ahankali Me'ad ta zagayo inda take zaune tana kallonta "bby let's go now tana me kamo tafin hannunta ta fito daita daga cikin motar, sa'an nan ta meida murfin motar ta rufe, tasoma tafiya rike da hannun ta.
yayinda ma'aikatan gidan suka shiga gaisheta cike da girmamawa, hannunta kawai ta iya d'aga musu tacigaba da tafiyarta batare da juyowa ba,
Momy tana zaune a parlour'n tana waya Me'ad tasanyo kai cikin parlour'n a matukar birkice bakinta d'auke da sallama, momy na ganinta tayi saurin katse kiran saboda yanayin data ganta ,wujiga wujiga tamkar wace tayi shekara tana jinya.
"me'ad lafiya kuwa naganki haka kmr wacce ta tashi a jinya?
"ko kuma kunyi Abind kuka saba ne da mijinki kika kwaso jiki zuwa gida?
momy tajirowa me'ad wannan tambyar Tana dubanta a matukar tsorace me'ad tasamu guri ta zauna a gefen kujerar da momy ke zaune batare da tace mata komai ba, illa wani tashin hankali data tsinci kanta ciki.
NASREEN ta isa gurin momy tashige jikinta tana gaisheta ,momy ta rungumeta ajikinta tsam kana tace "ykk nasreen?
"yana ji jikin naki da zafi ko bakida lfy ne?
Naunayen ajiyar zuciya me'ad ta sauke kana tace "fitowarmu kenan daga hospital yau kwananmu uku NASREEN babu lafiya Tak'arasa mgnr muryarta na rawa kmr zatayi kuka.
momy tayi Shiru tana kare mata kallo had'e da nazarin yarinyarta, a kallon da take mata ta fuskaci tana cikin matsananci damuwa da tashin hankali, yayinda ita kuma me'ad din tashiga share hawaye wasu na gangaro mata...
"To meye kuma abun kuka ?
" ko ciwon ne yayi tsanani?
Me'ad ta girgiza mata kanta wasu sabbin hawaye na sake gangarowa bisa kuncinta.
" meke damunki me'ad dan banji dadin ganin yanayinki ba ? " sannan meye damuwarki ahalin yanzu da kike zubda hawaye ko duk akan matsalar ciwon NASREEN ne?
ta sake girgiza kai kawai tana share hawaye, momy ta fuskanceta sosai hankalinta a matukar tashe "ke me'ad ki bud'e idanunki ,ki saka cikin nawa ni mahaifiyarki ce da duk duniya baki da kmr ni kuma nice nazama dole nasan damuwarki da abinda ya kawoki gida adaidai wannan lokacin daya kamata ace kina gurin aiki ne ko gidan aurenki "ki sanar dani damuwarki da abinda ke damunki domin Nasan mataki d'auka..
me'ad ta kalli momy fuskarta cike da tsantsar damuwa da tashin hankali still hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta tace "momy ina cikin babbar matsala ,ina cikin damuwa da tashin hankali, momy na cuci kaina da kaina na yaudari kaina,na zalinci kaina, na jawo kaina maseefar datafi karfina.... Momy nayi aure batare da farincikinku ba ,most especial dady, banyi muku biyayya akan aurena da fu'ad ba , gashi ayau an wayo gari komai na neman ta'bar'bare min, narasa gane komai nawa ,rayuwa na neman juya min baya ,
"ahalin yanzu na dawo gida ne saboda bana jin zan iya cigaba da rayuwar aure da fu'ad .......
jin wannan maganar yasa jikin momy yayi sanyi ta gyara zamanta tana duban me'ad cike da matsanancin tashin hankali, sannan tace "amman meye dalilinki na fad'ar duk wad'an nan maganganun hk ?
"abinda akayi shi tsawon shekarun goma sha meye na dawo shi ahalin yanzu?
"sannan meye dalilinki na cewar bazaki sake rayuwar aure da fu'ad ba wani mummunar abun yayi miki ? Momy ta tambayeta jikinta na wani irin rawa haka zalika gabanta na fad'uwa ..
me'ad ta kalli momy ganin damuwa kwance akan fuskarta ,yasa wani irin tausayin mahaifiyarta ya saukar mata, ta sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ta kwashe duk abinda ya faru ta gayawa momy.
momy tayi wata irin zabura daga zaunen datake rungume da nasreen ta mike tsaye kana ta zaunar da nasreen jikinta na d'aukar kyarma , dan maganar ta bugi zuciyarta matukar , ahankali tasoma kai kawo acikin parlour'n, lokaci guda kuma ta koma ta zauna ta kalli me'ad tace" yanzu ina najma take sannan a wani hali Sajid take ciki?
"momy nagaya miki na barsu agidan ,dan tunda abun nan ya faru ban sake taka kafata cikin gidan ba ,kinga sai suji dadin yin aurensu da tushe .
"shikena me'ad to yanzu meye abun yi?
me'ad tayi murmushi me tattare da takaici abinda sajida tayi mata ,sannan tace "momy kada ki damu ni nasan yadda zanyi da Sajida ,wallahi Momy sai tayi datasani tunanin auren fu'ad arayu....
"datasani uwar me zatayi tunda ke bakiyi dakinsani ba a aurensa da kikayi ? Wannan Sautin muryar ta katse mata hanzari ,ko ba'a gaya mata ba tasan sautin muryar mahaifinta ne yashigo parlour'n ,atare suka jiyo daga ita har momy suna mamaki jin Furucinsa.
Ahankali ya tako har zuwa inda suke yana tafi da hannunwansa Duka cike da tsansar jin dadin ganinta cikin damuwa da tashin hankali"ku daina mamakin jin abinda na fad'a "arayuwa kowa abinda yake so yake da burin mallaka, "kmr yadda kikayi tsayin daka kikace duk duniya babu wanda yayi miki sai d'an talaka dagin matsiyata, itama hkn ce zata kasance daita Dan hk banga abun tada jijiyoyin wuya ba .....
"Me'ad.... !!! dady Ya kira sunanta har sau uku in a serious thought wanda yasa kirjinta bugawa da sauri batare da tasan da hakan ba, "na'am dady ta amsa masa wasu hawayen na ciccikowa a idanunta sannan tasanya kwayar idanunta cikin nasa zuciyarta na sake lugud'en bugu da karfi saboda fargaban jin abinda zai sake fad'a.
" yanzu dai me kika zo yi gidana ?
"hope ba kashe aurenki kikayi ba akan mijinki zai aure aminyarki da yar aikinki?
"idan kashe aurenki kikayi ko yaji maza maza ki tashi ki bar min gidana, dan babu masaukinki acikinsa.
" idan kina tunanin zaki kashe aurenki ne ki dawo gidana ki zauna kiyi saurin canza tunani ,dan idan kin kashe aurenki har abada bazaki zauna tare dani ba. "idan kin manta sharrud'ana akanki bari in tuna miki .
" yaji ,mutuwar aure alkahari kowani iri ne damuwar rayuwa ,yasameki bazaki tunkaro hanyar gidana ba," kikace kinji kin gani kin yarda kin amince , kika zabi auren d'an matsayata akan mu iyayenki da mukayi silar zuwanki duniya.
"daman kuma wannan ranar nake zaman jira zuwanta wanda nasan komai daren dadewa zata zo gashi tazo kuma na godewa Allah datazo ina raye cikin koshin ..
" dan haka tun wuri ina shawartarki ki tashi ki koma gidanki, idan ba sakinki yayi ba, idan kuma ya sakeki ne sai kin nemi gurin zama amman ba'a gidana ba.
"haba dady wace irin mgn ce haka ? "da me kake son taji?
"Ina ruwana da abinda zataji, nace ina ruwana lokacin danake rokonta ta auri safwan me tayi min?"in ce komai ya faru ne akan idanunki ?
"kamata yayi ka duba lamarin da rabon dake tsakaninsu , idan basu auri junansu ba ,ta yaya kake tunanin za'a samun rabon NASREEN ?
"NASREEN din banza ina ruwana da wata nasreen?
"kuma wallahi bari kiji ingaya miki ni nan me d'aurawa mijinki aure ne da sajida matsawa tana son shi da gaske shima kuma yana sonta , ke koni sajida tace tana so zan aurenta balle wani mijinki din banza da wofi ,oya zo ki bar min gidana kije ki rungumi matsalarki ,ki bar rayuwarmu, dan tuni na manta da na haifeki arayuwata ,a halin yanzu diya daya gareni itace suhailat yar albarka yarinyar kirki kuma InshaAllahu zatayi albarka saboda tana min abinda nake .....
cikin kidima da tashin hankali me'ad ta durkushewa agaban mahaifinta tana wani irin kuka "dan girman allah dady kayi hakuri ka yafemin , na yarda nayi kuskure arayuwata,Amman na tuba dady karka min haka ,karka juya min baya, banida wad'anda suka fiku ,ka yafemin nasan hakinka ne ke bibiyata ya fixge karfarsa daga rikon datayi masa.
"baki ga komai ba tukun me'ad sai ranar da kikaji na d'aura auren sajida da mijinki ,kijira abinda zai biyo baya sai fu'ad ya zame miki annoba arayuwarki sai ya tarwatsa rayuwarki da farincikinki ,ke hatta wannan aikin da ni nasan wahalar dana sha kafin ki sameshi da har kike tinkaho da dashi, wallahil azim matsawr ina da haki akanki shima sai yabar hannunki kmr yadda Fu'ad ke shirin barin hannunki ......
"ki tashi ki bar min gidana ya k'arasa mgnr cike da hargagin 'bacin rai ...
Kuka me'ad take sosai tana Jan gwiwowinta tana bashi hakuri ,momy ma ta durkusa agabansa tashiga bashi hkr. "kayi hakuri Dan girman Allah kabarta ta zauna tare damu ,yanzu ina kake tunani zata ga yarinyar mara lfy atare daita ?
"khadaji ....dady yakira sunanta a zafafe "na'am dady. Ta amsa masa jikinta na rawa.
"a iya tsawon arayuwamu, mun ta'ba samun wata matsala dake ?
momy tayi saurin girgiza kanta tana jujuya hannuwanta alamun dai yayi hakuri .
"to karki bari musamu matsala akan wannan yar isakar yarinyar mara jin magana .
"gidan nan ma tukun naki ne ko nawa ?
Momy tayi saurin girgiza masa kai tare da cewar "naka ne.
"to nagodewa Allah daya kasance nawa ne ba naki ba, kuma lokacin dana tashi gidansa baki sanya sisin kwabonki ciki ba ,Dan haka bana bukatar ganin me'ad cikinsa taje can gurin wad'anda take tunani sun fini daraja agurinta, sannan ya fuskanci me'ad sosai yana huci "minti biyu kacal nabaki ,ki d'auki yarinyarki kibar min gidana bana bukatarku cikinsa, hakuri tashiga bashi amman sam yace bai san da zance wani hakuri ba sai ta bar masa gidansa .
Ta mike ta tashi tsaye jikinta na rawa ta janyo hannun NASREEN ta rike cikin nata gam kmr wace za'a kwacewa ita, tasoma tafiya tana kuka ,momy na kuka , hatta NASREEN kuka take sosai tana tausayawa momy'nta "yanzu saboda ta auri dady'nta yasa babanta yayi mata wannan wulakanci, daman grandpa dinta bayason auren iyayenta ?
Hakuri take son bashi Amman tashin hankali datake hangowa tattare da momy'nta da ita kanta yasanya ta kasa magana sai kukan datake har da shesheka.
Jikin momy na 'bari tabiyo bayan me'ad tana kuka tana kiran sunanta....shi kuwa dady ko ajikinsa, Sam bai ji wani abuba dangane da halin da ta tsinci kanta ba.
me'ad ta tsaya tare da cewa " momy ki daina kuka ki koma kawai duk abinda ya faru dani ,ni na jawowa kaina na zabi d'a namiji akan mahaifina ,na fifita soyayyar fu'ad akan ta mahaifina, yau wa gari ya waya?
""yanzu ina zaki?
"duk inda Allah yayi momy zan tafi na bar rayuwar kowa, zanje nayi sabuwar rayuwa tare da diyata, zan rungumi kaddarata....
"amman ki rokon min dady yayi hakuri ya yafe min abinda nayi masa wallahi nayi danasani arayuwata, ki min addua momy ko zan daina jin rad'ad'in da zuciyata ke min ... ta juya tacigaba da tafiya har ta isa jikin motarta tashiga ta tayar , ta fito daga cikin gidansu tana wani irin kuka.
Gudu kawai take shararawa akan titi, duk hanyar data gani ,bi take saboda bata San inda zata ba ,banda bugawa bubu abinda zuciyarta keyi, kuka take sosai tana dukan sitiyari motar "me yasa nayiwa mahaifina abinda nayi masa akan soyayyar fu'ad ta furta a fili?
" me yasa ban bi zabinsa ba nace lallai sai fu'ad zan aura gashi komai na neman birkice min ?
Ta sake fashewa da wani sabon kukan ,hakika na cuci kaina, iyaye duk lallacewarsu sun wuce wulakanci ,ballanatana irin nawa iyayen da samun irinsu ke da wuya, dady uba ne har da rabi ,wanda ke maye gurbin uwa idan tana raye ko amace .
"sun haifi ne sun min gata ,mahaifina ya inganta rayuwata sosai yabani abinda duk wani d'an Adam zaiyi tinkaho dashi arayuwar duniya ,bai rageni da komai ba a tun tasowata ,komai nace shi za'ayi .
",me yasa nayi masa abinda nayi masa?
" me yasa banyi masa biyayya ba alokacin dayace na auri safwan? " why why why !!! Me'ad meyasa nayi abinda nayi ?
"Wayyohlly Allah na cutar da kaina, Kuka take sosai Sam ta manta da nasreen dake zaune agefenta sai da taji yarinyar ta riko hannunta a matukar afirgice tare da sakin razananniyar k'ara sannan taja birki da karfi ta tsaya cak tana Jan ajiye zuciya, hawaye sha'be sha'be kwance Akan fuskarta, itama nasreen din kukan take sosai har lokacin da shesheka ,tana jin tausayin dady'ntan sosai fiyye da mahaifiyarta , Amman ayau tausayin momy'nta ne ya rinjayi nashi har batasan a mizanin dazata ajiye hkn ba, rungumeta me'ad tayi ajikinta tana kuka "am sorry bby gudun danake ya tsorotaki ko.. ?
Nasreen ta d'aga mata kanta al'amun Eh tana kuka.
"am sorry na daina bazan sake ba kinji bbynah, ta d'aura idanunta akan agogon fatan dake d'aure da tsinyayar hannunta , lokacin shan maganin nasreen din yayi ,Dan HK ta kai hannuta sit din baya ta d'auko ledar maganinta da ruwa ta balla ta bata ta sha sannan ta mai daita ta kwanta akan kujera, itama ta meida bayanta akan kujerar datake zaune akai, byn tayi baya kad'an daita, ta runtse idanunta still hawayen idanunta suki tsayuwa har lokacin nadama ce fal cike da zuciyarta.
Kusan minti talatin tana gurin tana zance zuci wayarta ta d'auki k'ara sauti me dadi da ta'ba zuciyar Wanda ya saurara,ko bata duba wayar ba, tasan ko waye me kiranta, sakamakon sautin dataji "fu'ad dinta ne ,dan shi kad'ai tasanya wannan sautin saboda matsayinsa gareta ," mutumin data sadaukar da rayuwarta da komai nata akansa, mutumin da shine silar 'batawarta da mahaifinta,a yau tayi datasanin a had'uwarta dashi a wancen lokacin" duk duniya tasani kowa yasani babu halittar da mahaifinta ke so sama daita Amman an wayi gari sanadin had'uwarta da fu'ad komai ya canza, soyayyarta ta juye zuwa kiyayyar da batasan ranar gushewarta ba..
Wani kukan ne ya kufce mata tasanya duk hannuwanta ta toshe bakinta ,"tarasa fu'ad rashi na har abada, sannan tarasa soyayyar mahaifinta, ga aikinta datake ganin shine gatanta da rufin asirinta shima tana nema rasashi adalilin takasa samun natsuwar zuciyar gabatarwa.
akalla bazata tuna karshen shigarta office dinta da sunan yin aiki ba, gashi tun rashin lfyr nasreen bata taka kafafunta zuwa cikin ma'aikatar ba, ko kiran chairman bata samu damar yi ba ,batasan me zai biyo bayan faruwar hkn ba ,tun yanzu tacire rai da tsammanin da aikinta bisa kaidodinsu ,na ko fashin rana daya mutun yayi zai fuskanci babbar matsala da chairman.
"zuwa yanzu tasan komai ya rigada ya tsaya mata ,shikenan rayuwarta zata zamo abar tausayi mara amfanin ..
Fu'ad yakira wayarta sau babu adadi ,Amman batayi yunkurin d'auka ba sai hawayen datake zubarwa .
jiki a sanyaye nasreen takamo hannunta"momy !!! dady na kira ,should I pick the call?
"No......tace mata atakaice tana me runtse idanunta"why momy ki d'auka mana.......," koni na d'auka plz...?
"Pick....ta fad'a saboda batason k'arin damuwa akan wacce take ciki .
Nasreen ta d'auki wayar tare da cewa "hello dady nah.
" hello my bby How are u doing ?
"Am fine dady .
"Ina momy'nki take ?
"gata a kusa dani tana kuka,Jimmmmm yayi da ransa sannan yace "okay bata wayar.....
nasreen ta miko mata wayar "momy dady yace nabaki..
Me'ad taki kallon inda take ballanatana ta amsa wayar hannunta ,"momy plz now ki amsa wayar dady'na.
Sam me'ad taki, " ta amsa tace masa me byn cutar da yayi mata ?
"Me zatacewa mayaudarin irinsa?
"Mayaudari maci amanar kauna ......"Har abada wata kalma bazata sake shiga tsananinsu ba, kowa yaje yayi rayuwarsa ....
yana jin yadda nasreen ke mata nacin ta amsa wayar Amman taki , tswon minti biyar wayar na tafiya sannan nasreen ta meida wayar zuwa kunnenta tana sauke numfashi "dady........
"taki amsa ko ya fad'i hkn Dan yasan abinda zata ce masa kenan ?
"Don't worry bby, yanzu kuna ina, na dawo hospital doctor yace yayi discharging naki ,na dawo gida bangan bbynah ba,gashi nayi missing dinki ,I want to see ur beautiful face, tayi murmushin jin dadi sannan tace "ai daga hospital gidan grandpa muka wuce nan tashiga koro masa duk abinda ya faru akan idanunta ,fu'ad ya samu guri ya zauna yana mai runtse idanunsa yana jin wani irin zallar 'bacin rai da tunda yazo duniya bai ta'ba jin irinsa ba, wani irin tafarfasa zuciyarsa ke masa "why me'ad ? Ya furta a raunane.
"Me yasa zata masa hk.? Ahankali ya hau sauke numfashi cike da takaicin dabbancin abinda me'ad tayi masa, ya d'auka iya shekarun da sukayi tare shi daita sun zama abu daya, sannan sun wuce wannan nevel din ,tazama shi shima yazama ita, sun chakud'e guri daya ta yadda duk runtsi duk wuya babu wanda zai ji kansu balle mahaifinta, daya fito ya nunawa duniya bayason zamansu tare, Sautin muryar nasreen dayaji cikin dodon kunnenshi ne yasa yayi saurin bud'e idanunsa "dady da gaske ne zaka auri aunty sajida da najma me aiki Dan kayiwa momy'na kishiya dasu?
Yayi shiru kawai ya kasa bata amsar tambayarta, sai ma d'aura hannunsa da yayi ya dafe goshinsa dashi yana shashshafawa ahankali ahankali ,while kirjinsa na bugawa da sauri sauri.
"daddy matukar da gaske zaka auresu ne ,plz change your mind, dan banason kayiwa mamana kishiya saboda banaso ganita cikin damuwa, saboda nima zan shiga cikin damuwa yanzu haka kirjina ciwo yake min dady tak'arasa mgnr kmr zatayi masa kuka .....
Muryarsa a matukar kasalance yace "bby kina bukatar kulawa wanda momynki ta kasa tsayawa ta baki, ni kuma amatsayin na mahaifi ba hurimina bane ,wannan hanyar kad'ai ce zatayi min maganin matsalata saboda nasan idan na auresu zasu kula dake shine dalilin....
" Amman ki za'bawa dady'ki mutun daya acikin auntynki sajida ko najma wanda kike son na aura ta zauna tare dake amatsayin second momy dinki, wace zata cigaba da kulawa dake da dady'nki..
"ni banason dukkansu ,ni banason kowa ni nafi son mummy'na kawai ..........
ya sake runtse idanunsa gam" yanzu kuna ina?
" zanzo na sameku na dawo daku gida, ta d'aga kanta tana duban yanayin gurin ta cikin mota, idanunta ya sauka akan wani green sambod da aka rubuta *main land bridge* Dan hk ta sanar masa a matukar firgice ya bud'e idanunsa ,gabadaya ya gigice ya kid'eme muryarsa na rawa yace "main land bridge?
"Yes dady shine abinda nagani ,yace "ki sa wayar a handafree.
Aiko take nasreen tayi abinda dadynta ya umarceta cikin d'aga murya yace"me'ad kina hauka ne, dazaki kai min yarinya har main land bridge?
"Wai meyasa kike son meida kanki wawiya ne akan yar kankanuwar matsala?
Tayi masa banza taki cewa dashi komai ,shi km ya dinga zuba mata bakaken maganganun ta inda yake fita bata nan yake fita ba still tana jinsa taki cewa komai, Dan idan tace zatayi mgn zagi ne zai fito daga cikin bakinta da hk tacigaba da sauraransa kawai take tana jin zallar 'bacin rai na ratsata, hawaye na bin kuncinta ji take a duniya yagama tozartata, ya gama wulakanta da abinda yake son mata,ganin taki kulasa yasa ya sausauta muryarsa,
"Kiyi kokarin dawo min da yarinyata so that ke ki cigaba da zama agurin tunda abinda kika za'barwa kanki kenan .
yana gama fad'ar hk ya katse kiran,Wanda alokacin ita kuma tayiwa motarta key dan tasan Sarai zai iya zuwa ya samesu agurin tunda yaji inda suke.
me gadin gidansu takira taji ko fu'ad din na gida , ya tabbatar mata da yanzu ya fita, hasashenta ya tabbata kenan, zuwa zai yi ya amshi nasreen din ya barta da tarin bakinciki da damuwa, kai tsaye gidansu ta nufa, bata tsaya bata lokaci ba tashiga ta dibi abubuwanta datasan masu amfani ne gareta, dana yarinyarta ta kulle kofarta ta fito tashiga mota tabar gidan.
Yayinda fu'ad Yayi maya tafi sau hud'u akan main land bridge, ya hau ya sauko Amman bai ga alamun tsayuwar motarta ba ko alamun wata motar daban ba ,gashi yana kiran wayarta taki d'auka haka ya hakura ya koma gida yana jin zallar bacin rai yana shiga gidan jikinsa yabashi tazo gidan . Da sauri ya fito ya isa gurin me gadi yana kwalla masa kira ,me gadi ya k'araso ya tsaya agabansa "maman nasreen tazo ne byn fitata?
"Eh yalla'bai tazo bata ma dade sa fita ba wani irin takaici yaji kmr ya d'aukeshi da mari, a fusace ya juya ya komai cikin gida yana huci gabadaya ya rasa meke masa dadi ,hankalinsa ya sake tashi so yake yasoma neman inda najma take Amman bashi da natsuwar zuciya a kalla ya kusan minti goma tsaye yana tunanin mafuta ya duba agogo karfe karfe biyar ta kusan ciki" ina bai ga ta zama dole duk yadda zaayi sai yaga me'ad da nasreen tare da dawo dasu gida sake bazama yayi ya fito harbar gidan kallo daya zaka masa kasan baya cikin natsuwarsa yashiga motarsa aguje ya bar gidan.
*********
A bangaren mahaifiyar me'ad kuwa kuka take a tun fitar me'ad gidan ,taso kiran fu'ad Amman ta kasa saboda a yadda zuciyarta ke cike da 'bacin rai zata iya gaggaya masa komai yazo bakinta ,abinda bazata so faruwarsa ba kenan atsakaninta da surinkinta ,me mutuntata da ganin kimarta, ita batace kar ya kare aure ba ,"amman meyasa sai sajida da najma?
Tasan zai auresu ne Dan kawai ya kuntatawa zuciyar mead dinta...
gidan yayi shiru kmr anyi mutuwa Dan koda suhailat ta dawo daga makaranta taji labarin abinda ya faru mutuwar tsaye tayi agurin, itama hankalinta yayi mugu mugun tashi..
ta dinga mamakin cin amana irin na sajida a ganinta har gara auren najma akanta.....
Bangaren me'ad kuwa yawo ta dingayi acikin gari, daga wannan titi zuwa wancan titi,tarasa inda zata taji sanyi aranta ,tayi tunanin zuwa dangin momy'nta Amman sai taga kmr zata tonawa kanta asiri ne, a yanzu ta d'auki darasi me girma a zamanta da sajida, bazata sake yarda da kowa ba arayuwarta ,zata koyi rike sirrikanta ,zata bawar cikinta damuwarta bazata sake sharing secret dinta da kowa ba bayan mahaifiyarta, itama Dan tasan bazata gayawa duniya bane ko ha'intarta sai dai ta d'aurata bisa turba .daga karshe zuciyarta ta bata shawarar takama hotel kawai ta cigaba da rayuwarta har zuwa sanda mahaifinta zai sauko ya amsheta ,bazatayi fushi dashi ba ,haka zalika bazata gaji da rokonsa ya yafe mata ba, har sanda zai furta ya yafe mata.
Dan hk Kai tsaye wani had'ad'en hotel ta nufa me suna city hotel, cikin Dan kankanin lokaci ta isa kawataccen hotel din Wanda hotel ne ,na isasu ta d'aki ,daya daga cikin mai'aikatan hotel din yayi gaba rike da key'n d'akin ita kuma tabiyosa abayan rike da hannun nasreen ,byn ya bud'e mata d'akin ta mika masa key'n motarta domin shigo mata da kayanta, ya amsa juya cikin sauri, suka shiga ta meida murfin kofar ta rufe .
Komai na agyare neat a acikin Had'add'en d'aki .
Ko cikakken minti biyar baayi ba maaikacin yashigo da akwati kayansu ya ajiye ya sake fita, ita kuma takarasa tayiwa kofar key tare da barin makuli ajikin kofar ta dawo ta tsaya atsakitar d'akin tana k'arewa falle d'akin daya kallo wanda ya k'awatu sosai , doguwar kujera kwaya daya ajiye , da TV bango sai air condition ,babban wardrobe na zuba kayan sawa daga gefe, mirrow da bedside, daga can bangaren toilet ne me murfin glass .
d'aki ne mai matukar kyau da fad'i ,ta d'auki lokaci tsaye tana k'arewa d'akin kallo sannan ta K'arasa ta kunna ac tare da rage karfinsa saboda nasreen ,
Jikinta a matukar sanyaye ta janyo hannun nasreen jikinta ta rungume yarinyar naji dumin jikinta muryarta a sanyaye tace "muje bbynah kiyi wanka nasan kin gaji dayawa ko?
Murmushi nasreen ta sakar mata sannan ta sake shigewa jikinta, "momy meyasa kika kawomu nan ?
"Mu koma gida nasan dady zai shiga damuwar rashinmu, plz momy mu koma ...
"Shiiiiiii kiyi shiru da zance komawar nan har abada nasreen bazan komawa mahaifinki ba ,idan kuma kinfi sonshi da son zama tare dashi akaina fine I can take you to him right now. "Ki kwantar hankalinki zamuyi rayuwa kmr muna gida kinji bby, zan siya miki duk abinda kike ,zamu dinga kallon TV tare muna enjoy ki manta da wani dady okay"taja hannunta suka shiga bayin tayi mata wanka da ruwan zafi ,tana tsaye akanta tayi alwala suka sake fitowa tare daita daure da towel.
tsab mead ta gyarata ta sauya mata wasu kayan masu kauri, ta Mike mata hijabi, "kiyi sallah kafin na fito, sannan ta juya ta sake komawa cikin bayi.
Mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
FAIZA HAMMADU BARAU
(YAR NUMAN)
Page 78
........tsaye tayi acikin bathtub din ,ruwa na tsiyaya akanta zuwa sansar jikinta,Wanda ke saukar mata da natsuwa kad'an saboda har wannan lokacin bakinciki abinda sajida da fu'ad ke shirin yi mata, yaki barin zuciyarta da gangar jikinta, "ta yaya zata iya sharing din fu'ad dinta da wata macen ,macen ma aminiyarta da suka taso tare... ?
"Suke yin komai nasu tare sannan babu abinda bata sani ba na sirrukan rayuwarta....
"A gurinta Fu'ad ba kmr sauran maza bane ,daban yake acikin mazan datake kallo , sannan natsatse ne kamili Wanda yasan ciwon kansa ,tana son shi fiyye da rayuwarta sai dai bata jin zata iya ganinsa yana rayuwa tare da wasu matan byn ita,tafin son duk runtsi duk wuya su kasance tare suka k'arasa rayuwarsu .
Ahankali take tuna moment dinsu dashi ,duk da ba wani bashi had'in kai takeyi ba ,amman hkn baya hanata jin dadin abinda yake mata. "Anya kuwa zata iya rabuwa dashi kmr yadda ta fad'a tayi rayuwarta ita kad'ai sai yarinyarta?
"Anya kuwa ba wata cutar Kan zata sake yiwa rayuwarta ba ?
Tayiwa kanta tambayar tana jin jikinta yana sauyawa, ahankali take jin feelings dinsa na bijiro mata duk da bata tsamaci zata ji hkn ba akansa, a wannan tsayuwar datake komai na rayuwarsu ke dawo mata daki daki cikin kwakwaluwarta ,yanzu ace agida ne kuma suna zaune lafiya dashi zai shigo bayin ,ya tsura mata kyawawan idanunsa masu maseefar burgeta da tsaya mata arai ,yana kare mata kallo ko kifta idanunsa baya son yi daga karshe kuma ya k'araso gareta ya riko kugunta yana me had'eta da jikinsa tare da shafa kirjinta yana goga mata gashin dake zagaye da fuskarsa zata lafe akirjinsa , koda kuwa bai yi niyyar yin wanka ba ko kwanciyar aure daita ba ,ganinta tsaye babu kaya zai janyoshi yayi koda kuwa acikin bayi ne yayinda ita kuma zata shiga tutturesa tana kukan shagwaba ita tagaji bazata iya da jarabarsa Amman ba zai ta'ba kyaleta ba har sai yacima burinsa akanta duk yadda tayi ta yakice tunaninsa abun yaci tura haka tayi ta tunaninsa ..
ganin tunaninsa daya d'arsu a zuciyarta yaki barin tayi abinda yashigo daita ,yasa ta sauke naunayen ajiye zuciya sannan tasoma sa'bawa jikinta sabulu ,sai dai duk inda ta gogo sabulu ajikinta sai taji kmr tafin hannunsa ne ke yawo ajikinta Dan haka tayi
Shap shap tayi wanka ta d'auro alwala ta fito ,koina a d'akin ya kama kamshi room freshener da'akayi amfani dashi .
jakar kayanta ta bud'e ta ciro doguwar riga ta sanyawa jikinta ta k'arasa inda pray mate yake ta tada sallah byn ta idar da sallah s ta janyo akwatin kayansu ta fiddosu daya bayan daya tasoma jerawa cikin wardrobe nasreen na tayata miko mata, wasu suna hirarsu cikin farinciki duk da ita ba wai nufinta tayi hkn ba ,Amman ya zame mata dole ko dan kwanciyar hankalin diyarta da lafiyarta ,batayi sha'awar kunna makeken TV dake makale da bangon d'akin ba ,Amman saboda ta d'bewa nasreen kewa yasa ta tashi taje ta kuna ta dawo tacigaba da aikin jera kayan.
byn tagama jira kayansu ta tmbyi nasreen ko zata ci abinci Dan ita bata jin cin komai ,yarinyar tace " ba yanzu ba sai zuwa anjima momy , Dan kafin me'ad ta yanke shawarar zuwansu hotel ta sai mata snacks taci a mota .
Kwanciya tayi akan gadon tabar nasreen na kallo ,ahankali ta runtse idanunta domin ta samu hutu da natsuwar zuciya, Kafin lokacin sallar magri tayi ,tunanin mijinta ne ya sake sanyo kai cikin zuciyarta dama gangar jikinta, wani irin sabon yanayi ta tsinci gangar jikinta ciki yayinda wani feelings dinsa yashiga bijiro mata idanunta har sun sauya, da kyar tasamu ta yakice shi ta Mike ta janyo system dinta data jona a caji ta kunna tasoma dudduba sakonin da aka turo mata ,cikin haka kiran chairman din company din datake aiki yashigo wayarta, take gabanta yashiga dukan uku uku ,da kmr karta d'auka Dan bata son K'arin tashin hankali akan Wanda take ciki ,ammam ta sanshi tasan halinsa shima ba kwanwar lasa bane ,Akan company dinsa babu abinda bazai iya yi ba ,Dan HK tayi saurin sanyawa jikinta kuzari ta d'auka ta manna wayar a kunnaneta tana gaisheshi a natse ya amsa tare da cewa "muna bukatar ganinki gobe by 10 :am atakaice tare da katse kiran ,jikinta yayi sanyi kmr wace akayiwa wanka da ruwan sanyi ,gbdy takasa cigaba da operating system din dake gabanta, ta ture system din gefe ta janyo nasreen ta rungume ajikinta hawaye na gangarowa daga cikin kwarnin idanunta ,"jikinta na bata aikinta ya kusan zuwa karshe.....har aka kira sallah magariba tana makale da nasreen tana jin karfin gwiwa a duk sanda ta rungumeta yayinda take cikin damuwa,ahankali ta zameta daga jikinta ta kwantar a saman cinyarta ta tsura mata ido kawai tana kallonta wani irin kaunar yarinyar nabin jikinta bacci take har lokacin tana sauke numfashi ahankali, ta Mike ta tashi taje tayi alwala bayan ta idar da sallah bata tashi ba tacigaba da zama tana lazami tarenda kaiwa Allah kukanta.
*********
Misalin karfe tara na dare mumy ta samu dady ad'akinsa cikin yanayi na rarrashi take ce masa "dady sam abinda kayi bai kamata ba ,yakamata kabi komai ahankali hannunka baya ru'bewa kace zaka yanke ka yar duk abinda me'ad tayi maka duk lalacewarta bazaka ta'ba canzata amatsayin diyarka ba ,kalaman daka furta mata a yau din nan yayi muni dayawa.....
dady yasoma magana cikin 'bacin rai "ina amfaninta arayuwata?
"Meye amfanin D'an da bai jin maganar iyayensa da yi musu biyayya?
"Ni tsine mata ma naso yi tabi uwa duniya kowa ya huta ,dady yana fad'ar hk numfashinsa ya fara sama sama sai faman haki yake ,mummy tana ganin hk ta fara salati game da waige waigen Kafin kace me tuni dady ya fara fita haiyacinsa ,mummy tayi matukar rud'ewa sakamakon numfashinsa daya tsaya a matukar gigice ta kwallawa suhailat kira itama tashigo d'akin a rud'e tayo gurin momy dake jijigasa , tare da taimakon sulahait suka dawo da dady parlour'n, ruwa sanyi mummy ta dinga shafa masa sannan ya dawo haiyacinsa ya jike sharkaf da ruwa kwance ya ganshi ajikin momy wacce idanuwanta tuni sun dade da yin luhu luhu saboda kuka, dady ya d'ago idanunsa ya kalli momy da take faman tofa masa adduoi, da kyar dady ya iya bud'e bakinsa "wai ,abinda nake tunanin ne ya faru..?
Mummy tace " a'a babu abinda ya faru ina dai tunanin BP dinka ne ya tashi bara nai ma doctor waya yazo ya duba ka.
Jikin momy na rawa ta tashi daga gun datake zaune tana rungume da dady tmkr wani karamin yaro ,bedroom dinta ta nufa ta d'auko wayarta dake ajiye akan gado ta fara lalubo lambar cikin kankanin lokacin takira doctor ya d'auka ,ta fad'a masa duk halin da'ake cikin doctor yace "gashin nan zuwa .
Doctor Peter ya faka motarsa ya fito da sauri ya nufi hanyar da zata sadashi da parlour'n dady ,Amman a wannan lokacin momy tai masa jagora zuwa bedroom din ,doctor ya fito da kayan aiki yasoma dubashi ,byn ya gama ya kalli mummy yace " "madam ya'akayi hkn ta faru jininsa ya hau dayawa sosai ?
"yakamata ku kiyayye 'bacin ransa domin ya samu cikakkiyar lafiya mai dorewa mumy tace "doctor yanayin rayuwa ne kawai Amman za a kiyaye InshaAllahu. Doctor
Ya bar magunguna da dady zai yi amfani dasu ,allurar bacci akayi masa domin ya samu ishashen bacci sannan yakama gabansa .
Ta bangaren fu'ad shima yana cikin tashin hankali mara misaltuwa, duk inda yasan zai ganta yaje har dama inda bayi tunani ba, hankalinsa yayi maseefar tashi yarasa inda zai sa ransa yaji dadi shi kam a yadda yake ji acikin ransa bazai iya hakura da neman me'ad ba ,kodan tilon diyarsa mara lafiya har hawaye ya zubar aranar ya samu guri gefen titi yayi parking din motarsa ya d'aura kansa a saman sitiyari yana kukan tausayin halin da nasreen dinsa Zata shiga a sanadin wannan tashin hankali, yasan me'ad bawani kulawa zata bata yana jin tsoron ya rasata, ya dade agurin sannan ya tada motarsa yayi hanyar gida ,koda isa gidan kasa zama yayi sai faman zariya yake acikin parlour'n sakamakon sautin bugun zuciyarsa daya addabi kunnensa "wayyohlly Allah nah ya furta yana me rike kugunsa da hannu daya .....
Daren ranar kuwa kwana me'ad tayi nafila Sam takasa runtsawa , saboda tashin hankali datake ciki yafi karfin tunaninta , tunanin mahaifinta yafi komai addabar zuciyarta, tayi shiru agurin tana lazimi tana jin kmr takirasa ta sake bashi hakuri ,daga inda take zaune ta mika hannunta ta d'auki wayarta tasoma neman layinsa ,takira wayarsa yafi sau biyar ba'a d'auka ba kawai ta rushe da kuka tana cigaba da addu'a, sai kusan ukun dare bacci 'barowa yayi awon gaba daita.
Washegari da wuri ta tashi ta shirya nasreen cikin uniform din school itama ta shirya kanta ,ta tasota gaba, tana gaba tana binta abaya har reception,ta bada makulin d'akin domin killaceshi sannan suka fice .
kai tsaye wani had'ad'en restaurant suka nufa tayi musu order abinci, ta turawa nasreen abinci agabanta tare da yin tagumi ta tsura mata ido "ki ci abinci ..... "Momy ke meyasa bazaki ci ba ?Tayi mgnr muryarta na rawa kmr zatayi kuka "kici kawai nasreen bazan iya ci ba .......
take idanun nasreen ya cicciko da kwalla "why momy.....ta fad'a hawaye na gangaro mata"tun jiya banga abinda kikaci ba ,idan bazaki ci ba nima bazanci ba takarasa mgnr hawaye na biyo kuncinta sharrrrrr ..
me'ad tayi saurin kai hannuta saman fuskar nasreen tana goge mata hawaye ", no my bby dont cry I will eat tasoma k'ok'arin dibar abinci ta kai bakinta "gashi ina ci kema ki ci kinji bbynah banason damuwarki ina matukar sonki duk da dadynki nagani kmr banasonki ,adalilin ban ajiye aikina ba Wanda hkn bashi zai nuna bana sonki ba ,nice nayi silar zuwanki duniya idan wuya ake ci naci idan dadi ne naci" ta yaya mutun zai d'auki ciki har na tsawon wata tara yayi na kuda ya haifi d'ansa ace masa bai sonshi .....
"ki daina d'aukar maganganun mahaifinki, abaya nasan nayi sakaci , rashin kulawa dake Wanda bashi yake nufin bana sonki ba ....ina sonki nasreen fiyye da kaina sannan a shirye nake Dana sadaukar da rayuwata akanki, akan mahaifinki nayi komai har sanda na mallakeshi matsayin miji gareni ,ina kuma ga ke dani kad'ai nasan azaba da wuyar Dana sha tun daga haihuwarki har zuwa yanzu.
Ta k'arasa mgnr tana bata abinci abaki suna ci tana kwantar mata da hankali har suka gama tayi dropping dinta a school takama hanyar zuwa office,Akan hanyarta ta zuwa aiki duk inda taga Almajiri sai ta tsaya tabashi sadaka maganin maseefa ..
Ahankali ta Sanyo hancin motarta cikin ma'aikanta tsirarrun mutanen da suka yi sammakon zuwa suka bita da kallo , inda take jikinta ya bata akwai abu dake tafiya a kasa, wata irin damuwa me tattare da tashin hankali ne sukayi mata diran makiya ,amman hk bai hanata sanyawa zuciyar Kwarin gwiwar ba ,ta nufi gurin data saba ajiye motarta tayi parking tana fargaban fitowa ,kusan minti talatin tana zaune works nata faman shigowa ciki har dasu mudansir da ma'aruf suka fito atare suna kyalkyake dry da alamun suna cikin nishadi suka shiga cikin ma'aikatan batare da sun lura daita ba.
tana zaune tahir shima yashigo ya wuceta.
ahankali ta fito da system dinta tasoma operating domin k'arasa tura sakonin da'akayita turo mata daga daren jiya zuwa safiyar yau din nan ,bata fito ba har sai da taga shigowar chairman sannan ta fito adaidai karshen dogon korido ta had'u da mudansir yayi saurin k'arasowa inda take ya amshi jakar hannunta da system, ita kuma tacigaba da tafiya ta nufi hanyar office dinta da niyyar shiga ta gani ko zata daina jin zafin dayake mata.
Mudansir yabiyo bayanta da Dan hanzarinsa "madam yau fa akwai meeting da chairman "nasani ta bashi amsa atakaice tana kusa kanta cikin office dayake tun shigowar mudansir ya bud'e, wanda ya zamemasa kaida .
ai da wani irin sauri me'ad ta fito daga cikin office dinta kmr zata hantsila tana furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun lahaula wala kuwata illa billa....
Shi kuwa mudansir kad'an yarage bai kyalkyale mata da dryr mugunta ba saboda yadda yaga tafito aguje kmr mota ....
numfashi take fitarwa ahankali tana jin zafi ajikinta, tayi saurin barin jikin kofar Dan tiririn dake ta'ba fatar jikinta, ta nufi conference room, koda ta isa ta iske chairman zaune tare da mataimakinsa Wanda yakasance ba indiye ne ,shine na biyu a company sai ita, duk sauran wad'an da ke zaune agurin akarkashin ikonta suke, ahankali ta samu guri ta zauna a natse zuciyarta na bugawa ,wannan shine karo na farko da za'a yi taro ta tsinci kanta cikin matsanancin fad'uwar gaba ,duk taron da za'a yi cike take da natsuwar zuciya da kwarin gwiwar tare da isa da mallaka da nuna ita din wata ce acikin ma'aikatar ,sai gashi yau babu wannan zarra da isa da mallaka sai tsagwaron tsoro dankare da zuciyarta.
Shiru ne yabiyo bayan zamanta , kafin daga bisani chairman yayi gyaran murya yasoma magana cikin kwararren turancinsa wanda bazaka ta'ba cewar ya had'a jinsi da hausa fulani ba"acikin yan kwanakin nan abubuwa dayawa sun faru Wanda yasa dole mu tautauna akai, Abu na farko da campay tasoma fuskanta shine karancin income din da company bai samu ,ta hanyar sakacin manager. Me'ad ta d'ago idanunta da sauri ta d'aura akansa tana kallonsa , chairman ya fuskanceta da kyau kana yacigaba da mgn "sakacin rashin tsayuwarki akan aikinki da rashin bawa aikin mahimmanci yana kokarin janyo mana babbar hasara, a halin yanzu dakatarwa ce tafi dacewa dake ,Amman saboda wannan shine karo na farko da muka ta'ba samunki da wasa da aiki, yasa zamu yi sausaci akai ,Dan hk daga wannan lokacin bama bukatar sakaci ko rashin bawa aikinki mahimmanci, Dan idan muka sake samun rashin ingancin tsayuwarki aiki zamu sallameki......
tunda chairman ya fara magana ta nemi miyo ko daya tarasa abakinta, zuciyarta ke wani irin bugawa da sauri sauri ,duk karfin ac dake aiki acikin conference room din ,hkn bai hana gumi tsatsafo Mata ba..
take furucin mahaifinta yashiga dawowa mata "aikin da kike takama dashi Wanda ni kad'ai nasan irin wahalar Dana sha akansa kafin ki sameshi shima zai bar hannunki ......
"inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kawai take furtawa a zaunen dake agurin gumi na sake tsatsafo mata , iya abinda ta iya fahimta kenan daga bakin chairman duk sauran maganganun da yacigaba dayi babu abinda ta fahimta hatta Wanda sauran ma'aikatan suka taunana bata fahimci komai ba ,sakamakon zuciyarta data tsaya ta daina aiki na wani lokaci ...
Lokacin da zuciyarta tacigaba da aiki ta dawo cikin hanlinta ta nemi kowa tarasa acikin conference room din sai ita kad'ai zaune ,ashe tuni taron ya watse .
runtse idanunta tayi sosai, wasu zafafan hawaye suka shiga kokuwar zubo mata "me ke shirin faruwa da rayuwata ?
"gidana babu dadi ,bani da jituwa da mahaifina , aikina na neman subuci min ,tabbas wata maseefa na kusanto rayuwata "ya Allah ka kawo min sauki cikin lamarina ,ya Allah karka barni haka, na tuba Allah kasanyaya zuciyar mahaifina akaina ya yafe min abinda nayi masa ,domin nasan bakinsa ne ke bibiyar rayuwata,
ta Dade zaune agurin tana kuka ,ganin kuka da tunani bazai bar kanta ba yasa da kyar tasamu ta mike tsaye tare da gyara zaman mayafinta zuciyarta bata shawarar ta nemi mutane suje su bawa mahaifinta hakuri ya yafe mata, mahaifin sajida shine mutun na farko da zuciyarta ta hasasho mata Amman ina bazata taka kafafunta zuwa gidansa ba, 'yarsa tayi mata katangar karfe Dan wannan gidan har abada bazata sake sanya kafafunta cikinsa ba ,ta kofar baya ta biyo Dan batason jama'a su ganta ,Dan zasu fahimci halin da take ciki ..
kmr jira ake duk inda ka yi acikin ma'aikatar maganar me'ad ake da irin matakin da chairman yace zai d'auka akanta, su mudansir kuwa ansamu abinda ake so ,sai murna suke har da rawa kmr wad'anda akayiwa albishiri da gidan aljannah " kai mutumina wallahi ina cikin farinciki mara misaltuwa ka koma gurin malamin nan naka ya sake k'ara wutar aiki, ayi ayi akoreta wallahi ban so uzirin da chairman yayi mata ba ,naso yayi mata me gabadaya ne injin cewar ma'aruf..
wata uwar dariya mudansir ya kwashe dashi "sha kuruminka abokina komai daki daki yafi ka zuba ido kasha kallo muna nan za'a yi mata me gabadaya..
Tahir ya saukar da ajiyar zuciya daman kuma tun da suka soma mgn bai tsoma bakinsa ba sai yanzu yace "gsky na fara jin tausayinta me zai hana abarta hk idan ka lura tayi sanyi ba kmr lukutan baya ba .
"Kunji shirme banza ,kai ta tafi can kabawa mutane guri ,da alamun ka soma sauya ra'ayinka na bukatar matsayinta daka furta tun farko?
"Ko ban sauya ra'ayina ba nima da wasa na fad'a mgnr , ina ni ina matsayinta, ku kanku kunsa wasa nake yi bazan ta'ba samun matsayinta ba sai wani ikon Allah.
Maaruf yace "mudansir rabu da da wannan shirmammen banza da alamun cutar hauka tasoma kama.....
ai bai kai ga karasa mgnr ba tahir ya cakumi wuyan rigarsa da iyakacin karfinsa "ni ne cutar hauka ta kama,?
"ni zaka cewa hk saboda kai Mara imani ne da tausayi " ina zamu da hakinta ?
"Meye ribarmu idan munyi sanadin rabata da aikinta da har zaka dangantani da kalmar hauka?
Mudansir yayi saurin shiga tsakaninsu "haba tahir meye hk ne ?
wasa yake maka fa bai kamata ka d'auki zafi ba ma'aruf ya fizgo mgn da kyar yace "rabu dashi ance masa me cutar hauka yayi duk uwar da zai yi ,mahaukaci dolo sauna dakiki..tahir ya kai masa mari sai ga jini ya balle abakinsa abu kmr wasa suka dinga zagin kansu da son yin dambe, da kyar mudansir yasamu ya rabusu tahir yana huci yace "ni... ni ...na cire hanuna acikin shirinku daman kuma ba dani akaje gidan malam ba ,daga yau babu hannuna cikin shirinku duk abinda zaije yazo karku sani ciki azzalume Kawai ya fita yana banko musu kofar da karfi .
suka tsaya sororo suka bi kofar da kallo kirjinsu na mahaukacin bugu"kaji abinda wannan D'an iskan ya fad'a ko ? Ma'aruf ya fad'a yana naushin iska "rabu dashi shima zan gama dashi wata killa kafin ita tabar aikin shi zai rigata barin aikin.
Kai tsaye tahir harabar ma'aikanta ya nufa inda ya iske me'ad tsayen tana zariya abar tausayi, kunnenta manne da waya "wallahi ta bani tausayi ya fad'a acikin zuciyarsa yana jin kmr yaje ya sameta ya sanar daita abinda aka yi mata,Amman yana jin tsoro saboda yasan halinta, yasan yadda take da saurin d'aukar zafi, karshen abun ya juye ya dawo kanshi ,shi kad'ai .
kad'a kansa yayi kawai ya kama gabansa ya koma bakin aikinsa .
************
Zaune Alhaji ediris takai yake agaban amininsa kuma abokin shawararsa mahaifin sajida suna fuskantar juna kafin daga baya yasoma mgn a natse cikin sanyayyiyar murya "me yasa zaka hanata auren abinda take so, ?
"A ganina daga me'ad har sajida abu daya ne agurimu ta wani fannin ma har gara sajida tunda duk rashin son da batawa emran ta hakura ta auresa daga baya Allah ya kawo rabuwa atsakaninsu, Dan haka banga dalilinka na hana auren fu...ya datse harshensa yakasa karasawa saboda baya tunanin zai iya karasa sunan wannnan D'an matsiyatan, shi kansa bazai so sajida ta auresa ba saboda irin tsanar da yayi masa Amman domin kuntatawa me'ad zaiyi tsayin daka ruwa da tsaki akan yaga yaron ya aureta shi da yasan inda zai ga najma har ita sai yabata makudan kudi ta auresa , kawai dan yaga me'ad cikin bakiciki kmr yadda tayi silar jefa safwan da shi kansa da har yanzu wannan bakinciki yaki barinsa.
"abinda bazai ta'ba yiwuwa bane wannan AI cin amanar kauna da yarda ne Sam sajida baza ta'ba auran mijin me'ad ba har abada ...iniji Cewar mahaifin sajida .
Dady yace "ta ina aurensu yazama cin amana ?
"Gsky ni banga wani cin amana ba acikinsa ba.
Mahaifin sajida yace "Ko babu cin amana ai ana barin halak Dan kunya, "banda wannan halak din mahaifin me'ad ya fad'a yana furzar da iska .
muhawura ce tashiga tsakaninsu kowa na kawo hujjarsa Akan auren daga karshe dcp aliyu ya Mike ransa a matukar 'bace ya bar parlour'n saboda idan yacigaba da zama agurin zasu raba gari ,da shi da amininsa da Allah kad'ai yasan tsakaninsu .
Mahaifin me'ad bai bar gidan ba har sai daya gana da sajida inda yake ce mata "ta gayawa wakilan fu'ad su zo su sameshi idan sun tashi ,ita kanta sai alokacin tasan tayi kuskuren son mijin aminiyarta , Amman yazatayi da tata zuciyar datayi kudin balan kamuwa da matsanancin soyayyarsa?
Bayan kwana biyu sajida tasamu me gidan fu'ad da maganar zance aurenta da fu'ad, Amman ta boye masa gurin Wanda zashi neman aurenta,"yace karta damu InshaAllahu zaije ....fu'ad Wanda ya kasa samun natsuwar zuciya gabadaya ya tattara zance wani auren najma da sajida dayake son yi gefe saboda bulayin neman me'ad da sanyin idaniyansa ya taho guest house din me gidansa inda yafi tunanin zai samesa ya nemi izinin agurin aikinsa domin samun gano inda iyalinsa Suke,yashigo cikin parlour'n dayake zaune yasamu guri ya zauna yana sauke naunayen ajiyar zuciya tare da dafe goshinsa sannan ya gaishe dashi .
Ya amsa yana ajiye magazine din dake rike a hannunsa,yana dubansa "yanzu nake shirin nemanka nan ya karo masa abinda sajida ta bugo ta gaya masa. wata mummunar tashin hankali ya tsinci kansa ciki take gefen kansa ya Sara ya d'ago agigice yana dubansa batare dayace masa komai ba me gidansa yacigaba da mgn yanzu sai ka sanar min da inda gidansu ita dayar yarinyar take sai ayi abun gabadaya a huta ,sosai fu'ad ke kallonsa da idanunsa da suka gama canza kalla har lokacin sunan mutumin dayaji yafito daga cikin bakinsa yake masa yawo acikin kwakwaluwarsa "to me hakan yake nufi da mahaifin me'ad yabada goyon bayan wannan aure?
Zuciyarsa tabashi amsa da ya yana nufin abubuwa dayawa .
a matukar zuciye ya runtse idanunsa yana tsuma bai tsaya gayawa me gidansa matsayin mutumin dazaije gurinsa neman aure ba ....
Mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
JIDDATULKHAIRI
MARUBUCIYAR
MATAR DATTIJO
Page 79
......Jikinsa ne yacigaba tsuma , kansa gaba ɗaya ya kulle, yayi mamakin jin abinda mai gidansa ya fad'a mishi, hankakinsa gaba daya yagama tashi ,xuciyar sa ta shiga rud'ani, "wai me surukin nashi yake nufi da shi, ?
"wane irin zato surukin nasa yake masa, ?
"me yasa ya gwammace kar'bar auren sajeeda alhalin lokacin da zai aure me'ad kin amincewa yayi ? Tambayoyin da ya rika yiwa xuciyarsa kenan .
"Yasan zai yi hkn ne Dan kawai ya bak'antawa me'ad rai .. ..
A fusace ya mike zai bar parlour'n, cikin natsuwa mai gidansa ya kira shi "fu'ad ina zaka je haka,? Tsayawa yayi yana haki batare dayace masa komai ba .
" me yasa naga yanayinka gaba daya ya canja? Dawo ka zauna"
A hankali cikin nutsuwa fu'ad ya dawo ya zauna yana fuskantar mai gidansa. "Gaya min menene damuwar ka fu'ad, naga daga yin wannan Maganar gaba daya ka canja daga farin ciki zuwa akasinsa, hankalinka ya tashi damuwa ta bayyana a idanunka, fad'a min idan akwai wata matsala ne musan yadda zamu shawo kanta "
Sunkuyar da kai fu'ad yayi sannan ya fara yin magana cike da ladabi da girmama ga mai gidan sa
"Yalla'bai shi fa wannan mutumin da zai kar'bi auren sajeeda ba kowa bane face mahaifin me'ad"
Wani irin shock mai gidan nasa yayi lokacin da yaji wannan maganar, "mahaifin me'ad fa ?" Ya maimaita yana kallon fu'ad cike da neman K'arin bayani
"Kwarai kuwa yalla'bai mahaifin me'ad ne ,"Abinda yake ƙara d'aure min kai shi ne ta yadda zai yi ya amshi auren sajeeda alhalin a da can baya lokacin da xan auri me'ad 'ke'kashe ƙasa yayi yace baxan aureta ba, to yanzu kuma wane dalili ne zai sa ya amince na auri sajeeda tabbas nasan akwai wata manufa a cikin zuciyar shi".
Shiru mai gidansa yayi yana nazarin Wad'annan maganganun da fu'ad ya fad'a masa, bayan sun kammala maganar da zasu yi ne suka yi sallama fu'ad ya tashi ya bar me gidansa zaune yana mamakin abinda ke shirin faruwa.
Yana fitowa harabar gidan Motar shi ya bud'e ya shiga sai yaji kamar baxai iya yin driving din ba saboda wannan Maganar da aka yi masa ,tambayar kansa ya shiga yi me Mahaifin me'ad yake nufi da wannan batun da da'akazo masa da shi da rana tsaka, ?
tunani ya rika yi gami da nazari, ba ƙaramin caji ƙwaƙwalwarsa ta rika yi ba a haka har ya isa gida wanka yayi ya sake fita neman me'ad sai bai samu ganinta bai yi tunanin zuwa gurin aikinta ba ,saboda yasan halinta ,kad'an daga cikin halinta su siyar da hali agurin shi kuma abinda bazai so faruwarsa kenan ba .
A ɓangaren me'ad kuma, har yanzu tana fama da matsalar da ita kanta bata san asalinta ba, ba kuma ta san dalilin da yasa ta tsinci kanta a wannan halin ba,sannan har wannan lokacin bata daina tunanin hakunci da chairman din office din su ya fara tunanin yanke mata ba ,ta hanyar dakatar da ita amma sbd kwarewar ta ga iya aikin da jajircewa wajen tsayawa tayi aikin yadda ya kamata yasa ya d'aga mata kafa gabadaya ta fige ta rame tafita haiyacinta ban da kuka babu abinda take ..
Hankalinta kullun sake tashi yake ganin yadda kullum matsalarta gaba take yi bata baya ,hkn yasa ta sake dagewa da addu'a da sadaka da kiyamullaili a kan Allah ya kawo mata karshen wannan matsalar da take ciki, duk da wannan jajircewar da take wajen addu'a da sadaka still dai har yanzu bata iya xama a office dinta domin gudanar da aikinta kamar yadda yakamata ,yayinda tsakanin su mudansir da tahir amintarsu ta dawo sama sama ko nace ta kusan Yankewa, saboda kusan kowa yanzu harkar gabansa yake sai dai a kasan zuciyar mudansir yana jin cewar bazai iya barin tahir hk ba sai ya bisa da bita da kulle.
sajida zaune a d'akinta tana tunanin yadda aurensu zai kasance da fu'ad , ita tana jin idan duk duniya zasu had'u akanta matsawar fu'ad ya amince da aureta zata aureshi ko da kuwa mutuwa me'ad zatayi ,ita Sam bataji kunyar ko tsoro acikin dady'n me'ad zai kar'bi aurenta ,a ganinta ma meye aciki Dan ta auri fu'ad?
"Tana son shi bugu da kari kuma ita me'ad tayi wasa da damarta ta hanyar rashin kulawa da gidanta, yanxu hk tana da labarin duk abinda ya faru daga korar da mahaifinta yayi mata har zuwa neman da fu'ad ya haukace agari yana yi akanta, gashi ita tasan hotel din da me'ad take gaya masa ne kawai ba zatayi ba ,tana nan tana jiran yagaji da nemanta ya hakura ya dawo haiyacinsa suyi aurensu a wuce gurin Dan ta najma me sauki ne ita me tasan yadda zatayi daita a karshe matukar ya aureta bazai ta'ba tunanin wani aurenta ba hatta me'ad din karon kanta zatasa ya manta daita arayuwarsa ,tana cikin wannan tunanin kiran khalid yashigo wayarta,taja dogon tsaki tare da furta another problem sannan ta d'auki wayar "meye ne zaka dameni bafa nason takura
"Ki fito ina jiranki a harabar gidanku ya fad'a atakaice tare da katse kiran .
khalid matashin saurayi ne D'an kimanin shekaru a shirin da shida zuwa da bakwai ,abokin aikinta ne dake bibiyarta da sunan friendship har ta kai daya fito fili ya bayyana mata sirrin dake ransa , Amman fur taki amince masa asalima sai yanke halaka tayi dashi saboda bataga wani abin so ajikinsa ba ,kuma tun daga ranar bata sake barin sun had'u da junansu ba balle ya karanto shirme ,shi kuma babu abinda yake kwadayi da son gani kmrta .duk da bata sanar masa ba yasan komai akan yadda take mugu mugun son fu'ad .
Ta fito sanye cikin wando da rigar body hook Wanda ya matse jikinta sosai ,A tsaye ta sameshi jikin motarsa dake kusa da nata motar ,ya hard'e hannuwansa duka akirji, tun sanda ta fito ya tsurawa surar jikinta idanunsa,yana kallonta daga sama har kasa yake kare mata kallo tsab irin macen da yake burin so da mallaka kenan arayuwarsa ,ji yake duk duniya babu mace me kyawunta sannan yana ji tmkr ya isa gareta ya rungumeta akirjinsa , yanayin yadda yake kallonta kwata kwata baiyi mata ba ,Dan har ya sata jin wani iri ajikinta saboda gabadaya ya tsurawa nonuwanta idanunta kmr zai cinyesu , kallo daya tayi masa ta d'auke idanunta akansa ta haye saman motarta ta zauna tana kallon wayar hannuta batare da tace masa komai ba
Khalid kyakkyawa ne shima sai dai bai kai fu'ad a komai ba , gyara tsayuwarsa yayi tare da matsowa gabanta still rungume yake hannunwansa a kirjinsa ahankali yasoma mgn cikin sanyayyiyar muryarsa "plz sajida kinsa na dad'e ina binki ta hanyoyi daban daban , ina sonki kuma tsakanina da Allah ,ki manta kowa ki bani damar na shigo cikin rayuwarki dan Allah....
Ta busar da iskar bakinta idanunta har lokacin yana kan wayarta, kanta tashiga girgizawa sannan d'ago ahankali tana dubansa a yatsine kana tace " Khalid Kake ko wa ?
"Wai me kake tunani Akaina ne?
"meyasa ba zaka fahimceni ba sannan ka fahimci ina na dosa ,?" Try to understand me Khalid ....."bana son ka bana kaunar wata halaka da kai kuma halakar da mukayi abaya ta mutunci Allah yasanya mata albarka Amman dan Allah ka fita cikin rayuwata , saboda kai ba irin namijin danake so bane ,you not can of man I like"
" am not can of man ?ya tambayeta yana tsareta da manya idanunsa "yes of course ta bashi amsa tare da shayi ko wata fargaba ba sannan ta maida idanunta kan wayarta tacigaba da abinda take.
muryarsa cike da rauni da in ina yace "meye bambamci tsakanina da kalar namijin da kike so?
"khalid.....bana tunanin yau ne zan fara gaya maka wannan mgnr ,I have my type, ina da type din namijin da nake so , wanda zuciyata take so da muradi ba kai ba ,kuma zan tabbatar da na bawa xuciyata abinda take so tak'arasa mgnr tana hura masa iskar bakinta me zafi sannan ta tsaresa da idanunta "just forget about any love you have for me coz I can't love you kaje gaba da rayuwarka watakila zakayi cath up wata tasoka but not me ....
"but ai ni ke zuciyata ta za'ba kuma take muradin rayuwa daita ina sonki saji...."enough khalid don't ever say that rubbish again..bazan ta'ba sonka ba koda kuwa zaka mutu ka dawo sajida nada ra'ayin mijin datake so okay ,"ina son namiji kamili natsatse wanda yasan darajar da ciwon kansa, dogo baki me faffad'an kirji me sex eyes me haiba da Kammala, ma'aboci kyau wanda a duk sanda na kallesa zanji Feelings dinsa na ratsani ...
" idan na kallesa zan ji dadi acikin zuciyata sannan zai sani na jini a new level ba kai ba me zaka min ?
"me zanji a tattare da..... ...?
"common short up there my friend karki tozartani akan wannan sifoffin da kika lisafa ... ni meye na rasa ajikina ?
" meye banda shi acikin abubuwan da kika lisafa?
ta kai hannunta ta gyara gashin kanta daya zubo gefen fuskarta sannan tace "karka fad'i abinda kasan ba haka bane, da kace duk abubuwan dana lisafa kana dashi khalid ta ina ?
"Ina suke ?
"ina abinda na lisafa?
"Sam ni banga komai ba danake so na namiji ajikinka , da kana da abinda na lisafa da yanzu mun wuce gurin ,abu na karshe da zan gaya Maka ka bar rayuwata ..
Muryasa a matukar sanyaye yace plz sajida wallahi ina .."
"Ka daina ronkona plz Dan ba zaka ta'ba samun abinda kake so ba kalleka fa D'an Allah wani gaja gaja da kai .
kai yanzu bakiji kunyar cewa Kana sona ba a girme na girmeka nesa ba kusa ba Khalid me zan ji aurenka ...? zai yi mgn ta katseshi ta hanyar cewa "stop beging me khalid kaje kaso wata plz..
ya sauke naunauyen ajiyar zuciya tare da zura hannunwansa duka cikin aljihun wandonsa yana fitar da wani hucin Numfashi me gyaraye da tsagwaron 'bacin rai"ammm.. amm naji baki sona sai mijin aminiyarki kike so, saboda shi ne wanda ke da dukkanin tsifofin da kika lisafa ,tell me i want know?
Ta d'ago fuskarta a d'aure tana dubansa shima kallon cikin idanunta yake cike da isgilanci rainasa din datayi "khalid am not long interested on you just live my life plz ...
ya juyar da fuskarsa kad'an yayinda dryrta ta subuce masa yayi murmushin mugunta sannan ya juyo ya fuskanceta "dole ki waskewa mgnta saboda kinsa nasan komai , auren cin amana kike kokarin yi amman bari nagaya miki wani good news, ki hakura ki aureni saboda nasan duk abinda kike bukata daga cikakken nmj wallahi zan miki ,Zan iya cika wannan bombom din naki tsab da zan mararki Dan hk ki daina rainani yaro ne ni a zahirance Amman baki San badini na ba ..kuma ki rubuta ki ajiye a inda bazai goge ba ni ne zan aureki as ending .......
A matukar tsawace tace "plz just go tana nurfafashi tmkr me cutar asma " i don't want see you near me ta fad'i hk cikin murya mai rawa ala'mun tana son yi masa rashin mutunci "
"sajida ...yakira sunanta muryarsa a kasalance "khalid can you live plz ? "dole ne nace bana yi bana sonka bana kaunarka bazan iya soyayya da kai ba ka bar rayuwata mana "naji amman yakamata ki duba girman son danake miki ki bari muyi ...."no no we are not talk to anything just go ...get out ..live ..bye... ta fad'a a matukar harzuke tana me dafe gefen kanta data ji yasoma Sara mata "plz i beg you sajida tayi saurin d'aga masa hannu out bey tana nuna masa kofar get da hannunta.
jimmmmmm yayi yana kallonta sannan ya meida hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa yasoma d'aga kafafunsa kmr kazar da kwai ya fashewa aciki tsaki taja ta gyara zamanta tayi consentret akan wayarta datake aikin turawa fu'ad text message tana jin lokacin da me gadi ya bud'e masa get ta juya a matukar fusace "you stupid man if you ever open get to that stupid boy you wil see what wil happen to you," a'a kunji min jaraba da maseefa irinta primature... karami yaro dashi sai jarabar naci ko ya zaiyi dani oho?
"nace banayi banayi !! ana so do.... shiru tayi ta kasa karasa mgnrta taja tsaki kawai ....
cikin sauri fu'ad ya fito daga cikin d'akinsa yana waya sanye da farar singlet da wando sai dai ya d'aura rigar t shirt a saman singlet din bai sanya botira ba "okay ina jinka tana wajen har yanzu ?
Can bangaren kabeer yace "tana wajen Amman kayi sauri da alamun ta kusan gama abinda tazo yi .."dan Allah ka tsayar min daita . Kabir yace "kaima kasan halin wannan rikitacciyar matar taka ba tsayawa zatayi ba ,yanzu ma data ganin bazata tsaya ba .", okay ganin nan zuwa suna tare da nasreen ne ?
"A'a injin cewar kabir cikin sauri fu'ad ya isa ya bud'e motarsa yashiga ya kunna tare da danna hon.....da karfi me gadi ya bud'e masa ya fita aguje.
sai dai yana zuwa yashiga bud'e idanun yaga ta inda zai ganta ,kai tsaye inda kabir ya gaya masa ya nufa da sauri Amman bai ganta ba Dan hk yak'araso gurin kabeer yana riko hannunsa "ina take kabeer ...?
Cire hannunsa kabir yayi cikin nasa yace "wallahil yanzu nan ta wuce naso na bita sai dai banzo da mota ba ,goshinsa ya dafe yashiga zagaye gurin tare da ya furta Allah yana me runtse idanunsa "why me'ad me yasa kike son ruguza mana rayuwarmu alhalin kinsa muna bukatar juna ..?
Da sauri ya sake dawowa inda kabir yake tsaye yana dubansa cike da matsanancin tausayawa "wani hanya tabi kabir ...?
Kabir ya nuna masa hanyar da tabi ..yabi hanyar da kallo yana tunanin yabita ne ko ya fita harkarta ya hutawa rayuwarsa, shi daman ba saboda ita bane yake wannan wahalar...
Jiki a sanyaye ya k'arasa jikin motarsa yana kokarin bud'ewa kiran sajida yashigo wayarsa ya ciro wayar daga aljihun gaban rigarsa yana duba screen din wayar,number da ya gani ne yasashi Jan tsaki , kmr bazai d'auka ba sai kuma ya d'auka "uhmmm meye kuma?
"I lost a lot of things arayuwata amman banaso kaima na rasaka fu'ad hope sir malik ya isa maka da sakona?
"Wani banzar sako kenan "sajeeda ya kirata ransa a matukar 'bace"karki k'ara min matsala da damuwa akan wanda nake ciki ,wai ma Sajid me kike nufi dani ne ?
"Babu komai sai alkairi kuma InshaAllahu zai tabbata ,tun da har ka furta tare da amincewa aurena wannan kawai ya isheni nacigaba da rayuwa har zuwa sanda zamu mallaki juna sannan kuma karshen matsalata tazo ,ka daina zurfafa tunaninka ,ka daina damuwa I promise zan baka dukkanin kulawar dakake bukata ,zan baka kulawar daka rasa saboda irin son Da nake ma ...
"common that was not on fear, sajida bakya sona ki duba kiga yadda nake cikin tashin hankali akan matsalar gidana nasan kinsa komai amman ke k'ok'ari kike kawai a d'aura mana
aure.
"Tabbas aurenmu shine agabana kuma shine abinda nake buri a halin yanzu sannan zanyi Iya kokarina naga na mallakeka , yanzu dai kana ina ,Dan ina son mu had'u da kai akwai maganar da zamuyi very important"
"bani da lokacinki a halin yanzu neman inda matata da yarinyata nake "ta kwashe da wata uwar dry sannan tace "ka sani ko nasan inda matarka take da yarinyarka just try and come...jikinsa yayi sanyi yasoma ya rage murya "Dan Allah ko kinsa inda take ne ki gaya min ...?
"Uhmm a'a ban sani ba ,Amman ka dai kazo akwai Wanda yasani "rubbish ya furta a harzuke ganin raina masa wayo take son yi akwai siyar data sake shirya masa ,shi kuma ya ranse ba zai sake barin su had' u ba either ko tazama matarsa ko km sun rabu ..."ba zaka zo ba kenan ?"yes of course banzo wawiya kawai maciya amana ke auren ma na fasa inga uban da zai sani aurenki ...ta saki wata razannaniyar k' ara tare da durowa daga saman gadonta tana furta "what?
"Abinda kunnenki yaji shi na fad'a na fasa aurenki kibar rayuwata simple as that "
Muryarta na rawa tace" Dan girman Allah Allah fu'ad kar ka fasa au..sai kuma kiyi ya katse kiransa tare da shigewa motarsa ya bar gurin aguje..
**********
Yau takama Monday Wanda ko bature na tsoron ranar da girmamata rana ce da duk wani ma'aikaci ke jin tsorota da taka tsantsar daita ,me'ad tana zaune acikin motarta kmr koda yaushe tana tunanin yadda xata bullowa wannan matsalar da ta addabe ta , taji an kwankwasa glas din motarta da sauri ta d'ago kanta, tare da bud'e murfin mota ,daya daga cikin staff din company ne ya bayyana agabanta bayan sun gaisa yake fad'a mata cewa chairman yana son ganinta a office din sa.
A sanyaye ta fito daga cikin motar tare yiwa motar key , da sallama ta shiga office din tare da neman kujerar da ke ajiye a gefe ta xauna gabanta na wani irin fad'uwa , bayan sun kammala gaisawa da chairman ya shiga jefa mata wasu tambayoyi.
"Har yanzu na kasa ganin wani canji daga gare ki me'ad ,dan Allah ki fad'a min abinda yake damunki bana so ki boye min komai, Ni dai nasan da ba haka kike ba sam ban sanki da sakaci ko wasa da aiki ba, me yasa Yanzu abubuwa suke neman tabar'barewa Company? Ina jiran amsa daga gare ki kuma bana so ki boye min gaskiyar abinda ke faruwa da ke.
Kuka mai tsanani me'ad ta shiga yi, sai da tayi kukan da ya ishe ta sannan ta zayyana mishi dukkan halin da take ciki.
Ya tausaya mata sosai kuma yayi alƙawarin insha Allah matsalar da take ciki da mahaifinta yazo ƙarshe godiya tayi masa, yacigaba da mgn yana duba file din su ma'aruf "kinsa cewa wannan rashin zamamki cikin office dinki , sammu akayi miki ?
mead ta d'ago kanta a matukar firgice tana dubansa cike da mamaki da matsanancin tsoro, "kina mamaki ko ,?tayi saurin d'aga masa kai alamun Eh "karkiyi mamaki mead akan samu irin haka .
bakinta na rawa tace " ni kuwa wa nayi laifi da har zai min samu akan aikina ?
Chairman yace "kina son sani ko su waye ?
Jikinta na rawa tashiga girgiza masa alamun eh"
"okay ina zuwa "ya d'auki wayarsa ya kira messenger cikin minti biyu yashigo jeka ka cewa acp ya shigo min da yaran nan kafi ya wuce dasu "okay sir ya fita da sauri ..
Ahankali taji an bud'e kofar gabadaya ta kasa juya saboda jikinta daya d'auki rawa har sai da charman yace "ki juya mana kiga yan iskan da suka miki aika aika da kokarin rabaki da hanyar abincinki "
jikinta na cigaba da kyarma ta soma juyawa ahankali har ta juyo gbdy idanunta ya sauka akan tahir da mudansir da ma'aruf dukanindu hannunwansu da handcuff, take gabanta yayi wani irin dukan uku uku yashiga fad'uwa tashiga nunasu da hannunta bakinta na rawa "ku..ku ne kuka min sai kuma ta rushe da kuka "laifin me na muku da kuka shirya min wannan munakisar?
"A halin yanzu ba sai kayiwa mutun komai ba zai nufeka da sharri inji cewar chairman "wasu mutane suna nan su kawai basa son ganin cigabanka ,sun fi so kullun suganka kana bara akan titi 'acp a wuce dasu sannan ayi musu azaba me rad'ad'i har sai sun gaya muku malamin dayayi musu wannan aiki, if possible ma a asakasu a under ground har sai sun fad'a Dan babu yadda banyi dasu ba, alokacin Dana kamasu suna tad'in Dana takurasu ne ma sukace tare da tahir akayi komai "
Acp yace"Karka damu kana zaune zamu zo maka da good news. "Okay nagode sosai tare da mikawa acp hannu sannan suka juya suka bar office din .
Wani irin kuka me'ad take kmr ranta zai fita chairman nacigaba da bata hakuri"ba kuka yakamata kiyi ba illa ki godewa Allah da asiri ya tono if not ,hk kina ji kina gani aikinki zai bar hannunki "nagode nagode har bansa kalar godiyar da zan maka ba ,a yau na k'ara sani duniya ba'akin komai take ba, nasan watakilla sunyi min hk ne saboda yadda nake takura musu akan aikinsu ,kuma fa ni ina yi musu hkn bada wata manufa ba sai Dan su tsaya akan aikinsu kar ya subuce musu Amman babu komai nagodewa Allah daya nuna min su a tafin hannuna ......
Tun daga wannan lokaci chairman ya nemi manyan mutane wad'an da yasan suna muamula da mahaifin me'ad Sannan ya nemi mahaifin sajeeda domin shine kan gaba a komai agurin mahaifinta,domin a zauna da shi a bashi hakuri a roke shi gafara a kan laifin da me'ad tayi masa.
sunje kmr yadda Chairman ya bukata sai dai da kyar alhj ediris ya yarda me'ad tashigo masa gida .
Bayan sun gama gaisawa suka soma magana akan abinda ya kawosu"alhaji jabir yace "alhj ediris abinda ya kawo mu akan batun yarinyarka me'ad ne..
Dady yayi sauron katse masa maganar ta hanyar cewa "ni bani da wata yarinya me'ad arayuwata ,yarinya daya gareni kuma sunan suhailat Dan hk kayi wata mgnr ban da wannan"
da sauri me'ad tashiga Jan gwiwowinta tana kuka "Dan girman Allah dady kayi hakuri ka yafe min ,kayi hakuri wallahi nayi nadama ka daina cireni acikin ya'yanka ...kuka take sosai tana bashi hakuri "Dan Allah ku bashi hakuri ya yafe min wallahi na tuba bazan sake ba, ku gaya masa duk abinda yake so zanyi masa bazan sake ketare zancesa ba, na tuba dady nabi Allah da manzonsa nabinka ka taimakeni ka taimaki rayuwata banida kamarka ,kaine ubana, bani da wani uban dayafika kamin komai arayuwa ka inganta rayuwata ka gatantani kayi min komai ,kayi hakuri nasan ban kyauta maka ba .....
"Banice yakamata nayi maka abinda nayi ba .....,Amman banida yadda zanyi ,bani da yadda zanyi da kaddara data gitta akaina, kayiwa darajar Allah kace ka yafe min ko al'amurana zasu daidaita jikin jama'ar dake gurin yayi sanyi hk ma dady karan kanshi .
Sai dai yayi shiru yana aikin jijiga kafarsa, nan kowa yashiga topa albarkacin bakinsa, wannan yayi nasiha yayi shiru ,wani ma yakama da kyar dai akasamu jikinsa yayi sanyi gbdy , ya sauke naunayen ajiyar zuciya Wanda ke nuna ya sauko.
mahaifin sajida yace "me'ad matsa kusa da mahaifinki sosai ki sake rokosa gafara kinji " cikin rawar jiki ta sake tsugunna har ƙasa ta roke shi gafara, bai yi gardama ba yace zai yafe mata amma tare da sharad'in kowa yayi tsuru tsuru agurin suna kallonsa tare da mamakinsa "
Mahaifin sajida ne yayi karfin halin cewa "wani sharadi ne wannan ?
"Sharadina shine zan raba aurenta da fu'ad saboda ni fu'ad din ne gaba daya bana sonta dashi ......."na tsine shi na tsani naga suna tarayya da 'yata , indai har tana buƙatar yafiyata to tabbas sai ta rabu da fu'ad..
kuma rabuwa ta har abada idan har ta amince da haka zan yafe mata kuma za ta zauna a gidana ta ci-gaba da rayuwa tare dani kmr can baya amma fa batare da auren fu'ad ba..
Mmn sudais ce
Merkur Super Platinum Slot Review | Play at the best casino!
ReplyDeleteFind all the games on Merkur Super Platinum Slot - a video slot with 제왕카지노 5 메리트 카지노 reels and 25 메리트카지노총판 fixed paylines in the free play mode.