Yau tana shiga batai kauyencin datayi jiya awajen kofa ba, glass din na budewa ta shiga ciki, mutane sai kallonta suke maza da mata, saukar da kanta kasa tayi tana tafiya ahankali kafafunta na neman hardewa sabida yanda ake kallonta, dukfa sun tsayar da aikin dasuke kallonta ake, this is the first time data shiga waje kowa ya tsayarda abinda yakeyi yana kallonta, wani irin rawa jikinta yafara kafanta na hardewa daidai tazo stairs tahau kafanta yaturgude baya tayi zata fadi, jitayi antareta ta baya an daura hannaye biyu akan kafadunta murya chan kasa taji ance. "careful" dawani irin sauri tajuyo ta kalleshi, Sharif ne yana sanye cikin suit black yay wani irin kyau, hannayenshi dakekan shoulder dinta ya kalla sanan yajanye su ahankali murya chan kasa yace "sorry about that" sanan yajuya daga inda yake yakalli ma'aikatan su da ganinshi yasa kowa yafara aikin gabanshi kaman da gaske dan kwafa yayi sanan yajuya yakalleta yace "let's go kinada aiki yau" yay maganan yana gaba ahankali tabiyoshi abaya, Cafeteria dinsu yaje yakarbi cup biyu yajuyo na tea yabata sanan yarike na coffee sukai stairs yana tafiya yace "omg, at this points knees dina sun kusan cirewa kuma duk kece Du'a, mezan fadama future wife dina idan suka cire" dan murmushi kadan tayi tana binshi abaya batare datace komiba hakan yasa yajuyo yakalleta, boye murmushin tayi dan zaro idanu yayi cikeda wasa yace "did u just smile knees dina na aching" ahankali tace "sorry" juyawa yayi yacigaba da tafiya yace "zan gayama future wife dina it's one gurl called Du'a tasani nake bin stairs zuwa 5th floor fa sabida tana tsoron elevator" murmushi tasakeyi batace komiba har sukakai office dinta, shiga sukayi ta ijiye komi kan table ta tsaya agefe, juyowa yayi ya kalleta yace "me kikeyi abayana sit akan kujeran ki nabaki aikin ki natafi" gyadamai kai tayi tazo ta gabanshi tawuce tazauna kan kujeranta ahankali kaman mai tsoro, wani karamin mini pad yamika mata yace "the CEO sent this, yanaso kiyi zanensu next week idan yashigo aikinsu za'a fara, 5 design na hills, 5 na loafers, 5 different design na croc and unhooked sandals" ganin yanda take kallon pad din yasa yace "it's a whole lot of work ko, don't worry take ur time zaki iya kadan yau kiyi sauran gobe" gyadamai kai tayi ahankali hakan yasa yajuya yace "in that case bari natafi" haryakai kofa ta dago kanta ahankali tace "ummmm" juyowa yayida sauri yakalleta yace "da wani abu ne"? gizgiza mai kai tayi tace "thank you, su Rahima gave me the money, Allah amfana Ya Sharif" tunda take maganan harta gama yake kallonta, dauke kai yayi yace "you are welcome" sanan yawuce yafita daga office din.
Ranan haka tawuce zane take a E-board dinan, bakaramin burgeshi zanenta Sharif sukayi ba, kafin 4 tagama gabaki daya ma dan she's so fast da zanen tawuce ta tafi direba yadauketa.
Tana shiga gida tafito tawuce ciki, Razika da Shemau tagani zaune a falo suna kallo TV tabi da kallo ganin film suke kallo yasa tace "ina Grandma" Razika dake kallonta tace "tana sama kaman ta kwanta bata dade da shigowa ba" sama tayi ahankali tabude kofan dakin Hajiya ganinta kan gado tana bacci yasa tawuce dakinta, kaya tacire tawuce bathroom wanka tayo tafito daure da towel tayi gaban wardrobe wani simple short gown tadauka tasaka, jin anyi knocking kofar ta yasa tace "shigo" shigowa Razika tayi dauke da tray na abinci tace "abinci nahado miki nasan kin gaji" wani irin murmushi tayi Razika nada kirki karban tray tayi tace "nagode Razika" gyadamata kai tayi tawuce tafita zama tayi kan gadon ahankali rikeda tray din tana kallon sinasir dake cikin plate, ga lafiyayyen miyan taushe dayaji naman kan Rago, dago kanta tayi sai kawai tacire tray kan jikinta ta ijiye agefe tamike tsaye da sauri switch din TV ta kunna tadau remote takoma kan gado ta zauna, gama booting yayi hakan yasa ta kunna tashar Channels Television News, daidai an nuno wani daga cikin audience ya daga hannu, hoster tace "go ahead" mikewa tsaye yace "My name is Samuel Madina Chris, My question to Mr Asad Abdullahi Kitse is you see we all know you come from a wealthy home/family, so setting up a business starting a company can not be a problem for you cus ur family are buoyant enough to support you with startup capital, mu yanzu that come from not so financially strong family how can we source for start up capital dan bamu da yan uwan dazasu taimaka mana"?
Nuno Asad akayi, yau yanacikin wani hadadden suit ash color dark ash da yamai bala'in kyau, yay crossing leg as usual, looking so elegant and classic, gashin kanshi sun kanannade suna wani irin kyalli, lips dinshi sunyi pink yirrrr....... Ahankali Du'a tawani irin sauke ijiyan zuciya idanunta kur akan TV akanshi gabanta nafaduwa dum dum dum.......
Gyara zamanshi yayi yay adjusting mic din dake gabanshi wani dan karamin cute smile yasaki dako hakoranshi basu bayyana ba cikin husky melodious voice dinshi yace "I appreciate this question Mr Samuel you know why" yadanyi shiru kafin yadan ciki lebe kadan yace "sabida mutane dayawa nada wanan misconception din, suna tunanin all mutanen dasuke business are from wealthy homes, lemme tell you all something, mahaifina nada companies, yanada kudi, but kunsan 1naira na mahaifina kona family na banyi amfani dashi a business dina ba, I strive for my business with my hard earn money" wani irin tafi hall din yadauka hakan yasa yay shiru yana jiran sugama yace "akwai lots of organizations that ayanzu the youth can reach out to dan su sami kudi and establish business dinsu ko expanding business dinsu, CBN, SMEDAN, BOI, and so much more, listen business is not for the lazy ones dayay depending on his families, and is not for the ones that doesn't have the zeal to strive hard and hard and hard to achieve his goals, business is for people that doesn't believe in impossible, don't tell ur self is impossible to establish a business because my parents are poor I don't have any source of income..." wani irin tafi aka fara a hall din kowa na having goosebumps sabida yanda yake maganan yana penetrating a zukatan audience din, saida sukai dan shiru sanan yace "business na mutane ne that believe in their self, people that have vision and are ambitious, people that are vasitile and strong hearted, we'll ladies and gentlemen I think we've reached the end of today's program saikuma gobe, thank you" wani irin tafi aka fara a hall din kowa yamike tsaye anamai tafi shikuma yawuce yana tafiyan nan kaman zaki looking damn elegant, classic and sexy yawuce yafita daga hall din, tashi itama Du'a tayi ahankali tama rasa mezatayi kawai saita koma ta kwanta kan gadon ahankali tana kallon TV da har anfara another program.
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️M SHAKUR
Free page
EPISODE 2️⃣3️⃣
Lumshe ido kawai tayi looking so somehow da bazaka tabace ga asalin yanayin datake ciki ba, ahaka bacci yay awon gaba da ita saida Hajiya tashigo ne ta tadata taje tai salla sanan ta sata agaba aka kawo mata wani abincin aka tafi danada dan bataci ba sanan tabarta ta kwanta dan akwai baccin sosai a idanunta.
******
Ahaka tai good five days a company from Monday to Friday Sharif has always been there for her, yanada kirki mara misultuwa, he's very nice and generous kaman ba boss dinta ba at all, yamaida ta kaman wata sister dinshi hakan yasa itama tadaukeshi kaman wanta Ya Hamad, itadasu Rahima kuma kaman sunsan juna tuni suka koya mata watsapp suka sakata group dinsu na yammata inda ake hiran samari da heart break ita saidai ta karanta taita mamaki, kullum 4 nayi take fitowa driver Hajiya ya dauketa tana dawowa gida zata gudu dakinta tasaka channels television news but kodaa yaushe ending din program din Asad take samu wani zubinma bata samin takalla kafin takai gida an gama barin ma ranakun da holdup yakamasu, har kasan ranta she wish zata iya ganinshi tace mai thank u for saving life dinta dan ko kadan takasa manta da fuskanshi da idanunshi dasune tagani da kyau danhar kasan zuciyanta takasa mantasu.
Yau Saturday su Rahima sunso sujata yawo Grandma tahanasu dan malamin ta zaizo, wuraren 10 malamin bayerabe yazo, Hijab tasaka har kasa tafito karatu yamata both na boko da islamiyya dan irin genius ustazan malaman nanne, karfe one suka gama yatafi, dakinta takoma ta kwanta yau kawai she's so happy koba komi tana gida zata kalli program dinan daga farko har karshe yau, salla ta tashi tayi jin ankira sanan takoma ta kwanta sai bacci, wuraren 3 Hajiya tashigo dakin tadata tayi. "ke Du'a oya tashi" bude ido tayi ahankali ganin Hajiya yasa ashagwabe ta daura kanta kan cinyarta murya chan kasa tace "Grandmaaa nagaji" smooth kumatunta Hajiya tashafa tai murmushi tace "oya tashi sonake ki shiga kitchen tareda su Razika kema kisoma iya girki, tuwon shinkafa zakuyi da miyan taushe sai farfesun kifi" ahankali tabude idanunta dahar sunyi dan ja sabida baccin datayi takalleta, tashi tayi zaune sanan tamike tsaye tace "grandma dakaina zanyi girkin ni kawai su nunamin yanda zan dinga yi" gyadamata kai Hajiya tayi tana murmushi tace "to gimbiya Du'a hakan za'ayi" wani kalan murmushi tayi cikeda murna tawuce tafita daga dakin dan tafi kowa so ta iya girki dan girki na burgeta, shiga kitchen sukayi aiko su Razika sun sha dariya dan targen tuwo bata iyaba haka suka dinga koyanata suna dariya gabaki daya ta manta da abinda takeso tayi, saida suka gama tuwon sanan ta kalli agogo dake manne abandon kitchen din, dawani irin gudu tafita daga dakin ta sama dakinta tashiga, TV kawai ta kunna dan decoder a kunne yake dama tana kan channels din, ganin angama program din yasa taji wani abu yatokare mata wuya, wata matace ta bayyana agaban TV tace "to jama'a ni karan kaina bakin cikin sanar daku nake cewa a yau ne wanan program din da gwamnatin Nigeria takawo muku sabida tallafawa Matasan kasa wanda wanan shahararen matashin nan dan kasuwan nan wato business Mr Asad Abdullahi Kitse ya gabatar muku yazo karshe, ku saurara kuji" matan tayi murmushi tace "channels television news tasami sakonni da dama kan shafukansu na sada zumunta da emails kan Mr Asad cewa mutane naso sugana dashi, toga wata sanarwa, gwamnatin Nigeria tashirya kyakkyawan liyafa wato dinner nagama wanan program din agobe karfe 4 na rana inda star dinku Mr Asad zai hallata, ana gayyatan marasa su fito duk kuzo dan Mr Asad zai sake bayarda jawabi wato speech awajen dazai taimakawa marasa wajen fara tasu sana'ar, za'ayi wanan taro ne ababban hall din transcop hotel, a huta lpy" daidai nan suka shiga talla kuma, zama tayi ahankali kan gado tai shiru, kwala mata kiran da akayi yasa ta tashi tafita daga dakin da sauri suka daura miya, suna gamawa ta debi nata tafito ta tafi dakin Grandma dinta dake waya hakan yasa tai zamanta tanacin tuwon. Gama wayan Hajiya tayi tace "iyye manyan mata anyi mana girki yau" washe baki tayi tace "grandma abincin nan dadi wlh sosai" hararanta Hajiya tayi tace "nidai tashi kikai plate dinan kitchen ki wuce kije kiyi wanka, haka akeso mace tadinga yi idan tagama aikace aikacen gida ko girki, wuce daganan sai kiyi salla" tashi tayi tadau kwanon tafito saida taje ta ijiye a kitchen sanan takoma dakin ta wanka tayi tanajin dan ciwo ciwon ciki kaman MP dinta zaizo, fitowa tayi ta tsaya gaban madubi ta kalli kanta tawani kara haske fatar jikinta na kyalli sabida man da Hajiya tasaimata mai bala'in kyau ne, tamadanyi kiba, wanan kumburin kukan da idanunta keyi a gidansu duk babu yanzu, gama shafa man tayi batabi takan kalaban kanta dake lilo ba dan batai parking nasu ba tawuce wardrobe dinta wani dogon riga tadauka na kanti mai kyau pitch color ne tasaka kawai ajiki batare datasaka bra ba sanan tasa hijabi tai salla, tana zaune kan dadduma tana biya karatun da aka mata aka kira isha'i tashi tayi tayi sanan tamike tsaye cire hijabin tayi ta ijiye kan kujera tadauki wayanta dake gaban madubi tawuce tafito, kasa ta sauka, ganin babu kowa a falo yasa tawuce dakin su Razika dake nan akasa, zaune suke su biyun suna assignment dinsu dan malamin su yabasu assignment, suna ganinta duk suna dagokai suna kallonta, murmushi tayi tace "kuma anbaku assignment" dukansu gyadamata kai sukayi, fadawa kan gadonsu tayi tace "to kugama bari nai chatting dasu Aneesa" saida suka gama sanan Razika tarufe book din ta ijiye tana kallon gashinta tace "yaushe zaki kwance kannan gashinan harya soma kwance kanshi sabida gashibki nada santsi" yatsine fuska tayi tace "ni bazan kara zuwa saloon dinan ba suncika kallon mutane wlh" dariya daga Razika har Shemau sukayi dan yanda tai maganan zaka dauka yarinyar ce harda dan turo baki She looks so cute, matsowa gaban gadon Shemau tayi tace "ai sabida kinada kyau ne saisa ake kallonki Du'a mu ana kallonmu ne Razika"? Girgizakai Razika tayi alamun a'a, yatsine fuska Du'a tayi tace "wlh ko bansan kyan nan, uhm, bari naje na kwanta" tai maganan tana tashi daga kan gadon tamike tsaye, hannunta tasa tadauki wayanta sanan ta musu murmushi ganin yanda suke kallonta tace "saida safe" "Allah tashemu lpy, Du'a gobe kezaki break" bude kofan tayi tajuyo cikeda murna tace "dagaske?" gyadamata kai Razika tayi tace " eh" fita tayi tana murna, Shemau ta kalli Razika tace "Razika daman haka takeda nono ni wlh nadauka breziya ce ke sa nononta yay girma a riga irin push up dinan sai yanzu naganta da ba breziya ajikinta" tashi Razika tayi tana gyara gadonta tace "haka takeda su harda bombom ma kaman ita tai kanta, wlh inason yarinyar sosai Shemau mugun burgeni take, dan she's so simple, batada wani ji da kanta sabida tanada kyau kaman yanda masu kyau keyi dinan kiga suna daddaukema mutane kai sabida sunga sunada kyau, Du'a ga kyau ga kamun kai ga natsuwa bakiga ko saurayi batada shi ba" Gyadamata kai Shemau tayi cikeda gamsuwa tace "hakane, Allah yabata miji kyakkyawa irinta, ni wlh daurewa kawai nake dabana tsareta da idanu dan wlh bangajiya da kallonta" murmushi Razika tayi tace "bacci nakeji".
Fitowa daga dakin Du'a tayi tana murmushi tana tattaba wayanta dan Aneesa ce kebata dariya tana kawomata karan Mariya waita sace mata zobenta, typing yakuri tayi sanan ta ijiye wayan kan dinning tawuce tana tafiyan nan ahankali takarasa gaban fridge din dake dinning din tabude dan kishi takeji sosai, wani karamin bottle water mai sanyi taciro tana kallon goran, maida kofan fridge din tayi tarufe kafin ahankali tashiga bude marfin goran sanan takafa ahankali abaki tawani lumshe ido tanasha.
"you know cold water is not good for the body" kaman daga sama taji murya kaman na Sharif akanta, dawani irin sauri tabude idanunta tareda juyowa, yana zaune kan dogon kujera shi kadai a falon yana sanye da 3quater na sojoji da farin t-shirt yana rike da system dake kan cinyanshi, dudda taga ba kallonta yakeba amman saida taji wani irin kunya dasauri ta ijiye ruwan sunnar da kanta kasa tayi amugun kunyace tace "Ya Sharif ina yini" batare daya kalleta ba still yana aikin dayakeyi ne yace "hope u good" gyadamai kai tayi ahankali tama rasa mezata ce tace "uhmm kaga Grandma dina? Tana sama bari nakira maka ita" tai maganan tana fitowa daga dinning tai stairs dasaurinta harda dan gudun ta, wani irin turgudewa tayi kafanta ya lankwashe dayasa tasaki wani irin wawan ihu. "wayyo Allah na kafata" tashi Sharif yayi daga kan kujera dasauri yawaigo daidai lokacin Grandma datagama wayan datakeyi tafito kenan taji ihun ta tazo stairs din dagudu tace "subhanallahi maiya faru? Muga kafan" Hajiya tafadi dasauri tana karban kafan da Du'a takasa ijiyewa kasa tsabagen azaba tana dan kuka mara sauti dan yamugun mata zafi, cikeda tausayinta Hajiya tace "sannu ijiye kafan nagani" gyadamata kai tayi tana kokarin ajiye kafan akasa wani irin ihu tayi saikuma tafashe da kuka sosai wanan karan mai kara tace "dazafi Grandma" cikin dan fushi Hajiya tace " kinsan wajen nan bene ne akan wani dalili zaki dinga gudu akai eh" cikin kuka sosai tana kokarin kama hannun Hajiya dake liliyamata kafan tace "zan kiraki ne naga Yaya Sharif yazo" cikin fada Hajiya tace "Sharif da tuntuni muke tare muna hiranmu har tuwo yaci, sama nazo nayi waya, koma bansan yazo ba gidan nan ba Bakin Sharif bane har sama zai iya zuwa wajena, Sharif zo dan Allah kadubamin kafarta kotasami targade ne, kosu Razika basu kadai ba duk wanda zaizo gidan nan hanashi gudu nake akan bene dan hatsari ne da bene yanzu jibi", karasowa wajen Sharif yayi dawani irin sauri takai hannunta ta share hawayen daya bata fuskanta, Hajiya data matsa gefe tace "au uban kukan dayagamaji kinayi dan yazo nanne zaki wani goge hawaye" turo baki tayi ta dauke kai, Hajiya tace "kaji Sharif dubamin kafan kagani" ahankali yakai yatsunshi biyu yadaura kan kafar datai ja sabida turgudewan yanabin dogayen feet dinta da kallo yace "does it hurt" yadan dagakai yana kallon fuskanta, hadiye zafin tayi tagirgiza mai kai alamun a'a hakan yasa Hajiya tace "kafan dakika gamawa kuka ne kike cewa baya zafi"? Murmushi yadanyi yace "buguwace kawai tashafa man zafi zai daina mata zafi" yay maganan yana sauka kasa abinshi, hararanta Hajiya tayi tace "wuce kije kishafa robb akai Allah kika karamin gudu agidan nan saina saba miki Du'a, kidena guje guje kinji" gyadamata kai tayi ashagwabe tace "tom" "wuce kitafi dakin ki, wani aiki Sharif ketayani yi" gyadamata kai tayi tawuce ta tafi tana tafiya ahankali Hajiya tabita da kallo saida taga tabude daki tashiga sanan tasauko tace "Allah kyauta" karasowa tayi tazauna kusada Sharif tace "wai shi gogan bazaizo yagaidani bane" dariya Sharif yayi yana abinda yakeyi yace "finally kinyi admitting kinyi kewan Asad" hannu tadaga kaman zata dakeshi ya kyalkyace da dariya yace "wlh aiki sosai ne aikin nan dayakeyi shi kanshi yagaji kinsan Asad ya tsani takura shida yasaba saidai yatakurama mutane shi baiso atakuramai Allah Allah yake gobe tayi yagama, da sassafe fa yake fita kullum" murmushi Hajiya tayi tace "Allah sarki Asad, kana ganinshi haka akwai kwazo da zuciya" murmushi Sharif yayi yace "nidai idan yazo kicemai wlh yafito da mata yay aure inba hakaba dudda ina kanninshi aure abuna ni zanyi na barshi" yay maganan yana batarai, wani irin baki Hajiya tasaki tana kallonshi tace "ohhh jama'a yauni naga takaina, kaiwai mara kunyan inane Sharif, yoo dan kaniyan kama duka duka da wata nawa ya girmeka wata uku ne fa tsakaninku haka Amminku tagayamini, Asad nada wata uku aduniya aka haifoka" dan dariya Sharif yayi yaturo baki cikeda rashin kunya yace "nidai gaskiya nafadi muku aiko Ammi nagayamata ni wlh aure nakeso kuma shi Asad banga alamun ya shirya aure ba Hajiya wlh yaron nan kaman aljani shi yama tsani mata, basa gabanshi the only matan dayakema murmushi yayi hira yay wasa dasu aduka fadin duniyan nan guda biyu ne daga ke sai Ammi, kinsan ko Anty Turai kanwar Abban mu bayama murmushi cewa ma yake he hates her, to ina zan tsaya jiran irin wanan saiyay aure zanyi ai namutu tuzuru hakanan Hajiya wlh a'a" wanan karan hannu Hajiya takai ta dakamai duka abaya dayasa yakusan sakin laptop din yace "aashhh" dauke laptop din tayi tace " naga alama kwana biyu ban jibgeka ba saisa bakada kunya, mugama aikin dakakemin Allah sa ba shirme kakeba dan naga hankalinka baikai" tai maganan tana saka glasses a idanunta tana kanne idanu danta karanta report din daya rubuta mata, karban system din yayi yace "ni dai tsaya na karanta miki natafi gida nai waya da budurwa ta kuma saina gayamata kece duk kika cinye mata time" dariya tayi tace "kagaya mata hala tamadan soka sabida yanda ba'acin kudinka at least ni Kakar ka ina moreka" dariya yayi sosai sanan ya shiga karantamata.....
wa.me/+2347012181461
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
Free Page
EPISODE 2️⃣4️⃣
yauma kaman kullum suka tashi suna breakfast malamin su yazo ta tafi wajen nata su Razika ma haka, as usual by 1 yatafi, daki takoma ta kunna TV tunani kala kala aranta, wanan sanarwan nan na iya tasake saurara rasa abinda zatayi yasa tabude kofa tafice daga dakin, dakin Hajiya tabude tashiga dake meeting a zoom na retired lawyers, ita kebada report din ga glasses akan idanunta, kallon Du'a dake kallonta tayi hakan yasa Du'a tashigo wani book dake kusada ita tadauka rubutu tamata sanan tabata kallon rubutun Hajiya tayi ta gyadamata kai tareda daukan purse dinta ta zaro 10k tabata, karba tayi cikeda jin dadi tafito daga dakin sanan tasauko kasa da sauri tana murna tai wajen Razika dake dakinsu tace "Grandma tace kirakani saloon jeki shirya nima bari na shirya" gyadamai kai Razika tayi tace "kinbar wayan ki a dinning tun jiya" murmushi tayi tace "zan dauka nasan Su Aneesa ne bari naje na shirya" sama tayi, shiryawa tayi cikin wani black abaya mai kyan gaske, sanan tazauna tai rolling veils dinta dayay kyau shima ta feffesa turare tafito rikeda handbag, a falo tasami Razika tace "yauwa kin shirya muje to" gyadamata kai Razika tayi suka fice, driver Hajiya ya kwashe su zuwa wani saloon daba na ranan nan ba dantace dagaske bazata wanan ba, tsife mata kalaban akayi sanan aka wanke mata kan sai murmushi take ta kosa agama, gamawa akayi aka mata blowing hair din yabushe tass sanan matan tace "Hajiya wani style za'a miki" dasauri Razika tace "asake mata kalba amman yan kanana kanana this time" dasauri Du'a tace "a'a ayi manya manya" dasauri Razika tace "please amiki kanana Du'a ai tanada sauri" dagakai Du'a tayi takalli matan tace "idan kikai kanana zaki gama kafin 4" kasa magana da kyau matan tayi sabida idanun da Du'a ta zubamata yarinya kaman ita tai kanta. "eh bakice komiba zaki gamamin kafin 4" kasa magana matan tayi sai kawai gyadamata kai datayi murmushi sosai Razika tayi tace "kingani na gayamiki za'a gama, afara to amata mai kyau mai style" fara mata kalaban matan tayi tana mamakin yawan gashin Du'a dakeda tsayi, tsayin shikecin lokaci ma ba asalin kitson ba, wajajen 3 Du'a takalli uban tulin gashinta da ba'ayi ba tace "3 yayi sai yanzu mukai rabi" kallon fuskanta matan tayi ganin Du'a tayi kaman zatai kuka yasa dasauri tace "yakuri gashinki nada tsayi sosai ne gashi robber hair, I am going as fast as I can, zan gama dawuri" gyadamata kai kawai Du'a tayi matan tacigaba da kitson da saurinta, tanaji tana gani 4 yayi ana kan kalaban ba'a gama gamaba sosai taji hawaye yazo mata amman ta daure tahana kanta wuraren 5 matan tagama, tashi tayi tsaye da sauri tana parking kitson da ribbon dinta tadau gyalen ta ta tafa wanan karan batama tsaya rolling ba duka kudin da Hajiya tabata tabama matar sanan takalli Razika tace "muje" tashi Razika tayi suka fito tace "wai ina kike sauri zakije ba gida zamuba" girgixa mata kai tayi suka shiga mota, tace "dan Allah transcorp hotel zaka kaimu" sanan tajuya takalli Razika tace "program liyafa akeyi na matasa kan fara sana'a tun karfe hudu aka fara" gyadamata kai kawai Razika tayi dan batasan wani program bane ba akeyi ba but yanda taga Du'a tasan it must be something very important to her.
Tunda suka shiga hotel din gabanta ke faduwa sosai parking yayi hakan yasa suka bude suka fito suna kallon kofan dazai sadasu to asalin cikin hotel din da wani security guard dake sanye da uniform ke tsaye yana kallonsu, kallon Du'a dataga ta tsaya sakakau Razika tayi yanda take kalle kalle tace "a ina akeyin abun" dan zaro idanu Du'a tayi irin na asalin wanda doesn't have any idea akan abu tayi tace "nima bansani ba" ganin haka yasa Razika tadan matso kusada ita murya chan ciki tace "to ki tambayi wanan security daman gashinan yanata kallonki" dan zaro idanu tayi saikuma tajuya takalli mutumin dake kallonsu har lokacin kafin Du'a tai magana yace "are you here for the program"? Gyadamai kai Du'a tayi batare datai magana ba, yace "to ku shiga hall din ma 8th floor" gyadamai kai tasakeyi sanan tawuce tafara tafiya tana kama hannun Razika suka shiga ciki tare, tunda taji 8th floor yasa tasan akwai elevator hakan yasa sukai hanyar stairs suka farabin bene, da sauri sauri gudu gudu take hawa stairs din, sosai sukai nisa dafa bango Razika tayi tana nishi sosai tace "wayyo Allah na kafana, Du'a nagaji wlh" kaman zata fashe da kuka tace "nima wlh nagaji kinga ankusan gamawa dan Allah muje" tashi Razika tayi tana nishi suka cigaba dabin stairs din ita karan kanta Du'a daurewa tayi kaman kaman kafafunta zasu tsinke, ahaka suka kai floor din tundaga tsayin corridor wajen sukaga mutane sunyi layi hadaddun yammata da maza anyi layi har zuwa hall din da cikin hall din da ake asalin abun, ganin anbisu da kallo yasa Du'a tabi Razika da kallo saikuma takoma tabayan Razika tana sussunar dakai kaman mara gaskiya dan wani iri takeji idan ana kallonta, murya chan kasa kaman mai whispering tace "Razika tambaya mana inane hall din me akeyi anan" dan Jim Razika tayi saikuma ta kalli wata mata dake tsaye alayi tana sanye da hijabi tace "dan Allah inane hall din" hall din dake gabansu matan ta nuna mata tace "ga hall dinan" ahankali Razika cikeda tausasa murya sabida karta gaji da ita tace "angama ne me kukeyi alayi dayawa haka"? File din dake hannunta matan ta nunama Razika tace "anriga angama liyafan, layin nan kuma na masu son irin su email dinshi ne sanan muna using opportunity din muna submitting CV dinmu akwai possibility na zaiyi recruitment koma baiyiba tunda gwamnati sunsan da zamanshi zaya iya sama mana aiki kingane, long layi ne about 100 people naciki duk sunata bashi kuma ya karba" gyadamata kai Razika tayi tace " nagode sosai, sanan tadan matsa baya still Du'a na labe abayanta tace "kinji ko, ina zamu iya jiran this plenty mutane dasunkai 200, Hajiya tasan kinzo nan" girgixa mata kai tayi alamun a'a, hakan yasa Razika tace "to gaskiya ki wuce mutane tunda anriga angama bazamu kafin akawo kanmu goman dare tayi" gyadamata kai Du'a tayi asanyaye Razika tace "muje" juyawa tayi ahankali suka fara tafiya saikuma ta tsaya Razika takalleta tace "menene?" ahankali tace "I want to say thank u" bata jira amsan Razika ba tawuce wajen da saurinta tai gaban hall din tana sussunnar dakai batai wata wataba kawai ta danna kanta ta kutsa tacikin mutanen dake layi tashiga hall din, tana shiga yan waje sukahau ihu chaaa barinma matan wasu suka biyota ciki ganin haka yasa tawani irin kwasa da gudu dan hall din nada makeken girma sunachan kan stage, dagudu itama Razika tashigo tana kwala mata kira. "Du'a, Du'a, Du'a ina zaki".....
Chak ya tsayar da rubutun dayake ma wata a littafin data bashi, yau yana sanye cikin wani gray suit dayafi na kullum mai kyau, yana zaune yadaura kafa daya kan daya agaban wani hadadden table, both sides dinshi bodyguards ne tsaye rike da gun, sai wasu manyan mutane dake kan stage din suma a zazzaune da suit, tsayar da rubutun chak yayi batare daya dago kanshi ba jin ana ihu da hayaniya a hall din amman suna daya kunnenshi ya iya karba Du'a!
Dawani irin gudu Du'a takaraso gaban hall din daidai inda mutum zai fara hawa yan kirgaggun stairs din dazai sadaka to stage din wanda anan line din yafara duk wanda yazo kanshi xaihau stage ne yaje yasauko, wani irin tsayawa Du'a tayi tana nishi sama sama kaman kirjinta zai fashe sabida gudun datayi tana kallonshi ganin yes yes tabbas shine, daidai lokacin matan dasuka biyota suka karaso cikeda fada sukace. "ke waye dazaki baromu alayi ki gudo ki shigo ciki" juyawa tayi tasake kallonshi cikin muryanta mai shegen zagin nan da dadi dake rawa kuma sabida tsabagen tsoro dakuma gudun datayi tana kallonshi still tace "thank u" duk binta akai da kallo ganin yanda take kallonshi tacemai thank you, wani mutum dakebinta da kallo ne dakekan stage din yace "Pretty lady ki koma kibi layi idan akazo kanki then you now tell him thank u, as it is so many people sun cemai thank you yours is not first kinga he is busy" yanuna mata Asad dayama cigaba da attending to mutane kaman ma baisan something is going on ba, gyadama mutumin kaitayi hawaye na neman zubomata amman ta daure tana kallonshi ahankali tace "thank you for saving my life" daya daga cikin matayen dasuka biyota ne tawani finciketa tace "dalla malama kizo kifita" dasauri Razika takama hannun matan tace "kisaketa dalla kema ai tafiya zamuyi, muje Du'a" kasa daga kafa daga wajen Du'a tayi tana tsaye kaman an dasata tana kallonshi, muryanta wanan karan narawa sosai hawaye yacika idanunta sosai tace "thank you for saving my life" fincikanta matan tasakeyi hakan yasa Razika tace "malama dalla kisaketa, Du'a let's go" kin motsi Du'a tayi kaman ba ita akeja ba, nan hall din yadau hayaniya, ahankali ya sallami guy din dake gabanshi sanan yajuyo da kanshi ahankali yadaura fararen idanunshi akan na Du'a da akeja taki tafiya tana kallonshi, faduwa gabanta yayi yanda yanda ya kalleta, wani irin yatsine fuska yayi sanan yadauke kanshi daga kanta yajuya yakalli security dake gefen damanshi batare daya kalleta ba yana jiran next person dake kan line yanuna Du'a da yatsanshi a wulakanci yace "fitarmin da yarinyar nan daga hall dinan please and throw her outside this premises".
wanna talk to me no problem just click on this link wa.me/+2347012181461
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
Chat me up directly by clicking on this link wa.me/+2347012181461
✍️ M SHAKUR
Free page
EPISODE 2️⃣5️⃣
Ko karasa maganan baiyiba katon bodyguard dinshi yataho hakan yasa Razika tawani ja hannun Du'a da duka karfinta, fashewa da kuka sosai Du'a tayi Guard din nabinsu Razika najanta da sauri tana kuka mutanen wajen namata dariya suka fita daga wajen sukai hanyar staircase suka farabi, sai alokacin bodyguard din ya tsaya ata gaban stairs din yace "idan kuka dawo cikin wajen nan saina bindigeku" dasauri Razika kejanta suna sauka sai alokacin tasan ashe kafafunta sun gaji, sosai take kuka Razika tace "waike bakida wayaune Du'a saikace wata karaman yarinya, jibi yanda kikasa akai embarrassing namu" da kyar ta iya karasa sauka daga stairs din kaman kafafunta zasu cire daga cinyanta suka fito waje, wani Alhaji ne suka gani tsaye awajen yana gyara zaman malum malum dinshi yana kallonsu, hannu Du'a tasa tai wiping hawayen dake kan fuskanta tass, wani irin murmushi mutumin yasakin mata yace "common pretty girls basa kuka, daina kuka" dasauri Razika tacigaba da janta da sauri dan magrib yayi, da dan gudinshi ko kunyan mutanen dake wuce su baiyiba yasha gabansu yakalli Razika yace "I guess ke kawarta ce ko dan Allah sakin mata hannu kibani minti daya nai magana da ita" yakalli Du'a data dauke kai yace "Pretty dance mata tasakin mata hannu" cigaba da tafita sukayi yana binsu har sukakai mota, bude motan Razika tayi Du'a tafara sawa aciki sanan tashiga itama taja kofa mutumin na bubbuga kofa takalli driver Hajiya tace "muje wanan mutumin na binmu" kunna motar yayi yaja shikuma mutumin yadaga hannunshi sama kaman mai kiran mutane saiga wata hadaddiyar jeep yazo baya yabude yashiga yace "mubi wanchan motan Auwallu amman ahankali zamubi motan sabida karsu sani suboye inaso nasan mahaifin yarinyar nan" yana biyedasu har suka shigo estate dinsu, nesa dasu yasa aka kashe motan ya gyara zama yana kallonsu, gate aka bude musu suka shiga ciki sanan aka maida gate din aka rufe, dasauri yace "tada motan kaga Auwallu" tasa motar driver shi yayi zuwa gidan da Du'a ta shiga, parking yayi akofar gidan sanan yabude bayan motan yafito yana gyara zaman malum malum yana leken gefen gate din kaman wanda yasami matsalan tabin hankali, ahankali yakai hannunshi zaiyi knocking gate din aka bude gate din aka fito, Sharif ne yafito daure da alwala dan masallaci zaije sallan isha'i, tsayawa yayi yabi mutumin da kallo, dasauri mutumin ya shiga leka gidan kaman zaiga Du'a ta gefen Sharif, ganin haka yasa Sharif yarufo gate din ahankali yace "lpy" wani irin murmushi Alhaji yayi tareda shafa kanshi saikuma yace "wai mugaisa wlh duk na rude ne naga abinda raina ke matukar so" yamikama Sharif hannu, kin bashi hannu Sharif yayi yana kallonshi still yace "lpy maikazo nema? Kokuma nace wakake nema?" sake sosa meya Alhajin yayi yace "wlh naje ba wata yarinya yar fara haka nabiyo naga tashiga gidan nan, inataso namata magana tun achan amman dayan datake tareda ita taja hannunta tahanata magana dani wlh, dan Allah ko zan iya ganinta kokuma zaka hadani da mahaifinku dan naga kaman kai yayanta ne naganka fari kaman ita dudda tafika fari da kyau" yay maganan yana lashe baki yace "Allah yayi mace awurin nan wlh" wani irin daure fuska Sharif yayi ganin tsohon banza ne, hakan yasa yace "sunana Sharif, kuma yarinyar dakake magana matata ce, ka kama girmanka ka tattara inaka inaka kabarmin kofar gida kafin nahadaka da hukuma" wani irin kwalalo idanu yayi saikuma yadaura hannu akan saman bakinshi yace "assha ai bansan matarka bace, bansan matan aure bace wlh nagayamaka bata kulani ba inda ace takulani tagayamin tanada aure daban biyota ba wlh, amin afuwa nabarka lafiya" yajuya yashiga mota dasauri sukabar wajen wani irin tsaki Sharif yaja yabi motan da kallo yace "tsohon banza kawai" saida yaga su fita daga estate din sanan yawuce yatafi masallaci.
Sharif na tsakar gida yana alwala yaga shigowansu itada Razika tana goge fuskanta da gyalen abayan dake kanta idanunta sunyi ja sosai, bama su luradashi ba suka wuce ciki, falo suka shiga kallo daya Hajiya dake zaune akan kujera tana magana awaya tamata tagano wani abu dasauri tacire wayan daga kunnenta tace "zan kiraki Hajara" katse wayan tayi takalli Du'a da Razikan da duk suke atsaye sun kasa karasowa gani suke kaman tana ganinsu zata gane abinda yafaru, yunkurowa tayi tana kallonta still tace "why did you cry Du'a? Maiya sameki?" Dan zaro ido tayi this is the first time datasan tama Grandma dinta laifi sosai, Grandma data taimaketa tabata freedom shine daga fara fita ta hartaje hotel ita maiyama kaita taje, duk ta tsaya tana tunanin nan zuciyanta fall da tsoro batare databama Grandma dinta amsaba, juyakai Grandma tayi takalli Razika tace "maiya sameta take kuka"? Baki Razika tabude zatai maganan da sauri ta tattaro duka karfinta ta tari numfashin Razika ahankali tace "Grandma hannun matan zafi sosai kuma gashi tadade kaina ke ciwo" sosai Grandma ke kallonta, ga idanun nan nata sundan kumbura alamun tasha kukan tace "to dan kanki na ciwon kitso sai kiyita kuka banace kidena all this abubuwan ba keba yarinya bace"? Gyadama Grandma kai tayi hawaye nasake taruwa a idanunta tace "sorry" ganin tana neman sake kuka yasa taidan murmushi dan she looks damn cute tace "zonaga kitson" tahowa tayi ahankali gabanta nafaduwa sosai ko kadan bataso tama Grandma dinta karya ba, zama tayi gefenta, Grandma tabude kan tana kallon kalaban dayay bala'in kyau tace "wow daman abu mai kyau yafi bada wahala, kinga yanda yay kyau kuwa, wow oya jekiyi salla kiyi wanka kizo nabaki abinci da paracetamol kisha" gyadamata kai tayi ta tashi ahankali sama, Grandma takalli Razika dake tsaye itama tace "sannu kinji Razika, Du'a dukta wahalar dake, jeki daki kiyi salla kihuta" ahankali tace "to" tawuce, tashi tayi itama dayake hijabinta nakusada ita dan tariga tai salla yasa ta tashi ta shimfida dadduma danyin salla.
Takwas daidai yabaro uban mutanen dake kan layi yafito dan yagaji iya gajiya, juyawa yayi yakalli security dake biyedashi abaya yamika musu hannu yace "car keys, u can go" daya daga cikinsu ne yadauko key daga aljihunshi yamikamai yace "Sir daka bari mun maidaka gida is not safe for you to be driving alone" dan yatsine fuska yayi yace "it's okay" juyawa yayi yakunna mad ride dinshi yabude kofa yashiga sanan yatada motar, tafiya mai tsawo yayi sanan yakai gaban wani eatry, shiga ciki yayi sanan yay parking inda ake parking ya kashe motar, wayanshi yadauka ya daddanna sanan ya ijiye wayan kan cinyanshi ya jinginar da fuskanshi jikin kujera tareda lumshe ido yana fuzarda iska, Asad wani irin mutumne da idan zaka kwana kana kallonshi bazaka taba tantance wani yanayi yake ciki ba sai idan kai mai lurane.
Knocking motarshi da akayi yasa yabude idanunshi ahankali yadago kanshi, wata doguwan fara mace ce tsaye gaban kofan tana sanye dawani arnen half gown daya tsaya daidai gwuiwanta sanan an tsaga tagaban da kadan yarage ba'a ganin pant dinta, kanta sanyeda attachment daya zubo har waist dinta taci uban makeup a fuska dayamata kyau ba laifi ga hill akafanta mai tsinin gaske, yarinyan dan kyau Allah yayi kyau ga hips ga boobs duka, danna lock din motar yayi kofan yabude hakan yasa tabude kofan ta shigo ta zauna tareda maida kofan tarufe sanan tajuyo takalli Asad din dake kallonta bayabo ba fallasa murmushi tamai tadan juya idanu tana chewing gum dinta tace "why call me wajen gari haka, wajen garin ma this local place, you are so lucky ma danazo" shiru yayi yana kallonta ta duhun harta gama tana wani yatsine yatsine, jin shiru yasa takunna flash din iPhone 11 pro max dinta tadaga ta haska fuskanshi tana kallonshi kaman yanda ko gezau baiyiba kallonta yake tace "woooww, bansan cewa mahaifinka nada kyakkyawan thick sexy boy hakaba, so you are the famous Asad da mahaifinka always talks about, only son, his father's pride, wowwww" cikin thick voice dinshi yace "would you mind turning that off" wani irin lumshe ido tayi kafin ahankali tasauke wayan ta kashe flash din tasan Alhaji yana yawan bata labarin Asad dinshi but bata taba sanin babban Matashi saurayi haka bane mai jini ajika ba gashi kyakkyawa yafi baban shi kyau sosai, ahankali tace "why did u call me here" shiru yamata yakai kusan 3min sanan yace "inaso kirabu da mahaifina ne!" dawani irin sauri takalleshi saikuma tanuna kanta tace "ni Zinariya kake cema narabu da mahaifinka? Sugar Dady nawa? Anya kasan girman abinda kake fadi kuwa, dakakirani cemin kayi we will talk business zakamin proposing offer da I can't resist saisa nazo, is this the offer"? Dauke kai yayi daga kallonta yajuya yana kallon waje yace "sunanki Zainab Garba Habu from kano, anguwan uku layin Murtala hamisu house number 3, mahaifinki yarasu, mahaifiyarki nada rai ita ke kulamiki da yaronki mara uba kekuma kina nan Abuja kina karuwanci dan kisami kudi kidinga turamusu....." yanda yake maganan komai waye sai wani kalan natsuwa yashigeka, batare daya kalleta ba yace "kaman yanda nagayamiki awaya I have an offer for you bana karya is true I have that offer, inaso kirabu da mahaifina is exchange ma 10million naira, gida akowani kasa kikeso acikin kasashen waje da visa da passport miki da mahaifiyarki da kannenki dakuma danki inkin yarda" tunda yake maganan jikinta ke tsuma amman tadaure tahana kanta tanuna tadai daure takalleshi tace "sabida 10million ne zan rabuda Alhaji shikemin komi, yabani kudi naturama yan uwana akan me zan rabudashi sabida yan chicken change dinan naka da balallai ne kabani ba" hannunshi yamika yadauko wani envelope daga kujeran baya yadawo dashi gabanta yabude yazaro takardan ciki yamika mata karba tayi ahankali tana kunna hasken wayanta tana dubawa maida kanshi yayi kan hanya yace "I am sure u can read, wanan agreement ne da lawyer na yarubuta nariga nayi signing inhar kin yarda zaki rabu da mahaifina kibarshi har abada without having any form of contact dashi aboye to komi dana fadamiki nakine sanan inda daga baya kikazo kika saba alkawari to inada right na na kulle ki agidan yari but all this saikin yarda ne zaki iya signing" duka abinda yafadi haka yake arubuce awajen, Alhaji nabata kudi but baitaba bata kudin dayafi 500k ba, yana bata kudi 50k 60k tasaima gidansu abinci, yasata awani gidanshi kullum ya ijiyeta cinta kawai yake amman yaki aurenta kotamai maganan aure saiya cemata shi bayida ra'ayin kara aure amman komi yamata, ga motanshi daya daya ijiye mata dudda bai bataba amman tana hawa, yanzu ga kudi malala har 10mil da rayuwa kasan waje manta manta, ubanme Alhajin ke tsinana mata banda uban jaraba yacita kusan sai shidda arana duka baya wuce 1min, sai bakin jaraba bakarfi kaman ammai baki anya bazata karbi wanan offer ba.
Anjiyan zuciya tasauke dashi kanshi saida yaji, sanan takalleshi dudda aduhune bai hanata kallonshi ba tundaga kai har zuwa kan cinya, yanda gaban wandonshi yadan tattaro yataru waje daya yay tsaho kaman wandon ya kwanta kan wani luteten maciji ne yasa tawani hadiye muyau, ko Alhaji nada zankaleliyan azzakari balle danshi kawai tashi ta kwan biyu ne, Allah yamata girma gatada shegen jin sha'awa amman yana shiga yakawo abin tadaina functioning sabida tsufa amma yanzu tasamu tadan dandana yaron nan nashi ai sharrr daga ganin wanan Allah zaiyi karfi da kuzari ajikinshi, gyaran murya tayi tace "kanada pen tareda kaine" hannunshi yamika yadauki pen batare daya kalletaba dan she disgust him yatuna ita ubanshi keci saiyaji kaman ya shaketa anan tamutu, mikamata pen din tayi ahankali takarba takai bakinta tadan gatsi duwawun byron tana kallonshi yanda ko kallo bata isheshi ba, zaro byron tayi daga bakinta tace "inada sharadi daya nima, gabaki dayan abubuwan daka rubuta anan nayarda nima kuma inada sharadi guda daya tall kana yardan mini zanyi singing" batare daya kalletaba kai tsaye yace "say it" dan gyara zama tayi tanawani irin kallonshi kafin tadan ciji lips dinta tace "inaso kacini muyi one night stand I promise no emotions attach kasan aiki nane karuwanci danka kwanta dani bazaisa narikeka ba konace dole saika soni, kawai kamin ne u are so classy, young, educated, rich and above all u are damn handsome gashi Allah yamaka jiki, zaka cini din? Ina bukatan kasa na manta da mahaifinka ta hanyar zuxxubamin ruwanka adurina yakora na Abban ciki sabida na manta dashi".
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
EPISODE 2️⃣6️⃣
daurewa yayi iya daurewa danko kadan baiso tagane yanayin dayake ciki but maganan datayi kiris yarage bai koro amai acikin motan ba, hakan yasa yakasa magana dawuri kafin ahankali yace "it seems u are not interested in my offer, keep the paper and get out of my car" ganin yanda babu wasa tattare dashi yasa tadanyi murmushi tace "wow yanda Abban ka keda raha bansan cewa zai iya haifan murdadden mutum haka ba, anyway naji tunda u don't wanna fuck me u have to add 2min akan kudin idan kayarda then we have a deal idan baka yarda ba we don't have" yana kallon waje har lokacin yace "deal zan baki 12M" signing paper tayi sanan ta mikamai hannu yasa yakarba yace "zan aiko miki da kudinki and everything dana fadi gobe with a copy of this document dakikai signing excuse me" wani irin murmushi tayi tacigaba da taunan cingam dinta tace "I am curious so I have to ask this question kana tunanin ayanda Babanka yake sabida nabace na barshi bazai nemi wataba ne?" batare daya kalletaba yace "at least idan baki zai dawo gidanshi to his family" wani kalan dariya tasaki tana tafa hannu saikuma tanuna shi da yatsanta dayasha uban nails tace "I am sorry Asad but bari nagayamaka this kaga mahaifinka neman mata nacikin jinin shi ne, kaga dudda yana taredani nasan cewa nice best dinshi da nikadai wacce ya ijiye akarkashin shi but still bai hanashi cheating on me ba yanabin wasu up and down, agabana baya kunyan kallon mace kaman zai cinye ranan nan harwata yar kyakkyawan yarinya yadinga kallo a saloon daya kaini, kawai zama nakeda shi sabida banda wanda yake kashemin kudi irinshi but baban ka is a certified cheat" batare daya kalletaba yace "can you get out of this car please" dan dariya tayi tana kokarin bude kofa tace "sure mana ganinan ma fita nake, but know this, bin matan Baban ka kana basu kudi dan surabu dashi is not a problem dan karuwai irinmu are just after money zamu karba muwuce, the problem is kudinka gabaki daya saiya kare akan babanka ne, that Man bayason mahaifiyarka yace batada komi kaman bamace ba haka take gar........" wani irin ihu daya dakamata yasa batasan lokacin datai wani irin tsalle tafadi waje akasa daga motan ba bura'uban wlh ta bala'in firgicewa, kunna motar yayi baima tsaye rufe kofan side dinta yake abudeba yawani irin yi reverse da mugun gudu tai flat akasan wajen danda sai marfin motan side dinta ya kwaye mata fuska yawani wanke ta da kura yabar wajen.
Yadade yana tuki sanan ya tsaya awani masallaci akan hanya yay salla sanan yafito yashiga mota yana tuki yana lumshe ido yana budewa, he just needs some time alone, he needs fresh air, kaman yatafi airport yashiga jirgi yabar garin yakeji amman bazai iyaba, he just wants to get away daga gidansu this night baimasan kowa ya ganshi na gidansu, yana tunane tunanen yakai anguwan su kasa karasawa yayi gidansu kawai saiya sami kanshi da tsayawa gaban gidan Hajiya horn ya danna hakan yasa Maigadi yafito ganinshi yasa yakoma yabude gate jan motan yayi ciki, yadade zaune a motan sanan yabude yafito yay ciki, ahankali kaman mara gaskiya yay sallama chan kasa yabude kofan falon yashiga, Grandma na zaune kan kujera ita kadai a falo tana kallon gidan Badamasi a Arewa24 ga bowl dake cike da sliced fruits ajikinta tajuyo da kanta, kallo daya tall tamai takarance shi tsaf, maida kofan yayi yarufe ahankali yakaraso cikin falon har zuwa gabanta ya tsaya, cikin wani kalan yanayi na bala'in sanyin jiki yace "har yanzu dakina na nan Grandma"? Duk gidansu Ammi shi kadai kecema Hajiya Grandma dan sauran gabaki dayansu Hajiya suke cemata, tunda yaga yanda Ammin shi tamaida Hajiya Mahaifiyar da Batada shi dan Ammi batada Mama, Maman Dadsuka raineta, tunda yaga yanda Ammin shi kesonta itama takeson Ammi yamaida Hajiya kakanshi saisa yake cemata Grandma, yawanci idan yana cikin kunci ko wani abu na damunshi wajen ta yake zuwa yakwana dan musamman tamai dakinshi agidan, saisa dazaran yazo wajen ta Ammi bamata nemanshi sai hankalin ta ya kwanta.
Ahankali tace "Asad are you okay"? Gyadamata kai yayi batare dayay magana ba, dan Jim tayi tana kallonshi sanan tace "jeka kwanta dakinka na nan, nakawo maka wani abu ne"? Girgixamata kai yayi yace "a'a I will eat in the morning" yay maganan yana hawa stairs, falon saman yawuce da dakunan dake wajen yay wani dan corridor da aka jera flowers awajen wanda bazaka taba sani da flower awajen bama, ahankali yabude kofan dake wajen yashiga dakin dakenan fess fess gahotonshi da aka makala a bango lokacin yay graduating a school a UK dashi da Grandma ne ajikin hoton suna murmushi duka.
wa.me/+2347012181461
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️M SHAKUR
Free page
chat me up by clicking on this link wa.me/+2347012181461
EPISODE 2️⃣7️⃣
Fadawa kan gadon yayi batare dayacire daidai da takalmin kafanshi ba balle kuma ayi maganan kaya, sosai kanshi kewani irin sarawa, he's so tired and everything and anything, he's working damn hard to keep his whole family happy, shi baida matsala idan da Dad zai natsu yace aure zai kara yasan Ammin shi she won't object to that dan tasan yafi mata alkhairi, but wanan wulakanta Ammi dayake yi yafi komai bakantamai rai, shi bawai yasaketa ba kotamai wani laifi ba amman saiya kauracemata dasu yaranshi for months kuma bawai yaje anywhere bane yana nan Abuja tareda matan banzan shi, yasan once Zinariya takarbi komi dazai bata gobe ta tafi zai dawo gida he hopes from there shi And Ammi can work something together, wani zubin he understands his Dad in the sense that auren hadi aka mai da Ammi but that doesn't zama excuse nashi dazaije yana Zina up and down, Ammi is very very sick low BP takeda shi ita ba high BP ba, and low BP yafi dangerous da high BP mutum can yanke jiki yafadi at any time yamutu, akanme Dad zai dinga wulakanta Ammi eh yamaida ita kaman trash his mother is very sick dudda bata nunawa, but yaga tanashan drugs aboye, gashi sai ramewa takeyi, she's depress dan yasan Ammin shi nason Dad sosai kodaga yanda take luradashi ma zakasan hakan he just wish yanada power to change things arayuwanshi, he wish ana iya chanza mahaifi, hannunshi yakai ahankali ya share wani dan gajeren hawayen daya zubomai ta gefen ido sanan ahankali ya fuzar da iska waje mai zafi, ko minti biyu baikaraba bacci yay awon gaba dashi mai nauyi gaske yana sauke ijiyan zuciya daman ance behind every thought face akwai thousands of weakness aciki.
Wuraren 5:30 nasafe Grandma tabude kofan dakinta tafito, hanyar dakin da Asad keciki tayi, ahankali tasa hannu tabude kofar tashiga yana bacci har lokacin baitashi ba ga takalmi nan baicireba kayama haka, maida kofan tayi tarufe sanan takaraso tazauna abakin gadon, ahankali takai hannunta taciremai takalman ta ijiye sanan tajuyo da kanta takalli fuskanshi tana kallonshi, harga Allah tana bala'in son Asad samada kowani d'a agidan nan, why because Asad might look harsh kana ganinshi zakaga bakin halinshi but he's weaker than any other person agidan nan dan abu yafi damunshi kan kowa, gashi da zuciyan nema dudda Asad baitaba nunawa ba ita tariga tasan yasan komi gameda halin Baban shi saisa yana gama school yanemi jari daga CBN batare daya karbi kudin Babanshi ba yabude kampanin kanshi cikin ikon Allah kuma kampanin sai albarka yake, yay wayon nanne sabida duk ranan da mahaifinsu zai juyamusu baya he will be able to take care of his family, bambamcin shi da Sharif kenan, Sharif is very nice but Asad yafishi hankali da hangen nesa dudda idan angansu kowa will go for Sharif dan physically yafi kirki and more welcoming, Asad is just a small boy daya Goya responsibility alot abayanshi saisa yake bata tausayi, she just wish zai natsu ya nemi mata ya aura koyasami natsuwa amman tsoron yanemi mace ma yake sabida baiso yagaji irin halin mahaifinshi beside ance blood is thinker than water, saisa gashinan ne kawai bakowa ke ganeshi ba. Hannunta takai ahankali tashafa tattausan sajenshi tace "kai tashi kayi salla" da kyar yabude ido, ahankali yace "okay Grandma " tashi tayi tawuce tafita daga dakin, dakin Du'a ta shiga tabitada kallo yanda take baccin ta hankali kwance, karasawa tayi gaban gadon zama tayi tashafa fuskanta ahankali tace "yammatana atashi daga bacci, Du'a Du'a" da kyar Du'a tabude idanunta takalli Grandma cikeda bacci a ido batare datai magana ba, kumatunta Grandma taja tace "da ace yanda kikeson bacci haka kikeson cin abinci danaji dadi saisa kullum cikinki kaman ana diba ayi biyan bashi dashi tsabagen yanda yake ashafe kaman cikin jinjiri" dan murmushi tayi saikuma ta jinkirto tadaura kanta akan cinyan ta takama hannun Grandma dake kan fuskanta ta rungume ajikinta sosai ahankali tace "Grandma agidan ki kadai nasami farin ciki haka tunda aka haifeni, Grandma please karki bari Abba yakomar dani gidanshi I am so happy anan da I don't wanna leave, da kullum sainai kuka Ya Hamad kadai ke lallaahina da Aneela" fadada murmushin dake kan fuskanta Grandma tayi tana kallonta tace "bazaki komaba ai nagayamiki sai inda karfina yakare babu wanda zai kara wahalar min dake, yanzu addu'a na shine Allah yakawo miki miji nagari" murmushi tayi sosai saikuma ta tashi tazauna takalli Grandma tace "Grandma nina isa aure ne? Ya Nana da Ya Hawwa fa duk basuyi aure ba, kumama ai sai mutum ya iya girki akemai aure ko nikuma ban gama iyawaba tayaya zanyi aure to"? sosai Grandma ke kallonta yanda take maganan saida tagama maganan sanan taja hancinta tace "har wayauma baki gamayiba dan Aneela zata iya sayarda ke agaban idanunki baki saniba, tashi kiyi salla ki shirya yau akwai office" gyadama Grandma kai tayi tana tashi ta sauka daga kan gadontai hanyar bayi kananun kalaban da aka mata sun zubo har waist dinta suna lilo kaman wata balarabiya tabude kofa tashiga bayi, ajiyan zuciya Grandma databita da kallo ta sauke sanan ta tashi ahankali tafice daga dakin.
Saida tashiga bayinma taga batada salla daman tun jiya takejin ciwo ciwon ciki, brush kawai tayi tai wanka da ruwan zafi sosai tafito daure da towel tanada feeling ciwon ciki kadan kadan dayake ita batada wanan serious ciwon aran nan saidan dan ciwon ciki kadan hakanan, wani black mickey riga tasaka, t-shirt ne amman irin na baccin nan babban gaske daya saukan mata har guiwa, batabi takan kama gashinta ba tasake shi ahaka yana lilo abinshi, komai ma bata shafa fa tasaka slippers dinta tabude kofan dakinta tafito ahankali, dakin Grandma tayi ganin bata ciki yasa tamaida kofan tarufe tai hanyar stairs tana sauka kasa, ganin Grandma zaune kan kujeran dakin rikeda Al Qur'ani tasaka glass a idanunta tana karantawa yasa takarasa wajenta zama kusada ita tayi ahankali batare datai magana ba tana sauraron yanda Grandma ke karatun anatse Akuma hankali Aya ta dire sanan takalli Du'a din alamun ya akayi, ashagwabe tana wani turo baki kaman yar baby tace "Grandma good morning cikina naciwo kadan kadan, MP ne, kinada magani"? girgiza mata kai Grandma tayi tace "bari zansa akawo miki, yanzu tashi kidebo ruwan lipton a flask kije daki kisha saikidan kwanta kafin lokacin zuwa office yayi" gyadamata kai tayi ta tashi dinning tayi cup tadauka tadauki flask ta tsiyaya ruwan shayi dayasha kayan kamshi sanan tadauki spoon tasa a cup din tawuce tai stairs tana tafiyan nan nata ahankali tana kallon shayin da kamshin shi sai ratsa mata hanci yakeyi, tsayawa tayi chak jin wani irin sanyi ya ratsa kafafunta dakenan abude zuwa jikinta gabaki daya, wani dan kara tafitar daga bakinta ashhhh sanan taduka kaman wacce zatai ruku'u tana duba kafafunta tana daga kafanta sama tana duba tafin kafan kota taka kankara ne ganin babu abinda ta taka yasa ta dago tacigaba da tafiya ahankali tana hawa stairs din zuwa karshe tashiga falon sama daidai Asad shima yafito daga corridor hanyar dakinshi yashigo cikin karamin falon yana lazy tafiyan nan irin na wayanda suka sha bacci, wani irin hada idanu sukayi dagashi har ita, chak ta tsaya tana kallonshi da duka idanunta awaje kaman zata hadiyeshi da ido, yana sanye da kayan jiya dataganshi dasu a hotel dinnan bambamcin kawai shine babu jacket din suit din da neck tie da alamu yaciresu ne, farin long sleeve t-shirt din ciki ne kawai ajikinshi daya bubbude boturan gaban rigan har zuwa kasan kirjinshi kana iya gashin kirjinshi dasuka kwanta lubbb idanunshi sundan tashi da fuskanshi lips dinshi sunyi pink yirrrr alamun yasha bacci sosai looking a bit scattered kaman ba shiba, yanda take kallonshi haka shima yake kallonta da wanan expression nashi dinan dabaka taba gane takamaimen wani yanayi yake ciki.
Wani irin rawa hannun data rike mug din shayin ta dashi ne yashiga wani irin rawa tana kallonshi jikinta na bar bar da batasan mesaba takasa koda motsi, tundaga kafa yakalleta zuwa kai saikuma ya basar kaman bai ganta ba yacigaba da tafiyanshi normal normal yazo tagefenta zai wuce kamshin da jikinshi keyi yawani yi splashing akan fuskanta wani irin salubewa mug din hannunta yayi ruwan shayin ya bare some of it yazuba akan kafanta kofin yay wani kara yahau tsalle yana tsaltsalleke stairs kafin daga bisani ya tarwatse, wani irin runtse idanunta tayi gam jin yanda kirjinta ke bugawa dum dum kaman zai fita jinta kusada shi kaman jikinshi zai gogi nata yattsun kafanta namata radadin zafi amman takasa ihu sabida yanda tashiga wani yanayi, wani irin beating kirjinta yakeyi tanajin sahun tafiyanshi yanabi ta gefenta yawuce yay stairs abinshi mayen kamshin turarenshi yagama wanke mata numfashi yasauka daga stairs din yay falo abinshi.
Sai alokacin tabude idanunta wani irin zama tayi a kasan wajen dagudu takama kafarta tadaura akan cinyanta tana hura yatsunta dake mata radaddin azaban zafi sosai tana kuka sosai amman mara sauti tana hura kafan.......
Zama yayi kusada Grandma dake karatu abinta har lokacin, murya chan kasa irin nawanda yasha bacci sosai yakoshi dinan yace "good morning Grandma" saida takai Aya sanan tai addu'a tarufe Al Qur'ani takalleshi tace "wanan bacci dakasha haka kaga yanda kai subu subu kuwa kaman wanda yay kwana uku yana bacci" dan murmushi yamata tareda lumshe ido yabude baice komiba, tashi tayi tace "bari kaga nakawo maka shayi mai zafi kasha zaisa kadan saki ko" gyadamata kai yayi yana kwanciya kan kujeran data tashi kaman wani dan yaro, itakuma tai hanyar dinning harzata wuce saikuma idanunta suna sauka kan mug daya gangaro zuwa nan stairs na kusa to the last dasauri takalli sama ganin Du'a zaune tana hura kafa tana share hawaye yasa tace "subhanallahi Du'a meya sameki kike kuka haka? Ince badai kin koma kafarki ba shine baki kirani ba" tai maganan tana hawa sama, tana kaiwa wajen takarbi kafan tana kallo aiko gashi nan yatsun sunyi jajir alamun sunsha ruwan zafi, hannunta takai takama kafadar Grandma tana kuka sosai mara sauti tace "Grandma zafi wlh" dasauri Hajiya tashiga kwalama Razika kira. "Razika Razika" Razika dake daki fitowa dagudu tari jin Hajiya na kwalamata kira, turus ta tsaya afalon tana kallon Asad dake kwance abinshi idanunshi bude kaman yasan ta inda zata fito kenan kallonta yayi shima, fitowa Shemau tayi ganin Asad yasa dasauri tadan rusunna tace "ina kwana" gyadamata kai kawai yayi batare data amsaba hakan yasa Razika itama tace "ina kwana" ko kallonta baiyiba yadaura idanunshi kan TV dasauri duk sukai stairs, Grandma tace "kawomin zuma Razika Du'a tazuba shayi akafa" dawani irin sauri tajuya tace " to" zuman dake dinning tadauko tadawo sama, karba Grandma tayi tashafamata sanan takalleta idanunta sunyi jajir tace "sannu dena kukan to" gyadama Grandma kai tayi tana share fuskanta takalli Razika tace "kaita dakinta ke Shemau biyoni ki debi wani shayin ki kaimata saiki gyara wajen nan" duk amsawa sukayi da to sanan tawuce kasa, Ganin Asad na nan inda tabarshi yasa tace "wai jikata ce shayi ya bare ayatsun kafarta take kuka shegen raki irin na Du'a bawani konewan kirki bane bafa, itace jikata datazo daga kano yar wajen Zainab, bari kaga nabaka shayin ka".
0 comments:
Post a Comment