-kala da Suhaib ya haɗa ta dasu.
Zuwa lokacin itama RAUDHA tuni ta koma school ɗin ta, sun sake ɗinke wa da su Rash sai abun da yayi gaba yanzu, sai dai yanzu babu Zen yayi tafiya na sati biyu zuwa asalin tushen su Kwara state, an yi musu mutuwa shine suka tafi gaba ɗaya ahalin su.
Yanzu RAUDHA, Rash da kuma Man suna tare ko ina tare suke zuwa, babu abinda suka fasa na game da rayuwan su, sai ma sake taɓarɓare wa da suke yi, ta kai ta kawo yanzu RAUDHA wani lokacin ba ta kwana agida, duk inda suka ce zasu tafi bin su take yi.
Suhaib ya tashi hankalin sa matuƙa da irin wannan sabbin halayen da RAUDHA ta tsiro da su, yana gudun abinda zai faru kamar yanda ya rasa ta kwanakin baya, sosai ya zaunar da ita yayi mata faɗa, but ko sauraron sa bata yi ba, a ranan ma sai da ta kwana biyu bata dawo gidan ba, dole sai shi Suhaib ɗin ya neme ta ya bata haƙuri, gaba ɗaya yanzu ya gama rame wa a tsaye sabida zullumi da tashin hankalin da yake ciki, ga kuma abun tashin hankalin da ya sake riskan su, ciwon Haneep kullum gaba yake yi, yanzu wani tsira ne ya fito masa a ciki, koda yaushe ƙara girma tsiran yake yi, wai ma don suna zuwa asibiti ana magani, dole ya yanke shawaran fita kasar waje don aduba lafiyan sa, daga nan sai yaje inda Daddy yake don sanin halin da yake ciki, tunda har yanzu be sake kiran su ba, duk wasu abokan sa da suke hulɗa sai da Suhaib yabi ya tambaye su ko sun san wani abu agame da Daddyn nasu, but babu wani bayani.
🌐🌐🌐
Yau dayake Saturday ne RAUDHA basu da school, shiyasa take ta sharan barcin ta, jiya a club suka kwana sai da asuba ta dawo, that's why tunda ta shimfiɗe akan gadon ta take barci tamkar kasa, har zuwa ƙarfe biyu taƙi tashi
Wayan ta dake faman tsiwa tana neman agaji, ita ta tashe ta daga nannauyan barcin da take faman yi, ƙiri-ƙiri ta kasa buɗe idanun ta sabida kumburan da suka yi tsaban barci, haka tayi ta kokawa wajen buɗe idanun suna lumshe wa, daƙyar ta iya buɗe su da suka gama ƙanƙance wa suka yi jazur
Wayan dake kan drower ta jawo, lokacin Three missed Call aka yi mata, but me kiran be gaji ba ya sake kiran na huɗun, tsaki taja wanda ko kaɗan be fita ba, ta sake ware idanu kan wayan don ganin nataccen dake kiran ta
Ai tuni ta wartsake sabida ganin sunan Daddyn ta na yawo a screan ɗin wayan, wani ƙara ta ƙwalla da dusashshiyar muryan ta, jikin ta na rawa ta amsa kiran tana kiran sunan Daddy cikin ihu
Lokacin Suhaib ya turo ƙofan ya shigo, jin RAUDHA na ihu tana faman kiran sunan Daddy, ai tuni ya iso wajen ta shima ya zauna yana son ƙwace wayan da faɗin
"Da gaske kike yi Baby? Daddy ne ya Kira ki?"
Cikin tsagwaron murna ta ciro wayan daga kunnen ta tana nuna masa tana faɗin "eh shine Yaya, ka gani ko wlh shine Daddy ne.."
"To saka a hans free Baby".
"To". Ta amsa mishi da sauri tana saka wa
A lokacin ne muryan Daddyn ya bugi kunnen su yana faɗin "Hello kuna ji na?"
"Daddyyyy.." RAUDHA ta sake faɗa tana me fashe wa da kukan jin muryan Daddyn ta
Shima Suhaib ɗin sunan Daddyn yakira ahankali
Daga can Daddy ya amsa musu cikin tsananin kewar yaran nasa, kana yaci gaba da faɗin "Auta na menene kuma na kuka? Ko kin fi son na kashe wayan ne ba kya son jin muryana?".
Cikin kukan take girgiza kanta tana faɗin "A'a Daddy na dena kukan, ina so Daddy.. Ina so.. nayi kewar ka ne sosai da sosai Daddy, yaushe zaka dawo I miss You so Much".
Sai tasake fashe wa da kuka tana faɗa wa jikin Suhaib, shine ya amshi wayan daga hannun ta ya riƙe
Daga can Daddy yace, "Very soon zan dawo gare ku Baby, ki dena kuka kin ji?"
Sai kuma yakira sunan Suhaib ɗin yana tambayan sa lafiyan sa da matar sa
"Daddy lafiya lau kowa lafiya, har Wifey ta sauka an yi maka takwara".
Daga cikin wayan sosai zaka gane Daddy yayi murna da maganar da yaji, nan yayi ta nuna farin cikin shi yana saka musu albarka gaba ɗaya
RAUDHA da take faman share hawaye tace, "to Daddy yaushe zaka dawo?"
Numfashi Daddy yaja kafin yace, "Baby bansan ranan dawowa na ba".
"Why Daddy?". Tafaɗa kamar zata yi kuka
"Ƙaddara Sweetheart, ƙaddara ce ta faɗa min, na faɗa muku kaya na sun sami matsala, bansan ya aka yi ba aka samu Cocaine cikin kayan mu, to har yanzu ana kan bincike ne, dole zamu zauna har sanda za'a gama, idan kuma basu gano waɗanda suka saka ba, zasu riƙe mu ne na shekara ɗaya a Jeil, wannan shine dokan su".
Tun be ƙarisa zancen ba RAUDHA take kuka sosai
Shi kansa Suhaib tuni idanuwan sa sun kaɗa sun yi jazur sun tara hawaye, rungume RAUDHA yayi cike da tsananin tausayin kansu
Daddy shima daga can hawayen yake ta faman share wa, taya zai iya rayuwa na tsawon shekara batare da ya ga Iyalan sa da suka fi soyuwa a ransa ba? Babu wanda yake tausayi sama da RAUDHA, yasan zata shiga wani mawuyacin hali sabida rashin sa, daɗin sa ma da akwai Suhaib, da be san ya zai yi da rayuwan sa ba
Shanye hawayen sa yayi, cikin jarumtan muryan sa yahau rarrashin su gaba ɗaya, yana faɗa musu kalamai masu daɗi
RAUDHA dai taƙi yin shiru sai kuka take yi tana kiran sunan Daddy
Ganin lokacin da aka ɗiba masa na yin waya dasu ya kusa ƙare wa, hakan yasa yakira sunan Suhaib ɗin
Murya na rawa Suhaib ya amsa yana share ƙwallan shi da suka zubo saman kuncin sa
"Suhaib ga amana nan na bar maka, kai kaɗai RAUDHA take dashi a yanzu, kai ne kaɗai gatan ta, a yanzu kai kaɗai ne zaka zame mata Uwa, uba, yaya da kowa ma, Ni yanzu addu'ar ku nake buƙata, idan har da rabon gaskiya zai fito zan dawo gare ku nan kusa, idan kuma Allah be nufa ba, ya ƙaddara dole sai nayi zaman Jeil na shekara ɗaya zan ɗau ƙaddara ta, Ni dai fatana a yanzu Suhaib ka kula da ƙanwar ka, ina so in dawo in yi alfahri da ita, ka kula da ita da kyau, kayi haƙuri da duk wani halayen ta, ina son ka kula da tarbiyyan ta".
Cikin raunin murya Suhaib yace, "insha Allahu Daddy nayi maka alƙawarin kula da Baby, zaka dawo kasha mamaki saboda sauyawan ta, babu abinda zai faru da ita, zan kula da ita sosai".
Murmushi me sauti Daddy ya saki, kafin yace, "yauwa Allah yayi muku albarka gaba ɗaya, kaci gaba da kula da komi nawa, nasan yanzu ba lallai ku sake ji na ba, domin wannan shine daman da aka bamu na ƙarshe da zamu iya yin waya, yanzu zan kashe wayan".
Suhaib addu'a ya soma ma mahaifin nasa akan Allah ya bayyana gaskiya, shi kuma yana amsa wa cike da ƙaunar ɗan nasa
Da zasu yi sallama Daddy yana ta kiran sunan RAUDHA, but ƙiri-ƙiri taƙi amsa wa sai kuka take yi, sai da taji ya kashe wayan kafin tayi saurin wawuran wayan tana me sake fashe wa da kuka, tana kiran sunan Daddy kamar wacce zata shiɗe
Sosai Suhaib ya rungume ta ganin yanda take kukan kamar ranta zai fita, sai faman sambatu take yi tana faman kwaɗa wa Daddyn ta kira
Abu kamar wasa Suhaib ya rasa gane kan RAUDHA, yayi rarrashin duniya taƙi yin shiru, daga baya ma dukan sa tasoma yi sai ya sake ta, kasancewar ya riƙe ta gamm ganin tana bige-bige, lokaci ɗaya kuma numfashin ta ya ɗauke a jikin ta.
[2/26, 1:34 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
𝐑𝐀𝐔𝐃𝐇𝐀
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
𝐌𝐀𝐋𝐋𝐀𝐊𝐀𝐑: ✍️
𝑁𝑎𝑓𝑖𝑠𝑎𝑡 𝐼𝑠𝑚𝑎'𝑖𝑙 𝐿𝑎𝑤𝑎𝑙 𝐺𝑜𝑚𝑎.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
\𝗙.𝗪.𝗔📚/
.
𝗡𝗢𝗧 𝗘𝗗𝗜𝗧𝗘𝗗 ___________________________📗
𝗦𝗘𝗔𝗦𝗢𝗡 𝗧𝗪𝗘𝗡𝗧𝗬 𝗦𝗘𝗩𝗘𝗡
_______📖 Farida ce tashigo ɗakin a rikice, sabida ihun RAUDHAN ne ya tashe ta daga barci shine ta hayo saman taga me ke faruwa
Dai-dai lokacin da Suhaib yake ƙoƙarin zuba mata ruwa a fuska, shima ɗin duk a rikece yake hankalin sa duk ya tashi
Da sauri taƙariso wajen gadon tana tambayan sa abinda ke faruwa
Be iya ce mata komi ba saboda hankalin sa na kan RAUDHA da ta kawo numfashi, sai dai bata buɗe idanu ba illa wani irin nannauyan barci da ya kwashe ta
Girgiza ta Suhaib ya soma yi yana kiran sunan ta, sai daga baya shima ya fahimci barci ne ya ɗauke ta, mamaki sosai ya cika sa da barcin nata, da sauri ya sake zuba mata ruwa ko wai zata farka, amma ko motsin kirki taƙi yi, ga dai shi numfashin ta na fita normal irin na masu barci amma taƙi farka wa
Farida dake tsaye kan su itama tana kallon RAUDHAN, duk hankalin ta ya gama tashi, sake tambayan sa tayi
Anan ne ya faɗa mata abinda ke faruwa, har zuwa suman da RAUDHA tayi, kafin yaja numfashi yana saka hannun sa a aljihu don ɗauko wayan sa ya kira doctor, domin dai hankalin sa ya gaza kwanciya da wannan barcin da RAUDHA ta kama a lokaci ƙanƙani
Shaf ya manta ma, yau be yi amfani da wayan sa ba, kuma a kashe ya barta tun jiya, wannan dalilin ne ma Daddy da ya kira sa be same sa ba, sai ya kira RAUDHA
Kallon Farida yayi yace, "Wifey ɗauko min wayana in kira Doctor, sabida hankalina ya gaza kwanciya da wannan barcin da Baby ta hau yi, anya ma barcin take yi?"
Umarnin sa Farida tabi, tafice da sauri taje ta ɗauko masa wayan
Kiran doctor yayi ya sanar masa da halin da ake ciki
Nan yayi masa alƙawarin zuwa nan ba da jima wa ba, tunda yau weekend ne yana gida.
Babu jima wa kuwa sai gashi yazo, duba RAUDHA ya hau yi, sai dai shima be gano komi dake damun ta ba illa barcin
Nan ya yi wa Suhaib bayani kafin yayi masa sallama ya fita
Sai alokacin ne hankalin Suhaib ɗin ya ɗan kwanta, rufe ta yayi da bargo sannan suka fito shi da Farida, a Parlour suka zauna zugum duk rai babu daɗi, musamman Suhaib da damuwar suka haɗu sukai mishi yawa, ga matsalan Daddy da be san ma ta ina zai soma ɓullo wa al'amarin ba, ga kuma halin da RAUDHA take ciki.
A haka ranan suka wuni sukuku, har dare RAUDHA bata farka ba, hakan yasa hankalin Suhaib ya sake tashi, dole ya sake kiran wani doctor ɗin ya duba ta, shima ɗin be gano komi ba, barcin dai ya sake faɗa musu shi take yi
Abun da zai basu mamaki shine duk yanda Suhaib yayi ƙoƙarin tashin ta amma ko motsi taƙi yi, ya zuba mata ruwa yayi duk wani dabara taƙi tashi, sai sharɓan barci take yi, dole ya haƙura ya bar wa gobe, idan ma bata farka zuwa goben ba ya yanke shawaran Hospital zai kai ta.
Washe gari ƙarfe 07:39am RAUDHA ta farka
Farin ciki duk ya cika Suhaib sai tambayan ta yake yi "ko akwai abinda ke damun ta?" sai dai kuma taƙi yin magana, juyin duniya Suhaib yayi mata magana but taƙi tanka sa, ga dai shi tana kallon sa amma taƙi ta kula sa, kuma taƙi cin abinci, ga idanuwan ta da suka sauya kala, su ba kore ba su ba ja ba
Sabon tashin hankali Suhaib ya sake shiga, shi da Farida gaba ɗaya sun tsorata da yanayin da RAUDHAN ta tashi
Koda yayi yinƙurin kai ta asibiti, ita RAUDHAN taƙi yarda, sai ma kwanciya da tayi ta juya masa baya taƙi koda kallon sa
A taƙaice dai a ɗakin Suhaib ya wuni yaƙi jirga wa ko nan da can, duk yanda ya kai da lallaɓa ta akan ta tashi koda abinci ne taci, taƙi kula sa, dole ya haƙura ya ƙyale ta ba don ya so ba.
Bayan sallan Asar da yadawo ɗakin ne ya ganta tana ƙoƙarin sauko wa daga gadon, da sauri ya ƙarisa wajen ta jikin sa na rawa yakira sunan ta
Ɗago kai tayi ta kalle sa da idanuwan ta da suka koma fari fatt a yanzu ɗin, ɗan kwaɓe fuska tayi cikin shagwaɓa tace dashi, "Yunwa.."
Hannun ta ya riƙe cikin farin cikin jin tayi magana, dasauri ya maida ita ta zauna, yana faɗin "yunwa ko Baby? To bari in kawo miki abinci, ki zauna kar ki tashi ina zuwa".
Ya saki hannun ta ya juya da sauri.
Yana fita itama ta tashi tabiyo bayan sa, be san tana bin sa ba har sanda ya dangana ga kichen ɗin, dasauri ya juyo yana kallon ta
"Baby biyo NI kika yi kuma?"
Gyaɗa masa kai kawai tayi tana ƙarisowa kusa dashi.
Abincin ya ɗiba mata cikin coolar sannan ya riƙo hannun ta suka fito daga kichen ɗin, a Parlour suka zauna yana bata a baki, ita kuma tana amsa batare da tace mishi uffan ba duk da kuwa maganan da yake mata.
Itama Farida fitowan ta kenan daga ɗaki ta gan su a parlour'n, tana riƙe da Haneep a hannun ta ta iso wajen su fuskar ta cike da annuri, zama tayi kan two sittern dake Kallon wanda suka zauna, idanun ta akan su tace, "Ƙanwata duk kin ɗaga mana hankali da rashin cin abincin ki, don Allah idan fushi kike yi damu ki dena wasa da cikin ki irin haka kinji? Baki ga yanda muka tashi hankalin mu ba akan rashin mana magana da kika yi".
Ɗago kai kawai RAUDHA tayi tazuba ma Faridan idanu, batare da tace komi ba dai take amsar abincin da Suhaib ke faman ba ta, yana yi yana shafa kanta tamkar wata ƙwai, ji yake yi kamar ya ɗauke ta ya maida ta ciki sabida ƙaunar ta
Farida dai bata damu da rashin mata magana ba, tunda ta saba da halin ta, girgiza Haneep take faman yi sabida kar ya tashi daga barcin da yake yi.
Be dena bata abincin ba har sai da ta ture hannun sa, hakan yasa ya janye yana ɗaukan ruwa a Cup ya miƙa mata
Amsa tayi tasha sannan ta ba shi ya'ajiye
Kallon ta kawai yake yi yana zuba mata murmushi, sai kuma ya saka hannu yana gyara mata gashin ta dake zube a gadon bayan ta babu Ribom, tattare mata ya hau yi yana ƙoƙarin ɗaure mata shi
Ita dai tana jin sa batace komi ba, ba wai don ba ta da abun cewa ba, a'a, sai don rashin daɗin da jikin ta ke mata, kamar an zare mata laka haka take ji, ga kanta da be gajiya da mata ciwo ko yaushe.
Tashi Suhaib yayi ya riƙo mata hannu yana faɗin "tashi muje ki raka Ni Baby".
Tashi tayi babu musu
Farida ta kalle sa tana cewa, "Husband sai ina kuma?"
Keey ɗin motan sa dake ajiye akan Centre table ya ɗauka yana bata amsa da faɗin "super market zan kai Baby".
Adawo lafiya tayi musu
Fice wa suka yi ita kuma ta raka su da ido, ajiyan zuciya ta sauke aranta tana tunani daban-daban.
🌐🌐🌐
Babu inda suka zarce sai super market, kayan ciye-ciye duk ya jido mata cikin leda, daga nan suka yo gida
Suna shigowa RAUDHA tanufi sama da kayan ta
Shi kuma Suhaib zama yayi akan sofa yana zaro wayan sa dake faman Ring, idanun sa ya kai saman wayan, sai kawai ya saki murmushi idanun sa a waje
Be ɓata time ba ya amsa kiran yana kara wa a kunne
"Wlh Ni nayi fushi ℝ𝔸𝕐, baka san da tuna wa dani ba sai yanzu". Suhaib ya faɗa hakan har yanzu da kyakkyawar murmushin sa shimfiɗe a face ɗin sa
Daga can wata dakakkiyar murya me tsananin daɗi da sanyi tasoma magana, shima daga ji mamallakin muryan yana a cikin nishaɗi ne
"Afwan ranka ya daɗe tuba nake, kaina bisa wuya Dude".
Suhaib yace, "Ni dai nayi fushi da kai, kuma ban san wa zai shirya mu ba, nayi ta neman Numban ka but a kashe koda yaushe".
Murmushi me sauti wanda aka kira da Ray ya saki, kana kuma yace, "Plz Dude I'm so sorry, wlh bansan da bakin da zan yi maka bayani ba, laifi na shine aiki ya mantar dani na bar waya ta a can Bayelsa, kuma na taho nan Nigeria da ninyan in zo har gida but aiki ya riƙe Ni, sai da na sauya waya kuma na tuna ban riƙe sabon Numban ka ba, har ta na Daddy ma ba na samu wlh, yanzu haka na koma gida ne na samu na kira ka".
Suhaib dariya yayi cike da farin cikin jin Abokin nasa, tare da tsantsan ƙaunar junan su yace, "babu komi Dude na amsa tuban ka, and sai dai ka kiyaye gaba don idan ka sake irin wannan babban laifin tabbas zamu samu matsala".
Gaba ɗayan su suka yi dariya wannan karon, sai Suhaib yayi saurin cewa, "wai ma tsaya, kar inyi saurin yafe maka, I tot kana Kaduna ne, Right?"
"Yeah Ina Kaduna wlh, wajen Six months kenan yanzu nayi".
"But I know baka taɓa nema na ba acan?"
"Sorry Dude aiki ne.."
"Eh na sani aiki ne zaka ce dama". Suhaib ya katse sa da faɗan hakan
Sai kuma suka yi dariya gaba ɗaya kafin su soma gaisa wa cike da kewan junan su, duk kan su farin ciki yalwace a fuskokin su, kai da gani kasan akwai soyayya da shaƙuwa sosai a tsakanin su
Suhaib ya tambayi iyalan gida gaba ɗaya
Ya ba shi amsa da "Alhamadulillah kowa lafiya" sannan shima ya tambayi lafiyan matar shi da ƙanwar shi RAUDHA
Murmushi Suhaib ya saki yace, "I know yanzu Baby ta manta da kai, ko kai ma nasan baza ka gane ta ba yanzu ai".
Murmushi shima yayi yace, "gaskiya ne, to shekaru sun ja, ina tunanin ma rabo na da ita 14years Ago fa, sa'ilin tana 5years, uhmm yanzu nasan ta girma sosai, ta zama ƴammata".
Suhaib yace, "really! gashi yanzu har ka zama Daddy yanzu ma".
"Dude da gaske?"
Murmushi Suhaib ya saki yana ƙara bashi tabbaci, kafin ya faɗa masa abun da aka samu
Sosai ya nuna farin cikin sa, cike da ɗoki yace, "kace zan zo a Sa'a kenan, domin zuwa gobe insha Allahu uwar haka ina nan Abuja, an dawo damu nan zamu yi 3years, so har na ba da cigiyan gida anan, domin ba zan zauna a Barrack ba".
Shima Suhaib murna ya hau yi, cike da tsantsan farin ciki yace, "ai gidana kawai zaka zo, taya ma zaka zauna a wani waje bayan kana dani, No No hakan ma bazai taɓa yiwu wa ba, ai kawai anan zaka zauna".
Dariya shi dai yayi, don daman ya san halin abokin nasa, shiyasa be wani ja zancen ba suka ci gaba da hiran su, daga ƙarshe suka yi sallama cike da farin cikin gobe zasu ga juna, tsawon shekaru uku kenan rabon da su ga juna ido da ido, sai a waya, a wayan ma yanzu kusan 7months
Koda aka yi auren Suhaib be halarci bikin ba, lokacin an tura su Jejin sambisa don kawo ƙarshen ƴan boko haram, a time ɗin kusan shekaru biyu suka yi acan suna karan batta, daga ƙarshe ma an yi tunanin sun mutu don tuni an rasa inda suke, an duba su ko ina ba'a same su ba saboda a lokacin an rigada an kashe mutanen su gaba ɗaya, sai su iya goma da suka sha, a wani ƙauye suka zauna tsawon shekara ɗaya da watanni suna a mawuyacin hali, domin duk kan su sun sha harbe-harbe babu kyan gani, sai da aka yi jinyan su har suka gama warke wa, kafin su samu su dawo gida daƙyar, don a hanya ma sai da suka sake cin karo da ƴan boko haram, gashi time ɗin basu da makamen aiki, daƙyar suka sha aka kashe musu mutum uku.
Sai dai sun san juna sosai a waya shi da Farida, don suna yawan gaisa wa akai-akai, har a hoto ma ta san shi tunda tana gani a wayan Suhaib.
Suhaib ɗin na sauke wayan a kunnen sa, Farida tafito daga ɗakin ta, zama tayi tana tambayan sa "shi da wa yake waya yake ta faman fara'a?"
Lokacin itama RAUDHA ta sauko daga sama, ta ƙariso wajen ta zauna gefen Yayan nata, tana jin duk amsan da Suhaib yake ba wa Farida but bata saka musu baki ba, tunda ita be shafe ta sai tasan ko wanene ba a ganin ta.
Sosai Farida tayi farin ciki itama da zuwan Ray ɗin, nan suka soma shawaran ɗakin da za'a gyara masa zuwa goben, Suhaib yace, "a gyara masa sama kusa dana RAUDHA, nan zai fi".
Ɓata fuska RAUDHA tayi kawai batare da ta tanka su ba
Suhaib ya janyo ta jikin sa yana cewa, "Baby baki ce komi ba, kina jin zamu yi baƙo?"
Baki ta taɓe tace, "to Ni ina ruwana dashi".
Murmushi Suhaib yayi yace, "ai kuwa ke kike da ruwan ki Baby, Yaron Uncle Hassan ne fa, wanda ada yake siyo miki chaculate time ɗin kina ƴar ƙararrama, sai ki maƙale masa idan yazo gidan mu kice sai kin bi shi, har kin manta sa ko?" Yayi maganar cike da tsokana
Turo baki tayi tace, "Ni Yaya na manta shi, kuma bazan iya tuna shi ba".
Hancin ta yaja yace, "dama wasa nake miki Babyna, time ɗin ai kinyi ƙarama da yawa, but ina so in faɗa miki zamu je Ƙasar India wajen likita, saboda Haneep, zaki bi Ni Ko zaki zauna ki kula da karatun ki?"
Kallon sa tayi, sai kuma ta kawar da kanta cike da sanyin murya tace, "bazan je ba".
Murmushi Suhaib yayi domin shima yafi son hakan, gwara ta zauna tayi karatun ta har sanda zasu dawo, tunda a ganin sa yanzu yana da wanda zai ba ma amanar ta, hankalin sa kwance zai bar ta yaje ya dawo.
0 comments:
Post a Comment