"Grandmaaa" Du'a data shigo falon takira Hajiya ganin bata falo, shigowa Razika dake biyeda ita tayi tace "tana sama, muje kinuna mata kalban da aka miki" dasauri Du'a tai stairs tana murmushi sosai dan kitson da aka mata yamata kyau dan ba'a taba yimata kalanshi ba, tana kaiwa falon sama takara kiranta. "Grandma" dasauri Hajiya take tareda Ammi tace "jikata tazo bangayamiki ba, Du'a gani nan adaki shigo" bude kofan dakin Grandma ahankali tayi tashigo Razika biyeda ita, ganin wata babbar mace baka tareda Grandma yasa ta tsaya batare data karaso ba, saukar da kanta tayi kasa ahankali ta gaida matar tace "ina yini" murmushi Hajiya tayi takalli Ammi tace "ana gaidake" wani kayataccen murmushi Ammi tayi tace "Masha Allah, sabida kin ganni kikaki karasowa ciki wajen Grandma dinki" dan murmushi Du'a tayi cikeda kunya ta girgixa kai saikuma tajuya dasauri tace "bye Grandma" sanan tabi ta gefen Razika tafice dasauri, dan dariya Hajiya tayi tace "kinganta haka take akwai kunya" takalli Razika tace "anmata kitson" gyadamata kai tayi tace "anyi kalba akayi, yayi kyau sosai" "haka nakeso, jeki bata abinci taci" ficewa Razika tayi, Ammi tace "Hajiya yar Muktar din UK ne" dariyan manya Hajiya tayi tace "yar Zainab din kano ce, Du'a, wacce nake baki labarinta" murmushi Ammi tayi tace "Allah sarki Yarinyar ga kyau ga natsuwa"
Saida tai wanka sanan ta chanza kaya zuwa wani gown data dauka daga wardrobe red iya guiwa ya tsaya mata yamata kyau, bata daura dankwali ba tasaki kalaban dayake nan har waist dinta kaman ansaka mata attachment tabude kofa tafito da saurinta ta sauko dan itada Razika sun biya wani super market tadauki drawing book babba da HB Pencils da eraser da colors, dakin kasa wanda shine dakin Razika da Amina ta shiga suna zaune sunacin abinci duk suka bitada kallo ganinta adakinsu, Razika ta kalla tace "ina drawing book dina"? Dan ware ido Razika tayi sanan tace "inama nasa ohh natuna suna dinning" dasaurinta harda dan gudunta tawuce tafita a dinning ta tsaya ganin komi yasa tasaki wani murmushi she's so happy and excited bayan reading novels wanda technically Ya Hamad ne yakoya mata the only thing datasan ta iya shine zane, babu abinda bata iya zanawa ba saida yawanci abinda tafi zanawa yanzu shine takalma tana bala'in son zama takalma sabida batada takalma agida dayawa dan bata fita saisa hakanan idan tazauna saita dinga zama dream shoes dinta.
fitowa tayi tazauna akan falon, bude komi tayi, tai sharpening pencil dinta sanan tabude hadadden drawing book din da Razika tasiya mata ta shiga zane, yanda take zanen kadai saika tsaya kana kallon hannunta sabida wani kalan burgewa datake yi kafin good 3min tagama zama wani tsantsararren takalmi hill na mata, murmushi tayi tadauki drawing book din tana kallon takalmin saikuma chan ta hura iska sabida all particles na eraser dakekai yafita sanan tace "to yanzu wani suna zansa maka kai takalmin nan kaga nadade banyi drawing ba tunda drawing book dina na gida yacika Ya Hamad baikara sayomin ba" shiru tayi tana tunani kawai saita sauke drawing book din akano saitama zanen tittle Du'aXAbuja, kallon rubutun tayi dayay kyau, kawai saita bude wani page tashiga zana wani daban.
Ahankali Ammi datai sallama da Hajiya ke tafiya kan stairs Hajiya bata rakota ba sabida wani office related call da aka mata, tundaga stairs take kallon Du'a, dudda batasan metake zanawa ba but ganin drawing book yasan tasan zane take, kitson kan yarinyar tabi da kallo da yanda take zane ita kadai saita daga ta kalla tai murmushi tasauke tacigaba, hakanan Allah mai daurama mutum so da ki kawai taji Du'a na burgeta tanason yarinyar, karasa saukowa tayi Du'a ma bataji saukowanta ba sabida yanda hankalinta yay nisa, karasawa cikin falon Ammi tayi ta tsaya tana kallon takalmin da Du'a ke zanawa batasan lokacin datace. "Masha Allah, you are gifted Du'a" dasauri Du'a tadago kanta ta kalli Ammi, murmushi tayi sosai tace "Mum yayi kyau"? Hakanan Ammi batasan mesa ba but kiranta da yarinyar tayida Mum yasa son datake mata ma yay double da sauri tazauna kan kujeran dake gefen Du'a tamika mata hannu tace "bani drawing book din naga" da sauri Du'a tadauki drawing book din tamika mata sanan ta matso kusada kafan Ammi ta daura hannayenta kan cinyan Ammi batare datama sani ba tana kara leka drawing din itama, gyara zama Ammi tayi jin yanda yarinyar ta dagata tafara duba drawing din daga farko tace "wow, haka kika iya zane Du'a, this is talent wlh" murmushi tayi sosai dan batasaba ayabeta ba agidansu Ya Hamad ne kawai yake cewa zanen ta yay kyau, murmushi takara yi tace "Ya Hamad ne kadai yataba cewa inada talent sai ke Mum" takarashe maganan looking damn happy dayasa Ammi taji suka matsalolinta ma sukau, hannunta takai tashafa kan Du'a tace "you are very very talented Du'a, kinsan nawa ake biyan wayanda suka iya zama abu haka" girgixa mata kai Du'a tayi tana kallon Ammi saikuma tace "Mum ni ai baza'a biyani ba, kinga banyi school ba a JSS2 na tsaya, wanda yay karatu ne ai ake bashi aiki ko"? tunda take maganan Ammi ke kallon yarinyar, idan tana magana sosai zakaga rashin wayau da yarinta aciki wanda yarinyar dakeda shekarunta bai kamata ace hakan yasameta ba, murmushi Ammi tayi tace "ko ina talent yake yanada kyau ayi acknowledge nashi, and it doesn't matter sabida kin tsaya da karatu a JSS2, with this" Ammi tanuna mata drawing book din tace "with this zaki iya samin aiki a companies da dama that are into shoes kuma abiyaki" wani irin kyalkyacewa da dariya Du'a tayi tawani kife kanta akan kafan Ammi tanajin dadi sosai data kasa boyewa dayasa Ammi takarajin tashiga ranta, Hajiya data dade a stairs tana jinsu takaraso tazauna kan kujera tace "ke karki karya ma mata cinya inba so kike Asad yashigo yay yaki dani ba kirufamin asiri yaron nan son maman shi yake kaman me" dariya sosai Ammi tayi tace "kundai fi kusa kedashi Hajiya" tashi Du'a tayi tana murmushi itama, Ammi tace "how about natafi da wanan drawing book din sabida nasaman miki aiki dashi" dawani irin sauri ta gyadamata kai tace "eh Mum kutafi dashi" tawani washe baki tajuya tana kallon Hajiya dake kallonsu itama tana murmushi tace "iyye Du'an baaa, tobazakima Mum din naki godiya ba za'a neman miki aiki kinata washe baki" cikeda farin ciki takalli Ammi tace "Mum nagode Allah amfana" tashi Ammi tayi rikeda drawing book din tace "bari nashiga gida" Takalli Du'a tace "yaushe to zakizo ki gaidani agida inada yammata nima kinga saikiyi sababbin kawaye ko" juyawa tayi takalli Hajiya dake kallonta tace "yo jama'a kome aka tambayi yarinya sai tajuyo takalleni, Razika da Shemau sa rakota suzo gobe" "shikenan, Hajiya sai munyi waya" "tom Walida ki gaidamin da Sharif dasu Aneesa, shikuma gogan kice nace Allah yataroshi" dariya Ammi tayi tana bude kofa tace "yau dai munjiku arana kuda ba'a shiga tsakanin ku" Jan kofan tayi tarufe tafice.
Hajiya ta kalli Du'a daketa murna tace "zansa driver yasayo miki wani sabon drawing book, kinci abinci"? girgizamatakai tayi tace "a'a" dasauri tana hararanta tace "tashi kije kici abinci banson kina wasa dacin abinci, anjima idan zasuyi girkin dare saiki bisu kidinga ganin yanda sukeyi ko" murmushi tayi looking so happy tace "tom grandma" sanan ta tashi tayi dinning dasauri Grandma tabita da kallo daga zuwanta harta fara murmurewa kwanan nan zatai kiba tai kyau abinta.
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
EPISODE 1️⃣6️⃣
Koda Ammi ta shiga gidan Sharif kawai tagani zaune a dinning yanacin spaghetti da Rahima tadafa, yana ganinta yace "Ammi ina kikaje" zama tayi akan dinning tace "daga wajen Hajiya nake" takalli Rahima data fito daga kitchen tace "iyye yammata na angirma harkinyi girki" murmushi tayi tazauna kusada Ammi ashagwabe tace "Ammi please sai next Monday zamu resuming school this week muhuta muyi shopping kinji Ammi" Sharif dakecin abinci ne yaharareta yace "why mesa yaran this generation basason school saison kula samari" murmushi Ammi tayi takalleta tace "bazakuyi lectures bane" ahankali tace "first week lectures baya serious sosai Ammi fa"gyadamata kai Ammi tayi cikeda gamsuwa tace "okay I will think about it inasu Aneesa da Mariya"? tabe baki tayi tanajan plate tace "sunyi bacci" kallon Sharif dayagama cin abinci Ammi tayi tace "ina Asad" ajiye cup din dayake shan ruwan dashi yayi yace "dazun nan yafita, bansan inda yajeba" "Ammi wai yaushe Daddy zai dawo" Rahima dake kusada Ammi tamata tambayan, murmushi Ammi ta kakalo tace "this week ko next week, bari kiga naje na kwanta" ta tashi tawuce sama Sharif yabita da kallo.
Wani dankareren building wanda nan a offices din senators na Nigeria suke ya dumfara cikin mad ride dinshi na Benz, tsayarda shi sojojin dake guiding building din sukayi, ahankali yasaukar da glass din motar, ganin wanda keciki yasa suka shiga gaidashi, Jan motar yayi ciki har zuwa inda ake parking yay parking sanan ya kashe motar yafito, wanan karan yana sanye cikin wani classic 3quater wanda dakadan yawuce gwuiwanshi dark blue color, sai wata white t shirt mai V neck dayasaka data kara fitar da kyawunshi kana iya hango kwantaccen gashin kirjinshi ta wuyan rigan sabida shape din dayake dashi na V, kafanshi Sanye cikin flat slippers na Gucci, kanshi ya sanya p cap na Gucci, lips dinan nashi yay pink yir looking damn moist and fluffy, sai black eye glasses na Gucci a idanunshi, hannunshi ya daura agogo da bracelet na Rolex akai sai zuba uban kamshi yake, kana ganin shi kaga irin yaran masu kudin nan yan gayu looking casual sabida yau Sunday, maida kofan motan yayi yarufe sanan yafara tafiya ahankali yashiga cikin premises din babu kowa ciki sai security personnel dake gadin wajen wanda dazaran sunganshi gaidashi suke dan sunsan koshi waye, elevator ya shiga zuwa 5 floor, wanda yasadashi dawani mahaukacin building dazaki dauka ataurai ne, ga kujeru na ma'aikata amman sabida yau Sunday babu kowa, cigaba yayi da tafiya zuwa gaban wani hadadden kofa wanda da finger print ake bude kofan, baiyi yatsanshi yasa abin yayi magana Authorize Mr Asad, kama handle din kofan yayi yatura kofan yashiga tashi daya, wani irin zabura mutumin yayi yasauka dagakan yarinyar dayakekai dataji uban attachment ja akai yanajan boxer dinshi dayadan sauke kasa kadan dama dagudu yana rufe abin datai wani automatic kwanciya jikinshi na mugun bari yakalli yarinyar da babu kaya ajikinta yana mata ihu. "leave this office, I said leave" Ahankali yaja kafanshi baya kadan bazaka taba iya tantance wani yanayi yakeba sabida glasses din dake kan idanunshi, dasauri mutumin daya rude yace "Asad look is not what u are think......" awani irin zuciya Asad yajuya fuuuuu, dagudu mutumin yashiga laluban kayanshi yana sakawa batare dayabi takan karuwanshi dake sa kayanta arude ba yasa riganshi baima tsaya saka malum malum ba yazura slippers din office yafice dagudu, sauka kasa yayi gudun da yakeyi yasa yacimmai shan gabanshi yayi yace "Asad listen to me listen to me son please" tsayawa yayi chak yana kallon mahaifin nashi dat so much disgust him now, ahankali yakai hannunshi yacire glasses din dake kan idanun nashi yace "wanan ne US din dakaje ko Dad? Almost 2month babu wanda yasaka a ido kana garin nan Dad" juyawa mutumin yayi yana kalle kalle ganin babu mutane inda suke yasa cikin muryan lallashi yace "listen to me Asad wlh naje US ba karya nayi ba kawaidai dana dawo banje gida bane" wani irin kallon mahaifin nashi yake kallon bakin ciki da tsantsan tsana, Dan murmushi mahaifin nashi yayi irin na marasa gaskiya, cikeda lallashi yace "how are you my boy? Your Mum told me kadawo kaima kaje kano gaida Dadda ka, sanan zakai hosting show ma Youth a TV station, I am so proud of you Asad dina, you are really my son" sosai idanunshi sukai ja ruwa yacika a idanunshi fall ahankali yace "why are you doing this to Ammi? After all the sacrifice da Ammi tamaka why are you treating her this way, why are you maltreating my Mum Dad eh"? kana ganin yanda yayi maganan kasan zuciyanshi namai zafi da daci, ganin yanayinshi yasa Baban yadan sosakai yace "listen Asad, inamaka kallon yaro but I think u are not more a little boy anymore, I love you morethan anything in this world, in fact ma darajan kane ma yasa nai deciding I will leave tareda mamanka har karshen rayuwa but banason mamanka Asad, ko kadan bani sonta, auren hadi akamana nida ita, ur Mum was never my choice, choice din Daddan kane, yar maigadin shine dayarasu dagashi har matanshi lokacin sunje gida kauye suna dawowa suka sami hatsari suka rasu, shine sabida how the gateman was good to Daddan ka yasa yadauki maman ka shida Mamana Allah yajikanta suka raini mamanka aka sata a makaranta aka hadani aure da ita dudda na nuna banso..." yanda idanun Asad sukaija zaka dauka zai makance ne, cikin wata irin murya datai rauni bama ta fita sosai tsabagen bakin ciki da kunci yace "is that the reason why kakebin all kind of useless matan banzan Abuja nan Dad" Dasauri yace "banason aure aure, da mata daya zan iya rayuwa since uwarka ce d lucky one saisa I am stuck with her, look son I don't wanna go into details with you now, nan gaba u will understand after all kai d'ana ne, my blood runs through ur veins, you are just like me" cikin wani irin huge voice yace "I will never be like you, bazan taba zama mutum irin ka ba, I despise you Dad, u are nothing but a shame to my name, wlh da ana chanza uba dana chanza ka cus u don't deserve a son like me much less a good wife kaman Ammi na" yana maganan yawuce yabude motan shi yashiga yana kokarin tadawa Dad yazo wajen. "Asad, Asad, come here son calm down nasan ranka abace yake, but yakakeson nayi eh ur Mum is such an old school babu abinda ta iya sai kunya, Asad" wani irin jan motanshi Asad yayi yabar wajen ubanshi na kwalamai kira. "Asad, Asad" tsaki yaja yadafa kanshi yace "yaro sai bakin zuciya, nima maiya kaini zuwa office yau" tsaki yayi shi kadai yace "to nasan zaizone yaron da fushi yake dani kona kirashi baya dauka" tsaki yasakeyi dukya bala'in damu yace "daka tsaya kajira Zinariyan ka daganan ma kona sami contact din kyakkyawan yarinyar nan dayafimin, yanzu look what I cause yanzu, shiit yanzu sai nakoma wajen wanan matar nan da nonuwan kirjinta sunfi silifas tsawo abu har cinya, dan Allah dai jibi nonon wanan cinyare dinan atsaye, na Zinariya ma haka, amman ace yaro yakasa ganewa uwarshi ba gaba ba baya gatanan ne gabaki dayanta zero ce" yaja tsaki yawuce yana tafiya zuwa ciki ranshi fall da damuwa.
Allah da ikonsa ne kawai yakawoshi gida lafiya, ko parking din kirki bai iya yayi ba yafito daga motan dawani irin gudu security su yace "subhanallah" ganin motan na tafiya yashiga yay parking da kyau shikuma Asad yay wucewan shi batare dayama juyoba, ko katon Sharif dake zaune a garden dake kusada flat dinsu baiyiba yawani irin buga kofa yashiga ciki, binshi da kallo Sharif yayi saikuma ahankali yasauke ijiyan zuciya yacigaba da aikin dayake yi akan system, karan zubarda abu dayaji yasa yatashi da sauri ya ijiye system dinshi awajen, bude kofa yayi yashiga falonsu sanan yamaida kofan yarufe yay kitchen dinsu da sauri tsayawa yayi awajen kofa yana kallon yanda Asad ke zubarda komi na kitchen din yana rotsasu akasa kaman wanda yazare, cikeda damuwa Sharif yace "what's wrong with u Asad"? Wani irin daga kafa Asad yayi yadaki fridge din kitchen din cikin zafin harshe yace "it's none of your business leave me alone Sharif" shiru Sharif yayi yana kallonshi yanda yake haukanshi shi kadai wanda is not new to him, kowa yasan Asad da zafin zuciya haka Ammi ta haifoshi da halin nan.
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
Freepage
EPISODE 1️⃣7️⃣
Yagama barinshi duk basu isheshi ba ganin yafara punching kofa da hannunshi yasa dasauri Sharif yashiga kitchen din wani irin kamashi Sharif yayi yasashi ajikinshi ya rungume tsam yace "calm down Asad ba Ammi tace idan ranka yabaci kadinga salati ba, calm down please" kokarin fizge kanshi yake yana ihu. "I said leave me alone Sharif, stay out of this" kankameshi sosai Sharif yayi with all the power he got yace "Ya isa Asad I am here for u, I am here, we gonna be brothers forever okay, ina kaje? what happen? Giran da kayi dazu ina kaje?" shiru yayi yakasa magana ahankali Sharif yace "you went to see Dad ko"?Murya chan kasa yace "I guess kaima kasan babu wani US din dayaje" shiru Sharif yayi sai chan yace "before muje kano lokacin kana UK I saw how worried Ammi is yasa naje office naduba shi, I saw him though shi baiganni ba baisan naganshi ba" shiru Asad yayi saikuma gently yatashi daga jikin Sharif zama yayi akasa ahankali yajingina da cabinet din kitchen din idanunshi sunyi jajir, zama shima Sharif yayi kusadashi yana kallon kasan wajen, ahankali Asad yace "I don't know why Dad choose this life he's 60 but jin kanshi yake kaman dan 20, that Oldman is lost Sharif completely, can u believe niyake gayawa I am just like him eh Sharif" yay dan shiru idanunshi sunyi ja yace "I can never be like that man, bazan taba neman matan banza ba, wlh bazan tababa cus I hate them kyama ma suke bani, I hate that I am his son, wlh da ana chanza uba da na chanza nawa, I hate that man Sharif" kallonshi Sharif yake bakaramin tausayi yabashi ba matsawa yayi kusada shi ya jingina da cabinet shima yace "bazaka taba zama kaman shiba that I am sure of Asad but we gonna do something right now" yay maganan ahankali yace "inaso ka share batun Dad for now dan is affecting u physically and mentally bayan kasan u need to be at ur best gobe zaka fara TV show dinka eh Asad, this whole mess will affect ur productivity as well as ur performance, I cannot be managing everything for u eh, u need to be at ur best mugama this TV program in the next 7days sabida kasamu muyi concentrating a office we need to release new collection eh Asad, banda ma haka kanason Ammi taganka ahaka ne kaga how I am better than u kenan, tunkafin mutafi kano nasan Dad na garin nan amman koda wasa ban nunama Ammi ba sabida I need her happy, kaiko look at u now bayan kasan mu Ammi ke gani taji dadi common be a man for Ammi, let's keep pretending we don't know what Dad has been up to koma yana gari" Ahankali yasaki dan murmushi saiya kalli Sharif din yace "kasami wanan illustrator din?" girgizamai kai yayi yace "no he's on his summer break wai, kaima I don't get u Asad why don't u wanna give Nigerians dinmu a chance" "cus they can't give me what I want" hararanshi Sharif yayi yace "shikenan haka zan zuba idanu inta kallonka wlh idan ka shiga tight corner kaida kanka zaka dinga neman su" tashi yayi ahankali yace "don't worry I will get one" fita yayi daga kitchen din Sharif yabishi da kallo cikeda so dakuma tausayin dan uwan nashi yasan wani zubin Allah kan jarabci yara da iyayensu and that's Asad da dukansu ma a family nan biggest test, Dad gashinan ne kawai living one kind of useless life kaman yaro, imagine Babba dashi he is willing yayi karya yabar gidanshi da sunan yatafi UK just dan yatafi wajen matan banzan shi, tsohon mahaifinshi baida lpy he don't care yaje yaduba shi saidai yayta tura kudin magungunan shi, ayanzu kuma shi kadai ne dandan Dadda namiji, dan dama Dad ne Babba sai mahaifinsu daya rasu, sai Anty Turai mahaifiyar Aneesa, Mahaifinsu daya rasu ne kawai ya haifi yara dayawa a family Shine first born sai Rahima sai Mariya, itakuma Aneesa ita kadaice yar Mamanta Turai, da mijinta yasakota tadaukota suka dawo gidan Dadda dazama kafin tabama Ammi ita aka zo da ita Abuja tafara school gudun kar mijin ya kwace ta dan Anty Turai yar rigima ce fitinanniya saisa ma takasa zaman gidan miji.
Banda haka Ammi is just the best woman aduniyan nan, sosai take tarbiyan yaran batare data nuna gazawanta ko gajiyanta ba, hasalima bala'in son yaran take suma haka suke sonta dan wajen Ammi yafi musu ko'ina.
Mikewa Sharif yayi ahankali yanabin kitchen din da kallo, kwashe abubuwan dabasu wani baci sosai ba yayi sanan yawuce yafita, sama yayi ahankali yabude kofar dakin Asad din, akan gadonshi ya ganshi yana bacci, ajiyan zuciya yasauke sanan yaja kofan yarufe yasauko kasa, masu gyaran gidansu yakira yasasu gyara kitchen din sanan yakoma falon sama yazauna tunawa ma yayi da system dinshi awaje dasauri yatashi yawuce waje.
Dayake tanada yammata hakan yasa Ammi bata dauki yan aiki ba, su take sawa girki, duk tana kitchen taredasu suna aiki takalli Aneesa dake wanke rice tace "namuku kawa fa" dasauri duka yaran suka tsaya suna kallonta, Aneesa ce tace "Ammi a ina"? murmushi Ammi tayi tana maida marfin tukunyan data bude tana rufewa tace "jikan Hajiya ce, sunanta Du'a, she will be ur mate Aneesa keda Mariya" tanuna Mariya da itama ta tsayar da peeling Irish din datake tana kallon Ammi, tafi Aneesa tayi da Mariya tace "yi sauri Mari mugama girki muje gidan Hajiya" murmushi Ammi tayi takalli Rahima data cigaba da aikinta tace "Anty Rahima kinyi shiru" wani irin murmushi tayi tace "Ammi bakina Ya Asad maganan wayoyin muba" dasauri sauran sukace eh Ammi, hararansu tayi tace "wai mesa kuke tsoron yayan ku haka, aiko babu wanda zai kara aikena wajenshi cikinku kuje kusameshi dakanku kokuma kuma Sharif magana yasaimuku" dasauri Mariya ashagwabe tace "Ammi wlh Ya Sharif mugune yace wai babu wanda zaici kudinshi cikinmu wai tara kudin aure yake, duk wanan wahalan inda Dad na nan muna gayamai zai sai mana wlh" shiru Ammi tayi tace "kugama girki kuje ku sami Asad to baruwana kudena sani a lamarin ku" nariga nahada muku komi ku karasa kuyi setting dinning up tai maganan tana fita daga dakin.
Wuraren 5 suka gama girkin tass sukai setting dinning dakinsu sukayi kowa yay wanka, Aneesa data gama shiryawa cikin wata yar rigan zaman gida half gown mai spaghetti hand ya tsaya mata a knee ta kallesu tace "kumuje wajen Ya Asad" kwalalo ido daga Mari har Rahima sukayi atare sukace "kidawo lpy nidai bazani ba" hararan su tayi tace "wlh naje nawa kadai zan fadamai" tawuce fuuu tafice tana tafiya ahankali gabanta nafaduwa, tsayawa tayi takalli kanta a madubin dake bangon falonsu tayi kyau sosai ga kitson kanta yamata kyau abunku da faran yarinya dan gidan Asad ne kawai black cikin yaran, bude kofa tayi tai flat dinsu Asad, tsayawa tayi abakin kofan tai knocking, jin ba'a amsaba yasa ta danna door bell har sau biyu, sake knocking tayi cikin wata irin isasshiyar murya akace. "waye"? faduwa gabanta yayi muryanta har rawa yake tace "Ya Asad is me, Aneesa" shiru aka sakeyi takai kusan 3min atsaye awurin sanan akace "come in" dasauri tabude kofan ta shiga yana zaune a falo dagashi sai towel daya daura a waist dinshi ya zaunar akan kujera ya mikarda kafa yadaura kan enter table yadaura MacBook akan cinyanshi yana aiki ruwan coily gashinshi nabin fuskanshi.
Kallo daya tamai tasaukar da kanta kasa dasauri, tunda take bata taba ganinshi ba rigaba sai yau, wani irin hadiye miyau tayi gabanta na dukan uku uku, tashiga wasa da yatsunta takasa magana, batare daya kalleta ba hankalinshi nakan aikin dayake yi akan system yace "why are you here"? Yanda kirjinta ke dukan uku uku yasa muryanta yama fara rawa tace "Y.....a As...ad, dama....dama...." saita karayin shiru tadan dagokai ta kalleshi aikinshi yakeyi comfortably a MacBook dinshi kaman baimasan tana wajenba, kirjinshi tabida kallo jitayi jikinta yadau rawa da sauri ta maida kanta kasa tadage tace "Ya Asad I want a new phone Ammi tace zata gayama shine yanzu wai muje musameka da kanmu, ahhmm kuma da shopping da resuming school, I want new school bags, pairs of shoes sai Abaya dakuma and kuma pads dinmu yakare duka" saida takai nan tai shiru kirjinta na bugawa fat fat fat bata taba sanin zata iyama Asad magana ba saiyau, juyoda kanshi yayi yakalleta for the first time tunda tashigo dakin, ahankali kaman baison yay maganan yace "what happen to your phone" dagokanta tayi ta kalleshi yanda yake kallonta yasa takasa mai karya langabar da murya tayi tace "babu abinda yasame shi I just wanted a new one" still kallonta yake babu alamun wasa kowani yanayi akan fuskanshi yace "and the other things nawa zai isheki kisaya" wani irin murmushi tamai cikeda jin dadi tace "150k zai isheni Ya Asad" Su Rahima da tuntuni suke gaban dakin suna jiran suji yanda zata kaya jin yana tambayanta nawa yasa suka turo kofan suka shigo suna sallama, duk atare suka gaidashi muryansu narawa. "Ya Asad good evening" dasauri Aneesa tace "Ya Asad kaga saida nace musu fa suzo muje tare sukaki wai tsoro sukeji sai yanzu dasukaji zaka bani kuma wlh ni bazan raba kudina daku na nawa kadai nafadi" dasauri Rahima tadan kyafta mata ido takalli Asad din tace "Ya Asad sorry" Mari ma ahankali tace "Ya Asad sorry ni wlh tsoro ya hanani ma biyota" duk tsayawa yayi yana kallonsu yanda duk suke trembling, ahankali yasaki dan murmushi, wani kalan dadi ne yakashe su dasauri Rahima tace "Ya Asad nima I want new phone" dasauri Mariya tace "Ya Asad nima" ganin suna neman samai ciwon kai yasa yakalli Aneesa yace "go to my room, check the left sidebed drawer bring all the money that is there" wani irin dadi taji tace "tom Ya Asad" dasauri tawuce stairs tai sama dakinshi tabude ta shiga wani kamshi ne yamata sallama, drawer taje ta kwaso duka kudin wrappers na yan dubu dubu ne guda 10, kwaso su tayi tasauko, Su Rahima na ganinta suka shiga murmushi, gabanshi tazo zata bashi kudin gefenshi ya nuna mata hakan yasa ta ijiye kudaden awajen, hannu yasa yadauki rapa biyu yabata dasauri takarba tawani washemai baki tama kasa godiya, "Rahima" "na'am Ya Asad" dasauri tazo dauka biyu yayi yabata dagudu Mari tazo itama yabata biyu dukansu yabasu 200k each, ahankali yace "u will get the phones tommorow" wani irin ihu sukayi sukahau tsalle awurin suna rungume juna. "Ya Asad thank u, yaaayyyy, Ya Asad u are the best wallahi" ihunsu yatada Sharif dake bacci hakan yasa yasauko ganin kudi a hannunshi suna rawa suna nunamai yasa cikeda wasa yace "yanzu sabida ku yan bakin ciki ne Asad na rabon kudi shine bazaku tasoni nazo na amshi nawaba " dasauri Rahima tace "bayan kahanamu damuka maka magana" hararanta yayi yaje gaban Asad dake aikinshi yana kallon ragowan 4 raps na kudin yace "Ya Asad nima abani nawa"? Dan hararanshi Asad yayi saikuma kaman bashiba yakalli su Aneesa yace "abashi" atare sukace "nooo Ya Asad" wani irin biyo su dagudu Sharif yayi aiko suka kwasa dagudu suka fita daga dakin yace "shegu yan bakin cikin yara kawai" murmushi Asad yayi sosai yace "kasai musu waya" juyowa yayi yaharari Asad yace " marasa kunyan yaran nanne zasuci kudina, ashe zasu mutu bawaya, Tara kudin aure nake" tabe baki Asad yayi yace "says wanda baida girlfriend" hararanshi Sharif yayi yace "Malam ya isheka fa kaita daga harkata tunda dai kahanani kudi".
wa.me/+2347012181461
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
EPISODE 1️⃣8️⃣
Tashi Asad yayi ya rufe system din ya ijiye sanan ya kwashe ragowan kudinshi yawuce wanshi sama, baiwani dade ba yasauko cikin jallabiya sabida sallan magrib da aka kira sai baza kamshi yake bayin falo shima Sharif ya shiga ya dauro alwala sanan yafito suka fice tare zuwa masallaci.
Ana Magrib suka shigo gidan, dinning direct sukayi, zama sukayi Ammi na fitowa, Sharif yace "Ammi ina yaran nan wai nisukema dariya" dan hararanshi Ammi tayi tace "toba dole suyimaka ba nan nan yaran nan suka rokeka kudi kahanasu, anyway suntafi wajen Hajiya, kasan jikan Hajiya tazo shine ita sukaje gani nace musu nai musu kawa age mate dinsu ce wai zasu cemata ta shirya suje shopping tareda ita gobe" tsaki Sharif yayi yace "Ammi bani abinci na naci nima naje naga jikan Hajiyan muga ko za'ayi ta gida ne, Ammi tanada kyau"? Hararanshi Ammi tayi tace "inkaje ka gano da idanunka" tai maganan tana bashi plate na biryani rice, karba yayi yafara ci sanan ta zubama Asad dake daddanna wayanshi kaman bashi awurin. Biryani ta zubamai sanan ta turamai gabanshi tace "ina kaje dazu Asad" dagokai yayi yakalleta spoon yadauka zai faracin abincin yace "naje nasha iska ne kawai Ammi" ture abincin Sharif yayi yamike yace "Ammi natafi" wanan karan dariya Ammi tayi tabishi da kallo fita yayi abinshi, tashi itama Ammi tayi tai sama bata wani dade ba tafito rikeda drawing book din Du'a samin shi tayi zaune inda tabarshi yanacin abinci, kujeran kusada shi taja tazauna sanan ta ijiyemai drawing book din agabanshi, Ammi yabi da kallo saikuma ya ijiye spoon din dayakecin abinci dashi yadauki drawing book din yabude yana dubawa, ahankali yakalli Ammi yace "Ammi who drew this"? murmushi Ammi tayi tace "zanen yayi kyau" dasauri yana kallon drawing din yace "this is classic, I mean the hands behind this drawings is a genius, Ammi wow, idan yanzu nabada wayan nan zanen akai bringing this shoe to life my company zai zama number show brand company in the whole Africa" murmushi sosai Ammi tayi tace "zaka bama mai zanen aiki kenan"? sai alokacin ya kalli Ammi yace "who drew it Ammi" ahankali Ammi tace "zan gayamaka, but my zanen is very dear to me nai alkawari zaka bama mai zanen aiki dudda batai makaranta ba" dasauri yace "Ammi u mean mace ce tai zanen!" gyadamai kai tayi tace "yes mace ce, but batai school ba sabida some matsaloli irin na rayuwa, but she's talented, inason kabata aiki sanan kabiyata tsakani ga Allah yanda kake biyan illustrators dinka" yatsine fuska yayi yace "Ammi kinsan qualifications din illustrators dina kuwa, how can I pay wacce bada da credentials haka is not possible ma" fizge drawing book din Ammi tayi tace "then forget it" dasauri yace "okay naji Ammi kawo" ya karbi drawing book din yana kara dubawa, Ammi tace "yanzu yaushe zata fara aiki" ahankali yace "gobe Monday, for now Sharif will handle everything dan sai next week zan koma"
wa.me/+2347012181461
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️M SHAKUR
Free page
EPISODE 1️⃣ 9️⃣
Gyadamai kai Ammi tayi cikeda jin dadi tace "Allah maka albarka Asad dina" murmushi yayi yace "Ameen Ammi, but who is the girl"? kaman bazata fadamai ba tace "jikan Hajiya ce, she's 21" yatsine fuska yayi yace "Ammi ni all those children banson raini fa" hararanshi Ammi tayi tace "to Uncle Asad, ya za'ayi ma tamaka raini, jikan Hajiya ai she's just like ur sister su Mariya idan tayi badaidai ba ka gyaramata, kuma batada raini ko kadan that I know" yatsine fuska yayi irin baimasan maganan nan ahankali yace "Ammi I want coffee" tashi Ammi tayi tace "bari nahado ma tunda yaran nan duka sun gudu gidan Hajiya sun barni nikadai" kitchen tawuce tashiga....
Yau idan kaga bakin Du'a har kunne, har Rahima dake feeling tagirme su bazata iya zama friend din Du'a ba jitayi tanason Du'a sabida yarinyar akwai kyau dudda sun lura duk sun fita wayewa basu wani damuba kafin kice me cika falon Hajiya sukayi da hayaniya, suka tasa Hajiya agaba sai tabama Du'a itama kudin shopping gobe duk suka tafi tare, itama 200k tadauko tabata daman tanason takai yarinyar shopping but bata sami lokaci ba waya ma tace "gobe idan zata dawo zata taho mata da waya" duk suna cikin uban hanayinan Sharif yay sallama, dasauri Rahima tace "kinga Du'a we have two brothers, wicked and harsh, yanzu zakiga weekend one din shike mana murmushi da wasa amman shine ba'acin kwandalan shi" Hajiya dake kallonsu tace "Au haka kikace Sharif shigo kaji yanda kannenka kebata maka suna" turo kofan yayi yashigo hakan yasa Du'a itama tadaga kanta dantaga wanda ake batawa, wani kyakkyawan gayene dogo mai tsayi gashinan fari fat kaman su Rahima, tana ganinshi taga kamanninshi da Rahima da Mariya, baida kiba ko kadan, sai uban kyau ga sajenshi baki sidik dasuke nan akwance, gashin baida tarin gashi irin na Asad amman akwai gashi kadan da lowcut yakeyi ko kadan bata ganeshi ba hakan yasa kawai ta tsaya tana kallonshi daga inda take zaune kusada Hajiya dasu Rahima.
Dauke kai yayi daga kallon Du'a ganin kannenshi da kowa na wajen yace "Hajiya yanzu har gidanki suka tattaro sukazo suna gulmana yaran nan, aiko wlh zan baku kashi" yay maganan yana dunfaro su, ihu sukayi duk suka tashi suka kankame Hajiya Du'a ko sai dariya dasauri Hajiya tace "jama'a na shiga uku, wani yamikomin wayata yaga wlh Ammin ku zan kira tazo ta kwashi yaranta kutafi gida tunda neman kasheni kuke kai kuma wlh bazaka taba yaran nan agidan nan na ko kazo kazauna kokuma kawice katafi idan mugunta kazo yi nagayamaka kukuma ku dagani" Da sauri suka dagata shikuma yazo gefenta yazauna kusa da ita yay folding hannu yace "Hajiya jikanki batada kunya ita batasan yayanta yazo tagaidani ba wlh idan tace zata biyema marasa kunyan yaran nan nida ita bazamu shirya ba" yay maganan yana hararan Du'a, sosai Du'a ke murmushi ganin yanda Sharif keda ban dariya, ahankali cikin yar muryanta tace "Ya Sharif ina yini" hararanta yayi yace "lpy lau" Mariya dake gefenta tace "Ya Sharif kaga harda ita zamuje shopping din gobe tunda Ya Asad yabamu namu kai kabata nata ai itama kanwarka ne yanzu" dasauri Hajiya tace "ohh ni yasu Mari ke Mariya yaushe kika dawo scammer eh, Sharif yaran nan damfaran ka zasuyi ba yanzun nan nabama Du'a nata 200k dinba" dan sosakai Sharif yayi yace "Hajiya ni bansan ko yaran nan basuso nai aure bane, kudin aure fa nake tarawa" saikuma ya kalli Du'a yace "nasan sun riga sunce miki banda kirki I will prove them wrong, kinga ban shigo da kudi ba, but zanbama Mari gobe tabaki okay" gyadamai kai tayi tana kallonshi irin kaman bata yarda ba dinan dan ita Grandma tariga tabata kudin ta, kaman Hajiya ta lurada hakan ne yasa tace "baki cema Yayanki kingode ba" murmushi tayi ahankali tace "nagode Ya Sharif" nan fa dakin ya kachame da hira, shi Sharif baida girman kai yana shiga kannenshi yayi hira dasu sosai iyayensu dasuka rasu yasa yafara haka dan he is all dasuke dashi couple with the fact Asad baida wasa, saisa yake hira dasu yasasu dariya yasasu bakin ciki komi ba, daga karshema zamewa Du'a tayi tai bacci shoulder ta nakan jikin Rahima, sai wuraren 11 Sharif ya tarkatasu sukama Hajiya sallama suka tafi kaman karsu tafi, itakuma ta tada Du'a tawuce taje ta kwanta.
Flat dinsu ya shiga yana maida kofa yarufe sanan yashigo ciki Asad yagani zaune afalo yana kallon wani horror movie a smart TV dake falonsu, tsaki Sharif yayi danya tsani horror movie zama yayi yace "kafara kallon film din aljannun nan naka ko" dagamai gira daya Asad yayi sanan yadauki drawing book din da Ammi tabashi ya jefama Sharif din, dasauri ya chapke yace "what is this" yay maganan yana budewa, ganin wasu hadaddun zanen takalma yasa yamike tsaye yacigaba da kallon su one by one. "woooooo Asad who drew this??? Wow Wow, waye yay zanen nan eh, we need this talent a company mu wlh, who drew this Asad" dan batarai yayi yace "Ammi takawomin wai I should hire wacce tai zanen a company mu" dasauri Sharif yace "of course Asad you should hire this talent karfi all those competing companies su gano mai zanen su rigaka hiring nashi, but waye mai zanen a ina Ammi tasamo maka" tabe baki yayi yace "tace wai jikan Ammi ce mai zanen, she's a small girl 21, kuma karatun ta a JSS2 ta tsaya due to some reasons best known to them, how can someone dabaida qualification zaimin aiki eh" dasauri Sharif yace "in this case don't look at qualification look at the talent, Asad ko bature illustrator dinka baitaba zana takalma masu kalan kyau dinan ba, this is masterpiece wlh, mukai takalman nan trust me all celebrities across the globe will be rocking ur brand, yarinyar nan tun wuri without second thought kadauketa" yatsine fuska yayi yace "Ammi tariga tasa nadauketa gobe zata fara aiki" dasauri Sharif yace "gobe" dan yasan gobe zasuje shopping, gyadamai kai Asad yayi yace "yes, inaso you should handle everything, interview her kasata a office na illustrator din let her get to work, guide her, before nagama this TV program in yaso once am back sai afara work on production" gyadamai kai Sharif yayi yace "okay Asad, bari naje na kwanta, kaine night owl" yay maganan yana stairs yana murmushi da gangan yaki fadamai wacece jikan Ammi yanaso yaga reaction dinshi ranan dazaiga wacce yace to daga rijiya ce jikan Hajiya ita yabama aiki.
Wuraren 5:30 Hajiya tashigo dakinta, tadata tayi ahankali tabude idanunta tashi tayi ahankali tazauna Hajiya dake kallonta tace "guess what" bude idanunta tayi tarr tana kallon Hajiya, murmushi Hajiya tayi tace "kinsami aikin" wani irin murmushi tayi tawashe fararen hakoranta, Hajiya tace "amma ance yau zaki fara aiki, danhaka tashi kiyi salla kiyi wanka ki shirya yarinya na is now a working class young lady, my lucky jika" murmushi sosai tayi ahankali cikin muryan baccinta tace "Grandma shopping dinmu dasu Rahima fa" murmushi tayi tashafa gefen fuskanta tace "don't worry about that karfe 4 zaki tashi daga office idan kindawo sai kuje, yanzu tashi kije kiyi salla" gyadamata kai tayi ta tashi dasauri tai bayi alwala tayi tafito tai salla saida tai karatun Al Qur'ani tai addu'a Allah ya sanyama aikinta albarka sannan takoma bayi tayo wanka tafito mata shafa ta shirya cikin riga da skirt na atampa sanan tafito falo, tunda take saukowa Hajiya ke kallonta ganin yanda mahaukacin shape dinta yafito akayan yasa taji bata natsu ba, ko aikin ma data bari tayi sabida tasan Ammi da yaranta ne tasan yanda sukeda natsuwa kuma tasan zasu sa ido akan Du'a, saisa ta natsu da bata bartaba, sanan kuma tanason yarinyar takara girma tai wayau tasan ya rayuwa take outside home, kujeran dinning Hajiya taja mata hakan yasa ta zauna tace "grandma cikina namin wani iri idan natuna zani aiki" dan dariya Hajiya tayi tana zuba mata tea da Irish tace "kina feeling butterflies a ciki, it's normal, yanzu ci abinci karki latti fa, 8 ake zuwa aiki" dasauri tashiga cin bata wani ci sosai ba dan bata iyacin abinci sanan ta tashi, Hajiya tace "anya bazan sayo miki Vitamin B complex ba kuwa Du'a baki iyacin abinci, oya tashi muje sama kiga" tashi tayi sukai sama, dakinta suka shiga Hajiya tabude wardrobe dinta, wani sabon abaya taciro mata black mai mahaukacin kyau ta ijiye kan gado tace "inaso ki zama very wise girl, kinga kalan jikin da Allah yabaki dan haka bazaki dinga saka atampa haka kina zuwa aiki ba, zan karo miki hadaddun abaya masu kyau su zaki dinga sawa kina zuwa office okay, inaso idan kikaje ki natsu ba ruwanki da gulma ko surutun office respect ur senior idan kikai laifi aka miki fada take ur correction, karkiga sabida kinga Sharif ko Asad sabida kin sansu suna kaman matsayin yarana ne kidinga musu magana anyhow ko rashin kunya no, a office is strictly work and formal communication okay, ki natsu kafin ki zauna akan kujeran aikin ki da za'a baki kiyi addu'a, kullum idan kika shiga office dinki kafin kifara aiki kiyi addu'a hakan zaisa kidinga samin cigaba Allah na Buda miki, ki zama mace mai kamunkai, abinda yasa nama barki kiyi aiki sabida inaso ki sami experience ne kisan menene rayuwa dan bakisan komi kan rayuwa ba Du'a, be very smart okay, karki damu yau zan sau miki wata" gyadama Hajiya kai tayi tace "thank u Grandma" ajiye mata kayan tayi tace "oya shirya nima bari naje na shirya zan shiga office yau saina saukeki a company ku" wucewa tayi tafice, shiryawa tayi cikin doguwan rigan ita kanta saida ta kallo kanta saboda yanda tai wani kalan kyau, parking kalabanta tayi sanan tazauna kan kujeran tadau gyalen abayan tana kokarin rolling bata iyaba aka turo dakin aka shigo, Hajiya ce ta shirya cikin ubansun gown din lace rikeda waya tamikama Du'a tace "ga Mamin Ki" karba tayi takai kunnenta ahankali tace "ina kwana Mami" ajiyan zuciya taji Mamin ta tasauke tace "Du'a ya kike" murya chan kasa tace "lpy lau" murmushi Mami tayi tace "ance kinsami aiki Allah ya sanya alheri ki kulada kanki kinji" murya chan kasa tace "to" "OK bye" bye tace Mami ta katse wayan karban wayan Hajiya tayi tace "bani gyalen kiga namiki rolling" rolling Hajiya tamata tsaf, saita juya tana kallon gaban mirror hannu tasa tadauko wani pink janbaki da kwallin saka mata kwallin tayi sanan ta shafa mata Jan bakin kadan daya saje da lips dinta, kafin tadau turaruka ta fesa mata sanan tadauko wata jaka tace "idan mace zata fita most especially office haka makesure kinada pad kwata daya aciki incase of period yazo miki, sai wipes, sai lip balm, sai dan karamin turare haka dayar hoda ko madubi, pen da dankaramin jotter haka" tai maganan tana daukan komi tana samata ajakan sanan tabata jakan, karba tayi tana murmushi Hajiya tawuce tafita tace "sa takalmi ki sako" takalmi tasaka sanan tajuya takalli kanta a mirror wlh kaganta bazaka iya tantanceta da balarabiyaba tai wani irin kyau akayan, hakanan saitaga tama kanta girma tadawo wata babba kaman yar mai kudi jin Grandma ta kwalama ta kira yasa tajuya da gudu tafice.
don magana dani M Shakur chat me up by clicking on this link wa.me/+2347012181461
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
Free page
EPISODE 2️⃣0️⃣
Razika da Shemau tagani a falo tsaye duk suna kallonta suna murmushi sabida tsabagen yanda tai kyau, sake washe musu baki tayi tace "natafi office" kwashe wa sa dariya sukayi sukace "adawo lpy Du'a, Allah yabada sa'a" Ameen ta amsa sanan tawuce tafita waje tana musu bye, tsakar gida tayi tana tafiya ahankali ita kanta Hajiya tsayawa tayi tana kallon Du'a to some extend bata wani cika blaming Kaka ba data dage cewa Du'a ba jikan ta bane dan wlh Du'a bata da banbanci da balarabiya ga kyau ga diri ance mutum tara yake baicika goma ba Du'a tamafi ashirin, fararen kafafunta Hajiya tabi da kallo dake kara haske bakin abayan data saka karasowa wajen tayi tace "muje grandma" murmushi tamata ta rungumo kafadan ta tace "kinyi kyau jikalle, yau kukaje shopping ki zabo takalma masu kyau da hills ba chan chan ba kinji, good shoes takes a woman to good places, takalman Du'a dina should be epic kaman cendarella koba hakaba" "hakane Grandma" tai maganan tana shiga mad jeep din Grandma, Grandma ma tashiga driver ta yajasu, hira Hajiya keta mata ganin she's a bit nervous daurewa kawai take wayaga sabon shiga, cikin wani ubansu glass building taga sun shiga mai tsawo wanda daga gani kasan akwai elevator dan sabida yanayin tsayinshi sunan company EPIC & COs LTD, parking direban Grandma yayi takalleta ganin yanda take kalle kalle tace "this is company dazaki dinga aiki aciki wuce kitafi" kallon Hajiya tayi idanunta sukai zuru zuru kaman zatai kuka tace "Grandma mezance" dariyan da Grandmaa keji ta hadiye tace "just go this is beginning of new phase, anriga an baki aikin so amsan da zuwanki idan kikaje akwai receptionist awajen ki gayamata sunanki she will tell u what to do, come here" Hajiya tama goshinta peck tace "Allah bada sa'a don't forget abubuwan dana fadamiki" gyadamata kai tayi gabanta nafaduwa sanan tabude kofan ta fita, direban grandma yajata suka wuce suka tafi suka barta tsaye awajen, haduwan ginin kadai yasa taji she's having change of mind ita daketa murna zatai aiki ita ko kadan batai picturing something like this ba irin wanan big organization dinne Ammi zata saman mata aiki ba, takai kusan 5min tsaye awajen sanan ta dage tafara tafiya towards the entrance door da kofan yay kala da kofan bank, taga yanda mutanen dake wucewa ke shiga hakan yasa itama taje, security dake wajen ne dake bada hand sanitizer ne yabita da kallo sanan yace "ur hand Miss" muka hannunta tayi aka zuba mata ta shafa yace "u can go in" shiga kofan tayi nan kawai taga glass yarufe ta ihu tayi tashiga buga glass din. "wayyooo Allah na innailaihi Grandm......" bata karasa kiranta ba taga kofan ya budu ga mutane dayawa awajen kowa na harkan gabanshi bama a lurada ita ba yasa tashare hawayen daya zubomata da sauri tashiga tana kalle kalle still ganin desk da counter da aka rubuta reception yasa tai wajen, wata hadaddiyar chic ce awajen kafinma Du'a ta isa wajen yarinyar ke kallon Du'a kaman zata hadiyeta tace "how can I help u Miss" ahankali Du'a tace "my name is Du'a Muhammad" dasauri receptionist din tace "the new illustrator, please come with me Miss Du'a" Receptionist din ta tashi tai hanyar elevator Du'a biyeda ita suka shiga, 4th floor ta danna da elevator yafara tafiya runtse ido tayi danji tayi hanjinta na neman fitowa, wani complete new section tagansu aciki saiga wata secretary dake zaune gaban system ga kujeru zaman mutane awajen, nunama Du'a kujera tayi tace "have a sir Miss Du'a" sanan takalli secretary dake kallon Du'a tace "she's the new illustrator, u take it from here" gyadamata kai tayi tawuce itakuma Du'a ta zauna tana kallon office din dake gabanta dakenan arufe jikin kofan anrubuta M.D Mr Sharif Alameen Kitse, takai kusan 1hr azaune awajen sanan aka bude kofan wasu manyan baki dake sanye da suit turawa suka fito tareda Sharif dake sanye da suit yayi wani irin kyau, binta yayi da kallo sai baice komiba yawuce yataka bakin har zuwa wajen elevator sanan suka shiga yadawo ya tsaya gaban secretary din cikeda fushi yace "tun yaushe Miss Du'a ke zaune anan Miss Amal"? dasauri matan tace "about an hour ago" "and u couldn't take her to her office" yafadi ranshi abace, tashi Miss Amal tayi tace "sorry sir I thought zaka fara ganinta ne tukunna saisa na bartaka sallami baki tukunna" cikeda takai takaici yawuce gaban Du'a yace "I apologize for that Miss Du'a, shall we" tashi tayi tana gyadamai kai yabude office dinshi yashiga tana biyeda shi sai kallon office din take yanda office din yahadu kujera yanuna mata ta zauna sanan shima yawuce ya zauna yakalleta da murmushi a fuskanshi yace "you want coffee kona kaiki cafeteria kici abinci"? Gizgizamai kai tayi ahankali cikin muryan nan nata mai bala'in dadi tace "I had breakfast thank you" cikeda gamsuwa yana kallonta yace "it's fine, anyway welcome to EPIC & COs LTD, company ne that is into creating and inventing all kind of shoes dakika sani da different materials, starting from animal skins har zuwa leather shoes, munada lots of investors da abubuwa da yawa which I believe since kina nan yanzu u will understand everything, Today is all about introduction babu abinda zakiyi gobe ne zaki fara aiki officially, that aside. My name is Sharif Al Ameen Kitse, nine MD wato managing director of this company, sorry bazaki sami daman ganin CEO dinmu ba dan he's officially on leave sai next week zai dawo, I will give u a tour around the company har zuwa warehouse dinmu dake kasa inda ake hada takalman da ire irenki ke zana mana, zan kaiki HR department zaki miki small abu za'a dauki hotonshi da some biometric dan za'a miki ID card na aiki, we have mosque we have church, rest room cafeteria duk acikin nan, and if u are having any difficulty with anything feel free to give me a call okay I'm ur brother banda haka Hajiya tace nakulan mata da jikan ta inba hakaba saitaci kaniyana" yay maganan cikeda wasa yana kallonta dan murmushi tayi itama dan sosai yanada kirki, ahankali yace "are you ready for ur tour ko kina bukatan wani abu, water juice ko cingum ko sweet kinsan mata da kwadayi remember I have sister nasanku, nabaki sweet"? yay maganan yana jawo wata yar locker shi yanuna mata, uban sweet ne na chocolate da sauransu aciki yana kallonta, kasa cemishi a'a tayi ahankali yasa ahankali tace "eh" ciko chocolate da sweet yayi a hannunshi yamika mata hannu tasa takarba ahankali tace "thank you" jakanta tabude ta zuba sanan tadauki daya tabude tasa abaki, murmushi yamata yace "let's go" gyadamai kai tayi tabishi suka fito tana biyedashi suka shiga elevator, ya danna 5th floor yace "let's start with 5th floor nanne floor na Oganmu duka, CEO anan kuma office din illustrator company yake dan haka anan office dinki yake" jin shiru yasa yajuyo yakalleta gani yayi ta kankame idanunta lips dinta na motsi, dan murmushi yayi yace "scared of elevator"? Gyadamai kai tayi ahankali daidai kofan nabudewa yafice ahankali tafito itama idanunta har sunyi ja sabida tsoro, tazaci 4th floor nada kyau dasukazo fifth floor dinnan saitaga wane 4th, ga mutane sai aikinsu suke sai gaida Sharif ake ana bin Du'a da kallo dashi kanshi Sharif saida ya lura, gaban wani office yaje dake kusada CEO dan tazaran ba yawa taga an rubuta illustration, bude kofan yay ya shiga yajuyo ya kalleta yace "come in" shigowa tayi tana bin office din dakallo table ne hadadden gaske da laptop ke kai ga kujera dake juyawa, ga dogon couch, sai frames a bango na zanen takalma masu kyau, sa shelf dawasu irin hadadden drawing book dabata taba ganinsu arayuwanta ba suke ganin su take kallo yasa, Sharif yadauko daya yace "anan zaki dinga zanen it's digital drawing book, kome kike zanawa is connection to this MacBook" yanuna mata laptop din dake kan kujeranta, yace "we can't wait for xanenki, you can keep ur bag dan nanne official office dinki" gyadamai kai tayi ahankali ta ijiye jakanta kan table sanan yakalleta yace "mucigaba kokin gaji" murmushi tamai ahankali tace "mucigaba" fita yayi tabishi wanan karan saitaga baibida ita elevator ba sun dauki stairs hakan bakaramin dadi yamata ba harsaida ya lura dansai murmushi takemai, suka tafi kowani floor yana nuna mata komi, sukaje Cafeteria company babban gaske all employees dinsu are entitle to lunch kaje za'a baka free lunch, dasafe kuma kowa is entitle to either coffee ko lip tea saisa kowa nan yake fara tsayawa dasafe ya karbi tea sanan kowa yawuce office, yakaita mosque incase tanaso tazo tai salla, yakaita warehouse, yakaita HR yana tsaye akai taking biometrics dinta aka mata passports saida tagama komi sanan suka taho abin har mamaki yadinga basu wanan tour din dayake bata ba aikinshi bane, sake komar da ita Cafeteria yayi yakalleta yace "tea or coffee"? murmushi tayi kaman mai tsoro tace "tea" sawa yayi aka hada tea a coffee aka kawo musu a disposable cup mai marfi yabata nata yana rikeda nah I yace "muje" sakebin bene yayi da ita suka tafi har 5th floor, office dinta yakaita yace "now sit round relax do anything dakikeso, if u want anything just dial my number awanan landline Din" yanuna mata telephone din wajen yace "dial 444 zaiyi connecting naki to me" gyadamai kai tayi, waving mata hannu yayi yace "bye" ahankali tace "bye" harya wuce saikuma yaleko yace "drink our tea kiji da dadi kafin yahuce" gyadamai kai tasake yi tana murmushi, wucewa yayi yatafi abinshi, zama tayi kan kujeran ta da tuntuni yake shigan mata idanu tahau wasa akai tana juye juye saikuma tamika hannu tadauki cup din tashiga shan tea aiko dadi hakan yasa tacigaba dasha tana murmushi ita kadai.
wa.me/+2347012181461
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
free page
EPISODE 2️⃣1️⃣
Sosai takebin office din da kallo kaman wacce bata taba ganin office ba arayuwanta, ga katoton TV dake makale a bangon office din, gawani camera Ata sama amakalle shima dabata san koname ba, ahaka tana zaune ita kadai har lokacin azahar tayi, knocking office dinta akayi saikuma aka budo kofan, Sharif ne murmushi lullube kan fuskanshi yana kallonta batare daya shigo cikin office dinba, dan murmushi tasakinmai itama dan wani irin kunyanshi takeji ganin yanada kirki sosai, ahankali yace "is time for zuhur u wanna join me?" Gyadamai kai tayi da sauri dan tuntuni takejin fitsari dama amman kunyan tafita ita kadai takeji taje, tashi tayi ahankali tafito duk yana kallon ta sanan taja kofan office din suka wuce tare har mosque yanuna mata side din mata ta tafi, wucewa tayi bayinsu sai kallonta matan dake wajen suke itadai babu wanda take cema uppan besides ma kanta akasa dan kunyan yanda suke kallonta takeji, fitsari tayi tayo alwala sanan tashigo masallacin ganin cupboard dake cike da hijabai yasa tadauki hijabi tasaka tai salla abinta, tana idarwa ta zauna tana kokarin rolling gyalenta babu yanda batayiba takasa hakan yasa takama gyalen ta wajen wuyanta gamgam tamike tafito, jigine da bango masallacin taga Sharif yay folding hannunshi akirji da alamu ita yake jira, ganinta yasa ya yunkura yataho inda take yana kallonta yace "maiya sami gyalen"? Ahankali tace "ban iya yanda Grandma tamini ba" Dan murmushi yayi yace "then u have to learn dagayau, let's go have lunch" yay maganan yana hawa stairs yay hanyar canteen dinsu tana biyeda shi, shiga sukayi ga few employees dinsu dake wajen suna cin abinci cikeda girmamawa suka shiga gaidashi amsasu yayi batare daya kallesu ba sanan yaja kujera yanuna mata alamun ta zauna zama tayi ahankali tana kallonshi ganin yanda yake wani kulada ita kaman yar kanwarshi, shima zama yayi yakalli yarinyar datazo cikeda girmamawa tace "mezan kawo muku sir" batare daya kalleta ba yace "I want pasta da salad, mezakici Du'a" yay maganan ahankali yana kallonta, kallon yarinyar tayi sanan tace "jallof rice" juyawa yarinyar tayi ta tafi itakuma tasauke kanta kasa tana wasa da yatsunta Sharif sai kallonta yake kaman yamata magana saikuma yay shiru shima ahaka har aka kawo musu abincin, cin abincin shi yafara hakan yasa yace "bazaki ci ba" Dan dagokai tayi ta kalleshi ahankali tadau spoon tafara cin abincin, bini bini yake satan kallonta, ta bala'in yima kyau, komi nata daban ne, harya gamacin abincin shi batai rabin nata ba hakan yasa yacigaba da jiranta, kadan takara akai ta ture hakan yasa yace "u okay" gyadamai kai tayi tasha ruwa sanan ta tashi alamun su tafi tafiya sukayi har office yasake rakata sanan yawuce nashi office din, wuraren 4 tana zaune a office dinta telephone din wajen yahau kara dasauri ta dauka, muryan wani security taji.
"Miss Du'a your driver is here to pick u up" dawani irin sauri ta tashi tana hada yan tarkacenta ajaka ta kosa ta ganta agida sanan tafito tana tafiya ahankali tasauka kasa zatai hanyar kofa taji magana a bayanta. "so you're living without saying goodbye" dawani irin sauri tajuyo ganin Sharif ne yana rikeda waya a kunnenshi da alamun ma waya yake but still saida yamata magana yasa adan kunyace tamai waving hannunta tace "bye" gyadamata kai yayi yacigaba da magana. "yes I can hear u Asad" waje tafita ta shiga motan Grandma dinta driver yatafi da ita, Allah Allah take takai gida, suna kaiwa gida tafito daga motan dasauri harda dan gudun ta tai falonsu tana budewa taga su Rahima Mariya da Aneesa duk sunci gayu sosai suna zaune afalon Hajiya atare sukace. "surprise" suka tashi suna rungumeta, wani irin murmushi tayi ta kallesu tace "yaushe kukazo sorry" dasauri Aneesa tace "bakomi Hajiya da Ammi daman sun gayamana kinji aiki, jekiyi wanka kizo kici abinci mutafi" gyadama musu kai tayi takalli Grandma dinta dake zaune tana kallonsu tana murmushi, wajenta taje ahankali tace "Grandma ina yini" fuskanta tashafa tace "Du'a dina sannu da zuwa, yi sauri kije ki shirya kunga tuntuni su Aneesa ke jiranki" wucewa sama tayi da saurinta dakinta ta shiga, wanka tayo tafito, tunawa da abinda Grandma tafadi mata yasa tasake dauko wata gown wanan is simple dan ba designers bane irin na dazu data sakaba milk color, saka shi tayi sanan tadauki mayafinshi ta feffesa turare tafito kasa, duk juyowa sukayi suna kallonta Aneesa tace "mena rike dankwali a hannu kiyafa mana" karasowa falon tayi tace "ban iya bane grandma zatamin" tabama grandma dan kwalin, dasauri Mari tace "Hajiya bari mu mata sabida ta iya" tana maganan ta karbi veil din daga hannun Hajiya sanan ta wani irin yafama Du'a akai gaban kanta daya cika da kwantaccen gashi yawani fito, Rahima tace "wow wlh kinyi kyau Du'a mutafi to, Aneesa ina kudinta da Ya Sharif yace mubata" dasauri Aneesa tashiga bude handbag dinta wani kudi taciro a envelope sanan tamikama Du'a din tace "ga kudinki, tundazu dasafe kafin yatafi office yabamu mubaki" dasauri Du'a takalli Hajiya danharga Allah batasan mezatayi ba, murmushi Hajiya tayi tace "karba Allah ne ya ciyar dake kafin aci kudin Sharif saidai idan Allah ya tsaga da rabonki ne" kwashewa da dariya yaran dukansu sukayi sukace "wlh kuwa Hajiya Ya Sharif kare bayacin kashinshi, karba muje" Ahankali tasa hannu takarba tace "thank u" sanan tasa ajaka, sallama sukama Hajiya sukai tafi direba ya kwashe su, sosai sukema Du'a hira a mota ita abin mamaki yake bata yanda suke sonta daga ganinta jiya dan har labarin samarin su suke bata, Aneesa data zauna agaban mota ne tajuyo ta leko takalli Du'a tace "ke baki bamu labarin saurayinki ba" Dan zaro idanu tayi tanuna kanta tace "ni"? dasauri Mariya dake gefenta tadan bugi kafadanta tace "common on don't be shy, tell us about the lucky guy" dan murmushi tayi saikuma tadauke kai dan tambayan tabata kunya ahankali tace "ni banda saurayi ko daya wlh" wani irin bude baki sukayi suna kallonta sabida mamaki, Rahima dake gefen Mariya tace "Du'a wasa kike ko" girgixa kai tayi tace "wlh ba wasa nake ba" shiru duk sukayi yanda yarinyar nan keda kyau ace bata da saurayi basu wani karyata ta sosai ba sabida sunga ko wayama batada shi, share maganan sukayi suka shiga wata hiran har sukakai mango dazasu, nan Du'a taga yanda ake shopping ita bama tasan mezata dauka ba hakan yasa kome suka dauka itama saisun daukan mata anata cart din, tundaga kan Bra da tuni suka gwadata suka shiga zakulo mata sizes dinta zuwa pants, pads kayan makeup, duk suna tura cart dinsu kowa na diban abinda akeso TV super market din dake makale asama na aiki Channels television news inda ake program REINVENTING THE NIGERIAN YOUTH....
Suna tsaye bangaren English wears Rahima ta amshi tape tana kokarin ana waist din Du'a dan asan size din jeans dinta itama ta dauka kaman daga sama wani kyakkyawan eloquent voice yadaki dodon kunnuwan Du'a da hakanan taji kaman tasan muryan, dawani irin sauri tadaga kanta sama takalli TV, chak ta tsaya ko motsi kirki tasaka, idanunta ne suka sauka kan fuskan da kusan kullum saitaga fuskan, wanda yacetota daga rijiya, yana sanye cikin wasu classic suit dark blue, ga necktie awuyanshi, yana zaune kan wata hadaddiyar kujera yayi crossing legs dinshi in a stylish way, yadaura hannunshi biyu kan cinyanshi wrist dinshi na daure da agogon Rolex, idanunshi fari kalll wanan karan babu bakin glasses akan su, lips dinshi sunyi wani masifaffen pink kaman ya shafa janbaki pin akai, gashin kanshi dake da yawa sunyi wani kalan extraordinary coils, yana magana da english da accent dinshi na bristish, kaman acikin mafarki taji ana Du'a, Du'a, Du'a, tabatan da akayi yasa tai firgigit tafarka ta kallesu da sauri dan sai alokacin ma tasan ashe tayi nizan tunani ne, neck dinta Rahima takai hannunta ta taba tace "baki da lafiya ne? Tunanin me kike haka kin tsare TV da ido eh harmun gama siyan kaya" binsu tayida kallo ganin yanda suke kallonta kaman sun damu yasa takakalo murmushi tace "tunanin abubuwan dazan saya fa nake" murmushi dukansu suka mata, Rahima tace "mungama da wanan shop din next stop is abaya store, mutafi mubiya mufice yamma nayi" gyadamusu kai tayi tabisu zuwa wajen cashier tana kara waigowa tana satan kallon TV da Asad har lokacin ke magana, kowa kudinshi yabiya sanan aka musu parking kayan a leda sanan suka wuce suka fita still saida takara waigowa takalli TV, sanan suka fice, ranan basu suka dawo gida ba sai 8 nadare kasa bude kayan tayi salla ta lallaba tayi sai bacci tashinta grandma tayi saida ta tasa ta agaba taci abinci sanan tabarta takara komawa bacci da tagaji bata saba fita ko wahala hakaba, all abinda tasani is wanka kwanciya da cin abinci shikenan saisa tai bacci awahale.
0 comments:
Post a Comment