Be hana ta ba, don shima be san sanda ya janyo ta ɗin ba, kawai dai yabi umarnin zuciyar sa ne, so kawai yake yi yaji ta a jikin sa, be iya ce mata komi ba har ta juya ta bar wajen itama batare da ta sake furta masa komi ba
Ɗakin ta tawuce ta faɗa kan gado, a ranta sosai take mamakin abinda Ray yayi mata, tsaki taja tana birkita kwanciyar ta
"Ko meye ruwan sa dani ne wai? Ni fa na tsani takura a rayuwa ta". Tafaɗa a fili tana sake jan wani dogon tsakin
Ko kaɗan ba ta son yanda zuciyar ta take damun ta da tunanin sa. Hannu ta saka ta janyo rigan ta tana shinshina, gaba ɗaya ƙamshin sa ya addabar mata hanci, miƙe wa tayi ta hau cire kayan a ranta tana mita, sauya wani kayan tayi ta koma tayi kwanciyar ta ta hau charting da Ƙalby ɗin ta.
Da dare suna zaune gaba ɗaya a Parlour bayan sun gama cin abinci, Uncle yace da Rayyan "gobe kace zaka tafi ko?"
"Eh Uncle".
"To sai ku wuce da ɗiya ta tunda itama goben zata tafi".
"To Uncle". Ray yace hakan cike da murna a zuciyar sa
Ita kuwa RAUDHA tamkar ma bata ji me ake cewa ba, Game suke buga wa ita da Abubakar
Sai da Uncle ya Kira sunan ta yana cewa, "ɗiya ta gobe zaku wuce tare da Captain, zuwa gobe insha Allahu zan baki kuɗi ku fita da Abubakar ki siya duk abinda kike so ko?"
Murmushi tayi tace, "Uncle ni ba sai ma na siya komi ba".
"A'a kina nufin ki koma haka babu tsaraba?"
Ammee itama tace, "ai hakan ma bazai yiwu ba, nima zan ƙara miki da nawa, tunda naga ba kya son kayan ku na Hausawa, Ni dai su na siyo miki, da fatan dai zaki saka ko ɗiya ta?"
Murmushi RAUDHA tayi tace, "eh mana Ammee zan saka insha Allahu".
"To shikenan, zuwa gobe za'a amso daga ɗinki, duk na rigada na bayar an ɗin ka miki".
"Nagode Ammee sosai".
"Ɗiya ta babu godiya a tsakanin mu, ai mu mun ji daɗin hutun nan da kika yi mana".
Zannurain ya amshe zancen da faɗin, "da fatan dai zaki sake ziyartan mu? ba wai da kin tafi kin manta damu ba".
Dariya tayi tace, "Ni ai ba don ku zan zo ba, don Uncle da Ammee zan sake zuwa, tunda ku ko tsaraban ma babu wanda yace zai bani a cikin ku".
Gaba ɗaya suka yi dariya har Ray dake sauraron su yana latsa wayan sa
Faruk ne yace, "kar ki damu Lil Sister, mun miki tanadin tsaraba sai zuwa gobe kowa zai baki".
Murmushi tayi tace, "Thanks Yaya Faruk".
A haka dai hiran nasu ta kasance, inda daga baya kowa ya wuce ɗakin sa don kwanciya
RAUDHA na tsaka da saka kayan barcin ta, taji ana mata Nocking a bakin ƙofa, tsayar da abinda take yi tayi tana kallon ƙofan, sai kuma taƙarisa saka doguwar rigan da sauri, don a tunanin ta Ammee ne taje ta buɗe mata, saɓanin tunanin ta sai taga Faruk ne, waro idanu tayi a kansa tace, "Yaya Faruk kai ne?"
"Eh Ni ne Ƙanwa ta".
"To me kake buƙata?" Ta sake jeho masa tambayar
"Magana zamu yi Sister, amma na rasa hanyar da zan bi don sanar miki, yanzu kuma naga dacewar na faɗa miki tun yau tunda gobe zaki tafi".
Murmushi tayi tace, "kai Yaya Faruk, to shigo mana".
Ta matsa mishi a hanyar ya shiga, sannan ta mayar da ƙofan ta rufe.
Kan kujera ya zauna, itama ta zo ta zauna a gefen sa tace, "ina jin ka Yaya, wani magana ne zaka faɗa min har ka kasa sanar min sai a yanzu?"
Idanun sa a kanta yayi murmushi yace, "ba abu ne me sauƙi ba shiyasa na kasa sanar miki, sabida wlh kullum na tunkare ki da maganar sai inji nauyin faɗa, ina son ki RAUDHA! ina ƙaunar ki matuƙa".
Waro ido tayi tana bin sa da kallo, sai kuma tayi dariya tace, "Yaya Faruk kenan, Allah ka bani dariya.."
"Sabida ban cancanci na so ki ba ko?" Ya katse ta da faɗan haka yana me tsare ta da ido
Sosai taji wani iri a kallon da yake mata, idanun sa iri ɗaya dana Ray, shiyasa ko kaɗan ba ta son suna kallon ta. kau da kai tayi tana cewa, "yanzu dai mu bar zancen nan Bro, dare yayi ina jin barci". Ta ƙare maganar tana shirin tashi
Riƙe mata hannu yayi, hakan yasa ta dakata daga tafiyan da tayi ninya
"Please Sister, ki bani amsa ta don Allah, wlh ina ƙaunar ki, tun sanda muka zo gidan ku na kamu da soyayyar ki, na kasa sukuni gaba ɗaya sai yanzu da na samu na faɗa miki".
Numfashi taja kafin ta juyo tana kallon sa tace, "meyasaka kake son yaudaran kanka ne Faruk? Kar ka manta Na san alaƙar ka da Suhaima".
Cikin marairaice fuska yace, "Yanzu ke nake so ba ita ba, wlh ina matuƙar ƙaunar ki, ƙaunar da ban taɓa wa Suhaima ba, kin ga kuwa ke Yakamata in aura ba ita ba".
"Kar ka ja maganar da tsaho, bazan so ka ba Yaya Faruk, ina da wanda nake ƙauna a halin yanzu".
Zai yi magana ta katse sa da faɗin, "Please ka fita min a ɗaki ina jin barci". Ta ƙare maganar tana janye hannun ta tabar wajen
Shiru yayi yana bin ta da kallo, sai kuma ya tashi ya nufi ƙofa, har ya buɗe zai fita kuma yaja ya tsaya, kallon ta yayi yace, "Bazan haƙura dake ba RAUDHA, zan bi duk ta hanyar da ya dace don mallakar ki".
Juya wa yayi ya fice batare da ya jira jin ta bakin ta ba, wanda itama bata yi ninyan maganar ba.
Da fitan sa suka ci karo da Ray da ya fito daga Parlour ɗauko ruwa a gora, mamaki ne ya kama Ray ganin inda ya fito, take wani irin faɗuwar gaba ya riske shi, cikin sauri yace da shi, "Kai daga ina ka fito?"
Shafa kansa Faruk yayi yana sunkuyar da kai
"Ba da kai nake magana ba? Daga ina ka fito? Yayi maganar cikin kakkausar murya cike da fushi
Sosai Faruk ya tsora ta da ganin yanayin nasa, cikin sauri yace, "Brother daga wajen RAUDHA na fito, lafiya?"
Mari ya wanke shi dashi, ya saka hannu ya finciki wuyan rigan sa, cikin tsananin fushi da har idanun sa sun kaɗa yace, "me kaje yi ciki? Me kuka yi?"
Mamaki sosai ya kama Faruk da abinda Yayan nasa yayi masa, wanda be taɓa tunanin haka a gare sa ba, idanun sa kawai yake kallo yana mamakin tsantsan kishin da ya hango a tattare dashi. Cikin sanyin murya yace, "babu kom.."
Be bari ya ƙarisa ba ya daka masa tsawan "ya bar gaban sa"
Da sauri Faruk ya wuce yayi hanyar ɗakin sa, yana me sake mamakin yayan nasa, "kar dai ace shima son ta yake yi?"
Ray kuwa na tsaye a wurin zuciyar sa na tafarfasa, sosai yake jin ƙuna a ransa, sabida abinda zuciyar sa ke raya masa, riƙe kansa dake sara masa yayi, sai kuma ya juya ya nufi ɗakin RAUDHA
Har ta kwanta taji an hankaɗo mata ƙofa, da sauri ta ɗago kai tana kallon Ray da ya nufo inda take, idanu kawai ta zuba masa tana kallon sa tamkar zaki
Gaban ta ya ja ya tsaya yana bin ta da kallo cike da tsantsan fushin da ya nuna a fuskar sa, cikin kaushin murya yace, "keee uban me ya shigo da Faruk cikin ɗakin nan?"
Mamaki maganar nasa ya bata, sai ta miƙe zaune don ta kalle sa da kyau, cikin taɓe baki tace, "kai kuma asuwa da zaka tambaye Ni abinda ya kawo sa?"
Sosai ransa ya sake ɓaci da maganar ta, cikin tsawa yace, "wato kina nan kina halin ki ko? Ke daƙiƙiyar ina ce da baza ki taɓa sauya wa ba? Wato iskancin naki ya tashi kan wasu ya koma kan ƙani na, ƙani na kike bi?"
Sosai RAUDHA tayi mutuwar zaune da jin zantukan sa, sai kawai tabi sa da ido domin ta kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi bare ta furta wani kalma, duk da kuwa laɓɓan ta sai motsi suke yi, sai dai baƙin cikin zantukan sa yasa ta kasa furta komi, kafe sa tayi da idanun ta ko ƙyafta su ba ta yi
Zai sake yin magana, sai yaji muryan Ammee daga bayan sa tana faɗin, "wai me ke faruwa ne? Menene haka Rayyan lafiyan ka ƙalau kuwa?"
Juyo wa yayi yana kallon ta da jajayen idanuwan sa, be ce komi ba kuma ya raɓa ta yabar ɗakin
Mamaki sosai ya kama Ammee da yanayin da ta gan sa, tabi shi da kallo tana aiyana abubuwa da dama a ranta, sai kuma ta juya ga RAUDHA dake zaune har yanzu ta kasa motsa wa, idanun ta na kafe a inda Ray ya bar wurin. muryan Ammee ya dawo da ita hayyacin ta, sai ta lumshe idanun ta hawaye na cika mata idanu
"Ɗiya ta wai lafiya? Menene ke faruwa? Me Rayyan ɗin ya zo yi wajen ki?"
Matse bakin ta tayi tana buɗe idanuwan ta da suka cika taf da hawaye, cikin rawan murya kamar zata yi kuka tace, "Ammee nima ban sani ba?"
"Baki sani ba kuma?" Ta sake tambayar ta da mamaki
Gyaɗa mata kai tayi don baza ta iya magana ba
Shiru Ammee tayi tana Kallon ta, sai kuma tace, "to meyasa zaki yi kuka Ɗiya ta? Wani abun ya faɗa miki ki sanar dani don Allah?"
Still sake girgiza mata kai tayi alamun babu komi
"Shikenan.. kwanta kiyi barci, zamu yi maganar dashi gobe".
RAUDHA ba dai tace mata komi ba, ta kwanta tana rufe idanun ta
Itama Ammee juya wa tayi tabar ɗakin tana me rufo mata ƙofa.
Ammee na fita RAUDHA ta buɗe idanunta, sai ga hawaye shaaa sun soma zubo mata
"Ni yake nufin ƴar iska?" Tayi maganar a fili cike da ƙunan zuciya
Duk da ada ya faɗa mata waɗannan kalaman masu ɗaci, amma bata taɓa jin ɗaci da raɗaɗin su a zuciya ba sama dana yanzu, sabida a baya ko kaɗan bata san ciwon su ba, bata san zafin kalman iskanci ba, bata san ma meye ma'anar su ba, da ciwon da yake saka wa duk wanda aka kira sa dashi, alhanin kuma shi ba ya aikata wa
Hawayen ta kawai take share wa tana sake jin tsanan Ray a zuciyar ta, sosai tayi kwanan ƙunci a wannan ranan, don daƙyar barci ya ɗauke ta.
*WASHE GARI*
Zuwa la'asar sun gama shirin su, har airport su Zannurain suka rako su, inda jirgin su ya ɗaga.
RAUDHA dai ta tafi cike da kewar ahalin gidan, sosai tayi shaƙuwa da su wanda bata taɓa yin makamancin sa ba a ƙanƙanin lokaci, tana zaune ne a gaban kujeran Ray, don wajen zaman su ma ba ɗaya bane, ta kwantar da kanta ta rufe idanu tana faman tunani a ranta.
A airport ɗin Kaduna suka sauka, time ɗin ƙarfe 08:02pm. Ne na dare
Suna fito wa Ray yace mata, "ta biyo shi su shiga mota".
Kasancewar an zo ɗaukar sa
Bata ce masa komi ba, taja Trolly ɗin ta tayi hanyar barin wajen
Ganin haka ya nufo ta da sauri ya sha gaban ta yana cewa, "ina zaki je kuma? Kin san dare yayi be kamata ki bi hanyar Zaria yanzu ba, tunda kin san doka ce ƙarfe 04:00pm ake rufe hanya, mu je gida na ki kwana, in yaso gobe a kai ki gida".
Wani kallo ta sakar masa, cike da tsantsan takaici da haushin sa da ta kwana dashi tace, "Ka sani bazan taɓa neman taimako a gare ka ba, ko meye zai same Ni a hanyar nan, na gummaci na bi ta akan dai na je inda kake, Never".
Ta juya taci gaba da tafiyar ta
Sakato yayi kawai yana bin ta da kallo har ta ɓace wa ganin sa.
[4/7, 9:37 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR:* ✍️
_Nafisat Ismail Lawal Goma._
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*RAMADHAN MUBARAKH*🤲🏽🕌
2021.
*TUNATARWA*
_Manzon Allah ya ce mana, "tsabta kam ita ce rabin imani kuma ita ce mabuɗin Sallah. Abu na farko da ake buƙata kafin a shiga sallah shi ne tsarki, tsabta ta zuciya da jiki, ta tufafi da kuma wurin yin sallar._
_Sallah ibada ce ta ruhu, kuma a cikin ta ne Bawa yake ganawa da Ubangijin sa, yake tsayawa a natse a gaban sa yana yabo yana godiya, yana roƙon Allah ya shiryar da shi bisa ga tafarki madaidaici. Saboda haka bai kamata Bawa ya shiga wannan ganawa ba sai bayan ya shirya kansa da kyau, ya tsarkake jikin sa da tufar sa da wurin sallar sa. Zai yi alwala in ƙaramin tsarki ya kama shi; in kuwa babban tsarki ne sai ya yi wanka don kuwa ta haka ne zai haɗa tsarkin jiki da na zuciya a lokacin ganawar sa da Ubangiji._
_Allah yasa mu dace._
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON FORTY EIGHT*
_______📖 Tafiya miƙaƙƙa RAUDHA tayi, but bata sami abin hawa ba, duk da kuwa ga taxi nan suna ta yawo, da zaran tace musu "Zaria" sai su ce "baza su ba, an rigada an rufe hanya, ko sun je sojoji za su iya kama su, idan ma basu kama su ba, ƴan kidnapped za su iya ram da su, yanzu duniyar abun tsoro ne, an dena tafiyan dare"
Memakon ta saduda sai taci gaba da tafiyan ta a titi, batare da ko tsoro ba, duk da kuwa hanyan ba wai babu ababen hawa bane, tamkar ma rana alokacin
Tana cikin tafiyan ne, motan da aka ɗauko Ray ta faka a gaban ta, taja ta tsaya don bata shaida motan ba, tana ganin ya fito ta ɗaure fuska tana me kawar da kai, har ta soma tafiya ya dakatar da ita ta hanyar shan gaban ta
Wayan sa ya miƙa mata fuskar shi shima babu walwala yace, "gashi Daddy Yana son magana dake".
Kallon sa tayi still fuskarta a matuƙar ɗaure, tamkar ta share sai kuma ta amsa ganin ya sake ce mata "ta amsa"
Hannu tasa ta amshi wayan ta kara a kunne, cikin raunin murya tana shirin kuka tace, "Daddy".
"My daughter meyasaka baza ki bi shi ki kwana a wajen sa ba? In yaso gobe ki dawo gida. kin san hanya babu kyau, yanzu kidnappers sun yi yawa, kuma kin san halin su yanzu sai su ɗauke ki".
Silalo wa hawayen ta suka yi, cikin shashsheƙan kuka tace, "Daddy bazan iya bin sa ba, zan je hotel na kwana".
"Hotel kuma Baby? please ki bi shi kinji, nasan Baby na yanzu ba ta min gardama tana jin magana ta, just ki bi shi, ba na son ki kwana a hotel sabida ɓata gari sun yi yawa, kina da mutuncin ki baza ki kwana a hotel ba, promise Zaki bi shi?"
Gyaɗa kanta tayi tana ci gaba da hawaye, sai kuma ta buɗe baki tace, "Zan bi shi".
"Yauwa good girl, Allah ya miki albarka uhm? Ki kula da kan ki, i love You".
"Me too Daddy".
Ray dake tsaye a gaban ta, kallon ta kawai yake yi yana sauraron abunda take faɗa, sai dai ba ya jin me Daddy ke cewa, tuni ya faɗa kogin tunani wanda har be san sanda ta ida wayan ba, sai jin dogon tsakin da taja yayi. Waro idanu yayi yana kallon ta cikin ido, kasancewar itama ta kafa masa nata idanun tana mishi kallon tsana, wayan da take miƙa masa yabi da kallo, dai-dai da ta sakar mishi wayan zai faɗi, yayi saurin tare wa yana me bin ta da kallo da har ta wuce zuwa motan. Numfashi yaja batare da yace komi ba yabi bayan ta
Baya ta shiga ta zauna
Shi kuma ya shiga gaba kamar yanda yayi ɗazu, Drever'n yaja motan suka yi gaba, har suka kai babu wanda yayi ƙwaƙƙwaran motsi
Cikin Barrack ɗin sojoji gidan nasa yake, yawanci ginin gidajen duk iri ɗaya ne, gidan sa shi ne number 7.
Drever'n yana parking Ray ya fito, RAUDHA kuwa bata fito ba sai da taga yayi gaba sannan ta fito tare da Trolly ɗin ta, Drever'n ya amsa ya haɗa dana Ray yabi bayan sa, itama sai ta taka tabi bayan su
Tana shiga parlour'n ta tsaya tana me ƙare wa ko ina kallo, ba wani karikitai bane me yawa a Parlour'n, daga kujeru sai Fridge da kayan kallo, sai wasu Flowers guda biyu da akayi ado dasu a gaban t.v'n, sai kuma hoton shi guda biyu manne a bango, ɗaya da kakin sojojin sa yayi matuƙar kyau, tamkar ka ɗauke sa ka saka a aljihu, ita kanta ya burge ta matuƙa, har ta ƙi ɗauke kai a hoton sai da ta gama ƙare masa kallo, sai kuma ɗayan yana duƙe tamkar yayi ruku'u yana dariya, farar riga ce a jikin sa sai wandon soja...
Maganar Ray ɗin ne ya dawo da ita daga tunanin da ta afka wajen ƙare wa hotunan kallo, sai ta zubo masa idanu cike da jin haushin kanta da ta tsaya tana kallon sa a hoto, don ta nuna masa ba burge ta yayi ba, sai ta taɓe baki ta furta, "ko kyau! Sai mugun hali".
Ray ya ji ta sarai, sai yayi murmushi kawai yana yin gaba zai shige ɗaya daga cikin ƙofofin biyu da suke jere, sai da ya kusa shige wa sannan yace da ita, "ta shiga ɗaya ɗakin"
Taka wa tayi ta buɗe ƙofan ta shiga tare da Trolly ɗin ta da ta ɗauka a Parlour, babban ɗaki ne me Toilet a ciki, gado ne kawai da sip, sai lallausan carpet ɗin ƙasa, baya ga haka babu komi ciki. Kan gadon ta nufa ta zauna tana me zare veil ɗin da tayi rolling da shi a kanta, babu abinda take yi sai faman taɓe baki tana bin ko ina da kallo, tare da karkaɗa ƙafafun ta dake lilo ƙasan gadon
Kamar shuɗewar mintuna goma sai ta miƙe ta shiga Toilet, wanka ta soma yi ta ɗauro alwala, ta saka riga da wando masu taushi na barci, sannan ta ɗaura Robber White Hijab tayi Sallah, bayan ta idar ta koma kan gadon ta kwanta tana me zame hijabin daga jikin ta. Shiru tayi tana tunani a ranta, sosai take jin yunwa a wannan gaɓar, amma kuma ba shi ne damuwar ta ba, illa kewar Ƙalby ɗin ta da ya addabi jiki da ruhin ta, yau kwata-kwata ba su yi waya ba, tunda tun jiya rabon ta da shi, ga shi ko text be tura mata ba, ta hau social media Nan ma bata ga saƙon sa ba, duk da kuwa ta ga ya hau, kuma ta tura masa saƙo be buɗe ba, ta rasa meyasa yau yaƙi kula ta, har kiran sa tayi ya ƙi ɗauka, daga ƙarshe ma sai ya kashe wayan, ko kaɗan bata san laifin da tayi masa ba, duk da kuwa tana ji a jikin ta fushi yake yi da ita..
Ajiyan zuciya ta sauke, kana ta janyo wayan nata ta sake kiran sa, wannan karon ya shiga, sai dai har ta gama ring be ɗaga ba, sake kira tayi, anan ne yayi peacking
Wani sassanyan ajiyan zuciya ta sauke har tana lumshe idanu, sai ta kara a kunne kawai ta sakar masa kuka
Shiru Ray yayi a ɓangaren sa, yana me sauraron kukan nata dake shiga masa can cikin kunne, yana saukar masa da kasala, lumshe idanu yayi batare da yayi ƙoƙarin dakatar da ita ba, domin kuwa sosai sautin kukan nata yake masa daɗi
Ganin yayi banza da ita, sai ta ƙara Volume ɗin kukan nata, har da buga ƙafafu
Dariya ne ya so kufce masa, domin kuwa yana jiyo buga ƙafan da take yi akan gadon, danne dariyan sa yayi yace, "Sweetheart mene ne?"
Cikin kukan take cewa, "ba kai ne ba!"
"To me nayi uhm? Faɗa min inji?"
"Ka ƙi kula Ni yau gaba ɗaya, kuma yanzu na kira ka, but kana son share Ni har kaƙi rarrashi na".
Murmushi me sauti yayi, cike da farin ciki a zuciyar sa yace, "I'm so sorry pretty uhm? Ki yafe wa Ƙalby bazai sake ba".
"To sai ka faɗa min abinda nayi maka yau kaƙi kula Ni". Tayi maganar cikin shagwaɓa
Lumshe idanuwan sa yayi, cikin sanyi yace, "Babe zaki kashe Ni da wannan shagwaɓar taki".
Daɗi taji a zuciya, sai ta sake ɓare baki ta hau masa shagwaɓa
"Pretty idan na kama ki ko!" Sai ya cije bakin sa yana me jan numfashi sosai
Ita kuwa dariya ta ƙyalƙyale masa dashi tace, "to ka sanar dani meyasa ka ƙi kula Ni yau?".
"Ina fushi dake ne sabida kin min laifi".
Waro ido tayi, sai kuma ta marairaice fuska kamar zata yi kuka tace, "to me nayi maka?"
"Kin yi min alƙawarin Ni kaɗai zaki so, Ni kaɗai zaki kula a matsayin wanda zaki aura, amma kuma kina kula wasu".
Sosai wannan karon ta waro idanun ta waje, cikin mamakin sa tace, "ban gane ba Ƙalby, ya akayi kasan cewa ina kula wani?"
"Ok da gasken kenan kina kula su?" Yayi maganar cike da kishin da dole sai ka gane ran sa babu daɗi
Tayi saurin cewa, "no Ƙalby, na rigada nayi maka alƙawarin kai kaɗai zan so, kuma kai zan aura, har yanzu kuma ban karya alƙawarin ba, har yanzu kai ne kaɗai wanda nake kallo a matsayin miji na uban ƴaƴa na, kai kaɗai ne a zuciya ta, domin tuni narigada na baka kyautar ta,".
Sosai Ray yaji daɗin zantukan ta, har yana jin wani irin sanyi sosai wanda tun jiya be ji irin sa ba, gyara zaman sa yayi daga kan kujeran da yake zaune, sannan yace, "Allah ko Baby na Ni kaɗai?"
Murmushi tayi tace, "kana tantama ne?"
"A'a na yarda dake ɗari bisa ɗari, I love You My pretty".
"Me too dear, amma yaushe zamu ga juna, na ƙosa wlh". Tayi maganar cikin shagwaɓa
"Pretty kenan! To ki saka mana rana".
"Da gaske Ƙalby? Tafaɗa da farin ciki
"Da gaske Baby na, ai nima na ƙosa mu riƙa soyayyar fili ba na waya ba".
"To shikenan, ka bari zuwa bayan bikin Besty na sai mu haɗu, sabida daga yau har Sunday ba na da time".
Yace, "amma kiyi min alƙawari duk rintsi duk wuya baza ki taɓa rabuwa dani ba, Ina jin tsoro Pretty, Ina jin tsoron idan kin ganni ki ce ba kya so na, baza ki aure Ni ba, idan kuwa haka ta faru mutuwa zan yi".
"Ƙalby wlh nayi maka alƙawari, duk rintsi duk wuya ina ƙaunar ka, bazan taɓa rabuwa da kai ba, nayi maka alƙawari zan aure ka".
Murmushi yayi me sauti yace, "Nagode Baby na, Allah ya bar min ke".
"Ameen ameen Ƙalby". Itama tafaɗa tana dariya
Daga nan sun taɓa hira kaɗan kafin suka yi sallama, ajiye wayan tayi tana lumshe idanu tare da faɗa wa duniyar kogin tunanin Ƙalby ɗin ta, murmushi kawai take zuba wa idanun ta a rufe
Numfashi taja kafin ta buɗe idanun tana ɗaura hannayen ta kan shafaffen cikin ta, sosai take jin yunwa don haka dole ta nemi abinci taci, tsaki taja tana tashi zaune tace, "bari inje wajen wancan mahaukacin sojan nace ya bani abinci, wlh yunwa nake ji bazan iya kwana a haka ba, dole ne ma yasan yanda zai yi dani..."
Bata ƙare maganar ba taji saukar muryan sa yana faɗan, "wato Ni ne mahaukaci ko?" Yayi maganar yana tsaye bakin ƙofa riƙe da handle ɗin, idanun sa a kanta
Waro ido tayi tana ɗan ja baya, mamaki ne ya kamata don bata ji motsin sa ba ko kaɗan har ta miƙe tana shirin fita
"Ki bar zaro min idanu ki amsa min tambaya na, Ni ne mahaukacin ko?"
Ɗaure fuska tayi tana me kawar da kanta, tare da kumbura baki, sai kuma ta taɓe shi tana me ɗage kafaɗa tace, "kafi kowa sani ai".
Murmushi Ray ya saki yana me takowa cikin ɗakin sosai, ledan da ke hannun sa ya miƙo mata yana me faɗin, "zan ko nuna miki Ni mahaukacin gaske ne, na kula sabida ban ɗaukar mataki a kanki kike yi min duk abinda kika ga dama, komi dake bakin ki kina faɗa min batare da kin ji tsoro na ba, kin manta Ni Yayan ki ne, zan iya miki hukunci a duk sanda naga dama".
Dogon tsaki taja cike da haushin maganar sa ta kalle sa tace, "waye kai? Ban san ka ba, kuma baka isa ka zama yaya na ba, idan ka isa kai kai ne, ka ɗauki mataki a kaina sannan zan tabbatar, ko kaɗan ba na jin tsoron ka domin kuwa baka kai matsayin ba, baka isa RAUDHA ta saka ka a cikin lissafin ta ba.."
Bata san sanda ya iso gare ta ba, sai ji kawai tayi ya murɗe mata baki, yana faɗin, "I will teach you a lesson now".
Be bata damar ma magana ba ya saki ledan hannun sa ya janyo ta jikin sa, sai kawai ji tayi ya haɗe bakin su waje ɗaya
Wani irin zaro ido tayi waje, babu shiri ta haɗiye yawu cike da tsantsan tsoro da mamakin sa.
[4/7, 11:42 PM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR:* ✍️
_Nafisat Ismail Lawal Goma._
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*RAMADHAN MUBARAKH*🤲🏽🕌
2021.
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON FORTY NINE*
_______📖 Sosai Ray yake tsotson bakin ta tamkar ya samu Lolipop, ko kaɗan yaƙi bata damar da zata iya ƙwatan kanta, duk da kuwa kici-kicin da take yi domin gujewa abinda yake mata
Sosai ta gaji dole ta ƙyale shi ta dena ƙoƙarin ƙwace kanta, sai kawai ta soma zubar da hawaye tana sauraron saƙon da yake bata, rufe ido kawai tayi zuciyar ta na ƙara cinkushe wa da tsanar sa
Ray sai da yaga ya kusa losing control ɗin sa, kafin yayi ƙarfin halin sakar mata bakin ta yana me ja baya a hankali cike da kasala
Kallon ta kawai yake yi yanda ta tsaya tana ta kwararan hawaye idanun ta arufe
"Daga yau ki sake yi min rashin kunya, tara ki nake yi dama, kuma duk zan fanshe, idan hakan ta sake faruwa a tsakanin mu, to ba iya nan zan tsaya ba, don dai Ni ina da tsoron Allah ne ba irin ki ba".
Juya wa yayi ya wuce ƙofa zai fice
A lokacin ne ta buɗe jajayen idanuwan ta tana kallon sa, cikin ƙunan zuciya tace, "har abada bazan taɓa yafe maka ba, na matuƙar tsanar ka fiye da mutuwa ta, komi da komi dake tare da kai ba na ƙaunar sa, MAHAUKACI KAWAI". Taƙare maganar cikin ɗaga murya, don ba kaɗan ba kalaman sa suka yi mata ciwo
Be ce mata komi ba, illa murmusawa da yayi ya buɗe ƙofan yana shirin fita
Hakan sai ya ƙara mata zafi a zuciya, domin so take yi ta ƙuntata masa kafin ya bar ɗakin, cikin tsanar sa tace, "Mutanen kirki ba sa nuna kansu, sai dai ayyukan su su bayyana su, kai ko kaɗan ba ka a cikin su, domin ayyukan ka tuni sun bayyana min kai tantirin ɗan iska ne, masu fake wa a cikin mutanen kirki, alhanin irin ku su ne ɓatattu".
Sosai kausasan kalaman ta suka taɓa sa, juyo wa yayi yana kallon ta ido cikin ido, sun ɗau two minutes suna aika wa junan su kallo, kafin ya tako ahankali zuwa wajen ta, har yanzu kuma idanun su na a cikin juna, sai da ya tsaya gaban ta kafin yace, "kina bani mamaki RAUDHA, idan kina yin wani abu sai in ga tamkar baki da wayau, koda yake har yanzu ke yarinya ce, amma kuma ina me miki nasiha ki zama na gari a duk inda kike, har yanzu da sauran ki a cikin rayuwar nan, abu ɗaya yake hana Ni faɗa miki kalaman da zaki dauwama kina me dana-sani, dana-sanin rayuwar ki, amma kuma.."
Sai yayi murmushi yana fito da harshen sa waje, ya karkaɗa sa yana cewa, "amsa ɗaya nake so ki bani, ɗaya tak. Da Ni da ke ina son sanin waye ɗan iska?".
Sai yayi dariya yace, "ba ma sai kin bani amsa ba shalele na, Ni ai ƙaramin ƙwaro ne a iskancin domin ban san komi ba, ke kuwa da, Kin dauwama ne a cikin ta tun kina ƙaramar ki, ga shi har yanzu kin kasa gane Allah ya faku bare ki tuba, ko ba ke ce na kama ki jiyan nan da ƙani na kuna abinda kika saba ba? To ki soma gyara kanki kafin ki ce zaki zagi wani".
Juya wa kawai yayi ya bar ɗakin batare da ya jira cewar ta ba, yana fita ya zauna kan sofa a parlour, yana me ɗaura kansa jikin kujeran tare da lusmshe idanu
Allah ya sani shi kansa ya san yaji baƙin cikin kalaman nan da ya faɗa mata, amma ya zai yi? Yana son ne ya saka mata zafi a zuciya, ta yanda zata gyara halayen ta, domin idan taji raɗaɗin maganar sa wataƙil ta iya gyara wa, amma kuma yaga da alamu yana son ɓata rawan sa da tsalle, ko in CE ma tuni ya ɓata, kullum daɗa ƙara tsanar sa a zuciyar ta yake yi, shin ya zai kasance idan har ta gane shine masoyin ta taƙi shi? Yasan babu ta yanda za'a yi RAUDHA ta so shi, amma ya zai yi? Wani hanya zai bi don cire tsanar sa dake zuciyar ta, ya rasa ya zai yi, duk da kuwa sosai yake danne duk wani ɓacin rai da take ƙunsa masa, ya kasa ɗaukar mataki, idan da ace babu soyayyar ta a ransa, da tuni ya aikata mata abinda baza ta taɓa manta sa a rayuwar ta ba.
🔵🔵🔵
Tun sanda ya soma maganar sa hawayen fuskar ta suka ci gaba da tsiyaya kamar an kunna famfo, yana fita ta fashe da kuka tana zame wa ƙasa anan, haɗa kai da gwiwa tayi ta soma rusa kuka cike da baƙin ciki a zuciyar ta, "shin me tayi wa bawan allan nan ne ya tsane ta? Meye alaƙar ta dashi ne da yake shiga rayuwar ta?" Babu abinda ke ƙona mata rai sai kallon ƴar iska da yake mata, kalman iskanci da yake jifan ta dashi, shi yafi komi ƙona mata rai
Ɗago kai tayi da fuskar ta yayi caɓe-caɓe da hawaye, cikin kuka tace, "I hate you RAYYAN! I hate you so much!"
Ta sake fashe wa da wani sabon kuka, ta jima a wajen a zaune tana ta faman kuka taƙi ta dena, dama RAUDHA ga taurin kai da naci. Ahaka ta kwana a zaune bata ko jirga ba, duk da uwar yunwar dake addabar ta, amma ta gummaci ta kwana a haka, da dai taci abinda ya kawo mata
Da asuba ta farka daga figaggen barcin da ya ɗauke ta, daƙyar ta iya ɗago kanta da ya riƙe yayi mata zafi, idanuwan ta kuwa sun yi luhu-luhu alamun tasha kuka da kuma rashin barci, gaba ɗaya fuskar ta yayi jazur tamkar tattasai
Miƙe wa tsaye tayi daƙyar, ƙafafuwan ta sun rigada sun yi tsami, dole ta kasa taka wa, ta daɗe tana yarfe ƙafafun kafin ta samu su yi mata dama-dama, ahankali ta taka ta wuce Toilet ta ɗauro alwala, sallah tayi da Hijab, sannan ta miƙe ta ɗauki veil ɗin ta da ta cire ta mayar
Baza ta iya sake yin wasu mintoci a gidan nan ba, ko kaɗan ta tsani komi da zai fito daga Ray, ba don jiya dare yayi ba, da adaren jiyan zata bar gidan, sai kuma ta yanke shawaran da asubahin nan zata bar masa gida
Tana gama rataya veil ɗin taja Trolly ɗin ta tafito Parlour, ƙofa tayi ta buɗe ta fice, dayake ya fita zuwa Masallaci kuma be dawo ba, har tabar haraban gidajen bata haɗu da kowa ba, tafiya sosai miƙaƙƙiya tayi har tafito bakin titi, zuwa lokacin daƙyar take iya ɗaga ƙafafun ta, amma haka ta daure take ta jan su har ta fice bakin titi, a lokacin gari ya fara haske sosai har ababen hawa sun soma wuce wa, nan ta tare keke napep tace "ya kai ta Kawo tasha ta hau mota"
Suna zuwa ta samu taxi ta shige, ita ce ta farko, amma dayake ta ƙosa ta bar wajen, kar ma ya biyo bayan ta, tace ma me motan "su tafi zata biya sa kuɗin" haka yaja suka bar tashan suka yo hanyar Zaria.
🔵🔵🔵
Sanda Ray ya tashi duba ta wajen ƙarfe 08:40am ne, koda yaga ba ta cikin ɗakin hankalin sa yayi matuƙar tashi, tunda yaga babu Trolly ɗin ta ya san tafiya tayi, nan ya biyo hanya ko zai ganta, amma Allah be sa ya ganta ba, dole ya ɗauki waya ya soma kiran ta, sai dai alokacin RAUDHA na cikin mota tana kallon wayan taƙi ɗauka, gaba ɗaya ba ta jin daɗin jikin ta, ga barci dake damun ta shiyasa taƙi ɗauka
Sai da taga ya ƙi ya dena kiran, kafin tayi peacking tana ƙara wa a kunne
Sallama yayi mata. Ta amsa shi cikin dashashshiyar muryan ta da ya ƙara shige wa sosai sabida kukan da tasha
"My Pretty lafiya dai naji muryan ki ba ta fita, ina fata dai lafiya ba wani abu ne ya same ki ba?"
Sai da taja majina tana jingina bayan ta da jikin kujeran kafin tace, "lafiya".
"Anya? ban yarda ba, but naji kamar ƙaran ababen hawa, ina zaki haka da sassafen nan?"
"Ƙalby gida zan je, kasan dama nace maka ina Kaduna ne".
"Ok yanzu har kin hau mota ne, ko kuma Yayan naki zai kai ki?"
Gajeren tsaki taja tace, "wa yace maka yaya na ne shi? Allah ya kiyaye".
Dariya ne ya so ƙwace masa, sai dai ya daure yayi murmushi yana cewa, "amma ai a matsayin Yayan ki yake, ko ba komi ma ya girme ki".
"Ƙalby ka dena min maganar mutumin nan, idan ba so kake yi mu ɓata ba, raina a ɓace yake wlh".
"I'm so sorry Pretty, Allah yasa dai ba shi ne ya ɓata miki rai ba?"
Cike da jin haushi tace, "shi ne mana, dama idan ba shi ne ba, waye ya isa ya ɓata min? wlh Ƙalby na matuƙar tsanar sa fiye da komi dake duniyar nan, da za'a bani bindiga wlh sai na harbe shi, babu wanda ya taɓa shiga rayuwa ta ya muzguna min irin sa, a kansa na soma kwana da baƙin ciki, kuma na tashi da shi, a kan shi nake zubar da hawaye a koda yaushe, bazan taɓa yafe masa ba".
Sosai jikin Ray yayi sanyi ƙalau, muryan sa a sanyaye yace, "Why kika tsani bawan Allan nan haka? Ni naga tamkar gyara yake miki, mene ne aibun shi a ciki?".
Lumshe ido tayi batare da tace komi ba
Sai da ya kira sunan ta sannan tace, "idan har kana so mu ci gaba da rayuwa a haka, kar ka sake min maganar sa, idan kuma ba haka ba". Sai tayi shiru kawai batare da ta ƙarisa ba
Murmushi yayi me ciwo yace, "wato nima zaki tsane Ni Ko? Ke kenan babu wanda ya isa ya faɗa miki Gaskiya? Pretty ki bi duniyar nan a sannu, komi kika gani a.."
Ƙit tayi cancel ɗin kiran, sannan ta kashe wayan gaba ɗaya tana me ajiye wa saman cinyan ta, rufe idanuwan ta tayi. Bata sake motsi ba har sanda Drever'n ya sanar mata sun iso Zaria, sai anan ta buɗe ido ta faɗa masa inda zai kai ta.
A bakin tanƙamemen gate ɗin gidan su ya faka, tayi masa maganar yayi horn
Horn ɗin yayi kamar yanda ta umarce shi
Me gadi ne ya leƙo, ganin taxi sai ya fito ya taho, har zai fara faɗan sa kamar yanda ya saba sai ya hangi RAUDHA dake zaune a baya, nan ya washe baki ya soma kwarara mata gaisuwa tare da maraba
Ɗaga masa kai kawai tayi, sannan tace masa, "ya buɗe musu ƙofa"
Da saurin sa kuwa ya koma ya buɗe, me Taxi yaja suka yi ciki
Dayake da tafiya sosai, shiyasa taƙi sauka tun daga wajen, har bakin ƙofan parlour'n gidan ya kai ta ya ajiye, sannan tafito ta miƙa masa 5k da ta zaro
Masu aiki biyu maza da suka hango ta, su suka ƙaraso suka yi mata sannu da zuwa, sannan ɗaya yaja mata Trolly ɗin ta suka yi ciki.
A lokacin babu Daddy a gidan ya fita, tunda ta tambaya akace mata ba ya nan, sai ta wuce ɗakin ta , wanka ta soma yi ta hau yin breakfast da tasaka aka shirya mata, sai da taji ta ta ƙoshi sosai sannan ta zauna tana me jingina da kujeran ta lumshe idanun ta, bata sake motsa wa ba har wajen shuɗewar mintuna 20, lokacin sosai idanun ta suka rufe da barci, kan gado ta faɗa ta hau sheƙawa.
Time ɗin da Daddy ya dawo, sannan tana barci, shiyasa be tashe ta ba har sanda ta farka don kanta, anan ne suka gaisa har yake tsokanar ta "ya ga ta sauya ne, duk tayi yaushi, ko dai tafiyan ne ya sata haka?"
Dariya tayi tace, "Daddy kenan, ai ba yau na saba tafiyan ba, kawai zaman mota ne daga Kaduna zuwa nan ya gajiyar dani".
Shafa kanta yayi yana murmushi yace, "Daughter kin ganki ko? Akwai ragwanta wani lokacin, amma Captain ɗin ya kawo ki, ko saka wa yayi a kawo ki?"
Tana jin sunan sa ta sauya fuska tana ƙara lafe wa ajikin sa, kamar bata so tayi maganar tace, "Ya saka an kawo Ni ne".
Domin tasan idan tace motan haya ta hau, ya dinga maganar kenan, ita kuma ta tsani duk wani magana da ta shafe sa a yanzu
Saurin ma sauya hiran tayi da maganar bikin Ramcy, haka suka ci gaba da hiran su, inda Daddy yake shawaran abinda Ya kamata yayi wa Ramcy ɗin a bikin
RAUDHA kuma ta bashi shawaran yayi mata kayan ɗaki
Yace, "ok babu damuwa, yanzu kuma zan buga waya a samo mata masu kyau koda a nan Nigeria ne, tunda naga yanzu su ma suna yin kaya masu kyau, zan kira mahaifin ta, idan za su yi mata sai su fasa su yi wani hidiman da kuɗin".
"Yauwa Daddy, Amma Daddy a ƙoƙarta idan na waje zai samu ayi mata, ka ga yanzu ana fita Abroad sosai ba kamar watannin baya ba".
"To my dear duk yanda kika ce ai, insha Allahu za'a samu ma kafin bikin"
Daga haka hiran suka ci gaba da yi, inda RAUDHA take ta mishi lissafin abubuwan da zasu kashe daga ita har Ramcy ɗin na hidiman biki, yace, "zai bata kuɗin".
[4/9, 8:37 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR:* ✍️
_Nafisat Ismail Lawal Goma._
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*RAMADHAN MUBARAKH*🤲🏽🕌
2021.
*HADHISI*
_An karbo dga Aisha Allah yqara yarda agareta tace " Manzon Allah s.a.w ya aureta tana da shekara shidda,kuma yatare da ita tana da shekara Tara,kuma Allah ya karbi ransa tana er shekara sha takwas.
Muslim ya ruwaito_
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON FIFTY*
_______📖 Washe gari RAUDHA ta haɗa Trollyn kayan ta ta wuce gidan su Ramcy, a ranan ma suka koma gidan RAUDHAN, ita da Ramcy da wasu tsirarun ƙawayen ta calss mate ɗin ta da suka zo mata biki, acan za su zauna ayi mata gyaran jiki da RAUDHA zata ɗau nauyi, da duk wasu shirye-shirye da ya kamata su yi
Duk a ranan ne dai me gyaran jikin ta iso aka soma wa Ramcy gyaran jiki, su kuma su RAUDHA da sauran ƙawayen su ne masu fita suyo abubuwan buƙata, duk a motan RAUDHA ake fita, duk da su ma ƴan matan ƴaƴan masu shi ne, wasu ma aciki da motan su suka zo, ga su suna da iyayi irin na gogaggun ƴan bokon nan ƴaƴan masu hannu da shuni, amma tunda suka ga RAUDHA sai suka raina kan su, ko wacce cikin su tana so ta shige mata
Ita kuwa ko kallo basu ishe ta ba, idan ma tana son yin abu, sai dai ta tambayi Ramcy, ita kuma Ramcy sai ta haɗa ta dasu su taimaka mata, shiyasa suke fita tare, ahaka har suka soma shige mata tana kula su, shima sai su ne suka tsulmo ta cikin zancen su
Itama RAUDHA har da ita akayi mata gyaran jikin kaɗan, ta ma ce ba ta so but Ramcy sai da tasaka akayi mata
Komi sun shirya agidan, inda suka koma gidan Aunty Nafeesa ana gobe bikin, don acan za su yi taron su na ƙawaye.
Gidan su Ramcy ya cika maƙil da mutane, domin babu laifi suna da dangi sosai, musamman dangin Mahaifiyar ta, su ma sun zo da yawa, duk da ba Mahaifiyar a raye amma sun yi mata kara sosai, haka zalika Amaryar Baban su ma tayi gayya sosai, tunda ita a wurin ta ta riƙe su Ramcy tamkar ƴaƴan ta ne, sai kuma dangin Mahaifin ta, duk da su anan Zarian suke ma.
Doctor Salman sunan Mijin da Ramcy zata aura, anan Zarian yake, a cikin samaru, babu laifi suna da hali sosai, don zan iya cewa ma, duk a cikin ƴan uwan sa ya fi su samun kuɗi, lokacin da Ramcy take zuwa A.B.U Zaria suka haɗu dashi, inda shi kuma ya je karantar wani course, kamar da wasa dai abun nasu, domin ita Ramcy taƙi ba shi damar yaga gidan su ma, a school kawai suke haɗuwa su gaisa, har ma sun rabu daga baya, tunda shi shekara ɗaya kacal yayi a lokacin. Sai kuma watarana kwatsam ya zo anguwan su wajen wani abokin sa, suka sake haɗuwa ita kuma ta fito gidan Aunty Nafeesa, anan yake faɗa wa abokin nasa "ita ce wacce ya so ta bashi dama taƙi" shine abokin yace "ai kuwa ga gidan su can idan kana so in Kai ka, ai Yayan ta Aboki na ne, Lawan".
"Haba dai kana nufin Lawan Jaga?"
"Shi fa". Abokin nasa ya sake tabbatar masa
Da wannan hiran nasu Salman yace, "ai kuwa zai sake dawowa, dama gida an matsa mishi ya fito da mata, shi kuma be shirya auren zumunci ba, kawai shi Ramcy ɗin ce tayi masa a yanzu, bari ya koma ya gwada sa'ar sa".
Tunda Salman ya soma zuwa gidan su Ramcy, sai kuma ta ɗauki maganar nasa da muhimmanci, domin itama ba wai son sa ne ba ta Yi ba, kawai dai bata saba tsaya wa da samari bane, shiyasa tayi masa kora da hali
Ahaka soyayya me ƙarfi ya shiga tsakanin su, a lokacin tana aji biyu ne a school ɗin ta, shine aka saka rana har sai da ta gama, kuma taƙi yarda ayi har sai da RAUDHA ta dawo, domin tace babu wanda ya isa yayi mata aure idan babu RAUDHA
Shi Baban ta ya san matsayin RAUDHA a wurin ta, shiyasa be damu ba, ya sanya musu ranan auren da yawa, ga shi yanzu har lokaci yayi.
Washe gari asabar dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren Rahma da Doc. Salman. Inda ya tara dubban jama'a sosai, har Suhaib ya zo mata tare da Farida.
Su RAUDHA iyayen biki, sai cakare wa take yi, ta shiga wannan ta fita wannan ita da Amarya, yawancin kayan da suke saka wa ma iri ɗaya ne, tunda duk RAUDHA ta ɗinka musu
Kasancewar akwai partyn da za su yi, zuwa huɗu aka kai amarya ɗakin ta, gaskiya Ramcy tayi dacen muhalli, komi yaji, kuma ita kaɗai ce a gidan, duk da akwai fili na sauran ƴan uwan Salman ɗin, idan zasu yi auren su ma anan zasu zauna
Ɗakuna biyu ne da Parlour da kichen tare da Toilet, kuma duka an cika ko ina da kaya, musamman ma parlour'n ta da bedroom, kayan da Daddy ya siyan mata ne daga Dubai, kowa ya kalla sai yayi santin su, sosai suka yi kyau ga tsada
Tare da su RAUDHA aka taho kawo Ramcy, zuwa biyar da rabi har sun hallara inda za'a yi partyn, sosai wajen ya haɗu Masha Allah
Duk ƴan uwa sun taru, inda akayi ta yaba kyan da Amarya da ango suka sha, sun yi anko masha Allah, an fara gudanar da shagulgula cikin tsari, inda aka fara kiran Aminin Ango yazo ya bayar da tarihin Ango, riririri haka ya soma basu tarihin Ango suna ta shan dariya, dayake shi ɗin me yawan barkwanci ne, shiyasa yana ba da labarin ne yana saka wasa. Sai da yagama ya koma ya zauna
Inda aka ce Aminiyar amarya itama tazo ta ba da tarihin Amarya, aka kira RAUDHA, sai dai babu RAUDHA a wajen, ba ma ta iso wajen ba, tana can tare da Zulain shi ya tsayar da ita, tasha mamakin ganin sa a bikin, shine yake sanar mata "sun je gidan su ne, Daddyn ta yake sanar dasu suna biki, shine Sharif Ya rako shi nan ɗin tunda shi ya san kan gari" suna zuwa kuma basu sha wahala ba suka gano gidan
Tare suka taho wajen partyn a motan Sharif, tunda duk an watse tana tare dasu bata sani ba, daga tace ma Ramcy bari ta dawo
Suna zuwa a lokacin ne ake neman ta a hole ɗin, Ramcy sai leƙa kai take yi ta gano inda take amma ina bata ganta ba, sosai taji haushi jin M.C na sanarwan "idan babu ita a turo wata ta wakilce ta"
Waya ta ɗauka tana shirin kiran ta, sai gasu sun shigo su uku, RAUDHA na gefen Zulain suna taka wa a tare gunun sha'awa, kasancewar doguwar riga ce a jikin ta, har ƙasa yake jan mata, duk da ta saka Hill shoes, dole take amfani da hannun ta ɗaya wajen riƙe gefen rigan, hakan sai ya ba da wani style ɗin me ban sha'awa, ga shi rigan sosai yayi mata kyau ya ɗauki white skin ɗin ta, golden colour ne da ƙyalƙyalin kwalliya da kuma net da akayi amfani dashi, sai akayi mata light make-up a kyakykyawar fuskar ta da ya ƙara ƙawata fuskar
Masha Allah, kowa ya ɗaura idanun shi a kansu, ba ƙaramin tafiya da imanin jama'an wajen suka yi ba, daga ita har Zulain da ya sha kwalliyan sa cikin Suit farare, da baƙar rigan ciki, kasancewar suna tafiya ne a gaba Sharif na biye dasu a baya, sai kayi zaton su ɗin Ango da Amarya ne, sun yi kyau matuƙa, wasu ma daga cikin matasan har sun gane fuskar Zulain tunda ba ɓoyayye bane a TV. News, ana yawan saka shi idan har kai ma'abocin kallon labarai ne, dana American Dana Nigerian ma gaba ɗaya, to zaka iya sanin sa.
RAUDHA jin ana kiran sunan ta, kai tsaye can ta wuce ta amshi abun maganar 🎤, tana murmushi ta soma ba da tarihin Ramcy da harshen turanci, duk da tana haɗa wa da larabci
Hakan sai ya sake birge mutane sosai, nan akayi ta mata tafi, sosai ta tafi da imanin duk wani saurayi me ji da kansa.
Tana gama wa ta koma inda su Zulain suka zauna, hakan ya hana mutane da dama zuwa wajen ta, tunda sun ganta tare da saurayin ta.
Ba'a tashi ba, su Zulain suka yi mata sallama suka tafi.
Koda aka tashi a motan amarya da ango RAUDHA ta koma gida, duk da abokan ango suna ta mata tayin hawa motan su, amma ko kallo basu ishe ta ba, hakan yasa ma ta hau motan su Ramcy suka wuce gida.
A can suka kwana da sauran ƙawayen, tunda dama al'adan su ne, ana kwanar wa Amarya, sai washe gari kowa ya watse, sanda RAUDHA zata tafi Ramcy tasha kuka, ta hana ta tafiya, RAUDHA me zata yi in ba dariya ba, ita abun ma dariya yake bata
Dama a lokacin akwai Salman sun zo da Abokin sa, su ma dariyan suka soma mata, sai daga baya da yaga da gaske dai kukan take yi taƙi barin RAUDHA ta tafi, shine ya zauna rarrashin ta, daƙyar ta yarda ta bar RAUDHA ta tafi
Abokin Salman ɗin shi ne ya dawo da ita gida, tunda Salman ɗin ne ya saka a dawo da ita
Tun a mota yake ta mata surutu, ita dai ko sauraren sa ba tayi, don ba ta son ma ta bashi ƙofan da zai iya ce mata yana son ta, saboda ta ga take-taken haka a wajen sa
Sabit ganin yanda ta nuna masa, shima sai ya kama kansa don yasan yarinyan ƴar zafi ce, yana kai ta suka yi sallama ta wuce gida, shi kuma yaja motan yabar gidan, duk da a ransa ba haka yaso ba.
🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵
*AFTER ONE WEEK*
Yau Sunday ranan da RAUDHA za su haɗu da Ray, sosai yau ta tashi cikin zumuɗi, tun jiya ta saka masu aikin ta suka yi mata irin su soye-soyen nan, cake🍰, cin-cin da su nama, duk ta saka aka soya mata, yau kuma ta sanya su suyi mata girke-girke kala-kala, sannan su shirya mata a ƙaramin parlour'n sama
Yau dama Daddy Yana da inda zai je, shiyasa tun safe ma ba ya gidan, duk da kuwa yasan da zuwan Ray ɗin, but yarigada yace wa RAUDHA tace masa ya jira sa, saboda yana so yayi masa maganar auren su ne, idan da gaske yake yi ya turo.
Sai da ta tabbatar sun gama shirya mata komi yanda take so sannan ta baro parlour'n taje ɗakin ta ta shiga wanka, tana fito wa ta zauna a gaban mirror ta soma tsara kwalliya a kyakykyawar fuskar ta, tana yi tana lumshe lumsassun idanuwan ta fuskar ta cike da annuri, tunanin kawai yanda za su haɗu da Ƙalby ɗin ta take yi yau, har ta ƙosa mintocin da suka rage haɗuwar su suyi ta haɗu dashi
Light make-up tayi, amma bakin nan ya sha jan jambaki tamkar zai dubo sabida maiƙon sa, kayan ta ta saka, riga da skert na atamfa, yau ce rana ta farko a rayuwar ta da zata fara saka kayan Hausa wa, tun sanda Ammee ta ɗinko mata ta dawo dasu bata taɓa saka wa ba, ko a bikin Ramcy babu kayan hausawan da ta ɗinka musu daga ita har Ramcy ɗin
Ray da kansa ya ce mata "ta saka mishi yau domin yaga yanda kayan za su yi mata" shi dai a rayuwa yana son ya ganta sak da kayan Hausa wa tushen ta, hakan yasa itama a ranta taji tana ƙaunar sakawan sosai, ko domin ta burge sa
Atamfar ba wata me karikitai bane, gaba ɗayan ta me ruwan silver ne, sai akayi zane-zane a jikin ta ƙalilan da kalan fari da blue, wanda sosai ya ɗauki white skin ɗin ta, yayi mata mugun kyau, ga shi ɗinkin kamar dama an gwada ta, skert ɗin ya zauna mata ɗas a jikin ta, da akwai tsagu ta baya har zuwa kusa da gwiwar ta, sai rigan kuma me collar akayi mata da hannun link, amma wajen ƙirjin ta zuwa bayan ta duk net aka saka mata blue colour, sai hannun ma na net ne, illa wajen link ɗin da aka zizara atamfar, sannan collarn shima da atamfan akayi mata, rigan itama ta zauna mata ɗas gunun sha'awa, tare da fito mata da kyakykyawar ƙirar jikin ta
Sai dai matsalan kuma ta rasa yanda zata yi ta ɗaura ɗankwalin, ga shi tana son ta ɗaura ba ta son saka wani abu a kanta, dole ta ɗauki waya tayi kiran Saude, ita ta samu ta ɗaura mata me Steps ɗin nan, gashin ta ya zubo ta tsakiya, sai ta yafa farin gyale a gefen kafaɗan ta na dama, hohoho Fans thinks about yanda RAUDHAN ku tayi kyau, amma Ni idan na faɗa dole zan rage wani abu aradun Allah kuwa
Tana cikin zira Hill shoes ɗin ta ne, wayan ta ta soma ƙara, ta ɗauka tana murmushi don tasan ko waye ne
Sanar mata yayi ya iso, sai tace, "bari zata aiko a wuce da shi masaukin sa".
Daga nan ta ajiye wayan, taci gaba da sanya takalmin, kasancewar me igiya ne, sai da ta gama sannan ta miƙe batare da ta ɗauki wayan nata ba ta fito daga ɗakin, Direct Block two ta wuce inda a nan ne aka sauke Ray
Da shigan ta ƙayataccen parlour'n dake ta faman tashin ƙamshi saboda gyaran da ya sha na musamman, sai ta hange sa can saman kujeru kansa a ƙasa yana latsa waya, yana sanye cikin ɗanyen shadda me ruwan ƙasa, da hulan sa zanna bukar
Sai da gaban ta yayi muguwar faɗuwa saboda kawai ganin sa da tayi, amma sai ta daure ta soma taka wa a hankali cikin tafiyan ta me tsananin burge duk mahalukin da ya gani
Abun mamaki! yawan kusantan ta da shi yawan jiyo daddaɗan ƙamshin turaren sa, wanda tuni ta rigada ta san waye mamallakin turaren, ko barci ta tashi idan har aka tambaye ta ƙamshin waye wannan? Zata buɗe baki tace na Rayyan ne, amma sai kuma bata damu ba, don ko kusa zuciyar ta bata taɓa kawo mata tunanin shi ɗin zata gani ba, shi ne wanda suke soyayya a waya ba.
Ta iso tsakankanin kujerun inda sosai a wannan lokacin turaren nasa suka yi mata muguwar shiga hanci, a zuciyar ta tana me mamakin "me zai kawo sa nan bare har turaren sa ya cika wajen?" Sai kawai ta haɗa idanu dashi sakamakon ɗago kansa da yayi yana kallon ta
Wani irin zaro idanun ta waje tayi, ido cikin ido suke kallon juna, bakin ta na rawa tace, Kai!.. kai me kazo yi nan?"
.
_Hhhh to tambaye shi dai? Shin me zai faru? Ga RAUDHA ga Captain Rayyan sun haɗu?_
_comment ɗin ku kaɗai zai saka nasan kuna son ci gaba, idan kuma ba haka ba, mu haɗu bayan sallah idan Allah ya kai mu da rai da lafiya insha Allahu._
_Love You Fans._
[4/12, 8:23 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR:* ✍️
_Nafisat Ismail Lawal Goma._
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*RAMADHAN MUBARAKH*🤲🏽🕌
2021.
*HADHISI*
_An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar Allah ya ƙara musu yarda, daga Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce, "kada wani mutum yayi nema akan ɗan uwan sa, har sai ya bar wannan neman kafin shi ya nema, ko kuma idan ya bashi izni." An ruwaito daga Bukhari da Muslim. Ingantaccen hadisi daga Bukhari._
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON FIFTY ONE*
_______📖 Murmushi ne ya suɓuce a kan kyakykyawar farar fuskar sa, sai dai be iya cewa komi ba illa kallon ta da yake yi
While itama ta kasa ɗauke idanun ta kansa, sai dai a wannan lokacin sosai fuskarta ta kumbura da ɓacin rai, cike da fushin da bata san na mene ne ba tace, "ba'a gaya maka nan ɗin inda zan ajiye baƙo na bane da zaka zo ka zauna?"
Sai kuma ta juya tana kwaɗa wa Saude kira, taku ɗaya biyu tayi ta tsinkayi muryan sa yana faɗin
"Pretty ki bar wahalar da kanki mana, Ni ne Ƙalby ɗin ki".
Cakk ta tsaya tana juyo wa gare sa, ido cikin ido take kallon sa but ta kasa magana, sai kai komo da zuciyar ta ke yi wajen bugawa da ƙarfi
Murmushi ya sake yi yace, "nasan zaki yi mamaki da jin kalamai na, but ba abun mamaki bane, na shirya tsab don bayyana miki Ni ne wanda kike soyayya dashi batare da kin san ko waye ba, Pretty Ni ne Ƙalby ɗin ki, wanda kike matuƙar ƙauna da.."
Tsayar dashi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu da faɗin, "ya ishe ka da Allah Malam".
Sake ware idanun ta da suke ɗigar hawaye tayi a kansa, wanda tun soma maganar nasa suka soma kwaranya. Sosai laɓɓan ta suke rawa but ta kasa furta abinda ke ranta, illa wani irin ƙunci da ya tokare mata maƙogwaro, juya wa tayi da sauri tayi hanyar fice wa parlour'n da gudun ta
Da sauri Ray ya tashi tsaye yana faman kwaɗa mata kira, amma ina tuni ta fice.
A tsakankanin farandan benen ta zube ƙasa ta hau rusa kuka, domin ko kaɗan baza ta iya kai kanta inda take son zuwa ba, saboda rawan da ƙafafun ta suke yi, gaba ɗaya jikin ta ma rawa yake yi tamkar an jona ta da shocking, ko gaban ta ma ba ta iya gani sabida hawayen da suke kwaranya cikin idanun ta, har wani jiri-jiri take ji Coz tuna maganganun sa dake dawo mata cikin dodon kunne, wani irin yawu take haɗiya tana jan numfashi tamkar zata shiɗe, daƙyar ta iya buɗe bakin ta daga laɓɓan ta ta furta "Noo! Ƙarya yake yi! Ƙarya ne! Bazai.. ba..zai taɓa za..ma shi.. shiii.." Lokaci ɗaya numfashin ta ya ɗauke sabida wani irin mahaukacin ja da tayi masa.
Dai-dai lokacin da ta ƙarisa sulale wa ƙasa, a lokacin ne kuma Daddy ya buɗo Lifter ya hange ta, Sunan ta ya kira da ƙarfi ya nufo ta cikin tashin hankali
A lokacin shima Ray ya fito a firgice ya tarar da abinda ke faruwa
Daddy na kallon sa yace, "taimaka Captain, taimaka min, Baby ba ta numfashi".
Cakk Ray ya ɗauke ta suka yi Lifter da sauri, suna sauka ƙasa suka fita waje, Daddy na kwaɗa wa Drever'n sa kira, nan da nan ya ƙariso, dama ba nisa yayi ba tunda yanzu ya sauke sa
motan aka shigar da ita, Ray ya shiga mazaunin Drever, Daddy kuma na zaune da ita a baya suka yi Hospital.
Suna zuwa babu ɓata lokaci aka amshe ta, aka yi da ita emergency word, inda anan likitoci suka soma ba ta taimakon gaggawa
Daga Daddy har Rayyan an kasa samun wanda sai zauna, sai kai komo suke yi ko wanne zuciyar sa da tunanin da yake yi, shi shaf Daddy tunanin sa be kawo masa ya tambayi zuwan Ray ɗin ba, ta ɗiyar sa yake yi hankalin sa duk a tashe.
Fitowar likitan da yayi jagora Wajen duba RAUDHAN, yasa gaba ɗaya suka dawo dogon tunanin da suka afka, suka nufe sa da sauri suna tambayan sa "shin ta farka?"
Likitan kwantar musu da hankali ya soma yi, kafin yayi musu bayanin "babu abinda ke damun ta, sun yi nasaran dai-dai ta numfashin ta sabida suman da tayi, dama abinda ya kawo hakan, sakamakon shiga ruɗu ne da tayi".
Daga Daddy har Ray nannauyan numfashi suka sauke sabida jin abinda likitan ya faɗa, ko wanne cikin su na faɗin "alhmadulillah"
"Za ku iya shiga ku duba ta, in yaso daga baya sai muyi magana". Cewar likitan yana murmushi
"Ok thanks doctor".
Ɗakin suka nufa, Daddy ne a gaba Ray na biye dashi a baya, har bakin gadon suka ƙarisa, inda Ray ya tsaya daga jikin gadon, Daddy kuma ya zauna akan farar kujeran Robber dake jikin gadon, ya riƙe hannun RAUDHA da idanun ta ke rufe ya kira sunan ta, "Daughter kina jina? Ya ya jikin naki?"
Shiru RAUDHA tayi duk da kuwa tana jin shi ɗin
Cike da damuwa Daddy ya sake cewa, "wai me ya faru ne lokaci ɗaya kika sume Baby? Me ke damun ki Baby na kiyi magana kinji? Meyasaka ki ruɗu?" Sai kuma ya sauya akalan tambayan ga Rayyan da cewa, "kai ne kake gidan, shin kasan abinda ya faru ne? Ni dai nasan na bar ta lafiya but sai na dawo na tarar da wannan tashin hankalin".
Sake runtse idanu RAUDHA tayi jin saukar muryan Ray a kunnen ta, hakan ya tabbatar mata da cewa ba mafarki ne take yi ba, gaske ne Ray shi ne Ƙalbyn ta, shi ne wanda ya zo gidan su a matsayin Ƙalbyn ta, sai kawai ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi
Sosai Daddy ya sake shiga tashin hankali, nan da nan ya ruɗe yana tambayan ta abinda ke faruwa
Shi kuwa Ray runtse idanun sa yayi yana jin babu daɗi a ransa, shi kaɗai yasan me yake ji a ransa, tashin hankalin da yake ciki baki ma bazai iya fasaltuwa ba, dauriya kawai yake yi da abinda yake shirin faruwa dashi
Daƙyar Daddy ya iya rarrashin ta, duk da ba shiru tayi ba, amma yanzu ta buɗe idanun ta, ko kallon inda Ray yake bata yi ba, tace wa Daddy "ita a sallame su, ba ta son zaman Hospital"
Yanda tace ɗin haka Daddy ya aiwatar, ya saka Ray Kiran Doctor ɗin ya basu sallama.
Ana sallaman su suka fito, Ray shi yaja motan su kuma suna baya, RAUDHA ta kwanta a jikin Daddy sai ƙananun kuka take yi, duk rarrashin da Daddy yayi mata taƙi haƙura, sosai ranta yake tsananin suya, baƙin ciki da ƙunci duk ya cika mata zuciya, har yanzu a ranta tana jin kamar mafarki ne take yi, idan ta farka zata tashi taga babu Ray a tare da ita, but da ta ɗaga idanu take sauke su a kanshi, sai ta sake jin wani baƙin ciki ya kanainaye ta, hakan ke sawa lokaci ɗaya sai ta sake fashe wa da wani sabon kukan
Sosai wannan abun da take yi ya so ba wa Ray dariya, duk da yana cikin damuwar me zai faru a soyayyar sa, but hakan be hana sa murmusa wa ba.
Suna isa gida, ta buɗe murfin motan tariga kowa yin gaba, Daddy na kiran ta but sam taƙi tsaya wa
Koda suka shiga parlour'n babu ita, hakan yasa suka zauna inda Daddy Ke tambayar Rayyan "zuwan nasa na bazata"
But shi dai Ray murmushi kawai yayi, don be san me zai ce mishi ba
Ɗaya daga cikin ƴar aikin su, da ta kawo musu Drinks ne, Daddy ya tambaye ta da cewa, "ko da suka fita baƙon RAUDHA ya zo ne?" Tunda a tunanin sa dai be rigada ya ƙariso ba, Maybe fitan su ya zo, su kuma ba sa nan
Cikin girmamawa take sanar masa da "Ray ne baƙon nata, kuma sun sauke sa tun ɗazu"
Da mamaki Daddy ya kalli Ray yace, "Captain maganar ta gaskiya ne?"
Cike da kunya Ray ya duƙar da kansa tare da amsa mishi
Farin ciki ne ya mamaye Daddy yace, "You mean Kai ne Ƙalbyn Baby, but taƙi sanar mana? Kaima haka? A cikin ku babu wanda ya sanar mana kuke ta ɓoyan soyayyar taku? Kai abu yayi kyau Masha Allah. To Ina muku fatan alkhairi, Allah ya tabbatar mana da mafi alkhairin sa".
"Ameen Daddy". Ray ya amsa cike da farin ciki shima a zuciyar sa, sabida ganin Daddy kansa yayi farin ciki da zamowan sa Saurayin Ɗiyar sa
"Amma to ta tafi ta bar ka anan? Ai sai ta zo taji da kai ko? Ko dayake gidan ba baƙon ka bane". Daddy yafaɗa yana dariya
Shima Ray dariyan yayi, but ya kasa cewa komi
"Tashi mu je saman, sai in Kira ta".
Tashi Ray yayi, suka haura sama, a parlour'n da ta shirya don tarban shi suka shiga, Daddy ya saka me aiki ta zuba masa abinci, sannan ya saka ɗaya daga ciki ta je ta kira RAUDHA. Har ta tafi kuma, sai ya ce "ta bar shi" shi ya tashi ya je kiran ta
Ray dai na zaune ya tasa abinci gaba, sai dai ko cokali ɗaya ya kasa kai wa bakin sa, hankalin sa kacokan yana ga RAUDHA.
🔵🔵🔵
Da farin ciki a fuskar sa Daddy ya ƙarisa ɗakin RAUDHA, but sai dai a yanda ya ganta ne hankalin sa yayi ƙololuwar tashi
Tana zaune a ƙasa, ta ɗaura kanta saman kujera tana ta riskan kuka, har da majinu
Da sauri ya ƙarisa wajen ta cikin tsananin tashin hankali yake tambayar ta abinda ke faruwa, duk ya ruɗe yana ta faman taɓa jikin ta yaji ko wani abun ne ke damun ta
Cikin kuka ta ɗago kanta tana kallon sa da jajayen idanuwan ta, tace, "Daddy RAYYAN ya zo gidan nan ne yau?"
Cike da mamakin tambayar ta yace da ita, "Ya zo mana Baby, ba ke kika gayyace sa ba? Kuma ya zo, yana nan a Parlour. Lafiya me ke faruwa ne?"
Kuka ta fashe da shi, idanun ta akan Daddyn tace, "Daddy kenan yana nufin shi ne Muhammad ɗina, shi ne wanda nake soyayya da shi?"
Sai kawai Daddy ya saki baki yana kallon ta, sai kuma yace, "baki san haka bane Daughter kike tambaya na? Ina ce ke kika gayyace shi ai?".
Girgiza kanta tayi, kafin tace, "no Daddy ba Ni ba CE, Sam ba shi ne wanda nake so ba, ya yaudare Ni ne, Ni ba shi nake so ba, wlh bazai taɓa zama Ƙalby na ba".
Sai kuma ta saka hannu ta riƙe masa nasa
"Daddy please ka farkar da Ni wannan mummunan mafarkin da nake yi, mutumin da na tsana shi ne zai zame min Mijin da na ke fatan aure? No impossible".
Daddy fa duk ya kasa gane abinda take nufi, dole ya saka hannu ya ɗago ta, yana jinginar da ita jikin sa ya hau rarrashin ta
"No Daddy bazan dena kuka ba, har sai na tabbatar da cewa ƙarya ne zancen nan, Daddy zuciya ta zafi take min". Ta ƙare maganar da saka hannun ta tana dafe ƙirjin ta, yayinda idanuwan ta suke kwararar da hawaye sosai
Sosai Daddy ya ruɗe, ya rasa yanda zai yi da ita, dole ya miƙe ya fita ɗakin, sai ga shi ya dawo tare da Rayyan, cikin tsantsan damuwa yake kallon Rayyan ɗin yake tambayar sa da faɗin, "Captain wani abun ne ya faru da kai da ita, na kasa fahimtar me take cewa, ka faɗa min tsakanin ku?".
Cike da sanyin murya Ray ya soma sanar masa da komi, idanun sa kan RAUDHA da ta kifa kai take ta rusa kuka, tamkar ana yankan naman jikin ta, duk da muryan ta ba ya fita amma sosai ta dage take kukan
Shi kansa Daddy sai da jikin sa yayi sanyi da abinda Ray ya sanar masa, sosai ya tausaya wa Ray ɗin, to abun tausayi mana, tunda ga shi yana soyayya but ashe ita wacce yake yi dan ita, ta kasa amsar shi a zahiri, sam ba shi ne take so ba
Zama Daddy yayi ya soma rarrashin ta, amma taƙi shiru
Ray dai tsaye yayi yana kallon su
"Baby tunda kin ce ba kya son shi meye to ya rage? Kiyi shiru mana kar ki saka wa kan ki ciwon kai". Daddy ya sake faɗan haka yana saka hannu ya soma share mata hawayen
Cikin dishewar muryan ta da ya ƙara shige wa, don daƙyar ma yake fita, har katse wa maganar nata yake yi tace, "I Hate him so much Daddy, na tsane shi sosai fiye da kowa Daddy, ko da zan zauna babu aure ne Daddy bazan taɓa auren sa ba, ba na son sa Daddy". Ta ƙare maganar tana dage wa tare da fashe wa da kuka
Daga Ray har Daddy babu wanda yaji daɗin kalaman ta, musamman ma Ray da har hawaye sai da suka zubo masa, ahankali ya tako zuwa wajen kujeran da suke, ya zuƙuna gaban ta, cikin hawaye yace, "Please RAUDHA ki taɓa zuciya ta ki ji yanda take harba wa da ƙaunar ki, duk socond ɗaya kullum ƙaunar ki sake wanzuwa take yi a raina, na jima ina dakon soyayyar ki a raina, na jima RAUDHA, don Allah gani a gaban ki, ki amince da soyayya ta RAUDHA, ina matuƙar ƙaunar ki, kuma ba na tunanin akwai wanda zai so ki fiye da yanda nake son ki, Ina matuƙar matuƙar ƙaunar ki RAUDHA, ke ce kika yi min alƙawarin baza ki taɓa bari na ba,".
Hannu Daddy yasa ya riƙe mata hannu, gaba ɗaya zuciyar sa ta gama karaya da tausayin Ray ɗin, yace, "Baby kin ga ya ba ki haƙuri, ko menene yayi miki ki yafe masa kinji? Babu kyau riƙo, bare shi da ya durƙusa gaban ki ya nemi yafiyan ki, na tabbata babu wanda zai fi shi son ki".
.
_to Fans muna cikin tsaka me wuya MASOYAN RAYYAN, wani amsa kuke tunanin RAUDHA zata ba su? shin zata amince ta yafe masa ko kuma a'a? Kuna dai jin kalaman ta._
[4/14, 8:14 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR:* ✍️
_Nafisat Ismail Lawal Goma._
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*RAMADHAN MUBARAKH*🤲🏽🕌
2021.
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON FIFTY TWO*
_______📖 Hannun ta ta zame daga na Daddy, ta tashi da gudu tabar ɗakin tana sake rushe wa da wani sabon kukan
Daga Daddy har Ray dake hawaye bin ta suka yi da idanu har ta fice
Daddy sosai jikin sa ya sake sanyi matuƙa, har ya kasa ma yin magana, illa shiru da yayi yana afka wa duniyar tunani
While Ray, shima ya kasa koda jirga wa ne, illa lumshe idanuwan sa da yayi yana sauraron bugun zuciyar sa da ya sauya, ba ya jin zai iya jure rashin RAUDHA a tare dashi, yana matuƙar ƙaunar ta, ya rigada ya saka ta can cikin zuciyar sa, kuma fitan ta zai yi wuya a gare sa, tabbas yana ji a jikin sa muddin ya rasa ta zai iya shiga wani hali, shi kansa be san iya adadin ƙaunar da yake mata ba, kuma be san meyasaka soyayya tayi masa muguwar kamun nan ba..
Muryan Daddy shi ya katse masa tunanin sa, yace mishi "ya je insha Allahu idan RAUDHA rabon sa ne, zai same ta, shi kansa yana goyan bayan ya kasance miji a gare ta".
Sosai Daddy ya ƙara masa ƙwarin gwiwa, kuma ya ce mishi ya dage wajen bata haƙuri, insha Allahu shi ke da nasara, shima zai taya sa roƙon ta
Rayyan yaji daɗin kalaman Daddy, haka yayi masa sallama ya wuce Kaduna, sai dai a ƙasan zuciyar sa tunanin RAUDHA ne maƙil, amma babu yanda zai iya tunda yasan hakan sai ya faru.
🔵🔵🔵
Fannin RAUDHA kuwa abu yayi tsamari, gaba ɗaya ta hana kanta sukuni, ko kaɗan taƙi sauraren Daddy da maganar, da ya faro zancen zata soma mishi kuka akan "ba ta son sake jin maganar Rayyan". A cikin kwana biyu sai gata ta zabge sosai sabida damuwar da ta saka wa kanta, sosai take wahaltuwa da rashin Ƙalby ɗin ta, ita kanta ta san zai yi wuya ta jure rashin sa, tana mishi mahaukacin son da baki ma bazai iya fasalta shi ba, soyayyar sa ya rigada yabi jinin jikin ta, duk yanda ta so ta manta shi a ranta, ta cire sa ta goge sa gaba ɗaya a babin rayuwan ta, tayi rayuwa tamkar ma bata taɓa sanin sa ba ta kasa, dole ciwo ya kwantar da ita
Daddy gaba ɗaya hankalin sa ya tashi sosai, tausayin ɗiyar sa ya cika masa zuciya, sai dai taurin kanta yasa tana wahalar da kanta bayan tana da maganin matsalan ta, Doctor ya samo mace tana kula da ita a gida, da abun yayi tsamari dole aka wuce da ita asibiti, abu kamar wasa sai ga RAUDHA magashiyan tana jinya me tsanani har da su ƙarin ruwa, damuwar da ta saka a ranta ya haifar mata da ciwo me tsanani
Dole Daddy ya kira Suhaib ya sanar masa da komi, a ranan sai ga shi ya iso, sosai hankalin sa ya tashi ganin ƙanwar sa ta rame matuƙa, tausayin ta sosai ya kama shi, ba ma ita kaɗai ba har Rayyan, domin yasan cewa shima yana cikin wani hali koda be sani ba, tun farko ya gane Rayyan na ƙaunar ta, amma be taɓa tunanin shi ke bibiyan ta har suke wannan soyayyan ba, Allah Sarki Rayyan, ya so kiran sa ya sanar masa abinda ke faruwa da RAUDHAN, sai kuma yaga wani sabon tashin hankalin ne zai ɗaura masa, dole ya zauna rarrashin ƙanwar tasa, yana faɗa mata "ta amince da Rayyan, ta yafe masa domin samun kwanciyar hankalin su gaba ɗaya, domin yasan cewa shima yana nan cikin tashin hankali fiye da yanda take ciki".
Kuka ta fashe dashi tana kallon sa tace, "Yaya Ni bazan iya rayuwan aure da shi ba, infact ma ban taɓa saka wa a raina zai iya zamo min abokin rayuwa ba, Yaya kasan yanda na tsane mutumin nan duk a sabida abinda yayi min a baya? shi ne ya koya min tsanar sa, kuma ba na jin tsanar nasa zai iya goge wa a raina, domin wlh ji nake yi tamkar in kashe sa abaya saboda tsanar da nake mishi, but yanzu ba na jin haka saboda ya ragu sosai a raina, amma hakan ba wai yana nufin zan iya rayuwan aure da shi bane".
Riƙe hannun ta yayi yace, "meyasaka Baby baza ki bar komi ya wuce ba? Kar ki manta Dude ya zuƙuna ya baki haƙuri, duk ƙimar sa da mutuncin sa ya ajiye gefe, a matsayin ki na ƙanwar sa ya duƙa a gaban ki ya baki haƙuri, meyasaka baza ki yafe masa ba uhm? Idan kin ce kin tsane sa ai kuma kina son sa tunda kin Yi soyayya dashi".
"Yaya ai ban san shi ɗin waye ba shiyasa na so shi a rashin sani, amma yanzu ba zan iya auren sa ba, zan iya rayuwa da kowa ban dashi".
Yace, "Baby idan har zan samu ki yafe ma Dude ɗina ki aure sa, to wlh nima zan duƙa a gaban ki domin nema masa alfarma, don Allah Baby ki yafe masa".
Da sauri ta riƙo hannayen sa da yake shirin tashi ya duƙa mata, kuka sosai ta fashe da shi tana faɗin, "me ye haka Yaya? Me zaka yi don Allah?"
"Duƙa miki zan yi domin ki yafe ma Aboki na, Baby Yana matuƙar ƙaunar ki, domin nasan haka tun ba yanzu ba".
Kuka taci gaba da yi batare da ta furta komi ba, dole ya zauna rarrashin ta tunda yasan matsalan ta yanzu, doctors ma sun CE a dena saka mata damuwa
Daƙyar ya samu tayi shiru, be sake mata maganar ba har Daddy ya dawo
Ganin yanda ta ɗan saki jikin ta sosai sai hankalin su ya kwanta.
Washe gari sai ga Rayyan, ba su san waye ya sanar masa ba, sai ganin shi suka yi a Hospital ɗin, lokacin ma RAUDHA tana barci ne
Daddy yace, "Captain wa ne ne ya sanar maka muna asibiti ka zo?" Sai kuma ya juya akalan tambayan sa ga Suhaib yana cewa, "ko kai ne?"
"No Daddy ba Ni bane, ban ma yi tunanin sanar masa ba".
Murmushi Ray Yayi yace, "Daddy duk abinda zai samu RAUDHA, wlh ina ji a jiki na! kuma duk halin da take ciki ina sane da komi, Daddy ƙaunar da nake mata bazai bar Ni kwanciyar hankali ba in har ba na bibiyan rayuwar ta".
Daga Daddy har Suhaib sosai yai matuƙar ba su tausayi, barin ma ganin yanda ya sauya duk ya faɗa, ga tarin ƙasumba da ya bari a fuskar sa ko gyara ba ya samu, kamar dai ba shi ne ɗan gayen nan ba
Ita kanta RAUDHA sai da zuciyar ta ta karye da kalaman sa, hawaye suka soma sintiri a fuskar ta, sabida tunda ya shigo muryan sa ya doki kunnen ta ta farka, ta rasa meyasa zuciyar ta ta kasa yafe masa, duk idan ta tuna abubuwan da yayi mata sai taji babu daɗi a ranta, duk da tana son ya fe masa amma kuma kasancewar akwai maganar soyayya a tsakanin su, sai ta ji sam ba ta ƙaunar ta yafe masa, da ace haka kawai ne dole zata yafe masa..
Maganar Suhaib ne ya dawo da ita duniyar tunanin ta, inda yake tambayar ta "meyasaka take hawaye?"
Ita bata san tana hawayen ba ma, sai kawai ta fashe da kuka
"Mene ne kuma na kuka Daughter? Me aka yi miki? Ke kenan kullum ba kya gajiya da kuka? Kin san abinda doctor yace miki ki dena saka damuwa a ranki, gaba ɗaya kin tsangwami kanki, kin ƙi kiyi abinda ya kamata, kuma kin san duk abinda ya same ki tamkar mu ya sama, damuwar da kike ciki mu ma muna cikin sa gaba ɗaya".
Sosai a wannan karon take kuka sabida kalaman Daddyn sosai ya shige ta, ta faɗa jikin sa cikin kukan take cewa, "Daddy ku yi haƙuri don Allah". Abinda take faɗa kenan tana ci gaba da kukan
Hannu Suhaib yasa ya ɗago kanta yana cewa, "haƙurin na meye ne Baby? Allah idan baki dena kukan nan ba zan yi fushi dake, kuma kin san abinda ban taɓa yi ba kenan".
Hannu ta saka da sauri ta soma share hawayen ta, Daddy na taya ta
Ray dai na zaune yana kallon su, zuciyar sa cike fam da soyayyar ta, tabbas da zai iya haƙura da RAUDHA, da tuni ya bar ta har ABADA
Daddy ya soma tashi ya fice bayan ya ce musu "zai je wajen doctor ne".
Shima sai Suhaib ya miƙe ya ɗauki waya ya fice batare da ya ce uffan ba, don ya gane manufar Daddy ɗin, shiyasa shima ya miƙe ya ba su wuri
RAUDHA da kallo tabi Suhaib dashi har ya fice, don bata yi tunanin wai fita zai yi ba, sai dai ganin ya fice kawai sai ta bi shi da ido ta kasa cewa komi..
Sunan ta da Ray ya Kira ne, yasa ta dawo da kallon ta gare shi, sai a lokacin ma ta kalli inda yake, shiyasa tayi saurin ɗauke kai da suka haɗa ido, sosai ta ga ya sauya mata saboda raman da yayi. Bata amsa mishi ba illa ɗaure fuska da tayi tana cin magani
Sarai ya lura da sauyawan ta amma hakan be dame sa ba, sai ya tashi daga kujeran da yake ya dawo na kusa da gadon, yana kallon ta yace, "Ya jikin naki Pretty?"
Shiru tayi masa tana sake jujjuya kanta don ko kaɗan ba ta ƙaunar kallon da yake mata, har cikin jikin ta take ji
Shiru ne ya ratsa na ɗan wani lokaci, kafin kuma ya sake buɗe baki yace, "Pretty idan har ban manta ba, ke ce da kanki kika yi min alƙawarin zaki kasance dani a duk halin da kika ganni, don me baza ki yafe min ba? Wlh duk abinda nayi miki a baya, nayi sa ne saboda ƙaunar da nake Miki, ki yarda dani, ina son ki sosai shiyasa ba na son wani abu ya same ki, duk abinda nayi miki a baya nayi hakan ne don ki kintsu ki dawo kan hanya madaidaiciya, amma duk idan na musguna miki, ina koma wa ne abun ya dame Ni matuƙa a rai, sai kuma naga babu hanyar da ya dace illa hanyan da nabi ɗin, duk kalaman da nake faɗa miki, na rantse da Allah, ba ke kaɗai suke ɓata wa rai ba, ina kwana ne da ƙuncin zuciya a duk sanda nayi miki irin furucin nan, sam ina ji ba na kyauta wa, sosai nake azabtuwa, amma kuma Ni duk a gani na hakan shi ne dai-dai, hanyar kawai da zan bi don ganin kin gane gaskiya, Pretty duk da nasan halin ki, na san ke wacece amma wlh ban hana zuciya ta ƙaunar ki ba, ina son ki da gaskiya Pretty! wlh ko da Zaki koma rayuwan ki na baya ne, zan kasance dake Pretty, sabida ƙaunar da nake Miki bazai bari na iya rayuwa cikin daɗin rai ba, ban taɓa son wata ba sai ke, a kanki zuciya ta ta fara soyayya".
Shiru yayi yana jan numfashi, sai kuma ya ci gaba da faɗin, "RAUDHA ina son ki, a gaban kowa zan fito in sanar cewa ina son ki, kuma ina me alfahri da hakan, ina roƙon ki ki bar komi ya wuce, ki amshe Ni a matsayin masoyin ki a yanzu, zan miki duk abinda kike so in dai zaki yafe min ki amshi tayi na, idan kuma kin ce ba kya so na, wlh zan bar rayuwan ki har ABADA kamar yanda kike so".
Tunda ya soma maganar nasa, ta haɗa kai da gwiwa a saman gadon tana faman rera kuka a hankali, sosai zuciyar ta ta karye da maganganun sa, "shin meyasa baza ta yafe masa ba?" Shi ne tambayar da zuciyar ta ke ta faman tambayan ta, tabbas tana ƙaunar sa itama, amma kuma bata san meyasa ba, sosai yake ba ta haushi, duk da kaso mafi yawa yanzu maganar sa yasa ta fahimci gaskiya, tabbas so ne, idan ba son ta yake Yi ba, da be mata abinda yayi mata ba, kuma da shi macuci ne a gare ta, tabbas tasan da tuni ya daɗe da cutan ta, saboda ya samu hanyoyi da dama amma be yi hakan ba..
Tashin da yayi ya saka ta dawo duniyar tunanin ta, ahankali ta ɗago kai tabi shi da kallo, har ya kai bakin ƙofa ta tsayar da shi da faɗin, "dakata Malam".
Cak Ray ya tsaya daga buɗe ƙofan da yake shirin yi, sai dai be jiyo ba yana jiran abinda zata ce
Sauko wa tayi daga kan gadon, ta saka hannu ta share hawayen fuskarta, duk da kuwa ba dena zubo wa suka yi ba, ta taka ta nufi wajen sa, tana ƙarisawa ta saka hannu tayi...
🤣 _wlh ina shan dariya da team-Ray, wai dama kun san zuciyar sa tana da rauni kuka turo sa wajen RAUDHA? Kun san halin ta ai._
[4/14, 11:22 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR:* ✍️
_Nafisat Ismail Lawal Goma._
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*RAMADHAN MUBARAKH*🤲🏽🕌
2021.
*HADHISI*
_An karɓo daga Baban Salma Allah ya ƙara musu yarda ya ce, "na tambayi A'ishah matar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, nawa ne sadakin Manzon Allah?" Sai tace, "sadakin Manzon Allah ga matan sa uƙiya goma sha ɗaya da rabi (nashsha). Sai ta sake cewa "shin kasan Nashshu?" Sai yace mata, "a'a" Sai tace, "rabin uƙiya shi ne darhami ɗari biyar". Muslim ya ruwaito. Ingantaccen hadisi daga Muslim._
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON FIFTY THREE*
_______📖 Hannun ta ta saka ta kamo nashi, hakan yasa ya juyo yana kallon ta, ido cikin ido suke wa junan su kallo, batare da ko wannen su yana ƙyafta wa ba
Sun ɗau tsawon soconni a haka kafin ita ta soma ɗauke kanta tana jan numfashi, sai tace, "I love you".
Tsaban maganar ta zo masa a bazata be san sanda ya fiddo idanuwan sa waje ba yana kallon ta da tsananin farin cikin da ya fito tun daga zuciyar sa, sai dai ya kasa magana illa kallon ta da yake yi
Jin yayi shiru sai ta mayar da idanun ta kansa, ganin kallon da yake mata sai ta taɓe baki tace, "Ina son ka ba yana nufin na amince zan aure ka bane". Tana gama faɗar haka ta saki hannun sa ta juya zata koma
Yayi saurin riƙe mata hannun, dole taja ta tsaya, but ta kasa juyo wa illa lumshe idanuwan ta da tayi tana sauraren bugun zuciyar ta
Tako wa yayi ya dawo gaban ta, idanun sa a kan ta da tsananin murna yace, "idan har kina so na, na tabbata zaki iya aure na, kenan kina nufin kin amince dani a matsayin masoyin ki?"
Huro hanci tayi sai dai ta kasa kallon sa, illa shiru da tayi tana haɗiyar yawu
Shi kansa ya lura akwai Magana a bakin ta, sabida yanda take ta motsa bakin tamkar zata buɗe tayi magana. Murmushi yayi yace, "I love You so Much RAUDHA! Ina son ki da yawa wanda baki ma bazai iya furta wa ba, kiyi haƙuri da duk abinda nayi miki kinji?"
Sai a lokacin ta ɗago manyan idanuwan ta ta sake kallon sa, sai tayi saurin ɗauke kai tare da janye hannun ta, ta gifta shi tana faɗin, "Ni fa ba ina nufin zan iya auren ka bane, duk da na faɗa maka wannan kalman, zuciya ta ce ta aiko Ni, but a zahiri baka yi min ba".
Sosai maganar nata ta ba shi dariya memakon haushi, sai da ya murmusa yana shirin magana, sai ji suka yi an buɗo ƙofan, daga shi har ita juya wa suka yi su ga wanene
Suhaib ne tsaye yana bin su da kallon tuhuma, ganin su cirko-cirko da yayi a tsaye kusa da juna, sai kawai ya saki fara'a a fuskar sa yana faɗin, "Baby kin.."
Saurin katse sa tayi da faɗin, "Yaya Ni dama Toilet zan je shi ne na sauko". Sai ta juya kuma tayi Toilet ɗin da sauri har tana kanannaɗe skert ɗin ta tun kafin ta isa don ya tabbatar Toilet ɗin take son zuwa
Daga shi har Ray da kallo suka bi ta, ko wanne na sakin murmushin da be shirya ba, sai kuma suka jiyo da kallon su ga juna suna ci gaba da murmushin
Suhaib yace, "Allah ya shirye ki Baby, har yanzu kin ƙi ki girma, Aboki na zaka yi aiki duk sanda ka auri Baby a matsayin mata, shawaran da zan baka kawai idan har ta kasance matar ka, to ka haɗa su biyu ka aura ka je dasu gidan a lokaci ɗaya, idan kuma ba haka ba, wlh zaka sha..."
Burum RAUDHA ta fito daga Toilet ɗin, fuskar ta gaba ɗaya a haɗe yake tace, "Yaya To dama wa yace maka zan aure sa? Wlh bazan taɓa zama da kishiya ba, be isa ya haɗa Ni da wata ba, idan ma yasan yana da mata yanzu tun wuri yaje ya sake ta.."
Wani irin dariya ne ya kufce musu su duka biyun
Dole yasa RAUDHA tayi shiru tana faman zare idanu, sai yanzu ta gane katoɓaran da tayi, sai tayi saurin kwaɓe fuska kamar zata yi musu kuka tace, "Ni fa ba ina nufin wani abu bane, misali nake yi idan zan kasance matar sa".
Suhaib na dariya yace, "to Baby dama wa yace miki muna nufin wani abu? Dariyan ne ya zo mana atare sabida tuna wani abu da muka yi, ko ba haka ba Dude?" Ya ƙare maganar da ɗage wa Ray gira ɗaya
Ray dai tsaban farin cikin da yake ji a ransa, sabida ganin cewa RAUDHA har yanzu tana ƙaunar sa, be iya magana ba illa gyaɗa masa kai da yayi yana ci gaba da darawa
Haɗa idanu suka yi dashi, sai ta banka mishi harara tana yin gaba, ta hau kan gadon tana koma wa ta kwanta, har da juya musu baya
Matso wa Suhaib yayi kusa da shi, ya zungure shi ganin yana ta kallon ta, murmushi yayi masa ya raɗa masa magana a kunne, sannan ya kalli RAUDHAN yace, "Baby bari mu je mu dawo, idan Daddy ya dawo ki ce masa mun shiga cikin anguwa zamu je wajen wani friend ɗina".
Shiru RAUDHA tayi bata ce komi ba har suka fice, suna fita ta tashi zaune tana tanƙwashe ƙafafun ta, tare da haɗa hannayen ta waje ɗaya ta tallabo haɓar ta, tsira wa waje ɗaya ido tayi tana me afka wa tunani.
🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵
Washe gari dole RAUDHA ta matsa aka sallame ta, su ma su Daddy sun ji daɗi ganin yanda ta samu lafiya, shiyasa Daddy shima yace "a sallame su" tunda dama damuwar duk akan Rayyan ne, kuma sun ga ta sauko sosai akan sa.
Suna komawa gida, Daddy ya Kira Uncle ya sanar da shi abinda ke faruwa, kar ku so ku ga murnan da ya nuna da shi da Ammee, kai gaba ɗaya ma ahalin, har Faruk da yake ƙaunar ta, tunda tuni ya ajiye makaman sa tun sanda ya gane cewa Yayan nasa yana ƙaunar ta, sosai kowa yake farin ciki da wannan haɗi.
Ita kuwa RAUDHA ko kusa nuna wa take yi har yanzu baza ta iya auren sa ba, kuma sun ci gaba da soyayyar su a waya, domin yana kiran ta tana ɗauka, sai dai ta dinga gaya masa maganganu kenan don dai ta ɓata masa rai, amma kuma be hana gobe idan ya kira ta taƙi amsa wa ba
Shi dai Ray dariya ma abun nata yake ba shi, tamkar dai har yanzu akwai aljanu a kanta, domin wani abun idan tayi, baza ka ɗauka ƴar shekara 24 bane, RAUDHA akwai shirme a kanta sosai.
Da weekend sai ga shi yayi mata bazata ya zo gidan, sosai a ranta tayi murna amma a fili ta nuna ko kaɗan hakan be burge ta ba, illa taɓe baki da take ta faman yi taƙi masa magana
Daddy na tashi a wajen yace da ita, "wai Pretty ko baki yi murna da gani na bane? Har yanzu kin ƙi ki yafe min gaba ɗaya ko?"
Kallon sa tayi, sai ta ɗaure fuska tace, "ai bazan taɓa yafe maka ba Ƙalby".
"Why?" Yace da ita cikin sanyin murya
"Sabida nima har yanzu kallon ƴar iska kake min, in har baka dena ba, Nima kuma bazan taɓa amince wa da kai ba, bare har in yafe maka".
Yace, "wlh nayi alƙwari daga yau bazan ƙara miki kallon haka ba, idan magana makamancin haka ya sake fito wa a baki na, na baki dama kiyi min duk hukuncin da ya dace dani, koda kuwa rabuwa dani ne, wlh Pretty soyayyar da nake miki ya wuce tunanin ki, ko da yanzu zaki koma rayuwan ki na Da ne, to Ni kuma nayi miki alƙawarin kasancewa da ke, bazan taɓa rabuwa dake ba, zan aure ki a haka, tabbas na yarda *SO ƘADDARAR ZUCIYA* ne! ( My new book), soyayyar ki shi ne ƙaddarar tawa zuciyar".
Kallon sa kawai take yi, amma a zuciya murmushi take yi tana me faɗin, "uhmmm Rayyan kenan! Tabbas zan fi kowa murnan ranan da zaka yi nadama da kira na da kalman ɓatanci da kake yi, zaka sha mamaki wlh". A fili kuwa cewa tayi, "Fine". Tana ɗage kafaɗa tare da karkaɗa ƙafafu
Murmushi ya sakar mata, itama ta mayar masa tana faɗin, "sai yaushe zaka tafi?"
"Kin ƙosa in tafi ne?"
Ɗan zaro ido tayi tana kama haɓa tace, "laa haza haramun".
Dariya yayi sosai, saboda ba ƙaramin dariya ta bashi ba, itama tana taya shi, gaba ɗaya a nishaɗi suke jin su, tamkar dai an sauya musu wani abu a jikin su, ko kuma sun sauke wani nauyi
Tashi tayi don tayi masa tsiya tace, "to Ni bari in Kira maka Daddyn, tunda dama wajen shi ka zo".
Langaɓe kan sa yayi yana sakar mata wani shu'umin kallo, cike da sanyin murya yace, "haba Pretty Kar ki yi min haka mana, kin san fa domin ki na zo".
Murmushi tayi tana cije leɓen ƙasa, itama ɗin ta sakar masa wani kallo da ya kusa zauta shi, har da wulla idanun tamkar zata rufe su ta sake buɗe su a kansa, taku tayi ɗaya zuwa biyu a gaban sa, kafin ta juya tana tafiya cikin yanga, tamkar dai da gayya take masa
Sosai Ray ya rasa nutsuwar sa, yana bin ta da kallo ko motsin kirki ya kasa, har sai da ta ɓace wa ganin sa kafin ya saki wani Gwauron numfashi yana lumshe idanu, babu abinda yake gani sai kyakykyawar surar jikin ta dake masa gizau, "Oh Allah! My beby Zaki kashe Ni!" Yayi maganar a maƙoshi yana jingina kansa sosai jikin kujeran.
Har Ray ya bar gidan be sake haɗuwa da RAUDHA ba, ƙiri-ƙiri ta maƙale a ɗaki taƙi fito wa, kuma ya kira ta duk taƙi ɗauka, duk da ga wayan a hannun ta tana yin Game, iyakan tayi murmushi ta katse kiran
Hakan ya tabbatar masa da tana ganin kiran nasa, murmushi yayi shima a zuciya yana faɗin, "Dani kike zancen Pretty, zan rama ne ai".
🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵
A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, har ana shirye-shiryen saka ranan auren RAUDHA da RAYYAN, soyayyar su yanzu abun sha'awa ne, kullum suna nane a waya tamkar za su cinye juna, duk weekend kuma sai ya zo mata, ta saki jiki sosai dashi suna gurzan soyayyar su kamar za su haɗiye juna, soyayyar da suka yi a baya ma ba komai bane kan yanda suke yi
An saka ranan auren nan da wata ɗaya, sabida kowa a shirye yake kuma kuɗi ke aiki, shiyasa aka ce baza a saka da yawa ba
Tun sanda aka tsayar da ranan auren nasu, ta kira Zulain ta sanar masa
Sosai ya shiga tashin hankali da alhinin rasa ta da yayi, amma babu yanda zai iya dole sai haƙuri, duk da a lokacin ma tamkar ƙara wutar son ta ake masa a zuciya, dole ya haɗa kayan sa yace musu "zai tafi" tun da dai ya san idan ya tsaya a nan damuwa ce zai illata shi, haka yabi jirgi ya koma ƙasar su tare da ɗumbin soyayyar RAUDHA a zuciyar sa
Shi kuma ya bar Sharifa tare da nasa a zuciyar ta, sosai tayi kuka ranan da ya tafi, ta so ta sanar masa amma ta kasa, sai da ya tafi tayi dana-sani ba kaɗan ba, haka tasha kuka ta gode wa Allah, ga shi kowa ta ƙi ta sanar amsa son da take yi wa Zulain ɗin.
_To Allah ya kyauta, inda rabon ayi dake ne to, in kuma babu shikenan, mu dai ƴan shan biki ne. 🤷_
🔵🔵🔵
Biki na ta ƙara to wa, inda ake ta shirye-shiryen bikin daga bangare biyun gaba ɗaya, su kuma masoyan suna ta shan soyayyar su.
.
_jama'a saƙo daga RAUDHA, tana miƙa saƙon gaisuwa tare da katin gayyata wajen masoyan ta, ta ce a gaishe ku matuƙa, bata cire kowa ba, kowa tana gayyatar sa taya ta murnan nasaran ƙwamushe Ray ya zama nata, daga *UMMU DAHIRAH FAN'S GROUP, NAFEESA GROUP NOVEL'S, da kuma *RAUDHA FANS* 😍 duk tana gaishe ku, kuma tana gayyatar ku baki ɗaya, har da ma maƙiyan ta masu mata hassadan samun Captain Rayyan._ 😲🤭🤣
[4/14, 11:23 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR:* ✍️
_Nafisat Ismail Lawal Goma._
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*RAMADHAN MUBARAKH*🤲🏽🕌
2021.
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON FIFTY FOUR*
_______📖Dama akace duk abinda aka saka mishi rana dole zai zo, to ga shi bikin su RAUDHA ya rage saura kwanaki ne, sosai Daddy ya ga jama'a a bikin nan, waɗanda suka zo masa daga cikin ƴan uwa, bare shi mutum ne na ƙwarai me kirki da hannun kyauta, shiyasa dangi duk suka taho masa, sabida sun san ba su za su ragu ba, sai dai ma su ƙaru, wasu tun ana kwana huɗu, uku duk suka zo da kayan kwanan su, sai bayan biki su koma, su suke yin komai tare da ƴan aikin gidan, Masha Allah gida ya cika maƙil
Itama Farida tun ana saura sati ɗaya suka zo, daga ita har Suhaib da ya ajiye aikin sa kacokan, don zuwa bikin shalele kuma mafi soyuwa a birnin zuciyar sa
Zuwa lokacin duk shi yake kai ta duk inda take buƙata, duk da dama duk wani gyara da ake mata, har gida ake zuwa ayi mata, Farida ita ta ɗau nauyin komi ake gyara ta ba ni da gyara ba, domin tun sanda aka soma mata gyaran amarcin RAUDHA ta sauya, gaba ɗaya baza ka taɓa kallon ta kace ita ce ba, ta koma hurun aini🤫😜, kamar ka latsa ta jini ya zuba sabida haske da sulɓi da take yi, ga wani ɗaukan idanu da take yi, dayake hasken ta yayi yawa har wani jajja take yi kamar dai zabiya, amma kuma ko ƙuraje bata dashi. Hasken ta me kyau ne, me fizgar mutane zuwa gare ta.
Bata da ƙawaye ita take yin komi nata, sai ana jibi biki ne Ramcy ta iso, a ranan kuma ƙawayen Ramcy ɗin duk suka zo, dayake sun ce idan bikin ta ya zo a gayyace su duk za su zo, to shi ne fa RAUDHA ta samu ƙawaye da ɗan yawa, ga shi wasu ma da suke chart a cikin Friends ɗin sun ce za su zo mata.
Ranan juma'a 8 ga watan April, dubu biyu da ashirin da ɗaya 2021. Dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren *CAPTAIN RAYYAN HASSAN* da Amaryan sa *RAUDHA MUSTAPHA MAKAMASHI*
Da dare akayi shirin Dinner, inda me kwalliya ta tsantsara wa RAUDHA kwalliyan da ya ɗauki fuskar ta ainun, ya ƙara fito da tsantsan kyawun ta, ba wani karikitai aka cika mata ba, saboda tace ba ta so, shiyasa akayi mata light make-up, aka shirya ta cikin ash colour ɗin gown doguwar riga, rigan fitet ne, domin dai-dai jikin ta ne, amma daga ƙasan gwiwan ta ya buɗe sosai har yana jan ƙasa, me siraran hannu ne, sai wani ƙaton flower da aka saka mata daga hannun damar ta, da net akayi shi, sai kwalliya a gaban rigan da kalan jan zare, sai akayi mata amfani da jan net aka rufe mata gashin ta da ya sha gyara har kafaɗun ta, duk da an tufke mata shi a tsakiyar kanta, takalmin ƙafan ta me tsananin tsini ne sosai, kalan ja tare da pourse ɗin hannun ta
Sosai ta tafi da imanin duk wanda yayi tozali da ita sanda me make-up ta fito da ita, sai haska ta suke yi a photo ana sauri ayi status da ita😜. Kuma na san duk aikin WhatsApp fan's ɗin ta ne.🤭🤣
A lokacin motoci duk sun zo ɗaukar mutane zuwa Shagalin ku restaurant, inda a nan ne za'a yi dinner ɗin. Sai da kowa suka shiga mota suka tafi kafin Farida tare da Ramcy suka rako ta zuwa motan da za su tafi tare da Ray, galleliyar mota ce fara tasha kwalliyan balo-balo
Su suka buɗe mata motan ta shiga ciki ta zauna, sannan suka rufe suka nufi motan Suhaib da zai kai su
Numfashi kawai taja lokacin da ta shaƙa daddaɗan ƙamshin su da ya haɗe ya gauraye waje ɗaya ya ƙara wani sinadarin daɗi, juyowar da zata yi suka haɗa ido dashi dake zaune ƙyam ya kafe ta da ido ko motsin kirki ya gaza yi, saboda ba ƙaramin zauta shi tayi ba, ta ɗauke masa gaba ɗaya nutsuwar sa da numfashin sa, ya tafi wani duniyar da ya kasa tantance a raye yake ko kuwa a mace 🙈😜, hege Ray! Zaka dawo ma duniyar mu ne yanzu. 🤣, Bari dai ta falla maka mari🤭
Murmushi tayi ta matso da fuskar ta kusa da nasa, ta hura masa iska
Hakan yasa ya dawo cikin hayyacin sa, har da ajiyan zuciya
Ita kuma sai ta taɓe baki tana matsar da fuskar ta kusa da nashi, tare da gyara zaman ta
"Kin yi kyau Baby na". Yayi maganar tamkar ana masa dole, nan kuwa tsaban shiga tention ne 🤣 ya rasa kuzarin sa
Sake kallon sa tayi, suka ƙura wa junan su idanu, sai kuma ta sakar masa murmushi ahankali tace, "kaima kayi kyau Ƙalby, I Love You so Much".
Lumshe idanuwan sa yayi yana buɗe wa a kanta cike da wani irin farin ciki dake gudana a zuciyar sa, sabida kasancewar yau ɗin na musamman ne a rayuwan sa, Mallakar Abokiyar rayuwar sa. Hannun sa ya saka ya kamo nata wanda suka sha lalle suka yi mata matuƙar kyau, hannun kawai yake kallo
While itama tana taya sa
"Yayi kyau". Ya sake faɗa ahankali
Murmushi kawai tayi ta kawar da kanta, sai kuma ta lumshe idanuwan ta saboda jin ya haɗe hannayen su waje ɗaya yana faman matsa mata
"Baby kin Yi kyau".
"I know". Tafaɗa tana ci gaba da murmusawan ta
"Ina kishin ki". Ya sake faɗa yana kisses ɗin hannun nata da ya ɗago zuwa bakin sa
Shiru tayi masa wannan karon, tana me sake runtse idanun ta, sosai take jin wani iri a tattare da abinda yake mata, amma kuma baza ta iya hana sa ba, inda so samu ne ma, taji ta a jikin sa, sabida ba ƙaramin son kasancewar hakan take yi ba, duk a sabida ƙamshin turaren sa da ya cika mata hanci, tamkar ta shige jikin sa tayi ta shaƙa..
"Tunanin me kike yi?" Yayi maganar yana shafa fuskar ta
Buɗe idon tayi a kansa, sai kawai suka sake ƙure junan su da kallo, ko wanne na jin son ɗan uwan sa a zuciya..
Tsayuwar motan shi ya dawo dasu hayyacin su, dole suka nutsu suna me mayar da hankalin su kan Suhaib da ya buɗe murfin ƙofan side ɗin Ray, yace masa "ya fito"
Sai da ya sake yi wa hannun nata kiss, kafin ya sakar mata, sannan ya fito, kafin ya zagayo ta side ɗin ta, itama har an fito da ita
A tare suka jera zuwa hole ɗin, masu sauraro bazan iya fasalta muku yanda couple ɗin nan suka haɗu ba, da kuma Shagalin da akayi, amma kuyi tunanin abinda zai faru, 🤣 kun san halin RAUDHA dai, a bikin nata ma bata ji kunyan yin rawa ba, koda aka ce su fito fili, ita zaƙe wa tayi ta tiƙa rawan ta ba ko kunya, har da riƙe masa hannu, shima da ya ga dai abun ba na yi bane, dole ya ajiye kunya suka bar tarihi a wajen
Yawancin abokan sa na wajen aiki duk sun hallara, har wasan su na soji sai da akayi, a hotel ɗin aka kai su suka sauya kaya zuwa kayan sojoji daga shi har ita, sun yi matuƙar kyau sosai, sai wanda ya gani _(🤣 nasan ku ma kun gani ai? Tunda babu wacce bata zo Dinnern nan ba, kuma duk na ga inda kuka ɓoye kuna afa shinkafa da nama😲🤭)_ ita rigan da ta saka t.shirt ne blue Black, sai wandon sojoji da ƙaton Combat ɗin su, sannan ta ɗaura hulan kayan a saman kanta, shi kuma yayi shigan kayan nasu ne gaba ɗaya, sun yi mugun kyau gaskiya babu ƙarya, ko kaɗan RAUDHA bata nuna tsoro a wajen wasan nasu ba, duk abinda aka saka ta tana yi, duk da sosai take tsoron bindiga bare Harbin shi, amma wayewan ta ya saka ta ɓoye haka, sannan tana jin cewa ita Matar Soja ne a yanzu, _(🤣zata yi muku gori ne walle, ku auri soja akwai daɗi auren su 😜)_ don haka tsoro be kamace ta ba
Ray ɗin da kansa ya koya mata yanda zata yi Harbin, Yana tsaye a bayan ta, ya riƙe mata hannaye suka saita mutum-mutumin da aka ajiye musu, ta har ba
Sai shewa ake yi sabida yanda komi ya ba da kala, ya burge kowa na wajen.
A gurguje Please.. Haka dai taron ya tashi cikin ƙayatarwa. gida aka mayar da RAUDHA tunda ba yau za'a kai ta ba, sai zuwa gobe za'a wuce da ita Bayelsa, daga can kuma sai su dawo ita da Ray Kaduna wajen aikin sa, a can aka shirya mata gidan ta uban-uban su, duk da a cikin barikin sojojin ne inda yake zaune, amma kayan da aka zuba mata wayyo Allana, sai mun haɗu acan dai fans, ku waso Ido amma. 😊
Washe gari ƙarfe 09:00am jirgin su ya ɗaga zuwa Bayelsa, tare da Farida da Ramcy suka tafi, sai wasu mata biyu daga cikin dangin Daddy da yace aje dasu
Ray kuma zai taho ne zuwa anjima, don tare za su dawo da RAUDHA.
Koda suka isa, an yi musu tarba na girma, su kansu sun san cewa sun zo dangi masu karama da waye wa, ko a fuska ka kalle su ka san haka, ko kaɗan ba su da ƙyashi ko hassada a zuciyar su, gaba ɗaya kansu a haɗe yake, bare yanda suke girmama Ammee, komi suna iya mata don ganin farin cikin ta
A family house ɗin su aka soma sauke su, inda aka ware musu ɗaki guda tare da Toilet, aka zube musu abinci da duk abinda za su buƙata, tunda suka sauka Suhaima ta zo ta maƙale wa RAUDHA, sosai tayi farin ciki da kasancewar RAUDHA cikin dangin su, har ta kasa ɓoye murnan ta, sai washe baki take yi tana nan nan da RAUDHA, duk gaba ɗaya ta maƙale mata, ba ma ita kaɗai ba, har sauran ƴan matan gidan, tunda sun kai su uku ne ƴan matan.
Bayan sallan Asar su Farida suka soma haraman tafiya, shiyasa aka ɗauke su gaba ɗaya aka mayar da su gidan su Ray ɗin, inda Ammee da ƴan uwan ta suka yi musu tarba me kyau, suka mutunta su sosai
Ba su wani daɗe ba, Faruk ya kai su Airport, sai ga RAUDHA tana hawaye sanda za su tafi, gaba ɗaya sai taji ba ta ƙaunar tafiyar nasu, duk da sosai ta ba wa Ramcy tausayi, amma sai Ramcy ta dage tana ta mata dariya, don baza ta manta ba itama haka tayi mata, sai tsokanar ta take yi tana taɓa mata kumatu tana ci gaba da mata dariya
Sai da Farida tace, "Kin ga ƙyale ta dan Allah kar ki ɓaro mana abinda baza mu iya ba, kin san halin RAUDHA da taɓara, yanzu wlh sai ta birkice mana".
Langaɓe kai Ramcy tayi tana sake kallon fuskar RAUDHAN da yayi caɓe-caɓe da hawaye, ta cika fam ko motsi ba ta yi
"Allah Sarki my Besty, ki kwantar da hankalin ki yau ɗin nan za ku dawo ai, zuwa da dare zan saka Dear ya kawo Ni, kin ga sai mu sha hira".
Kallon ta tayi, da ƙyar tace, "da gaske kike yi?"
Gyaɗa mata kai tayi tana sake ba ta tabbaci
Da haka dai suka bar gidan RAUDHA bata sake wani maganar ba, illa kwanciya da tayi tana hawaye, sai da Ammee ta shigo ɗakin ta rarrashe ta, sannan tayi shiru, inda ta saka ta ta sake yin wanka ta kawo mata wasu tsadaddun kaya na musamman, baƙin less ne, ta saka, riga da zani ne kayan, duk gaba ɗaya daga zanin har ɗan kwalin ɗaura mata akayi, babu wanda ta iya da kanta, sosai kayan suka yi mata kyau, kasancewar ta fara shiyasa baƙin less ɗin ya yi mata matuƙar kyau, gyale aka yafa mata me ruwan Powder, daga saman kanta har zuwa gwiwowin ta ya kai mata, sannan ta saka Hill shoes, Ammee ta fito da ita zuwa parlour'n Uncle, inda yake zaune daga shi har ƴan uwan sa
Sosai suka yaba da tarbiyyan ta, suka saka mata albarka ko wanne fuskar sa cike da farin ciki, haƙiƙa sosai ta shiga zuciyar su, ko dan kyawun ta dole ne ka so ta.
Wajen magriba Ray ya shigo gidan, har zuwa bayan isha'i ba su haɗu da RAUDHA ba, tunda ita tana ɗaki a kwance, sai da Suhaima ce ta zo shi ne ta tashi suke taɓa hira, a tare suka yi sallan isha'i a ɗakin, inda Ammee ta shigo tace "mata ta kintsa za su tafi da Mijin ta" ta sha mamaki sosai, sabida ganin dare yayi, ai ya kamata ace sai da safe za su tafi, amma kuma bata ce komi ba, ta saka Shadda maroon Colour da aka sake kawo mata, sai dai ɗinkin doguwar riga ne da ya ji aiki sosai daga saman ƙirjin ta kawai, Suhaima tayi mata light make-up sannan ta ɗaura mata ɗan kwalin, irin me Steps ɗin nan, sai ta yafa mata farin gyale a kafaɗan ta, sannan ta ciro mata takalmin ta me tudu me haɗe da jakan sa, kalan Baby maroon Colour, sai ɗan ratsin fari a jiki, ƙasan takalmin kuma baƙi ne.
Tare suka fito Parlour inda suke murmushi dukan su, kasancewar Suhaima tana faɗa mata yanda tayi kyau ne, wai "Yaya Ray zai zauce idan ya ganta". Shi ne take murmushi itama tana taya ta
Tunda suka fito Parlour'n ya sauke idon sa kanta, kallon ta kawai yake yi tamkar idanun sa za su faɗo, shima sanye yake da kalan shaddar ta, yayi mugun kyau sosai
Ita ma bata hange sa ba, tunda gaba ɗayan su ne suke zaune a parlour'n, shiyasa tunda tayi musu kallo ɗaya ta ɗauke kanta
Ammee tace mata, "ta ƙariso wajen ta".
Inda ta zauna a gefen ta, Ammee na riƙe da hannun ta
Su Zannurain sai faman tsokanar ta suke yi suna ce mata "Matar Yayan mu".
Ita dai sai murmushi take yi
Sai da Uncle ya dakatar da su sannan suka yi shiru, ya soma musu nasiha daga ita har shi ɗin, sannan suka saka musu albarka har Ammee, suka yi musu addu'an zama lafiya har ƙarshen rayuwan su, tare da samun zuri'a ɗayyiba
Gaba ɗaya wajen suke amsa wa, ban da su da suke amsa wa a zuciyar su.
Har waje suka rako su inda za su shiga mota, RAUDHA da Suhaima suka rungume juna har da hawaye
Faruk ya ja motan, su kuma suna zaune a baya, tunda suka shiga ko motsi ba ta yi bare ta ɗago kai ta kalli Ray ɗin, duk da kuwa tana jin sanda ya lalubo hannun ta ya riƙe gam
Tafiya suka yi kamar na mintuna sha biyar, sai suka tsaya, horn akayi suka shiga wani gida, ashe a nan ɗin za su kwana zuwa gobe su wuce Kaduna, Gidan Ray ne da Uncle ɗin sa ya ba shi, ko da wataran sun zo a nan za su riƙa sauka.
Sai da suka fito sannan RAUDHA ta ware idanun ta tana kallon gidan, a ranta tana mamakin kenan ba Kaduna za su koma ba? Sosai gidan yayi mata kyau duk da babu wani yalwataccen haske, haraban gidan ba wani faɗi bane, amma zai iya cin motoci kamar biyu haka, sai kuma yanda aka yalwata ko ina da flowers masu ban sha'awa da abubuwan more rayuwa
Sanda suka shiga parlour'n ne, ai sai kallo ya koma sama, domin babu ƙarya, ba ƙaramin kuɗi Daddy ya kashe wajen tsara mata gidan nata ba, ƴar gatan Daddy kenan, gida biyu duk ita kaɗai, kuma an kashe kuɗi ba Ni da kuɗi ba, ɗakuna uku ne da Toilet a cikin su, sai Parlour da kichen tare da store, ko ina yayi kyau matuƙa tunda duk an cika su da kaya masu ban sha'awa, gaba ɗaya babu kayan Nigeria a gidan, shiyasa komi zai ba ka sha'awa da zaran ka kalla.
Tun a waje suka yi sallama da Faruk ya koma, su biyun suka shigo. Suna shiga ya sake riƙe mata hannu, hakan yasa ta juyo tana kallon sa tunda ita ce a gaba, murmushi suka sakar wa juna, inda ya matso kusa da ita yana faɗin, "alhmadulillah! Yau dai ga Pretty a gidan Captain Rayyan, sai godiyar Allah".
Murmushi kawai tayi masa, batare da ta ce komi ba idanun ta a kansa
Janyo ta yayi ya jingina ta a jikin sa, sannan suka taka har zuwa cikin parlour'n, ya zaunar da ita yana me zama gefen ta, hannun ta still ya riƙe yana me jan yatsun hannun, ita kuma tana bin hannun da kallo kamar yanda yake yi
"Ina son ki pretty, ban San ya zan kwatanta miki ƙaunar da nake miki ba a zuciya ta, amma kuma zan so ki bani dama domin nuna miki tsatsan sa a fili, ina fata Allah ya bar mu tare har ƙarshen numfashin mu".
"Amin Ƙalby". Tafaɗa tana kallon sa
Murmushi suka sakar wa juna kafin tace, "I love You more than you Ƙalby". Ta ƙare maganar da jingina a jikin sa
Hannayen sa ya saka gaba ɗaya ya rungume ta yana me sumbatar goshin ta, sun ɗau kamar mintuna biyar a haka, kafin yace, "Pretty ko kina jin barci?"
Ɗago kanta tayi tana kallon sa, kafin ta girgiza masa kai tana cewa, "na yi tunanin yau za mu koma Kaduna?"
Fuskar ta ya shafa yana bata amsa da faɗin, "a'a, Uncle ya ce mu zauna a nan sai zuwa gobe, sabida ba ya son tafiyan dare".
Gyaɗa kanta tayi tana me mayar da kanta ta sake ɗaura wa a kafaɗan sa
Ahankali ya matso da bakin sa setting kunnen ta ya raɗa mata magana, sai ta ɗago tana kallon sa, suka sakar wa junan su murmushi. Tashi yayi yana tayar da ita, sannan ya ƙarisa bakin ƙofa ya rufe, ya dawo ya riƙe mata hannu suka yi cikin ɗaya daga cikin ɗakunan
Koda suka shiga alwala suka ɗauro gaba ɗayan su, inda ya sauya kayan sa zuwa jallabiya, itama ta sauya zuwa riga da wando na barci, ta saka Hijab suka soma jero salloli, kawai don godiya ga Allah, kamar yanda Ray ya alƙawarun ta, duk randa ya mallake ta a matsayin matar sa, to fa a ranan zai kwana godiya ga Allah ne, duk da sosai yake jure buƙatar sa a gare ta, amma kuma soyayyar da yake mata ya fi rinjaye a zuciyar sa a bisa sha'awar ta, don dai kwana ɗaya kacal zai iya jure wa, ya cije don ganin be mata komi ba. 😆 Kaji masoyan asali 😍😴
Tun suna yi har barci ya soma fizgar RAUDHA, dole ta kwanta a kan daddumar ta soma barcin
Shi kuma ya ci gaba da yi har sai da ukun dare yayi, sannan ya ɗauke ta ya mayar da ita kan gado, yana me zame mata Hijab ɗin, a gefen ta ya kwanta yana ta faman kallon ta yana lazimi, tare da tsarkake Allah da yayi wannan kyakykyawar halittan, RAUDHA tana da kyau matuƙa.
har sanda aka kira sallah, sannan ya tashi yayi nafila, ya tashe ta suka yi sallan asuba, a tare suka koma barcin har zuwa safe.
Sai da Abubakar ya kawo musu breakfast sannan suka tashi a lokacin, shima be tsaya ba ya koma tunda ya gaishe su, saboda aiki zai tafi
Ƙarfe 09:00am jirgin su zai ɗaga, shiyasa suka yi saurin shirya wa suka karya suka baro gidan, suna hawa jirgi sai Kaduna garin gwamna Nasiru El. Rufa'i. Me aiki domin ci gaban al'umman sa. Ba ya bari a ci sai dai a gani a ƙas..
[4/14, 11:24 AM] نفيسة أم طاهرة: 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*MALLAKAR:* ✍️
_Nafisat Ismail Lawal Goma._
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*RAMADHAN MUBARAKH*🤲🏽🕌
2021.
.
*NOT EDITED* ___________________________📗
*SEASON FIFTY FIVE*
_______📖 Zan iya cewa komi na gidan nan ɗaya yake da wancan, sai dai banbancin colour da kuma haɗuwa, amma tsadan su ɗaya, wannan dai ya fi haɗuwa sosai, akasarin komi fari aka saka mata shiyasa yafi ɗaukar ido da burge wa.
A gajiye suka shigo gidan, don haka sallah suka soma gabatar wa na azahar da asar, sannan Ray ya aiki Drever'n sa don ya yo musu take-away, kafin ma ya dawo har RAUDHA ta soma barci, sabida ba ƙaramin barci take ji ba
Tashin ta yayi yace, "ta zo su ci abinci".
Daƙyar ta tashi tana ɓata fuska, gaba ɗaya tayi yaushi sabida barcin ya rufe mata ido, zama tayi gefen gadon, ta dafe gadon da hannayen ta tana me lumshe idanun ta
Ahaka Ray ya fito daga Toilet ya sake tarar da ita har barci ya soma ɗaukar ta, ruwan hannun sa ya yarfa mata yana me faɗin, "Baby wake-up mana".
Buɗe ido tayi ta ɗan kalle sa kaɗan da idanun ta da suka sauya kala, sai ta ɓata fuska tace, "Ka bar Ni inyi barcin don Allah, ba na jin yunwa".
"Ban yarda ba, ke dai kawai ki ce barci kike ji, amma ba wai ki ce ba kya jin yunwa ba. miƙe kin ga idan kin ci sai ki koma ko?" Yayi maganar yana me lallaɓa ta
Turo baki tayi tana sosa kanta, sai kuma ta miƙe tana nufan ƙofan zata fice
Riƙe ta yayi suka fita Parlour, ya zaunar da ita saman kujera, sannan ya wuce kichen don ɗauko Plate
Jingina tayi da jikin kujeran tana me lumshe idanun ta, har ya dawo ya sake abincin bata motsa ba, shi da kansa ya bata abincin tunda ta ƙi ci, yana ta faman lallaɓa ta, sai daga baya ne ta Ware sosai taci tunda tana jin yunwa
Sai da suka gama yace mata "ta koma ta kwanta, shima fita zai yi".
Bedroom ta koma ta kwanta akan gado, babu jima wa barci ya ɗauke ta
Shi kuma sai da yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya, gezna ne me ruwan kore, amma Light ne, ta sha aiki sosai har da babban rigan ta, sai dai be saka babban rigan ba, ya murza hulan sa mu haɗu a banki, sannan ya feshe ko ina nasa da turaruka, sak ya fito a Angon sa sai ƙyalli yake yi, fuskar sa na fid da annuri, keey ɗin mota ya ɗauka tare da wayan sa, ya matso gadon yayi mata kiss a leɓen ta, sannan ya shafa kanta yana murmushi a ransa yana aiyana abubuwa da dama. Fita yayi ya hau motan sa ya nufi gidan su RAUDHA
A can ya wuni wajen Daddy, har magriba be dawo ba, sai da RAUDHA ta kira sa tana masa shagwaɓan "ya bar ta ita kaɗai" sannan ne yayi haraman taho wa, da zai dawo sai da ya biya ya siya kazan amarcin sa, don yau so yake yi ya zama cikakken Angon sa
Da fara'an sa ya shigo gidan, inda ta tarbe sa tana me rungume sa tana faɗa masa "how much she missed him" kafin ta amsa kayan hannun sa tana me ƙara masa sannu da zuwa har da duƙawa alamun girmamawa
Sosai Ray yaji daɗin tarban nan da tayi masa, har ya kasa ɓoye wa ya janyo ta jikin sa yana cewa, "Baby ashe kin iya tarban miji haka? Gaskiya zan sha mamaki ashe, gaba ɗaya ina miki kallon wacce dole sai na koya mata irin waɗannan abubuwan na kula da miji".
Kallon sa tayi ta ɓata fuska kafin tace, "kenan kana nufin ban iya ba?"
"No Ina nufin dai abubuwan nan na Hausa wa nake son koya miki".
Taɓe baki tayi tace, "Ok na gano ka, wai don na amshi kayan hannun ka?"
"Yes ashe kin gane". Yayi maganar yana murmushi
Turo baki tayi, kafin ta kamo hannun sa tace, "to amshi kayan ka, bazan sake ba".
Dariya yayi sosai yana son ƙwace hannun sa da take tura masa ledan sai ya amsa, cikin dariyan yace, "sorry Baby, bazan sake ba, wlh suɓutan baki ne, ai na san duk wanda ya koyi ilmi dole zai san wannan, amma kuma.."
"Amma kuma me?.." tayi maganar tana tsare sa da ido
"Bar shi kawai ya wuce, bari in je inyi sallah ana kiran Isha'i, ki je ki ajiye ledan please".
Bata ce mishi komi ba ta juya da ledan a hannun ta
Shi kuma ya fice zuwa Masallaci.
🔵🔵🔵
A wannan dare ne Ray ya tabbatar wa kansa, RAUDHA cikakkiyar mace ce, ba kamar yanda yake mata kallo ba, be taɓa tunani ko a mafarki zai iya samun ta a yanda ya same ta yau ba, sai ga shi ya sha matuƙar mamaki, har kuka yayi sabida nadaman abinda yayi mata, tabbas yau yayi dana-sani, dana-sanin abubuwan da yayi mata, da kuma sanya zargin ta a zuciya, ba don soyayyar ta tayi masa kamu ba, da tuni ya daɗe da rabuwa da ita, duk a sabida yana mata kallon mazinaciya
Wannan ranan ta zo masa a matuƙar farin cikin da bazai taɓa manta ta a kundin rayuwan sa ba, ya kuma sake neman yafiyan ta sosai, tare da nuna mata nadaman sa
Dama wannan ranan take jira, kuma ga shi ya zo mata yanda take so, yau Mijin ta zai dena mata kallon ballagaza har a cikin zuciyar sa, ko da be nuna ba, tayi imani da Allah duk da yayi mata alƙawari, da ace ba haka ya same ta ba, dole sai ya riƙa kallon ta da abun, kuma hakan zai iya kawo saɓani a auren su, abinda yasa ta sake amince wa da auren sa, saboda ta nuna masa kuskuren sa, ta san cewa da ta aikata Zina kafin auren su, to, baza ta taɓa amince masa da auren su ba, domin kuwa ta san zargi shi zai riƙa yawo cikin auren su.
Alhmadulillah zaman auren su suna gina ta ne ta santsan kulawa da nuna tattali da soyayya, Ray ya dage yana ta gurzan Angon cin sa yanda yake so, hutun sati biyu aka ba shi a wajen aiki, kullum yana gida be fita ko ina, yana liƙe da Matar sa har sai da ya cinye kwanakin nan, sannan ne ya soma fita, kuma kullum duniya aika wa yake yi ayi musu take-away, sai daga baya ne aka turo Saude don ta riƙa mata aiyukan gidan, shiyasa RAUDHA babu abinda take yi yanzu sai zaman hutu da kuma tattalin mijin ta, duk hanyar da tasan zata faranta masa tana yi sosai matuƙa, duk da a yanzu tana buƙatar koyan girki itama don ta riƙa mishi, sabida ta san ladan da ake samu, shiyasa take kwaɗayin komi na gidan ta ace ta iya, a sannu- a sannu Saude take koya mata wasu abubuwan, irin su gyara gado da kunna Kuka gas, da dafa ruwan zafi, coz tunda take bata taɓa shiga kichen da sunan girki ba, bata ma san yanda ake kunna Kuka gas ɗin ba, sai yanzu da ta soma koya. Alhmadulillah tana ɗan gane wa kaɗan, duk da kasancewar ta me saurin gane abu, amma kuma sosai take shan wahala, domin sanda aka soma koya mata gyaran gado, sai da aka shafe wajen sati biyu ana abu ɗaya, daƙyar ta samu ta iya, idan kuma tayi dole sai ka gane ba gwana tayi ba.
Shi Ray dariya yake yi duk sanda ya zo ya tarar ana koya mata irin waɗannan abubuwan, wai kamar ta har shara sai an koya mata, to riƙe tsintsiyan ma ba yanda ake yi take yi ba, to ana haka ne ta soma ciwo gadan-gadan, faraɗ ɗaya ciwo ya kamata me tsananin gaske, wanda har sai da aka dangana da asibiti, duk a tunanin su ciki ne, amma kuma abun mamakin ba shi ne ba, kawai ciwo ne dai take fama dashi, daga tace ciwon kai, sai ta ce cikin ta na mata ciwo, to duk dai ba'a yi tunanin wani abun bane, haka ake kula da ita, tsawon sati ta ɗan samu sauƙi kafin suka koma gida
A ranan da suka koma kuma, sai ga shi cikin ta ya murɗe mata da ciwo me tsananin gaske, lokaci ɗaya jini yayi ta zuban mata
Hankalin Ray ya tashi tsantsa, haka ya sumgume ta sai asibiti, abun mamaki da al'ajabi, wai ɓari tayi, su kan su likitocin sun sha mamaki, domin kuwa basu gano tana ɗauke da ciki ba, amma kuma sai ga shi ciki suke gani tayi ɓari
Hakan da Daddy yaji, sai kawai tunanin sa ya basa tabbas akwai matsala, dole su dangana dana Islamic, ko za'a iya gano abinda ke faruwa. Malamin da suka nema mata magani a baya shi suka koma masa, kuma shi ya basu magani a wannan karon, domin ce musu yayi, "tabbas har yanzu akwai aljanun nan suna bibiyan ta, kuma sun yi alƙwarin sai sun cutar da ita, kuma su ne suka ɓoye cikin, daga ƙarshe suka zubar mata, domin su ne suke saka ta ciwon nan, dole sai sun tashi tsaye da yin addu'a da neman magani, ta hakan ne kaɗai za a iya tsira daga kaidin su".
To tun daga ranan, ba su zauna ba, an ci gaba da nema wa RAUDHA magani, sannan itama tana yi sosai, tana kiyaye duk abinda zai jawo su gare ta, sallan dare kuwa tun bata saba ba, idan Ray ya tashe ta su yi, har yanzu ta saba, tare suke raba dare suna ibadan Allah, sai ga shi har azumin Litinin da Alhamis idan ta samu iko tana yi
Alhmadulillah sun ga sauyi sosai, domin lafiya yanzu babu abinda ke damun RAUDHA tunda ta samu wannan cikin, bata ƙara yin ciwo ba, har sanda ya soma girma suka soma zuwa awo
A lokacin ne kuma Ramcy ta haihu ɗiya mace, zo ku ga murna wajen RAUDHA tamkar ita ce ta haihu, musamman yanda ranan suna suka bata bazata, yarinyan taci sunan ta RAUDHA, tayi farin ciki tsantsa har da kukan ta, tabbas ta san cewa Ramcy na matuƙar ƙaunar ta, baza ta taɓa yin ƙawa kamar ta ba, duk da a yanzu ta zame mata ƴar uwa rabin jiki.
Abubuwan da akayi a sunan RAUDHA, da suke kiran ta, Little RAUDHA, ba ya faɗuwa, Daddy, Suhaib da kuma Ray, sun Yi bajinta sosai a sunan nan, babu abinda basu yi ba, duk abinda ake wa ƴar gata Ramcy da ɗiyar ta sun samu, ita kanta RAUDHA abun da tayi ba a magana.
Wata huɗu da haihuwar Ramcy, itama RAUDHA ta haihu ɗiya mace, yarinyan sak Mahaifiyar ta, tamkar dai tayi kaki ta tofar, sai dai ita bata da irin hasken nan jawur tamkar zabiya irin na RAUDHA, hasken ta irin na Ray ne. Ranan suna taci sunan Maman RAUDHA, wato Ruƙayya suna kiran ta Iman.
Rayuwa kenan, sai ga RAUDHA da ɗiya, tamkar dai ba ita ba idan kuka duba rayuwan ta na baya, sai ga shi itama ta samu wacce zata riƙa wa faɗa, domin dai yarinyan tunda ta soma wayau halin ta ya bayyana tamkar RAUDHA, ko kaɗan ba ta ji yarinyan, ga taɓara kuma baka isa ka hana ta ba, tana da taurin kai irin uwar ta, don har ta ƙere ta tunda akwai ta da zuciya, yanzu da za su yi mata faɗa, ta dinga kuka kenan har sai ta kwana tana naci, kuma baza ta ci abinci ba saboda ita a ganin ta sun ɓata mata rai, gaskiya Rayyan da RAUDHA suna fama da Iman, sai dai nema mata shiriya suke wajen Allah, tare da dage wa wajen sun ga sun bata tarbiyya me kyau.
Shekarun ta huɗu cif, RAUDHA ta sake haihuwa, wannan karon namiji ne, inda ya ci sunan Uncle, wato Hassan, suna kiran sa da Aslam. Watan shi bakwai sai ga RAUDHA da wani cikin, nan RAUDHA ta haukace "wai baza ta ƙara yarda ta haihu yanzu ba". Tun Ray na lallaɓa ta har dai ya gaji ya kai maganar wajen Daddy, shima Daddy duk rarrashin duniya yayi mata akan ta bar cikin, amma ina ta ƙi, wai bata san zancen ba, tunda a lokacin so take yi ta koma school, sannan tana son soma aiki a Companin Daddy da ya buɗe domin ta, ƙaramin Company ne irin kayayyakin mata na kwalliya, da suturu, har da na ƙananan yara duk akwai, kuma nan ba da daɗe wa ba ake son kawo injina waɗanda za su iya haɗa kayayyakin a Companin, ba sai an je ƙasashen waje an siyo ba, tunda dama daga can ake kawo komi, kyauta Daddy ya danƙa mata, inda aka saka wa Companin sunan Ta, *RAUDHA M.M Company.*
Ƙarshe dai sai da suka yi faɗa sosai akan wannan maganar, RAUDHA fa sosai ta tubure sai ta zubar, har tayi yaji ta koma gida
Ran Daddy be taɓa ɓaci ba akanta, sai wannan karon, amma kuma sai ya danne yayi mata nasiha tare da nuna mata illan yin hakan, amma tamkar zuga ta ake yi, har Suhaib sai da ya zo musamman ya bata haƙuri ta koma gidan ta, ta haifi cikin ta, ganin dai rarrashin bazai mata ba, dole suka nuna mata ɓacin ransu, kuma Daddy yace, "muddin ta bari cikin nan ya zube, ko ba da sanin ta bane, wlh sai yayi mummunan saɓa mata, daga ranan zai cire hannun sa a komi nata".
Ba ita kaɗai ba, har ta Suhaib yayi mamakin furucin Daddy, amma kuma babu damar magana tunda tuni ya bar wurin da ɓacin rai.
A ranan RAUDHA ta haɗa komi nata ta koma gidan Ray, dama acan ta bar Iman, sai ta taho da Aslam. A ranan kuwa kowa sai da ya ga fushin ta, daga yaran har uban nasu, domin gaba ɗaya ta ɗauke wa Ray, ko magana ba ta masa, Iman kuwa duk ɓarnan da zata yi, kamata take yi ta duka kamar jaka, haka ma Aslam, sai ya gama jiga ta da kukan yunwa kafin take kama shi ta bashi nono ya sha, a ranan ma ta sami Ray yana zaune a ɗaki, tace masa, "gwara ya nemo masa abinci, don daga yau baza ta sake shayar dashi ba" haka dai ta ƙarishe haukan ta ta tafi, duk dai neman hanyar da za su yi faɗa tsiya-tsiya take so
Shi Ray idanu kawai ya zuba mata yana kallon ikon Allah, domin wlh tausayi take ba shi tsantsa, har yanzu gani yake yi aljanu ke juya mata ƙwaƙwalwa wani lokacin, domin abubuwan da take yi me hankali kamar ta bazai yi ba, shiyasa ya zira mata idanu, duk hanyoyin da ta ɓullo na tsiyan ta, ba ya biye mata.
A haka rayuwa taci gaba, inda har ta samu ta haihu ɗiya mace, har kuma lokacin ba su shirya ba, domin har yanzu RAUDHA gani take yi duk abinda Mahaifin ta yayi mata a wancan ranan laifin Ray ne, inda be kai ta ƙara ba, babu ta yanda mahaifin ta zai mata abinda be taɓa mata ba
Yarinya taci sunan mahaifiyar Ray, Hansa'u, za su kira ta da Islam.
A taƙaice dai daƙyar Ray ya samu suka shirya da RAUDHA, inda suka koma kamar da, amma da sharaɗin dole za su yi family planning, sai nan gaba za su sake haihuwa, babu yanda zai yi haka ya amince mata, tunda dai yana ƙaunar ta.
Alhmadulillah yanzu komi ya wuce, inda RAUDHA ta soma zuwa makaranta, kuma tana zuwa Company, kasuwanci sosai take yi, a gida da kuma wajen aiki, lokaci ɗaya Allah yasa mata albarka, sai ga shi ta zama wata Hajiya, tuni ta jawo Ramcy cikin Companin, tare suke yin komi, kuma tare suke saka hannun jarin su, itama yanzu Ƴaƴan ta uku ne, duka mata.
Fannin Farida ma yanzu ta koma aikin ta, tare suke zuwa da Suhaib, yanzu yaran su haɗu ne su ma, ban da Haneep da Abdul, yanzu sun ƙara haihuwar me sunan Maman Suhaib, suna ce mata Ummee, sai Meenal Auta, wannan sunan sun saka mata ne kawai saboda suna so, amma ba sunan kowa ba ne.
*TAMMAT BILLAH. ALHMADULILLAH! ALHMADULILLAH!! ALHMADULILLAH!!!*
_Duka-duka anan na kawo ƙarshen littafi na me suna RAUDHA, abubuwan da na faɗa dai-dai Allah ya bani ladan su, abubuwan da na faɗa ba dai-dai ba kuma, Allah na roƙe ka, ka yafe min, albarkacin wannan wata me falala. 🙏🙏_
*RAMADHAN MUFEEDA YA IKHWANY.*
*SAƘON NA MASOYA NA NE*
_Bazan taɓa manta wa daku ba, ina alfahari daku sosai, domin idan baku to ba na jin akwai Ni nima, Masoyana ako ina kuke, Ni taku *JIKAR LAWALI* ina ƙaunar ku, Allah ya bar mu tare._
_sai mun sake haɗuwa a sabon littafi na *NAFEESAT RETURN* Nan da bayan sallah. Bissalam._
0 comments:
Post a Comment