fu'ad Muhammed argungu d'an asalin karamar hukumar argungu ne dake jahar kebbi, cirani ne yashigo da kakaninsa garin lagos , wato malam musa da mai d'akinsa halima da yaronsu muhammed , inda sukayi masauki a unguwar g'begulori dake karamar hukumar agege, fu'ad bakabe ne daya fito daga cikin kabawan asalin jahar kebbi ,yayinda danginsa gbdy suka kasance talakawa ne tulis .
tunda malam musa ya dira a garin lagos bai ta'ba zama daidai da rana daya da sunan hutu ba, kullun yana fita neman abinda zai ci da iyalisa ,ba wata sana'a malam musa yake ba illa aikin dako cikin kasuwar matuwaf zuwa ketu ,Allah yasanyawa aikin dakonsa albarka domin basu ta'ba neman abinda zasu ci sun rasa ba ,kuma tun daga kan muhammed Allah bai sake basu haihuwa ba ,dan haka suka d'auki soyayyar duniya suka d'aura akan tilon d'ansu da Allah ya basu ,duk da kasancewarsu talakawa amman hkn bai sa sunyi sakaci da tarbiyar yaronsu ba ,suna iyakacin bakin kok'arinsu akan ganin sun inganta rayuwarsu data d'ansu ,domin sunyi kok'arin sanyashi makaranta gwanati dan samun cigaban rayuwarsa .
"haka rayuwarsu tacigaba cikin talauci da babu har yasamu ya kammala secondary school dinsa a ikeja high school daga nan bai cigaba da karatu ba , sai dai ya Kan fita buga bugarsa duk inda yaga aikin karfi zaiyi fassakare ne wanki da guga zaiyi . Muhammed ya taso tare da mahaifansa har zuwa girmansa , kafin Allah ya had'ashi da ramlat, wace suka kasance diyar makotasu ce ,sukayi aurensu bisa amana da soyaya.
fu'ad shi kad'ai iyayensa suka samu ya tsaya a duniya ,dan haihuwarsu biyar yaran suna mutuwa akansa suka samu ya tsaya wanda sanadiyyar haihuwarsa, mahaifiyarsa
ta rasu ,a cewar mutane bama tasan abinda ta haifa ba ta cika, sai rikonsa ya dawo gurin kakaninsa, lokacin daya kai shekara bakwai mahaifinsa ya rasu sakamakon ciwon hawan jinin daya kamu dashi a tun mutuwar matarsa ramlat, ba a d'auki wani lokaci me tsawo ba malam musa shima yace ga garinku. gidan ya saura daga halima sai fu'ad.
fu'ad yayi karatunsa na primary har zuwa jami'a ahmadu bello, bisa tallafi na gwanati da taimakon Allah dana kakarsa inda ya karanci business administration.
,fu'ad ya sha matukar wahala gurin karatunsa saboda rayuwar babu da suke ciki ,da taimakon scholarship dana abokai da tsohuwar kakarsa halimatu yasamu ya kammala karatunsa da kyar ,bayan kamala karatunsa da bautar kasa yashiga wahalar rayuwa sakamakon rashin samun aiki , kafin had'uwar sa da mom dinki ya kwashe shekaru sama da shida yana zaman banza batare da yasamu aiki ba duk da kyawun da takardunsa sukayi.
" sun had'u da me'ad ne
A wata safiyar litinin .
labari ya karad'e koina akan zance batakashin da'akayi a garin lagos duk gidan tv da radio daka kuna a lokacin fuskar ACP Aliyu rano ake nunawa da tawagarsa rike da bindigunsu suna harbi .
ni da fu'ad ne muka shiga cikin wani d'an madaidacin shago inda muka saba yada zango ,muna shiga na ja na tsaya ina murmushin jin dadi,yayinda fu'ad dake tsaye a bayana yasa hannusa ya buge min keya "banza kawai munafukin Allah ,gulma nacinka ko?
bud'ar bakina sai cewa nayi "abokaina yau fa fu'ad yayi kasuwa da ala'mun shima yau ya fad'a tarko kauna nakarasa mgnr ina kwashewa da dry har da tafa hannu.
"kajika da wani zance iska inji cewar sauran abankanmu, sudais, Abdul da kabeer .
kabeer yacigaba da magana idanunsa na kan kallon tv "yayi kasuwa fa kace kmr wani kayan marmari.
"allah kuwa yau naga qunjinsa domin ya had'u da yarinyar da bazai iya hakura daita ba.
" dan Allah malam karka damemu zauna ka kalli abinda duniya take ciki.. zaro ido nayi sa sauri lokacin da idanununa ya sauka akan TV "kai kai ai naga wannan mutumi da'ake nuno yanzu , wannan batakashin da kuke kallo agabana fa akayisa ,shi dai fu'ad bai ce komai ba yakarasa kan doguwar kujera ya zauna yana duban abinda ake nunowa a TV wanda agabansu komai ya faru.
"kana nufin ka ganshi inji cewar kabeer?
"Kwarai da gaske na ganshi da idanuna, "kai dai wallahi babban makaryaci ne ,yau kuma da karyar daka zo mana kenan?inji cewar abdul ..
"Na girgiza kai tare da kallon fu'ad ,"fu'ad dan girman allah kayi magana zasu fi yarda da maganarka saboda muna tare da kai lokacin da abu ya faru .
fu'ad na jinsa ya sake mikewa akan doguwar kujera yayi kwanciyarsa tare da lumshe idanunsa duka , ya d'aura hannunsa ya dafe goshinsa dayan hannunsa na saman ruwan cikinsa, kasancewarsa marason hayaniyya.
duk surutun danakeyi banza sukayi dani suka cigaba da sauraron labarin da'ake watsowa suna kur'ba ruwan Lietop.
" kunga wallahi da gaske nake kai dai fu'ad wallahi banza ne ,kana ji ana kokarin meidani makaryacin karfi dayaji amman kayi shiru.
"me ka keson nace fu'ad ya fadi hkn atakaice batare daya bud'e idanunsa ba.
"ka gani ba dan Allah kayiwa mutane shiru, shi kansa fu'ad din bashi da tabbas da zance dake fitowa daga cikin bakinka duba da yanayin da yayi magana to yaya kake son mu dake zaune agida mu yarda bayan karyar abincin ruhinka ne daka kashigo fa zance yarinya kake yi ,cikin minti biyu kacal kasanyo wani zance daban .
"eh naji karya abincin ruhina ne, amman wallahi wannan zance ba karya bane ,koda nasaba yi muku karya ,ku matso kuji yadda abun yakasance nakarasa maganar ina me zagayo na zauna akan table ,gabayansu suka zagayeni " muna jin ka fad'i kuma wallahi kana somawa da karya zan gane ka kuma san karshen abun..inji cewar kabeer.
"ina zaune wancan dan iskan yace na rakashi inji din ciro kudi ,muna isa aka fara ruwan sama tare da walkiyya.. nakarasa mgnr ina zabgawa kabeer duka ajikinsa "kai dan Allah malam da baki ake bada labari ba da hannu ba "yi hakuri abokina abinda idanuna suke hangomin ne abun birgewa ,tsawon lokaci muna tsaye har ruwan yasoma tsagaitawa mukayi tunanin mu fita saboda hango inuwar mutun tsaye"bude kofarmu ke da wuya sai naga wata kyakkwar yarinya kirar Japanese tsaye cikin doguwar rigar har kasa hannunta rike da lema ,kyakkwa ce yarinyar sosai ,ku tamabayi fu'ad dan lokacin na lura har yafini gigicewa akanta, amman sai naga ya waske ita kuma yarinyar idanunta na kansa ta tsura masa ido tana kallonsa, bud'e bakin yarinya keda wuya tace "sannu amman gsky kunjima da yawa sai wani zarar kudi kuke kmr wad'an da zaku cire kudin bank din duka.
nayi saurin cewa "dan Allah kiyi hakuri ai tuni muka cira , tsayawa mukayi domin fakewa ruwa ,amman bamu aron lemarki sai mun d'an tsaya daga waje ke km sai shigo idan kin cira sai mu dawo mu tsaya ana .
"a tunanina ni zatabawa lemar tunda ni nayi mata magana ta fahimta , amman sai naga ta mik'awa wancan dan isakan lema, ya nuna inda fu'ad ke kwance ,in dai takaice muku ko damuwa da kulawar data nuna masa bai yi ba ,sai ma zagayeta da yayi ya wuce yayi gaba ya tsaya tare da tura hannunwasa duka cikin aljihun wandonsa , ina lura da yadda yanayin yarinyar ya sauya, ba dan taso ba ta miko min lemar wanda kad'an yarage hannunmu bai had'e da juna ba, na matsa mata tashiga, ni kuma na fito na tsaya ina karewa halitar jikinta kallon , ina gaya muku kywaun yarinyar ya had'u sosai.cikin mintunan da basu wuce goma ba ta fito idanunta akan fu'ad ,sosai fa kura masa ido tana takowa zuwa inda yake tsaye.
cikin hk ruwan saman ya tsaya cak sai kuma harbi takoina a harabar gurin, harbi fa sosai ban san yadda akayi ba sai dai ganin nayi fu'ad ya kamo hannuta sai ga yarinyar manne da kirjinsa nan take suka tsurawa junansu ido suna kallon junansu, wanin harbin yasa tayi saurin shigewa jikinsa gabadaya domin neman mafaka.
cikin minti biyu kacal duk ilahirin gurin ya har gitse, jamar dake wucewa a gurin bubu wanda ya damu da halin da kowa yake ciki, kowa gudun ceton ransa kawai yake saboda gabadaya gurin ya hargitse da k'arar harbi, police na harbi ,y'anta'ada na meida musu .
"ai in gaya muku na rud'e tare da gigicewa amman fu'ad da yarinyar nan ko ajikinsu kallon junansu suke karasowa garesu nayi ina girgiza fu'ad domin shi nake da yancin tabawa, nayi sa'ar ya dawo cikin haiyacinsa amman ita yarinyar ruhinta yayi nisa akansa ,girgizata fu'ad yasoma yi amman ina bata ma san yanayi ba, cikin rud'u ya rike hannunta ya kwasa aguje yasoma gudu daita, ganin harbin na sake yawa, sannan yana kiran sunana ,ni kuwa daman tuni na boye bayan inji din cire kudi ina kirma..
"kusan awa daya ana batakashin tsakanin 'yanata'ada da police har zuwa sanda acp aliyu rano yayi nasarar harbe wannan mutumin a kirji sannan komai ya lafa gurin gbdy ya turnuke da hayaki daya bayan daya mutane suka soma bayyana fuskarsu cike da matsanancin firgici daga mubuyarsu, ni kuwa sai ware ido nake naga ta inda fu'ad zasu fito, ahankali sai ga fu'ad da yarinyar nan makale da juna sun fito daga mabuyarsu aiko gama bayanarsu ke da wuya sai agaban acp wanda naji yace"a'a me'ad me km kike yi anan ?
hankalinta kwance tace "uncle nazo cire kudi ne ina fatan babu abinda yasameka? ta fadi hkn ne saboda ganinsa rike da hannunsa ga jini na tsiyaya alamun an harbeshi .
" ina jin dai lafiya kalau nike me'ad, waye wannan da kuke tare dashi ?
da sauri ta juyo gefenta fu'ad tagani tsaye agefenta hannunwansu malake cikin juna ,jin Abind acp yace yasa fu'ad yin sauri zare hannunsa cikin nata yana shafa sumar kanshi .
d'an runtse idanunta tayi kana tace "amm bansashi ba ucnle ,yanzu muka had'u dashi ta juya tana kallon fu'ad kmr zata cinyeshi muryata a sanyaye "tace sunana me'ad nagode da taimakona dakayi.
"muryarsa a dake yace ni kuma fu'ad karki damu ya juya ,naga yasoma waige waige ala'mun yana nemana, ita kuma tabishi da kallo yayinda acp aliyu yakira daya daga cikin yaransa "md .
"na'am yallabai .
" taimaka ka'ajiye min wannan yar tawa a gida.
"ok yallabai kasa daga kafafunta tayi agurin, tacigaba da kallon bayan fu'ad .
ina kallonta, jiki a sanyaye tashiga bayan wata hadadiyar mota kiran toyata camry .
Ina kawowa karshen labarin nace ni dai dan Allah ku gaya masa idan bai sonta ni dai ta min, ina sonta kuma aurenta zanyi, aikuwa suka ce me zasuyi ba dariya.... "kai wallahi bazan ne a gbdy labarinka fu'ad take so bakai ba ,koda yace baya sonta kana tunanin zata soka ne?
take na marairaice murya da fuska "ni dai ku taimaka ku tambayar min shi idan bai sonta ya tsaya min na aureta, wallahi dagani yar babban gida ce kunga motar da za'a kaita gida dashi kuwa , kuma dagani akwai halaka me karfi atsakaninta da acp Aliyu rano..
"kai dan Allah malam rabudamu da wannan shirmen banza suka soma kokarin watsewa su barni ,nayi saurin kamo hannun sudais, kai ma tafiya zakayi kabarni?
"Kai rabu dani, idan kana son yarinyar da gaske kawai ka nemi gidansu Dan gsky nasan fu'ad ba sauraranta zaiyi ba ,dan shi bashi da lokacin mace ,mata nawa suka nuna suna son shi Amman yaki?
********
bangare me'ad kuwa zuciyarta ce ke mugun buguwa a tun sanda tashiga bayan motar tare da hasko mata kyakkwar fuskarsa "tun datake bata ta'ba had'uwa da saurayin daya tsaya mata arai ba kmr shi, sai dai daganin zai yi jin kai da girman kai tattare da isa.
zaune suke su uku sajida misna hailat , sun mugun tsurawa TV plazma ido dake manne da bango suna kallon batakashin da'aka tafka tsakanin 'yanta'ada da ma'aikan sack a dapemu express way dake jahar lagos "barkanmu ,a yau anyi musayar wuta tsakanin 'yansanda ,da 'yanta'ada an samu nasarar harbe wani dan ta'ada me hatsari, acp aliyu rano da jamiansa su sukayi nasarar harbe nabel wanda ya kasance babban dan ta'adar da jamian tsoro suka dade suna nemansa a fadin jahar nan.
"yeeeeee babana yazamo zakaran gwaji..... sajida tasoma murna har da tsallenta "nasan kwanan nan za'ayi wa babana k'arin girma...murna take sosai tare da rungume misna dake kusa daita "gsky na taya dad dinki murna sosai inji cewar misna , hayaniya ce ta kaure atsakaninsu kowanensu na fad'ar albarkacin bakinsu.
me'ad tashigo hadadden parlour'n gidan wanda ya k'awatu tamkar da tayis akayi ginin ,gashi an zagaye shi da manya furanin.
hannuta rike da karamar jaka wace bata wuce a sakalata a tsintsiyar hannuta ba tana juyi sanye cikin doguwar rigar " kawayena yau na had'u da wani saurayi kuma ko wallahi kyakkyawa gaske ne kalar launi danafi so.. takaraso garesu tana murmushin jin dadi "kunji aunty dan allah da wata magana ana labari da d'umi d'uminsa ke kuma kina labarin wani saurayi , "dan Allah malama kiyiwa mutane shiru had'ad'd'e ne fa sosai, Allah ina gaya muku duk fadin garin nan babu me kyawumsa ta karasa fad'ar hk tana sake juya jikinta .
"haka zakice tunda zuciyarki ta yaba dashi ba ,da baki yaba dashi ba duk kyawunsa sai kin nemo makusansa" kmr kinsani kuwa inji cewar misna .
"wai ina miki wasa ne suhailat, ko dake nake maganata? ta fad'i hkn tana tsaki sannan ta fuskanci sajida da misna.
"ku kuma daku fa nake mgn amman kuka min shr , ba ma zaku saurareni ba ,kuna can kallon kwazon da acp yayi "ke dai bari me'ad Allah ina cikin jin dadi yau ,ina ma mama tana raye ta dinganin irin cigaban da baba yake samu, wannan furunci da sajida tayi yasa me'ad kasa cigaba da tsayuwa a gurin ta nufi hanyar d'akinta tana magana "Allah ya jikanta sai dai ki shiyawa jinyar dad dinki bayan kingama tayasa murna k'arin girman da zai samun saboda 'yanta'ada sun harbeshi .
da sauri sajida ta mike jikinta na rawa tabiyo bayanta atare suka shiga dakin "da gaske an harbi dady?
"ke baki lura ba, bakiga ya dafe hannunsa na dama ba?
"ina tunanin anan aka harbe.......
ai sajida bata jira jin karashen zance ba, tayi waje aguje tana kiran layin dad dinta, tayi sa'a ya d'auka "hello dady..
"sajida kina lfy?
" ina lafiya dady kana ina?" yanxu me'ad ke gaya min wata mgn da gaske ne 'yan ta'ada sun harbeka?
"gaky ne sajida ,duk boyewar dana yi ashe ta lura, to dai ki kwantar min da hankalinki, yanzu haka an cire min harsashi , mu had'u a gida, kashe wayarta tayi tare da bud'e murfin motata tashiga ta bar gidansu mead a guje.
mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 42 to 44
......Ahankali malik ya sauke kwayar idanunsa akan NASREEN dake kwance ajikinsa ,wacce bacci yasoma kok'arin d'aukarta amman son jin labarin had'uwar iyayenta ya hanata runtsawa .
shiru malik yayi yana dubanta batare da yacigaba ba, ya d'auki sama da minti goma a zaune kawao yana kallon NASREEN cike da tausauawa, yarinyar tana bukatar kulawa takowani bangare, amman tarasa shirun da NASREEN taji yayi yawa ne yasa ta, bud'e idanunta dake runtse taki sunansa "Uncle malik continue now.... kacigaba ina son jin komai, domin kai kad'ai ne zaka iya 'bata lokacinka ka gaya min.
"NASREEN ...ya kira sunanta a sanyaye "na'am unlce "kwalkwaluwarki bazata iya d'aukar sauran labarin ba.. "zan iya uncle am getting to 10yrs now babu abinda zaka fad'a da bazan fahimta ba.. ina jin tausayin dad dina dayawa, ina son nasani wani abu akansa takarasa maganar tana meida kanta bisa cinyarsa..
naunayen ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "daga bangaren fu'ad da me'ad babu wanda bansan halin dayake ciki ba, akoda yaushe muna tare da fu'ad, haka me'ad duk inda tasanya kafa ina biye daita sai dai a iya nan zan tsaya ... ya d'auke kanta akan cinyarsa ya meida kan karamin kushin din dake jingine da kujera, sannan ya mike tsaye yana duba agogon bangon parlour'n karfe tara ta wuce da wasu 'yan mintunoni, wayarsa ya ciro daga gaban aljihun gaban rigarsa yana kokarin neman layin fu'ad, sai gashi ya fito "yauwa zo kaji da wannan yar rigimar taka, ta matsa,lallai sai taji haduwarku da me'ad, ni dai nayi kok'arin sanar daita kad'an daga cikin had'uwarku sauran kuwa na barta da bagudo takarasa mata yakarasa fadar hk yana murmushi, murmushi fu'ad yayi shima sannan yakaraso inda take kwance kmr ruwa , ya komata ya zaunar daita tare da yi mata makari da pillow ta bayanta "kinji abinda uncle malik yace ?
"ni ..ni naji amman babu ruwana dashi tunda yaki yacigaba dabani labarin, takarasa mgnr muryarta a shagwabe kmr zatayi kuka,kissing din goshinta yayi "don't cry my bby rabu dashi kinji bby nah ni da kaina ma sai nabaki, ai zaki fi son nawa ko?
ta gyda masa kai kawai batare da tace komai ba fu'ad ya fuskanci malik "yanaga kana kok'arin tafiya batare da kaci komai ba?
"kai rabani da cin abincin nan, yanzu ina ci idan naje gida sai nayi bayani daya bayan daya, an dinga yi min qausetion's kenan ,gara kawai idan na koma gidan naci gbdy, ok muje na taka maka "baby nan ina zuwa just give me w minti .
har waje fu'ad ya rako malik suna sake tautaunawa akan sha'anin rayuwa, da hakuri da rayuwar ita karon kanta ...
koda fu'ad ya koma parlour'n bai iske NASREEN ba ,dan hk kai tsaye ya nufi d'akinta ,inda ya isketa kwance cikin blanket dinta, ya yaye blanket din tare da d'aura hannunsa kanta "my bby kin sha maganinki? "yes dady .
"ok kiyi bacci abinki Allah ya baki lfy me d'aurewa .
"ameen babana, shiyasa nake sonka.....
"i love you more yacigaba da zama yana dubanta tana matukar bashi tausayi yana jin kmr ya ajiye komai ya bata kulawar data dace, ita kad'ai garesa kmr yadda ya kasance, a zahirin gasky baya son yarasata duk da kasancewarta mai karancin lfy yana sonta hk... tsawon lokaci yana zaune yana tunani har sanda bacci ya d'auketa sannan ya yunkura ya tashi ya nufi d'akinsa ya kwanta lamo akan gadon yana tunani ya saka wancan ya kwance wancan, runtse idanunsa yayi sosai yana kiran sunan Allah, ahankali ya bude idanunsa wanda suka kad'a sukayi jawur saboda tuno abinda yake yi masa cikin rayuwarsa, a filli yace "nayi dana sanin aurenki me'ad dana san hk zaki zamomin arayuwata da ban yi kuskuren aureki ba...hawaye ne yaji suna sauka masa akan kuncinsa ,cikin sauri ya sharesu, lokacin ne wayarsa ta d'auki kara, ya kai hannunsa ya d'auka akan bed side ya manna a kunnesa batare daya duba ba.
sautin muryarta yaji ta doki dodon kunneshi ,yayi Shiru tare da janyo pillow ya manna akirjinsa ya rungume tsam sbd d'and'anon dadin muryar "hello hello fu'ad kana jina !! ta sake maimaitawa akaro na biyu.
"uhmm ya'akayi kira adaidai wannan lokacin ko kin manta ina iyali ne ?
"am sorry for disturbing you , but ina son ka saurareni fu'ad kaji abinda za....
saurin katseta yayi ta hanyar cewa "sauraran me zanyi miki, karki meidani wani shasha mana ,ta yaya kike kokarin manta dangantakarki da me'ad mana ,karki manta har yanzu me'ad matsayin matata take, dan me kike kokarin sanyo damuwa acikin wace nake ciki....?
" fu'ad ka saurareni mana, haba fu'ad ya dace ace nasamu kar'buwa a wajenka a daidai wannan lokacin, na d'auki sama da shekaru goma ina dakon soyayyarka batare dana fayace maka ba .
" wannan damace tazo mana, kabari mu dama mana dan Allah ... karka ki amsar soyyayata saboda dan adam daraja garesa, idan ka amince zaka aureni zan ajiye komai har aikina domin na baka farinciki dakarasa.
"dakata dakata malama enough is enough don't talk any rubbish.. "kinsa yadda zaki bani faricikin any not ki fahimtar da me'ad tabi abinda nake so domin a zauna lafiya?
" ni dai ka ajiye mgnr wata me'ad kawai ka amince da au..
"ok baxaki iya bata wannan shawarar ba amman zaki iya shigowa gidanta amatsayin kishiyarta ko...?
"ka fahimceni fu'ad ba ...
"babu wata fahimtarki da zanyi idan ma aure nake da bukata ,bake zan aura ba.... bake ya dace na aura ba, ina da ido nasan inda mata suke okay, dan haka ki shafa min lfy if not zan gayawa me'ad da kaina tasan yadda zatayi dake ya katse kiran yana fitar da numfashi sama sama.
"meyasa kayi haka?
zuciyarsa ta kismamashi hkn, "m e yasa baka amshi tayin soyayyarta ba?
take yabawa zuciyarsa amsa da, bazan k'ara wannan kuskuren ba bazan sake kuskuren auren ya'yan masu arziki ba.......
a ranar fu'ad baiyi ishashen bacci ba, juyi kawai yake ga tunanin ciwon NASREEN ga kewar iyayensa dake addabarsa uwa uba matsalar me'ad da sabuwar matsalar dake shirin kunno kai, har karfe daya ta buga fu'ad bai san yadda zai yi da al'amura dake kokarin kusowa rayuwarsa ba. ahankali tunanin haduwarsa da me'ad ya dinga zuwa masa daki har zuwa lokacin da sajida ta bar gidansu me'ad agigice zuwa gidansu taga lafiyar mahaifinta .
"koda sajida ta koma gida hankalinta yayi matukar tashi saboda ganin raunin harbin da d'anta'ada yayi masa, kuka take sosai tana "furta sannu dady ..shi kuma yana rarashinta da kyar dai yasamu tayi shiru.
ita kuwa me'ad bayan ta tagama kimtsa kanta tattare da tunanin sabon fuskar data tsaya mata arai ta nufo hanyar parlour tana kwallawa me aikinsu kira " ummi ummi!! har takaraso parlour'n shiru babu kowa hatta misna da suhailat basu gurin, nan ranta ya soma baci tashiga kai kawo ta sake dawowa cikin parlour'n tattare da matsancin damuwa tasamu guri ta zauna tare da d'aura kafar daya kan daya tana girgizawa tare da cizon yatsanta ummi dake d'akin suhailat tana mata guga tayi saurin ajiye Iron ta fito da gudu tana haki, cikin rawar murya tace "aunty gani me'ad ta d'auke kanta cikin isa tace, "ummi ina son tambayarki...
ummi ta d'aga kanta da sauri cikin tsoro jikinta yana rawa tace "kiyi duk irin tambarki da kike so.
me'ad ta sake d'aure fuska kana tace "wai shin nan gidan ubanki, ko kuwa da gadonki acikin wannan gida..?
da sauri ummi ta sake d'ago fuskarta ta kalli me'ad lokaci guda, kuma tayi saurin d'aukewa dan wani irin kallon da me'ad ta watso mata, sannan cikin rawar muryar tace babu ko daya sai dai kawai cin arziki danake yi acikinsa.
"okay a she kinsan cin arziki kike yi amman kike neman kifi ya'yan gida sakewa, ki km fisu iko ko?
ita dai ummi tayi shiru kawai tana kallon kasa dan daman hk halin me'ad din yake duk wanda yake kasanta ,sai yayi hakuri, in kuwa ba hk ba zai rasa aikinsa acikin kankanin lokaci. me'ad ta girgiza kafarta cikin isa da iko "daga yau duk sanda na sake kiranki, kikayi banza dani wallahi kinji na rantse in har baki rasa aikinki ba, zaki had'u fushina jahila kawai dabba mummuna.......
mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 45 to 46
........."Wallahi Ba kiga yadda na tsanaki ba, ji nake kmr na kasheki ta had'e hannunwanta duka biyu al'amun da gaske zata iya aikatawa abinda ta furta .
da sauri ummi taja baya tare da furta " Dan Allah aunty kiyi hakuri Insha'allahu bazan sake ba,zan kiyaye ....
"Kar ma ki kiyayye kiga yadda zanyi dake .
"Kiyi hakuri ta sake furtawa jikinta a sanyaye "Dan Allah malama banason long talk tashi ki bani guri kazama kawai.
Ummi ta mike jiki a sanyaye babu laka ta fito, idan da sabo tarigada ta saba da wulakancin me'ad.
Me'ad taja dagon tsaki lokaci daya taji gabanta yayi wani irin mahaukacin bugu da karfi , tayi shiru tana tunanin abinda ya sata jin hk, take fuskar fu'ad tasoma yi mata gizo acikin 'kwal'kwaluwarta ,runtse idanunta tayi kawai ta d'auki wayarta tare da mikewa tsaye ta haye sama inda mahaifiyarta take zaune da system agabanta tana tura sakonni, shigowarta d'akin yasa mom dinta d'agowa tare da cewa " yauwa gara da kika shigo, yanzu nake son aikawa akira min ke, me'ad takaraso jiki a sanyaye ta zauna kusa daita "gani sweet momy dina,ina matukar alfahari da kasancewarki mamana "uhmmmmm dan kinga abbanki baya kasar ba,?
"kai momy wai meyasa kike kishi da dad ne?
"nifa gbdyanku ina sonku domin banida abin so fiyye daku a duniya ku ne komai na.
"kinga bason zance karya ina file din da hjy maryam tace ta tura dazu da safe?
tsam tayi da ranta sannan tace" yana cikin jakata "okay je ki zo min dashi yanzu akan aikinsa nake.
cikin mintina kad'an me'ad ta fito daga d'akin mom dinta , ta nufi d'akinta tasoma duba jakarta amman abun mamaki babu diary dinta ballanatana file din dake ciki, gabanta ne ya sake fad'awa , lokacin da 'kwal'kwaluwarta ta hasko mata ko dai ta yarda dashi agurin batakashin da ya rutsa daita gurin cirar kudi.. "tabbas in har bata ganshi ba definitely acan ta yar, ta furta hkn a fili tana cigaba da bincike gefe da gefen jakarta sannan cikin sauri ta fito da niyyar komawa gurin, har zata fita sai taga kmr shigarta batayi ba, basani ba, ko zata sake had'uwa da wannan kyakkyawan fu'ad , Dan haka takoma cikin d'akinta .
ta fito cikin wani koren voyal dinki doguwar riga har kasa ba D'an kwali a kanta ,sai koren mayafin data yane kanta dashi, takalman kafarta suma duk kore ne, ta cigaba da tafiya cikin yanga, ta isa inda aka tanada domin ajiye motocin gidan, ta tsaya tana karewa motocin kallo ,4mart itace wace zuciyarta tabata umarnin shiga .
Tun kafin ta kunna motar me gadi ya zabura ya mike tsaye, yasoma kok'arin bud'e mata get, ahankali tasanyo hancin motarta wajen gidan..a natse take tukin m .
kai tsaye ta d'auki hanyar isa inda suka had'u da fuad ,cikin kankanin lokaci ta iso ,tasamu guri tayi parking din motarta ,tana bin gurin da kallo abubuwan da suka faru a d'azu da safe ne suka shiga dawo mata, tun daga kan sanda ta d'aura idanunta akansa ,har zuwa lokacin data nutse a tsakiyar faffad'an kirjinsa...fuskarsa , ajinsa, jin k'ansa da komai nashi sunyi mata ,ta dad'e bata ga halitar da kai tsaye aganin farko ya mamaye zuciyarta ba .
fitowa tayi daga cikin motar ahankali tana dube dube, duk da zuciyarta na tabbatar mata bazata gansa ba adaidai wannan lokacin ,dan haka tasoma duba inda suka had'u, bata jin ATM dinta domin tasan cikin kankanin lokaci zata mallaki wani ,tafi bukatar diary din dake d'auke da manya sirrinkan rayuwarta tare da file din momy dinta, da shi kanshi fu'ad ,Saboda idanunta na matukar kwad'ayin sake ganinsa .
ta kasa hakuri tsayuwa guri daya, tayi tafiya me nisa dan har ta kusan shiga alimoshi local government, amman bata ga ko mai kama da fu'ad ba da diary dinta , sannan ta dawo gida cikin wani irin 'bacin rai ,cikin sarsarrafa ta shiga parlour'n, yau kam gabadaya a sama take jin kanta, kuma duk wanda yayi kok'arin shiga track dinta zai had'u da 'bacin rainta.
a daidai tsakiyar parlour'n suka ci karo da mahaifiyarta "ke kuma daga ina haka kika yi wani wujiga wujiga dake?
me'ad ta dan tsosa tsakiyar kanta batare da tace komai ba, "dake fa nake magana kina jina?, kinsa banason wannan fitar ta babu gaira babu dalili ko.
takarasa mgnr tana jan tsaki sannan tace "ina file din danace kin kawo min?
"uhmm ammmmm daman shi naje nema ,daxu da safe ko da direbanta ya kawo na shirya zanje injin ciro kudi sai na kar'ba na saka acikin diary dina ,amman narasa komai nawa ina tunani agurin bata kashin nan ya subuce acikin jakata ,"yanzu hk gurin na koma ko zangani amman .....sai tayi shiru ta kasa k'arasa maganarta sakamakon wani irin kallo da uwar ta jiho mata ....
"abinda kike kok'arin cewa baki gani ba, ko ba abinda zaki ce min kenan ba?
me'ad tayi saurin d'aga kanta "kinsan ko file menene kika yarda shi? "
file ne dake tattare da mahimman bayane akan kudad'en marayun ya'yanta, amman kalli yadda sakacinki yasa aka rasashi , keda zaki ajiye abu a gida amman kika fita dashi, nan fa suhailat tafiki kaifin baseera "am really sorry momy zanyi kokari na nemo.. " a ina zakigani?
" zan sake komawa gurin ko Allah zai sa nagani takarasa mgnr tana narke fuska alamun shagwaba.
"ke bar shi kawai zan sake tuntubarta ko tana da wani copy "thank you my mom .... hjy khadeeja ta shige d'akin mai gidan . Ranta babu dadi ta shiga d'akinta tana shiga ta fad'a saman gadonta ta kwanta flat tare da runtse idanunta
*******
Misalin karfe tara na dare ranar a kwance da fu'ad yake ya ciro D'an karamin diary dinta brown me d'igon ruwan zinari, daya tsinta bayan rabuwarsu da me'ad ,yana kallonsa dagani kasan me tsada ne ,ahankali ya kai diary din daidai saitin hancinsa yana shinshina, ni'imtaccen kamshin, Dior addict daya kama jikin diary sosai ,sai kawai yasamu kanshi da lumshe idanunsa tare da bud'esu duka atare cikin wani sabon alamari da ba zai iya kwatantawa ba, a lokacin fu'ad matashi ne Dan kimanin shekaru talati cif da haihuwa ,duk inda ake neman kyau ga d'a nmj fu'ad ya mallakeshi ,fari ne tass me dagon hanci da yawon suma me kyawawan idanu farare kal kuma manya masu cike da nagarta .
Cikin sand'a malik ya iso inda yake kwance ya fixge diary din yana dubawa yaga wasu mahimman file da ATM atsakiyarsa, fu'ad ya d'ago idanunsa ya kalleshi a matukar tsorace.
" uhmmmmm daman nasan ka fad'a tarkon son yarinyar nan ,amman kake wani son waskewa, shiyasa fa nace idan kana sonta ni na hakura nabar maka , kaje ka nemi soyayyarta, amman ka tsaya wani jin kai ..."kana sonta ko ba hk ba abokina?
"Tsaki fuad yaja a d'an hassale sannan ya juya masa baya "kai dai ayi D'an matsala wallahi, kaje man kayi introducing kanka agurinta Dan ni bata gabana .....
" shiyasa naga ka tsurawa diary dinta ido ba ,tare shakar kamshin turarenta? inji cewar malik yana me tuntsurewa da wata uwar dry.
Wani tsakin fu'ad yaja "kanka ake ji, ga diary din nan a hannunka kayi duk abinda zakayi dashi ,sannan kayi kok'arin ya isa gareta a duk sanda kaje gabatar mata da kanka ,ina maka fatan alkhairi tare da samun soyayyarta ...
"Dan Allah abokina, da gaske ,da gaske addu'ar samun nasara kamin? yakarasa mgnr yana me karasowa zuwa inda fu'ad ke kwance ya rike hannuwansa duka cikin nasa "na...gode abokina amman tare zamuje gidansu tunda ga addresse dinta acikin diary..?
"a'a kaje kai kad'ai ,hallo dai ina maka fatan samun nasara akanta sannan ya meida idanunsa ya runtse ya cire hannunwasa cikin na malik yana dafe goshinsa da hannunsa daya.
malik yayi saurin boye dryrsa sannan ya mike tamkar wanda akayiwa wanka da ruwan tsanyi ya isa makwancinsa "wannan shine karo na farko daya ganshi cikin damuwa hk, yammata dayawa suna kawo masa farmaki amman babu wace yaga tsan tsan damuwarsa akanta kmr me'ad, ayau suka soma ganinta amman da dukkanin alamu ta tafi da zuciyar abokinsa, ya kwanta yana dryr mugunta, domin a zahirin gsky shi ba son me'ad yake ba, amman ganin fu'ad yana neman waskewa akan sonta, yasa shi son shiga rayuwarsa tunda daman sukanyiwa junansu hk shi dasu kabeer , daga baya komai ya daidaita, Amman banda fu'ad da duk macen data kawo masa hari baya yarda ya amincewa soyayyarta ,acewarsa ba soyayya ce agabansa ba, yadda zai samu aikin da zai kula da kakarsa yake .
"itama bangaren me'ad kasa runtsawa tayi duk ta inda ta juya fu'ad take gani acikin kwayar idanunta,wani irin canji take ji a gabadaya ilahirin jikinta, ahankali take jin feeling's na bijirowa gangar jikinta wanda wannan shine lokacin na farko dataji hk ajikinta, domin duk yadda sajida ke bata labari akan yanayi makamancin hk, bata ta'ba yarda ba, ta d'auki lamarin amatsayin shirme, ashe ba shirme bane da gaske ne?" mutun kanji wannan yanayi ajikinsa idan ya had'u da abinda yake so...
kudundune jikinta guri daya tayi acikin bargonta, tana kok'arin basar da abinda take ji yana tafiya da bugun zuciyarta ,wanda a zahirin gasky mamaki faruwar hkn ya soma kamata, a kallo daya komai ba neman birkice mata....... da kyar da taimakon bacci barawo tasamu tayi bacci.
Abu fa kmr wasa kullun me'ad sai fita zaga gari ko Allah zai sa ta had'u da fu'ad amman shiru ka keji ,har kusan sati daya , tana garari agari. yadda take zariyar neman fu'ad, haka malik ke zariyar nemanta domin bata diary dinta dake d'auke dakatin ATM dinta ,da kyar ya samu shigowa cikin estate dinsu ya isa bakin tafkeken get din gidansu da'aka nuna masa, yasamu daya daga cikin masu gadi gidan bayan ya gaishesa ,me gadi ya amsa yana masa wani irin kallo sannan yace" wa kake nema?
"dan Allah ina neman me'ad.
Me gadin yayi shiru kawai yana duban malik daga samansa har kasa, ba dan yana da wata makusa ba ajikinsa, sai na talauci da babu daya nuna ajikinsa, me gadi ya sake maimaita tmbyr da malik yayi "kace kana neman me'ad ko me?
malik ya d'aga masa kai ala'mun eh.
"Ita me'ad din tasan da zuwanka ?
"Aa amman idan kashiga kace mata wanda suka had'u agurin injin din ci...
"Dakata anan da shirmenka, sannan ka juya ka 'bace daga gurin nan , daganika irin yan yunwan nan ne, jobless marasa aikin yi," kaga yarinya yar babban gida shine ka lallabo ko? "oya maza ka 'bace tun kafin ita kanta tasan da zuwanka kasha dukan banza.
Batare da mutsu ba jiki a sabule malik ya bar unguwar tamkar wanda kwai ya fashewa acikin yana mamakin girman al'amarin, sai dai kullun zai zo amman baya samun ganinta hk zai juya ya koma da diary dinta , inda fu'ad ya d'auki zafi sosai dashi "kana wahalar da kanka abanza daga karshe ka had'u da wulakaci .
"ka fahimceni fu'ad Allah ba wai .."dakata malam kaje kacigaba da bibiyarta rayuwarka ce, abinda zai min ciwo bai wuce naga ko naji kace an wulak'anta ka ba, yana karasa mgnr ya fice daga d'akin yana huci. Malik ya girgiza kansa ,tabbas ya fahimci irin son da abokinsa kewa me'ad amman ya dakewa zuciyarsa, shi zai yi iya kokarinsa yaga ya had'a ruhinsu guri daya....
*******
Yau takama litinin wanda kowa yake sauri ya shirya ya samu halatar makaranta da wuri ,ko neman aiki da sauransu , ita kuwa me'ad tana gado tana juyin da tunanin fu'ad dinta ,har kafe tara sannan ta tashi tasa aka had'a mata ruwan,tayi wanka ,nan ma sai da ta'ba lokacin gurin tunaninsa ganin take kmr yana tare daita, duk inda ta juya shi take gani har mafarkinsa take, suna rayuwar aure tare.
ahankali ta fito daga bathoorom gurin shiryawa ma sai data bata tsawon lokaci ta fito ta karya sannan takama hanya dan zuwa bank domin amsar sabon ATM.
tun da ta cusa hancin motarta cikin harabar zenieth bank ta sauya yanayin tukinta tayi parking sai dai tajima acikin motar saboda ganin kmr mutane sun yi yawa kafin daga baya ta fito, tana taku ahankali da rangwad'a tashiga .
kai tsaye gurin costume's care ta nufa , somi itace wace jinisu ya had'u daita sosai, somi na ganin me'ad ta sakar mata murmushi tare da cewa"me'ad you are welcome hade da tmbayarta abinda ke tafe daita, cikin harshen tsadadden turancinta tasoma mata bayanin abinda tazo yi, hannunta ta zura karkashin table ta zaro wani file ta mika mata tare da nuna mata wani madaidaicin office da hannunta "ki shiga can ki cike sai kawo min.
"okay me'ad ta furta sannan ta amshi file din ,cikin mintuna kad'an ta cike ta fito "ta mika mata batare da 'bata lokaci ba akayi mata komai akace taje ATM ta canza pin dinta tare da mika mata envelop ,cike da rausaya ta nufi injin cire kudi bata wani canza pin dinta ba, ainhin pin dinta na da 5996 ta sake sakawa sannan ta kama gabanta wanda dayawa mutanen dake tsaye agurin hankalisu na kanta.
Yau ma kmr kullun tana fita malik yazo gidan sai dai me gadin bai bi ta kansa ba ,saboda kallon wani mahaukaci dayake masa har sanda ta sanyo hancin motarta, ana kok'arin bud'e mata get shi kuma yana kok'arin isa inda motarta take, sauran security suka dakatar dashi, dan wani har ya kai masa mari ya goce da sauri.
Me'ad ta bishi da wani irin kallon sani ,sannan ta kusa hancin motarta cikin gida tayi parking , ta fito tana gyara zaman glass din dake manne da idanunta ,ta kira daya daga cikin masu kula da bakin get "waye wancan mutumin da kuke dambe dashi kan sai ya iso gareni?
sai da obi yayi jim..
sannan yace "wai gurinki yazo yau akalla ya kai sati kenan yana zuwa " what? ta furta arazane sannan tace.
"how dare him yazo gurina akan wani dalili ?
"hk dai yace ranki ya dade.
"Karku sake ku bashi damar sake shigowa estate din nan ballanata har ya iso bakin get din gidan"yes ma .
ta juya zuwa cikin gida tana tunanin inda tasan fuska amman sam ta kasa tunawa.
obi ya juya cikin sauri ya isa ga malik yasoma tura keyarsa "dan Allah ka saura ni abunta nazo kawo mata data yar bawani abu nazo nemana gurinta ba, amman ina sam obi yaki sauraransa har sai da kai ga fitar dashi gbdy daga estate din.
*******
tafe suke ita da sajida a Shopprit domin siyaya wa mahafinta dake jinyar hannunsa agida,kuma a yau din nan suke expecting dawowar abbansu me'ad daga kasar America wanda yaje cheek up , ahankali suke takawa kmr basu san taka k'asa me'ad na sake bawa sajida labarin fu'ad sannan suna daukar duk wani abun amfanin daya kai su bayan sun gama sukaje inda ake biyan kudi me'ad ta bada ATM dinta, suna daf da fitowa suka had'u da Malik cikin saurin yake binsu yana kiran sunanta" me'ad me'ad!! me'ad ta juyo tana ganinsa tayi saurin kawar da fuskarta tacigaba da tafiya "kai kawata wannan mutumin fa ke yake kira.. ki tsaya mana da ala'mun yasanki "baki da hankali aganni na tsaya da wannan ai sai mutane su raina da ajina .
biyota malik yayi" dan Allah ki tsaya abunki zan baki. da sauri taja hannun sajida ,haba me'ad ki tsaya mana wulakanci bashi da amfani balle d'an adam daraja garesa "bawani abun fad'a anan kawata , wancan banza nema yake na kulashi ,ni km ina i can't suka shiga motarsu cikin sauri suka bar gurin kafin malik yakaraso.
"okay mubar zancesa cigaba da gaya min labarin kyawawa nan , ko shima kmr sauran samari gari yake ?
birki taja sakamakon gitawar da wani me okada yayi ta gabanta.
ta Leko da kanta cikin bacin "kai ina zakaje kake sauri hk?
" jiki da wata banzar mgn kisawa motarki alamar koya tuki Dan da alamun baki kware ba .
" kai koya min tuki zakayi ko me ?
"Kina bukatar hkn ai.
"kutumar uban can... "kinga malama duk abinda za'a yi ayi ammam ban da zagin iyaye yar rainin hankali kawai, ko dan kinganki cikin wannan kememiyar motar kike tunanin zaki zageni na kyaleki?
sajida ce tayi masa alamun ya wuce kawai tare da cewa "kinga manta da wannan " kibani labarin kyakyawan saurayin nan da kuka had'u last week wallahi ina jin dadin yadda kike fassalta shi, me'ad tayi shiru ta kasa cewa komai ,kafin daga baya ta furta sunansa "fu'ad kenan ....
"suna me dadi tunda kike furta min sunasa naji sunan har cikin raina inji cewar sajida "Allah ko ai sai ma kinganshi kawata hadadden gaye aji farko zance fu'ad suke har suka shigo harabar gidansu sajida inda suka iske motar gidansu me'ad"kai kinga da ala'mun dady Dina ya sauka? Cikin sauri suka fito hannunwasu rike da farar laylon.
Da dariya suka shigo parlour ,n inda suka iske mahaifin sajida da nata zaune suna tautaunawa akan abinda ya faru " ai ina gaya maka Aliyu tabbas zakasamu k'arin girma nan ba da jimawa ba akan wannan kokarin naka,mead takarasa kusa da mahaifinta ta rungumeshi "dady sannu da zuwa.
"yauwa yar baba fatan kina lfy?
"ina lfy amman ba lau ba takarasa mgnr tana nufar mahaifin sajida "gashi uncle "ka gwada wannan kaji yana da dadi sosai .
" yar baba aliyu ya gaya min cewa tsalake rijiya kikeyi a wajen harbe harben da'akayi? batare data juyo ba tace "eh baba amman babu abinda yasameni ,uncle ka fa zama jarumi a gari "kalli can kagani ta nuna masa tv da yatsan hannuta, kowani gidan talbijan kai suke nunawa tun daga last Week har yau din nan sajida ta zauna kusa da mahaifinta tana gyara masa zaman bandage dake d'aure da hannunsa.
Mahaifin me'ad ya gyara zamansa tare da cewa " yar baba kawo min coffee mara madara "okay dad.
"uhm yar baba nima ki kawo min, me'ad ta nufi hanyar kitchen tana karasa shiga ta ja ta tsaya tana kiran "sajida ........
"na'am.
"a ina kika ajiye sugar?
takarasa mgnr tana kallon wasu jerin robobi dake ajiye a kitchen cabinet ,acp ya bata amsa daga zaune dayake " ai in dai wannan yar zaki tambaya ,to kuwa kin saba lamba.
sajida ta kaiwa babanta naushi a dayan hannunsa mara ciwo tana dry "kai baba "kai baba ko gsky na fada? " ko sau daya bata ta'ba shiga kitchen din nan da sunan d'aura wani abu ba, bari nazo na d'auko miki yakarasa mgnr yana me mikewa tsaye "me'ad..... sajida takirata tana murmushi nima kizo min da coffee da k'arin sugar kinji kawata.
" hmmm yarinyar idan zaki koyi had'a shayi Da kanki , ki tsaya ki koya ko Dan aure da zakiyi watan gobe "ni imran din ma nake tausayi inji cewar acp "in tambayeki yar baba, waye wancen yaron dana samun labarin yana xuwa gurinki kullun bayan ga maganar safwan da'aka ajiye "uhmmmm wannan Shashan , ai kwana hudu data wuce na fara ganinsa ban san inda yasan ni ba amman har sunana ya sani abun tsoro .
"uhmmm?
" uhmmm uncle nifa abun ya fara damuna yau ma sai da muka had'u dashi a shopping, acp ya juya zai bar kitchen din fuskarsa da ala'mun rashin yarda "uncle kar ka fahimceni ba daidai ba "ai shikenan yar baba na fahimceki ....
********
tsaye suke su duka acikin had'ad'd'en boutique dake depomu wanda yakasance mallakin mahaifin kabeer ne .wasu yammata ne su biyu suka shigo cikin harabar gurin, kowace sanye da riga iya cinyarta wanda ke nuni da yare ne, makale da yar karamar jaka suna tautaunawa, kabeer dake tsaye kusa da malik yana dan kurban fiver alive "yace kumeless tare da binsu da wani shu'umin kallo malik yayi saurin juyawa shima ya bisu da kallo ,sannan ya juyo ya kalli fu'ad yana dage masa gira kana ya sake juyowa ga kabeer "idan kabiyi wad'an yammanta kai ka zasuyi su baro ,duk bugi ne wallahi ina gaya maka. "kai dan Allah banason shirme ka juya ka kalleshi da kyau gsky sun hadu inji cewar kabeer.
Malik ya sake juyowa ahankali yana kare musu kallon tsab sannan yace "uhmmmmm wad'an yammanta lagos din suna da tsabagen wayo tsiya ,su sha kwaliya su dinga maganganu irin na birgewa, amman duk fanko suke,ya dan sake kallon inda fu'ad yake sannan yacigaba "daya nagani acikinsu me nagarta da kamalar madarar kyau ...... sudais yayi saurin cewa "da gaske ?
"yace uhm.
"kallesu da kyau kagani duk kwaliya ce kawai "yanzu kayi kok'arin kallonsu batare da kwaliya ba kagani .
"kamar yaya kenan? inji cewar kabeer .
"ka aiyana da tunaninka mana ..
"kai dan Allah banason shashanci da ala'mun fa kwal'kwaluwarka tasoma samun matsala inji cewer kabee .
"kai ne dai mahaukaci amman ni nasan abinda nake duk da cewar akwai yammata dayawa amman me'ad dina ta zarce kowa yakarasa maganar yana ware hannunwansa duka..
"kaji mahaukaci suka kwashe da dry "matar da jiya jiyan nan tagama shuka maka rashin mutunci, wai har da wani cewa me'ad dinsa suka sake kwashe da dry suna nunashi .
fu'ad dake tsaye rungume da hannuwansa duka a kirji bai kulasu ba illa fuskantar kofar shigowar dayayi tare da takaicin malik, aiko tamkar a mafarki yaga shigowarta sanyi cikin doguwar rigar abaya har kasa ta nad'e kanta da mayafin abayar hannunta rike da karamar jaka saurin runtse idanunsa yayi yana cigaba da kallonta ahankali ya mutsutsuka idanunsa" itace ko kuwa wata ce me kama daita ,tabbatar da itace yasashi saurin waskewa alokacin da suka had'a ido daita itama kallonsa ta tsaya yi cike da matsanancin mamaki ta mutsumutsuke idanunta tagani ko shaukin sonshi ne yasata ganin hk oho.
muryarta a sanyaye tace "sajida ga fu'ad dina tare da nuna mashi, tsura masa ido sajida tayi, lokaci daya numfashinta ya nemi d'aukewa ganin halitar da bata ta'ba ganin irinta ba, tana ganin kyawun imran wanda zata aura amman na fu'ad ya zarta nashi,kad'an kad'an taoma jin tsigar jikinta na tashi abinda ta kasa fassalta ma'anarsa, wani irin sanyi soyayyarsa ne ya tsarga mata ya fara bin ilahirin jikinta, take ta lumshe idanunta zuciyarta na wani irin harbawa da sauri sauri, gbdy ta kasa d'auke idanunta akanshi har sanda ya juya musu baya.
shi kuwa malik na ganinta yasoma murmushin tamkar wanda akayiwa bushara da gidan aljanna sannan yace "kai kabeer sudais itace fa gata can yarinyar nan wallahi itace ..me'ad najin hk tayi saurin riko hannun sajida "kinga wanda na nuna miki?
"uhmm sajida ta iya cewa still idanunta na kan fu'ad "wance dake sanye da kaya shine fu'ad dina amman zo mubar nan yanzu yanzu saboda banason wancan mahaukacin ya dagula min lisafi ,sai yanzu na tina shi, ranar da muka hadu da fu'ad suna tare sai dai bansani ba taren suke ko kuwa anan suka had'u, wanda nake so daban shi kuma yana kokarin hanani rawar gaban hantsi .
"haba me'ad dan Allah ki tsaya naga fu'ad din da kyau shine dai sanye da riga pinky?
"eh shine amman mu wuce kawai...
da sauri malik ya biyo bayansu yana kiran sunanta "me'ad...jimana me'ad!! dan Allah ki tsaya ya kwaso aguje su kabeer suka biyosa" kai majinun ina zaka bayan gasu can, cangurin fa sukayi, ba itace me kaya ruwan d'aurawa ba?
"eh itace "mead dan Allah ki tsaya ita kuwa tafiya kawai take tana jan hannun sajida, "gsky fu'ad kyakkywa ne ajin farko amman me zai hana ki tsaya ki saurari wancan wata killa abokinsa ne fa.
"kinga da ala'mun magana yake son yi dake.
me'ad tayi mata banza sai janta take har suka shiga lift "ki daina turani mana, shi Wanda kike so ma bai san kina yi ba, ba gara ki tsayawa me binki ba, watakilla ma abokinsa ne ya taimaka ya janyo miki hankalinsa ,aguje malik ya biyosu yana ihun" jimana dan Allah ki tsaya minti daya abunki zan baki ta cikin lift sajida ta d'agowa fu'ad hannu wanda ya sake juyowa "sannu tana dariyar da za'a iya kiranta na farinciki "kibari mana sajida kina magana zai ta binki ne ya d'auka muma irinsa ne.ta fadi hkn ne a tunanita ko Malik sajida ta dagawa hannu, sajida tayi murmushi tana sake daga masa hannu.
" haba sajida meye hk ne? Karki manta fa watan gobe ne za'a yi bikinki.
"kinga bangane mgnrki ba nifa fu'ad nake d'agawa hannu ba wancan me bin namu ba "stop it sajida.. .." ki daina kallonsa dayawa da fa sadakin wani akanki "ki kyaleni nayita kallonsa tun yanzu kafin aurena bayan nayi auren shikenan... me'ad tayi shiru kawai takasa cewa komai har sanda lift ya tsaya suka fito da sauri me'ad janye da hannun sajida .
malik kuwa sai kokarin saukowa yake daga step domin ya iske su akasa .
yayinda fu'ad ke tsaye a inda suka barshe yana kallonsu batare da yayi yunkurin motsawa ba....
mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 47 to 48
.....yana nan tsaye a gurin da suka barshi har sanda suka dawo suka samesa, malik ya dafa kafad'arsa yana fidda numfashi sama sama sannan yace "abokina kaga me'ad dina ko?" gsky yarinyar ta had'u iya had'uwa ,dan Allah abokin ka taimakeni ka tayani yakin shawo kanta,dan zan iya rasa raina akanta yakarasa mgnr yana kwashewa da dry....
on expecting malik yaji sautin muryarsa " Allah yasa ka mutu yanzu in har sai na tayaka yakin neman amincewarta sannan ya juya yasoma takawa ahankali ya bar malik tsaye, sake da baki yana kallon bayansa sai dai fuskarsa kunshe da dry ..kana ya juyo yana fuskartata kabeer "kungani ko zargina fa yana neman tabbata fu'ad son yarinyar nan amman miskilancinsa ya hanashi fahimta, amman ni nan zansashi ya fahimci ya fad'a tarko dan bazan bari yarinyar ta subuce masa ba.." tabbas zanceka hk yake,yana sonta, itama yarinyar da ala'mun ta kamu da matsanancin sonshi inji cewar sudais.
kabeer ya numfasa kana yace "kar dai ku manta da halin fu'ad, tunda bai ce yana sonta ba ku yanzu meye naku a ciki ?balle kai malik da kabi ka hakikance akan yariyar , ka dai bi ahankali kar ka je ka jefa kan cikin wahala shi dai fu'ad bai aikeka ba har gara ma kayiwa kanka yaki neman au...shigowar wasu costumer's ne yasa kabeer katse zance yaso garesu tare da kiran daya daga cikin yan dake kula gurin..
bangarensu me'ad da sajida kuwa tunda suka shiga mota babu wanda yayi kokarin yin magana kowace da abinda zuciyarta take kismamata akan fu'ad, har suka karasa gida jiki a sanyaye suka shiga parlour'n inda suka iske hjy Khadija zaune tana kallon labarai "momy sannu da gida.
"sannunku yammatana har kun dawo ?
"ina siyayyar da kuka fita yi?
sajida ta zauna jagwab akan kujera tana fuskantar momy "me'ad ta hana mu yi taba amsa da hkn tana runtse idanunta.
"bangane hausar ta hana ba?
" nan sajida ta gaya komai amman banda sunan fu'ad. momy taja numfashi da ajiyar zuciya atare sannan ta dubi inda me'ad take tsaye tana cizan lip's dinta "karki soma janyowa kanki tashin hankali kinsa dai an gama maganar aurenki da safwan jiran dawowarsa kawai ake... tun da momy tasoma mgn tayi yunkurin barin gurin dan zuciyarta baxa iya sauraran maganganunta akan safwan ba, wanda a halin datake ciki yanxu ta manta dashi balle wani magana da'aka tsayar a tsakaninsu.
dare yayi sosai yanayin garin yayi sanyi baka jin sautin komai da sautin komai sai na iskar garin dake kad'awa ahankali yana bin jikin bil'adam ciki kuwa har dasu sajida da me'ad da idanunsu ke bud'e ,babu wani ala'mun bacci acikinsu juyi kawai suke akan gado suna tunani rai daya wato fu'ad, sosai sajida ke zurfafa tunaninta akansa sam bata tsamaci kyawunsa da nagartasa ta Kai yadda tagansa ba,a zahirin gasky bacin me'ad tasoma furta tana son fu'ad ba, da tsab zata rusa zance aurenta da emran ,tayi yakin neman soyayyarsa tare da aurensa, amman kashi ....me'ad tayi mata tawayar da baxata iya kai kanta garesa ba ...... sam ranar sajida bata samu runtsawa ba, har gara ma me'ad ta runtsa da taimakon mafarkinsa daya kawo mata ziyara.
abu fa kmr wasa kullun mee'ad ta kwanta sai tayi mafarki fu'ad yana romacing dinta wani lokacin har saduwa daita, saboda zurfafa tunaninsa datake.
parlour'n gidan momy ta fito sanye cikin doguwar rigar har k'asa da madaidaicin hijab ,tana gyara zaman takardun dake rike a hannunta tare da kiran sunanta "mead..me'ad!!
ummi tayi saurin cewa "tana d'akinta bata fito ba tukun.
kai tsaye hanyar d'akin momy ta nufa tana cewa karfe takwas fa har tayi me'ad amman har yanzu kina kwance, koda tashiga d'akin kwance ta isketa akan gadonta kmr yadda tazata ,ta lullu'be jikinta da blanket me taushi , momy tak'araso har inda take kwance tare da zame bargon data lullu'ba dashi "me'ad kitashi mana karfe takwas fa tayi "uhmmmm momy bacci nake ji tayi mgnr tana mika ...ki d'aure ki tashi ....
tashi zaune me'ad tayi idanunta a runtse "maza tashi mana wannan fa shine karo na biyu fa dana dana shigo tashinki bazan sake dawowa ba kin san dai kina da interview yau ko?
nima na shirya zuwa aiki momy ta juya abunta idan kingama ga abincinki can har ta kai bakin kofar taja ta tsaya tace "me'ad ...."na'am momy ya sunan yaron ?
da sauri ta bud'e idanunta sosai sannan tace sunan wa kenan momy ?
"sunan yaron dakika jarabar so har kika kwana kina marfakinsa.
runtse idanunta tayi ta sauko daga kan gadon zuwa kan doguwar ta kishingid'a ,sannan tace fu....... ad "uhmmmm idan na dawo mayi magana akanshi ,sai na dawo dan gsky na kusan makara ki hanzarta tashi.
goshinta ta dafe tana tunanin, "yanzu son fu'ad hk zai mata ?
ta dad'e zaune kafin daga baya ta mike tashiga wanka shap shap ta fito sanye cikin riga da siket na atamfar super exclusive me zanen fuluwa ja da baki a had'e wanda ya d'an kamata ajiki kad'an, kanta babu d'an kwali kasancewar bata fiyye son d'aurawa ba sai karamin bakin mayafi data yane kanta dashi ta fita cikin takunta na yanga da nuna ita yar wani ce ta shiga motarta oil and gas dake cikin apapa.
koda ta isa ta iske dubbanin mutane suna jira amman da zuwanta kiran waya kawai tayi sai gashi an bada umarnin tashigo kai tsaye batare da bata lokaci ba ta fito wanda fitowarta sai days bugar da zukatan tarin mazan dake zaune agurin ciki kuwa har da fu'ad dake tsaye rike da takardun neman aiki, zuciyarta taji tayi wani irin bugawa da karfi ahankali ta d'ago idanunta kmr ance ta waiga gefen hannunta na dama taganshi tsaye shi da wani da batasan kowaye ba, kallo daya tayi masa taji zuciyarta ta sake bugawa kmr yau ta fara ganinsa ,duk da bawai yau ta fara daura idanunta akanshi ba, sai dai kusancin na yau ya sha bambam da sauran lukuta wani irin kyakkyawan kallo take masa, yau gashi a gabanta ba daga nesa nesa ba, shima gabansa ne ya fad'i sakamakon ganinta dayayi a aininhin shigarta ta hausa fulani.
ahankali take daga kafafunta har zuwa office din alhj Ibrahim wanda yake shugaba ga maikatan kuma aminin mahaifinta, bayan sun gaisa ya tambayeta lafiyar mutanen gidansu, tace "duk lfy atakaice sannan akabata aiki wanda zata dinga daukar albashi me tsoka batare da wani interview ..kusan minti biyar tana zaune alhj ibrahim ya d'ago yana dubanta sannan yace "ko akwai wani abu ne, shiru tayi na minti biyu kana tace akwai "ina sauraronki ya fad'a tare da meida idanunsa kan tarin takardu dake gabansa "akwai wani danake son ka taimakawa kabashi aiki a ma'aikatar nan.
"yana ina?
" shine kika tsaya jan maganar abinda zaki fad'a da confidence ai ba mutun daya ba diyata ko mutun goma kike son a d'auka za'a d'auka masengen sa ta aika yaje ya shigo da fu'ad, wanda shigowarsa yayi daidai da tashin da alhj ibrahim yayi, yakaraso shigowa sanye da suit da bakin glass frada a idanunsa take office din ya gauraya da kamshin turarensa kafafunsa rufe cikin cover shoe baki ,taja masa kujera tana nuna masa gurin zama amman yaki zama "ka zauna zaka samu aiki karkashin jagorancina matukar shi kazo neman ,idan kuma kaki zaka karad'e garin nan batare da kasamu aiki ba saboda mu 'yan alfarma gama maganarta keda wuya ya juya kawai batare yace mata ko uffan ba, ta mike da sauri tabi bayansa tana kiran sunansa "fu'ad ka tsaya zan saka abaka aiki me mahimmaci .
amman ina ko juyowa baiyi ba har ya isa inda sudais ke tsaye yana jiransa ya rike hannunsa "zo mu wuce kawai ya iya furtawa "ka tsaya mana bakaji tana kiranka bane ?
kana ji fa taimakonmu zatayi "banason duk wani taimako daga gareta kazo muje kawai idan km baxaka ba na wuce.... ya fixge hannunsa cikin nasa "to bazani ba shekara nawa ina neman aikin bansamu ba yau zamu samu amman kake girman kan banza ...
fu'ad ba tsaya ba ballanatana ya juyo gareta yacigaba da tafiyarsa shi kuma sudais yakarasa gareta "ranki ya dad'e kiyi hakuri hk halinsa yake, shegen girman kan tsiya shi ba... "dakata karka soma furta kalmar 'batanci garesa, daya tsaya har kAi zaka iya cin albarkansa tana karasa fad'ar hk ta juya fuuuuuu zuwa inda tayi parking din motarta ta figa aguje, mutane kuwa sai zagin fu'ad suke akan wasa da damarsa da yayi.
tana barin oil and gas kai coffter coffe ta zarce inda suka saba had'uwa da sajida ,dukkaninsu shiru sukayi suna kallon junansu bayan labarin da me'ad tabata akan abinda ya faru atsakaninta da fu'ad. "me zai hana ki hakura dashi, tunda yaki saurararki.
"i can't sajida ina son shi bansan ina son shi ba sai yau dana yi masa kallon gani ga shi, ni dai ki tayani adduar samun shi kawai dan matsawar ban auresa ba sai dai na mutu babu aure ..
"all the same inji cewar sajida "what?
"no babu komai suka cigaba da zance fu'ad batare da sun kai coffen da'aka kawo musu bakinsu ba tsawon lokaci suna zantawa sannan suka mike atare daga nan gidansu sajida suka nufa ,trafic ya kamasu suka tsaya inda malik shima yana d'ayan gefen hagu bai lura dasu ba sai danja tabasu damar wucewa sannan ya gansu, nan fa yashiga binsu akan lefan dinsa .
kmr ance sajida ta kalli mudubin gefenta ta hangosa yana daga musu hannu, leko da kanta tayi domim tabbatar dashi din ne "me ad duba madubin gefenki kiga wannan d'an jagaliyar fa mu yake bi inji cewar sajida "kai dan Allah tayi mgnr tana dubawa ,"tabbas mu yake bi amman nasan yadda zanyi maganinsa k'ararsa zan kai gurin uncle ya jefa min shi cikin magark'ama ayi masa dukan tsiya haba dai ke kuwa kamar shi yace kar fu'ad yasoki takarasa mgnr tana dry a daidai lokacin da suka iso kofar gidansu sajida shims yaja ya tsaya tare da parking din mashin dinsa suna fitowa daga cikin motar ya iso garesu yana cewa jimana me'ad. nasan kinsani amman kike pretending kamar bakisani ba ...dau dau ta d'auke shi da mari "how dare you calling my name? yayi saurin dafe kuncinsa yana kallonta.
"me ma yasa kake bina? "kasan ko ni wacece?
"dan jagaliya irinka kake bibiyata "waye ubanka a duk fad'in garin nan ?
jiki a sanyaye yace" daman bawani abu bane amman idan baki tunani ba, ni ne malik wanda muka had'u agurin ciro kudi ..
"and so what?
"jibeka kawai wani wawa dashi ,ko iya fitar da maganar bai iya ba,da muka had'u sai akayi yaya?
"daman kin yar da diary dinki ne shine fa na amsa gurin abokina fu'ad dan nasan shi ba bazai ta'ba biyoki domin yabaki ba ,shi nake ta ajiyarsa kullun ina son nabaki amman bakya saurarata..
"inna ilaihi wa inna ilaihi rajiun ta furta acikin zuciyarta ...........idanunta a kansa
mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 49 to 50
....kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu duka uku sajida me'ad malik, shiru me'ad tayi tana kallonsa batare da ta sake yunkurin cewa dashi komai ba ,sai dai gabadaya nadama tattare da kunyar abinda tayi masa a yanzu ya kamata tare da raunata wani shashi na gangar jikinta," ta wulakanta mafi kusanci ga zuciyarta bisa ga mummunar d'abi'arta...."me yasa tayi saurin marinsa?
"why why why!!! me'ad?
"why did you slap him..?
tana nan tsaye jikinta na rawa har malik yakaraso zuwa inda take tsaye jikinta nacigaba da kyarma ya miko mata diary dinta ......nadama ce fal dankare da zuciyarta "hakika ta cuci kanta ta cuci rayuwarta ba zata ta'ba yafewa kanta abinda ta aikata masa ba matsawar yayi silar rasa fu'ad dinta....."ki amsa ko nabawa kawarki ne?
jin sautin mgnrsa yasa tayi saurin dawowa cikin haiyacinta domin natsuwar tasoma barin gangar jikinta, kallo daya zaka mata kagane kalar damuwar datake ciki.
sai daya sake mgn sannan jiki a sanyaye tasanya hannuta ta amshi diary dinta, shi kuma ya juya tamkar wanda kwai ya fashewa aciki yasoma tafiya , har ya kai gurin mashin dinsa yana shirin hawa yaji sautin muryarta ahankali "tsaya dan Allah sannan tasoma kok'arin takowa zuwa inda yake, jikinta a matukar sanyaye .
muryarta na rawa tace "dan...dan girman Allah kayi hakuri ta furta hkn tana mai runtse idanunta kasancewar wannan shine Karo na farko data bai wa wani mutun hakuri ,bayan iyayenta da suka kawota duniya "kayi hakuri ta sake maimaita kalmar muryata a raunane tare da bud'e idanunta fess akansa tana kallon yanayinsa da gbdy ya sauya, a yanzu dayake gabanta ganin take tamkar fu'ad dinta ne tsaye a gabanta cikin matsanancin damuwa , "hakika nayi abinda bai dace ba ,da rashin kamata gareka,
tun ranar farko dana soma ganinka a gidanmu nayi tunanin kmr nasan fuskarka amman alokacin na kasa tuna inda nasanka, sannan lokacin dana ganka tare da fu'ad a boutiq shima ban tantance alakarku dashi ba amman dai kayi hkr dan Allah.
" babu komai ,komai ya wuce Allah ya kiyaye na gaba, hk daman rayuwar take ,da nabi shawarar fu'ad da ban jawo wa kaina wulakanci ba, domin babu abinda ya kai wulakanci kmr a tsinkaka ta hanyar mari..... ...amman babu komai "me'ad yakira sunanta ,nasan kina mutuwar son abokina fu'ad duba ga yanayin nadamarki bayan kinsa alakata dashi, amman shi mutun ne me matukar kamewa ,kai tsaye hk bazai ta'ba fuskantarki ba ....
"nasani ....nasan da haka amman ko zaka iya taimaka min plz takarasa mgnr muryarta na craking ?
domin zan iya yin komai akansa ,"da fari dai ka taimaka min da number wayarsa tare da sake bashi hakuri.
"sajida plz ki matso kusa mana ki bashi hakuri kema bawai ki wani ja kin tsaya kina kallonmu ba.
"me zance masa me'ad?
"me kike son nace masa after kingama aikata son ranki ?
"i think kin bashi hakurin kuma yace ya hakura.
"eh amman ni dai kice masa wani abu dan Allah har yanzu akwai damuwa a tattare da shi.
"dole kuwa kiga damuwa atare dashi me'ad , bashi ba koni kika karewa kallo zakiga ala'mun hk atare dani "ta yaya daga ambatar sunanki zaki maresa?
" tun ranar farko daya kira sunanki na gaya miki definitely wannan mutumin yasanki wani guri amman kika nuna min sam ba hk bane yanzu wa gari ya waya?
" komai sai kin saka zafin rai aciki, sosai sajida tayi mata fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ba har sai da malik ya nuna abar zance ya isa hk "kuma har ga Allah komai ya wuce daga karshe ya karanto mata number fu'ad bayan tayi tsore, tace yabata nashi yabata sannan ya wuce .
" a she dai mutumin kirki ne nake masa wani irin kallo ta furta hkn tana kallon bayansa .. .......
juyawa sukayi zuwa cikin gidan suna shiga d'akin sajida tasoma neman layinsa amman kiran duniya tayi bai d'auka ba haka takarar da wunin ranar akan kiran layinsa bai d'auka ba.
shi kuwa malik a sanyaye ya karaso gida, duk da har cikin zuciyarsa yana jin abinda me'ad tayi masa ya wuce, amman gangar jikinsa takasa hakurin hk, ganin yanayinsa yasa sudais dake bawa kabeer labarin abinda ya faru a oil and gas a safiyar yau din nan ya karaso gurinsa yana tmbyrsa, shima kabeer yazo ya tsaya dayan gefensa "lafiyarka malik?
" me yasameka duk ka dawo wani iri hk? yayi masa tmbyr ajere. naunayen ajiyar zuciya ya sauke tare da gaya musu abinda ya faru har zuwa Number wayar fu'ad daya bata, dan basa boyewa junansu komai, daga karshe yace "karsu sanarwa fu'ad saboda ya sha ja masa kunne da gargadin abinda zai je yazo .
abinda malik bai sani ba gbdy mgnrsa acikin kunnesa yayita,wanda take ran fu'ad ya 'baci zuciyarsa tazo har wuya tana tafarfasa sai dai ya kudirici aniyar zai ganar daita kurenta ta hanyar tarkonsa data fad'a .
sai gurin tara na dare me'ad ta sake gwada kiransa da dayan layinta, bugu biyu ya d'auka cikin dakakkiyar muryarsa duk da bai san ko number waye ba, "hello..... ji tayi tamkar an mata bushara da gidan aljanna ne dan dadi, lokacin dataji sautin muryarsa ta ratsa cikin dodon kunneta, tayi sallama cikin sanyayyiyar muryarta amadadin "hello din daya ce mata, ," daga can bangarensa yayi shiru kawai yana sauraran yaji ko waye duk da zuciyarsa ta soma gano masa ko wace saboda sautin muryar mace dayaji, ita km hucin Numashinsa dake fita ta cikin wayar ne yayi nasarar kashe mata ilahirin jikinta har yasa ta kasa mgn, jin shirun yayi yawa ne yasa shi cewa "waye yake kok'arin shiga cikin lokacin hutuna?
murmushin fariciki tayi gefe daya kuma hawaye ya cika kwarnin idanunta sakamakon sake jin sautinsa a hassale , sai da ta sake kwantar da muryarta sosai sannan tace "me'ad ce.
"wace hk?
jin abinda yace ya sata mikewa zaune daga kwance datake "uhmm ammm dan Allah karka ce baka ganeni ba, gurin abokinka malik na amshi numberka ?
"kit taji ya katse kiran ta sake kiransa back bai d'auka ba daga karshe taji ya kashe wayar gbdy ranar dai kwanan zaune me'ad tayi ,duk inda ta juya fuskarsa take gani da komai nashi bata ta'ba tunanin zata fad'a tarkon d'a nmj irin hk ba. washegari bata tashi da wuri ba saboda rashin baccin dabata samu yi daren jiya ba. sai gurin 12 ta tashi tashiga wanka.
ta sake neman layinsa da wata number daban yana d'auka tace "barka dai me'ad ce take magana ...kit taji ya katse kiran wani irin sarere tayi agurin ahankali tayi kasa ta zauna akan gadonta sai ga hawaye yasoma ciccikowa a idanunta ta tsurawa wayar ido tana kallo gani take kmr shine acikin wayar.
wani tunani tayi ,zuciyarta ke umartata data kira number malik, take batayi sanya a gwiwa ba tashiga neman layinsa, bayan ya ta sake bashi hakuri akan abinda ya faru sannan ta d'aura da damuwarta "hakuri yabata Inshaallahu zan masa mgn. "ok nagode sosai sai kaji kirana ta katse kiran shi km ya sauke idanunsa akan fu'ad dake tsaye yana shirin zuwa gurin inna kakarsa "fu'ad yakira sunansa.. ya d'ago kansa tare sauke kyawawan idanunsa akansa batare da yace komai ba "dan Allah saurari yarinyar nan ,ka duba kaga yadda ta ajiye jin kanta, gadara takama da komai nata akanka ...
"an so what?
"na aiketa ko nasata?
"kai nifa banida lokacinta yakarasa shirinsa tare da barin d'akin ..misalin karfe 11 :00 na dare kiranta yashigo cikin wayar malik ya d'auka dan lokacin idonsa biyu yana kallon ball tare da su kabeer fu'ad ne dai ke kwance har yasoma bacci ,gaisawa sukayi sama sama "dan Allah malik ka had'ani da fu'ad "ok ya mike tsaye yayinda su kabeer suka bishi da wani irin kallo har yakarasa inda fu'ad ke kwance ya manna wayar a tsaitin kunnenshi ,sautin muryarta yasashi bude idanunsa ahankali yana duban malik dayayi saurin had'e hannuwansa guri daya yana rokonsa daya saurarera. lumshe ido kawai yayi batare da yace komai ba yaji ta sake mgn "fu'ad... dan Allah kayi hakuri da kiran danayi adaidai lokacin nan dole ce tasa hk gbdy na kasa runtsawa.. lip's dinsa ya ciza da k'arfi kmr zai huda, sannan ya kamkame jikinsa guri daya sakamakon jin muryarta, kai bazai iya cigaba da sauraronta ba, saboda zai iya shiga wani yanayi a dalilin jin muryarta da kuma ya birkita masa lisafi idanunsa ya rufe gam yana kawar da tunaninta tare da tunanin hanyar da zai bi ya musguna kmr yadda ta wulakanta malik..... "ina son mu had'u da kai gobe a coster coffee domin akwai bayanai masu matukar mahimmanci danake son mu tautauna da kai "gud dama tasamu ya furta acikin zuciyarsa, wanda a zahirance cewa yayi "okay.
"nagode sai mun hadu gobe karfe biyar na yamma ya katse kiran batare daya tanka ba.
bai je kmr yadda ta bukata sai dai shi yana tabbacin taje tagama tsamanin ganinsa ta wuce sai bayan kwana biyu malik ya matsa akan zance,sannan suka had'u a coster coffee dake awolowo waya gabadaya ta rame fuskarta tayi fayat kallo daya zaka mata kasan bata cikin natsuwarta da hankalinta tsawon minti talatin tana tsaye kmr ance ta juya taganshi sanye cikin riga green me adon pinky a gabanta, gashin kansa a gyare sai sheki yake" kallo kallo sukewa juna kafin daga bisani ya runtse idanunsa tare da zube hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa muryata na rawa tace "ammmmm uhmmm sannu da zuwa gsky ka ..kayi kyau ..wannan ce maganarki mafi tsada ?ya fad'a tare da meida idanunsa ya runtse .
"eh but ta mika masa karamar flower ga wannan kai na kawowa ,dan girman allah ka amsa koda kuwa bazaka amshi tayin abinda nazo maka dashi ba.
a banzace ya kawar da flowers yasamu guri ya zauna yana juya mata baya zagayowa tayi ta zauna ta gabansa tana fuskantarsa "me zaka sha ice cream coffe ko shayi da madara?
"da kyar ya fizgo numfashi kmr zaiyi mgn sai kuma ya fasa .
Zuciyartace tayi tunanin watakilla zai bukaci coffee
Dan hk take tabawa masu kula da gurin umarnin akawo masa coffee ta meida idanunta a kanshi tana satar kallonsa juyar da kanshi gefe yayi kmr baisan me takeyi ba tare da datse lip's dinsa ....
Ganin ta kasa d'auke idanu akansa yasashi yi mata wani irin kallon wanda yasa kirjinta bugawa da karfi, sannan ya d'auke kansa dan shi duniya babu wanda yake jin yana matukar so kmr ita,amman ji da kanta gadara takama da kudin mahaifinta tare da wulakacin abinda tayi malik yasa yake jin kaunarta na neman riked'ewa ,a lokacin ji yake kmr ya tashi ya bar gurin sai dai kafin yayi hk sai ya wulakantata, sun jima tare da yin shiru kowanensu zuciyarsa na saka da warwara, fuad yaji shirun yayi yawa har sanda maikacin gurin ya ajiye tire me d'auke da cups guda biyu ya juya siririn tsaki yaja batare daya kalleta ba " yana da kyau kiyi abinda ya kawoki domin duk lokutana atsare suke babu wata dakika da take a wajena dazata zo face tana cikin tsari don haka kiyi gaggawa sannan ki takaita wajen maganarki dan banason mutun mai surutu ko dogon magana dan hk ina sauraranki .
Me'ad tayi mugun tsaresa da idanunta tare da gyara zamanta tana saukar da numfashi" hakika so wani shu'umin abu ne wanda yake sarrafa duk wanda ya shigesa ,fu'ad da fari dai sunana me'ad kmr yadda na sanar maka a ranar farko da muka had'u muna zaune agarin nan tare da mahaifana ,ba sai na tsaya gaya maka waye mahaifina ba, kana ganinmu kasan muna da milloyoyin Kudi da bazasu lisafu ba sannan...."dakata dan Allah malama kafin ki cigaba da wad'an banzayen kalaman naki "jikeke ke wata jaruma ce ko me dakike zubo dogon bayanai hakan kmr agidan radio ?
kanta ta girgiza tare da cewa "aa.
"ok Kamata yayi ki yi magana me ma'ana da takaitawa kmr yadda na fad'a miki tun farko,
"Ko kin d'auka da hkn da kika soma zaki birgeni ne ?
"dan kin wani zo kina zancen dukiya, kin d'auka soyayya ce a ganin farko bari kiji ba wata soyayya irin haka kin siyo furi kin kawowa saurayi abu ko tsari babu sannan saurayin dasani minti kwanaki kalilan kika yi masa, ki kashe kudinki a wasu abu na kirki wata killa zaki iya samun lada..
Me'ad batayi musu ba tabishi da shu'umin kallo wanda ke bugar masa da zuciya sannan tayi wani irin murmushi duk abinda take bukatar nmj dashi, fu'ad ya tattara, aji kyau kamewa tare da sanin Ciwon kai shima ya juya ya kalleta wani irin shaukin sonta na dibarsa.
" a zahirin gsky maganar dakayi tasa ilahirin jikina yayi sanyi ...
" go straight to your point dan Allah malam.. tsura masa ido tayi gbdy ya d'aureta duk ta inda tayi tunaninsa ya zarta hkn cikin sanyi murya tace ".tun ranar farko dana d'aura idanuna akanka naji kamin, na dad'e ina tunani kmr bamu dace ba amman zaune da nake agabanka na tabbatar da babu nmj daya dace dani kmrka ,ka cancanta kazamo uban ya'yana shiyasa zanyi kok'arin domin naga na fayyace maka na kamo da matsanancin sonka, duk da nasan kaima hk ne dan na cika budurwar da dole nmj ya kalleni ya soni ,ba dan komai kodan kyawuna kudina da kuma tarin ilimi na, da iya kalamai duk da nasan a yanzu hk ka gama amincewa, amman zanso ka furta kanasona kmr yadda na furta maka, sannan ga sakon zuciyata danazo maka dashi takarasa mgnr cikin murya me sanyi ta mika masa wata karamar akwati , amman sam yaki amsa illa idanunsa daya tsura mata"ka amsa dan Allah ni fa sonka nake tsakani da Allah kuma a shirye nake dana aureka.. zan iya sadaukar da komai nawa akanka ciki kuwa har da rayuwata.
Fu'ad yaji gbdy dry ta kufce
Masa yayita dry abinda bai taba yi ba kenan dryr data bayyana hakorarnsa "ni kike so...?
" yes ofcourse dole nasan zakayi mamakin kamata na furta ina sonka, amman kayi la'akari da so ba karya bane ,kuma kagaggen abu ne tunda kan Annabi adamu (a.s) kaga kuwa babu mamaki dan nace ina sonka.
"Tabbas kin burgeni dan naga ala'mun kema jaruma ce da har kika iya kallon wad'an idanuwana kikace wai kina sona duk da kinsa ko acikin mafarki baxakiyi tunanin ni fu'ad zan amince da uzirinki ba, yayi shiru tare mikewa a fusace yasoma kok'arin barin gurin batare da ya amshi abinda ta miko masa ba da sauri tabiyo bayansa tana share gumin daya jikata mata fuska "ka tsaya dan Allah ko coffee din fa baka sha ba , tafiya yake tana biye dashi tare da kokarin son magana " yayi saurin daga mata hannu "karki dameni da banzayen kalamanki, I thought tun farko nace banso mgn dayawa ko? "Ummmm amman Dan girman allah ka tsaya ka saurareni bakasan yadda nake jin zuciyata .
" yi min shiru tare da d'auketa da wasu maruka har guda uku ajere sannan yace "wawiya kawai kinyi zaton a banza zaki samu soyayyarta ko? Har da zuwa da shukun fure da akwatin zoben masoya, kina zaton zan amince da soyayarki ne saboda kina da kudi, iyayenki ma hk kisani wannan talakan daban yake da sauran talakoki koda nake talaka ina tabbar miki wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa dan kije ki samu daidai dake mai kudi da duk abinda kike takama dashi .
"fu'ad ka mareni a bayyanar jama'a dan nace ina sonka?
"yes na mareki ko zaki rama ne?
girgiza masa kai tayi kawsi ala'mun a'a, "ok na d'auka tak'amarki zai sai ki rama dakikiya kawai yana gama karasa wannan mgnr ya juya kai tsaye bakin titi yaje yana tsaida me adaidaita "kai zaka capitol road?
ta biyosa da sauri "kabari na rage maka hanya nima hanyar zanbi "kai me adaidai wuce abunka tare muke dashi batare da bata lokaci ba me adaidaita ya wuce ya sake saida wani nan ma ta hana tare da fito da id card din acp aliyu ta nuna masa kana kuskuren d'aukarsa sai dai ka iske kanka amagark'ama nan take ya wuce yana cewa "kan wani dalili aiko bazam jawowa kaina ba.
tafiya fu'ad yke tana binshi a baya tana rokonsa yazo ta rage masa hanya amman yaki saurarata har sukayi nisa da inda tayi parking din motarta
tsaida me okada yayi kawai kafin tasoma dogon bayaninta tuni me okada ya wuce hk jiki a sanyaye ta koma tashiga motarta cikin tsananin damuwa da bakin cikin abinda fuad yayi mata ta figa motar aguje ta nufi estate dinsu kai tsaye tana wani irin mahaukacin gudu Wanda zai kayi mamaki matuka in idan akace macece take tuka wannan motar ta miliyoyin kudi ,wani irin sautin kidan soyaya ne ke tashi acikin motar tamkar zai tarwatsa motar.
Yayinda samarin dake zaune a layi masu ji da kansu kuma yayan masu kudi irinta sai binta suke da wani irin kallo cikin bakinciki domin duk isarka duk iyawarka da iya wankanka baka isa tayi ma koda kallon arziki bane ballanatana kasanyawa ranka zata saurareka, hk ta ratsa har ta iso makeken gate din daya lullube ilahirin gidan hon daya ,tayi duka mutun ukun dake kula da get din suka taso suna kokarin bud'e mata get tare da jero mata sannu da zuwa amman babu wanda ya isheta kallo balle har ta amsa gabadaya idanunta a rufe suke .
bayan tayi parking a inda aka tanada domin ajiye motocin ta fito jikinta a sabule still zuciyarta na mamaki tareda alajabin abinda fu'ad yayi mata wanda ko a mafarki bata taba expecting wani bil adama zaiyi mata ba da wannan tunani ta taka zuwa parlour mahaifiyarta, inda ta cusa kai tare da yin sallama aciki .
Momy ta d'ago tana dubanta kallo daya tayi mata tasan tana cikin damuwa amman sai ta ajiye hkn akan aikin data fara ne, yasanya yanayinta ya sauya cikin sakin fuska momy tace " duk gajiyar hk?
Naunayen ajiyar zuciya ta sauke batare datace komai ba illa kwanciya datayi akan kujera tace ".ganin nan dai momy kwata kwata bansa abinda ke damuna ba "allah ya kyauta momy tace kawai tare yin shiru kana ta sauke ajiyar zuciya momy tayi "ni kuwa me'ad ina son nayi wata tambaya . " kai momy zaki fara ko, kwana biyu kin barni nayi kiba amman yanzu zaki soma yi min zance safwan abinda kika san banason jin a halin yanzu....
Momy ta maso kusa daita tare da dafata "haba me'ad yanzu arayuwa babu wanda baya son cigaba ,idan kika aure safwan zaki samu cigaba arayuwarki da wata daraja ta Musamman..
"Kai momy meyasa zaki dinga yin irin wanna bayanan , ada kinsa duk duniya babu mutumin Dana fi muradin kasance dashi kmr sa, amman yanzu an wayi gari bana bukatar hk, momy kudi fa da kike ganinsu a yanzu nasan basa siyan kima daraja mutunci kwarjini soyayya ,dan hk momy ki daina irin wanna tunanin kiyi fatan na auri wanda zai bani farinciki ina son fuad .....
Duk da nasan takala ne tulis......kuma zan auresa duk da talau...
Subuhallahi karki sake ki karasa wannan kalmar domin fiyayen halita ma yanemi tsari da ita dole ina son kiyi aure wanda duniya take damawa dashi wanda shi da mahaifinsa, suka maza masu abin hannunsu kuma bazan so ki auri Wanda bai kai ubanki kudi ba, sai wanda yafi shi dan haka a kullun adduar da nake miki kenan, ki janye batun yaron nan tun mahaifinki bai ji ba, idan dad dinki zai amince da aurenki dashi ni meye nawa aciki ?duk yadda nake son kiji dadi a gidan safwan hk zan hakura amman da zaki yarda ki amince kwarya tabi kwarya atsakaninku dana ji dadi sannan ki shiry tarban safwan yana kan hanyar dawowa .
Me'ad ta ta'be baki aranta tana jin zata iya yaki da kowa akan fu'ad , ahankali ta mike ta nufi bangarenta inda ta iske ummi tana faman goge goge tayis din dake barandar .
Ummi tana ganinta ta mike da sauri tana cewa "aunty sannu da zuwa, tsaki me'ad taja a maimakon ta amsa mata tayi shigewarta ummi tacigaba da abinda take yi aranta tana mamaki yanda me'ad ta d'auki duniya da zafi hk, duk da tun kafin tazo duniya anyi wad'an da suka fita wulakanta mutane amman babu wanda aka taba nunawa aka ce yayi nasara, balle itama tasanya ran wata rana zatayi nasara wannan girman kan nata ta sake ajiye numfashi tacigaba da aikinta.
mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
Page 51 to 52
.......kwance take akan makeken gadonta kiran italy tana kallon saman d'akinta ,sosai tayi zurfi cikin tunanin lamarinta da fu'ad tare da neman mafutar yadda zatayi, ahankali ta mike zaune ta koma gefen gadonta ta zauna tare da lullu'be kanta da hannuwanta duka sakamakon bugawar da zuciyarta keyi akansa ,tamabayoyi tashiga jerewa kanta d'aya byn d'aya "me yasa fu'ad yaki amincewa da tarin soyayyata garesa?"me yasa ya mareni akan nace ina sonshi? "Kodai Malik ya gaya masa abinda ya faru ne da hkn yazamo silar d'aukar fansa gareni ta hanyar disgani cikin bayanar nasi..."ga shan mari har uku ga rashin amincewa da soyayyata da bai yi ba... "yanzu ya zanyi da rayuwata ? Ta sake jehowa kanta tmby.
" ina bukatar fu'ad arayuwata kuma zanyi komai akansa domin naga na mallakesa. wani abu ne data samu yazo wa zuciyata shine sake jin fu'ad datayi ajikinta yana yawo cikin jinin jikinta, tayi saurin goge hawayen da suka cicciko a kwarnin idanunta ya kawowa kuncinta ziyara, tasa hannunta ta dango d'igan hawayen tana kallo "yau itace ke kuka akan nmj?"nmj ma d'an talakawa wanda ba kowa bane...mikewa tayi ta isa gaban dress mirror dinta ta tsaya tana karewa kanta kallo daga samanta har k'asa "meye tarasa ajikinta kyau ne ko me da har fu'ad yake mata kallon ita bakowa bace?
Ahankali take karewa cikar halitar da Allah yayi mata, tayi imani ko ita ta isa tasa fu'ad ya fuskanci lamarinta yasota fiyye da yadda take masa, sai alokacin ta lura da irin yadda gashin kanta data d'aure duk ya wargaje a saman kafad'unta adalilin tunaninsa ,hannuta ta kai kan wayarta tasoma neman layinsa, Amman yaki d'auka, kasa hakuri tayi tacigaba da kiransa har sai data yi masa kira yafi sau goma bai d'auka ba sannan ta nemi layin malik kira daya biyu malik ya d'auka, bayan sun gaisa tace "malik kuna tare da fu'ad ne ka had'ani dashi?
" a,a ina gurin kallon ball, na dai barshi tare dasu kabeer a gida.
"Okay idan bazaka damu ba zanyi maka wasu 'yan tambayoyi, amman ina bukatar jin gsky daga bakinka ."uhmmm ina sauraranki?
"Ka ta'ba gayawa fu'ad abubuwa da suka dinga faruwa atsakaninmu da kai har zuwa kan marin danayi maka?
sai daya ja naunayen ajiyar zuciya ya sauke da kyar sannan yace"alahakikanin gsky wasu Abubuwan yasani sai dai batu na mari bai sani ba, dan ban gaya masa ba, wani abu ne ya faru da har kikayi tmby?
"Nothing ,Amman yanzu wani irin taimako zaka min malik akan abokinka?"na maseefar kwadaituwa da aurensa, ina son shi sosai kuma zan iya yin komai akansa matsawar zan sameshi, ka taimakawa rayuwata malik nasamu fu'ad, nayi maka alk'awarin zan maka komai ciki kuwa har da samammaka aiki a karkashin ikona tunda shi yaki amsa daga gareni ..?
Numfashi da ajiyar zuciya ya sauke atare kana yace "zaki iya mallakar zuciyar fu'ad cikin sauki dashi kansa gbdy, bisa dalilin abu daya da sauri ta katse Shi ta hanyar cewa"meye shi malik ka fad'a meye shi zan iya yin komai akansa "meye zanyi fu'ad yasoni?
"Bawani abu bane daya wuce kyautatawa, fu'ad na matukar son kyautatawa ,da km kyautatawa wanda ya cancanta most especial mara shi,ina tabbatar miki matukar kika kasance daya daga cikin masu kula da kyautatawa zaki mallaki zuciyar fu'ad cikin sauki batare wata matsala ba, ni kaina ina miki sha,awar aurensa domin idan kika sameshi amatsayin miji ina me tabbatar miki zaki yi alfahari samun miji kmrsa "shikenan malik nagode sosai da shawararka, km InshaAllahu zanyi kok'arin naga na kasance cikin masu kyatatawa mutane, gobe karka manta kasameni a oil and gas.
" InshaAllahu bazan manta ba Na gode sosai Allah ya mallaka miki zuciyar fu'ad "ameen nima nagode da wannan adduar taka sai mun had'u goben ta katse kiran ta koma gadonta ta zauna inda zuciyarta take bata umarnin me zai hana ta tura masa ko da sakon text message ne tunda yaki d'aukar wayarta hannuwanta duka tasa ta rike wayar tasoma rubutu sako kmr hk.
_Assalamu alaikum ina fatan kana cikin koshin lfy, daman na turo maka wannan sakon ne domin na k'ara baka hakuri bisa ga kalamaina na d'azu danayi amfani dashi ,wanda sukayi silar 'bacin ranka har ka mari kyakyawar fuskar matarka, azahirin gsky naji babu dadin abinda kayi min ,sai dai tarin soyayyar danake maka ta hana rashin jin dadin nawa tasiri ,ina sonka fu'ad har bansan yadda zan misalta maka ba, ka daure ko ba yawa nima kasoni kwatankwacin yadda nake sonka I really sorry for what I did ..sai da safe daga mai sonka Me'ad Ediris Takai_
Tana tura masa ta koma kan ganta, ta kwanta lamo tare da runtse idanunta bawai dan tana jin bacci ba, sai Dan shaukinsa dake dibarta ,gudundune jikinta tayi, lokacin da tunaninsa ya yawaita ajikinta dan har ta fara hango sunyi aure dashi da yadda yake sarrafata akan bed gurin aika mata da zafafan romancing dinsa masu birkita 'kwal'kwaluwa.
A kwancen dayake a d'akinsu sanye cikin jallabiya fara sol hannunsa rike da wayarsa yana brownsin sakonta yashigo ,amman bai bi ta kai ba yacigaba da abinda yake, km ko bayan daya gama bai duba ba yayi kwanciyarsa, ranar dai me'ad bata samu ta runtsa ba duk inda ta juya fu'ad take ganin da hannunsa dake yawo a ilahirin jikinta .
Washegari tun 7:00 malik ya tashi yayi shirinsa ya iso oil and gas, sai dai bai iske me'ad ba dan bata karaso ba tukun, yasamu guri ya zauna zaman jiranta, sai gurin takwas tashigo cikin hadaddiyar motarta kiran toyota Camry ta gabansa ta wuce amman bai ganta ba saboda ba'a cikin irin motocin daya saba ganinta ciki bane, bayan ta isa office dinta da kmr minti 2 tasa ayi kiransa,cikin wasu 'yan mintuna malik ya bayyana a office dinta cike da girmama ya gaisheta, ta amsa da kulawa sannan ta nuna masa gurin zama da hannunta kana ta bukaci takardunsa ,batare da 'bata lokaci ba ya mika mata, bayan ta duba ta mike tsaye "kabani minti 20 "ok badamuwa ranki ya dade. Kai tsaye office manager ta nufa domin neman alfarma.
Acikin awa daya kacal malik yasamu aiki a ibadan karkashin kulawar me'ad amtsayin wanda zai dinga kula da ficen da shigen kud'ad'en kasancewar accounting ya karanta
Lokacin da wannan labarin yasameshi a zaunen dayake a office dinta, yayi matukar murna da farinciki, godiya ya dinga yi mata kmr zai mata sujada, aikin daya d'auki sama da shekaru biyar yana nema sai gashi yasamu acikin awa daya nigeria kenan kayi karatun kagama sai kana da hanyar zaka samu aikiyi..
"Kabar min godiya hk nan ,ka godewa Allah daya nufeka dasamu, sai dai shawarar da zan baka ,ba wuce ka rike aikinka da mahimmanci ba ,domin mutane dayawa irinka na can suna nema kasa danaka basu samu ba , sai abu nagaba ka taimaka min nasamu fu'ad.....
"Angama ranki ya dad'e InshaAllahu zanyi iyakacin kok'arina akan lamari, "ok ranar Monday zaka soma aikinka yanzu zakayi dropping account number dinka, akwai wasu kudin daza'a tura maka domin siyan sutura.
"Nagode nagode!!! ranki dad'e wallahi har bansan irin godiyar da zan miki ba ,hk suka rabu malik na farinciki samun aiki ita km tana murnar zata samu fu'ad cikin sauki tasan idan yaji itace tasammansa aiki zaiyi farinciki wata killa adalilin hk burinta ya cika.
Koda malik ya jewa fu'ad da labarin samun aikinsa ta hanyar me'ad, yace "tayi kokari sosai, sai dai kajira ranar zuwan wulakanci daga gareta, domin wannan aikin daka amsa daga hannunta daidai yake da ka amsarwa kanka wulakanci ne da damuwa, ni dai babu ruwa duk abinda yaje ya dawo sai dai ya kare akanka.
"Wace irin magana ce hk fu'ad?
" gskyar lamarin nagaya maka sai kayi taka tsantsan "Naji ni dai ka min addu'a shi nafi bukata daga gareka bawani dogon sharhi ba ,sai agame da zance me'ad , yarinyar nan ta damu da lamarinka dayawa , ka duba kagani kyau ilimi nasaba duk tana da, uwa uba gata da zuciyar taimako "ai ta taimaka maka dole ka fad'I hk mana , ni dai ina umartarka ka takaita maganarta anan dan kadameni da zance ina da abubuwan yi.
Malik yayi dry sannan yace "ni da zakabi shawarata da ka amince ka aureta komai cikin sauki zaka samu aikin ma dake bulayin nema ba sai kaje ba, kana daga kwance za'a yi maka komai."to baza'a d'auki shawarar taka ba ,idan ka damu da lamarinta har hk ka aureta mana ,ai daman kana sonta.
"Ina sonta bata sona kai take so, da kace ni ta nuna tana sona wallahi ina tabbatar maka babu abinda zai hanani aurenta,"yanzu ma zaka iya gwada sa'arka yana karasa fad'ar hk ya wuce ya bar malik tsaye yana kallon bayansa.
*********
Duk abinda me'ad zatayi domin shawo kan fu'ad tayi, tabi abokansa da duk wani wanda tasan suna muamula, duk inda tasan zata ganshi kafafunta na gurin amman ko kallo arziki bata isheshi ba ,asalima yana ganinta zai bar gurin yakama gabansa, acikin tsakankanin wannan lokacin ne labarin rashin lfyrsa ta risketa, bata tsaya sanya a gwiwa ba ta nemi malik da yayi mata rakiya, shine yayi mata jagora har gidansu inda ta tsaya kallon ruba'b'ben gidan dake shirin zubowa "kace na ne gidansu malik?
"Kwarai kuwa nan ne gidansu "kina mamaki ne?
Shiru tayi batare datace masa komai ba illa tsurawa gidan idanu datayi "yanzu anan fu'ad dinta ke rayuwa tun tasowarsa? A she fili tayi zance batasani ba ,
"Ki daina mamaki ranki ya dad'e nan ne gidansu kuma inda yayi rayuwa acikinsa idan kin mutsu ne mushiga Kigani d'aki na d'aya na biyu nan ne d'akin kakarsa.
Tana gama sauraransa ta juya ahankali Jikinta matukar a sanyaye tashiga cikin parlour gidan me cike da duhun tsiya ,hannunta rike da karamar jakarta da kyar take ganin inda take sanya kafafunta duk rana ce ba dare ba ,yayinda malik ke biye daita da manya manya fararen lododi guda biyu ,taja ta tsaya abakin kofar shi km malik yayi sallama tare da kutsa kanshi cikin d'akin sannan itama tayi sallama tashiga "a'a Malik kai ne hk da rana tsaka ?"to marhabun lale ku karaso ciki mana inna ta fad'i hk tana mai mikewa ta shimfid'awa me'ad dadduma ,Dan shi Malik tuni ya ajiye lododin hannunsa yakarasa inda fu'ad yake.
Duk wanda yasan d'aki marasa shi hk d'akin yake bawani shararrun kaya ne acikinsa ba illa wani D'an madaidaicin gadon, sai kayan miyar dake ajiye gefe guda mai nuna alamun na siyarwa ne, gefe daya km wata katuwar akwati ce ajiye kallo daya tayi wa d'akin tasan d'akin marasa shi ne kmr yadda gidan yake sai da ga dukkanin Alamu yana samun kulawa ta hanyar gyara da tsaftaceceshi .
cikin ladabi tamkar ba ita ba, ta durkusa har kasa kanta a sunkuye cikin sanyi murya"inna barkanmu da warhk ya gida da me jiki.. inna ta amsa cikin sakin fuska da kulawa batare datayi tunanin inda tasanta ba saboda ganinta tare da Malik .
ahankali me'ad ta juya inda fu'ad ke zaune Wanda ke aikawa malik da uwar harara sanye cikin gajeren wando da T shirt fara sol gashin jikinsa kwance luf Luf tmkr na jarirai ,ta gaida uban gayyan da ko kallon inda take bai yi ba " ina yini ya jikin ? abunda me'ad ta fad'a Kenan taja bakinta tayi shiru.
ya d'an d'ago kad'an yace lfy atakaice shima dan inna tayi masa ala'mun da kafarta ne ,me'ad ta sake yin wani kayataccen murmushi sannan tayi shr.
Malik yayi gyaran murya sannan yace "inna ga surakarki budurwar fu'ad tazo duba lfyrsa ..inna tayi dry "kace kishiya ce shine har da bata gurin zama ,shi kuma jairin sai wani cika yake yana batsewa kmr ba yanzu nagama fama dashi gurin shan magani. Me'ad ta sunkuyar da kanta alamun kunya .malik yace " har yanzu fu'ad bai bar gudun magani? " ina fa har tsoron rashin lafiyarsa nake saboda hkn.
Mead ta dago da niyyar ta saci kallonsa ,karaf suka had'a idanu atake kirjinsu ya buga, tayi saurin d'auke idanunta Dan bazata iya cigaba da kallon surar jikinsa inna na gurin, sai dai muryarta a sanyaye tace "inna me yasa aka barshi a gida ba'a kai shi hospital ?
"Wannan za'a kai hospital inna ta nuna fu'ad daya yatsina fuska alamun damuwa inna tacigaba "mutumin dake gudun magani balle allura idan kika ganshi kuzarin jiki kawai garesa amman laulauyi garesa sai ki kishirya, murmushin jin dadi mead tayi ganin tasamu karbuwa agurin inna .
sun jima shr sannan inna ta mike tayi waje ,shima malik yace "bari nabawa masoya guri, tsaki fu'ad yayi batare daya tanka masa ba .
Yana fita fu'ad ya gyara zamansa cikin rashin jin dadi fitar da inna da Malik sukayi dan ba'a son ransa ba, dan babu yadda zaiyi ne.
me'ad ta matso zuwa inda yake ta tsuguna tare da cewa "fu'ad...
Sam bai kalli inda take ba hasalima cigaba da danna wayarsa dake rike a hannunsa yayi, tayi kusan minti uku sannan tayi kokari kai hannunta da zumar Kwace wayar hannunsa ya kallota a fusace tana dakatar daita da manya idanunsa domin bayason kusancinsu a yadda yake Dan shi kadai yasan abinda tafiya acikin jikinsa tsawon minti 2 yana tsare daita da manya idanunsa kafin daga baya yasoma mgn kasa kasa "karki wahalar da kanki da wata banzar kalmarki ko gaya min uzirin abinda ya kawoki,domin ina tabbatar miki sam banyi murna ganinki kusa da innata ba ,ni a bangarena bai zama lallai dole sai na soki ba ko yin wata muamula dake ba, dan haka ki daina wani rawar kafa dan sam ba birgeni zakiyi ba, dani bakowace mace ce zata iya yaudareni ba ..
me'ad datayi masa kuri da idanunta tana kallonsa ta saukar da numfashi tace" na jinka fu'ad sai dai abinda nake son kasani tunda nice naganka kuma na aminta da kai, zan iya d'aukar komai tare da shanye duk wasu kalamanka gareni sannan zanyi komai dan ganin na mallakeka amatsayin uban ya'yana koda dukiyata zatakare da numfashina..
wani irin kallon banza fu'ad yayi mata irin na sama da kasan din nan sannan yace "iska na wahalar da mai kayan kara .
"Ina tabbatar maka wannan iskar bazata wahalar da mai kayan kara ba ,domin zamu kasance cikin inuwa daya koma nace bargo daya . tana gama wannan mgn ta juya cikin fushi tayi ficewarta shi kuwa fuad daya bita da kallo ya saukar da numfashi cikin sanyin jiki ya mike daga inda yake zuciyarsa cike da tunaninta tabbas tana matukar burgeshi muttaka, har yana jin idan bai sameta ba komai zai iya faruwa dashi .
bayan tafiyarta tashi yayi ya sake yin wanka yasanya kananan kaya marasa nauyi ya tsaya fesa turare inna tashigo hannunta rike da bakar leda mai dauke da ruwan roba da Malta Amman taga wayam babu yarinyar dazu babu alamunta cikin sauri tace " kai fu'ad ina yarinyar da malik?
Kafadunsa ya daga mata alamun bai sani ba sannan yasanya kai yayi waje inda machin dinsa ke parke.
tuki take cikin 'bacin rai tana ciza yatsan hannuta gbdy ta kagara taje gida domin ta samawar kanta mafuta akan lamarinta da fuad wani irin taka birki tayi dan karfi gudun kada ta buge abinda tagani a gabanta.
a matukar fusace ta fito daga cikin motarta tayo waje inda tsohuwar take tattakawa ahankali saboda tsufa datayi Dan har ta d'an rankwafa "haba matar nan wannan, wani irin mugunta ce hk wato ke kin gama cin kuruciyarki A cikin tsiya shine zaki ja min masifa wato idan na bugeki kika mutu a kamani ko? to in har hk kike nufi ki sani idan na bugeki na kad'e banza dan dake da kuda daya ne agurina dan hk ki matsa kafin nabi ta kanki da mota..
tsohuwar ta d'ago da kyar ta kyalleta tace yarinya kiyi ahankali ahankali domin an yi wasu kafin ke kuma basu ta'ba cin riba ba kinga kema baxaki ciki riba.
me'ad taji wani irin 'bacin rai ya turnukota sai dai lokaci daya shawarar da malik yabata ya fad'o mata "fu'ad na matukar son kyautatawa da kyautatawa marashi kenan irin wannan kyautatawa yake nufi?
"bugu da kari mgnr tsohuwar ta kashe mata jiki murus,Dan HK tasoma nadamar abinda ta aikata da farko ta matso sosai kusa tsohuwar tare da rage sautin murya kasa sosai"inna dan girman Allah kiyi hkr nayi nadamar abinda na aika miki, ni kaina bansa abinda yasa wani lokacin nake reacting hk ba, amman kiyi hkr idan magana ta 'bata miki ,muje na tsalakar dake ta kai hannu zata ta'ba tsohuwar tace "dama kin bar shi yar nan zan iya tsallakawa, sai dai naji dadi da kikayi saurin gane kuskuren abinda kikayi ,ita duniyar ma guda nawa take?" ku dunga d'auka da mai kudi da talaka duk abu daya, saboda Allah da yayi mai kudi shi yayi talaka ba kuma dan baya son shi ba.
"Haka ne inna na gode sosai amman kiyi hkr kibarni na taimaka miki tayi saurin komawa cikin motarta ta kirgo kudi wanda zasu kai kimanin dubu goma ta dawo inda tsohuwar take ta riko hannuta tasanya mata kudin "inna ki amshi wannan dan Allah karki aa"kai yar nan har da wata hidima to nagode kwarai da gaske Allah yayi albarka, Allah yayi miki abinda kike so Inshaallahu zaki gama da duniya lafiya. "Ameen inna na gode.
fu'ad da fitowarsa kensn abun ya faru akan idanunsa duk da bai ji tautaunawarsu ba ,Amman ya ji dadin taimakon datayiwa matar har sanda ta tsallakar daita dayan bangaren tsohuwar na dariya tare da d'aga mata hannu ta koma tashiga cikin motar ta figa a guje yana kallon sannan ya taka mashin dinsa yacigaba da binta abaya batare da tasani ba ,har inda ta sake tsayawa saboda hango wata makauniya rike da yar jagoranta wace bazata wuce kamin shekara takwas ba ta mika musu sadakar dubu daya bayan ta tsaya sun tsallaka abu kmr wasa hk ta dinga taimako mutane wanda abin yacikasa da mamski "daman tana da zuciya irin hk me kyau ?"gsky idan har tana da irin wannan halin na taimakawa marasa karfi ta cancanta tazamo abokiyar rayuwarsa, adaidai jection din bankole suka rabu shi yayi titi dopemu road ita kuma kai tsaye gida ta nufa inda ta iske sunyi bakin da suka dade suna expecting zuwansa, wato safwan almustapha maitama daga kasar hollond, mahaifin safwan baban mutun ne a kashen duniya gbdy ,sannan me gidan mahaifin me'ad ne a can baya kafin yayi rites . Safwan ya dawo daga kasar Holland ne da niyyar abubuwa guda biyu, na farko cima burin auren mead daya kwalafawa ransa tun shekarun baya, sai abu na biyu cigaba aikinsa amatsayin shugaban shashi na kasuwancin Nigeria.
jin ana jera mata sannu ne yasa mom dinta yin saurin fitowa dan tayiwa yar tata gargadi kada ta kawo musu wargi .
me'ad ta kalli uwar cike da mamaki "ni wai momy meyasa kike min hk ne?" narigada na gaya miki na canza mind dina akansa yaje gaba ya auri matarsa ni matar fu' ... momy tayi saurin rufe mata baki "karki sake me'ad kiyi ganganci, karkiyi wasa da damarki,domin damar mutun sau daya take zuwa masa arayuwa, ina shawartaki karki bari taki ta subuce miki.
me'ad tayi wani irin murmushin sannan tace, karki damu momy da subucewar wannan damar ni dai fu'ad nake so simple as that tana gama fad'ar hk tashiga cikin parlour'n mahaifinta wanda sai bakinsa masu mahimmanci yake tara acikinsa ,ta samu gefe daya ta zauna "dad sannu da zuwa ya hanya ?
mahaifin safwan ya amsa da kulawa sannan ta waiga inda safwan wanda tun shigowarta idanunsa ke kanta yana kallonta saboda wani irin azababben kyau dayaga takarayi masa sai dai ta rame kad'an Wanda bai San dalilin faruwar hkn ba ,sautin muryarta ce ta dawo dashi "yaya ina yini?
ya lumshe idanunsa na second biyu sannan ya bud'esu fess akanta kanwata kin yini lfy?
tayi masa wani irin kallo mai bugar da zuciya sannan tace lfy atakaice.
sun jima a parlour'n dad dinta ya dubeta yace ki kai yayan naki lambu ya huta mana , babu mutsu me'ad ta mike shima yabi bayanta cikin matsananci farinciki yayinda ita kuma ba'a son ranta ba Dan dai babu yadda zatayi ne.
wani parlour'n ta kai shi al wanda duk gidansu babu irinsa an maserfar zuba abun duniya agurin ,an zuva komai wanda me rai yake burin mallaka.
bayan ya zauna tasa aka gabatar masa da abubuwa sha kmr yadda tasaba sannan ta sake tashigowa batare da wani abu ba ta zauna shiru batace masa komai ba gbdy sai yaji baya bukatar cin komai dake gabansa illa matsowa da yaayi ya saita bakinsa daidai kunneta "ina sonki mead dayawa amman banji dadin yanayin dana ganki ba at least kinsa ina bukatar kulawa daga gareki. .tace har da gaske kana sona har yanzu ka mayar da akalar soyayyata ga wata in har kana son farincikina .
A matukar firgice ya tsura mata ido yana kallonta Kafin daga baya yace "no no hkn ba zai yuwuba "saboda me ?"saboda bana sonka yanzu sannan karka kazamanto me yawan wahalar da kanka wajen sake tadda zance aurenmu domin ahalin yanzu zuciyata bata gareka , ta kamu da soyayyar waninka ,da sauri safwan ya kalleta cike da matsanancin mamaki abinda take fad'a masa yayi shiru ya kasa cewa komai illa jikinsa dake rawa..
"kaji abinda nace amman har yanzu ka kasa Cewa komai, ko magnata ta kurmanta da kai ne?
. "ko daya kawai mamaki kikabani shin kin manta matsayina a gidan nan dama duniya gbdy?
"sam maganganunki a yau babu girmamawa balle nuna tarbiya, "dan Allah ki gyara maganarki sam banji dadin yadda kika min ba saboda har yanzu ina sonki me'ad kuma banga abinda zai hanani aurenki ba matukar ina raye.
da sauri me'ad ta kalleshi cikin mamaki tayi wata dry na rainin hnkl " amman baka kyautawa xuciyarka ba sannan bakayi tunani me kyau ba, karkayi takamar dan mahaifinka me gidan mahaifina ne bazai sa nagaya maka abinda ke cikin zuciyata ba, idan kuma kayi kuskuren aurena girmamawa zai yi wahala ka samu romon da maxa dayawa in sunyi aure suke samu ba sai nagaya maka ba dan nasan kaima agidanku akwai irina safwan kake ko wa kake ;? ina son nagaya maka wallahi ban ta'bawa yiwa kowani mahaluki karya ba ko shi waye to kaima bazan ma karya ba, safwan har ka aureni bazan maka biyyaya aure ba sannan bazakayi min kulle ba, duk abinda nake so shi zanyi agidanka,kuma ba lallai ne na dinga maka girki ba idan taka ma har Wanda nake so sai na kawoshi gidanka kuma nayi duk abinda nake so dashi ,idan har kaga zaka iya to kana iya turo a karasa mgnr aurenmu da kai ,idan km ka janye niyyar aurenka akaina sai mucigaba da muntuncinmu , tayi shiru tare da mikewa tayi hanyar kofa, har ta zira kafarta daya a kofar parlou'n sannan ta tsaya batare data jiyo ba tace zaka iya fitowa ka tafi tunda na sallameka ..
tana gama fadar hk ta juya shi kum safwan da bita da kallo sannan ya saukar da numfashi ckin sanyi jiki ya tashi ya nufin parlour'n zuciyarsa cike da tunaninta tabbas yasan yana son me'ad so kuwa me tsanani har yana ji aransa matukar bai aureta ba tabbas akwai Matsala dan wannan abun datayi masa mugun burgeshi tayi shifa bai ga dalilin da zai bar wani me'ad dinsa ba alhalin yana raye bai mutu ba ,babu wannan nmj a duniya kuma kowaye sai ya nemoshi da karfinsa da dukiyarsa .
ita kuwa me'ad byn tafiyarsu ta shige part dinta ta sake wanka tasanya kaya marsa nauyi sannan ta fito paloun mom dake zaune ita kadai tana kallon labarai a CNN jin takun me'ad tana saukowa daga step " momy kallon kike ke kad'ai a parlour'n ina suhailat ?
momy tayi dry ai daman yanzu zan kiraki dan ina son naji yadda kuka yi da safwan.
me'ad tayi saurin kallon momy tace "waye km hk an?
da sauri momy tayi saurin kallo me'ad cikin mamaki da tsoro, cike da in ina momy tace " me'ad me ye nufinki?
batare da ta kalli momy ba tace "nufina bawai wuce ya nemi wata ya aura ba danni har abada ta fu'..
"yi min shr me'ad kada ki meidamu kanana mutane tare da meida hannun agogo baya dan wallahi tallahi baki isa ba a wannan karon mune muka haifeki dole muyi duk yadda muke so dake wallahi baki isa kiyi mana mugunta ba dan hk ki meida hankalinki cikin jikinki tun kafin mahaifinki yaji .
"momy kingama ?
me'ad ta fad'a batare data kalleta ba, bata jira abinda momy zata ce tacigaba "mom ni babu ruwana da dady yasani dan nafi son hk, kowa fa takasan yake yi yanzu dan hk baxaku matsamin ba, dan kawai kun kawoni duniya, ku dai yi hkr zanyi shawara da zuciyata idan na rarrashita akan fu'ad taji zata iya rabuwa dashi fine then zan iya auren safwan ,amman idan taki hakura sai dai kuyi hakuri, duk yadda nayi da zuciyata zan gaya muku tana gama fadar hk ta mike zata fita momy itama ta mike cikin bacin rai da fushi ta riko hannunta har sai datayi kara.
"momy cire min hannuna zakiyi dan kawai banason safwan ?
momy dataga ala'mun fa yarinyarta tayi zurfi sai ta kwantar da murya "kiyi hkr me'ad ki zauna muyi mgn nasan zaki fahimci mamanki.
me'ad ta kurawa momy ido tana saukar da numfashi momy "kema kiyi hkr ki barni da zabin raina sannan mgnr da zamuyi ,mayi idan na tashi daga bacci tana karasa fadar hk ta mke ta koma samanta momy tabita da kallo cikin takaicin domin ita kad'ai tasan bala'in daza'a yi idan mahaifinta yasan tana soyayya da talaka abunda shi ya tsana kenan had'a hanya da talaka arayuwarsa .
me'ad kuwa gadonta ta haye tayi kwancinyarta tare da rufe idanunta fu'ad fess take gani acikin idanunta har ga Allah wani irin so take masa me tsuma zuciya da wuyar bari ..hk tayita tunaninsa har bacci ya dauketa bayan ta tashi momy tashigo d'akin tayita rarrashita amman furrr taki yarda da zabin iyayenta "momy tun farko banason safwan ke dady kuka matsa min ,ta yaya yanzu nasamu wanda nake ku nemi hanani aurensa.
"Ba hanaki aurensa mukayi ba ki tuna alkwarin dake tsakani Dan allah yarinyata ki duba lamarin nan "momy kema uwa ce nasan kinsa abinda ake kira da soyayya tunda nasan ba hadaku akayi da dady ba, ku kuka ga junanku ,ina rokonkanki momy ku barni da fu'ad wallahi akansa zaku iya rasa takarasa mgnr tana kuka . ..tsakanin uwa da 'ya tuni itama ta sauko taji zabin diyarta yayi mata, zata bata damar ta auri zabin zuciyarta..
Ranar da kyar safwan ya runtsa kwana yayi yana zubawa cikinsa giya da tunanin abun yi, "tabbas yakamata ya d'auki mataki nemo kowaye ke kokari kawo rayuwarsa nakaso ,tun da sanyi safiyya ya baza yaransa domin bincike akan wanda mead take so .
Tashin farko bincike ya zo masa akan yadda bai so ji ba ,domin duk wani abinda ya danganta da fuad da rayuwarsa sai daya zo masa daki daki ya sha mamakin" wai Dan talakawa me'ad take kokarin neman gujewa aurensa ,aransa yace" idan kinsa wata ai baki San wata ba ,nasan dai babu ta yadda za'a mahaifinki ya yarda ki aureshi, balle shi karan kanshi yaron bai sonki ,gbdy safwan yazaba yaransa a gari domin cigaba da kawo masa rahoton komai akan fu'ad.
******
ranar monday da misalin karfe 1:00 na Rana kabir yazo gidansu fu'ad domin zuwa office din Alhaji Abubakar aminin mahaifinsa Wanda zai samarwa fu'ad aikin da kaninsa ,a shiryensa yake zaune a kofar gida yana zaman jiran karasowar kabir yana hangosa yashiga cikin gidan inda yakewa inna sallama "inna mu za fita akan zance neman aikin kiyi min adduar samun nasara kansa ta dafa "InshaAllahu zaayi nasara zaka samu wannan aikin ina jin hk ajikina sai dai Wani tsananin rabo"allah yasa ni na wuce, "a dawo lfy Allah ya tsare, "ameen ya fice daga dakin .
kai tsaye company da alhj Abubakar ke tafiyar da aiki suka nufa akan lefan din fu'ad suna isa suka iske jama'a wanda dayawansu neman abunyi ya kawosu, batare da bata lokaci ba suka nufi office Alhaji Abubakar inda suka iske shi yana sallah sai mataimakinsa sukagani suka gaisa ya nuna musu gurin zama "ku zauna ga guri nan ,suka zauna har zuwa sanda ya idar yakaraso garesu inda kabir yayi saurin cewa dady barka da Warhk "a'a kabir har kun iso?ya fad'i hk tare nufar hanyar office dinsa dake cikin wanda suke zaune da sauri kabir da fu'ad suka mike sukabi bayansa atare suka shiga kabir yasamu guri ya zauna akan daya daga cikin kujerun gurin tare da jawa fu'ad shima ya zauna "ai kuna da sa'a duka takardun mutun biyu din da ka kawo sun samu aiki,Amman D'an bani minti 2 ya fadi hk sakamakon wayarsa dayaji ta d'auki kara ya zagayo ya zauna mazauninsa tare da d'aukar wayar ya manna kunnesa abinda yaji ne ya kusan bugar masa da zuciya "safwan almustapha maitama ne ke mgn da kai daga nan office din jakandancin na kasuwancin Nigeria, naji ance wani mai suna fu'ad yazo neman aiki gurinka ko ba hk ba ?
"Haka ne ranka ya dade.
"To kasani bashi aikin da zakayi yana daidai darasa kujerarka da matsayinka gbdy. .." a,a ranka ya dade ba zayi hkn ba InshaAllahu yadda kake so hk zaa yi,"idan kabi umarnina ka tsira da aikinka kit safwan ya kashe wayar .
shi kuma alhj Abubakar yashiga goge gumin dake keto masa, bayan yagama goge gumi ne ya fuskanci kabir "yauwa kabir batun aikin abokinka a gsky babu shi a halin yanzu ,Dan bazai samu aiki akarkashinmu ba sakamakon wasu dalilai da ba sai na bayyana maka su ba .
"Kmr yaya dady?"da fari kace zasu samu ,yanzu km ka..fu'ad ya dafa kafad'arshi yana mai mikewa tsaye "karka damu abokina da rashin samunka aikina ka d'auka komai mukaddari ne bani da rabon samun aiki anan ne... yana karasa fad'ar hk ya juya.
"Amma fu'ad...."nace karka damu kayi facing din na abdulrashid
alhj Abubakar da zuciyarsa ke cike da matsanancin tausayin fu'ad yacigaba da mgn sai zance aikin kaninka shi yasamu aiki, maiduguri zashi ,zuwa wata mai zuwa ,wannan aikin mutane dayawa na nema Amman acikin sa'a yasamu kad'an jira takardar tabbatar da samun aikin domin zata iya zuwa a kowani lokacin .
fu'ad yataso daga inda yake zaune yana tunanin dayasa zancen samun aikinsa ke neman shan ruwa, ya kwankwasa glass din office inda kabir ya d'ago yana dubansa cike da tausayawa, alama yayi masa da zaije kasa ya jirasa, shi ma da kai ya amsa da badamuwa .
Fu'ad ya sauka kasan maikatan ya isa inda yayi parking din maching dinsa yana waige waige a gurin hannunwasa duka zube cikin aljihun wandosa ,karaf idanunsa ya sauka Akanta tana tuki cikin karewa, itama tun daga nesa ta hangosa tayi saurin ware idanunta bakinta na furta" fu'ad Dina ...... sai dai tun kafin takaraso inda yake taga ya haye maching dinsa tare kunnawa yayi gaba aiko itama tabishi abaya..........
0 comments:
Post a Comment