Hakan yasa ya ɗan ƙyafta idanun sa yana mayar da su kanta, kana kuma ya gyara sosai yana zama
"Abban Habeeb don Allah ka rage damuwar nan, kwata-kwata ba na jin daɗin ganin ka a haka, yanzu tunda ka shigo nake tambayar ka in kawo maka abinci? but kayi shiru."
"Jalila ba na jin yunwa ne ko kaɗan, ki bari zuwa anjima zan ci."
"Ok to in haɗa maka ruwan wankan ne?"
Girgiza mata kai yayi da cewa, "no bar shi."
Numfashi ta ja kawai tana ɗauke kai daga kallon sa
"Ina ganin gobe ya kamata ku koma gida saboda makarantar Habeeb, ki haɗa kayan ki ku bi jirgin safe."
"To." Tafaɗa tana kallon sa, sai kuma tace, "amma Abban Habeeb don Allah ka cire damuwar nan haka insha Allahu za'a ganta in Allah ya yarda, idan har kidnappers ne suka ɗauke ta da yardan Allah zasu nemo mu, Ni dai fata na ka cire damuwar nan a ranka."
Kallon ta yayi fuskar sa babu walwala yace, "muddin na samu waɗanda suka ɗauki daughter wlh tallahi bazan bar su ba, duk sai na kashe ƴan iska." Ya ƙare maganar da irin fushin nan nashi
Hakan yasa ta ɗaura hannayen ta a kan nashi, ba dai tace uffan ba sai kallon sa da take yi
"Ki haɗa min ruwan wankan zan sake fita in koma wajen ƴan sandan can, ƴan iska su ma har yanzu sun kasa taɓuka komi, ban ga amfanin su ba, zan tashi tsaye in Yi da kaina tunda baza su iya ba." Ya ƙare maganar yana tashi da hanzari ya soma cire rigan jikin sa
Jalila ita kuma tashi tayi ta wuce Toilet ɗin zuciyar ta duk babu daɗi, suna cikin matsala gaskiya musamman ma ita tunda mijin ta ya fi kowa tashin hankali, ko lokacin kansa yanzu be samu kullum yana tafe zuwa Ofishin ƴan sanda, damuwa tayi masa yawa wanda har ya shafi zamantakewar su dole itama ta shiga damuwar, fatan ta da burin ta yanzu a samu ganin MEEMA domin sauwaƙewan wasu al'amuran. Bayan ta gama haɗa masa ruwan ta fito ta sanar mishi sannan ta wuce ta fita ta sauka ƙasa.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
"Wai yanzu Luwaira me kike jira ne har yanzu da baza ki sake tura masa wani saƙon ba? Allah Ni kin fara bani haushi." Sai ta ja dogon tsaki tana ƙarawa da faɗin, "ki zauna kwaɗo zai miki ƙafa, yanzu damar ki ne kika samu tunda har kika ce yarinyar da yake so an neme ta an rasa, wlh wlh kisan inda kika kwana tun kafin ki rasa chance ɗin ki."
"To Abida ya kike so inyi? Na fa tura mishi saƙon he's still haven't received a reply."
"To nace miki ki sake tura masa wai me kike jira? Baki yi masa bayani gamsashshe ta yanda dole zai gane abin da kike nufi ba taya zai yi tunanin ba mistake ne kika yi ba?"
"Kuma fa haka ne ko?" Tafaɗa tana ware ido a kan Abidan. "Allah kuma sai yanzu tunani na ya je a kan hakan domin kwata-kwata be sanja min fuska ba, ko kaɗan be nuna min wani yanayin da zai saka in gane ya ga saƙo na ba. But bari in sake tura wa." Wayan ta ta ɗauka ta soma yinƙurin rubuta saƙon domin ta tura masa
Abida tace, "and apparently you want to miss him wlh, ki zauna kina sakin leɓe zaki ji a salansa al'ƙur'an."
Hannu ta kai Luwairan ta duke ta a cinya tana cewa, "ke dai baki da dama wlh."
"Ato Ni gaskiya nake faɗa miki kar ki ɗauki magana ta a wasa wlh."
Luwairan bata ce komi ba sai da ta gama rubuta text ɗin kafin ta ɗago wayan tana nuna mata da cewa, "kin gani yayi?"
Amsa tayi ta karanta tace, "yauwa ko ke fa, wannan ai dole ya san da shi kike yi, bari in tura masa." Sai ta tura tana kallon Luwairan da cewa, "sai mu jira amsar shi kuma.
Daga nan suka sanja hiran nasu duk a kan yarinyar da yake so ɗin wato MEEMA, duk da har yanzu Luwairan bata san wace ce ba. Har suka gaji suka tashi daga wajen shaƙatawan da ke cikin school ɗin suka koma class babu reply ɗin Umar Faruk, duk Luwaira ta gama damuwa domin a tunanin ta, "kar dai ace ya sake gani ne bazai ce mata komi ba?" Shirun sa shi ne babban tashin hankali a wajen ta, gwara ya faɗa mata halin da take ciki ko zata san madafa
Abida ce me kwantar mata da hankali a haka har suka gama lecture ɗayan da ya rage musu. Sannan suka fito zasu tafi. Abidan tace, "su wuce gidan su domin ta yiwa Auntyn ta barka." Kasancewar ta haihu yau. Shiyasa suka tafi a motan gidan su Abidan
Yayinda Luwaira ta cewa nata drever'n, "ya je zata kira sa ya ɗauke ta idan zata dawo".
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Umar Farouk yana tsaka da meeting ne a lokacin da Luwaira ta tura masa text, shiyasa be duba ba sai da suka fito ya koma katafaren Office ɗin sa wanda ya gaji da haɗuwa don kyau. Bayan ya zauna a luntsumemen kujerun da aka jera a Office ɗin domin huta wa ya ɗauki wayan yana duba wa da zummar kiran Hashim. Sai dai cin karo da saƙon Luwaira ya matuƙar firgita masa lissafi domin yanda tayi amfani da kalamai me nuni da tabbas da shi take yi, wanda har sunan sa sai da tayi amfani da shi, shiyasa lokaci ɗaya ya ɗauke wuta yana lumshe idanun sa, shiru yayi kawai yana faman tunani a ransa, ba komi ke dawo masa a rai ba sai mu'amalar su tare, a haƙiƙanin gaskiya a yanda ya nutsu yana tunanin ta sai yanzu ya gane wasu halaye nata wanda take yawan nuna masa da zai tabbatar da cewa tabbas tana ƙaunar sa, sai dai shi be taɓa kallon hakan da wani manufa ba domin ya ɗauke ta tamkar ƴar uwan sa na jini wacce suka fito ciki ɗaya, ba ya tunanin akwai irin wannan alaƙar da zai shiga tsakanin su shiyasa ko kusa be taɓa kawo wai zai iya son ta ba. Idan ko haka ne akwai matsala dole ne ya ja mata birki domin gudun ɓacin rana, shi kwata-kwata ma be taɓa mata kallo me kama da soyayya ba, kuma ba ya jin a ransa zai iya auran ta tunda ita ɗin ƙanwar sa ce, but me zai faru idan Momy ta ji zancen nan? Ace ɗiyar ta tana son shi kuma ya kasa amsar tayin ta? Nan da nan sai kansa ya hau zafi sakamakon wani irin damuwa da ya tabaibaye shi a yanzu-yanzu, kasancewar sa wanda be iya saka abu a rai ba yanzu sai ya cutar da shi, zancen soyayyar Luwaira ya tsaya mishi a rai wanda yake jin shi nan da nan ya rasa walwalan sa da jin daɗin sa, dama ba a cikin mood ɗin shi yake ba, daƙyar ya iya kawar da zancen nata zuciyar sa na masa zafi ya danna wa Hashim kira. Ring ɗaya ya ɗauka sai suka soma waya yana tambayar sa inda yake? Daga nan kuma suka yi sallama bayan ya sanar masa, "idan ya koma gida zai zo ya same sa."
Har ya ƙarisa zaman sa a Office ɗin ya rasa madafa. Daga ƙarshe a haka ya koma gida, sai dai ya kasa zuwa Part ɗin Momy kamar yanda ya saba illa wuce wa nashi Part ɗin da yayi
Yau su Hafsah suna Part ɗin a zaune suna wasa. Kasancewar tunda suka dawo school da suka je Part ɗin Momy Talatu me aikin ta ta cire musu kaya ta basu abinci suka ci, sai suka dawo nan tunda Momy ko bi ta kansu bata yi ba, tana ɗaki ta ƙule ta bar su nan, shiyasa da suka gaji suka dawo nasu Part ɗin. Suna ganin Dadyn nasu sai suka nufe shi suna mishi Oyoyo
Dauriya ya aza wa kansa yana yalwata fuskar sa da murmushi, kana ya soma jan su da hira yana tambayar su school? Daga ƙarshe kuma sai ya zame jikin sa ya bar su a nan ya wuce ɗakin sa, wanka ya fara yi sabida huce gajiya kafin ya saka farar Singlet da dogon wando Robber coffee color da fatsi-fatsi kaɗan na kalan ruwan ƙasa a jiki. Sannan ya sauko ƙasa ya nufi dainning inda aka jera mishi abinci. Kasancewar yanzu babu kukun shi shiyasa Talatu take mishi abinci ta zo ta jera masa a nan Part ɗin tunda ba ya cin abinci a can wajen Momy, sai dai ko yaran sa wani lokacin. Yanzun ma yana zama suka biyo sa suka hau mishi surutu, dayake jikin sa babu daɗi shiyasa kaɗan-kaɗan yake iya biye musu yana tusa abincin a baki kamar ba ya son ci. Sai kuma can ya dubi Hafsah yace, "ta je ta kira mishi Luwaira idan ta dawo school."
Da gudu ta fita
Yusra tana take mata baya da ƙorafin, "ita zata je kiran ta."
Duk kiran da yayi mata don, "ta dawo."
But tuni ta fice ta bi bayan Hafsan.
Yana nan zaune a kan dainning ɗin koda ya gama cin abincin, sai ga su sun dawo tare suna sanar mishi, "Momy tace bata dawo ba."
"Ok ku je ku zauna kuyi karatun Alkur'ani inda aka ƙara muku before Malamin ku ya zo."
"To Dady." Suka faɗa suna tashi da gudu suka soma rige-rigen shige wa ɗakin su
Shi kuma tashi yayi ya bar wayan sa a wajen ya haura sama. Sauya kaya yayi zuwa farar shadda me tsananin maiƙo da ɗaukar ido, tamkar ango haka kayan suka yi mugun fito da shi, har ƙara gyara gashin sajen sa dana kanshi yayi, ya sake liliye su da mayuka masu saka sheƙi da ƙamshi, sannan ya ƙwama hulan sa tangaran me kalan aikin kayan. Ya ɗauki keeys ɗin mota ya fice. A parlour'n ya zauna inda su Yusra suke karatu yana faman sauraron su, idan da gyara kuma sai ya gyara musu
Haka har malamin su ya zo wanda ya ke musu karatun islamiyya, ɗaya security ya zo ya sanar mishi
Don haka yace, "su shiga ɗaki su saka hijabin su su wuce wajen karatun."
Tashi suka yi suka ɗauko suka zura suka fice
Shi kuma yana zaune har yanzu ɗin, sai dai yanzu ya mayar da idanun sa a kan fantsamemen t.v plasman da ke jikin bangon parlour'n yana kallo.
Luwaira ce ta shigo parlour'n da sallama
Hakan yasa ya bi ta da kallo yana amsa mata sallaman nata a hankali
"Yaya gani, Momy tace kana kira na?" Tayi maganar itama idanun ta a kanshi. Yanda ya ƙure ta da kallo ne yasa ta sauke kai ƙasa domin baza ta iya juran kallon ƙwayar idanun sa ba, sosai take jin faɗuwar gaba da shiga wani mawuyacin hali da haɗa idanu da shi
"Ki zauna." Ya bata umarni ba tare da ya ɗauke kai har yanzu daga ƙare wa jikin ta kallo ba, tun daga sama kuwa har ƙasa, domin haka kawai ya ji yana buƙatar yau ɗaya ya kalle ta sosai
Sai da ta ɗago ta kalle shi suka sake haɗa ido, sai tayi maza ta ɗauke kai tana zama a kan sofan da ke kallon nashi, kamar wata salaha ta wani tattare waje ɗaya hannayen ta a haɗe wuri ɗaya
Wayan sa da ke saman dainning ne ta soma ƙara. Sai ya bata umarnin, "ta ɗauko mishi."
Hakan yasa ta tashi da sauri ta nufi wajen
Shi kuma sai ya samu damar ci gaba da kallon ta, sai da ya ga zata juyo sannan ne ya ɗauke kansa yana wani lumshe idanu tare da buɗe su ya sake mayar wa a kanta. Wayan ta miƙa masa ya kai hannu ya amsa
Sannan ta je ta koma ta zauna
Hashim ne ya kira shiyasa yayi peacking suka yi magana kaɗan kafin ya kashe kiran ya ajiye wayan. Ya mayar da hankalin sa gare ta yana faman kallon ta, sai da ya ja ɗan soconni be iya cewa komi ba kafin ya cije leɓe yana ɗan lashe na ƙasan, before ya Kira sunan ta a hankali a cikin sanyin muryan sa wanda a koda yaushe haka take
Ita kuwa amsa mishi tayi tana sake jin gaban ta na matsanancin faɗuwa domin tabbas ta san zancen text ɗin ta ne yasa ya kira ta, ba ta raba ɗayan biyu
"Luwaira Did you really send me text today and that day? Do you want to send your message to me?"
Kai ta gyaɗa mishi kanta a ƙasa tana sake duƙar dashi
"Magana zaki yi min ba ɗaga kai ba".
A hankali ta furta, "Eh."
Shiru ne ya biyo bayan amsar ta. Ya kasa yin magana sai da ya ɗau lokaci me tsawo wanda ita har ta sare da jin maganar nasa, yayinda ta sake shiga tashin hankali da jin me zai faɗa mata. Numfashi ya ja yana tsayar da idanun sa a kanta kana ya buɗe baki a cikin sanyi da daɗin muryan sa yace, "kiyi haƙuri Luwaira duk da na san ba ƙaramin ƙoƙari kika yi ba wajen bayyana min abin da ke ranki, sai dai kuma Ni na ɗauke ki tamkar ƙanwata wacce muka fito ciki ɗaya da ita, kinga kuwa babu zancen maganar aure a tsakanin mu, ba wai don ba na son ki ko wani abun ba, a'a, look at my words and understand, Ina da wacce a halin yanzu nake neman auren ta, so don't think of anything in your heart ok?"
Shiru ne ya biyo bayan zancen nasa domin ta kasa ko motsi, nan da nan hawaye suka cika mata idanu wanda har wasu tsiraru sun soma ɗigowa, hakan yasa ta sake duƙar da kanta sosai
Shi kuma jin tayi shiru sai ya kirayi sunan ta
But ta kasa amsa wa, sabida tabbas idan ta buɗe baki kukan ne zai taho gadan-gadan
"Ke ƙanwata ce Luwaira, kuma ba na son ki saka damuwa a ranki, ba naƙi amince wa da ke bane a kan wani abu ba tunda kin kai ko wanne ɗa namiji ya so ki, But you heard my argument, Ina so ki bar zancen nan a tsakanin mu domin ba na so Momy ta ji, You promise?"
Kanta ta gyaɗa tana kai hannun ta ɗaya ta goge hawayen fuskar ta
Shima ya fahimci kuka take yi, sai dai be da yanda zai yi, gwara yayi mata magana tun yanzu ta san makomar ta tunda ba ya son ya cutar da ita, bazai iya auren ta ba, yanzu zuciyar sa Mutum ɗaya kacal take so, da ita take son ƙare rayuwar ta, idan har ya shigo da Luwaira a cikin rayuwar sa ƙwaran ta kawai zai yi domin be taɓa son ta ba, kuma ba ya jin zai taɓa. Umarni ya bata a kan, "ta tashi ta tafi."
Don haka ta miƙe da sauri ta juya ta tafi
Kallon ta kawai yake yi har ta fice a parlour'n. Sai ya kwantar da kansa a jikin kujeran yana lumshe idanuwan sa zuciyar sa cike da tausayin ta, domin shi Mutum ne me tsananin tausayi, yana da rauni matuƙa musamman ma a kan Mace. ya jima a haka ko motsi ba ya yi sai yatsun hannayen sa da yake ƙas-ƙas da su. Almost five minutes ago before ya buɗe idanun nasa yana miƙe wa ya ɗauki wayan sa ya zura a aljihu, sannan ya nufi ƙofa ya fice.
💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
💎💎💎
*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*SHAR'ANTATTUN SALLOLI*
```A dukan mazhabobi sallolin da aka shar'anta sun kasu kashi biyu ne, farilla da nafila. Amma shi kuwa Abu Hanifa ya ce uku ne: farilla, wajiba da nafila. Ita farilla ɗin ta kasu biyu.
_1. Farlu aini._ Wannan ita ce sallar da take kama baligi kansa, ba wani da zai iya ɗauke masa yinta, kamar dai su sallolin nan biyar da sallar juma'a.
_2. Farlu kifaya._ Ita ce sallar da take kama baligi, amma idan wani ɓangare na mutane suka yi ta, ta faɗi ga sauran jama'a, misali sallar jana'iza. Idan sashin mutane kuwa ba su yi ba, jama'a duk sun yi laifi.
A mazhabar Abu Hanifa wajibi kashi biyu ne:
_1. Wajibi don kansa-_ watau abin da wajabcin sa bai dogara akan wani abu daban ba, kamar sallar wuturi da sallar idi da sujadar tilawa.
_2. Wajibi don wani abu-_ wannan shi ne abin da wajabcin sa yake dogara ga wani abu daban, kamar sujadar rafkannuwa da raka'o'in ɗawafi da bakantacciyar sallah da ramakon sallah wadda ta ɓaci. Watau, sujadar rafkannuwa ba ta wajaba sai don rafkanar wani abu a cikin sallah. Su kuma raka'o'in ɗawafi ba sa wajaba sai don ɗawafi, bakantacciyar sallah ma ta wajaba ne saboda bakance. Ita nafila kuwa ramakon ta bai zama farilla ba sai da ɓacin tun farko.
A mazhabobin maliki da shafi'i da Hambali nafila ita ce duk abin da yake ba farilla ba. Watau, abubuwan da Hanifawa suke ɗauka wajibi ne don kansu, a wurin sauran mazhabobi suna cikin sunna ko mustahabbi sabida cewa wajabcin ba don zatin su ba ne, illa dai sabuban da aka ambata.
Ita nafila ɗin an kasa ta gida biyu:
_1. Nafila mu'akkada,_ watau wadda aka ƙarfafa sunnancin ta, kamar su sallolin idi da wuturi da raka'o'in ɗawafi, waɗanda Hanafawa suke kira wajibi.
_2. Nafila wadda ba mu'akkada ba,_ watau wadda ba a ƙarfafa sunnancin ta ba, kamar su nafilolin da ake yi gabanin azahar ko bayanta, da waɗanda ake yi gabanin la'asar da bayan magriba da kuma gabanin isha'i da bayan ta.
Allah yasa mu dace.```
*NO_34*
Babu ranar da ya kai wannan lokacin a wajen Sajjad domin mallakar abar ƙaunar sa, wanda yana jin ya fi kowa farin ciki a duniyar nan tamu, tsantsan ƙaunar da yake yiwa MEEMA shi ya jawo duk abin da yake mata a halin yanzu, izuwa yanzu ya mallake ta a matsayin Matar sa kuma ya zamar da ita cikakkiyar Matar sa. Kasancewar ba ya son ta riƙa mishi gardama a zamantakewar su shiyasa har yanzu ya ci gaba da ɗura mata ƙwayoyi wanda ke gusar mata da hankali
A sannu a sannu sai ta koma tamkar mara hankali domin ba ta sanin ma a halin da take ciki. Shiyasa yake kiɗan sa yake rawan sa da ita duk yanda ya juya ta haka take bin shi
Yanzu ba shi da wani matsala bare shamaki da ke hana sa kusantar abar ƙaunar sa. Shi ke mata komi na rayuwa, ya cika gidan da kaya yanzu komi na more rayuwa ya zuba. A nan yake kwana yake wuni sai idan yayi kwana biyu ne sai ya koma can Yola gudun kar iyayen sa su zargi wani abun. A yanzu ya yanke shawarar da zaran zai tafi abroad karatun sa zai tarkata har da ita ne ya tafi, tunda dama yana neman karatu a UK.
Haka rayuwar ta ci gaba inda a yanzu ga shi har MEEMA ta shafe wata ɗaya a hannun Sajjad. Kuma har a lokacin yana ci gaba da banka mata magunguna ba tare da yayi la'akari da hakan zai cutar da ita ba, domin shi ya fi son ganin ta a haka su zauna lafiya babu wani gardama da zata yi masa, muddin tana a cikin hankalin ta ya san zai sha fama da ita, ƙarshe bazai taɓa jin daɗin rayuwar sa ba. A sannu a sannu sai ga shi ta soma ciwo wanda lokaci ɗaya ta fita hayyacin ta ta rame sosai. Hakan yasa dole ya ɗauko Likita tunda ya ga jikin nata ya ƙi daɗi
Likitan bayan ya duba ta shi yayi masa bayani a kan, "ya dena bata ƙwayoyin da yake bata saboda sun soma mata illa a ƙwaƙwalwa, idan har hakan ya ci gaba da faruwa zai iya rasa ta sabida a halin yanzu magungunan sun fi ƙarfin ta." Kasancewar shi Likitan dama shi yake ba shi maganin da yake ɗura mata wanda zai riƙa gusar mata da hankali ya zamana ba ta iya taɓuka komi sai yanda aka yi da ita, kuma tunanin ta zai riƙa gushe wa a jikin ta
Shi kuma Sajjad bayan ya bata ne sai ya ci gaba da bata don kawai ta ci gaba da zama a haka
Likitan ya sake mishi bayani a kan, "tana da shigan ciki."
Koda jin haka sai hankalin sa ya tashi domin shi be shirya haihuwa yanzu ba, yana son sai ya gama more rayuwar sa inyaso daga baya sai su soma tara yara, shiyasa yace mishi, "a zubar da cikin."
A nan take kuwa yayi mata allura aka zubar
Sai dai ta sha wahala matuƙa tunda har suma tayi kasancewar ta zubar da jini
Haka likitan ya ƙara mata ledan ruwa sannan ya tafi
Shi kuma Sajjad zuwa yayi ya zauna a gaban gadon da take kwance ya zuba mata idanu har da yin tagumi
Tana kwance ne idanuwan ta a rufe ruf, fuskar nan nata ta ƙara zama ɗan siriri tayi fayau tamkar mara jini a jiki. Daga ita sai shimi fara wacce ya sanya mata, sai ya rufa mata blanket a jikinta
Hannun ta ɗaya mara drip ɗin ya riƙe, kana kuma ya duƙa ya sumbaci hannun yana shafa mata saman goshi har izuwa gashin kanta. Cike da shauƙin ƙaunar ta yake kallon ta da cewa, "very soon zaki samu lafiya my dear, I love you so much! Ina yin komai ne domin Ƙaunar ki kar ki ga laifi na." Ya sake faɗa yana kai bakin sa kan nata ya sumbata, har ya cire kuma sai ya sake mayar wa yana saka bakin nasa a cikin nata ya ci gaba da tsotso na tsawon lokaci kafin kuma ya tashi ya fice zuwa kichen. Daga shi sai gajeren wando a jikin sa ya shiga ya ɗaura girki, taliyan makoronni ya girka sannan ya sako rabi a flet, sai da ya koma ɗakin ya ga har yanzu tana barci kafin ya wuce Parlour ya zauna ya soma cin na flet ɗin, yana yi yana kallo a t.v cike da nishaɗi da walwala a face ɗin sa.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Bazan iya misalta muku a halin da mutanen gidan su MEEMA suka kasance ba a cikin wannan watan. Tun suna saka tsammanin za'a ganta ga shi yanzu har sun gajiya sun soma cire rai da ganin ta, abun ya sake ɗaga musu hankali musamman yanda suka ji shiru wanda hakan ya sa suka cire tsammanin kidnappers ne suka ɗauke ta, tunda da su ne da tuni sun kira sun buƙaci kuɗi
Babu irin fafutukar da Uncle Hashim be Yi ba don ganin an samu MEEMA, sai dai abun ya cutura. Izuwa yanzu dole yayi haraman koma wa Abuja tunda hutun da aka ba shi a wajen aiki ya ƙare, dama wata ɗaya suka ba shi lokaci har yayi yana neman gotawa, babu yanda ya iya haka ya shirya kayan sa ya wuce Abuja tare da danƙa komi na binciken a hannun Umar Faruk tunda komai tare suke yi
Shi kansa shima yana cikin halin damuwa da tashin hankali da rashin MEEMA, tunda soyayyarta ta matuƙar kama mishi zuciya wanda a yanzu ta hana sa sukuni matuƙa. Tafiyar Uncle Hashim ne ya kwanta ciwo sabida yanda yake saka damuwa a ranshi ga shi yana fama da ciwon zuciya. Dole aka wuce da shi asibiti yayi jinya na ɗan kwanaki
Likitan shi ya yiwa Momy bayanin halin da yake ciki
Shiyasa koda suka koma gida ta tsare shi da tambayar abun da ke damun sa?
Ya ƙi sanar mata da halin da yake ciki sai da ya ga ta nuna damuwarta ƙwarai kafin ya sanar mata da damuwar sa
Cike da tausayin sa a fuska tace, "My son don Allah ka cire damuwa a ranka, yarinyar nan fa idan rabon ka ce zaka same ta, Allah zai bayyana ta a duk inda take, amma kuma be kamata ace kana saka damuwa har ya kwantar da kai ciwo ba." Sai tayi shiru tana jan numfashi, sake kallon sa tayi da cewa, "Ni bazan zauna in zura maka idanu kana cutuwa a haka ba, idan da ace kana da Mata da duk hakan be faru ba, da tuni ita zata riƙa kula da kai sosai yanda ya kamata, ka ga kuwa dole ne kayi aure yanzu, bamu san lokacin da za'a ga yarinyar nan ba, Ni ina ga a shawarata idan har zaka iya bin abun da nace maka ka auri Luwaira, ka ga ita ƴar uwan ka ce zaku zauna lafiya, ina matuƙar tausayin ka shiyasa ban son ganin ka a cikin damuwa."
Shiru ne ya biyo bayan zancen nata domin ya kasa yin magana, maganar sosai ta buge sa shiyasa ya kasa ɗago kai bare ya bata amsa
Sai ta kira sunan sa da cewa, "Umar na san ko ba Luwaira ba dole zaka sake aure, amma idan ka tsaya jiran yarinyar nan baka san sanda zata dawo ba, sannan mutanen gari suna yamaɗiɗi da kai a kan rashin ajiye mata hakan ke jawo ka-ce-na-ce a tsakani na da ƙawaye na idan na fita waje, to yanda ake yawan maganar ne ba na jin dadi, Ni kai na zan fi so ace ka aje mata ko don lafiyar ka shiyasa na zaɓa maka ƙanwar ka, wacce ta san ka ta san halayyar ka, haka zalika kai ma haka. Idan baka amince ba babu komi wlh ka faɗa min ra'ayin ka."
"Haba Momy ta ya ya zan ƙi ƙaunar ƴar ki? Bazan iya bijire miki ba domin tamkar umarni nake ganin zancen naki. Allah ya zaɓa mana abin da ya fi zama alkhairi." Yafaɗa a cikin matsanancin sanyin murya
Murmushi ne ya suɓuce a fuskar Momy da cewa, "kana nufin ka amince?"
"Eh Mom."
"Masha Allah. Haƙiƙa zan fi kowa farin ciki da wannan haɗin, Allah yayi maka albarka ya sanya albarka a auren naku. Alhamdulillah." Ta faɗa a cikin farin ciki
Shi kuwa be iya cewa komi ba har ya bar parlour'n. Sosai ya shiga damuwa sai dai ba shi da yanda zai yi, bazai iya duban idanun Momy ya ƙi amince wa da buƙatar ta ba, Momy tayi mishi komi bazai taɓa bijire mata abun da ta saka shi ba, amma ya zai yi da zuciyar sa da ta mutu a ƙaunar wata? Ko kaɗan ba ya ƙaunar Luwaira, to sai dai kuma akwai tausayin ta a zuciya zai iya yin haƙuri da ita ya zauna da ita, sai dai kuma bazai taɓa haƙura da MEEMA ba. "Allah ya baiyana min ke My love, nayi kewar ki sosai!". Ya furta a laɓɓan sa yana me mayar da idanun sa ya rufe ruf.
Daga ranan ne aka soma shirye-shiryen auren su tunda har an tsayar da ranan aure
Murna wajen Luwaira kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha tunda Momy ta sanar mata da zancen. Ta kasa yarda da gaske zata auri Umar Faruk. Har kuka sai da tayi tsaban farin ciki
Shi kuwa Umar Faruk baza ka taɓa gane a halin da yake ciki ba a kan zancen auren, ko kaɗan ba ya nuna abun da ke ransa a fili. Uncle Hashim ne kawai yake kwantar masa da hankali tunda ya sanar mishi da komi
Shima ya ga dacewar auren nasa tunda bazai zauna haka be da mata ba, bare shi ɗan siyasa za'a yi ta yamaɗiɗi da shi ne, sai dai kuma ya jiwa MEEMA haushi a kan rasa masoyi kamar Umar Faruk, ya so burin sa ya cika a kan ta auri abokin sa domin ba ƙaramin dacewa suka yi da juna ba. Sai dai basu da tabbacin sanda za'a ganta, basu san a wani hali take ba a halin yanzu? Basu san tana raye ne ko tana mace ba? Sai dai addu'a da ƙarfafa wa kansu haƙurin rashin ta da suke faman yi a halin yanzu. Insha Allahu Allah zai bayyana ta tunda sun tashi tsaye sosai wajen addu'o'i da saukar alƙur'ani
Ba dare ba rana ake sauke Al'ƙur'ani don dai aga inda take. Tuni walwala da farin ciki ya ƙwaurace wa su Ummee a halin yanzu. Burin su kawai su ga MEEMA ta dawo gida. Ɓacewar ɗan Mutum sulluguda? Abun ɗaga hankali ne.
**** ***** ***** **
Wata ɗaya aka saka bikin shiyasa aka tasar wa gyaran gidan su gadan-gadan, kama tun daga Part ɗin Umar Faruk har izuwa part ɗin Momy, gaba ɗaya gidan sai da aka sauya mishi sabon penti. Gyara sosai ake yi a gidan ana kashe mishi maƙudan kuɗi
Umar Faruk shi ya ɗau ragamar komi na bikin, har kayan da za'a zuba wa Luwaira, a ƙasan Dubai aka yo odan komi, tunda shi Yakamata yayi mata komi na biki a matsayin sa na Yaya a wajen ta, bare kuma yanzu shi zata aura.
Yau da gobe kayan Allah sai ga biki ya ƙarato inda har an soma shagulgulan biki, yanda aka tsara bikin ana yin shi cikin girma da arziƙi sosai hakan ya faranta ran Luwaira, dama haka take so ta ga bikin ta na kere wa Sa'a wanda za'a riƙa faɗan shi a ko ina. Ita kanta ta san yanzu ta zama big classes Girl domin har a makaranta zuwa ake yi ana ganin ta, musamman ƴan mata wadanda suka ci burin auren Umar Faruk, da waɗanda suka san shi a zahiri da waɗanda suke jin labarin shi
Ba irin gyaran Amaren da Luwaira bata yi ba, musamman suka ɗauko me gyara ita da Abida ake mata a gida. Kasancewar ta kyakykyawa itama son kowa ƙin wanda ya rasa shiyasa ta fito a Amaryan ta sosai, sai shainnig take yi gunun sha'awa
Sun shirya events kala-kala ita da ƙawayen ta. Shiyasa tunda aka shiga satin bikin aka soma yin event ɗin
Babu wanda Umar Faruk ya halarta domin shi har yanzu be wani damu da auren ba, kuma har yanzu be taɓa neman Luwairan ba, sai ma da bikin ya zo ne ya kira ta ya ba ta ATM card ɗin shi yace, "Ta je ta dauki kuɗin da take buƙata, idan ta gama hidiman bikin ta kawo mishi."
Ita ko a jikin ta wai don be damu da ita ba, tunda Abida tana kwantar mata da hankali a cewar ta, "idan suka yi aure zai zamo nata ita kaɗai, a nan ne zata mayar da hankali ta sace zuciyar sa sai yanda tayi da shi." Shiyasa bata damu ba don ba ya nuna kulawan sa a kanta.
Yau ma party suka shirya a haraban gidan ita da ƙawayen ta. Ƙawayen ta sun yi ankon doguwar riga Robber brown color, sai aka yi design da zare kalan coffee aka ɗaura flower a gefen kafaɗan rigan na hagu, gaba ɗayan su ƙawayen nata ɗinkin iri ɗaya ne har Abida, sai suka yi amfani da farin ɗankwali aka yi musu ɗauri me Steps
Itama kuma Luwairan doguwar riga ce ta ɗinka, sai dai nata Golden corral ne, daga bayan yana jan ƙasa sosai yayinda gaban rigan aka ɗigile shi da designing ɗin love aka yanka gaban rigan, ita Stones aka yi mata amfani da shi wajen kwalliyan rigan a gaban; masu tsananin ƙyalƙyali da ɗaukar idanu, sai tayi amfani da ashobe ja aka yi mata ɗauri me kyau irin na Amare, fuskar nan ta sha make-up na zamani wanda ke sauya halitta, don ko ka san ta baza ka gane ta ba a ranan sabida yanda ta koma, tayi amfani da dogayen takalma masu tsinin gaske don daƙyar take iya tafiya tamkar zata faɗi.
Sun gabatar da taron su gunun sha'awa sun kuma cashe irin na wayayyun ƴan mata, kasancewar da yamma aka yi har sai da aka kira magriba kafin suka tashi.
Zuwa gobe kuma shi ne zasu yi dinner Wanda shi Abokan Umar Faruk ne suka shirya masa, gaba ɗayan su zasu halarci wajen, zuwa jibi kuma sai a ɗaura Aure akai Amarya ɗakin ta.
_To Fans na Luwaira muna gayyatar ku shagali fa, an soma ya kamata ku hallaro, saura ku ce baza ku zo ba._ 🙄😂
💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
💎💎💎
*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_35*
Da sannu-sannu MEEMA ta soma samun lafiya. Zuwa yanzu ta soma dawowa a cikin hankalin ta kasancewar Sajjad ya dena bata maganin sosai, sai yayi kwanaki ma be bata ba saboda shi be so ta riƙa mishi gardama. A kullum sai tayi kuka sabida baƙin cikin halin da ta tsinci kanta, ji take yi kamar ta kashe kanta sai dai bata da ƙarfin ƙwatan kanta, a haka ta zura wa Sajjad idanu yana yin duk abin da ya ga dama da ita, sai dai tana iya bakin ƙoƙarin ta wajen hana shi but ya fi ta ƙarfi haka tana ji tana gani take ƙyale shi
Shi kuwa ce mata yayi, "she calmed down because she became his wife saying, no one should take her from his hand and be his property."
Ta kan yi kuka sosai ta share hawayen ta ta zira masa idanun ta kamar yanda ya zame mata jiki tunda babu abinda take iya yi. Sai dai tunda ta soma samun lafiya take ta yunƙurin guduwa amma Allah be bata Sa'a ba tunda ba ya wasa da barin ƙofa.
Kamar ko yaushe yau ma tana zaune a ɗakin da ya zame mata nata, ta haɗa kai da gwiwa tana ta sharɓan kuka, ƙunci da baƙin ciki ya addabi rayuwar ta, tana jin baza ta iya ci gaba da rayuwa a haka ba gwara ta kashe kanta, shiyasa kawai ta tashi da hanzari ta fita Parlour, dube-dube ta soma Yi sai kuma ta zarce kichen, a nan idon ta suka faɗa kan wuƙa sai ta nufi wuƙan da sauri ta ɗauka, ta saita da ninyan lumawa kanta har ta kai cikin nata sai kuma ta tsayar da wuƙan tana me fashe wa da wani irin kuka me ban tausayi, yayinda ta faɗi a kan gwiwowin ta ta dinga rerawa kamar ana yankan naman jikin ta. Kuka take yi sosai wanda ta shafe tsawon lokaci a wajen. Sai da ta jiyo ƙarar motan Sajjad wanda ya dawo daga yawon sa; hakan yasa da sauri jikin ta na rawa ta miƙe, sai ta wawura wuƙan ta ɓoye a Bayan ta ta nufi ɗakin da gudu, pilow ta ɗaga ta ɓoye wuƙan sannan ta hau kan gadon ta zauna, sai ta mayar da kanta a saman cinyanta ta ci gaba da kuka
Shi kuma yana shigowa kanshi tsaye ɗakin ya shigo, yana sanye da ƙananan kaya ya saka ear phone a kunnen sa, sai takawa yake yi sakamakon waƙar da yake sha yana juyi, dayake waƙar soyayya ce shiyasa yake a cikin farin ciki ya nufe ta fuskar sa cike da walwala. Hannu ya kai ya taɓa mata kai yana kiran sunan ta, "my Baby I'm back." Sai ya saka hannu ya ɗaga kanta saboda ganin ta ƙi motsa wa. Zaro idanun sa yayi ganin yanda fuskar ta tayi jazur da cikin idanun ta sakamakon kukan da ta sha. "common Baby what's wrong with you?Why do you worry? I am your husband. Stop worrying about me you are already mine. No one is enough to separate you from me." Sai ya shafo fuskar ta yana sakin murmushi
Ita kuwa ta kasa yin motsi illa tsayawa da tayi tana kallon sa hawaye na ambaliya a fuskar ta, lokaci ɗaya kawai zuciyar ta ta bata mummunan shawara wanda take jin gwara ta kashe shi ta huta. Shiyasa lokaci ɗaya be yi zato ba domin har ya shige jikin ta ganin ko motsi ta ƙi yi yana ta faman shinshinan ta; sai ta zaro wuƙan ta tura shi da ƙarfinta ta luma mishi a ciki. Kafin kace me ta sake zaro wa ta sake luma masa
Tuni ya saki ƙara ya faɗa saman gadon yana ƙoƙarin riƙe hannun ta, sai dai yanda ta zare wuƙan ta sake luma mishi ne yasa shi sakin wani bahagon ihu me kama dana kenwa, lokaci ɗaya jini ya soma ambaliya a jikin sa har ta cikin bakinsa aman jini yake yi, yayinda numfashin sa ya ɗauke gaba ɗaya
Ruɗewan da MEEMA tayi ne yasa ta kasa guduwa, hannun ta na kan wuƙan daƙyar ta saki, sosai hankalin ta ya tashi wanda lokaci ɗaya tabi ƙofa da gudu har tana cin tuntuɓe, kuka ta saka sanda ta isa bakin ƙofan ta jijjiga taga a rufe yake. Tsaban ruɗe wa ta gaza inda zata je domin tunanin ta ya gushe ta manta inda zata samu mukullin, sai da ta gama wuri-wuri a wajen sannan ta koma ɗakin inda Sajjad yake a kwance a mace ta laluba aljihun wandon sa jikin ta na rawa kamar ace ket da gudu. Tana cin karo da keey ɗin ta ɗauka ta fita aguje, tunda ta buɗe ƙofan ta zura aguje bata tsaya ba. Cin gudu kawai take yi kamar sabuwar mahaukaciya domin kanta ko ɗankwali babu, daga ita sai doguwar riga ƴar kanti wanda da kaɗan ya wuce gwiwan ta. Gudu take yi sosai har ta fito cikin jama'a ta tasar wa titi, babu tsammani ta yanki titi sai ga ta a yashe wani me moto yayi ƙwallo da ita sakamakon hawa kan titin da tayi ba tare da ta duba ba
Nan da nan Mutane suka yo wajen ana zuba salati
Mutumin da ya bige ta shima tuni ya fito yana salati
Tsaban tsorata ne yasa ta sume gau, sai kuma ƙafan ta da a yanzu ɗin suka ga yana zubar da jini
Shiyasa nan da nan jama'ar wajen suka soma bata taimakon gaggawa, wasu har sun soma mata fifita, wasu na faɗin, "a kawo ruwa."
Mutumin da ya buge ta yace, "a taimaka a saka mishi ita a mota sai akai ta asibiti tunda akwai asibitin a kusa."
Nan kuwa ɗaya ya ɗaga ta aka saka ta a mota. Sannan ya shiga ya ja ya nufi asibitin da ita.
A asibitin an bata taimakon gaggawa kuma ta farfaɗo, sai dai babu abinda ya same ta illa buguwa da tayi a ƙafa sosai, wanda har targaɗe ta samu ga kuma ciwo, an mata treating wajen. Tunda ta farka ɗin take kuka
Shiyasa mutumin yayi ta rarrashin ta but ta ƙi shiru. Shiyasa ya ƙyale ta ya fita ya kira likita
Shima da yazo ya tambaye ta, "ko akwai abin da ke damun ta ne bayan ƙafar?"
But ta ƙi magana sai rera kuka take yi. Sai daƙyar suka samu tayi magana, ce musu tayi, "She will go home, they will take her home and she will not stay."
Duk yanda Likitan ya so ya rarrashe ta domin ta zauna ko zuwa anjima ne sai a sallame ta but ta ƙi
Dole mutumin yace, "a basu sallama." Sannan ya je ya biya Bill ɗin yace mata, "ta tashi su je."
Sai dai ta kasa tafiya dole aka kira wata Nurse ta taimaka ta riƙe ta zuwa wajen motan Mutumin
Shi ya tambaye ta address ɗin ta sannan ya wuce da ita kai tsaye gidan Hajiya.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Ƙarfe huɗu aka soma shirye-shiryen tafiya Dinner
A wannan karon ƙawayen amarya sun sha ankon jan atamfa ce wanda aka yi silƙi da fari da me ruwan toka, sai suka yi amfani da farin ɗan kwali. Yayinda Abokan Ango duk suka sha fararen shadda
A mota ɗaya aka ɗauki Ango da Amarya zuwa hall ɗin da za ayi taron. Tunda suka shiga babu me yin motsin kirki
Shi Umar Faruk ya kwantar da kansa a jikin kujeran ne while idanun sa a rufe ruf. Yana sanye da farar gezna uban-uban su me tsananin tsada. Riga da wando ne da malin-malin ɗin sa, sai yayi amfani da hula kalan aikin rigan, yayinda agogon hannun sa da takalman sa suka kasance farare su ma
Haka itama Luwaira ta saka farar gown ne me dogon hannu, rigan tayi matuƙar kama ta tare da fito mata da kyakykyawar surar jikin ta, sai aka yi mata amfani da golden ashobe aka yi mata ɗaurin Amare, fuskar nan nata ya sha makeup wanda ko ka santa ma baza ka iya gane ta ba tsaban yanda kwalliyan yayi mata ɗau a face, yayinda hannayen ta suka sha zanen lalle ja da baƙi suka ɗau white skin ɗin ta. Itama kanta na sunkuye ne ta ƙame waje ɗaya ko motsi ba tayi
Motan gaba ɗaya ta gume da ƙamshin turaren su wanda ya sake bayar da wani irin sassanyan ƙamshi me saka nutsuwa a zuciya
Koda motan ta faka a haraban hall ɗin abokan ango ne suka zo suka buɗe musu. Su suka haɗa su waje ɗaya tare da saka shi ya riƙe hannun ta
Sai dai shi ya ƙi sabida gani yake yi ai bata zama matar sa ba tukunna, shiyasa koda suka matsa mishi sai yayi gaba ya bar su a wajen. Dole suka bi bayan sa suka tsayar da shi suka jera da Luwairan zuwa hall ɗin da ya cika maƙil da Mutane, yayinda music me sanyin daɗi ke tashi na tarban su
Kasancewar harkan na manyan Mutane ne babu inda be ƙayatar ba a wajen, musamman yanda suke gudanar da abubuwan nasu a cikin tsari
Amarya da Ango sun zauna a mazaunin su inda aka fara gudanar da shagulgula cikin girma da arziƙi
Bazan iya misalta muku farin cikin da Luwaira take ji a wannan lokacin ba, bakin ta ya ƙi rufuwa don daɗi. Abun da take buri da fata kenan ya zamana bikin ta ya zama babban biki da ko ina sai an sani, ga shi ta cika burin ta, ta auri muradin ranta sannan kuma tana ɗaya daga cikin Matan da suke da Sa'a a duniya
Umar Farouk baza ka taɓa gane a halin da yake ciki ba, duk da ba ya farin ciki a zuciyar sa but ko kaɗan baza ka ga hakan a fuskar sa ba, musamman kasancewar sa me kwarjini da kamala a fuska, ko be yi fara'a ba baza a taɓa gane hakan ba, yanzun ma fuskar sa sai shainnig take yi tana fizgar ƴan matan wajen wanda gani suke yi ba kowa ne me dacen samun santalelen kyakykyawa kamar shi ba, haƙiƙa ƙawar su tayi Sa'a babba.
Taro ya soma yin nisa inda masu hotuna da bidiyo sai haska su suke yi
Daidai lokacin ne kuma wayan sa tayi ƙara. Ganin sunan Hashim shiyasaka ya ɗaga saboda dama ya san da tahowar sa a yau ɗin domin halartan bikin sa
Luwaira wacce ta ɗago kai ta zuba masa idanu tana kallon sa, sai dai ba ta jin abinda yake cewa kasancewar ya kare bakin sa tare da kawar da kansa gefe. Gani tayi kuma ya tashi zumbur kamar wanda aka tsikare shi ya sauka a wajen ya tasar wa ƙofa ya fice. Kasa ɗauke idanu tayi a kan ƙofan tana jiran ta ga dawowar sa, sai dai kuma har kusan mintuna goma suka wuce babu shi babu labarin shi, take a nan zuciyarta ta soma mata ƙunci wanda har ta soma tara ruwan hawaye a cikin idanun ta
Abida wacce ta kula da ita; ita ce ta taho wajen tana raɗa mata cewa, "ina Angon nata ya tafi ne? Ya kamata ace ya dawo."
"Nima ban sani ba Abida, ban san inda ya je ba be faɗa min ba."
"Ok bari in duba wajen, but ki ɗan saki fuskar ki sabida kinga yanda kika yi ne?" Daga nan ne ta fice domin duba shi, sai dai ko me kama dashi babu a wajen haraban, kuma babu motan da suka zo na Amarya da Ango
Dayake ita ya hau ya bar gidan ya wuce gidan Hajiya. Kasancewar kiran da Hashim ɗin yayi mishi ya masa albishir da dawowar MEEMA ce, wanda hakan yasa ya kasa jure wa ya fice domin zuwa ganin ta.
Abida koda ta dawo ta faɗa mata. "babu shi da alamun ya bar wajen ma."
Sosai Luwaira ta shiga damuwa. Kuka ne kawai bata saki a wajen ba tsaban baƙin ciki, wannan wulaƙanci da me yayi kama? Ana taron ta but Ango ya tafi ya bar ta babu ko sallama?
Abida ita ke ta kwantar mata da hankali
Su kansu Abokan sa da suka ga ba ya wajen sun ta neman sa a waya but switch off. Dama ya san za a neme sa shiyasa ya kashe wayan
Haka aka tashi a taron ba tare da Ango ba wanda hakan ya soma jawo zance daga wajen ƙawayen Amarya, har ma da Mutanen wajen
Yayinda Luwaira ta sake shiga tashin hankali matuƙa. Suna koma wa gida ɗaki ta shige ta faɗa kan gado ta dinga rera kuka sosai
Abida wacce ta biyo bayan ta; ita ta kulle ɗakin kar ma wani ya zo ya tarar da ita a hakan, sannan ta zo ta zauna a gefen gadon ta dinga rarrashin ta
Sai dai Luwaira ta kasa yin shiru, daga ƙarshe ɗago kai tayi tana kallon Abidan yayinda idanun ta suka Kaɗa suka yi jazur hawayen ciki sun kasa tsayawa tace, "don Allah wannan abun da me yayi kama Abida? Kenan kowa sai ya tabbatar ba ya so na? Da ya san zai min wannan wulaƙancin ai da tun farko ba'a yi ba hakan zai fi min, baki ji yanda nake ji ba a zuciya ta! ina ne ya fi masa da zai je ya bar taron bikin sa? sai yanzu na soma dana-sani da auren nan, ban san kuma wane baƙin ciki ne zan tarar a gaba ba?"
Abida numfashi ta ja tare da dafa ta tace, "Ni don Allah ban ga wani abun tayar da hankali haka ba duk da be kyauta miki ba, amma kiyi masa uzuri mana ba fa ya ƙi zuwa taron bane gaba ɗaya, Ni na tabbata bazai miki haka domin ya wulaƙanta ki ba, akwai abun da ya sha mishi kai ne wanda ya aikata hakan..."
"Wanne abu ne ya sha mishi kai da har zai kasa sanar min ya tafi ya bar Ni? A bainar jama'a fa Abida." Ta katse ta da faɗan hakan a cikin kuka
"Don Allah kiyi haƙuri mana tunda komi ya rigada ya faru, daga yau ne fa gobe kin zama tashi komi zai wuce, sai yanda kika yi dashi idan kika zama matar shi, ke ce zaki jawo hankalin sa gare ki, wannan dai ya rigada ya faru amma ki cire damuwa kar wani ya fahimci halin da kike ciki Please." Da haka Abidan tayi ta rarrashin ta har ta samu ta kwantar mata da hankali.
💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
💎💎💎
*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_36*
Bazan iya misalta muku farin ciki da murnar da su Hajiya suke ciki ba sakamakon dawowar MEEMA
Ita MEEMA kuka sosai ta fashe da shi da tayi arba da su, musamman da ta ganta a jikin Ummee wacce ta rungume ta itama tana zubar da hawaye. Sake ƙanƙame Ummeen tayi tana ta kuka me tsuma ran me sauraro, ko kaɗan ta kasa sakin ta sabida dama tana matukar kewar jikin ta, rabon da ta ji ta a jikinta ta manta shiyasa yau ta kasa sakin ta
Sai da Uncle Hashim ya zo sannan ne ta basu labarin abun da ya faru, ta kuma sanar musu da Sajjad ne ya ɗauke ta
Babu wanda be yi kuka ba sabida tausayin ta.
Da ƴan sanda da Mutumin da ya taimaki MEEMA suka wuce anguwan da ya ɗauko ta kasancewar ita bata san gari ba. Bayan ya kai su wajen ne itama kuma ta nuna hanyar da ta biyo domin ta kai su gidan, daƙyar aka samu ta iya tuna inda ta biyo tunda a lokacin a rikice take
Sun shiga gidan sun tarar da Sajjad kamar yanda ta bar shi, ya zubar da jini sosai domin sun yi tunanin ya mutu, sai dai koda aka kai shi asibiti an tabbatar yana da rai
Uncle Hashim shi ya saka aka je har Yola aka kamo Kawu Ali a daren, domin yace, "duk da halin da Sajjad yake ciki bazai yarda ba sai an hukunta shi." Kotu za'a kai shi kai tsaye
Shima Kawu Ali da ganin abun da ke faruwa da gudan ɗan shi hankalin sa a tashe ya dinga masifa, a cewar sa, "bazai yarda ba shima sai ya ɗau mataki."
Rikici fa sosai ya kaure a tsakanin su
A lokacin an wuce da MEEMA asibiti don jikin ta ya rikice sosai
A can asibitin Umar Faruk ya je ya tarar da su. Tunda ya ji labarin abun da ya same ta zuciyar sa tayi wani irin tuƙuƙi tare da tsantsan baƙin ciki da ya turnuƙe sa, bazan iya fasalta muku a halin da ya shiga ba domin yadda zuciyar sa take tafarfasa haka yake huci kamar wanda zai dambe, ya kasa jure a halin da yake ciki dole ya silale ya koma cikin mota ya haɗa kai da gwiwa, taya ma za'a ce mishi wani ne ya auri wacce yake ƙauna? Yanzu kenan akwai igiyar auren wani a kanta? Gaskiya bazai iya juran hakan ba, idanun sa gaba ɗaya sun kaɗa sun yi jazur kasancewar sa me rauni wanda ba ya iya jure tashin hankali ko ya ya ne
Ƙarshe Hashim ne ya bincika inda yake tunda ya neme shi ya rasa, a nan ya tarar da shi a cikin mota a matsanancin tashin hankali domin ciwon sa ne yake neman tashi, hankalin Hashim a tashe ya yunƙura da nufin kiran likita
Sai dai shi ya riƙe shi da cewa, "ba ya buƙata, ya san idan ya koma gida ya sha magani zai warke."
Dole ya haƙura sai dai shi ya tuƙa shi ya mayar da shi gida. Sai da ya zauna da shi a can har ya samu ya sha maganin sa barci ya ɗauke shi kafin ya baro gidan. Ya san saboda MEEMA ya shiga wannan halin shiyasa yake matuƙar tausaya mishi
Momy kuwa da taji labari tunda Hashim sai da ya kira ta, itama ta tashi hankalinta ta nuna damuwar ta tsantsa, sai dai a ranta tayi murna tunda ta san bazai taɓa tsallake auren Luwaira ba kasancewar gobe ne, ko ba komi dole ya ƙyale wancan, shiyasa bata wani damu da dawowar MEEMAN ba
Yayinda Abdul ya shiga murna shi kuwa. Ya rigada ya saka a ranshi duk sanda aka ganta zai je har gida ya sanar mata soyayyar shi ko zata amince, tunda ya san yanzu an yi mishi maganin matsalan shi Umar Faruk ya sami wata, yanzu hankalin sa kwance zai je ya same ta da zancen
Luwaira kuwa a ranan haka ta kwana da baƙin ciki, musamman da ta ji inda ya tafi, ashe dama sabida dawowar MEEMA ce ya bar wajen taron su? Tabbas akwai matsala sai yanzu take ganin haka. Haka suka kwana da Abida suna ta shirya abubuwan da zasu yi duk sanda Luwaira ta shiga gidan Umar Faruk, baza su taɓa bari ya aure ta ba duk hanyar da zasu bi sai sun bi wajen ganin sun raba su.
Washe gari aka ɗaura auren senator Umar Faruk Aliyu Bature da Amaryan sa Luwaira Shamsudden Aliyu Bature cikin sadaki mafi ƙaranci.
MEEMA wacce take gadon asibiti a wajen su Hajiya ta ji labarin bikin tunda har su ma sun leƙa a sa'ilin tana barci suka bar ta da Zabba'u. Sosai maganar ya daki zuciyar ta wadda har sai da ta ɗauke wuta na tsawon lokaci, ta kasa yarda ko shi Umar Faruk ɗin da ta sani ne shiyasa ta sake buɗe idanuwan ta waɗanda suke rufe har sun tara ruwan hawaye ta kalli Zabba'u tace, "You mean Uncle Umar Faruk who says he loves me?"
Zabba'u wacce take kallon ta; sai ta ji ta bata tausayi, hannun ta ta riƙe da cewa, "it's he MEEMA, I'm sorry don't say you will raise your mind kinga you are not feeling well."
Gyaɗa kanta tayi hawayen na sauka a kan fuskar ta, sai ta saka hannu da sauri ta share su, har ta kawar da kai kuma ta sake kallon ta da cewa, "But he says he loves me. Did he lie to me? Why would he do that to me?" Sai kuma tayi saurin kwanciya jin kuka ya taho mata, ƙudundune kanta tayi tana sakin kukan bayan ta toshe bakin ta yanda baza a ji ba
Zabba'u ta rigada ta gane a halin da take ciki, shiyasa tayi ta bata baki but ko kula ta ta ƙi yi
Ana haka sai ga Umar Faruk ɗin da Hashim sun shigo ɗakin
Dalilin da yasa Zabba'u ta tashi ta ba su wuri kenan, ta fice bayan sun gaisa
MEEMA wacce ta ji muryan su tuni ta shanye kukanta ta saka hannu ta share hawayen
Sai dai Hashim yana kallon idanun ta ya gane tayi kuka, shiyasa ya rikice da tambayar ta abinda ke damun ta?
Ta kasa yin magana bare ta ɗago ta kalle su
Yayinda Umar Faruk na tsaye a setting ta yana faman kallon ta kamar zai cinye ta, yana sanye da wani uban-uban su na farar shadda bugaggiya sai maiƙo take yi, kowa ya kalle sa ya san Ango ne saboda yanda yake wani walƙiya ga tashin ƙamshi da yake yi. Fuskar sa har ta zurma shima saboda damuwar da ke ransa
"Daughter please what's wrong with you? What happened to you? Tell me?" Uncle Hashim ya sake faɗa yana tallabo kanta ta yanda zasu haɗa idanu
Ita kuma saka idanun ta tayi a cikin nasa sai ga hawaye sun sake cika mata idanu. Sai kawai ta ɓare baki ta saka mishi kuka
Hakan yasa ya sake rikice wa ya hau rarrashin ta duk hankalin sa ya tashi
Ita kuwa ta ƙi shiru sai kuka take yi domin yanda take ji a zuciyar ta baza ta iya jure wa ba dole sai tayi kuka, ita kanta bata san me ke damun ta ba sai dai kukan ta na da alaƙa da jin zancen auren Umar Faruk, haka kawai take jin matuƙar baƙin ciki da haushi a ranta
Yayinda shi kuma lumshe idanun sa kawai yayi yana sauraron kukan nata, ya kasa cewa komi illa sake buɗe ido da yayi yana kallon ta, a duk sokon ɗaya ƙauna da begen ta na ƙara shigan sa. Jin son ta yake yi har a can cikin jini da ɓargon sa, ko son da ya yiwa matar sa Nusaiba be ji makamanciyar abin da yake ji a game da soyayyar MEEMA ba a halin yanzu, be san ya zai yi ba idan ya rasa ta.
Daƙyar Uncle Hashim ya rarrashe ta tayi shiru tana faman shashsheƙa
"Please daughter tell me what's wrong with you?"
Shiru tayi ta kasa yin magana
Dole ya ƙyale ta sannan ya kalli Umar Faruk yace, "ka zauna mana ka tsaya a tsaye. Ka ga Daughtern nawa iya rigima ce dole sai an ta fama da ita."
"Nan ya isa." Yafaɗa a maƙoshi sabida halin da yake ciki
Shi kuma kansa ya jinjina masa alamun ya gane. Sai ya kalli MEEMA yace, "Daughter did not congratulate my dude. Today he is married." Ya ƙare maganar da murmushi a face ɗin sa
Wani irin ƙunci ne ya sake tabaibaye ta wanda lokaci ɗaya ta ji wani kukan zai taho mata, sai tayi saurin sauke kanta ƙasa tana tsiyayar da hawaye, sosai tayi juriya wajen ta hana bayyanuwar kukan nata but ina ta kasa, kawai kifa kanta tayi a kan cinyanta ta dinga rera kukan har wani jijjiga take yi
Mamaki ne ya cika su, sai dai shi Uncle Hashim sosai ya gane tabbas zancen auren ne ya saka ta kukan nan, dama ya gane tana son shi domin ya ga soyayyar abokin sa a idanun ta, sai dai be yi tunanin har haka ba, sai wani irin tausayin ta ya kama shi, yanzu ya za suyi tunda an rigada an yi auren shi? Dole ya koma rarrashin ta
Yayinda Umar Faruk tuni ya fice a ɗakin sabida bazai iya sauraron kukan ta ba, hakan na ɗaga masa hankali tare da ƙara masa raɗaɗi a zuciya.
Koda Zabba'u ta shigo ta gansu a haka itama nan ta zauna tana sanar da Uncle Hashim ɗin, "da alamu saboda Umar Faruk ne take kuka. Ya kamata ka san yanda zaka yi ka saka yarinyar ka a cikin farin ciki, tana son abokin ka be kamata a bar su haka basu mallaki juna ba, zancen wancan Sajjad ɗin a saka shi ya sake ta don baza a barta da auren shi ba."
"Ki dena ma zancen wancan banzan don Allah, maganar auren su ma babu shi don ba na son ana sake maganar." Cewar sa cikin zafi
Dole Zabba'u tayi gum da bakin ta ganin ya nuna fushi nan da nan tunda dama a ɗane yake. Dayake likita yayi musu bayanin halin da take ciki. Yanda yayi mata amfani da drugs waɗanda suke gusar mata da hankali, har abortion ɗin da aka yi mata wanda ya ja mata matsala a halin yanzu, ko yaushe zubar da jini take yi, ga ciwon ciki da ya saka mata shiyasa aka riƙe ta a asibitin a halin yanzu
Daga ƙarshe tashi yayi ma ya fice ba tare da ya sake cewa uffan ba
Zabba'u tace, "an shiga uku! Mutum sai zuciyar tsiya, wannan da ace yaron nan ba ya a halin da yake ciki ai ina tunanin kashe shi zai yi, don ɗaukar shi zuwa barikin su zai yi ya gana masa azaba, sojoji ko mugaye! Allah ya cece shi shima".
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
*TO FA... BABBAN MAGANA... NESA TA ZO KUSA KENAN....*
*Albishirin ku masoyana masoyan littattafai na.... Nesa ta zo kusa... Ƙasaitacce kuma fitaccen littafi na da zai fito muku a sabuwar shekara, salon na daban ne domin Ni kaina ban taɓa yin littafin da ya ɗaukar min hankali kamar wannan ba, iya basirata da ƙwarewata duk na bazar dashi a cikin wannan littafin. _ƊAN SANDA 👮🏻_ kai daga jin sunan ma kun san akwai badaƙala a cikin sa, ƴar uwa ko ɗan uwa kar ka bari kar ki soma a baki labari ki nemi naki kawai ki ga cakwakiyar da ke ciki, ke da kanki zaki san tabbas littafin yayi, tabbas ya ci kuɗin sa domin sai Abu me kyau ake iya cire kuɗi a siya... A kan farashi me sauƙi ɗari biyun ki zai biya miki buƙata domin samun farin ciki a zukata... Tirƙashi _ƊAN SANDA_ labarin wani murɗaɗɗen saurayi ne da ke cike da burin ɗaukar fansa, ya hana kansa sukuni sai ya zaƙulo waɗanda suka kashe mishi Mahaifi, inda kuma gefe ɗaya yana tare da maƙiyan sa ba tare da ya sani ba, Matarsa ita ce ke da burin ganin bayansa, itama zuciyarta cike take da burin ɗaukar fansa, ta sha alwashi sai ta ga bayansa zata haƙura, dalilin da yasa ta shiga aikin ƴan Sanda kenan... Shin mene ne yayi mata da zafi haka?... Tirƙashi ƙa-ƙa ƙa-ƙa ƙa-ƙa muje zuwa FAN'S kar ku soma a baku labari ku nemi naku.. littafin zai zo a watan January a kan farashi me sauƙi 200 kacal. 👌 Domin ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan Numban only WhatsApp 07065334256 ko kuma 08146470539*
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Zuwa dare aka kai Amarya Luwaira Part ɗin Angon ta Umar Faruk. Ɗakunan ƙasa aka ajiye ta tunda nan ya zaɓa mata aka saka mata kayan ta
An kai Amarya an watse har ƙawayen Amarya sun tafi babu Ango babu labarin shi. Abida ce kaɗai zaune da ita
Luwaira kuka take ta mata domin ta kasa jure wa
Dole Abidan tayi ta bata baki tana faɗa mata, "daga yau shikenan, ta kwantar da hankalin ta, idan ma be sanja ba zasu ɓullo masa ta hanyar da dole zai sanja, ko ta halin ƙaƙa sai sun juyar da hankalin sa zuwa gare ta." Haka Abida ta zauna tayi ta ziga ta tana bata shawarwarin da ita taga ya kamata. Ƙarshe itama tafiya tayi ta bar ta tunda be zo ba kuma dare nayi
Su Hafsah suka zauna da ita, daga ƙarshe su ma suka wuce ɗakin su saboda barci suke ji, kasancewar Hafsah ta fi wayau sosai ita ta ciro musu kayan barcin su suka saka suka kwanta, dama wata rana ita take saka musu kayan idan Dadyn su ba ya kusa suna jin barci.
Luwaira ta kasa kwanciya saboda hankalin ta ya gaza kwanciya, a yanda take ji tamkar ta mutu tsaban baƙin ciki, wai yau ranan farin cikin ta, ranan da ta ci burin zuwan ta shi ne ta zame mata a haka? Taya zata iya jurewa? Dole tayi kuka, kuka ba kaɗan ba. A haka ta kwanta a gadon ko kayan jikin ta ta kasa sauyawa sai barza kuka take yi, tun tana yi da karfi ta koma yi a hankali.
Shi kuwa Umar Faruk sai ƙarfe 11:00pm. Ya shigo gidan, ko irin ledan nan na tarban Amare be shigo da shi ba, shi da farko ma yayi tunanin ta daɗe da barci, tunda da ya shigo ɗakin su Hafsah ya shiga yayi musu addu'a kafin ya fito zai zarce ɗakin sa. A nan ne ya tuna da ita ya tura ƙofan ta ya shiga, ganin haske tarwai sai ya tsaya kallon ta, a lokacin ne ya ji shashsheƙan kuka na tashi wanda ya tabbatar ita ce ke yi, hakan yasa ya nufe ta jiki a sanyaye tare da jin tsantsan tausayin ta na shigan sa. Kiran sunan ta yayi bayan da ya tsaya a bakin gadon
Hakan yasa ita kuma ta ɗago da kanta hawaye sharkaf a fuskar ta, har yanzu ta kasa yin shiru kuwa sai ma wani kukan ne ta sake taho mata
Ya kasa ce mata komi domin be san ta ina zai fara ba, sai mulmula hannayen sa yake yi daga ƙarshe kuma ya daure ya soma bata haƙuri da cewa, "kiyi haƙuri Luwaira na san ban kyauta miki ba, but ban yi hakan domin in ɓata miki ba, don Allah kiyi min uzuri ki yafe min kinji?"
Shiru tayi sai dai ta kasa ɗago kai ta kalle shi bare tayi magana, har a cikin zuciyarta ta ji sanyi sai dai ƙuncin da ke ciki ya gaza tafiya, zuciyar ta na mata ƙuna idan ta tuna Mijin da take Aure ba ta ita yake yi ba, ta wata banza can yake yi, wanda har a ranan auren su ya fifita ta a kanta, wannan abun baƙin cikin da me yayi kama?
Shi kuma jin tayi shiru sai ya samu waje ya zauna a gefen gadon, ya ɗau fiye da three seconds be iya furta komi ba. Daƙyar ya iya saka hannu ya janyo ta jikin sa wanda sai da yayi dauriya da jarumta wajen aikata hakan, hannun sa ɗaya kawai ya ɗaura a kanta ya soma rarrashin ta ba tare da ya furta komi ba
Sai dai ita tuni tayi tsit ko motsin ta ba a ji, ta gama sandare wa da shiga wani hali da jin ta a jikin wanda ta fi ƙauna fiye da rayuwar ta, yau ce rana ta farko da hakan ta taɓa faruwa da ita a game da shi, yau ita ce wai a jikin Umar Faruk yana faman rarrashin ta. Wayyo Allah daɗi! Bazan iya misalta muku a yanayin da ta shiga ba
Shi kansa ya gane hakan da yake mata ya saka ta shiga wani hali. Shiyasa ya janye jikin sa tare da ɗaga kanta da ta sake luƙume shi a jikin sa, cikin sanyin murya yake kallon ta da faɗin, "ki kwanta ki huta sai Allah ya kai mu gobe kinji?" Be jira kuma amsar ta ba ya tashi da sauri yayi ficewar sa
Tsaban baƙin ciki ya turnuƙe ta sai ta fasa kuka tana komawa ta kwanta. Kuka take yi sosai tare da sake shiga baƙin ciki. Ranar da ta ci burin zuwanta ta kasance da masoyin ta wai shi ne zai tafi ya barta a haka? Babu yanda ta iya; a haka sai dai barci ɓarawo ya sure ta cike da baƙin ciki da damuwa a ranta.
Washe gari da sassafe Umar Faruk yayi shirin sa ya bar gidan ko bi ta kanta be yi ba, yaran sa kawai ya duba, burin sa kawai ya isa asibiti wajen MEEMA ya ga lafiyan ta daga can sai ya wuce Office, domin shi ko ɗaukan hutun nan ya ƙi yayi tunda be ga amfanin zaman shi a gida ba, ba wannan ne karon farkon sa na aure ba.
Luwaira sai ƙarfe takwas ta tashi barci. Shima ɗin su Hafsa ne suka tashe ta da ƙiriniyar su, kasancewar suna murnan kawo musu Luwaira a matsayin Aunty da suke yi. A wajen su ta ji labarin Dadyn nasu ya fita, tunda a lokacin har tayi wanka ta cancare a cikin wata farar atamfa me silƙin ja da ruwan goro, ɗinkin riga da skert sun matse ta gam sun yi mata daram tamkar zata fashe tsaban yanda suka yi mata, kasancewar ta me jiki Masha Allah. Yayinda Fuskar nan nata ta ɗauki make-up kamar wacce zata je gasar kyau. Sai dai tunda taji ya fita sai ta koma ta zauna kamar ta fashe tsaban haushi. Tsawa ta daka wa su Hafsan a kan, "su bar mata ɗaki ko ta ci uban su."
Sun rikice yaran kasancewar ba haka suka saba gani ba, in fact ma babu wanda yake musu tsawa bare hantara yau sai ga shi sun samu a wajen Luwaira, shiyasa suka fice da gudu Yusra har da kukan ta suka wuce Parlour suka zauna. Ko abinci sun kasa ci dama suna jira ne Luwaira ta zo ta basu tunda Talatu ta kawo ta jera, amma yanda ta nuna musu ne yasa suka koma suka zauna zugum suka yi shiru.
Ita kuwa tana ɗaki tana waya da Abida yayinda take sanar mata da komi abinda ya faru, wulaƙancin da Umar Faruk yayi mata na ƙin kwana da ita, ko irin tarban nan na Amare be yi mata ba
Abida tace, "gaskiya dole mu tashi tsaye Ƙawata don zancen zama be taso ba. Wlh sai kin yi da gaske wajen samun zuciyar mijin ki tunda har yana wajen wata, wai to kin san yarinyar da yake so ɗin ne ya kamata fa idan zamu tashi tsaye dole sai mun san ita kuma da me ta fi ki da har yake rawan ƙafa a kan ta?"
Da damuwa Luwaira tace, "nima ban santa ba gaskiya, sai dai na ji Momy tana faɗin ƴar Abokin sa ne."
"Kina nufin ƴar abokin sa zai aura? Wato yarinya ce kenan?"
"No yarinyar Auntyn Abokin sa ne, sai dai kuma ba a nan tayi rayuwar ta ba daga Abroad Wai ta zo."
"Cab ɗi... Ai ko dole ya rikice a kanta don ko ban ganta ba na san zata fi ki gaskiya, kin san nan da can ba ɗaya ba wayewan ku zai bambanta, wa ya sani ma ta ba shi ya sha? Well. Yanzu ki bari zan zo sai mu zauna mu sake tattaunawa, idan ma ya kama mu sanar da Momy komi domin ta taimaka mana sai muyi..."
Da sauri Luwairan tace, "a'a ba na son a saka Momy a zancen nan gaskiya domin har yanzu ba wai yarda da ita nayi ba..."
"Kamar ya? Ban gane ba?" Abida ta katse ta da faɗar haka
"Idan kika zo zamu yi maganar please. Sai kin zo ɗin". Daga nan suka yi sallama ta ajiye wayan tana kwanciya tare da tsira wa waje ɗaya idanu ta hau tunani.
💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
💎💎💎
0 comments:
Post a Comment